RANA DAYA CHAPTER 11 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI

RANA DAYA CHAPTER 11 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI

Www.bankinhausanovels.com.ng 


Mun tsaya 

Don Allah tashi muje koda zugata kayi ka
ji?” Abokina haka sai ya gaji da matsin Shatima ya tashi suka fita.
Allah yasa bata kai ga shiga cikin daki ba, lokacin da suka yi sallama a falonta. Bayan sun gaisa Shattima ya shiga kame kame ya rasa ta inda zai bullo ma al’amarin. Www.bankinhausanovels.com.ng
Ya ce, “Kaka nasan dai muna tare ko me nazo da shi, ba za ki kware min baya ba.” Hajiya ta ce, “Kayi magana kai tsaye ni bacci nike ji in shiga ciki, don ka taki sa’a yau a nan nayi sallah.”

Ya ce, “Ko kin shiga sai na bi ki. Dama dai ta hudun ce na samu, shi ne ni ke son ki sa ba ki a jone ta cikin bikin.”
Ta hade fuska, “Kai bana son maida bara bana, an riga an wuce nasan tunda kayi uku ai dole zaka yi ta hudu, amma ka bari sai can gaba.”
Ya ce, “Haba Kaka! Don Allah ni a hada rana daya, dama su hudu na gani a cikin gara kawai mafarkina.” Taja tsaki, “Mafarkin ka na banza tunda kai ba Annabi ba ne ba wani tabi’i ba ko Malami, har wani mafarki ke gare ka?”
Munnir ya ce, “Shi ne nima na gani da anyi magana sai ya ce mafarkin shi.” Shatima ya dubi Munnir, “Haba abokina! Kai fa ka san komai.”
Ya dubi Kaka, “Wallahi yarinyar Marainiya ce, na san ki da tausayi.” Ta ce “Ni har a fada min maraici, ni da ubana ya mutu tun ina ciki, uwata kuma ran da ta haife ni ta rasu?”
Shatima ya ce, “To ni dai kiyi hakuri in Alhajina ya zo ki ce kin yarda. Ta soma yunkurin mikewa. Munnir ya yi saurin mika mata sandarta. Ta amsa tare da fadin “Na gode dan nan kaje gida gurin iyalinka ka fita batun wannan uban wautar. Shatima ya taimaka mata har cikin daki yana kara rokonta amma sam ta ki magana. Www.bankinhausanovels.com.ng
Bayan ya sauke Munnir ya nufi gida. Bai zaci zai samu Hajiyarshi a falo ba tun da sha daya ta gota, bai ma lura tana nan ba sai da ya nufi samanshi ya ji ta ce, “Kai zo nan.
Gabanshi ya fadi, don tun jiya ta fada mishi cewa tana son ganinshi. Da safe a gurguje ya gaishe su wai yayi latti, da yamma ma haka ya yi ta goce ma haduwarsu, yanzu kuwa an ritsa shi.”
Ya zauna gabanta, “Gani Hajiya.” Ta ce, “Wai ka manta na ce ina son ganinka ne ka ke ta yi min goce-goce?” Ya ce, “A’a abubuwan ne, kiyi hakuri.”
Ta ce, “Ni ban yi fushi ba amma zan yi “Ai matsawar ka kasa fada min gaskiya.” Ya ce, ” ban taba yi miki karya ba Hajiya.” Ta ce, “Mene ne gaskiyar zancan da Momiyo ta fada min, wai ka samu mace ta hudu, haka ne?”
Ya ce, “Haka ne, dama da safe zan zo muku da batun.” Ya daure ya kau da tsoron shi ya fada. Ta ce, “To wannan karon babu hannuna a ciki, kaji na fada maka.” Ya ce, Hakuri za ki yi Hajiya, in na cike ai ba sauran in da zan saka wata ko?”Ta ce, “Tunda kai naga kamar Namamajo ne sarkin mata ai in ka hango wata zaka iya zuwa ka saki wata ka shigo da wata.
Ya ce, “Haba Hajiya, kar ki yi min fatan haka. Ki daure ki sama abin albarka gaba daya.” Ta mike tare da fadin, “Ba zan sa ba, dama kai ni ke jira in ji tabbaci, in haka ne in ce maka ba da yawuna ba.” ta nufi dakin Maigidanta ta bar shi nan zaune turus ya rasa tunanin da zai yi. Www.bankinhausanovels.com.ng
Ya mike yana rangaji ya nufi samanshi, zuciyarshi bata taba mai zafi irin wannan ba, gani yake kamar gara ya fasa auren sauran matan guda uku ya auri Salma kadai, domin ita ce ya dauki alkawari tsakaninshi da MahaliccinShi zai taimake ta.
Ya kalli abincin shi, ya kauda kai. Ya nufi gadon shi ya fada. Ruf da ciki ya kifa kanshi a kan filo, rabin kan shi ya soma ciwo, ya rasa tunanin da zai yi.
A haka bacci ya soma fizgarshi. Can kuma sai ya soma jin sanyi, yaja bargo. Abin kamar wasa sai jiki ya yi zafi.
Haka ya kwana, yana jin agogonshi yana kiran sallah amma ya kasa tashi. Badi’atu tazo kawo mishi abin kari sai ta ganshi a bargo, yana ta rawar sanyi ta ce, “Yaya! Yaya!!”

RANA DAYA

Da kyar ya ce”Kira min Hajiya.” Da gudu ta sauka, tun daga benen take kwala ma hajiya kira. A falon Alhaji ta same su tana kokarin hada ma Alhajin shayi.
A tsorace ta waiwayo ta ce, “Mene ne?” Ta ce, “Yaya ba shi da lafiya.” Alhaji da ke cikin dakin baccin shi ma ya fito da sauri.
“Ba shi da lafiya kuma?” Badi’atu ta ce, “Eh, yana ta rawar sanyi.” Gaba dayansu suka nufi saman. Sun tsorata da ganin yanayin shi, domin gaskiya ba shi da yawan ciwo.
A tare suka bude bargon, ya kanannade
jikinshi yana ta bari. Alhaji ya kama shi ya
tallafo mishi kai. “Babana me ke damunka?”
Hajiya ta ce, “Badi’atu, maza ki taso Mustapha ya fito da mota, yi sauri.” Ta tafi da gudu.
Uban ne ya tallafe shi suka sauka kasa zuwa mota. Alhaji ya koma ya cire malun-malun yasa jallabiyya ya dauki kudi. Asibiti mafi kusa suka je ana shiga dashi, Likitan baya nan.
Alhaji ya hau fada, yana cewa wane irin Likita ne har yanzun bai zo asibitin shi ba. Nurse  ta ce, “Yi hakuri Alhaji, bari a kira shi, gidan shi babu nisa. Sauran Nurses kuma suka sa shi a gado don yi masa taimakon farko. Sun duba shi suka sa
masa ruwa tare da allura. Www.bankinhausanovels.com.ng
Iyayan da Mustapha kaninsa suna tsaye a kanshi suna yi masa sannu har lokacin jikinsa yana rawar sanyi, gashi ba su rufe shi ba, kuma sun kunna fanka.
Likitan ya shigo da sauri. Ya ba Alhaji hannu suka gaisa, Alhaji ya ce, “Haba Likita! Bai kamata ace ba ka fitowa da wuri ba, asibiti mai zaman kanshi a ce an zo babu Likita?”
Ya ce, “Kayi hakuri Alhaji, jiya sai kusan karfe uku na dare na bar asibitin nan mutum uku muka yi wa tiyata. Ya isa gaban Shatima ya soma da bude idanunsa yana tambayar abin da ke damunsa.
Alhaji ya ce, “To mu dai lafiya ya kwanta jiya.” Hajiya ta ce, “Ni da har magana mun yi da shi kafin ya kwanta din ma.”
Likitan ya taba jikinshi ya ji rau da zafi. Ya dubi ‘su Alhaji ya ce, “Ku dan zauna a waje.” Suna fita ya cire ma Shatima ruwan sannan ya taimaka mishi ya cire rigar jikinshi. Shatima ya ce, “Sanyi ni ke ji.” Likita ya ce, “Kar ka damu, zaka daina ji yanzun.” Ya kalli Nurse din da ke tsaye ya ce mata ta kawo mishi wata allura, ya fada mata sunan
allurar ta fita. Ya maida masa ruwan yana ci
gaba da yi masa tambayoyi. Bayan an kawo allurar ya yi masa ita a cikin ruwan, sai ya ce “Kar ka damu gajiya ce da zirga-zirga, sai kuma rashin bacci. Yanzun za ka yi bacci ka huta a nan zuwa jibi zaka wartsake sarai.”
Shatima yayi saurin kama hannun Likitan mai kokarin fita. Ya ce, “Likita don Allah ina son kayi wani taimako daya, nima dai taimakon zan yi. Www.bankinhausanovels.com.ng
Likitan ya dawo ya tsaya. Shatima ya ce, “Ina son ka ce ma iyayena damuwa ce ke tare da ni, don haka kada suke yawan matsa min, kuma ka ce musu su tambaye ni damuwar don suyi saurin kauda min ita saboda zata iya haifar min da wani ciwo.”
Likitan ya ce, “Amma kai Lauya ne ko?” Shatima ya yi dan yake tare da fadin “A’a.” Likitan ya ce “Ka iya tsara magana. Zan fada
musu haka din tunda ba
cewa kayi a ce kana da wani ciwo ba.”
Ya leka ya ce, “Alhaji za ku iya shigowa.” Suka shigo. Allah Sarki, iyaye duk sun damu suji me ke damun dansu har suna hada baki gurin tambayar Likitan “Me ke damunsa?” Ya ce, “Akwai rashin samun ishasshen bacci, zirga zirga da gajiya.
Sannan kuma akwai wata damuwa a tare da shi wadda ya ki fada min ita. Ya kamata ku san ta don kuyi gaggawar raba shi da ita, domin zata iya haifar masa da katuwar matsala.”
Suka ce, “To Likita, zamu bincika.” Yana fita Hajiya ta ce, “Shatima me yake damunka ne ka boye mana?” Alhaji ya ce, “Haba Hajiya, ki bari tukunna ya samu sauki mana. Zai fada mana kuma za a magance ta.”
Shatima na jin su ya yi lamo, a hankali naman jikinshi ya daina rawa, bacci ya kwashe shi.
Labari ya watsu a dangi cewa Shatima yana asibiti. Nafisa ta samu labari, hankalinta ya tashi take ta fasa zuwa Makaranta ta ce “Mama ba zan jira ku ba, bari in je in ganshi.” Ita ce ta fara zuwa a cikin Amaren Shatima.
Lokacin da ta zo Hajiya tana zaune a bencin kofar dakin da wasu kawayenta. Nafisa cikin kunya ta durkusa ta gaida su, ta kuma tambayi jikin nashi. Hajiya ta ce, “Da
sauki, ki shiga yana dai bacci, Mustapha ma yana ciki.”
Tana shiga idanunta na kanshi, yana kwance sambal jikin shi babu riga, tausayinshi yasa idanunta kawo ruwa. Ta kalli Mustapha.yaya me ya ke damunsa?” “Zazzabi ne kawai, kar ki damu. Da ya farka
zai warware.” Muryarta na rawa ta ce, “Allah
yasa haka. Allah dai ya ba shi lafiya.” Mustapha ya tashi daga kan kujerar da yake zaune ya ce, “Ki zauna.” Ta ce, “A’a da ka bar shi.” Ya ce, “Bari in dan fita in mike kafa ma. Ta zauna shi kuma ya fita. Ta tsura ma halittarshi ido, a ranta tana godiya ga Allah da ya zaba mata Shatima a miji.
Tamkar ta kai hannunta ta dafa nashi, amma
sai ta tsawaci zuciyarta don addininta bai bata damar yin hakan ba.
Lokaci-lokaci mutane na shigowa duba shi su fita. Iyayen Nafisa suka iso har su Hamida. Dauke da kuloli da kalolin abinci da kayan Www.bankinhausanovels.com.ng
shaye-shaye. Su kansu masu asibitin sun shaida cewa dan gata ne ya zo jinya asibitinsu, tunda ba a yi awa shida ba amma motocin da suka shigo ba a magana.
Abokan Alhaji kawayen Hajiya ga kuma dangi. Haka nan sai waya ake buga ma Jama’a, ana fada musu Shatima yana asibiti. Nafisa ta ce ma Mustapha lokacin da ya dawo dakin Ban ga Munnir ba.”
Ya ce, “Ai ko ina ga bai sani ba.” Nan take ya kira shi ya fada masa. Ashe kuwa bai sanin ba, ya ce yana ta buga wayar Shatima ba a daga ba.
Mustapha ya ce “Duk wayoyinsa suna gida. Bari ma yaje ya dauko.” Ya fita ya fada ma Hajiya, ta ce yaje ya dauko ya samu missed call sama da talatin.
Yana dubawa ne ma ya kira lambar Aliya da aka sa my love, ya fada mata. Ya kira sweety sai da ta daga ya ce, “Amna ce?” Ta ce, “Ni ce Nafisa.” Mustapha ya ce, “Ok.” Ya kashe ya samu ta Amna.
Itama ya fada mata. Ta ce, “Me ke damunsa?” Ya ce “Zazzabi ne. Ta tambayi sunan asibitin ya fada mata. ya kira Kaka, Maryama ta daga, ya ce “Maryam ki ce ma Kaka Yaya Shatima yana asibiti.
Kaka ta rude ta ce, “Maryama ta kira shi. Da ya fada ma Hajiya nan ta rufe shi da fada. Ta ce, “Wa ya ce ya fada ma Kaka?” Sai ko ga kiran Kakar a wayar Hajiya tasa Maryama ta kira.
Tana dagawa ta ce, “Maza ki sa a zo a ďauke ni in ga jikin dan nan.” Hajiya ta ce “Da kin hakura jikin nashi da sauki.” Ta ce “A’a ban yarda ba, a zo a kawo ni. Jiya ban yi baccin kirki ba na rasa me ke damuna, ashe jikinsa ne.” Www.bankinhausanovels.com.ng
Hajiya ta ce, “Shi ke nan gashi nan zai zo yanzun.” Ta kalli Mustapha, sai kaje ka dauko ta dan sarki a surutu da ka tada mata hankali.”
Aliya tana asibiti lokacin da Mustapha ya kirata ya fada mata ciwon angonta, duk hankalinta ya tashi. Taso taje gida ta canza kaya amma zuciyarta ta fada mata ciwon da aka kwantar da mutum, kuma har aka kira ta aka faca mata gaskiya da matsala.
Ta dauki uziri, sannan ta dubi kawarta Aisha ta ce, “Kina ga in tafi a haka?” Ta ce “Kijo mana ai kayan ki a goge suke tsaf!” Ta kira

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *