HEEDAYA CHAPTER 54 BY By Khaleesat Haiydar

HEEDAYA CHAPTER 54 BY By Khaleesat Haiydar

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Heedayah ta ki yarda su hada ido, yana kallonta yace “Why were you eavesdropping?” Kin cewa komai tayi, bayan 

few seconds ta d’an daga kai suka hada ido da shi, ji tayi gabanta ya fadi ta fara kame kame, da sauri ta juya xata bar 

wajen taji ya riko wrist dinta, ta kalli hannunsa, 6ata fuska tayi taki bari su kara hada ido tace “Ni bana so ya 

Shureen, I wasn’t eavesdropping, zobe na ne ya fadi nake dubawa kuma ban gani ba a wajen” Lkci daya tayi shiru, 

can tace “Toh ka sake ni” Yace “In contrast to that?” Kamar xata yi kuka tace “Ni dai ka sake ni” Dago kanta yyi 

yana kallon tun daga lips dinta har xuwa eye balls dinta, suna hada ido, ta rufe bakinta da hijab dinta da sauri tuna 

wani abun da tayi, gabanta ya shiga faduwa, saketa yyi a hankali yace “Kin dai makale kina sauraron ranan da xa a 

kawo gaisuwar ki ko?” Ita dai bata ce masa komai ba, yace “To nan da sati biyu ne” Turo baki tayi tace “Gaisuwana 

da wa?” Yace “Ahmad Junaid” Ta 6ata fuska tace “To ni nace ina son sa da aure ne, bayan shi yayana ne, ta ya xa ace 

xa mu yi aure???” Yace “Ta yanda ake yi” hawaye ya kawo idonta tace “Ni dai baxan iya ba, ta ya xa ace haka” Yace 

“Toh kina da wanda kike so ne?” Tace “Ehh” Yace “Waye shi?” A takaice tace “Khaleel…” murmushi yyi yana 

kallonta yace “Sai ki gaya masu” Ta share idonta a hankali tace “Ni baxan iya ba” Yace “Why?” Tayi shiru, yace 

“Idan ma kin iya fada masu Allah ya sa su bar ki da shi” Tana kallonsa da sauri tace “Me yasa baxa su bar ni da shi 

ba??” Yace “Aa ban sani ba, ae xa ma su bar ku” Shiru tayi bata ce komai ba, ya fara tafiya ta bi bayansa har suka 

dawo parlor, juyawa yyi yana kallonta yace “You rinse another cup and make me a cup of tea” Ta kalli shayin da 

suka bari a parlon tace “How will I use a cup without rinsing it at first?” Ya xauna yana kara kallon shayin yace 

“Rinsed or not…. We left it open” Ta hade girar sama da ta kasa, shi dai idonsa na kan tv dake aiki a parlon, ta karaso 

ta durkusa ta dau shayin ta wuce kitchen, ba a dau lkci ba ta fito ta ajiye masa wani shayin, dauka yyi yace “Did you 

come over to kano with ur laptop?” Tace “Eh” yace “Let me see” shiru tayi tana kallonsa, can tace “Ina son tambayar 

ka ya Shureen” Ya daga kai ya kalleta yace “Ok… but before then, what’s Shureen?” Tace “Nima ban sani ba” yace 

“Don’t call me that again” Ta d’an ta6e baki don ba kallonta yake ba, can tace “Me yasa lkcn da nake gidanku baka 

min magana, baka kulani sai yanxu? This is really weird” Yyi shiru yana kallonta directly in the eyes, can ya d’an yi 

murmushi yace “Apart from you… kin ga ina kula kannina ko wani a gidan? And if I am not mistaken kin ta6a min 

wnn tambayar kwanaki ae” Ta buda masa hannu alamar bata san ko yana kula kannin nasa ba snn tace “I am asking 

you again because ina mamaki ne har ynxu, I never knew u can talk for 3 mins without stopping, why ur sudden 

change toward me??” Kallon cup din hannunsa ya dinga yi kafin yace “Baki ta6a xuwa kin tareni ko kin xo inda 

nake kin min magana naki kulaki ba, ko an ta6a haka duk period din da kika yi gidanmu?” K’in cewa komai tayi, ya 

ajiye cup din hannunsa yace “Look Heedayah, babu abinda xaman ki a gidanmu ya rageni da for good 5 years da 

kika yi tare da mu, tun kafin Abba ya kawo ki responsibilities dina ya fita kansa I was independent then, rayuwa 

kawai nake yi a gidan, balle ace ko haushin wani abinda xa ayi maki nake, kinga ynda nake da kannina har yanxu, 

Even my Grandmum I don’t spend much time with her, So why didn’t u complain about them too…” Heedayah ta 

girgixa kai kawai, yace “Ohk let me let you know this, At first I was confused xuwan ki gidanmu, coz then my family was a happy one, all of a sudden xuwan ki abubuwa suka fara faruwa marasa dadi, and I can’t just disappoint 

my Mum a lkcn, I don’t want to double her disappoinment, nasan kina bukatan taimako sosai at then I even advice 

Abba ya bar ki gidan Marayu and I will take every responsibility naki a can, snn I promise duk weekend xan dinga 

xuwa duba ki, shi ma idan yana da lkci sai ya je, but he was reluctant, ni kuma na kawo idea din ne ganin Mumy 

baxata ta6a rike ki ba no matter, a ranan da kika dawo gidanmu da Mami da daddare mum dita ta kirani daki…” 

Shiru yyi, Heedayah dai sai kallonsa take, can ya girgixa kai yace “I don’t want to say anything about that, you can’t 

make me say anything about that, but just know that there is no one to console her, and I have no choice then to 

follow her instructions ko xata samu sauki ta wani bangaren, because of you or Mami baxan iya bata ma mahaifiyata 

ba tunda dai abinda tace inyi ba abinda xai cuceni ko ya cuce wanin ku bane, shi yasa ko karatu naki koya maki idan 

kin tuna….” Heedayah dai kawai murmushi tayi, Yace “Get this, I am not telling you all this for you to change ur 

silly thinking toward me, stick to ur thinking” Heedayah tace “Toh ka ci gaba ina ji” yace “Ohk… Duk da bana maki 

magana bana shiga harkan ki a gidan mu, ni nasan irin taimakon da na maki wanda ke baki sani ba kuma baxa ki 

ta6a sani ba, just know that i kept an eye keenly on you, ban bada room for anyone to get you harmed ba duk da ko 

kowa yasan bna sake maki a gidan, kuma sake maki da bana yi yasa bbu wanda xai kawo xanyi abubuwan da na 

dinga maki most especially my mum, I missed a lot of opportunities don kada inyi nisa da ke ki cutu, har kika bar 

gidanmu you weren’t safe, barin ki gidanmu ya bani courage din tafiya soldier da ban tafi ba bayan na sake samu for 

the 3rd time, ko da ace ni din me magana ne rashin maki magana a lkcn shine mafi alkhairi Heedayah, balle ma ni 

bani da lkcn magana, a ta dalilinki Mahaifiyata ta jefa kanta ga halaka wanda har gobe nake fatan Allah ya ganar da 

ita, but ban ji haushin ki ba duk da ta dalilin ki hakan ya faru, ni dai kawai I made sure I protect you by all means” 

Heedayah tace “Wai Protect me from what?” Yace “Bana tunanin gaya maki xai maki wani amfani, Back to what I 

was saying…. Duk da biyayyar da nake ma mahaifiyata sai da na tsallake umarninta na bi ku har New Delhi na duba 

lafiyar ki, kuma da kike cewa ashe ina maganar minti uku without stopping, go ask Zainab, I talk when I am 

comfortable doing so, kuma da ita kadai nake magana haka sae ko colleagues dina, ko kannina baki ga ina masu 

haka ba, it’s a 

nature I know I can’t eradicate, coz I’ve tried my best doing so but no result, Kar fa kiyi tunanin don ki canxa 

ra’ayinki a kaina nake gaya maki abubuwan nan…” Yana fadin haka ya mike ya dau laptop din yace “Idan na shigo 

gobe, will bring u ba
ck ur laptop, idan kuma ban xo ba sai Thursday, good night” Bin sa da kallo tayi ganin ya nufi 

kofa tace “Toh shayin fa?” Juyowa yyi ya kalli shayin yace “Oh, thank you” daga haka ya fice ya kulle kofar, tafi 

minti biyar xaune tana naxari kafin ta mike ta karasa kujeran da ya tashi ta dau shayin ta xauna ta fara sha. Heedayah 

na gama shirin kwanciya Ammi ta shigo dakinta tana kallonta tace “Ki xo ku gaisa da Abbanki” Daga haka Ammi ta 

juya ta fita, Heedayah ta dau hijab dinta har kasa ta saka snn ta bi bayanta har xuwa babban parlon Abbanta, Yana 

xaune ta shigo parlon ta durkusa kasa gefensa ta gaishesa ya amsa da murmushi yace “Kun xo lafiya Heedayah?” 

Tace “Alhmdllh, Ya aiki Abba” Yace “Mun gode Allah, ya kika baro iyayenki na can” Tace “Duk suna lafiya, suna 

gaisheku” Yace “Toh maa sha Allah, hope babu wani matsala baki bukatar komai” Tace “Abba ina son in canja waya, 

ban xo da nawa ba” Yace “Toh xa a kawo maki gobe idan Allah ya kai mu” Tace “Toh nagode Abba” Yace “Allah 

yayi maki albarka” Tana murmushi tace “Ameen, kuma Abba wani makarantar xan yi ynxu?” Yace “Aa wnn we are 

not to decide, iyayenki na can xa su yi deciding ko?” Ta gyada masa kai tace “Toh Abba” Yace “Sai ki tambayi 

Barrister, ko Hajiya Rahinah” Tace “Toh” Nan tayi masa sai da safe snn ta mike ta fita parlon, bangaren Ammi ta 

koma tana shiga parlonta taga wayarta kan kujera ta dauka ta wuce dakinta, sai bayan da ta kwanta tayi dialing 

number Farida da ta haddace, Farida na dagawa da taji muryarta tace “Why did you leave ur phone Heedayah?” 

Heedayah tace “Mancewa nayi, ya Mami fa” Farida tace “Alhmdllh, kun isa lafiya?” Heedayah tace “Lafiya lau” 

Farida tace “Kun hadu da Ya Shuraim?” Murmushi Heedayah tayi tace “Ehh, ya ma ce in gaishe ki idan muka yi 

waya” Farida tace “Ki gaisheni kuma??” Heedayah tace “Ehh mana, sai da ya tambayeni me yasa ba mu xo tare ba, 

Kinga dama kun kusa mid semester, kawai ki taho nan kiyi hutun” Farida tace “Toh ai Mami might not let me” 

Heedayah tace “Ba sai Ammi tayi mata magana ba” Farida tace “Uhm” shiru Heedayah tayi kafin tace “Ya Khaleel 

sun kai Lafiya?” Farida tace “Ehh daxu suka yi waya da Mami” Da sauri Heedayah tace “plss ki turo min number da 

ya kira da shi” Farida tace “Wani number Mami ne da ta bashi ya sa a karamin wayar Ya junaid” Heedayah tace 

“Send me the number plss” Farida tace “Ohk I will now, but tell me Ya Shuraim din kullum yake xuwa?” Dariya 

Heedayah tayi tace “Eh mana, kullum sai ya xo, ni dai ki turo min number yanxu” Daga haka ta katse wayar, cikin 

few minutes sai ga number Farida ta turo mata, bude kofar dakinta aka yi Ammi ta shigo tace “Ke kika dau wayata” 

Heedayah ta marairaice tace “Ehh Farida na kira” Ammi tace “Ina naki wayar?” Heedayah tace “Na mance a 

Kaduna” Fita Ammi tayi daga dakin, Heedayah tayi dialing number da Farida ta turo mata, yana fara ringing tayi 

murmushi, Daga kiran aka yi amma ba ace komai ba, a hankali Heedayah tayi sallama, Khaleel dake kwance har ya 

fara bacci ya bude idonsa dake a lumshe bayan ya daga kiran yace “Heedayah?” Tayi murmushi tace “Ka gane 

muryata ashe, good evening” Yace “Evening, Mami tace min kun tafi kano” tace “Ehh bayan kun tafi muka wuce” 

Yace “Yaushe xa ki dawo?” A hankali tace “Lkcn da xaka dawo” Shiru yyi kafin yace “Uncles dina sunce sai next week” Tace “Nima next week xan dawo” Yace “Toh Allah ya kai mu lafiya” Tace “Ameen” Shiru ne ya biyo baya, 

bayan few seconds a hankali yace “In tambayeki Heedayah” Tace “Ina jin ka” Jin bai ce komai ba tace “Hello?” 

Yyi kasa da murya yace “Xa ki iya aurena?” Sosai gabanta ya fadi, a hankali tace “Me yasa ka min wnn tambayar?” 

Yace “Ina ga kamar baxa ki yarda ki aureni ba” Tace “Toh ka daina wnn tunanin” Yace “Ban ta6a son ‘ya mace ko 

kula ‘ya mace duk tsawon rayuwata ba sai kanki Heedayah, ni kai na ban san irin son da nake maki ba, ko fado min 

kika yi sai naji xuciyata ya dameni, and I have to nurse it for sometimes kafin in dawo dai dai, kin san condition dina 

Heedayah kar ki gujeni plss” a sanyaye tace “I won’t in sha Allah….” A hankali yace “But have you ever thought of 

living In same roof as husband and wife with someone that was once a Hoodlum??” Hawayen dake makale idonta 

ya gangaro cikin sanyin murya tace “I am happy u said with someone that was once a Hoodlum, I love you not 

minding ur past dear” Jin yyi shiru bai ce komai ba, a hankali tace “Are you there?” Yace “Sure, I love you with 

every breath of mine” Murmushi tayi tace “I love you same” Yace “Xan kwanta yanxu, coz I am very tired, how can 

I reach you always?” Heedayah tace “Ae wayar Ammi ne you can call me anytime” yace “Baxan dameta ba?” Tace 

“Aa” yace “Alright, thank you, sleep tight” Tace “But have u eaten?” Yace “Sure na ci abinci” Tace “Alright, Sweet 

dreams” Yace “Yes love” Daga haka ya katse wayar. Washegari da sassafe Heedayah ta tafi gaida Abbanta a 

bangarensa, Yakumbo ta samu a parlon, Ta duka ta gaida Yakumbo snn ta gaishesa, Yakumbo tace “Amadi in ji dai 

baxa a wani lafta uban lkci ba idan masu auren yarinyar nan suka xo, kaga gwara kasan ka sauke nauyinta a kanka, 

don kana gwamna bbu ruwanmu da lalacewar tura yarinya kasashen shegu karatu, gwara idan an mata auren mijin 

ya kai ta can ya jira har ta gama barin ma wayayye xata aura d’an boko” Shi dai Abba bai ce komai ba, Yakumbo 

tace “Kayi shiru” Yace “Aa su xa su yanke lkcn da yyi masu ai Yaya” Yakumbo tace “Aa ni fa babban damuwata 

Heedayah fa tana da budadden ido wllh, yanxu tana ganin fuska xata fara hotuna a babban gidan nan ta baxa shi a 

yanar gizo ayi ta yawo da shi ana cewa ai yar gwamna gari kaza ce, to kafin hakan ya faru gwara a mata aure don ni 

baxan ji dadi ba, ba naga yanda ‘Yan yan manyan kasan suke ba, wani ma kusan a tsirara xai yi hoton” Abba dai bai 

ce komai ba, Yakumbo ta mike tace “Mu kam da mutunci da martabar mu, bamu yada al’adarmu da kunya ba don 

mun samu duniya” Abba na kallon Heedayah da hawaye ya kawo idonta yace “Ae kina son yaron ko?” Lkci daya ta 

fashe masa da kuka tace “Abba a matsayin Yaya na daukesa fa, ni bana sonsa” Da mamaki yake kallonta, can yace 

“Baki son sa?” Ta gyada masa kai hawaye na sauka idonta, yace “Kina da wanda kike so ne?” Nan ma ta gyada masa 

kai, yace “To waye shi?” A hankali tace “Khaleel” Abba yace “Waye kuma Khaleel?” Shiru tayi bata ce komai ba, ya 

dinga kallonta yace “Who is he?” Kasa basa amsa tayi, yace “Talk to me a ina yake?” Ta girgixa masa kai kawai, 

bayan wani lkci yace “To tashi ki tafi” Mikewa Heedayah tayi ta fita daga parlon, part din step mum dinta ta tafi, a 

parlonta ta sameta tana feeding din Islam, Ta xauna kusa da ita ta gaisheta, da fara’a ta amsa tace “Har kin tashi 

Heedayah” Heedayah tace “Na tashi Aunty” Mum Islam tace “To ya gajiyan jiya” Heedayah tace “Alhmdllh” Mintin 

Heedayah kusan talatin a parlon kafin ta mike tace mata xata je ta gaida Kaka, tana fita parlon ta tafi wajensu kaka, 

Kaka na ganinta tace “Yauwa gantalallun masu aikin nan shiru shiru ban gansu ba, gashi ki kira min Shureen in ji ya 

jikinsa” Heedayah ta amshi wayar tace “Toh wai me ya samesa ba ya warke ba har ya xo jiya” Kaka tace “Atoh 

kuma baxan ji yanda ya kwana ba, bashi da kowa fa garin nan Allah ya rufa masa asiri na dawo garin” Heedayah ta 

tabe baki ta nemo numbersa tayi dialing ta mika mata, yana fara ring ya daga, kaka tayi sallama, ya gaisheta tace “Ya 

ka kara jin jikin Shureen?” Yace “Naji sauki” tace “Toh Allah ya kara lafiya, ka fita aikin ne?” Yace “Ehh” Heedayah 

ta amshi wayar ta kai kunne tace “Ya Shureen you didn’t go with the laptop Charger, kuma charging bashi da yawa 

kamar” yace “Ohk baki bani ba” tace “Are you coming to collect it?” Yace “Ohk I will” Tace “Tohm sai anjima” 

Daga haka ta katse wayar, Kaka ta rike ha6a tace “Yaushe kuma ku ka fara shiri da Shureen har kuna juya yare??” 

Dariya Heedayah tayi tace “Aa ba shiri muke yi ba, kawai abu na ya ara” Kaka tace “Meye ya ara?” Heedayah ta 

ajiye mata wayarta tace “Idanuwan kaka” Daga haka ta fice da sauri daga parlon tana dariya. Bayan Magrib 

Heedayah na xaune kan darduma ta idar da sllh daya daga house maid dinsu ta kwankwasa kofar dakinta, mikewa 

tayi ta isa gun kofar ta bude, Maid din ta gaisheta da ladabi snn tace “Hajiya tace ki je” Heedayah tace “Ohk” juyawa 

Mai aikin tayi ta wuce, Heedayah ta cire hijab din jikinta ta linke ta ajiye snn ta fita xuwa bangaren Amminta, Ammi 

na kallonta bayan ta shigo parlonta tace “Waye kika kira da wayata?” A hankali Heedayah tace “Khaleel ne” Ammi 

tace “Waye Khaleel?” Heedayah ta sauke kanta tace “Yayan Junaid”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *