ABBAS CHAPTER 8

ABBAS




CHAPTER 8








Zuwa yanzun satin Abbas uku agidan su Teemah inda adaidai wannan lokacin yaci kimanin rabi da quarter daga cikin hutun da ya samu na aikinsa.


Shikansa yanzun ak’age yake ya koma ya fara aikin,har ji yake zaman gidan yafara isansa dan dama bak’aramin so yake yiwa aikin nasa ba dalilin hakan ne yasa yafara k’irga ranar tafiyarsa.



*****
Mummy ce zaune akan kujera Teemah kuwa na gefenta sai zun6uro baki takeyi gaba tana guna guni k’asa-kasa, mummy kuwa ko kallon inda take ma batayi ba kanta na gefe.

Teemah data ga mummyn bata da alamun sak’k’owa sai ta k’ara risina ta had’iye miyau tare da daidaita bakinta sannan tace ” mummy dan Allah kiyi hak’uri ki barni naje mana Allah idan naje bazan dad’e acan d’in ba”
tana kawo wa nan sai zamo daga kan kujerar ta zube akan gwiwoyinta tayi kalan tausayi agaban mummyn nata, mummyn ma sai tak’i ko kallon inda take balle ta san tanayi.

“mummy please”
ta k’ara fad’i kamar zatayi kuka.

Sai a sannan mummy ta juyo ta kalleta, suna had’a idanu sai ta k’ara rausayar da kanta gefe alamar rok’o.


Sai kuwa taji mummyn tace “zan barki kije Teemah amma kuma cikin 2hours zakije ki kuma dawowa, idan kika kuskura kika wuche hakan wallahi ni da ke ne agidan”.



Wani tsallen da Teemah ta buga ta fad’a jikin mummyn har sai daya firgita ta.

Sai tace ” haba Teemah miyeh hakan kuma kin kuwa san yanda kika tsoratar dani?

Dariya Teemahn tayi sannan tace “duk murna ce kawai mummy”


“Hmm Allah ya shirya minke nikam Teemah”

“Ameen mummyna”


“Ki zauna kina min iyayi anan yarinya duk cikin lokacin ki ne ai ni babu abinda ya dameni”

Dawuri ai ta mik’e dataji abinda mummyn ta fad’a sai tace
“Banaje in dubo Habibu in fad’a mar zai kaini unguwa in bayanan kuma sai ki k’iramin shi awaya dan kar yayi nisa yamin cikas”
Kai mummyn nata ta d’aga mata alamar taji.

Har ta fara tafiya sai mummyn ta dakatar da ita da fad’in ta k’yale habibun kawai dan ita bata yadda Habibun ya kai Teemahn ba , domin tariga da tasan halin Teemahn tsab, acewar mummyn wai Teemah tariga ta raina Habibun kuma koda sun fita ba bin maganarsa zatayi ba sai dai nata.

Duk mummy tayi maganar ne Teeemah na tsaye a inda tatsaya tun sanda mummyn ta dakatar da ita.

Sai da taji k’arshen maganar mummyn kafin tafara tafiya ta dawo ta zauna a kusa da mummyn.

“Toh mummy idan bashi d’in wa zai kaini?
ta jefawa mummy tambayar.

Amsa mata mummyn tayi da fad’in ” zan rok’i Abbas ne ya kaiki kuma zai jira ki idan kin gama zai dawo dake “” kafad’a ta d’aga tana kallon mummyn alamar tak’i ita bata yadda ba.
+

“Then sai kiyi zamanki agida abinki tunda bakya son zuwa ni kinga banda problem”.
Mummyn ta fad’a tana mai nuna halin ko in kula ga zancen.

Da Teemah taga kamar mummyn nata dagaske take sai tace” Mummy kinsan mugun halin yayan kuwa, nidai kibari Habibu ya kaini dan Allah mummy”!

“Ai na riga da nagama magana nikam Teemah, inba iskanci ba da Abbas d’in da habibun miye banbancinsu wato dan kinga kin raina Habibun shiyasa kike son shi ya kaiki ko?

“a a fah mummy yah Abbas d’in ne ni kawai bana so ya kaini”

“Ai shine dai-dai ke Teemah gara yana yin maganin kin ai inkuwa ba haka sai ki zamanki agida ba lallai ba dole”

Zatayi magana mummy ta dakakar da ita da fad’in idan fah bazaki ba babu dole nace kuma nasan kinjini, ni bazan canja magana ta ba”

Ai tana jin hakan ta mik’e dan bata so tayi missing d’in zuwa wajen.

“Bari inje in shirya toh, ai da babu gara ba dad’i .

“Daya fi miki kam” mummy tace mata.

Daganan ta tashi da gudu ta nufi d’akinta da niyar shiryawa.

Tana shiga ta hau cire kayan da ke jikinta sai data ciresu gaba d’aya kafin ta nemi towel ta d’aura.

Kayan da ta cire d’inma sai ta tattare su ta ninke ta bud’e ma’ajiyar kayan wankinta ta jefa su aciki.


Tana juyowa daga wurin sai taci karo da k’adangare mai jan kai a tsakiyar d’akin. Jikinta take yafara k’yarma tafara rawan baki awurin.

Shi kuwa k’adangaren kansa asama yana wani jijjigawa alamar da warginsa ya taho

Aikuwa sai ya d’an motsa daga inda yakrn sai akayi rashin sa’a inda ya nufa d’in anan Teemah take tsaye.

Wani ihun da Teemah ta saka sai da ya firgita duk ahalin gidan gaba d’aya.

Abbas da shigowansa kenan daga masallacin sallar la’asar yana k’ok’arin shiga d’akinsa sai yajiyo ihun ta.


Fasa shiga d’akin nasa yayi ya dawo ya isa main parlourn gidan,inda shigowansa yayi dai-dai da 6acewar mummy daga parlourn itama bin bayanta yayi shima ya nufi inda yaga tabi, hanyar da zai sada mutun da d’akin Teemah sukayi.

Tana tafiya yana binta abaya batare data sani ba, isowan mummy sai yayi dai-dai da fitowan Teemah daga d’akin nata arikice sai sukayi karo da mummyn takuwa k’ank’ameta jikinta sai rawa yakeyi takasa cewa komai.


Ko fad’an damuwarta ma ta kasayi illah rintse idanunta da tayi da k’arfin gaske.

mummy duk ta shiga damuwa sai tambayarta take ta faman yi amma ko amsa d’aya bata samu ba daga Teemahn ba..


Abbas na isowa sai ya wuce d’akin nata ya shiga, anan yaga k’adangaren shima anan inda Teemah ta ganshi har yanzu bai motsa ba, sai ya tsaya kallonsa da mamakin ta inda ya shigo d’akin.

Har ya fara rarraba idanunsa a d’akin.
Ai kuwa take ya tuna da ranar dayaga windown ta a6ud’e harya mata magana akan tana rufewa.


Tunowa da yayi da hakan yasa ya d’aga kansa ya kallo 6angaren da windown yake, ga mamakinsa sai kuwa ya gansa a bud’en yauma, hatta net d’in ma ta zuge tabarshi a bud’eko miye fa’idar hakan oho.


Zuwa yayi ya bud’e wurin datake ajiye kayanta da niyar d’auko wani abinda zai kama k’adangaren dashi sai kawai ya d’auko wani farin vest d’inta ya je ya d’au k’adangaren dashi .Ta windown data bud’e d’in ya jefa k’adangaren tare da vest d’in gaba dokin yasan ya tsaji a aiki , sannan yaja ya rurrufe glass da net d’in sannan ya sake labile.

Koda ya fito su mummy basa inda ya barsun sai kawai ya wuche parlourn mummy, anan yatarar dasu dukkansu Teemah tawani shige jikin mummy kamar me shirin komawa cikinta.

Zama yazo yayi shima agefen su sai mummy tajefo masa tambayar” wai miye ad’akin ne Abbas inata tambayar ta tak’i tabani amsa tun d’azu sai rawar jiki takeyi”

Amsa ta yayi atakaice da fad’in
“K’adangare ne mummy”

Baki mummy ta kama sannan tace ikon Allah nikam garin yaya kuma ya shiga har cikin d’akinta?”

Baiyi magana ba illah d’aga idanunsa dayayi ya kalleta sai yaji ta matuk’ar bashi tausayi, musamman yanda yaga duk tayi laushi, idanunta a lumshe yake hakan yasa ya k’are mata kallon da kyau sai dai daya lura ba kayan kirki bane ajikinta sai ya kauda kansa gefe tare da korar shaid’an azuciyarsa.

Tambayar dayake so yamata ne yasa shi adole badan yaso ba ya sake kallonta ahakan ” _Fateemah_ ” ya k’ira sunanta asanyaye ta bud’e idanunta batare da ta amsa k’iran daya mata d’inba.

Sanin datayi cewa shine yak’iratan yasa ta sauk’e idanunta akansa.

“Ban ta6a cewa ki rufe windown d’akin kinnan ba? ya tambayeta

K’asa tayi da idanunta dan tasan taurin kantane yasa tak’i rufewa ba komai ba.
“Tambayarki nakeyi fah!
Da kyar ta bud’i baki tace “ehh kafad’a yayah”

” Owk ban isa inyi magana kiji bako ”
Yafad’a ad’an harzuk’e.

Jin hakan yasata jijjiga kanta alamar “a’a”.

Sai yanzun mummy takar6e maganar da fad’in “ai in juninki taurin kai ne kuwa kina tare da wahala wallahi, ashema dagangan kike barin windown kenan kuma har amiki magana amma bazaki ji ba, yanzu toh wa gari ya waya?!

Ran mummy a6ace yau tketa sababi ta inda take shigaa bata nan take sauk’a ba sai da Abbas ya ga kamar ran mummyn k’ara 6aci yake yi kafin ya fara bata hak’uri musamman daya lura akalar fad’an naso ya canja gaba d’aya.

Dan mummy duk tana masifar ne akan rashin bin maganar Abbas d’in data k’iyi ne bawai dan shigar k’adangaren d’akin ba.

Teemah kuwa tun fara fad’an mummy take zubda ruwan hawaye dan tun d’azun batayi kukan komai ba tun faruwar al’amarin sai yanzu sai hawayen yak’i tsayuwa abin sai ya zame mata biyu.

Sosai jikin Abbas yayi sanyi sai yaji ba dad’i,dan kana ganin hawayen zaka san cewa kukan daga zuciyarta yake fitowa.


Tausayinta yakeji na k’aruwa masa a zuciya sosai da sosai kuma saboda hakanne yasa yayi wa mummyn magana akan tayi hak’uri.

Sai da yaga komai yayi normal ne kafin yace Teemahn tatafi tasa kaya ajikinta aikuwa tak’i taje fir sai ma k’ara shigewa jikin mummy data keyi.

Ganin hakan yasa mummyn cewa “aww bazaki partyn bane ko kin fasa”

Sai kawai ta jijjiga kanta ” mekenan?
Mummyn tasake tambayarta dan bata fahimci takamammiyar manufar wannan amsar ba wato jijjiga kai d’in da Teemahn tayi.

Sai Teemahn ta bud’i baki tace “zani ban fasa ba mummy “

murmushi mummyn tayi kafin tace ” ai kuwa dai sarkin yawo babu fashi da yake fita unguwa neai, sai Teemahn ta sake  6oye fuskarta a jikin mummyn ita nan wai taji kunya.

“Tashi maza kije ki shirya toh inyaso sai yayankin ya kaiki”
Cewar mummy
Sai da Teemah ta tashi ta zauna kafin ta ce ” mummy toh kiraka ni “.

Duk wannan dramar Abbas na zaune yana kallonsu fuskarsa tallafe da hannayensa amma baiyi magana ba.

Mummy ce ta kalleshi wannan karon batare data  amsa maganar da Teemah tayi mata ba, sai ta dawo da kallonta ga Abbas tace masa ” kayi hak’uri dan Allah ka kaita wai zata je birthday partyn k’awarta ne a _Abbah ibrahim_kuma idan na had’ata da Habibu ba dawowa da wuri zatayi ba kasanta da rashin kunya shiyasa na keso kai ka kaita”Ai bakomai mummy taje ta shirya d’in sai tazo kawai mu wuce”

” yauwa d’an albarka ai nasan bazaka k’i ba”

Daga nan ta dawo da kallonta ga Teemah sannan tace “tashi muje toh ki shirya”

Tashi tayi tafar tagiyah sai mummy ta biyo bayanta suka wuce d’akin nata da mummy sai da aka kusan isa d’akin kafin taja ta tsaya mummyn ce ta wuce gaba tare da yin tsaki dan tasan manufar yin hakan domin duk cikin salon tsorone irin na Teemah.


Da d’ari-d’ari ta shirya suka fito daga d’akin,  mummy naganin ta sa kaya sai tayi hanyar waje itama sai ta kwaso mayafinta da takalminta tabiyo bayan mummy dagudu sai suka fito atare.

Dariya ne wannan karon yaso kwacewa Abbas ganin yanda Teemah take tafiya tana waiwayen bayanta.

Aparlourn tak’arasa shirinta sannan taje d’akin mummynta ta d’auko kayan make up d’in ta tazo ta yi kwalliyar aparlourn sannan suka fito atare da Abbas d’in bayan sunyi sallama da mummy akan cewa sai sun dawo.


Sosai Teemah tayi kyau acikin shigar datayin sai ta zama tamkar tauraruwa mai haskaka zuciyar…………(mamuda)lolz😜


Abbas har satan kallonta yakeyi tsabar yanda yaga tayi shar da ita,sai da suka hau titi taga ya nufi Gashua road sai alokacin tace masa ” yayah kawuce fah Abbah ibrahim zamu”

Ko kulata baiyi ba yaci gaba da tuk’insa……..Cikin gari ya wuce da ita shikanshi da farko baisan inda zashiba,sai da yaga ya shigo cikin garin kafin ya yanke shawarar zuwa bayan tasha.

Koda suka isa bayan tashan
guri ya samu yayi parking sannan ya bata umarnin fitowa daga motar.


Kamar bazata fitoba sai kuma taga ya k’ureta da kallo fuskarsa ba alamun walwala sai kawai ta bud’e motar ta fita bakinta kamar zai fad’i k’asa tsabar yanda ta turo shi gaba, dan ita bata san mai yake nufi da hakan ba, inda akace ya kaita daban inda kuma ya kawo ta daban, haushi ne ya sake cikata data tuno irin rok’on data tayi kafin mummy tabarta zuwa birthday party d’in sai gashi kuma wannan mutumin yakama ya yi wani guri da ita.


Tafiya kad’an suka yi sai taga ya shiga cikin wani babban shagon kayan make-up.


Dakansa ya dinga nuna abinda za’a mik’o musu While Teemah na zaune a gefe ko kallo bai isheta ba dan ita gaba d’aya zuciyar ta tatafi ne ga tuanain zai 6ata mata lokaci dan bata son ta makara zuwa birthday d’in da’ake yi na k’awartan hartana zooming d’in yanda k’awayenta zasu fara cashewa ba ita, tasan da tana da waya da yau d’innan k’ira sai ya isheta. 

Haka yayi sayayyansa kaca-kaca sannan ya jagorancesu suka fito daga shagon suka kuma shiga mota.

Atunanin Teemah daga nan gurin partyn zasu wuce dan harta fara murna amma sai taga ya d’auki wani hanya daban haka yaita zaga cikin gari kamar me neman wani abu daga k’arshe sai ya nufi hanyar gida.

Teemah tayi ta masa magana yafi sau a k’irga amma ko kallon 6angaren da take ma baiyi ba ballantana ya kulata balle har  tasamu amsar maganar da ta masa.


Sai da taga ya d’auki hanyar gidan kafin tasake masa magana akan batun birthday party d’in,  duk da bata da tabbacin zai amsata amma sai da tayi dan tasan ko bai bata amsa ba ai dai ya ji ta.

Ga mamakinta kuwa sai taji yanzun ya bata takaitacciyar amsa da ” bazaki ba” ya bata amsan ne batare da ko kallon kirki ba.


Ai tanajin haka sai ta fara bori da kuka dan harga ba k’aramin haushin fita da shi d’in nan tayi yau ba, data sani dama adaidaitan ta hau……….
data sani dama Habibu driver ne ya kaita…….
Data sani tayi shi yafi sau ak’irga.

Shikuwa koda yaga tana kukan sai bai kulata ba illah juya kan motar da yayi ya shiga u-turn ya dawo da baya,murna tafara daganin hakan atunaninta zai kai tan ne, dan daman wucewarsu unguwar su Leemah (birthday girl) kenan dataga bayada niyyar shiga shine tamasa magana dajin amasr daya bata kuwa sai tafara wannan iskancin kukan.Ganin yasake wucewa sai kawai ta yi tagumi dan zuwa yanzun tagama sawa ranta tayi missing birthday d’in kenan har ma tanaji aranta cewar ya wuceta already.

+

Hanyar Jerusalem ward ya d’auka dake gefen nursing school, sai kuma tafara tunanin toh me suka zo yi anan kuma?
Kar dai wata yarinyar kuma ya kwaso acikin unguwar nan kuma?

Kauda kai tayi gefe tare da jan tsaki aranta ta kuma fad’in mutun sai kwashe-kwashen tsiya har arn……ma bai bari ba.


YETIM care foundation (gidan marayu) taga yayi parking awurin ya fito sai da tayi kalle-kalle kafin ita ma tafito tabiyo bayansa suka shiga ciki.

Sun tarar ma ana wani programme sai basu wani dad’e ba suka fito bayan ya gaiggaisa da mutanen wurin akan sai gobe insha Allahu zai dawo.

Mota suka koma yaja ya nufi hanyar gida.

Yanzun kam da suka fito bata wani tsaya mamaki ba bud’e bakinta tayi ta tambayeshi muryarta wasai tace” yayah yaushe kasan nan wurin?

Sai da ya kalleta kafin yace “Mahmud ne ya kawo ni nima kwanaki”

“Sai ta sake cewa ” toh shi yah Mahmud d’in wa ya nuna masa ai naga shima bai san nan garin ba akace”?

“Toh sai ki jira idan yazo ki masa wannan tambayar?

Yayi maganan ne fuskarsa ba yabo ba fallasa sai ta d’an ji dad’in hakan hartaji tasamu k’arfin gwiwar sake yi masa magana, aikuwa ta kuma cewa” yayah toh ni mai yasa kak’i ka kaini inda mummy tace ka kaini d’in?”
” Banyi ra’ayi bane”
ya bata amsa a takaice.

Tura b aki tayi gaba sannan tace ” amma yayah k’awata ce fah ita seat mate d’ina kuma”

” Kice mata ni na hana ki zuwa”
Ya bata amsa lokacin dayake k’ok’arin tada mota. 

” Dan Allah ni………..
Zata sake yin magana ya dakatar da ita da fad’in
” ya isheni please kimin shiru”


Dan dolenta tayi shiru bawai dan ta gama fad’ar abinda ke ranta ba. 

Suna zuwa gida kuwa tafice daga motar da gudu tayi ciki.
Kamar anjeho ta ta fad’awa mummy ajiki tana k’ananun kuka kamar wata yarinya k’arama.

Mummyn ce tace wai nikam ke kullum bakya ganin kin k’ara girma ne Teemah?

Cikin shesh-sheka dajan magana tace…” mummy k’in kaini fah yayi ya dinga yawo dani acikin gari kamar nace masa inaso”

“dai-dai kenan maganin irinku kenan ai”

Mummyn tafad’a tare da murmushi kwance akan fuskarta.

” mummy ke kullum-kullum bazaki bi bayana ba sai shi ko?, Allah in Daddy ya dawo sai na fad’a masa nima ” 
tana gama fad’in hakan ta tashi tayi d’akinta da sauri amma sai dai me…….. tana zuwa harta shiga tafara zuge zif d’in rigarta ai sai ta tuna da k’adangaren d’azun sai kuwa tafito da gudunta ta dawo parlourn dai-dai Abbas ma ya shigo sai ya ganta aguje
“ke lafiyarki kuwa?”
ya jefa mata tambaya da mamakin irin yanda ya gantan kamar an koro ta.

Bata kulashi ba har sai da taga kanta zaune akusa da mummyn ta kafin ta d’anji dama-dama.

Abbas d’inma k’ara sowa yayi ya zauna akan kujera yana ta kallonta so yakr yaji me yakuma korota, yarinya kamar mai ta6in hankali.Mummyn nata ne tasake tambayarta the same abinda Abbas d’in ya tambaya, sai a sannan tace ” mummy k’adangare a d’akin fa kin manta?” +

“Hmm”kawai Abbas yace kuma sai a sannan ya ajiye ledojin dake rik’e a hannunsa.

Mummy kuwa masifa tafara yimata inda tace
” banason hauka ni kinga Teemah, kadangaren da aka fitar tun d’azun shine kike wannan uban gudun akansa?”Waye ya fitar dashi toh?
Teemah ta sake tambayar mummyn.
+

Mummyn ma amsa ta sake bata da fad’in ” yayanki mana”

Sai ta zaro idonta waje tare da fad’in ” yah mahmud ya dawo ne dama”?.

Dank’walinta mummy tayi dan tasan dagangan tayi tambayar sannan tace “bafa nason iskanci ya dawo d’in ne kuma bazaki ganshi ba, koshi kad’ai ne akace yayanki?”

‘Kasa tayi da kanta sai ta jiyo muryar Abbas yana fad’in ” zo ki kwashe kayan nan anan” yafad’i tare da nuna mata ledojin daya shigo dasu d’azu a hannunsa.

Dayake atsare yayi maganar sai bata wani yi iyayi ba taje ta tsugunna ta kwashe ledojin ta mik’e tsaye sannan ta kalli inda yake d’in sai suka had’a idanu, sai da ta kauda kanta kafin tace “ina zan kai kayan”

Kallonta ya tsaya yi aransa yana mamakin yanda yarinyar nan ta gama raina shi gaba d’aya ya kuma rasa dalili.

Dayake baiyi magana ba sai tayi zaton ko baiji tambayar data masan bane sai ta sake maimaitawa a karo nabiyu.

Baiyi niyar bata amsa ba dan gani yake kamar iskanci ne ke damunta baya ga haka ai tasan dai ita yayiwa siyayyar tunda da ita suka je, darajar mummy dake gurin a zaune ne yasa shi bata amsa da  ” naki ne “
(nikuwa nace oga Abbas d’in mar-yerm sai a hankali, in ba haka waya san meke cikin zuciyarka da har kake tunanin Teemah tasan cewa siyayyan ta ne kayi).😅


Tana jin haka sai ta fara tafiya batare da ta kuma cewa k’ala ba.

Haushi mummy taji da wautar Teemahn sai kawai ta k’irata amsaw tayi kafin ta dawo da baya ” baki da hankali ne Teemah?,bazaki iya bud’an bakinki kiyi godiya ba bayan mutun ya miki kyauta, bakinki ciwo yake yine? ko kuma iskanci da rashin hankalin kinne yayi k’wari”

” Kiyi hak’uri mummy daman inada niyyar yi “
Teeman tafad’a da kwa6a66an fuska

mummy kuwa tsaki kawai taja ta kauda kanta gefe dan halin Teemah gaba d’aya yafara isanta.

Ita kuwa sai ta juya ta kallo inda yake kamar baya wurin  kansa na k’asa fuskarsa na kallon wayarsa dake rik’e a hannunsa sai tace ” nagode yayah”

Ko ya nuna yasan ma da shi take bai nuna ba balle tasa ran yajita, sai ta k’ara maimaitawa ai kuwa sai taga ya d’aga waya yasa a kunnensa yafara magana cikin natsuwa kamar bashiba, jitayi ya matuk’ar birgeta ashe daman yana magana haka anatse, tsabar yanda ta tsaya kallonsa har abinda ke rik’e da hannun damanta ya fara zamewa, taroshi tayi da wuri ta daidaita rik’on ledan sannan ta d’an juyo ta kalli mummy da k’asan ido gani tayi mummyn na hararar ta.

Sai kawai tace ” mummy kinga yak’i ya kulani ko “

“Toh tsoronki yake jine Teemah da godiya ma sai an saki kafin kimasa”

sai Teemahn tace ” “toh ai shine mummy”

“Shine me?
Mummyn ta sake  tambayarta.

Amma kafin Teemahn tasake magana sai mummyn ta kuma cewa ” jeki ajiye kayan sai ki dawo kima sa godiyan kafin nan yagama wayar ma “.

Tanajin haka sai ta juya da farin ciki a zuciyarta har tana ayyana babu wanda zai sake ganin ta ma ayau kam, dan batayi niyyar yiwa mutun godiya ba ita kam tunda bata rok’i kaya agun mutun ba.

Amma sai dai me………tana fara tafiya sai ta tuno da abinda ke d’akinta.

Sai ta fasa shiga kawai ta nufi hanyar d’akin mummy 
” Karki kuskura kishigan min d’aki “
Muryar mummy tajiyo tana fad’in haka.

Kwafa tayi sannan ta karkata kanta gefe ” ayyah mummy toh ina zan kai”?
” Baki da d’aki ne ke”?cewar mummyn. Teemah ma sai tasake fad’in
” mummy toh kizo ki rakani d’akin nawa “

” karkije inhar saina rakaki”
Dajin hakan tasan mummy ba rakata zatayi ba tunda tafad’i haka sai kawai ta nufi d’akin nata tsoro fal ranta.

Koda taje bakin d’akin ahankali ta tura k’ofar sai ta mimmik’a kayan hannun nata da sauri sannan ta kuma jan k’ofar ta rufe sai ta wuce kitchen tafita ta k’ofar baya tayi zamanta awaje.

Tana zaune awurin tanata sake-saken missing birthday da tayi kusan 15mins can sai ta ga Abbas ya fita amma ganin yana d’an sauri sai ta gane cewa masallaci zashi.Mthceeeeew” taja dogon tsaki tare da banka masa harara dan a duk sanda ta kalli Abbas d’in sake tunowa take da batun birthday d’in daya hanata zuwa “mugu kawai ” ta k’ara fad’i afili..
(Ni kuwa nace kanki akeji y’an mata).😜
+

Bata tashi awurin ba sai da taga gari yad’an fara duhu kafin ta tashi ta zagaya ta shiga ta k’ofar parlour.

D’an zaman da tayi awajen sai ta manta da batun tsoron k’adangaren, dan haka tana shigowa sai ta wuce d’akinta saboda tana sauri taga tayi sallahr maghrib dan lokacin yad’an shige kad’an.

Hartayo alwala tazo tahau sallaya bata tuna ba tana cikin yin ik’ama kafin ta tuno da batun sai kawai ta daure tayi ta a’uzubillah sannn tacigaba da sallahn.

Da ikon Allah kuwa harta idar tsoron bai zo mata ba, sai data idar kafin ta juya ta kakakkali cikin d’akin sai taga babu komai, tunowa tayi da maganar yah Abbas akan window, nan ma sai taje ga windown amma sai ta ganshi arufe dad’i taji har aranta sai taji Abbas d’in ya matuk’ar birgeta.Dan tasan bazai ta6a barmata k’adangaren a cikin d’akinta ba, tunda har mummy tace ya cire toh ya cire d’in ne.
+

Dawowa tayi cikin d’akin sai caraf idonta ya sauk’a akan kayan ledan data ajiye d’azu.

Da saurinta taje ta d’auko kayan ta zauna a bakin gadonta ta cicciro su tafara dubawa.

Teemah kam dama badai son kayan make-up ba, d’azun ma da haushin k’in kaita partyn da baiyi bane yasa ta nuna halin ko inkula da kayan kamar irin bata so d’innan ne.


Zazzage su tayi gaba d’aya sai farin ciki ya cika mata zu, dan ganin man da take amfani dashi acikin kayan datayi set d’insa kuma gaba d’aya, ga wani had’ad’d’en tarkacen powder daya tafi da imaninta harda hair removal cream(shavingcream) dasu turare da sauran abubuwan amfani.

Sosai wannan siyayyan ya birgeta, domin a kayan make-up d’in daya dace amatsayinta na ‘yan mata tana amfani dashi abubuwa kad’an ne basu zo a siyayyan ba.

Haka tayi ta murna da farin ciki har taso ma ta manta haushin Abbas d’in da ta keji aranta.

Agun kayan ta shantake har aka k’ira isha’i, sai da taji ank’ira isha’i d’in kafin ta fara tattare kayan gaba d’aya.

Kan mirrorn ta taje ta jajjera su sauran kuma da bana kan mirror ba takaisu bayi ta ajiye su suma, haka ta rink’a jin kanta wata so special irin an girma d’innan.

Sai data sallaci sallar isha’i kafin ta fito ad’akin ta koma, parlour tunkan ta zauna ta d’auki remote a hannunta ta fara canja tasha sai da ta samo inda yamata kafin ta zauna ta cigaba da kallo abinta.

Anan mummy tazo ta sameta itama ta zauna suka ci gaba da kallon tare ko kuma nace surutu dan Teemah tun zaman mummy agurin data mata sannu da fitowa shikenan ta hau bata labarin kayan da Yah Abbas ya siya mata sai yaba kayan take tana k’arawa daga kaji yanda take yi d’in zaka san cewa kayan sun matuk’ar birgeta, mummy data gaji da sauraran surutun ne sai tace mata ” amma d’azu da kike yangan d’aukan kayan fah?”
Amsa tabawa mummyn da fad’in ai haushi yabani ne d’azun shiyasa”
Ta6e baki kawai mummy tayi tare da fad’in “hmm” ciki-ciki dan bata buk’atan wani bayani akan batun Teemahn saboda  tariga da tasan manufar haushin.

Sun kusan ak’alla 40mins zaune awurin kafin Teemah ta karkata kai tace ” nifah yunwa nake ji mummy”

“Je k’ira yayanki toh tun d’azu banji motsinsa bama!”mummyn tafad’i tana me daidai ta zamanta akan kujera.

Kuka kawai Teemah ta sanya wa mummyn nata, abin sai ya bawa mummyn mamaki sai kace ba ita keta zuba surutu anan kamar wata parrot ba.

Baki mummyn takama dan abin na Teemah ya fara d’aure mata kai sosai.

Sai bata takura ta ba kawai ta tashi ta koma d’akin ta ta d’auko wayarta ta dawo wajen dinning d’in tazauna sannan tayi dialling numbern sa.

Shikuwa yana can kwance shikansa bai san takamamman me ke damunsa ba har zuciyarsa, sai dai wani lokaci yakanji aduk sanda ya tuno da tafiyarsa (komawarsa wajen aiki) jiyake kamar zaiyi wani abu ne wanda ilahirin gangar jikinsa da zuciyarsa basu son hakan.Amma tunaninsa yagagara tantance masa menene matsalar ko kuma meke damunsa.

Yau d’in ma hakane yana kwance ne shiru yana tunani  amma idan da tsare shi za’ayi ace tunanin me yake yi da shikanshi bazai ce ga abinda ke sashi tunanin ba.

Ringing d’in wayarsa ne ya dawo dashi cikin natsuwarsa, dayake wayar na d’an gaba dashi kad’an so baya ganin sunan me k’iran hakan yasa koda yabar tunanin bai wani motsa ba illah ido daya tsurawa wayar kawai batare da yayi yunk’urin d’auka ba.

Haka har k’iran ya yanke wani yasake shigowa amma still bai motsa ba.

K’iran na gab da yankewa ne sannan ya mik’a hannu ya d’auko wayar, ganin sunan da ke kai ne yasa shi mik’ewa zaune da sauri sai dai yana shirin d’auka sai wayar ta kuma yankewa atake yabi bayan k’iran amma cikin rashin sa’a sai yaji ance masa ai katinsa yak’are kaf gashi kuma bata sake k’ira ba, sai kawai ya yanke shawaran zuwa can ya sameta duk dama yasan batun bazai wuce na abinci ba, amma yasan tunda har ta masa 2missed call bai d’auka ba zata iya tunanin ko ba lafiya bane shiyasa ya yanke shawara zuwa d’in.
+

Tashi yayi ya shiga bayi tukunna amma kuma koda yashiga sai ya manta da batun k’iran da mummyn ke masa, ya d’an 6ata lokaci kad’an abayi, daya fito kuma sai yayi tunanin kawai gara yayi recharging through VTU awayar tasa inyaso sai ya k’irata kawai.

Teemah kuwa wani rigimar ta saka da mummy ta ajiye wayar bayan k’iran nasan datayi, sai ta ce Teemahn ta je ta dubo shi tunda gashi ta k’ira bai d’auka ba.

Toh rigiman da Teemahn ta sanya ne yasa mummyn bata wani takurata akan sai taje dubo shin ba sai ta tsaya kallon Teemahn kawai dake ta bubbuga k’afafu tana fad’in “nikam bazani ba, Allah mummy idan naje mugunta yake min kullum idan naje”

Kuka takeyi da hawaye take fad’in hakan, da mummy taga haka sai cikin hikima ta tambayeta asalin dalilin da yasa bata son zuwa aikan domin kar arashin sani ta cigaba da tura y’arta inda bai dace da rayuwar ta ba.


(wannan haka yakamata iyaye mata su ringa yi domin haka na yawan faruwa azahiri ma, sai kaga yarinya/yaro wani lokaci yakanso yafad’i wa iyayensa damuwarsa ko kuma wani abu dai daban da shi baida ikon d’aukan mataki amma sai kuga rashin goyon bayan iyayen da kuma rashin tsayawa mu fahimci ‘ya’yanmu da kyau sai kuga abu yazo ya lalace sai daga baya kuma azo ana dana sani wanda ta kansance k’eyace bata kuma ta6a dawowa gaba, koda abun ba haka yakeba yi k’ok’ari dai ki fahimci y’ay’anki kodan gyaran kuskuren da ba’ason ma ya auku idan kuwa ya aukun matuk’ar wahalan gyara ne dashi.).


Teemahn kuwa cewa tayi 
“Mummy kullun fah cewa yake ni incinye abincin wallahi kokad’an bayaci shi, kuma kona k’oshi sai yace dole sai naci in bahaka ba wai harbeni zaiyi”

Mummy dataji haka take ta sauk’e ajiyar zuciya, sai tayi istighfari aranta akan tunanin daya d’arsu azuciyarta d’azun, wani sanyi ne taji azuciyarta tare da wani nutsuwa dan sai yanzu taji dama-dama.

Amma sai ta wani had’e rai tace “zoki wuce ki dubo min yarona ni banason shashanci”

Wani kukan tasake sanyawa tajuya da nufin zuwa duboshin kenan sai wayar mummyn yafara ringing.

Tsayuwa tayi cak dataji mummy na fad’in ” au kaine?
“Naga sabuwar number ne”
Okay ba matsala ai, amma lafiya kuwa?

toh shikenan za’a kawo d’in”
Abinda mummyn tafad’i kenan daga d’aukar wayar zuwa ajiyeta.

Hakan yasa Teemah tagane da Abbas mummy tayi wayar kenan.

Bata juyo ta kalli mummyn ba haka kuma bata cigaba da tafiyan ba sai ta sake jiyo muryar mummyn na fad’in ” zo Teemah ki had’a abincin ki kai masa kinji”

“Dawowa tayi ta wani tura baki kana ganinta kasan aiken ne bata so duba da yanayin data koma gaba d’aya ta wani canja.

Sai mummy tace mata ” wai ni da kike ta wannan abin so kike ni nakai ne ko yayah”

Sai Teemah ta jijjiga kanta ahankali alamar “a’a.

” Toh wa kike tunanin zai kai masa idan bake d’in ba?”

Sai tace ” ga baba mai gadi ko kuma ak’irashi awaya mana mummy ya dinga zuwa yanaci da kansa”

” Ai yau d’in baijin dad’i yace shiyasa”cewar mummyn.

“Ai kullum haka yake cewa mummy”

” nidai kiyi sauri “

Teemah kuwa haushi sai ya hanata yin wata magana dan tasan bawani rashin jin dad’i da yake saboda tasan halinsa yanzu tana zuwa zai fara wani bubbud’awa da iyayi dan ya ganta k’arama afad’arta, duk da yau d’in tanajin yunwa sosai amma ita ba agurinsa taso taci ba tafiso taci atare da mummy zata fi ci a nutse amma shi nashi harda na haramun yake sata taci (injita nefah amma)🤣Had’a abincin tayi ta kai masa d’akin nasa amma yau d’in sai tayi sa’a dan cewa yayi tare zasuci dashi, sai ya bata mamaki daya fad’i hakan har sai da ta d’aga kai ta kalle shi sai ya d’aga mata gira d’aya sama, aranta tace 
“dama ai nasani bawani rashin jin dad’i kawai so yake yaga nazo ya wulanka tani abanza”
+

Tare suka fara cin abincin dashi sai kawai take jinta wani iri dan abun ban barakwai ya mata saboda tunda  ya zo garin nan hakan bai ta6a faruwa atsakaninsu ba.

Dayaga ta tsaya bata ci sosai sai ya d’iba yakai mata bakinta ita kuwa batayi wani musu ba kawai ta bud’e baki ta kar6a taci.

Daganan yace mata sudinga d’iba atare dan bayaso yaga ta tsaya batare da taci abincin ba.

Ahakan kuwa har suka gama ci gaba d’aya sai ta tattaro ta dawo da plates d’in kitchen, yau d’in dai da d’an sauk’i batajita a sama ba dan yau d’in ya tayata cii bakamar na baya dayake sata ci ita kad’ai ba.



*****
Wata ranar laraba da azahar tana parlour akwance har aka idar da sallah tanaji gaba d’aya kasantuwar tana fashin sallah yasa bata tashi taje tayi ba, sai ta mik’e kawai tanufi d’akin Abbas dan tasan yana masallaci adai dai wannan lokacin. 


Ahankali ta tura k’ofar tashiga idonta baikai ga kan doguwar kujeran dake d’akinba gado kawai takalla dataga wayam shikenan dayake tariga da tasa aranta yana masallaci ne shiyasa bata wani damu da ko yana d’akin ko bayanan ba ita dai oho.

Zuwa tayi bakin gadon ta zauna can kuma sai ta tashi ta nufi gaban madubin dake d’akin,  turarensa tafara d’auka dan dama turaren ba k’aramin birgeta yake yiba musamman idan taji ya fesa ajikinta feffeshe jikinta dashi tayi itama dukka sai data fesa turatukan nasa sannan tajawo stool ta zauna sai ta buga tagumi agaban madubin tunaninta ya tsaya cak dan yanzu jitake kamar Yah Abbas kar ya tafi.

Tun shekaran jiya dataji suna maganan komawarshi da Daddynta tarasa meke damunta.

Bata so taji wai zata yi missing d’insa irin yanda tayi missing Yah mahmud dan shi Yah Abbas ba sonta yake ba, amma ga mamkinta sai taga tagagara samun natsuwa gaba d’aya.

Ko yanxun ma ita kanta bata san me yakawo ta d’akinsa ba jitayi kawai tana sha’awar shigowa d’akin.

Shikuwa yana kwance yana ta kallonta da mamakin abinda ya kawota d’akin nasa.

Dayaga hankalinta bai zo gareshi ba ne yagane cewa tayi zaton baya d’akin ne shiyasa ta shigo.

Akwance yake shima tun d’azu, duk ya rasa sukuni yana ji aka k’ira sallahn har aka idar amma bai motsa ba,for the first time yayi missing jam’i tunda ya girma ya san kansa.

Dayaji anyi sallama ne kawai ya yanke shawarar cewa zai bari kawai ya watsa ruwa idan yaso kawai sai ya fita gaba d’aya daganan sai yawuce shagon barbing amar aski da gyaran fuska.

Toh yana kwancen ne sai yaga shigowar Teemah cikin d’akin.

Ita kuwa tana zaune agaban madubin kusan mintina takwas sai kawai ta mik’e tsaye da nufin ficewa daga d’akin dan kar ya dawo ya sameta yaci k’aniyarta.

Fara tafiyan datayi kenan dayake tana rarraba idanu ad’akin sai ta hango shi kwance akan doguwar kujera tsoro yaso ya kamata amma koda taga kamar yana bacci ne sai ta dake ta wani tsaya k’arewa fuskarsa kallo.

Gani tayi yayi mata kyau sosai a yanda yake d’in,take sai tunanin waccen yarinyan yazo ranta wato _Muhibbat_ take sai taji ranta ya 6aci atunaninta itama taga kyan nan dayayi sai ta fara d’aga k’afanta ahankali-ahankali harta tsinci kanta tsaye gaban kujerar dayake kwancen.

Tsayinta ta rage tayi k’asa ta tsugunna daidai yanda kujerar take.

Cigaba tayi da kallonsa sai taji kamar tasashi acikin jaka kar ya tafi yabarta amma tasan inah no way.

Har ta d’ago hannu zata kai kan fuskar tasa sai kuma take fuskar muhibbat ya bayyana mata a idanu dai-dai sanda tafito daga gida ranar daska je dashi d’innan,  fuskar _Muhibbat_ d’in k’unshe da murmushi har ana hango wushiryarta, tuna hakan ne yasata ta maida hannun nata k’asa dan wani sabon 6acin rai ne taji ya lullu6eta.

Take ta mik’e kamar an bata umarni bata kuma tsaya wata-wata ba ta fice daga d’akin ta nufo nata d’akin.

Sai da yaga ta kafin ya bud’e idonsa yabi k’ofar data fitan da kallo.
+

Mamakinta yaji dan duk abinda ta aikata yana kallonta itace kawai tayi zaton bacci yake, abinda yake zuciyarta ne kawai bai sanda shi ba sai kuma yanda yaga tafita d’akin da zafi-zafi da kuma had’e rai wannan ma bai san manufarsu ba.


Idansa kawai ya bud’e bayan ya gama tunanin kuma yasake kulle su baiyi zaton zata dawo ba amma cikin ikon Allah kwata-kwata bai san dalilin daya sa yagagara motsi ba dan koda d’an yatsansa bai motsa ba murmushi kawai yayi sai ya sake maida idanun ya kulle su.

Cikin haka ne yaji an sake bud’e d’akin an shigo bai wani damu yasan wanda yashigo d’in ba dan baya raba d’ayan biyu itace tashigo jin babu alamun sallama daga bakin mai shigowar.

Ita kuwa kansa tazo ta tsaya hannunta rik’e da robar hair removal cream.


K’asa ta maida idanunta daga gefensa ta k’asa.Tunani takeyi a zuciyarta dan gani take wannan abin da take shirin aikatawan kamar ba dai-dai bane.

Shikuwa hakan da tayinne yabashi chance d’in ganin abinda ke rik’e ahannunta batare da tasan yana kallont ba.

Ahankali ya maida idanunsa ya lumshe bai bari ta lura da bud’e idanun dayayi d’in ba.Tayi tsayuwan mintina yakai hud’u tana tunanin tayi abinda zuciyarta ke raya mata ne ko kuma kartayi.

Kawai sai ta yanke shawarar data ga yafi kwanciya mata azuci……musamman idan ta tuno irin muguntar daya ke yimata da masifah ga kuma _Muhibbat_data mata karan tsaye itama azuci.

Sai take ganin ai idan bahaka tayi masa ba bazata rama abinda yake mata ba.

Dawo da kallonta tayi kan fuskarsa sai taga har yanzu baccinsa yakeyi bai ma san tana tsaye akansa ba.

Kamar wata mai hankali haka ta tsugunna agabansa ahankali idonta na kansa tafara matso mai d’in, koda ta matso sai ta tsaya kallon hannun nata, jin wani kuzari tayi yazo mata farat d’aya ai kuwa batare da wani dogon tunani ba tafara shafa masa man afuskarsa gaba d’aya duk gurbin data ga akwai gashi (beard) sai da tabi tashafa shi.

Shikuwa mamaki ne yaci kasa dayaji abinda take yi masa a fuskarsa, saboda ko lokacin daya ga abin rik’e  a hannunta baiyi tunanin shine target d’inta akan abin ba.

Sosai yayi mamakin hali irin na Teemahn da ko da wasa bai ta6a tunanin rigimarta har ta kai haka ba.

Sai yanayin rashin tsoro da kuma k’warin gwiwarta akan abu yaji ya birgesa, duk dama ga dukkan alamu kafin ta aikata hakan sai da tayi d’an nazari akai, duba da yadda tayi tsaye akansa batare da wani dalili ba hakan yana nuni ne da cewa tana jin tsoro, amma still tsoron bai hanata aikata abinda zuciyarta tariga ta sak’a mata ba.

Teemah kuwa harda cije baki sanda take shafawan dan ita a tunaninta idan ta gama shafawa sai tayi tafiyarta ta barshi so ko ya tashi daga baccin ba zaiyi tunanin ita ce ta aikata masa ba.

Sake matso manli d’in kuwa tayi dayawa ahannunta tafara shafawa amma tana cikin shafawan sai taga ya bud’e idanunsa ras akanta, ” yah subhanallah” tace ahankali garin janye hannayenta cikin gaggawa kuma sai ta d’an goche hannun ya shafu a goshinsa, dayake bawani gashi mai yawa bane akannasa sai mai d’in yayi saurin ratsawa har k’asan gashin.

Sa ke lumshe idanu yayi yace ” yah salam” dan ya riga yasan ba k’ara min aika-aika tayi masa yau d’in nan ba.

Da sauri ta mik’e tsaye zata gudu shima kuma kamar yasan hakan zai faru sai ya sake bud’e idanunsa sai ko ya ga tana shirin guduwa,sai ya mik’e da sauri ko taku hud’u batayi ba taji anrik’o hannubtaShikuwa mamaki ne yaci kasa dayaji abinda take yi masa a fuskarsa, saboda ko lokacin daya ga abin rik’e  a hannunta baiyi tunanin shine target d’inta akan abin ba.

Sosai yayi mamaki hali irin na Teemahn da ko da wasa bai ta6a tunanin rigimarta har ta kai haka ba.

Sai yanayin rashin tsoro da kuma k’warin gwiwarta akan abu yaji ya birgesa, duk dama ga dukkan alamu kafin ta aikata hakan sai da tayi d’an nazari akai, duba da yadda tayi tsaye akansa batare da wani dalili ba, amma still bata ji tsoron yi masa abinda zuciyarta tariga ta sak’a mata ba.

Ita kuwa harda cije baki sanda take shafawan dan ita a tunaninta idan ta gama shafawa sai tayi tafiyarta ta barshi so ko ya tashi daga baccin ba zaiyi tunanin ita ce ta aikata masa ba.

STORY CONTINUES BELOW

Sake matsowa tayi dayawa kuwa tafara shafawa amma tana cikin shafawan sai taga ya bud’e idanunsa ras akanta, ” yah subhanallah” tace ahankali garin janye hannayenta cikin gaggawa kuma sai ta d’an goche hannun ya shafu a goshinsa daya bawani gashi mai yawa bane akai d’in sai mai d’in yayi saurin ratsawa har k’asan gashin.

Sa ke lumshe idanu yayi yace ” yah salam”.

Da sauri ta mik’e tsaye zata gudu shima kuma kamar yasan hakan zai faru sai ya sake bud’e idanunsa sai ko ya ga tana shirin guduwa, sai ya mik’e da sauri ko taku hud’u batayi ba taji ya rik’o hannunta d’aya, okda ta gwada ja kuwa sai tajita k’yam dan dolenta ta waigo ta kalle shi, suna had’a idanu sai tayi k’asa da kanta.

Shikuwa jan hannun tan daya kama yayi batare da yayi magana ba yajata zuwa gaban madubi suka tsaya awurin, kallon kansa yayi acikin mirror d’in sai ya maida idansa kanta, gani yai idanunta na kallon k’asa a hankali ya k’ira sunanta ” _Fateemah_”.

Ciki-ciki ta amsa da ” na’am” batare da ta d’ago ta kalleshi ba dan tasan yau d’innan mai raba su sai Allah, ita sam bataso yatashi yanzun ba taso sai bayan tagama abinda zatayi tatafi kafin ya tashi amma sai ya 6ata mata plan yatashi da wuri. +

” D’ago ki kalleni”
Ta sake jiyo muryar shi yafad’i haka.

Amma sai ta gagara aikata yanda yake so d’in sai ma ta k’ara yin k’asa da idanunta.

Cikin tsawa ya sake cewa ” nace ki d’aga kanki ki kalle ni ko!”

Take jikinta yafara 6ari cikin idanunta yafara tara hawaye.

Tsura mata ido yayi yana kallonta batare da ya sake magana ba itanma a hankali tafara d’ago idanunta yayin da ruwan dake cikin idanun suke k’ara yawaita.

Da farko lokacindata fara d’ago kai d’in idonta a bud’e yake amma data ga tana gab da d’agowa gaba d’aya sai tayi saurin rintse idanun take kuwa hawayen daya taru a gurbin idanun ya gangaro zirr ya jik’a kumatun ta…..ahakan ta k’ara sa d’agowa takuma k’i bud’e idanun nata.

Tsayawa yai yana kallonta da kyau, a kullum gani yake yarinyar na k’ara yin kyau ne tafiya take da imaninsa da kuma tunaninsa gaba d’aya.

Kusan mintina uku babu wanda yayi magana a tsakaninsu illah jikin Teemah dake ta faman 6ari dan yau tasan tashigo hannu sai yanda Allah yai da ita abanza ma yaya balle ta aikata laifin azahiri.

Ganin yanda jikinta ke karkarwa ne yasashi murmushi aransa yace ” halin yarinyar nan sai ita, ga uban tsoro ga kuma fitina da neman magana”.

Sai kuma yaji ta bashi tausayi sosai sai ya tsurawa crying face d’in nata idanunsa shima na tsawon sakanni bai d’auke idanun san daga kallon fuskarta ta ba yace ” open ur eyes”! Atsare yayi maganar amma bada zafi ba.

Duk da tana son bud’ewan amma sai ta gagara bud’ewa saboda tsoron yanayinsa dazata gani takeyi, shikuwa da ya ga bata da alamun bud’ewa sai ya sake maimaita mata ” I said open ur eyes Fateemah”
Wannan karan ma asanyaye yayi maganar.

Ita kuwa jin yana yi mata magana da muryar rahama sa6anin yanda ta zata da farko sai hakan yasa ta jin d’an sanyi-sanyi sai ta bud’e idanun kamar yanda ya buk’ace dayi.

Cak idanun nata suka sauk’a a cikin nasa tana niyyar sauk’e nata idan ne yayi saurin dakatar da ita da d’an k’arfi…” don’t try it!”

Dan dolenta itama ta bar idanun tan akan san duk da yanda take jin bugun zuciyah aduk lokacin data had’a ido dashi, amma haka ta daure batare data so ba.

Tambaya taji ya jefa mata amma sam ta kasa bashi amsar tambayar tashi saboda kwata-kwata ita bata ma san me zata ce dashi ba koda ta bud’i bakinta.

Sai tayi shiru kawai tana rarraba idanu, ganin tayi shirun shikuwa sai ya sake maimaita mata tambayar kamar yanda ya fad’i da farko batare daya canja ko kalma d’aya ba ” me yasa kika shafa min nace”!

Wannan karon ma a nutse yayi tambayar sai hakan da yayi yasa taji kusan 40% daga cikin tsoron data ke ji d’in ya kau.

In-ina tafara sai yayi saurin dakatar da ita da jijjiga kansa.

Hannu ya sa ya kamo fuskarta ya d’ago saitin fuskarsa suna kallon juna ” then tell me now” Ya sake fad’i.

Ita kuwa sai tak’i magana sai ta sake jin jikinta wani iri tsoronsa ya k’ara kamata ga kuma bugun zuciyarta dake k’ara yawaita, zuwa yanzun koda tace zata yi masa magana toh bata san me zata ce masa ba domin bakinta kansa yayi mata nauyi.

Da yaga bazata yi masa magana ba sai ruwan hawayen ta dake matuk’ar ta6a masa zuciya,  sai ya sake mata fuskarta ta ya mik’e tsaye singlet d’in dake jikin sa kad’ai ya cire sai ya dawo inda take ya kama hannunta ya fara tafiya da ita.

Bata yi turjiya ba tunda tasan itace da laifi sai kawai tabisa.

Shikuwa bayi ya nufa da ita,koda taga yana niyyar shigar da ita bayin ne sai ta d’an turje, juyo yayi ya bata wani dirty look take kawai ta d’aga kaf’afu tabishi.Shahada tayi ta bishin duk da bata san mai zai biyo baya ba sai kawai ta rink’a addu’a azuciyarata akan cewa Allah ya ubangiji ya d’ora ta akansa Allah ya ku6utar da ita.

Suna shiga bayin yayi zamansa akan wani stool da ke ajiye musamman acikin bayin.Sai yace mata ” bismillah k’arasa aikinki”.

Bata gane mai yake nufi ba amma dana haka sai taja tayi tasaye tana wasa da yatsun hannunta.

Tsawon mintina sai yakuma fad’in “banaso idan ina ma mutun magana ana shareni ki kula sannan kuma warning naki na k’arshe kenan”

Haryanzu bata fahimci mai yake nufi da bismillan ba amma tsab ta fahimci warning d’in daya mata kawai dai bata san mai zata yi ba ita.

Shi da kansa ya fahimci bata gane manufarshi ba sai yace mata ” ni nace miki ina buk’atar aski ne ko shaving?”

Sai ta jijjiga kanta alamar ” a’a”

” Ni nace ki shafa min mai jikina?”

Nan ma jijjiga kanta tayi.

” Ni sa’anki ne agidan nan?”

Harta fara jijjiga kai sai taji ya daka mata tsawa inda yace open your mouth and talk to me or are u deaf?” 

Da sauri tace ” umm-umm”
Dan gani tayi take ya juye mata tamkar mayak’i idanunsa taga sunyi jajir.

” Raini ne kenan yasaki yimin haka ko?”

Da rawar murya ta ce ” ah….’ahh….. yayah….. dan…..dan girman Allah kayi hak’uri.

Bai sake yi mata mata magana ba kawai ya sa hannu ya matso da ita kusa dashi ya d’aga mata fuskar sai da da lumshe idanu kafin ya furta ” clear it”………

Dan dolenta tasa hannu ta kunna tap sannan tafara wanke masa fuskar tasa duk inda cream d’in ya ta6a sai da tabi ta wanke tas.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *