UKU BALA’I CHAPTER 4

UKU BALA’I CHAPTER 4

                     Www.bankinhausanovels.com.ng 

Juyi kawai yake yi kan kafcecen gadon sa yana faman kai komo da zuciyarsa da ta hana idanuwansa barci ko na yan mintina ne yayi iya yin sa amma abun ya ci tura sosai yake ganin komai na dawo masa kamar yanzu fuskarsa yake hangowa tana yi masa shawagi a cikin idanuwansa in ya rintse guntun murmushin da ta sakar masa a waccan lokacin yake hangowa na yi masa barazana sosai yayi nisa cikin tarkon ta da yake tsammanin ta ɗana masa ba wai aiki kawai ta zo nema kamfanin sa na AFC ba har da da faraunatar zuciyarsa wacce cikin dakiku ta zabare masa ita ta tafi da ita bai sai hakan ya afku ba sai cikin wannan sulusun daren wanda ya dace ace yana kwance yana barci domin baiwa zuciya da gangar jiki hutu amma ina! hakan ya gagara.

A hankali ya kai hannunsa wajan makunnin wutar dakin ya kunna haske ya gauraye dakin agogonsa kirar Rolex da ke ajje saman yar karamar dirowa dake girki gefen gadonsa ya dauko ya duba karfe 3:15am. ya nuna masa sosai ya ware idanunsa yana jin yarda kirjinsa ya buga kadan maidawa yayi ya ajje sannan ya juya gefen hannunsa na hagu kafun ya dan tashi kadan ya jingina da fuskar gadon sosai hannu bibbiyu ya tallaɓe haɓarsa abun duniya yake ji duk ya addabar masa rayuwa ya surkutar dashi cikin yan awanni da ba su haura goma sha tara bs komai ganinsa yake yi kamar wanda akayi shekara goma sha tara kafun ya tabbata sosai yake jin wani iri a duk wani sassa na jikinsa da zuciyarsa sosai yake hangowa kansa tashin hankali in har abin da zuciyarsa ke sanar dashi bai tabbata ba sosai yake ganin komai zai iya faru in har Areefa Saif ba ta bashi dama ba.

Zuciyarsa yaji ta fara yo masa kuwwa da zancen amincewa daga bangaren Areefa tana mai sanar dashi in dai da kudi komai zai kasance kamar yarda ya fuskanci ita kanta Areefa din zata so jindadi da hutu kamar yarda hakan ya nuna ba tare da yaji daga gareta ba. Ba ya zaton zai samu matsala in dai ta bangaren kudi ne  tabbas za suyi masa abin da yake so kuma a lokacin da yake so ko tattama ba zai yi ba yana da kudi yana da kadara wacce zai iye sayr zuciyar Areefa da komai nata da ta mallaka ya zama dole ta yarda dashi ya zama dole ma ta amshi bukatarshi hannu bibbiyu ba tare da tsaya yawo da hankalin sa ba.

Gyaɗa kai ya shiga yi yana hada hannayensa waje daya yana lakwasasu suna ba da wani sauti mai amsawa sosai yake sakin murmushi mai karfi a fuskarsa sosai yake jin wani farinciki na samun gurbi a filin zuciyarsa sosai yake hango amincewar abin da yake bukata daga Areefa sosai yake ganin yarda ta amshi bukatarsa cikin lokaci kalilan ba tare da ya samu wata tangarɗa ba gareta.

A hankali ya koma ya kwanta yana kai hannunsa wajan makunnin wutar yana kashewa rufe idanunwansa yayi har lokacin fuskarsa bata rabu da murmushin da yake yi ba sosai yake hango Areefa a wannan lokacin tana yi masa shawagi a duniyar idanuwansa da suke rufe sosai yake hango wani tattausar murmushi na samun gurbin zama a fuskarta tana jefa masa wani kallo wanda yake kara rugurguza duk wani sashi na filin zuciyarsa yana jin yarda wani abu mai girman gaske yana wanzar da mazauni a filin zuciyarsa ta shi, sosai yake ganin rashin samun Areefa tamkar rasa rayuwarsa sane da duk wani buri da kudiri nasa da ya kafa akanta gani yake yi in har ya rasa abin da yake bukata a gareta tamkar yayi wa rayuwarsa babban gibi ne wanda ba ya tsammanin yana da abin da zai cike masa wannan gibin.

Cikin wannan yanayi barci barawo ya zo yayi awon gaba dashi ya jefashi wata duniya mai dauke da Areefa a cikinta…

****

A hankali ya shiga rage sautin wakar ‘Don’t Judge Me’ ta Chris Brown dake tashi cikin sifukun motar wayarsa dake hannunsa ya shiga latsawa a yan sakanni ya kai ta zuwa kunnansa yana faman jan numfashi kamar wanda yayi gudun tsira sosai fuskarsa ke bayyanar da halin da yake ciki na damuwa sosai kunci ke wanzuwa a fuskarsa da kwayar idanuwansa.

Laɓɓansa yake turawa cikin bakinsa ya na cizawa kamar ba a jikinsa suke ba sosai yake jin wani irin yanayi da zuciyarsa take haifar masa a duk sakan daya na jan numfashinsa.

A hankali ya sauke wayar fuskar na kara ya mutsayewa cikin yanayi na damuwa da rashin abin yi sosai yake jin komai na kwance masa sosai yake jin lissafin kwanyarsa na wargajewa cikin yan dakiku bai san abin da ya dace yayi ba, bai san me nene ya kamata ace yayi ba a daidai wannan lokacin ba yana bukatar mataimaki yana bukatar wanda zai tayashi zaman jajen zuciyarsa daga halin kuncin da take ciki…

Kamar wanda aka zungura da sauri ya sake dauko wayar da ya ajje gefe cikin yan dakiku ya kai ta kunnansa bayan ya binciko lambar da zai kira.

A hankali yake jan numfashi yana motsa laɓɓansa zuciyarsa yake jin tana wani irin mataki da ya tabbata gaf take da kamuwa da cuta mai girma gareshi dama gabadaya gangar jikinsa.

“Khairiyya…”.

Ya fadi cikin wani irin sauti mai rauni sosai a hankali ya sanya hannunsa daya yana dafe kansa da yake jin yana kokari wargajewa.

Yana jin yarda numfashinta ke sama da kasa daga bangarenta sosai yake so ya fahimci wani abu cikin yanayin da take ciki zuciyarsa ta cilla shi wata duniyar tunani ya shiga nazarin yanayin da yaji Khairiyya sosai zuciyarsa take sanar dashi wani abu na daban da bai yi tsammani ba.

Girgiza kai yayi cikin yanayi na kin yarda da zancen zucin nasa kafun ya nisa cikin yanayi na damuwar zucci.

“Ban san mai nayi miki ba kika gujeni tsayin kwanaki Khairiyya, tun da nake dake daidai da kwana daya ba mu taba kin sa junanmu a idanuwanmu ba, amma cikin wannan lokacin gabadaya na lura sauyawa kike yi me yasa?”.

Ya ida muryarshi da sanyi a cikinta sosai yayi shiru yana jiran tsammani daga bangaren ta amma shiru kusan mintina biyu a hankali ya sauke wayar yana duba screen amma ba alamun yankewar wayar har yanzu akan kira take.

“Uhmm…”.

Ya kokarta nisawa domin tunatar da ita yana kan layi in mantawa tayi take wata sabgar ta daban.

Jan numfashi yaji tayi mai karfi kafun ta fara magana da wata murya wanda da ka jita zaka gane akwai abin da ke damun mai muryar.

“Huzaif…”.

Ta fadi da sauti kafun ta sake jan numfashi ta dora.

“Bakomai kawai dai…kawai gani nayi kana bukatar a baka fili a duniyar rayuwarka domin daidaita halin da kake ciki na damuwa…”.

Da sauri ya tare ta.

“Haba mana Khairiyya wacce irin magana ce kike yi haka wanda sam bata dace ace ta fito daga gareki ba”.

Ya karashe yana mai jan numfashi sosai ya hasaso wani abu mai kama da bacin rai a cikin kalamanta sosai ya fahimci akwai abin da ke dawainiya da ita a zuciyarta.

“Yi Hakuri…”.

“Huzaif!”.

Ta fadi da sautin murya mai nuna da bata so abin da yace ba.

“me kayi mani kake bani hakuri, wanda ni ban sani ba?”.

“Ban ce nayi miki wani abu ba amma kuma muryarki ta fallasa asirin zuciyarki da halin da kike ciki”.

Yana jin yarda ta saki numfashi mai karfi kafun yaji maganarta ta doki dodon kunnuwansa.

“bana gari nayi tafiya kuma gaskiya ban san ran dawowa nan kurkusa ba…”.

Bai bari ta ida batun nata ba ya tare da sauri.

“What! me kike nufi Khairiyya kin yi tafiya ba tare da na sani ba mai haka ke nufi shin kin manta halin da nake ciki kuma kin san ina bukatar taimako daga gareki amma ki kayi min haka Well..shikenan..shikenan”.

Ya karashe cikin wani irin yanayi mai sanya daci akan harshe da zuciya

Ita kan ta haushin nr cinkoshe a zuciyarta take faman kokawa dashi kar ya kufce ya yo waje domin ta tabbata komai zata iya gayawa Huzaif akan bacin rai da cin kashin da yayi mata. Sosai take jin bacin rai da takaici wanda ta hakikance haka a matsayin raini tsagwaron sa da rashin sanin darajar ta.

Alkawari tayi sai ta bashi mamaki sai ta nuna masa asalin wacece ita sai ta ganar dashi ‘YA MACE irin ta ba kowa yake dauka ya wulakanta ba sai ta nuna masa suma ‘YA’YA MATA akwai daraja garesu ba wai ledar pure water bace duk in da ka gilma zaka tsince ta kuma ka zabi wanda tayi maka.

“Sai Anjima!”.

Ta fadi a zafafe gami da kashe wayar bakidaya.

Sakato yayi da baki bayan ya sauke wayar ya kafe Screen din da kallo wani abu yaji yanayi masa yawo akai ji yake yi duniyar na juyawa dashi a hankali komai na kwancewa akansa runtse idanu yayi mamaki ne da tu’aji yake kunno wa daga zuciyarsa sosai  yake ganin kamar a mafarki wai Khairiyya ce tayi masa haka ita ce take fada masa magana cikin bacin rai abin da tun da suke da ita bata taba yi masa ba sosai take nuna kulawa da tattali gare shi amma a yanzu lokaci guda komai ya wargaje.

Gyaɗa kai ya shiga yi yana hango rashin sa’a rayuwarsa wanda ƙaddara ta kinkimo ta kawo masa lokaci guda kuma take kokarin tarwatsa komai na ginin rayuwarsa da yayi a baya mai cike da kayan kwanciyar hankali da jindadi.

Sosai ya jima cikin shiru hannayensa rungume da kansa zuciyarsa sai faman harbawa take yi da wani irin yanayi wanda ke kara hargitsa masa tunanin kwanyarsa sosai ya fuskanci rayuwarsa gaf take da tarwartsewa koma yace ya tarwatse domin kuwa shi dai bai ga amfanin haduwa da wannan yarinyar ba wacce ta dagula masa lissafi da komai nashi kuma take kokarin zautar dashi bai san abin da ya dace yayi mata ba bai san mai ya kamata ace yayi akan ta ba domin daidaituwar komai nasa sosai yake kasa aiwatar da niyyarsa gami da kudirinsa akan ta bai san mai yasa hakan na tunaninsa ya zama abokin sa a kowani lokaci dare rana dama cikin barcinsa ba wanda hakan ba karamin tashin hankali yake shigar dashi ba sosai ya fuskanci yarinyar ta samu gurbi a filin zuciyarsa tayi kane-kane ta hana zuciyarsa sak! da ruhinsa sosai take haifarsa masa da wani ciwo mai girman gaske a duk wani sashi na zuciyar tashi har da kasan ruhinsa.

Numfashi yaja mai karfi kafin ya kai hannunsa saitin kirjinsa inda yake tsammanin nan ne zuciyarsa take girke wani irin bugu takeyi a hankali a hankali wanda hakan ya tabbatar masa ta kamu da ciwo mai tsanani har yake kokarin sumar da ita.

Girgiza kai ya shiga yi yana jin yarda idanuwansa suke kokarin tara wani abu cikinsu wanda ko shakka ba yayi hawaye ne wanda shi kan sa bai san ya akayi har hakan take kokarin faruwa da shi ba da sauri ya sauke hannunsa yayi wa motarsa Key gami da kure karar sautin sifukun cikin motar yayi hakan ne ko zai samu sa’ida da saukin tunanin zuciyarsa sosai ya fizgi motar kamar zai tashi sama.

*****

A hankali yake tafiya yana jin yarda kafafuwansa ke wata irin karkawa kamar za su fice daga jikinsa sosai ya ke jin tashin hankalin da zuciyarsa take hakilo akai kamar zai tarwatsa masa kirji sosai yake jin lissafin tunaninsa na kwanya na kara wargajewa.

Bai san mai zai yi ba bai san abin da zuciyarsa take kokarin tunkuɗa shi yayi ba sosai ya barwa zuciyarsa gangar jikinsa take sarrafawa.

“Yaa Allah!”.

Abin da ya fadi kenan a wahale kafun ya buɗe idanuwansa da yake jin su tamkar wanda aka daura musu wani abu mai girma sosai sun  kaɗa suyi jajir.

Mutum ya gani tsaye yana kallonsa sosai fuskrsa na bayyanar da wani irin yanayi wanda shi ya kasa fahimta shima kallonsa yake yi da duk ganinsa sosai yake jin zuciyarsa tana sanar dashi ya san shi ya taba ganinsa ko ba ma a zahirance ba zai iya kasancewa a cikin mafarki sosai ya cigaba da ware idanuwansa akan sa yana karaton a inda ya san shi lokaci guda zuciyarsa ta canko masa.

Tabbas ya san shi sun taba haduwa kuma ko shakka ba yayi cikin asibitin nan ne suka hadu kwanakin baya can gyaɗa kai yayi kafun ya dan kauce gefe har lokacin idanuwan Dr.Aqeel na kansa sosai yake kallonsa yana karantar yanayin da yake yana kallonsa a ciki sosai ya fuskaci ba cikin hayyacinsa yake ba akwai abinda yake dawainiya dashi wanda ya kasance ba mai sauki ba ne.

Daga kafada yayi kafun ya gyaɗa kai alamun ko a jikinsa a hankali ya fara taku kan kafafuwansa yana jin wani abu na samun gurbi azuciyarsa akan Huzaif sosai yake jin abu sosai yake jin gabansa na bugawa a hankali ya tsaya da tafiyar da yake yi ya waigo ya sauke kallonsa kan Huzaif har yanzu yana yarda ya bar shi sai hannu da yaga ya saka cikin sumar kansa yana cakuɗawa.

Sosai Dr.Aqeel ke jin Huzaif bai kwanta masa azuciya ba sosai yake jin wani abu daban game dashi sosai yake jin abu mai girma na samun masauki game dashi tsaki ya dan ja kadan yana mai tsuke fuska, hada idanu sukayi tsakaninsu wani irin kallone ya sarke a idanuwansu kallo na rashin fahimta kallo ne na ba kayi  mani ba.

Da sauri Dr.Aqeel ya janye idanuwansa a dan haryarce yayi hanyar Get din domin fita yana TUFKA DA WARWARA game da Huzaif sosai yake jin hankalinsa bai kwanta dashi ba…

“Yah Dr.Aqeel”.

Kamar daga sama yaji muryarta na fadin haka ko bai ma dauki muryar ba mace daya ce ya sani ta na ambatar sa da wannan sunan a hankali ya lumshe idanunwa yana buɗe su kanta yana ware idanuwansa sosai lokaci guda ya jefa tunanin da yake yi a kwandon shara ya sanyawa fuskarsa murmushi mai karfi hannayensa ya sarke a kirjinsa yana jiran karasowarta fuskarta ita ma da murmushi numfashi taja lokacin da ta iso gareshi.

“Daga ina kike Mariya?”.

Ya fadi yana mai tsare ta da idanu da alamun tuhuma.

Gyaɗa kai tayi kafun ta numfasa tayi kasa da kai.

“Umma ce take bukatar wannan”.

Ta fadi tana mai nuna masa bakar ledar dake hannunta dauke da kankana da ayaba.

Ware idanu yayi kafun ya gyada kai

“Naje dakin ai bakya nan ita kuma ta zaga bandaki ganin ki da banyi a dakin ba shi yasa ma na fito waje”.

Ware idanu tayi tana murmushi.

“Sai kace wacce za a sace shine ka biyo sahu”.

“Uhmm Mariya kin ga wuce muje ciki nan ai a hanya muke ko”.

Ya fadi yana mai kafeta da ido ba ta ce da shi komai ba suka fara takawa yana gaba tana biye dashi a baya sosai take kallon yarda yake tafiya cikin kwanciyar hankali da natsuwa lokaci guda ta dubi kanta sai taji wani iri a zuciyarta yanayin shi da ita sun bambanta sosai.

Sosai hankalin ta yayi nisa wajan kallon Dr.Aqeel tana tunanin yarda har ya amince ya shigo  rayuwarta a yarda take wanda take ganin rashin dacewar haka kamar akwai nakasu a tarayyar sosai…

Ba ta kai ga gama lissafin tunanin ta ba kamar ance ta daga kanta wa zata gani da sauri taja da baya tana Ambaton Allah idanuwanta a warwaje wani irin bugu taji kirjinta yayi har sai da ta kai hannunta ta dafe rintse ido take yi gani take kamar a mafarki ba gaske ba sosai tsoro da wani irin yanayi yake bayyana a jikinta sosai take jin wani abu mai girma na saukar mata a zuciyarsa sosai taji zuciyarta ta ta shiga tsalle cikin wani irin yanayi wanda ta rasa a mizanin da za ta ajje shi ba abin da ke mata yawo aka sai sautin marin da tayi masa a can baya gani take kamar yanzu komai ya afku sosai taji ranta na baci da wani irin abu mai girma a hankali ta buɗe idanuwanta tana sauke su akansa sosai ta hango yarda idanuwansa suka kaɗa sukayi jajir sosai take hango wani abu mai kama da tashin hankali cikin idanuwansa gabadaya take ganin yanayinsa a firgice yake sosai take hango yarda ya sauya ba kamar da ba yarda ta ganni sosai ta hango rauni mai girma a tattare dashi ba tare da jarumatar da ta san shi da ita ba

“Yaa Allah!”.

Ta furta cikin karfin hali domin ji take komai yana wargaje mata na tunaninta sosai take jin wani abu na yawata mata cikin gangar jikinta gami da zuciya da ruhi wanda ta kasa gane menene haka din.

A hankali ta fara kokarin taks kafafuwanta da take jin sun sunyi mata nauyi sosai ji take kamar dutsen dala aka daura mata numfashi take ja yana kufce mata sosai tayi kokarin jan kafarta har ta iso in yake jingine jikin motarsa tana kokarin gifta shi kamar sautin muryarshi taji ya ambaci sunanta da sauri ta waiga ta sauke masa idanuwanta shima ita yake kallo da wani yanayi wanda ta kasa fassara ko na mene ne abu mai nauyi da girma ta ke hangowa cikin idanuwansa wanda hakan ba karamin narkar mata da jiki yake yi ba gabadaya taji tunanin kwanyarta na wargajewa.

Muryar Dr.Aqeel ta jiyo kamar daga sama hakan ya farfado da ita daga sumar da take tsammanin tayi sosai ta dago kanta ta dube in da yake dan nesa da ita tsaye hannayensa cikin aljihun wandonsa wani kallo taga yana yawatawa dashi a kanta wanda hakan ya kara firgitata sosai da sauri tayi kasa da kai kafun  ta dago ta dubi Huzaif wanda ya gama zama kalar tausayi wani kallo ta watsa masa wanda ita kanta ba ta san ya akayi tayi masa shi ba.

A hankali ta fara takawa kafafuwanta na rawa sosai abu mai girma take jin ya danne mata zuciya yana kara luguiguita mata da gangar jiki da ruhi kanta a kasa ta isa wajan Dr.Aqeel wanda take jin kallon da yake watsa mata kamar ana watsa mata garwashi wuta.

“Waye waccan?”.

Taji muryarsa ta ambata da wani irin yanayi wanda ta tabbata bacin rai ne a cikinta sosai da sosai ba ta san mai zata ce masa ba bata san wata irin amsa ya dace ta ba shi ba sosai ta fuskanci yana cikin yanayin bacin rai wanda ta rasa mai yasa hakan ya bayyana shin ko dai ya san Huzaif ne ko dai ya san wanene shi.

Tambayoyin da su dinga mata shawagi kenan cikin kwanya suna kara haifar mata da tashin hankali mai girman gaske.

“Dake fa nake Mariya kika yi shiru wanene waccan kin san shi ne?”.

Sosai taji muryarsa ta kara buɗewa da sautin fushi a cikinta wani kaɗawa taji cikinta yayi ba ta taba zaton akwai ranar da za taji muryarsa haka ba bata taba zaton akwai ranar da zata ji magana irin haka mai dauke da daci a cikin ta ba girgiza kai ta shiga yi a hankali kafun ta kokarta jan numfashi.

“Ban san shi ba kawai dai…”.

“Kawai dai me?”.

Ya tare ta da sauri har lokacin muryarsa ba ta canza ta koma yarda ta santa ba.

Wani karfi taji ya zo mata cikin zuciya da sauri ta dago idanuwanta a rintse ta sauke su saitin Dr.Aqeel kafun ta juya ta kalli inda Huzaif yake tsaye har yanzu tana hango irin tashin hankalin da yake ciki.

“Gani nayi kamar yans cikin Matsala  sosai naga haka a idanunsa shiyasa na ji ba dadi…”.

Ba wai don ya yarda da maganar ta bane dari bisa dari domin zuciyarsa taki yarda da abin da yake gani jan numfashi yayi mai tauri yana kokari ajje maganar tata a zuciyarsa yana yarda da cewa ita  ta hango tashin hankali game dashi ne shiyasa ta nuna jajantawa gareshi duban Huzaifa yayi daga inda yake tsaye yana hango tashin hankalin da yake ciki idanunsa sosai ya fuskanci wani abu cikin Maganar Mariya kuma zuciyarsa na karyata abin da yake zargi ba tare da yace da ita kala ba ya juya ya cigaba da tafiya jan numfashi tayi ita ma tana sake kallon Huzaif kafun ta kau da kai hadi da hadiye wani abu mai girma da ya tsaya mata a wuya ta daga kafafunta ta bi bayan Dr.Aqeel zuciyar cunkushe da abubuwa ma bambanta wanda ta kasa gane in da suka sanya gaba..

Abu mai girma taji ya zo mata wuya ya tsaya cak! Numfashi ma da kyar ta ke jansa don ji take kamar zata shiɗe a hankali ta kai hannayenta duk biyun ta dafe kanta da take ji yana kokarin tawatsewa sosai take jin kirjinta na buga a duk sakan sai take hango tashin hankalin da ta gan shi a ciki sosai take hango yanayin fuskarsa mai dauke da kayan damuwa masu girma sosai.+

Sosai take jin wani abu mai kalar tausayi yana saukar mata a wani sashi na zuciya yana haifar mata da wani yanayi mai sanya kasala da sanya wani wani ciwo mai girma.

Ba ta san ya zata yi ba, ba ta san me  take ji game dashi ba, ba ta san mai zuciyarta ke kokarin yi gareta ba, ba ta san mai yasa tunanin wannan mutumin yake kokarin samun waje a filin zuciyarta ba, ba ta san mai yasa komai ke kokarin wargaje mata da tunaninsa sa ba ta tsane shi bana ta son ko ganin fuskarsa a filin rayuwar duniyarta sosai take jin ɗaci da bauri a zuciyarta duk lokacin da ko sunansa taji sai taji kamar ta kurma ihu amma a halin yanzu wani irin yanayi take ji game dashi sosai KUDIRI da tayi akansa a zuciyarta taji yana kokarin rushewa sosai taji bangarori na sashin zuciyarta sun kasu kashi biyu suna faman tamka muhawara wanda hakan ba karamin sanya ta tashin hankali yayi ba wanda ita kanta ba ta san mai ya dace tayi ba, ba ta san mai ya dace tayi akan wannan lamarin na zuciya ba.

A hankali take sauke hannayenta daga kanta idanuwanta take rintsewa tana buɗewa a hankali gani take yi komai da yake faruwa da ita a yau kamar mafarki ne ba gaskiya ba za ta so ace a cikin barci ne komai ke faru da ita za ta so ace ba a zahiri bane za ta so ace kamar tatsuniyar kanzon kurege ne wannan lamarin.

Sosai take jin wani sashi na filin zuciyarta na halittar wani abu mai girma wanda yake kara tsuke mata da zuciya a duk sakan sosai take jin jikinta na samun wasu abubuwa da su ka danganci zuciyarta sosai take jin duk wani sashi na jikin ta na amsar abin da zuciyarta ke halitta ba ta san a yarda zata dauki abun ba bata san a wani irin ma’aunin hankalin ta zata ajje wannan lamarin ba komai take ji sabo na halitar kansa da kansa a zuciyarta da gangar jikinta.

Nisawa take yi a hankali tana faman fizgar numfashi wanda take jinsa kamar yayi mara karanci sosai a gareta.

A hankali ta fara kokarin tashi saman kafafuwanta tana jin yarda suke wani irin kokarin kasa daukar gangar jikinta sosai take ji wani abu mai sanya rauni a duk sassar jiki da zuciya yana samun gurbin zama a jikin nata.
Safah da Marwa ta shiga yi cikin rashin tsammanin abin dake faruwa da ita ba ta san mai zata ce ba mata san wani irin tunani ya kamace ta ba bata san mai rayuwart take kokarin dauko mata ba ta jiho filin duniyarta bata san wani irin tashin hankali bane ƙaddara ke kokarin dauko mata a wannan lokaci zuciyarta! Sosai take ji kamar ba ta ta ba sosai take ji kamar wata zuciyar ce ta daban ta sauya a filin kirjinta.

Komai take jin sa ba dadi sosai take jin saman harshenta na haifar mata da wani ɗandano mai bauri gareta sosai take jin zafin da zuciyarta da can kasar ruhinta suna kokari kwatar kansu a kansa.

STORY CONTINUES BELOW
A hankali ta fara taku har ta isa inda Mu’azzam ke kwance idanunusa biyu da alamun farkawa tayi daga barcin da yake yi sai faman wasa da hannayensa yake yi yana kaiwa bakinsa yana tsotsa alamun yinwa yake ji.

Sosai ta ware idanu akansa tana kallon sa mamaki ne sosai ya bayyana a gareta bata ji mptsinsa ba kuma da alamun ya jima da tashi daga barcin a hankali ta mika hannayenta ta dauko shi gami da rungumeshi sosai ajikin ta sosai take jin wani irin yanayi game dashi sosa take jin so irin na DANGANTAKAR YAN’UWANTAKA na ratsa ko ina najinta sosai take jin so dan’uwan nata a duk lokaci tausayin sa da jikan ke kara samun gurbi a filin zuciyarta na kara haifar mata da so mai tsanani game da shi idanuwata take saukewa akan nasa tana faman sakin wani murmushi wanda ita kanta ba ta san tayi shi ba shima Mu’azzam din murmushin yake saki don akwai shi da arhar dariya.

“Ehem! Nikam ina jiye miki ranar da za ta zo ta kasance ta rabuwa da Mu’azzam ban san ya zaki yi ba?”.

Kamar daga sama ta tsinkayi muryar Dr.Aqeel na dukan kunnuwanta sosai taji wani irin faduwar gaba ta ziyarce ta a hankali taji takunsa na iso gareta sosai take ji a jikinta idanuwansa na kanta sosai take jin komai na jikinta ya zama kamar ba nata ba ita kam! ba ta san abin da ke dawainiya da ita ba a duk lokacin da Dr.Aqeel ya fado duniyar rayuwarta sosai take shiga wani yanayi na rashin gane kanta.

A hankali ya karo ya ja kujera ya zauna yana fuskantar ta sosai fuskarsa kunshe da murmushi.

“Umma ba ta tashi bane har yanzu?”.

Ya fadi yana kai dubansa ga tsintsiyar hannunsa mai dauke da wani hadadden Agogo Gold-Colour  kirar Rolex sai faman sheki yake yi yana kara wa hannun nasa wani irin kyau na musamman.

“Uhmm ba ta tashi ba. amma… Ai kai kace sai nan da awa uku kuma naga daga lokacin da kayi mata allurar zuwa yanzu ba a ci awanni uku”.

Yanayin yarda take ajje kalmomin da take kokarin furtawa da laɓɓanta a hankali hakan ya shagalar da shi sosai komai cikin natsuwa da hankali take yin sa kamar mai tsoron kuskuren fadin wata kalma daya da bata dace ba gyaɗa kai yayi gami ya sake kai dubansa ga Agogon hannunsa.

“Yaa Allah! Kin ga shaf! na mance  Wallahi”.

Ya fadi yana fama yatsine fuska gami da dafe kai.

Yanayin da yake nunawa sai ya sanya Mariya sakin baki tana kallonsa sosa take kallon yanayin da yake nunawa kamar karamin yaro sai faman turo baki gami yake yi yana cizon laɓɓansa.

Ta gefen idanu ya kalle ganin yarda ta saki baki tana kallonsa sai ya cigaba da abin da yake yi don ya lura abin da yake yi din ne ya shagalar da ita cikin kallonsa sam bata lura ba tsayin lokaci har Mu’azzam dake hannunta ya kusan zuwa kasa cikin hanzari Dr.Aqeel ya kai hannayensa duk biyun ya tallebe shi wanda ita ma a daidai lokacin ta zabura ta kai hannunta domin gyarashi aiko sai hannayensa suka sarkeda na juna wani irin Shock ne gabadaya ya kama jikinsu da sauri Mariya tayi baya gami da sakar masa da Mu’azzam din idanuwanta a warwaje sai faman yarfe hannayenta take yi fuskarta na ya mutsewa kamar zata yi kuka.

Yaa Salam!.

Abin da ya fadi kenan cikin zuciyarsa da wani irin yanayi wanda ya kasa gane na menene sosai ya rungumi Mu’azzam amma har zuwa lokacin jikinsa bai daina sanar dashi Shock din daya ji ba.

Bugun zuciyarta sosai ya kara sauri sosai take jin wani tashin hankali yana samun waje a jikinta da zuciyarta da can kasan ruhinta sosai take jin wannan yanayi mai ABOTA da bakon lamari wanda tun da take bata taba jin irinsa ba mutane da yawa suna sarkewa bisa rashin sani amma bata taba jin irin wannan yanayin ba.
Wani fili na zuciyarta ya shiga sanar da ita:-

STORY CONTINUES BELOW
‘shin kin manta waye kuka yi haka dashi. shin kin manta ɗa namiji ne kuma hakan sam bai dace ba mace da namiji su taba juna in har ba muharraman juna bane’

Astagafurullah wa’atubu ilai!

Abin da ta fadi kenan cikin zuciyarta wani irin tsoro taji ya game jikinta da sauri ta fara ware idanunta domin karantar yanayin sa bata fuskanci komai ba domin hankalinsa ma bai gareta yana can wajan Mu’azzam yana gyara masa kwanciya a jikinsa hakan da ta gani ya sanya ta samun natsuwa domin abin da zuciyarta ta fara hasaso masa ba hakan bane.

“Amma dai yanzu Mu’azzam ya tashi ko. Naga yanayin barci game dashi”.

Kai ta shiga gyaɗa masa kamar yana kallonta domin ta kasa cewa komai bakin ta take jin yayi mata nauyi sosai tsoron magana take yi domin bata san mai zata ce ba jin jikinta take yi har yanzu shock din bai sake ta ba.

A hankali ya dago idanuwansa jin bata ansa masa ba sosai yake kallonta ya ganin yanayin da take ciki sosai ta fahimci ita taji abin da ya ji a jikinsa sosai ya gane haka murmushi yayi kafun ya ce.

“Magana nake yi fa ko akan Mu’azzam din masa sai an yi halin rashin son maganar?”.

Ya fadi har lokacin fuskarsa akwai murmushi ita ma wani yaƙe ta dauko ta daurawa fuskarta a tunaninta wai murmashi ta mai da masa kafun ta kokarta motsa laɓɓanta.

“Uhmm yanzu ya tashi kai kuma.ka shigo”.

Ta fadi tana mai nuna kamar shine dalilin rashin yin komai akan Mu’azzam.

Ya gane in da ta dosa don haƙa ya mike a kafafunsa yana kallonta ya mika mata Mu’azzam a hankali takai hannunta ta anshe shi.


Mu’azzam
“Sai anjima”.

Ya fadi yana mai shafar kan Mu’azzam dake ta faman kallonsa yaka dariya.

A hankali ya fara taka kafafuwamsa ya ficewa dag cikin dakin sosai yake jin wani irin yanayi a jikinsa sosai yake jin ranar yau a gareshi ta fita daban sosai yake jin yanayi mai zubi da wani yanayi mai armashi a jikinsa a haka har ya karasa ficewa daga cikin dakin.

Wani ajiyar zuciya ta saki tana mai lumshe idanuwanta ta bude su akan Mu’azzam wanda ya  kafeta da idanu kamar yasan abin da take yi ja masa kumatu tayi ya bangale mata baki sukayi hanyar Toilet din dake cikin dakin domin gyara masa jikinsa.

*****


STORY CONTINUES BELOW
HUZAIF
Tun ranar da ya hadu da Mariya ya sake jin filin duniyar rayuwarsa ya sake hargitsewa sosai yake jin ciwon da zuciyarsa take masa yana kara girma matuka gaya sosai yake hango tashin hankali mara musaltuwa na kara wanzuwa gareshi.

Juyi yake yi saman gadonsa lafiyayye wanda yaji kayan shimfida amma duk da wannan taushin gadon da laushi da yake dashi hakan bai hana shi jin sa kamar akan ƙaya yake kwance ta take faman sassoke shia ko wani sashi na jikinsa.

Bai sa mai ya dace ya yi ba, Bai san abin da ya kamata ace ya aikata ba domin ceton kansa, sosai yake jin kwanyarsa ta toshe gabadaya tunaninsa ya daina kawo masa abin kirki na a zo a gani.

Zuciyarsa sosai yake jin tana kara ciwo mai girma a cikin filin ta sosai yake jin zafi da raɗaɗi a duk sakan sosai yake tsoron abin da zai faru dashi nan gaba in har zuciyarsa ba ta saman masa mafita ba sosai yake hango rayuwarsa gajarcewa take yi a duk sakan…

handle din kofar dakinsa da yaji an kama ya sanya shi saurin buɗe idanuwansa da suke kulle yana.jin tunanin da yake ta faman yi na kanzon kurege ya tsaya cak!.

Mu’iz ne ya shigo fuskarsa kawai zaka kalla ka gane akwai abin dake damunsa yanayin kallon da yake wa Huzaif zai tabɓatar maka akansa yake samun damuwa  a filin zuciyarsa.

“Ban san wata irin rayuwa kake kokarin rakitowa kan ka ba, Ban san mai yasa kake kokarin sanyawa kan ka abin da zai hanaka walwala a duniyarka ba, Ban san mai yasa ka kasa kokari wajan yaki da abin dake damunka ba?”.

Mu’iz ne yake fadin haka muryarsa  cike da damuwa hannunsa harɗe a jikinsa ya jingina a kofar dakin ba tare da ya karo cikin dakinsa amma idanuwansa masu ciƙe da damuwa suna kan Huzaif dake ta faman juyi kan gadon gabadaya lokaci guda ya hargitsa shimfidar gadon.

A hankali Mu’iz ke takowa saman kafafuwansa jikinsa na bayganar da yanayin sanyi da halin da abokin nasa yake ciki a haka ya iso bakin gadon ya zauna yana kallons sosai kafun ya kai hannunsa ya ja babban bargon da ya lullube kansa dashi jikinsa daga shi sai Boxer da singilet murɗanɗan jikinsa mai cike da kirar mazantaka sosai ya bayyana kau da kai Mu’iz yayi ganin yarda da yake ciki.

“Ban san mai yasa kake haka ba ban san mai ka dauki rayuwa ba ban san mai yasa kake daukar abu da girma ba wanda bai dace sam ace hakan ba haba Huzaif mana”.

Ya fadi da rarrashi a muryarsa a hankali yake jan numfashi yana ajjewa kafun ya numfasa.

“ji ka don Allah a hakan kake tunanin zaka cigaba da zama a Huzaif din da a ka san ka, haka kake tunanin zaka samu walwala a rayuwarka ba tare da kayi maganin abin da ke damun ka ba kana tunanin wannan halin da ka jefa kan ka zai maka maganin matsalarka kayi ganganci Huzaif…ba ma wannan ba sosai nake mamaki Huzaif da har zaka kasa fada min abin dake damun ka nayi mamaki a zuciyata yanayin da ka nuna ace abu na damunka amma a matsayina na abokinka shakiki amma ka kasa sanar dani gaskiya bakayi ABOTA adalci ba dake tsananinmu”.

Numfashi ya ja mai zafi kafun ya ciza laɓɓansa.

“Ka tashi ina son magana da kai in kuma bani da wannan matsayin sai naji in san in da dare yayi mani”.

Yanayin yarda yayi maganarsa da muryarsa mai zurfi da zafi a cikinta ya sanya Huzaif motsawa yana faman cizon laɓɓansa a hankali ya ja jiki ya riko hannun Mu’iz.

STORY CONTINUES BELOW
Da sauri Mu’iz ya kalle shi hawaye ya gani suna sauka a idanun Huzaif da sauri ya ware idanu ya na kallonsa yana mai kara rike hannunsa sosai.

“Haba mana Huzaif! me nake shirin gani haka wai shin meke damun ka ne haka wai kuwa kasan yarda kake kuwa kana kallon kanka a MADUBI kuwa ka ga halin da ka jefa kan ka Huzaif Hawaye Huzaif hawaye a idanun ka By God Sake don Allah karka ce mani abun har ya kai haka kar kace mani matsalar da kake ciki har ta kai matakin da zaka zubda mata da hawaye…Yaa Allah!”.

Janye hannunsa yayi daga na Huzaif sosai yake ware idanunwasa yana jin yarda gabansa ke bugawa cikin wani irin mataki mai girma.

“Ban san abin dake damu na ba, Mu’iz abu daya na sani Mariya ita ce ta dalilinta komai…”.

“Mariyaa!”

Mu’iz ya fadi muryarsa da sauti sosai a cikinta da mamaki yake duban sa cikin wani irin yanayi wanda shi kansa bai san yarda zai fassara shi ba.
“WACECE ITA?”.

Mu’iz ya fadi muryarsa da zurfi a cikinta yana mai kallon Huzaif da izuwa lokacin hawayen da yake zubda sun tsaya illa numfashi mai girma da yake ta faman ja kamar zai kufce masa.

“Ban san ya akayi kudin ƙaddara ya rakito mani ita ba ban san mai yasa kaddara ta kinkimomin ita ba ta jeho cikin rayuwata ba sosai nake cikin tashin hankali mai girma Mu’iz ban san ya zan kwatatta maka yanayin da nake ji a zuciya ta ba abu ne mai girma nake jinsa ya samu gurbi a filin zuciyata wanda ban san menene ba ban taba jin irinsa ba koma.na taba ji ban taba jin mai girma kamar wannan ba”.

Zuciyar Mu’iz ce ta buga a hanzarce har sai da ya kai hannunsa ya dafe kirjinsa tsayin mintina masu auki kafun ya ja numfashi mai zafi ya fesar ya dubi Huzaif da yayi shiru numfashin sa sai kai kawo yake yi a hankali.

‘u’r in love’.

Mu’iz ya fadi a zuciyarsa da wani murmushi mai girma a fuskrsa kafun ya nisa.

“Tashi ka zauna ka bani labarin yarda abun ya kasance”.

Mu’iz ya fadi fuskarsa da murmushi yana mai bubbuga bayan Huzaif sakato yayi Huzaif din yayi ganin yarda Mu’iz ya nuna masa a hankali ya ja jiki ya tashi ya zauna tsakiyar gadon har da tankwashe kafafuwansa hannayensa tallabe da haɓa ya warsa idanuwansa kan Mu’iz da shima idanuwansa na kansa sun shafe fiye da mintina goma a haka kafun Mu’iz yayi kokarin kau da shirun.

“Bani labari mana Huzaif”.

Ya fadi yana kafe shi da idanu
Sosai Huzaif ke kallonsa gabadaya ya rasa inda Mu’iz ya nufa sosai maganganunsa suka rikita shi ya rasa ina zai ajje su ya rasa ina suka nufa sai faman sauke ajiyar numfashi yake yi yana kallon Mu’iz.

“Ban gane ba Mu’iz me kake nufi”.

Ya tsine fuska yayi kafun ya gyaɗa kai.

“Bani labarin wacece Mariya”.

tsura yayi da idanu yana tunanin mai zai ce da Mu’iz ta yaya zai ba shi labarin Mariya mai zai ce masa ya hada su kai ya shiga girgizawa yana cizon laɓɓansa a hankali shiru ya shiga tsakanknsu kafun ya kokarta sanar da Mu’iz yarda ƙaddararsa ta watso masa Mariya cikin duniyar rayuwarsa take kokarin rikita masa komai da komai.

“Yaa Allah!”.

Mu’iz Ya fadi yana mai girgiza kai cikin wani irin yanayi wanda Huzaif ya kasa gane in da hakan ya dosa.

STORY CONTINUES BELOW
“Ban san mai yasa kake haka ba ban san mai yas kake rayuwa haka ba ban san yaushe zaka yi wayo ba a rayuwarka ba ban san mai yasa kake daukar rayuwar duniya a abun azo a gani ba”.

Kau da kai Huzaif yana mai yatsine fuska don ya lura da inda maganganun Mu’iz suka dosa.

“Mtss”.

Ya ja dogon tsaki kafun ya dubi Mu’iz a karo na ba a dadi.

“ni ba abin da nake bukata ba kenan so nake ka samo mani mafita ba wai wani zance na daban ba”.

“tsiya ta da kai kenan Huzaif ya kamata ace ka fuskanci rayuwa tun yanzu kai ga ka da son yin abu amma sam abin bai yi maka kyau”.

Cikin rashin fahimta yake kallonsa yana nazarin kalamansa.

“Na rokeka ka rabu dani Pease I don like this at All wallahi ya kamata ace ka gane ni sosai izuwa wannan lokacin…Mtss”.

“Huzaif you sport to no u’r in love…Yaa Allah abu kamar almara ban san ya zan fassara maka ba halin da kake ci amma dai akwai alamun so tattare da kai…”.

Ihu Huzaif ya fadi yana mai kaiwa Mu’iz wani wawan naushi a fuska da sauri ya kau ce cikin hanzari yana mai tashi daga kusa dashi cikin yanayin mamaki da kuma murmushi a fuskarsa shi dama ya san sa haka ta faru.

“U’r so stupit Mu’iz baka da hankali wallahi na lura kana hauka sosai Yaa Allah ni kake wa wannan maganar kan uban ce…”.

Wani sarawa kansa yayi da sauri ya sanya hannu ya dafe yana mai yatsine fuska yana jin yarda zuciyarsa ke raɗaɗi da zafi.

“Please I beg u in the name of Allah to leave me alot I don’t  wanna see you please and please…”.

Kansa ne ya sake dauka wata irin jiwa yaji tana sama da kasa dashi da sauri ya koma ya kwanta yana tattare jikinsa waje daya kamar mai jin sanyi sosai yaji numfashinsa na kokarin kwace masa wani irin tashin hankali yana zuciyarsa ta bankado masa lokaci guda gabadaya yaji duniyar na sukuwar doki dashi sosai yake hango tashin hankali ta yaya hakan za ta faru ta yaya Mu’iz zai kawo masa wannan mahaukacin tunanin nasa ya fada masa yace hakan ce take faruwa dashi ina! ba zai taba yuwuwa ba ai wannan hauka ce da rashin hankali kamar shi Huzaif ace wai son ta yake yi kaicon wannan mummunar labari.
Wata irin zabura yayi ya dire daga kan gadon ya isa gaban Mu’iz dake tsaye kamar wanda aka dasa mamaki ne ya cika shi ganin yanayin da Huzaif ya nuna game da maganar da yayi masa wanda in da yasan haka ce zata faru ba zai fada masa ba.
wuyar rigarsa da yaji an shaƙa ya sanya shi katse tunanin da yake yi da zuciyarsa.

“Ban san baka da hankali ba sai yau, Ban san kwakwalwarka ba ita kadai bace akan sai yau, ni zaka kawo wa wannan takaicin da bakin cikin rayuwata ashe dama ba so na kake ba ashe dama zaman tsana muke yi tsakanina da kai Well..Well ban yi mamaki ba Mu’iz dama ance makashinka yana nan tare da kai ba tare da ka sani ba yau ka nina min true colour din ka kuma na gani”.

Yanayin yarda yake maganar zai tabbatar maka ba ya cikin hayyacinsa idanunsa gabadaya sun canza kamar ba nasa ba sosa jikinsa ke rawa hakan da Mu’iz ya gani ya tabbatar masa Huzaif ba ya cikin natsuwarsa yake wadannan sambatun masu kama da mai hauka tubaran dole yayi masa zuri’a domin ba ya cikin tunaninsa a hankali ya sa hannunsa ya zare na Huzaif dake wuyansa a hankali ya ja shi ba tare da gardama ba har ya isa dashi kan gadon ya kwantar dashi yana mai jama masa bargon ya lullubeshi sosai jikinsa ya wanzar da wani irin zafi sosai yana faman karkarwar sanyi sai jan numfashi yake yi da sauri sauriA hankali yake ajje komai na shi kan table din dake girke cikin kayataccen office din sa kallo daya zakayi masa ka gane hanzarin da yake yi cikin aikinsa gabadaya hankalin sa bai wajan abin da yake yi idanuwansa na wajan kofar office din ji yake yi ajikinsa akwai wanda zai shigo zuciyarsa tana sanar dashi hakan.+

Bayan ya kammala komai a hankali ya fara takawa kan ƙafafuwansa don ji yake yi kamar abin da yake muradin gani kuma zuciyarsa na sanar dashi tabbatarsa kamar ba zai tabbata ba gareshi sosai yake ganin tafiyar lokaci wanda yake hango kurewa a cikin sa duk dakika daya gani yake yi kamar tafiyar awa daya ce.

Wajan sakatariyarsa ya dosa yana faman jan numfashi.

“Sir Morning”.

Abin da ta fadi kenan bayan ta dago kanta jin alamun mutum kusa da ita.

Hannu ya daga mata alamun amsawa kafun ya shiga waige-waige na yan dakiku sannan ya sauke idanuwansa akanta yana mai nisawa.

“Areefa ta shigo aiki yau kuwa?”.

Mamaki taf! A fuskarta take dubansa sosai take lura da canjin ogan nata tunda Areefa ta shigo cikin ma’aikatar nan gaɓadaya hankalinsa da natsuwarsa suka karkata akanta ba ta san mai hakan ke nufi ba…ko da dai bai kamata tayi mamaki ba domin ta san waye Dr.Erena tuni ta diga masa ayar tambaya katotuwa.

Kaɗa idanu tayi kafun ta motsa tika-tikan laɓɓanta wanda suka sha jan jambaki sai faman kyalli suke yi.

“gaskiya bana zaton ta shigo don ban ji duriyar ta ba yau sam!”.

Ta karashe tana mai kafeshi da idanuwa sosai da sosai kai taga ya shiga girgizawa yana faman cizon laɓɓansa gami da haɗa hannayensa waje daya yana lankwasawa suna bada wani sauti mai zurfi.

A hankali ya fara taka kafafuwansa da sanyi a cikin su amma yarda yake tafiyar cikin hanzari bai bayyanar da haka din ba kofar fita daga sashi ya dosa yana faman hanzari cikin tafiyarsa cikin kankanin lokaci ya sauka daga benen zuwa tsakiyar cikin company din idanuwansa ya ware yana yawatawa cikin sashi da sashi na ko ina.

Ya jima cikin wannan yanayin kafun ya isa wajan daya daga cikin ma’aikatan da suke nan din ko wanne da bangaren sa kamar office.

“Mufeeda Please ko kin ga Areefa ta shigo yanzu?”.

ya fadi har lokacin idanuwansa ba su tsaya waje daya ba.

Dago kanta tayi jikinta sanye da abaya kamar ko yaushe dubansa tayi da wani irin yanayi kafun ta kau da kanta sosai taji sunan da ya ambata ya shiga kuwwa cikin kwakwalwarta sosai take jin sunan yana haifar mata da wani irin yanayi mai girma gareta zuciyarta taji tana zaro mata wani lamari mai girma da ta daɗe da binne shi a filin zuciyar ta ta sunan Areefa take ji kamar a mafarki abubuwa da yawa take ji a ranta game da sunan.

STORY CONTINUES BELOW

Nisawa tayi cikin wani irin yanayi mai girma kafun ta dago kanta ta sauke ga Dr.Erena wanda shi a wannan lokacin sam! hankalinsa baya kanta sai faman watsa idanuwansa yake yi cikin ko wani sashi na ma’aikatar har izuwa babbar kofar.

“Areefa”.

Kamar daga sama taji bakinta na nanata sunan da wata irin murya mai zurfi da wasu abubuwa masu girman gaske.

“Ban san taba ban ma taba ganin ta ba!”.

Muryarta da zurfi a cikinta tashiga fadin haka da alamun bacin rai tattare da ita musamman yanayin da fuskarta ta sauya lokaci guda bacin rai sosai ya samu masauki a ko wani sashi na filin zuciyarta da ruhinta.

sosai yaji sautin muryar Mufeeda akansa wanda tunda suke da ita bai taba jin tayi magana mai zafi haka ba sosai yake kallon ta cikin yanayi na mamaki kafun ya nisa.

“bakuwar da ta zo last week fa nake magana wacce kuke matsayi daya da ita”.

Sosai yake yawatawa da idanunsa akanta yana kallon yarda komai nata ya sauya lokaci guda kai ya shiga gyaɗawa kafun ya juya ya doshi babban kofar da zata sadashi da reception din Company din.

Tsaye yayi hannayensa zube cikin aljihun bakar suit dinsa sai faman yawata idanuwansa yake yi ta in da zai hango ta can wajan Parking ya tsayar da ganinsa yana bin motocin wajan da idanunsa daya bayan daya bai dire a ko ina ba sai kan wata bakar marsandi wacce kallo daya zakayi mata ka gane sabuwa ce fil.

Ajiyar zuciya ya ajje hakan ya tabbatar masa da Areefa na cikin Company din nan amma kuma ya akayi bai ganta ba har sashinta ya duba nan ma bai ganta ba ya tambayi abokan aikin ta suma sunce ba su ganta ba mai hakan ke nufi?.

A hankali ya fara juyawa kan kafafuwansa domin koma cikin Company zuciyarsa cike da tunanin Areefa da dalilin da yasa bai ganta ba cikin Company kuma alamun ya nuna ta na ciki tunda ga motarta nan hakan ya tabbatar masa da zuwan ta da wannan tunanin ya koma ciki bai sake duban kowa ba ya hau matattakalar da za ta haura dashi zuwa sashin sa.

Mufeeda dake zaune tun dazu ta zabga tagumi tun da ya zo ya sanar da ita wacce yake nema ya fada mata sunan da yake cigiya shikenan taji ta komai nata ya canza sosai taji wani iri a jikinta har ma da zuciyarta sosai take jin wani abu mai nauyi mai dauke da bacin rai ya samu masauki a zuciyarta a hankali take ajje numfashi tana duban Dr.Erena zuciyarta na kara tabbatar mata da abin da take zargi.

Gyaɗa kai takeyi tana yatsine fuska gami da tura laɓɓanta cikin bakin sai da ta dauki lokaci mai tsayi a haka kafun ta ajje komai gefe ta cigaba da aikinta amma  zuciyarta sai kawo mata abubuwa take yi wanda suke kokari addabatar su hana ta aikinta.

Tana cikin kokawa da zuciyarta kamar daga sama taji sautin takalmi ya karaɗe cikin wajan gabanta ne ya buga ko ba a fadi mata ba tabbas ta gane ko wacece mai wannan tafiyar bata dago kanta ba sai dai aikin da take yi cikin Computer ta tsayar dashi cak! hannayenta ta janye daga madannan computer din ta hade su waje guda tana sarke su a hankali kafun ta dago kanta a daidai lokacin ita kuma ta karaso daidai wajan da take hannunta rike da jaka mai kalar Gold da wasu yan duwatse masu kyalli da akayi mata ado da su jikinta kananun kaya ne wando da riga sai abayar da ta daura a kai gaban rigar abuɗe yake ta yane kanta da gyalen abayar fuskar nan ta sha Make-up sosai wayarta a kunnan ta sai faman sakin murmushi take yi da alamun wayar da take yi din tana jefa cikin nishaɗi.

Kuri Mufeeda tayi mata da ido tana saka dan guntun biron dake hannunta cikin bakinta tana jujjuyashi tana yawatawa da idanunta sosai akan Areefa da ta tsaya daidai saitinta bugun zuciyarta na karuwa sosai da sosai abin da take zargi ne take ganin tabbatarsa zuciyarsa na kara hasko mata abubuwa da dama da suke kara tabbatar mata da zarginta.

STORY CONTINUES BELOW

Yaa Allah!.

Abin da ta fadi kenan lokaci guda tana dafe kanta da taji yana sarawa runtse idanuwanta tayi sai sai da ta dauki sakanni kafun ta buɗe su har zuwa lokacin Areefa na nan tsaye sai dai ta gama wayar ta sauke duban Mufeeda tayi wacce ita idanuwanta na kanta lokaci guda suka sarke a idanuwansu sosai suke kallon junansu wasu abubuwa ne masu girma suke wanzuwa a zuciyoyinsu sun dauki mintoci a haka kafun Mufeeda ta kau da idanuwanta gami da yin kasa da kai ita kuwa Areefa kafadunta ta daga gami da nuna halin-ko-in-kula ta ƙyaɓe baki tana mai daga wa Mufeeda hannu ta raba ta ta wuce cikin takunta na musamman da duk lokacin da zata shigo cikin Company din take yin sa.

*******

Sosai hawaye ke kwaranyowa zuwa saman fuskarta sosai take jin zuciyarta na zafi da raɗaɗi sosai take jin tashin hankali wanda ba tayi tsammanin ba mai girma ne a rayuwarta ba ta san ya zata koyi rayuwa ba a yanzu bata san ya zata koyi rayuwa ba batare da wadannan dangin ran ba bata san ya zuciyarta zata koyi kewarsu ba sosai take jin abu mai girma na samun waje a filin zuciyarta yana zama duk jikin ta take jin yayi sanyi yana haifar mata da abubuwa masu girma da kara dagula mata lissafi ba ta san ya rayuwa zata kasance mata ba nan gaba ba ta san wata irin rayuwa zata buɗe ba a shafin duniyarta in ta bar wannan wajan.

Hannunta ta sa ta shafe hawayen da suke sake balle mata wasu na bin wasu hada kayan su take yi cikin yanayi wanda ita kan ta ba ta san ya zata fassara shi ba ta  san dai akwai tashin hankali mai girma da zai zo mata ko ma tace ya zo mata ba ta san ya zata dauke shi ba ta san ya za ta ajje tashin hankalin nan a zuciyarta  za ta bar su za tayi kewarsu ta tabbata dole ne su rabu rabuwa ta har abada wanda bata tsammanin za su sake haduwa a duniyar nan domin da ma can matsayin su ba daya bane ta sani sam ba su dace da zama a inuwa daya ba har su shaku ta sani

zuciyarta…zuciyarta ba tayi mata adalci ba ba ta yi mata daidai ba ta sani tayi sake sosai da ta bar zuciyarta ta shaku da mutanan da ta san tabbas su rabu ko tana so ko bata so domin duniyarsu ba daya bane suna da tazara mai girma a tsakaninsu akwai katanga mai girma da tayi musu SHAMAKI a tsakani yau ta ga ILLAR SABO a rayuwarta tabbas sabo shi ake yi wa kuka dole tayi jinyar zuciyarta wanda ba ta san ranar da zata warke ba daga ciwon da ya kamata mai girma wanda laifinta ne da tayi sake har ta bar zuciyarta da gangar jikinta sukayi sabo da wadannan mutanan masu ALHERI da YAƘANA.

“Mariya!”.

Taji muryar Umma na ambaton ta cikin yanayi mai cike da rauni da kuma rarrashi.

Da sauri ta sanya hannunta ta shafe hawayen da suke saukar mata kafun ta kokarta janyo yaƙe muryarta na rawa ta ansa mata gami da juyowa ta na fuskantar ta kallon ta take da duk wani rauninta dake cikin zuciyarta tana jin yarda ruhinta da gangar jikinta suke haifar mata da wani irin yanayi mai wuyar fassaruwa sosai take kallon Ummanta da yanayin da take ciki ta rame sosai sai dai kallo daya zaka yi mata kasan tana samun kulawa komai nata yayi normal duk wani abu dake damunta ya kau yanzu lafiya kalau take tana iya magana sosai cikin hankalinta ba tare da an samu matsala ba  sosai tayi wa Allah godiya da wannan ni’imar da yayi musu sosai take sake gode masa tafi kowa farinciki da wannan lamarin tafi kowa farin ciki da samun lafiyar Ummanta sosai take jin zuciyar na rage duk wani nauyi mai girma abu daya yake kara dakula mata lissafi in ta tuna shi Mahaifinta sosai take shiga tashin hankali mai girma sosai komai nata ke kara hargitsewa in ta tuna rashin matsaya da take dashi akan mahaifinta kullum cikin tunaninsa take ba ta san mai yasa ya tafi ya bar su ba a daidai lokacin da suke bukatarsa a filin duniyarsu ba ta san mai yasa ya bar su tsayin wannan lokacin ba bata san mai yasa ya dauki kafarsa ya bar su ba ba tare da ya sanar da su in da ya dosa ba sosai take shiga tashin hankali mai girma in ta tuna wannan lamarin.

STORY CONTINUES BELOW

Nisawa tayi kafun ta amsa kiran da Umman nata tayi mata.

“Ban san mai kike nufi da wannan kukan ba Mariya, Ban san mai kike so kuma ki daukowa kan ki ba, na lura sosai kike jin dadin zubda hawayenki baki san hakan yana matukar sanya ni cikin damuwa ba”.

Shafe hawaye tayi sosai take jin maganganun Umma a zuciyarta sosai take fuskarta gaskiyar abin da Umma ta fadi sai dai bata san ya za tayi da abin da yake a zuciyarta ba sosai take jin rashin dadi ba ta san ya za tayi ta hana idanunta zubda hawaye ba.

“Umma Kiyi hakuri ban san ya zan yi in hana su zuba ba ne sosai nake jin kewa a raina sosai nake jin rashin jin dadi a ko ina nawa saboda su mun shaku Umma suna da alheri sosai a duniyar su ban san yaushe za mu sake haduwa ba in muka rabu…”.

Zuciyarta tayi rauni sosai muryarta ta karye hakan ya sanya ta yin shiru tana mai toshe bakin ta da taji kuka na shirin kufce mata.

“Yaushe zaki girma Mariya mai yasa kike abu kamar wata yarinyar da ke goyewa wa ya gaya miki kun rabu kenan har abada shin ce miki akayi daga nan lahira zaki tafi ba a duniyar zaki zauna ba to bari kiji mutum da mutum suna rabuwa sai su shafe shekaru masu yawa har su fidda tsammanin sake haduwa amma cikin iko na Rabbi sai ki ga sun hadu har sun sake wata rayuwar a filin duniyarsu don haka ki daina YANKE TSAMMANI akan abin da bakin san yarda zai kasance ba Allah kawai za ki saka a lamarin ki ba fa rabuwar rigima a kayi ba balle ki ce tsakanin juna ba za a so sake haduwa ba ALHERI ne ya hada ku kuma kin san shi alheri a ko ina yake ba ya tafiya a banza”.

Ba wai tana maganar nan ba ne don ta yarda ita akaran kan ta a,a kawai dai so take yi ta kwantarwa ‘yar ta ta da hankali domin yanayin da taga ta dau lamarin mai gira a zuciyarta ko da yake tana da gaskiya zama lafiya aka ce yafi zama dan sarki zaman da akayi cikin aminci da mutunta juna dole a ji ba dadi wajan rabuwa ko zama da mutum kayi kullum kuna fada dole in za ku rabu kaji rashin dadi a ranka ta sani ita a akaran kanta abin da Mariya tayi ba ta ga laifin ta ba domin ta lura akwai sabo da shakuwa sosai a tsakaninta da likitocin asibitin tana kallon yarda suke mutunta ta da ahalin ta tana kallon yarda ‘yar ta ta take ganin girman su  ba tare da raini ko wani abun ki ba fiye da KWANA SITTI da tayi a asibitin nan kamar yarda taji likitan na fadi ta san dole ne su shaku sosai shakuwar da ba za su so rabuwa ba amma ba yarda za suyi rayuwa ta gaji haka aka rabu da mutum ma zuwa lahira kuma aka hakuri balle wannan a na cikin duniyar sai dai ace ba waje daya ake zaune ba.

Gyaɗa kai tayi cikin yanayi na tausayawa shiru ne mai dan tsayi ya ratsa cikin dakin ba abin da kake ji sai ajjiyar numfashin Mariya lokaci lokaci tana jan hanci da alamun kuka a ciki kawai daurewa take yi ba ta taba zaton za su rabu ba ba ta taba zaton maganar rabuwarsu a wata rana ba za ta tabbata kamar yarda Dr.Karami ke fada mata ashe da gaskiyarsa wannan ranar za ta zo filin duniyar su kowa ya kama gabansa ashe duk maganganun da yake mata masu shige da WASIYYA gaskiya ne amma ta kasa sanya hakan a zuciyarta taki yarda da maganar tasa da take kallo a matsayin kanzon kurege bata san ruɗi da ya dauke ta ba bata san abin da ya shigar mata kai da zuciya ba ya hana ta hadda ce karatun Dr.Karami yanzu ga ranar ta zo gata cikin ta tsamo tsamo amma ta kasa yin komai sai nauyin zuciya da tashin hankalin da ta ke hangowa…

Sallamar da ta amsa kuwwa cikin dakin ne ta dakatar da ita daga zancen zuccin da take sosai taji wani irin bugun zuciyarta ya canza salo sosai taji wasu katangun tashin hankali suna kokarin rikito mata akai wani kuka mai karfi taji yana kokarin kufce mata bakin ta na rawa ta shigo kokarin amsa musu amma hakan ya gagara da gudu tayi hanyar Toilet din dakin hannayenta rufe da bakin ta kuka sosai take jin yana taho mata ta na shiga ta mai da kofar ta rufe durkushewa tayi a tsakiyar Toilet din gami da sakin wani irin kuka mara sauti mai matukar taba zuciya da ruhi da duk wani mai jinsa.

STORY CONTINUES BELOW

Sosai Dr.Karami yaji gabansa ya buga yanayin da ya ga Mariya a ciki idanuwansa ya sauke kan Umma da tayi kasa da kai sosai take jin wani iri a zuciyarta raunin da ta gani game da ‘yarta ya haifa mata da tausayi mai girma a zuciya ta sani ‘yarta ta shaku da su sosai shakuwar da sai anyi dagaske kafun a rabu dole zuciyoyi su shiga halin damuwa dole gangar jiki su shiga hali na rashin jin dadi sosai da sosai.

Kallon kallo suka shiga yi tsakanin su Dr.Karami da Dr.Aqeel sosai suke jin wani iri a zuciyoyin su musamman Dr.Karami don ji yakeyi kamar ya falla da gudu ya bita ya rarrasheta don ya san tabbas ba abin da yake damun ta sai maganar rabuwarsu ba tun yau ba ya lura sosai take nuna damuwa da tsoro duk ranar da ya yi mata maganar rabuwar su bai san abin zai yi tsanani haka ba ko da yake shi tashi zuciyar yanzu haka ciwo mai girma yake jin yana fama dashi jarumta ce kawai take hana shi bayyanar sirrin dake ransa sosai yake kewar Mariya duk da dai a ransa ba ya tunanin rabuwa za suyi ba ya hangowa rabu sam-sam cikin wannan lamarin amma dai yau a wannan rana shi a karan kan sa yana jin ba dadi don ji yake yi kamar wanda ya tashi daga cuta saboda rashin kwarin jiki.

Duban Dr.Aqeel yayi wanda shima dai yanayinsa ya nuna akwai abin dake damun sa a ransa sosai da sosai fuskarsa ta nuna rashin walwala jikinsa yayi sanyi sosai idanuwansa sun kada kadan kamar mai son fashewa da kuka.

Ba tare da yayi masa magana ba ya doshi kofar Toilet yana kwankwasawa a hankali yana kiran sunan ta sosai yake jiyo shasshekar kukanta wanda haka ba karamin taba masa zuciya yayi ba sosai yake jin tausayi da wani abu mai matukar girma suna wanzuwa a filin zuciyarsa a hankali ya cigaba da kwankwasawa amma ko alamun za ta yi magana juyowa yayi ya kalle su suma shi suke kallo musamman Umma wanda ta gama karantar yanayin su su duka sosai take jin tausayinsu duk su ukun na samun waje a zuciyarta ji take ina ma tana da wata dama da zatayi amfani da ita domin fidda su cikin wannan yanayi amma ina! ta san ba ta dashi gyaɗa kai tayi tana kau da kai daga barin kallon Dr.Karami.

A hankali ya rike Handle kofar ya turo sai ya  ganta a bude take da sauri ya karasa turawa yana mai sanya ƙafafuwansa da yake ji kamar za su zubda shi kasa saboda raunin da ya ji sunyi sosai.

Durkushe ya hango ta ta hade jikinta waje daya sai faman jan numfashi take yi mai zafi sosai zuciyarta take jin tana wani irin harbawa kamar zata faso kirjin ta ta fito waje komai take ji yana kwance mata komai na cikin duniyar take ji yana sauya mata lokaci guda.

“Mariyaaa!”.

Ya fadi muryarsa da wani irin rauni mai girma  idanunwansa a kan ta a hankali ta shiga kokarin dago idanunta da suka kaɗa sosai sukayi jajir kamar wanda aka watsawa barkono wani irin bugu zuciyarsa tayi wanda hakan sai da ya sanya shi sanya hannu ya dafe kansa duniyar yaji tana juya masa lokaci guda kau da kansa yayi don ba zai iya kallon idanuwanta a yarda suke ba wasu abubuwa ne masu girma yake ji game da kallonta suna faru dashi a filin zuciyarsa.

“Ban san meye kike haka ba, ban san mai yasa kike wahalar da kan ki haka ba, Haba mana Mariya mai yasa kike zurfafa lamarin nan haka rabuwarmu ai ba ta na nufin mun rabu har abada bane a,a muna nan tare a duniya daya har zuwa numfashinmu na karshe.”

Ba ta san ya zata dauki maganar ta sa ba bata san ya zata daura su a MIZANIN HANKALI ba sosai take jin zuciyarta taki aminta da zancen sa sosai take jin kawai  fadi yake yi domin ganin ta daina kuka rintse idanunta tayi kafun ta mike kan kafafuwanta cikin wani irin yanayi mai rauni.

“Ta ya ya kake so na anshi maganar ka ta ya ya ka ke so na gasgata abin da kake cewa bayan nasan dole mu rabu dole mu raba duniya bana zaton maganganunka za suyi tasira Yah Dr.Karami kawai ka fito fili kace mani yau ce rana ta karshe a DUNIYARMU da za   mu rabu yau ce rana ta karshe a garemu yau ne za mu rabu da juna…”.

Wani irin nishi tayi kafun ta gyaɗa kai hawaye su zubo mata wanda Dr.Karami yake jin su kamar saukar ruwan zafi a jikinsa.

“Ban san ko zaka yi mani alkawari ba sosai na yi sabo da kai a duniya ta ban sani ba ko za kayi mani adalci a duniyarka ka kasance dani mu ke mutunci ba zan taba mance alherin ka ba kai da sauran Al’umma sosai nake hango matsayin ka a matsayin dan uwa na jini ban da yan uwa so nake ka zama dan uwa gareni ka kasan ce mani dan uwa bayan Mu’azzam don Allah in kayi mani haka zan yarda kuma zan rike duk abin da kace mani in har ka rike mani abin da nace da kai”.

Rintse idanu yayi sosai zuciyarsa da kwakwalwarsa yake jin suna wani shawagi dashi a wani mataki wanda bai taba jin kan sa a cikin sa ba bai san mai zai ce mata ba bai san wani kalamai zai yi amfani da su wajan yi mata magana ba abu daya ya sani shine ba zai iya rabuwa da ita ba zai so ace yarda take maganar nan shima ya fadi mata shima haka yake ji ransa kamar yarda take ji.

Nisawa yayi kafun ya kokarta dubanta yana wani murmushi mai karfin gaske.

“Na yarda tuni na yarjewa zuciya ta zan ci gaba da zama dake a duniyata har zuwa karshen numfashi na na yarda na aminci da maganarki na rike miki alkawari ke ma ki rike mani kamar yarda kika fadi”.

Shafe hawayenta tayi kafun ta saki wani murmushi kamar yarda ta ga yanayi mata.

Alamu yayi mata da kai su fice daga Toilet din yana yatsine fuska alamun kyankyami kunya taji kai a kasa ta bi bayan sa zuciyarta na rage duk wani nauyi da ya tokare mata kirji tun lokacin da aka sanar da su sallamar su da akayi.

Bin su sukayi da kallo Umma ta dubi Mariya tana harararta kasa tayi da kai kafun ta dubi Dr.Aqeel wani kallo taga yanayi mata wanda sai da ya sanya gabanta bugawa da sauri tayi kasa da kai tana cizon laɓɓanta abubuwa da yawa suna rikita mata kwakwalwa a tsakanin Dr.Aqeel da Dr.Karami abubuwa da yawa take hangowa a tsakanin su wanda ta kasa gane menene iya tsayin tunaninta da tsayin lokacin da ta diba tana nazarin su ta kasa gane mai suke nufi da wasu abubuwa da ta lura suna yi mata.

Sun dau lokaci mai dan auki kafun su gama hada kayansu waje daya Mariya ta goya Mu’azzam da ke barci bai san ma abin dake wakana ba Dr.Karami yace a motarsu za su taba domin ya san gidan nasu Dr.Aqeel bai so haka ba ya so ace shi zai mai da su gidan su amma ganin Dr.Karami kamar yafi karfi a wajan su sai ya shanye komai da zuciyarsa ke kawo masa…Innalillahi wa inna ilaihir raji’una mai nake shirin gani ni marka? Hafsi! Hafsi!! Hafsi!!!.”

Goggo Marka dake zaune bakin kofa tana kadin zarenta ta mike tana tafa hannaye tana fadin haka idanuwa warwaje lokacin da ta ji sallamar su Mariya jikin ta har ɓari yake yi ta shiga dubansu kamar wanda ta ga wani mugun abu.+

Cak! Suka tsaya suma suna dubanta musamman Mariya da idanuwanta su kayo waje tana duban ta ganin yanayin da ta nuna juyawa tayi ta dubi Umma kafun ta sake mai da kallonta zuwa wajan Goggo Marka.

“Mariya Habeeba daga ina kuma haka?”.

Ta fadi cikin yanayi na mamakin ganin su.

Suma mamaki ne ya cika musu zuciya sosai da sosai sun rasa abin yi gabakidayan su sai bin ta da kallo kawai suke yi suna faman gyaɗa kai a hankali Mariya ta ja jiki a sanyaye ta isa bakin kofar dakin su da yayi kaca-kaca kamar wani kudundubi kofar dakin su har an girgiɗe ta labulan kuwa an yi fata-fata dashi ta na hango tsakar dakin yarda ya zama kamar wajan wasan yara sosai taji ranta ya sosu matuka gaya tsaki ta ja kadan kafun ta ajje kayan da suke hannunta wani irin duba tayi wa Goggo Marka da tayi tsaye fuska cike da mamaki sosai Hafsi da ta fito da daurin  kirji kai ba dan kwali gashin kan nan nata yayi wani kerere kamar dambun karangiya sai fama yawatawa da idanunta take tsakanin Umma da Mariya cikin yanayi na mamaki kallo daya zakayi mata ka gane a firgice ta fito daga cikin dakin barci ne a idonta.

Kau da kai Mariya tayi kafun ta isa in da Umma tayi tsaye kamar wacce aka dasa kallo daya zakayi wa fuskarta ka gane bacin ran dake kunshe a zuciyarta ansar Mu’azzam tayi ta goya sannan ta dubi Umma tana mai rike mata hannu suka baro wajan suka iso kofar dakin nan bari ta samu damar dan gyara wajan sannan ta dauko zani cikin kayansu ta shimfiɗa wa Umma ta zaunar da ita daga nan ta shiga dakin tsaye tayi tana bin sa da kallo wani haushi da takaici gami da tukukin bakin ciki suka cika mata zuciya sosai take ganin yarda dakin ya sauya gabadaya kamar dakin mahaukata kallo take tana tunanin ta ina ma zata fara gyaransa don ta san tabbas wannan dakin ba zaunuwa zai yi ba haka kwafa tayi sannan ta fito daga cikin dakin Umma ta duba cikin yanayi na damuwa.

“Bari na siyo tsintsiya Umma domin wannan dakin ba zaunuwa zai yi ba dole a gyara shi”.

Gyada mata kai kawai tayi itama ba tare da ta sake cewa komai ba ta duba cikin kayan su gudan duba ta dauko cikin kudin da Dr.Aqeel ya bata ta fice daga cikin gidan bisa mamaki har yanzu suna nan ba su tafi ba baki ta saki tana duban su kafun ta taka ta isa wajan su.

“Uhmm wai har yanzu…”.

sai kuma tayi shiru ba tare da ta karasa abin da tayi niyyar cewa ba ganin irin kallon da Dr.Karami yake yi mata na alamun tuhuma.

“ina zaki je kuma da wannan ranar daga dawowarku?”.

Shiru tayi kamar ba za tayi magana ba can ta nisa.

“tsintsiya zan sayo dakin zan share yayi kura ne sosai da sosai ba zai zaunu ba”.

ta karashe tana mai yatsine fuska kamar za tayi kuka sosai take jin wani iri a ranta ba ta so ta fito ta tadda su ba ba ta so a wanna lokacin ta sake saka su a idanuwanta ba ta so ace yarda ta baiwa zuciyarta hakurin kewarsu na dan lokacin nan suma sun yi hakan sun tafi ba za ta so wani sabon lamari ya sake afkuwa ba a nan wajan domin ba zata manta tsawon lokacin da suka shafe a nan wajan ba tun isowarsu ake abu daya sai da Umma tayi da gaske sannan suka shiga cikin gidan bayan sun yi sallama amma kuma abin mamaki ta fito ta tadda su.

STORY CONTINUES BELOW

“Bari naje na sayo Umma na jira na”.

Ta fadi cikin yanayi na damuwa domin ba za iya tsayuwa tana kallon su ba sosai take jin zuciyarta na zafi da raɗaɗi ba ta jira cewarsu ba ta  fara tafiya cikin yanayi na sanyi jiki sosai ko da ta isa shagon mai tazara kadan da gidan su makalewa tayi taki dawowa tana hango su ba ta ga alamun suna da niyya tafiya ba sam! ita kuma ba ta so su sake gamuwa a cikin halin da take ciki a yanzu so take ta bai wa zuciyarta hakuri so take ta fara koyon zaman kadaici tun yanzu don ta san tabbas dole wata rana su dau lokaci mai tsayi kafun su hadu kuma ya zame mata tilas ta yi abin da Ummanta ba za ta shiga damuwa ba dole ta kau duk wata damuwa a zuciyarta don ganin walwala ga Ummanta.

Numfashi taja kafun ta hango sun shiga motarsu ta lura sosai kamar sun damu da rashin dawowarta kuma ta san saboda su taki dawowa don haka suka yanke hukunci tafiya hakan yayi mata dadi sosai da sosai sai da taga sun fice daga layin su sannan ta tako cikin sarsarfa domin a tunanin ta kila su dawo.

*****

“Mun shiga uku”.

Cewar Hafsi tana daura hannu akai idanuwa warwaje kafun ta sake jan numfashi mai dauke da tashin hankali.

“ki ka ce mani sun tafi kenan har abada ba za su dawo ba, amma kuma ga su sun dawo kuma kin ce mani Habeeba ta zama MAHAUKACIYA amma dube ta kalau ba alamun hauka a tare da ita”.

Goggo Marka da ta yi zaman yan bori kofar daki ta zabga tagumi tana duban Habeeba da ɗan dake hannunta wasu katangun tashin hankali taji suna rigizo mata akai ji take yi duniyar na juya mata ba ta yi zaton haka zata faru ba bata taba kawo hakan akan ta ba ta yi zaton sun tafi kenan ko duriyar su ba za a sake ji ba a duniyar nan tuni ta saki jiki take shan sharafin ta ganin lokaci sai tafiya yake yi kuma ba su dawo ba hakan ya kara gasgata mata zatonta amma yau rana tsaka irin wanna mugun abu ya zo mata wani numfashi taja ta fesar kafun ta dubi Hafsi murya kasa-kasa domin bata so Habeeba ta ji maganganun da suke yi.

“tuni fa aka tabbatar mani da ta haukace ita da ‘yar ta ta da mijin nata…”.

Da sauri Hafsi ta katse ta.

“Injiwa ya fada miki to wallahi duk wanda ya fada miki hakan karya ne ki dube su fa su duka kalau suke ba abin da ke damun su”.

Nisawa tayi ta kai hannunta ta na susar kanta.

“ina ganin mugun abu kenan da gaske Habeeba ba hauka tay…”.

Sallamar da Mariya tayi ne ya katse musu hirar da suke yi sukayi wuri-wuri da ido alamun rashin gaskiya  kallo daya tayi musu ta kau da kanta a jikinta take ji akwai maganar da suke yi wanda ya dangance su kunuwanta sun jiyo mata kalmar hauka da Goggo Marka take fadi a zancen hakan ya tabbatar mata da Ummanta suke yi wato hauka tayi kenan daukar ta suke a matsayin  mahaukaciya wani kunci taji ya tokare mata kirji sosai taji ranta na ɓaci amma sai ta share su ta baiwa banza ajiyarsu ta isa in da Umma kenan zaune ta zabga tagumi da alamun ita ma ta ji hira da suke yi a kanta don idanunta har sun tara kwalla kadan.

Sauko da Mu’azzam tayi barci ya ke yi hankali kwance a haka ta mikawa Umma shi ba tare da tace da ita kala ba ta dauki tsintsiyar da ta sayo ta shiga dakin a hankali ta fara tattara kayan su waje daya ta na fitowa da su waje zuciyarta na kunci da bakin ciki sosai take jin tausayin kan su sosai take hango irin kalar zaman da za suyi a gidan nan duba da tayi da halin Goggo Marka yana nan yarda yake ba sauyawa tayi ba  sai abin da ya ci uban na da sosai take ganin za su fuskanci yanayin rayuwa a gidan musamman yanzu da suka kasance su kadai ba mahaifinta wanda shi kadai suke samun sauki a wajan sa to yanzu baya nan Allah kadai yasan halin da za su shiga cikin wannan halin ta hau tsaftace dakin yayi kura sosai bayan ta kwashe komi ta samo ruwa ta yayyafa a dakin saboda ba simitin in tana sharewa kuma kura na tashi sosai a haka cikin jarumta ta kammala sharewa sannan ta fito ta barshi ya sha iska kayan su ta ajje su gefe domin sun yi datti sosai suna bukatar zama na musamman domin wanke su sai da ta zauna ta huta sannan ta sake fita ta sayo kayan wanki sabulu da omo ta zo ta ja ruwa sosai ta jika kayan duk abin da take yi akan idon Goggo Marka da Hafsi sai faman bin ta da kallo suke suna faman yatsine fuska kamar sun ga abin kyankyami..

STORY CONTINUES BELOW

*********

Satin su Mariya biyu da dawo gida izuwa lokacin mutanan unguwa da yawa sun san sun dawo ana ta zuwa musu barka da arzuki da kuma ya mai jiki a nan suke samun labari wajan mutanan gari wai ai Habeeba hauka cewa tayi ta shiga duniya tun da ta haihu cutar hauka ta same ta ba a san in da take ba Mariya da babanta kuma suma sun ba zama duniya ne neman ta tun da suka tafi ba labarin su.

Abin yayi matukar daurewa Umma da Mariya kai sosai suka ji a ransu bisa wannan mugun fata da akayi musu na halaka ko daya ke ba suyi mamaki ba tun da sun san halin wacce ta kulla musu wannan makircin kadan daga aikin ta.

Ba su ce da ita komai ba sai dai suka barta da Allah domin kuwa halinta yafi karfin su.

Kamar ko yaushe yau ma Mariya na goye da Mu’azzam tana dauraye musu kayansu domin tun da suka dawo ko tsinke ba ta bari Umma ta dauke komai ba ita take yi rainon Mu’azzam duk yana wajan ta tun da ba nono yake sha ba sai madara anyi anyi amma ina yaki kamawa ko ya kama ya fara sha sai ya saki dole ta kasance madara ake bashi.

“Mariya”.

Ta jiyo muryar Umma ta na kiranta  da sauri ta ajje wanki tana amsawa ta doshi dakin.

“Yawwa yar Albarka amshi nan maza ki je gidan kultum ki sayo mani tafarnuwa”.

Da mamaki Mariya ta dubeta.

“Umma Tafarnuwa kuma, me zakiyi da ita?”.

“Yaa Allah! Mariya kenan. ba  fa wani abu bane zan yi da ita kawai kafafuwa na ne naji suna rikewa na san kuma sanyi ne ba wani abu ba shine fa zan yi amfani da ita”.

dan tsuke fuska tayi alamun rashin son abin da Umma tace.

“kawai ki bari Yah Dr.Karami ya zo sai a fada masa ƙafarki na ciwo nasan zai baki magani ni kam ban yarda ki yi amfani da tafarnuwar nan ba tun da ba likita bane yace ki yi amfani da ita”.

Murmushi tayi ta san halin Mariya sarai tun da ta warke a cutar nan in dai za tayi abu to tabbas sai taji daga bakin Dr.Karami tun da yana zuwa musu lokaci lokaci ya duba jikin Umma.

“Shikenan naji taimaka dai ki sayo mani na ajje in ya zo duk abin da ya ce dashi zan yi amfani”.

Fuskar a dan tsuke ta amshi kudin ta ficewarta Umma na bin ta da ido murmushi a fuskarta sosai take jin kaunar ‘yar ta ta a ranta sosai yanayin rayuwarta take burgeta da komai na ta godiya take yi wa Allah da ya bata ‘ya kamilalliya mai natsuwa da sanin ya kamata duk da karancin shekarun ta hakan bai hana ta sanin ya kamata ba idanuwanta lokaci guda suka kawo kwalla.

“Ina ka shiga ne ina son ganin ka a duniyata ya Allah duk in da wannan bawan naka yake Allah ka tsareshi ka tsare masa rayuwarsa ya Allah ka karkato masa da hankali ya dawo gaban iyalansa suna matukar buƙatarsa”.

A bayyane take zancen zuciyarta take ji tana yi mata zafi tun lokacin da ta tsinci labarin tafiyar mijinta shikenan komai ya kara jagule mata ta rasa ina zata sa kanta abubuwa da yawa sun rikita mata rayuwa ita ba dangi ba ita ba iyaye ba sannan gashi yanzu miji ba ta san a halin da yake ba  sosai take godewa Allah da irin ƙaddarar da ta samun kan ta a ciki sosai take goɗewa Allah da irin jarabtar da ya jeho mata cikin rayuwarta.

Dauke hawayen ta sake yi tana mai gyaɗa kai ita kadai ta san abin da take ji a zuciyar ta da kasan ruhin ta sosai rayuwar duniyar nan ke tsorata ta sosai take tsorota da komai na duniyar nan baki dayan sa.

STORY CONTINUES BELOW

*******

Sosai zuciyarta ta buga lokacin da idanuwanta suka hango mata shi zaune saman motarsa ya tallaɓe haba kamar wanda aka aikowa da mutuwa cikin dangin sa runtse idanuwa tayi gani take kamar a mafarki ba gaske ba laɓɓanta ta tura cikin baki tana cizawa a hankali zafin da take ji yana ratsa ta ya tabbatar mata da gaske shi din ne ba wani ba.

Kallon sa take da duk wani yanayi da ta tsinci kanta sosai ta hango sauyin yanayi game dashi sosai ta hango canji a gareshi ba kamar kwanakin baya ba wani abu taji yana mata yawo a zuciya sosai take jin  jikinta na sakin wani irin yanayi yana kaiwa ga kafafuwanta kamar ba za su dauki gangar jikin ta ba.

“Yaa Rabbi!”.

Ta fadi tana mai kau da kanta tana gargaɗin zuciyarta da ta daina abin da take yi akan Huzaif…

“Mariyaaa!”.

Kamar daga sama ta jiyo sautin amon muryarsa mai cike da wani irin yanayi wanda ba ta san yarda zata ce yake ba amma dai da alamun rauni a cikin ta dago kanta tayi ta hango ya sauko daga kan motarsa ya doso in da take da sauri ta juya za ta koma cikin gida domin ba zata iya tsayuwa dashi ba sosai take jin ta a wani mataki wanda ya canza mata komai nata yake yaki da natsuwarta yake haifar mata da abubuwa masu tsoratar mata da zuciya da gangar jiki.

“Don Allah…”.

Tsak! ta tsaya ba tare da ta waigo ba jin abin da yace sosai taji wani abu a muryarsa wanda ya kara rikita mata zuciya da kwakwalwa.

“Ban san mai zance miki ba, ban san abin da ya dace na fada miki ba wanda zai canza komai da komai a idanuwanki”.

Nisawa yayi yana mai dafe kansa da yaji yana wani irin juya masa kamar zai watsar dashi a kasa bai san abin da zai ce da ita ba bai san abin da ya dace yace da ita ba bai san ya akayi ya zo nan wajan ba bai san akan abin da  kawo shi nan ba gashi dai ga Mariya amma shi a karan kan sa bai san mai zai ce mata ba.

Sosai ta  gane inda ya dosa sosai ta fahimci akwai abin da ke addabar zuciyarsa.

“Kayi hakuri na san ban kyauta maka ba…”.

“Please Mariya mana”.

Ya yi saurin katse ta jin abin da take fadi sosai ya ji wani iri a zuciyarsa.

“Ni ya dace na baki hakuri ni ne nayi miki laifi ni ne na aikata miki ba daidai ba afuwarki nake nema ba ban yi zaton kalamai na za su sanya ki ki tsane ni ba…ko da yake komai ya faru ni na jawa kai na don Allah kiyi hakuri”.

Wani irin nauyi taji kanta yayi mata sosai taji rashin dacewa sosai taji kunya ta kamata ace mutum kamar Huzaif yake bata hakuri ta ya ya hankali zai dauka anya kuwa ba wata manufa a zuciyarsa anya kuwa zata yarda da maganarsa domin ita tun haduwarsu ta farko ta raina wa a zancin sa sosai ta gane bai iya lafuza ba…

“na san dole ki ji ba dadi a ranki amma duk da hakan ki daure ki yafe mani Mariya sosai da sosai na shiga tashin hankali a rayuwa tun haduwa dake na kasa sukuni komai nawa na rasa gane kan sa na sani kece…kece silar  komai ya faru kuma na sani nine ban da gaskiya”.

“Na yafe maka Allah ya yafe mana baki daya ni dama ba kayi mani komai ba”.

Sosai ta gaji da maganganunsa shiyasa ta katse masa hanzari da amsar bukatarsa.

STORY CONTINUES BELOW

Wata irin a jiyar zuciya yayi kafun ya dubeta da wani irin kallo.

“Na gode sosai Mariya”.

Gyaɗa kai tayi kafun ta dago idanuwanta ta dube shi sosai taji gabanta ya fadi saboda wani irin kallo da taga yana yi mata sosai taji wani iri a ko ina nata da sauri tayi kasa da kai.

“So Fine Boy waye wannan yaro mai kyau dashi”.

Ya fadi yana shafar kansa.

“Kanina ne”.

Ta fadi a hankali sosai taji dadi da yabon da yayi wa Mu’azzam hakan ya kara rage haushin sa da take ji.

“Don Allah bani shi  mana mu gaisa”.

Ya fadi yana mai kasa da murya gami da mika mata hannu a hankali ta kwance Mu’azzam ba tare da komai ba ta mika masa wata irin runguma yayi masa gami da manna masa kiss a fuskarsa a daidai lokacin Mu’azzam ya buɗe idanuwansa yana kallon Huzaif murmushi yayi masa shima nan da nan ya wangale masa baki hakan ba karamin burge Huzaif yayi ba sosai ya shagala da kallonsa yana yi masa wasa har ya so mantawa da Mariya ma a wajan.

Sai da tayi gyarar murya sannan ya dago ya dube ta da murmushi a fuskarsa.

“Yana da kyau sosai ina son sa.

Ya sunansa?”.

“Ibrahim amma Mu’azzam muke kiran sa”.

“Nice Name sunan nashi ya dace dashi sosai, ya fi ki kyau fa”.

Ya fadi da sigar zolaya

Dariya tayi kadan kafun ta mika masa hannu.

“kawo sa Umma ce ta aike mu fa?”.

Ba musu ya mika mata shi

Kamar daga sama sai ga Hafsi tsaye akan su ta na duban su daya bayan daya a sheke Huzaif ya dube ta sannan ya dubi Mariya kau da kan ta tayi hakan da ta nuna sai ya karanci wani abu game da ita shima sai ya tsuke fuska kamar ba shi bane yake yiwa Mu’azzam wasa yanzu.

Tsaki ta ja ganin sun ba banza ajiyar ta tayi cikin gidan tana kunkuni.

“Sai anjima ma ko nagode”.

Ta fadi tana juyawa da sauri ya tsaida ita yana mai sanya hannu cikin aljihunsa kudi ya zaro masu dan dama ya mika mata.

“Gashi ki sai wa Mu’azzam cakulat sannan don Allah in kin shiga ki gaida Umma”.

Irin kallon da ya ga ta na yi masa ne mai cike da tuhuma da ban so abin da kayi mani ba duk sai ya tsargu jikin sa yayi sanyi duk sai ya ji ya rikice ya rasa ma mai zai yi.

Girgiza kai tayi kafun ta saki wani murmushi.

“Uhmm rike kudin ka na gode sosai”.

Ta na fadin haka ta taka kafa da sauri ta bar wajan kallo ya bita dashi yana faman gyada kai kamar wani kadangare har takule a sabule ya mai da kudin sa aljihu ya jima a tsaye cikin nazari kafun ya ja kafarsa ya isa wajan motarsa ya bar unguwar cike da abubuwa masu girma da suka saka zuciyarsa nauyi.

Duk abin da yake yi Mariya na laɓe a zauren gidan da tashige tana kallonsa sosai taji ya bata tausayi sosai take jin wani irin abu game dashi a zuciyarta musamman yarda ya baiwa Mu’azzam kulawa duk sai taji duk wani kunci da take ji game dashi yana bacewa daga filin zuciyarta gyaɗa kai tayi ta kara sa cikin gidan ta sayo tafarnuwar ta fito a hankali take tafiya zuciyarta na ta kawo mata abubuwa masu yawa suna samun gurbin zama a kofar gida ta ja burki ta tsaya tana gyara goyon Mu’azzam.

Horn taji anyi mata a bayanta da sauri ta juya gabanta na faduwa duk a tunaninta Huzaif ne ya dawo amma sai ta ga akasin hakan Dr.Karami ne zaune cikin motarsa ya zuru kafafuwansa waje ya sauke gilas din yana kafe ta da idanu sai faman murmushi yake yi ita ma murmushi tayi tana mai yin kasa da kai.

A hankali ya mike kan kafafuwansa ya karasa fitowa ya kulle motar yana takowa zuwa gareta har lokacin kanta na kasa.

“My Boy ya kake?”.

Ya fadi yana taba Mu’azzam shi kuma sai faman zillo yake yi alamun yana so yaje wajan sa sosai suka saba tsakaninsu sosai Dr.karami yake son Mu’azzam in dai ya zo gidan to tabbas Mu’azzam na hannunsa har sai ya tashi tafiya.

“Ina yini”.

Ta fadi kanta a kasa bai kula ta ba illa kokarin zare Mu’azzam da yake yi a bayan ta ganin haka ya sanya ta kwance shi.

Daukarsa yayi ya rungume shi yana mai manna masa kiss shikuwa sai faman Dariya yake yi.

“me kika fito yi waje tare dashi da ranar nan?”.

“Umma ce ta aike ne sayan tafarnuwa”.

Kallon hannunta yayi ba tare da ya ce da ita komai ba ya fara taka kafafuwan sa zuwa cikin gidan domin ba ai masa shamaki ba Umma ta bashi dama ya dinga shigowa duk lokacin da ya zo ya daina tsayawa a waje.

Mariya bin sa tayi a baya har suka isa cikin gidan bakin Kofa suka hango Hafsi baje tana cin awara tayi ɗaiɗai da kafafuwanta sai faman jan hanci take yi tana gumi alamun yaji yayi yawa ko kallon su ba tayi  ba su ma ba su bi ta kan ta ba sukayi sallama dakin Umma su ka shiga bayan ta ba su izini.

Bayan sun gaisa nan Mariya ta shiga korawa Dr.karami bayani akan tafarnuwar da ta sayo wa Umma dariya yayi sosai kafun ya numfasa.

“Mariya iyayen tsari to ai ba wani abu bane tafarnuwa tana da amfani sosai a jikin mutum ba ta da illar komai ana so mutane suke amfani da ita sosai ko a cikin abinci ne domin magani ce kamar yarda kika ji Umma ta fadi don haka sai ki kyale tayi amfani da kayanta”.

Dariya Umma tayi mata itama dariya tayi tana mikawa Umma tafarnuwar.

Shiru ne ya gifta tsakanin su na yan dakiku kafun Dr.Karami ya ja numfashi ya dubi Mariya sannan ya dubi Umma.

“Umma dama akwai maganar da nake so muyi game da Mariya akan karatun ta ya kamata ace ta koma makaranta zaman ta hakan ba zai yuwuwa ba ya kamata ace a yarda take da kuruciyar ta ace tana makaranta yanzu”.

shiru Umma tayi tana gyaɗa kai sosai taji dadin maganar Dr.Karami domin tafi kowa son Mariya tayi karatu domin karatun Mariya abu ne mai muhimmanci a garesu dama al’umma baki daya sai dai WANI HANZARI ba gudu ba ba a nan gizo ke saƙar ba…

“Umma karki damu nasan abin da kike tunani wannan duk ba wani abun da zai gagara ba ne ni aka ran kai na nayi alkawari zan dauki nauyin karatun Mariya tun daga yanzu har zuwa lokacin da zata kammala shi”.

Wani irin duban hanzari Umma tayi masa tana girgiza kai ba ta san wani irin mutum bane shi sosai ta fuskanci mutum ne shi mai yaƙana da alheri a rayuwarsa ba abin da ya hada su ba dangin iya babu na baba amma jibi yarda yake dawaniya da su tun daga lokacin da ta shiga matsalar cutar ta har zuwa wannan lokaci bai gajiya ba ga shi yanzu ya dauko wani gagarumin aiki wanda ya kamata ace su iyayenta ya dace ace duk sun yi sa.

rintse idanu tayi wasu hawaye suka zubo mata ganin hakan ya sanya Dr.Karami saurin dubanta.

“Don Allah Ki daina wannan kukan bai dace da ke ba sam! Addu’a ya kamata ace kin yi kawai Allah ya tabbatar da alheri”.

“Hisham ban san da bakin da zan gode maka ba kayi mani komai na rayuwa ba tare da kasan su waye mu ba nagode sosai Allah ya saka maka da alheri ya cika maka burukan ka na alheri ya kare maka rayuwa da zuri’a” .

“Ameen Summa Ameen”.

Ya fadi yana duban Mariya wacce tayi kasa da kai tana faman hawaye sosai ya ji ba dadi a ransa ba zai iya cigaba da zama yana ganin hawayen su ba don haka ya mike ya na mai ajje Mu’azzam.

“Zan tafi Sai gobe kuma in Allah ya kai mu zan zo domin yin abin da ya dace”.

Ya na fadin haka ya fice daga cikin dakin ya bar su Mariya shanye da baki suna duban junansu…Dubansa take yi da wani irin yanayi na na raina wayonka da azanicin ka kafun ta kau da kai tana mai sakin guntun tsaki ta nisa cikin yanayi na haushi.+

“Ban san mai ya hau kan ba Dr.Erena sosai ka bani mamaki ban taba zaton kalaman nan za su iya fitowa ɗaga bakin ka ba ka dube ni up zuwa down ban yi maka kama da mai karamin tunani irin naka ba aiki na zo yi a wannan company ba zaman zance mara kan gado ba”.

Ta karashe tana mikewa kan kafafuwanta fuskar dauke da tsananin bacin rai sai dai kuma acan kasar ruhinta da zuciyarta ba haka bane domin kuwa murna take har da tsalle-tsalle Dr.Erena ya kusan fadowa komarta abin da ta jima tana KUDIRI da muradin tabbatarsa kenan.

“Areef..”.

Da sauri ta daga masa hannu kafun ta dauki jakarta dake ajje kan table din Office din nasa.

“Ya isa haka bana bukata ban so ka takura min, in kuma kace takura min zakayi wallahi yanzun nan zan rubuta maka takardar ajje aiki…”.

Da sauri ya mike jin abin da take fadi jikinsa har ɓari yake yi ya iso inda take tsaye ya kafeta da idanunsa da suka gama tafiya a duniyar Areefa.

“No Please ba sai mun je wannan matakin ba…But Areefa ya kamata ki fahimce ni mana  alkawari nayi miki komai kike so kuma ko me kike so ayi na miki alkawari…”.

Da sauri ta watsa masa wani kallo wanda yake kara rikita masa lissafi kafun ta tsume fuska.

“Ban san ta ya  zan maka bayani ka fuskanta ba Dr.Erena ban san da wani irin kalami zan yi amfani ka gane abin da nake nufi ba”.

Tana gama fadin haka ta fara taka kafafun ta ta doshi kofar fita zuciyarta cike da abubuwa masu matukar yawa.

Shi kuwa shanye baki yayi yana kallonta har ta fice kafun ya ajje wani numfashi mai karfi ya koma ya zube kan daya daga kujerun Office din nasa.

******

First Class International School Gwada.

Sosai farinciki ke wanzuwa a fuskarta tun lokacin da Dr.Karami ya danko ta  daga gida zuwa haɗaɗɗiyar makarantar da ya zaba mata zata cigaba da karatun ta.

Zaune take zuciyarta falla da farinciki mara musaltuwa har da guntayen hawayen na farinciki duban Dr.Karami take cikin wani irin yanayi wanda ita kanta ta kasa tantacce matsayin da take ji ya samu a zuciyarta sosai take jin matsayi mai girma game dashi a filin zuciyarta sosai take jin komai na canzawa a duniyar rayuwarta a yau daya kadai sosai take hango mafarkinta zai tabbata na son karatu da ta jima tana rokon Allah ya bata damar da za tayi shi yau gashi Allah ya jeho mata Dr.Ƙarami mutumin da bata taba zaton za ta gan shi a duniyar mafarkin ta ba balle a zahiri amma gashi Allah ya kawo matashi ta hanyar da bata yi zato ko tsammani ba.

Numfashi ta ja kafun ta dago kai ta na kallon Office din da ta baro shi a ciki shi da shugaban makarantar suna zantawa.

Kamar daga sama taji an dafa mata kafaɗa da sauri ta dawo daga duniyar tunanin da ta fada dago kanta tayi ta sauke kan wata matashiyar yarinya wacce a shekaru za suyi kai daya sai faman murmushi take sakar mata cikin yake ita ma Mariya ta sakar mata da martani.

“Sannu ko sunana Baseera Haruna Sa’eed ni sabuwar daliba ce da Dadyna ya kawoni yau ke ya sunanki”.

Mariya da ta saki baki da idanuwa ta na kallon ikon Allah sai yanzu ta kyafta idanu kafun ta sake murmushi tana motsa laɓɓanta cikin mamaki da wannan kanzagi da zalaka na wannan yarinyar sai kace ta tambaye ta saki baki sai ratata zance take yi kamar an kunna rediyo ana sauraron shirin INDA RANKA.

STORY CONTINUES BELOW

“Karki damu haka nake shi kansa Dadyna aku yake ce mani wai na fiye surutu shiyasa yace kawai nafi dacewa na zama yar jarida”.

‘Kuma dai!’

Mariya ta fadi a zuciya tana tallaɓe haɓa kafun ta nisa.

“yo ai ni kin hanani ma cewa komai sai zuba kike yi dole dadynki yace dake Aku ke ba ki san ni ba nima ban sanki ba amma kin saki baki sai watso mani zancen ki ke kamar na tambaye ki”.

Da sauri ta caɓe.

“Woohh ai na san ke ba mai cutar wa bace daga ganinki kina da kirki da natsuwa sosai da sosai domin dady yace in zan yi abokiya na samu mai natsuwa ba irina mai shegen surutu ba”.

Dariya sosai Mariya take yi har tana rufe bakin ta mamaki take yi da halin Baseera sosai da sosai taji lokaci guda taji ta kwanta mata rai.

“to ni dai zancen ya tsaya nan naji abin da Dadynki yace yanzu dai ke a ina kike kuma aji nawa kike…”.

yarfar da hannu tayi tana mai yatsine fuska.

“wai fa ss-1 nake daga makarantar da muka baro da yake dadyna ma’aikaci ne sai aƙayi masa canji aka kawo sa nan garin shine zai canza min makaranta wai sai dai a mai dani js-3 ki ji fa don Allah ai wannan ci baya ne kamar ni kuma fa ina da kokari sosai da sosai…”.

“Yaa Allah! Baseera wai don Allah bakin ki baya ciwo ne don Allah tsaya ki ja numfashi mana”.

Mariya ta tare ta tana mai kama hannunta ta na zaunar wa kan kujerar da take zaune a kai.

“karki damu akan haka nima yanzu placement zan rubutu na tafi ss-1 kin ga kawai sai mu tafi tare…”.

Wata irin zabura tayi tana dariya.

“da gaske ki ke don Allah to shikenan ma na hakura da fa balli na tayar nace ban yarda ba amma tun da kin ce haka zan zauna saboda ke my abokiya”.

“Yaa Allah Baseera Oh My God wai ke don Allah yaushe zaki yi hankali ne Yaa Allah!”.

Wata murya ce suka ji kamar daga sama tana fadin haka da sauri Baseera ta zabura tana dosar mutumin da yake tsaye nesa dasu hannayensa sarke a kirjinsa sai faman kallon su yake yi da yanayi na damuwa a fuskarsa.

“dadyna zo ka ga my new ƙawa wallahi mai kyau da ita ga ta da natsuwa irin ƙawar da kace nayi…”.

Janyo ta yayi yana jan kunnan ta wata karamar kara ta saki.

“Dady Please don Allah ba zan sake ba”.

“Ban san yaushe zaki girma ba Baseera ke ko gajiya ba kya yi da surutu haba mana! a ko ina sai kin nuna halin ki nikam zan ce ma na fasa saka ki a makarantar ba zan iya da rawar kan ki ba…”.

“wayyo Allah dadyna Please for give me I’ll never do that again”.

Yanayin da ta marare ce taka langwashe murya ya sanya shi dungure mata kai yana murmushi halin Baseera sai ita duk yarda ta san zai sanya ka ki daukar hukunci akan ta ta sani.

“Zo mije ka ga my New Ƙawa please dadyna”.

ta fadi tana jan hannunsa shi kuwa sai fizgewa yake yu  amma taki dai nawa  har sai da ya bi ta sannan ta daina magiya har zuwa lokaci Mariya na zaune idanuwanta akan su duk abin da suke yi tana kallo wani burgewa da sha’awa suke mata sosai da sosai taji Baseera da mahaifinta sun burgeta yarda suke kulawa da juna da nuna soyayya tausayin kanta take tana tuno nata mahaifin in da yana nan da shi ma haka zai nuna mata soyayya fiye ma da ta Baseera amma ina! hakan ya gagara ƙaddara ta rabata dashi rabuwar da ba ta san a wani hali yake ba ba ta san yaushe ne zai dawo duniyarsu ba su cigaba da rayuwa a tare a inuwa daya.

STORY CONTINUES BELOW

Tsiwar Baseera ce ta dawo da ita duniyar zahirin ta daga ta tunani nisawa tayi taja murmushi kafun ta dubi mahaifin Baseera da yake tsaya yana dubanta.

“Ina yini dady”.

Mariya ta fadi cikin muryarta mai sanyi da girmamawa a ciki.

Sosai yaji ta burgeshi sosai yaji yana so su kulla ƙawance da yarsa ya lura akwai natsuwa da hankali a tattare da ita.

“lafiya yau ya hakuri da aku mai bakin magana”.

Murmushi ta saki don ta fahimci in da ya dosa da maganar sa kasa tayi da kai tana mai amsa masa.

“Dadyna ka ga ba ta fada min sunanta ba amma ni na fada mata”.

Baseera ta fadi tana mai duban Mariya da take kallonta fuskarta dauke da murmushi.

“Yaa Allah! ta ya ya za ta fada miki bayan kin cika mata kunne da surutu Allah yasa ma tace ba za tayi kawancen ba…”.

“Dadyyy!”.

Baseera ta fadi da rigima a muryarta kamar zata fashe da kuka duban Mariya tayi cikin yanayi na mararecewa.

“Please don Allah fada min sunanki kin ji in ba haka ba nace ba zan yi makarantar ba ma”.

Yanayin da tayi maganar da gaske take hakan ya baiwa Mariya dariya ganin da gaske take.

“sunana Mariya Bello Gwada”.

“woohh so Fastastic Nice Name”.

Baseera ta fadi tana mai kambama sunan Mariya.

Ya tsine fuska Mariya tayi kamar wacce aka tsikarawa allura da sauri Baseera ta ware idanu alamun tsoro tashiga tambayar ta lafiya mai ke damunta?.

Girgiza kai tayi alamun bakomai amma ita kadai ta san abin da take ji tun da ta tashi yau take jin wani iri a jikinta kamar bata da lafiya lokaci-lokaci take jin cikin ta da mararta na murɗa mata sai taji kamar numfashinta zai dauke amma ba wanda ta fadawa haka sai dauriya da take yi taki bari kowa ya gane sai dai in ya motsa mata take cizon laɓɓanta har ya lafa.

Miƙewa tayi jin mararta ta daure sosai tana faman cizon laɓɓanta sosai Baseera ta lura da haka da sauri tayi wa mahaifinta nuni da abin da Mariya take yi da sauri shima ya ware idanuwansa sosai akan ta kafun ya dafa kafadarta.

“lafiya Mariya me ke damun ki ko baki da lafiya ne?”.

haɗe jikinta tayi waje daya ji take yi kamar kayan cikin ta za su zubo kasa da sauri ta durkushe kasa tana mai sakin numfashi da sauri-sauri hakan da Alhaji Haruna ya gani ya sanya shi firgita kadan da sauri ya kamo ta sosai yana mai duddubata Baseera dake tsaye kuwa jikinta sai faman ɓari yake yi idanuwanta lokaci guda suka kaɗa sukayi jajir.

“Dady what is wrong?”.

Muryarta a raunane kamar mai son fashewa da kuka.

“Mariyaaa!”.

Muryar Dr.Karami da karaɗe wajan lokacin da ya fito daga office idanuwansa suka gane masa abin da ya sanya shi faduwar gaba idanuwansa a warwaje da sauri yayi jifa da ledar dake hannunsa ya tako cikin sassarfa kamo ta yayi sosai izuwa lokacin har ta fara ficewa daga hayyacinta hakan da ya gani ya kara tsora tashi da sauri ya dubi su Baseera da Mahaifinta cikin yanayi na tuhuma kafun ya kau da kansa cak! ya dauke ta yayi hanyar ficewa da ita daga wajan hakan da suka gani su ma sai suka rufa masa baya wajan da yayi Parking ya isa ya buɗe gidan baya ya sakata ya rufe kafun ya dawo gaba ya shige duk abin da yake yi cikin yanayi na tsoro da fargabar abin da zai je ya dawo key yayi mata kafun ya fizgeta ya bar harabar wajan suma Su Baseera motarsu suka hau suka rufa masa baya.

Wani clinic ya nufa da ita dake kusa da makarantar cikin sauri yayi parking ya zo ya sungume ta yayi ciki da ita  ba wani bata lokaci aka amshe ta kayi emergency da ita sosai Dr.Karami ya shiga tashin hankali ba abin da yake tsoro illa wani abu ya samu Mariya bai san abin da zai ce da iyayenta ba bai san da wani ido zai kalle su ba bai san a me za su dauke shi ba fata yake yi Allah ya saukaka lamarin Allah yasa ba wani abu ne ya same ta ba.

STORY CONTINUES BELOW

Kafadarsa yaji an dafa hakan ya san yashi tsayawa cak! daga Safah da Marwa da yake faman yi a kofar dakin da aka shigar da Mariya da sauri ya juye ya dube shi shima shi yake kallo kafun ya kau da kai bai san shi ba bai ma taba ganinsa ba amma sosai zuciyarsa ke nazarin mutumin domin kuwa abun da yafaru da Mariya a wajan su ne yana zargin su komai ya faru da ita su ne sila numfashi yaja kafun ya sake dubansa.

“Mene ne hadinku da Mariya mai kuka mata?”.

Abin da ya fadi kenan muryarsa da zurfi a cikinta yana faman haɗe fuska waje daya.

Sosai Alhaji Haruna yayi murmushi kafun ya bugi kafadar Dr.karami kadan.

“Haba mana abokina karka zarge mu da komai a kan yar uwarka ba abin da muka yi mata…”.

“Ta ya kake so na yarda da

maganarka…”.

Kafun ya dire ya jiyo muryar Baseera cikin kuka tana cewa ‘Ina Mariya?’.

Mamaki ne sosai ya cika sa ya shiga duban Baseera da alamun tambayoyi masu yawo sosai yake kallonta ko zai gane fuskarta amma ina bai ga alamun sanayya ba a tattare da ita kuma bai san taba balle yace yar uwar Mariya ce.

“ya kamata ka fahimci wani abu a kan Baseera ba mu da niyyar cutar da ita kamar yarda ka ganmu a yau mu ma haka a yau mu ka fara ganin ka Baseera Da Mariya cikin wannan lokaci suka hadu na kawo Baseera zan saka ta a wannan makarantar to a nan ta gano Mariya har take cewa dani tayi ƙawa shine fa na zo ganinta har mun gaisa ma sai naga ta shiga wannan halin Dan’uwa karka zargemu da komai wallahi  zuciya daya muke tare da ku ba mu da niyyar cutarwa gareku don nasan illar haka”.

Tun da ya fara magana Dr.Karami ke dubansa da idanunsa sosai ya fuskanci gaskiya a cikin kalaman sa sosai ya gane mutum ne mai kamal da hankali gami da natsuwa lokaci guda yaji kunyar abin da yayi domin kuwa Alhaji Haruna zai girme masa nesa ba kusa ba.

Murmushi yayi yana sosa keya kafun ya dubi Alhaji Haruna.

“Afuwan na tuhume ku akan abin da ban san ya yake ba kuyi hakuri Mariya amana ce a waje na dole in shiga yanayi in na ganta cikin wani hali”.

“kana da gaskiya hakan yayi daidai yanzu dai wani hali take ciki”.

Gƴaɗa kai yayi kafun ya nisa.

“sun shigar da ita ciki domin dubata…”.

Bai kai ga karasawa ba likitan da ya shiga duba Mariya ya fito yana duban su kafun ya ba su hannun suyi musabaha yana mai duban su daya bayan daya har ya dire kallon sa ga Alhaji Haruna.

“Kai ne mahaifinta ko?”.

Ya tambaya kafun ya dora.

“karka damu tana lafiya lokacin ta ne yayi nasu na  mata kuma bata saba ba shiyasa ta shiga wannan hali amma Alhamdulillah muyi settling din komai yanzu haka ta samu barci nan da 30mint komai zai zama normal”.

Hamdala sukayi su duka kafun Alhaji Haruna ya nisa.

“Muna godiya Doctor sosai da sosai Allah ya bata lafiya”.

“Ameen.Yanzu dai zan muku last na magungunar da za a sai mata tana amfani dashi”.

Gyaɗa kai sukayi Dr.Karami shi dai shiru yayi yana mamaki yarda Alhaji Haruna ya zage yana nuna shine Mahaifi gareta ba tare da nuna eh da gaske ba ‘yar sa ba ne hakan yayi masa dadi a rai lokaci guda yaji mutumin na burgeshi sosai da sosai.

Ko da ya dawo daga duniyar tunani mamaki ne ya sake kashe shi ganin Alhaji Haruna yabi likita Office din sa sakato yayi da baki ya duban hanya kafun ya dawo da kallon sa wajan Baseera da ta zauna ta zabga tagumi hannu bibbiyu kamar wacce aka aikowa da mutuwar wani a dangin su duk bakin surutu ya mutu kamar ba ita ba ce aku a dazu.

STORY CONTINUES BELOW

“Ya sunanki?”.

Dr.Karami ya fadi yana mai duban ta cikin yanayi na mamakin yanayin da ya ganta aciki kuma ya san duk a dalilin Mariya ne.

Ba ta an sashi ba illa kallo da ta yi masa tana mai sauke numfashi mai kwari sosai.

“C’mon Baby girl tell me your name…ko ba kya so ƙawancen da Mariya ne”.

Ba tayi niyyar ansa shi ba amma jin abin da yace ya sanya ta sauri dubansa da murmushin yake.

“Please don Allah karka hana Mariya ƙawance dani sosai nake son ta a raina a lokaci guda naji ta burgeni kuma Dadyna ya na son ta ya yaba da hankalinta sosai da sosai”.

“Oya C’mon tell Now”.

Murmushi ta saki ganin yarda  yayi mata cikin yanayi na wasa.

“Baseera Haruna Sa’eed”.

Sosai yake dubanta yana tunanin in da ya san sunan mahaifinta sosai yake zaton ya san sunan amma ya manta a ina ne ya san haka gyaɗa kai yayi kafun ya nisa fuskarsa da murmushi.

“Masha Allah to naji na amince kuyi ƙawance But…akwai sharaɗi kafun amincewar…”.

“Na yarda wallahi tell me”.

Ta fadi cikin yanayi na zagwadi dubanta yake yi sosai, sosai ya lura  Baseera irin mutanan nan ne masu barkwanci da wasa da dariya a ko ina suke.

“ban da wasa in an fara karatu ina so ku hada kan ku waje gudu sosai nake so naji ana alfahari da ku a cikin makarantar nan”.

“Promise”.

Ta fadi tana mai dariya burin ta ya cika na samun ƙawa a lokaci daya daga zuwa makaranta.

“hala tana nan tana yi maka halin nata na surutu kamar aku”.

Muryar Alhaji Haruna ta yanke musu hirar tasu Murmushi Dr.Karami yayi kafun ya dubi Baseera da ta cuno baki gaba alamun ba ta so abin da dady yayi mata ba.

“Yaa Allah! Ai ba za tayi ba tayi mani alkawari dainawa in kuma ta cigaba ba zan barta ta cigaba da ƙawance da Mariya ba”.

“yawwa kayi mani daidai”.

“kai dady”.

Baseera ta fadi fuska a shagwaɓe har sai da ta basu dariya su duka.

“ku tashi mu shiga mu duba ta ko?”.

Ya fadi yana mai dubansu ai kamar jira take cikin hanzari ta mike tayi hanyar shiga dakin har tana kokarin buge Dr.Ƙarami shi kam dariya abin ya bashi shikuwa dady dafe kai yayi kawai yana mai duban Dr.Karami yana mai masa nuna da ido yayi hakuri ba ta da hankali murmushi kawai ya yi yayi gaba.

Kwance suka tadda ita sai faman sharar barci take yi kallo daya zakayi mata ka gane ta ji jiki a dan lokacin don har fuskarta ta fada sosai

Dr.karami yaji wani iri a ransa ganin yanayin da Mariya take ciki ji yake yi kamar ciwon da yake jikinta ya dauko ya mai doshi nashi jikin bai son abin da zai sake taba mata rayuwa bai son abu ko ya yake ya rikita Mariya sosai yake jin tausayin ta sosai yake jin wani iri game da ita duk lokacin da take cikin hali na damuwa sosai yayi KUDIRI a zuciyarsa da ruhinsa da izinin Allah sai ya canza mata rayuwa sai ta ji dadin rayuwa sai taji dadin yan uwa sai ya zame mata yan uwan da take kwadayi a rayuwarta sai yayi iya kokarin sa don ganin ta fuskanci rayuwar ‘yanci duk wani kunci da damuwa sun bar duniyar ta sai dai bai san ta yaya zai yi wannan aikin ba bai san wacce hanya bace da zai bi amma dai zai yi iya bakin kokarin sa don ganin rayuwar Mariya ta zama normal like others.

Sai da suka shafe awa daya kafun Mariya ta farko sosai da sosai take duban su da idanuwanta da suke bude runtse idanu tayi ta shiga tunano abin da ya faru da ita wasu hawaye suka zubo mata a hankali ta ja numfashi kafun ta buɗe idanunwanta Baseera ta gani kusa da ita ta mai sakin mata murmushi ta sanya hannu ta dauke mata hawayen da suke zubo mata.

STORY CONTINUES BELOW

“Sannu ƙawata”.

Ta fadi cikin yanayi na taushin murya da jajantawa.

Ba ta ansa ba sai duban Dr.karami da tayi da ya tallaɓe haɓa ya zuba mata manyan idanuwansa masu firgita mata tunani gyaɗa kai tayi tana masa kallon tambayar me ke faruwa mai ya kawo ni nan?.

Sosai ya gane abin da take nufi amma sai ya kau da kai domin bashi da bakin da zai iya cewa ga abin da ke faruwa da ita so yake yi sai sun koma gida komai a natse sannan sai suyi magana sosai da sosai.

“ina ke miki ciwo Mariya?”.

Alhaji Haruna ya fadi cikin yanayi na tausayawa gyaɗa kai tayi alamun babu.

“Masha Allah haka ake so Allah ya kara lafiya ko Mariya”

Gyaɗa kai ta yi kawai sosai take hango karamin ci irin na wadannan mutanan daga haduwa amma sun yi mata abun da wasu nata suka gagara yi mata sun bata kulawa da duk lokacin su sun tausaya mata da halin da ta shiga sosai taji sun samu matsayi mai girma a zuciyarta sosai take hango martaba da karamci tattare da su bata da bakin da zata ce da su komai sai fatan alheri.

Ba su jima cikin asibitin ba bayan dube dube da likita ya sake yi mata ya tabbatar da ba komai ya ba su sallama domin tafiya gida a tare suka fita Baseera da Dady su ka hau mota daya ba don ta so ba don cewa tayi sai dai ta bi Mariya gidan su amma Dady yace tayi hakuri zai kai ta da kan sa zuwa da yamma suna cikin wannan yanayin ne Mariya  dake tsaye jingine da motar Dr.karami tana kallon diramar da ake yi da Baseera sosai taji wani abu a kafarta yana bin ta da sauri ta duba.

“Yaa Allah! Jini”.

Ta fadi muryarta da karamin sauti da sauri ta dubi wajan da suke tsaye tana duban su a daidai lokacin Baseera ta dubeta ganin yarda tayi da ido ya sanya tambayar ta ko lafiya nuni tayi mata da kafarta da sauri ta iso gareta tana dubawa to da yake zata girmewa Mariya a shekaru sai ya kasance ta gane abin da ke faruwa kuma dama dazu taji abin da likita ya fadi da sauri ta dubi Dady da Dr.karami.

“Dady muje da ita gida don Allah She need help please dady”.

Yanayin da tayi maganar sai ya sanya su duban Mariya da sauri don ba su gane akan me take magana ba.

Da idanu tayi musu nuni tsaf! Su ka gane ita dai Mariya kanta na kasa cikin hanzari suka shiga motar su suka dauki hanya da yake ba nisa gidansu Baseera tafiya kadan sukayi suka isa  Babban gida ne kallo daya zaka yi masa ka gane mai shi yana da rufin asiri sosai da sosai get ne babba mai ruwan blue sai ratsin gold da kayi masa Horn daya sukayi aka buɗe musu gabadaya suka shige ciki bayan sun yi Parking duk suka firfito ita dai Mariya duk a tsora ce take sai faman haɗe jikinta waje daya take yi da sauri Baseera ta kama ta sukayi cikin gidan a falo su ka tadda Hajiya Abida mahaifiyar Baseera babbar mace ce mai cikar kamala da mutunci sosai ta dubi Baseera fuskarta da tuhuma.

“ba dai har kun dawo ba ina dadyn naki yake?”.

Tana magana ta na duban Mariya da take haɗe jikinta kanta a kasa duban Baseera tayi da kallon karin bayani.

“later please Momy”.

Ta fadi tana zarcewa da Mariya in da dakin ta yake suna shiga ta zarce da ita Toilet duk wani abun bukata sai da ta tadanar mata kafun ta nuna mata duk yarda zata yi sannan ta fito ta bar ta a Toilet din ma’ajiyar kayan ta ta nufa ta buɗe wata doguwar riga ta fiddo gami da wani hijabi mai kalar pink da ratsin kalloli daban daban wanda suka karawa hijabin kyau sosai bakin kafcecen gadon ta ta ajje su sanna ta zauna ta na mai zabga tagumi mintina goma Mariya ta shafe a toilat kafun ta fito tana raɓe-raɓe kamar mara gaskiya da sauri Baseera ta mike ta isa wajanta.

“dafatan kin yi yarda nace ko?”.

Gyaɗa mata kai tayi domin wata irin kunya ce taji ta lullubet sai sunne kai take yi kasa.

STORY CONTINUES BELOW

“Uhmm Karki damu kin ji ko Mariya ba abin da zai sa me ki in Allah ya yarda”.

Kai kawai take gyaɗa mata a haka har ta taimaka mata ta kara gyara jikinta  bata kayan da ta dauko mata ta saka da kanta ta gyara mata fuska ta baɗe mata jiki da wani lafiyayyan turare mai sanyin kamshi.

Suna cikin kwalliyar ne Hajiya Abida ta shigo fuskarta dauke da murmushi tana duban Baseera.

“dakyau Auta ta kin kyauta da wannan taimakon da kikayi dadyn ku ya fada min komai dake faruwa”.

Murmushi Baseera tayi ita kuma Mariya kasa tayi da kai don kunya.

“‘Yawwa Mariya kisan mi yanzu lokaci ne da ya kamata ki kula da kan ki sosai ban da wasan banza ko kule-kule kuma don Allah karki sake ki kasance mai yawan zama cikin maza ke ‘ya mace yanzu girma ya kamaki dole kiyi taka tsantsan da rayuwarki domin abu kalilan zai ruguza miki rayuwa ba fata  ake ba amma tunatarwa na da dadi in Allah  ya yarda Allah zai kare muku rayuwa da sauran ‘ya’ya mata masu wannan lokacin Allah ya tsare muku rayuwa ku duka kin ji ‘ya ta Mariya”.

Sosai Mami tayi mata nasiha da tsoratarwa akan abin da zai rugaza mata rayuwa ba karamin dadi Mariya taji ba ta shiga mata godiya nan aka kawo mata abinci Mami ta saka ta gaba sai da ta ci sannan suka hada mata goma ta arzuki su ka rakota har falo in da Dr.Karami yake zaune da Alhaji Haruna  ba karamin bugawa gaban Dr.karami yayi ba ganin Mariya ta sauya lokaci daya kamar ba ita ba ya shiga cizon laɓɓansa don tabbatar da Mariya ce ba wata ba wani murmushi ya sakar mata kafun ya mike bayan yayi wa su Alhaji Haruna godiya da karamci da sukayi musu har wajan mota suka rakosu  nan Baseera ta sanar da Mariya anjima da yamma in sun taso islamiyya zata zo gidan su a haka sukayi sallama suka tafi zuciyoyin su fal da farin ciki mara musaltuwa.

Tun da suka baro gidansu Baseera ba wanda yayi magana a tsakaninsu Mariya sosai ta haɗe jikinta waje daya kirjinta taji yana bugawa a hankali ba abin da ke yi mata yawo akai sai abin da ya faru da ita da kuma irin maganganun da taji Mami na fada mata wanda ta tabbatar haka abin yake rintse idanu tayi ganin abin take yi kamar almara kamar cikin mafarki ba gaske.

A bangaren Dr.karami shima mamaki ne ya cika shi ko da yake in yayi duba da yanayin ta lokacin ta yayi a matsayin sa na likita zan iya gane haka wanda ma ba su kai shekarunta ba ma  sun yi balle ita da yake zaton za tayi 16years.

Da wannan tunanin da zuciyoyin su suke suka isa gida daidai kofar Gidan yayi Parking tsayuwar motar ne ya dawo da Mariya duniyarta da sauri ta dago kai dubi bangaren Dr.Karami da sauri tayi kasa da kai domin ita yake kallo a hankali ta sanya hannu ta buɗe kofar ta fice kamar daga sama idanuwanta suka hango mata abin da ya kusan sanyata sakin fitsari Huzaif ta hango zaune saman motarsa  ya haɗe kansa da gwuiwarsa bisa alamu ya jima a wajan zaune da sauri ta juya ta dubi Dr.karami wani irin kallo ta ga yanayi mata mai cike da tuhuma sosai ta hango wani irin yanayi mai kama da bacin rai a fuskarsa kasa tayi da kai da sauri ta fara taka kafafunta wanda take jin su kamar za su narke sosai take jin kanta na wani irin juyawa kamar zai dare gida biyu duk taku daya in tayi sai ta ja numfashin ta da taji yana barazanar daukewa ba ta kai ga shig gida ba taji kugin tsayuwar mota da sauri ta juyo Dr.Aqeel ta hango yana fitowa daga ciki motarsa idanuwansa akan ta sosai ta firgita ganin wani kallo da shima yake yi mata wanda bata san da me zata fassara shi ba a ranta ta furta.

“Yaa Allah! me ke shirin faruwa da ni ne?”.

Ai ba ta san lokacin da ta ja kafa tayi cikin gida ba sai faman haki take yi ba ta tsaya ko ina ba sai cikin dakin Umma ta baje kan katifar dake yashe cikin dakin sai faman sakin hirji take yi gabanta na faman bugu kamar zai tarwatse komai taji yana juya mata Umma da ke zaune ta shiga dubanta da mamaki da farko ba tayi zaton Mariya ba ce sai da ta kalleta sosai domin kayan da ke jikinta ba ta san ta da su ba tana kokarin yin magana ta tsinkayi sallamar Dr.Karami da sauri Mariya ta kara dunkulewa waje daya tana cusa kanta cikin hijabin dake jikinta gabanta na kara tsananta bugawa.

Ko ta kan ta bai bi ba Umma kawai yayi wa bayani abin da ya faru mamaki sosai taji nan ta shiga yi masa godiya amma shi ina hankalinsa na kan Mariya wani kallo yake watsa mata ta gefen ido kafun ya dubi Umma muryarsa da sanyi.

“Umma na mance shaf! in Allah ya kai mu gobe zan koma can wajan aikina domin hutun da na dauka ya kare ina muka fatan alheri sai na dawo”.

yana gama fadin haka ya mike saman kafafuwansa Umma kuwa sai faman sheka masa addu’a take yi da neman tsari.

A haka ya fita ba tare da ya dubi Mariya ba baya ya ajje wa Umma bandir din kudi masu yawan gaske duk da zuciyarsa sai a zalzalar sa take yi

ita kam Mariya ba a maganarta domin lokacin da taji abin da ya fadi ba ta san lokacin da hawaye suka wanke mata fuska ba wasu katangun tashin hankali suka rikito mata akai lokaci guda taji wani zazzabi na shirin rufe ta gabadaya ta kasa motsi jikinta gabadaya taji ya canza kamar ba na ta ba komai taji ya sauya mata a kankani lokaci tsoronta daya Allah yasa ba fushi yayi da ita ba ya yanke mata wannan danyen hukuncin mai barazanar tafiya da numfashim ta kuka take yi na zuciya idanuwanta sai zubda hawaye suke yi sosai take hango tashin hankalin da za ta shiga in ba Dr.karami ta dade a wannan yanayin kafun wani mugun barci yayi awon gaba da ita ya je fata wata duniya mai dauke da Dr.Karami wanda ta kasa tantace ta mene ne sannan ta kasa gane wata irin rayuwa ce suke yi sosai ta hango tashin hankali mutane uku take hangowa ko wanne kuma ita ya dosa da abu mai girma wanda ta kasa gane mene ne?.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *