ABBAS
CHAPTER 18
Abbas kam yanzu girma ya ‘karu, ta’kama da izzah sai abinda yayi gaba, Daddynsa ne ka’dai yake ‘dan kashe masa gwiwa aduk lokacin da yayi masa zancen aure walau awaya ne ko kuma azahiri, sam bayason maganar auren nan amma yarasa yanda ze 6ullo masa, babban damuwarsa kenan ayanzu shiyasa ya tsani maganar ma kwata-kwata.
*****
Kamar yanda Abbah ya yiwa Alhaji Muhammad al’kawari hakan ne ya faru domin acikin satin ranar wata laraba ya sau’ka garin Kano, Alhaji Muhammad yaji da’din zuwansa dan kuwa ko ba komai yana ganin yanzu ne ze san matsayin da ‘yarsa ta take awurin Abbah, dan haka bayan gaishe-gaishe har Abbahn ya huta ma sannan Alhaji Muhammad ya nemi jin salin abinda ke faruwa daga bakin sa, Abbah kam be sanar da shi komai ba yace masa kawai tace ne zata zo ta duba iyayenta shi kuma yace ta bashi lokaci in yayi settling sai suzo tare, ganin kamar lokacin tmya’ki samuwa ne shi yasa ta taho, batun kuma cewa shine yace ta zo ‘din bahaka bane, yace wata’kila bata ahirya komawa yanzu bane shiyasa ta fa’di.
Alhaji Muhammad kam shiru yayi masa amma bawai dan ya gamsu ba, duba da yayi da cewar tun tsawon shekarun auren su da ita hakan be ta6a faruwa ba, toh me yasa sai yanzun kuma, yana kyautata zaton matsala suka samu amma Abbah yake 6oye masa, Alhaji be tsawaita tunani ba shima ya basar da zancen dan yasan basu ta6a samun matsala har abin yazo gabansa ba sai de lokacin auren marigayi Mahmud da ya kawo ‘karar ta, wannan ma Abbah ya kawo ‘karan ne dan kawo gyara wa lamarin, kafin da bayan hakan kuwa be ta6a sanin ya yanayin zamansu ba, yanzu kuwa da babu ran Mahmud be san takamam man menene matsalar su ba kuma ya san de baza’a rasa ba dole akwai wani abu, kawai de Yusuf na 6oye masa ne shikuwa ba haka yaso ba, yaso yaji abinda ke faruwa domin ya ‘dan gyara al’amarin idan Allah ya bashi dama, dan shi da kanshi wani lokacin Maryam na bashi tsoro duk kuwa dayake ‘yar cikin sa ne amma tun lokacin dayaji asalin 6oyayyen halinta gaba ‘daya ya tsinke da lamarinta.
Alhaji aikawa yayi akayi masa ‘kiran Anty (Maryam), koda tazo kuwa mamaki tayi da ganin Abbah ita kam, domin bata ta6a zaton zuwansa adai-dai wannan lokacin ba.
Sai ma taga ya ‘dan murmure yanzun ba kamar da ba, fuskarsa se wani 6oyayyan annuri ke haskawa.
Alhaji Muhammad ne ya nemi jin abinda ya faru daga bakinta karo.na biyu, sanin da Anty tayi cewa yariga yasan komai yasa bata bata 6oye masa ba ta kwashe duk abinda ta aikata da dalilin da Abban Mahmud ke fushi da ita duk ta sanar dashi.
Alhaji Muhammad beyi mamaki ba dan yariga yaji duk abubuwan da yafaru ‘din tun a Lagos sai de be san cewa hakan.ne ya kawo sa6ani tsakanin su ba, duk da kuwa cewa yasan ba kowa ne ne zai juri faruwar hakan ba, ko shi kanshi idan hakan yafaru cikin iyalinsa yasan da ‘kyar ya iya sake zama da me shi shiyasa sam be ga laifin Abbah ba ko ka’dan sai ma ya jinjina masa da be aikata fiye da wannan ba, sake tambayar Abbah yayi inda ya tambayan ne kawai dan tabbatar wa.
Nasiha dukkan su ya ha’da su yayi musu game da zamanta kewar su, sosai yaja hankalinsu game da tsoron Allah cikin al’amuransu, sai da ya gama nasihar kafin ya baiwa Abbah dama yace yana da ikon za6an duk abinda yaga yayi masa wanda ya dace dashi, yace ” _karka damu dani Yusuf, ni tamkar mahaifinka nake bazan takuraka akan komai ba, sannan ina so_ _kayiwa kanka adalci karka dube ni kowani abu daya shafeni, Maryam matar kace,_ _kuma_ _kai ke da ikon za6an sake zama da ita ko kuma akasin haka, duk ra’ayinka_ _ne_ _Yusuf_ ,
_bazan ta6a tilas ta ka dan ka zauna da ita ba dan tana matsayin ‘yah agareni, wallahi_ _Yusuf da ace ni ni ke da iko da kai da bazan ta6a barinka kasake zama da Maryam a matsayin_ _mata ba, kuma ko yanzun ma kana da damar za6a ni nawa_ _shawara ne koma me ka aikata ni.kam.ina maraba dashi Yusuf domin kuwa nasan kai ‘din’dan halak ne me matu’kar ha’kuri sosai wanda ina zaton da iznin Allah rayuwarka bazata ta6a birkicewa ba Insha Allahu_ “.
Story continues below

Tuntuni Anty take zubda hawaye tana ‘karawa tasan koma me ya faru duk laifinta ne, laifinta ne da ta saka.son.zuciya ya rinjayi duk kan al’amuranta, yau gashi mahaifinta da kansa yake bada shawarar kar azauna da ita.
Godiya Abbah yayi masa sannan ya sanar dashi cewa shi bashi da burin ‘kuntata mata koka’dan kuma.duk abinda zaiyi zaiyi shi ne dan gyara duk wata 6araka da ke tsakaninsu, yace ha’kika Maryanlm.ta 6ata raina ta shammace ni alokacin da banyi zaton faruwar hakan ba, Maryam ta ninke ni a baibai da sunan ta kar6i maganar auren Mahmud bansani ba ashe mugun sa’ka tayi a6oye wanda warwareshi ke da matu’kar wahala, ban ta6a zaton Maryam zata aikata haka ga ‘dan cikinta ba, wanda ya kamata ace ta so shi fiye da komai arayuwarta, amma kash!
Mahmud be yi dacen samun hakan ba sa6anin haka sai ma ya rasa rayuwarsa.
Bayan jin hakan na tsani Maryam irin.tsanar da banta 6a zaton zan mata shi ba, naso in hukunta ta ta yadda bazata ta6a ma tunanin sake aikata wani abu makamanciyar wannan ba, sai de banyi hakan ba saboda ganin girma da kake dashi Alhaji a idanu na, bayaga haka ma Fateemah sai ta nutsar dani muhimmancin yafiya da falalar ta, kuma na gamsu sosai sanadin hakan na yafi Maryam azuciyata sai de bakina nawi yamin in furta mata haka nabari har se naga nadama ya ratsata tukunna.
Cikin hakan Allah ya nufe ni da neman aure kuma nasamu Alhaji zancen ana danake maka ayanzu kwanaki goma ne suka rage a ‘daura aure “
Fuskar Alhaji tuni ya cika da murmushi ya ringa sanya masa albarka tare da fatan alkhairi yace yayi matu’kar farin ciki da faruwar hakan kuma yana bayansa ‘dari bisa ‘dari.
Anty kam hawaye masu zafi ne suka zubo mata wanda tun rasuwar Mahmud basu fasa zuba ba, sai de na yau yasha bambam dana kullum, akowani ‘digon hawayen ta nadama ke lullu6e ta tare da wanke duk munanan halayenta dake zuciyarta, yanzu kuwa kukanta na godiya ga mahalicci ne da Abbah ya furta mata yafiya, ta tsani kishiya abaya amma yanzu kam ji take matu’kar ze yadda ya amince ya sake zama da ita toh a shirye take ta zauna da kishiyoyi uku ma ba ‘daya ba.
Komai faru laifin tane, Abbah be ta6a yi mata maganar kishiya ba tunda suke dashi sai yau ‘din, yanzu kuwa da duk abubuwa suka yimata yawa ina ita ina ‘daga hankali dan zeyi aure, tace Allah ubangiji ya ha’de kawunan mu ya sa hakan shine mafi alkhairi.
*****
Abbas tunda ya tafi kusan 3weeks kenan har yanzu be dawo ba, kullum sai dai su gaisa dashi awaya sai ya ta cewa ayyuaka ne suka yi masa shiyasa be le’ko gidan ba, Ummah bata damuwa dan tasan yanayin aikinsa dama fiye da hakan ma zai iya faruwa shiyasa kullum da addu’ar nasara da kariya kawai take binsa.
Daddynsa kam ko ajikinsa, sarai yasan matsalar Abbas ‘din gudun ha’duwarsu yakeyi saboda batun aure shiyasa ya’kizuwa Abuja shikuwa babu fashi lokacin daya ‘dibe masa na cika zaiga abin mamaki dan kuwa ba ze fasa ba.
Ranar da Teemah ta gama watannin takabarta ranar har se da tayi mamaki dan yanda Ummah ta fitar da ita tsab, sai dama ta ha’da ta driver suka je saloon suka dawo sannan tabata wasu ha’da’d’dun gown ‘yan italy matsu kyau da tsada sai alokacin ne Teemah take jin labari ashe wai Mummy ce ta aiko musu dashi tun zuwan Abbas kwanaki shine Ummah ta 6oye su sai yau ta fitar ta bata nata na Hannah kuma tace sai ta dawo zata ksr6i nata.
Data shirya tafito kuwa ita kanta tasan tayi kyau har jin kanta takeyi, ji take yi kamar wata dabance ba Fateemah ba, for about 4months da wasu kwanaki tana ta fama da atampopi yau kam wani iska takeji yana shiganta me da’din gaske, tun ba ma da Ummah ta bata wasu turaruka masu kyau tace nata bane, take ta rungume Ummahn tana dariya tare da godiya.
Haka taringa fesawa ajikinta tana ‘karawa har se da ‘kamshin ya ‘dan fara yimata yawa kafin ta sarara.
Jin kanta yau ‘din takeyi tamkar wata sarauniya gaba ‘daya ta dawo daban.
‘Daki ta koma ta ringa kashe selfie kala-kala wasu abin dariya wasu kuma abin birgewa ita adole tana farin ciki yau tasamu freedom afa’darta.
Ummah da kanta tace idan Hannah ta dawo da wuri ko da da yamma ne sai sunje shopping musamman kawai saboda Teemah.
Story continues below

Ai kuwa Teemah taringa ‘kiran layin Hannah amma baya shiga kusan 5 missed calls ta mata, data ga bata ‘daga ba sai ta tura mata text ” _Hii bae, pls ki dawo da wuri today is my day, Ummah tace zamu_ _fita_ “
Hannah na can tana rubuta test dan haka bata ma bi takan wayarta ba sai da tagama rubuta test ‘din tafito sannan ta ga missed calls ‘din Teemah tare da text ‘din da tayi mata, ai kuwa tana gani ta hau murnan yau zasu fita da ‘yar uwarta , bata ‘kara bi takan sauran lectures ‘din da zata yi ba batare da jiran komai ba ta kamo hanya ta dawo gida.
Tana zuwa suka rungume juna suna murna, Hannah da kanta itama sai da taga canjawar Teemah har ta kasa daurewa sai da ta tambaye ta aka wai yaushe kuma har tayi saloon batare da tasani ba?
Murmushi Teemah takeyi ta bata amsa da fa’din ” _yau da safe naje nayi lokacin already kina school ai shiyasa_ .
‘Bata rai Hannah tay tace
” _shine kuma kika ‘ki jirana muje tare ba, duk laifin Ummah ne_ _ai da ta gaya min da wuri_ _da sai in fasa makarantar mutafi amma shine aka ‘kyaleni harna tafi_ “
Teemah tana kan haska selfie tace
” _yanzu kam ai ya wuce ki, yi sauri ki shirya muje yawo yarinya yau zanga gari yarinya, kayanki ma na gurin Ummah, ke ko irin kice nayi kyau ‘din nan ma baki fa’da ba kintsaya surutu_ “
Tashi Hannah tayi taje wurin Ummah ta amsa kayanta tare da shigar da complain ‘din bata je saloon ba ita.
Ummah lalla6ata tayi har zancen ya wuce sannan ta wuce ‘daki domin watsa ruwa.
Abbas kam be dawo Abuja ba har sai da ya cika sati hu’du cif-cif kafinnan, ranar daya dawo ‘din kuma sai yayi dai-dai da ranar da Teemah ta gama takabanta.
Bayan shigan Hannah wanka ne Teemah ta ‘kira Anty tana ‘dauka tace ” _Anty albishirin ki_ ?
” _Goro fari ‘kal-‘kal_ “
Anty tabata amsa tana murmushi.
” _Anty yau zan fita_ _yawo nida___ _Hannah…._
” _Kai dan allah kice_ _yau sabuwar_ _rayuwa_ ‘ _yata zata fara_ “
Labari Teemah ta bata na irin kayan da ta saka da sauransu.
Daga ‘karshe Anty tace mata itama insha Allahu gobe tana hanya zata zo Abujan, Teemah murna kamar tafasa wayar da ihu, sai da Anty ta kauda wayar akunnanta tana murmushi da gode wa Allah ga dukkan baiwarsa.
Tana gama wa da Anty ta ‘kira layin Mummyn ta.
Mummyn ma tace ai tana ta ‘kiran layinsu be tafiya tun jiya har na Ummah ma, tace Teemah ta ha’da ta da Ummahn pls.
Fita tayi dan kaiwa Ummah wayar inda ahanyan ne take bawa Mummy labari akan yau zata fita yawo ita da Hannah tace Mummy kinga kayan da kika aiko manan nan kuwa yanda yamin kyau dan Allah Mummy ki ‘kara siya min wani, idan nazo kawai in samu, zan ro’ki daddy ai yabar ni inzo.
Mummy cewa tayi
” _Nima zanzo ai insha Allahu gobe ko jibi_ ”
Wani tsalle da ihun da Teemah ta buga da jin furucin Mummy tare da gwalo idanun ta yasa Abbas dakatawa daga tafiyar dayakeyi ya tsaya kallonta.
” _Dan Allah Mummy_ _dagaske_ _zaki zo_ ?
Ta tambaya da murna kamar zata fasa wayar ta ganta agaban Mummy.
Mummyn ma cewa tayi ” _zanzo mana Teemah ina miki ‘karyane_ !
Tsalle ta buga tace Anty ma zata zo tace min Mummy, dan Allah karku fasa kinji…….
Maganar tata yankewa yayi jin an fizgo wayan daga kunnanta daga bayanta, juyi tayi da ‘karfi zaton ta ma Hannah ce harta gama shiri ta fito hakan yasa ta fara furta ” _banason iskanci_ _Hannah da_ _mum…._
ganinshi tsaye tayi yana kallonta, baki ta rufe da hannunta tare da zaro idanu waje.
Wani kyau da kwarjini taga yayi mata, muryarta na rawa tace ” _sannu_ _da zuwa Yayah_ “
Kallonta yayi kawai batare da ya amsa mata ba, sai ma yace mata ” _welcome back Nana_ _parrots_ !
_Ke ihun naki be_ _damunki ne_ , _ke ‘daya amma kinbi kin cika gida da hayaniya kamar kasuwa_ ?
Anutse yayi mata maganar bada masifa ba ita kanta tayi mamakinsa yau ‘din.
Amma duk da haka sai tayi shiru tai ‘kasa da kanta batare da ta furta komai ba.
Dayaga bata da niyyan yin magana sai ya huya kansa tare da fa’din
” _Any ways, i heard u said zaki yawo ko?, har zuwa ina kenan haka_ ?
” _Shopping zamu_” Ta bashi amsa atakaice.
Sake tambayarta yayi
” _ke da waye_ ?
Tace da ” _Hannah_ ”
” _inji wa_ ?
‘Dago idanu tayi ta kalleshi jin yanata jero mata tamabayoyi kamar wani ‘dan jarida, da suka ha’da idanu sai ya ‘dage nashi idanun zuwa sama.
Ta fahimci manufarsa dan haka sai tace
” _inji Ummah_ !
Tana fa’din haka tafara ro’kon Allah azuciyarta akan Allah yasa kar ya hanasu fita tasan ka’dan ga aikin sa ne yace bazasu ko’ina ba, ita kuwa tana jin da ya hanata fitan nan gara yayi mata komai ma amma banda shi.
Cikin haka wayan ta dake hannunsa yafara ringing ‘dagowa yayi sai yaga Mummy ce ta’kira, yana ganin haka sai ya mi’ka mata wayar yana kallon cikin idanunta.
Ahankali tasa hannu ta kar6a tare da sada ta da kunnenta tace
” _hello, Mummy_ !
” _Ah ah ban kai ba tukunna bari nayi sauri inkai mata_ “
Iyah abinda yaji ta fa’da kenan.
Tana fa’din haka ta yanke ‘kiran tare da juyawa da niyyar tafiya.
Muryarshi tajiyo yana fa’din
” _In kin kai mata wayan ki kawo min ruwan sha_ “
Shima yana gama fa’din haka ya juya yafara tafiya, Teemah kam bayansa ta tsaya tana kallo tana kwa6a baki, mutun kullun kamar ghost be ta6a yin dariya.
‘Dan ‘karamin tsaki taja da ta tuna cewa duk da hakan da yakeyi bata san meyasa lokuta da dama takanji son ganisa ba duk da kuwa bawani abin kirki ke ha’da su ba amma zuciyarta na yawan janta zuwa tunaninsa ko son ganinsa.
Kamar yanda yace ‘din kuwa tana kaiwan wayan ta taho domin kawo masa ruwan tasa meshi tsaye yawani zuba hannaye acikin aljihun army green ‘din wandon dake jikinsa.
Ita kanta da ta shigo tayi mamakin yanda ‘dakin yayi ‘kura ko dan an kwana biyu ba ayi amfani dashi bane oho.
Tana shirin fita daga ‘dakin ya dakatar da ita da fa’din ” _Zo ki kintsa min ‘dakin nan_ _please_ “
Waro idanu tayi waje idanunta har ya fara tara hawaye bata san ma lokacin da bakinta ya furta ” _Yayah yanzu fah zamu fita mun gama shiryawa_ !
Gira ya ‘dage zuwa sama yace
” _So_ ?
_Come on zo ki kintsa min ‘daki, kwaje shopping ‘din gobe in Allah ya kaimu_
‘Bangaren Hannah kuwa harta gama shirinta tafito bata ga Hannah ba sai ta yi gurin Ummah dan ganin ko tana can ne, amma kuma sai ta tarar da Ummah zaune ita ka’dai, tambayar Ummahn tayi tace ” _Ummah ina Teemah fa ko de tagaji da jirana ta wuce abinta dan naga_ _yau zumu’di_ _takeji_ _dashi_ ”
Murmushi Ummah tayi tace
kafin ma ta rufe bakinta sai Ummah tace mata ” _Ta kaiwa Yayanku abin sha ne bari ta dawo_ “
” _Yayah ya zo ne dama Ummah_ ?
Hannah ta tambaya lokacin tana shirin zama agefen Ummah.
Amsa ta bata da fa’din ” _ehh be ma da’de da isowa ba yanzun nan ya shiga ciki, kije mana ku gaisa_ “.
‘Dan ‘karamin tsaki Hannah tayi tace ” _barshi Ummah sai mun dawo kawai naje kafin nan ma kinga ai ya ‘dan huta_ “
‘Dan hira suka ‘dan fara ta6awa da Ummahn kafin Teemah tazo, anan ne Ummah ke sanar da Hannah batun zuwan Mummy harma da Anty da Teemah tafa’da mata.
Hannah tayi murna sosai har zuciyarta da jin cewa Mummy zata zo saboda ita kam tana son Mummy ko dan goya mata baya ma datake yi akan komai sa6anin na Anty data kya6e baki tace ” _Allah ya kwaota lafiya_ “
Teemah kuwa nacan tana aiki tana share hawaye, haushi gaba ‘daya ya bi yacikata shima Abbas yana tsaye har yanzu be motsa ba har ta shiga tagama kintsa bedroom ‘din ta wanke bathroom ta fito yana nan tsaye ,tasan cewa zefi fara bu’katan can ‘din kafin parlour shiyasa tafara gyara cikin.
Tana aikin takaici fal zuciyanta tarasa meke damunsa shi akullum yafi son yaga ya ‘kuntatawa mutun in bahaka mi ye ruwansa da fitan su harda zai ce wani bazasu fita yau ba sai gobe, salon yanuna halinsa afili kawai, bayan gobe Mummy da Anty zasu zo shine kuma zata fita yawo? tama rasa me ya dawo dashi wallahi, mutum sai fitinan tsiya.
Yana nan tsaye, yana tunanin yanda yaga yau duk ta canja tayi wani kyau na musamman da ita, duk da yake dama ita ‘din me kyau ce amma na yau ‘din na musamman ne, sai de har yanzu tana nan arame bata mai da jikinta nabaya ba.
Hawayen da yaga take ta sharewa ne ya ‘dan ‘dauki hankalin sa sai ya fara bin duk wani moves ‘dinta da idanu, gani yayi da gaske kuka takeyi da hawaye, alokacin ma barta kammala shara ta goge ko’ina saura goge center table ‘din dake tsakiyan parlourn ne ka’dai yarage take kan yi, sai ya taka ahankali ya isa inda take.
Hannunta ya kama ya mi’kar da ita tsaye sai kuma ya tsaya yana ‘karewa cikin idanun nata kallo, ‘kasa tayi da nata idanun jin gaba ‘daya sun mata rauni, sam yanzu bata iya juran kallon tsakiyar idanunsa, intayi hakan kuwa jikinta har rawa yake ‘dauka gaba ‘daya, Yayah Abbas kwarjini yake yi mata sosai.
Ko yanzun ma ‘kasa tayi da nata idanun hawayenta na sake gangarowa ahankali.
Da yatsan sa ‘daya ya shafo hawayen nata sai ya sake nuna mata a saitin idanun ta wanda dolenta ta ‘dago ta kalli yatsan daga nan ta ‘dan kalle shi ka’dan, suna ha’da idanu sai shi ya sake bu’de nashi tare da ‘dage gira sama da sauri tayi ‘kasa da kanta ahankali yace ” _dan nasaki aiki kike yin kuka_ ?
Story continues below

Kai ta jijjiga masa alamar ” _ah’ ah_ “
” _Toh menene_ ?
Ya sake tambayarta.
” _bakomai_ “
Teemah ta bashi amsa ahankali.
” _Ohh dan na hana fita yawo ne ko_ …?
Kafin ma ya rufe ba kinsa cikin shagwa6a66iyar siririyar muryarta ta tare shi da fa’din
” _Na da’de fah Yayah banje ko’ina ba, kuma kullun ina son siyan abu_ _amma bana fita ko’ina, sai yau Ummah tace zamu ni da_ _Hannah…kuma…kuma_ …
Sai ta ‘karashe da in-inah ta kasa ‘karasawa illah sabon hawaye hawaye daya gangaro .
Abbas ne ya ‘karasa mata da fa’din
” _Kuma sai na hana_ _ko_ ?
Shiru tayi masa bata tanka ba, sai ta sake kwa6a fuska kawai.
Abu ‘daya ke sanyaya ranta idan ta tuna zata ga Mummynta shiyasa ma take ‘danjin dama-dama.
Abbas kam tsayawa yayi yana kallonta yarintarta na birge shi, komai nata ma shi birgeshi yake yi sai de kukan da takeyi ‘din har zuciyarsa yake jin ciwonsa, tausayinta yaji ya kamashi, hakan yasa shi lowering voice ‘dinsa yace mata ” _banace gobe zakuje_ _ba_ ?
Kai ta ‘daga masa alamar ” _ehh_ “.
” _so why d tears_ ?
Yayi maganar tare da ‘dage gira ‘daya.
Cikin wani shagwa6an tace ” _gobe fa Mummy zatazo, kuma banaso tazo bana nan_ “
Murmushi yayi mata da jin wannan shirmen kuma sai yace mata ” _kin fiye kwa6a ke kam,_ _angaya miki idan tazo ‘din zata koma kafin ki dawo ne_ ?
Jijjiga kai tayi.
” _Toh oyah wipe all those tears ban son shirme_ ”
Fara share hawayen tayi da hannunta ‘daya, sai ya ‘dago ‘dayan hannunsa ya fara tayata gogewa ahankali, yana gogewan yake fa’din, ” _kar na ‘kara ganin_ _hawayen nan kinji, idan bahaka ba naga kin sake yin wani kuka toh goben ma baza’a je_ _ko’ina ba kuma zance da Mummyn ma karta zo_ ……
Hannah ce ta iso da sallamarta da niyyar duba Teemah ganin lokaci na tafiya kuma tajita shiru.
Cak ta tsaya tana mamaki ganin su tsaye daf da daf Kamar ze mai da ta cikinsa yana share mata hawaye.
Abbas kam ko ajikinsa sallamar Hannah kawai ya amsa tare da ‘dauke hannunsa daga kan fuskar ya yi kamar babu abinda yayi.
” _Ina yini Yayah_ “
Hannah ta fa’di tare da kawar da kanta gefe.
Da
” _lafiya_ ” kawai ya amsata daga nan ya juya ya shige cikiabinsa, itama Hannah bata damu ba dama tasan iya amsar dazata samu kenan dan haka sai ta nufi gurin da Teemah ke tsaye da sauri ganin ta wata iri.
Hannunta takama taja ta suka nufi hanyar fita, sai da suka ‘danyi nisa da ‘dakin nasa kafin Hannah ta tsaya ta tambaye ta cewa
” _me Yayah yake miki afuskarki yau kuma_ ?
Bata bata amsar tambayar taba sai tace
” _Yayah yace wai ba zamu fita yau ba, sai de gobe_ “
Duk da taji haushi sosai da jin abinda ya fa’da ‘din amma ita bashi take son ji ba dan haka sai tace ” _that a side Teemah bani amsar tambayata_ ”
Shiru Teemah tayi mata dan bata san me zata ce mata ba,tace da hawayen ta ya goge mata ko kuma tace me?
Juyawa Teemah tayi ta nufi hanyar ‘dakinsu.
Shan gabanta Hannah tayi tace ” _to shikenan tsaya,_ _wai dagaske cewa yayi bazamu_ _ba_ ?
Cikin sanyin murya tace ” _Dagaske ne mana Hannah zan miki karyane_ “!
Hannah cewa tayi
” _Toh shi dama baya zo ba sai ya damu mutun, sarkin kwafsi ai nasan ze aikata tunda naga kin da’de baki dawo ba sai dana ayyanah, Allah Yayah ya cika bada mutun wallahi, sai dana gama ‘daga wa kaina hankali nagama shiri ina murnar zan kaiki kiga gari shine ya hana kuma_ “
Story continues below

‘Dakinsu suka koma ko wajen Ummah basu kuma zuwa ba. sai can da Ummah taga shirun yayi yawane shine tafito dubasu.
Direct ‘dakin Abbas ta nufa dan tayi zaton ko shi yari’kesu.
Koda ta isa ‘dakin nasa zaune tasame shi akan cujera ya na duba system ‘dinsa ganinta yasa shi ‘dago kansa zuwa kallonta.
Ummah kam ganin ko’ina fes sai tayi mamakin yaushe kuma aka gyara shi, atake ta tuna ashe fa ba’a gyara ‘dakin ba shaf ta manta wallahi, wata’kila akan aikin yari’ke min yarinya.
Kauda zancen tayi ta jefa masa tamabayar ” _ina yaran nawa suke_ ?
” _Ummah ai sun da’de da barin nan_ ”
Mamaki tayi tace masa ” kamu su wani abin ‘kila dan nasa haka banza bazan ji shiru har haka ba”
Murmushi yayi yace mata ” _toh ni me zan musu Ummah_ ?
Tace
” _Ni da kai ne ai idan_ _naji wani abu_ ”
Be yi magana ba kawai ya sunkuyar da kansa yana murmushi da jin maganar Ummahn.
Ahankali Ummah tace
” _ya bangansu ba toh, bari dai_ _induba ko suna ‘daki_ “
Tayi maganar tare da juyawa ta koma zuwa dakinsu.
Tana tafiyar take tunanin kardai tafiya sukayi batare da sun mata sallama ba, in kuwa haka ne tasan duk tsirin Hannah ne.
Tura ‘kofar Ummah tayi ta ri’ke ahannunta batare da ta ‘karasa ciki ba ganin kowa na sabganshi a’dakin tamkar sun manta da batun fitan da zasuyin gashi har yamma ta kawo kai basu tafi ba.
Sukuwa ‘karan bu’de ‘kofan ne yasa dukkansu hankalinsu ya kai gurin ‘kofar afirgice domin basuyi zaton mutun ba sai suka ga ashe Ummah ce
Cewa tayi
” _har kunje kun dawo ne_ ?
Hannah ce tayi saurin bata amsa da fa’din ” _ba Yayah ya hana mu ba, wai sai gobe zamu_ “
Murmushi Ummah tayi cikin nuna halin ko’in kula tace ” _toh Allah_ _ya kaimu goben_ “!
Zaburowa Hannah tayi tace ” _haba Ummah kema haka zaki ce kuma?_
” _Toh me kike so in ce Hannah bayan lokacin daya hana ku fitan baku zo kun sameni ba, yanzu da lokaci ya ‘kure kuma me zance in banda Allah ya kaimu goben_ “!
Kwafa Hannah tayi tace
” _Allah Yayah yaban haushi Ummah, kuma fah shi ya ri’ke Teemah da aiki har sai da yaga_ _lokaci ya ‘kure tukunna_ “
Teemah kam ko ‘kala bata ce ba dan kwata-kwata ma bata san me zata furta ba ita.
‘Karasowa ciki Ummah tayi ta zauna akan stool ‘din dressing mirror sannan ta dubesu tace.
” _kuyi ha’kuri ai inda rai gaben ma kamar yau ne karku damu kunji?_
Kallonta ta mayar kan Teemah tace
_Fateemah kiyi ha’kuri kinji halin Yayan naku ne_ _sai a hankali_ “
Murmushi Teemah tayi itama ta sunkuyar da kai ‘kasa yanzun bata jin yin magana ne.
*****
Washe gari kuwa dawuri suka gama shirin su tun 11am, saboda su samu su sake sosai sun gama tsara cewa yau ‘din sai sun sha yawo sosai kafin su dawo duk da suna tsammanin ayau ‘din bazasu fasa ba.
Hannah ce ma data tsaya waya da Bilal ita ce ta ‘dan 6ata musu lokaci, dan Bilal baya ‘kasar shi kuma ba ko da yaushe suke samun damar yin waya ba sai lokaci zuwa lokaci saboda abubuwan dake gabansa hakan yasa duk lokacin da ya ‘kirata hirarsu bata yankewa da wuri, Teemah haushi kamar ta ‘kwace wayar ta jefar ganin har kwalliyarsu na shirin dusashewa amma basu fita ba, musamman idan taji yanda Hannah ke ‘ko’karin lan’kwashe muryarta idan tana waya da Bilal ‘din sai haushin Hannah ma ya ‘kara kamata tace ai duk da laifinta ma tunda take biyeshi gashi sai 6ata musu lokaci yake abanza.
Story continues below

Ba ita ta ‘kare wayar ba sai 11:28am wanda tana cire wayar akunnanta Teemah taja tsaki tare da banka mata harara.
Hannah murmushi tayi tace mata ” _ya haka ne ‘yan mata, let me be please ko dan ke baki san so ba ko? yes na_ _tabbata hakane, shiyasa ma naga kike wani banka_ _min harara…_ “
Dakatar da ita Teemah tayi cikin jin haushi da fa’din ” _ban san so ba kika_ _ce_ ?
_Karki manta fah har aure nayi kinga kuwa ‘karshen sanin so kenan ko_ “
Dariya ka’dan Hannah tayi idanunta akan wayarta tace
” _wancan ai is different, aure kikayi amma ba soyayya ba, na tabbata duk ranar da soyayya ta kamaki zaki gane cewa nawa wasa ne, wancen auren kin ai bashi da bambanci da babu,_
_ehh toh kuma, bansani ba kam ko kafin ya rasu ya koya miki soyayyar shi, kuma fah ba mamaki dan yanda naga kika_ _rin’ka kuka kina damuwa da rashin san nan ze yiwu son mijin naki ke damunki……._
Mi’kewa tsaye Teemah tayi tace
” _Ya isa dan Allah Hannah kitashi mutafi ni surutun ya ishe ni haka_ “
Tayi maganar tana ‘ko’karin ‘daukar mayafinta.
Ganin ko motsi Hannah batayi ba yasa Teemah taja tsaki ka’dan tace ” _Haba dan Allah kina gani ko Hannah lokaci na tafiya salan Yayah ya sake hanamu fita ko me_ ?
Tana gama fadin haka ta nufi gaban mirror tasake duba jikinta ganin batada matsala yasa ta dauki turare kawai tasake feshe jikinta dashi.
Sai lokacin Hannah kuma ta ajiye wayar tata
ta sau’ka a agadon tana dariya tare da fa’din ” _da kin barni na fa’di gaskiya ai yarinya_ “
Juyawa Teemah tayi tace
” _Ni dai muje dan_ _Allah, inkin gama ki sameni wajen Ummah._ “
Teemah ta fa’di tare da barin ‘dakin gaba daya.
Hannah kam Teemah na fita ta janyo wayarta tacigaba da chat ‘din da takeyi da Bilal.
Tana isa parloun ta hango Ummah zaune akan kujera nesa ka’dan da kujerar dake gefenta kuma Yayah Abbas ne zaune suna ‘dan hira.
Kallo ‘daya Teemah tayi masa sai ta ‘dauke kanta, sanye yake cikin black trouser da wata longslip ash colour me zanen ba’ki layi-layi ajiki, sosai kayan sukayi masa kyau suka kar6eshi.
Kirjinta taji yana bugawa wanda hakan yayi sanadin rage mata speed ‘din tafiyarta, ahankali ta ‘karaso har inda suke ‘din ta zauna gefen Ummah, sai da ta iso ma sannan taji mahaukacin ‘kamshin turarensa mai da’di ya bigi hancinta, daya ha’du da nata ‘kamshin kuwa sai ya riki’de ya bada wani ‘kamshi me ‘kayatarwa, Ummah ce ka’dai zatayi iya bayyana hakan saboda ita ce atsakaninsu.
Abbas kam yi yayi kamar be ganta ba, amma Allah ne ka’dai yasan yanda zuciyarsa ta yaba da yarinyar, sosai yaga zallan kyaun ta ayau ‘din dan purple atamfar data saka ba ‘karamin fito da ita yayi ba.
” _Har kun gama_ _shiryawa ne_ ?
Ummah ta tambayeta bayan ta maida dukkan hankalinta zuwa ga Teemah.
Kai Teemah ta ‘daga mata alamar ” _ehh_ “
Kasancewar sun gaisa da Ummahn dasafe Abbas ne kawai basu gaisa ba dan shi ba’a zuwa ‘dakinsa haka kawai dan gaisuwa idan ba shine yanemi mutun ba toh sai de inya fito ka gaisheshi, hakan yasa ta ‘dan ‘dago kanta ka’dan tace
” _ina kwana Yayah_ !
Be amsa ba sai da ya ‘dago shima ya kalleta kafin ya amsa da fa’din ” _lafiya ‘kalau_ .”
Bata ‘kara wata gaisuwar ba dan tasan ko tayi ma ba sake amsata zaiyi ba.
Abbas kam yanzu kasa ‘dauke idanunsa yayi akanta Allah ma sai ya taimakeshi Ummah ba shi take kallo ba hankalinta nakan Teemah ne, Teemahn kuwa kanta na kasa shiyasa ma yasamu chance ‘din kare mata kallo hankalinsa kwance.
” _Dan Allah Fateemah inkun je_ _karki biyewa Hannah kinji, nasanta iyayi gareta gashi inta fita shopping tana da’dewa kafin ta dawo kamar zata na’do komai pls_ _karki biyeta Fateemah ku dawo_ _da wuri kinji Antynki ma tana hanya yau zata zo_ ?
Ummah ce tayi maganar cikin sigar lallami.
Story continues below

Kai Teemah ta ‘daga mata alamar ” _toh_ ” Tana murmushi dajin cewa Anty na hanya sai de gaba ‘daya jitake ta takura da zaman, hakan yasata lafewa ajikin Ummah kamar wata ‘yar yarinya ‘karama.
Muryar Abbas suka jiyo yana fa’din ” _wai Ummah ina zasu ne ba fah na son yawon nan ni_ “
‘Dagowa Teemah tayi da mamaki ta kalleshi suna ha’da idanu kuwa sai ta kauda kanta gefe tare da turo baki aranta tace _lallai ma Yayan nan, bacin shine jiya ya hanamu fita yace sai yau kuma da_ _yau ‘din tayi sai_ _yawani ce be san da_ _zancen ba_ .
Ummah tariga tasan halinsa na nuna ko’in kula akan abubuwa shiyasa ma bata meda zancen baya ba duk da tasan yasan da batun fitan amma sai kawai tace masa ” _Shopping zasu je ko_ _zaka kaimin_ _su_ “
” _Ni kuma Ummah? Inada inda zani fah_ “
” _Nasani ai Abbas naga akn hanya shiyasa_ ” ummah ce ta fa’di hakan tana kallonsa.
Yana so yace ina driver amma sai yaji bakinsa yayi masa nawi, kawai sai ya koma baya ya ha’da jikinsa da jikin kujera yayi wa Ummahn shiru, minti ‘daya be cika ba sai ga Hannah ta fito cikin ‘dan sauri-sauri ta nufo su.
Sai da ta gaida Yayan kafin tace da Teemah su tafi.
Dayake alraedy Ummah ta sallame su inda ta tura ma Hannah ku’din shopping ‘din a account bata basu cash ba.
Tashi Teemah tayi suka yiwa Ummah sallama ,
Ummah nata yi musu addu’ar Allah ya bada sa’a suka amsa da (Ameen) kafin suka nufi ‘kofar fita.
Abbas ma tashi yayi ya bi bayansu yana wannan ‘kasaitacciyar tafiyar nan tasa me birgewa.
Ahanya yazo ya wuche su Teemah nayi mata gulmar wai shi ai zai kaisu.
Haushin ha’da su da Ummah tayi Hannah taji dan tasan ba barinsu zaiyi su sake ba.
Koda suka isa jikin motar ma Hannah ‘kin shiga gaba tayi dan har yanzu basu gama da Bilal ba chat sukeyi dashi shiyasa ma bata son shiga gaban don tsoro takeji kar Abbas ya kamata.
Muhawara suka tsaya yi dan Teemah ma ‘kin shiga gaba tayi sai da ya daka musu tsawa kafin kowa tayi saurin bu’dewa tashiga.
Koda ya kai sun kuwa ‘kin barin su yayi sai da yaga sun gama yabiya ku’din kafin yasako su agaba suka dawo gida.
Shopping sosai sukayi dan suna da ishashshen ku’di a account ‘din Hannah shiyasa ma suka saki ransu suka jidi tarkace harda na banza, cikin sa’a kuwa sai Abbas ma ya biya bill ‘din.
Koda suka isa gida kowa ‘diban kayan yayi, Hannah ce tafara ‘diba ta wuche ciki, koda Teemah ta ‘diba ta fara tafiya kuwa kasawa tayi sai da ta ajiye dan wanda Hannah ta bar mata sunfi yawa.
Numfashi take sau’kewa ahankali tana watsa hannu ga dukkan alamu zafi suke mata.
Tana ‘ko’karin sake ‘dauka ta tsinkayo muryarsa yana fa’din ” _idan bazaki iya ba dole sai kin ‘dauka duka lokaci ‘daya ne_ ?
Sai lokacin ma tunanin hakan yazo mata dan haka sai ta raba kayan ta ‘dauki ka’dan ta nufi ciki inda ta bar sauran awurin akan inta dawo ta ‘karasa ‘dauka.
Tana cikin tafiya taga yazo ya wuche ta hannunsa da ragowar kayan, bin bayansa tayi sai ya kasance kusan tare tafiyar tasu take.
Yana shiga parloun kuwa itama ta 6ullo sai ya kasance atare suka shigo.
Anty na saitin ‘kofa ne dan haka ita tafara ganinsu take kuwa taga dacewar kasancewarsu a inuwa ‘daya, zata so Fateemahn tasamu jajirtaccen namiji irin Abbas wanda zai kula da rayuwarta ba kamar yanda ta so cin zarafinta abaya ba.
Teemah na shigowa idanunta kan Anty ya sau’ka ai bata san lokacin data sake kayan ta nufe ta da gudu ba ta fa’da jikinta.
Abbas bin ta yayi da kallo yana mamakin hakan kuma, wanda sai alokacin shi kuma ya hango abinda yasa Teemahn gudu.
Ahankali ya ‘karaso bayan yayi ‘ko’karin danne ba’kin cikinsa ya yi mata barka da zuwa sannan ya ajiye kayan su Teemah ya shige ciki.
Anty bakinta kamar gonar auduga ganin Fateemah ta warware.
” _Anty dagaske dama ashe zaki zo_ ?
Ta tambaya tana dariya.
Antyn ma dariyar tayi tace ” _zanzo mana Fateemah bani na fa’da miki ba_ ”
” _Mummy ma tace zata zo ai itama_ “
Cewar Teemah
Washe baki Anty tayi tace ” _Allah ya kawota lafiya ashe shiyasa naga bakinki ya’ki rufuwa duk murnar za’a ga Mummy ne?_ “
Dariya dukkansu suka sanya har Ummah Teemah ce ta ‘karasa da fa’din ” _harda kema ai Anty_ ”
Bayan sun gama dariyar ne Ummah tayi mata bayanin cewa ai Mummyn ba yau zata taso ba sai zuwa gobe in Allah ya kaimu.
Hannah kam tuntuni ta shige ciki tunda ta gaida Antyn tayi shigewar ta dayake dama ita bason matar takeyi ba.
Ranar kam Fateemah murna kamar ta tashi sama dan taga Antyn ta.
Awurinta ta wuni tabi tacika ta surutu har yamma suna tare da ‘kyar Ummah ta korata dan Antyn ta samu ta ‘dan huta.
Da daren ranar Daddyn Abuja ya dawo, Abbas kam beji da’din haka ba danshi tsoron ha’duwa dashi yakeyi dama kafin yazo ma sai da ya tabbatar baya gari kafin ya zo ashe ma yakusan dawowa.
Daya san haka kuwa da ya koma abinsa tun da safe.
Ai kuwa da daren ya gama shirinsa da sassafe ya fito yaje ya gaida daddyn yayi masa sallama.
Daddy yariga ya fahimce shi ayanzu be 6oye ba kuwa yace masa ” _wato kana guduna ne ko Abbas_ ?
‘kasa yayi da kansa yace ” _ah ah Daddy bahaka bane dama yau ‘din na shirya komawa_ “
Daddyn ma ce masa yayi
” _Toh ba komai, Allah ya bada sa’a amma karka manta kadawo da wuri domin nextweek za’a ‘daura auren ka nariga nagama shirya komai ranar kawai ake jira tazo, sai ka fara shiri_ “.
Abbas a firgice ya ‘dago idanunsa ya sau’ke su akan Daddy,
Daddy kam ko ajikinsa dan yana gama fa’din abinda ze fa’da ya shige ciki.
Motsi me kyau Abbas kasawa yayi sai de yabi bayan Daddy da kallo da idanunsa da suka gama riki’de wa zuwa ja, har ya shige cikin kuwa Abbas be daina kallon ‘kofar ba tsawon mintina biyar kafin ya tashi ahankali ‘kafafunsa ma nauyi suka masa da ‘kyar yake ‘daga su ya nufi 6angaren Ummah.
Zuciyarsa ce kawai ke beating da ‘karfi ajikinsa bayaga haka kuwa gaba ‘daya jikinsa yayi sanyi ‘kalau.
Fasa zuwa wurin Ummah dan yi mata sallamar yayi kawai sai ya wuce ‘dakin sa ya zauna a kujera tare da dafe kansa.
Tsawon mintina yana a haka shi ka’dai yasan me yake ji azuciyarsa baya fatan abinda Daddy ya fa’da ya kasance gaskiya, aure!……aure kuma da waye haka toh?
Yana jin wannan karan kam ba ze sake yin saken da zata ta kubce masa ba, ba ze ‘ki yiwa Daddy biyayya ba amma shima zai auri za6insa koda daga baya ne.
Su Teemah ne yau a kitchen suna aikin breakfast ita da Hannah, sunayi suna ‘dan ta6a hira inda duk hirar tasu Hannah ce ‘kwa’kulo ta wani lokaci har fa’da sukeyi in maganar Hannah ya bawa Teemah haushi garin haka ruwan zafin jikin marfin tukunya ya zuba wa Hannah a ‘kafarta.
Tare da su Ummah da Anty suka ci breakfast ‘din, bayan gamawar su ne Ummah ta ‘dauki na Daddy tace zata kai masa, Anty ne tace da su Hannah sukai na Yayansu ma tun da be fito an karya dashi ba, take Ummah ta hana tace abarshi yanzu akaran banza zai koro min yara na tace abari sai yazo dakan sa dan baya son ana damunsa idan yana ‘dakinsa, dayake bata san da batun tafiyar sa ba.
Koda takai na Daddyn kuwa ta same shi ne yana amsa waya hakan yasa ta gama harha’da masa kafin ya kare wayar ta kawo center table ta ajiye masa agabansa, dan tasan shi be fiya cin brekfast akan dinning ba.
Yana sau’ke wayar kuwa yace mata
” ‘ _danki ya wuche ko?_
Da mamaki tace masa
” _wani ‘dan kuma Alhaji?_
Tea cup ‘din dake gaban sa ya ‘dauka ya ‘dan kur6a ka’dan sannan ya cire daga bakin sa ya kalle ta da kyau ya ce ” _Abbas nake nufi!”_
Mamakinta kasa 6oyuwa yayi har sai da ta bu’di baki ta tambaye shi dalili dan kuwa daya zo be cemata zai koma so soon haka ba, bayaga haka ma ko sallama be je yayi mata ba haka kawai sai take jin bata yarda ya tafin ba.
Anan daddy yayi mata bayanin komai dake faruwa yace ” ‘ _kilan haushi na da yake ji ne ya shafeki kema shiyasa har ya wuche be sanar da ke ba, amma ni kam yazo yayi min sallama da sunan zai koma bakin aikinsa ni kuwa ban dakatar dashi ba”_
Ummah kam gaba ‘daya kanta sai ya kulle da maganar Daddyn bata fahimci komai ba dan haka sai tace ” _Alhaji haushin ka na me Abbas zaiji kuma, ko de akwai wani 6oyayyan_ _abinda yafaru ne da_ _bansani ba_ ”
Story continues below

Juya kai Daddy yayi tare da fa’din
” _Ehh toh kusan zance hakane gaskiya, sai de wannan al’amarin daban ne, kinsan dama ina shan yawan yi masa batun aure while shi kuma baya so, toh ina ganin dalilin kenan da ya sa ko ha’duwa dani be son yi shiyasa daya ga na dawo jiya sai shi kuma ya shirya komawa ayau, lokacin daya zo min sallama ni kuma nasanar dashi hukuncin dana riga na yanke, wanda dama ko da be zo Abuja ba ni zansa shi yazo saboda dole ana bu’katarsa_ _domin auren sa za’a ‘daura a sati me zuwa in Allah ya kaimu_ ”
Ummah kam wani banbara’kwai taji maganar tamkar amafarki cewa tayi
” _haba, haba Alhaji aure kuma da gaggawa haka ba wani shiri kamar_ _wani abin sirri, gaskiya be kamata ba, meyasa baza kayi hakuri ka ‘kara masa lokaci ba_ ?
” _Nagaji da jiran lokacin nasa ne shiyasa nayi haka, ke kanki kin san mun dad’e muna fama dashi a kan maganar nan, ba sai na gaya miki ba, amma yaron nan baya ma saka zance na acikin al’amuransa ballantana ya bata muhimmanci, sanadin haka ma kina gani wasan 6uya ya fara dani, duba fa kigani jiya-jiya na zo gidan ga_ _amma dan ya nuna min halinsa yau da sassafe sai ya zo min da batun komawa, duk nasan manufar sa ai tunda ni ne na haife shi, har yaushe zan ta maimaita masa abu iri ‘daya kullum?_
Kwantar da murya Ummah tayi ta ringa bashi ha’kuri dan taga kamar beji da’din abinda Abbas ‘din ya masa ba amma sai Daddy ya dakatar da ita da fa’din ” _ni ai banda matsala dashi yanzu, na riga na yanke decision ‘din dana ga yayi min and bazan fasa ba, munyi magana da Yah Kabiru akan haka kuma Alhamdulillah nasamu ya amince amma fah da ‘kyar dan kin san shima ‘dan partyn Abbas ne, wai taya zance ya auri bazarawa bayan shi be ta6a zama da mace ba”_
Zaro idanu Ummah tayi akansa tace ” _Yah subhanallah, me kakae shirin fa’da ne Alhaji? dan Allah Alhaji ka daina wannan maganar ai ko ni nan ba yadda zanyi ba inde har bazawara kake nufin zai fara aura, wallahi bazan ta6a goyon bayan hakan ba, kayiwa Allah Alhaji ka dakatar da wannan zancen, zanyi magana dashi insha Allahu cikin ‘kan’kanin lokaci zai zo maka da_ _magana mai kyau_ …………”
Kafa’da Daddy ya ‘dage alamar wannan ba damuwar sa bace shi, sannan yace ” _ai da zaiyi hakan da ya da’de dayi tun ma ba azo wannan_ _matakin ba daya da’de dayi tun abaya, kuma da_ _kike cewa wai bazawara menene….ki gaya min auren bazawaran haramun ne_ ?
Dolenta ta jijjiga kanta domin tasan bata da hujjan haramtashi tunda annabin mu haka yayi.
Duk da haka sai tace
” _Amma dai Alhaji ka duba lamarin kaima dan Allah, dududu nawa Muhammad ‘din yake ne har ayanzun fa be gama cika shekara talatin ba, amma kake ta faman damun kanka da batun yayi aure har yanzu fa yana da sauran lokaci……._
Taran ta yayi da fa’din
” _Bazaki gane bane ke, nifa da kike gani zaman sa hakan nan ‘din ne sam banso, musamman da ya kasance aikinsa na yawo ne, sosai na yadda da tarbiyar yarona kuma na bana zarginsa ,dalili ma kenan da ya sanya na ke so naga yana da iyalin kansa dan gudun_ _kar wata 6araka ta 6ullo daga baya shiyasa nake son taran ta da wuri_ , _dan Adam duk ‘dan Adam ne, hankali na zaifi kwanciya sosai idan ya_ _kasance yana_ _da iyali_ ”
Kauda kai Ummah tayi gefe dan ta lura Daddyn ba canja ra’ayi zaiyi ba sai tace ” _Toh Alhaji in kuma iyalin ne dole sai ya kasance bazawara_ ?
‘Dan 6ata rai Daddy yayi ka’dan yace mata
” _Kinsan banason musu ko_ ?
Sai tace
” _Kayi hakuri Alhaji_ ”
” _bana so na sake jin kin fa’di haka, inada iko akan yarana shiyasa na yanke hukunci, kuma nasan dukkansu zasu min biyayya, kuma babu fashi auren nan da iznin Allah sai anyishi, iin kuwa_ _har kikaga ba’a ‘daura auren yaron nan da Fateemah ba to ikon Allah ne ka’dai_ _ya hana hakan faruwa_ “
Shiru Ummah tayi tana juya zancen a ‘kwa’kwalwarta dake cushe tab da tashin hankali, bata sake furta masa komai ganin kamar maganganun nata basu da wani amfani dan ga dukkan alamu wannan mutumin bashi da niyyan sauya ra’ayi, tsawon da’kiku tana ahaka yayin da da Daddy ke ta shan tea ‘dinsa cikin kwanciyar hankali, can Ummah ta mi’ke tsaye jikinta sanyi ‘kalau ta nufi hanyar barin ‘dakin tare da fa’din ” _Allah ya kyauta_ “
Story continues below

Daf da zata fita ta tsinkayo muryarsa yana fa’din ” _baki tambayi wacece yarinyar ba kike shirin tafiya kuma_ ?
Juyowa tayi ta kalleshi sannan tace ” _babu amfani ai tunda ba saninta nayi ba, sunan ta danaji ma ka’dai ya_ _isheni_ ……..”
Da sauri ya tare ta da fa’din ” _who told u that jin sunan ta ka’dai ya ishe ki?, Fateemah ce fah , Fateemahn gidan_ _nan_ !”
Ummah najin haka ta washe baki tace ” _haba dan Allah Alhaji , gaskiya baka kyauta min ba Fateemah ce shine_ _kuma ka barni nake ta 6ata bakina abanza_ ?
Murmushi Daddy ya mata yace ” _yanzu kam ai kinji sai kuje ku fara shirye-shirye dan nasan ba’a rabaku da shi_ ”
Yana gama fa’din haka yaci gaba da cin abincin sa.
Ummah ce ma ta ‘kara fa’din ” _Shirye- shirye sosai ma_ _kuwa_ “
tare da barin ‘dakin.
Daga wurin Daddy Ummah direct 6angaren Abbas ta wuce, bata same shi a palournsa ba dan haka sai ta nufi ciki da sallamar ta inda tasame shi zaune abakin gado sanye da dogon wandon jeans da farin singlet , bazaka ta6a gane yanayin da yake ciki ba in ba kasani ba, sa6anin Ummah da suna ha’da idanu dashi ta fahimci ba dai-dai yake ba.
Da sauri ta ‘karasa kusa dashi ta ‘kira sunanshi.
Jin yanda tayi maganar ne ya sashi ‘ka’kalo murmushin dole ya sanyawa fuskar sa tare da ‘dagowa ya kalleta amma be tsawaita ba ya kauda kansa gefe dan ba ya son ta fahimci halin dayake ciki.
Da ‘kyar ya bu’di baki yace ” _ina kwana Ummah_ ?
Da ” _lafiya ‘kalau_ ” ta amsa masa, kafin ta sake yin wata magana kuwa ya tareta da fa’din ” _Ummah baki bari naje ba sai kika zo da kanki kuma_ ?
Cewa tayi ” _bakomai ai duk ‘dayane_”
sannan ta ‘kara da fa’din ” _u look tensed Abbas meke faruwa ne_ ?
Abbas kansa ya shafa yace ” _ba komai fah Ummah kawai na tashi da ciwon kai ne yau_ _’din_ ”
Tace
” _Ahakan kuma da kace zaka hau hanya_ ?
Shiru yayi mata beyi magana ba.
Ummahn ma sai ta zauna a gefen sa tare da fa’din ” _look Abbas, mahaifinka yagaya min cewa nextweek za’a ‘daura aurenka, hakane ko_ ?
Cemata yayi
” _Haka nima haka yagaya min ‘dazu_ ”
Tace
” _good, kasan me nake so da kai_ ?
‘Dagowa yayi kawai ya kalleta sai taci gaba da fa’din ” _banson ka sanyawa raka damuwa da wannan batun balle har yayi affecting al’amuranka dan Allah, ni nan inada_ _tabbacin auren ka alkhairi ne Abbas kuma ha’din Allah ne, da izninsa kuwa bazaka ta6a yin kuka da Fateemah ba, zakaji da’din auranka insha Allahu domin na yadda da tarbiyar Fateemah ‘dari bisa ‘dari kuma kaima kanka shaida ne akan haka…….”_
Tun anan kan Abbas ya fara yi masa nauyi be san wace Fateemah bace amma yanaji ajikinsa kamar ya santa.
Har Ummah tagama surutunta ma be jiba hankalinsa duk ya ‘dauku ga tunanin ko wacece yarinyar sai ya ji Ummah na sake fa’din “……… _please ka cire damuwar nan aranka kaji_ ?
Ahankali bakinsa ya furta ” _insha Allahu_ “
Dan be san me ze ce da Ummah ba bayaga haka.
Ummah kam tashi tayi tsaye tana fa’din ” _yauwa babana Allah ubangiji ya albarkakaci rayuwarku gaba ‘daya ya sanya haske cikin al’amuranku”_
Da ” _Ameen-Ameen_ ” ya amsa mata.
Daga nan tayi hanyar fita tana fa’din ” _yaran nan zasu kawo maka breakfast ‘dinka yanzu sai ka samu ka ‘dan ta6a please ko ka’danne_ “
Shikam yanzu ba breakfast bane damuwar sa maganganun Ummah ne ke masa yawo a ‘kwa’kwalwa, so yake yasan wacce Fateemah ce haka da har mahaifiyarsa ma da kanta ta yadda da ita har kuma take ikirarin shima shaida ne akan halinta haka?.
Story continues below

Wani sanyi yaji ya lullu6eshi tare da ratsawa har cikin zuciyarsa wanda hakan ya sashi lumshe idanu. Be san wacce yarinya bace amma ji yayi zuciyar sa tayi na’am da batun auren nata, azahiri kuwa sam bahaka bane domin ‘kwakwalwar sa bata daidaita ba har yanzu yakasa tantance yanayin da ya shiga, yafi so ya san yarinyar kafin komai yabiyo baya, Ummah yakamata ya tambaya amma yakasa aikata hakan yana gani harta tayi tafiyarta.
Tunda Ummah tafa’di sunan yarinyar ya ‘danji dai-dai damuwar sa kaso hamsin duk ya kau, natsuwa yaji ya ‘dan shige shi ka’dan da be san dalili ba, shi kansa yana so yaji da’din auransa kamar yadda Ummah tayi masa fata sai de kafin hakan ya kamata yasan yarinyar tukunna.
*****
‘ Bangaren Mummy kuwa yau ta gama duk wani shirin ta na shigowa Naija, dama tun jiya taso ta taho amma wani sabon al’amari data ji daga bakin Daddyn Teemah sai yasa ta fasawa a jiyan kawai ta shiga kasuwa ta bugo siyayya na fitan hankali sai yau ne take shirin tahowa da 6oyayyen farin cikinta azuci da Daddy ne ka’dai yasan tana ciki.
Sun rabu da Daddy akan shima yana bayanta nan da ‘yan kwanaki, da kansa shine ma ya rakata airport har se dayaga tashin su kafin ya koma gida.
Abbas na zaune har yanzu abakin gadon motsin kirki ma bayayi kamar an dasashi, ringing ‘din wayarsa da yajiyo a parlour ne ya fargar dashi amma be ko motsa ba balle ya je ga wayar tasa.
Sai da yasake jin ringing karo na biyu kafin ya tashi tare da yin tsaki ka’dan dan shi ayanzu besan damuwa wanda yake ciki ma ka’dai yana jin ya isheshi.
Ganin sunan B-Daddy da yayi akan fuskar wayar ne yasashi ‘dagawa da sauri amma kafin yayi receive har ‘kiran ya yanke dan haka sai yabi bayan ‘kiran tare da zama akan ‘daya daga cikin kujerun ‘dakin, ringing ‘daya na biyu Daddy ya ‘dauka Abbas ne yayi saurin yi masa sallama.
Daddy ma amsawa yayi daga ‘dayan 6angaren tare da fa’din ” _na ‘kira baka ‘daga ba_ ?
” _Afuwan Daddy bana kusa ne wallahi_ “
Ya ‘kara da fa’din ” _Daddy kana can ana shirin yimin aure ba shiri_ ?
Murmushi Daddy yayi jin ya maida abin kamar wasa bayan acikin muryarsa ma zaka fahimci ‘kuncin dake tattare da shi.
Yace masa
” _Nima haka sama ta ka labarin yazo min, Hassan ne ya ‘ka’kabo mana_ , _nayi ‘ko’karin hana dan ban goyi bayan al’amarin ba amma Hassan ya dage ‘karshe dole sai da na amince, amma karka damu amince wata ba yana nufin tauye maka hakki_ _bane ni nan ina tare da kai, ya ake ciki gaya min yanzu, ra’ayinka dama na ‘kira inji idan kayi na’am toh shikenan sai in kar6a maka in kuwa kaga baka so toh feel free ka sanar dani babu wanda ya isa yayi_ _maka dole matu’kar ina numfashi, karka damu da cewa Fateemah jinina ce ita bandamu ba_ _dan nima ha’din be birge ni ba, dan kaga ita ta ta6a yin aure sa6anin kai, ni sam banga dacewa_ _anan ba………..”_
Dai-dai nan Abbas ya dakatar da shi da fa’din ” _Daddy_ …..!”
” _Ya akayi, sanar dani karka damu_ “
Daddyn ya sake fa’da masa.
Be san me ze ce ba dan haka sai ya yanke ‘kiran kawai yana murmushi, komawa yayi da baya bayan ya sar’ka hannayen sa biyu cikin junan su tare da maida su ‘kar’kashin kansa yayi pillow dasu, idanunsa na kallon cielling ‘din ‘dakin kamar me karanta wani abu ajiki, daga bayane ya lumshe idanun sa maganar Ummah ce ta dawo kansa ” _…..da izninsa kuwa bazaka yi kuka da Fateemah ba, zakaji da’din auranka insha Allahu_ ”
Wani farin ciki yakeji yana lullu6e shi, kamar a mafarki wai yau auransa da Fateemah saura 1week, jiyake kamar bashi ba, finally burin sa na gab da cika cikin sau’ki batare da ya wahal da ransa ba.
*****
A can parlour kuwa har yanzu Ummah nata dramma da yaranta akan kawowa Abbas breakfast.
Farko Hannah akace ta kai masa take kuwa tace ” _Ummah nafa ‘kone da ruwan zafi a’kafata ‘dazu da muna kitchen kuma zafi yake min,_ _Teemah ta kai masa please_ ”
Story continues below

Hannah na maganar ne tana satan kallon Teemah afakaice.
Juyawa Ummah tayi ta kallo Teemah ta tambayeta wai dagaske ne Hannah ta ‘kona ‘kafarta akitchen ‘dazu?
” _Dagaske ne Ummah amma ai ka’dan ne fah kawai bata son zuwa ne_ “!
Ummah cewa tayi Hannah ta nuna mata gurin ta gani tukun na.
Sai Hannah ta nuna wani guri daya ‘danyi ja ka’dan.
Ummah ma cewa tayi ai wannan ba ze hana ta tafiya ba dan haka maza ta tashi ta ha’da ta kai masa yana can har yanzu bakomai acikinsa.
Rigima Hannah tafara irin na shagwa6a66u kamar gaske wai ita zafi waye-waye.
Anty na murmushi ta ‘dan juyo ta kalli Teemah tace ” _yi ha’kuri kinji mamana daure ki kai masa ki dawo tunda yau ‘din_ _’kafarta na ciwo_ “
Turo baki Teemah tayi tace ” _Allah Anty ruwan fah ‘diga kawai yayi….”_
Tare ta Anty tayi da fa’din ” _bana ce kiyi ha’kuri ba! maza tashi kije kinji_ ”
Tsaye Teemah ta mi’kewa tana bankawa Hannah harara da har yanzu dramar su da Ummah be kare ba, afakaice ta yiwa Teemah gwalo ganin ita zata kai.
Teemahn ce ka’dai tagani takuwa ‘kara sha’ka har wuyanta tare da jin matsanancin haushi .
Aranta tace ” _zan rama ai_ “
Da Ummah taga ta ha’da masa kuwa ta ringa saka mata albarka tana ‘karawa, duk da haushin da take ciki amma bakinta be kasa amsawa da _AMEEN_ ba.
Tana tafiyar take tuna iskancin interview ‘din da Hannah taringa yimata ‘dazu a kitchen ita adole sai taji abinda yafaru jiya tsakanin ta da Yayah, tasan yanzun ma iya shege ne kawai bawani ciwo daya dameta.
Abbas kam jiyake kamar idan yaci gaba da zama agarin nan toh kowa ma zai iya fahimtar yanayin farin cikin dayake ciki, dan haka take ya yanke shawaran gara ya tafi kawai tunda yanzu yanada tabbacin mallakarta inyaso sai ya dawo lokacin auren.
Dama already kominsa a ha’de yake dan dama da niyyar tafiyan ya kwana,maganar daddy ne ya dakatar dashi, yanzu kuwa da ya san cewa za6in Daddyn cikar farin cikinsa ne ai shikenan, da yake dama shi ba ya yin tafiya da kayan sawa in dai tsakanin Abuja da Rivers ne sai de kayan da yasan zasu masa amfani, dangin su wayoyi, system da sauransu.
Acikin wata jaka kalar Army green ya ha’da komai, Rigarsa daya cire ‘dazu bayan ya dawo daga gurin Daddyn sa ita ya maida jikinsa tare da ‘daukan jakan ya rataya akafa’dan sa ya nufo palour.
Teemah na isa ‘dakin ta tarar dashi tsaye agurin switch yana ‘ko’karin kashewa, kafa’dar sa rataye da jaka sallamarta ne ya dakatar dashi sai ya juyo ya zuba mata idanu bayan ya amsa sallamar tata.
Itama bata ajiye abin hannunta ba sai ta ri’ke tare da yin ‘kasa da kanta tace ” _ina kwana_ _Yayah_ !
Be amsa ba sai ya tako ahankali zuwa inda take tsayen ya jefa mata tambayar ” _Yau kuma fushin me kike yi? Me ya sameki_ ?
_Ya tambayeta tare da tsare ta_ _idanunsa masu rikitata gaba ‘daya_ .
Jikinta har na rawa saboda irin kallon daya ke binta dashi.
‘Kasa-‘kasa ta amsa da ” _bakomai_ ”
Juyawa yayi ya koma gurin switch ‘din da be kashe ba ‘dazun, yana kashewa kuwa take ‘dakin ya dawo duhu ba’ki’kirin.
Sannan ya mi’ka hannu ya kakkashe conditioners ma gaba ‘daya daga nan ya sake dawowa inda take tsaye.
Yanzun kam da hasken ‘dakin ya ragu har ‘daga kanta tayi ka’dan ta kalleshi sannan ta kauda idanunta gefe.
” _Kunyi magana da Daddy ne_ ?
Jijjiga kai tayi sannan ta furta ” _ah’ ah_ ”
” _Okay ba matsala, amma make sure that baki tsallake duk wani umarninsa_ _ba koda bana nan, and ki daina fushin nan haka abincin ne bakyaso ki kawo_ _min ko kuma menene_ ?
Afirgice ta ‘daga idanu ta kalleshi, hakan kuwa datayi sai yasa shi saurin fahimtar ya harbo jirgin ta, zuwa inda yake ne bata so.
Murmushi yayi sai yace ” _Yes, ai nasan halinki baki ta6a appreciating yin wata hidima agareni ba, nima ban son abincin ki koma da abinki am ok na hutar dake_ ”
Cikin shagwa6a tace ” _bahaka bane fa Yayah!_
Jakar dake kafa’dansa ya gyara
Sannan yace ” _toh menene gaya min naji_ ”
” _Ni….ni…nifah_ ….
Kame-kame ta hauyi ta rasa takamamman abin fa’da.
Murmushi Abbas yayi yace mata _”maganata gaskiya ce kenan_ ?
Yana gama
fa’din haka ya juya zuwa ‘kofa a hankali.
Teemah kam baki ta tura tabi bayansa da kallo.
Har ya kusan rabin ‘dakin sai kuma yajuyo ya sake kallanta yace ” _ki saki ranki ki daina fushin nan kin manta yau Mummy na hanya_ _ko_ ?
Da kai ta bashi amsa sai yaci gaba da fa’din ” _kinga nima yau ina cikin farin ciki kema ki tayani kinji_ “?
” _Uhmm_ “
Tace masa
Shi kuma yasake fa’din ” _natafi_ ”
” _Allah ya tsare_ “
Tace ahankali shima asaman la66ansa ya amsa da ” _Ameen_ “.
Daga nan yafice abinsa be sake juyowa ba.
Teemah ma tsayuwa taci gaba da yi agurin tama rasa mai ke damunta, jitake kamar tafiyar tasa ne bata so amma sam tarasa dalilin hakan, yau ka’dai sai taji tamkar zatayi missing ‘dinsa idan ya tafi.
Komawa tayi kitchen ta ajiye kayan kafin ta wuche ‘dakinsu ta kwanta agado tayi luf abinta.
Hannah ma a ‘dakin ta sameta wanda barinta gun su Ummah kenan bayan wuchewar Abbas.
Tana barin gurin su, Ummah ta bawa Anty labarin abinda ke faruwa.
Anty taji da’din hakan sosai tace kamar an shiga ranta anga ni, dama ita ta jima da ganin dacewar hakan, tace ai kuwa zama be kama ta ba, shiri ne gagarumi ya kusanto ta dan ma abin yazo a ‘kurarren lokaci ne in ba dan haka ba ai da bikin sai ya zama bikin ‘yar gata wanda aka da’de ba’ayi irinsa ba, duk da haka de tace bazatayi ‘kasa agwiba dole ne tafitar da ‘yarta yanda zata zama abin kwatance.
Ummah ce ta dakatar mata da tunaninta ta hanyar shigo da ‘korafi akan rashin sanar da Fateemah da Daddy be yi ba inda tace da Anty
” Sai de ina ganin kamar fa ba’a kyautawa yarinyar ba, saboda bada yaddan ta mahaifinsu ya yanke wannan hukuncin ba, ina tsoron kar a shiga hakkinta sosai dan kinsan yanzu tana da daman da zata za6i miji da kanta ba sai an za6a mata ba musulunci ne dakansa ya bata wannan damar, duk da cewa za6a matan ma ba haramun bane amma naso da an nemi yardan ta tukunna”
Murmushi Anty tayi tace ” karki damu da wannan dan Allah, ni nan nasan halin Fateemah bazata ta6a yin musu ba, shima mahaifin nasu yana da tabbaci akanta ne shiyasa kika ga ya yanke hukuncinsa kai tsaye batare da wata fargaba ba saboda yasan dukkan su zasu yi masa biyayya shiyasa be damu ba, kuma yawanci idan kinga mace tayi jayayya da iyatenta akan maganar aure toh already zaki samu tana da wani me daban, Fateemah kuwa ai nasan bata da wani manemi daban ko akwai?
Anty ta ta’karasa maganar tata da tambaya.
Jijjiga kawai Ummah tayi tace “
Bana tunanain haka gaskiya”
“Toh kin gani, insha Allahu bazata damu koda ta damun ma zata sakko da yaddar ubangiji”
Shiru Ummah tayi tana tunani aranta, ita aganinta duk da haka ya kamata Teemah tasan me ake ciki, kafin lokaci yazo ya ‘kure yakamata aji nata ra’ayin, ita Ummah ‘daukan alhaki ne take tsoro shiyasa ma ta damu sosai, wanda tunanin nan yayi mata karan tsaye a zuci ya hanata sakat dan haka sai ta yanke shawarar samun mahaifin nasu da batun.
Anty kuwa baruwanta da’di
taji dajin wannan labarin sai de kuma wani 6angaren tana tunawa da marigayi Mahmud, amma bata bari hakan ya nuna afili ba sai kawai ta takaita tunanin da ro’ka masa addu’ar dacewa wurin mahalicci.
Sai da ta koma ‘daki sannan tasha kuka har ta godewa Allahn ta, babu wanda yasani, dan haka da kanta ta ha’kura tayi shiru.
Ayanda akasa ranar bikin Abbas ‘din zai kasance kwana ‘daya tsakaninsa da na Abban Mahmud domin shi nashi ranar Saturday ne sa6anin na Abbas daya kasance ranar Friday.
Da yamman ranar Mummy ta iso su Hannah murna kamar zasu ha’diye ta baran ma Teemah da tayi matu’kar missing ‘dinta sosai kuka ta sanya ta rungume ta da ‘kyar Anty ta lallashe ta tayi shiru.
Mummy kam dataji labarin bata wani damu ba dan ta riga da taji abakin Daddy tun a Dubai, sai de tana tunanin ko shi Abbas ‘din baze amince ba tunda yanzu Teemah matsayin ta daban, bazawara ce ayanzu.
Story continues below

Abinda kenan ya tsayawa Mummy ama’koshi ya kuma hanata jin da’di.
Amma ganin yanda kowa ke farin ciki da al’amarin musamman Anty dan kane-kane tayi ta hana Fateemah zuwa ko’ina bayan ta nemo matar da zata ringa yimata komai, hakan ne yasa Mummy ta saki jiki tabi ayari aka cigaba da hidima da ita.
Ummah tasamu Daddy da abinda ya dameta amma shima nuna mata yayi ba komai shikansa yanaso yayi mata maganan amma yafi son idan Yah Kabiru ya iso, dan shi ka’dai bazai iya ba yarinyar na matukar bashi tausayi ganin bataje ko’ina ba amma rayuwa ya gwara kanta, kuma yana tsoron kar jin labarin ya dawo mata da past ‘dinta baya.
Babu wanda ya sanar da Fateemah cewa auranta za’ayi kowa kawai harkar gabansa yakeyi, su Mummy tunanin su wai kar atuna mata da baya kuma ta ‘daga hankalin.
Ummah cema ke yawan yawan damun Daddy akan asanar da ita saboda kar garin neman gira kuma a rasa ido, ita kullun damuwarta gudun shiga hakkin yarinyar, ganin ba’a bata daman daya kamata abata ba aka hau shirin ‘daura mata aure.
Daddyn kansa abin na damunsa amma jiran Yayah Kabiru yakeyi idan yazo sayi maganar tare, yanada tabbacin cewa Fateema bazata ta6a gujewa umarninsa ba, dama Abbas ne matsalan dan kuwa har yanzu be san inda al’kiblarsa take ba akan auren, duba da yanda ya tattara yayi tafiyarsa duk da kuwa yasan cewa auren ya iso, hakan kuwa dayayi sai Daddy ya bari akan rashin son auren ne yasa, shi kuwa bayajin akwai abinda zai hana auren nan yiyuwa koda ma Fateemahn tace bata so toh dole sai tayi ha’kuri tunda ita da Abbas ‘din ‘yan uwan junane, saje can su ‘karata.
Idan yaga akwai cutarwa ne sannan zai ‘dau matakin daya dace akan Abbas ‘din.
Tuntuni su Teemah sun can cewa Yayansu zaiyi aure amma kuma hakan ba dalili bane da zai sa har a tsare ta a’daki da gyaran jiki ,wata rana kuma harda Hannah akeyi musu, hakan da aka mata kuwa sai ya dinga tuna mata da lokacin aurenta da Mahmud wancan ma kusan hakane yafaru.
Bata san dalilin daya sa za’a ringa yi mata gyaran jiki ba, dan wani zaiyi aure amma dayake gwanar son kwalliya ce ita sai kawai ta basar da zancen ta saki jiki aka cigaba da gyara ta.
Duk kuwa da yanda aka kai da yimusu abubuwa tare amma cikin lokaci ‘kan’kani Teemah ta yiwa Hannah zarra ta fita haskawa, wani lokaci dukkan su suna mamaki wai duk akan auren Yah Abbas ne ake musu wannan shirin?
Lallai Anty na bala’in sonmu sosai.
Hannah ce ma me ‘dan ‘ko’karin tambayar Mummy wai a ina Yayah ya samo matar auren da ake wani uban shiri haka?
Gaba ‘daya gida ya ‘dau ‘dumi, ga ba’ki sai zuwa suke tako ina, duk da maganar bata fito da wuri ba amma fah yadda dangi ke ‘ko’karin zuwa abin na basu mamaki sosai.
Tace
” gaskiya ni Mummy abin na bani mamaki sosai, kamar wani ‘yar gidan minista ko shugaban ‘kasa zai auro?
Murmushi Mummy tayi tace mata
” _Za6in Daddyn ku ne shine ya za6a masa matar_ “
Zaro idanu Hannah tayi cikin mamaki tace ” Mummy kuma Yayah ya yarda?
Mummy amsa ta bata da fa’din
“Abinda nima bansani ba kenan har yanzu”
Ta6e baki Hannah tayi tace ” _ta6 gaskiya ina jin tausayin yarinyar nan, kinsan fa halin Yayah sai a_ _hankali, da wuya ake fahimtar sa_ “
Teemah kam banda bugu babu abinda zuciyarta keyi alokacin dan kuwa fargaba ne taji ya kamata na fitan hankali da batasan dalili ba, bata sani ba ko itama tausayin amaryar Yayan takeji.
Bata sa musu baki a maganar ba amma tsuru-tsuru tayi kamar wata marar gaskiya.
Kanta na ‘kara kullewa ne aduk lokacin da ta ga yanda Anty ke sata a gaba da abubuwa , shafa wannan, sha wannan, yi kaza, abin sai ya fara bata tsoro mafi yawa ita da Hannah ake yiwa amma idan abin sha ne ita ka’dai ake bawa tasha, idan kuwa ta tambayi Anty dalili sai tace shima ‘din na gyaran jikin ne ko bata ganin cewa Hannah tafita haske, Anty sai ta dulmiyar da ita da fa’din haske kawai zai ‘kara mata itama, tace ai kinga Hannah tafiki haske ka’dan shiyasa ita ba’a bata.
Hannah kam kullun jimanta wa wannan amaryar Yayan takeyi, tasan shi bashi da yawan fa’da amma tasan halinsa shi bau’da’d’den mutun ne, da gane al’kiblarsa nada matu’kar wahala, magana wannan sai yaga dama yake yinta koda kuwa babu abinda ya damesa, idan ransa na 6ace kuwa wannan ‘kasaita da miskilancin na musamman ne, ita kuwa a tsarin ta bata son mutun haka, tana ganin kamar ita bazata iya auren mutun irin sa ba, dan wani lokaci magana da baki ma na sanyaya al’amura akan mutun ya ‘kyale ka, shi kuwa wannan yazama jinin jikinsa, tana ganin miskilancin Yayah ya shahara sosai da ita kanta abin na damunta balle matar da zai aura su rayu tare.
Idan fannin kyau ne, ita kanta tasan Yayah ‘karshe ne a wannan fagen dan ko ita ma bazata nuna masa komai ba duk kuwa da tana matsayin mace amma Yayah ya mata fintinkau, yana da kyau da kwarjini na musamman wanda ba kowa ke dacen samun irin sa ba.
Sannan ya nada sanyi hali aduk lokacin da dayaga dama baka gane hakan har sai rayuwa ta ha’daka wauri guda dashi.
Ranar da Hannah taji cewa Teemah Yayanta zai aura……..
Ranar da Hannah taji labarin cewa Teemah ne Yayah Abbas zai aura ba ‘karamin farin ciki tayi ba, sai de kuma tana jin tausayin Teemah ka’dan saboda halinsa, amma damuwar ta be yi yawa ba danta fahimci cewa tsakanin Teemah da Yayahn akwai wani 6oyayyen sirri da har yau takasa gane ko menene shi.
*****
Sai da bikin ya rage saura kwana biyu kafin Daddy yazo, hakan ma Mummy ce ta matsa masa akan yayi saurin zuwa saboda Teemah, amma da shi niyyan sa sai ranan Thursday zai taho inyaso friday sai a’daura aure aranar kuma sai ya wuce lagos saboda auren Abbahn Mahmud da za’a ‘daura ranar saturday.
Amma da Mummy ta matsa kawai sai ya taho, ganin sa kuwa har sai da ya sanya Teemah kuka taje da gudu tafa’da jikinsa tana ta rungume shi tana kuka, Daddy kam murmushi yayi ya dinga bubbuga bayanta ahankali yana bata ha’kuri harta yi shiru sannan sukayi gaisuwa me kyau da ita ha kama Hannah da suka zo gaida Daddyn tare.
Hannah kam mamaki ba ‘karamin cika ta yayi ba na ganin shagwa6ar da Teemah ke yiwa Daddy dan ko ita da take auta ma wani abin idan Teemah tayi sai dai ta tsaya kalonta dan ita bayi take ba duk kuwa da take autar gida ce ita, kuma Yayah Abbas ne ya hanata, dan baya barinta aduk lokacin daya ga tana yiwa Ummah shagwa6a taka mata birki yake yi ‘karfi dayaji sai da ya hanata.
Tun shigowan su ta kama guri ta zauna tayi shiru tana jiran Teemah ta gama kukan dan gani da tayi hankalin Daddy gaba ‘daya ya koma kanta da rarrashin ta kamar wata yarinya ‘karama.
Dasuka gaida shi kuwa suka fito ahanyar koma wan su Hannah ke tsokanan Teemah cewa ” _taji kunya ai da shagwa6a kamar wanda Daddyn goya ta zai nayi dan ta da’de bata ganshi ba shine harda irin wannan kukan?_ “
Tayi maganar tana ta6e baki.
Amsa Teemah ta bata da fa’din
” _Anyi ‘din ina ruwanki_ ”
Kai Hannah ta ka’da taci gaba da tafiya take fa’din ” _hmm, kiyi dai a hankali dan ina jiyake miki watarana, wannan_ _irin shagwa6an sai kace wata ‘yar shekar uku? ke da_ _aure ke gabanki_ “
Azafafe Teemah tace
” _ai kema auren ne ke a gabanki tunda kema macece_ “
” _Nasani ai shiyasa ma nake gaya miki, shi aure ai duk sunansa aure, amma kuma mazan kala-kala_ _ne_ !”
fa’din Hannah
Teemah kuwa cewa tayi
” _shiyasa ai naga kina wa Bilal shagwa6an kuma yana kar6a miki tun_ _ma kafin yazama mijin naki_ “
Dariya Hannah ta saka sannan ta juyo ta kalli Teemah tace tace ” _aini nawa daban ne dan indai Bilal ne ze kar6a min fiye da haka ma shiyasa ma ai nace miki mazan_ _kala-kala ne_ “
Tafiya Teemah ta fara tare da fa’din ” _nima indai mijin irin Yah Mahmud ne toh bana fargaba koka’dan_ ”
Da gudu Hannah tasha gabanta tace
” _Waye ya gaya miki irin marigayin mijinki ne_ ?
_naki tamkar dodo yake inkin ce zakiyi ta masa haka wahala zaki sha_ “
Story continues below

Haushi ne yacika Teemah sai ta ja ta tsaya tayi kwafah sannan tace ” _Hannah bana son wula’kanci da mugunta_ “!
Gaba tayi tana mita, Hannah ma sai ta bita abaya tana murmushin mugunta, ita kam tana son ‘yar uwarta kuma tausayin Teemahn takeji sosai.
Teemah kam sai mita takeyi ‘kasa-‘kasa take fa’din.
” _akan me zaki rin’ka yimin mugun fata ? angaya miki dodo zan aura ne da har zansha_ _wahala a wurinsa? Wama yace miki zan sake yin auren ?_
_Ni babu wani aure da zanyi bari kiji yanzu, ko da zanyi ma ba yanzu zan_ _sake auren ba kuma ma sai na za6a na tace wanda nasan bazai kawo_ _min matsala ba sannan zan yadda na aure shi_ “
Dariya sosai ne ya kama Hannah dan duk taji abinda Teemahn ta fa’da amma sai ta mazge ta maida shi murmushi tace ” _kice kafin nan ma har na haifi ‘yata ko ‘dana sannan muzo musha biki mu kwashi shoki a bikin babbar uwa mama Fatee!”_
Teemah kam ko kulata bata yi ba ta wuce hanyar bayi direct tana tsaki asaman la66a tace ” _ke kika sani ai mara kunya kawai_ “
Hannah zubewa tayi akan gado tana murmushi aranta tace ” wai yaushe za’a sanar da Teemah cewa auren ta ne ya kusanto? ya kamata asanar da ita gaskiya hakanan, ai lokaci na tafiya ni sam banga anfanin 6oyewan ba, ni kam idan bazasu fa’da ba wallahi anjima zan gaya mata meke faruwa inyaso sai ince karta fa’di cewa abaki na taji”
” _Yes!, hakan ma za’ayi_ !
Ta karashe da murna ita ka’dai kamar me ta6in hankali.
Da daren ranar kuwa sai Daddy ya ‘kira Teemah yafara da bata ha’kuri akan tafiyarsu Dubai batare da ta sani ba, da kuma lokacin rasuwar Mahmud da be tsaya ya tausheta ba be wani ke6e da ita a matsayin sa na uba ya bata baki ba wanda shi kanshi yasan be kyauta ba, sai de alokacin tsananin tausayin ta da yakeji ne yasa hakan, ya kara da fa’din mata batun gadon ta wanda aka bata cewa komai a hannun Abbas sai yanda sukayi, yana cikin maganar ya shigar da batun auren da ake kai ayanzu, inda yaringa ‘ko’karin fahimtar da ita cewa bawai rashin gata ko so bane yasa duk hakan ke faruwa face tsananin son da ake mata.
yace
” _duk abinda zanyi ina yi ne Fateemah saboda ke da farin cikin ki, abaya ni na za6a miki mijin aure wanda Alhamdulillah kin cika ‘ya ta gari Fateemah da_ _kika yi min biyayya wanda har shi Marigayin_ _ya koma ga mahallici banji wata sa6ani a tsakanin ku ba, naji da’din haka_ _sosai da kika amince da za6ina Fateemah yau ga ni na sake dawowa da_ _wani ‘ko’kon barata, kuma mai girman gaske ban sani_ _ba ko zaki iya tayani cika shi!, a karo na biyu Fateemah na sake za6a miki mijin aure wanda na yadda da nagartar sa, nasan yanzu ‘yancin kine ke keda wannan damar kuma addini ne yabaki, amma na shiga gabanki_ _na tauye ki, kiyi ha’kuri Fateemah ki ya femin sannan_ _kimin uzuri ki kar6i za6ina, duk abinda zanyi ina ‘ko’karine inga na baki abinda nasan ya dace_ _dake domin na tabbata ba zakiyi kuka dashi ba ba zakiyi dana sanin amincewa da za6ina ba insha Allahu_ “
Fateemah kuka takeyi sosai amma na zallan hawaye, hawayen ta ya kasa tsayuwa, kuma ta kasa bu’dan baki tayi magana aranta take fa’din ” _na amince Daddy na amince da za6inka, ni ‘yarka ce kaine ka haifeni kabani dukkan gata insha Allahu bazan ta6a_ _baka kunya ba, bazan ta6a bijirewa umarnin ka ba, bazan ta6a cewa_ _me yasa ka aikata hakan agareni ba_ “
Hakan takeso ta furta amma bakinta yayi mata nauyi ga kuka daya ci ‘karfinta sosai har sai da Daddyn Abuja ya sanya baki shima yayi ta rarrashinta kafin tayi shiru ta tsagaita kukan amma dayake daga zuciyarta kukan ke tasowa sai hawayen ta ya kasa tsayuwa gaba ‘daya, dole cikin kukan ta tabbatar wa Daddy amincewar ta.
A tare suka ha’da baki wajen sanya mata albarka da kuma haske mai ‘dorewa har ‘karshen rayuwarta sannan suka sallameta.
Tana jin ‘kunci, takaici da ba’kin ciki ga memories ‘din Mahmud da ya dawo mata sabo yabi ya cika mata zuciya tab amma ko dan irin yadda taga farin ciki kan fuskar iyayen nata ma dole zatayi musu biyayya dan kawai ta faranta rayukansu kuma taci gaba da ganin hakan har abada hakan ma ka’dai ya isheta.
Story continues below

Kwance take akan gado amma hawayen ta duk yabi ya ji’ka pillown jagab kamar wanda ruwa ne ya zuba akai, ita kanta tana so ta daina kukan amma hawayen ta yakasa tsayuwa.
A wannan halin Hannah ta shigo ta same ta tana kan kukan, tana jin motsin Hannah kuwa ta taso ta taho gurinta ta rungume ta sai yanzu ne sheshshe’kan ta ya bayyana, Hannah ma duk jikinta yayi sanyi sai de bata raba ‘dayan biyu cewa maganar aurenta taji shiyasa take kuka, dan haka sai ta bata chance sai da tayi kukan ta isheshshe sannan ta fara bata ha’kuri wanda da ‘kyar tayi shiru har sai da Hannah tace zata je ta sanar da su Mummy cewa tana kuka kafin ta ‘dan sarara ta sanar a Hannah meke faruwa.
Hannan bata yi mamaki ba danta riga ta sani dan haka sai ta ringa lallashinta tana bata ha’kuri har ta samu tayi shiru.
Abakin Hannah taji labarin cewa Yayah Abbas shine mijin da za’a aura mata nan da kwana biyu, zuwa lokacin kuwa zuciyarta da idanunta sun riga sun bushe ta fawwalawa Allah komai, ta fahimci cewa duniya dama kowa da kalar ‘kaddarar sa da Allah yake jarabtarsa dashi wata’kila nata kalan ‘kaddarar kenan na fannin aure, shine *auren za6in iyaye* , hakan ma ta gode Allah tunda nata iyayen na raye kuma tasan son da suke yi mata ne duk yasa haka, tasan dayawan mutane na son su kasance tare da iyayensu ko dan su ri’ka yi musu biyayya ma amma babu su basu samu wannan damar ba kuma sunyi ha’kuri, balle ita da nata iyayen na raye toh me ze hana ta yin biyayya agare su ko dan gudun dana sani agaba ma dole zata basu farin ciki koda kuwa wani iri ne indai har tana da daman yin hakan zatayi shi koda menene kuwa.
Yanzu ne ta fahimci manufar komai, yanzu ne tagane cewa gyaran amare akeyi mata wanda wasu lokuta ake ha’da ta da Hannah ayi mata a fahimtar ta dan kar tunaninta ya yi tsayi ne shiyasa ake yin hakan.
Ke nan kowa ma na farin ciki da wannan auren, kowa murna yake yi akan zatayi aure shiyasa tun ranar da taga aka fara yi mata gyaran farin ciki ya sa’k’ko cikin gidan nasu, zuwan Mummy ne ma ta ‘dan ga canji daga gareta dan ita Mummy bakace ga damuwar ta amma tana yawaita tunani wanda ita kanta Teemah abin na damunta.
Yanzu ne ta fahimci manufar maganan Hannah da tace *nata mijin dodone* !
Tare da tunowa da kalaman Yayan ranar da zai tafi inda yake cewa ta tabbatar tayiwa maganar Daddy biyayya koda baya nan.
Tarasa ina tunaninta ya tafi tun farko da batayi noticing komai akan lamarin ba.
Aranar kasa bacci tayi tunanain Mahmud duk ya dameta gaba ‘daya baccin da ya kamata tayi ma kasawa tayi, har kusan 2:00 am idanunta biyu.
Tunowa tayi da wayarsa dake cikin kayanta tayi sai kuwa ta tashi da sauri taje ta lalu6o wayar.
Tayi ‘ko’karin kunnawa amma wayar akashe dan haka sai ta jona a charge ta zauna tayi tagumi agabanta.
Shawara ta yanke dan haka sai ta mi’ke ta nufi bayi ta ‘dauro alwala tazo ta tada sallar nafilfili bayan ta idar ta ringa jero addu’o’i sannan ta shafa.
Tana idarwa kuwa sai ta fara jin bacci dan haka akan sallayar bacci yayi awon gaba da ita.
Ba ita ta farka ba kuwa sai da Hannah ta tasheta cewa ta tashi tayi sallah lokaci ya ‘dan ja.
Hannah na idar da sallah ta tafi gurin Mummy ta sanar da ita abinda ya faru na cewa Teemah tasan da batun auren ta yanzu, Mummy cewa tayi ” _dama mahaifinku yace idan yazo shi zai sanar a ita da kansa ai_ “
Mummy taji da’din haka dama ita tafison asanar da ita barinta cikin duhun bashi da amfani sam.
Teemah kuwa Tunda ta idar da sallah ta gama addu’o’in ta shafa sai ta ‘dauko wayar Mahmud ta kunna tare da kwanciya akan gado, Gallery ta shiga ta dinga bi ‘daya bayan ‘daya tana kallon pictures kala-kala nashi dana wasu da bata sansu ba, sai nasu da suka ‘daka tare ita da shi tare wani suna dariya wani kuma ma ba’a gida sukayi ba.
Story continues below

Sosai pictures ‘din suka tuna mata da baya ta ringa gani tana ‘kara maimaitawa, sabo fil Mahmud ya dawo mata, haka mutuwar sa ma sai ta ke jin tamkar yau ne suka rabu…..
Takai 1hr da wayar a hannnunta sosai ta shagala da kallon pictures ‘din dama tun rasuwar sa bata ‘kara bi takan wayar ba sai yanzun shiyasa duk hankalin ta ya ‘dauku ga kallon hotunan kawai sai taji wayar ta ‘dauki ‘kara.
Firgita tayi har sai da ta tashi ta zauna tarasa yanda zatayi har ‘kiran ya yanke bata ‘daga ba wanda atake wani ‘kiran ya sake shigowa a karo na biyu duk numbern ‘daya ne da na farkon kuma babu suna yafito.
Daurewa tayi ta ‘dauka da niyar sanar da me ‘kiran cewa me wayar ya rasu ‘kilan bashi da masaniya ne shiyasa.
Receive ta danna tare da bu’de speaker, bata ‘kai wayar kunnan ba sai ta ri’ke ahannu.
Tanajin yanda me ‘kiran ya furta _Alhamdulillah_ daga ‘daya 6angaren ga dukkan alamu ‘daukan da akayi ne yasa shi jin da’di.
” Assalamu alaikum, Yalla6ai Rabi’u ne daga Katsina, kullun munata neman layinka bama samu sai yau ‘dinnan, wallahi duk na damu akan baka zo kaga aikin da aka yi agidan ba, gashi da sauran ku’din ma har na sa Meram a makaranta tafara zuwa ga…..
Ko sallamar be bari ta amsa ba yaci gaba da koro bayani.
Cikin rawar murya Teemah ta tare shi da fa’din ” _bashi bane, shi ‘din ya rasu tun wata hu’du da suka wuce_ ……
Kuka ne ya kubce mata tana jin yanda me ‘kiran yafara jero salati sai tayi saurin kashe ‘kiran tare da kashe wayar ma gaba ‘daya.
Sai yanzu tunanin waye Rabi’u yazo kanta, yanzu ne ta tuna da labarinsu.
Ranar ‘karshe ranar da Mahmud zai rasu ma sunyi magana da shi akan komawa katsina kamar yanda yayi al’kawari.
‘Kiran da Rabi’u yayi mata ne yasa kukan ta ya kasa tsayuwa ta ringa zubda hawaye tana tuna baya, dama tana tunanin Maman Amal (matar Umar) kullum, yanzu da abubuwa sukayi mata yawa kuwa jitake bau wanda tafi bu’katan ha’duwa dashi sama da ita gashi bata da contact ‘din ta batada na Umar ma, cikin haka Hannah tazo tayi ‘kiran ta akan cewa wai Anty ne ‘kiran ta, dayake yanzu kullum da safe ne ake yi mata wankan turaren sauran duk abinda za’a mata already an gama shi tun jiya sai de abin da Anty ke bata kullun tana sha ne har yanzu bata daina bata ba.
Tashi Teemah tayi tana wani kauda kanta wai dan kar Hannah ta ga hawayenta, amma tuntuni Hannah tasan kuka takeyi amma bata kulata ba, dan ita kanta tana jin tausayin ta ahalin yanzu.
*****
Ana gobe ‘daurin auren ne Abbas ya iso da ‘karfe bakwai na dare, sai da yayi alwala ya sallaci sallar maghrib kafin ya shiga cikin gida domin gaida iyayensa da burin ganin ta azuciyarsa.
Ummah kuwa sai da ta ganshi hankalinta ya kwanta saboda kafin yanzun hatta layukansa ma basa shiga, hankalinta duk ya bi ya tashi da rashin zuwan nasa tsoronta ‘daya kar Abbas ya ‘ki zuwa ne tasan mahaifinsa bazai ji da’din hakan ba, kuma idan har hakan ya faru kenan ‘kiyayyar sa ga auren ya nuna ‘karara wanda ita sam bahaka take bu’kata daga gareshi ba.
Gaida su yayi gaba ‘daya fuskar sa normal ba yabo ba fallasa yana yi yana rarraba idanu afakaice ko zai ganta amma be ganta ba ko Hannah ma be gani ba.
Ko da ya tashi zai tafi sai Ummah ta tashi tabi bayansa awani corridor suka tsaya ta tambaye shi dalilin daya sa be taso da wuri ba tace ” _harka ‘daga min hankali wallahi_ _sosai na ‘dauka bazaka zoba, bansan har sau nawa na gwada ‘kiranka ba ayau amma duk ban same ka ba_ “
Murmushi Abbas yayi mata yace ” _haba Ummah zanzo mana ai Daddy ne da kansa yace in dawo_ .
” _Yauwa Babana kayi ha’kuri dan Allah ka kar6i_ _auren nan da hannu bibbiyu, dama ai kace Fateemah amanarka ce, kai kace an baka amanarta tun abaya so kaga sai kaci gaba da kulawa da_ _amanarka cikin sau’ki tunda ta dawo ‘kar’kashin ikon ka, dan Allah Muhammad karka bani kunya, karka_ _cutar min da yarinya kaji_ ?
Story continues below

Tabbaci ya bata da fa’din
” _Insha Allahu Ummah karki damu_ “!
Albarka tasa masa tare da yi masa zancen abinci yace akwo masa coffee ma ka’dai ya isa.
Ummah da kanta ta ha’da masa sannan aka fara cigiyar Hannah akan tazo ta kai masa coffee ‘din da ‘kyar aka samo ta a 6angaren Daddy yasa ta gyaran wasu kaya daga.
Hakan yasa dole sai de Teemah ce za ta kai masa tunda kam Hannah na aiki.
Tana kwance akan gado rufe ruf da blanket kanta ciwo yakeyi mata ga jikinta zafi rau amma ahakan ta aure ta mi’ke lokacin da sa’kon ana ‘kiran ta ya risketa.
Hijab ta zun6ula har ‘kasa kan shararar rigar da ke jikinta sai ya kasance fuskar ta ne ka’dai ake gani.
Ahaka ta kar6i coffee ‘din ta taho zuwa ‘dakin nasa.
Tunani takeyi na yadda Yah Abbas zai kar6e ta amatsayin mata, sannan ga Zazza6i ciwon kai da mara da yasa ta agaba tun ‘dazu tarasa yadda zatayi, Hannah taso sanar mawa ko zata samo mata magani amma tun lokacin data fara jin ciwon marar bata sanya Hannah a idanunta ba.
Ahankali take tafiyar kamar bazata yi ba har ta isa ‘kofar ‘dakin inda tun kan ta shiga zuciyarta ya fara harbawa, ahankali ta tura ‘kofar tare da yin sallama ta
shiga.
Abbas kam be amsa ba sai ma ya lumshe idanu aransa yace ” _Alhamdulillah_ “
Da ganinta, dama idanunsa da zuciyarsa ba ‘karamin son ganinta suke ba.
Teemah kam rashin amsawan nasa sai ya sa ta shiga ru’dani tunda tasan sarai yaji ta duk kuwa da cewa ahankali tayi sallamar amma ta tabbar yajita sai de ko in beyi niyyan amsawan bane kawai.
Shi kuwa Abbas tsayawa yayi kallonta duk da ba wani wadataccen haske bane a’dakin amma kallo ‘daya yayi mata yaga canjawar da tayi afili tayi wani kyau na musamman ga haske data ‘kara na gyaran data sha ya kuma sake ha’duwa dana menstrual period, daya ke idan tanayi haske yake ‘kara sata ka’dan.
Gaban sa tazo ta ajiye ‘karamin tray ‘din bata mi’ke ba sai da ta gaida shi tukun na.
Abbas amsawa yayi yana kallonta dan tuni ya shagala da sha’kan da’d’da’dan kamshin dake tashi ajikin ta, ‘dakin bawani haske sosai illah hasken television da ke aiki kawai a palourn shi ‘din ma be wani wadaci ‘dakin ba dan wani guri idan aka nuno yakan yi duhu ne gaba ‘daya hakan kuwa sai ya sa ‘dakin ya kasance ba shida maraba da wanda babu hasken ma gaba ‘daya.
Lokuta da dama tana mamakin sa yanda yake son kasance wa a cikin duhu shi, kamar wani marar gaskiya.
Tana ‘ko’karin mi’kewa sai kamar an matsi bakinsa yace ” _tafiya zakiyi kuma_ ?
Fasa mi’kewan tayi sai ta koma kamar yadda take tsugunne da farko.
Zazza6i takeji sosai ga ciwon kai sanadin haka kuwa har yanasa idanun ta tara ruwa.
Data rasa me zatayi sai kawai ta ‘dauki cup ta tsiyaya masa coffee ‘din tare da mi’ka masa.
Hannu ya sa ya kar6a tare da fa’din ” _I thought kin manta ne ai_ ”
Maganar tasa bata bu’katar amsarta dan haka sai ta yi shiru.
” _Wai meke damunki ne_ ?
Yasake tambayar ta yana kallon ta.
Tambayar kuwa sai ya sa ta sakin hawaye, da sauri ta kai hannu ta share hawayen wai dan kar ya gani amma
ina yariga yagani.
Zaro idanu yayi yace ” _me aka miki_ ?
_Ko yau ‘din ma ba’a son ranki kika zo ba, nifa bance dole sai ke zaki kawo_ _min abu ba!_
_Ko wani abu na miki yanzun_ ?
Girgiza masa kai tayi alamar ” _ah ah_ “
Hawayenta naci gaba da zuba.
” _So kukan fah na_ _menene_ ?
yasake tambayarta.
Story continues below

Cikin in i nan kuka tace ” _Kai…kaina ke min.. ciwo_ “
Abbas be yi mamaki ba dan lokacin data mi’ka masa coffe ‘din yaji ‘dumin da jikinta ya ‘dauka dama yasan za’a rina.
Ajiye coffee ‘din yayi yakai hannu ya ta6o fuskarta sai yaji zafi gau take yace
” _Sabhanallah tun yaushe yafara miki?_
” _D’azu_ ” tabashi amsa atakaice.
” _Kinsha magani ne_ ?
Ya sake tambayarta.
” _ah ‘ah_ “
tabashi amsa tare da jijjiga kanta.
Mi’kewa yayi yace mata
” _tashi muje_ “
Yayi maganar yana fita daga ‘dakin, itama Teemah sai ta bishi abaya a hankali dan har jiri takeji yana ‘dibanta, hatta haske bata son gani dan sai taji idanunta na mata zogi sosai.
Wurin driver ya wuce ya kar6o key sannan ya nufi gurin motar har ya bu’de zai shiga kuma sai ya tuna wani abu.
Jiranta yayi sai data iso sannan yace mata ” _zonan wato dana tafi bakya cin abinci sosai ko_ ?
Shiru tayi masa tana rarraba idanu.
Tsaki ka’dan yaja sannan ya juya ya shiga motar tare da tada ta.
Teemah ma shiga tayi yaja suka fita daga gidan.
Sai da yabi da ita wani eatry yasata dole sai da ta ‘dan ta6a abinci tukunna kafin suka wuce inda zasu.
Wani ‘karamin private clinic dake kusa dasu ka’dan ya kaita.
Suna zuwa kuwa suka samu wata nurse ce a duty dan haka itace ta duba Teemah.
Abbas kam kamewa yayi akan kujera yace Teemah tafa’di abinda ke damunta wa nurse ‘din.
Nurse ‘din itama murmushi tayi tace ” _meke damunki ne_ _’yan mata_ ?
Ahankali Teemah ta bu’di baki tace ” _Zazza6i nakeji da ciwon kai da….da kuma…._
Kasa ‘karasawa tayi sai ta ‘dan saci kallon Abbas sai taga shikan idanunsa nakan wayar sa ne.
Muryar Nurse ‘din tasake ji tana fa’din
” _inajinki, da me kuma?_
Sai da sake kallonsa kafin ta fisgi maganar tace
“…. _da…Menstrual_ _pain_ “
Tana gama fa’di sai ta wani rintse idanu da ‘karfi.
Abbas kam murmushi yayi ganin akan wannan abin take wani jan magana.
Nurse ‘din ma murmushi tayi mata tace
” _kina jin kunyar_ _Yayah ko_ ?
Bata kulata ba sai ta kauda kanta gefe.
Tashi Nurse tayi taha’da mata magungunan da suka dace, taso tayi mata allura amma Teemah tace bata so, harta fara lalla6ata sai Abbas yace abar alluran kawai tunda bata so.
Koda suka koma gida kuwa be barta ba sai da ya tabbatar tasha maganin ta tukunna , tana shiga ‘dakin su kuwa ta tarar da Hannah tsaye da waya a hannunta Anty ma na zaune a gefen gado ta zubawa Hannah idanu.
Sallamar ta ce ta dawo da hankulansu gareta Hannah harda ajiyan zuciya Anty kuwa da sauri ta zo ta tareta.
Hannah ce ta jefa tambaya tace
” _Teemah ina kika shiga dan Allah duk kinbi kin ‘daga mana hankali_ _gashi mun ta ‘kiran wayarki bakya ‘dagawa har ‘dakin_ _Yayah naje fah ban same ki ba?_
Teemah da dafe kai tace.
” _Wayar na nan ‘ka’kashin pillow ne kuma tana silent_ “
Anty ne ta taho da sauri ta ri’ke ta tare da fa’din
” _Fateemah meya faru kuma naji jikinki da zafi_ _sosai_ ?
Ledan magungunan ta ‘dago ta bawa Anty a hannunta tare da fa’din “
_Anty clinic mukaje_ _da Yayah_ “
daga nan ta basu labarin zazza6in daya dameta ‘dazu.
Anty kar6a tayi da mamaki tace ” _Ya akayi baki sanar da_ _kowa ba toh_ ?
Tana shirin yin magana Anty ta dakatar da ita da fa’da akan shirun da tayi bata sanar musu halin da take ciki ba, tace karta sake yin irin haka
yanzu ba dan shi Abbas ‘din ya lura ya tari abin ba da tasan meze faru ne? Su suna can suna shirin biki while ita wacce akeyi domin tan kuma tana nan tana fama da jinya ina anfanin haka?
Ha’kuri Teemah tayita bawa Anty tace bazata sake maimaita irin haka ba.
Anty bata bar ‘dakin nasu ba sai da ta tabbatar da sassaucin zazza6in kafin nan taje ta kwanta itama.
Abbas kam da kansa yazo ya duba ta lokacin ‘karfe 11:48pm su suna ma bacci basu san yazo ba, ganin tana bacci yasashi jan ‘kofar ya rufe ahankali tare da hamdala dan yasan zazza6in ya sau’ka kenan tunda har tasamu tayi bacci, yaso ya shiga ya ta6a yaji lafiyar jikin amma saboda kasancewar Hannah na ‘dakin yasa kawai ya juya batare da ya shigan ba.
*****
Washegari yakama ranar Friday wanda ya kasance aranar jama’ah da dama suka shaida ‘daurin auren Muhammad Abbas Al’hassan tare da amaryar sa Fateema Kabeer inda yasamu hallatar alummar musulmai da dama dayake a masallaci aka ‘daura auren bayan an idar da sallah juma’ah.
Abbas kam farin cikinsa ba ze ta6a misaltuwa ba domin shi ka’dai ne zai iya fassara irin yanayin daya shiga alokacin daya ji an sar’ke sunansu waje guda, godiya kawai ya ringa zubawa mahalicci dan bashi da abin da zai iya furtawa bayan haka.