AMANAR MU CHAPTER 9

AMANAR MU CHAPTER 9

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Tun daga wannan lokacin Barrister bashir ya sama k’anwar tasa ayarin tambaya,kuma yasa a ranshi sai ya binciko abinda k’anwar sa take 6oyewa,dan duk alamu sun rigada sun nuna mai Zee batada gaskia sannan kuma she is up to something.Amman sai mai?tun lokacinda Barrister Bàshir ya bar gidan Zee (kaduna) ya koma Lagos dan fara tsananta bincike akan k’anwar tasa.Sai yaji yana son tsananta bincike akan lamarin daya faru da Humairan sai yaji kawai wani abun yana sha masa kansa,tun yana sa ran zai duk’ufa dan bincike har dai daga baya yazo yayi biris da al’amarin gaba d’aya ya jingine maganan abinda ya faru da Humairan har k’anwar tasa (Zee)a gefe.ya cigaba da harkan gaban sa musamman auren da yake son yi,ya maida hankalinsa kachokam wajen naiman auran sa da yake so ayi nan kusa.Bai sake zuwa kaduna ko abuja ko zamfarah ba tun wannan lokacin saidai ya kira iyayensa a waya su

gaisa,kuma ya shaida masu naiman auran da yake yi,mama taso tambayan sa dalilin yin auran nasa a yanzun bayan yana ganin irin yanayin rayuwar da suka tsinci kansu aciki yanzun,amman da zaran tana son yi masa maganan sai taji kaman an mantar da ita,sam tana shafa’a kullum sai sun kammala wayan take rasa dalilin kawo masa zancen.ta rasa wannan wani kalan abune gashi dai 6aro-6aro tana son kawo masa maganan amman sai taji ta manta.!
+
*********************************

Sosai Umar ya dage yad’aga hankalin kowa akan dukiyansa,dan yaga kaman ma kotu nason yin biris da zancen dan kawai Dady na siyesu da kud’i(cewan Umar)kwanaki haka yaje har abujan yana tada jijiyoyin wuya akan dady wlh sai ya fito ya basa dukiyansa:
“Ni ban son iskanci,kawai a fito a bani dukiyata kafin na 6ata ran kowa dake rayuwa acikin gidanan eeheeee”!

Dady da fitowan sa kenan zai fita ya jiyo muryan Umar d’in da hanzarin sa ya sauko daga matakalan benen,ya nufo falan k’asan,Momy,Yaah khalil,yaah fareed ne zaune dan tun mutuwan Humy basu sake tafiya sun bar iyayensu ba dan sun san yadda suka matuk’ar shak’uwa da k’anwar tasu,barin su cikin wannan yanayin zai sasu cikin damuwa,shiyasa suka yanke shawaran dawowa nigeria gaba d’aya.
Hankalin dady a tashe
yace:

“Yanzun Umar ni kake yiwa wannan abu?sai kace nace ma na cinyema dukiya?”

Cikin d’aga murya Umar yace:

“Eh nikam koma dai menene,a fiddo abani dukiyata “

Lumfasawa dady yayi sannan yace:

“Toh shikenan kaje zan kirawo ka za’a baka gadon naka kaman yanda kayi magana in sha Allahu,ka tafi zan naimeka “

Ba tareda Umar d’in yace uffan ba yayi juyawan sa ba tareda ya damu da irin kallan mamakin da en uwan nasa ke yimasa ba yayi ta fiyansa ya barsu da mamakinsa fal ransu!

Yaaah fareed ne ya lumfasa yace:

“Tir k’ashi wlh Momy naga Umar ya matuk’ar chanzawa “

Yaah Khalil yace:

“Kai dai bari fareed,wlh Umar has totally changed kaman ba shiba,wai yau shine ke sa’insa da dady abinga da mamaki “

Ya ida maganar yana kallan su momy da dady dasuka yi mutuwan tsaye.shi fa dady wlh dama yayi alwashin kirawo lauyoyi azo a raba dukiyan a baiwa Umar Nasa kason ,ba sai ankaiga zuwa kotu ba! Amman dai ba yanzun zai basa ba, har sai ya gama shawaran daya yanke tsaka ninsa da mutanensa da suke shawara dashi da kuma en uwa da abokan arziqi ta kunnan.

Haka dai suka cigaba da tattaunawa tsakaninsu (Momy,yaah fareed,Khalil,dady).
*******************************
*Zaria*

  Nurse d’in tace:

“Hany’a d’ayan shine sai dai fa kisa a ruk’a tatso nonon mahaifiyar tasa ana kawo maki kina shayar dashi da wannan nonon,mijinki kuma kya ce masa nononki ya k’i fiddo madara ruwan nono bai fara zuwa ba !.”

STORY CONTINUES BELOW
Shuru Zee tayi tana tunanin zancen nurse din lumfasawa tayi sannan tace:

“Toh nurse ni kaduna nake faa tayaya zan ruk’a sawa ana tatsomun nonon mahaifiyarsa ?baki ganin kafin akawo mun zai lalace?”

“Aa ai akwai na’urar da ilimin kimiya ta kawo yanzun ,akwai wani abu da’ake kira milk-extractor da kuma breastfeeding bottle!shi kawai zaki siya.in kika siya dashi zaki ruk’a tatso ruwan nonon,kuma yana kai kusan 18hrs kafun yaa lalace amman in kisa a fridge yana kai 24hrs ,”

Jinjina kai Zee tayi dan wannan abu mai sauk’i ne zata iyayi!

*******************************
Koda Umar ya sama labarin haihuwan Zee harda rawar murna saida yayi sosai yayi farin ciki ,daga nan yaje ya d’auko matar sa da d’ansa suka dawo Kd ko mutum d’aya basu sanar mawa ba dan Zee tace bata buk’atan su sani,shi kuma Umar dama haushin su yake ji shiyasa yabi-yema Zeen ma.
Son duniya Umar ya d’auka ya d’orama wannan jaririn da yake matuk’ar kama dashi amman lura da cewa kaman irin bakin Humy da kuma haskenta ya d’auka abin ya d’an basa mamaki dan shi harga Allah yama rigada ya manta wata wai ita Humy a rayuwarsa gaba d’aya dan ko ya kad’aice yanzun baya wani tunaninta kaman yanda yakeyi a baya.He forgot about her totally!yanzun d’inma kawai yana ganin cewa dan jini d’aya suke da Humyn shi yasa yaron ya d’an d’auko wani abu nata.daga haka ya cire tunanin Humyn akansa gaba d’aya ,ya cigaba da ririta matarsa da kuma d’ansa.

*****************************
Direba na musamman Zee ta ajiye da zai ruk’a zuwa kullum duk bayan sallan asuba yake zuwa Zaria yana amso mata wannan breastfeeding bottle d’in wajen baabaa tsohuwa sai ya kawo mata kaduna tun kafin kowa ya farka.

Ita kuma baabaa tsohuwa tana anfani da wannan milk-extractor d’in da Zee ta bata wajen tatso mata ruwan nonon Salamatu (Humy).A farko salamatun k’in yarda tayi akan Babaa bazata ta6a mata nonon taba sai ta ruk’a tarewa da hannayenta tana mik’e kafad’unta alamun aa bata so.Sai da baba tsohuwan ta zaunar da ita tace:

“Kinga Salamatu taimako fa zaki ruk’ayi,kuma Allah zai baki lada,kinji?akwai wani yaro da aka haifeshi babarsa ta mutu aka rasa mai basa nono,shiyasa nace masu ni zan taimake su akwai wata ‘yata da ita ma kwananan ta haihu d’anta ya rasu,zata taimaka maku da ruwan nononta tunda itama haihuwa tayi ruwan nono zaizo mata,dan Allah ki taimaka masu Salamatuna kar yaron ya mutu kinji?”

Gyad’a kai Salamatu tayi cikeda amincewa dan koda ace bata gane wasu zantukan ba ta dai san taimako akeso tayi shiyasa babaa ke bud’e mata nononta ashe?da kanta salamatun ta ciro kan nononta ta nuna ma Baabaa alaman ta tatsa d’in!

Ba tsoro ba tsoron Allah da ma’aiki wannan tsohuwan ta kafa abin tatso ruwan nono akan nonon Salamatu ta tatsoshi dayawa ta cike bottle d’in ta rufe ta kaiwa direba shi kuma yayi gaba dan kaiwa Zee,.

Dukda Salamatu taji zafin tatso nonon da baabaa tayi mata hakanan ta daure ta cigaba da linkema baaba kaya!

Toh tundaga wannan lokacin kowani safiyan Allah koda ace bacci Salamatu keyi sai wannan tsohuwa ta shugo ta tatso ruwan nononta takaiwa direba yakai ma Zee.Tun abin nama Salamatu zafi hardai ya zama jikinta wani zubin ma da kanta take tatsowa ta baiwa tsohuwan dan tayi haddan yanda tsohuwa
r ke tatso ruwan nonon shiyasa itama ta iya kuma wani sa’in takeyi daa kanta.Baabaa kuma tayta shimata albarka!(d’anka dai d’ankane komin rabaku da’akai the bound is always there)

**************************************

A duk lokacinda Zee zata shayar da Abul-islam (sunan da Umar ya sama d’ansa kenan dan ko suna basuyi ba)a 6oye take yi bata ta6a barin Umar ya gani dan nuna masaa take tana shayar dashi da nononta agabansa dan bata d’au shawaran nurse d’innan ba akan cewa ruwan nononta ya kafe!

Shi dai Umar yana ta kiciniyan raba gadan sa tsakanin shi da dadyn Humy da za’ayi shiyasa kullum yake sintirin hany’an abj.

***********************************

Barrister bashir kuwa yanzun kam maganan auran sa yayi nisa dan har IV aka fitar har abj yaje yakai masu Iv.Yau sunday yake ta shirye shiryen Zuwa zaria dan anan amaryar dazai aura take,tunda safe ya shirya ya hau motan haya ya nufa zaria.Akan hany’ar su na shiga Zaria motarsu tayi faci,nan suka tsaya aka shiga kiciniyan gyara pacin.
Suna zaune a bakin titin dazai shigar dakai Zaria suna saida Bredin su yanda suka sabaa a kullum,salamatu zaune agefenta tayi jugum yanda ta saba a koda yaushe.

Waiwayo wa yayi dan ganin ko angama gyaran pacin amman sai dai mai?yana waiwayo wa idanuwan sa suka sauka akanta.Gaban sane yayi munmunan fad’uwa kuma zaro idanun sa yayi dan tabbatar ma kansa wacece yagani ganinda tabbas ita d’ince ya furta a fili:

“Humy?!”

Kai! Shidai yasan Humy ta mutu toh ya za’ayi ya ganta anan?kodai kamannine kawai?

Da saurinsa ya fito daga cikin motan ya ganta da wata tsohuwa a zaune!yasoma takowa wajen su gaba d’aya ma yaji duniyan tayi mai wani iri!

Mutanen motan suka shiga kwalamasa kira “MALAM kafa zo motar ta gyaru,kazo mu tafi “

Atak’aice yace masu:”su tafi kurum “

Shikuma ya k’araso inda suke zaune suka kasa biredin saidawa:

Sallama yayi masu baabaa ta amsa ita kuma salamatu ta d’ago da niyyan amsa masa sai suka had’a ido.Wani kalan zaro idanu tayi tana kallansa baki bud’e…….:………✍🏻Wani kalan zaro idanuwa tayi,tana kallansa baki bud’e,kallanta yayi itama ta kallesa,ido cikin ido.sadda kanta gefe tayi ba tareda ta kuma kallansa ba,mamaki fal ran barrister dan kam yaga tayi wani kalan re-action amman daga baya sai yaga ta dawo normal .+

K’are masu kallo tsaf barrister Bàshir yayi sannan ya d’an kalla wannan tsohuwar da take ta binsa da wani irin kalan yayaa dai ?da sauri ya d’an murmusa abinka da lauyoyi sun iya takunsu.Yace mata:
“Nawa -nawa ne biredi innaaa?”
Baabaa tace:
“D’ari dagoma-goma duka “
“Aban guda d’aya”

Saka hannunsa yayi a aljihu ya ciro 1k ya mik’ama Baabaa,kallan kud’in tayi sannan tace:
“Kayyaa babu chanji yaroo “
Barrister cikin jin dad’in rashin chanjin da bata da shi yace:

“Babu chanji?”
Babaa tace :”eh babu chanji gaskia cinikin namu bai kai nan ba “

Murmushi bashir yayi sannan yace:
“Toh shikenan ban biredin sai ki rik’e chanjin “

Washe hak’oranta da sukai jajajir tsaban cin goro baabaa tayi tana mai matuk’ar jin dad’in barin mata chanjin da wannan mutumin yayi,cikeda fara’a tace:
“Toh-toh d’an nan mun-gode sosai da sosai Allah ya saka da alkairi ,Allah yak’ara bud’i “
Ta mik’a masa biredin a hannu shi kuma ya amsa!
Murmushi yayi sannan yace:”Ameen baabaa.Amman wacchar ‘yar taki bata magana ne?”

Ya ida maganar yana mai nuni da salamatu da d’an yatsansa,kallan Salamatun dake ta wasa da yatsun hannnunta baabaa tayi sannan ta kalla Bàshir tace:

“Ai ita wannan haka take bata magana”
Barrister bashir yace:”ok Allah sarki “
Ya maida kallansa wajen Salamatun wacce itama a dede wannan lokacin tad’ago tana-mai kallansa,murmushi barrister ya sakan mata sannan yace:

“Sannunki “
Gyad’a masa kai kurum tayi sannan tacire idanuwanta akansa ta-mayar k’asa ta cigaba da daddanna yatsun hannunta.daga haka Barrister ya-gane cewa da’akwai matsala a tattare da ita (salamatun)kuma d’agawon da tayi ta kallesa yasa-shi k’ara tabbatar da cewa lalle tabbas wannan Humairah ce,hankalinsa inyayi dubu ya gama tashi a wannan lokacin da sauri ya-juya ya-soma tafiya ba tareda ya tsaya jin adu’oin da baabaa ke-masa ba,dan kawai yabar mata chanjin d’ari takwas da en kai.

Straight wani hotel dake kusa Barrister yaje ya kama,dan baijin zai iya k’arasawa gidan su matar da zai aura .Da kyar ya iya k’ara-sowa cikin d’akin daya kaman,kansa a dafe yana mai wani irin saraa kaman zai tsage biyu tsaban tashin hankalin daya-shiga,wani kalan rud’u da masifaffan tashin hankali barrister ya tsinci kansa aciki tambayan zuciyansa ya shigayi:

“Toh ta ina ma  zai-fara?taya zai kamo bakin zaran?mai ya kamata ya fara-yi?mai abunyi? Dan dai tabbas bawai direct zai d’auko humairan ba dan yaga alamun tsohuwan nan er drama ce.sai ta kwashe masa en kallo in yanuna yasan Humairan ,anan dolen sa yayi anfani da kwakwalwansa da kuma dabarun sa irin tasu ta lauyoyi dan ku6utar da Humy a wannan k’angin.Dolen sa sai yabi ya san ya akayi aka haihu a ragaya !

Daga nan sai ya shiga tunano duk abinda ya-faru a baya,tambayan kansa ya shigayi :
“Toh waima shi ya’akayi yayi sany’i har bai cigaba da binciken da yace zaiyi akan k’anwarsa ba??”!

Kaman wanda aka tsungula yayi saurin mik’ewa daga kan kujeran da-yake zaune,ya fito da saurinsa har reception sannan yace ma receptionist din zai fita amman yanzun zai dawo!

Da sauri saurinsa yak’araso wajenda suke,ya gansu zaune dai kaman yanda ya barsu k’arasowa yayi wajen nasu yana mai murmusawa sannan yace:

“Baaabaa kinga na dawo ko?wlh harda zan wuce sai nayi tunanin tsayawa nayi salla.Dan Allah kozan sama buta inyi alwala?”

STORY CONTINUES BELOW
Ita dai baabaa cikeda jin dad’i duk dan anbarmata chanji ta murmusa tace:
“Aiko mai zai hana?”
Da saurinta ta mik’e ta wuce rumfar su da suke d’an zama su huta,ta d’auko mai buta cikeda ruwa,ta kawo gaban sa ta ajiye .sannan ta koma gefe inda Salamatu ke zaune tana kallan titi ,ta zauna,bayan barrister ya kammala alwalan sai yazo ya zauna akan wani d’an dakali yana fuskan-tansu.ya d’an murmusa ya d’an soma jan tsohuwar da hira,yace:

“Kai wlh garin Zaria akwai cunkoson mutane inason garin wlh “

Tsohuwa kuwa dama baki kaman reza ta sake baki ta fara basa lbr  ririiiiii-rii,ganin jirginsa da yake taso ya d’aga ya soma d’agawan sai shima ya shiga yankoma tsohuwan lbrn k’arya  har yake ce mata:

“Ai inada mata ma,na shugo garin nan saran wasu kayayyakine,kin san abu da iyali ga kuma yara dole sai ka d’aura himma “

Baabaa ta kalla Salamatu wacce hankalinta kwata-kwata baya wajensu tana wasa da kitson kalaban da tsohuwa taymata wanda zai kai tsawon wata 3 akanta duk yayi butu butu har baka ganin shedan tsagu!sai sa gashin abaki take tana tsotsa da miyau,Barrister ya bita da idanuwan tausayi yana mai tunanuka kala-kala.shin wajen hatsarin da tayine ta sama mental problem?ko dai dama chan ba mutuwa tayi ba?! Yadai kasa sanin amsan da zai baiwa kansa kwararra dole sai ya tsananta bin cike!

Baabaa ce ta katsesa da fad’in:

“Wlh kaidai bari d’annan nima haka nake ta fama,abin dai sai du’aee kawai”

Murmushi barrister bashir yayi sannan ya muskuta yace:

“Amman nasan garin nan dukan su zazzagawa ne amman ke naga bakya zazzaganci kuma bakida zanen zazzagawa daga ke har d’iyar ki?”

Ya ida maganar yana mai kafeta da sexy oily eyes d’insa:

Shek’ewa da dariya baabaa tayi sannan tace:

“Aini ba asalina nan nake ba,ni ‘yar Kano ce,kawai dai zama ne ya kawo ni nan “

Barrister ya jinjina kai dan ankawo wajen da yakeso akawo kuma lauyan ce zancen yayi (abinga da lawyoyi 😂wayau da iya tweestin
g zance kaman ruwan sama,jinjina gareku Barrister’s 🙌🏻❤️Allah yak’ara ilimi da fasaha)

Yace:

“Aiho  shiyasa kenan?aiko gashi kam hausan kano rad’a-d’au a bakinki kanon dabo kenan tinbin giwa koda mai kazo anfika “!

Jinjina kai Baabaa tayi harda gyara zaman ta dan ta fara jin dad’in maganansu!

“Aiko d’annan wannan karin maganan gaskiya ce koda mai kazo mun fika wlh a kano sai munan jinin kanawa,.hausawan usuli ka sama d’an Kano ka gama koyan yaren hausa koda uwata-da ubatai naka jikokin oduduwa ne sarkin yarbawa,jinjina dai maga-bashin hausa jigon kafuwan yaren hausa bayo jidda,dakai da ‘ya’yanka banza bakwai “

Murmushi kawai barrister yayi yana mai jinjina surutu irin na wannan tsohuwa gashi bata magana a hankali,saurin kawarda zancen nata yayi dan ba nan yakeso su koma ba,yace:

“Aiyah duk sauran ‘ya’yanki a chan kanon kuke?”
Sai tace ma-shi:
“eee amman aini ban ta6a haihuwa ba!”

“Anzo wajen “
Barrister ya ayyana a zuciyansa yasoma d’ano jirgin matar nan.Amman sai yayi murmushi yace:

“Aiyaa Toh mai gidan naki faa?”

Tace:
“Yana chan kanon bamu ta6a samun raboba dani dashi ba,ni kad’ai kuma iyayena suka haifa shiyasa suna mutuwa nata fi yawon bara abuna dan wanga fak’irin mijin nawa babu abinda yake azurta ni da shi “
Yace:
“Ashshaa abu baiyi dad’i ba,Amma-kenan wanchan ba ‘yarki bace?”
Ya ida maganar yana zuba mata idanuwan sa dan son ganin yanayin da zata shiga ko kuma gaskian zancen da zata fad’i masa!

STORY CONTINUES BELOW
Juyowa baabaa tayi ta d’an kalla Salamatun sannan tayi d’an turus tana tunanin mai take fad’a hakane wai?ya akayi tace ma mutumin nan Salamatu ba ‘yarta bace?bayan kowa dake cikin k’auyensu babu wanda yasan da zaman cewa Salamatu ba ‘yarta bace!wannan wani kalan su6ul da baka tayi?! Saurin murmusawa tayi sannan tace masa:

“Eh ‘yar gidan ‘yar uwana ce uwa d’aya uba d’aya muke da mahaifiyarta,iyayenta suka rasu,suka barmun salame .rik’onta ya dawo wajena “

Murmusawa barrister ya kuma yi dan anan ma ta kuma kama kanta dan tace masa ita kad’ai iyayenta suka haifa yanzun kuma kafun ta amsa masa tambayansa sai daa tayi turus alaman mara gaskia sannan ta basa amsan ‘yar gidan ‘yar uwarta ne !kenan ta manta tace masa ita kad’ai iyayenta suka haifa?

Jinjina kai yayi dan ko a iya nan ya tsaya da binciken ko waye wannan mai kama da Humairah ya isa yasan cewa Humairan ce sai dai akwai wata mak’ark’ashiya ak’asa! Wanda shima gab yake da kamo bakin zaran wajen. (Weldon barrister bash 🙌🏻)

Sai yace mata:
“Aiyah shi yasa bakwa kama ashe?”
Sai ta k’ara shek’ewa da daria tace:

“Eh wlh bama kama .ai ita kana ganinta kaga zubin mahaifinta,bafullatanin usul,Allah dai ya jik’anka Adamu ,kaabar ‘yarka mai kama dakai sak .

Murmushi barrister yayi yana jinjina k’arya irinta wannan tsohuwa gashidai 6aro 6aro alamu sun nuna a fuskanta zancenta k’aryane fad’in baki ne bai kai zuci ba!Amman tayi biris tana zuba mai zance ita anan bata son ya gano ta!

Bata san cewa k’arfin tunaninta da basirarta basu kai kwatan-kwatan _barrister Bàshir Ahmad Daleel_ ba!

Abinda yayi kusan shekara 7 zuwa 8 yana karanta cases da suka shafi tunaninta yanada masani da basirar gano zantuka da yawa a lokaci d’aya inyaso maida ma da abu fari bak’i ko abu bak’i fari a dak’ik’u da basu wuce 3 ba zaisa mutum yayi na’am da cewa abinda yayin hakan ne babu mushkila,amman kaman ita tsofe-tsofe da ita wanda ko police ya kira suka suburbud’eta ko nuna mata bindiga tsaf zata fallashemasa gaskia amman wai tana nan tana shuka masa k’arya tana kuma tunanin ai ya rigada ya zauna akan kilasar k’aryanta!
(Hmmmmm baabaa u don enter barrister Bàshir black list )

Amman yasan abinda zaiyi akanta,ita d’in ba matsalan sa bane yanzun Zee itace babban matsalansa.Dan wlh baida shamaki ya tabbatar Zee ce tayi wani abin ta gusar masa da binciken da yayi niyyan yi.Dan tasan halinsa tsaf yace zaiyi abu toh wlh sai yayi kuma tabbas sai yacimma nasara sannan yake hutawa.Amman kam yanzun tayi kad’an tashugo hany’ansa acikin ruwan sany’i zai dafata a rana d’aya kawai zata wayi gari taga ya tona mata asiri sannan kuma ya dak’ule duk wata hany’a da dabaru nata datake tunanin zasu iya ku6utar da ita.yanzun aikin CID zai komayi zai chanza takunsa.dashi Zee ke magana!

“Zainab wait am coming for u,sake had’uwan mu shine ranar nadaman sanina da zakiyi.Wait and watch how bashir will destroy each and every single part of ur evil deeds! The time starts now,click…click ……tik……tiik “

Bayan ya gama maganan zucinsa yayi masu sallama,ya koma Hotel (masaukinsa)

Daganan barrister Bàshir ya gane cewa al’amarin nan fa ba sany’a ya kamata yayi ba dukda lokacine na bikinsa,toh bazaiyi k’asa agwiwa ba,bayan yasan shari’an da Umar da dady suke ta tafkawa shidai Umar alalun a dole yace dukiya duka ta baban sane ,inda kuma Dady yake musawa har yake kafa hujjoji ,gashi -shi yace ma dadyn zai shiga cikin tawagar lauyoyin dadyn Amman dadyn yace aa ya bari tukun yana so yaga iya gudun ruwan Umar d’in,duk da dai yana ganin cewa kaman ma  yaron ma ba’a cikin hayyacinsa yake ba!”

Dagon lumfashi Barrister Bàshir ya kuma jaaa daya tuno wannana al’amarin kuma (dady and umar)

“Kai Amman wlh Zee ke shed’aniya ce,ire irenku mutane ke naiman tsari dashi,rayuwanki nan gaba bazaiyi kyauba Zee koda kin tuba,wlh ni dakaina blood brother d’inki da hannuna bayan nagama bincikena akanki kuma komai ya tabbatar mun daidai da hasashena akanki Wlh ni bashir nine zan mik’ak’i ga kotu kuma na rok’a alfarman yanke maki hukunci dai-dai da yadda kika aikata laifukanki ba tareda kotu tasha wahala ba!lokacin nanan Zuwa Zee nasan bazaki shiryawa wannan lokacin ba but trust me that will be ur end dake da duk wani evil deeds naki,sai kinzama abin ishara ga sauran mutanen baya masu bak’in hali irin naki.I promise u!”

Dunk’ule hannunsa yayi ya buga a bango yana huci tsaban tak’aici ji yake wlh da Zee na kusa da-shi a yanzun wlh sai dai azo a d’auki gawarta.Amman he won’t take action with his own hands ,yafi so hukuma ta yanke mata nata hukuncin yanda zata zama izna ga sauran mutane masu hali irin nata!
******************************
Zainab zaune tana bawa Abul-islam breastfeeding milk sai faman rarraba idanuwa yake yana tsotsan fidan.Ni sawa tayi sannan tace:

STORY CONTINUES BELOW
“Banzan yaro idanu sai shegen kwala-kwala kaman na uwarka Aisha “

Zun-guran yaron tayi tana faman mita ita kad’ai daga k’arshe kuma Abul-islam ya fashe da kuka,tsaki taja sannan ta ajiyesa akan kujeran tayi mik’ewar ta,tace:

“Inka gaji da kukan kabari dan kanka,mtswwweew in banda ma k’addara ai wlh babu abinda zai sani zama dakai har ina wahal da kai na,mtswwwe yanzun in ansan cewa kai d’an Humairah ne duk dukiyan dana keta sintirin araba na had’a kansu nayi gaba abuna,dakai zaa baiwa kenan?toh k’aryanka yaro,yanda ban haihu d’ana bai moraba kaima haka bazaka moraba,dukiya ta Zee ne kawai kodaga al’arshan Allah ma na tabbatar hakan take a rubuce Zee Ahmad Daleel sai tayi kud’i na bugawa a jarida.kai kuma Umar bari dukiyanka su shugo hannuna zakaga yadda zan wulak’anta rayuwanka wlh “!

Ta ida maganar tana had’e rai sannan ta haye sama ta wuce d’akin humairah da yazama mallakinta a yanzun,Abul-islam kuwa sai kuka yake kaman zai shid’e har launin fuskansa ya sauya-ya fara komawa jaaa.

“Subhanallahi “
Umar ya furta da k’arfi ganin yanda Abul-islam keta risgan kuka har muryarsa ta dashe.gashi kuma yana motsi-motsin mirginowa a k’asan tiles,wanda kam yanda manuniyan sa bata yi k’arfi ba in ya fad’a a k’asan nan ya bigi center table din wajen tsaf babu abinda zai hana wajen nan fashewa!

Da hanzarinsa yaje ya taryosa yaron ya fad’a a k
‘irjinsa rungumesa gaba d’aya Umar yayi yaron sai faman ajiyan zuciya yake jin d’umin mutum a jikinsa.mik’ewa Umar yayi hakanan kawai ya tsinta kansa da yima yaron tofin adu’a wanda wlh rabansa da yayi adu’oi har ya manta dan ko salla yake fatiha da iklas yake karantawa kuma yana sallamowa babu batun tsayawa tasbihi da hailala zai mik’e kawai yayi tafiyarsa.Kuma bai bin sallan jam’i ya gwammace yayi sallansa shi d’aya tak.!

Jijjiga abul Umar ya shigayi yana masa tofi har yasamu yaron ya daina firgici da ajiyan zuciya.Straight d’akin Zee ya nufa dan ganin mai take yi da tabar yaro yana kuka kaman zai shid’e.ita ko Zee dama tun parking d’in motarsa taji dawowan sa hakan ya sata saurin mik’ewa ta gyara jikinta dan yau wlh sai ya mayarda takardun dukiyoyinsa akan sunanta dan dama nawajen aiki kam sai data matsa ya maida sunanta his next KIN ,sims d’in da yake receiving alerts duk ta amsa ita da kanta ke ganin duk wani shige da ficen kud’ad’ensa Na duka bankunan sa.Inta tashi tatsa kuma mak’udan kud’i take iba tamaida anata account d’in shidai Umar bai da tacewa komai Zee tayi daidai ne awajensa.!

Turus ya tsaya yana kallan irin fitinan niyar shigan da tayi,ta mugun tafiya da hankalinsa sai yaake ji ma tamkar yau ya fara ganinta a rayuwarsa tsaban yanda ta rikid’e masa ta dawo shar-shar abinta!
Muk’ut ya had’iya wani kalan yawu sannan ya idasa shugowa cikin d’akin itako sai faman karairaya da kad’a mazaunanta dam Zee ba baya ba wajen k’ugu,sai faman rausaya su take dan ta lura duk k’ugunta yafi jan hankalinsa a gareta.Saurin kwantarda Abul yayi akan soffa wanda tuni baccin wahala ya d’aukesa har jikinsa ya d’au zafi.

K’arasowa inda take ya shigayi itama ta shiga matsowa wajensa cikeda kissa,chak ya tsaya yana k’are mata kallo ita kuma ta k’araso inda yake tana ta faman rangwad’a,hannunta ta sakalo akan fad’un sa,wani kalan fitinanniyar k’amshin turaren ta ya bigi hancinsa wannan turare kaman misk dan dad’i nanko turaren mallaka ne wanda malam ya baiwa Zeen yace da zaran k’amshin turaren ya bugi hancin Umar ko uwarsa tace ya yanka mata tohm shifa mai aikata hakanne.sunsunata ya shigayi tun yana iya sakan mata hot kisses itama tana mayar masa hardai tsayuwan gabaki d’aya ta ishesu suka fad’a
Kan gado.Daga nan suka soma lulawa wata duniyan na daban Umar sai faman sunbatu yake itako Zee sai k’ara azaman tayasa biyama kansa buk’ata take dan dai duk tasama burinta ya cika yamaida sunanta akan takardun dukiyansa.

Ganin zasu wuce tunanina dan Zee yanda kasan 🤭haka ta iya chanza salo kala kala tabar Umar da nishi da sunbatu 😂🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️nidai nayi ficewata bani ganin abinda yafi k’arfina!

STORY CONTINUES BELOW
Umar and his Zee a fito lfy 🙌🏻

*******************************
Tun daga wannan ranar barrister bashir ya maida gurin tsohuwa wajen zuwanta ya siya biredi yazauna a gefe yata janta da lbrai ita kuma tata 6aro masa zance shi kuma yata recording d’insu dan zai iya anfani da wasu anan gaba.kwanansa 3 yayi shirin komawa dan sanin kuma ta inda zai d’aura dan ya gama samun all informations da yake son samu wajen tsohuwan nan dan har gidansu na anchau saidata kaisa kuma yaga inda Humairah ke rayuwa a yanzun,ya matuk’ar tausaya mata dan kam wanda suka maida Humy haka wlh Allah bazai barsu ba!

Da barrister bashir ya tashi tafiya tunda ya fuskanta wannan tsohuwan mayyar kud’i ce dazai tafi ya ciro dubu biyu ya bata.aiko daman abinda take ta jira kenan nanda nan tashiga saka masa albarka :

“Allah dai ya saka da alkairi sulemanu (sunan da ya fad’a mata kenan a matsayin sunansa)ya k’ara tsareka ya kuma k’ara bud’i mungod mungde,Allah ya tsare hanya,yakaika gida wajen iyalanka lafiya itama ta farantama kaman yadda kazo nan ka faranta mana nida Salamai na “

Barrister bashir yayi murmushi yace:
“Ba komai in sha Allahu idan na kuma shugowa zan ruk’a zuwa muna gaisawa,dake kinsan shi zumunci ko akan hanyama sai Allah ya had’aka da mutum ayi zumunci “

Cikin d’oki baaabaa tace:

“Eee wallahi sulemanu haka zancenka yake,gashi yanzun munzama kaman en gida baka gajia da mana hidima,Allah dai ya tsare ya k’ara tsawon rai da lafiya na gode nagode”

Murmushi yayi kawai sannan ya kalla gefen salamatun wacce ya lura sam bata ji dad’in ta fiyansa ba tana son masa magana ko kuma tayi wani tunani akansa ta kasa gane ta yanda zata ganosa dan ko jiya da yazo saida ya gwada mata wani abu daya saba mata lokacin idan yazo nigeria hutu amman da zaran Salamtun ta shiga tunano fuskan wanda yake mata abinda wannan mutumin ke mata sai ta kasa ganin fuskan mutumin da nata amman dai 6aro-6aro gashi dai a kwakwalwanta amman picture din yak’i yayi clear tayadda zata gani komai dishi-dishi yake nuna mata!

“Salamatu na tafi kinji sai kuma idan na kuma shugowa “

Ya ida maganar yana mai kallanta yana son su had’a idanuwa yaga re-action dinta aiko idonta tab kwalla ta d’ago tana kallansa tadai kasa tunanin komai da cewa komai har Barrister ya gama nazarin yanayin data shiga yayi juyawansa ya tafi bata daina kallansa ba!

“Keee salamatu wai sai kallansa fa kike ,kodai ya maki ne??”

Baaabaa ta ida maganar tana dariya,ita dai Salamatun bata ce uffan ba kuma bata mata sign da kanta ba yanda ta saba yi adaaa in baabaar ta tambayeta,sadda kanta kawai tayi k’asa ta cigaba da wasa da yatsun hannayenta.

***********************************

Barrister bashir nan ya koma zamfara abin yana ta damunsa tunda ya dawo gusau yace:
“Toh shi yanzun mai ya kamata yayi?kabarinta ya kamata yaje anuna masa ko yaayaa?”

Bayan yaje ya gaida iyayensa yayi kwana d’aya ya koma chan abj dan a tanan zai fara samo bakin zaran.

Isan sa Abj ya sauka a gidansu Humairah ,babu kowa a gidan in banda khalil duk sun tafi kotu dan ayau zaayi zaman k’arshe in Allah ya yarda,khalil shikam yay buris yace ba inda zaije bare ya kwaso ma kansa abun bak’in ciki ,shiyasa yayi zaman sa a gida.Khalil yayi mamakin zuwan bashir amman sai ya wayince yace:

“Ango,ango!angon k’arni “

Murmushi barrister bashir yayi sannan yasama guri ya zauna yace:

“Kaji dashi dai kai kananan kak’i fiddo mata salan ka tsofe a gida ka dawo tuzuru ai “

Dariya khalil yayi sannan yace :

“Nakusa ai bar ganin wai kai ka kusa innaji haushi aranar d’aurin auranka sai nasa a d’aura da nawa “

Dariya sosaii barrister yayi sannan yace:

“Ah haba dai?toh inba tsoroba kafitar ayi ranar!ni bama wannan bace ta kawo ni nan so nake ka kaini kabarin Humairah “

Tsayawa chak da dariyan da yake yi yayi sannan ya kalla Bàshir din cikeda mamakin abinda yace:

“Kabarin Humairah kuma?!”

Gyad’a kai Barrister yayi alamun yes nan nake nufi:

“Mai zakaje kayi kaiko a kabarin Humairah barrister? Yanzun fa Humairah na k’ok’arin shiga shekara d’aya da wasu watanni ne fa.Toh mai za-kaje yi kabarinta a wannan lokacin?”

Murmushi bashir yayi sannan yace:

“Nasan Humairah takai shekaru d’aya ta rasuwa ai amman dai still I insists ka kaini wajen kai kam “

Sororo khalil ya shiga kallan barrister sannan yace:

“Toh wai mai so spacial da duk tsawon watannin chan bakaje kadubo kabarin nata baa sai yanzun?mai zakayi a kabarin nata?”

Murmushi barrister ya kuma sake wa sannana yace:

“Ohhhhh Khalil kaiba d’an sanda ba amman sai shegen jero tambayoyin tsiya,tambaya kake mai zanje yi kabarin humairah ko?toh mai ake zuwa yi a kabarin mamaci idan anje?”

“Yooo toh ai nima tambayar danake yima kenan “

Barrter yace:”umm nasan kasani ai amman dai bari na kuma gaya ma adu’a zanje na mata achan dan ance ziyaran mak’abarta ma lada ne kaga innaje na ziyarci mak’abarta sai in biya inma k’an
wata adu’a komai kace?”

“Hummm ok wooo all this whiles ba kazo ziyaran mak’abarta ba sai yanzun ko?tashi muje nakaika toh “

Nan suka mik’e suka shiga motan khalil suka wuce mak’abartar da aka kai humairah!

Bayan sunyi adu’an ziyarar mak’abarta suka shiga suka gaida mai gadi suka mai bayanin kabarin da suka zo gani,nan mai gadi yayi masu jagora har kabarin Humairan shi kuma barrister ya tsaya k’arema kabarin kallo gadai signboard d’in karantowa ya shigayi a zuciyansa:

“Late Aysha humairah abbaz mai goro died at the age of 21 “

Tabbas nan ne aka binne humairan!

Toh yanzun hoton kabarin zaisa amasa ne ko yaya wai?…………….✍🏻😫😫😫baka sanin masoyinka sai wani abun ya faru dakai jia zuwa yau kawai da banyi postn amanarmu ba masoyana dayawa suka ruk’a kirana dan jin lafia kuwa wasu kuma suka turamun private chat ❤️💕nagde sosai wlh da kulawanku kuma indo tana nan lfy jarabawa ne ya d’an sha kaina shiyasa thank u so much I love u all fisabilillah!

+

Yanke shawara yayi da zuciyansa akan kawai zai cigaba da yin bincike tunda dai babu ko shakka yasan wanchan salamatun ba kowa bace face Humairah dolensa sai yabi diddigi dan yasan ya’akayi aka haihu a ragaya!.k’anwar shi kuma bazai barta a haka ba ,dolen sa sai ya sama mutanen da zasu ruk’a kulamai da dukkanin wani takunta da motsinta dan sai yaa mata kamun kazan k’ofa,lallai k’anwar sa ba k’araman hatsabibiya bace,barin irinsu a duniya bala’i ne da musiba.Tabbas sai ya mugun koyama Zee hankali,sai tayi nadama sosai wanda a lokacin babu wani anfani dazai mata,shi wlh har yanzun bai samu wani kwakwaran dalilinta ba na tauye AMANAR Humy da tayi ta watsa ma Humy k’asa a ido,ta shuka mata rashin mutunci na bugawa a jarida,wlh yasan har cikin ran Humy da zuciya d’aya take zama da Zee kuma take ma iyayensu abinda Zee ta gagara yi masu.Amman kam tayi kuskuren cutar wa’inda suka taimaka masu dan koda ace shi bai tashi tsaye wajen taimakonsu ba,komin daran dad’ewa rabbi sai ya saka masu dan basuda hakki ko d’aya akan Zee.Duniya sai ta juya maki baya wata rana Zee tabbas wannan ranar yana gab da zuwa,butulu mai saka alkairi da bak’in sharri!.

Haka dai barrister bashir ya ruk’a zancen zuci,har suka gama yi ma kabarin adu’a sannan suka ma mai gadi sallama had’i da basa kud’i masu tsoka,dan yana k’ok’ari ba kowa ke danna zuciyansa yana zuwa gadin mak’abarta ba!.

*************************************

“Dadyn su Humairah,wlh inka bi ta tawa kawai karka bama yaron nan mak’udan dukiyan nan,dan wlh Umar baya cikin hayyacinsa,basa kud’ad’an nan kaman rusa rabin rayuwarsa ne.”

Dogon lumfashi Dady ya sauke sannan ya kalla momyn wacce ta kafesa da many’an idanuwanta,murmushi ya saki sannan yace:

“Ko Umar na cikin hayyacin sa ko baya cikin hayyacinsa,hakan bazai haneni basa dukiyansa ba,dama ai tun lokacinda ya kammala digree d’insa na farko nace masa zan basa gadonsa yayi biris harda kukansa akan baiso ni in cigaba da juyamai dukiyan nasa,har sai sanda yayi aure.Fine and good haka na cigaba da juya mai dukiyan nasa,yanzun kuma yaro yace abasa kayansa sai nak’i basa hakkinsa kike magana Ramlah ko mai?”

Kallan Dadyn momy tayi taga iyakar gaskiyansa ya fad’a mata,lumfashi taja sannan tace:

“Had’uwa yayi da azaluman mata dan haka banda shakku wlh Zee ce tama Umar asiri,dan babu wanda zai kalla Umar yace ba asiri ke d’awainiya da shi ba,tun lokacinda wannan Zee d’in ta aura Umar wlh yariny’an nan ta siremun acikin zuciyana,sabida wlh nasan kayan bak’in cikin su da suke d’and’ana ma humairah shine sanadin barinta kaduna ta taho abj daga nan kuma Allah ya amsa ran baiwar sa dan baiso ta cigaba da kwasan ma kanta kayan bak’in ciki da tak’aici,ace wai mutum daka aminta dashi kake komai naka dashi yau shine zai watsama k’asa a ido.Wallahi ban ta6a tsammanin Zee da hali irin haka ba,Na rasa dalilin dayasa lokacin auran nan nasu na kasa magana akan auran har fad’a Na ruk’ama ‘yata ashe sanadin auran sanadin mutuwar ta kenan,kaicho da hali irin naki Zee”

Momy ta ida maganar tana mai zubda kwalla,shuru Dady yayi sanan daga baya ya nisa yace:

“Zato zunubi Ramla koda ya kasance gaskia,aure Allah ne ya rigada ya rubuta a littafin k’addaran ko wannan su Zainab sai ta aura mijin Humy,so don’t judge a book with it cover “!

Daga haka dady ya mik’e yayi haurawan sa d’akinsa,yabar momy zaune tana binsa da kallon mamaki.

Murmushi momy tayi sannantace “kaima ba a haka ta barka ba Alhaji,nima ai a daaa Zee tayi nasara akaina amman banda yanzun,duk inda malamin tsubbunki yake Zainab ni mai bin diddigin inda yake ne sai na ci ubanki daga ke har shi,sai kun biya ran ‘yata wallahi tallahi wannan alk’awarin uwace! Humairah na Allah cigaba dakai haske kabarin ki “

STORY CONTINUES BELOW

(Tirk’ashi da alamu sammun da Zee tama momy ya karye toh yaya kenan?😳mujede zuwa k’ak’aaaaaaa)

*******************************

Kwanan Bashir d’aya a abuja,ya tattara ya koma kaduna dan fara guda nar da aikinsa akan Zee kachokam,dan gida na musamman yayi renting,dan jin dad’in aikin nasa amaryar sa ma anan kadunan zata zauna har lokacinda zai kammala abinda ya kamata yayi!

‘Yan zaune gari banza barrister ya samu, ‘(samari guda uku)ya sasu akan lalle lalle su ruk’a lura da duk wani shige da ficen zee,da duk wani abu da take aikatawa ,in har suka mai wannan aikin toh zai basu mak’udan kud’i kuma a take ya rubuta masu check d’in 200thousand yace insun kammala masa aikinsa zai cika masu sauran,sosai samarin suka ji dad’in wannan aikin daya sasu dan dama sukam sun rigada sun kware akan sama ‘yan unguwa ido waifa a hakan ma ba biyansu ake ba dan k’ashin kansu suke yi,toh yanzun kuma da’aka biyasu irin wa’innan mak’udan kud’in wanda saidai suji kud’in abaki badai su surik’e ba ai aiki kaman yankan wuk’a zasu mai! Sosai suka tabbatar masa akan in Sha Allahu zasu yi mai aiki sosai akanta kar ya damu,daga haka sukai sallama,shi kuma ya k’arasa bakin gate d’in gidan Zee d’in kowai Allah zaisa wani ma’aikacin gidan ya fito.Yakai kusan mintuna 30 tsaye yana nazarin abin yi kuma next,kaman Allah yasan intention d’insa ya wurgo Zee haraban gidan tana kwalama direban ta dake amso mata sak’o wajen baba tsohuwa!

“Sadi direba wai bakaji ina mitan kiranka bane!?”

Ta ida maganar cike da masifa,da sauri Sadi ya k’araso wajenta ya durk’usa yana fad’in:

“Allah huci Zuciyanki uwargijiyata wlh na zaka ban d’akine “

Tsaki taja sannan ta ta6e baki tace:

“Aikin kenan aci aje toilet nikam yi maza kaje nan supermarket ka siyo mun abincin Abul ,”

Ta mik’amasa dubu 10 jiki na rawa sadi ya amsa sannan ya wuce parking lots ya shiga ya tada motar,mai gadi kuma ya soma wangale masa gate.

Jin kamar ana kiciniyan bud’e gate d’in gidan yasa barrister saurin juyar da bayansa ya ciro waya yasa a kunnensa tamkar mai amsa kira.a idonsa direban ya fiddo motan yayi corner da sauri barrister ya k’araso wajen mota yad’an kwankwasa window d’in motar Sadi ya zuge glass din motar yana k’arema Barrister kallo sai yaga tamkar yana kama da Uwar d’akinsa Zee hakan ya sashi tsaida motan dan bama barrister d’in girma,hannu barrister ya mik’a masa sukai musabaha sannan barrister yace:

“Dan Allah kozaka iya ajiyeni nan lugard hall?”

Jim Sadi yayi sannan yace:

“Shugo tam ba damuwa hany’an na nufa nima “

Murmushi barrister ya saki sannan yace:”ngde”

Ya bud’e d’ayan side d’in Sadi yaja motan suka bar unguwan suka hau kan titi a hankali barrister yaja lumfashi sannan yace:

“Hummm unguwan nan da k’arancin mutane yake?”

Ya ida maganar yana mai satan kallan Sadi dan ganin yanayin da zai amsa tambayar tasa,daria Sady yayi sannan yace:

“Wlh kuwa abunka da GRA,jefi-jefi zaka ruk’a ganin mutane a waje “

Barrister yace :”hakane kam,aiki kake yine halan a unguwar?”

Murmushi sadi ya kuma yi sannan yace:”eh wlh yanzun ma abincin yaro aka aikini siya faa,fisabilliahi kaga fa wai abincin yaro wanda baifi shekara d’aya baa wai aban dubu goma insai mai abincin gwangwani kuma fa karkayi mamakin gwangwani 2 ne kawai fa dubu goman ko wanne dubu biyar “

Barrister ya kuma sakin Murmushi sannan yace “asshaa inkanada kud’i babu abinda baza kayi ba wallahi “

“Hakane amman mu talakawa ina mukaga kud’in siyama yaro abincin dubu goma,ai yaro kaman Abul wallahi ya iya cin tuwo miyan kuka an kuma yaye sa,amman rayuwan masu kudi kam ‘yan boko yaro har shekara 3 wai yana cin abincin gwangwani “

STORY CONTINUES BELOW

Sadii ya ida maganar yana mai conner da motar,Murmushi barrister yayi sannan yace:

“Hakane kam talaka bawan Allah,amman matar gidan nada yarane?”

“Eh d’anta d’aya,amman naga tamkar kuna kama da hajian gidan wlh “

“Hhhhhh any’a?in bazaka damu ba inason kamun wani d’an aikine dan Allah “

Kallansa Sadiii yayi sannan yace:

“Kaman name faaa??”

Ciro ID d’insa barrister yayi Na shaidan zamansa cikakken lauya mai zaman kansa ya nuna maa direba,direban na kallo yayi saurin taka birki ya waiwayo ya kalla barrister sannan ya d’an had’iye yawu yace:

“Lafia dai ko barrister ???wani aiki ne zaman haka?kaf mutanen kaduna ka rasa wanda zai ma aiki saini direba?mai nake dashi da zan maka aiki akai?”

Murmushi barrister yayi sannan yace:

“Relax ok?kawai aikin ba mai wahala bane muddin ka bani had’in kai ni kuma na tabbatar maka da cewa zan baka mak’udan kud’i  wanda zai saka barin k’ark’ashin wasu ka dogara da kanka “

Parking sadi direba yayi sannan ya muskuta ya kalla Barrister babu abinda yake hangowa shimfid’e a fuskan bashir d’in sai iyakar gaskian saa daa ya fad’i masa a yanzun!

Yace “Toh toh wani kalan aiki kake so nama kai kuwa?”

“Akan uwar d’akin ka?”

Kaman zararre sadi ya zaro idanuwa yace:”Uwar d’akina kuma?akan mai zaman aiki akanta?wani abun tayine?”

Murmushi barrister yayi sannan ya ciro naira dubu hamsin ya ajiyema direba sannan yace:”are we good to go?”

Kallan kud’in direba yayi yaga ko nasa albashin bai wuce 30k ba amman gashi yanzun nan atake barrister yabasa 50 da kyar ya iya cewa:

“Amman mai kake son sani akanta ne wai!?”

Murmushin gefen baki Barrister yayi sannan yace:”komi ma amman dai inason kasoma min aikin ne kaman haka…..,,,,………

Nandai barrister ta zayyano ma Sidi tas yanda yake son ya masa aiki,jinjina kai Sadi yayi sannan yace:

“Tabbas ranka ya dad’e a kowani safiyan Allah sai Hajia ta aikeni chan zaria na amso mata wani abu acikin bak’in leda amman koda wasa ban ta6a tsayawa na bud’e dan ganin mainene aciki saboda yanayin gargad’in da take mun a kullum akan kar na sake na bud’e abinda ke ciki.Ko yau naje na amso abin wallahi “

Shuru barrister yayi sannan yayi hasashen badai wani abun Zee take sa wa Humy ke bata ba?as in badai wani abun take ma Humyn ba?huuuuuuuu huuuuu wlh Zee ta wuce Zaton sa sosai da sosai Zee makirar macece wlh amman koma dai mainene take sawa ake kawo mata wallahi sai ya binciko,kuma yana gab da had’e mata dukkanin wani shirinta ya wargaza su!”

“Yauwa inaso toh gbe inkaje ka amso abinda take saka amsan kafin ka kai mata straight ka kawo mun nagani bfr ka kai matan kaji?”1

Gyad’a kai sadi direba yayi sannan yace:”in Sha Allah zan kawo maka “

Nandai suka tattauna ya nayin yanda zasu gudanar da aikin nasu sannan sukai sallama.

***********************************

3wks leta a gurguje plss

Sosai da sosai mutanen da barrister yasa sumai aiki akan Zee d’in suka tattaro mai da jawa bai akan abinda take yi ciki harda ruwan nonon Humy da take sawa ana ta tso mata ana kawo mata da kuma yawan zuwanta zaria da takeyi sosai dai Barrister ya girgiza da wannan al’amarin kai Zee batayi ba wlh,kuma tsaf aka bin ciko masa kuma ya gane cewa tabbas wannan tsohuwan k’arya ta masa akan Salame,salamatu dai ba kowa bace face Humairah ,Amman kuma humairan sam sam bata cikin hayyacinta bama tasan wacece ita ba.

Kuma sun k’ara d’ora masa bayanin cewa Zainab tana zuwa wajen wani malami wanda yake zaune achan wani jeji a k’auyan suleja.Sosai da sosai barrister ya tattaro bayanai daga wa’innan mutanen da yasa aiki kuma sosai yake cika bujen ko wannan su da bugun abuja,shiyasa basa shakkan kawo masa ko wani kalan informations da suka samu akan Zee.

Koda wannan bayanan dake hannunsa kawai ya isa ya tona asirin Zee ,amman sai dai bazaiyi hakan ba sai ya tabbata ya gama samun crook evidence sannan sai fallasata abainin duniya.Sosai ya soma shirin bikinsa dan 1wk kawai ya rage yanzun so yake ya gama settling da matarsa sannan ya d’ora daga inda ya tsaya dan hakan zai fi masa sauk’i kuma babu wanda zai d’agoda cewa yana wani abun na sirri,musamman Zeen in taji an d’aga maganan auransa zata iya sa malamimta ya bin ciko mata komai a kansa.k’arshenki dai yazo daf da kusa Zee in Sha Allah “

Musamman barrister yasa aka kuma bin ciko masa al’amarin malamin Zee sosai,dan ya yanke shawaran cewa bayan auran saa tsaf zai taka yaje har gurin malamin tsubbun Zee d’in duk abinda ta Panjama  panjam!

Amman kam tabbas sai yaje wajen malamin ya mai magana face to face!………………✍🏻

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *