ABBAS
CHAPTER 15
Washe gari Mahmud asibiti ya je aka duba shi aka bashi magani hadda allurai daga nan sai ya wuce office ‘dinsu amma ko 2hrs mai kyau beyi ba awurin yadawo gida kafin haka kuwa yayita ‘kiranta yafi sau biyar yanajin ya take.
Yana komawa gidan kuwa Fateemah tafara yi masa rigima akan wai dole sai sunje sun yi wasan basket ball dashi, Mahmud duk da yana cikin damuwa amma haka ya daure ransa ya amince mata suka fita wurin wasan dan kawai ya faranta mata, daya ke akwai wurin yi ‘din acikin gidan nasu daga ‘dan nesa ka’dan da bakin get, wurin ‘dan daidai ne bawani babba ba musamman aka tsara shi saboda masu gidan.
Bomshort ne ajikin Teemah wanda yakama jikinta sosai sai wata ‘yar 6ingilar ba’kar riga da bata ko rufe cibiyanta ba kanta kuwa wani bakin shararan hula ne da aka sa’ka shi da zaren lilo, ba ‘karamin kyau tayi acikin shirin nata ba, Mahmud kansa gani yayi tayi masa kyau sosai ba ‘karamin birgeshi tayi ahakan ba, yakan juyo ya kalleta lokaci zuwa lokaci dan yasan iya abinda Allah yabashi iko kenan akanta tunda ga halin daya tsinci kansa aciki, duk dama yana saka ran samun sau’ki akowani lokaci tunda likita yayi masa bayani mai kyau kuma ya gamsu, ya sa hope ‘din sa akan magungunan da aka bashi tare da taimakon Allah da kuma izninsa zai sami sau’ki.
Isar su filin keda wuya suka fara buga wasa, Fateemah daman bawani iyawa tayi ba tsabar rigima ce, garin shige shigen ta acikin gidan ne idonta yaci karo da wurin wasan shine fah ta dage sai anyi, 3:0 Mahmud yamata tana ganin haka kuwa tafara tsalle tana fa’din a’a bata yadda ba gaskiya wai itama yajefa mata ko sau ‘daya tunda ita ta kasa.
Dariya ma abin yabashi, yakuwa dara, acikin dariyar yace ” _a ina kika ta6a ganin anyi haka, nine kuma zan jefa miki?_ _Hhhhh_ ya ‘karasa maganar tasa da dariya.” _U ar so funny Fateema “_ tare da nunata da yatsa.
Baki ta turo tayi fushi har zata juya yasa hannu ya cafko hannunta ‘daya yace mata ” toh shikenan amma sau ‘daya zai jefa mata tana jin haka tace ehh ta amince.
Jefawan yayi da sunan nata ne, ai kuwa take tafara tsalle da murnan taci ‘daya, da ya ‘kara yi kuma take sai yabata 4:1 daga nan kuma tace ya ‘dagata itama tasaka da kanta, yazaro idanu tare da fa’din _” kai……. ke ‘katuwan nan ne zan ‘daga ?_ Yafa’da da sigar zolaya, _”gaskiya kina cutata haka ake wasan ne?_
Bubbuga ‘kafafu tafara yi a’kasa cikin shagwa6a tace _” ni de sai ka ‘daga ni bayan sai shana kake yi kawai dan ka ga ka fini tsawo, ai da yah Abbas na nan nasan da zai tayani nima”_
Kwa6a fuska tayi kamar zatayi kuka ganin haka sai yace toh tazo ya’daga ta, tana jefawa tasake sakin murna tana dariya kamar wanda yin kanta ne bada taimakonsa ba, tsalle take tana fa’din ” _yeehhhh naci_ _biyu”._
Shima sai ya yatsaya kallon ta yana dariya yace.
_” kinmanta 4:2 muke, ratar biyu fah nabaki”!_
_”Ehh ai biyu ne kacal kuma nima yanzu zan taro ka”_
Tana fa’din haka sai taci gaba da murnarta abinta.
Horn sukaji an danno daga waje, mai gadi yaje da gudu yale’ka sannan yadawo ya tura gate ‘din batare da yayi magana ba dan ganin wanda ke cikin motar.
Teemah kam jin horn ‘din koka’dan be dakatar da ita daga murnar data keyi ba dan bata ko damu da waye yazo acikin motar ba.
Mahmud kuwa bin motar yayi da kallo ganin dayayi cewa motar ta gidan sune ta shigo sai dai bai gane wacce ke cikin motar ba dan sun ‘dan yi nesa dasu ka’dan, motar na tsayawa su Anty suka fito atare ita da ‘kawarta daga cikin motar idanunsu gaba ‘daya nakan su Teemah, dan tun shigowansu suka hango su a filin wasan.
Wani tuku’kin takaici ne yacika zuciyar Anty ganin cewa wai har lokacin yin wasa suka ke6e acikin gidan domin kawai su sha’kata, lalle nayi sake, shirun nawa yayi yawa, shiyasa har yarinyar dana so na wargaza auren ta tun ranar farko tasami saken da har zata buga basket ball agidan da na tsani ganinta aciki har ma da ‘dana ‘daya tilo dana mallaka aduniyan nan kuma na tsani ganinsu atare.
Zagayawa tayi da sauri ‘daya 6angaren da ‘kawarta take tsaye dan ita tun fitowanta daga motar bata ‘kara ko motsin kirki ba awajen, ta tsaya saroro tana kallon Teemah kamar zata cinyeta ‘danya.
Dafa kafa’dar ta Anty tayi sai ta juya da hanzari, akufule Anty tafara magana
” _kin gani ko, kinga abinda nake ta faman gaya miki amma kika ‘ki_ _taimakona saboda wani dalili bayan kinsan sai da kene nasara take zuwar min, yanzu gashi_ _shirun danayi na zuba ido yasa har sha’kuwar su tayi nisa, dubesu kiga……..”_
Ta ‘karashe da nuna su.
” _Come down mana mum Mamud,_ _everything ll be alright since am here komai zai zo da sau’ki in dai har kika goya min baya_ _zan taimake ki kirabasu kamar yanda kike so amma sai kin tayani cika_ _*BURINAH* “_
Kallon Anty Chideh kawai Anty keyi dan koka’dan bata fahimci manufarta ba, karta ce har yanzu tana kan bakanta na wancen maganar ne, in de kuwa har hakane toh sai de kowa ya ha’kura da ‘kudirinsa dan bazata iya aikata wancan aikin ba da girmanta ba yarinya , infact tunda ma har ta iya bari akayi auren akan ta’ki amince mata toh kuwa bayan auren bataga dalilin da zai sata ta aikata ba.
Anty Chideh kuwa murmushi tayi ganin Anty ta tsaya shiru tana tunani, tasan cewa maganar su nabaya take tunawa dan haka sai ta dago hannu tashafi fuskar Anty ,baya Anty taja da sauri, Anty Chideh kuwa sai ta sake murmusawa tare da fa’di.
” _feel free mum Mamud this time around daughter in-lawn ki nakeso not_ _u, tunda ke kin’ki bani ha’din kai na ha’kura dan nasan bazaki amince ba, amma yanzu kam matu’kar kika tayani fighting_ _nasameta toh na miki al’kawarin raba auren nan rabuwa_ _na har abada, zan kaiki duk inda kike so kika kuma za6a_ _dan kawai ki cika naki burin._ “
Sosai maganar Antyn Chideh ya suprising Anty, bata ta6a zaton iskancin nata har zai koma kan ‘yar cikinta ba, no wonder shiyasa tun ranar da aka kawo yarinyar ta yabeta dan ma tayi wata ‘yar tafiya ne inbahaka ba tasan da tunda wuri tagama ya’da manufarta, tunowa tayi lokacin da Anty Chidehn bata nan kullum sai ta ‘kirata awaya takuma tambayi lafiyar amarya ashe akwai ‘kunshin abu aranta, harma ranar tace abawa Fateeman waya dan kawai taji cewa sunzo suna kusa, amma Anty bata wani damu ba jin cewa abin ya bar kanta ya koma kan makiyarta ai ita hakan yafi komai yi mata da’di tunda kuwa hakane dole in goya mata baya.
Daga nan ta tabbatarwa Anty Chidehn cewa duk yadda take so haka za’ayi dai dai nan Mahmud ya iso wurin da suke tsayen cikin ya’ke yace ” _ahh barkanku da zuwa Anty ya kuka tsaya anan kuma?, mu_ _’karasa daga ciki pls”!_ ya ‘karasa maganar tare da juyawa.
Anty batayi magana ba illah kallon bayanshi datake yi sai kuma bata ga Teemahn ba.
Kasa ha’kuri tayi sai da ta tambaya inda tace ” _ina amaryar taka kuma Mahmud batare_ _naganku bane_ _’dazu”,_ kai Mahmud ya sosa tare da fa’din _” ta_ _wuche ciki yanzu?_
Sababi Anty ta fara akan wai ” _tsabar ta raina ta ne shiyasa tana ganinta ta wani yi wucewarta_ _inbahaka ba me yasa bazata zo ta tar6eta anan ‘din ba kamar yanda Mahmud ‘din yayi, kodan tana ganin ba nice na haifeta ba, na tabbata da Khadija tagani anan da sai ta riga ka ma zuwa inda isowa”._
Mahmud be yi magana ba da be san me zai ce da Antyn tasa ba, toh yace mata kunyar kayan jikinta yasa tayi ‘dakin ko kuwa yace mata tatafi suturta jikinta ne.
Murmushi ne ya kubce masa daya tuna lokacin da zai taho inda su Anty suke Teemah ma fara biyo shi tayi ahakan dan ko damuwa batayi da kayan da yake jikinta ba kota manta ne oho, sai da yace ” _kiyi sauri ki wuce ciki ki saka gown akai kar su ganki ahaka ko bakya jin kunya ne_ _su ganki ahakan…….?_
Yana fa’din haka ta juya da gudu ta koma ciki, may be lokacin data wuche ‘din hankalin su Anty baya kansu shiyasa ma basu lura ba.
Anty Chideh ce tace da Anty tayi shiru mana bata son yawan fa’da bayan tasan cewa yanzu Teemahn propertyn tace, tace mata kayan jikinta ‘kanana ne may be tana jin kunyane shi yasa bata zo nan ‘din ba.
‘Kasa-‘kasa tayi maganar yanda Anty ka’daice zatajita.
Duk da Anty Chideh cikakkiyar bayerabiya ce amma yawacen yawacen data tayi a wurare da dama yasa tasan dayawa daga cikin al’adun hausawa shiyasa tayi saurin kare Teemah da wancen maganar.
Anty kuwa ta6e baki tayi, ‘kasa-‘kasa tace _” iskancin banza da ‘din me yasa ta saka kayan tunda tasan tana jin_ _kunya aganta dasu”_
Mahmud ne agaba lokacin da suka shiga cikin parlourn, bayansa Anty ce sai Anty Chideh daga ‘karshe, a’kofa ma suka ha’du da Teemah tana ‘ko’karin fita ganin su yasa ta basu hanya suka shishshigo, hijab tasako babba akan doguwar rigar data saka ‘din sosai tayi kyau acikin hijab ‘din dan ya ‘kara fito mata da hasken ta da kuma ‘dan madaidaicin fuskarta tayi ‘das aciki.
Abinsha tawuce ta ‘dauko musu sannan ta zo ta zauna ta gaidasu Anty Chideh ce kawai ta amsa da fara’ah tana wani kallon cikin idanun Teemah, Anty kuwa ayatsine ta amsa mata, bata wani damu da yanayin da Anty ta amsa gaisuwar ba, illah kallon da Anty Chideh ke binta dashi ne ya ‘dan so ya ‘daure mata kai dan haka sai tayi ‘kasa da kanta tana wasa da yatsun hannunta.
Tashi Mahmud yayi ya shiga ciki da niyyar saka ko jallabiya ma akan wandon three quatern dake jikinsa, da wannan lokacin Anty tayi anfami tayiwa Teemah bayanin wacece Anty Chideh awurin ta, tace saboda watarana ko bani zata iya zuwa duba ki ita ‘daya ina so ki san cewa matsayina danata tamkar guda ne awajenki karki kuskura ki yi mata badai dai ba, kinji ko baki jiba, da _” Naji “_ Teemah ta amsa mata ahankali.
Mahmud na sako rigar ya fito yadawo parlourn.
Su Antyn ma basu wani da’de ba dan ko 10mins basu yi ba suka ce zasu tafi dama Anty Chideh ce ta matsa sai sun zo wai tanaso taga daughter in-law ‘din nasu ne, Anty bata so zuwan ba dan haka tace bari kawai ta ‘kirasu suzo sai Anty Chideh ta’ki amincewa da hakan, dolen ta ta shirya suka taho, alokacin ma Anty bata san meke ran Anty Chideh ba sai bayan isowarsu ne da ta mata bayani.
Har gurin mota su Mahmud suka musu rakiya, Teemah nata ra6ewa ajikin Mahmud dan avoiding ha’da idanu da Anty Chideh datakeyi, Mahmud kansa ya lura da haka amma ya basar dan be san dalilinta na yawan kallon Teemahn ba, sam ta tatsani ganin matar ita, ganin cewa ‘katuwar babbar mace da ita amma tana mata abu kamar mara hankali ,inbahaka ba miye abin yawan kallo awurina, sai kace bata ta6a kallon mutum kamar ni ba”.
Acikin ranta taketa wannan masifar, azahiri kuwa kanta na gefe bata ma kallon inda suke.
Sai da suka ja motar sannan ta sau’ke ajiyan zuciya tare da dokawa bayan motar harara, ta kalli Mahmud sai suka ha’da idanu take sai yayi sama da girarsa, ga dukkan alamu yaga abinda tayiwa bayan motar su Antyn, da sauri tace _” wallahi Yayah banason matar nan ni koka’dan”_ hannunta yakamo suka fara tafiya sannan anutse yace
_” wacce daga ciki?_
_”Wannan inyamuran matar mana, sai ta ta wani kallona tana smiling bayan ni banma_ _santa ba, ban ta6a ganin ta ba ma ni, haushi tabani sosai yau ‘din nan”!_
Murmushi yayi sannan yace mata ” _’kawar sirikar ki ce kinga kuwa dole ki_ _sota ai “_
_” ehh ai Anty ta fa’da min ‘dazu.”_
da wannan hirara suka koma parlour suka zuzzube , Teemah na shiga ta fincike hijab ‘din tare da rigar data saka wai zafi yadameta, dama garin sauri ko na cikin bata tsaya ta cire ba ta ‘dora doguwar rigar akai.
*****
Mahmud har 10:00pm ya kai a parlour yana kallon News a NTA, yayinda Teemah tayi kwanciyarta tai bacci dan dama ita ba gwanar zama tayi kallo bace, sam kallo be dameta ba arayuwarta.
10pm cif Mahmud yatashi tare da kakkashe switch ‘din sannan ya shige ciki, sai da yaje ya watso ruwa kafin yazo ya kwanta, yana sa jikinsa akan gadon kuwa ko addu’ar bacci be gama ba yaji wani bacci me shegen nauyi from no where yana firgarsa har idonsa ma baya iya bu’dewa, be masan lokacin da baccin ya ‘daukesa ba danko addu’ar yin baccin be gama karantowa ba, be tashi sanin kansa ba har se lokacin sallar asubah, har alokacin kuwa baccin be bar idanunsa gaba ‘daya ba still yanajin idanunsa na masa nauyi, da ‘kyar ya ya’ki zuciyarsa ya samu ya tashi, koda yatashi sai be ga Fateema akan gadon ba, sai yayi zaton ko tana bayi, zaman kusan minti biyar yayi amma beji motsinta aciki ba kamar yadda bega alamun ta a bayin ba, tunowa yayi yau ko motsinta beji ajikinsa ba _”where_ _is she_ _toh_ ? dan har yanzu wutar ‘dakin akashe yake, in kuwa Fateemah ta tashi ne yasan dole sai ta kunna wuta saboda tsoron da ya san tana dashi.
Sai da ya duba cikin toilet yaga bata nan kafin ya wuche parlour ‘a’dan rikice dan zuwa yanzu ya ‘dan fara shiga ru’du da rashin ganin Fateeman, switch ya kunna na parlourn sai ya hangota kwance a’kasa ta kwanta akan ruwan cikinta tana baccinta cikin kwanciyar hankali, ajiyar zuciya ya sau’ke daya gantan sai ya sake kashe mata wuta ya wuche ya yo alwala, sai da ya idar da sallah ya ‘daga hannu ya jero addu’o’i sosai kamar yanda yasabayi kullum, sannan ya tashi ya koma parlourn domin yatashe ta.
Lokacin data tashin ita kanta taso tayi mamakin inda ta ga kanta saboda kalle-kalle tafari da mamakin meyasata kwana ana ‘din, sai daga baya da ta’dan yi recalling abin da yafaru sannan ta tuna ashe da ‘kafafunta tazo parlourn.
Koda ta ganshi agefenta kuwa take sai ta tura baki gaba tare da kau da kanta gefe tana wani yatsina fuska
_” meya faru ne Fateema, meyasa kika dawo nan kika kwanta ke ‘daya”?_
Mahmud yayi maganar cike da kulawa.
Yana kaiwa ayar tambayar tasa kamar jira take yayi shiru sai kawai ta mi’ke tsaye bata ko ‘kara kallon inda yake ba, binta yayi da idanu harta 6acewa ganinsa yana mamakin ‘kin kula shin data yi, wanka tayi tafito , lokacin ma gari har gari yafara haske, gurin dressing mirror ta nufa tana goge jikinta da towel , Mahmud kuwa yana zaune agefen gado yana kallon bayan ta, sai da tazo ta bu’de closet ‘din kayanta kafin tace _” ina_ _kwana yayah”_ tayi maganar kanta akan kayan batare data ko kalli inda yake ba, shima be amsa mata ba illah hannunta da ya jawo ta dawo gefe dashi ya zaunar da ita, tana ‘ko’karin sake tashi ya dakatar da ita da fa’din ” _inajinki me kika ce_ ” yafa’da yana kallonta, ” _ina_ _kwana_ ” tasake fa’di atakaice kanta na ‘kasa.
Murmushi yayi batare da ya amsa gaisuwar ba yasake fa’din _” sallar fah sai yaushe zakiyi?”_
_” Nayi”_
Yace
_”Yaushe?_
_'”Dazu”!_
Tabashi amsa tana yun’kurin tashi.
_” a ina kenan?”_
Yasake tambayarta.
Sai ta bashi amsa da fa’din _”a parlour._ “
Jijjiga kansa yayi dan yasan ‘karya take bawani sallar datayi.
_” wai laifin menayi ne haka lil sis please tell me kinji_ _banson kin……_
Be ‘karasa maganar ba ta tare shi da fa’din _” bakai bane,_ _jiya ciki na ciwo yatayi dadare_ _nakasa bacci, ina ta tashinka kai kuma ka’ki ka kulani, bayan nasan kana_ _jina “_
Kansa yadafe tare da fa’din
_” innalillahi, ya akai duk bansan anyi haka ba, pls_ _Fateemah kiyi ha’kuri kinji aikinsa bahaka nake yi miki ba ko, wallahi jiyan_ _ne baccin ya min nauyi ni kaina nayi mamaki, amma insha Allahu hakan_ _bazai sake faruwa ba kinji”_
Shiru tai masa batayi magana ba,
_” bazaki ha’kura ba_ _ko Fateemah?_
Tashi yai kamar zai tafi irin yayi fushi ‘din nan shima, take sai Teema ta kamo hannunsa koda ya juyo kuwa sai suka ha’da idanu, kai ta jijjiga masa sai yace mata _”kin_ _ha’kura”_ da kai ta amsa masa alamar _”ehh”,_ yana ganin hakan sai yadawo gefenta ya zauna yace toh tayi dariya yagani, murmushi tayi tare da sunkuyar da kanta ‘kasa shima murmushin yayi yace cikin zolaya yace _” wato dan na ‘ki kulaki shine kika yi fushi kika koma parlour kika barni ni ‘daya a ‘daya a’daki ko?._
Dariya sukayi atare daga nan maganar ta wuche suka shiga harkokinsu kamar kullum.
‘Karfe takwas 8:am na safe Mahmud ya wuche offfice tare da rakiyar Teemah har wajen da zai shiga motar sa, tana ‘kara jaddada masa wai ya dawo fah da wuri dan ita tsoro take ji, kullum dama inzai fita sa’kon ta kenan, sai kuma tace ya siyo mata tarkacen fruits da har yau tafi sansu akan abinci, takan sha ko ci aduk lokacin da Mahmud ya matsa mata akan taci abinci, wani lokaci kuma sai taci abincin musamman ranar da ya ‘ki siyo mata fruits ‘din, yauma daya tambayeta abinda zai kawo mata sai tace masa Apple kawai takeso yau, murmushi kawai yayi ya juya ya shige mota dan baya so ta sake yin fushi dashi akaro na biyu badan haka ba da bazai siyo mata ba, dan yasan idan tana ganin fruits ‘din bata ta6a waiwayar abinci akan lokaci sai ta ga dama.
Bye-bye ta masa daga nan yaja mota ya fita agidan shima yana me ‘daga mata hannu.
*****
Duk wani abu daya rage na tafiyarsu Daddy yayi ya kammala komai harma yarage saura kwana biyu kacal su tafi, Mummy taso taga ‘yarta kafin su tafi amma Daddy ya hana ko awaya ma yahana ta sanar da ita saboda baya so ta ‘daga hankalinta, yafi son tayi zamanta hankali kwance agidan mijinta batare da sa damuwar komai aranta ba, Mummyn ma damuwarta ayanzun bai wuce tasan irin zaman da Teemahn keyi da Anty ba abinda yafi damunta kenan, dan tasan 6angaren Mahmud da sauki duk dama tana zargin bason auren yake ba, amma koda ta ‘kira Teemah awaya bata samun labarin komai, Teemah bata sanar da ita matsalar dake damunta, akullun cikin farin ciki take jinta, tun tana zargin ko Teemah na 6oye mata ne har tazo ta yarda cewa Teemahn bata tare da damuwa, fatanta dai Allah yasa hakanne, Allah ya wanzar da farin ciki da zaman lafiya a tsakaninsu gaba’daya.
Wata’kila shiriyace tazo wa Antyn shiyasa ta yada makan ya’kinta ta ri’ki Teemahn amatsayin matar ‘danta Mahmud.
Mummy takanyi murmushi ita ka’dai idan hakan yazo ranta domin babu abinda ya fimata da’di da farin ciki ayanzu irin taga Teemah na rayuwa cikin walwala ga dukkan alamu kuma burin ta ya cika.
Hatta Ummah da su Hannah basu sanar da ita tafiyar da iyayentan zasu yi ba, dan gaba ‘daya Daddy ya hana kowa sanar da ita, bayan kwana biyu ranar wata litinin da ‘karfe biyar na yamma jirgin su yatashi zuwa dubai tare da rakiyar Abbas daya baro bakin aikinsa anan cikin maidugurin dan yakusan sati anan ‘din da aka kawo su, domin kwantar da tarzoma da irin matsalolin ‘yan ta’adda dake addabar yankin na arewacin Nigeria musamman ma jihar Borno, koda zasu rabu ma su Daddy na ta sa masa albarka da zuba masa ruwan addu’o’i na kariya daga dukkan munafukai da mahassada dama dukkan wani abin ‘ki musamman ma yanzu daya taho nan domin yin ya’ki da ‘yan addacin ‘kasar tamu ta Nigeria, da Ameen kawai Abbas ke amsawa dan shi kanshi yasani zuwa yin aiki a Borno a wannan zamanin shi yafi komai risk ga rayuwar duk wani ma’aikaci irin sa, zuwa borno awannan lokacin tamkar sai da rai ne, ‘kalilan daga cikin ma’aikatan nasu kan ajiye aikinsu dazarar sunji cewa zasu jihar borno, masu ‘karfin imani, zuciya da tawakkali sune ke aimincewa zuwan sa6anin Abbas da dakansa ya sa aka sanya sunanshi acikin jerin list ‘din amatsayin jagoran batallion nasu, domin yana ganin zamansa a borno shi yafi masa dan yasan akoda yaushe zai kasance ne cikin shirin kota kwana tunaninsa zai kasance ne akan aikinsa akowani lokaci bazai samu lokacin tuna past dinsa ba yafi son yamanta da komai.
Daga ‘karshe Daddy yace masa
_”Nabar Fateemah agidan mijinta bai san awani hali take ciki ba, yace Abbas_ _duk lokacin daka samu lokacin zuwa Abuja ka daure ka ‘karasa ka dubo_ _min ita amma bawai nace dole sai kaje bane karka takura kanka sai in_ _kaga kana da lokaci sannan,”_
_” bakomai daddy insha Allahu zan ‘ko’karta inje da iznin Allah.”_
” _Yauwa Babana Allah ya ma albarka yabaka sa’a_ _adukkan al’amuranka “_
_”Ameen Daddy_ _nagode sosai”_
Kallon daddy yayi da kyau sannan yace
” _Inason zuwan farko da zan sakeyi awannan ‘kasar yakasance taron daurin auran_ _Babana nazo”_
Mummy najin haka ta dawo da kallonta ga Abbas din sai kuwa taga yayi shiru ya tsurawa Daddy idanu amma ga dukkan alamu hankalinsa da tunanainsa ba akan daddyn yake ba, sai daddyn ya dafa shi kafin ya dawo dai dai.
_”Tunanin me kakeyi kuma ?,ina fatan dai kaji abinda_ _nafa’da”._
_” ehh naji daddy insha Allahu zan_ _’kokarta.”_
Jinjina kai daddy yayi cikin farin jin kyakykyawar amsa daga bakin Abbas .
Abbas sai da yaga tashin jirginsu kafin yajuya ya tafi yakoma bakin aikinsa yana me alhinin rabuwa dasu tare da tunanin dalilin dayasa su irin wannan tafiyar _.(safe trip mummy and Daddy)._
Daddy ya yanke wannan shawarar ne sanadiyyar tashe-tashen hankula da suka yi yawa a jihar yobe, har ya kasance akullum ba’a kwana atashi cikin kwanciyar hankali harin kullun da kalan yanayin sa, so ‘yan uwa da dangi duk sun masa cha akan yabar garin ko dan yawan hare-haren da ake yawan kaiwa, da farko ya yi biris da maganar amma daga baya da yaga abin na neman yin yawa kawai da kansa sai ya aminche.
Daddy ya shirya musu komawa Dubai ‘din ne tun kafin ayi zancen auren Teemah, da maganar auren yataso ne kuma sai ya danne nashi ‘kudurin azuciyarsa har sai da aka kammala komai ya mi’ka Teemah gidan mijinta kafin nan.
Ciwon cikin Teemah da yamma ya ‘kara dawo mata sabo fil, gashi ita ka’dai ce agida kuma har alokacin bata sha magani ba, data rasa yanda zatayi sai kawai ta fara kuka tana mirgine-mirgine dan tayi iya ‘ko’karin ta dan ganin ta danne ciwon amma sai da ya fi ‘karfinta tafara kuka.
Acikin wannan halin Mahmud ya dawo gida ya sameta, ai kuwa jifa yayi da jakar dake hannunsa arikice ya kinkimeta yayi waje da ita be ma tsaya tambayarta dalilin kukan ba saboda yaga tana ta ri’ke cikinta tana mur’kususu, be manta ciwon datace cikinta yamata jiya cikin dare ba, shiyasa yana ganin ta awannan halin kawai ya nufi asibiti da ita.
Allah ma ya taimaka ba wani nisa sosai ne tsakaninsu da asbitin ba, dan haka be 6ata lokaci akan hanyar ba, duk dama zuwa lokacin hold-up yafara taruwa amma dai yasamu ya isa akan lokaci, kanta ko mayafi babu lokacin da suka isa asbitin, amma duk wannan be zo kan Mahmud ba shi dai damuwarsa aduba masa lafiyarta a kuma bata magani.
Cikin sa’a ma sai yasamu wani likita ya duba masa ita akan lokaci tare da yimata allurai guda biyu, cikin ikon Allah kuwa daga nan tasamu bacci ya ‘dauke ta.
Bayani likitan yamasa game da abinda ke damunta, da kuma yadda za’a magance shi cikin sau’ki, sosai Mahmud ya fahimce shi, dan shi da farko hakan ma be zo ransa ba sam, yama manta da cewar mata na irin wannan abin lokaci zuwa lokaci, dan ko data fa’da masa cewa jiya cikinta yayi ciwo ma shi zaton shi wata matsala ce daban be kawo hakan aransa, ko data masa ‘karyar tayi sallah ma yau da safe be yi wani dogon nazari akai ba dukda yana da tabbacin bata yi sallar ba.
Ya ‘dauka ko abinda tasaba yi ne kullun cikin dare shiyasa ma yau daya fita ya ‘kara zuwa wani ‘kwararren asbitin daban domin asake duba masa lafiyarsa da kyau, yafi so yaji gamsashshiyar amsa game da matsalar dake damunsa, amma ako ina baya samun amsa mai kyau su kan tabbatar masa da cewa lafiyar sa ‘qalau baya tare da wata damuwar da har zata hana shi amfanuwa, sai dai ko ‘dan abinda ba’a rasa ba, ko yau ‘din ma wasu magungunan daban aka sake rubuta masa tare da tabbatar masa abinda likitan daya ganshi da farko ya fa’da masa inda yabaro asbitin da zummar bada himma ga shan maganin ko dan matsalar da matarsa ke ciki domin kar ya kaita ma’kura, shikan shi yana so yaji kansa amatsayin cikakakken namiji yanaso mazantakar sa ta dawo kamar da, dukda ma acikin jikinsa baya ji kamar yana tare da wata matsala ajikinsa, jinsa yake garau, amma me yasa ba ze iya biya wa matarsa bu’katar ta ba bayan likitoci ma sun shaida cewa lafiyarsa ‘kalau?
Wannan abin na ‘daure masa kai ba ‘dan ka’dan ba.
Baccin kimanin mintina talatin Teemah tayi sai ta farka, Mahmud tagani zaune agefen gadon da take kwance ya ‘kura wa ‘karfen gadon idanu, sai da ta juya ta kalli ‘karfen sannan ta dawo da kallonta gareshi, _”Yayah “_! tace da dasashshiyar siririyar muryarta da bata gama warwarewa daga baccin da tashi yanzun ba.
Mahmud be ji ta ba domin be amsa sunansa data ambata ba kamar yadda be kawar da idanunsa daga inda yake kalla tun ‘dazun ba.
Ganin haka yasa Teemah ta yun’kura ta tashi ahankali ta kai hannunta ta dafa kafa’darsa tare da sake ‘kiran sunansa, juyowa yayi ya kalle ta take sai ya ‘ka’kalo murmushi tare da dawo da dukkan hankalinsa gareta
_” kin_ _tashi?_
Ya tambayeta yana ‘ko’karin kamo hannunta dake kan kafa’darsa.
Story continues below

Da kai ta amsa masa alamar
” _ehh_ “
” _Ya jikin naki_ ?
Ya sake tambayarta da kulawa.
Sai ta bashi amsa da fa’din
” _na daina jin komai_ _yanzu”_
Fa’da’da murmushinsa yayi tare sa fa’din
” _Masha Allah, ubangiji Allah ya ‘kara sau’ki, zaki iya tafiya kuwa ko de na ‘dauke ki?_
yayi maganar yana kallon cikin idanunta.
_” a’a zan iya tafiya_ _ma da kaina_ ”
Teemah tabashi amsa tare da yun’kurin sau’kowa daga gadon, sai de bata kaiga ajiye ‘kafafunta a’kasan ba taga gurin wayam ba alamar takalmin ta, sai ta juyo ta kalleshi tace. ” _Yayah takalmi_ !
Mahmud kai ya dafe tare da fa’din
” _oups, ni ai duk ma na manta, ko tunawa banyi da batamun takalmanba garin_ _sauri, kin rikitani sosai Fateemah har ma bansan inda_ _hankalina ya tafi_ _ba”_
Murmushi tayi masa kawai dan bata san mezatace dashi ba alokacin.
Tambayarta ya sakeyi da fa’din
_” yanzu ya za’ayi ne_ _toh ?_
sai tace yakoma gida ya ‘dauko mata kawai sai yazo su tafi.
Ido yazaro waje yace
” _kina nufin wai har gida zan koma in kuma sake dawowa nan?_
Da kai tabashi amsa alamar _ehh_ , jijjiga kai Mahmud yayi tare da fa’din se kace bani da hannaye, yana maganaar yana ‘ko’karin cicci6anta, be zame ko’ina ba, sai inda ya faka motarsa, daya ke already likita yariga yagama dasu yagama sallamarsu
,dama Mahmud zaman jiran farkawanta kawai yake su wuche gida.
Dakansa yasata acikin motan sannan yazaga ‘dayan 6angaren yashiga.
Tun kan ya ‘karasa daidai ta zamansa tafara fa’din
_”alluran da wannan likin yamin fah akwai zafi sosai “_ tayi maganar tana kaiwa hannuta wurin da aka mata alluran tare da langa6ar da kanta .
_”Eyyah sorry , very soon zaki daina jin zafin ai”._
_”Ni de karka ‘kara_ _kawoni gurin nan Yayah ……….!_
_”Bana ma fatan ‘ki ‘kara yin ciwon har_ _abada”!_
Ya tari bakin ta da fa’din haka.
Sai itama tace _”Ameen Yayah, Allah mutumin mugune, ai har nayi niyyan cizon shi danaga ya ‘dauko allura kawai de_ _nabarshi ne yamin dan yanda cikina kemin zafi sosai, amma fah har guda biyu yamin dan mugunta”_
Murmushi yayi mata kawai tare da shafo fuskanta sannan yace ” _Alluran ai shine daidai baki ga acikin ‘kan’kanin lokaci kin samu lafiya ba”_ .
Dai-dai wani babban store Teemah tace ya tsaya tana son ta siyi abu, kallonta Mahmud yayi da sauri yace _” ina fatan de ba dangin su choculates bane, dan doctor yace ki rage shan su saboda ciwon cikin nan naki”._
_” ah ah Yayah basu bane wani abu daban nake so”_
Sai da yayi parking agefe kafin yace ta fa’da toh yaje yakawo mata yanzu sai su wuce gida dawuri ko dan tasamu ma ta’dan huta gashi maghrib takusa.
Teemah kuwa cikin shagwa6a tace masa.
_”Ni fa zan sayo dakaina “_
Kwafa yai yana kallon ta da mamaki, ganin ta’ki ta fa’da masa abinda take so ‘din sai yace mata _” ba_ _takalmi ba mayafin zakije “_
Jijjiga masa kai tayi tare da fa’din masa yanda za’ayi.
Tana gama masa bayanin yafice amotar batare da yayi magana ba.
Minti goma me kyau be yi ba yadawo da leda ya mi’ka mata, kar6a tayi ta ciro takalmin ta sanya a’kafarta dayake ya san size ‘din ‘kafar ma sai ba ‘a samu wani kuskure ba, ‘dan ‘karamin mayafin dake cikin ledar takuma cirowa ta yafa shi akanta.
Story continues below

” _Muje toh_” tafa’da tare da bu’de bangaren data ke zaune, shima fita yayi ya bi bayanta bayan ya dannawa motar lock.
Dakanta ta ‘debi duk abinda takeso Mahmud na gefe yana kallonta sai da aka zo wajen biyan ku’di kafin ya ga abubuwan da ta kwaso, harara ya doka mata sai ta kauda kai tare da yin fi’ki-fi’ki da idanu, tasan daman ai hakan sai yafaru shiyasa ma tace da kanta zata shigo dan tasan inshi ‘din ka’dai ne yazo ‘kin siya mata zaiyi.
Be kulata ba yabiya ku’din tare da ‘daukan ledan itama sai bishi abaya suka fito suka koma mota, har suka isa gida be ‘kara yi mata magana ba.
Data ga haka sai ta dawo kusa dashi lokacin yana zaune akan cough a palourn su, _” Yayah_ _inkawo maka ruwa kasha_ ?
Be yi magana ba sai ya jawo ta zuwa gabanshi ya nuna ta yatsa yace _”wato_ _ke ba kya ji_ _ko?,_ _ciwon cikin be ishe ki ba ko”_
Hannayenta ta ‘da go tarufe gefe da gefen fuskarta dan zaton ta marin ta zaiyi yanda taga yake maganar sosai yaso ya firgita ta.
Ledar ya sa hannu ya janyo ya ajiye agabanta yace
_” oyah fara ciro su ‘daya bayan ‘daya kina min bayanin su”_
Haka ta yi kamar yanda ya bu’kata amma sai da ta ciro su pads ‘din data siya da farko ta ajiye ta ciro wani turare ma ta ajiye sannan ahankali tana kallon fuskarsa tafara ciro dangin choculate ‘din data ta jida kusan kala hu’du.
Harara ya doka mata yakai hannu zai kamo kunnanta take tayi saurin matsawa baya tace _” Allah Yayah sunmin kyau ne shiyasa fah na ‘dauko, kuma fah sabon product_ _ne baka ta6a kawo min irinsu ba shiyasa ne ‘debo, bama yanzu_ _zan sha ba sai na sami sau’ki”_
_”Waye yace miki sabo ne “_ ?
Yafa’da atsawace
Sai Teemah tace ” _ni ai ban ta6a gani_ _bane”_
Mahmud ‘kyaleta kawai yayi ya tashi ya wuche ciki domin ya watsa ruwa ajikinsa dan yasan inya biye wa Fateemah har ciwon kai sai ta sashi abanza.
*Bayan kwana biyu*
Mahmud sosai ya dage yana kula da shan magungunan sa akan lokaci saboda shi kansa ya ‘kagu yaji shi cikin ‘koshin lafiya, hakan yasa sam baya wasa da lokutan shan maganinsa ko agida ko a office baya ta6a sa6a lokaci.
Acikin kwanakin kuma Anty Chideh ta ziyarci Teemah inda tasameta ita ka’dai agida saboda Mahmud na office ita ka’daice gida.
Alokacin ma Teemah na kwance tana ta trying layin su Mummy taji baya shiga abin sosai yadameta ya ‘daure mata kai, dan ko no. ‘din Daddyn ta ma baya shiga a’yan kwanakin, kuma kullum haka takeji in ta ‘kira su Hannah da Ummah kuma sai suce mata wai sede in matsalar network ne amma su kam wai suna ‘dan yawan gaisawa da mummyn ko basu kira ba ita tana ‘kiran Ummah su gaisa.
Mamaki yakan cika wa Teemah zuciya, tarasa meyasa se da ita hakan zai faru, takan yawaita tambayar kanta _”toh me yasa Mummy zata ‘kira kowa amma ni ta manta dani, ko dama in akayiwa mutun aure shikenan kowa agidansu mantawa yake da shi?…….._
Tana cikin wannan halin taji door bell na kara, tsaki taja ta share kawai, sai da akayi tayi kusan sau uku kafin azuciye ta tashi taje ta bu’de sai taga wannan ‘kawar Antyn ce tsaye ita ka’dai, dariyar ya’ke ta ‘dan saki tare yi mata maraba da zuwa sannan ta bata hanya ta shigo ciki.
Anty Chideh na gaba Teemah na biye da ita abaya, sai ta ta6e baki tare da ‘karewa shigar Anty Chidehn kallo.
Sanye take da wani ba’kin mini skirt wanda be ko rufe gwiwarta ba hakan ma da ‘dan tsago ka’dan daga baya wanda hakan ya taimaka wurin ganin fararen cinyoyinta afili, sai wata riga wanda ta wadaci jikinta domin bata kamata sosai ba, yadin rigar kamar yadin material ne da zanen ‘kananun flowers ja, kanta kuwa yasha fixing na ba’kin attachment irin wanda kana gani kasan hula ne ba gashinta bane ba.
Duk cikin ‘yan da’ki’ku tayi wannan lissafin sai ta ta6e baki tare da ‘fa’din _” arnanci de beyi ba, har yaushe zaka rin’ka yawo da_ _irin wannan ‘dan iskan kayan acikin gari kamar baka da mafa’di.”_
Afili kuwa sai ta saki fuskarta tare da yiwa Antyn barka da zuwa, bata zauna ba sai data kawo mata abinsha Kafin nan ta zauna nesa da Anty Chidehn ta gaidata.
Cikin fara’ah ta amsa mata sannan ta tambayeta ya zaman gida Teemah ta amsa da ” _lafiya_ ‘ _kalau”_
Sake tambayarta tayi wai ina Mahmud sai *Teemah* tace ” _ya_ _tafi office”_
Jinjina kai tayi tana murmushi, ‘yar hira ka’dan taja Teemah dashi ganin Teemah bata saki jiki sosai da ita ba yasa bata da’de ba ta mi’ke da niyar zata tafi Teemah ma mi’kewa tayi tsaye kamar yanda Anty Chidehn tayi.
Sai alokacin data mi’ke sannan ta lura da irin she’danin kallon da Anty Chideh ke binta dashi musamman ma ‘kirjinta daya kasance ana ‘dan ganin kusan rabinsa awaje dan wata armless red top ne ajikin ta mai bu’dadden round neck wanda ya ‘kara bayyanar da haske fatarta afili, ba karamin kar6an jikinta rigar tayi ba, ta sanya shi da wani jeans trouser daya kama jikinta sosai, gashi kanta ko ‘dan kwali babu gashin kawai takama da wani ‘karamin jan ribbom ba mayafi balle tacire ta lullu 6a dashi.
Afakaice ta samu taja rigar sama yarufe mata ‘kirjin sannan tama ta rakiya iya bakin parlourn tadawo ciki tare da jan wani uban tsaki.
Wayarta ta ‘daga ta buga shi akan kujera kamar shine Anty Chiddyn afili tace
” _Duk sharrin wayar nanne, in bahaka da nasan bazan manta ‘dauko mayafi ba balle har matar nan ta ganni ahaka ba, kamar mayya sai ta ta kallon mutum tana_ _murmushi_ .”
Washe gari ma haka Anty Chideh tazo wurin Teemah bayan Mahmud yatafi office.
Yau ma daurewa Teemah tayi ta kar6eta hannu bibbiyu ba yabo ba fallasa ta ‘dan saki fuskarta, sai de yau ‘din Anty Chiddy cewa tayi da Teemah wai zata na zuwa kullum tana tayata hira tunda ita ka’dai take wuni agida, Teemah murmushi kawai tamata batare da ta bata kykakkyawar amsa ba, dazata tafi yauma Teemah iya ‘kofar parlour tayi mata rakiya amma duk da haka Anty Chiddy kasa ha’kuri tayi har se data ‘dago hannu ta shafi fuskar Teemah tare da fa’din _” I really love u”_ ‘kasa-‘kasa tayi maganar, Teemah kuwa rintse idanu tayi cikin takaici, sannan ta 6ata ranta afili hatta Anty Chiddy ta lura da hakan amma itan kuma sai tayi murmushi ta ‘kara ‘dago hannu da niyyar shafo la66an Teemahn daya ke matu’kar ‘dauke mata hankali a kowani lokaci sai Teemah tayi baya da sauri, Anty Chiddy ganin hakan yasa kawai tajuya ta tafi aranta tana kissima ranar da aka ce tasamu wannan yarinyar ahannu, ga dukkan alamu she is hot, tace ha’kurinta yakusan ‘karewa akan yarinyar bazata iya jira har se lokacin da sukayi sabo da ita sosai ba sannan tasameta kamar yadda mum Mahmud ta ce da ita, afa’dar ta in har tace hakan zatayi zuciyarta ze kusan bugawa ne abanza, tace gara taje tasamu mum Mahmud su sake shawara dan she is in need of her, she so much love the girl yadda ita kanta batasan yaushe hakan yafaru ba, bata da buri ayanzu daya wuce taga ta samu yarinyar a hannu.
Teemah kan takaicinta na yau na musamman ne dan ita ka’dai tasan yadda takeji azuciyarta , dama akwai damuwar rashin samun iyayenta da bata yi awaya daya matu’kar tsaya mata azuci, ko da ta yiwa Mahmud maganar kuma shima sai ya nuna mata rashin damuwarsa akan hakan, sai ma ya tabbatar mata da matsalar network ne kawai bakomai ba, tana cikin wannan takaicin kuma Anty Chiddy tazo tasake jagula mata lissafi, ita ka’dai sai zuba tsaki takeyi, haushin Anty Chideh da haushin abinda tamata duk yabi yacika mata zuciyarta, wani mugun ‘daci takeji aranta, taci alwashin sanar da Mahmud damunta da matar nan takeyi dan ita baso takeyi ba gara ayi mata magana ta daina zuwa gidannan tunda ita bata san girma da arzi’ki ba.
Sai akayi rashin sa’a kuma ranar Mahmud be samu yadawo gida da wuri ba, sanadiyar aiki da ya musu yawa a office, hakan yasa be shigo gidan nasa ba sai kusan 9:01pm ya dawo, alokacin ma Teemah harta fara yin bacci.
Koda yadawo a parlour yasameta kwance tana bacci, da shigowarsa kuwa ta ta shi ta zauna ta na mar barka da isowa.
Zama yayi agefenta tare da sakin ajiyan zuciya ga dukkan alamu amatu’kar gakiye yake, Teemah ma bata bu’katan wani ‘karin bayani saboda tun da yamma ya ‘kirata yayi mata bayanin abinda ya ri’ke shi a office ‘din, awa biyu da suka wuce ma ya ‘kara ‘kiranta yaji lafiyarta hakan yasa bata wani damu ba yin daren nasa, duk dama tana ‘dan jin tsoro amma zuwa yanzu dolenta ta’dan fara sabawa da zama ita ka’dai agida.
Ruwa Mahmud yaje ya watso ya dawo parlourn da niyyar yi mata magana akan ta tashi ta koma bedroom ta kwanta, sai yasameta ma harta koma bacci abinta, kyaleta yayi dan shi be fiya son tada mutun ba idan yana bacci dan haka sai yaje shima yakwanta aparlourn akan doguwar kujera bayan yagyara mata nata kwanciyar tare da gabatar da duk wani al’adunsa daya saba yi kafin yayi bacci.
Story continues below

Kamar kullun yauma yana kwanciya bacci me shegen nauyi ya ‘dauke shi da be san inda yasamota ba, badan ma ya kasance yana da iyali ba, da bazai ta6a sanin cewa yana irin wannan baccin ba saboda ada idan yariga yayi bacci toh yatafi kenan domin shi bashi da irin al’dun tashi cikin daren nan, ko nafila zaiyi yakanyi ne kafin ya kwanta bacci sai de hakan.baya hana shi sanin duk lokacin da ze juya cikin baccin ko kuma yaji motsi ya farka, amma yanzu sam baya ‘kara sanin ina kansa yake da zarar ya ‘dora jikinsa a makwanci, kasancewar yana da Teemah akusa dashi ne tasa yagane mummunar lalurar daya ke tare da ita da be san tsawon yaushe yafara ta ba, abakinta yake fahimtar wannan sabuwar lalurar data sameshi, mamaki yake yi idan gari ya waye yaga ta canja wurin kwanciya ko kuma yaga ta bar ‘dakin ma gaba ‘daya.
Sau tari yakan ji kunyar kansa da kansa idan tafara yi masa mitan ya’ki yi mata abu kaza da dare ko ya’ki yi mata kaza sai yasaki baki kawai yana kallonta, akullum so yake ya nemo mafitar wannan abu amma ya rasa, bayan yasan sarai shi bahaka yake ba.
Da gari yawaye yau kam da sauri-sauri yayi kominsa yagama, ya fita daga gidan tun 7:o clock dan baya son Teemah ta samu chance ‘din yi masa complain akan wani abu daya faru cikin dare domin hakan na matu’kar sanyaya masa jiki da zuciya, be san wani irin ha’kuri ze jero mata ba, shiyasa yafice da wur wuri batare da ya bata wani 6ari daga cikin lokacinsa dazata yi anfani dashi wurin kawo ‘kararsa wa kansa ba, toh wani irin hukunci yakamata inyiwa kaina tunda kullum nine me yin laifin kuma ni ake kawo wa ‘kara, Mahmud tun yanzu su fara ‘yar hakan ba, tun ba’a je ko’ina ba su fara wasan ‘yar 6uya da ita ba amma gani yake yi inbahakan yayi mata toh akullum kunyarsa gareta ‘kara ‘karfi zai rin’ka yi, saboda bashida wata mafita, sai de akullun yana ro’kon Allah ya ye masa wannan matsalolin da suka kunnowa rayuwarsa wuta suke son su hanashi sakewa da walwala shida iyalinsa, dan zuwa yanzu abubuwan sun fara zarce tunaninsa dole ne ya nemi mafita, mafitar dazata 6ille musu gaba ‘daya batare da an shiga hakkin juna ba, aransa ya ayyanacewa idan yadawo gida ayau duk zai zauna su fahimci juna da ita, ze yi mata bayanin matsalolin daya fuskanci yana tare dasu in yaso ita tasani, saboda ta daina zarginsa da yawan shareta dayakeyi cikin dare wata’kilha ma inta fara saka shi acikin addu’arta sai yaga yasamu sassauci.
Da burin hakan ya’kara office ‘din su, yana zuwa kuwa yaga aiyuka sun taru masa dayawa saboda rashin kula dasu sosai da baya yi acikin ‘yan kwanakin.
Rarrabasu yayi wa’danda ze sa hannu da wa’dan da ze tura su ne zuwa wani guri da kuma wa’dan da zai ‘dora a Internet.
Signing ‘din yafara sai de be yi nisa da yi ba wauarsa tafara ‘kara , ajiye biron dake hannunsa yayi sannan ya ‘dauki ‘kiran, Abbas ne ya ‘kira shi suka gaisa atakaice dashi ya tambayi lafiyar kowa, sannan ya ‘kara da fa’din suk lokacin da yasamu lokaci da iznin Allah ze ziyarce su.
Sosai Mahmud yaji da’din furucin Abbas ‘din har ma yakasa 6oye murnarsa sai da bayyana ta har Abbas yagane.
Mahmud yaso yayiwa Abbas maganar abinda ke damunsa amma daya tuna cewa sirrinsa ne, sirrin auren sa kuma Abbas tamkar wa yake agurin Fateemah so da kunya ace yasana sirrin zaman aurenat irin wanann dan haka sai yayi shiru kawai yayi tagumin yana tunanai bayana sun gama waya da Abbas.
Fitar Mahmud daga gida agag gaucen ne ya dakatar da Teemah ga fa’da masa abinda tayi niyyan sanar da shi, amma duk da haka bata ha’kura ba dan har ga Allah ita bata son damuwa, matar nan kuwa tafara shiga rayuwarta ta inda bata so, so take ayi musu tsakani kowa yayi rayuwarsa yadda yakeso.
Wani abokin Mahmud a office ‘dinsu ne wanda yakasance mataimaki ne ga Mahmud ‘din mai suna Umar yashigo yasame shi da tarin files agabanshi amma yayi zugum yana aikin tunani.
Umar ‘ dan asalin garin katsina ne aiki yakawo shi nan garin Lagos har suka ha’du da Mahmud kuma sukayi sabo da juna dai-dai gwargwado, domin har damaturu akaje dashi wurin ‘daurin auren Mahmud.
Story continues below

Umar yanada mata har da ‘yaransa guda biyu mace da namiji inda yake tare su anan garin Lagos ‘din.
Ya nemi jin asalin meke damun Mahmud ne saboda yawan samunsa cikin damuwa da yakeyi a office musamman ma dayake shine mataimaki agare shi so yakan sha ganinsa cikin halin tunani da damuwa.
Bayan ‘dan nazari da Mahmud yayi sai yaga dacewar sanar dashi matsalar daya ke ciki wala Allah ko ze samu kyakkyawan shawaran da zata anfane shi.
Umar kansa dayaji matsalar dake damun Mahmud ‘din kansa sai da ya ‘daure domin hakan be fiya faruwa ga mutane ba, sai dai ko in da akwai wata matsalar ta daban wanda takasance sirri ne 6oyayyiya.
Jin dayayi Mahmud yace masa ya ziyarci likitoci a’kalla kusan guda uku amma duk furucin bakinsu iri ‘dayace kamar sun ha’da baki sukance azahiri baya tare da matsalar komai, sai yace da Mahmud
toh inkuwa hakane sai ko aljanu ke son hana ka sakewa, sai de insune ke son shiga rayuwarka inbahaka ba kuwa samo dalilin ze yi matu’kar wahala tun da shikanshi Mahmud ‘din ya shaida akan cewa bahaka yake ba ada, yasan kansa da yawan bu’katar mace amma yanzu rabonshi da ya tsinci kansa a irin wancen halin ma har ya manta, sosai Umar yake jinjina lamarin tare da tausaya wa abokin nasa.
Daga ‘karshe shawara Umar yabashi akan cewa matu’kar yanason zama da matarshi toh dolene ya nemi mafita, mafita wacce zata 6ille musu.
Mafita a garesu kuwa za6i biyu ne acikinsu kuwa dole sai anyi ‘daya domin zama haka ba zai ta6a haifar musu ‘da mai ido ba babu anfani sam, dan haka ya za6a ko ya saki matarsa taje ta auri wani namijin lafiyayye wanda ze iya da bu’katun ta, ko kuma yatashi tsaye ya shiga neman magani, ma’ana magani ingantacce wanda musulunci ya yarje mana muyi anfani dashi, Umar yace ” _a dun’kule dole ne ka nemi sanannun malamai abokina, kuma ashawarce inaga yakamata iyayenka su san halin da kake ciki tun yanzun ko dan gudun abinda zai je yadawo duk dama ba’a fatan komai marar kyau amma dai ka sanar dasu wata’kila za’a sami wata mafita daga ‘bangarensu”_
Sosai Mahmud ya gamsu da bayanan da Umar ya masa daga ‘karshe godiya yai binsa dashi domin Umar ya tunasar dashi abinda yakasa tunawa da kansa, kalaman Umar ‘din sosai sukayi tasiri azuciyar Mahmud, domin shi hankalinsa be je ga neman magani ta wannan 6angaren ba face da Umar ya farkar dashi hakan, yace zasu sake zama da Umar ‘din insha Allahu.
*****
Aranar da Teemah tacika kwana hu’du tana fashin sallah kuma aranar tayi wankan tsarki tacigaba da ibadar ta kamar kowa.
Allah cikin ikonsa kuwa adaren ranar kusan ‘karfe biyu kamar an tsikareta ta tashi cikin wani matsanancin sha’awa idanunta har basu iya bu’du wa gaba ‘daya ga marar da take jinsa a dunkule guri guda.
‘Yar rigar baccin dake jikinta ta fincike shi tayi jifa dashi sannan ta cigaba da juye-juyenta cikin matsancin damuwa, ahankali ta jawo jikinta ta dawo kusa da Mahmud tashige cikin jikinsa amma tamkar gawa be san tanayi ba, haka tayi ta lalu6an jikinsa, amma Mahmud kam ko motsin kirki beyi ba, daga kuka tafara abin tausayi tun tana yi na zallan hawaye har tadawo yi da sheshsheka, da kukan ta kwana ajikin sa har zuwa sallar asubah.
Mahmud yarigata farkawa dan haka yana tashi sai ya ganta ta cusu acikin jikinsa kuma har alokacin bata daina ajiyan zuciyan kukan da tayi cikin dare ba, Mahmud dafe kai yayi yana jin ba bu da’di aransa, dan sosai yarinyar take bashi tausayi musamman idan yaga tashiga irin wannan halin, danma yaga ta ‘dan kwana biyu bata yi ba, acikin kwanakin ko ya tashi baya ganin alamun sauyi atattare da ita, har yana jin da’di sai kuma kwatsam yau abin yasake tashi mata.
Ashe muguwar sha’awar da ke damun Teemah yana bin yanayinta, domin lokacin data ke cikin rashin tsarki ko ka’dan sha’awar bata tashi mata ba, ko dan lokacin ko tayi bazata samu biyan bu’kata bane oho, sai yanzu cikin ikon Allah gashi tana yin tsarki sai ya tashi mata.
Ahankali Mahmud ya janye jikinsa daga nata sannan ya janyo mayafi ya lullu6a mata ganin jikinta bakaya.
Zuciyarsa cike da tausayinta har ya gabatar da sallarsa, bayan yayi addu’o’i da dama yashafa ne sai ya tasheta ahankali cikin sanyin jiki.
Ahankali ta tashi tare da jero salati azuciyarta kana addu’ar tashi daga bacci ya biyo baya.
Kwata-kwata ta manta da cewa babu kaya ajikinta har sai data mi’ke zaune, ganin irin kallon da Mahmud yake binta dashi ne yasata ta kalli jikin nata itama.
Da sauri ta kai hannu ta janyo mayafin ta kare jikinta dashi Mahmud kuwa sai ya yi ‘kasa da kansa cikin kunya.
Ehh kunya mana tunda shi be yi mata anfani alokacin data ke bu’kata ba yanzu kuma yazo yana bin jikinta da kallo.
Teemah sai da ta rufe jikin kafin tafara recalling abinda yafaru jiya da da dare, tsaki taja acikin ranta, zuwa yanzun abin Yah Mahmud ‘din yafara bata haushi, dan me yasa yake share ta kullum bayan cikinta sai ya tadata da ciwo acikin daren meyasa sai ‘kyaleta tayi ta fama bazai ko kawo mata magani ba, gashi har garin ciwon cikin ta cire rigarta daga jikinta bata sani ba.
Duk wannan abinda da takeyi ‘din ita aganinta ciwon ciki ne kawai da ‘kullewar mara ke damunta, domin ita bata san wani abu wai shi sha’awah ba, ko lalu6an jikinsa datakeyi tana yine ayanda zuciyarta ta raya mata kuma take jin tana matu’kar son haka koma fiye, har ma takejin kamar zata samu sassauci idan Mahmud ma yamata irin yadda takeji tanaso ‘din, bazata iya fa’dan asalin meke damunta ba alokacin domin wanda takeji azahiri shine yafi damunta, sai de da ace zata samu kamar yadda jikin nata ke so bazata ta6a ‘ki ba sai ma ta’kara kaimi wajen ganin bu’katar tata ta biya.
Da mayafin ta tashi ta wuche taje ta ‘dauko rigarta sannan sai da ta sa shi ajikinta kafin tacire mayafin ta na’de shi ta ajiye, ko magana.bata masa tayi wuche warta toilet domin yanzu haushin Yah Mahmud take ji aranta.
Shima Mahmud shawara yayi da zuciyarsa ganin kamar yafara kaita ma’kura tunda gashi tafara canja masa fuska dan harta zo ta idar da sallahn ta bata yi masa magana ba, sai da ta idar tagama addu’o’inta kafin ta ce masa ” _ina kwana_ ” atakaice, shima.da ” _lafiya_” kawai ya masa mata yana fargabar sake yi mata magana domin be san meke cikin zuciyarta ba, yana nan azaune agurin yaga ta wuce parlour tabarshi a’dakin shika ‘dai.
Dafe kai yayi yana.tausaya wa halin da rayuwa take shirin jefa su aciki, take agurin ya yanke shawarar zama su da ita su fahimci, domin tasan halin da yake ciki tasan cewa ba laifinsa bane duk abninda ke faruwa wala Allah ko zata rage haushin sa data ke ji ta fuskoki da dama, inyaso sai su cigaba da addu’ah tare ko Allah zai tausaya wa rayuwarsu ya kawo masa sau’ki, amma sai ya dawo daga office sannan suyi maganar yamzu kam binta zai yi ayanda take so har yasamu yatafi.
11:30am su Anty su ka shigo gidan lokacin tana kan waya da Ummah tana sake yi mata complain na rashin samun wayar Mummy da Daddyn ta da batayi kamar zatayi kuka take maganar, Ummah kuwa sai ha’kuri take ta bata tare da fa’din ta bari idan Daddyn su yadawo zata fa’da sai yaje har damaturun yagani ko lafiya…..
Suna cikin yin wayar taji ‘karar door bell, ‘kin kulawa tayi aranta ta ayyana cewa wannan jara babbiyar matar ne yau kam bazan bu’de ba.
Ci gaba tayi da sauraran Ummah har suka gama wayar sannan taci gaba da buga game ‘din Candy crush da wayar.
Can taji shiru door bell ya daina ya ‘kara afili ta furta ” _yafi miki._ “
Befi 2hrs ba taji ana sake danna bell ‘din sai taja uban tsaki tare da tashi ta le’ka tajikin ‘kofar,Anty ta hango tsaye ta qajen da gudu takoma ‘daki ta burmo hijab akan kayan jikinta sannan ta tazo ta bu’de ‘kofar.
Anty (mahaifiyar Mahmud) ce agaba dan haka ita ta far kutso kanta ciki, bayanta kuwa Anty Chiddy ce data bi tagama rikice wa da tunanin abinda yasamu Teemah , dan dataga ba’a bu’de mata ‘kofar ba ‘dazu tana barin nan gidan Anty direct ta nufa tayi mata bayanin abinda ke faruwa arikice don ita zatonta ma ko wani abu ne yasamu yarinyar shiyasa, amma Anty sai bata wani damu ba tace iskanci ne kawai ke damunta ba wani abu ba duk da haka Anty Chiddy sai da ta tattago ta suka zo tare.
Anty na shigowa tafara bin Teemah da wata muguwar harara tare da ta6e baki gefe, Teemahn na musu barka da zuwa ma amma Anty ko kulawa batayi ba tace da Teemahn” _hamsha’kiya amaryar Mahmud….., ashe kina ciki?_
da wani dirty look ta ha’da tayi maganar tata.
Jikin Teemah sosai yayi sanyi da yanayin Antyn amma duk da haka sai ta daure ranta ta ‘daga mata kai cikin sanyi tace
” _ehh Anty, ina_ _nan”_
Muryarta har crashing yake lokacin datayi maganar .
Anty sai ta ta6e baki ta juya ta kalli ‘kawarta tare da nuna wa Teemahn ita tace
_” wace_ _wannan awajena_ ?
_” she is your friend “_ Teemah ta bata amsa da rawar baki.
” _me na fa’da miki game da ita_ ?
Anty tasake dokawa Teemah wata tambayar tare da kure ta da idanu.
Teemah kuwa yanzun sai tayi shiru ta sunkuyar da kanta ‘kasa hannayenta sar’ke cikin junansu batayi magana ba. Anty kuwa haushi hakan yabata dan haka
sai ta daka mata wani uban tsawa akanta daya matu’kar firgita Teemah sannan ta sake maimata tambayar tata ga Teenma cikin masifa.
Take idanun Teemah suka fara tara ‘kwalla jikinta yafara rawa.
Anty kuwa sai ta fara kewayata tana ‘kara nazarin Teemahn sannan ta wuce taje ta zauna akan cushion ta ‘dora ‘kafa ‘daya kan ‘daya kamar wata me fa’da aji..
_” Zo nan ke !_
Tasake dakawa Teemahn tsawa hatta ‘kawarta se data juya ta kalleta, Teemah kuwa se ta juya tatafi ahankali ta zube akan gwiwoyinta ta zauna, ta sake yin ‘kasa da kanta, tsoron Antyn yagama cika mata zuciya ayau ‘din dan bata ta’ba sanin cewa ‘dayan side ‘din Anty haka yake ba, sosai takejin wani iri gameda hakan duk da ma bata san taka mamman abinda ta mata ba ko kuma abinda ke faruwa ba bata san wani laifi tayiwa Antyn ba, sai de tana kyautata zaton wannan arniyar ce takai ‘karanta gurinta.
Anty Chiddu ma takowa tayi tazo ta zauna gefe da Anty tana idanunta akan Teemah.
Tana cikin tunanin ta tsinkayo muryar Anty na fa’din
” _har ke kin isa kinyi girman da zaki ja da maganata ko?, toh bari kiji uwar data haife ki ma bata isa tamin gadara ba domin ba’a bakin komai take wurina ba balle kuma ke……… kuma kisani baki isa kice zaki hana duk wanda yayi ra’ayin shiga gidan nan shigansa ba saboda baki da wannan damar, kinyi ka’dan, wannan da kike gani tamkar nice…….tamkar mahaifiyar Mahmud take……inajin da kaina na tako musamman nazo nayi miki bayani_ _akanta shine kuma zaki ce zaki hanata shiga gidan_ _nan?…….,_
Story continues below

‘Kwafah tayi tare da jijjiga kanta sannan tacigaba da fa’din
” _daga yau baki da wannan ikon Fateeema, banyarda ba_ _kuma ban amince ba ma daga yanzu a’kara saka lock a’kofar nan saboda akowani_ _lokaci zaki iya ganin ba’ki wa’danda zasu zo musamman saboda ke, sannan kisan wani abu guda karki ga tun_ _zuwanki ban nuna miki asalin ko wacece ni ba ki saki ranki cewar kinsanu wurin zama harma_ _hakan yasaki za’kewa ki zarce huruminki, tace bakomai ne yasani yin sanyi ba face wani gagarumin_ _tanadi da na miki me ban mamaki kuma inafatan kin shirya tar6arsa_ _kamar yanda kika shiryawa zama amatsayin matar Mahmud”_
Ta ‘karashe da wata muguwar murmushi tare da mi’kawa Anty Chiddy hannunta ‘daya alamun kar6ar abu.
Teemah kam kanta na ‘kasa inbanda kuka babu abinda takeyi, ita duk ma ba wannan surutan Antyn bane suka dameta, tunaninta nacan wurin iyayenta data rasa samun ji daga garesu ta kowani kafa.
Anty Chiddy
tablet ‘din dake hannunta ta mi’ka wa Anty.
Fuskar Anty cike da murmushi ta ke duban cikin tablet ‘din, wasu ‘yan shige-shigen ta ‘danyi sannan ta ‘dago ta mi’kawa Teemah tablet ‘din tare da fa’din.
” _kalli kigani amaryar Mahmud…………. wannan shine_ _babban tukuicinki na amincewa auran ‘dana ‘daya tal danake_ _dashi…………….wato_ _Mahmud”_
Hannun Teemah na rawa ta’dago ta
Kar6i Tablet ‘din, bata san menene ba, bata san me zata gani ba amma kawai sai ta tsinci zuciyarta da harbawa da ‘karfin gaske.
Ahankali ta sau’ke idanunta akan wayar abinda idanunta ya sau’ka akai ne ya matu’kar gigita numfashi da tunaninta, take sai ta rintse idanu wasu zafafan hawaye na rashin gata suka gangaro mata take sai ta fara jero istighfari azuciyarta na kallon abinda bata ta6a tunanin wanzuwarsa ba.
Dukkansu suka dawo saitin kanta suka tsaye dan mugunta Anty ta daka mata wata uwar tsawa akan wai dole ta bu’de idanunta ta kalla da kyau saboda so ake ta koya, daga yau akai zata fara practice akai.”
Teemah hawaye kawai take fitarwa jikinta na mugun rawa tsoron Anty na ‘kara ‘karfafa azuciyarta badan haka ba da babu abinda zai sa ta bu’de idanun nata akaro na biyu, ahakan ta bu’de idanun ta sau’ke su akan Fuskar tablet ‘din, ganin yanda wata baturiyar mata ta kwanta tsirara ta bu’de ‘kafafunta wa wata wacce itan ma takasance irin ta domin dukkansu babu komai a jikinsu tana sucking mata hq ita kuma sai nishi takeyi tare da shafa kan lespartner ‘din nata ga dukkan alamu ba ‘karamin enjoying take yi ba, abin ba kyan gani ko ka’dan.
Duk cikin 3 to 4 seconds tayi wannan nazarin tana gamawa kuwa ta kife tablet ‘din tare da sakin wasu sabbin zafafan hawaye helplessly idanunta a rintse.
Bazata iya kallon wannan abin ‘kya mar ba koka’dan koda kuwa Anty kasheta zatayi bazata ta6a iya ‘kara gani ba, abin har tashin zuciya yake sata ayanzun jitake yi kamar zatayi amai.
Da rawar murya tace _”Anty dan Allah… kiyi ha’kuri……. wal..lahi bazan iya kallon wannan abin….ba kuma babu kyau ma mu….tun yaga tsiraicin wani Allah ya haramta mana kuma ya tanadar da azaba mai ra’da’di ga me aikatawa”._
Dariya Anty tasake na ban maki tana tafa hannaye tace
_” Sannu Alshekiya uztaziya Fateemah……toh ki sani wa’azinki be samu shiga ba, and wannan abin da kike gudun ganin ina tabbatar miki da cewa yariga ya kusanto ki, is better ki fara shirin tararsa kamar yanda na gaya miki cewa tukuicin kine_ _hakan kinga kuwa dole na baki”_
Kuka Fateemah ta rushe dashi mai sauti cikin kukan take ce da Anty ita wallahi ta yafe bata son wani tukuici ita a kaita wurin Mummynta kawai dan Allah”.
Dariya Anty tayi cikin mugunta tace ” _ki kwantar da hankalinki ‘yan mata….dole ai zaki koma gidanku_ _amma kafinnan sai na sabauta rayuwarki na_ _wula’kantaki nasa kin zama abin gudu da ‘kyama acikin mutane yanda duk_ _wanda yasanki abaya inya ganki sai yayi ko kwanto……… “_
Story continues below

Da sauri ta matso da kanta kusa da Teemah tana kallon fuskarta tace
_”Kin san dalili?_
Teemah bata iya bata amsa ba illah baki data sake tana kallon Anty da mamakin irin muguwar nufin data ke dashi akanta.
” _anya Anty kece_ _kuwa_ ?
Ta yi tambayar asaman la66anta badan tana neman jin amsa ba sai don yanda kanta ya daure.
Amma Anty sai data jiyota dan haka sai ta mi’ke tsaye tace ” _idanunki ne ko zuciyarki ke son sanin asalin ko ni wacece?_
_” hmmm”_ ta murmusa daga gefen bakinta sannan taci gaba da magana in a serious tune inda tace
” _baki gama tabbatar da ko wacece mother-inlaw ‘dinki ba ko?, toh let me clear up_ _your doubt”_
kirjinta ta nuna tare fa’din _” sunana Maryam matar kawunki Yusuf kuma mahaifiyar mijinki Mahmud, sannan wannan da kike gani itace lespartner ‘dinki as from now kuma banson taurin kai and you must obey my rules in bahaka ba……….kasheki zanyi Fateemah in kuma binne gawarki_ _yadda babu wanda zai ‘kara sanin labarinki da abinda yasameki_ .”
Kukan Teemah sosai ya tsananan ta ta ha’da hannaye tana ro’kon ta tana bata ha’kuri akan bazata iya ba pls karta kasheta ta barta ta tafi wurin Mahaifiyarta.
Anty ko kulata bata ‘karayi ba ta juya abinta ta koma ta zauna.
Anty Chiddy ne ta iso wurin Teemahn da sauri tafara ‘ko’karin share mata hawaye tana fa’din
” _it’s ok babe…. stop crying huh……..please just trust me i only_ _love u I ll not going to harm u ok….”_
Teemah duk da hankalinta yagama tashi amma hakan be hanata kau da kanta gefe ba tare da yiwa Anty Chiddyn wata muguwar harara.
Ashe Anty na kallonta sai kuwa tace
” _gara ma ki saki jiki yarinya ki fara ‘daukan darasi domin bagudu babu ja da baya wannan tamkar cikar_ *BURINA NEH!!* “.
Tana gama fa’din hakan ta tashi ta nufi ‘kofar fita, harta kusa barin ‘dakin sai kuma ta juyo ta dawo baya, tsayuwa tayi ta fuskanci Teemahn sannan tace _” ban baki izinin sanar da kowa abinda yafaru ba da ma wanda zai cigaba da faruwa,_ _ciki kuwa harda Mahmud da duk wani wanda kika sani, idan kika sake wani yasanda_ _labarin nan wallahi Fateemah yanka wuyanki zanyi da_ _wu’ka inkuma farka cikinki inba karnuka hanjinki,_ _kuma kar ki kuskura kiyi mata gardama like I told_ _u before nasan ai baki_ _manta ba”._
Idanunta ta mayar kan Anty Chiddy tace _” in ‘taki baki ha’din kai ko tayi miki gardama pls let me know”_
Tana gama fa’din haka ta wuce ta tafi abinta.
Teemah kam kuka takeyi tunda Anty ta tafi kusan mintina ashirin tana ta kuka abin tausayi sai yanzu tafi jin ba’kin cikin rashin samun mummy awaya, inba dan haka ba da babu abinda zai hana ta sanar da mummy sai de in kashetan zasuyi su kashe, amma yanzu wa take dashi , waye yarage mata?……..Tasan idan tasanar da Mahmud toh dole ne Anty tasani domin ayanda tasan halinsa ba shiru zai yi ba shikam zuwa zai yi yasamu Antyn wanda hakan dai-dai yake da tsayuwar numfashinta.
Tun tana kukan da sauti harta komayi azuci Anty Chiddeh kuwa tagumi kawai tayi ta zauna jigum tana kallonta, acikin ranta takejin babu da’di, saboda kukan Teemahn ba ‘karamin ‘daga hankalinta yake ba, ita haka kawai ta tsinci kanta da son yarinyar kuma bata jin zata iya janye ra’ayinta koka’dan akanta tariga tasanyawa ranta sha’awar kasancewa da ita amma ga dukkan alamu hakan ba ze faru ayau ba, dole ne tayi mata uzuri zuwa wani lokaci kafinnan ta warware, in hakan ya’ki yiyuwa kuwa zata yimata na dole ne koda ranta be so she can do anything just to have her as her lover.
Taso ta rarrasheta akaro na biyu amma Teemah ta nuna mata ‘kyama da tsana azihiri dan haka kawai sai ta tashi tafice ri’ke da tablet ‘dinta ahannu.
*Toh fah readers*
~Yah kuke ganin~ ~abin zai kasance ne…..?~
Da yamma Mahmud yadawo gidan kamar yanda yasaba dawowa a mafi yawan lokuta, kallo ‘daya yamata ya fahimci bata cikin hayyacinta duba da yadda idanunta suka ‘kan’kance suka kuma yi ja tare da yin luhu-luhu, ga kuma fuskarta ma data nuna alamun kumburi 6aro-6aro musamman saman idanunta.
Da ta bu’di baki kuwa tayi masa barka da dawowa sai gaba ‘daya yanayin nata yasake rikita hankalinshi, domin muryarta ma adashe take da ‘kyar ta harha’do maganan ta furta masa.
Tambayarta yayi abinda ke damunta cikin kulawa tare da ri’ko hannayenta zuwa kusa dashi.
‘Kasa tayi da idanunta ta kasa furta masa komai, sai ma wani sabon kuka daya kubce mata.
Arikice yajata ya ha’de ta da jikinsa ya rungumeta tare bubbuga bayanta ahankali, shikanshi ji yayi hankalinsa ya tashi tsoronsa ‘daya kar Fateemah tafara gajiya da zama da shi ayanayin da yake ciki ne, abinda kawai tunaninsa yabasa kenan dan haka sai yabarta ajikinsa tayi ta kukanta son ranta harta gaji tayi shiru tafara sau’ke ajiyan zuciya.
Sai a lokacin Mahmud ya ‘dagota daga jikinsa ya zuba mata idanu yana sake karantar yanayinta.
” _me yasami Fateemah na ?,pls sanar dani me aka miki, waye ya ta6a minke ?_ ‘daya bayan ‘daya ya jero tambayar ta sa cikin natsuwa wanda hakan yasamo asali daga karyewar da zuciyarsa tayi shikanshi jinsa yayi gaba’daya yayi laushi ganinta awannan yanayin, baya so hasashensa ya kasance gaskiya, domin in har hakanne yasan tashin hankalinsa yazo kenan.
Kanta ta komar kan ‘kirjinsa tayi shiru domin aha’ki’kanin gaskiya ita bata san me zata ce dashi yasa meta ba.
_” please Fateemah ki sanar dani damuwarki kinji I’m always here 4u, nima hankalina_ _yakasa kwanciya, zargin kaina nakeyi akan duk wani abinda ya sameki_ _nakan rasa sukuni nima pls daure ki sanar dani kinji”_
Yanzun ma shiru tayi masa sam bata da niyyan bashi amsa ko labari dangane da abinda yafaru tsakaninta da Anty. Ko dan kasheta data ci alwashin yi akan hakan, ita kuwa ba mutuwar take tsoro ba ayanzun dan akan wannan ‘kazamin aikin da suke son tayi tanaji gara mutuwan yafiye mata sai de ahalin yanzu bata so mutuwa ta risketa batare data san ainihin meke faruwa da iyayenta ba, tanaso taji daga garesu taji meyasa ta daina samunsu awaya kuma suma suka daina nemanta suka manta da ita, abinda ke gabanta kenan awannan lokacin.
Ahankali cikin sanyin murya ta furta ” _Yayah_ !”
Sai ya amsa mata da irin yanayin data ambace san da fa’din
_” Na’am matar_ _Yayah”!_
Murmushi maganar tasa yasata jin ya kwaikwayi kalar muryarta sai ta ‘kara yin luf akan ‘kirjin nasa ta lumshe idanunta sannan taci gaba da fa’din ” _Mummy da Daddy na sun manta dani ko_ _Yayah_ ?
‘Dagota yayi daga kan ‘kirjinsan da sauri sai yace mata _” waya gaya miki Mummy sun manta dake,? Mummy kullun idan muka yi waya sai tace in gaisheki hakama_ Daddy shima yake fa’damin kullum”
Story continues below

Idanu ta waro akansa alamar ” _dagaske?_
Sai ya jinjina mata kai tare da medata ya sake kwantar
da ita akan ‘kirjin san shima ya lumshe idanunsa shiru yayi yana jin bugawar da zuciyarta keyi da ‘dan sauri-sauri ,sannan yaciga ba da fa’din
_”Daddy yace zaizo yaganki da kansa amma sai inyaga kin kwantar da_ _hankalinki tukun na, mummy kuwa bata son ku ringa yawan waya ne saboda ita aganinta_ _kamar inkuna waya da ita akai-akai tunanin gida bazai barki da wuri har ki_ _kyautatawa auranki ba, itama tafiso sai kin saba da gidan mijinki tukunna.”_
Wannan duk shirin Mahmud ne ya ha’da ya irga mata ayanda zuciyarsa ta lissafa masa sai ya gaya mata da sunan abinda iyayenta suka fa’da masa kenan akanta, kuma yayi hakane domin ya kwantar mata da hankali badan komai ba, saboda yasan da zaran Fateemah tasan iyayenta basa ‘kasar nan rigimarta ba zai ta6a ‘karewa ba.
Aikuwa yana gama fa’din haka ta ‘dago ta kalleshi _” kuna waya da mummy kullum ko Yayah?_
Yace ” _ah ‘ah fah Fateema ni bance ba, ba kullum muke waya ba lokaci_ _zuwa lokaci ne yawancin ‘kiran ma sai na fita office muke wayar”_
” _meyasa kuma bakuyi idan kana gida?, Yayah_ _Mummy bata sona yanzu saboda anmin aure ko?, ko to gaya mata idan_ _kunyi waya kace mata ni na fasa auren zan dawo_ _gida muyi zaman mu tare da ita”_
cikin dasash shiyar shagwa6a6-6iyar muryarta ta yi masa maganan.
” _waye ya gaya miki auran nan zai rabu Fateemah?…..wannan auren babu wanda ya isa yaraba shi sai mahalicci wanda yayi dalilin faruwarsa…..ke ba kya tunanin halin da zan shiga ne idan kika barni?, pls karki sake cewa zaki tafi ki barni kinji”_
Jin yace auren nasu ba me rabuwa bane take sai ta turo ‘dan ‘karamin bakinta dake zagaye da pink lips ‘dinta gaba alaman ta ji haushin hakan kenan.
Sai daya kai ayar maganar tasa kafin ta ‘daga masa kai alamar taji amma still bakin ature.
Mahmud kam Sosai yanda tayin ya matu’kar birgeshi, idanunsa ya sau’kar akan la66anta da sukayi jajir dasu dayake tayi kuka sosai, take sai ya ‘dago hannunsa ya wari yatsa ‘daya yashafa su ahankali.
Teemah kuwa ‘dan jan jikinta tayi daga na Mahmud da niyyar tafiya tabar inda yake, amma Mahmud be bari tayi nisa ba yasa hannu yadawo da ita jikinsa, duk da jikinsa be nuna alamun son kasancewarta ra6e ajikinsan ba amma zuciyarsa na matu’kar son hakan shiyasa ya dawo da ita.
” _kin gaji da zama da niko Fateemah_ ?
Idanuta ta ‘dago da sauri ta sau’ke su akansa.
” _pls tell me kinji, banaso hakkin ki yamin yawa akaina dan nasan Allah sai_ _ya tuhumeni akan zama na da k…….”_
Da hannunta tayi saurin rufe masa baki wanda hakan ya tilasta masa yin shiru da maganar da keyi .
_” Kinsan wani abu?_
Ya tambayeta da nutsatstsiyar muryarsa.
Da kai ta bashi amsa yadda zai fahimceta.
Sai kuwa yaci gaba da fa’din ” _kinason yin waya da Daddy_ ?
Da sauri ta ‘daga masa kai alamar ” _ehh_ “
Sai yace
” _alright…., zan ‘kira miki shi amma da shara’din sai kin_ _sanar dani_ _abinda yasaki kuka_ _da bana_ _nan……..”._
Tunkan ya ‘karasa rufe bakinsa tabashi amsa da fa’din
_” cikinta ne yadameni da ciwo shiyasa tayi kuka”_
_” toh me yasa baki ‘kirani awaya ba ki ka zauna da ciwo har haka, kuka yana magani_ _ne Fateemah…?, kin ga kuwa yadda kika dawo , Allah_ _dana ganki hankalina yatashi sosai”_
Shiru tayi tana jinsa sai da taji yayi shiru kafin ta ce
” _Yayah kira min Daddyn toh mana yanzu !_
Murmushi yayi ganin yanda ta ‘kagu dajin muryar Mahaifinta, hannunta yaja suka koma kan cushion suka zauna sannan ya lalu6o phone number ‘din daddy ta Nigeria dagangan yayi dialling dan yasan sarai bashiga zaiyi ba.
Story continues below

A speaker yasaka wayar dan haka ba sai ya bu’di baki yayi mata dogon bayani ba akan wayar daddyn, saboda da kunnuwanta taji ance numbern is switch up.
Langa6ar da kai tayi gefe kamar zatayi kuka ganin haka sai Mahmud ya hau bata baki akan wai tayi ha’kuri may be Daddyn ya ‘danyi wata tafiya ne, yace nikuma kinga bani da numbers ‘dinsa na waje ko’daya balle muyi trying, amma bari zan tambayi Abbah I’m sure bazai rasa agunsa ba.
” _Toh yayah ‘kira ka tambayeshi mana tun yanzu kar ajima kuma ka manta_ “
Ajiyan zuciya ya sau’ke tare da ajiye wayar agefensa bayan ya dannata tashiga security dan kar ma Teemah ta ‘dago ‘karyar da ya shirga mata, sai yace da ita
_”Nagaji kinji yanzun lil sis ki bari idan na ‘dan huta anjima sai naje gidan ma gaba ‘daya da kaina inkar6o inajin_ _hakan zaifi ko?”_
Yana maganar ne tare zamowa ya kwantar da kansa akan cinyarta.
Teemah kuwa zuciyarta tsinkewa yayi dajin ya ambaci zuwa can gidan ita ayanzu in akwai abinda ta fi tsana aduniya toh be wuce Anty ba ta tsani ko ganin tama , amma bata yi masa magana ba sai kawai ta ‘daga hannunta ‘daya ta cusa acikin kwantaccen ba’kin gashin kansa tana shafawa ahankali.
Mahmud kuwa lumshe idanunsa yayi tausayinta na ‘kara ratsa shi, akullum yanajin kamar baya mata adalci a zaman su, balle yau ‘din dayaga yanda ta dawo duk sai komai nasa ya tsaya cak, in ba tunanin mafita ba baya komai.
Kusan minti sha biyar suna ahaka kafin Mahmud ya yun’kura yatashi yace zai watsa ruwa.
Fita yayi bayan yagama shiryawa be zame ko’ina ba sai gidan Umar abokin aikinsa yayi masa bayanin meke tafe dashi yace yana so in zai yiwu su tafi gobe, daya ke dama Umar yace masa akowani lokaci idan ya shirya zasu iya tafiya shi ba shi da matsala.
Hakan kuwa akayi domin Umar take yabashi tabbacin samun rakiyarsa aduk lokacin daya bu’kata yanzun ma cewa yayi babu komai Allah ya tashemu lafiya”.
Da farin cikin sa yabaro Umar din yana me jin ‘kwarin gwiwa da fatan samun nasara ji yake ajikinsa kamar matsalarsa ta kusan zuwa ‘karshe, da yardar Allah komai zai daidai su shida matarsa kamar yadda kowa su irin ma aurata ke rayuwa agidajensu.
Daga wurin Umar Mahmud gidan mahaifinsa ya nufa amma be samu Abbah agida ba sai de Anty da ya samesu tare da Munnirah suna tattaunawa be san akan miye bane amma yanda yaga fuskarsu kamar gonar auduga yasa yagane anin farin ciki ne agare su, saboda musamman Anty tayi ‘kiranta tazo domin tayi mata albishir ‘din abinda take shirin aikatawa daughter inlawn ta, takuma ‘kara lallashinta akan sun kusan rabuwa ai tunda Anty Chiddy yanzu matar Mahmud ‘din take hari, kuma da zaran burinta yacika zata sada ta da gidan bokan dake mata aiki,shikuwa aikinsa kamar ayi yanka da sabuwar rezor blade yana yi maka aiki toh labari ze canja shiyasa nafi gane zuwa wurinsa, shegiya itakuma dan iskanci sai take ta min yanga da ‘kyar nasamu ta amince zata kaini amma sai ta samu abinda take so.
Dariya Munnirah tayi tace ” _kice nafara shiri na kusa zama amarya”_
Anty ma dariyar tayi tace _” ai ki kwantar da_ _hankalinki ina gaya_ _miki aure tsakaninki da_ _Mahmud tamkar_ _anyi shi angama ne!_
Sunan cikin wannan yanayin Mahmud ya shigo yasame su sai de be ji abinda suke fa’di illah dariyar ya tarar.
Mahmud ganin Munnira na gurin yasa be ko kula da su ba yayi wucewarsa ciki bayan sun amsa masa sallamar da yai musu.
Munnira bin bayansa tayi da kallo tana murmushi musamman dataga yanda yawani basar yai shigewansa ciki aranta tace ” _ohh boy…..ka gama fa’din ranka da girman kanka yanzu….. domin very soon ka kusan dawowa hannuna, kuma nawa ni ka’dai injuya ka yanda nakeso babu me takurani”_
Anty ne tabi bayansa zuwa ‘dakin daya shigan bayan ta gama sallamar Munnirah ta tafi gida dan tasan ganin Munnirah ne yasa shi shigewa cikin.
Gaishe da ita yayi tare da sanar da ita batun tafiyar da ta taso masa amma be gaya mata ainahin tushen tafiyar ba sai kawai yace da ita zashi katsina gobe in Allah ya kai rai domin akwai wani urgent meeting ‘din da ze je yi acan.
Fatan alkhairi tamishi daga nan be zame ko ina ba ya koma gida wurin matarsa.
Yana zuwa kuwa ta tare shi da batun numbern Daddy sai yace mata ashe Abbah ya tafi cotonou shi be ma sani ba, amma de yana kyautata zaton dawowarshi cikin satin.
Dolen ta ta ha’kura sai kuma tabawa zuciyarta tabbacin Abbah na dawowa zataje dakanta ta kar6o no.