ABBAS CHAPTER 14

ABBAS





CHAPTER 14






‘Kasa Teemah ta maida idanunta batare data yi niyyan yi masa magana ba dan rawar da jikinta keyi ma ka’dai ya isheta ba sai ta ‘kara da wata damuwar ba sanadiyyar ganowa datayi cewa Abbas din zahiriyya ne ba mafarki ba, bugu da ‘kari ma ita babu wanda ya ta6a ha’da jikinta dashi tunda take hatta da Abbas da Mahmud ada iya kacinta dasu surutu ne na fatar baki, amma sai taga Yah Abbas ‘din yau kamar bashi ba tsoro ta keji sosai dan batasan yau kuma da wacce kalar masifar yazo ba, ‘kila yau kan zaneta zaiyi tunda ranar ma bata yi magana bama ya daka mata uban tsawa ballantana yau da tayi masa dogon surutu.

Agogon hannunsa ya kalla sai yaga lokaci ya ‘danja dan haka sai ya raba jikinsa da nata, hannu yasa a aljihu ya ciro wani ‘karamin case ya bu’de hannunta ya sanya mata shi ahannun ya kuma rufewa.

Sai ya saketa ya juya da sauri ya nufi ‘kofah taku ‘daya ana biyu sai ya dakata cak ya tsaya amma be juyo ba yana kallon ‘kofan yace ” _ina miki fatan alkhairi arayuwar auren ki Fateemah”._

Be sake juyowa ya kalleta ba kawai ya sa kai ya fita daga ‘dakin ita kuwa tsaye tayi kawai ta bishi da idanu har ya 6acewa ganin ta, kawarta da ke kwance agadon da tun ‘dazu ta ke kallon ikon Allah sai ta taso da saurinta ta iso wurin Fatiman,” _Fateema wai meke faruwane waye wannan ‘din,? shine mijin naki ,? shi zaki aura ?”_
Ta jero mata tambayoyin ‘daya bayan ‘daya da buri, samun amsarsu daga bakin Teemah.

Yayin da ko kallon kirki bata samu daga Teemahn ba ta dai ka’da mata kai alamar kawai alamar _”a’a”._

Kwafah yarinyar tayi yarinyar sannan ta sake fa’din _”meaning”_!!!

Shiru Teemah tayi kamar ma bada ita yarinyar keyi ba.

Data ga haka itakuwa sai kamo kafa’dar Teemahn da nufin dawo da attention ‘din Fateeman zuwa gareta.

Teemah dan haushi sai ta dallah mata harara take takuma juya kanta da nufin _kin_ _dameni_ sai taci gaba da kallon ‘kofar da ya fita ‘din ji take tamkar zata ganshi yasake dawowa.

Yarinyar bata damu ba sai ma wasu tambayoyin data sake bin Teemahn da shi.
” toh wanene shi naji yana cewa fatan alkhairi ko minene dai namanta, dan Allah ki fa’da min waye shi ?
Tafa’da tare da dawowa ta fuskanci Teemah
dan ita harga Allah bata san shi ba bata ta6a ganinsa bama ‘ kawar Fatima ce da suka ha’du lokacin sunje yin wani programme a (Y C A) Yobe Childrens Academy, bata ma san ina yarinyar tasamu labarin bikin ba shine harta wani zo da sassafe ita adole me ‘kawa, dan ita Teemah bata gayyaci kowa ba, ‘kawayenta na makarantar su ma duk zuwan kansu ne Teemah ‘kin yin gayya tayi wai bata son damuwa, mummy tayi-tayi da ita harta gaji gaskiya ba laifi Teemah akwai taurin kai, akan hakan Mummy takan ce mata ” mutum fah rahama ne Teemah ko su ka’dan ne ki daure ki kai musu invitation card ‘din ai zasuji da’di”
Teemah azuciyarta cewa take ” sun da’de basuji da’din bai ndai har se naje na gayya toh su ne”
dolen mummy ta ha’kura ta ‘kyaleta kawai akan ra’ayinta, dama ita Mummyn so takeyi Teemah tasamu masu ‘debe mata kewa amma tunda ta’ki sai mummyn ta kyaleta

Story continues below


Haka duk wacce taji labari inta yi ra’ayi sai tazo wacce kuwa taga bazata iya ba sai tayi zamanta.

Kafin Teemah tayi magana sai ga Ummah tashigo bayan ta da wasu mata guda biyu mummy kuma na bayansu hannunta ri’ke da kaya da wata jaka.

_” kin yi wankan?”_
Abinda Ummah ta fara tambaya kenan data shigo, Teemah sai ta maida idanunta ‘kasa dan bata san me zata ce da Ummahn ba ahalin yanzun bayan duk kashedin da ta mata akan ruwan wankan kafin tabar ‘dakin ‘dazu.

Ganin hakan sai Ummah ta fahimci cewa bata samu tayi wankan ba kenan.

Hannunta Ummah takawo danta ganta wata iri ma duk ta canja, mummy dake gefe dasu ne ta sake jefo wata tambayar kamar yanda Ummah tayi.

‘Kawar Teemahn ce tace ” a’a yanzu dama zatayi”

Ran mummy 6aci yayi da jin furucin ‘kawar Teemahn abin ya bata haushi sai da akace tayi wankan dawuri amma tsabar iskanci ta’kiyi suka tsaya shirme bayan uban ha’din da aka yiwa ruwan mai shegen tsada dan kawai a ga tafita daban.
Mummy cewa tayi ” tsayuwar me kukeyi toh anan ‘din da har yasa ta’kiyin wankan dawuri”Mummy ranta a6ace tayi maganar dan ba ‘karamin ‘kuluwa tayi ba.

‘Kawar Teemahn ce ta bu’di baki zata fara bayani sai Teemah ta ‘dago hannunta da sauri ta sau’ke shi akan na Ummah, dukkan su akan idanunsu hakan ya faru dan Teemahn na tsakiyan su ne, dan haka sai yarinyar ta dakata da maganar da tayi niyyan yi ‘din dukkansu suka zuba ido dan ganin ko menene manufar hakan da Teemahn tayi.

Ummah ‘dago hannunta tayi tana jujjuya abin ahannunta, sai take tambayar Teemahn wai ” menene wannan ‘din kuma ?.

Mummy kuma tace ” a ina kika samu?
dan tuni kwakwalwarta ta canja daga haushi da masifar da ya turni’keta zuwa tambaya tun lokacin da Teemah ta dan’kawa Ummah abin ahannunta.

Teemah a hankali ta basu amsa da fa’din.
_” Yah Abbas “_ !!

” wani Abbas ‘din’?
Ummah da Mummy suka ha’da baki wahen fa’din haka.

_”Yaayah Abbas “_
Tasake maimata musu.

Tsaki Mummy tayi dan zuwa yanzun ba’karamin haushi ne ya’kara kamata ba, haushin rashin cikakken bayani daga bakin Teemah.

“Tun yaushe yabaki “?mummy tasake tambayarta.

_” yanzu”._

“YANZU kuma!! ?
Ummah da mummy suka ha’da baki wajen tambaya da mamaki, kai Teemah ta jinjina musu alamar tabbatar wa

Mummy bakin gado tatafi ta zauna ta dafe goshi tare da fa’din
” _na shiga uku_ .!!!

Ummah tana bu’de case ‘din take fa’din ” shi da akace bashi da lokacin zuwa ashe kuma zai taho shine harda ‘karyar aiki sun masa yawa”? tana murmushi tayi maganar.

Yayinda mummy take tunanin yaushe toh har ya
zo gidan batare data sani ba.
_” WOW!!”, “DIAMOND”_!!!

Mummy taji yo muryar Ummah na fa’din haka, sai kawai tayi tagumi, sosai take tausayin ‘yartata ita, bata ta6a jin ‘kin son Abbas ba ko ka’dan arayuwarta amma wannan karan jitayi dama ace be zo ba dan tasan hankalin Teemah zai zama wani irine bayan tasamu ta nutsu ta daina damuwa wata’kila yanzu kuwa sai yanda Allah yayi duk dama tasan Teemahn tana tafiya damuwar ne batare da tasan damuwar tata ba, amma idan ta fiya ha’duwa da Abbas ba mamaki ta iya gano meke damunta shi yasa take tsoron yawan ha’duwarsu dashi, bata son abubuwa suyi wa Teemahn yawa tun tana ‘yan ‘kananun shekarunta.
Da zata iya data mantar da Teemahn nata kowa da komai dan kawai taga ta zauna ta rungumi auran ta hannu biyu tayi facing reality, wata ‘kila in hakan yafaru damuwarta zata kasance ‘yar ka’dan inyaso sai ta ci gaba da binta da addu’ah Allah ya ha’de kansu da mijinta da kuma Anty yasa Antyn ta ‘kaunaci ‘yarta ‘kauna mafi girma, amma bata da wannan damar sai de ta ha’da dukka tata ro’ka mata ubangiji ya ‘kara sassauta mata kamar yanda ya hanata fahimtar takamman abinda zuciyarta ke ciki, bata san me yasa Abbas yake yiwa Teeman haka ba, bata sani ba ko shi’din yariga yagane Teemahn na son shine!!……..kai Allah ya kiyaye sam bata fatan hakan ma ya kasance”.

Kallon Teemahn tayi taga yadda takoma lokaci guda duk da dama yau ‘din bata tashi da walwala sosai ba amma gara yanayinta na ‘dazu fiye da na yanzun, Ummah ma da ta lura da ita sai tace
” hala yau ‘din ma sai da kukayi fa’dan kafin yatafi ko dan naganki duk wata iri haka ?….!

Dai dai shigowan su Hannah da suka dawo daga kasuwa yanzun, da sallamar su suka shigo Hannah nashigowa ta tsaya turus tace ” ya haka kuma dan Allah? wai har yanzu amarya bata shirya ba Ummah meyasa?…… kai !kai !!kai !!! Ummah nawaye wannan gaskiya ya ha’du ta kar6a tana ‘ko’karin gwadasu ahannunta ta saka bangles tacire tana ‘ko’karin gwada zoben ne tace “dan Allah Ummah nawaye ne?
Cikin zumu’di take maganar as if ance mata nata ne.

” na amarya ne Yayanta ya kawo mata”?
Ummah na murmushi ta bawa Hannah amsar tambayar ta.

Sai Hannah tace
“wani Yayan kuma Ummah…….. kar dai Yah Abbas?”

“Shi dai”
inji Ummah atakaice.

” kut….lalle ma Yayan nan, toh ni ina nawa ?”

” kanta Ummah ta dungure tare da fa’din ‘kaniyarki. Hannah ance miki na amarya ne toh ke ‘din amaryace “?

” Ummah toh ainima zanyi kwalliyar naga”

“Ki jirashi toh inkin ganshi kwa gama dramar dashi ni kan ki barni na sha iska…..
” Yaushe ma yazone Ummah ba ance bazai samu damar m zuwa ba”?

” nima jinayi ance yazo amma banganshi ba”,…. kinga ‘kyaleni in shirya ‘yata lokaci nata tafiya har yanzu bata yi dressing ba” Ummah tayi maganar tare da nufar hanyar bayin dake vikin ‘dakin Teemah………tace ” Biba yanzu kam sai kin ‘kara ha’da mana wani ruwan ko dan inaga wannan yagana yin sanyi.” Da ” toh” Biban ta amsa tare da ajiye mayafinta itama ta nufi bayin domin ha’da ruwan wankan.

Hannah kuwa gurin Mummy ta nufah da set ‘din ‘dan kunnan tace.
” Mummy kinga Yah Abbas abinda yayi ko…….
” tunkan ta ‘karasa Mummy tace rabu dashi zai zo har gida yasame ni, sai naji dalilin dayasa ya ware ki be siyo miki naki ba ke ma”.

Daga mummy ta juya gurin Teemah tana kallon ta tace ” maza ki hanzarta ki yi shirin wankan toh gashi za’a ha’da wani ruwan.

“Gaskiya kam kiyi dawuri danni har na matsu inga anyi angama shirya amarya naga irin kyan da zakiyi da wannan abubuwan”.
Hannah tayi magaban tasigar zolaya.


*****
Babban limamin masallacin Yobe mosque and islamic centre da ke cikin garin damaturu aka gayyato domin ‘daurin auren Teemah, guri yacika ma’kil da jama’ah na nesa dana kusa, su daddy suna daga gaba gaba kusa da Limamin, duk hankalinsu yatafi ga sauraron Hu’dubar da akeyi na ‘daurin auren yayin da Mahmud ya sunkuyar da kansa ‘kasa sam yakasa jin farin ciki da wannan auren yakasa amincewa zuciyarsa kasantuwar Teemah a’kar’kashin ikon sa,yana ji kamar bazai iya ri’keta ba, jiyake kamar nauyin da zau kannashi yafi ‘jarfin sa sosai, kamar ya bu’di baki yace adakata da ‘daurin auren a ‘daura da waninsa, wanda zai iya ri’ke masa amanar Fatima da hannu biyu amma bazai iya ba,bazai iya furta hakan ba gani yake idan yayi hakan tamkar yayi wa mahaifinsa butulci ne da kuma tozarci musamman idan yayi duba da yanda dubban al’ummah suka bar ayyukan dake gabansu suka taho dan kawai su shaida ‘daurin auren sai yaji kawai ya saduda ya barwa Allah kawai, fatan shi de Allah ya zama gatansa yaba shi ikon kulawa da amanar dazata hau kansa, Allah yabashi ikon yin ri’ko da ita da gaskiya.

Daddyn Abuja ne da kansa ya kar6i wakilcin Fateema saboda rashin zuwan Abbas ‘din.

Daf da za’a ‘daura auren Mahmud yaji mutun ya zauna daga gefensa na hagu da farko ya share dan sanin yawan mutanen dake zaune agurin wata ‘kila saboda yawansu ne yasa dole sai sun ha’da jiki, amma sai yaji zuciyar sa takasa ha’kura da sharewan dayake so yayi ‘din ‘dagowa yayi ya kalli gefen nasa sai kuwa yaga Abbas zaune akusa dashi yana kallonsa

Take yaji wani sanyi azuciyarsa kasancewar Abbas ‘din awurin sai yaji wani sabon ‘karfin gwiwa ya shige shi, murmushi yayiwa Abbas ‘din tare da bashi hannu shima Abbas sai ya mayar masa da martani daga nan sai suka maida hankalinsu wurin da ake hu’dubar.


11:50am awannan ranar dubban jama’a suka shaida ‘daurin auren FATEEMAH ZAHRA KABIR da Angonta………………!!!!!🤞🏻

…………..,Abbas lumshe idanu yayi jiyayi da ‘ace shi ka’dai ne awurin da babu abinda zai hana hawayen shi zuba a dai-dai wannan lokacin amma yanzu kam daya kasance acikin mutane, mutanen da bazai ta6a iya sanin yawan su ba sai kawai yace _” Allah_ _kaine gatana, Allah_ _ka ji6anci_ _lamura na”_.

‘Daurin auren ba ‘karamin al’ummar annabi ya tara ba kama daga kan manyan ‘yan kasuwa da manyan ‘kusoshin gwamnati da sauran jama’ar musulmai baki ‘daya.

Mahmud da kansa sai da yaji fa’duwar gaba, zuciyarsa tsinkewa tayi da ‘karfin gaske _innalillahi wa innah_ _ilaihirraji’un_ dukkansu suke faman ambata azu’katan su.

Abbas ne ya daure ya ‘ka’kalo murmushi na dole ya azawa fuskarsa sannan ya ciri hannunsa ya mi’ka wa Mahmud suka yi musabiha ” _Inai muku fatan Alkhairi ‘dan uwa, Allah ubangiji ya baka ikon yin ri’ko da gaskiya da amana ya sanya fahimtar juna a tsakaninku”_

Shima Mahmud murmushin ya ‘ka’kalo yayi wanda ta tsaya masa a iya saman la66ansa ko ka’dan ba wannan bane azuciyarsa amma dan kawai ya nuna wa Abbas ‘din yabawa da godiyarsa sai ya ‘kir’kiri murshima shima sai yace ” _Ameen-Ameen Yayan mu godiya marar iyaka”._

Kasa sake hannun Abbas ‘din yayi suka tsaya ahakan, Abbas gefe ya maida idanunsa yana jinjina al’amarin ubangiji acikin ransa, in just a month gashi an raba shi da farin cikinsa, wannan aikin kam sai de a’kira da _’kaddara_ saboda shi koda wasa be ta6a tunanin faruwar hakan ba yariga ya barwa zuciyarsa cewa Teemah tashi ce shi yasa be ta6a damuwa ya kauda irin hakan ba, sai gashi rana tsaka ta inda bai ta6a zata ba, aka datse masa mafarkinsa batare da kai ga idda shi ba, sai gashi Teemah ta barshi, bari kuma na har abada.

Tunda suka gama maganganun su kowa sai murmushinsa ya kau.

Abbas na so ya cire hannunsa daga cikin na Mahmud amma sai Mahmud ya sakin masa hannun, dole tasa ya dawo da kallonsa ga Mahmud ‘din gaba ‘daya.

Idanun Mahmud na cikin na Abbas ‘din yace _” Abbas_ _nagode, nagode_ _sosai da irin ‘kokarin ‘da kai ta faman yi akaina dan ganin na cika BURIN mahaifina_ ,  _nasani cewa mai sonka shine wanda  akullum yake ‘ko’karin ganin baka_ _kauce hanya_ _ba, wannan itake tabbatar da son gaskiya da aminci!, Abbas yau gashi BURIN_ _ABBAH NA yacika, amma ni na kasa jin farin ciki azuciyata, inajin tamkar bazan iya ba, inajin tamkar_ _wani gagarumin nawi ne ya hau kaina, Abbas taya kake ganin zan_ _iya ri’ke wannan babbar amanar bayan ban shirya amsar ta ba?”_ 

Abbas ‘din sai yace mishi
_” Daure wa zakayi Mahmud, nasani cewa nauyi ne, nauyi ne ya hau kanka Mahmud sai de ba irin wanda kai kake zato ba, kai dai kawai ka mi’kawa Allah komai nasan zai maka jagora”_

Ahankali ya janye hannunsa daga cikin na Mahmud da ya tsaya shiru kamar me tunani dafa kafa’darsa Abbas yayi sai ya ‘dago ya kalli Abbas ‘din Abbas sai ya daga girarsa sama batare da yayi magana ba, ya kuma ‘dan juya jajayen idanunsa yayi wa Mahmud nuni ga mutanen dake gurin.

Story continues below


Atare suka mi’ke tsaye ganin yanda guri ya har’de da jama’ah ana faman gaisuwa yayin da dayawa daga cikin mutanen ma tuni sun kama gabansu zuwa gidajensu da masana’antun su saboda an riga an kammala komai, aure yariga ya ‘dauru.

Kamar jira ake su mi’ke kuwa sai aka fara mi’ko wa ango gaisuwa da fatan zaman lafiya mai ‘dorewa.

Yanda Abbas yasaki ransa yake amsa gaisuwa agurin har inbaka sani ba zakayi zaton ko shine ma angon domin azahiri annurin da ke kan fuskarsa ta nunka ta Mahmud ‘din banbancin kawai shine kasantuwar Mahmud ‘din a matsayin ango ya riga ya bayyana domin shike sanye da fararan kaya harma da babbar riga, Abbas kuwa be sa babbar riga ba shi kam.

Dukkansu suka ha’du suke amsa gaisuwar da duk aka mi’ko musu sai de kowa abinda ke ransa daban, kowa damuwar shi kala dabance, da haka har suka isa wurin da su daddy ke tsaye da sauran abokan Mahmud ‘din dake tare dashi suna binsu abaya, suma su daddy sai faman gaisuwa suke yi da jama’ah suna kuma mi’ka  ‘dumbin godiyarsu marar iyaka.

Daddyn Abuja ne yafara ganin tahowarsu take sai ya fa’da’da  fara’arsa fiye da ta baya.

Hararan Abbas yayi yana murmushi irin ka shammace mu ‘din nan sa’annan ya mi’kawa Mahmud hannu da sauri, Mahmud sai da ya ‘dan rissina tare da ‘ka’kalo murmushi ya ya6awa fuskarsa kafin ya mi’kawa Daddyn hannun nasa suka gaisa Daddy nata yi masa addu’ah da sanya alkhairi cikin zolaya ya’kara da fa’din 
_” saura abokin ka ko Mahmud tunda kai ‘din ansamu kayi da ‘kyar saura kuma shi dan na_ _lura ra’ayoyin kusan_ _iri ‘dayace “._ 

Murmushi kawai Mahmud yayi tare da sosa ‘keyarsa yana wani sukuyar da kai.

Abbas kuwa gurin Abbah ya nufa ya fara gaidashi sannan yadawo kan Daddy babbah ( daddyn Teemah).
Daddy bai amsa gaisuwar da Abbas ya mi’ka masa ba sai ya mi’ka masa hannu kamar zasu gaisa sai kawai ya zarce da hannun ya kamo kunnan Abbas dashi yaja  ” _Awshhhh daddy_ _zafi

Sake ja daddy yayi sai kuma ya sake atake yana murmushi. Abbas yasan dalilin yimasa hakan da daddy yayi ba zai wuche baki biyun dayayi bane akan zuwan shi shiyasa daddy yake purnishing ‘dinsa da haka
dan haka sai yace da daddyn
” _ango nake fah yau ‘din daddy”_ 

Dariya suka sanya dukkansu dake wurin inka ‘dauke Mahmud da ‘yar murmusawa kawai yayi sai shi Abbas ‘din da haryanzu hannunsa ke kan kunnansa yana shafawa su ka’dai ne basuyi dariyarba.

Sai da suka gama dariyar sannan daddy ya juyo da kallonsa gurin Mahmud suka sake gaisuwa akaro na biyu shima daddy yasa masa albarka a auren nasa.

Daddy gurin Abbas ya juyo ya kamo hannunsa suka fara tafiya ahankali kamar masu yin wata shawara sai daddy yace masa ” _ya akayi kuma na ganka bayan kace babu dama?_ 

” _Da ‘kyar na taho daddy sai da nayi roko tare da cancelling wata tafiya da zamuyi tun aji yan kafin nasamu dama”_ 

_” amma ba wata matsala_ _ko ?_ 
Daddyn ya sake tambayarshi

Da _” insha Allah babu komai Daddy”_ Abbas ya amsa mishi tare da fa’din anjima ka’dan ma zan koma. 


_”Toh Allah ya tsare ya bada_ _sa’a_ ” daddyn yafa’da dai dai isowarsu su daddyn inda suke.

Sallama Abbas yafara yi musu dan afa’darsa cewa yayi zai koma dama wai ‘daurin auren ne ya kawo shi.

Abbah ne yace da Abbas ‘din wai ko dan bikin ba da’di ne shiyasa zai tafin ,Abbah yace abokin ka ne yace ba zaiyi kowani event ba da ‘kyar ya yadda mahaifiyarsa ta shirya yin dinner inajin shi ka’dai za’ayi “

Sai da Abbas ya juya ya kalli Mahmud sai ya dawo da kallonsa gurin Abbahn kafin yace _” ai mu Abbah_ _albarkar auren kawai muke bu’kata”_

Abbahn ma cewa yayi
_”Hakane, hakan ma yayi Allah ubangiji ya sanya alkhairi ya albarkace ku gaba ‘daya”_

_”Ameen Ameen_ _Abbah”_
Abbas ya amsa masa dashi.


*****
Yanda aka tsara wa Teemah kwalliya ba ‘karamin fito da ita yayi ba, tayi kyau cikin wani code-less ‘din ta blue-green mai kyan gaske da ratsin golden ajiki,’dinkin dai dai jikinta akayi shi, Head, net, bridal shoe and purse ‘dinta ma duk golden colour ne sai wani set ‘din ‘dan kunnan ta na gold da daddy ya sai mata kwanaki, ba’karamin kyau tayi ba, light make-up akayi mata daya ‘kara fito da asalin kyaunta afili.

‘Kawayenta nata rawar kai amma ita banda ita, ko ajikinta kamar ma ba bikinta akeyi ba, photuna suka yita ‘dauka da ‘kawayen nata har sai taji tagaji, da ta ga kamar sun dame ta sai ta ce da Hannah su tafi ‘dakin Mummy hayaniyar ta isheta haka.

‘Dakin mummyn suka tafi suka yi zaman su acan suka bar ‘kawayen nasu. Teemah cewa tayi ” _wallahi ba dan ina tsoron masifar mummy ba da cire kayan nan zanyi Allah insha iska, duk sun bi sun_ _dameni”._ 

_” ke kika sani ni dai baruwana idan ta kamaki dan kina cire kayan tafiya zanyi inbarki kinga_ _bata ganni tare da ke bama balle abin ya shafe ni”_ 

Tsaki Teemahn tayi kawai ta cire takalman dake ‘kafarta tana wani yatsina fuska duk da haka sai data ‘daga net ‘din da aka rufe mata kai dashi zuwa sama.

Hannah tace yauwa bari na ‘dauke ki a pic.

Su mummy da Ummah nacan hararabar gidan ta baya inda ake shirya abinci suna ta ‘ko’karin ganin komai ya kammala saboda ba’kin daddy da suka zo kuma an riga an gama ‘daurin aure shiyasa suke ta hanzari dan suga sun ha’da musu abinda zasu bu’kata.


Lokacin da Abbas ya shigo domin ya gaisa da su Mummyn ya kuma yi musu sallama dan daga nan wucewa yake so yayi be gansu ba shikuma ba son ratsa cikin taron matan nan yake ba takaici yake ji idan ya gansu ayanzu bashi da burin daya wuce yaga ya bar garin Damaturu, yana ganin zai fi jin sassauci.

Koda yashigo bai gansu mummyn ba sai ya ciri wayarsa ya ‘kira layinta sai kuma bata ‘dauka ba, haka ma na Ummahn sa itama bata ‘daga ba.

Hakan yasa da ya shigo kawai sai ya wuche ‘dakin Mummyn direct dan zatan shi acan suke tunda bai gansu a babban palourn ba.

Da sallamar sa ya shiga ‘dakin Hannah ce kawai ta amsa sallamar yayin da Teemah taji ta wata mummnar fa’duwar gaba ta zubawa ‘kofar idanu har ya shigo, shima yana shigowa idanunsa akanta ya fara sau’ka.

Kallon kallo suka tsaya yi wa junansu, Abbas kyan da Teemahn tayi ne ya tafi da imanisa sai yaji wani ‘daci azuciyarsa na takaicin dakilin kwalliyar tata.

Tunowa da yayi cewa yanzu fah Fateema matar mutun ce bashi da damar yi mata irin wannan kallon, take sai ya kauda kansa gefe tare da yin istigfari acikin ransa.

Dubansa ya mayar gun Hannah data tsaya tana ‘kare musu kallo da mamaki inda ta kasa tsaida idanunta kan mutun ‘aya sai juya idanunta take idan ta kalli wannan sai ta dawo ta kalli wannan.

_”Hannah ina Ummah na ‘kira layinta bata ‘daga ba?”_
Cikin sanyi yai maganar.

‘Ko’karin fita daga ‘dakin Hannah take yi tare da fa’din ” _bari_ _indubo ta”_

Dakatar da jta yayi da fa’din _” a’a ‘_ _kyaleta ki sanar da ita na wuche kawai “_

_”Bata yi nisa bafa Yayah kuma ma dama tana so ta ganka injita”._

_”Toh sauri ki dabata karki 6ata lokaci “_ Inji Abbas ‘din tare nufar wajen window ya tsaya yana kallon waje.

Teemah ma bayansa ta kalla ahankali ta tashi tare da saka takalmanta ta bar masa ‘dakin dan bata san me zata ce dashi ba, wani lokaci sai ta ji tarasa ‘kwarin gwiwar da har zata iya yimasa magana , ballantana yanzu da taganshi duk yayi sanyi sai taji ya cika mata idanu bazata iya ce da shi komai ba shiyasa ta yanke shawarar barin ‘dakin.

Sallama yayi da su bayan Teemah ta’kira Mummyn saboda Ummah abubuwan dake gabanta dayawa, dama Hannah tace ya tsayan ne saboda ta tunawa Ummah fa’da mishi batun sar’kar ta data ke so ya siyan mata itama sai kuma Ummah bata samu daman zuwa sai dai Mummy duk da haka sai da ta tuna wa Mummyn.

Murmushi mummy tayi sannan tace.
_” ki bari bayanzu ba bayan kwana biyu idan ya koma da kaina zan sanar dashi kin ga lokacin_ _taro duk ya ‘kare kowa hankalinsa ya dawo jikinsa zai fi_ _fahimta amma yanzu kinga al’amuran jama’ah_ _ko”_ .

_”Hakane mummy amma pls karki manta fah”_ 

” _Bazan manta ba insha Allahu”_

Duka akan tafiya sukayi wannan maganar daga nan suka yi shiru suka ‘karasa ‘dakin mummyn inda Abbas yake, Ummah ma ana tasame su bayan tagama abinda ke gabanta.

Abbas yau ko hanyar maiduguri be kalla bakawai ya shiga Tasha ya hau motar Kaduna dan takaici bai ko tsaya ya wuni agidan ba.

Ana idar da sallar azahar alace za’a tafi da amarya saboda yanayin nisa n da gurin ke da shi.

Tun lokacin da Teemah taji labarin tafiyar tafara kuka, hatta sabo shirin da ake sake yimata ma acikin kuka aka yishi har aka gama sai de ba’ayi mata make-up ba saboda hawayenta ya’ki tsayawa.

Daddy da kansaya ratso cikin matan yazo har ‘dakin Mummy yakama hannunta izuwa sashen sa. Shi kanshi dadyn dauriya kawai yakeyi amma zuciyarsa ba da’di sam sai dai bazai iya barin hakan ya baiyana afili ba dan baya son Fateemah taga kasawarshi koka’dan, dan haka sai ya zaunar da ita agefensa akan kujera ganin su Daddyn Abuja na ‘dakin sai ta zamo ta dawo ‘kasa ta zauna tana maici gaba da kukanta.

Mahmud ne yasgigo shima da sallamarshi dan Abbah ne ya’kira shi awaya yace yazo nan’din yanzun nan shiyasa ya taho.

Dukkansu aka ha’da si aka yi musu fa’da sosai akan rayuwa Abbah ne yafara nasa akan kyautata mu’amala sai Daddyn Abuja yayi nasa akan tsoron Allah da bin dokokin sa azaman takewarsu, Daddy ne yayi daga ‘karshe inda yaja hankalinsu akan ha’kuri da kaiwa zuciya nesa, Sosai nasihohin nasu suka ratsa su Teemah sai kuka takeyi harda shashshe’ka.

Dasuka gama ne Abbah, Daddyn Abuja harma da Mahmud ‘din suka tafi suka bar ‘dakin domin zuwa fara arranging yadda tafiya da amaryan zai kasance aka bar Daddy da Fateemansa ka’dai.

Dawowa tayi da kanta akan cinyar Daddyn ta kwantar dashi tana mai cigaba da kukanta.

Daddy sai ya fara bubbuga mata kai ‘din ahankali alamar rarrashi tare da fa’din _” Haba_ _Daddy’s Angel stop crying mana”!_ 

Cikin kukan tace 
_”Dad…dy ni bana son in….tafi inbarku, bana son……auren Da…ddy “_ 

” _Kiyi ha’kuri Fateema!, aure dole ne zakiyishi, ko bakiyi yanzu ba dole watarana sai kinyishi ko dan cika sunnar ma’aiki sallallahu alaihi wa sallam (S.A.W), balle ma yanzu ke da kike tare da yayanki Mahmud, ga Antyn ki, ga Abbahn ki ma duk akusa dake, ai can ‘dinma kamar gidane, karki damu kinji”_

Cikin shagwa6a tace
_” a’ a ni Daddy nan nakeso”_ 

_”Toh shikenan kiyi shiru, zanje kwanan nan inkun tafi sai dai bazan gaya miki ranar ba, zanje amma idan naga kina kuka da rashin ji kullum toh bazan dawo dake gida ba, idan kuwa bakyayin ko ‘daya daga ciki kika kwantar da hankalinki kika zauna da mijinki lafiya kika yi masa biyayya toh zan ‘dauko ki in kawo ki gida kiga mummyn_ _ki kinji”._ 

Da kai ta amsa masa alamar taji.

Sai yace _” yauwa_ _my Angel share hawayen ki toh karki sake yin kuka”_ 

Share hawayen ta tayi harama da murmushi sai Daddy ya’kira mummy awaya yace zuso su tafi da ita.

Suma su mummy nasiha suka mata sosai sai dai Mummy kasa ri’ke nata hawayen tayi daga ‘karshe ma kasa magana tayi dan yanda kuka yaci ‘karfin ta.
Kusan duk wa’danda suke wurin sai da suka share hawaye dan ganin yanda Mummyn ke kuka.

Baranma Teemah data ji mahaifiyarta na kuka ai shikenan, da sauri tatafi jikin mummyn ta rungumeta tace ” _Mummy ni bana so intafi inbarki…….mummy tunda ba…kyaso nima ba zanje ba”_
Kuka take tana maganar yayainda tausayinta ke ‘kara cika zuciyar mummyn kamar tace Teemah bazata ko’ina ba, kamar tace babu inda yarta zata, karo na farko kenan da Teemahn zatayi doguwar tafiya batare da ita ba , she can’t bear the pain, bazata iya jurewa ba , tayaya bazata tausayawa yarinyar da tsawon rayuwarta bata yishi batare da iyayenta ba,dai dai da rana daya bata ta6a kwana a inda ba mahaifiyarta ba sai gashi kwatsam zata tafi inda zai dauke ta tsawon lokaci kafin sugana. Kai Mummy ta dagata sama tace _” Allahu ga amanar ka nan Allah ka kula min da ita ka kareta daga sharrin masu sharri ka kareta daga dukkan abin kii!”_

Dai-dai nan Daddy ya shigo da niyyar sanar da su cewa angama komai lokacin tafiya tayi, sallamarsa ma bai ‘karasheta ba ganin irin abinda ke faruwa a’dakin.

Cikin tsawa yace ” _menene kuma haka Khadija_? _Yazakisa yarinya agaba kina aikin kuka inabaso kike ki karya mata gwiwa ba ?”_

Bai jira ji, cewar kowa ba ya ‘karaso yaja hannun Teemahn yatada ita tsaye, _” tashi_ _mamana kyalesu ba mun gama magana ni da ke ba, meyasa zaki zo nana kuma_ _kina_ _kuka ?_ 

_”Daddy kuka_ _mummy takeyi_”

Baiyi magana ba kawai yaja hannunta suka bara ‘dakin daf da ‘kofa yatsaya yace _” mai_ _niyyan tafiya ta fito motoci na ready”_ 
Yayi maganar batare da ya juyo ya kalle su ba yana gama fa’da kuwa yasa kai yafice hannunsa ri’ke dana Teemahn.

Da kansa yahe yasanta amota,Ummah ne tazauna agefenta ‘daya yayinda wata ‘kanwarsu daddy da suke cousins tazauna ‘daya gefen, Hannu da waus ‘kawayen Teemahn su biyu suka zauna awata motar daban .

Mummy ko gurin tafitar ba ta fito ba ita kam tana ciki kawai tana jimamin rabuwa da ‘yartata tana so ta tashi ta ko leke su ta window ma takasa ji tayi ga6o6in ta duk sun mata nauyi aranta sai take jin tamkar ta rabu da Teemahn nata ne rabuwa ta har abada, tana jin dirin tashin motocin kawai sai ta rintse idanun ta.

Basu tsaya ko’ina ba sai a Airport na Maiduguri inda daga nan suka hau jirgi sai garin ikko (LAGOS).

*****
Zaune acikin mota shiru ko wanda ke gefensa be kalla ba tunda ya shiga motar tunani ya sako shi agaba, tunanin yadda kunnan sa suka jiyo masa ‘daurin aure tsakanin 
” MAHMUD YUSUF MUH’D da Fateemah, yanaji yana gani aka ‘daure sunan Fateema da waninsa, bashi ba.

Har suka isa kaduna babu wanda yako samu kallon arzi’ki acikin motar daga gurin Abbas, yana sau’ka ya tari adaidai ta yayi drop zuwa _Barrack 44_ dake cikin kadunan
inda Saleem abokinsa yake.




*Wash……..* 
*Naso yafi haka amma wallahi ansamu akasi, Please ayi ha’kuri da wannan* *insha Allahu zuwa gobe zakujini*


_Ina Team Mahmud ina jira daga gareku , idan naga sharhi ruwa-ruwan ta insha Allahu I_ _ll not fail_ _you agoben_ _zakujini idan muntashi cikin rayayyu._ 


Agidan Anty akayi musu masau’ki inda Anty ta matu’kar bawa kowa mamaki, sau’ka tayi musu na mutunci da karramawa tamkar ba ita ba.

Anty da wasu ‘kawayenta ‘yan bani na iya da suka yi ruwa suka kuma yi tsaki abikin sune zazzaune a palour suka tari amaryar Mahmud ‘din.

Bayan gaishe-gaishe da ban gajiya sai su Ummah suka mi’ka amanar amarya Teemah ahannun Anty inda Anty ta matu’kar nuna vajinta wurin kar6ar amanar harma ta nuna musu ai bakomai duk ‘daya suke tace ai itama amaryar ‘ya ta ke agurina, mu’karraban Antyn kuwa cewa suka yi wai su Ummah su kwantar da hankalinsu domin amanar su ta kar6u sai fatan Allah ya bada zaman lafiya mai ‘dorewa, mutane nata amsawa da Ameen,Ameen Anty kuwa acikin ranta ta ce _” ba Ameen ba, can da su gada gayyar tsiya Allah ya tarwatsa”_!!!

Har su Ummah sun mi’ke zasu tafi masau’kin su sai wasu daga cikin mutanen Antyn suka ha’da bakin cewa su basu ga fuskar amarya ba gaskiya abu’de mata fuska su ganta.

Murmushi Ummah tayi tare da umartan Hannah data bu’de mayafin Teemahn.

Ahankali Hannah ta matsa jikin Teemahn dan ita iyayin wa’dannan matan yafara isanta.
‘Daga lullu6in tayi ahankali kamar mai tsoron ta6awa sai data dangana shi da saman kan Fateeman kafin ta barshi.

Dukkan su sun yaba da kyaun amaryar hatta Anty sai da ta yaba da amaryar Mahmud ‘din dan ta jima bata ga yarinyar ba tun tana ‘yar ‘karama, tace ashe Khadija harta haifi ‘yah kamar wannan?!
Sosai suka yabi kyau da tsariwar amaryarta su dan duk munafurcin ka baka isa ka kushe kyaun Teemah ba ballantana kuma an ha’da da kwallliya da ‘kyalkyalin amarci.

Dai-dai nan Anty Chiddy ta shigo dayake taje gida bada jimawa da niyyar daman zata dawo sai kuma aka samu akasi kafin ta dawo har amarya ta iso, tana shigowa kuwa idanunta ya sau’ka akan fuskar amaryar.

Anty Chiddy kam baki ta sake tana kallon inda tsagwaron kyawun halitta yake, sosai tayaba da Teemah har aranta, tace kamar daga indiya tazo yanayin shiga da kwalliyarta shigen taau ce, banbancin ta au ka’dan ne sai dai su nuna mata hasken fata ita kuwa ‘daurin kai zata nuna musu domin ‘daurin da akayi mata ba’karamin zanuwa yayi ba, indiawa kuwa basu ‘daure kai irin namu na Naija .

Take taji masifar son yarinyar yashige ta karaf ‘daya, a hankali ta tako ta iso ta samu gurin zama ta zauna itama tare a zubawa yarinyar idanu.

Hannah rarraba musu idanu taringa yi jin yadda kowa ke fa’din albarkcin bakinsa akan Teemah, haka taringa binsu da idanu tana kallon su itama, garin ‘kare musu kallon ne idanunta ya kai ga Anty Chiddy data zubawa Fateemah idanu kamar zata cinyeta ‘danya, kallon kallo tayi atsakanin Fateema da Anty Chiddyn sai data ‘kara tabbatar wa idanunta inda Anty Chiddyn ke kallo sannan ta buga uban tsaki tare da ha’de rai kamar anzagi wani nata ne, jan mayafin tayi ta maida shi ta rufe fuskar Teemahn sannan tasake ‘dagowa karaf sai suka ha’da idanu harara Hannah ta banka mata tare da murgu’da bakinta aranta tace _” aniyar_ _ki ta biki inma maita ce dake dan mu jinin mu tamkar acid yake sai gani sai hange sai ta Allah bade ta mutun ba, mutun ‘dinma irinku, daga ganin tama arniya ce wannan, tawani baza attachments kamar mahaukaciya….mthewwww “_ ta ‘karashe da jan tsaki.

Story continues below


Anty Chiddy kam gurin Anty ta nufa ganin an rufe fuskar data ke kallo ‘din, sai data kai kanta kusa da kunnen Anty kafin ta furta _” your_ _daughter in-law is so beautiful”._ 
(‘Kalubale na farko)

Anty murmushi kawai tayi mata dan hankalinta naga matar da taga ta mi’ke tana ‘ko’karin tada amarya, Ummah ce tace mata zasu wuche masau’kin su saboda suna da uzirirrika ciki kuwa harda sallah da basuyi ba, lokacin anyi suna kan hanya. 

Kamar gaske gmsu Anty suka bisu da godiya da kuma fatan alkhairi sannnan Anty tasa aka kaisu 6angaren Mahmud tare da sawa aka wadatasu da dukkan wani abin bu’kata domin anan aka shirya tar6ar amarya ayau ‘din har se an’kare hidiman gobe kafin asada ta da gidan mijinta na ainahi.

Bayan fitar su Ummah ne Anty da mu’karrabanta suka zauna maida zance akan amaryar da danginta inda suka yabi na yaba tare da kushe abinda suka ga be musu ba, Anty kanta aranta cewa tayi ” ha’ki’ka Mahmud yayi dacen mace kyakyawa da kyakykyawan asali, sai de hakan bazai hanani cin uban yarinyar ba, har se da kanta ta nemi saki daga gurin mijin dan neman sassauci, dama tajima da yin wannan al’kawarin tace sam babu zancen zaman aminchi tsakaninta da dangin miji, afa’darta wai duk munafukai ne, auren ma na ‘daya daga cikin munafurcin nasu saboda sama taka taji wai za’a yi aure tsakanin Mahmud da ‘yar Kabiru (Daddy) batare da anyi shawara da ita ba ko kuma a tambayi ra’ayinta ba, dan anga yaronta mai hankali son kowa ‘kin wanda yarasa shine aka li’ka masa ita daga zuwa bautar ‘kasa agarin dan haka itama sai inda ‘karfinta ya ‘kare bazata ta6a amincewa dasu ba itama _shege ka_ _fasa._ 

Washe gari ma tun kafin wasunsu su gama tashi a bacci har breakfast ya iso su mai rai da lafiya, inda akaiyshi kala daban daban kusan kala uku sai wanda yayi maka zaka za6a kaci.

Ta wannan fannin sosai Anty tayi ‘ko’kari dan tun zuwan su basu nemi komai sun rasa ba agidan, sau da dama ma tun kafin su nemi abu ake bayyanar dashi agabansu, su Ummah sun matu’kar yabawa da karamcin Antyn hankalin su sam be tashi ba Ummah bata damu ba koka’dan tatafi tabar Teemah da tunanin zata samu farin ciki da yardar ubangiji, tunda ita bataga wani abu na daban daga mahaifiyar Mahmud ba har ma sai taga kamar tsoron da Mummy kullun take anbata wata kila hasashen ta ne kawai dan ita ko ka’dan bata ga haka daga Antyn ba, bataga alamar komai ba.

Ummah da sauran manyan matan ne suka wuche aka bar Teemah da ‘kawayen domin yin shirin dinner, inda already Anty tariga ta shirya komai hatta ‘yan mata sai data kawo wasu daga 6angarenta inda suka ha’du da sauran ‘kawayen Teemah sai suka bada ma’ana instead of su hu’dun da suke dukda amaryar.

Kaya da zasu saka duk Anty ta tanadar musu gaba ‘daya hakama amarya dan wani kaya ta ‘dinka mata mai kyau da tsada pitch colour da Teemah tasa kuwa ba’karamin fito da ita yayi ba, Hannah ce tace sai dai Teemah tasa wannan set ‘din earings da Abbas ya kawo mata ‘dazu acewarta zaifi fito da ita.

Ammah sun nema acikin kayan sa suka zo dashi basu samu ba ashe mummy ce ta6oye bata bari yabiyo kayansu ba tace daga zata bawa Daddyn ta ya kaimata.
Dole tasa wanda Anty ta ha’do dashi shi’dinma mai kyau ne yafi ‘karfin kushe.

Ummah na isa gida Abuja ta nemi layin Mummy tasanar da ita irin kar6ar mutuncin da Mahaifiyar angon tayi musu tace gaskiya sai de su godewa Allah domin ita sam bata ga wata matsala atattare dasu ba tace may be Allah ne yashiryeta tun ma kafin Teemahn tazo, mummy ba’karamin da’din hakan taji ba, sosai canjawar Antyn yabata mamaki matu’ka, dama burinta kenan, burinta taga ‘yarta tasamu farin ciki agidan auren ta, dama ita ba Mahmud take gudu ba halin mahaifiyarsa ne yake yawan sata damuwa, yanzu kam sai de tace ” _ALHAMDULILLAH_” tunda Antyn ta sau’ko.

Tun daga lokacin da Mummy tasamu labarin meke faruwa sai ta warawre walwalarta ta dawo dukkan damuwarta ta kau , dama abinda ya dame ta kenan kuma yanzu taji good news akai so no more worried…….

Story continues below


Zakayi mamakin yanda event centern ya ‘dinke da jama’ah kuma duk Anty ce ta gayyato su musamman dan suzo su kwashi shokky. 

Ai kuwa ba ‘karamin cashewa akayi ba awurin dinner ‘din, Mahmud kuwa ‘kin zuwa yayi ballantana abokansa, sai gurin yakasance mata zallah ne agurin babu maza sai ‘dai’daiku hakan sai ya maida dinner ‘din ya riki’de ya juya izuwa mother’s night. 

Teemah duk inda ta juya walwali takeyi kuma idanun Anty Chiddy ‘kur akanta har mantawa takeyi da abinda akeyi agurin idan ta tsaya kallon Teemah.

Idan kuwa akace Teemah na tsakiyar fili itama bata iya zama, fitowa takeyi ta bu’de bakin jaka tayi zazzaga mata li’ki wanda hakan sai yazama na tamkar gasa kowa yafara ‘ko’karin ganin ya nuna tasa bajintar, hatta Munira ma ba’a barta abaya ba dan itama da ita akayi komai agurin taron haka kuma tayi ta zuwa tana watsa wa amarya li’ki wanda garin yin li’kin ne ta samu ta ha’da ku’din da wani hatsabibin maganin dake hannunta ta watsa asaman kan amarya Fateemah, duk kuwa maitar mutn bazai ta6a fahimtar abinda yafaru agurin ba, tana gamawa kuwa ta koma tayi zamanta tana dariyar mugunta tun daga nan bata ‘kara tashi ba har taron ya watse domin tariga tagama abinda ya kawota.
_(‘Kalubale na biyu)_ 

Fateemah na tsakiyan jama’ah tafara jin kanta na matsanan cin sarawa sai ta dafe kan nata jiri na neman kadata, Hannah ce ta lura da hakan sai tayi saurin ri’keta ta maida ita mazauninta tana tayi mata aikin sannu sannan tatafi wurin Anty ta sanar da ita abinda ke faruwa.

Anty waya ta lalubo ta’kira Mahmud akan cewa yazo yatafi da Fateema gida saboda bata jin da’di, da ” okay” Mahmud ya amsa tare da yanke ‘kiran tsawon mintina ashirin ya ‘dauke su isowa wurin daya ke daman ba da nisa suke ba already sun riga sun shirya zuwa ‘dauko sun.

Ba’a maida su gidan Anty ba sai aka kaisu asalin gidan da Fatima zata zauna, Hannah ce ta yi ‘ko’karin ganin ta aikata komai da Ummah ta tsara mata kafin tatafi dan haka dazasu shiga gidan sai tace da Teemahn tayi bismillah kuma ‘kafar dama zata fara sawa agidan, hakan tayi niyyah dama domin already tu, a Damaturu Mummy ta karantar da ita hakan takuma ‘kara da nata addu’o’in na neman kariya daga dukkan ma sharranta daga ‘karshe ta rufe addu’ar tata adaidai ‘kafar shiga palour da fa’din (A uzubillahi minash shai’danir rajeem, Bismillahi tawakkaltu alal lah wala haula wala kuwwata illah billah) tana gama fa’din hakan tasa kanta tashiga parloun gida.

Cikin sa’a ma data ‘dan watsa ruwa ajikinta sai taji dama-dama aranar kam basuyi da’de ba sukayi bacvi dan duk sun gama gajiya.

Da safe da Teemah tatashi ji tayi kanta yayi mata nauyi sosai sai data nemi panadol tasha bayan sunyi breakfast kafin tajita ‘dan dai dai.

12:00pm nayi abincin rana ya iso musu daga gidan Anty lokacin ma duk basu fara jin yunwa ba kasancewar basu ci break fast ‘din da wuri ba gashi Anty tasake lodo musu wani abincin.

Sai da suka yi sallar la’asar kafin suka fito dan tafiya gida, Mahmud da kansa yagama musu komai na tafiya inda sukkansu zasu sau’kane a Abuja zasu kwana agidan Ummah inyaso washe gari sauran ‘kawayen Teemah sai su bi mota su wuche gida.

Dazasu tafi Teemah kuwa sosai takeyi ji tayi kamar ta bisu amma badama, haka ta ‘karaci kukan ta tayi shiru danko mai lallashi bata samu ba,Mahmud daga wajen gate ya tsaya ya turo aka ce su fito dan haka ko ganin sa bata samu daman yi ba balle har tasamu ban baki daga gareshi.

Bai dawo gidan ba sai ‘karde tara na dare 9:00pm wanda alokacin idanun Teemah tsuru tsuru duk tsoro yagama cika mata zuciyata na rashin jin motsin kowa acikin gidan sai ta samu guri ‘daya ta takure akan kujera tunda suka tafi bata tashi awurin ba ko sallah bata je tayi ba dan tsoro, motsin kirki intayi jitaje tamkar za’ a cafkota ne, anan maghrib da isha duk suka sameta batayi su ba, kuka kuwa tayi shi har sai da idanun ta suka daina fitar da ruwa ta komayi azuciyarta.

Tana zaune agurin taji an mata knocking tare da sallama duk alokaci ‘daya, sanin muryarsa ne yasa tatashi da sauri taje tabu’de masa ‘kofar dan dama a’kage take taji motsi sai kuwa taji yazo ai ba 6ata lokaci.

Mahmud shi ka’dai yazo gidan nasa batare da neman rakiyar kowa daga cikin abokansa ba.

Mahmud shika’dai yazo gidan nasa batare da neman rakiyar kowa daga cikin abokansa ba, fuskarsa ba yabo ba fallasa lokacin daya ganta ,be yi mata magana ba kawai yasa kansa zuwa ciki itama sai ta bishi abaya ahankali bayan ta tura ‘kofar. 

Babbar rigarsa yacire ya ajiye sannan yakoma ya kukkule ‘kofofin gidam gaba ‘daya ya daqo yasameta zaune akan kujera. 

Umartan ta yayi da tayi alwala taje tayi ta dawo sai ya mata nuni da dadduma ma’ana ita yake jira. 

Ahankali tace masa ” _banyi maghrib ba_” dan ita zaton ta sallar isha’i zasuyi. 

Kallon ta yayi da mamaki ya ce ” _meyasa bakiyi ba tun ‘dazun”_? 

” _Ni tsoro nakeji Yayah tun ‘dazu fah nika’dai ce agidan kuma su Hannah tafiyar su sukayi suka barni”._! Cikin shagwa6a tayi maganar tamkar zatayi kuka. 

Shi kuwa sai ya samu ya zauna yace mata ta hanzarta tayi toh dan lokaci na tafiya yace kuma kiyi harda isha’i ma. 

Sai data jero sallolinta duka biyu sannan ya tshi ya jasu suka yi wata raka’ah biyu ,sosai yajero musu addu’o’i kusan na mintina ashirin sannan suka shafah zuwa lokacin kuwa Teemah tayi hamma yafi sau a ‘kirga idanunta duk sunyi luhu-luhu. 

Cemata yayi taje kitchen ta ‘dauko plate da cups takawo. 

Batayi musu ba kuwa ta tashi taje har wani jiri jiri takeji tsabar baccin daya ci idanunta, babu ma inda tasani acikin gidan ita dan tunda tashigo gidan bata je ko ina ba su Hannah keta shige da ficen su tana kallonsu batare data nemi sanin ko’ina agidan ba. 

Ko yanzun ma da ta tashin bata da’de ba ta dawo ta e masa ita bataga kitchen ‘din ba. Sai kawai ya ‘mi’ke yakama hanyar zuwa itama sai ta bishi abaya, dakamsa yashiga ya ‘dauko plate ‘din suka dawo parlourn. 

Yayi-yayi da ita taci abinci ta’ki ci sai kawai tayi kwanciyarta akan kujerar dake  gefensa tare da yin pillow da ‘dan ‘karamin throw pillows ‘din dake kan kujerun, take sai bacci ya ‘dauke ta awurin bada jimawa ba, shima be wani ci abincin ba dan shi’din ma ba ra’ayin cin abincin yake ba dama dan ita ne kuma ta’ki ci dan haka sai ya ture daga gabansa. 

‘Debe tarkacen yayi gaba ‘daya ya mai da su kitchen sannan ya dawo ya tsaya akanta kamar ya tasheta dan ta koma ‘daki amma sai ya barta ganin yanda ta saki ranta take baccin cikin kwanciyar hankali ga dukkan alamu akwana kin bata samu wani baccin kirki ba. Sai de duk da haka yana ganin kamar kayan dake jikintan zasu mata nauyi, anyways bari na barta in sun dameta ai dakanta ma zata tashi ta nemi rabuwa dasu. 

Komawa bedroom yayi yawo shirin baccinsa sannan ya ‘dauko pillow yazo ya jefa akan carpet for d first time arayuwarsa ya kwanta bacci ba akan gado ba. 

Duk da sanyin da tiles ‘din ke badawa amma haka ya daure ya kwanta awurin dan kawai ya kasance kusa da ita, domin cika amanar aya kar6a baya so hakkinta yafara hawa kanshi tun daga ranar farkon auren su. 

Story continues below


Da zai iya kwantawa akan kujerar shima amma kuma 2seater yayi masa ka’dan bazaiji da’din kwanciya akai ba, Teemah kuwa baccin ta ya riga yayi nisa akan 3seatern shiyasa kawai ya yanke shawarar kwanciya a’kasan. 

‘Karfe biyu da mintina sha takwas 2:18am tafarka garin yin juyi sai idanunta ya sau’ka akansa taga yanda yatakuru ga dukkan alamu sanyi sosai yakeji, sai data ta tashi ta zauna ta fahimci manufar kwanciyarsu aparlourn tunowa datayi cewa tariga shi yin bacci dan ta barshi ne yana ‘ko’karin cin abinci. 

Sake kallonsa tayi sai taji tausayinsa ya kamata “Allah sarki Yah Mahmud” tafa’di aranta. 

‘Dakin da duhu amma ta daure ranta ta tashi dayake ma akwai hasken farin wata kuma ya ‘dan ratso ka’dan ta jikin windown glass ‘din dake parlourn dan haka batayi wahalar gane mashigar bedroom ba, sai data shiga kafin ta kunna bulb ‘din bedroom ‘din sannan haske ya gauraye ko’ina a’dakin, abin rufa ta ‘dauko ta dawo ta lullu6a masa ahankali sannan ta koma ta sake yin kwanciyarta ko kayan jikinta ma bata tuna cirewa ba haka ta dawo ta kwanta. 

Kusan 22mins ta ‘dauka idanunta biyu kafin wani baccin yakuma ‘daukanta.   

Washe gari Mahmud ya rigata tashi, koda ya tashin kuwa mamaki yayi daya ga jikinsa lullu6e da abin rufa domin a iya saninsa shi be ‘dauko wani abin rufa ba jiyan amma sai gashi ya tashi yagansa dashi, kallon inda take yayi sai yaga tana ta baccin ta kamar dae jiyan be ga wani canji atattare da ita ba. 

Ture abin ruafar yayi ya tashi yaje yayo alwala dan gabatar da sallar asuba sai da ya idar da nashi salkahn yayi azkar kafin yatashe ta dan itama tayi tata sallar. 

Koda ta idar sai ta hau gado tasake bu’de wani sabon babin bacci. 

‘Karfe shida da kwata 6:15am Mahmud ya shiga bedrrom ‘din da kayan da yayi amfani dasu wurin bacci sai yaganta na’de agado, dama yayi tunanin haka tun daya ga shiru bata fito ba kuma tun ‘dazu baiji motsin ta ba. 

Ajiye su yayi sannan yashiga yayo wanka ya dawo ya shirya cikin ‘kananun kaya ya fita parlour ya zauana tare da bu’de system ‘din sa. 

Teemah kuwa bata tashi ba sai takwas saura 7:46am ta tashi wanda ba ‘karamin baccin safen datayin taji ba dan in har batayi baccin ba da wannan farkawan daren datayin ba’karamin ciwon kai zai sata ba kuma bacci zai dameta darana sosai amma yanzun kam tasan kozai dameta da sau’ki. 

Sai da tayi wanka ta shirya cikin atamparta suoer holland mai kyaun gaske ‘dinkin dai dai jikinta, powder kawai ta shafa afuskarta sai kwalli data saka acikin idanunta ta, simple’dauri tayiwa kanta amma duk da haka sai gata tayi fess da ita, fitowa tayi parloun tasame shi zaune yana aikin duba system ‘dinsa. 

Sai data zauna agefensa kafin tace _” ina kwana Yayah”_! 

Tafa’da tana kallonsa, shima sai ya ‘dago ya kalleta sannan ahankali ya amsa da “lafiya ‘kalau Fateemah kin tashi lafiya?” 

Da kai ta amsa yanzun kam tare da kauda kanta gefe dan ganin irin kallin dayake binta dashi. 

Tunani yake aransa wai dama haka auren yake ne?, shi be ta6a zaton haka ba, ba yau ya fara kallon Fateema ba, ba yau yafara kallonta cikin kwalliya ba amma yanayin dayake ji azuciyarsa yau ‘din ya bambanta da kullum, ko ‘kanshinta na yau ‘din ma daban yake. 

Maida idanunsa yayi wurin da system ‘din daniyar vmcigaba da abinda yakeyi sai ya tsinkayo muryarta tana fa’din ” Yayah nifa yunwa nakeji sosai”. 

Kallonta yayi shima sai suka ha’da idanu take yagane cewa asalin gaskiyarta kenan tafa’da masa dan yadda yaga tawani marairaice ta lan’kwasa kai gefe. 

Tashi yayi bayan ya rufe system ‘din yace tashi muje kitchen mu samu abinda zamuyi ” yayi maganar tare da juyawa ya nufa kitchen ‘din Teemah ma sai ta biyo shi abaya. 

Story continues below


Tambayarta yayi me takeso taci ita kuwa tace Tea kawai takeso, Mahmud kuma yace “alright nikuma inaso da irish chips dan haka araba aikin, ki ‘debo irish ki fara fere shi nikuma zan ‘dora Tea ‘din idan nagama sai inzo intayaki mu fere tare dan yayi sauri ko? 

Kai ta ‘daga masa alamar “ehh” 

Da haka suka gama duk abinda zasuyi suka dawo kan dinning domin karyawa. 

Da rana ma tare dashi sukayi girkin abincin su suka ci, dan ranar Mahmud beje ko’ina ba agida ya wuni abinsa. 

Sai da dare ne yafita yace mata bazai da’de ba zai dawo, koda ya fitan kuwa gida yaje ya gaida iyayensa Abbah nata saka mai albarka yayinda Anty keta ta6e baki daga gefe amma bata bari kowa yaganta ba.
Sai da zai tafine tace ya gaida amarya. 

Sai daya biya ya siyo mata kayan za’ki dangin su choculates kafin yadawo gidan dan yasan halinta bacin abinci zatayi ba musmman da dare, da ranan ma da ‘kyar ta ‘danci dayawa sai dayayi ta bata abaki kafin na ‘dan kar6a, dan cewa takeyi wai ita bawani yunwan datakeji ai basu da’de da yin breakfast ba, shikuwa yace dole sai ta jar6a tunda har shima yaji yunwa ai yasan itama zataji saboda tare suka ci abincin. 

Yana komawa gida ya Teemah tafara yimasa rigimar son yin waya da Mummyn ta Mahmud kuwa yace bayanzu sai zuwa safiya dan yanzu dare ya ‘danyi yace dasafe zasu ‘kirata, ‘kin amincewa tayi har fushi tayi dashi wai dan yace se da safe, sai da yayi mata cakulkuli kafin yasamu ta sau’ko bayan tasha dariya. 

Kamar yanda yafa’din kuwa washegari ya ‘kira mummyn suka gaisa sannan ya ha’data da Mummyn yayi tafiyarsa cikin gida dan yasan tsakanin ‘da da uwa dole akwai wani sirri. 

Mummy kuwa ba’karamin da’di taji ba yanda taji muryarsu ka’dai ma ya wadace ta, domin dama tana ‘dan jin tsoro dan sarai tasan Mahmud ma bason auren yake ba duba da yanda ya nuna halin ko inkula da Teemah kafin ayi bikin, amma yanzu dataji muryarsu wasai batare da wata damuwa ba sai ta ‘kara godewa mahallici daya sau’ka’kawa Teemahn abubuwa. 

Duk da haka sai data ‘kara tambayarta cewa ko akwai wani damuwa, Teemah ta bata amsa da ” a’a bakomai mummy ni dai inaso in ganku ne, daddy yace min zai so shi idan muka taho kuma har yanzu banganshi ba ya’ki yazo” 

Ashagwa6e tayi maganar, mummy kuwa sariya abin yabata ma, tace ” haba Teemah dududu yaushe 
ma kuka tafin , kiyi ha’kuri ai kinsan yana yawan zuwa lagos ‘din akan lokaci kuma duk ranar dayaje zaki ganshi tunda shi yayi al’kawari, yanzun yana da wata tafiya ne agabansa Dubai zashi kuma inajin zai ‘dau lokaci kafin ya dawo” 

_”Toh mummy ke yaushe zaki zo”?_ 

_” zanzo insha Allahu, amma ba yanzu ba sai naga kin nutsu kin kwantar da_ _hankalinki_ _tukunna”._ 

Zata sake magana mummy ta dakatar da ita da fa’din ” ina Yayan naki,?
“Bari inkai maa mummy baya kusa “
Da ” toh mummyn ta amsa mata sannan tacigaba da jan kunnan Teemahn akan tayi wa Yayah Mahmud ‘din biyayya, banda taurin kai tace komai yace kiyi masa kiyi kinji inde bana sa6on Allah bane, dan dah da tanzu ba ‘daya bane komai yanzu inkika masa Allah zai rubuta miki lada kuma banda rashin kunya kinji” 

“Toh mummy”
Yauwa ‘yar albarka kuma banda ‘kazanta, nama sanki da kwalliya kidingayi kullum, kuma banda taron ‘kawaye barkatai, ki ringa ri’ke sirrinki kinji ko”? 

“Uhmm”
Teemah ta amsawa mummy. 

Sai mummyn tace “
Yauwa ina yayan “? 

” bari inkai masa da sauri” 

Koda ta kaiwa Mahmud ‘dinma Mummy ce masa tayi kar fa yace zai biye mata dan tana ‘yar uwarshi yace komai tayi daidai ne, tace dan nasan halin Teemah da rawar kai, idan tayi badaidai ba ka hukuntata dan ta kiyaye gaba kaji” 

Murmushi yayi tare da amsawa mummyn sannan yayi mata godiya sosai daganan suka yi sallama tana me sanya musu albarka. 

Yana gamawa Teemah tace ” saura Hannah ” 

“Me kuma ya sami Hannahn”? 

Ya tambayeta dagan gan batare da ya kalli inda take ba yariga yasan manufarta na fa’din hakan. 

Teemah kuwa sai ta wani turo baki gaba cikin shagwa6a tace _” zamu gaisa ne harda sauran friends ‘dina dasuka tafi tare”_ 

_”Duk da wacce wayar za’ayi wannan gaisuwar, wai nikam ina taki wayar take ne ?_ Mahmud ya tambayeta yana ‘ko’karin mi’kewa. 

_” Banda credit ko ka’dan aciki Hannah duk ta gama dashi “_ ! 

Cewa yayi _”jeki_ ‘ _dauko ingani “_ 

Zuwa tayi ta lalubo wayar da kyar tasamota cikin drawer dan tun tafiyar su Hannah bata ‘kara bi takai ba. 

Gani tayi ma anmata har 12misssedcall dayake wayar na silent shiyasa bata ji. 

Atsaye tasame shi lokacin da ta
kawo mishi wayar, sai ta mi’ka mishi tare da fa’din _” har ma ta’kirani ashe duk_ _banji ba”_ 

Mi’ka hannu yayi ya kar6a yana dubawa yace _” taya zakiji bayan ke da kanki baki san inda kika cusa wayar ba”!_ 

Yana gama maganar ya mi’ka mata yace _” sata a_ _caji naga ma 1percent yarage dab yake da ‘daukewa, inya ‘danyi cajin sai_ _kiyi ‘kiran bari_ _na miki VTU kona bari sai na dawo_ ? 

” _a a yanzu_ “
Tabashi amsa da sauri. 

Har ya juya zai fita sai ta dakatar dashi da fa’din ” _Yayah pls_ _karka da’de”!_ 

Murmushi yayi sannan ya dawo baya ahankali zuwa inda take yace ” _karna da’de kika_ _ce?_ 

Da kai ta bashi amsa, sai yace mata _”saboda_ _meyasa?”_ 

” _Tsoro nakeji ni agidan idan ni ka’daice”_ 

” _idan nafara_ _fita office_ _fah”_ 

_”Rakaka zan nayi_ _ai kullum”._ 

Murmushi ya sakeyi tare da kaiwa nannunsa yaja kumatunta ka’dan sannan ya juya ya nufi ‘kofar fita, har ya kusan fita daga parlourn sai yace mata
” _me zan kawo_ _miki?”_ 

_” Berries da pineapple”._ Tabada amsa da sauri. 

Da kai ya amsa mata kawai daga nan sai yasa kai yafice zuwa harabar gidan hannunsa ri’ke da makullin motarsa. 

Koda ya shiga cikin motar be tada ta ba sai da ya tabbatar yayi mata VTU ‘din kafin ya tada motar tare da dannah horn, wani ‘dan guntun bayaraben me gadinsa yazo da gudu ya bude masa gate yafice daga gidan.


A kwana na hu’du da auren nasu, da dare suna cikin bacci Teemah taji tamkar ana tashin ta abaccin, ahankali tabu’de idanunta sai kuma taji tsoro ya shige ta karab ‘daya, zaune ta tashi afirgice tana rarraba idanu tare da yin salati acikin zuciyarta.

Matsawa tayi jikin Mahmud ta sake kwantawa tare da shigewa cikin jikin sa kamar wata ‘yar baby tayi luf amma still sai taji hakan be yi mata ba, jitayi zuciyarta na fisgarta zuwa wani abu daban daya girmi tunanin ta, hakan kuma sai yasa tsoron ta yasake ‘karuwa, danne fuskarta ta ‘kara yi sosai ajikin katifar haka zalika kafafunta da hannayenta duk ta baibaye su ajikin Mahumd ‘din.

Dole tasa Mahmud sai da ya farka daga baccin daya ke yi, yana farkawa kuwa idanunsa ya sau’ka akanta mamakin abinda yasata yin hakan yayi, sai kuma yaji jikinta da ‘dan ‘dumi ka’dan, tunani yayi ko bata jin da’di ne, ‘kila ko zazza6i ke damunta.

Yun’kuri yayi da niyyar tashi sai yaji ta ‘kara ‘kan’kame shi kamar me tsoron kar ya gudu ya barta, _” Fateemah”!,_
Ya ‘kira sunan ta ahankali adaidai kunnuwanta yanda ya tabbatar zata jishi.

Teemah kuwa bata amsa ba sai ma ‘kara yin luf datayi tana mai ‘ko’karin cusa kanta a’kirjinsa.

_” meke damunki ne_ _Fateemah?”_ 

Shiru ba amsa. 

” _Zazza6i kike jine_ ?”
Yasake tambayarta. 

Yanzun ma shiru be samu amsar tambayarsa ba.

Mahmud binta yayi da idanu mamakinsa na ‘kara yawaita, ganin bazata yi masa magana ba sai ya koma ya kwantar da kansa akan pillow ya barta ayanda ta ke so ‘din, yace ‘kila sanyi take ji ne shiyasa, dan in bahaka ba yasan Fateemah baza tayi haka ba, tunda ba yau ne farkon ranar da suka kwanta tare ita ba, be wani da’de da kwantar da kansa ba yaji hannunta akan a’kirjinsa tana shafawa ahankali.

Rintse ido yayi tare da fa’din ” _innalillahi_ _wa_ _inna ilaihiraji’un, wai meke faruwa_ _ne?,meke damun Fateemah? , kardai ina shiga hakkin  Fateemah azaman mu da ita batare da na sani ba?, amma har yaushe Fateemah tayi wayon da zata san haka?, this is unbelie………..”._

Tunanin sa ya yanke ne lokacin daya ji numfashin ta awajen kunnansa, ga dukkan alamu tayi nisa acikin yanayin da take ‘din, dan ko daya ‘dan matsar dakansa ma sake biyo shi tayi da nata kan da azama.

Afirgice ya mi’ke da ‘karfinsa sanadiyyar wani sabon salon daya ji take ‘ko’karin yi masa.

Dafe kai yayi tare da zuba mata idanu   yaga yadda hannunta ke yawo akan gadon a inda ya ‘daga jikinsa ga dukkan alamu shi take lalu6awa
” _Fateemah!,_ 
” _Fateemah_ !!……..
_Tashi kiji…._ _tashi_ _ki gaya min_ _meya faru, meke damunki?_ Yayi maganar yana me kusanta kansa da kunnuwanta yanda ya tabbatar zata jishi da kyau koda kuwa bancin me take yi dole zata jishi.

Story continues below


Amma ga mamakinsa kota nuna alamun taji anyi magana da ita ma bata yi ba balle yasa ran zata bi umarnin daya bata, ganin haka sai yasa hannayensa ya tada ta zaune, tana tashi ta zauna ‘din sai ta yi luuu tadawo kan jikinsa ta kwantar da kanta akan kafa’dar sa tare sar’ko shi izuwa jikinta da hannayenta.

Kai ya dafe duk abin Fateeman yabi ya ‘daure masa kai gaba ‘daya yama rasa me ze yi mata, jiyake tamkar ba Fateema bace kamar ba Fateemansa ba, tamkar an canja masa ita haka yake gani, asanin da yayiwa Fateemah ma sam bata da gigin bacci balle yace ko mafarki ne ko kuma gigin baccin ne yasata yin hakan.

Shima kawai sai yasa nasa hannun ya rungume ta izuwa jikinsa ya jinginu da jikin fuskar gadon yana shafa bayan ta ahankali, ahaka bacci ya ‘dauke su gaba ‘daya har zuwa asubah.

Da asubah da ya tashi sai ya gyara mata kwanciya ahankali yanda baze farkar da ita ba, sannan yaje yayo alwala ya tada sallah, bayan ya idar addu’o’i yadinga jerowa yana ro’kon Allah ya sanya zaman lafiya da fahimtar juna atsakaninsu, Allah ya tabbatar da alkhairin dake cikin wannan auren yakuma kawar musu da Sharrin dake ‘kunshe dashi, kuma ya shirya masa mahaifiyarsa shiriya na gaskiya.

Sai daya idar da sallahn kafin yaje yatashe ta dan itama tayi nata sallahn, yana tashinta kuwa ta tashi ta zauna tare da rero salati tana kallonsa.

Kanta taji yayi mata nauyi sosai sai tasa hannu ta dafe kan tayi shiru tare da sunkuyar da kanta.
_”Ya dai”_
Ya tambayeta bayan ya zauna daga gefenta.
_” kaina ciwo Yayah_”! 

” _Ohh very sorry, ki watsa_ _ruwa kafin kiyi alwalar zakiji sassauci bi’iznillah_ _inyaso ingari yawaye sai mu je_ _clinic abaki magani_ _ko”?_ 

Kai ta ‘daga masa alamar “toh”.

Sai yasa hannunsa ya tayata ta mi’ke tsayen ya rakata har bakin toilet  sannan yace mata ta shiga.

Nuni tayi masa da towel sai ya ‘dauko ya mi’ko mata da sauri dan yanda yaga idanunta yanda take bu’de su ma da ‘kyar sosai yaji tausayinta ya kamashi.

8:00am ya kaita wani ‘karamin private hospital aka dubata aka rubuta musu magani kawai suka taho gida,  amota ya ce ta jira shi yashiga wani babban chemist dake kan hanya ya sissiyo magungunan da aka rubuta musun sannan yazo suka koma gida.

Ranar Mahmud beje ko’ina ba ya zauna ya dinga kula da ita, sosai yake bata kulawa ita har yana bata dariya ma dan ta da’de da sanar dashi cewa ciwon kan ya daina amma sam ya ‘ki yadda motsi ka’dan intayi sai ya tambayeta ko menene.

Ranar da kansa ya tafasa musu indomie da rana suka ci da dare kuwa yace ta shirya suje eatry suci acan dan ba ze iya girkin komai ba yanzu duk ma be fi exercise ba, Teemah tace yaje yaci ya dawo ita kam bata jin cin komai yanzu, Mahmud kuwa yace dole sai taje, tayi-tayi dashi ya’ki barin ta har tace toh yaje in yaso yazo mata da nata still ya’ki amincewa saima ya ‘kara da fa’din wai idan ya fita bazai dawo gidan ba sai 11:pm yace in dai zata iya zama agidan ita ‘daya toh shikenan sai yatafi karkuma ta kuskura tayi masa complain idan yadawo, dagangan Mahmud yafa’di haka dan yasanta gwanar tsoro ce ita, aikuwa yaci nasara dan yana fa’din haka tami’ke taje ta ‘dauko zunbulelen hijab tasa akan kayan dake jikinta suka fita tare.

Mahmud nata cin abincinsa yayinda Teemah tari’ke spoon ‘ahannunta tana ta juyawa tare da kallon abincin, murmushine ya kubce mata sai ta ‘dago kai ta kalli Mahmud sai kuwa suka ha’da idanu ”  ‘ _yanmatan Daddy ya_ _dai_ yace mata.

Sai itama tace bakomai. 

” Yah Abbas na tuna wallahi, shifa sam be son cin abincin waje ko yunwa zata masa illlah ne baya ta6a ci har se yadawo gida”

Murmushin shima yayi tare da fa’din ” _Abbas zakin fama ba, haka halinsa shikam ai kominsa yana da nasa tsarin.”_

Hirar Abbas suka tayi har suka ‘kare cin abincin inda Mahmud ne kawai yaci Teemah ‘dan cakula tai tayi kawai daga nan kuma sai suka wuce shopping store  suka ‘dan siyi wasu abubuwan anfani.

Story continues below


  Mahmud gidan mahaifinsa yawuce dasu basu sami Abbah agida bama sai dai Anty na nan sun same ta tana waya ne sai suka yi zaman jiran ta, jisuka yi tana fa’din “ehh lafiyan ta gasu nanma yamzu suka zo, ok ta’kqre maganar dashi tare da mi’kawa Teemah wayar kar6a tayi tare da fa’din “Hello” atakaice duk da bata san waye akan layin ba amma sai ta tsinci zuciyarta da rashin son yin magana alokacin.

Daga cikin wayar taji wata murya da bata san ta tana fa’din _”Baby how are_ u?. 

Da ‘yar muryarta da haushi yafara cikawa ta furta
_” Fateemah ce !”_ atakaice 

_” i know naa, don’t_ _worry u ll_ _soon………_ 

Bata bari ta ‘karasa jin mai matar zata fa’da ba tacire wayar akunnanta tare da mi’kawa Anty wayar, afakaice Anty ta doka mata harara batare data bari sub lura ba sannan ta kar6i wayar dan ayanayin response ‘din Fateeman Anty ta fahimci ba gaisuwar kirki suka yi ba hakan kuwa sai yasata ‘kara jin haushi amma bata bari yanuna akan fuskarta da yanayinta ba sai ta tsare ta daidai ta nutsuwarta atake.

Tana kar6ar wayar ta yanke ‘kiran tare da ‘ka’kalo murmushi tace ” ga dukkan alamu dai amarya tayi uwar ‘daki, kinga kuwa yanda ta damu kullum sai ta tambayeki idan ta’kira awaya ,ai dan tayi tafiya ne ma inbahaka ba nasan da yanzu har kun saba ma da ita tun ranar da kuka sau’ka agidannan taji kin manta……………..

Teemah baki ta ta 6e lokacin da idanun Anty yabar kanta, aranta tace ” _su uwar ‘daki manya, shine har da wani cemin baby, ce_ _mata akayi ni inason uwar ‘daki ne?, mummy na_ _ma ta isheni nikam_ ”  

Mahmud kuwa shiru yayi kawai yana nazari dan kuwa yasan wannan uwar dakin bana gaskiya bane, bazai so ya tankawa mahaifiyarsa magana a gaban Teemah bane dan gudun watarana kar kuma yazamana shine da kansa yabada kofar raini ga mahaifiyarsa, inba dan haka ba daya ce baya son wannan ala’kar saboda yasan duk wani abu dazai tunkaro su ta 6angaren Anty toh ba alkhairi bane shiyasa yake tsoro, amma azuciyarsa sai yayi alwashin cewa ze tsaya tsayin daka dan ganin ya ruguza wannan ala’kar tun kafin tayi ‘karfi.

‘Bangaren Anty
kuwa kar6an su tayi ba yabo ba fallasa suka gaisa, tare da gabatar musu da abinsha agabansu sai dai suna gama gaisuwan ta tashi ta shige ciki tace dasu tana zuwa, zaman kusan 1hr sukayi ba Anty ba labarinta, Mahmud daya gaji sai yace mata ta tashi su wuche be ko sake neman Antyn ba sukayi tafiyarsu dan yasani sarai Anty dagangan tayi musu hakan.


*****
Tun ranar da Abbas yabar garin damaturu bayan ‘dauri auren Mahmud be ‘kara samun lokacin kansa na kirki ba, harma hakan sai ya zamana kamar taimako ne agareshi da zuciyrsa harma da rayuwarsa dan sam  be samu lokacin da zai zauna har yayi tunani akan rayuwarsa da rabuwarsa da Fateema ba sai dai duk da haka ‘yar walwalar dayake da ita yanzu babu shi koka’dan, yanayin komai ne ayanda sabuwar rayuwarsa ta zo masa da shi.

Saleema kansa tunda Abbas ‘din ya sau’ka a wurin shi be gane kansa ba, kuma sam ya’ki ya bu’di baki yayi masa bayanin meke faruwa dashi, ya dai   ce masa daga damaturu yake yaje ‘daurin auren sister ‘din shi, tun daga nan be ‘kara yi masa wani bayani akai ba, dayake Saleem yasan halin kayanshi sai ya ‘kyale shi dan yasan matu’kar Abbas be yi niyyan yin magana ba toh babu wanda ya isa yasashi dole, dan haka sai shima yabarsa kawai yaci gaba da abinda ke gabansa, toh dama ma yaya lafiyar kura……


Washe garin ranar daya bar Barrack 44 Kaduna, aranar ko zama beyi ba ogansa ya wakiltashi zuwa wani taro acikin garin porthacourt ‘din.

Ranar lahadi ne ka’dai ya ‘dan samu ya huta washegari kuwa rakiya yayiwa ogansa zuwa Biu Borno state domin halartar wani taron bu’de wata makaranta acan cikin garin Biu Nigerian Army Institute of Technology & Environmental Studies (NAITES).

Sosai hakan ya’kara taimakon Abbas dan kuwa taron sosai ya me dashi busy man harma sai ya ‘dan manta da damuwarsa ya ajiyeta agefe guda ganin cewa saka damuwa aransa ayanzu tamkar yana kashe kansa tabaya ne dan kuwa cutar kansa kawai zaiyi batare da yasami dan taimako ba idan har yace sai ya zauna yayi tunaninta, yarinyar datariga ta tafi ta barshi, bari na har abada toh miye abin 6atawa kansa lokaci shi kuma akanta.


*LAGOS*
Mahmud duk wani ‘ko’kari dayasan ze wanzar da zaman lafiya da fahimtar juna atsakanin sa da matar shi yayi ‘ko’karin ganin ya aikata shi duk dama har yanzu beji cewan shima magidanci me iyali bane shi gani yake kamar wata ‘kaddara ce tasasu kasancewa atare, amma hakan bai hana yabata dukkan kulawan daya dace ba, ko dan kasancewarta matsayin matar sa da jama’ah da dama suka shaida, sannan kuma ‘kanwa ce mafi soyuwa azuciyarsa,  abu ‘daya ke ‘daure masa kai yanda akowani dare sai yanayin Fateema ya canja yakasa fahimtar inda matsalar take tasowa yama rasa gane meke yawo akanta da har yake sata lalu6ansa akowani dare bayanshi hakan kokadan baya gabansa.


Ranar da suka cika 16days da aure aranar anyi ruwan sama sosai kuma duk ruwan akansu ya ‘kare dan Fateema duk ranar dataga za’ayi tunkan ruwan ya sakko take fara shirin shiga ruwan , shiri zatayi cikin riga da wando marasa nauwi ko bra bata sawa idan zata yi shirin wasan ruwan sai ta rufe kanta da shower cap.

Da farko Mahmud ‘kin barinta yayi amma data rin’ka rokonsa dolensa sai daya amince ya barta, daga baya kuma sai ya fara tayata shiga ruwan,   tun daga lokacin be ‘kara hanata ba kodan lura da yayi hakan na ‘daya daga cikin abubawan dake matu’kar sata farin cikima,  sai ma su shirya dukkansu sushiga ruwan sunata juyi suna dariya wataran kuma sukama hannaye suyi ta juyi aruwan  suna tsalle-tsalle kamar ‘kananan yara.

Mahmud da kansa yafara mamakin kansa dan irin kayan da take sawa su fita wasan ruwan dashi shika’dai ma abin kallo ne, sau da dama yana mamakin kansa yanda yake ganin Fateemah akowani irin yanayi amma be ta6a jin wani sauyi tattare da shi ba, sau da dama yakan tsaya ya ta kallon yanda kayan jikinta suka manne mata suka bayyana dukkan surorin jikinta sanadiyyar ruwan saman da ya ji’ka su, awannan lokacin kowani irin ‘da namiji yaganta sai yaji wani abu aransa da jikinsa koda kuwa ya yake amma ga mamakinsa shi be ta6a jin wani canji ajinkinsa game da hakan ba, da farko abin baya damunsa dan ya ‘dauka ko rashin ‘daukar auren nasu amatsayin aure ne yakawo hakan amma daga baya abin sai ya fara damunsa, shikansa yaji yana so yaji wani sauyi tattare da shi amma sam yarasa dalilin hakan, tsakaninsa da ita sai de kallo da ido and nothing more.

Exactly that day kamar yanda Fateemah tasaba yi masa hakan tayi, zuwa yanzun ma yafara sabawa da yanayin nata ya fahimci kawai hakan take bawai rigima bane kawai ko wani abu daban,  saboda tun ranar data fara yi masa irin wannan ‘din dai-dai da rana ‘daya bata ta6a fashi ba akullum sai ta lalu6e shi, tun baya kulata har ya fara taimaka mata, wasu lokutan yakanyi romancing ‘dinta duk dan yataimaka wa yanayin nata dake ciki bawai dan yana jin da’din hakan ba, cikin sa’a kuwa sai yaga bacci ya ‘dauketa bayan hakan wataran kuwa idan abin yafaskara baya sanin lokacin dayake fara jero mata addu’o’i ma da ikon Allah kuwa sai yaga tayi la’kwas tayi bacci tare da jero ajiyar zuviya acikin baccin.

   Idan darana ne kuma kamar ba ita ba sam bazama kace ita ce ke neman sa arikice da dare ba.

Na yau ‘din kam yasha bam-bam dana kullum, dan  kukanta ne yatashe shi abacci, kukan take sosai tana danne cikinta tare da takura kanta guri ‘daya tana shiga jikinsa, koda ya nemi yi mata kamar yanda yasaba ‘din sai ta nuna masa alamun bahaka take so ba ita.

Rasa yanda zaiyi da ita yayi gashi sosai take bashi tausayi,  mamakin kansa sai ya hana shi taimaka mata illah tsayuwa dayayi saroro yana kallonta, so yake ya lalu6o dalilin amma yarasa dan ayanda yasani da ba haka yake ba, be san me ya maida shi mara anfami yanzu ba, gashi yanzu taimakonsa ka’dai Fateemah take nema awannan yanayin while shikuma badama.

Dayaga kukan data keyi yana so yayi yawa sai ya koma yajawota jikinsa ya rungumeta da ‘kyar, tausayinta ya da’da karya masa zuciya ganin da kanta take neman raba jikinta da kayan baccin data ke sanye dashi, zafi rau yaji jikintan kamar wacce take tsaka da zazza6i, hawayene yaji ya gangaro masa sai ya lumshe idanu ahankali yafurta 
_” ki yafe min Fateemah, bansan haka ne zaizo yafaru dani ba_ _kamar yanda bansan haka yanayin ki yake ba tun farko, wallahi_ _dana san haka ne da bazan amince da auran ki ba ko dan gudun kar nashiga hakkin_ _ki, da ha’kuri zan bawa Abbah na da Daddy akan afasa ‘daura mana aure, amma nasan ‘kaddara ce ta ha’da auren mu kuma ni ban isa na dakatar da ita zuwa garemu ba,  ki yafe min kinji……_ _ki yafe min Fateemah insha Allahu zan nema miki mafita……….”_

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *