ABBAS
CHAPTER 16
Sai da dare Bayan sallahr isha’i Mahmud ya sanar da Teemah batun tafiyan nasa, take kuwa tafara mai daru akan ita wallahi sai de sutafi tare ita bazata zauna ita ka’dai agidan ba, yace toh zai kaita wurin Anty su zauna kafin ya dawo.
Ai tana jin haka sai kawai tafara yi masa kuka tana cewa ita bata so dashi zata tafi, wai dan Allah yatafi da ita, da ‘kyar yasamu ya shawo kanta tayi shiru bayan ya amince cewar bazai kaita wurin Antyn ba kamar yadda baze barta ita ka’dai agida ba.
Washe gari da sassafe bayan kowa ya shirya suka tafi tare zuwa gidan Umar, sai da suka tashi tafiya kafin ya sanar da su cewa Teemah zata zauna da iyalan abokinsa Umar ‘din kafin su dawo, saboda tace tana tsoron zama agida ita ka’dai.
Matar Umar murna tayi sosai da zuwan Teemah dan dama ba ‘karamin kewar ‘yan uwanta hausawa take yi ba.
Bayan tafiyar su Mahmud matar Umar ta ringa jan Teemah da hira ganin ta zauna shiru kamar me tunanin wani abu.
Tun Teemah bata sakewa da su har tazo tasaki jiki gaba ‘daya ta saki ranta suka rin’ka surutu da yaran Umar ‘din.
Tare da matar Umar suka shiga kitchen suka yi girkin abincin rana (lunch) suka ci bayan sun yi sallar azahar.
Sai de duk yadda Teemah ta so ta 6oye damuwarta abin ya faskara, takan zauna tayi shiru wani sa’in har se matar Umar ta ta6ata kafin take dawo da hankalinta garesu.
Hakan yasa matar Umar ta fahimci akwai wani abinda ke damun Teemah.
Sai de bata tsawaita tunanin ko mene ba ta de barshi akan wata’kila tafiyar da Mahmud ‘din yayi ne ke damunta dayake amarya ce ita batawani da’de da yin auran ba, bayaga haka ma kuma Teemah yarinya ce dole zata damu tunda da shi tafi sabawa agarin.
Bayan sallar la’asar ne Mahmud ya’kira Teemah awayarta dan yaji ya walwalarta take agidan.
Cikin sa’a kuwa lokacin Teemah na tsakiyar yaran Umar suna ta hayaniya, kuma koda ta ‘dan matsa gefe da su ma kafin ta ankara sun ‘kara biyota dan haka kawai sai ta zauna tayi maganar acikinsu hakan yasa be wani fahimci komai daga wajenta ba har suka ‘kare wayar , se ma yaji da’di ganin tasaki jikinta agidan Umar ‘din.
Matar Umar nada mutunci sosai kuma tana da son jama’a gata da kula da duk wani abu da ya shafi mutuncin auranta hakan yasa take da son taga duk wata ‘ya mace na da babbar fada awurin mijinta bata son taga mace na wulan’kanta sanadin aure.
Awayar da Teemah tayi da Mahmud sau uku a wunin ranar sai ta fahimci rayuwar auren sun kamar ba daidai yake tafiya ba, domin bata ga wani kula ko nuna damuwa da rashin junan sun da sukeyi ba awayar da sukayin face jin lafiyarta da kuma ko wata matsala na damunta abin da ka’dai Mahmud yadamu yaji kenan daga gareta duk da suna matsayin sabbin ma aurata, sa6anin ita data ke da ‘ya’ya har biyu ma amma sam bazata iya yin waya da mijinta agaban kowa ba saboda bako wani irin magana zata iya fa’da agaban mutane ba idan suna waya da mijinta.
Story continues below

Zatonta zataga fiye da natan awajen Fateema da mijinta saboda ita ‘din har yanzu amarya ce amma sai taga yanayin sha’kuwa da kulawarsu yayi ‘kasa da nata ne ma sosai, ko irin missing ‘din junansun nan bataga alama acikin kalaman su ba.
Hakan yasa taci ‘damarar ankar da Fateemah babban matsayi da muhimmancin mijinta agareta.
Da dare bayan anyi sallar Mahgrib suka ci abinci inda duk cin abincin Fateemahn ya kasance kamar kullum sai de ta ‘dan caccakula tabari wanda matar Umar ta fahimci ko darana ma hakan ne ya kasance.
Abin na bata mamaki yanda damuwar Fateemah na rashin mijinta ya bayyana kansa afili amma kuma cikin kalamanta sam babu hakan.
Sai da sukayi sallar isha’i sannan suka yi zaman su apalour suna ‘dan ta6a hira inda ba awani da’de ba yaran duk sukayi bacci sai su biyun suka rage.
Da wannan damar matar Umar tayi amfani ta dinga jan Teemah da magana da kuma shan cikinta akan rayuwar aurensu, anan ta ‘dan fahimci wani abu ka’dan, sai de bata gama fahimta ba sai washegari data bata wani magani sinadarin mata tayi mata bayanin yadda ake amfani dashi da kuma irin tasirin dayake dashi harma ta nuna mata cewar zata ji da’din mu’amala da mijinta matu’kar tayi anfani da maganain, anan ne Teemah ta nuna mata cewar ita bata san me take nufi ba kwata kwata.
Matar Umar batayi ‘kasa agwiwa ba ta bayyana mata komai a yanda zata fahimta.
Nan kuwa Teemah ta to na ma kanta asiri dan atake ta nuna jin kunya da maganar da matar Umar ‘din ta mata ta kuma nuna bata san komai akan hakan ba, sai tace da ita ai su ba irin wannan zaman sukeyi da Mahmud ba, ta ce ai yayah Mahmud ba irin mutanen nan bane shi baze yi mata haka ba.
Mamakin matar Umar ‘karuwa yayi akan nada da jin maganar da Teemah tayi mata ayanzun.
Take sai ta saki ranta ahankali ta ringa yiwa Teemahn bayanin menene aure da kuma abinda ya ‘kunsa, ita matar Umar duk akan Mahmud ta ‘dora laifin tunaninta ko shima yana ‘daya daga cikin irin mutanen da ke raina mace idann an aura musu ita da sauran ‘kuruciyarta, amma ai zuwa yanzun Teemah tayi girman dazata iya ‘daukan bu’katun mijinta duk kuwa yanda yake tunda a’kalla zata kai 18yrs da haihuwa ayanzun, dayake bata san da batun matsalar dayake damunsu ba shiyasa ta ke gani kamar laifinsa ne da har yanzu be fahimtar da Teemah ma’anar zamansu aguri ‘daya ba, amma duk da haka tayi ‘ko’kari wajen jawo hankalin Teemah inda ta bayyana mata asalin manufar aure a addinance.
Teemah ta ‘dan fahimce ta harma hakan yasa ta ‘dan saki jiki ta baza kunnuwa tana ‘daukan darasi domin ita sam bata san da wannan batun ba.
Daga nan matar Umar ta bata wani ha’din magani me zuma aciki, maganin yamata da’di dan haka ta ringa sha abinta tana lasan baki dama ta nan tafi kauri gurin kananun ciye-ciye da kayan zaki.
Daga nan suka zarce hiran rayuwa acikin hiran ne Teemah ta tuna da mahaifiyarta, take kuwa sai jikinta yayi sanyi tafara bawa Matar Umar labarin rashin jin iyayen nata da batayi ba gashi tarasa yazata yi ta same su tace kota ‘kira gidan ‘kanin mahaifinta ma (Daddyn Abuja)
bata samun gamsashshiyar amsa daga wurin su.
Ta tausaya wa Teemah har ranta da jin cewa tun bayan aurenta da kwanaki ka’dan bata ‘kara jin iyayenta ba, gashi guri da nisa ba kusa ba balle ta je ta ganosu, bayan hakama garin ba zaman lafiya ake yi ba dole hankalin Teemah yatashi.
‘Dan tunani ka’dan matar Umar tayi sai tace da Teemahn ta ‘dauko wayarta suyi wani abu.
Tashi tayi taje ta ‘dauko wayar sai matar Umar tace ta gwada ‘kiran Mahmud su gaisa tunda basuyi waya da safiyar yau ba sai ta tambaye shi ko yanada layin Umman Abujan kode wani haka acan tace yatura mata domin tayi loosing wasu contact ‘din ta kuma tana son ta ‘kira su ne.
Story continues below

Koda ta ‘kira shin kuwa sai yace bashi da numbern kowa sai na Abbas, amma zai tambaye shi sai ya tura masa idan yaturo zai mata sending.
Da ” _toh_ ” ta amsa masa daga nan sai ta kashe ‘kiran.
Shiru matar Umar tayi tana tunanin wata mafita dan kuwa tana ganin kamar idan Mahmud ya turo numbers ‘din shirinta ya wargaje, taso ne kowa ya zamana bashi da contact ‘din tsakaninsu.
Teemah kuwa tsayawa tayi tana kallon ta domin jin manufar hakan daga bakinta.
Tsawon mintina biyar suna ahaka sai ga ‘kiran Mahmud yadawo wayar Teemah, bin wayar tayi da kallo kafin daga bisani ta ‘daga wayar ta sada shi da kunnan ta.
Daga ‘daya 6angaren Mahmud jikinsa da sanyi yake ce mata ” _Tayi ha’kuri zuwa wani lokaci dan Abbas_ ‘ _din yanzu_ yana cikin maiduguri yana kan aiki kuma anyanke gaba ‘daya network ‘din Borno harma da wasu garuruwan dake makwabta ka dasu, so ba zai same shi ayanzun ba sai de ko inya ‘kira shi ko kuma idan yadawo sai suje gurin Abbah yabasu numbern Daddyn Abujan inyaso sai ya ha’da ta da su Hannah. Daga ‘karshe yace taringa yiwa Abbas ‘din addu’a pls, yanzu shima ake fa’da masa cewar maidugurin ba lafiya ahalin yanzu an kai musu harin bazata.
Teemah ji tayi hankalinta yatashi da batun Mahmud ‘din na ‘karshe.
Tana sau’ke wayar tafara dialling numbern Abbas amma baya tafiya, tayi harta gaji ta ha’kura.
Yanda abin ya tsaye mata kuwa har yasa tafara hawaye, yanzun hankalinta yafi kullum tashi saboda damuwarta sun kara yawaita ne musamman data ji cewa Yah Abbas na cikin maiduguri kuma ankai hari ga kuma iyayenta a damaturu kuma bata samunsu awaya ga kuma sarka’kiyar Anty to me ke faruwa ne ? Abin nan na matu’kar damunta sosai.
Da ‘kyar Matar Umar ta lallashe ta ta samu ta ‘dan nutsu sai ta ringa kwantar mata da hankali ta ce mata bari suyi wani game wata’kila zata samu jin labarin iyayen nata idan tayi sa’a.
Tace Teemah ta ‘kira Hannah tace mata tana hanya yau zataje dubo iyayenta.
Hakan kuwa akayi Teemah ta ‘kira Hannah ta gaya mata abinda matar Umar ‘din ta ce ta fa’da sai taji Hannah ta rikice tana mata masifar waye yace mata ta hau hanya, tasan kuwa irin abinda ke faruwa awancen yankin, tace tun wuri ki nemi damar da zaki koma gida inba so kike kiyi tafiyar banza ba”
Cikin sanyin murya Teemah tace
” _tafiyar banza kuma Hannah, nida zanje inga mummy da Daddy nah_ ?
” _angaya miki mummy tana can ne? Me yasa baki_ _fa’dawa Ummah ba kafin ki fara shirin tafiyar?_
arikice Hannah take duk wannan maganar.
Matar umar najin haka aranta tace ” _anzo gurin_ “
Domin wayar a handsfree take duk atare suke jin komai.
Suna jinta ta cikin wayar tana ta kwallah ‘kiran _Ummah_ arikice, _Ummah_ !…… _Ummah_ !!……… _Ummah kinji abinda Teemah ta ke shirin_ _yi kuwa? Wai fah takama hanyar zuwa_ _damaturu ayau ‘din nan._
Kar6ar wayar Ummah tayi tana kar6a itama tafara fa’din ” _Fateemah meyasa kika yanke wannan shawaran batare da kin sanar_ _dani ba!_
shiru Teemah tayi Ummah kuwa sai taci gaba da magana tace ” _ina Mahmud ‘din yake?_
Sai alokacin Teemah tace
” _Nabarshi agida yasani a mota ne shi ya koma gida_ “
Azabure Ummah tace
” _kina nufin amota zakiyi duk wannan doguwar tafiyar_ _Fateeemah kuma ke_ _ka’dai?_
” _a ina kuke yanzun?_
Ummah tasake tambayarta.
Kame-kame Teemah tafara kamar irin zata fa’di wurin ‘din nan sai Ummah ta tare ta da fa’din ” _koma a ina ne ki maza ki dakatar da tafiyar nan ki koma gida dan kuwa Khadeeja basu_ ‘ _kasar nan a halin_ _yanzu suna Dubai”_
Story continues below

Wani sanyin da’di Teemah taji ya ratsata take farin ciki ya bayyana akan fuskarta tana murmushi tace ” _har Dubai mummy ta tafi shine bata sanar dani ba_ _Ummah…..toh ki tura min numbernta idan na koma sai_ _in’ kirata.”!_
Da sauri Ummah ta tare ta da fadin
” _Ehh zan tura miki amma ki kula da zarar kun shigo cikin gari ki ce da su su sau’ke_ _ki ki nemi mota ki koma gida indai bakuyi nisa ba, in kuma_ _kunyi nisa ki iso_ _nan Abuja”_
” ah ah bamuyi nisa ba Ummah”
Teemah ta da ita.
” _toh maza ki koma gida zansa Hannah ta tura miki layin Mummyn naki_ _yanzu”_
Ummah ta ‘karasa da mita inda take cewa
” _amma ni wallahi wannan karan Mahmud be birge ni ba, taya zai biye shirmenki yasaki_ _amota ke ka’dai kuma ya kwantar da hankalinsa agida_ _da sunan kinyi tafiya, wannan ai rashin hankali ne, inkin koma gida ki_ _ha’da ni dashi dan_ _Allah”_ !
Da ” _toh_ ” Teemah ta amsa mata sannan ta yanke ‘kiran tana me farin ciki da wannan al’amarin har tsalle ta buga ta rungume matar Umar da ‘karfi tana me zuba mata ruwan godiya da wannan babban kyautan datayi mata, itama dariyar takeyi tana me nuna farin cikinta afili ganin yau Teemah tasaki ranta sosai.
Mintina biyu basu cika ba taji wayar ta tayi ‘karan shigowan text, da sauri ta ‘daga ta duba sai kuwa taga international number aka turo mata harda ‘karamin plus a afarkon numbers ‘din.
Godiya ta ‘kara yiwa Allah tare da fa’din ” _Yah mahmud ka gafarceni na maka sharri nasan yanzun zuciyar_ _Ummah acike take taf da jin haushinka amma_ _zan warware komai_ _daga baya_ “.
Take ta gwada ‘kiran layin da aka turo matan sai kuwa taji yashiga.
” _Assalamu alaikum_ “
Tajiyo muryar Mummy na fa’din haka.
Lumshe idanu tayi sai taji zuciyarta ta karye take hawaye ya ratso tacikin lumsassun idanun ya gangaro kan kumatunta,
Ahankali tace ” _mummy ke ce_ ?
Ita kanta mummy jikinta rawa yafara da jin muryar ‘yar tata bayan tsawon wasu kwanaki, sai tace ” _nice mamana ya kike”_
” _Mummy shine kika manta dani keda daddy kuka yi tafiyarku wata ‘kasa kuka barni anan ko_ _nemana baku ‘kara yi ba, mummy daman idan anyiwa mutun aure_ _mantawa ake yi dashi?,mummy ina daddy na yake inji muryarsa”_
Shiru mummy tayi tausayin ‘yartata na ratsa zuciya da gangan jikinta ita ma ba ‘karamin dauriya tayi ba harta kai tsawon wannan lokacin bata nemeta ba, takan yawaita jero numbers ‘din Teemah kamar zata ‘kira amma sai ta fasa saboda bin dokar da Daddyn yakafa mata bata son ta karya masa dokarsa har ransa ya 6aci shiyasa takasa ‘kiran Teemah koda sau ‘daya ne.
ahankali tafurta ” _hoo Teemah irin wannan tambayoyin wanne daga ciki zan fara amsa miki?_
” _Duk kansu mummy_ “
Teemah tabata amsa cikin za’kuwa.
Murmushi kawai mummy tayi sai ta fara bata ha’kuri tana mai tambayarta yanayin zamanta da Anty da kuma mijinta. Teemah tace komai normal babu matsalar komai.
Teemah taso ta sanar da Mummy matsalar dake tsakaninta da Anty amma tana tsoron abinda ze biyo baya dan tasan mummy ba shiru zatayi ba idan taji maganar dole sai ta nemi fitar da ita daga al’amarin wanda hakan ke dai dai da tsayawar numfashinta akowani lokaci.
Suna cikin yin wayar daddy ya shigo sai kuwa mummy ta mi’ka masa wayar batare da tayi masa magana ba ” _waye_” ya tambayi mummyn ‘kasa ‘kasa yanda mummyn ka’dai zataji shi.
Sai dai Teemah ta jiyo shi itama sai ta ce dashi ” _daddy_ _nice fah_ ” cikin shagwa6a tayi maganar.
” _ahh ah Angel ‘dina kece yau akan layi?_
Story continues below

” _daddy shine kaima ka manta dani ko?_
” _Waye ya gaya miki haka? bana so mu ringa damunki ne shiyasa kika jimu shiru amma yanzu_ _ma haka ina planning zan shiga lagos ‘din next_ _week”._
Take tace
” _Allah daddy dagaske?_
Murmushi kawai yai mata batare da ya yi magana ba.
Sai itace tasake fa’din ” _daddy dan Allah idan kazo karka tafi bamu ha’du ba akwai maganar danake_ _so ingaya maka!”_
Sai yanzun yace
” _Toh shikenan insha Allahu zan zo har gida karki damu ki kwantar da hankalinki muma_ _bamu ta6a_ _mantawa da ke ba_ _kinji_ “
*****
Yau ba ‘karamin da’di take ji ba, tana gama waya dasu ta ‘kira Mahmud tasanar dashi cewa yau sunyi waya da Mummy harda daddy ma”
Tambayarta yayi taya hakan yafaru kode sune suka kirata, sai tace ah ahh ita ta ‘kirasu daga nan tabashi labarin yanda akayi harma da maganar da Ummah tafa’da akansa, yana dariya yace ” _lallai yarinyar nan wuyanki yayi ‘karfi wato harda ni acikin shirin ‘karyan_ _naki_ _ko_ ?
Dariya itama tayi tare da yanke wayar.
Ba’a jima ba sai ga ‘kiran Ummah tana me sake tambayarta kota koma gidan, sai Teemah tayi mata ‘karyar yanzu ta sauka za’a sata motane yanzun, sai tace idan ta koma gida zata ‘kirata
” _yauwa Fateemah maza ki koma gida kinji, Allah ya tsare ya kare ya kuma_ _bada sa’a_ “
cewar Ummah
” _ameen Ummah_ , _nagode a_ “.
Farin cikin Teemah yau baya 6oyuwa yanda taji muryar iyayen nata ita ka’dai sai tana sakin murmushi musamman idan ta tuna cewa daddy zai zo nextweek sai take ganin kamar matsalarta ta kusan zuwa karshe, dan tagama sawa ranta cewar daddy na zuwa zata ma’kale masa sai ya tafi da ita ko dan ta huta da fitinar su Anty ma.
Sosai take jin farin ciki wanda hakan yagama bayyana kansa azahiri kowa ya kalleta take zai gane hakan, sai de deepdown her heart tana jin zuciyarta ajagule kamar bata da nutsuwa, da ‘kyar tasamu ta lalu6o damuwar tata da dare bayan ta kwanta bacci alokacin ta zurfafa tunanin ta sai data gano 6oyayyiyar damuwar tata.
Lumshe idanu tayi take tausayin sa ya tsarga mata azuci ta ringa tuno rayuwar su dashi abaya abu na ‘karshe data tuno shine ranar da za’a ‘daura auren ta da Mahmud daya zo yabata gift har cikin ‘dakinta.
Tsintar kanta tayi da tausaya wa rayuwarsu shida ita take ta tashi tayo alwala tazo ta tada sallah bayan ta sallame ta ringa jero addu’o’i na nema musu kariya wurin mahallici, musamman ma shi da yake fama da ‘yan ta addah.
Mahmud kuwa sosai ya samu tarba wurin shehin malami kakan Umar abokinsa, yayi masa tambayoyi akan abubuwan da ke faruwa dashi, Mahmud duk yayi masa bayani.
Sosai ya jinajina wa al’amarin tare da sanar da Mahmud ‘din cewa matsalarsa ba abin damuwa bace matu’kar za’a yi anfani da abinda ‘qur’ani ya karantar, yace matsalar sa bakomai bace face matsalar aljanu amma da iznin Allah komai zai daidaita.
Atake yabashi wani ruwan addu’a ha’de da ganyen magarya yace yayi bismillah yasha ya kuma wanke fuskarsa.
Hakan Mahmud yayi kamar yanda malamin ya umarce sa da yi daga nan yabashi wasu addu’o’i yace ya ringa yi akoda yaushe sannan ya yaiwata yin istighfari, sadaka da neman yardar Allah akowani lokaci.
Washegari malamin ya ha’dawa Mahmud magunguna na islamic medicine tare da bashi wata jarka da ke chike da ruwan rubutu yayi masa bayanin yanda zai na anfani dasu.
Sosai Mahmud yaji da’din al’amarin harma yarasa da me zai sakawa malamin, banki ya tafi yaje ya chiro ku’di kusan 200 thousand naira ya kawo yabashi, amma fir ya’ki kar6a, sunyi-sunyi ya kar6a ya’ki Mahmud kamar ze yi kuka domin gani yayi kamar in be kar6a ba tamkar wani nauyi ne akansa.
Dayaga sun dage ne shine ya kar6i twenty thousand yace ya isa Allah ya sa adace yakuma bada sa’a, yace da Mahmud ‘din shi bashi da matsala da ku’di amma ze iya ya bayar da sadakan ku’din ga koma wanene inyaga me shi nada bu’kata.
Godiyar Mahmud kamar su yi wa malamin rumfah suka masa sallama suka fito da niyyar tafiya.
Taxi suka tara suka hau tun acikin unguwa suka samu, dayake cikin unguwa ne sai suke tafiyar ahankali.
Wani gida suka wuce daf da zasu fita a unguwar ginin ‘kasa duk ya lalace ma katangar gidan ruwa duk ya wanketa ta dawo yar guntuwa har kana hango abinda ke faruwa acikin gidan, ‘kofar gidan ma da wani tsohon buhu aka tare shi daga shi kuwa babu komai.
Acikin ‘yan sakanni Mahmud ya gama karanto fasalin gidan, take kuwa zuciyarsa ta karye, tausayin wahalar da al’ummah suke ciki duk yabi ya cika masa zuciya.
Gaba ka’dan sai yaga wata yarinya da bazata wuche 10-11yrs ba, kayan jikinta kuwa ko goge takalmansa aka ce za’a yi dasu sai ya hana ayi balle har su kasance ajikin mutun, tsabar yanda ko’diya da datti suka cikasu ko gane zanen zanin da kyau ma ba’a yi.
Dur’kushe take tana kwasan wani farin abu a’kasa hankalinta duk yabi ya tashi tana yi tana waiwaye ga dukkan alamu bada sanin ta ba ya kuskure ya zube.
Mahmud dakatar da drivern taxi ‘din yayi bayan sun wuce yarinyar ka’dan, amma kafin Mahmud ya yi yun’kurin fitowa har wata mata ta fito ta iso inda yarinyar take tsugunne tana masifa itama ta tsugunna tana tayata kwasan abun.
Ahankali ya tako ya iso kusa dasu basu ma lura dashi ba hakan yasa wannan matar bata dakata da masifar datake yi ba amma ba da hayaniya takeyi ba tanayi ne yanda yarinyar ka’dai zata jita sai ko Mahmud daya musu la6e.
Jiyayi matar na fa’din ” _yanzu fisabilillahi meram bazaki dinga kulawa ba, akullum_ _magana ‘daya kike son inyita maimaita miki?, ke ko duba yanayin da aka samu ‘dan_ _ku’din nan bakiyi kika zo kika zubar da alabon nan yanzu dan Allah a_ _ina kike so mu shiga mu samu ku’din da za’a siyi wani ga yara duk yunwa tabi ta ishesu,_ _badan albarkacin surfen nan da matar yakubu takawo_ _bama da yau Allah ne ka’dai yasan yanda zamu kasance, kuma muna murna zamu_ _samu abin ta6awa sai kizo kuma ki zubar?_
Ahankali Mahmud ya ‘karaso kusa da su tsabar yanda yaji tausayinsu har idanunsa na tsatstsafo da ruwan hawaye amma be bari sun sau’ko ba kawai ya dinga fa’din _Alhamdulillah_ azuciyarsa da rufin asirin da Allah yayi musu, ha’ki’ka rayuwar bin Adama ma aya ce babba, yanda damuwoyin junanmu suka bambanta kowa da kalar tashi damuwar, kamar shi yanzu yanda Allah ya rufa masa asiri takowani 6angare bashida matsala da komai sai kawai ya jarabce shi da dakushewar wani sassa na jikinsa wanda hakan ya matu’kar ‘daga masa hankali, balle wa’dannan, ya zasuji da damuwar su takasance akan rayuwa ce gaba ‘dayanta, ha’ki’ka Allah buwayi ne gagara misali domin shine yayi al’kawrin jarabtar kowa daga cikin mutane harma da ajannu da kowani irin al’amari, sai de fatan Allah ya sassauta mana ya kuma bamu ikon cin jarabawar.
Adaidai lokacin ya iso kansu ya tsaya sai yaga sun ma gama kwashewa sauran wanda ya gaurayu da ‘kasan ne suke sake kwasa.
Da sauri yace ” _ah ah Innah wannan ai ‘kasa ce ta rage_ ”
Bata ‘dago taga me yi mata maganan ta bashi amsa da fa’din ” ‘ _kyaleni yaro, inban kwashe duka ba ‘dan waken ba isan yaran zaiyi ba hakan ma daya za’a ci ballantana kuma ya gaza haka_ “
Mahmud cikin tsananin mamaki yace
” _wai kina nufin wannan abin abinci za’ayi da shi Innah_ ?
Sai wannan karan matar ta dakata da kwasan abin da takeyi ta ‘dago jin tambayar yayi matan kamar ta rainin hankali.
Tana mi’kewa taganshi tsaye kusa da ita ga wasu su biyu ma tsaye abayansa, ita tsoro ma ya bata dan yanda taganshin take tsoro ya tsarga mata azuci.
Hannun ‘yarta takama tayi baya ka’dan sannan tajuya suka nufi gidansu da saurin gaske.
Wannan gidan da Mahmud yagani ‘dazu nan yaga suka shiga shima sai ya biyo su abaya amma kafinma ya iso su har sun shige ciki abinsu.
Tsayawa sukayi suna ‘dan dube-dube can suka hango wani matashin saurayi da bazai wuce shekara 20 ba yana kallon su daga ‘dan nesa ka’dan.
Hannu Mahmud ya masa sai kuwa ya taho da sauri kamar dama jira yake su ‘kira shi.
Yana iso wa ya gaida su suka amsa sannan Mahmud ya tambayi sunansa .
Matashin yace sunan sa _Rabi’u_ .
Mahmud ne yace ” _yauwa Rabi’u dan Allah ko zaka mana magana da mai gidan nan_ ”
Matashin mai suna Rabi’u yace ” _Allah sarki ai maigidan ya kwan biyu da rasuwa, matarsa da ‘ya’yansa ne ka’dai_ _suka rayuwa_ _agidan_ “
Tausayin mutanen ne ya sake shiga dukkanin azuciyoyin su har drivern taxi ‘din.
Bayani Mahmud yayi wa Rabi’u akan abinda ke tafe dasu, nan take kuwa farin ciki ya baibaye ilahirin fuskar Rabi’u yafara yi musu godiya tunma be tabbatar da gaskiyar lamarin ba, shiga gidan Rabi’u yayi yai wa matar gidan bayani wanda da ‘kyar ta amince da batun da Rabi’un yazo mata dashi, domin ita rayuwar yanzu tsoro yake bata, mutane sam babu tsoron Allah azu’katansu, dayawansu basa taimako saboda Allah sai dan su cuceka ko dan wani abu daban, ita kuwa da take ta fama tana lalla6a rayuwarta da ‘yan yaranta guda hu’du sam bata son wata sabuwar fitina ta 6ullo musu.
Da ‘kyar Rabi’u ya shawo kanta ta yadda ta amince da su Mahmud ‘din sannan Rabi’u yakoma yayi musu iso.
Su Mahmud basu tsinke da al’amarin matar ba har sai da suka sanya kawunansu acikin gidan, inda suka ga komai kamar ba inda ‘dan adam ke rayuwa ba, babu komai da zai birge mutun acikin gidan face tarkace da tsummokara, Mahmud sosai ya tausaya musu jikinsa yayi sanyi ‘kalau.
Rabi’u ne da kansa ya je ya janyo wata ru6a66iyar tabarma ya shinfi’da musu suka zauna akai, ganin yanayin matar ne yasa Umar yayi mata bayani abayyane cewa ta saki jikinta karta ji tsoro sadaka suka kawo musu ba cutar da su zasu yi ba, amma intaga kamar bata yadda dasu ba har yanzun tana iya yi musu bayani sai sukoma inda suka fito.
Story continues below

Rabi’u ne yayi saurin taran maganar da fa’din ” _ah ah ai baza ‘ayi haka ba nariga nayi mata bayani ‘dazun ai kuma ta fahimta_ ”
Mahmud kam shiru yayi yana sauraransu yariga da yasawa ransa cewa ze taimaka musu cikin abinda Allah ya hore masa, so ko matar nan zata na dukansa tana koransa ne ba ze fasa ba.
Ku’di masu yawa Mahmud yaciro ya mi’kawa Umar shikuma ya bawa Rabi’u yace ya nemo masu gyara su ‘dan ‘kara tsayin katangar gidan saboda rufin asirin masu gidan, sannan yaciro wannan ku’din da malam ya’ki kar6a ya mi’kawa matar yace wannan sadaka ce taringa siyawa yaran abinci me kyau suna ci ba irin wannan ba, sannan kuma ta na siya musu omo da sabulu sunayin wanki akan lokaci, yace karta damu da ‘karewar ku’din insha Allahu ze dawo ba da’dewa ba ya sake dubasu.
Kuka matar tasaki tare da godiya ta ‘dago kudin ta ri’ke ahannunta hawayenta na sau’ka akansu yayinda yaranta duk suka matso sukayi jigum agefenta suna kallonta.
Tun bayan rasuwar maigidanta yauce rana ta biyu da wasu suka dube su da fuskar rahama, inka ‘dauke masu basu zakkar abinci na kowacce shekara idan lokacin sallar azumi yayi Rabi’u ne mutun na farko daya taimakesu kuma yake kan taimaka musu aduk lokacin daya samu dama, domin har yau be ta6a fasa taimaka musu ba, aduk lokacin daya samu canji yakan kawo musu ku’di wataran har ledan taliya yakan siyo yakawo musu yace su dafa suci, randa hakan be samu ba kuwa yakan basu har naira ‘dari yace su sayi wani abin dashi.
Atarihin rayuwarsu bazasu ta6a mantawa da Rabi’u ba, na biyunsa shine yau da wa’dannan bayin Allah suka zo suka taimaka musu, cikin kukan taketa jero musu addu’ah, ” _Allah ubangiji ya saka muku da alkhairi ya haskaka rayuwarku, Allah yasa ku gama_ _da duniya lafiya, kamar yanda kuka ji ‘kanmu kuka taimake mu_ _Allah ubangiji ya ji ‘kanku kuma ya………._
Da ” _Ameen_ ” kawai suke ta amsawa. Sai da suka mi’ke sazu tafi ne sannan Mahmud ya kalli yarinyar dayaji ‘dazu mahaifiyarta ta ‘kira ta da suna meram yace ” _mamana ana zuwa makaranta kuwa?_
Sai data juya ta kalli bayanta dan ganin koda wa yake maganar ganin saitin ta yake kallo sai taga babu kowa agurin illah ita ka’dai, da kai ta amsa masa alamar ” _ah’ah_ ”
” _islamiya fah_ ?
Yasake tambayarta
Nanma ta’kara jijjiga masa kanta wanda manufar amsar duk ya bada ma’anah daya.
” _meyasa haka toh_ ”
Yayi maganar tare da ya hannu.
Kafin meram tayi magana se mahaifiyarta tariga ta yin maganar da fa’din
” _kayyah ‘dannan abincin daza’a ci ma daya aka samu, gagararmu yakeyi ballantana har_ _asamu ku’din biyan makaranta, wannan dakake gani……._
Ta nuna Rabi’u sannan tacigaba da fadin ” _shi ka’dai yasan damuwarmu yasan halin damuke_ _ciki, shine akullun yake da burin yagama makaranta domin yasamu abinyi_ _nima kuma shi ‘din nakewa addu’ah yasamu yagama koda baze taimaka mana agaba bama_ _bazanji haushi ba kokadan, domin wanda yayi abaya ma ka’dai ya isa, hakanma ya isa_ _yasa nayi ta masa fatan alkhairi har ‘karshen rayuwarsa, domin Rabi’u mutun_ _ne yaro ne shi amma me zuciyar manya, burina inga Rabi’u yasamu abinda_ _yake so, amma inbashi ba mukan ai tamu rayuwar daban take, ba wai dan bandamu da_ _rashin karatun yaran bane ah’ ah kawai dai inaga kamar mu’din haka Allah yaso ganinmu shiyasa ya yomu daban, kaga kuwa ai bazamu yi shishshigi wa lamarin ubangiji ba_ “
” _hakane kam Innah amma ai ba a yanke kauna da rahamar ubangiji domin idan yaso_ _akowani lokaci ya kan iya sauya ma rayuwa, kuma kinga zama hakan ba ilimi ai babu da’di_ , _duk da Allah ne dakansa ya halicci mutane iri daban daban amma kinga ta 6angaren_ _neman ilimi be bambanta mu ba yace ne kowa ya nemi ilimi………. amma bakomai_ _nafahimci sosai…….yanzun muna kan hanya ne, da iznin Allah zan sake dawowa_ _kwana kusa insaka mamana amakaranta_ ”
Ya dubeta yace ” _ko_ _bakyaso_ ?
da murnarta ta bu’di baki tace ” _inaso_ “.
” _Yauwa Mamana sai dawo ko_ “
Yafa’da tare da juyawa suka nufi hanyar fita matar nasake zuba musu ruwan albarka da godiya har suka 6acewa ganinta.
Story continues below

Rabi’u ne ya rakasu har gurin motarsu, wanda anan Mahmud ya ciro card ‘dinsa yabashi yace ze iya nemansa idan ana da bu’katar wani abu kafin yadawo ‘din ko kuma idan ku’din daya bashin suka gaza yin aikin yace ya’kirashi.
Sannan ya ‘kara ciro 10 thousand yabawa Rabi’un yace wannan nashine ya ri’ke agurinsa.
Rabi’un ma godiya yayi yana ‘daga musu hannu har motar tayi nisa ya daina hangosu.
Katin ya tsaya yana kallo aransa yake tunanin dama ashe har yanzu akwai irin mutanen nan ne aduniya, lallai kuwa Allah yayi gaskiya ha’kuri nada riba watarana, gashi yau ha’kurin innah yayi mata rana.
Allah ubangiji yasaka musu da gidan Aljannah ya biya musu bu’katunsu na alkhairi ya ‘karashe da fa’din haka.
Mahmud tasha suka zarce suka nemi motan zuwa kano shi Umar, gidan kakansa Alhaji muhammad ya nema.
Alhaji muhammad ba ‘karamin farinciki yayi da zuwan jikan nasa ba hakama matarsa, sosai suka rin’ka nan nan dashi, kamar su goyashi, Mahmud kansa yaji da’din hakan harma yakeji aransa dama tun farko agurin kakan nasa yatashi dayafi masa yanzun ma jiyake kamar karya tafi badan yabaro aikinsa da kuma matarsa ba da babu abinda zai sa shi komawa lagos.
Gidan ‘yan uwan Anty kaf sai da ya zaga ya gaidasu kowa na farin ciki da ganinsa, musamman ma dashi ‘din suka ga sam beyi halin ‘yar uwar tasu ba hakan yasa suka ‘kara sonshi fiye ma da mahaifiyar tasa.
Kwanansu biyu suka wuce ‘kauye gurin danginsu na can, wato ‘yan uwan mahaifinsa, nan ma haka suka ta hidima dashi kowa na tambayarsa iyalinshi da iyayensa, kafin yatafi sai da yabi yaraba musu ku’di 100k ma dukkansu mazan dayake lokacin damina ne sai yace suyi aikin gona dashi.
Hakan dayayin ba ‘karamin farin ciki ya sanya azu’katansu ba, nan kam be kwana ba aranar suka wuche kuma ko tsaraba ‘kin kar6a yayi yace bagida suka yi ba tukunna kuma kayan zai zama musu damuwa ne tunda motar haya suke hawa.
‘Karfe hu’du na yamma suka baro ‘kauyen suka dawo kano.
Da ‘kyar suka sami flight ‘din da zai sau’ka a Lagos da daren ranar, dan haka suka je suka gabatar da salllolinsu kafin nan.
‘Karfe 11pm suka sau’ka acikin garin Lagos ganin dare yariga yayi yasa suka wuche gidan Mahmud suka kwana acan sai washe gari da safe suka shirya suka fita atare inda Mahmud ke jan motar Umar na gefensa.
Dayake ma already Teemah tasan da dawowar shin so tun dawuri tagama ha’da kayanta suna zuwa bawani 6ata lokaci tabi mijinta suka wuche gidansu amma zuciyarta cike da kewan matar Umar da ‘yaranta musamman ma little Amal.
Aranar Mahmud beje shi ko’ina ba acikin gidansa ya wuni dayake ma ranar takama ranar asabar ce shiyasa ma be fitan ba, sai da akayi sallar azahar kafin yafita yaje masallaci yayi sallah daga nan yawuche gidan mahaifinsa.
*****
Washegari kuwa tunda sassafe suka tattaro inner wears ‘dinsu gaba ‘daya wa’danda basu sawa a loundry machine suka wanke atare, Teemah natayi masa dariya wai be iya wanki ba, itanma bawani iyawa tayi ba amma yanda taga Mahmud ‘din keyi sai yana bata dariya shiyasa take ganin kamar tafishi iyawa.
Kasuwa suka shirya suka tafi bayan sungama wankin, sukayo siyayya ni’ki-ni’ki tarkacen kayan abinci.
Dangin su stock fish, ice fish, naman kaza dana ‘karamar dabba, cry fish, ganyen su oghou, tarkacen fruits da sauransu kaya de dayawa suka siyo.
Atare suka shiga kitchen suka adana komai a inda yadace nasawa a fridge suka saka na , ajiyewa haka duk suka adana abinsu.
Fruits salad Teemah ta ha’da musu mai da’di suka sha aranar wanda shi ka’dai dasuka sha basu ‘kara neman abinci ba har sukayi bacci.
Story continues below

Washe gari tunkan yagama shirinsa Teemah ta shirya ta yi zaman jiransa yagama nasa shirin, suna gama yin breakfast yatashi da niyyar tafiya anan Teemah ma ta ce itafa bazata iya zama agidan ba gaskiya tsoro takeji sai de sutafi tare, bayason ta 6ata masa lokaci dan haka yace toh sutafi .
Gidan Umar yakaita daga nan yawuche wurin aikinsa.
Matar Umar ta’danyi mamakin zuwan Teemahn amma bata tambayeta dalili ba haka suka wuni abinsu dan yanzu kam Teemah tariga da tasaba dasu sosai.
Da yamma Mahmud yabiya ya ‘dauko ta suka dawo gida.
Mahmud kansa yanzu yana mamaki yanda yake samun damar yin baccinsa cikin natsuwa da kwanciyar hankali tun bayan da ya fara amfani da magungunan da aka ha’da mai, yanzu kam Alhamdulillah, dan ko jiya da Teemah ta tashi cikin dare ma dakansa ya farka dayaji motsinta, gashi yauma har ya kwanta suna hira da Fateemahn sa6anin da da yana ‘dora jikinsa akan gadon zaiji wani bacci me shegen nauyi harma baya sanin lokacin da baccin yake ‘daukansa.
Labarin duk abinda yafaru wajen tafiyar sa yake bata, na yanda yaga wannan matar da ‘yarta dama duk abinda yafaru agidan yace tausayin matar da yaranta yakasa barin zuciyarsa, duk lokacin dayasamu chance zai koma yasake duba su, Teemah najin haka tace itama zata bishi tana so tagansu itama.
Be musa taba ya amince, dan yasan ko yace baza bishi bama ba yadda zatayi ta zauna agidan ita ka’dai ba dan haka gara yatafi da abinsa yafi masa.
haka suka ci rabin satin yana fama da ita, sam ta’ki zama agida kuma ya kaita gurin Anty ta’ki, sai de ko su tafi office ‘din tare ko kuma ya kaita gidan Umar.
Sosai abin yafara isansa yarasa takamamman dalilin dayake sata wannan abin while ada da bata saba bama bata yi masa haka, ya tambayeta kuma sai de tace bakomai kawai tana tsoro ne.
Toh tsoron na menene sam yarasa.
Anty Chiddy kuwa zuwa yanzun hankalinta sam ya daina kwanciya da rashin samun Fateemah, domin tagama saka rai da samun yarinyar sai gashi kuma bata samunta agida, kullum bata nan tarasa ina take zuwa, gaba ‘daya ta ‘dora ranta akan yarinyar har hakan yasa ta sallami yaran datake hul’da dasu ganin tasamu sabuwa.
Tayiwa Anty maganar ma kuma duk abanza dan da kunnanta taji ranar da Mahmud yake fa’din wai ai islamiya take zuwa shiyasa bata zama agida.
Da yamma kuma ai Mahmud nagida babu damar taje.
Daga baya sai tayi wani tunani wanda take ganin shine dai-dai, ta yanke shawarar kawai gara tasa ayi mata kidnapping yarinyar taje ta 6oyeta sai ta gama abinda zatayi da ita sannan tadawo musu da ita gida.
Wannan shawaran ita ka’dai tayishi azuciyarta ko Anty bata sanar mawa ba, domin dama kawai tana yaudarar Anty ne akan zata kaita inda za’a warware auren bawai dan tana da tabbacin hakan ba, dafarko taso ta samu kan Anty ne sai kuma ta’ki amincewa da ita suna cikin haka kuma saita yi arba da amaryar Mahmud yarinyar sai ta gama tafiya da imaninta taji kaf duniyan nan ita ka’dai take da burin kasancewa da ita shiyasa plan ‘din yadawo kan Teemahn madadin Anty, sai gashi kuma itama Teema tana neman fin ‘karfinta ita kuwa bazata iya ha’kura da ita ba sam.
*****
Haka yauma Mahmud suka fito daga gida shida Fateemah ya sau’keta agidan Umar yatafi wurin aikinsa.
Abin nabawa matar Umar mamaki na yanda Teemah take ‘kin zama agidan mijinta ta gwammaci zama agidan mutane domin tariga tasani Teemah bata son zama agida, matu’kar bata gidanta toh Mahmud yawuche office da ita, dan haka yau ta yi ‘damar sanin dalilin hakan bawai dan ta gaji da zama da ita ba, sai dan kawai ta gyara mata kuskurenta domin tasan Mahmud bazai ta6a jin da’din hakan ba sai de yabiye mata kawai saboda jin da’di da farin cikinta, sam babu namijin da za’a ce matarsa bata son zama agidanta kuma yayi farin ciki da haka.
Story continues below

Koka’dan bata ta6a canjawa Teemahn fuska ba aduk zuwan datakeyi saima ta’kara jawo ta ajiki tare da bayyana mata wasu sabbin abubuwan da suka shafi zamantakewar aure, wanda zuwa wannan lokacin sosai Teemah tayi nisa da sanin menene shi auren kansa takuma gane irin zaman da sukeyi da Mahmud ‘din daban yake da kowa.
Gata da jarabar son yara musamman ma yarinyar Umar ‘yar karamar da bata wuce 1yr da haihuwa ba ( Amal), kullun idan tazo yarinyar najikinta, ita take mata kitso kullun
watarana jitake yi kamar tatafi da ita gidansu.
Matar Umar nayi mata dariya amafi yawancin lokuta idan taga tana ‘ko’karin goya yarinyar amma kamar wata me wasan yara sam bata iya ba.
Takance da ita
” _zanga ranar da zaki goya naki’ dan ai Fateemah gaskiya zansha dariya in ‘koshi_ “
Sai Fateemah cikin za’kuwa tace mata ” _da gaske nima maman Amal zan haihu na sami ‘dana da ‘yata watarana_ ?
” _Zaki haihu mana lokacine ai, in Allah ya yarda kamar yau_ _ne_ “
Fateemah na matu’kar jin da’di idan taji ance zata haihun nan har ta ‘kagu taganta da babyn ta itama.
Matar tana so tayiwa Teemah magana amma kwata kwata tarasa ta ina ma yakamata tafara dan tasan ko ayaya tayi maganar zai iya bada cewa tagaji ne da zuwan Teemah gidanta itakuwa bahaka bane manufar ta burinta Fateemah ta kasance mace ta gari abin alfahari agidan aurenta.
Duk wani motsinta tanayi ne da tunanin yanda zata fara tunkarar Teemah batare data jahilci niyyarta da manufarta ba.
Bayan sunyi sallar azahar sunci abincine da suka gama matar Umar take ce da Fateemah ” _yanzu idan Mahmud yadawo gurin aiki_ _me zaici_ ”
” _bakomai_ “
Fateemah tabata amsar tambayarta atakaice.
Sai tasake fa’din
” _kode shima irin kinne duka bakusan cin abinci hala_ “
” _Ah’ah maman Amal muna ci mana harma shi yafini!_
” _Toh meyasa bazakiyi zauna agida kiyi masa girki ba”_
Fateema Sai cewa tayi
” _shima yasani bana gida ne da ina nan zanyi masa ai_ ”
” _Me yasa toh bazaki zauna agida kiyi masa ba, Fateema kinsan kuwa ‘dimbin ladan da_ _mace ke samu idan tayiwa mijinta hidima yaji da’di?” inji matar Umar_ .
Narai-narai Fateemah tayi da idanu tace ” _Allah ni Maman Amal tsoron zama agidan nakeyi ni ka’dai shiyasa_ ”
” _daurewa zakiyi kinji ahaka sai kiga kinsaba, amma idan kika ce bazaki na zama ba toh yaushe_ _zaki saba Fateemah_ “
Shiru Fateemah tayi tana tunanin taya za’ayi ta zauna agida bayan Anty da ‘kawarta so suke su maida ita ‘yar ma’digo tace gara tayi ta yawo agurare data zauna agida su tarar da ita har zuwa ranar da daddynta zaizo sai su tafi abinsu yafi mata.
Ji datayi matar Umar nasake lalla6a ta akan taringa zama agida yasa ta fayyace mata duk abinda ke faruwa, wanda ya matu’kar ‘dagawa matar Umar hankali fiye da zaton mutun , abin ya kulle mata kai dataji cewar mother in-law ‘din ta ce ke jagorantar abin, wannan wani irin al’amari ne haka.
Fateemah dataga hankalinta yatashi tana ta maganganu sai tace mata tayi shiru dan Allah kar kowa yaji tasake tunatar da ita cewar Anty tace kashe ta zatayi idan tafa’di maganar wa wani tace dan Allah karta fa’dawa kowa.
Jinta kawai matar Umar tayi domin bazata iya yin shiru akan maganar ba sam dole ne Mahmud yaji domin ya ‘dau matakin daya dace tunda kam mahaifiyarsa ce, ze iya dakatar da ita.
Koda Mahmud yazo ‘daukan Fateemah kuwa cikin sa’a sai be shigo ba horn kawai ya danna mata daga waje dayake tunkan ya ‘karaso yake ‘kiranta ya sanar da ita.
Fita tayi ta sameshi suka tafi.
Matar Umar kuwa yanda maganar ya tsaye mata arai yasa takasa ri’keshi har sai da ta sanar da Umar komai.
Umar kansa yayi mamaki, ya de san Anty bata son auren Mahmud da Fateemah amma be ta6a zaton ‘kiyayyar Anty har yakai haka ba, domin be ta6a zaton Anty zata nemi lalata rayuwar yarinya ‘karama irin Fateema ba.
Umar har gani yayi dare yayi masa tsayi dan kawai yanda ya ‘kagu gari ya waye ya ha’du da Mahmud.
Mahmud kuwa tunda ya ‘dauko Teemah sai yaga kamar ba’a daidai take ba haka dai ya ‘kyaleta yana karantar duk yanayinta, har kusan ‘karfe 8 na dare bata dawo daidai ba, tana kwance akan 2 seater yayinda shi kuma yake zaune daga gefenta ta ‘dora kanta akan ‘kafarsa tayi shiru, sai alokacin ya tambayeta meke damunta.
Shiru tayi masa kamar bata ji abinda yace da ita ba, sai ma tayi yun’kuri ta tashi ta wuche bedroom, bayanta yabi da kallo har ta shige ciki, jijjiga kansa yayi tare da dawo da hankalinsa kan labaran da yake kalla.
Minti shabiyar be ‘kara ba yatashi yabi bayanta bayan yakashe dukkan swich ‘din, domin gaba ‘daya daina fahimtar labaran yayi zuwa wannan lokacin hankalinsa gaba ‘daya ya tashi da ganin Fateemahn ahaka, ya tabbata akwai abinda ke damunta.
Koda ya shiga ‘dakin akwance yasameta dan haka sai ya wuce bathroom tsawon mintina biyar kafin ya fito yadawo kusa da ita ya zauna wanda tana ganin hakan tawani lumshe idanu kamar me bacci.
Duk ya kula da hakan dan haka sai yayi murmushi kawai tare da ‘kiran sunanta ahankali, sai da ya ‘kira ta kusan sau uku kafin ta amsa kamar me yin baccin gaskiya.
” _Tashi maza ki zauna tambayarki_ _zanyi_ ”
In a serious tune yayi maganar dan haka dolenta tami’ke zaune badan ranta naso ba.
” _meke damunki ne wai yau ‘dinnan please Fateemah banason ganinki a_ _irin wannan yanayin koka’dan, gaya min_ _kinji_ ”
ahankali tace
” _bakomai fah yayah ni babu abinda ke damuna_ ”
” _me ‘karya_ “
ya fa’da da sigar zolaya.
murmushi kawai Teemah tayi masa .
” _Haba akwai mana, nasani akwai abinda ke damunki_ ……..”
Yana fa’da yana murmushin shima.
” _Allah yayah babu komai_ “!
Fateema ta tareshi da fa’din haka.
Shiru yayi ya zuba mata idanu ita kuwa sai tayi ‘kasa da idanunta tana wasa da yatsunta.
Mahmud kwata-kwata kansa ya kulle ma yarasa ya zaiyi da ita.
Hannunsa ya mi’ka yakamo nata hannun datake wasa da shi ‘din yace mata
” _me kike so toh gaya min kinji, i promise ko menene zanbaki shi_ ”
Jikinsa ta dawo ta kwantar da kanta akan kafa’darsa tayi shiru tana tunanin _toh me ma zatace dashi_ ?
Ganin tayi shirun ne yasa Mahmud yasake ce mata
” _gaya min mana Fateemah karkiji tsoro kinji_ “
Murmushi tayi data tuno hirarsu da matar Umar ‘dazun sai ta ‘daga kanta ta kai bakinta kusa da kunnansa ahankali tace ” _Yayah kasan me nake so_ ?
Jijjiga kansa yayi alamar ” _ah’ah_ “.
” _Ni baby nakeso_ “.
Tafa’da tana murmushi tare da komawa daga bayansa ta 6uya.
Mahmud kam mamaki ma hanasa magana yayi kawai ya bude baki tare da zaro idanu.
Tausayin ta ne yakama shi dan yasan kamar yanda bakinta ya furta hakan toh ko cikin zuciyarta ma hakan ne, kuma duk wanda yace ma yanasan ‘da toh yana so ‘dinne da dukkan zuciyarsa, saboda soyayyar ‘ya’ya ‘ka’k’karfar soyayya ce dake wanzuwa azu’kanta dukkan iyaye.
Juyawa yayi gaba ‘daya ya fuskance ta sai ta fara ‘ko’karin guduwa daga inda yake.
Hannu Mahmud yasa ya dawo da ita inda take zaunen sai tayi maza ta me da kanta ‘kasa yanda baze ga fuskarta ba, ‘kafafunsa dake tan’kwashe ta kifa kanta akai tana murmushi, hannunta kuwa ri’ke acikin nasa.
Hakan kuwa datayi sai yasa Mahmud baya ganin komai sai bayanta.
Shima murmushin ne ya kubce masa yana murza yatsunta dake hannunsa yace mata
” _kinsan cewa abin kunya ne meyasa dama kika fa’da_ ?
Luf tayi ta’kiyin ko motsi kamar ma bada ita yake maganar ba illah murmushin data keyi ‘kasa-‘kasa.
Kunyan iyayin nata ba karamin birge shi yake yi ba, aransa ya yanke shawaran gara kawai ya gaya mata gaskiyan abinda ke faruwa dashi tunkan shirun nashi ya ‘kurewa ha’kurinta.
Mahmud jan jikinsa yayi ya jinginu da jikin gadon ya lan ‘kwashe hannunsa akan ‘kirjinsa tare da mi’kar da ‘kafafunsa wanda hakan yabawa Fateemah daman kwantar da kanta da kyau akan ‘kafafun nasa tana kallon gefe, har yanzu ta’ki ta kalli inda yake ma balle har su ha’da idanu dashi ita adole kunya takeji.
Mahmud ne yafara magana da fa’din
” _Fateemah kinsan kwanan nan nayi tafiya ko_ ?
Shiru tayi masa taki yin magana, shima yasan bazata tanka sa ba dan haka sai yaci gaba da maganarsa.
” _Daga Umar abokina babu wanda yasan dalilin tafiyar danayi wacce nayi ta ne dan neman magani wa matsalar data same ni da ni kaina bansan_ _takamamman lokacin da hakan ya faru ba, daga zuciyata sai Umar sai kuma ke da zan sanar dake ayanzun bayaga haka babu wanda yasan abinda ke damuna. Fateemah ada na kasance mutun ne ni lafiyayye ta ko wani 6angare wanda ni kaina na shaidi hakan bana bu’katar sai nayi_ _wani dogon nazari akan haka, dai-dai da rana ‘daya ban ta6a tsintar kaina cikin wata matsala_ _acikin jikina ba, wanda badan nasan hakan ba da babu abinda zai sa in amince da batun auranki, bama ke ba koda kuwa wata_ _macece daban bazan taba yadda in aureta ba ko dan gudun kar na shiga hakkinta_ _ma_ .
_Kwatsam bayan aure na dake sai na tsinci kaina cikin wani hali, halin da baze ta6a barina in rayu da iyalina cikin kwanciyar hankali ba, nakan gode Allah amafi yawancin lokuta daya sanya kece kika kasance mata agareni ba wata daban ba, wanda na tabbata da wata daban ce da yanzu mun da’de da samun matsala da ita ko ma mun_ _rabu, saboda ba kowacce mace bace zata iya zama dani ahaka yanayin da nake mu zauna cikin rufin asiri ba sai ko in nayi sa’a_ , _kinga ke kuwa kin zauna dani ahakan baki ta6a nuna min damuwarki akan haka ba baki ta6a_ _nuna min_ _gazawarki ko canjin fuska akan zama dani ba duk da nasan ba asan ranki bane, ni da kaina_ _nasan kina da bukatar kasancewa da mijinki alokuta da dama ba sai an_ _sanar dani ba ni ni shaida ne akan wannan.Fateema_
_kinga ko awannan 6angaren ma ka’dai dole in godewa Allah na tare da yabawa da za6in_ _Abbah na, domin shi yayi ruwa yayi tsaki wajen ganin kin kasance mata agareni. Ko_ _yanzun ma banyi mamaki ba dan kince kinada bu’katun baby_ _domin nasan wannan shine burin dukkan ma’aurata, ni kaina Fateemah inason baby amma_ _ayanayin dana tsinci kaina kinga dole ne na ha’kura na sanyawa_ _zuciyata salama har zuwa lokacin da Allah ya bani lafiya inda rabona sai kiga yabani”_
Story continues below

Hannuntan yasake kamawa ya rike cikin nashi tare da ran’kwafo da kansa kusa da nata kan sannan yaci gaba da maganarsa.
” _Fateemah kema ina so kiyi ha’kuri kinji kitayani ro’kon Allah ya bani lafiya cikin gaggawa_ _wala Allah ko zamu dace dasamun farin_ _cikinmu_ “
Yana kaiwa nan yasa hannunsa yadafa kanta sai ta juyo ahankali ta kalleshi, take kuma sai ta kauda kanta da barin kallon shi, ita bazatace ga yanayin datake ciki ayanzun ba domin maganganun Yah Mahmud gaba ‘daya sun karya mata zuciya tama rasa tunanin me zatayi kwata-kwata, data san hakane ma da bazata kawo maganar babyn ba, ashe ita bata sani ba ashe matsala ce dashi har da take ganin kamar wai shi daban yake harda cewa matar Umar cewa su ba irin zaman dasukeyi ba kenan dashi, batasani ba ashe sirrin aurenta ta fitar.
Mahmud kuwa hannunta dake acikin nasa ya kallah tare da ‘dora ‘dayan hannun nasa ya lullu6e natan dashi sannan ya ‘kira sunanta ahankali.
Kallonsa tajuyo tayi batare datayi magana ba jin yanayin da ya ambace tan cikin slow voice da sanyi, shima Mahmud be saurari jiran amsawarta ba ko hankalinta data bashi ma ka’dai ya wadace shi sai yace.
” _Fateemah……ki yafe min_ _kinji……kiya femin dan Allah nasan ban kyauta miki_ _ba koka’dan ban miki adalci ba dana zauna dake ahalin danake ciki, amma inaso kisani banyi_ _haka dan na ‘kuntata wa rayuwarki ba koka’dan face_ _dan rufin asirinmu dana mu, kuma insha Allahu inasa saran samun sau’ki acikin kwanakin_ _nan…….ki daure dan Allah ki taushi zuciyarki ki yafe min hakkinki dana kasa sauke miki a iya zamanmu_ _dake kinji………_
Da sauri ta ‘kwaci hannunta ta tashi ta toshe mai baki da hannun nata sai suka tsaya kallon kallo dashi, kanta ta jijjiga masa ahankali tare da fa’din
” _Ni baka min komai ba yayah kuma nasan har abada bazaka_ _ta6a yin wani abu dan ka cutar dani ko rayuwata ba, don Allah ka daina_ _neman gafara ta kaji Yayah_ !
_Kaifa kace ka godewa Allah da ya sanya nice matarka_ , _toh ni me yasa bazaka bani dama ingode masa ba da ya Yah Mahmud yakasance_ _shine miji ba agareni, dan kawai Allah ya jarabcemu da wata kaddara sai hakan_ _ya sanya ka neman yafiyata?, toh in hakane Yayah ni agurin nemo_ _yafiyar_ ?
Hawaye ne yaji suke shirin gangaro masa saboda yanda kalaman nata suka ratsa shi, da sauri ya janyo ta ya rungume ta acikin jikinsa sannan ya lumshe idanu take hawayen nasa suka ‘karasa gangarowa suka sau’ka akan wuyan Teemah.
Akan la66ansa ya furta ” _Allah ya miki albarka matata Allah ya albarkaci rayuwarki duniya da lahira_ “
Yana gama fa’din haka sai ya rintse idanunsa da ‘karfi tare da sake matse ta ajikinsa tamkar wani na shirin ‘kwatarta.
Damshin dataji asaman wuyanta ne yasa ta yunkuri ta ‘kwaci jikinta daga nashi ta kalli fuskarsa sai taga still yana hawaye.
Da rawar murya ta furta ” _kuka kakeyi_ _Yayah_ ?
Yatsansa yasa ya rufe mata baki alamar tayi shiru sai yasake janyota ya rungume ta akan kirjinsa tare da gyara zaman nasa zuwa kwanciya yayinda idanunsa ke kallon ceilling fan ‘din dake saman ‘dakin, Fateemah kuwa kanta akan kirjinsa ta kwanta tayi shiru itama gaba ‘daya jikinta yayi sanyi.
Hannu Mahmud yasa yana bubbuga bayanta ahankali tamkar wata yarinya ‘karama yayinda yakejin wani sabon yanayi tattare dashi da be ta6a tsintan kansa aciki game da ita ba sai yanzun, ahankali bakinsa ya furta ” _I love u Fateemah, i really love u with all my_ _heart, ha’ki’ka ke daban ce acikin mata, Allah ubangiji yabani lafiya da tsawon rai_ _dan kawai inkula dake da rayuwarki, in cika rayuwarki da soyayya ta yadda bazaki ta6a dana sanin kasancewa tare dani ba_ “
Rasa takamamman yanayin da take ciki tayi alokacin farin ciki ne ko akasin haka kasa ganewa tayi, aru’de ta bu’di baki da niyyar magana
“Ya…….
da sauri Mahmud ya dakatar da ita da fa’din ” _shiiiii_ ”
Story continues below

Take kuwa tayi shiru kamar yadda ya bu’kata ‘din bata ‘kara yin magana ba, shima kuma shirun yayi yana cigaba da kar6an duk wani sa’kon da zuciyarsa ke bashi game da Fateemahn, ahaka bacci yayi awon gaba dasu gaba daya.
‘Karfe ukun dare yaji Fateemah na mutsu-mutsu ajikinsa sai kuwa ya bu’de idanu akanta gani yayi tana sake cusuwa masa ajiki tare da yamutse jikinta guri guda.
Sunanta yafara ‘kira ahankali yana ‘ko’karin tada ita, bata amsa masa ba sai ma kuka data sanya tare da ‘ko’karin janye rigarta tamkar rigar na mintsinin jikinta ne fincika take yi da ‘karfinta kamar rigar nayi mata ‘kai’kayi.
Ganin haka yasa Mahmud ya ri’ke hannun nata sannan ahankali yajanye mata rigar yacire kamar yadda yaga take da burin yi.
Mahmud idanunsa ya ‘kura ‘kur akan ‘kirjinta wanda suka matu’kar tafiya da imaninsa.
Tun aurensa da ita be ta6a tsayawa ya ‘kare musu kallo har haka ba sai yanzun, ha’ki’ka Allah yayi halittarsa awannan gurin.
Hannu yakai da niyyar ta6a wa sai yaji sau’kan numfashinta ahankali, dubansa ya mayar kan fuskanta sai ya ga ma har tayi bacci.
Ajiyar numfashi ya sau’ke tare da hamdala azuciyarsa daya kasance abin nata be ja tsayin lokaci ba yau ‘din.
Fasa ta6awan yayi kawai sai yaja mayafi ya lullu6a mata.
Yana rufa mata mayafin ya mi’ke ya wuce bathroom alokacin ‘karfe uku da mintina ashirin (3:20am) dan haka alwalarsa ya ‘dauro yazo ya tada sallah raka’ah hu’du yayi ha’de da sallamarsa guda biyu sannan ya ‘daga hannu ya dinga zuba musu addu’o’i na kariya da zaman lafiya harma da nemawa aurensu albarkar mahalicci, yana shafawa ya janyo Al qur’ani yafara karantawa kafin lokacin sallah yayi saida ya karance suratul Ankabut sannan ya rufe karatun nasa da suratul Ikhlas, Nasi da Falaq ya shafa da salatin Annabinmu Muhammad ( S.A.W).
Saida yayi raka’atanil fajri kafin ya kawo sallar asubarsa abayanta.
Be tashi agurin ba sai da yayi azkar ‘dinsa na safiya kafin yatashi yaje ga Teemah domin yatashe ta itama tayi tata sallar, alokacinma gari har ya ‘dan fara haske.
Koda yatashe tan ma da ‘kyar ta bu’de idanunta saboda nawin dataji kanta yamata ga kuma bacci da har alokacin be bar idanunta ba, tana daga kwancen ta bu’de idanunta sai kuwa ta hango windo gani tayi gari har ya fara haske.
Da wuri ta mi’ke arazane ganin lokaci yatafi, sai kuwa takoma da sauri sanadiyyan ganin jikinta bakaya.
Mayafin data yaye ajikin tan ta kuma janyo wa ta ‘kara rufe jikinta dashi.
Mahmud yi yayi kamar be ganta ba ya wani fuske ya kauda kansa gefe.
Teemah kuwa baki ta turo gaba tana gunaguni ‘kasa baya ma gane mai take fa’di.
Mahmud kuwa murmushi yayi mata kawai tare da fa’din
” _Gara ma ki bu’di baki ki fa’di abinda ke ranki yafiye miki dan kukkuni ba ze kaiki ko’ina ba_ “
Baki ta ‘kara turawa gaba tana kalle kalle shikuwa sai ya rin’ka binta da kallo kawai murmushinsa na ‘kara yawaita.
Data ga bata samu abinda take neman bane sai ta bu’di baki cikin shagwa6a tace
” _Ni kam wallahi Yayah ka daina ciremin rigata idan ina bacci_ “
Ido ya ‘dan zaro waje yace ” _waye yagaya miki ni ne_ _na cire miki_ ?
Kamar zatayi kuka tace
” _Ehh mana kaine idan ba kaiba wayene naga ni dakai ne kawai acikin gidan_ “
cewa yayi
” _Dan ke da ni ne kawai agidan kuma sai aka ce miki ni ne na cire ko_ ?
” _Toh waye ne yacire min_ ?
Da muryar kuka
ta tambayeshi tana kallonshi.
Story continues below

” kai ya kaudar gefe cikin ko inkula yace ” _toh idan ma ni ‘din ne ai ke kika sani, kece kika ce incire miki saboda tana_ _damunki_ “
Yanzun kam kukan tafara yi masa acikin kukan kuwa tace
” _bawani ni kam wallahi ban fa’di haka ba, kawai dan kaga ina bacci na sai kakama kayi_ _min sharri_ “
Ta ‘karashe da kukkuni ‘kasa-‘kasa tace ” _kawai ka kama ka wani ganewa mutun jiki abanza_ “
Tsayawa yayi yana kallon ta domin ayanda yasan Fateemah sarai yasan da iya gaskiyarta take wannan fitinan babu zancen wasa aciki.
Ita kuwa tana cikin fa’dar hakan ta hango rigar tata daga ‘kar’kashin pillown dake gefenta sai ta sa hannu ta janyo ta still bakinta ature.
Tana ‘ko’karin sawan ta ‘dan saci kallonsa sai kuwa taga ita yake kallo.
Kwa6a fuska ta’karayi tare da tura ‘kafafu kamar wata karamar yarinya cikin sakalcin kuka da takaici tace
” _toh Yayah ka daina kallona mana nii dan Allah_ “
Shima cikin halin ko inkula yace
” _Idona yana cizonki_ _ne_ ?
Ya tambayeta batare da ya kauda idanun nasa akanta ba.
” _Toh ka juya zan saka riga ne fah_ ”
Cewa yayi
” _me kuma za’a 6oye min, kin manta ne nagama ganin komai_ ?
Kukan shagwa6a ta fara tare da dukansa da rigar hannun nata tana ‘kara ‘ri’ke mayafin data kare kirjintan dashi da hannunta daya.
Mahmud kam yana dariya yatashi yabar mata ‘dakin ya koma parlour.
‘Karfe shidan safiyar ranar Hannah ta danno mata ‘kira alokacin ma ko tashi akan sallaya batayi ba jin ‘karan wayan ne yasata ta tashi ta ‘dauko ta.
Ganin Hannah ce ke ‘kiran yasa ta zauna abakin gado tare da amsawa.
Gaisawa suka yi Teemah ta tambayeta Ummah da lafiyarta.
Hannah kuwa tace da Teenahn
” _Ai itace ma tasa na ‘kiraki tun jiya ta damu akan na ‘kiraki wallahi, wai bata ce idan kin dawo gida ki ha’data da Mahmud_ _bane shine taga shiru har yanzu baki ‘kira ba shiyasa ta damu_ “
Teemah Cewa tayi da Hannah
” _ke nifa babu inda naje dama shirin ‘karya nayi dan nasan idan akaji hakan za’a sanar dani abinda ke faruwa dasu Mummy, kuma baga shi ba ‘karyata tayi min rana nayi waya dasu mummy harda daddy ba, amma fah dan Allah Hannah karki fa’dawa Ummah haka kawai kice mata wayata bata shiga ne kinji_ “
Dariyar mugunta Hannah tayi tare fadin
” _Na yaushe kuma yarinya kin makara ai Umnah kan gata nan agefena_ .
“
Ido Fateemah ta zaro waje tace da Hannahn ” _dan Allah dagaske_ ?
” _ko de inbata wayar ne ‘kilan zaki fi yadda….._
‘Kit Fateema takashe ‘kiran tare da kashe wayar ma gaba ‘daya tana rufe baki kamar Ummahn na gefenta.
Aranar ma da Mahmud zai tafi aiki binsa tayi ya sau’ke ta agidan Umar, shikansa yana ‘dan jin kunya yanzun da yawan zuwan Teemahn gidan be san da me zasu fassara hakanba, kuma kar yazamana yawan zuwan Teemah gidan ya kasance yana cutar da matar Umar, shikansa bayason hakan amma be san yadda zeyi ya dakatar da ita ba.
Domin koda yace zai kaita gidan Anty ma ba yadda take ba har intaji hakanma sai yaga tafi rikicewa fiye da idan yana ro’kon ta akan ta zauna agida, kuma shi aganinsa ai gidan Anty yafi tunda ko ba komai gidan mahaifinsa nan ne gadaransa .
Wannan sabon salon Teemahn na ‘daure masa kai matu’ka yanda fir ta tsani zama agida yanzun be san dalilin ba amma shi bayajin da’din hakan ko ka’dan.
Haka ya isa office zuciyarsa cike da tunani.
Yana zuwa ko zama beyi ba Umar yatare shi da wani sabon batun daya kusan juya mai ‘kwa’kwalwa, jiyayi badan abakin Umar abokinsa maganar ke fitowa ba da babu abinda zai hana yayi wa wanda yafa’da ‘din mugun dukan da sai yaga stars a idanunsa.
Amma dayake Umar ne sai kawai yayi shiru yana sauraransa ransa kuwa gaba ‘daya a6ace yake jinsa, daga ‘karshen ma daina fahimtar komai yayi yade yi shiru ya zuba wa bakin Umar ‘din idanu motsin da bakin yakeyi ka’dai yake iya gani.
Har Umar yayi yagama maganar be tankasa ba sai da ya matso ya dafa kafa’dunsa yace
” Ban fa’da maka maganar nan dan in tozarta ka ba Mahmud face dan kawo gyara wa lamarin, kai da kanka ka zauna kayi nazari akan haka inajin dakanka zaka fahimci gaskiya, ni kaina naso nayi jayayya kan maganar amma idan kaduba yarinyar nan ka kula da tsanar zama agida datakeyi ita ka’dai shika’dai ma ya isa yasa ka yadda cewa akwai wani abin a’kasa, inaso kabi ahankali harka gano asalin meke faruwa kuma suwaye ne suke shirin yi mata hakan”
Umar nagama fa’din haka ya juya ya fita ya bar Mahmud zaune saroro yana tunani.
Jiyayi komai ma ya tsaya masa cak, waye…..waye da wannan mugun nufi akan Fateemah,Tunaninsa yakasa bashi ko waye ne.
Haka ranar ya wuni a office be tsinana abin kirki ba, koda ya biya ‘daukan Teemah ma jikinsa duk da sanyi ita kanta Teemahn sai taji wani iri babu da’di sanadiyyar ganin Mahmud ‘din ahaka.
Zaton ta ko abinda tamasa da safe ne ya6ata masa rai shiyasa har yanzun be sau’ko ba, amma ai da zasu fita gida ba haka yake ba alokacin har tsokananta yake yi ma.
Shiru tayi tana satan kallon shi lokaci zuwa lokaci shikuwa gaba ‘daya hankalinsa akan tu’kin dayake yi ya mai dashi wanda hakan yasake rikita zuciyar Fateemah sam takasa samun natsuwa.
Koda suka koma gida ma harkokin dake gabansa kawai yayi yayin da Teemah kuwa hankalinta duk yana wajensa sam bata jin da’din yanayin Yayan nata ayau.
Har se da akayi sallar maghrib bayan ya dawo gida daga masallaci ya zauna a parlour wanda jin motsinsa yasa ta fitowa tazo gefensa ta zauna tsabar yanda hankalinta yakasa kwanciya ma ko hijabin datayi sallar bata cire ba
Fuskar tausayi tace ” _Yayah nayi maka wani laifine_ ?
Shiru yayi beko kalleta ba.
Sai tasake fa’din
” _Pls Yayah kayi ha’kuri toh ka yafe min bazan sake 6ata ma rai ba_ “
” _Kaji_ !
Be yi magana ba illah juyowa da yayi ya kureta da idanu, itakuwa kasa tayi da nata idanun ganin yana kallonta, kamar ba zeyi magana sai can shima yajefa mata tambaya
yace ” _Fateemah idan na miki tambaya kinyi al’kawarin zaki_ _sanar dani gaskiya_ ?
Zuciyarta taji ya tsinke duk da bata san tambayar da ze matan ba amma gaba ‘daya sai taji bata son yayi tambayar.
‘Daga idanu tayi sai kuwa caraf suka ha’da ido da Mahmud shikuwa be jira jin amsarta ba yaci gaba da maganarsa.
“Fateemah kigaya min meyasa baki son zama agidannan idan ke ka’dai ce?
Da rawar murya tabashi amsa da fa’din” banace maka tsoro nakeji ba”
” Tsoron me kike ji inason yau ki gaya min”
Mahmud ya fa’da da sauri.
Kame kame tafara tarasa ma me zata ce dashi
sai ni…….ni….tsoron…….
ts
Ganin batada niyyan fa’da masa sai yasake jefa mata tambayar su waye suke zuwa gidan nan idan baya nan.
Da sauri tace
“Bakowa “
Tana rarraba idanu.
Shima ce mata yayi ” ‘karya kikeyi Fateema nasan akwai, ki fa’da min zansa ayi maganinsu kinji, bazan ta6a bari su cutar min dake ba muddin ina numfashi, ko kinfiso kullum ki dinga zama agidan mutane yafi miki akan gidan mijinki?
Shiru tayi tana sauraransa sai ya kamo hannayenta yari’ke acikin nasa da sigar lallashi yace
” _Fateema nifa mijinki ne,me burin ganin farin ciki da walwalarki akowani lokaci, meyasa kika_ _za6i ki 6oyemin damuwarki bayan ni yakamata in fara sanin me_ _kike ciki amma sai de naje naji awani guri Fateema kinajin hakan kinmin adalci_ _kenan_ ?
_nine fah me hakkin kula da duk wani hakkinki da_ _damuwarki ayanzun meyasa bazaki bani wannan matsayin ba_ “
Fateemah kam haushin kanta take ji ayanzun dan tasan da bata nemi jin damuwarsa ba da baze tuhumeta da wannan maganar a dai-dai wannan lokacin har haka ba, ita kuwa ayanzun da jiran zuwan Daddy kawai takeyi me zesa tafa’da masa abinda ke faruwa, kalan aje akasheta kafin Daddy yazo.
Shirun da Mahmud yaga tayi masa ne yasa shi bu’dan baki yana ‘karfafa mata zuciya da fa’din
” _kar kiji tsoro Fateemah karkiyi kokwanto ko shakka dan Allah ki gaya min kinji_ _am always here 4u_ “
Kalmar nan dayafi tsana tasake maimaita, masa wato ” _bakomai fah Yayah in akwai ai zan gaya maka_ ….
Kallonta yayi cikin idanu domin zuwa yanzun haushi tafara bashi
” _Fateemah kina ganin kamar 6oye min damuwarki shine zai kawo miki masalaha acikin_ _al’amuranki ko_ ?
_Shikenan idan hakan kike ganin yafimiki so be it nima bazan damu_ _ba, bazan ‘kara damuwa da irin hakan ba tunda baki san ina shiga_ _lamuranki_ !”
‘Kasa tayi da idanunta da suka cicciko da hawaye tsawon mintina biyu bata ‘dago tasake kallonshi ba, hakan yasa Mahmud ya fahimci cewa bazata sanar da shi ‘din ba kenan.
Tashi yayi da sauri ya tsaya tare da sa hannunsa ‘daya ya naushi cikin ‘dayan da ‘karfi.
Kansa yadafe zuciyarsa na masa suya sam yarasa ya zaiyi da ita, 4d first time arayuwarsa da taurin kan Fateemah ya 6ata ransa, daya san bazata sanar dashi ba da be bari Umar yatafi batare da ya sanar dashi ko suwaye suke neman lalata masa rayuwar mata ba.
Damuwarsa be wuce yasan kosuye ba, domin yana mamaki, tsawon watanni biyu kenan da zuwan Fateema garin Lagos amma be ta6a jin tamasa hiran wasu da tasani anan ‘din ba, kamar yadda yasan bata ta6a fita da sunan ziyartar wani gida ba haka itama bayaga Anty mahaifiyarsa babu wanda ya ta6a zuwa gidan nasu hatta abokansa tun bayan aurensa basu ‘kara zuwa ba, mamakinsa shine ya akayi masu neman nata suka santa, da wani lokaci kuma a ina da har zasu nemi maida masa ita jinsin ‘yan ma’digo.
Story continues below

Toh in dagaske ne meyasa kuma bata sanar dani ba tunda har bata so wanda dalilin hakan nema yasa bata son zama agida, kenan har cikin gidanta suka sameta wannan ai rainin hankali ne.
Tunowa yayi da maganar Umar inda yace wai anmata barazana da kisa ne idan har tashigo da wani cikin lamarin, kenan hakan ne dalilin daya sanya ta’ki ta sanar dani, in hakane kuwa lallai mutanen nan basu da hankali, har yaushe zaka sa yarinya ‘karama irin Fateemah agaba, meyasa bazasu je su cigaba da yin sha’aninsu a iya junansu da suka saba ba har se sun shigar da innocent soul irin wannan a haukansu.
Fita yayi haraban gidan ya ringa gwada ‘kiran wayar Umar amma baya ‘dagawa haushin haka ya ‘kara sa shi jin suya acikin azuciyarsa, jiyake badan dare bane yanzun da babu abinda zai hana shi zuwa wajen Umar ‘din ya tuhume shi sai ya sanar dashi kosuwaye ne, dan yanada ya’kinin Umar ze san wani abu akai tunda har labarin ya iso kunnansa, sai de ayanzun shikanshi baya so ya rin’ka garajen barinta agida saboda rashin sanin me ze iya biyo bayan hakan.
Haushin kansa ma yake ji da shi da kansan be tsanantawa ransa tunanin dalilin dake hana Fateema zama agida ba, ya tabbata daya nutsu ya bincika da kansa wata’kila da tuni ya san meke faruwa,
amma bakomai ko yanzun ma lokaci be ‘kure masa ba, da iznin Allah zai bincika ‘din kuma zai samo su dakansa koda Umar be fa’da masa ba.
Wannan karan kam ba ze yi shiru ba Abbah zai samu yafa’da masa abinda ke faruwa inyaso sai yayi magana a division sukawo masa security ana yi masa gadin gidan a 6oye, kodan ayi saurin kama wa’danda ke da hannu akan lamarin cikin sau’ki.
Umar kuwa ya 6oye wa Mahmud sunan dayaji ne akan lamarin badan komai ba sai dan saboda gudun kuskure, kar yaje kuma bayan yafa’a masa bincike yazo ya nuna bahakan bane yaji kunya daga baya shiyasa ya 6oye masa sunan yafi so idan ma su’din ne toh binciken sa ya nuna masa base yaji daga bakinsa ba, kuma idan ya bincika dakansa yaganecgaskiya zefi yadda da batun sa6anin idan aka sanar dashi baze yadda ba sai kaida ka fa’dan idan kayi wasa kanka fushin zai dawo.
*****
*MAIDUGURI BORNO* *STATE*
Rayuwa yanzu tayiwa Abbas zafi, sam baya ta6a jin da’din duk wani abu dayakeyi, wanda tun farkon auren Mahmud da Fateemah ya tsinci kansa a wannan yanayin, dalilin ma daya sanya shi neman hanya ya taho Barno kenan amma still ya kasa saita al’amuransa, wanda ada yake ganin kamar yin hakan ze ‘dabe masa kaso mafi yawa daga cikin damuwarsa amma sai yaga hakan ya kasa yiwuwa agareshi, be tashi fahimtar Fateemah ce rayuwarsa ba har se da ya tabbatar da cewa yarasa ta, shikanshi be san iya adadin soyayyar da yake mata ba sai da yaji labarin za’abawa Mahmud auren ta sannan ya farga da hakan.
Rayuwarsa bayan auren Fateemah ta kasance ne gaba ‘daya ajuye alokacin komai yakeyi Fateemah ce kawai ke zuwa tunaninsa da idanunsa akowani lokaci, ganinta yakeyi tare da wani da sunan mijinta ne wanda shida kansa shaida ne akan haka.
Ya kan 6ata lokaci yana tunaninta ko kuma yayita kallon pictures ‘dinta dake cikin wayarsa wanda ita kanta ma bata san da zamansu ba, musamman yake yawan zama da wayarsa agefensa saboda yawan ‘dagowa yaga hotonta daya keyi akan lokaci sam baya gajiya, wani write up data ta6a rubutawa ranar da hutunsa ya’kare a Damaturu wannan ma baya ta6a gajiya da karantashi idan yana karantawan kuwa harji yake kamar muryan ta ne ke karatun azuciyarsa tsaban yanda yasata aransa, idan kuwa yazauna yana tuno childish behaviourn ta shi ka ‘dai se de kaga yana murmushi duk kuwa da ‘kuncin da zuciyarsa take ciki amma baya ta6a denying murmushi akan tunaninta, yagama bawa ransa tabbacin cewa Fateema daban take agurinsa, bayaga mahaifiyarsa da Hannah arayuwarsa be ta6a bawa wata mace muhimmanci ba kamar Fateema shikansa ya yadda cewa irin soyayyar dayake matan nan ba me yankewa bace har abada domin ko bayan auren nata ma be ta6a jin soyayyar ta taragu acikin zuciyarsa ba koda da ‘digo ‘daya ne.
Story continues below

Ganin kamar abin na neman illata masa future ‘dinsa ne yasa yanemi hanyar zuwa Borno alokacin har angama cire list ma amma ya nemi asaka shi, wanda kusan kowa idan yaji yana mamaki domin dayawan mutane basu so koka’dan ace sunan su yafito ajerin masu zuwa borno sai gashi shikuma dakansa ma ya nemi asakaya shi, ogansa yaso ya’ki amincewa amma Abbas ‘din yadage ya kwantar da kansa yace ko na 5months ne pls akaishi yagaji da zama anan ‘dinne kuma shima yanaso adama dashi cikin masu karawa da ‘yan ta’addan.
Da hakan yasamu aka sanya sunanshi aciki.
Bayan bikin Fateemah da sati uku Abbas ya gudu Maiduguri, tunda yazo kuwa abubuwa suka so shan kanshi domin har alokacin dai-dai da kwayar zarra zuciyarsa bata sarara masa daga tunanin Fateemah ba, inda yasami sau’ki ma yanzun baya waya da Mahmud saboda rashin network dan Mahmud baya kwana hu’du me kyau batare da ya ‘kira sa ba, wani lokacin sai yaga kamar da gangan Mahmud ‘din keyi masa hakan, domin he can’t deny it, ba’karamin kishin Mahmud yakeji ba har zuciyarsa ya tsani ganin ‘kiran Mahmud awayarsa amma ahakan yake daurewa wani lokacin har shima yake ‘kiransa kafin yadawo Maidugurin kenan.
Rashin hanyoyin sadarwan dake Jihar Borno yasa ya’danji dama dama yanzun yarage masa ne tsakaninsa da zuciyarsa kawai tunda ba zaiji labarin komai daga wurin kowa ba.
Yakan yiwa wayarsa caji duk da batada anfani saboda ba ‘kira yakeyi da ita ba kuma shima babu damar a’kirashi amma dan kawai ya ringa kallonta aciki yasa sam wayar bata rabo da caji, duk da idan ya farga da abinda yakeyi ‘din yakan yi gaggawan bari tare da neman yafiyar ubangijinsa saboda ayanzu amatsayin matar waninsa take, amma he can’t help it baya sanin lokacin da yake zurfafawa atunanin nata ko kuma duba hotunanta da har yau yakasa maye gurbinta azuciyarsa da wa ta.
Yanaji tamkar yagama da al’amarin mata arayuwarsa, tun rabuwarsa da Fateemah be ‘kara kallon wata mace sau biyu bama balle har yamata kallon mata.
Bayaga mahaifinsa dake ta matsa masa akan aure shi kan baya jin kamar ze iya zama da wata mace amatsayin matarsa, ita ka’dai yaso ta ya ‘kaunace ta ita ka’dai yabawa muhimmanci arayuwarsa, ita ka’dai take da gurbi da matsayi babba azuciyarsa kuma baya jin akwai wacce zata maye wannan gurbin har abada.
Wani sa’in yakanyi mamaki domin kafin rabuwarsa da ita yasan already Fateemah nada feelings akansa, amma be san meyasa ta ta amince da auren Mahmud ba, ko dayake wasu soyayyarsu ba guda bace takan rarraba kanta zuwa wani 6angaren daban.
Da yawan lokuta Fateemah yake ‘daurawa laifi dan shi aganinsa da amincewarta ne komai ya wakana badan ta amince ba da yasan daddy bazai ta6a ‘daura mata aure da Mahmud ba, wani lokaci sai yaga kamar da gangan ne taza6i Mahmud akansa danta muzant shi.
Bayan zuwan sa Maiduguri da ‘yan kwanaki ne ya ‘dan fara jin dama-dama azuciyarsa game da Fateemahn badan komai ba sai dan yariga yasawa ransa cewar tabarshi kenan har abada, kuma sai yake ga dama haka ‘kaddarar rayuwarsu tazo kaddara kuwa dolen kowani musulmi ne ko ya so ko ya’ki sannan aikin daya kawo shi maiduguri ma sai ya ‘kara ‘dauke hankalinsa gaba ‘daya daga kan mafi yawan abubuwan rayuwarsa,
abubuwa duk suka rinca6e masa, komai na rayuwarsa yaja baya, be fiya samun lokacin da ze zauna yayi tunanin rayuwarsa ba ko wani abu daban, abinda kawai yasa agaba shine ta’addacin dake bawa jahar borno kashi yake kuma sasu rayuwa cikin ‘kunci da tashin hankali akowani lokaci.
Wannan dalilin ne yasanya komai ma yabar kansa hatta Fateeman yakan wuni ya kwana bata shigo cikin tunaninsa ba, sai yake jin ma hakan yafi masa gara ya fuskanci rayuwarsa ya manta da duk wani abinda ya wuce tunda bashi da ikon canja komai, sai de dukda haka al’kawarin daya yiwa daddy kullun yana cikin ransa so yake abubuwa su ‘dan tsagaita masa yasamu damar cikawa daddyn al’kwarinsa kamar yadda ya ‘dauka, lokaci ne basamu ba amma be ta6a mantawa da hakan ba, yariga yasawa ransa zuwan duk da zuciyarsa bataso amma dole ne yaje Lagos saboda Daddy yafi ‘karfin wasa arayuwarsa.
Story continues below

*****
*LAGOS STATE NIGERIA*
_8:21am_
Munnira ce zaune agefen a kan dinning table Anty yayinda ke siffing tea ka’dan-ka’dan at d same time kuma Anty ke bata ha’kuri tare da sake jaddada mata cewa takusan samun Mahmud a hannu domin Chiddy nasamun abinda takeso komai zai zama tarihi.
Dariya Munniran tayi tace ” _ai na dena damuwa Anty, tunda naje ni aka_ ‘ _kara duba min cewa har yanzu aikina na jikinsu hankalina yakwanta_, _dan nasan kowan nan ka’dai na dogara dashi ma makami_ _ne babba balle kuma ke da kanki kinsa min hannu_ “
Anty ma murmushi tayi tace ” _ke kuwa ‘yar nan wani irin aiki kikayi haka_ ?.
Munnira kwashe komai tayi ta sanar da Anty.
Tace ” _ai tun ranar dinner ‘din auren su_ _nayi_ _maganinsu, kinsan yanda nake son Mahmud haka nake kishin sa, toh taya zan bari inagani ya_ _ra6i wata mace daban ni ina nan………_
Kaita ta juya ka’dan tace
” _zuciyata bazata iya ‘dauka ba Anty, shiyasa nasaka akayi musu_ _katanga wanda bazai ta6a bari su anfani juna ba , ita nasa akasawa_ ‘ _karfin sha’awa wanda idan ya ‘debe ta dole sai ta nemi atallafa mata….._ _amma fah Anty da ‘kyar nasamu aikin yayiwu……._
” _Mtheww wai su adole masu rotson Allah, kinsan kuwa wanda nayi mata ranar dinnern_ _ma ko kamata beyi ba, sai da na koma shine bokan yace min wai sede atura mata aljani wanda zai ri’ka sata jin_ _sha’awar ammafa bakowani lokaci ba, sai in lokacin daya samu kanta_ _tukunna sannan se sakata, shi ‘dinma Anty da ‘kyar yasamu yashigeta_ _inji bokan, amma jiya dana koma yace min komai_ _normal, shirina yana tafiya akan_ _tsari banda_ _matsalar komai_ “.
Kallon Anty tayi wacce tabaza kunnuwa take jin tsaban shu’umanci irin na Munniran sai ma taji ta ‘kara birgeta data yi maganinsu, ai ita da farko ma tunaninta beje ga hakan ba tazauna sa’ka’ka kawai tana jiran rabuwarsu ashe hauka tayi, inbadan Munniran ta yun’kura bama ai tanajin abun nasu sai yafi haka.
Sai de kuma ai yiwa Fateeman haka bashine mafita ba, domin koda abun yatashi mata mijinta ze iya yin maganin matsalar ai tunda shi ba ‘a yi masa komai ba.
Sai de duk da haka ta wani guri batun Munniran ze iya samun kason maki mafi girma idan aka gangara 6angaren yawan bu’katuwa da kuma sashin gazawa.
Ta iya yiwuwa hakan ya ta6a zaman lafiyarsu idan mijin yaga ji da yawan bu’katan Fateeman ze iya nuna gazawarsa wanda ta nan babban matsalan zai iya bayyana harma ya illata farin cikin dake cikin zamankewarsu……. lallai Munnira tayi tunani me kyau.
Anty na cikin wannan tunanin se Munnira ta katse ta da fa’din
” _Anty kinsan iskancin dana sa akayi musu kuwa_ ?
Da kai Anty ta bata amsa alamar ” _a’a_ “.
Murmushi Munnira tayi sannan tace ” _Mahmud bashi da daman taimakon Fateemah koda jarabarta ta tashi_ _saboda shi bashida anfani, tsakaninsa da ita sai de kallo Anty, kinga idan_ _abun ya isheta dole zata nemi mafita mafitar danasan bazai wuce tace_ _araba auren sun ba, kinga dazarar auren yarabu sai inkoma insa adawo wa_ _Mahmud da lafiyar mazantakarsa sai muyi aurenmu dashi, ko kuma ince ya aureni ni zan iya_ _zama dashi ahakan tunda ita ta’ki kinga bayan an ‘daura auren sai lafiyarsa ta dawo ni_ _kuwa zama daram Anty sai ke sai jikoki”_
Ta ‘karashe maganar da dariya.
Anty ma murmushi tayi da farko dataji batun Munniran akan Mahmud hankalinta ba ‘karamin tashi yayi ba amma ‘karshen labarin sai ya wanki wancen ‘din tunda taji komai zai dawo normal daga baya sai taji ranta wasai.
” _lallai kanki naja ‘yan mata shiyasa nake ‘kara sonki ai, dan nasan ki akwai kishin kai, sai dai kuma fah karki kuskura wannan abin yata6a min lafiyar yarona dan kinsan mutuncinsa kenan_ _ako’ina_ “
Story continues below

Wani dariyar ‘keta Munniran tasaki kamar wanda Anty sa’ar ta ce,
Sannan tace
” _Haba Anty,ni da nake farautarsa dan anfanin kaina taya kuma zan bari gangancina ya illata sa, komai da kike gani akan tsari nake yinsa kuma kafin ayi aikin sai dana tabbatar da cewa za’a iya rabashi da hakan_ _aduk lokacin dana bu’kata kinga kuwa ai ba abin damuwa_ _anan_ “.
Anty kuwa tamkar wawuya haka take binta da idanu domin gaba ‘daya ta tsinke da lamarin yarinyar gani takeyi tamkar wannan tamafi uwarta shu’umanci, amma tsabar haukan Anty bata ji ko ‘diris aranta cewa wannan ba kalan auren ‘danta Mahmud bane sai ma taji ‘karin ‘kwarin gwiwa akan Munniran.
Ita kuwa Munnira
tana gama fa’din maganar ta mi’ke tsaye tare da gyara zaman rolling ‘din dake kanta tace
” _Yauma ni kinga son ganinshi nakeyi wallahi shiyasa ma kika ga na fito_ _da sassafen nan office ‘dinsa zani gara tun wuri mu fara_ _fahimtar juna tunda gab muke da zama_ _abu ‘daya_ “
” _Aikuwa da gaskiyarki_ “
Anty tabata amsa gami da fa’din, ” _inkinje ki dawo dan Allah kafin ki wuce gida akwai sa’kona_ “
” _Toh Anty bazan_
_ma da’de ba_ _zandawo_ “
Munnira tayi maganar tana nufan ‘kofar fita daga parlourn.
*****
Mahmud kam lokacin daya shirya fita aiki exactly be sa6a lokaci ba yakan yawaita barin gida 7:30 dayake sai 9:00 ake bu’de kamfanin nasu so yana samun time yayi komai atsanake.
Ko yau ‘din ma haka yayi shirinsa cikin wata arniyar shadda gezna milk colour, Fateemah nata binsa da idanu domin ita yau ‘din gaba ‘daya bata jin da’di, fargaba ne yacika mata zuciya da batasan kona menene ba, hatta ga6o6inta asake take jinsu, duk abinda Mahmud yakeyi da idanu kawai take binsa.
Break fast ma yau tea ka’dai taha’da masa ita kam tasha ma sam ta gagara shine dai yasha ka’dan sai ya tashi da niyyar tafiya, itama mi’kewa tayi dama already mayafinta yana ajiye agefenta sai kawai tafara warware shi.
Ganin hakan yasashi tsayuwa saroro yana kallonta sai data gama warwarewan kafin yace mata ” _yau fah ba inda zakije, agida zaki zauna tunda kin’ki ki sanar dani_ _dodon dake hanaki zama, kuma ma kinga yau friday ne bazan da’de ba zandawo 12:00_ _za’a rufe office ki_ _zauna agida kijirani_ “
Fateemah najin hakan tafara masa kuka dayake daman acike take da damuwa so kamar jira take yayi maganar kawai tafara masa kuka tana fa’din “wallahi ita bazata zauna ba.
Yayi -yayi ta sanar dashi matsalan amma ta’ki, sai kawai taci gaba da kukanta, haka Mahmud ya6ata tsawon lokaci yana bata baki da lallami akan ta ha’kura ta zauna agida amma ta’ki.
Daga ‘karshe kawai ya ha’kura yasata agaba yace toh suje a lokacin ma har 8:01am tayi.
Haka suka kulle ‘kofan suka nufi inda motarsa take.
Har yayiwa motar key sai ya tuna ashe ya baro jakansa aciki wanda ke ‘dauke da dukkan muhimman abubuwansa na wajen aikin.
Fita yayi yakoma ya ‘dauko jakar wanda ya barta anan kan cough inda ya zauna dan rarrashin Fateemah.
Gurin motar ya koma ya bu’de baya ya ajiye jakar duk da idanu kawai take binsa.
Be shiga motar ba taga yasake komawa cikin gidan can bayan mintina biyar sai gashi yafito da ‘dan saurinsa yashiga yace ” _kin wani ha’da min Tea me sa fitsari sai da na koma na yi kafin naji dama dama_ .
Kauda kai kawai tayi dan batasan me zata ce dashi ba damuwar ta ma ka’dai ya isheta.
Horn ya dannawa Gate man ‘dinsu dake daga can baya yana duba flowers ‘din gidan.
Da gudu yazo yafara ‘ko’karin bu’de gidan, kafin ya ‘karasa tura gate ‘din ne sai Mahmud yasake ce mata ” _inajin kamar nayi mantuwa aciki wallahi, kuma fah bakomai bane tsaban yanda kika_ _rikitani ne da rigimarki yasa nake ganin haka_ .”
Shiru tayi masa yanzun ma shima kuwa sai ya shareta yaja motar yayi gaba dai-dai inda gateman ‘din yake ya tsaya kamar yanda suka saba kullum suka gaisa sai de yau Mahmud yaciro ku’di ya dan’ka masa ko jiran godiya be yiba yaja motar suka fita.
Sai da suka hau kan titi kafin ya ‘dan kalleta yace
” _inajin nextweek fah zan koma katsinan nan, se ki shirya tafita bakince_ _zaki_ _rakani ba_ ?
” _Umm_ “
Tace a’kasan ma’koshi.
” _toh sai ki fara shiri domin da mota zamu_ “
‘Dan sake fuska tayi ka’dan tace ” _zamu har Abuja ko_ _Yayah_ “
” _Insha Allahu, ko ni banje ba ke zaki je_ “
ya bata amsa atakaice.
_Toh fah readers sai ku mammatso kusa domin jin yanda ha’duwar Mahmud, Munnira da kuma_ _Teemah_ _zai_ _kasance_ ……..za’a kafta🤞🏻
Sa’kon gaggawa ne ya iso musu cewar kayan da za’a kawo musu a Lagos za’a sau’ke su so sai aka wakilta Abbas akan zuwa kar6o kayan, dama da farko maiduguri za’a taho da kayan direct sai kuma aka samu wani matsala inda dole sai de a sau’ke a Lagos sai suje su ‘dauko.
Ko ka’dan Abbas be kwana da niyyan tafiya ba amma da asubar fari aka sanar dashi lokacin ma yana zaune dafe da kansa bayan farkawar da yayi daga bacci da mafarkin Fateemah sosai mafarkin ya tsaya masa aransa, wai tana ta kuka saboda tarasa hanyar zuwa ko’ina ne oho, duk inda tabi de sai taga gurin yah mata duhu gashi wai tana ganinsu agabanta sun kewaye ta, a wurin akwai Mahmud, yaga Hannah, Antyn Mahmud yaga Daddy ma da kuma wasu mutane kimanin biyar da be sansu ba, amma inda akwai hanyan 6angaren Mahmud ne, Antyn Mahmud, wata da be santa ba da kuma shi kanshi, so take ta wuce amma tarasa ta ina zatabi, cikin wa’yancan ukun duk inta bi 6angarensu duhu ke mamaye gabanta, dalilin haka sai ta sake sakin kuka tana yarfe hannu, shi ka’dai ne kawai 6angarensa be yi mata duhu ba, amma ko data biyoshi ‘din sai hanyan yayi mata nisa sosai yanda zai yi mata wahalar cimmasa shi kansa ma nisan yayi mata tana hangoshi yayinda har hannunsa yake mi’ka mata dan ta kama amma bata iya kamawa, hakan sai yasa taci gaba da kuka tana fa’din ” _Yah Abbas_ !
_Ya…… Abbas_ !!
Yana san taimaka mata shima amma sai ya kasa, Mahmud kuwa daganin tana bin inda Abbas ‘din yake tana ‘kiran sunan shi sai shi kuma ya juya bayansa yana murmushi, taku ‘daya biyu zuwa uku yayi sai ya 6ace 6at suka daina hangoshi sai haske ya mamaye gurin gaba ‘daya tare da wani lumshi me ‘kayatarwa.
Dai dai 6acewar Mahmud ‘dinne Abbas ya farka daga baccin yatashi ya zauna dafe da kansa yana sake bitan mafarkin dayayin tare da juya al’amarin acikin ransa, yarasa ma’anar mafarkin gaba ‘daya, abu ‘daya ya iya fahimta shine Fateemah na bu’katar taimako arayuwarta sai de be san dalilin da ze kawo hakan ba.
Yana cikin tunanin mafarkin ne sai ya samu sa’kon tafiya zuwa Lagos, wanda yazo masa a bazata a kuma dai dai lokacin da ze fi bu’katan hakan, haka ya tashi yayi komai cikin hanzari ya gama shirinsa tsaf.
Su shida suka tafi , jirgin ‘karfe 6:30am na safiyar ranar juma’ah suka bar Maiduguri zuwa Lagos.
Sai dai kuma cikin rashin sa’a sai da suka isa Lagos suka sake tarar da sa’kon cewa sai zuwa yamma zasu iso dan haka sai suka nemi gurin da zasu huta kafin yamma amma sam basuji da’din hakan ba.
Da wannan damar Abbas yayi amfani ya nufi office ‘din Mahmud wanda a’kage yake yaji ya Fateemah take agurin Mahmud ‘din, dan shi gani yake kamar rashin son auren da Mahmud yace baya yi ne yasa shi ya kasa kula da ita, be san gidansa ba office ‘dinsa yasani dan haka sai ya nufo office ‘din, yana da tabbacin adai dai wannan lokacin Mahmud na office.
*****
Fateemah da Mahmud kuwa basu suka isa office ‘din ba sai 9:13am
dayake ansamu ha’duwar holdup sosai ahanyar shiyasa ma suka ‘dan 6ata lokaci kafin su isa.
Story continues below

Da isarsu office ‘din ko zaman 20minutes be yi da ita ba, bayan isowarsun Mahmud ya amsa ‘kira through landline ‘din dake kan table ‘dinsa, yana gama wayar kuwa ya mi’ke tare da sanar da Teemahn cewa yana zuwa bazai da’de ba zai dawo.
Tashi tayi da sauri tace zata rakashi itama, saboda sosai yau ‘din take jin babu da’di aranta, fa’duwar gabanta kara yawaita yakeyi acikin kowani da’ki’ka.
Mahmud kuwa yadakar da ita da fa’din ” _ah’ah please wait 4me mana Fateemah u ar safe here karki damu_ , yace mata files ‘din da ze kai ‘din masu matu’kar muhimmanci ne dole akwai wasu ‘karin bayanin daya kamata shi zaiyi kafin aturasu zuwa China shiyasa zashi.
Duk tunanin Mahmud tsoron da takeji ne yasa har a office din ma takasa sakewa.
Haka ta tsaya ‘ki’kam batare da tayi masa magana ba domin haka kawai yau ‘din take jin wani sabon yanayi game da Yayah Mahmud ‘din har bataso yayi nesa da ita.
Da fitarsa kuwa Fateemah ta ‘daga hannu ta dafe goshinta, bata san dalili ba amma akowani sa’a takan tsinci kanta cikin tsananin fargaba, wanda tun da safiyar yau data’ farka daga bacci ta tsinci kanta cikin wannan yanayin.
Bazata ce ga ainahin matsalarta ko damuwarta ba ayanzun ita de kawai tana ji har cikin zuciyarta ba ta da nutsuwa a hargitse take jin kanta gaba ‘daya, dan haka kawai sai ta ringa maimaita _inna lillahi wa inna ilaihi raji’un, lahaula wala quwwata illah_ _billah_ acikin zuciyarta wanda yin hakan ne yake ‘dan sama mata sukuni idan taji fargaban ya yawaita.
Da rigimarta sai ta wuce kan kujerar da ya ke zama a office ‘din ta wani hakimce tana juyi ahankali tare da lumshe idanunta yayinda ta ringa faman sarrafa tunaninta ko zata gano babban damuwarta alokacin.
Mahmud be da’de da barin office ‘din ba Teemah taji anturo ‘kofar ahankali batare da annemi izinin mamallakin office ‘din ba.
Dubanta takai wurin ‘kofar sai ta ga wata matashiyar budurwa ce tsaye da fuskar mamaki wacce zata girme mata ahaife.
Sanye take da wata riga doguwa yellow rigar roba ce sosai kuma bawata me fa’di ba, hakan yasa rigar tabi duk jikinta ya kwanta, tare da bayyana duk wata halitta dake jikinta, kanta kuwa da wani jan mayafi ta zagaye shi, ba laifi kam ayanayin zubi da tsarinta tayi kyau sosai sai de atsarin musulunci sam bata da maki ko guda ‘daya.
Kallon kallo suka tsaya yi da Teemah kowa da abinda yake sa’kawa acikin ransa, tunanin Teemah ko itama ‘daya daga cikin ma’aikayar su Mahmud ne, tace wata’kila haka suka saba shigowa gurin Mahmud ‘din batare da neman izini ba, sam Teemah bata san Munnira ba tunanin ta ta6a ganin ta wani guri ma sam be zo kanta ba, saboda ko lokacin dinnern auren sun akwai mutane da dama so bazata iya tunawa da kowa da ta gani awurin ba.
Yayinda Munnira aranta take jinjina kyaun da ta ga Teemahn ta ‘karayi, duk da yake ta ganta alokacin hidiman bikinta kuma kwalliyar biki daban yake dana kullum amma duk da haka bata ga aibin Teemah ba koka ‘dan sai ma wani fresh data ‘karayi tayi kyau bayaga haka bata ga wani abu daban ba, take kuwa tsantsan kishin datake ji azuciyarta game da Teemah ya motsa, amma duk da haka sai da ta ‘dan yi dariyar mugunta wanda ta ‘dan cije ta maida shi murmushi yanda Teemah bazata fahimci manufarta ba.
Ahankali take takowa izuwa gaban Teemahn yayinda takalmin dake sanye a ‘kafafunta yasamu daman bada sauti ‘kwas…..’kwas me ‘dan ‘kara ka’dan saboda yanayinsa.
Teemah sam batada niyyan kulata ko yi mata magana ba duk da taga cewa ta tunkaro ne, ita tun ganinta nafarko ma yarinyar bata birge ta ba koka’dan ganin cewa girmanta be sa tasan muhimmancin yiwa mutun sallama ba sai de ta tsaya kallonta.
Komawa tayi ta jinginu da kyau da jikin kujerar ta kwantar da kanta tare da ‘dora ‘kafa ‘daya kan ‘daya harda lumshe idanu tana juyi da kujerar ahankali tamkar itace mamallakiyar office ‘din, sai tayi kamar irin ba matsalarta ba ce zuwan Munniran.
Story continues below

Idanunta alumshen ta tsinkayo muryar Munniran akusa da ita tana fa’din
” _Amarya me da’din_ _tuwo!!!_
muryarta cike da murmushi tayi maganar.
Ahankali ta bu’de idanunta ta sau’ke su akan Munniran daga idanun kuwa bata motsa koda ‘yan yatsun ta ba.
Kallon a ina kika sanni tayiwa Munniran tare da ‘dan zaro idanu ka’dan ta juya su.
Murmushi Munniran tayi itama ta zuba wa Teemahn idanu,
Idon su cikin na juna Munnira ta’kara fa’din
” _soyayyan be ‘kare agida ba kenan shine kuka kawo sauran a office ko mrs Mahmud_ ?
_Sai de kuma naga ai angon naki ba me amfani bane……..ko de akwai wani sirrin ne bayan wannan?_
Teemah bata kulata ba saima mamakinta daya ‘karu tambaya ta fara yiwa kanta shin wacece wannan haka sam Teemah ta tsani shishshigi.
Munnira tagama fahimtar Teemahn da abinda ke cikin ranta dan tasan dama Teemah da wuya tagane ta dan haka sai ta gyara zama tare da yin murmushi tace
” _kina mamakine amaryar mijina?Ki kwantar da hankalinki ‘yan_ _mata kinsan fah Mahmud shine rayuwata kinga kuwa dole insan_ _abubuwa da dama game da rayuwarsa, saboda in ‘karfafa soyayyata wanda nake tunanin shi_ _kansa ma ‘kila be san da su ba, amma inke kina so ki sani zan iya sanar dake bawani_ _abu_ ! ”
Ganin da tayi Teemahn bata tanka ta ba har yanzun illah idanu data ke binta dashi yasa tayi murmushi, murmushintan da aduk sanda tayi shi tana jin izzah ne aranta irin kamar tagama dasu ‘dinnan.
Kamar an matsi bakinta ta furta.
” _kin san wani abu amarya_ ?
Bata jin cewar Teemahn ba taci gaba.
” _ni ‘din nan da kike gani babbar_ _masoyiyar mijinki ne tun ranar farko dana ganshi naji wani mahaukacin_ ‘ _kaunarsa yakamani amma cikin rashin sa’a sai Mahmud_ _yayi watsi dani da_ _bu’ka’ata ta duk da kuwa yasan ina matsanancin son shi hakan be sa yayi min duban_ _masoyiya ba koda kuwa sau ‘daya ne tak, nayi ‘ko’karin ganin na fahimtar dashi ‘dimbin_ ‘ _kaunar danake masa amma sam yakasa bani dama, ana cikin haka_ _sai maganar aurenku ya 6ullo daga bakin mahaifin sa, Anty ne tasanar da_ _Mamina komai, nayi ‘ko’karin ganin na hana auren yiyuwa amma hakan ma befaru_ _ba, saboda ance auren Mahmud dake zanannen ‘kaddara ce da dole sai ya faru,_ _Malamin mami na ne ya fa’di ne yafa’di haka, badan naso ba na ha’kura har aka ‘daura_ _auren ki da Mahmud………… Fateemah kina ganin zan iya ha’kura naga_ _rayuwar farin ciki_ _na wanzuwa atsakaninku ne dukda tarin ba’kin cikin da Mahmud ya ‘kunsa min_ ?
Kai ta jijjiga tace
” _sam bazan iya ba, bazan iya juran ganin wannan ranar_ _ba…………._
_”Inajin kamar inasonki ne shiyasa nake gaya miki wannan….”_
Dai dai nan Teemah ta hango Mahmud tsaye abakin ‘kofar office ‘din ganinsa kawai tayi bata san tun yaushe yake wurin ba, dayake Munnira data shigo
ganin Fateemah yasa bata tura ‘kofar da kyau ba hakan ne kuwa yabawa Mahmud damar gani da jin kalamanta da kyau ba batare da wani tangar’da ba.
Teemah ce ke saitin ‘kofa dan haka ita ka’dai ce ta hango shi sai yayi mata ido akan ta ‘dauke kanta akansa ta daina kallonsa hakan kuwa tayi sai ta meda hankalinta da idanunta wajen Munniran dan kalaman data gama furtawa yanzun yasa ta ji tausayinta sosai harta fara jin cewa dama Yah Mahmud be mata haka ba tunda tana tsananin son shi daya daure ya aure ta, Munnira bata san da zuwan Mahmud ba, dan haka sai taci gaba da maganarta kanta tsaye, Teemah kuwa taci gaba da sauraro bata ‘kara kallon ‘kofar ba koda asace.
” _Tun kafin auren ku nake ta neman hanyar da zan hana auren ku ya’duwa tunda hana yiyuwar_ _auren ya gagareni, nasha fama sosai da ‘kyar nasamu hanya_ _wacce itace ta ‘dan sanyaya min zuciya har tasa na rage damuwata domin na yadda da aikin_ _danayi_ ”
Ido ‘daya takashe wa Teemahn tana murmushi taci gaba da fa’din,
” _ba sai na tuna miki ba nasan kinsani tunda ke ke fama da matsalar……._
Cikin izgili tace ” _ya kike yine idan jarabar ki ta tashi cikin dare? ai an gaya min cewa da dare ne kawai kike da damuwa da rana kina rayuwarki ne kamar kowa_ “
Story continues below

Dariya ta yi ita ka’danta sannan taci gaba da fa’din
” _ranar dinnern aurenku da nasa Anty ta shirya shi nasamu nasaran_ _aiwatar da niyyata akanki… zaki iya tunawa dani kuwa_ ?
Goshi Teeemah ta ha’da tare da kawar da kanta gefe alamar ita ta manta.
” _Ai nasan bazaki iya tunawa ba, yanzun ma inajin fah kamar inasonki ne shiyasa na_ _ke fa’da miki wannan maganar dan kinsan sirri ne_ _babba awajena fiye ma sirrin dake_ _tsakaninki da Mahmud.Kuma kinsan wani_ _abin birgewa aciki mother in-law ‘din ki ce take ‘kara min_ ‘ _kwarin gwiwa akan komai wanda har hakan yasa tayi kyautar ki gaba daya wa ‘kawarta_ _musamman saboda farin cikina………._
Sau’kar mari kawai Munnira taji akan kuncinta wanda yakusan gigita ta kafin ta gama fahimtar ta inda marin yazo sai ta sake jin wani marin, sai da ya mata mari lafiyayyu guda hu’du wanda yasa har takai ‘kasa ta zube tana kuka tare da dafe kuncin nata da hannayen ta duka biyu.
Kalle- kalle yafara yana neman abin duka kasancewar ba belt ajikinsa jumpa ya saka shiyasa shi neman abin, haka ya gama kalle-kallen sa be ga komai ba.
Tunawa yayi da wani toshon cable ‘din daya daina amfani dashi da sauri ya tashi ya bu’de drawern yajanyo wayar ya fara nanna’de ta ransa amatu’kar 6ace kana ganinsa zaka san an ta6o shi yau ‘din dan Mahmud ba haka yake ba.
Teemah ce taje dagudu ta ri’ke masa hannu dan ita tuni ma harta fara kuka saboda bata ta6a ganin tsantsan 6acin rai azahiri na Mahmud ‘din ba irin yau .
” _Yayah please karka daketa kaji! dan Allah…. Yayah kayi ha’kuri._ “
ta yi maganar da muryar kuka.
Mahmud kuwa ko kulata ma be yi ba dan shi ka’dai yasan abinda yakeji azuciyarsa game da kalaman Munniran be ta6a tunanin haukarta har ya ha’da da cin zarafi da shiga hakkin wani ba.
Yana isa inda take ya sau’ke mata cable ‘din abayanta, yayi niyyan yamata dukan tsiya ne na fitan hankali yanda gaba ko ganinsa tayi ahanya bazata tunkari gabansa ba ballantana hartayi tunanin cutar dashi.
Amma yana ‘daga cable ‘din akaro na biyu Fateema tazo dagudu ta ru’kunkume shi ta baya tana kukan itama, idan baka sani ba zakayi zaton ko dukkan su biyu yake duka.
” _Yayah……..please kabari, karka daketa dan Allah Yayah kayi_ _ha’kuri………kaifa musulmi kar kabiye sharrin zuciya_ _Yayah please kabarta ka yafe mata kaji….._
Cikin sanyin jiki ya sau’kar da hannunsa daga barin dukan nata.
Munnira kuwa gaba ‘daya tabi ta rikice dana sanin zuwan ta office ‘dinsa ma takeyi ayanzun, domin tunda take arayuwarta, ba’a ta6a marinta bama balle har takai ga duka da cable.
Kuka takeyi kamar ranta zai fita tana so ta fice a office ‘din amma babu dama dan Mahmud sai da yarufe da lock kafin ya ‘karaso ciki.
Dawo da Fateemahn yayi ta gabansa yana bubbuga bayanta alamar rarrashi yace ” _yi shiru ya isa haka Fateenah, bakya ganin cutar da rayuwarmu datayi_ _ne, Fateemah wannan da kike gani babbar shai’daniya ce_ _ki bari in koya mata_ _hankali_ ”
Kai Teemah ta jijjiga masa alamar ” _ah ‘ ah_ ”
Sai yace
” _okay……on one condition, zan barta amma sai ta fa’damin komai_ _data sani game da munafurcin da suka ‘kulla gaba ‘daya in_ _bahaka ba wallahi ba zan ‘kyaleta ba_ ”
Munnira kam tun kafin ya rufe bakinsa cikin sheshshka tace
” _wallahi Mahmud zan gaya maka gaba ‘daya nayi al’kawari_ “
Idon su gaba ‘daya suka maida shi kanta inda taci gaba da basu labari gaba ‘daya.
Asirin datayiwa Teemah dashi kanshi Mahmud ‘din sai da ta fa’da tace ” _manufar hakan kuma shine wanzar da fitina da rashin aminta da junansu wanda_ _hakan ne zai iya yin sanadin rabuwarsu cikin sau’ki_ .Tace kuma Anty ma tasan da maganar dan ita ta’kara goya mata baya kuma itace ta ke jagorantar ‘kawarta Anty Chiddy domin samun kan Fateema wanda hakan ma wani shirin ne daban a6oye.
Story continues below

Kasa jurewa Mahmud yayi saida ya zauna tsaban haushi da takaici.
Zaman ma sai ya gagare shi yasake mi’kewa.
Yana huci yace
” _Ai kuwa kinyi kuskure, Munnira munafurcin ki beyi tasiri ba koka’dan, domin Fateema bata_ _san ma tana da wannan_ _matsalarba balle har ta ‘daga min hankali akai, har yaushe……Munnira_ _har yaushe zaki tsaya 6ata lokacinki akan yarinya_ ‘ _karama irin wannan, ko angaya miki ma ko na rabu da Fateema zan aureki ne?, wallahi_ _ko babu mata aduniya Munnira bazan ta6a auranki ba………_
_Kuma aurena da kike gani ni da Fateema auren zobe ne in bakisani ba ma yau ki sani, Allah_ _ne ya ha’da kuma shika’dai zai iya rabashi ba de ke ba kam Munnira_ “.
Yana kaiwa nan yayi Wulli da wayar ya ja hannunta zuwa gabansa wanda hakan ya tilasta mata tashi tsaye tare da fasa wani ‘kara, zaton ta ko wani dukan ze kuma mata.
Teemah ma da sauri tace
” _Yayah please…….._
Juyawa yayi ya kalli Teema sai ya sake kallon Munniran, fasa fa’dan abinda yayi niyya yayi sai kawai yaja hannunta suka nufi ‘kofar fita.
Be damu da takalmanta da mayafinta dasuke jefe a’kasan office ‘din ba haka yajata suka ratsa cikin Companyn har zuwa inda yayi parking, yana zuwa yaturata abaya yarufe sannan ya zagayo ya shiga driver seat.
Teemah ce cikin sauri ta tattaro sauran tarkacen Munniran ta ri’ko ahannunta da gudu tabiyo bayansa amma kafin ta iso har yaja motar da ‘karfi ‘kuran bayan motar kawai ta tarar.
Zuwa lokacin kuwa hankalin dayawa daga cikin ma’aikatan yadawo kansu dan ko lokacin daya bar cikin companyn ma wasu nata mamakin dalilin daya sashi hakan.
Umar ne da shigowansa kenan ya ‘dan fita waje yasamo Teemahn tsaye hannunta rike da wasu kaya.
Mamakin dalilin hakan yayi sai yanemi ji daga bakinta.
Amma bata sanar dashi ba sai ma ro’konsa data fara yi akan ya taimaka yakaita gida wata’kila Mahmud can yanufa da Munnira.
Tana cikin ro’kon Umar sai ta hango Abbas na ‘kokarin giftasu, gaba ‘daya sai hankalinta ya koma gurinsa.
Hatta Umar sai da ya juya ya kalloshi dan yanda hankalin Fateemah ya ‘dauku izuwa kallonshi dole tasa Umar ma yabi gurin da kallo.
Take ya gane shi domin sun ha’du wajen ‘daurin auren Mahmud a damaturu duk da be da’de tare da su ba amma hakan be sa Umar ya manta da fuskarsa ba.
” _Yah….. Abbas_ !
Ta fa’di sunansa da tunanin shi ‘din ne ko kuwa wani ne me kama dashi.
Cak kuwa ya tsaya duk da be gama tantance shine ake nufi da ‘kiran ba ko waninsa, amma muryarta ba ze ta6a mantawa ba ko a ina yaji ta.
Hakan ne kuma yashi waigowa ahankali sai caraf idanunsu ya sar’ke cikin na juna.
Teemah kam kasa juran hakan tayi dan haka sai ta meda idanun nata ‘kasa ta taho ahankali zuwa inda yake kayan Munnira rungume a ‘kirjinta.
Mamaki Abbas yakeyi ganin Fateemah a harabar companing su Mahmud kuma batare dashi ba.
Tana isa inda yake sai taji idanunta na ‘ko’karin tsatstsafo da ruwan hawaye ahankali tasake ‘daga idanu takalleshi amma kwarjininsa ya hanata sakewa.
” wai ke faruwa ne? Ina Mahmud ‘din?
Ya tambayeta cikin sauri.
Daidai nan Umar ya iso ya mi’ka masa hannu suka gaisa sai ya sanar dashi cewa yana zaton Mahmud ‘din be jima da fita ba saboda wata ‘yar matsala dake faruwa yace shima yanzu yake so ya sau’ke ta agida.
Tare suka koma motan dukkan su inda Teemah tashiga baya sukuma Abbas da Umar na gaba.
Rintse idanu yayi yana sake recalling mafarkinsa wato dagaske Fateema na bu’katan taimako, in bahaka ba meyasa yaganta haka tana kuka?
Amma ba ze iya bu’dan baki ya tambayeta ba.
Story continues below

Ganin da Umar yayi kamar abin ya sar’ke zuxiyar Abbas ne yasa shi sake tambayarta abinda ke faruwa.
Zuciyarta na tsananin bugu ga damuwa da suke son suyi wa zuciyarta yawa amma haka ta daure tayi musu bayani atai’kace dan muryarta shaking yakeyi sam bazata iya dogon magana ba ahalin yanzun.
Abbas jiyayi tamkar zuciyarsa zata fito waje tsabar haushi ba’kin ciki dan Teemah batun Anty Chiddy ka’dai ta sanar dasu bazata iya fa’da musu ‘dayan maganar ba.
Jikin Abbas har rawa yake yi saboda yanda ransa ya 6aci amma ko ‘kala be ce ba shi de yayi shiru Allah ne ka’dai yasan yanda yakeji azuciyarsa wato Mahmud zuwa yayi ya watsar da ita har wasu banzayen ‘yan iska suka samu daman shiga rayuwarta da haukarsu.
Jiyake da zaiga mutanen awannan lokacin dashi ka’dai yasan abinda ze musu.
Da wannan tunanin suka isa gidan Mahmud amma baya nan, Abbas ne yayita gwada ‘kiransa amma kusan missed call uku yamasa be ‘daga ba.
Hakan kuwa ya ‘kara tunzira zuciyar Abbas aciki yake jin ciwo da ‘kunan abin.
Shiru Umar yayi duk da be gama fahimtar abinda yafaru duka ba amma ayanayin labarin da Fateemah ta basu ya fahimci cewa ran Mahmud yagama 6aci ayau ‘din. Tunanin inda zai samu Mahmud yake a dai-dai wannan lokacin, ina yanufa da yarinyar da Fateemah tace yafita da ita.
*****
Mahmud kuwa be zame ko’ina da Munnira ba sai gidan Anty, yana shiga kuwa ya hangota tana shirin shiga mota itama ga dukkan alamu fita zata yi.
Ko gama parking beyiba ya fita tare da jawo hannun Munniran yakawo ta gaban Anty da tun shigowar motan ta tsaya saroro tana ganin ikon Allah dan ayanayin daya shigo ka’dai ma sai da mamaki ya kamata balle data ga Munnira ahannunsa wujuga wujiga ai shikenan tunaninta ya tsaya cak.
Yana isowa yatura Munniran kamar kayan wanki ta fa’di agaban Anty tana kukan fitan rai.
Azuciye yace
” _saurari yarinyar nan Anty kiji abinda take fa’da, Anty bana fatan abinda_ _naji ya kasance gaskiya domin hankalina baze iya ‘dauka ba._
_Anty wai dake za’a ha’du acutar dani da rayuwata, Anty idan ma kina_ _gadaran ‘danki ne ni toh ita Fateemah fa?,miye yarinyar nan ta tsare miki_ _aduniyan nan da har zaki nemi sata a mummunan harka irin ma’digo_ , _Anty_ _bakya tunanin alhakin Allah ne_ ?,
_Kun hana yarinya rayuwa me kyau agidan aurenta kun hanata sakewa, kun sanya tsoro yazama abokin tafiyarta duk meyasa hakan Anty dan kawai kin tsaneta, wallahi ni cewa kikayi insake ta takoma wurin iyayenta daya fimin da wannan alhakin!!_
_Itan fa jinina_ _ce……Fateema_ _dangina ce da ko ba aure atsakanin mu ni me iya ri’keta ne_ _awajena, banda haka ma Anty_
_me kike so ingayawa mahallici na idan ya tsaida ni akan amanarta_ _dana kar6o a hannun iyayenta ?_ _Anty_
_bakya tunanin ranar da Allah ze tuhume mu gaba ‘daya_ ………
” _Ya isa haka ni Mahmud_ ……
Anty ta daka masa tsawa tare da ‘dago Munnira ta jingina ta da jikinta.
Taci gaba da fa’din
” _ai kariga kasan dalili, nasan baka manta ba, lokacin dana yi ta fama_ _daku kaida mahaifinka akan karka auri yarinyar kun saurareni ne?_ _ko kana zaton dama i ll give up so easily ne haka da har kayi saurin manta abinda_ _yafaru? …..Mahmud wannan da kake gani ita ce_ _za6ina agareka kuma har abada bazan canja ra’ayi ba, ko ka ‘kyaleta ko ka illata ta_ _Munnira itace uwar ‘ya’yanka bawata ba, dan haka kama kama kanka ka_ _nutsu banason hauka, duk abinda na aikata kuma ina yi ne_ _saboda kai, ai nagaya maka bana ‘kaunar ganinka da yarinyar nan,_ _banaso, bazan iya juran ganin jinina na rayuwa da dangin matsiyata_ _ba_ .
_Kuma da kake batun ancutar da ita ka je ka tambayeta mana, ita tace tanason a tallafa_ _mata dan tana da bu’kata shiyasa na ha’da ta da ‘kawata saboda akore mata_ _kishirwar dake damunta, bayaga haka me kuma na aikata agareta_ ?
Mahmud hawaye kawai yaji ya zubo masa na ba’kin ciki yanzun kam yasan Anty bazata ta6a canjawa ba yariga yasan tayi nisa tunda har ta iya tsayawa gabansa amatsayin sa na ‘dan data haifa ta gaya masa maganganu son ranta gameda aurensa, ha’ki’ka yasan idonta ya rufe da tsanar da take yiwa dangin mahaifinsa wanda kwak’kwaran dalilinta nayin hakan bazata iya fa’da ba.
Har ya juya zai tafi sai yakuma dawowa gaban Antyn idonsa taf da hawaye ya furta ” _Anty ki yafemin…….._
_ni ‘danki ne ke kika haifeni, albarkar ki dole in nema_ _adukkan al’amurana, ke da Abbah kun yi fama dani tun ina ‘karami_ _har girmana….. kun bani dukkan gatan daya kamata, ban_ _ta6a yin kuka dan rashin wani abu ba, amma Anty ki_ _gafarceni….. wannan karon bazan iya ‘dauka ba, bazan iya zuba_ _ido ina gani aci zarafin yarinyar da bataji ba batagani ba….. zuciyan_ _Fateemah awanke yake tas bata da hakkin kowa dan haka bazan bari_ _acutar da ita ba , kicewa Abbah na ya yafemin idan ya_ _dawo Anty_ “
Be ‘kara magana ba ya juya ya tafi yana share hawayen sa daya kasa controlling ‘dinsu.
Yariga ya sanyawa ransa cewar zai ‘dauke Fateemah su bar Lagos bari na har abada, zai yiwa Anty nisa, nisan da zai sa ta harse ta manta da kalar fuskan Fateemah ma balle rayuwarta, abu ‘daya zai iya dawo dashi shine Abbahn sa, yanaso yasake ganin Abbah kafin yatafi sai de hakan baze samu ba dan haka dole watarana ze dawo kawai domin Abbahn sa.
Tafiya yake yana share hawaye, damuwarsa gaba ‘daya ya tattaro ya taru masa akan idanunsa zuciyarsa kuwa cike take da hanzari jiyake ko awa ‘daya ba ze iya ‘karawa acikin garin Lagos ba, zai ‘dauke matarsa suyi nisa yanda ze nisanta ta da dukkan ma’kiyanta.
Kwakwata ma Mahmud mantawa yayi da cewan yana driving ne, ya manta duk wani doka da tsarin tu’ki abinda ya dameshi ne ka’dai yake yawo a ‘kwa’kwalwar sa.
Be ta shi sanin hakan ba har se da yaji ‘karan wani horn ha’de da taka birki me ‘karfin gaske take ya rikice yarasa me ma zaiyi dishi dishi idanunsa suke gani hakan ya sa be ma lura sosai da gabansan ba bayan ‘karan da ya ji be sake gane komai ba, kafin ya ankara kuwa rabin motarsa tashige ‘kar’kashin wata babbar motar da ke gabansa .
Mafiya yawan mutanen dake gurin Hannu kawai suka ‘dora akawunansu wasunsu na fa’din ” _jesus crist_ ” yayin da tsirarun su ke maimaita _innalillahi wa inna ilaihi raji’un_ …………..