ABBAS CHAPTER 20

ABBAS







CHAPTER 20







Rausayar da kanta tayi gefe tana kallon shi, Abbas baya son taga kamar yana matsa mata ne dan haka sai yace ” _owk, zan barki kiyi amma make sure that mura na kamaki ba sassauci Anty nurse zan’kira ta ringa yi miki_ _injections har sai muran ya tafi…kin yarda_ ?

Tana jin haka ta karya mai kafa’da alamar bata yadda ba.
Abbas sakin ta yayi tare da nuna mata hanya yace
” _Toh oyah go inside!_ “

Dolen ta ta shigo ciki tana ‘kun’kuni ‘kasa-‘kasa, shima Abbas take mata baya yayi bayan ya rufe ‘kofar.

Teemah ‘dakin ta ta wuce cikin fushin an hanata wanka inda tana komawa ‘dakin ta hau cire kayan dake jikinta dan sun ji’ke sosai.

Sai da ta cire su gaba ‘daya kafin ta nemi towel ta ‘daura ajikin ta sai ta shiga bathroom ‘din ta ta cika bathtub da ruwa ta shige ciki afili ta furta ” _in ka hana wancen ai baka isa ka hanani shiga wannan ba, mutun_ _kullum sai de ya hanaka rawan gaban hantsi…..abu ka’dan sai ya wani ce injection! Wannan da ace shine yake yin alluran ai da anshiga uku nasan da kullun sai ya min goma ko.biyar dan mugunta! “_
Ta ‘karshe da jan tsaki daga ‘karshe.

Abbas ma a parlour ya zauna inda ya ‘dau lokaci yana amsa waya sai da ya gama kafin ya wuce ciki dan watsa ruwa be ko sake bi ta kanta ba.

Teemah kuwa ta jima cikin ruwan hankalinta kwance sai da ta fara jin hanjin ta na motsi ne sannan ta fita aruwan tayi wanka mai kyau tafito.

Koda ta fito sai ta tsaya kuma ta ‘debi wayarta dana Mahmud ta zauna bakin gado, layin Umar ta nema cikin wayar marigayin ta’kira shi lokacin ‘karfe sha ‘daya ta wuce sosai 11:42am.
Umar yayi mamaki sosai data ‘kirashin ya kuma ji da’di musamman dayake shima Maman Amal na yawan damunsa
akan batun Teemah.
Nan yayi mata al’kawarin zai ha’da su da zaran ya koma gida.

Cikin hanzari ta shirya tare da kwaso wayoyin harma dana Mahmud saboda sauri ta fito dan nemawa cikin ta dake ‘kugin neman agaji mafita.

Turus taja ta tsaya ganin babu komai akan dinning, bata 6ata lokaci ba sai ta wuce ‘dakin sa ta same shi yana sa kaya shima.

Bata damu da yanayin dayake ba ta isa wurinsa ta ha’de goshi ta ita adole tana fushi dashi tace ” _Yayah nifa yunwa nake ji kuma banga komai a dinning ba_ “!

Be kalleta ba yace ” _Ya za’ayi kenan_ ? _dama nace a daina kawowa ne saboda bakya ci….._ “!

Da sauri ta tare shi da fa’din ” _inaci mana bagashi yanzu ma ina jin yunwa ba_ ”

Kwafa yayi yana kallon da ta gira a’dage jin yanda tayi maganar, cikin salo yace da ita
” _Harda fa’da ne kuma_ ?

Baki ta tura gaba ta kauda kanta tace ” _Ni ba fa’da nayi ba ai yunwa nake ji ne shiyasa_ “!

Story continues below


Cigaba yayi da 6alle bottuns ‘din longslip ‘din daya sanya ajikinsa yace

” _Sai kije kitchen ki samu abinda zakici ko noodles ma ki tafasa kici zaifi sauri_ “

Dan haushi ma Teemah ko jira ya gama maganar batayi ba tafice abin ta, jitayi badan yunwa na damun ta ba da babu abinda zai sata shiga kitchen yanzu.

A parlour ta ziba wayoyin dake hannun ta sannan ta wuce.
Koda ta shiga kitchen ‘din kuwa sai ta wuce fridge ta ‘dauko fruits ta gyarashi ta hau sha har da zaman ta kan stool ‘din dake cikin kitchen ‘din.

Sai da ta ‘danji dama-dama acikin ta kafin nan ta kunna gas ta dafa indomien ta dai-dai cikin ta tajuye a plate tarufe da wani plate ‘din harda ‘dora forkspoon ‘din ta akai, sannan tayi mixing fruits tayi juice ‘din ta ‘dan dai-dai a ‘kasan glass jug da extra cup ‘daya batare da wani 6ata lokaci ba kuwa ta kammala duka tafito.

Kan dinning taje ta ajiye su sannan takoma kitchen ‘din domin kimtsa shi dan bata son idan tafita tasake dawowa dan kim tsawa ba.

Batafi 9mins a kitchen ‘din ba ta kammala tafito da ruwan ta mai sanyi a hannunta kawai sai idanun ta ya sau’ka akan Abbas yana siffing mata drink ‘din data ha’da cikin kwanciyar hankali kamar ance shi aka ajiyewa abincin.

Ga plate ‘din abincin ta ma bu’de a gabansa da ga dukkan alamu yana kan ci ne.

Turus taja ta tsaya dan haushi ma sai tarasa me zata ce dashi, shima sai yayi tamkar beganta ba yaci gaba da cin abincin cikin natsuwa.

Data ga haka ne sai ta taho da sauri har idanun ta na tara ruwa dan takaici sai ta tsaya agaban sa tace ” _Yaya abinci na ne fah_ !

Gira ‘daya ya ‘dage ya kalle ta sai ya kuma kallon abincin yace ” _really!_ ?
_Ai ban sani ba ne i thought nawane kika ajiye min ai_ “

” _Ai baka ce min zaka ci ba_ “!

‘Da, zaro idanu yayi yace
” _Au sai ma na fa’di zanci kafin adafa dani_ ?

Shiru tayi masa bata yi magana ba sai hawayen ta da suka gangaro, harga Allah yau ‘din yunwa takeji sosai kuma tayi niyyan cin abincin ta sosai take son jin wani abu acikin ta.

Ganin tafara kukane yasa yayi murmushi tare da janyo hannun ta ya zaunar da ita kan kujerar kusa dashi, be yi magana ba sai kawai ya ‘debo abincin ya nufo bakin ta dashi.

Babu musu Teemah ta bu’de bakin ta ta kar6a.
Sai yayi mata murmushi aransa yace da din waya gaya miki Borno gabas take? ai yunwa maganin kowani fitinanne ne yasan badan taji yunwa ba da yau ‘din yanda tayi fushi dashi ‘din nan dako kulashi ma bazatayi ba sai gashi kuma har abinci yabata abaki kuma ta kar6a, afili kuwa sai yace da ita” _ni ban ta6a ganin inda mata ta hana mijin ta abinci ba sai_ _yau awurin ki! wato cikin ki ka’dai kika sani ko?_ ”

Shiru taui kamar bada ita yake ba sai ma kauda kanta da tayi gefe, Abbas sai ya sake ‘dibowa ya mi’ka mata itama sai ta bu’de baki ta kar6a.

Sai daya bata kusan spoon biyar batare da yaci ko ‘daya ba data kar6i na biyar ‘din ne sannan cike da tsokana yace da ita ” _cinye abinki tunda bakya so inci nima zanje wurin Zahra ta ta dafa_ _min_ ” 

Tsayawa tayi tana kallonsa shima kuma haka dan kawai ta tabbatar da abinda yace ‘din, ganin hakan shima ya tsare ta da idanu sai ta kauda nata idon ta maida shi gefe, duk iskancin ta da rashin jinta bazata ta6a iya kallon kallo da shi na tsawon lokaci ba, sosai kwarjinin sa ke karya mata zuciya, tsawon mintina kusan biyu babu wanda ya furta komai acikin sannan Teemah ta ha’diye abincin dake bakinta ahankali.

Yana shirin ‘kara ‘debowa sai ta yi sairin rike mai hannu, bata kalle shi ba koda yabi ta da kallon mamaki ma bata san yayi ba, dan ita plate ‘din abincin take kallo. 

Story continues below


Kar6i spoon ‘din tayi ta ‘dibo abincin tayi dauriyan kai masa bakin sa batare da ta sa idanun ta cikin nasa ba, Abbas kuwa sai ya’ki bu’de bakin sai ma kauda kansa gefe da yayi.

Hakan ne yasa ta kalli idanunsa sai ya’ki bata hankalinsa. 

Cak ya mi’ke tsaye ya koma cikin ‘dakin sa domin tsabtace bakinsa. 

Teemah tamkar statue haka ta zauna ri’ke da spoon a hannu sai ta rasa me yake mata da’di, Abbas be da’de da shiga ‘dakin ba ya fito hannunsa ri’ke da makulli ko kallon inda take be sake yi ba ya kama hanyar barin ‘dakin.

Ganin haka yasa Teemah ta mi’ke da hanzari cikin sassanyan murya ta ce da shi ” _Yayah wurin Zahran zaka tafi_ ?
Da ” _umm_ ” kawai yabata amsa batare da waigo ba, yana me cigaba da tafiyar sa ahankali.
” _Nima zan bika_ “
Ta sake cewa da shi wanda jin hakan ne yasa shi waigowa ya kalle ta dai-dai lokacin kuma sai waya ta ‘dau ‘kara daga cikin parlourn dukkan su sai hankalin su ya koma wurin.

Teemah ce taje da sauri dan tasan ita ta ajiye waya a parlourn, hannu tasa ta ‘dauki wayar hannun ta har na rawa dan yanda zuciyar ta ta tsinke tun daga jin ‘karan ringing ‘din dan tasan ba wayar ta bace ta kuma riga tasan kalan ringing ‘dinsa tun yana raye, gani tayi number ce ba suna.
Aduk lokacin data ga wani abu daya danganci Mahmud sai ta tuna da shi balle wannan daya kasance ‘karan wayar sa ne da ta saba ji atare dashi tuni sai ya sa zuciyar ta bugu cikin sauri.

Kafin tayi wani yun’kuri har wayar ta tsinke.

Abbas ma ganin wayar da kuma yanayin data shiga yasa hankalin sa ya dawo kanta shima ahankali ya dawo baya ya tsaya nesa da ita ka’dan yana sake karantar yanayin ta, be san wayar waye ba ce kuma yasan ba tata bace dan yariga yasan nata dayake shine da kansa ya canja musu bada jimawa ba ita da Hannah iri ‘daya. 

Take wayar tasake ‘daukan wani ‘kara wanda yasa Teemah sai da ta danganta jikinta da kujera kafin ta iya amsa ‘kiran tana me danne hawayen ta ta kai wayar kunnan ta da rawan jiki.

Shiru tayi tana sauraran me ake fa’da mata wanda tuni hawayen tan suka kasa tsayuwa suka gangaro kan kuncin ta.

Ganin haka yasa Abbas ya ‘karaso kusa da ita ya kai hannu ya cire wayar akunnan ta ya ha’da ta da kunnansa.

Yin hakan keda wuya sai Teemah ta fa’da jikin ‘kafafunsa ta rungume ‘kafafun tana mai cigaba da kukan ta. 

Yana sada wayar da kunnan sa yaci gaba da saurara batare da ya furta komai ba. 

Sai yaji ana fa’din”………… _kullum na’kira bana samunka yalla6ai_ _sai yau dan Allah kazo ka duba aikin daka bani, inaso in gaya maka cewar Innah_ _na cikin farin ciki yanzu ha kama yaranta kuma tanaso ta gode maka bisa_ _taimakon dakayi mata amma bama samun ka shiyasa ta damu, ni ma_ _kuma ina so kazo kaga aikin daka bani jagoranci bansani ba kona yi_ ‘ _ko’kari”_ __ !

Abbas be san kan maganar ba be kuma san inda ta dosa ba, tunda baiji farkon ba kuma ko yajin ma be san waye akan layin ba amma duk da haka sai yace dashi ” _Allah yayi wa mai wayar rasuwa tun ba yau ba, amma karka damuni dan uwansa ne kuma insha Allahu zanzo kwanan nan idan nasamu lokaci… yama sunanka_ ? 

Jikin Rabi’u sosai yayi sanyi ya rinka maimaita innalillahi wa inna ilaihiraji’un….Daga ‘karshe ne ya sanar da Abbas sunansa tare da jero adduoi wa marigayin. 

Da ” _Ameen-Ameen_ “
Abbas ya amsa masa tare da ajiye wayar, daganan kuwa rabata jikinsa ya zauna gefen tare da fa’din ” _who is he_ ?

Cikin kuka tace masa ” _Nima bansan shi ba Yayah, amma yace sunan shi Rabi’u wai daga Katsina yake kuma_ _Yayah Mahmud yake nema_ ” 

” _Toh ke me kika ce_ _da shi?_ Ya sake jefa mata wata tambayar 

Amsa ta bashi da fa’din
” _Nace masa ya rasu amma ina ga ba yadda bane, dan naji alokacin har ya fara salati amma may be dayaji wayar na tafiya har yanzu ne shiyasa be yadda ba, lastweek ne ya’kira….._ .(daga nan tabashi labarin duk abinda yafaru tun farko kamar yanda Mahmud ya labarta mata.

Story continues below


Fa’da sosai Abbas yayi mata akan amfani da takeyi da wayar Mahmud ‘din bayan tasan babu shi, ai dama baza’a rasa wa’dan da basu san da labarin rasuwar sa ba kuma ba mamaki su neme shi. 

Shiru tayi kawai tana share hawaye, tana son sanar dashi cewa ba amfani take yi da wayar ba amma bakinta sai ya mata nauyi ta kar6i laifin kawai. 


Wayar ya sake ‘dauka ya ‘dauki layin da Rabi’un ya ‘kira dashi awayar sa tare da ‘daukan numbern Umar abokin Mahmud duk yayi saving a wayarsa sannan ya cire Sim cards na Mahmud ya tashi ya koma cikin ‘dakinsa harda wayar ya ajiyesu a drawer.

Ranar haka ta wuni wata iri da ita dan ma Allah ya taimake ta ya fasa fita shima ‘din agida ya zauna.

Ummah kuwa ta aiko musu abincin rana dan ranta yakasa yadda ta daina kawowan kamar yanda Abbas ya bu’kata dan tariga tayi niyyan yin na sati guda kuwa bazata fasa ba tunanin ta ma ko mugun halinsa ne yasa yace kar akawo da safen.

Babu ma wanda yabi takan abincin har la’asar tayi, Abbas masallaci kawai yaje yadawo.

Ganin kamar bazata saki ranta bane bayan sallar la’asar ‘din sai yace ta shirya su fita.

Taji da’din hakan kuwa sosai musamman daya kaita gidan wani abokinsa a Asokoro, matar kyakkywa da ita da yarinyar ta ‘daya me suna Nasreen ‘yar kimanin shekaru biyu.

Yarinyar ce tasa Teemah tasaki ranta gaba ‘daya dan yarinyar badai ‘kiriniya ba shekarar ta biyu kacal amma akwai wayo ga ta da son mutane.
Abbas yaji da’din ganin ta saki ranta tana wasa sosai ma yarinyar balle data biyeta tana tayata surutu tamkar ‘karamar yarinyar ita ma ta koma sai hakan ya ‘kara birge shi.

Da suka fito zasu tafine har Abbas ya kunna mota ma sai Teemah tace dashi ” _Yayah plz ka ce su bamu aron Nasreen mana ko na sati ‘daya ne mutafi da ita ni kam ina son_ _ta_ “! 

Be kalle ta ba yace ” _suma ai suna son abin su, kema ki haifi naki mana_ “! 

Dayake son yaran yariga ya cika mata zuciya sai ta ce dashi “ai _nima ‘din inaso in haifa, kuma idan nasami baby na bazan_ _bawa kowa ba, Maman Amal ma tace insha Allahu zan haifi baby na in rin’ka goya kayana_ “

Kallon ta yayi da mamaki dan yanda yaga son yara ‘karara a kalaman ta da kuma yanayin ta yasan bada wasa bane. 

Da suka ha’da idanu sai tace ” _kaima ai kanason Baby ko?_ 
_Toh ka haifi naka dan ni bazan ta6a baka nawa ba_ “

Dariya taso sashi amma sai yayi murmushi kawai yace ” _zamu gani ai_ “
tare da jan motar suka tafi.
Yana mamakin ta shikam lokuta da dama intayi abu kamar wata babba wani lokaci kuwa sai kaga tafi kowa kwa6a.

Da suka hau titi ne Teemah tafara ro’kon sa akan ya kaita gida amma ko ci kanki bece da ita ba, haka tayi ta ro’kon sa har ta ha’kura tayi shiru.

Sai da ya biya dasu shopping store suka ‘danyi siyayya kafin ya sake ‘daukan hanyan gida, Teemah kam duk wannan abin ba birge ta suka yi ba tunda be amince da bukatar ta ba.

Gidan sa ya wuce da ita inda Teemah ta sau’ka tayi ciki abinta ko kallo ma be ishe ta ba. 

Kayan ma dasuka siya shine yashigo dasu ita Teemah adole wai tana fushi.

Fruits salat tasha da daren ranar shikuma Abbas coffee ya ha’da da kansa yasha.

Duk da haka fushin nata be hana ta tahowa ‘dakin sa yin bacci ba da lokaci yayi.

Yau kam Abbas ko kulata beyi ba har ta zo tayi kwanciyar ta shima ficewa yayi parlour ya tsaya kallon wani Hollywood movie da ake haskawa wanda ya ‘dauke shi har kusan 11 na dare.

Story continues below


Lokacin daya shigo ‘dakin baccin Teemah yayi nisa sosai harta fara birgima dayake gwana ce ta wanan fannin. 

Jijjiga kai kawai yayi ya shige bayi, sai da yazo yayi sallar nafila yayi addu’o’i kafin ya kwanta agefen ta dan tuni har ta dawo tsakiyan gadon.

Fuskar ta ya kallah zuwa ‘dan ‘kara min bakin ta daga nan ya maida kallon sa zuwa jikinta, ‘yar guntuwar sleeping dress ‘din data sanya har ya ‘dago zuwa sama inda ya bar duk cinyoyin ta afili hatta da pant ‘din dake jikin ta ma yana gani.

Tsayawa kallon fresh santala-santalan cinyoyin ta yayi yana jin wani yanayi na daban na ratsa shi game da ita.

Wani abu yake jin yana fizgansa zuwa gareta tare da ra’da masa ai halalin ka ce kana da damar ra6ar ta aduk lokacin daka so.

Rintse ido yayi da sauri ya tashi zaune ya dafe kansa harda ambatan innalillahi wa innah ilaihi raji’un afili kamar wanda yaga wani abin tsoro.

Kwanciya ya koma yayi harda juya mata baya amma sai hakan yakasa yiwuwa agare shi, sha’awar ta daya hadu zafin son ta dake zuciyar sa ya yi tasiri akansa matu’ka.

Dolen sa sai da ya sake juyawa ya dawo da kallan sa  gefen da taken yaci gaba da kissima abubuwa aransa.

Data dawo jikinsa kuwa kamar jira yake sai yasa hannu ya rungume abinsa hadda ajiyan zuciya yana sha’kan ‘kamshin jikin ta tsawon lokaci, bahaka yake bu’kata ba amma sam sai yake ganin kamar ita bata shiryawa kar6an bu’katar sa ba awannan lokacin shiyasa ya ha’kura.

*****
*BOMB BLAST* 
           Acikin satin sai ya kasance kusan kullun sai anyi ruwa da safe, dama wani lokaci haka yanayin damina yake yakan juya ne aduk lokacin daya ga dama, inda wani lokaci zakaga koda yaushe da yamma ake fiye yin ruwa wani lokaci kuma da rana tsaka inda wani lokaci kuma ruwan yakan ri’ki safiya ne na wasu lokaci.

Ko yau ‘din ma da hadari agarin suka tashi amma ruwa be sakko ba har kusan ‘karfe bakwai na safiya.

Teemah luf tayi a gadon tana jin sau’kan ruwan ga wani iska me ha’de da sanyi dake hurawa yana ratsa ta, tana so ta tashi amma ganin sa zaune da system agaban sa yasa ta ki tashi tayi shiru.

Juyawa yayi ya kallo 6angaren da take wanda yasa take Teemah ta maida idanun ta ta kulle kamar me bacci, ganin ‘dakin babu wadataccen haske sai tayi tunanin ko be ganta ba ne.

Abinda bata sani  ba kuwa shine tuntuni Abbas yasan ta tashi musamman data zuba masa idanu ‘dazu kawai shima ya shareta ne dan yaga gudun ruwan ta.

Tashi yayi ya shiga bayi hankalinsa akwnce dan beyi zaton zata sake yin rigimar fita ruwa ba.

Teemah kam kamar jira take yi yana shigewa itama ta yun’kura tafito tabar ‘dakin.

Bata wani tsaya taran ruwan da hannun ta ba yau kawai ta shige ciki gaba ‘daya tana juyi tana dariya da tsefaffen gashin ta da ko shower cap bata nema dan rufe shi ba. 

Gaba ‘daya jikinta da gashin ta suka ji’ke dayake ruwan da ‘karfinsa yake sau’ka shi yasa komai na jikinta sai da ya ji’ke amma bata bar juyi aruwan tana tsalle ba. 

Sosai ta shagala da wasan ruwan har tana watsa gashin ta a iska, unexpected kawai taga hasken wal’kiya kafin ta ankara kuwa sai ta ji ‘karan tsawa me ‘karfin gaske ya biyo baya, shaf ta manta ma da cewa thunder na ‘kara idan ana ruwan sama tsabar yanda hankalinta ya ‘dauku ga wasan ruwan.

Arazane tayi ciki da gudun gaske har ji take tamkar yana biyo bayan ta, da ‘karfi ta maida ‘kofar ta buga sannan ta wuce da gudunta.

Abbas kansa sai da ya tsaya da abinda yakeyi lokacin da ‘karan ya sau’ka shi be ma san bata ‘dakin ba fitowar sa kenan daga wanka kukumin sa ‘daure da towel, so be kai hankalin sa wurin ta ba tukunna.

Story continues below


Teemah kuwa bata zame ko’ina ba sai ‘dakinsa tana ganinsa sai ta nufe shi dagudu ta je ta ru’kun’kume shi tare da rintse idanunta har sai daya firgita ya ‘daga kalle ta da sauri sannan ya juya ya kalli gadon da kyau sai yaga bata gadon, yayi mamakin lokacin fitar ta ma.

Jin jikinta ajike kuwa sai yayi saurin fahimtar daga inda tafito, beyi mamakin firgicin nata ba dan  shima yaji ‘karan thunder ‘din.

Jikin ta yaji yana kakkarwa sosai gashi ta’ki bu’de idanunta, ‘ko’karin raba ta da jikinsa yafara amma babu dama saima sake ‘kan’kame shi da takeyi hawaye na sakko mata sirara, gashi shima ‘din so yake ya shirya yasa wadatattun kaya amma dole ya danne nashi uzurin ya hugging nata back.

Yaso ya barta ahakan amma ganin kamar sanyi ze shiga jikin ta yasa shi ‘dan yun’kuri ka’dan take kuwa tasake ‘kan’kame shi.

Sunan ta yafara ‘kira ahankali da niyyar sata ta cire kayan amma ko amsashi batayi ba tsawon mintina uku suna ahaka.

Daya ga cewa ta riga ta rikice sosai bazata kula shi ba sai ya kai hannu bayanta yafara 6alle ‘kananun bottuns ‘din dake jikin rigar ahankali har ya 6alle su gaba ‘daya. 

Hannunta dake zagaye dashi ya yi ‘kasa dasu wanda hakan yabawa rigar daman sau’ka ‘kasa itama.
Take kuwa Teemah tasake maida hannun ta sake ri’ke shi tana mai sau’ke numfashi. 


Shima ‘din Abbas canjin yanayi ne ya ziyarce shi na bazata tun daga cikin jikinsa har zuwa ‘kwakwalwarsa gaba ‘daya sanadiyyan ha’duwar fatan jikin su.

Bra ne ka’dai yarage mata sai kuma pant yanzun dayake da bra take kwana indai zata zo ‘dakinsa wai dan bata so yagane mata shape ‘din jikinta shiyasa take daure kwana da bra ‘din duk kuwa da bata saba hakan ba.

Abbas ‘dagata yayi ya maida ta kan gado ya kwantar da ita tare da 6alle hook ‘din bra ‘din dan shima yaji’ke sosai har ‘digan ruwa yakeyi.

Yana ‘ko’karin raba jikinsa da nata amma sai Teemah ta’ki bashi wannan damar sai ma ta ‘kara ri’ke shi.

Ahakan ya ‘kyaleta sai ya ‘dan ‘dagota ka’dan yazare bra ‘din wanda hakan sai da yasashi rintse idanu tare da bu’dewa atake ya sau’ke su akan ‘kirjinta. 

Musamman dayaga yanda boobs ‘din ta suka tsaya tsam dasu tamkar zasu tsone masa idanu.
Sanyin daya shigeta da kuma tsoratan datayi sai ya ‘kara bada gudummuwa wurin sashi yin ‘dim yana shai’ki gwanin sha’awah dashi.
Abbas kam tasbihi kawai yake ga mahalicci me kowa me komai.

Teemah kuwa sai ‘ko’karin sake shiga jikinsa takeyi saboda sanyin dayake sake ratsata.

Ruwane yasake sau’kowa tamkar da bakin ‘kwarya fiye ma da wanda ya sau’ka da farko dai-dai lokacin kuma Abbas yakai hannunsa kan boobs ‘dinta ya shafa ahankali, laushinsu da kuma yanda suka cika masa hannu yasa yanayin sa sake birkicewa kwata-kwata natsuawar tabarsa.

Kasa sakinsu yayi ya ringa shafawa har zuwa wuyanta saima yafara ‘ko’karin sada su da bakinsa.
Be yi hakan ba sai kawai ya zarce da romancing ‘dinta azafafe, kissing ‘dinta yakeyi ta ko’ina, lokacin da ya ‘dora bakinsa saman boobs ‘din ne Teemah ta sanya masa kuka tafara ‘ko’karin tureshi sai yayi saurin ha’de musu baki wanda hakan shiya tilasta mata yin shiru tana mutsu mutsu. Abbas kam yariga yayi nisa cikin yanayin da bazai ji ‘kira ba koda kuwa ace an’kira shin, shiyasa ma kukan Teemah be dakatar dashi ga abinda yake yi ba.
Pant ‘din dake jikinta ya zare ya wullar dashi a’kasa.

Ranar kam Teemah taji maza sosai tagane kurenta ahannun captain dan koka’dan beyi mata dawasa ba, beyi mata ahankali ba sanin dayayi cewar hanyar sa abu’de take. 

Sai da ya riga ya shige ta kafin ya fahimci cewa sa’ar tashi ce, sosai ya girbe ta son ranshi  be ‘kyale ba kuwa sai daya tabbatar ya maidata cikakkiyar mace aranar.

Story continues below


Teemah tasha kuka harda na banza, masifa ro’ko da yakushi babu wanda be samu ba amma be saurare ta ba.
“…. _Zan ha’da ka da Daddy.. yaja kunnanka… yacire maka shi…….. dan Allah yayah_ _zan mutu……zan ha’da ka da Ummah da Anty…waiyo Hannah_ _ta kuzo ku ceceni_ _plz….Mummmyyyy_ !
_Yayah kasheni zaiyi….dama baya sona! Waiyo Yayah_ _wallahi na daina ma rashin kunya Allah bazan sake rashin ji ba…..!_ 

Duk da haka Abbas be barta ba harsai da ya gama da duk abinda ya tara tsawon lokaci sannan ya koma gefe yana sau’ke numfashi tare da tunanin halin daya tsinci Fateemah, be ta6a zaton hakan ba bayan zaman datayi gidan wani namijin har na tsawon wata uku koma fi. 


Janyo ta yayi ya rungumeta hawayenta na cigaba da sau’ka akan ‘kirjinsa, jiyake tamkar ya maida ta cikinsa dan so, wani sabon salon babin ‘kaunarta ne yake sake nin kuwa masa fiye da na baya, Teemah kam jikinta duk ya saki dan azaba, motsin kirki wannan bata iya yinsa illah hawaye.

Abbas kam tunanin wautar daya so tafkawa yayi lokacin da shai’dan ke yawan kawo masa rayuwar ta da Mahmud azuciyar sa ashe duk sharrin shai’dan ne, Zahran sa ajiyar sa ne shi ka’dai cikin nufin ubangiji da kariyar sa sai gashi yasame ta fiye ma da yanda yake zato.

Godiya ya ringa zubawa mahalicci, lalle ya yarda komai ‘kaddara ne, ‘kaddarar aure ne kawai ya ha’da su da Mahmud bakomai ba tunda kam gashi tadawo masa batare da ko kwarzane ba.
Ha’ki’ka Fateemah tashi ce, Allah ne ya tsara cewa shine mijinta shiyasa ya adana masa ita da kyakkyawar kulawarsa.

Teemah ce tafara ‘karfin halin tureshi daga jikinta, Abbas be hanata ba sai ma yatsaya kallon idanun ta da suka kumbura sukayi luhu-luhu, tausayin ta ne yaji ya kamashi, yasan be kyauta mata ba yanda yayi mata da ‘karfi.
Duk dama yaga ‘ko’karin ta da ‘karfin halin ta sosai yaji da’din hakan dama baya son raguwar mace.

Tashi yayi ya wuce bayi ya ha’da mata ruwan ‘dumi mai yawa a bathtub sannan yadawo ‘dakin.

Teemah kam tana ganinsa sai ta sanya wani sabon kukan tana yun’kurin tashi amma sai taji duk jikinta tamkar an ‘daure mata shi.

Abbas yana daga tsaye yake kallon duk ‘ko’karin nata baya son takurata shiyasa ya barta dan ganin gudun ruwanta.
Data kasa tashin kawai sai ta sanya kuka tafara ambatan sunan Anty.

Abbas da sauri ya matso kusa da ita beyi wata-wata ba kawai yasa hannu ya ‘dagata tana fa’din ka ajiye ni ni bana so, ba ruwana dakai daga yau”
Muryar ta ma duk ta dishe ba sosai yake fita ba maganar tsaban kukan da tasha.

Abbas be ajiyeta ko’ina ba sai cikin bathtub da sauri Teemah ta taso tare da sakin wani wahalallan kukan dan sosai taji zafin ruwan daya ta6a ta.

Abbas kuwa be barta ta ‘dago ‘din ba sai ya ri’ke kafa’dun ta tana kuka tana mitan bata so kuma duk muguntan daya yi mata sai ta ha’da shi da Ummah ta rama mata. 

Murmushi yai yace da ita ” _naji amma kibari idan nagama yin duk muguntan sai ki fa’da mata kinga sai ki ji da’din cemata girma ne ya kamaki_ ” 

” _Naki bazan fa’da_ _ba’din_ ” tafa’da afusace.

Abbas daya fahimci cewa maganar sa ne bata so sai yayi shiru ya ‘kyaleta taci gaba da mitan ta, be barta ba har se daya tabbatar ‘dumin ya ratsa ta sannan yasake canja mata wani ruwan wanda be kai na farkon zafi ba. 

Yanzun kam da ‘kyar da lallami da ban baki tashiga, amma data shiga sai tayi shiru dan ita kanta taji da’din ruwan dayake ta rage jin zafin.

Fita yayi ya barta bayan yace da ita tayi wankan tsarki da niyyan janaba.

Tura baki tayi tabi bayansa da harara.
Koda ya fitan kuwa sai taci gaba da zamanta aruwan harse da taji yayi sanyi sannan ta fito daga cikin bathtub ‘din da dabara dan har yanzu tana jin zafin kuma ‘kafafunta na ciwo da cinyoyinta.

Ahankali tayi wanka sannan ta ‘dora da wankan tsarkin sai data gama sai kuma ta duba bataga komai ba da zata suturta jikinta dashi.

Kukan shagwa6a ta sanya daga cikin tare da fa’din ” _toh ni haka zan fito ne_ ?

Da sauri Abbas ya tashi ya matso yace ” _me ya faru_ ? 

” _banga towel ba ne_ “
Tace dashi cikin muryar kuka. 

Murmushi yayi acikin ransa yace ” _zakiyi abinda yafi haka ma indai kece_ “!


Wani sabon towel ya ‘dauko ya shiga bayin dashi a hannunsa, Teemah naganin sa sai ta juya da sauri tana gunguni ‘kasa-‘kasa. 

Kan kafa’dar ta Abbas ya ajiye towel ‘din yana murmushi ya juya shima yafita a hankali aransa yake ayyana ” _banda shirmen ta miye kuma yarage harda wani 6oye jiki_ ?

A hankali tafito bayan ta ‘daura towel ‘din, kamar wata me tsoron taka ‘kasa take tafiyar, sosai takejin zafi aduk lokacin data motsa jikin ta musamman yanzu da take ‘daga ‘kafafu tana tafiya sai take jin wani sabon azaba na ratsata, kasa jurewa tayi sai tasaka kuka tana tafiyar tana kuka, Abbas ma sai ya tsaya kallon ta domin ya nemi tallafa mata amma ta’ki sanadin haka ma sai ta ‘kara volume ‘din kukan nata.

Bata tsaya ba ahakan ta nufi hanyar barin ‘dakin, sau ‘daya ta kalli gadon sai taga ya janye bedsheet amma bai sa wani akai ba, ta6e baki tayi ta nufi hanyar ‘dakin ta, Abbas kam still da idanu ya rakata dan a wannan halin yasan ko yace zai dakatar da ita ma ba sauraran sa zatayi ba nd shima dakansan ji yayi baida guts ‘din tsareta a wannan lokacin ban dama sabon so da ‘kaunar ta gami da tausayin ta da suka sake cika masa zuciya bayajin komai shiyasa ma ya ‘kyale ta kawai.

Bayi ya kai bed sheet ‘din daya cire da niyyar wankewa amma tun kafin ya kai ga wankewan yajiyo muryar ta.

Tafiyan ce ta gagare ta bayan har ta isa parlour ma sai ta zauna tare da sakin sabon kuka tana ‘kiran sunan Mummy.

Da sauri ya ‘karaso inda take shima ya zauna agefen ta yana tambayar ta meke faruwa.

Cikin kuka ta bashi amsa da fa’din tagaji ne kuma ‘kafanta ma ciwo yake yi mata.

Koda ya nemi ganin inda ke ciwo a ‘kafan nata kuma sai ta’ki ta nuna masa sai ma fa’dawa jikinsa datayi tare da sakin wani kukan.

Da kansa ya fahimci inda keyi mata ciwon musamman da yaga ta’ki nuna masa wurin sai yaji tausayin ta sosai, hannu yasa yana bubbuga bayan ta ahankali kamar yarinya ‘karama yace ” _daina kukan haka kinji, laifin Yayah ne ko_ ?

Kukan ta taci gaba dayi amma tana ‘dan ‘kara rage masa ‘karfi da haka har yasamu tayi shiru sai yasa hannu ya ‘dauke ta da niyyar maida ta ‘dakinta, Teeemah kam cike da rigima take fa’din ” _bana so ni ka barni ba ruwana dakai……._ ” 

Be kula ta ba har se daya dangan tata da ‘dakinta kasancewar nasa gadon ba’a gyare yake ba.

Koda ya kwantar da ita kuwa zama yayi agefen ta tare da ran’kwafo da kansa kusa da fuskar ta, fuskar sa na kallon nata yasa hannun sa cikin nata ya sarke su wuri guda nata, ‘dayan kuma yasa kan fuskar ta yana ‘kara goge mata hawayen dake gangarowa ka’dan-ka’dan tare da tallafan kuncin ta yace
” _Stop crying owk…… ko kin fiso ki ringa ‘daga min hankali_ ?
Shiru tayi bata bashi amsa ba illah hawaye.

Story continues below


Rintse ido yayi ya bu’de akanta, shi be san me ze ce da ita ba, lallashi ba layinsa bane be iya ba sam, shiyasa ko yanzun ma ya rasa ya zaiyi da ita, duk kalaman daya tattaro ya dage ya furta amma still she’s crying, what can i do now?
Ya tambayi kansa. 


Lallashin ta yaci gaba da yi cikin natsuwa ra’da-ra’da kamar be san yin maganar amma shi ka’dai yasan yanda yake ji azuciyar sa game da ita jiyake tamkar ya maida ta cikin sa dan so, yafi so ta nutsu tukunna kafin ya san taimakon da ze iya bata amma hakan yakasa yiwuwa shi kuma sam be ‘kaunar ganin hawayen tan har ransa, da ‘kyar ya samu tayi shiru gaba ‘daya da ya sake cewa zai gani kuwa ta’ki yarda sam.
Sai yace 

” _Ki bari inga yanda ciwon yake sai in shafa miki magani awurin_ _ya daina zafin ko kinfi son in’kira Anty nurse tazo da_ _injection_ ?

Kai ta jijjiga masa a hankali tare da fa’din ” _ni banaso_ ” 

“Toh ki bari ingani ko?
  maganar yana raba jikinsa da hannayen su dake sar’ke. 

Ganin kamar ta amince sai yace “Yauwa ‘yan matan Yayah! 

A hankali yake bu’de towel ‘din dan har yanzu tana ri’ke  da shi da hannunta, bata iya ha’da kafafun ta amma ta ri’ke towel ‘din da hannu.
” _Bari ingani da wuri kafin ciwon yayi tsami kar ya ‘kara wani zafin ko_ ? 

Hannun ta cire ta kawar gefe.
‘Kafar ta ‘daya Abbas ya ‘daga a hankali ya ‘dora kan kafa’dar sa sannan ya gani, ba zai iya cewa ga yanayin data ke ciki ba dan shi ba likita bane amma sosai yake jin tausayin ta.

Towel ‘din ya rufa mata sannan ya fita kitchen sharp-sharp yasa ruwa a kettle ya jira yayi zafi sannan ya ha’do mata lafiyayyan tea be ko sa lipton ba illah milo da ovaltine daya zabga mata aciki.

Teemah na nan har yanzu akwancen tayi luf da ita sai ma rufe ilahirin jikinta datayi da blanket tana fidda siraran hawaye da.

Stool ya janyo zuwa gaban gadon yasata agaba sannan ya ajiye cup ‘din akan side drawer tare da janye mayafin a hankali.

Yana janyewa ta sake jan abinta ta shige ciki gaba ‘daya tace ” _ni ka ‘kyaleni ba ruwana da kai…._ 
Taran ta yayi da fa’din ” _naji ai nima baruwana da ke tafiya ma zanyi_ _amma yanzun kitashi kisha tea sai in tafi in barki in_ _ba haka ba in ‘kira Anty nurse ‘din tazo da allura uku tayi_ _miki_ “

Tana jin haka ta bu’de kanta tana ‘kwaba fuska, Abbas ne ya sa hannu ya talla fota zuwa jikinsa ta jinginu, anan yaji jikin ta ya ‘dau zafi rau yasan zazza6i ke shirin kamata, baya son kukan nata ko ka’dan dan tana karya masa zuciya ne sai yaga tamkar be aikata daidai ba laifin kansa yake kamawa tsaban tausayin ta daya ke ji yake tamkar ya cire mata ciwon da ana yin hakan be san wani irin lallashi zai mata tayi shiru ba.

Kanta ya ‘dago ya ritsa ta idanu yace ” _bar kukan haka nan mana ko so kike in ‘kara miki_ ?

Jijjiga kai tayi da sauri alamar “ah ah”
sai yace
” _toh shikenan share hawayen ki bazan sake ba ai wancan ‘dinma laifin ki ne bana hana ki wasan ruwan nan ba amma ki ka ‘ki jina shiyasa nayi miki amma in kina jin_ _magana ta bazamu sake yin fa’da ba ko kina so muna fa’da_ ?
Da kai tabashi amsa alamar “ah ah”.

Abbas sai yace ” _yauwa ‘yan matan Yayah, Allah yayi miki albarka ya haskaka rayuwar ki fiye da yanda kika hasakaka min zuciya ya saka_ _maki da aljannar sa ma’daukakiya ……_ 
Hannu yasa ya ‘dauko tea cup ‘din a hannunsa yana juyawa fuskar sa da murmushi yace “…… _ya kuma baki baby mai kama da waye ma…….?_ 
Ya ritsa ta da idanu.

Murmushi maganar tasa ta tasa ta sai ta tarasa mai ma zata ce dashi kuma sai kawai ta ya mutsa fuska tare da rike cikin ta alamar yunwa takeji.

Abbas ma murmushin yayi mai sauti sai ya bata cup ‘din a hannun ta ta ringa sha a hankali bata shanye ba ta mi’ka masa cup ‘din tace ya isheta dan bata jin da’din bakin ta sosai.

Abbas be matsa mata ba sai ya kar6a ya ajiye tare da tambayar ta zafin ciwon muryarta ciki ciki ta bashi da fa’din yana mata zafi ka’dan-ka’dan amma idan ta motsa ‘kafarta sosai takejin zafin. 

Abbas cewa yayi da ita ” _sorry… zai daina very soon da iznin Allah kinji_ “
Shiru tayi masa tafara ‘ko’karin kwanciya, Abbas sai ya gyara mata kwanciyar tare da lullu6e ta da kyau yace bari yana zuwa daga nan yafita a’dakin.

Yana komawa ‘dakin sa ya’kira layin nurse sukayi magana inda ya roketa cewa kar ta 6ata lokaci bayan haka sai ya tura mata address ‘din gidan nasu sannan ya ajiye wayar.

Bayi ya koma ya wanke bedsheet ‘din daya cire a gadon harda kayanta da suka jike ‘dazun gaba ‘daya ya hada ya wanke ya fita corridon baya ya shanya su.

Yana kammalawa ya shiga bathroom yayi wanka na biyu sannan yafito ya shirya cikin wani ba’kin long trouser da jan T-shirt kamar bashi ba, yana shirin fitowa sai yaji ‘karan door bell, yasan Anty nurse ce ko kuma driver cikin su ‘dayane ya iso.



Zuwa yayi ya bu’de ‘kofan sai yaci arba da driver a tsaye kar6an abincin yayi bayan sun gaisa harma drivern na bashi ha’kurin jinkirin da aka samu yace ruwane yasa ba’a kawo dawuri ba.
Abbas kuwa yace masa bakomai ai sannan ya wuce dinning.

A gate motar driver da Anty nurse suka yi clash yana fita itama ta shigo, Abbas na ajiye abin hannunsa sai ya kama hanyar ‘dakin ta domin duba yanayin datake ciki kafin ya isa sai yasake jin door bell karo na biyu, be ‘karasa ‘dakin ba sai ya juya izuwa ‘kofan dan a ‘kage yake Nurse ta iso dan ta duba masa ita.

Anty nurse ce tsaye tana murmushi shima murmushin yayi tare da matsawa yabata daman shigowa yana fa’din ” _har ina shirin sake ‘kiranki ai_ “

Nurse tace 
” _na hutar da kai ai tunda gani na iso”_ !

Zama take ‘ko’karin yi a kujera Abbas ya dakatar da ita da fa’din ” _muje dai tana ciki ai ba batun zama kuma_ “!
Dariya nurse tayi itama tace ” _toh bakomai yalla6ai ai dama ba zaman nazo yi ba_ ” 

Gaba yayi ta bishi abaya har zuwa ‘dakin Teemah inda suka same ta har tafara bacci, motsin shigowar su ne ya farkar da ita sai ta sau’ke idanu a kansu.

Tana ganin nurse sai ta maida kallon ta kan Abbas tana kwa6a fuska.

Nurse ‘din ne tana dariya tace mata ” _Ashe ‘yar shagwa6an Yayah me tsoron allura ce ma! Ya jikin naki_ ?

Ahankali tace ” _na warke tun ‘dazu!, ina kwana Anty_ “

” _Lafiya lau Alhamdulillah_ “
Anty nurse tace tare da zama agefen ta, Abbas kuma yana tsaye ya kama kunkumi da duka hannayensa biyu yana kallon ta.

” _Meke damunki_ ?
Anty nurse ‘din ta sake tambayar Teemah tare da ta6a wuyanta.

Take idanun ta suka tara ruwa sai ta ‘daga kai ta kalli Abbas ‘din suna ha’da idanu ya taho kusa da ita ya zauna tare da tallafan ta zuwa jikinsa sai ta 6oye fuskanta a’kirjinsa a hankali tace ” _Ni bana son allura Yayah_ ” 

Jinjina kai yayi tare da fa’din
” _Alright ki nutsu bazata miki ba magani kawai zata baki idan ta dubaki, kinji”_ 

Dayake yariga yayiwa nurse ‘din bayani tun a waya so bawani sabon bayani datake bu’kata daga wurin su illah ha’din kan Teemah.

Hanglove take sawa a hannun ta take fa’din ” _ina jin guri zaka bamu fah yalla6ai dan naga alama in kana kusa ba zamuyi abinda ya dace ba da wannan shagwa6a66iyar_ “.

Raba ta da jikinsa yayi yari’ke kafa’dun ta yace ” _ki nutsu ta duba ki kinji in har kika yi mata rashin ji_ _kinsan tana da allura ko, ni kuwa bazan hanata yimiki ba, zan dawo yanzu bari in ‘dauko_ _wayata_ “.

Fita yayi ya bar su inda Anty nurse ‘din tace mata ta gyara da kyau ta dubata, hawaye tafara yi ka’dan-ka’dan tare da fa’din ” _Anty dan Allah kar kimin allura in kika yimin mutuwa zanyi, Yayah ma mugunta yamin ‘dazu………_ “

Story continues below


” _Shiii…! yi shiru bazan miki allura ba karki damu kinji_ ” 

Kai ta ‘daga mata sannan ta bata chance ta duba ta.

Bama wani ciwo taji ba kawai dai ‘kan’kanta da rashin ‘karfi da jikintan ke dashi ne ha’di da rashin sabo yasa take jin bada’di, ga kuma shigan ‘karfin da akayi mata shiyasa take jin zafi sosai. 
Da farko nurse ‘din tayi tunanin ko ciwo sosai Teemahn taji amma sai kuma taga abin da sau’ki musamman dayake ta yi anfani da ruwan zafi so ba wata matsala sosai.

Data ga haka sai tace da Teemahn ” _Dama shi mijin kine_ ?
Da 
” _Ummm_ “
Teemah ta bata amsa tana mai jin kunyar ta ga jikinta. 

Nurse na cire hanglove ‘din hannun take fadin shine kike cewa yayi miki mugunta ko? Waye ya gaya miki ana fa’din haka?ko bakya son shine akayi muku auren ? 

Teemah kam shiru tayi tana tunanin me zata ce da Anty nurse ‘din, ita kuwa nurse tana har ha’da magunguna taci gaba da fa’din ” _kar kinayin taurin kai in bahaka ba kullum ciwo zaki rin’ka ji kinji_ ? 

Kai ta ‘daga mata alamar ” _toh_ “

” _Yauwa Fateemah, ko kinfi son mijinki yana neman wasu matan awaje_ ?
Yanzun ma da kai ta bata amsa daidai  Abbas ya turo ‘kofan ya shigo dan hankalin sa yakasa kwanciya.
Dukkan su sai hankalinsu yakoma kansa.

Gefen Teemah yazo ya zauna sai nurse tayi masa bayanin babu ma matsala sosai idan taci gaba da amfani da ruwan ‘dumi ma komai zai dai-dai ta. 

Sai ta bashi wasu magunguna kala biyu tace ta sha wannan zazza6in nata zai sau’ka kuma zai ‘kara taimakawa wajen healing ciwon da wuri. 

Godiya Abbas yayi mata inda a take yabawa Teemah maganin ta sha sai suka fita tare da nurse suka bar Teemah ita ka’dai inda ta koma ta sake kwantawa.

Suna fita parlourn nurse tace dashi ” _yalla6ai kafa so kayi 6arna gaskiya_ ” 

Kai Abbas ya sosa yace ” _Allah ya takaita ai na kuma gode masa_ “!

Sai tace ” _hakane amma dai a kiyaye  gaba saboda gudun matsala duk dama farkon shine_ _me wahala amma gaskiya a’dan sarara mata na kwana biyu_ “

” _Bakomai wannan ba matsala bane dr. nagode sosai_ “

Daga nan sukayi sallama ta tafi. 

Teemah kam fitsari ne ya matsata ta tashi ta shiga bayi, tana tsugun nawa sai ta mi’ke dan azaba zafi take ji sosai amma sai ta daure ta sake tsugunnawan sama-sama tayi fitsarin idanun ta harna hawaye amma haka ta daure dan bata so Yayah yasan da  ciwon balle yayi mata batun allura.

Abbas ma ‘dakin nata ya koma sai ya be ganta ba motsin ruwa da yajiyo a bayi ne yasa ya fahimci tana ciki, tsayuwa Abbas yayi yana jiran fitowar ta.

Teemah na share hawaye ta fito, tana ganinsa sai tayi turus ta sunkuyar da kanta ahankali ta isa gefen sa kanta a’kasa.

Hannunta ya kamo yajawo ta zuwa jikinsa yace ” _me yasame ki kike kuka, what’s wrong kuma ba kince kin warke ba_ ” 

Kai ta ‘daga masa.
Abbas shiru yayi yana kallon ta ya san tana jin zafin kawai de tace ta warke ne dan kar yace allura. 

A hankali ya sake fa’din
” _Toh meyafaru_ ?
Tace _”ni ka kaini wurin Mummy_ !”

” _Ba yau ba sai kin warke zan kaiki owk!_ 

Shiru tayi bata masa magana ba sai shine ya sake fa’din
” _Baki gaji da zama da towel ‘din bane har yanzu_ ? 

” _Yanzun ma kaya zan saka_ ” tace da shi a hankali.

Sakin ta yayi taje ta dubo kayan sai kuma ta tsaya ta rungume su a’kirjin ta tana kallon shi.

Story continues below


” _Ya akayi in zo insa miki ne_ ? 

Da sauri ta jijjiga kanta
” _ko sai na fita_ ?
Yayi maganar tare da ‘dage gira.

” _Umm_ “
tace dashi.
Sai yayi murmushi tare da barin ‘dakin yace ” _ina jiranki a parlour yanzu kar ki sake kwanciya fah kinji._ “

Kayan tasaka cikin natsuwa sannan ta fita ta same shi akan dinning yana break fast, wurin sa ta isa ta zauna tayi shiru daya nemi taci dai tace ahh sai anjima zata ci,sai daya gama sannan suka koma ‘dakin sa dukkan su Teemah bacci take ji dan haka sai da ta kwanta Abbas kuwa system ‘dinsa yasa a gaba yana operating zaune kusa da ita seconds-seconds yake juyawa ya ganta.

Ranar haka ya wuni agida babu inda yaje illah masallaci, da azahar Teemah ta tashi ta koma ‘dakin ta sallah itama, dayake data yi baccin sai taji jikinta yayi mata wani iri zazza6in babu yanzu amma kuma still bata koma normal gaba ‘daya ba, ruwa ta watsa ajikin ta ta reda sake zama cikin ruwan ‘dumi dan ta fahimci shine ya ‘dan sanyaya mata zafin ‘dazu dasafe.

Wata ba’kar doguwar riga ta sanya ajikin ta me adon golden colour stones manya, sai data idar da sallah sannan ta ‘dauki veil shima golden ta yane kanta dashi, parlour ta dawo dan yanzun kam ba laifi ta ‘dan ji dama-dama, anan Abbas yazo yasame ta ya kuwa ji da’din hakan shima cikin shigar ‘kananun kaya yake bai so fitan ba amma daya tuna cewa gobe ne tafiyar su Mummy sai yaga dacewar kaita dan suyi sallama ma kuma ko dan ya faranta mata tunda dakan ta ma ta nemi zuwa ‘dazun, shaf ya manta da batun tafiyar sai yanzu daya fita Daddy ya ‘kira shi dan ya isar masa da wani sa’ko shiyasa ma ya tuna sai kawai ya ce da ita tatashi ya kaita gurin Mummy.

Yana tafiya zuwa ‘dakin sa domin ‘dauko key yayi maganar so be kula da yanayin da ta shiga ba abinda ka’dai yasani shine zataji da’din hakan.

Teemah kam farin ciki ne yacika sosai har da tashi da ‘karfinta dan murna alokacin ne ta tuna da taji zafi a’kasanta amma ahakan ta daure dan kar yace yafasa.

Abbas sam hankalin sa be je kan yanayin tafiyar ta ba saboda yaga ta warware shiyasa ma be damu ba be sani ba ashe idan an kula sosai za’a ga chanji tattare da ita.

Suna shiga parlourn suka tarar da su Ummah ga6a ‘dayan su zaune a cikin parlourn, Teemah taso ta isa da gudu amma sai taji tsoron kar taji zafi sai ta ‘karasa a hankali, hakan ma dan tana daure wa ne shiyasa sosai take ‘karfin hali wurin ganin ta 6oye ciwon ko dan gudun allura ma.

Tana isa ta fa’da jikin Mummy sai kuma ta saki kuka, wanda ya jawo hankalin dukkan su zuwa gare ta, Abbas kam mamaki ne yacika shi ganin lafiya ‘kalau suka taho toh menene kuma na kuka yanzu anan.

Anty murmushi take yi dan tana ganin Teemah ta fahimci yanayin ta data ke ciki, Ummah kuma mamaki ne ya ziyarce ta yayin da tausayin Teemah ya cika zuciyar Mummy nan take.  

Abbas zama yayi daga ‘dan nesa da su ya zuba mata idanu.

Mummy bata tam
baye ta me yafaru ba illah kawai rungumar ta da ta yi itama tana babbuga bayan ta alamar rarrashi.

Ummah kam Abbas take kallo ganin duk ya zama kamar a birkice da ganin kukan Fateemahn.

Anty ne tace da ita
” _zo nan Fateema wai me ya sameki kike kuka haka nan ko duk missing ‘din namu ne_ ?

Taso wa tayi a nutse ta dawo wurin Antyn tana me cigaba da zubda hawaye.

Anty mi’kewa tayi tare da kama hannunta suka shige ciki inda sika bar parlourn batare da ko gaisuwa sunyi da Abbas ba. 

Fitan sun ne yabawa Abbas daman gaida su Ummah, gama gaisuwar keda wuya kuwa Mummy ma ta bar ‘dakin dan sosai yau ‘din taji nauyin sirikin nata ya kamata.

Story continues below


Ummah kuwa ganin anbar su su biyu take sai ta 6ata rai ta kalle shi tace dashi 
” _Muhammad wace mugun ta kake yiwa yarinyar nan da har_ _take irin wannan kukan_ ?

Ido Abbas ya ‘dan zaro waje yace ” _mugunta dai Ummah ni ‘din_ ?
_Ai kinsan halin yaron ki ba mugu bane, Allah shagwa6a ce ke kawai damun_ _ta wai dan kanta na ciwo_ “
Ya ‘karashe maganar da sosa kansa.

Ummah cewa tayi 
” _Ni dai kasan banason zalinci koka’dan ballantana rashin imani da tausayi, komai zakayi ka rin’ka tuna cewa shekarun ku ba ‘daya da ita ba da kuma raunin ta na ‘ya mace_ “! 

” _Toh Ummah insha Allahu zan kiyaye_ “
Yasan halin Ummahn sa  adun’kule yanzun tayi masa fa’dan, yasan ba mamaki tagano matsalar su ne shiyasa tafa’di hakan dan ta gama gano abinda yafaru.

Yanzune ma yake jin dama be kawo ta ba yazo abinsa shi ka’dai,  bayan yasan su Ummah sun girmi tunanin sa, sai dai kuma a wannan yanayin ba ze iya fita yabar ta ita ka’dai ba hankalinsa ba zai kwanta ba sam, dama beyi niyyan zuwa ko’ina ba sai kuma Daddy ya aike shi. 

” _Tasha maganin ciwon kan ne_ ?
Ummah ta tambaye shi.
Da ” _ehh Ummah tasha magani tun ‘dazu ma_ ” yabata amsar tambayar tata.
” _Allah ya sauwa’ka toh”_ 
Toh Ummahn ta sake fa’di atakaice.

Anty kam suna shiga ciki ta zaunar da Teemah a bakin gado tare da tsare ta da tambayar me yafaru. 

Da in-inah Teemah tafara magana cewa ” _Ya….yah ne…!_ 

Da sauri Anty ta tare ta da fa’din ” _dukan ki yayi_ ? 

Sai ta jijjiga kanta alamar ” _ah ah_ ” 

Anty kuwa bata sake tambayar ta sai tace
” _Toh shikenan kiyi shiru ki daina kuka, jikinki na ciwo sosai ne?_ 
Cikin shagwa6a Teemah ta bata amsa da fa’din
” _K’afata na min ciwo idan…zauna da tafiya… ma_ “
” _Toh yi ha’kuri a hankali zai daina kinji, ina kinyi amfani da ruwan zafi_ ? 

Kai Teemah ta ‘daga mata. 

Anty ma sai ta jinjina kai kawai batare da furta wata kalma ba. 

Wani abu ta ha’da mata a cup da madara tabata ta ce ta shanye zafin zai daina da iznin Allah. 

Teemah da bata san ko menene ba kar6a kawai tayi ta shanye abinta dan so takeyi zafin datake ji ya daina gaba ‘daya ko dan tana yin fitsari ba fargaba ma.

Yanzune Anty ta fahimci cewa barrier ‘din da Munnira tayiwa Mahmud da Fateemah yayi tasiri akan su, yanzu ne ta  sake tabbatar da gaskiya cewa Mahmud be ‘dorawa Fateemah iddar komai ba har yakoma ga mahallicin sa.
Ha’kika ta cutar da rayuwar ‘danta ta fuskoki da dama, addu’ah tayi masa cikin ranta tare da nema masa gafarar mahalicci.
Lallai da gudummuwar ta rayuwar gidan ‘dan ta na cikinta ya ta6ar6are, ha’ki’ka bata kasance uwa tagari ba, bata fatan irin hakan yasake faruwa ga rayuwar wanin ta har abada.

‘Ko’kari tayi ta maida hawayen ta tace yah Allahu kayafemin, ka kai haske cikin ‘kabarin Mahmud.

*2:20pm* 
Hannah ta dawo da mugun gajiyar ta inda tasami Ummah da Abbas zaune a parlour suna ‘dan ta6a hira, zama tayi a kusa da Ummah tare da fa’din ” _wash Allah na, Ummah na gaji sosai yau ‘din nan,_ _Allah gudowa ma nayi_ “.

Abbas kallon ta yayi da mamaki yace 
” _saboda me kenan_ ? 

Hannah juya idanu tayi sai suka ha’da ido da Ummah afakaice, sai tace ” _Yayah lecture ‘daya ne yarage mana kuma ance lecturer ‘din baya gari shiyasa na taho_ ” 

Abbas shiru yayi ya dai ji tane kawai ba wai dan ya yarda ba, amma be kulata dan shi yanzu damuwar da ta dami ransa dabance, so yake yasan halin da matar sa ke ciki kafin ya wuce. 

Story continues below



Hannah gaishe shi tayi sai ta tambaye shi ” _Yayah ya Teemah fah_ ?

Kafin yayi magana sai Ummah ta bata amsa da fa’din ” _tana ciki tare suka zo, ba mamaki tana wajen Antyn ta_ “

Hannah najin haka ta tashi da sauri jakar ta ma anan tabari ta nufi ciki.

Teemah har yanzu tana wurin Anty inda take ‘kara jan hankalin ta akan ri’ke mutuncin aurenta sanin girma da kuma darajan da mijin ta ke dashi tare da ri’ke sirrin dake tsakanin su. 

Da sallama Hannah ta shiga ‘dakin ta samu Anty na ‘daure wa Teemah  gashin kanta.

Da gudu taje ta rungume ta tana fa’din ” _i so much miss u matar Yayah!tun yaushe kuka zo_ ?

” _Zaki karyani Hannah dan Allah_ !
Inji teemah 

Hannah kuwa sai tace
” _Ba laifi ai kona karyakin be wuci ace ‘kiyayyar dangin miji ba_ “

Murmushi Anty tayi tace musu maza su koma ‘dakin su suje su huta wannan hayaniyar ta isa haka. 

Suna shiga ‘dakin Hannah ta sake tambayar ta wai tun yaushe suka zo? 

Da
” _Bamu da’de ba_ ” Teemah ta bata amsa tana yatsina fuska.

Abbas har zai tafi sai yace da Ummah bari yaga Mummy kafin ya wuce.

Yana shiga 6angaren da zai kaishi ‘dakin da Mummyn take sai yajiyo hayaniyar Hannah yasan may be suna tare ne tunda yaji hayani ya har haka.

Canja hanya yayi ya isa ‘dakin Hannah be tsaya bugawa ba kawai ya tura ‘kofar sai ya tsaya batare da ya shigo ba. 

Shiru sukayi da ganin san dama ita Teemah ba wani dogon magana takeyi ba Hannah ce me surutun.
Shi kanshi be san me yakawo shi ba, zuciyar sa ke bu’katan hakan, dama ganin ta yaso yi kuma daya gantan sai ya rasa abin fa’da kawai sai ya ‘karaso cikin ‘dakin a hankali, yazo gabanta ya tsaya yana kallon ta  a hankali ya furta  ” _ya jikin naki_ ? 

Da sauri tace dashi ” _da sau’ki_ ” 

Yace ” _toh zan tafi amma anjima zan dawo mu koma gida kinji_ ” 

Teemah shiru tayi masa shima sai kawai ya juya ga Hannah yace 
” _Hannah plz ki tabbatar taci abinci_ ” Yana gama fa’din haka ya fice a ‘dakin cikin takunsa na ‘kasaita, shi kansa yana mamakin kansa a yau ‘din yanda yake ji game da matar tasa, Hannah na wurin ne ma shiyasa be son jan magana sosai.

Yana fita Hannah ta tashi da sauri ta le’ka bayan sa ganin yatafin yasa ta sake dawowa wurin Teemah ta dafa kafa’dar ta da mamaki tace ” _matar Yayah nifa bangane ba, me ya sameki naji Yayah yana tamabayar jikinki harma da bani kwangilar saki cin abinci_ ?

” _banda lafiya ne_ “
Teemah ta bata amsa a takaice.

Karkata kai Hannah tayi da zararran ido take kallon Teemah da sigar tsokana tace ” _Ciwon amarci ko?_ 

” _Wata’kila_ “!
Teemah tace tare da gyara zamanta. 

” _Kede fa’di gaskiya matar captain ai nima naganki badai ba_ ” 

Da ‘dan ‘karfi Teemah tace
” _Bansani ba Hannah plz ki ‘kyaleni ke dama ba mutun ya ha’du dake ba duk_ _yadda yakai ga kewar ki sai kin 6ata ran mutun kike jinda’di_ “

Dariya Hannah tayi tace ” _Come down mana amarya! 6ata ran me kuma nayi miki amaryar Yayah fisabilillahi? ke de kice bakya so in san cewa Yayah ya fa’da_ _ne, amma ai tun ‘dazu ma bangane kanki ba duk kin canja Allah kinyi wata iri_ _ashe ashe yarinya taji da bambanci ne_ !”

Saukar da murya Teemah tayi tace
” _Hannah Allah banaso bambancin me kuma naji?_ 

Da murmushi Hannah tace 

Story continues below


” _Kin fini sani ai yarinya keda kika san komai kuma ni zaki tambaya, jifa yanda yazo shima ‘daya ko kunya_ _bai ji wai ya jikin naki.? Bayan yana gani na wurin ko kunyata fa be ji ba”_ 
Baki ta kama tace ” _kai Allah ya shiryi Yayah wallahi_ “.

” _Kema Allah ya shirye ki ai kema ba kunyar ne dake ba da kike waya da Bilal a inda nake kina jin kunyata ne? kuma kamar a kunnan sa hakan da kika ce”_ 

” _Bazan yi mamaki ba ai nasan yanzu amarya kike kuma ba kya laifi, so ko kin kareshi ma nasan ba laifin ki bane, ballantana_ _yanzu da kika san da’din miji nasan fiye da haka ma zakiyi, sai dai plz kiji ‘kaina karki fa’dawa Yayah_ _abinda nace nayi al’kawarin indai da raina zan tayaki zaman jego da rainon baby_ “

Duka Teemah ta kai mata tare da fa’din “‘ _yar rainin sense_ _kawai_ “
sai ta goce tana dariya tace ” _Toh ina laifi da zan miki zaman jego tunda wannan ‘din ba a gayya ceni ba wancen kam_ _ai kinga ko babu gayyata sai naje may be ma sanadin haka na samu namesake_ ” 

” Allah ya kiyaye ‘yata tazama takwararki” 

Hannah kwafa tayi tace ” _Harma_ …..”? 

Da ” _ehh_ “

” _aw ashe ma zaki haihun kinga kuwa zuwana tabbas_ ” 

Teemah ta amsa mata tayi da fa’din ” _bismillah sai ki je ai mugani_ “

” _Dai na gagagwa kamar yau ne insha Allahu matar Yayah ai anyi me wuyan…. kai amma fa nasan kin ji jiki da ganin_ _yanda kika koma har kina bani tausayi wallahi_ “

Juya wa Teemah tayi ta kwanta kawai tana mita wai Hannah ta tattare surutun duk ‘yan gidan nan akanta, she is so talkative ita bazata iya da surutun Hannah ba.

Hannah ma tashi tayi tana rage kayan jikin ta take sake fa’din ” _dan Allah matar Yayah in zaki haihu ki haifo min baby girl me kama dani_ _kinji_ ? 

Teemah ‘kin kulata tayi da Hannah taga  haka sai tace bari ta je ta kawo musu abinci……tana fitan tasake fa’din ” _ko baki kulani bama de sai kin haifa_ “

Abbas daga wurin Mummy ya wuce bai sake dawowa ba.

Ko gurin cin abincin Hannah bata bar Teemah da tsokana ba har suka ‘kare.
Sai daga baya suka koma wajen su Mummy anan ta sake suka ta hira abinsu kamar ba ita ba.

Sai bayan sallar isha’i Abbas ya dawo gidan dan su tafi, lokacin kuwa hajiya Fateemah an saki jiki a gida kawai sai taji labarin wai yazo.

Ummah ce tace ko za’a barta agida kawai zuwa gobe sai ta koma saboda ganin kamar Teemah batason tafiyar.

Teemah kam da murnar ta ta amsa da ” _ehh Ummah…._ “
Da sauri Mummy da Anty suka ce ” _ah ah tafiya zatayi, zaman me zatayi musu kuma anan, gara ta koma gidan_ _mijinta yafi_ “

Dole Ummah tayi shiru dan bakin su yafi nata.
Da fushi kuwa ta tafi suka bar su Hannah da kewa.

Bayan tafiyar su ne Anty tayi wa su Ummah bayanin cewa dama ba iddar Mahmud akan Fateemah, Mahmud be ‘dora mata iddah ba, tabasu labarin duk abinda ya faru game da hakan da yake a baya lokacin rasuwar Mahmud bata bayyana wannan ‘din ga kowa ba saboda aganin ta sirri ne.

Dukkan su sunyi mamaki sosai sai abin yaso ya dawo musu sabo aransu kowa na tunanin ashe har haka Teemah tayi zaman ‘kunci tare da Mahmud lalle duniya abin tsorone, tunda gashi wanda akayi domin san ma babu shi yatafi ya bar kowa da tarin nadama.
*Allah Ubangiji ya sa mufi ‘karfin zu’katan mu ya kyautata mana ‘karshen mu.* 
( ~Ameen~ )

Mummy ce ke wannan addu’ar acikin ranta, Anty kam hawaye take sharewa a hankali dan ta tuna da ‘danta marigayi, Ummah kuwa har taje bacci tana tunanin wannan abin aranta.

Story continues below


Suna komawa gida direct ‘dakin Abbas suka wuce amma bai bari ta kwanta ba sai da ya bata magani tasha sannan ya bari ta kwanta yaraka ‘dakin ta canjo kaya ma ‘ki yayi dole sai da ta saka wata t-shirt ‘dinsa mai ‘dan girma sai kuwa rigar ta rufe mata jiki ka’dan domin ya’dan sau’ko mata, shi kanshi Abbas rigar tana bashi balance bai fiya sakata ba sai in yanada bu’katar shan iska., wanka ya shiga koda ya fito ya shirya ma sai da yayi sallah sannan ya hawo gadon, jikinta yazo ya matso ya rungumo ta Teemah take ta fara ‘ko’karin barin jikinsa da sauri dama ‘dari-‘dari takeyi dashi shiyasa tun ‘dazu bacci yakasa ‘daukan ta, Abbas sai ya ra’da mata ” _come on… ki nutsu ban son rigima i thought rage miki wahala zanyi, naga anjima dakan ki ma zaki shige min jiki_ _ko da banaso_ ”  

Shiru tayi kawai ta zubawa ‘kirjinsa idanu tana jin tsoron sa har ranta  amma data ga bai yi mata komai ba sai ta saki ranta ajikin nasa har bacci ya ‘dauke ta. 

Abbas ma dagangan ya ‘kyaleta be mata komai ba dan ya fahimci tsoronsa dake cikin ‘kwayar idanun ta, kuma baya so tsoron yayi tasiri azuciyar ta shiyasa.

Washe gari da safe bayan sunyi sallah Abbas wanka ya shiga yafito da hanzari yake yin komai yayin da Teemah ke bin sa da idanu, yana gaban mirror yana gogec ruwan kansa ta cikin mirror ya hango yanda take kallon sa.

Juywa yayi yace da ita ” _kallon fah_ “
Tare da ‘dage gira.

Take ta tura baki ta tayi sama da idanun ta zuwa kan photon sa dake sama tace ” _ni kai nake kallo ne_ ? 

” _Toh wa kike kallo gaya min_ ?
Ya sake tambayar ta. 

Sai ta nuna masa photon da hannu. 

Murmushi yayi yace ” _photon ki ne toh wannan ‘din_ ? 

” _Umm-umm_ “
Tace a hankali. 

Sai ya sake fa’din 

” _Photon mijin ki kike gani ko_ ? 

Shiru tayi masa tana ‘kun’kuni Abbas kam ‘dauke idanun sa yayi a kanta yaci gaba da abinda yake yi.

Shine yaje ya raja su Mummy da Anty ranar duk suka wuce kano gaba ‘daya, Mummy ma naso ta gaida dangi wa’dan da ba su ha’du da su ba dan basu samu halattan bikin ba.

Kafin ya dawo kuwa Teemah ta tashi dayake taji ‘karfin jikin ta yanzun bata jin zafin komai, aiki tayi agidan sosai inda ya dawo tsab da shi sannan tayi wanka ta shirya cikin ‘kananun kayan ta riga da ta kai mata ko gwiwa ba da dogon wandon skinny tayi kyau kamar asace ta, gashin ta ta kama ta ‘daure a tsakiyar kanta da ‘karamin ribbom.

Abbas kansa daya dawo yaji da’din hakan sai ma yaji wani sabon san kasancewa da ita a lokacin.

Zama yayi a kujera yana kallon ta da lumsassun idanu yace ” _nagaji yau ‘din nan zo ki tayani rage kaya na plz_ !

‘Kasa-‘kasa tace ” _kai baka da hannu_ _ne_ ?

Sarai yaji ta amma sai yayi kamar be ji ba sai ma cewa da yayi ” _quickly plz yunwa nake ji fah_ !

A hankali ta ‘kara so inda yake ta fara 6alle masa bottuns ‘din rigar batare da ta kalli idanun sa ba.

Abbas hannu yasa daga bayan ta ya tura ta ta fa’do jikin sa tana ‘ko’karin mi’kewa Abbas ya ‘ki bata dama sai ya matso da fuskar sa kusa da tata, rintse idanu tayi da ‘karfi hannun kan ‘kirkinsa tana so ta ture shi amma hakan ya gagare ta dan ko motsi be yi ba, bakin su ya ha’de ya fara bata lafiyayyan kiss me tsayawa azuciyar masoyi.

Teeemah kam tsintan kanta tayi awani irin yanayi bazata ce ga yanayin data tsinci kanta ba amma duk da haka sai take mutsu-mutsu dan ta ‘kwaci kanta, Abbas be bar ta ba sai da ya tabbatar cewa sa’kon sa ya isa sannan ya ‘kyaleta.

Story continues below


Muryar sa ciki-ciki yace ” _tashi ki bani abinci_ “!

Shiru tayi kamar bata ji ba tana maida numfashi a hankali kanta akan ‘kirjin sa ” _kina son ‘kari ne?_ 
Ya tambaye ta sai ta mi’ke a hankali ta isa dinning shima Abbas a baya yabita yana ‘ko’karin daidaita nutsuwar sa.

Haka Abbas yaci gaba da kulawa da ita be ‘kara ra6an ta ba duk kuwa da cewa yana tsananin bu’katan hakan amma ya danne saboda tausayin halin da zata shiga.
Sai de yakanyi ‘ko’kari wajen koyar da ita karatun sa mai wuyar fassaruwa  musamman idan suka zo bacci, sosai yake ‘daura ta akan alayi mai wuyan mantawa, dan baya barin ta kwanciya haka batare da yayi wasa da albarkatun jikin ta ba koda kuwa da wani lokaci ne yakan ritsata da hakan. Wani lokaci idan zatayi masa gardama yakan yawaita tsorata ta da Anty nurse abu ka’dan sai yace zai ‘kirata tayi mata allura tun Teemah tana masa taurin kai har tazo ta daina balle data ga baya mata irin na rannan me zafi sai kawai itama ta rin’ka barin shi koda wani lokaci ne kuwa.


*****
Kwance take ajikin sa wani dare, idanun Abbas na lumshe lokacin har ya fara bacci ma sai ta rin’ka ‘kiran sunan shi ahankali, bai bu’de idanun sa ba ya amsa mata da fa’din ” _inajinki_ ” 

Muryarta a sanyaye tace dashi
” _Yayah yaushe zaka kaini inga Zahra_ ?

” _Sai ranar da kika zama cikakkiyar doctor_ ?
Ya bata amsa da lumsassun idanu. 

Teemah ta 6ata rai tace  
” _Hum-umm ni nace ma inason zama likita ne_ ?

” _Zaki zama ai da iznin Allah ki rin’ka yiwa wasu allura kema harda Zahra ta sai kin mata_ _dan bataji kullum rashin kunya take min…. irin alluran Anty nurse zaki nayi mata mai zafi_ ” 

Yatsina fuska Teemah tayi harda karya wuya  tace
” _Ni kam banaso_ !

” _Toh kuwa babu ke babu ganin Zahra ta_ “! 

Shiru tayi kawai tana tunanin wannan Zahran.


*****
Kwana biyu bayan hakan da wata safiya fitowan ta daga wanka kenan ta tsaya gaban mirror tana goge ruwan dake jikinta, al’adar ta ce wannan, kusan ma za’ace tasaba da hakan tuntuni idan ta fito daga wanka bata damuwa da komai take raba jikin ta da towel ‘din wani lokaci ma dashi take goge jikin ta sannan idan tagama sai ta shanya shi, sanadin haka yasa har yau bata son yin wanka a ‘dakin Abbas saboda gudun masifar sa.

Turo ‘kofa kawai taji anyi batare da ko sallama ba sai ma ” _excuse me_ ” daya fa’di dai-dai da tura ‘kofan.

Firgita tayi daga inda take tsayen take kuwa ta fara lalu6en towel ‘din da sauri.

Koda ta ‘daukan kuma garin sauri sai ta kama ba daidai ba bakin sama dana ‘kasa ta kamo sai ya kasance a mur’de kamar ta kama, kamar ta tsala ihu haka taji dan takaici gashi ya ‘kura mata idanu kamar zai cinyeta.

Sai data samu ta daidai ta towel ‘din kafin ta juya baya,  ‘kasa-‘kasa tace 
” _sai kace ba musulmi ba zaka wani shigowa mutun ‘daki babu ko neman izini_ “

Caraf taji an kama hannun ta tare da juyo da ita, Teemah bata san lokacin daya iso kusa da ita ba sai hakan ya ‘kara tsora tata.

Cikin idanun ta yake kallo ita kuwa sai tayi ‘kasa da nata idanun ta sau’ke su akan  ‘kirjinsa, bata juran irin wannan kallon daga gareshi, kwarjininsa rauni yake sata.

Abbas idanun sa ya mayar kan wuyan ta sai ya ‘kara matso da ita zuwa jikinsa sosai daf da juna yace ” _zagina kike yi ko_ ?

Kai ta jijjiga masa da sauri
” _toh menene_ ?
Ya sake tambayar ta tare da sake rage ‘yar ‘karamar tazarar dake tsakanin su.
Yayinda Teemah tayi shiru sosai ta ke tsorata da wannan yanayin.
” _Me kika ce fa’da min naji_ “
A hankali yayi maganar yanda ita ka’dai ce zata ji.

Itama a irin yanayin tace ” _da kaina nake yi fah!_ 

Tun kam ma ta ‘karasa yace ” _shiyasa nake so in sani ai_ ” 

Baki ta tura gaba dan bata san me zata ce dashi ba a wannan halin gashi ya takurata banda numfashin sa bata sha’kan komai.

Murmushi yayi tare da ‘dage idanu sama ka’dan yace ” _kinji haushi ne dana kalli jikin ki?_ 

Shiru tayi dan takaici sai ma idanun ta suka fara tara hawaye. 

Abbas kam sai yasake fa’din ” _an gaya miki haramun nagani ne toh ko kin manta jiya da da_ ……

Da sauri Teemah ta toshe masa baki da hannunta ‘daya dan kar ya ‘karasa fa’da,  ita kanta ta manta cewar yagama ganin dukkan ilahirin jikin ta musamman jiya da yi mata wani mahaukacin romance ‘din da be ta6a yimata irin sa ba, ita kanta sai da taji cewa ta isa, yanzun daya tuna mata kuwa bata so tasake ji ya furta da bakinsa, kunyarsa zataji sosai.

Idanun ta cikin nashi suna kallon kallo, take kuwa hawayen ta suka gangaro wanda yasa dole sai data lumshe idanunta.

Abbas kam hannun ta ya cire daga bakin nasa sai ya samu daman ha’de musu baki, bai barta ba kuwa har se da ya tabbatar ya danganta ta da gadon dake cikin ‘dakin.

Sosai ranar ya sake maimaita wa, gara ya kwasa son ranshi sannan ya ‘kyale ta.

Teemah kam yau bata ji zafi ba amma kuma hakan be hana ta kuka ba inda taringa ha’dawa har dana shagwa6a ma.

Tare sukayi wanka a bathroom ‘din ta Abbas nata tsokanan ta wai ai ranan tace zata ha’dashi dasu Daddy da Ummah su cire masa kunne,  meyasa yau kuma bata fa’di hakan ba sai ma ita ke ‘ko’karin cire masa kunnan nasa saboda santi.

Dayake yau ‘din da ‘dan karfin ta ba kamar rannan ba, duk dama Abbas din bana wasa bane sosai ya galabaitar da ita amma hakan  be sa bakin ta ya mutu ba, sai ta bu’di baki a hankali ta maida masa martani da fa’din ” _bawani santi ita kam dataji banda azaba……. kuma ai sai ta gaya shi da Daddyn tunda baze_ _daina yi mata muguntan ba_ ” 

Abbas kam cemata  yayi ” _bari na ‘kara toh sai ki ji da’din fa’da musu mai dalili_ “

Tana jin haka ta tashi ta fito ta barshi abayin da sauri.
Dariya yabi bayan ta dashi kawai, daman ma tsokanan ta kawai yakeyi.

Sai da yafito kafin ta koma tayi wankan tsarki Abbas na sake cewa da ita wai ” _matsoraciya_ “.

Kwana biyu bayan hakan Abbas ya koma Rivers dan dama hutun 1week aka bashi, kafin hakan kuwa sun sha drama da Daddyn Abuja akan tafiyar, Abbas ya so su koma tare da matar sa amma Daddyn Abuja ya hana shi, dan cewa yayi baza’a tafi masa can wata uwa duniya da yarinya ba, salon aji da’din cutar da ita acan ba, shi be yadda da zaman sun ba har yanzu yana ganin kamar Abbas mugun hali zai yi tayi mata, amma idan tana kusa da su toh abin zai zo da sau’ki kuma dole ne ya rin’ka kulawa da ita ko dan ganin idanun su ma.

Daddy gani yake kamar a bayan idanun su Abbas zai na zalintar ta ne kawai, shiyasa yace tukunna sai yaga yanayin zaman nasu kafin ta bishi.

Shi kansa daddyn cewa yayi bazai bar Abbas ‘din yaringa daukan tsawon lokaci ba dole zai na zuwa duba ta.

Abbas be iya musu ko jan magana ba dan haka sai ya yi shiru kawai amma ba wai dan ransa ya so hakan ba, ya so ya sanar da Daddy babbah saboda yasan shi ka’dai ne zai sa Daddy amincewa amma kuma nauyin sa yake ‘dan ji yanzun kuma ma dan kar Daddyn nasa yaga kamar yana jayayya ne da maganar sa shiyasa kawai ya fasa.

Ya dai ‘dora hope ‘din sa akan Teemah da tunanin ko zata yadda itan tace zata bishi, amma ko daya zo ya same ta da batun sai ta nuna ‘kin amincewar ta sai ma tace zata koma gidan Ummah  kawai idan ya tafi. 

Bai san dalilin ta na ‘kin amincewan ba, amma ba ‘karamin haushi yaji ba yasan da ita ta amince toh da Daddy ma zai yi shiru akan lamarin.

Ai kuwa shima Abbas yace babu inda za taje agida zata yi ta zama ita ka’dai tunda bazata bishi ba.

Sosai ta tsorata da zaman da zata yi a gida ita ka’dai ‘din saboda tuna baya da tayi, amma sai take ganin da ta bishi ‘din gara ta zauna agidan in yaso idan ya tafi sai ta koma abinta ai baze sani ba.
Sosai Teemah ta ‘dauki abin wasa.

Haka har Abbas ya tafi da haushin ta ha’di da kewar ta da zaiyi azuciyar sa.


*****
Anty ma a cikin week ‘din ta bar kano ta koma Lagos, yanzu kam zuciyar ta fes ba wani damuwa, bata da burin cutar da kowa aranta illah taga ta gyara tsakanin ta da ubangijin ta ta kuma gyara lahirar ta, gidan ta ma ba ‘daya da kishiyar ta ba amma bayan ta koma Abbah ya kawo amaryar sa har gida suka wuni tare dan Abbah kansa zuwa yanzun ya yadda da cewa Anty ta yi nadama ta gaskiya ta gyara halin ta gaba ‘daya ta canja su daga munana zuwa kyawawa musamman daya ga yanda taje har Abuja  musamman saboda Fateemah shiyasa ma batare da fargaban komai ba ya bar amaryar sa tare da ita.

Anty ma a’dan zaman nasu ne ta fahimci cewa kishiyar ta irin alkahiri ce mai sanyin hali, dangin albarka, tariga ta ‘dauri aniyar kar6an kaddarar ta aduk yanda tazo mata, ta yarda cewa zata zauna zaman amana da kishiyar ta, cikin aminci da salama shiyasa ma bata damu ba ta budewa Anty Sadiya zuciyar ta gaba ‘daya.

Story continues below


Haka kishiyar ta ma bata nuna mata komai ba suka ha’de kansu tamkar ‘yan uwan juna, kowa ya ri’ke matsayin dayake kai.

Raba kwanakin su sukayi kamar yadda dukkan ilahirin masu kishiya keyi wato kwanaki bibbiyu.


*****
Ummah ma taso Abbas ya koma Porthacourt da matar sa sai Daddy ya hana, tayi ko’kari sosai wajen ganin ta gyara abin amma be yiwu ba, bayan haka kuma sai tayi tunanin ko Teemahn zata dawo gida ne kafin ya dawo, sai kuma Abbas shima ya yi nasa ikon ya hana.

Mamaki Ummah tayi sosai akan hakan kuma sai ta tambayi Teemahn ko tayi masa wani laifi ne tace ah ah wai dan ta’ki binsa ne shiyasa, Ummah batayi mamaki ba dama tasan sai da dalili kafin zaiyi hakan dan tasan baze yi purnishing ‘din ta akan laifin Daddy ba, tasan yayi hakan ne dan yayi purnishing ‘dinta akan ‘kin amincewa binsa da tayi, Ummah sam hakan beyi mata da’di ba, aganin ta tunda abaya nema ake yayi auren amma ya’ki har sai da akayi masa za6i, Alhamdulillah kuma sai ya kar6i za6in nasu da hannu bibbiyu toh me yasa kuma ba za’a bar shi ya nutsar da hankalin sa wuri guda ba, me yasa baza’a barshi ya tafi da iyalinsa ba ko dan ma sha’kuwar su ta ‘mara ‘karfi.

Aranan da ya tafi Ummah ta ‘kira Abbas akan zaman Teemah ita ka’dai agida ‘din tace masa ai be yiba tace yayi ha’kuri Teemah ai yarinya ce kar yana biye ta akan wasu abububuwan tunda yasan bazata iya ba, shi kam rufe ido yayi yace da Ummah abar ta kawai, akwai security aciki da wajen gate babu komai insha Allahu, yace Ummah ai kowa ma haka take zama agidan auren ta so ba wani sabon abu bane, Ummah taso tayi convincing ‘dinsa amma Abbas yakasa fahimtar ta dolen ta tabar shi akan ra’ayin sa kawai sai ta tura Hannah akan su zauna tare.

*****
Teemah yanzu hankalin ta a kwance yake bata da damuwar komai, duk kuwa da cewa Abbas ya hana ta zuwa ko’ina amma hakan be dame ta ba, yace ta zauna a gidan ta bai yadda taje ko wajen gate ba, suna zaman su da Hannah lafiya  domin Hannah na taya ta surutu sosai ta ‘dauke mata tunanin komai dan Hannah ba dai surutu ba, lokacin zuwa makaranta sai ta tafi, in sun gama lectures sai ta dawo gida.

Suyi fa’da suyi da’di dan Hannah akwai tsokana na fitan hankali. 

Abbas tunda yatafi yau kwanan sa biyu amma sau ‘daya tak ya ‘kira ta shi’ din ma da tunanin ta ya ishe shine ya ‘kira ta dan kawai yaji muryar ta, Teemah kuwa gaishe shi tayi tare da tambayar sa ya ya isa. 

Jiya yai muryar ta ras hankalinta akwance lokacin datake tambayar tasa bata tare da wata damuwar komai. 

Bai amsa maganar ta ta ba sai ma ya tambaye ta yace ” _wato ke bakya missing ‘dina ko_ ?
Dan ransa yakasa yin ha’kurin bata damu da rashin sa ba.

Shiru tayi masa bata yi magana ba, sai dariya datakeyi ‘kasa-‘kasa, sosai Abbas yaji haushin hakan sai ma yaga kamar farin ciki take yi daya bar ta a Abujan dan haka shima sai ya kashe ‘kiran kawai ya dafe kansa.

Teemah kam bata damu ba taci gaba da walwalar ta bata ‘kara bi ta kansa ba haka shima.

Tana waya da su Anty da Mummy harma da Daddyn ta ha kama maman Amal itama suna waya akai-akai musamman dataji cewa Teemahn tasake yin aure ma sai ta ke yawan bata shawar wari wa’dan da bazasu cutar da rayuwar kowa ba,
Anty ma kullun maganar ta kenan guda ‘daya shine ta kula da mijinta ta kula da hakkin da ke kanta, kuma ta daina rashin ji da taurin kai.

Sosai maganganun sun yake tasiri azuciyar ta musammman sai dai bata san ta yanda zata yi handling wasu abubuwan ba dan ta fahimci Yayahn 6au’da’d’de ne.

Amma data ga ya ‘kara kwana da wuni be ‘kira ta ba sai abin sai ya fara damun ta, da kanta ta fahimci bata kyauta masa ba.

Wasa-wasa kusan kwana biyar bai ‘kirata ba sai dai Hannah ce ke yawan sanar da ita cewa ai Yayah ya ‘kirata data na school kusan kullun hakan Hannah ke sanar da ita, amma idan tana gida bata ganin yana ‘kiran Hannah, kuma Hannah bata ta6a cewa da ita ya neme ta ba ko yace a gaida ta ba abin na ‘daure mata kai sosai.

Story continues below


Hannah kuwa bata san cewa basa waya ba da yake ba’a gida take wuni ba, sai dai itama daga baya tafara yiwa Teemah mitar bata ta6a ganin suna waya da Yayah ba shin basa missing juna ne ko kuma sai abayan idon ta akeyi.

Teemah “hmm” kawai ta ce da ita, dan ita kanta zuwa yanzun tafara shiga ru’du, missing ‘din sa takeyi sosai shi kansa, muryar sa, fitinar shi, touches ‘din sa da komai nasa. 

So ma take ta  ganshi gaba ‘daya dan ba ‘karamin missing ‘din sa takeyi ba, tunanin sa kullum na damun ta musamman ma idan taje bacci da dare. 

Sau tari idan ta tuna da Zahran sa takanji ba da’di har zuciyarta, inda take sai taji hankalin ta yakasa kwanciya wani sabon tsanar yarinyar take ji na tsarga mata.

Hannah ma da kanta ta fahimci Teemah ba daidai take ba a kwanakin nan dan tafiya ganin ta cikin tunani amma data ga bata sanar da ita meke faruwa ba sai itama bata tambaye ta ba.

Ranar daya cika kwana bakwai da tafiya ranar Teemah na kwance da dare takasa bacci sai juyi take yi, Hannah har ta gama waya da Bilal ta kwanta har ta ‘dan yi bacci ta farka garin yin juyi sai ta ga Teemah zaune idanun ta biyu lokacin kuwa sha ‘daya da kusan rabi na dare, batayi mamaki ba sai ma tausayin Teemahn daya kama ta.

Tashi tayi ta zauna tare da dafa Teemah tace ” _Me yafaru ne naga har yanzu idanun ki biyu, bakya jin da’di ne_ ?

Kai Teemah ta jijjiga mata tare da fa’din ” _bakomai Hannah ki kwanta abinki nima yanzu zan kwanta_ “.

Tana gama maganar sai ta juya ta kwanta ita bata so Hannah tasan matsalar data ke ciki.

Hannah kam da kallo ta bita ganin ‘karfi da yaji take ‘ko’karin 6oye damuwar ta bayan fuska da yanayin ta sun riga sun bayyana komai.

Teemah kam baya ta juya mata da tunanin zata kwanta itama, yayin da Hannah ta bi bayan nata da kallo tsawon da ‘ki’ku biyar tausayi Teemahn take bata ita musamman daya kasance auren ta biyu amma har yanzu batayi dace da samun farin cikin daya kama ta ba duk da yanzun tana mata kwa’dayin samun farin ciki da Yayahn amma tana ga hakan bazai yiwu ba dole sai ta yi nata yun’kurin kafinnan, dan duk wacce Allah ya jarabce ta da auren miji irin Yayah Abbas toh dole sai ha’kurin ta yazarce nakowa sai tayi nin kin wanda kowacce mace keyi agidan mijin ta sannan ta’kara da du’a’i saboda neman agajin mahalicci.

Duk mijin da ze nuna maka abu bai damesa ba ya nuna maka bashida matsala da komai bacin ba hakan bane aransa toh kuwa dole mace sai ta tsaya tsayin daka wurin ganin ta sai ta hankalin sa wuri guda, bako wani namiji bane wanda soyayya ke sashi bin duk abinda kike so, wanin shi ba damuwar sa bane koda kuwa yana yi miki irin son da ya  zarce nakowa ne a duniyan nan.

A hankali kamar ba zatayi maganar ba tace da Teemah ” _matsalar Yayah ne ke damun ki ko_ ?

Zaro idanu Teemah tayi tana daga kwancen sannan ta juya a hankali ta kalli Hannah bata so Hannah tasan abinda ke faruwa tsakanin su dan haka sai ta jijjiga wa Hannah kai tare da fa’din
” _ni fa bance miki haka ba Hannah plz mukwan ta dare yayi  fah!_ 

Kwafah Hannah tayi ganin yanda Teemah keso ta bin ne ta abaibai bayan kowa yagan ta a wannan yanayin yasan tana tarexda damuwa, ita kanta Hannah bataso yin shidshigi wa lamarinsu ba musamman ma daya kasance mijin Teemah ‘din wanta uwa ‘daya amma wani lokacin idan abu ya so barin hanyar da ta dace inkana da dama taro shi zai yi matu’kar amfani ko dan saboda gaba ma.
A hankali ta kuma fa’din
” _Karki maida ni shashasha mana Teemah, kin ‘dauka bansan meke tafiya bane har yanzu_ ?
_na jima da fahimtar kina tare da damuwa a gidan nan kawai 6oye_ _min kike yi shiyasa nima na ‘kyale ki, kuma nasan ba zai wuce matsalar Yayah ba hakane_ ?.

“Ah ah”
Teemah tace da sauri.
Hannah kuwa cewa tayi ” _Allah idan baki gayamin ba ina fita gobe Ummah zan samu in fa’dawa_ _nasan zata sanar da daddy kamar yanda nasan cewa Daddy ba zai yi shiru hakanan ba dole sai ya tambayi Yayah_ _kinga ai lokacin dole ki bu’di baki kiyi magana ko_ ?

Story continues below


Teemah da hanzari ta kamo hannun Hannah tace ” _dan Allah Hannah kiyi ha’kuri karki fa’dawa Ummah, Hannah yaushe_ _ma akayi auren da har irin haka zai fara faruwa ki taimake ni karki fa’da ma kowa plz_ “! 

Goshi Hannah ta ha’de irin boss din nan tace ” _sanar dani toh if dont want me to tell Ummah about it_ “

Baki Teemah ta tura gaba ” _tace ai nagaya miki bakomai tun ‘da zu_ ” 

“Kin tabbatar?
Hannah ta tambaye ta.

Kai ta daga kamar yarinya ‘karama. 

Hannah kuwa tace ” shikenan toh, ni bazan musa ki ba amma kisani babu abinda zai hanani sanar da Ummah gobe sai dai in ban tashi cikin rayayyu ba”!

Tana maganar ta juya ta kwanta. 

Teemah ri’ko ta tayi tace ” _Haba Hannah nice fah_ ! 

Da jin haushi Hannah tace ” _ai nima nice!!_ 

Shiru Teemah Teemah tayi na ‘dan lokaci sannan bayan har Hannah ta cire rai da cewa zatayi nagana ma sai taji a hankali tace 
” _Hannah laifi ne dan ina yawan tunanin Yayah?Inajin kewar sa sosai Hannah kuma gashi kinga baya ko ‘kirana nima_ _kuma tsoron ‘kiran sa nakeji dan bansan me zance da shi ba_ “

Hannah muguwa duk da haushin dataji ‘dazu amma hakan be hana ta darawa ba dataji abinda Teemah tafa’da.

Teemah kam tsayawa tayi kallon ta idanun ta na tare hawaye dan bata san dalilin dariyar ba, HANNAH sosai ta dara son ranta ganin Teemah na zubo da hawaye ne yasa ta ‘dan tsagai ta da dariyar tace ” _ashe lokacin da sauri zai zo haka_ ? _Kin manta nace miki naki son idan kika fara sai kin fini amma kika ‘ki yadda gashi nan tun ba’aje ko’ina ba abu ya bayyana kansa_ , _yanzu kam ai kin yadda cewa banyi ‘karya ba ko_ ?

Teemah shiru tayi mata sai ma tafara ‘ko’karin kwanciya dan taga alama abin dariya tazama harta regretting fa’da matan da tayi ji take badan ance magana zarar bunu bace da babu abinda sai hanata mai da maganar ta cikin ta ta rike damuwar ta ita ka’dai.

Hannah naganin ta kwanta sai ta ha’diye dariyar tata tace ” _yi ha’kuri matar Yayah tashi muyi magana plz na daina dariyar_ ” 

Teemah ‘kin kulata tayi sai Hannah ta dawo ta gabanta ta fuskanceta tare da fa’din ” _I’m serious Allah tashi kiji, nayi al’kawarin bazan sake yimiki dariya ba yanzu”_ 

A hankali Teemah ta yun ‘kura ta tashi ta zauna.
Hannah ma zamanta ta gyara da kyau sannan tace “Kin san Allah ko tun ranar da naga Yayah yayi ‘kirana awaya nayi tunanin ko dai be same ki bane shiyasa amma daga baya sai naga ya zage da ‘kirana ba gaira ba ‘dan dalili sai na fahimci akwai dalilin hakan dan ba haka muka saba da shi ba, Yayah be fiya ‘kiran layin na ba sai dai in akwai wani dalili, na fahimci bakwa waya ne kuma saboda ban ta6a ganin kunyi ba, nasan halin Yayah da zuciya akan abu koda kuwa yana son abin zai iya basarwa idan ransa ya 6aci wannan kadan ne cikin halayyar sa.
          Ni kaina banso kika ‘ki binsa ba tunda yanason hakan bazai ta6a cutar dake ba, wallahi Teemah Yayah na matu’kar son ki tun ba yau ba na fahimci hakan, ya na ‘kaunar ki da dukkan zuciyar sa irin son da be ta6a yiwa wata ‘ya mace irin sa ba a dunitan nan bama na tunanin ko agaba akwai wacce zata taro ki a zuciyar sa bansani ba ko in wani ikon Allahn ya sanya, Yayah na miki son da kowacce mace take burin mijin ta yayi mata irin wannan son, Teemah ki lura mana yanda kike yiwa Yayah abu son ranki wanda na tabbata ba ze ‘dau hakan daga wurin kowa ba koda kuwa nice danake autar ‘kanwar sa Yayah ba ze sarara min ba shiyasa ma kika ga bana farawa, sau tari ina mamakin yanda kuke rayuwar ku dashi kamar abokan gaba wani lokaci kuma na kanji kuna birge ni sosai, a hankali sai na fahimci 6oyayyan soyayyar dake tsakanin ku wanda bakowa ne yasan da shi ba, daga zuciyoyin ku sai de ko Mummy”!

Da sauri Teemah ta ‘dan bu’de idon ta akan Hannah da Mamaki, sai Hannah ta jinjina kanta tace
” _Yes… Mummy ce ka’dai tasani, lokacin auren ku ta sanar dani yanda tayi farin ciki da ha’din auren_ _naku take ce min ta jima da fahimtar son Yayah Abbas dake 6oye a zuciyar_ _ki, wanda tana ganin kamar ke kanki ma baki san dashi ba, tace damuwar ta Abbas_ _ne bata sani ba ko zai kar6i auren ko ah h, nice nan take_ _na bata tabbacin Yayah baze ‘ki ba danshi ma yana tsananin sonki_ _fiye da zaton mutun_ .  
     _Bazan 6oye miki ba Teemah duk da nasan kin fini sanin menene aure tunda kinyi shi har sau_ _biyu, amma har ga Allah kina sakaci da kulawa da mijin ki, lokuta da dama_ _nakan ji wani iri idan naga kina nuna halin ko in kula da shi, mijinki ne fah, naki ne_ _Teemah me yasa zaki ‘ki binsa bayan kinsan yana da bu’katar hakan zaman me zakiyi_ _anan ‘din tunda wanda kike zama domin sa baya nan, ba ‘da ba ba komai_ _ba me yasa kika za6i raba muhalli dashi?_ 
_idan baki kila dashi yanzu ba yaushe kike son rayuwar auren ki tayi saiti_ ? _kin fi son sai ranar da wata ta shigo tsakanin ku ko kuma yaushe_ _Teemah_ ?
_Ki duba fah duk da ransa a 6ace amma bai fasa ‘kirana dan yaji lafiyarki ba_ _ke da kanki ki duba wannan lamarin dan Allah_ ” 

Story continues below


A hankali Teemah tace
” _Ni kaina Hannah naga kuskure na kuma Allah yayah fushi yake yi dani ban san yanda zanyi ba banson fushin san_ _koka’dan_ ” 

Hannah cewa tayi
” _Nima banaso Teemah, dukkan ku ‘yan uwa nane kuma mafi soyuwa abin ‘kaunata, lokacin danaji auren ku bazan iya misalta miki_ _irin farin cikin dana shiga ba, inson ku sosai bazan ta6a son ‘daya na bar ‘daya ba har abada kamar yanda bazan so ganin ba’kin_ _cikin ‘dayan ku ba ballan tana na dukkan ku biyu_ “
_Wannan laifin kinsan naki ne ko_ ? 

Kai Teemah ta ‘daga mata, sai ta cigaba da fa’din ” _so kinga ke ya kamata ki gyara laifin, nasan Yayah ma be kyauta ba daya share ki amma kema da naki laifin me yasa da kika ga baya ko ‘kiran_ ki _baki ‘kira shi ba……._
_kinsan wani abu ne matar Yayah_ ?

Kai Teemah ta jijjiga wa Hannah alamar ” _ah ah_ ” sai Hannah tace 
” _wannan taurin kan dake kan kin nan shine ya haifar miki da girman kai, zaman aure_ _da hakan kuwa baya ta6a yiwuwa, ki sau’kar da wannan shirmen ki nutsu ki gyara auren ki ki jawo mijin ki ajiki ki kula dashi da hakkin sa, sannan_ _ki dinga ro’ka muku haske wurin mahallici, Allah_ _Teemah banaso ko da wasa inga wata ta ra6i rayuwar ku, ke kanki kinsan hanyoyin kulawa_ _da mijin ki dan nasan Anty da Mummy suna_ ‘ _ko’kari sosai akan haka ni shaida ce……._ 

” _……….Harda maman Amal ma Hannah itama tana bani shawara sosai_ “
Teemah ta tare da fadin hakan. 

Hannah jinjina kai tayi tace ” _toh kin gani ma ashe suna da yawa masu sin ganin rayuwarki  cikin farin cikin_ , _amma abinda ke kanki ne yah hana ki fahimtar cewa Abbas ‘din nan_ _dai yanzu shine rayuwar ki kuma aljannar ki, dole_ _ne ki sauke naki dan biyu bata ha’duwa kinga kece ‘karama akanshi, kafin yazama miji agare ki Yayan ki ne, kinga dole biyayya naki ne kuma ke ka’dai_ _banda shi, sai kin dage dan maza yanzu babu ruwan su tun kafin_ _yaje yayi miki kishiya awaje ba fata ba amma ki dage gaskiya”_ 

” _Hannah plz ni yanzu ya zanyi toh ki gaya min”_ Teemah ta fa’da tare da kamo hannun Hannah.

Agogo Hannah ta kalla tace ” _yanzu dare yayi may be yana bacci, amma ki daure ki ‘kira shi gobe, in kinyi sa’a zai sau’ko, sai kisan me zaki ce dashi wanda zai sanyaya_ _masa rai tunda ke ce da laifi sai ki bashi ha’kuri ki kuma kiyaye gaba”_ 

” _Bakomai insha Allahu gobe zan gwada ‘kiran sa naji”_ 
Hannah tace 
” _Toh Allah ya kaimu ya kuma daura ki akansa_ ” 

Da haka suka rufe maganar zuwa safiya.

Washe gari Hannah  na da lectures a makaranta ita ka’dai tayi break fast ‘din ta daya ke Teemah babu inda take zuwa so ba da wuri take yi ba ita, tare sukayi aiyukan da zasuyi dukka ‘dakin Abbas ne ka’dai Hannah bata taya ta gyarawa ba ita ka’dai take yin abinta, ‘karfe bakwai da rabi Hannah ta bar gidan dan 8:00 zata shiga lecture.

Teemah data gama komai tayi wanka tayi shirin ta tsab kamar me zuwa unguwa, sai ta dawo ‘dakin sa tayi dialling number ‘din sa, sai de har ta gama ringing bai ‘daga ba, sake ‘kira tayi shima still har yayi miss called be ‘daga ba.

Take ta rintse idanun ta da ‘karfi sai ga hawaye ya gangaro mata baya tayi ta kwanta, fuskarta na kallon cielling ‘din ‘dakin afili tace ” _plz Yayah na ka yafemin, ka ‘dauki wayata”!_ 

Abbas na bayi lokacin data ‘kira ‘din shiyasa be ‘daga ba ko daya fito yaga miss called ‘din kuwa sosai yayi mamaki amma sai ya ajiye wayar batare da ya ‘kirata ba.

Shi kansa yana rayuwa ne amma kewar matar shi na damunsa sosai, tunanin ta na matu’kar hana shi sukuni da walwala yayin da soyayyar ta ya tsaye masa azuciya koda yaushe tana cikin ransa. 
Abinda kullun yake fama da shi kenan tare da jin haushin rashin ta a kusa dashi, duk kuwa abin nan dayake yi mata yanayi ne dagangan duk da cewa shi kansa hakan na cutar dashi amma ya nuna mata cewa bai ji da’din ‘kin biyo shin data yi ba yasa ya daure ransa, dan yana tunanin idan hakan ya ishe ta next idan yace su taho bazata masa gardama ba koda Daddy ya nuna bai so, dan yasan ita bata fiye 6oye ‘kudurin ta ba. 

Story continues below



Teemah bata tashi a kwancen ba sai ta sake gwada ‘kiran sa da niyyan daga wannan bazata sake ba in har be ‘daga ba.

Cikin sa’a kuwa sai ya ‘daga Teemah har sai data toshe bakin ta dan farin cikin data tsinci kanta aciki.

Abbas shiru yayi yanajin yanda ta sauke ajiyan zuciya, shima sai ya lumshe ido ya kuma bu’dewa atake.

Teemah a hankali tace ” _Yayah_ ! 

” _Na’am_ ” shima ya amsa ta da shi kamar wanda akayi masa dole.

Kuka kawai Teemah ta sanya mai me tsuma zuciyan ma’abocin sauraro.

Cikin kukan ta furta ” _Yayah shine ka manta dani ka daina ‘ki rana ko_ ? 

Yace
” _Ni ban manta dake ba abubuwa ne sukayi min yawa ma shiyasa_ ” 

Da sauri tace ” _Amma Yayah ai kana ‘kiran Hannah nice ka’dai baka ‘kirana_ !” 

Dan ya takaita zancen sai yace
” _Shikenan toh zan na kiranki… owk_ ?

Shiru tayi masa tana share hawaye. 

Da yar ka’dan ‘din muryar tace ” _Yayah fushi kake yi dani ko?_ 

Sosai yanayin data yi maganar ya ratsa shi har ‘kwa’kwalwar shi amma ya basar.
Sai ma yace ” _i ll hang d call now office zan je…..see u later ummm_ “

Bata yi magana ba har ya yanke ‘kiran sai kawai tabi wayar da kallo da mamaki, lalle ta 6ata ran Yayah sosai acikin muryar sa ta fahimci hakan dan duk wasu abubuwan shi dayake yi abaya bata ta6a jin muryar sa a irin wannan yanayin ba, sai dai abinda takasa ganewa shine haka ‘din da yake yi soyayyar da Hannah tace yana yi mata ne yasa ko kuma haushin kawai ta’ki binsa?

Share hawayen ta tayi tare da tabbatar wa kanta cewa zata bishi aduk yanda yake so ‘din harta gano asalin matsayin ta awurin sa.

Abbas ma daya yanke ‘kiran sai daya jinginu da jikin kujera ya lumshe idanu baya son irin wannan na faruwa tsakanin su koka’dan amma tunda hakan take so, so be it!, shi zai daure rashin ta na tsawon lokaci ko dan ya koya mata yanda ake kewar masoyi da yanda tasirin soyayya yake a zu’kata.

Tun daga ranar Abbas yafara ‘kiran ta safe da kuma dare, amma kullum daga gaisuwa baya sake fa’da mata komai, duk da hakan Teemah najin da’di domin yafi ace baya ‘kiran gaba ‘daya, sau tari har ‘kaguwa takeyi ya ‘kirata dan kawai taji muryar sa ita hakan ma ya isheta.

Baya yi mata magana mai tsayi sai in har bu’katan hakan ya taso, farkon dogon maganar su shine ranar da ya ta6a tambayar ta cewa bai ga debit alert ko sau ‘daya har yanzu ko bata da bu’katan komai ne? 

Sai tace masa Hannah na zuwa musu shopping every week. 

Ya sake tambayar ta cewa ku’din fa sai ta bashi amsa da fa’din ” _Ummah ce ke bada ku’din idan Hannah zata_ “

Shine ranar da maganar tsakanin su tayi tsayi, na biyun sa kuma ranar da Hannah zata je saloon kuma itama Teemah tanaso tayi dan kanta cunkus take jinsa.

‘Kiran safiya da yayi mata sai ta tambaye shi zuwa saloon ‘din, ai kuwa hana ta Abbas yayi sai ma yace in har yazama dolene sai tayi ‘din toh Hannah taje ta siyo komai zai turo ayi mata agida, Teemah sosai taji haushi dan kuwa ba ‘karamin gajiya tayi da zaman gidan ba.

Sosai take so ta’dan fita amma Yayah fir ya hana ta.

Hakan kuwa akayi dan da yamman ranar wata mata tazo gidan Teemah bata san ta ba, Hannah ce dai ta gane ta dan ta ta6a zuwa gyaran gashi wurinta sau ‘daya,  sunan ta madam Mansoora, agida tayi musu komai harda Hannah ma, hatta da gyaran farce sai da tayi musu mai kyau ta kuwa yi ‘ko’kari dan su kansu sai da suka yaba da aikin nata.

Story continues below


Sai daga bayane ma da Hannah taje gida n Ummah sai suka ji labarin ashe Ummah yasa ta turo ta.

Duk abin nan dake faruwa bai sa Teemah taji haushin sa ba sai ma ‘kara ganin shi data ke sonyi ga begen sa dake yawan damun ta.

Ita kanta wani lokaci mamakin kanta takeyi, yanda ta damu sosai da rashin sa kusa da ita yanzun bata san dalilin wannan canjin ba, sosai take kewar mijin ta a yanzun sai dai bata bari ko Hannah tasan hakan ba saboda Anty tace mata komai dake tsakanin ta da mijin ta sirrine mai girma,  kar ta yarda ta ringa bari wani na sani, shiyasa ta ri’ke sirrin ta aranta.

Kullum take shiga ‘dakin sa ta share koda babu dattin komai amma bata gajiya da share shi, ta tsaftace bayi kullum ta kunna burner, anan take wuni da rana har in bacci yakama tayi abinta da dare kuwa tare da Hannah suke kwana a’dakin ta, idan gari ya waye suka kammala ayyukan su gaba ‘daya sai Hannah ta shirya ta wuce makaranta.

Teemah kuwa nan  ‘dakin san take komawa tayi baccin ta kwanta tana kallon photon sa tare da rungumar pillow a ‘kirjin ta.

Tana fitowa sai ta kulle ‘dakin ta kai key ‘din cikin drawer ‘dakin ta ta ajiye shi.

Duk weekend Hannah ke zuwa shopping idan ta dawo kuma sai ta gudu gidan Ummah ta ‘karasa yinin both saturday & sunday acan haka takeyi, amma bata kwana sai ta dawo, hakan ma Ummah bata barin taringa mitan ta baro Fateemah agida ita ka’dai.

In kuwa zata dawo Ummah sai ta ha ‘data da wani abin ta6awa na zamani ko na gargajiya tace ta kawo wa Teemah.

Su hajiya Teemah kam najin da’din hakan har sai ya zamana ma duk ranar da Hannah taje gida bata cin komai jiran ta kawai takeyi ta dawo sannan taci abinda Ummah ta ha’do ta dashi, tasan Ummah na ‘ko’kari sosai dan kamar tasan abinda ranta ke ‘dan iya bi takan rin’ka yiwa Hannah santi musamman ranar da aka kawo mata pepper soup ‘din hanta ko dambu mai ha’din isassun kayan lambu, ranar kam har rowa take yiwa Hannah ma.

Haka rayuwar ta ya kasance agidan auren ta batare da mijin ta agida ba, satinsa uku yanzu da tafiya, zuwa wannan lokacin kuwa har ma Teemah ta riga ta saba da rashin san azahiri amma sai dai damuwar datake ji aranta koka’dan be ragu ba sai ma abinda ya ‘karu musamman data ga cewa dagaske yakeyi bazai dawo Abuja dawuri ba, sau tari idan ya ‘kirata takanji kamar tayi masa mitan hakan amma sai ta danne ranta dan tafi son idan suna tare burinta ma be wuci tasan matsayin ta ba, amma a yanda tasan halin sa ma tasan idan yaga dama baze ma tsaya ya saurare ta da kyau ba dan shi bai fiya son jan magana ba.

Dramar su da Hannah kuwa sai ma abinda yayi gaba musamman da har yanzu Hannahn bata fasa ‘kiran ta da suna mrs dodo ba, yanzu kuwa sunan na 6ata ranta, sosai yake jin  haushi idan Hannah ta ‘kirashi da dodo.

Ranar da Hannah ta ishe ta kuwa ce mata tayi ” _kar ta ‘kara ‘kira mata miji da suna dodo, tace ita mijin ta ba dodo bane koma miye ne ita a hakan yafi birgeta_ “

Hannah ido ta zaro da zolaya tasake fa’din ” _iyeeh, kice abin yafi najiya bansani ba, yi ha’kuri toh matar Yayah bazan sake ba”_ 

Teemah a tsare tace da Hannah 
” _Daya fi miki_ 
_in bahaka ba kuwa in tona miki asiri awurin Ummah ince kina da 6oyayyan saurayi bata sani_ _ba_ “

Cikin ko in kula Hannah tace
” _Toh miye aciki ban kai nayi saurayin bane?_ 

” _kin kai harma kinfi, karki damu yarinya zaki gani zan baki mamaki ai_ “!

Da sauri Hannah ta dakatar da itada fa’din
” _Ah’Ah baiwar Allah abin be kai haka ba, wasa fah nake yi miki, indai mijinki ne ai nace na bar zancen sa ko, da Allah rufe wannan_ _chapter ‘din bana so Yayah yasan ina da wani saurayi dan da kaina nace masa makaranta zanyi kinga kuwa ai_ _idan yasani na 6allo ruwa_ “

Story continues below


Teemah cewa tayi
” _Sai ki kiyaye bakin ki in kina so nima na rufa miki asiri_ ” 

Hannah ma da sauri tace
” _Kwantar da hankalin ki matar Yayah wannan shi yafi komai sau’ki_ “

” _Dayafi miki_ “
Fa’din Teemah daga ‘karshe.

Murmushi kawai Hannah tayi tace 
” _ni kaina ya kulle fah Allah, wai yaushe yafara yi miki ne_ ?

Atakaice Teemah tace
” _Jiya da safe_ ! 

Hannah ma sai tace
” _Ai kuwa ba mamaki gaskiya, amma fah kin ban tausayi wallahi, abin yakama ki da ‘karfi sosai_ ?
   

Ringing ‘din da wayar ta ta ‘dauka ne ya katse musu hiran, Hannah kam naganin me ‘kiran sai tayi murmushi tare da ‘dagawa.


*****
Tun ranar da Abbas ya cika sati hu’du da tafiya be ‘kiran ta ba tun daga ranan, itama kuwa bata damu ba dan halin san yanzun tafara sabawa dashi, itama batayi tunanin ‘kiran sa ba kamar yadda bata sanar da Hannah meke faruwa ba, wasa-wasa har suka kwana biyu amma shiru ba labarin sa, ranan na ukun ne abin yafara damun ta sosai, tanaso ta ‘kira shi taji me ya faru amma sai zuciyar ta ta rabu kashi biyu, inda ‘daya ke bata ‘karfin gwiwan ta’kira shi yayin da ‘dayan ke bata shawaran ta ‘kyale shi itama, kamar yanda yayi ‘din wata’kila tana damun sa ne shiyasa.

Wannan 6angaren tunanin ne yayu tasiri azuciyar ta har ma sai ya rinjaye ta gaba ‘daya.

Bata ‘kira shin ba amma kuma sam nutsuwa ya’ki zuwa mata, haka ta wuni wata iri da ita, hatta wayar ma yau ko bi ta kanta batayi ba tsaban yanda tunani ya yawaita a brain ‘din ta, ‘dakin nasa ma yau ko bu’de shi batayi ba acikin nata ‘dakin ta wuni.

*1:13pm* 
Ta tashi tafara rage kayan jikin ta a hankali dan so takeyi ta watsa ruwa ko zata ‘dan ji dai-dai, ga mararta ma dake ‘dan mur’da mata ka’dan-ka’dan wannan karan period ‘din ta yayi mata jinkirin kwanaki dan kuwa wata har yawuce da kwanaki amma bai zo ba, jin mur’dawan da yake yi mata sama-sama ne yasa ta saka ran zuwan sa daga yanzun zuwa kowani lokaci, ga tsoron ciwon maran dayake tasan baya yi mata da wasa, sosai yake damun ta.

Tana tsayen sai taji ‘karan door bell tasan Hannah ce dan haka sai ta ‘daura hijab kawai akan skirt ‘din dake jikinta, dayake tariga ta cire riga sai bra ne ka’dai yarage asaman ta shiyasa ma tasa hijabin, a haka ta nufi ‘kofan ta bu’de batare da tunanin komai ba dan tasan bayaga Hannah bata tsammanin kowa.

Turus tayi ha’di da wani bugu da zuciyan ta yayi har sai da yasata ‘dauke wuta na ‘yan seconds kafin ta dawo dai-dai, kallon-kallo suka tsaya yiwa juna na ‘dan lokaci kowa na ayyana irin yanda yaga ‘dan uwansa ya canja, kowa ji yayi aransa babu da’di ganin duk da irin ‘kuncin da zu’katansu ke ciki amma be hana ‘dan uwansa yin wani sihirtaccen kyau da ‘kiba azahiri ba.
Teemah kam harda mamakin ganin sa ma duk suka cikata.

Abbas ne yayi gyaran murya sannan Teemah ta bashi hanya ya shigo, bata sake kallon shi ba ta tura ‘kofan ta rufe sannan ta dawo ciki itama, haka tawani ‘dauke kanta gefe tana tafiya tace dashi ” _sannu da_ _zuwa_ ” 
bata ko jira taji ya amsa ba balle tayi tunanin kar6an jakan sa talkless of welcoming nasa da  abin sha ko kuma wani abu daban ba ta wuce ciki abinta.

Abbas ma be amsa ba sai ya bita da idanu kawai, tana shigewa ‘dakin ta sai ya jijjiga kansa  tare da nufan hanyar nasa ‘dakin, amma sai ya jita akulle, beyi mamaki ba dan haka sai ya koma nata ‘dakin har yanzu da jakarsa akan kafa’dan sa.

Ga mamakin sa kuwa yana shigowa tana fa’dawa bathroom ga dukkan alamu wanka zatayi.

Jakar tasa ya sau’ke ya ajiye sannan ya zauna abakin gadon nata, he wish yasan inda ta ajiye keys ‘din da bazai tsaya jiranta  ba ‘daukan abinsa zai yi ya.

Story continues below


Zaman sa keda wuya sai kuma yakoma ya kwanta rigingine akan gadon yayiwa kansa matashi da  hannayen sa biyu dake bu’de kuma  sarke da juna, ‘kafar sa ‘daya na lan’kwashe akan ‘dayar yayin da ‘dayan ‘kafar ke tsaye yana faman jijjiga su.

Teemah tana bayi tayi zaman ta sarai tasan yana cikin ‘dakin nata amma haushin irin wannan zuwan dayayi matan yasa ta share shi duk kuwa da tasan cewa ‘dakin sa a kulle amma hakan be sa tayi tunanin tayi hanzarin fitowa ba.

11mins ya ‘dauke ta  a bayin kafin ta fito d’aure da towel ajikinta, koda ta fito ‘din ma idanun ta kansa suka fara sau’ka amma sai ta ‘dauke kanta tamkar bata ganshi ba, shirin ta ta hau yi a tsanake tayi light make up tare da zura wata doguwar riga da hijabin sallahn ta. Sam Teemah ‘dauke hankalin ta tayi daga kansa tamkar bata san cewa akwai wani abu mai rai dangin halittar mutun acikin ‘dakin ba. 

Dadduma ta ‘dauko ta shimfida ta tada sallah abinta.

Duk abin nan dake faruwa Abbas na kallon ta shima be tanka ta ba, iya gudun ruwan ta yake so yagani, ganin ta fara sallah batare da ta ko kalli inda yake ba yasa yatashi a hankali ya zauna yana kallon bayan ta dayake yana daga bayan ta ne, kamar an tsikare shi kuma sai ya mi’ke, daukan jakarsa yayi     ya juya yafice agidan ma gaba ‘daya.

Sai da ya tsaya a masallaci ya sallaci azuhur kafin ‘dan adaidaita ya sau’ke shi a ‘kofar gidan mahaifinsa.

Teemah koda tayi sallamah bata juyo da wuri ba sai data ‘dan ‘dauki lokaci tana ro’kon ubangijin ta bu’katun dake gabanta sannan ta shafa ta tashi, taji motsin fitar shi tana sallahn amma batayi zaton gidan yabari ba, tayi zaton ko parlour ya koma ne.

Tana na’de daddumar taji aranta cewa bata kyau ta ba dan haka bata 6ata lokaci ba tafito parlourn sai kuma taga empty babu kowa, da mamaki tajuya zuwa ‘dakinsa nan ma adatse yake tun rufewar ta na safe, ‘dakunan gidan duk tabi ta dudduba amma bayanan arikice ta dawo ‘dakin ta da tunanin inda ya shiga.

Wayar ta ta ‘dauka ta ta ‘kiran layin sa amma baya ‘dagawa.
Take taji komai ya tsaya mata cak.

Abbas kam ga mamakinsa gani yayi kowa dake gidan su na farin ciki da zuwan sa tun daga kan ma’aikatan gidan har mahaifiyar sa gaba ‘daya, sa6anin ita waccen yarinyar da ko kallon arzi’ki ma bai samu daga wurinta ba. 

” _Toh me ya faru ne_ ? _Me ke damunta?_ ya tambayi kansa.

Wani 6arin zuciyarsa ne yabashi amsa da fa’din ” _babu komai iskancin ta ne kawai yau ‘din ya motsa mata_ “.

Firgigi yayi lokacin daya tsinkayi muryar Ummah ya daki dodon kunnan sa da ‘dan ‘karfi, ga dukkan alamu ba farkon maganar ta kenan ba ” _Muhammad meke faruwa ne wai_ ?
Yaji ta fa’da da kulawa ganin ya shiga ‘dan guntun tunanin daya yi saurin tafiya da hankalinsa gaba ‘daya, sosai hankalin Ummah ya tashi da ganin hakan, mussamman ma da yake yanzu isowar sa bata san kuma da me yazo mata ba. 

Abbas bai bata amsar tambayar ta na farko ba sai data ‘kara maimaitawa kafin ya kauda kai tare da fa’din ” _bakomai Ummah_ “

Kafin Ummah tasake yin wata magana sai taji ‘karan wayar ta, dayake ma wayar na gefen ta shiyasa tayi hanzarin ‘dauka ta sada shi da kunnan ta.

Abbas baya yayi ya jinginu da kujera tare da ‘daga kansa sama ya lumshe idanu kamar mai tunani.

Gaisuwar da ake yi mata daga ‘dayan 6angaren ta amsa tare da fa’da’da fara’ar ta, afili zaka fahimci matsayin me ‘kiran awurin ta musamman idan kayi duba da yanda ta bada hankalinta sosai tare da 6acewan damuwar dake kan fuskar ta tashi guda.

Bayan gaisuwar sai Teemah ta tambayeta a ‘dan kunyace inda tace  ” _Ummah Yayah yazo ne_ ?

Sai da Ummah ta juya ta kalleshi kafin tayi dariya ka’dan tace da ita ” _ehh yazo, gashi nan ma agefe na, inaga anan yafara sau’ka dan na ganshi da jaka!, bakuyi waya bane_ ? 

Da sauri Teemah tace
” _Ah ‘ah Ummah na ‘kira layin sa fa baya ‘dauka bansan dalilin ba_ “

Jin hakan yasa Ummah ta kauda wayar a kunnan ta sannan ta juya ta kalle shi tace ” _ina wayar ka Abbas_ ? 

Yace
” _Tana nan Ummah_ ! 

” _Meyasa baka daukan ‘kira toh_ ?

Dagangan ya’ki ‘daga ‘kiran nata duk da yagani amma sai yace da Ummah ” _wayar na silent ne banji ba_ “

Murmushi Ummah tayi domin ta fahimci kamar wani abin ne ke faruwa a tsakanin su.

Maida wayar tayi a kunnan ta inda ta tsinkayi muryar Teemah nata fa’din ” _hello_ !
_Helloo_ !!

” _Ina jinki Fateemah_ “
Ummah ta bata amsa da kulawa. 

Teemah cigaba tayi da fa’din ” _Ummah sai dafa yazo nan dan yaga ina sallah shine yayi tafiyar sa ko ganin sa bai_ _tsaya nayi ba_ “!
Cikin shagwa6a ta kare maganar tamkar da Mummyn ta take wayar.
Sai data gama fa’din maganan kuma sai taji kunya harda rufe baki.

Ummah da mamaki ta juyo ta kalle shi jin abinda yayi, shi kuwa Abbas sai ya ‘dauke kansa ya mayar gefe tamkar baiji abinda Teemah tace ba. 

‘Karasa maganar Ummah tayi da fa’din ” _yi ha’kuri toh kinji zai dawo yanzun nan insha Allahu……._ 

Ko jira taji ‘karshen maganar ma bata yi ba ta yanke ‘kiran sanadiyyan wani nauyi da kunyan Ummah dataji ya kamata.


Ko da Ummah ta yi masa magana akan hakan sai yace mata ai yana sauri ne zai wuce Ekiti state shiyasa bai tsaya ba.

Ummah kam dalilin nasa be gamsar da ita ba koka’dan sai ma sake cewa dashi tayi 
” _Tashi dai ka koma gidan ka bana Abbas bafa nasan son kai da rashin adalci, ni ban san ranar da zaka daina wannan miskilancin ba wallahi, ace kabar yarinya_ _tsawon wata guda hakanan amma kuma ka zo ma bazaka tsaya ka ko duba lafiyar_ _ta ba sai ka wani ce kana sauri_ ? _Ko uzurin ta idara da sallah ma bazaka iya yi mata ba Muhammad? To ni ‘din daka zo gaishe ni har da zama min a’daki ‘din bamu a saurin ne?_ 

Ummah tana sababin tasa shi agaba har gaban mota jakar shi na hannun ta haka ta tisa ‘keyar sa tare da driver dan ya sau’ke shi sannan ta koma ciki.

A hankali yake tafiyar kansa a ‘kasa kamar bazai yi ba har ya isa kofar dazata shigar dashi parlourn gidan nasa, yanzun kam shigan sa kawai yayi dan ‘kofar babu lock.

Ciki-ciki yayi sallamar dan daga shi kansa babu wanda yasan yayi sallama agidan balle Teemah da can cikin bedroom take.

Teemah tana bedroom tana ‘dan murzawa fuskar ta powder a hankali, kunyar tambayar Ummah da tayi akansa gaba ‘daya yasa ga6o6in ta yin sanyi saboda jin nauyi, atamfah tasa ajikin ta mai fulawa ja riga da skirt ne sun kuwa amshi jikinta sosai.

Har ya shigo ‘dakin bata sani ba dan hankalin ta gaba ‘daya ya tafi ga tunani, duk da tasan cewa zai zo shi kamar yanda Ummah ta fa’da ‘din zai dawo amma duk da haka sai ta tsinci kanta cikin matsanciyar damuwa.

Tana gama shafa powder ‘din ta ‘dauko jambaki kenan ya shigo cikin ‘dakin bata ji shigowarsa ba ‘karan ajiye jaka kawai taji daya ajiye yana daga tsaye hakan yasa ta waigowa a ‘dan firgice tare da mi’kewa tsaye.

Kallon juna suka tsaya yi na ‘dan lokaci tsawon mintina biyu batare da kowa ya furta komai ba. 

Abbas kam gani yayi ta masa mugun kyau na fitan hankali tayi 6ul-6ul da ita he wish data ganshin ace farin ciki tayi da kuwa yau sai ya nuna mata yanda nasa farin cikin ya zarta nata, amma sa6anin hakan daya samu daga gare ta yasa sam baiji da’din hakan ba.

Yaso da bata ‘kira Ummah ba da kuwa yau ‘din nana da taga halinsa na asali, dan tafiyar sa zaiyi Ekiti ba zai dawo ba har sai ya kammala abinda ya kaishi, dan kuwa sai ta ‘kara lafiyayyan 1month koma fin hakan kafin tagan shi.

A hankali yafara takawa zuwa inda take batare da ya ‘dauke idanun sa daga kanta ba.

Teemah kam tsayawa tayi tana kallon ikon Allah sai da taga ya kusan iso ta kafin tafara ja da baya itama ganin hakan sai Abbas ya fara magana inda yace ” _wato ke duk duniya ni kadai kika  raina_ _ko_ ?

Teemah da sauri ta jijjiga masa kai alamar ” _ah ah_ ” dan yanda ta ganshin sosai yabata tsoro, ko ‘yar fara’an da take ‘dan gani akan fuskar tasa ma yau babu ita. 

Story continues below


” _Me yasa kika ‘kira_ _Ummah_ “? 

Ba ta bashi amsa ba sai kawai ta tura baki gaba tana ‘dan kallon shi da fuskar shagwa6a66u.
A ‘dan hassale yace ” _tambayar ki nake yi why did u called Ummah_ ? 

Jin kamar ransa yafara 6aci ya sa ta fa’din 
” _To ba kai bane?_ 
Tayi maganar tamkar zata yi kuka.

Shima da sauri ya sake furta ” _ni ne me? I think har gidan nan nazo kika ‘ki kulani kuma bayan na tafi ki wani ce nine da na yi me ? Tell me!_ 
Ya ‘karashe da ‘dan tsawa.

Teemah bata bashi amsa ba sai hawaye daya gangaro mata sirara.

Abbas kuwa ‘kura mata idanu yayi ka’dan sai ya ‘dago hannun sa yana kallon agogon dake ‘daure a tsintsiyar hannun.

Tahowa yafara yi zuwa inda take tsaye, Teemah kam naganin haka sai ta fara ja da baya again.
Amma da ya ‘daga ‘kafa taku biyu yayi ya cimmata, tana ganin ya iso ta sai ta juya tare da yun’kurin guje masa, sai hakan ya bashi daman cafko hannun ta ‘daya wanda yasa  dolen ta sai da ta tsaya tare da waigowa cikin firgici da rawan murya tafara bashi ha’kuri akan bazata sake ba.

Shi kuwa Abbas fuskar ta ma ya tsaya ‘karewa kallo tare da sauran sassan jikin ta ganin gaba ‘daya ta canza masa a wata ‘daya kacal da barinta.

Hannayen ta ya ha’da duka biyu ya maida su ta bayan ta ya ri’ke dan mugunta batare da damuwar komai ba yasa hannu ya zuge zip ‘din rigar ta sannan ya sake hannun.

Yana sake ta tafa’da ga’do dan shi ne a kusa da ita taci gaba da maida numfashin azaba dan sosai ri’kon daya yi mata ‘din nan ya shigeta.

Biyota gadon yayi a hankali yana ‘ko’karin 6alle mata bra, hakan yasa ta kalle shi da sauri sai ya ‘dauke kansa yayi kamar be san tana kallon sa ba yaci gaba da abinda yakeyi.

Yana 6alle mata ta kifu da cikin ta dan tasan hakan ne ka’dai zai sitirta mata jikinta.
Ba ‘karamin tsoro ya bata ba yanzun dan gaba ‘daya ya juye mata ne zuwa Abbas ‘din da ta sani tun farko.
Duk kuwa da cewa a nutse yake yi mata dukkan abubuwan amma yanda fuskar sa ke a’daure ne take ji yana bata tsoro.

” _Bashi kike so ba_ “
Taji ya fa’da yana 6alle botilan rigar sa daga tsaye. 

” _Nifa bance ba Yayah_ “
Da sauri ta bashi amsa da fa’din hakan. 

” _Ki min shiru ni_ “
Ya tare ta fa’din haka.

Koda ya cire rigar san ma dawo wa yayi sannan ya juyo da ita dan dolen ta saboda ‘karfin su ba ‘daya ba ne, sai kawai tasa hannu ta rufe ‘kirjin ta duka biyu.

Shima bai kula ta ba sai yabi hannun nata ‘daya a hankali ya ‘dora nashi akai yana shafawa slowly sannan ya ha’de musu baki.

Good 5minutes kiss ya bata sannan yafara ‘ko’karin saka hannun sa cikin nata dan sosai yake so yaji lafiyan su, abu na farko kenan dayafi ‘dauke masa hankali ajikin ta sosai yanayin boobs ‘din ta ke birgeshi balle yanzu daya ga sun wani canja masa gaba ‘daya, sosai yake jin son ta6a abinda ta rife da hannun nata, zuwa lokacin kuwa Teemah tafara yin laushi ga mamakin sa sai yaga hannunsa ya maye gurbin nata hannun cikin sau’ki batare da ta bashi wahala ba.

Cigaba yayi da murzawa a hankali yana feeling cikowan da suka yi a hannun sa sannan ya cire bakin sa a nata yabita da kallo still hannun sa nakan boobs ‘din yana murzawa, wanda har lokacin idanun ta arufe suke ba bata bu’de ba sai numfashi datake sau’kewa a hankali amma da sauri-sauri.

Wuyanta ya maida kansa ya ringa kissing ko ina yaci karo da shi har zuwa ‘kirjinta.
Idanunsa ya mayar kan boobs ‘din tare da saita bakin sa akai ya ‘dan ciza ka’dan, idanunsa akan fuskar ta sai yaga taja dogon numfashi, bakin san ya sanya ya ringa sucking mata boobs ‘din tamkar zai rabata dasu.

Story continues below


Teemah kam kuka tafara yi masa tana jan jiki sai yacire kansa a hankali ya dubeta yace ” _in bar ki ko?_ 

Da sauri ta ‘daga kanta sama alamar ” _ehh_ ” 

Sai ya juya a hankali ya kwanta a gefenta yana kallon yanda take sau’ke numfashi.

Tsawon mintina sannan da yaga ta nutsu tana yun’kurin tashi taji yace ” _ha’da min ruwan wanka kinsan bansan kan bathroom ‘din ki ba_ ” 

Yi tayi tamkar bata jishi ba dan bata nuna alamun tajin ba. 

Ganin hakan yasa Abbas ya kamo ta dayayi wani juyi sai ta koma ‘kasan sa nan take yayi mata rumfa.

” _Allah…ya…yah naji zanje in ha’da ne fa yanzu, plz ka ‘kyale ni……_ “

“Shiiii”
yatare ta dashi data yi shiru sai ya ce da ita 
” _kina so ne ai shiyasa kika ha’da ni da Ummah ta dawo dani bayan natafi yanzu kuma kina min pretend_ _as if nii ne na dame ki ko?”_ 

Da sauri ta jijjiga kanta alamar “ah ah 

” _to menene_ ?”
yasake tambayar ta 

Sai tace ” _nifah ganin kawai nake so nayi dama_ “

Bai bi ta kan maganar tata ba sai ya maida idanun sa da hankalin sa wani wurin daban yace   
” _me ya kumbura wannan_ ?” tare da nuna boobs ‘din nata da baki.

Sai lokacin ma ta tuna ashe bata rufe ba, da sauri ta kai hannun ta ta rufe kafin ta harha’do magana da in ina tace masa ” _wannan?….zanyi…lokacin period ‘dina ne yayi shiyasa_ “

” _D’auke hannun ki ingani_ “
Ya fa’da idanun sa nakai.
A tsare yayi maganar dan haka babu wani musu ta janye hannun ta a hankali.
Sai da ta ‘dauke hannun sannan ya sake fa’din ” _dama haka yake miki ne_ ?” 

Tace
” _ehh amma ba koda yaushe ba_ “

Bai sake magana ba sai kawai ya tsaya yana kallo tsawon mintina biyu sannan ya barta ya koma gefe. 

Teemah kam da sauri ta mi’ke bata tsaya neman abin rufe jiki ba kawai ta fa’da bathroom ‘din dan kar ya’kara tsaida ta.

Tana shiga ta cire kayan dake jikin ta ‘dan ‘karamin towel ne a bayin so sai ta ‘daura shi ajikinta, sannan ta ha’da masa ruwan wankan da turaruka masu ‘kamshi.

Tun ma kafin ta fito a bayin taga ya shigo da boxer ajikinsa, hakan yasa ta nemi hanyar barin ‘dakin da sauri tare da tunani aranta inda tace ” _kai Yayah zai yi abu dayawa shi bazai ‘daura ko towel ba ko kunya ta baiji haka?_ 
mtheww taja ‘karamin tsaki.

Tunanin ko bai gani bane yasa ta ‘dauki nata ‘daya duk da dai tasan zaiyi masa ka’dan amma ai yafi ace babun gaba ‘daya.
‘Kofar ta tura  batare da ta shiga ba ta mi’ka hannun ta ciki fuskanta ta waje tace masa ” _Yayah ga towel_ ” 

Kallo yabi hannun nata dashi sannan ya saki murmushi yasan manufarta nayin hakan kenan bata so yasake fito mata daga bathroom a irin yanayin daya shiga. 

Hankalinsa a kwance ya bu’di baki yace da ita
” _shigo ki mi’ko min to”_ 

‘Kafa ta buga a’kasa ta ha’de rai kamar zatayi kuka, amma dayake tanaso ya ‘daura ‘din sai ta daure ta shiga kanta a’kasa ta je kusa dashi ta ajiye batare da tayi masa kallo ‘daya mai kyau ba tana shirin juyowa yasa hannu ya jawo ta cikin abin wankan. 

Teemah agigice ta ‘dago ta kalle shi tana shirin yin magana sai yayi mata ra’da a kunnan ta yace 
” _Ke de Allah ‘yar ‘kauye ce, ni bansan lokacin da zakiyi wayo ba, Zahra tafa kullum ita ke_ _tayani wanka amma ke kin wani ha’da ruwa kin barni kinyi tafiyar ki a hakan ne kike_ _so ki ganta_ ?

Story continues below


Da ‘karfi tayi yun’kuri zata fita daga ruwan dan haushi har idanun ta na tara hawaye, sai yayi saurin maida ta yace ” _relax babe, na yau ka’dai kinji_ ?

Yanayin rungumar dayayi mata a ruwan bazai barta ta samu daman fita ba dan haka dole ta ha’kura sukayo wankan suka fito.

Amma bata daina hawaye ba, shi kuwa yana ganin ta amma bai hana ta ba sai ma murmushi daya ke yi ciki-ciki na mugunta.

Ganin ba kayan sa a nan yasa shi ‘kara neman ta da fa’din ” _bagashi ba kayan ma baki cira min ba a hakan ne kuma harda ‘kiran Ummah da mitan_ _natafi baki ganni ba bayan ba abinda nake so kike min ba_ “.

Hawayen tane ya ‘kara gudu fiye da na ‘dazu sai ta koma bakin gado ta zauna ta kauda kai gefe tana mai cigaba da sauraran sa.

Abbas kam tsayuwa ya gyara ya fuskance ta da kyau sannan yace ” _dama da kike so inzo ‘din me kika tanadar min tunda gashi inga jikinki ma hana wa kika yi sai ma kika hau kuka inajin dan_ _haka yasa kika sani na dawo ko_ ?

Shashshe’ka tafara tana murza idanu batare da tace dashi komai ba, ganin dagaske takeyi yasa shi matsowa kusa da ita ya ‘dan sassauta muryar sa ahankali yace ” _me ya faru kuma, kuka ya isheni plz ?_ 
Yayi maganar as if bai san kukan kishi da maganganun sa  take yi ba. 

Bata kula shi ba sai shine ya ‘dan sauko da muryar sa da sigar lallashi ya sake fa’din ” _shikenan to daina kukan haka nan, ‘dauko key ‘dina muje ki nema min kayan dazan saka kinga kema sai in fara cewa kina nema min kaya ko?_ 

Ya ‘karashe maganar tare da ‘dago ta tsaye, bata daina kukan ba sai dai ta daina sheshshekan illah hawaye ne yanzun, amma a hakan ta wuce ta ‘dauko key ‘din sai ya mi’ke tabishi a baya a hankali suka fita.

Koda suka isa ma guri ya bata ta bu’de ‘kofan sannan suka shiga ciki a tare wanda suna shiga Abbas ya tura ‘kofan tare da ha’da ta jikin ‘kofan yace ” _bazaki daina kukan ba_ ?
_Owk gaya min to kukan na menene, na son Yayah ne_ ?”
Sai ta jijjiga kanta gefe da gefe.
” _Ohh na missing ‘dina ne_ ? 

Sai tayi shiru ta sunkuyar da idanun ta ‘kasa bataso tayi ‘karya yanzun domin ita kanta tasan tayi missing mijinta kafin yazo tsoron kuma kar tace “ehh” ya tsokane ta tuna hakan yasa ta tayi shiru da tunanin idan tace ah ah ma duk bata tsira awajen sa ba.

Hannun sa ‘daya yasa ya ‘dago fuskar ta zuwa sama idanun ta arufe yasa ta bu’de ta sau’ke shi acikin nasa. 

Sukayi kallon kallo na ‘dan lokaci yayin da Abbas yake sake rage ‘dan tazarar dake tsakanin fuskokin nasu har suna jin tiririn numfashin juna, a hankali sai ya ce da ita ” _did u missed me?_ 
Yayi maganar ne ta yanda baya ga su biyun babu wanda zai ji abinda yafa’da   cikin wani salo na daban.

Ru’du, fargaba gami da da rikicewar datayi yasa batasan lokacin data bu’di baki ta furta ” _ye…ss_ ” a hankali ba, bakin ta ne ka’dai ya bu’du shima ‘din yagane me tace ne sanadin kusancin dake tsakanin su.

” _kina son Zahra ta ?_ ya sake tambayar ta.
Sai ta jijjiga kanta ahankali alamar ” _ah ah”_ 

” _kina son ni kuma in fi sonta_ ?
yasake tambayar ta. 

Nanma da kai tabashi amsa sai yace ” _to inbaki so in so ta zaki nayi min fiye da abinda take min kin yarda_ ?

Sai ta ‘daga kanta sama alamar “ehh ta yadda.

‘Dan tazarar dake tsakanin su ya 6atar tare da ha’de bakin su wuri guda, sosai yake kissing ‘din ta yana ‘karawa duk da bata mayar masa da martani amma yanda ta nutsu ma ka’dai ya wadatar dashi, yawo hannayen sa suke yi ajikin ta tako ina har ya dawo da bakinsa zuwa wuyan ta yana chigaba da bata lafiyayyan sa’ko mai shiga jiki, bata yi yun’kurin hanashi ba duk da tana tsoro amma yanayin da ta shigan sosai ya dilmiyar da tunanin ta, sau’kan bakin sa kan boobs ‘dinta ne yadawo da hankalinta jikinta take sai tayi baya da kanta tana sau’ke numfashi.

Story continues below


Abbas be barta ba sai daya samu yanda yake so sannan ya ‘kyale ta ganin lokaci yaja kuma gaban sa da tafiya, aranan ne kuma Teemah ta fahimci cewa ita ‘din ce dai Zahran Yayah bawata ba duk da bata cikin nutsuwar ta amma hakan be hana ta fahimtar kalaman sa ba daya ke ta sa mata albarka na yabawa da jin da’di.

Anan ta fahimci ‘dumbin son da yake mata da jimawa wanda duk hakan yafaru ne ta sanadin ha’din kan da tabashi ya biya bu’katar sa da kyau ita kanta sai data gane bambancin dake tsakanin ha’duwar su na yau da na baya musamman ma data ga bata samu matsalar komai ba, bataji zafi kamar na kwanaki ba.

Wani wankan suka shiga kowa ransa wasai babu wata damuwa sannan suka dawo suka shirya cikin kyakkyawan shiga.

Yunwa yace mata yakeji wanda ko itama yau ‘din wani mur’dan yunwa ke damunta na fitan hankali duk da ‘dazu kafin yazo taci abinci amma sai take jin tamkar bata ci komai ba zuwa yanzun.

Abincin Hannah daya rage wanda idan ta dawo zataci shine ta ‘dauko musu suka ci, Abbas har yana mamakin ta yanda yaga ta zage tana cin abincin batare da wani iskanci ba kamar yadda ta sabayi kullum, bai ta6a kallon ta cikin wannan yanayin ba sai a yau ‘din.

Agaba yasa ta da mamaki ya zuba mata idanu harma ya daina ci yatsaya kallon ta.

Ganin hakan yasa ta fara bashi tana murmushi dan tasan kallon na menene yake yi mata, ita kanta jiya zuwa yau abin na bata mamaki yanda yunwa ke saurin kamata wanda yasa dole sai taci abinci.

Kasa ha’kura yayi sai da yace da ita ” _shi kuma wannan canjin fah ko duk missing ‘din Yayah ne ya kawo shi shima? Dan_ _nasan wasu idan suna cikin damuwa in suka rasa abinyi sai su sa abinci agaba suyi ta ‘durawa inaga ma shiyasa_ _naga kin zama ‘katuwa har kika fini……next idan na dawo oyoyo na goyo ne dan ke ‘din_ _nan naga alama zuwa gaba sai de in zama ‘dan baby a wajenki”_ 

Dariya ma yabata sosai ta kuwa dara har fararen ha’koran ta na fitowa fili.

Abbas kam murmushi yayi yace ” _bawasa fa nakeyi ba, ke baki san kin fini ‘kiba yanzu ba ko”_ 

Idanunta da suka cika da hawayen dariya ta waro akanshi sannan tace  ” _ka ganka ne Yayah? Allah kamar ba kai ba inajin ko tunawa dani ma bakayi shiyasa kazama kamar ba kai ba”_ 

Cewa yayi
” _Me yasa bazan tuna dake ba ke fa matata ce dole ai na yi tunanin ki, wataran ma sai inji kamar inzo in miki bulala da kika ‘ki bina_ “

Baki ta ta6e sannan tace
” _Ca6! da na ha’da ka da daddy kuwa ya ramamin nima_ ” 

” _Nima Zahra ta zata rama min ai akanki kuma_ “

Ranta fari ‘kal tace ” _wacce kenan, Zahra matar ka ko kuma Zahran ‘karya_ ?”

‘Dan bu’de ido yayi yace ” _karya niii_ ?”

Tashi tayi tsaye da sauri dan yanda ya matso fuskar sa sanda zai yi tambayar sai ta ‘dan ji tsoro.

Tana tsayen tace ” _ai naji ka fa’da ‘dazu_ ” 

Da mamaki yace mata
” _Me nace ‘dazun kuma_ ?” 

Ido ta ‘daga sama kamar wata mai tunani tace
” _Ka….ce…..kace…._ 
In ina ta tsaya yi ta kasa fa’din abinda ke ranta sai ta tsaya tana murmushi.

” _Fa’da min mana inji_ ?”
Yayi maganar yana kallon ta.

Bazata iya maimaita masa ba saboda kunya takeji dan haka sai ta matsa zuwa bayan sa da sauri ta sa’kalo da hannayen ta a wuyan sa ta sar’ke su tare da kwantar da kanta akan kafa’dan sa tana cigaba da murmushin ta a kunne tara’da masa ” _kunya nakeji ni_ “

Murmushin kunyan iyayin nata yayi sai yace ” _rufe idon ki to zaki daina jin kunyan sai ki fa’damin naji_ “

Kai ta juya a kafa’dan sa alamar “ah ah” 

Story continues below


“Hmm” yace sannan ya tambaye ta
” _Kunyan wa kike ji anan ‘din ni ka’dai ne fa bawani ko ni ‘din kike jin kunya_ ?

” _Ummm_ “
Tace atakaice 

Sai yace ” _naji to, ni bari in fa’da miki tunda banjin kunyar ki, nace Allah Allah yayi wa matata_ _Zahra albarka ya haskaka rayuwar ta ya faranta mata kamar yanda ta_ _faranta min ko haka nace ba_ ?”
ya ‘karashe da tambaya. 

Teemah kuwa tace
” _Hakane amma ai dayawa ka fa’da ‘dazun_ “

Dagangan yace mata
” _d’azun dawani lokaci kenan ni na manta wannan ka’dai nasani……._ _oww na tuna ‘dazu lokacin da……_ “

Da sauri Teemah ta ‘dage gira sannan ta ‘daga hannu ta kai bakin sa ta rufe dan kar ya fa’da.
Ahankali bakin ta dai-dai kunnan sa tace ” _Yayah kai baka jin kunya ko_ ?

Kai ya jijjiga mata tare da fa’din ” _inaji mana amma banda na matata_ “
Hannu yasa ya dawo da ita ta gaban sa idon su cikin na juna yace ” _wato ke ana baki sa’ko ma kina tsayawa ‘diban gulma ko_ “?

Zara ido tayi tace
” _Ni kuma gulma Yayah ni banyi gulma ba_ “

Sai yace
” _Wanda kikayi yanzun fah, inba jin gulma ba ya akayi kika san abinda na fa’da duka_ ?”

Rintse ido tayi da ‘karfi tana dariya tafa’da jikinsa ta rungume shi.

Murmushi yayi shima tare da fa’din ” _silly girl_ ” sannan shima ya saka hannayen sa ya rungume ta, a kunne ya ra’da mata ” *i luv u Zahraty* ” 

Batayi magana ba sai ta ‘kara yin luf ajikinsa ji take tamkar su kasance a haka har abada, wani tsuma take jin zuciyar ta nayi game da shi, sabon yanayi ke shigan ta wanda bata bata ta6a jin irin hakan ba sai yau ‘din nan, ita da kanta tasan cewa tana so da ‘kaunar mijinta sosai fiye da yanda mafarkin ta yake bata.
Kalmar ‘daya fa’da ‘din kuwa ji take shine mafi soyuwan kalmar da tafi mararin son ji daga gare shi koda kuwa zasu dawwama ahaka ne bazata damu ba.

Abbas ma kansa wannan moment ‘din yatafi dashi he wish da ace Rivers zai koma da babu abinda zai hana shi ‘dauke matar sa su tafi, shi ka’dai yasan yanda yayi kewar ta a wata ‘dayan nan, bai ta6a zaton zaiyi missing komai nata har haka ba sai daya tsinci kansa acikin damuwa sosai da rashin ta, yarinyar ta, rashin jinta, ‘kun’kunin ta, ‘dan ‘karamin bakin ta na rashin kunyan nan, jikinta da komai nata kafin ya ya gama amincewa zuciyar sa cewa itace farin cikinsa, haushin ‘kin binsa datayi kuwa har yaso ya ninka haushin daya shiga lokacin da aka bawa marigayi ita suka tafi.

Yanzu kuwa da yake da ita a gidan sa take kuma kwance akan ‘kirjin sa sai yake jin kaf duniyan nan bayaga ahalin sa baya jin akwai abinda yakai girman matsayin ta a zuciyar sa.

*4:30pm* 
Yabar gidan domin flight ‘dinsa na zuwa Ekiti ‘karfe 5:00 ne inda suka rabu da matsananciyar kewar junan su afili da kuma zu’katan su.

5:28pm Hannah ta dawo gidan sai taga Teemah cikin annashuwa ko bata bu’di baki ta fa’da ba amma farat ‘daya zaka gane cewa yau walwalar ta na daban ne, musamman idan ta tuna kalmar I LUV U daya fizgo daga bakin sa ‘dazun hakan ka’dai ke sata sakin murmushi, jin kanta take sosai tana jin tamkar tafi kowa she feel very exiting, wai Yayah na son ta.

Hannah kam dayake bakin ta baya gani ya ‘kyale sai tace da ita ” _albishir ‘din menene ya iso ki haka da kike irin wannan walwalar_ ?”

Da sauri tace da ita ” _uwar sa ‘ido kawai……..to Yayah ne yazo yau_ “
Tayi maganar da cikakkiyar murmushi kwance akan fuskanta. 

Hannah ‘dan gwalo idanu tayi tace 
” _dan Allah?_ 
_Kice intattara in koma kunkumin uwata_ “
Hannah tayi maganar tare da mi’kewa tsaye dayake dama a parlour suka zauna.

Story continues below


Dariya ka’dan Teemah tayi tace  ” _sai ki je ‘din kuma ai, abinda har ya tafi ma_ “

” _Haba dan Allah dagaske, shi kuma kamar ana koran sa haka?_ 
Hannah tayi maganar da mamaki. 

Teemah kam hankalin ta kwance ta bata amsa da fa’din  ” _Ekiti state ya nufa dama yana kan hanya ne shine fa yabiyo ta nan ‘din”_ 

Hannah komawa tayi ta zauna da jin abinda Teemah tace, sai data zauna sannan da sigar zolaya tace ” _Yayah yazo duba amarya kenan_ ” 

Teemah cewa tayi
” _To ko laifi ne yin hakan_ ?”

” _Haba! wace ni ince haka? Ai ban isa ince laifi bane dan ban san sirrin dake 6oye bayan wannan gagarumar fara’ar_ _ba, abinda kawai nasani shine rai yasamu abinda yake so that’s all_ “
Fa’din Hannah kenan tana watsa hannu sai Teemah ma tace ” _toh ya za’ayi ne Hannah abinda yafi haka ma inajin idan_ _nayi ai ba laifi bane, mijina ne fah Hannah tsawon wata guda bangan shi ba…_ 
” _hmmm bazaki gane yanda nayi kewar sa bane yarinya_ “
Ta ‘karashe da murmushin tsokana.

Hannah ma murmushin tayi tace ” _ke kika so hakan ai, amma yanzu da kika ganshin fah_ ?

Da sauri Teemah ta tare ta fa’din ” _sai naji tamkar kar yatafi wallahi_ “

Baki Hannah ta ta6e tace ” _ehh lallai yarinya kin hau layi Yayah ya koya miki halin sa ni dai ba ruwana_ “

Dariya ma tabawa Teemah wanda cikin dariyar ta furta ” _dai-dai kenan, ai baki san wani abu ba Hannah? har fa da kyautar I LUV U na samu yau daga wurin sa_ “

Ido Hannah ta zaro tana dariya tace ” _kice dara taci gida kenan_ ?” 

Dariyan sukayi dukkan su, suka sha hannu cikin so da ‘kaunar junansu.
(TeemHan)


*****
Yanzu kam sau ‘daya yake ‘kiran ta a duk lokacin da ya samu dama wata rana kuma ma ko ‘kiran nata baya yi.

Haka kuma salon ‘kiran nashi bai canja ba sai ma abinda ya ragu dan yanzun baya fin 2-3mins kullun idan ya ‘kirata saboda abin da yake gabansa, daga gaisuwa baya jan magana ahakan ma yafi yin ‘kiran da dare wani lokaci ma  har sai tayi bacci kafin ya ‘kira da safe ne kawai take ganin missed call.

Tana kuwa jin haushi sosai idan hakan yafaru kuma ko ta ‘kira shi baya ‘dagawa har sai lokacin da ya ga dama sannan sai yayi calling nata back, daga baya ma sai ta ha’kura ta daina ‘kiran nasa gaba ‘daya.

Shikuwa Abbas rashin sakewa da ita a wayan ya samo asali ne da kasancewar Hannah na tare da ita, sam baya iya tambayar ta komai daga yaji lafiyar ta da damuwar ta shikenan dan baya so yayi wani abinda zai sa Hannah ta ringa yi masa kallon wani abu daban.

Satin sa shida (6weeks) A Ekiti yanzun amma sau ‘daya tak yabata daman zuwa gaida Ummah tun farkon tafiyar sa daga nan bai ‘kara barin taba, takan yawai ta mamakin hakan aran ta sau da dama Hannah ce ke ‘dan wayar mata da kai akan wasu abubuwan da suka shige mata duhu.

Damuwar ta ‘daya yanzun shine yanda ‘karfi da yaji ta zama chop-chop daga wayewar safiya zuwa dare tana cin abinci a’kallah kusan sau shida ko ma fi, wani lokaci har cikin dare ma yunwa na damun ta wani lokaci dole sai ta tashi ta nemi abinda zata saka abakin ta koma wani iri ne kafin take jin dai-dai.

Abin na damun ta sosai musamman ma da taga sai ‘kara huruwa takeyi tasan bakomai ne yake sata yin ‘kiban ba sai lodin data ke yawan yi acikin kwanakin nan, bata so amma dole zuciyar ta ke tilastata yawan cin abincin.

Gashi wani sa’in sai ta kasa bacci da dare sai dai tayi ta gadin Hannah har sai ta kusan raba dare kafin bacci ke ‘daukan ta.

Takan yawaita blaming sabon salon cin abincin datake yi yanzun game da komai dan aganin ta duk shine yake sata yawan baccin dama shiyasa ta tsani cin abu mai nauyi ita tun asali, Hannah na tafiya school itama take yin bacci dayake sai sun kammala dukkan ayyukan su kafin Hannah take wucewa shiyasa take iya yin baccin ganin babu wani aiki a gabanta, dan ma baccin nata baya tsayi dududu in tayi dayawa shine takai 30mins tana baccin.

Story continues below


Lokacin data lura da yanda ta ‘kara haske boobs ‘din ta ma ya ‘kara huruwa shima yawani cicciko bakin yayi ja sai abin yafara bata tsoro ma data yiwa Hannah mitan hakan sai Hannah tace ” _ki bari idan Yayah ya dawo sai ki sanar dashi in ciwo ne zai nema miki magani ai, in kuma kiwona ke da kyau kinga sai in samu kyauta da lambar yabo daga wurin sa_ “

Hannah na maida abin wasa kullum while Teemah kam abin har ranta yake damun ta.

Ranar da zai dawo ya sanar da ita da safiyar ranar bayan har Hannah ta wuce makaranta.

Ranar kuwa Teemah sam bata jin da’din jikinta sai dai bata ko sanar da Hannah ba dan kar tace bazata je school ba saboda hakan, jitake kamar anyi mata dukan tsiya a ga6o6in ta duk nayi mata ciwo.

Da ‘kyar ta samu ta shiga ‘dakin sa dan yau ‘din ko le ‘kawa batayi ba, babu ma wani ‘kura da yake kullun tana gyara shi yau ne kawai bata yi ba, amma duk da haka sai ta daure ta fara da tsabtace bathroom sannan ta dawo ‘dakin ta share ta kunna burner tare da canja bedsheet ‘din dake kan gadon ta fito ta jawo ‘dakin yana tashin dadda’dan ‘ka
mshi.

Kitchen ta shiga inda sai data samu wuri ta zauna tukunna ta ‘dan huta harda maida numfashi, zazza6i ne take jin kamar zai kamata.

Adaddadfe ta ha’da masa lafiyayyan abinci irin na hausawa wanda yaji  kayan lambu dan ita yanzu sune cimar ta bata son ganin abinci batare da veggies ba.

Juice ‘din zo6o ta ha’da masa mai ‘dan karan santi ta sashi a fridge abincin kuma ta kai su dinning, tana dafe kai dan sosai take jin ba da’di a duk ilahirin jikinta, gajiya take jin na damunta.

Koda ta koma ‘daki ma da ‘kyar ta samu ta watsa ruwa tana yi tana hutawa yau ka’dai sai data fita a hayyacin ta, shirin ta tayi cikin wata doguwar rigar atampa data kama ta sosai daga ‘kirji, ganin rigar zai takurata ne yasa ta cire ta canja da wata mai ‘dan fa’di marar nauyi maroon colour sai ya ‘kara fito da hasken ta afili.

Duk yanda take jin jikinta kuwa hakan bai hana ta neman abincin ba saboda mur’dan yunwan da cikin ta keyi mata.

Sosai ayyukan suka ja mata lokaci, tana idar da sallar la’asar tajiyo ‘karan door bell, zuwa tayi ta bu’de ‘kofan da fatan Allah yasa shine kowani  wanda zai iya taimaka mata dan tasan Hannah kam da sauran lokaci tace ma zata bi gidan Ummah kafin ta dawo so zuwan ta yanzun da ‘kyar ne.

Cikin sa’a kuwa shi’din ne, tana bu’de wa taganshi tsaye kafa’darsa rataye da jakar sa, fuskarsa ba yabo ba fallasa koda ya gantan beyi wani reaction ba sai ma ya tsaya yana mamakin canjywar ta na yanzun. 

Teemah kam gaba ‘daya sai tayi loosing control tasaki murmushi sai sannan ya maida mata martanin murmushin nata, dan farin ciki ma har bata san lokacin data fa’da jikinsa ba sai kuma tafara hawaye a tun safen da take jin ta wani iri ‘din batayi kuka ba sai yanzu da ta ganshi, a hankali ta furta ” _sannu da zuwa Yayah_ “

Abbas kam fuskar sa ba yabo ba fallasa sa6anin zuciyar sa dake cike tab da farin cikin ganin ta.

Bai amsa mata sannun data masa ba sai hannun sa ‘daya dayasa shima ya rungume ta, jikin ta babu zafi illah ‘dumi da yayi shiyasa ko’ka’dan Abbas be fahimci yanayin datake ciki ba.

Dayaji sau’kan hawayen ta a’kirjin sa ne ma sai ya ‘kara sakin murmushi, zaton shi duk kukan na ganinsa ne.

A kunnan ta ya ra’da mata ” _kin koyi rashin kunya ke ma ko? Shine harda kukan farin cikin gani Yayah_ “

Duk da yanayin datake ciki amma sai datayi murmushi ta ‘dan motsa ka ‘dan sai ya sake fa’din ” _jakata zaki kar6a nagaji sosai fah_ “

Da sauri ta tashi a ‘kirjin san tana mai sau’kar da idanun ta ‘kasa dan kar yayi saurin fahimtar halin datake ciki.

Story continues below


Kar6ar jakan tayi batare da ta kalli fuskar sa ba tana jin ta cikin wani yanayin farin ciki marar misaltuwa.
Sanyin da ga6o6in ta sukayi ma duk sai taji ya ragu batasan dalili ba.

Abbas kam ‘kura mata ido yayi da mamakin yanda take avoiding ha’da idanu dashi yau ‘din bai san dalilin ta ba amma sai yaji hakan ya birgeshi ganin kamar tafara yin wayo ne tunda har take kunyar shi.
Cikin hakan sai kuma ya fahimci kamar akwai abinda ke damunta.

Bayan ta yabi da kallo har ta shige ‘dakin sa da jakar sannan ya ‘karaso cikin parlourn inda ya yada zango akan kujera tare da ‘daga kansa sama ya lumshe idanu, yana tunanin damuwar tata ko ta mecece oho.

Wani zazzafan iska ya huro daga bakin sa take sai ajiyan zuciya ya biyo baya.

Teemah bata fito ba sai da ta ha’da masa ruwan wanka sannan ta fito inda ta same shi zaune ya jingina da jikin kujera, afili ta fahimci tsantsan gajiyan daya kwaso sai taji tausayin sa sosai dan tasan irin aikin su babu sau’ki sam.

Fridge ta wuce ta ‘dauko masa ruwa mai sanyi da cup ta zo gefen sa ta zauna wanda hakan yasa shi ya ‘dan bu’de idanu yabi jikinta da kallo.

Sai data tsiyayi ruwan sannan ta mi’ka masa, ya kuwa kar6a ya shanye, koda tayi yun’kurin ‘kara masa sai ya girgiza mata kai tare da mi’ka mata cup ‘din.

Komai cikin ‘karfin hali take yinsa dan bata so tabawa ‘dan ‘karamin zazza6in data ke ji ‘din ‘kofar da zai sanya har ya dawo mata babba balle ayi mata zancen injection, she hate it at all.

Cup ‘din ta ajiye agefe sai ta sau’ka ta tsugunna dai-dai  ‘kafafun sa tafara warware igiyar boot ‘din dake ‘kafar sa tare da socks ‘din gaba ‘daya ta cire su ta matsar gefe.

Tana jin ‘dan nauyin sa amma haka ta daure ta kama ‘kafar tasa ta dinga mammatsawa ahankali tana mi’kar da yatsun ‘daya bayan ‘daya. 

Sosai Abbas yaji da’din hakan sai ma yasake lumshe idanu yana jin tamkar karta daina yi masa.

Bata wani da’de a hakan ba ta tatashi ganin agajiye yake dole zai bu’kaci freshing up saboda ya’dan warware sai  ta dawo ta zauna inda ta tashi ‘dazu daga gefen kujera a hankali ta fara 6alle masa botilan rigar tana ‘kara sau’kar da idanun ta ‘kasa.

Abbas kam yana jin hannun ta a’kirjin sa ya bu’de idanu yana kallon kan fuskar ta zuwa idanun ta amma ta’ki bari su ha’da idanu.

Bai hana ta ba dan yanda yake jin gajiya bai ‘ki wan kan ma ta taimaka masa ba saima yake ‘kara mamakin wannan sabon sauyin dayake gani daga gareta komai ma canja masa yayi, daga ita har rayuwar ta gaba ‘daya.

Idanun sa ya lumshe ya sake yin baya da kansa Teemah kam har ta ji da’di taci gaba da 6allewan cikin natsuwa bata sani ba ashe a hakan yake ‘karewa halittar ta kallo.

Gani yayi ta ko’de sosai farin ta ya ‘karu, ga wani ‘dan ‘kiba datayi hips ‘dinta ma suka ‘kara fitowa sosai, aransa yace ” _sam bata damuwa da rashina ji yanda tayi kyau ta ‘kara ‘kiba abinta ta manta dani da rayuwata.”_ 

Har ta gama 6alle bottles ‘din yana karantar yanayin ta, sai data gama kafin tayi ‘karfin halin ‘dago idanu ta sau’ke su akan nasa sannan tace ” _Yayah saura kayi wanka ko sai kaci abinci tukunna_ ?”

Bakin ta kawai ya tsaya kallo harta gama maganar bai ko yi yun’kurin nuna alamun yaji bama balle tasaka ran samun amsar ta,  aransa yake tunanin…..how on earth zai gaji da kallon wannan yarin yar? Angel ‘dinsa, kyautar Allah, amanar sa, matar sa, kuma ‘kanwar sa, his first and last lover wacce yake fatan ta kasance uwar ‘ya’yan sa gaba ‘daya kuma ‘kar’kashin ikon sa har abada.

Acikin muryar ta ya ‘dan fahimci damuwar dake tare da ita inda ya gaskata zarginsa saboda muryar ta kansa fizo shi takeyi ta harha’da kalaman data furta masa.

Tana shirin mi’kewa yasa hannun sa ya janyo ta sai ta fa’do jikinsa, zafi taji acikin ta dan yanda ta tafi ba shiri da sauri ta yamutsa fuska sannan tace  ” _awwshhh….Ya…._ 

” _…….Tell me! Me ke damunki_ ?”
ya tare ta da fa’din hakan.

Take sai ta tura baki dan bata san me zata ce dashi yake damun ta ba. 

Turo bakin datayi ne yasa shi ya kai yatsan sa ‘daya kan bakin ya shafa slowly tare da ‘kara rage ‘dan tazaran dake tsakanin su sannan ya sake  fa’din 
” _gaya min mana inji me yake damunki ko ciwon rashin Yayah ne ya shige ki sosai haka_ ?”

Goshi ta ha’de tare da niyyan fara gunguni sai yayi saurin ‘daura bakin sa akan nata wanda hakan ya tilasta mata nutsuwa. 

Passionate kiss ya bata wanda ya matu’kar ratsa ta har cikin jikinta tare da sake matso ta zuwa jikin sa sosai.

Door bell ne ya fara ‘kara wanda yasa ta tafara mutsu-mutsun ‘kwace jikin ta, ganin hakan sai Abbas ya sake mata bakin amma be raba jikin sa da nata ba, taga kamar baida niyyan ‘kyaleta ga door bell nata bada sauti sai ta juya ta kallo 6angaren ‘kofan tare da da dawo da kallon ta gareshi duk yana kallon ta.

Bu’dan baki tayi zatayi wata maganar sai yasa ‘dan yatsan sa akan bakin nata hakan sai yasa tayi shiru tabi hannun da kallo sannan ta kuma maida kallon nata kan fuskar sa.

Sake matso da kansa yayi yabata wani peck a tsakiyan goshin ta wanda yasa ta har sai data lumshe idanu sannan yaraba jikinsa da nata sai ta mi’ke tsaye  ahankali ganin ya sake ta shima take ya mi’ke tsayen kamar yanda tayi ya nufi ‘dakinsa.

Teemah binsa tayi da kallo har ya shige sannan tasa hannu ta ‘dauki 
mayafin ta ta rufe kanta dashi ta tafi ta bu’de ‘kofan.

Tana bu’dewa Hannah tace ” _hala bacci kike yi da la’asar ‘din na ko, tun ‘dazu fah nake ta faman aikin danna bell amma shiru_ “?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *