ABBAS
CHAPTER 9
Tana k’arasa wankewa sai ta d’age hannunta daga fuskar tasa shima daidai sai ya bud’e idanunsa ya sauk’e su akan madubi, tacikin mirror d’in suka had’a idanu ai kuwa tana ganin yanda yakoma sai taji dariya yakamata.
Hannunta ta d’ago ta rufe bakinta dashi wani shape da goshinsa yacire ne yasa takasa rik’e dariyar tata sai ta juya kawai da gudu tabar bayin.
Bata zame ko’ina ba sai a d’akinta tana shiga kuwa ta tura k’ofar ta danna lock.
Dariya tayi taci abinta harda rik’e ciki.
Abbas kansa shima dariyar taso kamashi amma sai kawai ya maidata murmushi ya k’yale dariyar, haka ya k’urawa mirrorn idanu yana kallon kansa yanda Teemahn ta sauya mar kamanni, ita kawai yake hangowa lokacin da ta ke shafa masa cream d’in gani yake kamar yanzu ta ke yi masa hakan, sai kawai ya lumshe idanunsa bai dad’e ba ya kuma bud’esu.
Tunanin yanda zai je agyara masa kan nasa ne yafad’o masa, take sai yaji ba dad’i jiyayi ransa na so ya 6aci akan hakan, amma sai ya danne 6acin ran nasa, taimako d’aya Allah ya mata dan dama he is about to leave kuma dole kafin ya tafin sai yayi aski, amma badan hakan ba yace ” hmm”
kawai sai da yakai hannu ya na shafa kannasa kafin yace ” yayarinyar nan ta gama raina ni wallahi dole inkoya miki hankali”.
Tashi yayi yafara rage kayan jikinsa dayake daman bai cire su ba d’azun.
Sai da yayi wanka kafin ya fito daga bayin d’aure da towel yana tsane ruwan dake jikinsa.
Shiri yayi dolensa cikin captan mint green yasa hula ya daidaita ta da kyau ta rufe gurbin kannasa sannan ya fice daga gidan ya nufi barbing saloon d’in dayafi kwanta masa arai domin a gyara masa 6arnar da Teemahn tayi masa.
*****
Teemah ce kwance ad’akinta akan gado sai kwasar dariya take harda hawaye, ko tayi niyyan bari amma sai taji sabuwar dariya na k’ara zuwa mata seconds-seconds take sake jin wata dariya na kamata, cikin dariyar take fad’in ” kad’anma kagani ai tunda dai ni kace zaka sa agaba kam sai dai mu zuba mu gani”.
Juyi tayi ta kifu agadon sai tunanin yanda suka kwashe da Leemah yazo mata a washegarin ranar daya hanata zuwa birthday.
Har kusan fad’a suka so yi da ita dan tagama saka ran Teemahn zata je sai kuma taga shiru ga shi kuma babu waya a hannun Teemah balle tak’irata sai hak’an ya k’ona ran Leemah sosai.
Haushin mitan da Leemah ke wa Teemah ne aranar ya had’u da haushin da yah Abbas ya k’unsa mata sai kawai ta fara yiwa Leemahn masifah toh dayake Leemahn itama ba baya bace wurin magana sai suka dinga yi atsakaninsu da k’yar suka yi shiru sai da Fauzee(class representative d’insu) tace zata had’a su da Uncle d’insu (Uncle Hasheem) kafin sukayi shiru dayake suna jin tsoronsa sosai.
Har kuwa kusan kwana uku sukayi basuyin magana da junansu kafin daga baya suka zo siluka shirya kowa ya huce.
Shiyasa ko yanzun data masa hakan kokad’an batayi dana sani ba acewarta tunda itama yana had’ata fa’da da mutane gara ta rama.
Wunin ranar kuwa kaf d’insa acikin d’akinta tak’arasa shi dan k’in sake fitowa waje tayi dan ma kar su had’u da shi yaci k’aniyarta ko kuma ya had’ata da mummy.
Batama san ya fita agidan ba dan hatta islamiyah ma yau k’in kulawa tayi da al’amarinsa, Mummy cema data ga shirun yayi yawa ga kuma lokacin islamiya har ya wuce bata ga gilmawarta ba shine tazo ta bubbuga mata k’ofar, amma sai tak’i bud’ewa tace da mummyn wai kanta naciwo ne sosai shiyasa bata fito ba tanaso tayi bacci ne.
Mummyn dataji haka sai tace mata “toh Allah ya sauwak’a” sai kawai ta juya ta koma d’akinta.
8:02 pm
Abbas bai dawo gidan ba sai da dare yana shigowa kuwa yawuto parlourn domin ya gaida mummy kasancewar tun gaisuwan safe da yayi wa mummyn basu kuma k’ara had’uwa da ita ba.
Yana gab da shiga parlourn sai wayarsa tafara ringing, dakatawa yayi da tafiyar sannan yaciro wayar ya duba mai k’iran nasa Saleem ne abokinsa wanda sukayi course tare dashi sai ya tsaya awurin yayi receiving k’iran.
Teemah na daga cikin parlourn suna zaune da Mummy sai taji ringing d’in wayarsa daga waje aikuwa ta wani razana hatta mummy sai data tsorata da yanda tayi d’in, da gudu ta tashi tayi d’aki batare da ko mummy tayiwa magana ba.
+
Abin ya d’aure kan mummy sosai yau Teemahn na yin wani abu kamar marar gaskiya ta kasa gane inda gakan kuma ya dosa, ko d’azaun da k’yar tasamu tafito bayan sallar maghrib sai da mummyn ta kusan 6ata ranta kafin tafito daga d’akin ahkan ma tana wani d’ar-d’ar da kalle-kallen gefe.
Shikuwa d’an dakali yasamu aga hanyar shigowan parlourn ya jingina sannan yasamu damar amsa wayar da kyau saboda wata gajiya yake ji sosai.
Duk magana ce sukayi da Saleem d’in akan komawarsu wurin aiki dake k ‘ara k’aratowa, bayan sun kammala da wayar ne ya dawo ya shiga cikin parlourn da sallama abakinsa.
Mummyn ce ta amsa masa sallamar ta sa dan tuni Teemah kam ta ware d’akinta.
Sai da suka gaisa kafin mummy take tambayarsa ko akwai abinda ya had’a au da Teema ne dan ta lura da ita kamar tana d’ari-d’ari da shi.
Shi kuwa bai 6oye mata ba ya sanar da ita abinda Teemahn tayi masa yau d’in kaf bai 6oye mata komai ba.
Salati mummyn tasanya da jin abinda Teemahn tayi fad’a tafara bayan ta kammala da salatin kamar ta ari baki.
Daga k’arshe kuma sai fad’an yadawo kan Abbas d’in shima dan acewarta shi yajawo har hakan ya faru ai tana lura da shi bata ta6a ganin ya hukunta Teemahn ba duk da irin iskancin data ke masa”.
Shiru yayi yan jinta sai da ta dasa aya kafin yafara bata hak’uri dak’yar kuwa ta hak’ura bayan ta hak’uran ne yasake rokon ta akan karta yiwa Teemahn komai dan Allah ta bar shi da ita zaiyi maganinta kafin yawuche.
‘Kin kulashi tayi kawai ta kauda kanta gefe hakan ne yasa Abbas yagane ba k’aramin 6aci ran mummy yayi ba da jin maganar nan.
Har sai yaji yana dana sanin sanar matan da yayi ma.
Hira yafar kawo mata sama kamar yadda ya saba saboda shi daman kalaman bakinsa kad’an ne.
Mummy kuwa daga ” uhmm ko ehh “
Bata k’ara wani abu akai saboda tagama fahimtar shi so yake abin yawuce dan yaga ranta ya 6aci shi adole ya kauda zancen.
Haka yayita d’an surutunsa yagama dayaga ba response mai kyau sai ya yi mata sallama ya wuce d’akinsa.
Washe gari da safe……………Washe gari da safe da ya tashi sai yayi shirinsa da wuri ya fito, har kuwa lokacin daya fito d’in Teemah bata fito ba, gashi lokaci yad’anja dayake bahaka tasaba ba duk da bai fiya yawan fitowa a irin wannan lokacin ba amma dai yasan Teemahn bata fiya makara zuwa makaranta ba.
Har zai basar kuma sai ya waske kawai ya wuce d’akinnata da niyyar tada ita, sau uku yana yana buga k’ofar amma shiru ba’a kulasa ba ganin hakan yasa kawai ya tura k’ofar yashiga ko sallamar ma bai yi ba.
Kwance ak’asa ya tadda ita tana ciccije baki tare da mammatse cikinta duk ta had’a gumi ga kuma robar ruwa ajiye agefenta.
Da sauri ya k’arasa inda take ya tsugunna ” lafiya kuwa” ya fad’a yana tatta6a jikinta daga fuskarta zuwa hannunta da niyyar jin temperaturen ta, azatonshi ma zazza6i ne amma sai yaji jikin normal sai dai d’umi babu wani abu.
” meke damunki ne wai” yasake
tambayarta jin bata amsa masa tambayar farkon ba.
Ita kuwa Teemah dukda tana d’anjin ciwon kad’an-kad’an amma sai hakan bai hanata jin dad’in har cikin zuciyarta da jin muryar Abbas d’in cikin rahama akusa da ita duk da tana tsoron hukuncin da zai mata amma tasan tana cikin wannan halin bazai ta6a yi mata mugunta ba dan duk abinsa yana da tausayi, balle yanda taga yake tambayarta cikin kulawa da k’yar ne ma idan bai manta abinda yafaru d’in ba.
Yunk’uri tayi kamar zata tashi sai yayi saurin tareta ya zaunar da ita da kyau, ” ina……kwana yayah” ta fad’a idanunta na k’asa da d’an in ina saboda cikin yad’an sake murd’a mata ga kuma tsoronsa data keji.
Atakaice ya amsa mata da ” lafiya ” sannan ya k’ara da fad’in ” wai me yasame ki ne Fateemah”
” cikina ne yake ciwo, amma nasha magani yafara raguwa ma ciwon yanzu”Teemahn ce tafad’i haka
Shikuwa tsayawa yayi yana kallonta sanda take kan maganar sai da ta dasa aya kafin ya sake cewa ” wani magani kika sha”?
” ibuprofen” tabashi amsa.
” tun yaushe yafara miki ciwon”
” bayan an idar da sallah ne”.
Yariga yagane meke damunta tunda shi ma atleast yayi zaman class koba komai yasan amfanin shan ibuprofen musamman ma ita da nata period d’in baya mata da wasa amma hakan bai sa ya fasa k’udurinsa akanta ba daya d’aukarwa kansa al’kawari.
Kallonta yasakeyi dakyau sai yaga tayi wata fayau da ita tamkar wacce ke jinyar satikai.
” me kuke yi a makaranta yanzu.”
Ya tambayeta.
” test ” itama tabashi amsa atakaice da irin sigar da ya mata tambayar dashi.
” toh yaza’ayi kenan, zaki iya zuwane?”
Kai ta d’aga masa alamar ” ehh”
sai yace “okay hanzarta ki watsa ruwa sai in sauk’e ki inyaso inkin rubuta Test d’in sai mu dawo gida Toh” tace tare da fara yunk’urin mik’ewa sai ya sa hannu ya da’agota suka mik’e tare
sannan yasaketa.
Bayi ta nufah da niyyar yowan wankan, shikuma sai ya tsaya yabita da kallo sai yanzu ma yake ganin yanayin kayan dake jikinta ashe ma na bacci ne shi duk bai kula ba.
Juyawa yayi ya fita daga d’akin nata yana mai korar shaid’an azuciyarsa.
Yasamu mummy na shirin shiga d’aki itama ganin sa yasa ta dakata suka gaisa anan yake ce mata ai cikin Teemah na ciwo amma wai tasha magani……..
Taran bakinsa tayi tunkan ya dasa aya tace ” Allah ya sauwak’a mata, makarantar fah ko bazata ba”, a yatsine tayi maganar kamar bata so shid’inma yagane tun 6acin ran jiya ne bai barta shiyasa take hakan ga dukkan alamu ranta ya 6aci sosai da Teemahn, sai kawai ya bata amsa yace mata ” a’a zataje tana shiryawa ne”.
Tana jin hakan ta juya abinta ta wuce ciki.
Dakansa yau ya had’a mata tea tun kafin ta fito daga wankan,sugar d’an dai-dai yasaka mata aciki saboda condition d’in datake ciki.
Itama Teemahn dawuri tayi wankan ganin lokaci yad’an ja sai ta yi shirin nata da gaggawa tafito dayake ma tadaina jin ciwon marar sai dai kad’an-kad’an shiyasa tayi komai da kuzarinta.
Bak’aramin dad’i yaji ba dayaga ta fito normal kamar ba ita ba sai kawai yace ” zonan ki yi breakfast mu wuce karkiyi latti ”
Ahankali ta taho ga dinning d’in danji tayi banbarak’wai dayake bahaka Yah Abbas d’in yasabar mata ba, tsakaninsu sai dai kallo, kallonma sai ranar daya ga dama sannan take samu, a kullum miskilanci agurinsa shine gaba da komai, Daddy da mummy ne kad’ai bata ganin yana musu hakan.
Haka yasata agaba yace tasha Tea d’in sosai, tana kur6a taji salam sai ta d’aga kai ta kalle shi had’a idanu skuayi dashike shima d’in ita yasa agaba da kallo.
“Ba sugar aciki”
tafad’a tana kallon gefen fuskarsa.
” ahakan zaki sha ai, ke baki san illar sugar agareki ba ko?
Tsoron masifarsa yasa tadinga kur6a tana kuma danna bread a bakinta kamar wasa sai gashi tasha mai yawa dan cup d’in daya had’a mata gaba d’aya ta shanye shi.
Dire cup d’in tayi bayan tashanye d’in sai ya kalleta yana murmushi yace ” iyehhh, irin yau anyi abin kirkin nan”.
Maganar tasa sai ya sata dariyah shima dayaga tana dariyar sai ya tayata suka yi tare gaba d’aya yau ya canja mata kamar ba yah Abbas d’in data sani ba, zata iya cewa yau ce rana ta farko data ta6a ganin dariyarsa tun zuwansa gidan nan, take sai tata dariyar ta tsaya sanadiyyar tunanin data shiga.
Ita data ke tsammanin mummunan hukunci daga wurinsa sai kuma akasin hakan ya faru, bata ta6a zaton yah Abbas zai yafe mata laifin sata masa da wuri haka ba amma ga mamakinta sai ya sauya hakan da wani sabon salon annashuwa da farin cikin da bazata ta6a mantawa dashi ba.
Idonta k’ur akansa amma sam hankalinta ba’a kansa yake ba, sau d’aya ya mata magana da yaga bata amsa ba sai kawai shima ya yi shiru ya k’ura mata nasa idanun yasan bai wuci mamakin sauyin data gani tattare dashi take yi ba wanda yasan dole ne daman tayi wannan tunanin,bama ita kad’ai ba duk wanda yasanshi idan yaganshi yanzun sai yayi mamakin sauyawarsa.
Sai dai shikuma kokad’an baya so ta samu chance d’in da zata yi tunani akan hakan har sai ya bar garin tukunna dan haka sai ya d’ago hannunsa yaja kumatun ta tare da jijjigawa, ai kuwa sai ta dawo daga tunanin tare d’an firgicin tsoro bayyane a cikin k’wayar idanunta dayake daman bata gama sake jiki dashi ba har yanzu, amma ganinsa da smiling face yana kallonta sai ta saki ajiyan zuciya slowly, ” kin manta zakiyi Test a school ko?, tashi kije ki gaida mummy sharp-sharp kizo muwuce”.Asanyaye ta tashi tsaye tana duban fuskansa afakaice shikuma alokacin agogon dake d’aure a tsintsiyar hannunsa yake dubawa amma duk da haka sai yace ” kiyi sauri kije nace kuma kin wani tsaya anan kina kallona!
Fuskarsa sake take aduk lokacin da zai kalle ta ko zai furta mata wata magana shikansa jin kansa yake wani iri daya ke bahaka ya saba ba amma wannan d’in aganinsa dolensa ne yayi mata hakan kodan ya yi maganinta saboda rashin jinta.
Bata fi 3mins agun mummyn ba ta fito da d’aurarren fuska, tana fitowa kuwa shima ya mik’e tsaye ya iso gareta dan ganin dayayi bata da walwala
” ya akayi ne “
ya tambayeta bayan ya tsare gabanta wanda dan dolenta hakan ya dakatar da ita daga cigaba a tafiyan datakeyi.
” ba mummy bace ta min masifa…….
” me kika mata “
Ya jeho mata tambaya tunkafin tak’arasa fad’in abinda tayi niyyar fad’a.
” Nima bansani ba”
Tabashi amsa ashagwa6e sai baiyi magana ba kawai ya juya yafara tafiya sannan yace “oyah hurry up muje kiyi test d’in idan mun dawo sai ki bata hak’uri.
Bin bayansa tayi itama batare da ta yi wata magana ba.
Shikuwa bai tsaya ko’ina ba sai wajen parking sai da ya bud’e motar ya shiga kafin ma ta k’araso itama ta shiga.
Ahanya ne yayi tajan ta da hira yana tsokanarta har sai dayaga ta sake gaba d’aya kafin ya kyaleta.
Koda yakaita makarantar ma dakansa yakama hannunta ya isa har office d’in shugaban makarantar yayi masa bayani tare da neman alfarma akan cewa bata jin dad’ine kuma tace zasu yi test shiyasa ya kawo ta so idan sun gama test d’in yana so ya wuce da ita clinic a dubata.
Principal d’in ne ya tambayeta sunan malamin da zaiyi musu test d’in tagaya masa, sai kawai yak’ira shi awaya ya tambayeshi lokacin dazai yi test d’in sai yace masa nan da 30mins ne.
Bayani yayi wa Abbas d’in daganan suka fito atare gaba d’ayansu sai Abbas yayi musu sallama akan cewa Teeman taje class ta jira lokacin yayi inyaso idan sun gama sai tasame shi amota.
Daga k’arshe suka yi musabiha da principal d’in yakoma office Abbas kuma ya tafi ga motar sa yayinda Teemah ta wuce class.
Tana zuwa ma bata dad’e ba akazo akayi musu test d’in
alokacin kusan 11:00am tayi, ko da suka gama sai class rep d’in su (Fauzee) da wata friend d’insu suka rakota har wajen motar.
Abbas kuwa hankalinsa naga wayarsa bai ga tahowarsu ba har sai da Teemah ta k’wank’wasa masa glass kafin ya ankara dasu.
Ahankali ya sauk’e glass d’in yana murmushi yace ” lil sis yadai ko har kun gama test d’in?”
Kai kawai ta d’aga masa alamar “ehh”.
” Shiga mu wuce “
Yace da ita.
Su Fauzee kam tun da ya sauk’e glass d’in suka k’ura masa idanu suna k’are masa kallo dan sosai yatafi da imaninsu.
Jin da Teemah tayi shiru bataji sun gaishe shi ba gashi har yana cewa tashiga su tafi sai ta d’an waiga ta kallo su gani tayi dukkansu suna kallonsa take sai ta ji ranta ya 6aci da hakan sai ta juya shima ta kalli 6angaren dayake taga nashi yanayin, cikin sa’a sai taga shi d’in bai masan suna yi ba dan hankalin sa ma sam baije ga inda suke ba.
Sai da ta bud’e marfin motan kafin takuma kallonsu tace musu “toh Fauzee nikam na wuce sai gobenku”.
D’agowa fauzeen tayi ta kalli Teemahn sai ta kuma maida kallonta ga Abbas d’in tare da fad’in ” ina kwana Yayah”
‘Dago kai yayi ya kalle su dan shi harga Allah bai kula dasu awajen ba, sai lokacin da yaji Teemhn na musu sallama kuma ko a sannan bai zaci suna tsaye agurinba atunaninsa wucewa sukayi.Lafiya ya school ” ya amsa mata dashi.
+
Ga mamakin Teemah sai taga
ya amsa mata wasai bawani d’aure-d’auren fuska kamar yadda yasaba fitowa a asalin millitary force d’insa ba.
Sai d’ayan k’awartasu mai suna Ameena itama ta gaisheshin kamar yadda Fauzee tayi abin mamaki bayan amsa gaisuwar harda tsokanar su yayi akan test d’in da suka yi wai ina de basu yi satan amsa ba” yanda ya sake musu fuska sai suma take suka sake dashi yayinda suka bashi amsa da fad’in ” haba dai ai an girma anwuche wurin yanzu mun girmi satan amsa”
“Ohh daa anyi kenan” yafad’i da d’an zaro idanu waje.
Sai suka d’anyi dariya su Fauzeen
Shikuwa cewa yayi
” toh Allah yasa dai hakan ne”, bari mu wuce kunga lil sis d’ina ba lafiya ina so in kaita clinic yanzu”
Har karo muryoyinsu sukeyi wajen fad’in ” toh Allah ya kawo sauk’i yayin da d’aya ke fad’in Allah ya sawwak’e .
Jinjina kai yayi kawai tare da d’aga musu hannu daga nan yaja motar suka tafi.
Sosai su Fauzee suka ji Abbas d’in ya yak’ara birgesu.
Sai da ya hau titi kafin ya kallo Teemahn jin tayi shiru tun d’azun, sai yayi gyran murya ita kuwa fuskanta na saitin gabanta amma sai ta fahimci da it hakan dayake yana kallonta yayi.
Sai juyo itama ta kalleshi yayin da shi kuma yariga da ya maida hankalinsa ga tuk’I.
” wai dama kasansu ne yayah?
Ta jefa masa tambayar tana kallonsa.
” shi kuwa murmushi yayi mata dan dama abinda yake so kenan, amma sai yace mata ” me kuma yafaru?,ko laifi ne dan mun gaisa dasu?
” a’a” tace ahankali tare da kawar dakanta gefen hanya.
Sarai ya fahimci damuwarta kishin Teemah sam baya iyah 6uya, he can recalled that lokacin daya zo gidansu batason ko gaishe shi ma tayi balle magana ya had’asu, haka ma da Mahmud yazo tai tayin rigima dan dai mahmud d’in ba irin sa bane da yasan har lokacin barinsa gidan bazasu yi wani shirin arzik’i dashi ba, kuma duk hakan yana faruwa ne sanadiyar son kanta sam bata so wani yafita ko kuma afifita wani akanta tafison a kullum ta zama tasha gaban komai akuma ko’ina ta kasance A.
Bai sake kulata ba har sai da suka zo daidai wajen mai saida kayan itatuwa harma ya d’an gota shi sai kuma yadawo da baya.
Fita yayi bayan yai parking sai yaje ga mai saida fruits d’in yasayo da d’an dama kuma kala-kala sannan yadawo motar aka zo aka sa masa su a boot daga nan yaja yafara tafiya yanzun ahankali yake tuk’in har suka zo gida suna yin parking yace mata “ki bud’e baya ki shigar da kayan can na ciki, “toh tace tana k’ok’arin fita ya kuma cewa ” kinsan mai yasa na saya?
Da kai ta amsa masa alamar “a’a”.
” toh tuna baya nayi ko kin manta?
Murmushi kawai tayi dan tasan labarin baya d’in kaf abakin mummy, shima sai yafara gaya mata irin abinda take masa abaya d’in lokacin tana k’arama da irin muguntar datake masa da rigimar sai an saya mata fruits kullum.
Dukkansu abin sai basu dariya sai ta bud’e motar tafito shima ya fito suka nufi bayan atare shi ya bud’e ita kuma tasa hannu ta d’auko ledar, tana fitarwa tayi saurin dire shi ak’asa tana nishi
” miye kuma” ya tambayeta da mamaki.
Karkata kai tayi gefe tare dayin
k’walk’wal da idanu tana kallonsa.
” gara ma ki zage ki d’auka domin ni nayi nawa tun abaya yanzu kuma lokacin kine kema”
Yana rufe boot d’in yake maganan.
Cikin shagwa6a tace ” Allah akwai nauyi sosai yayah”” koma menene fah sai kin d’auka yau d’in nan dan na fahimci ba k’aramar raguwa bace ke d’in kina nan kullum sai surutu amma ba amfani.”
+
Baki ta tura sannan azuciye ta cicci6i ledan tayi ciki da shi, shima bayanta yabiyo hannunsa rik’e da wayarsa da kuma key d’in mota.
Tafiya kad’an ce ta iso dashi inda take tafita da k’yar kamar zata fad’i, tausayi tabashi da ganin yanda take kokuwa da ledan sai alokacin kuma ya tuna da bata da jin dad’i ma ashe sai yasa hannu ya kar6i ladan ya rik’e ahannunsa ” muje intayaki d’auka kafin ki fad’i wa mutane”.
Yaryarfe hannu ta fara bayan ya kar6a d’in ita adole wai zafi, yana tafiya tana binsa abaya har suka isa kitchen sai da ya ajiye ya juya kafin yace mata ” inkin gama ki had’a min fruits salat ki kawo min”
“Ayyah yayah kamanta banda lafiya ne ” Tafad’a kamar zatayi kuka dan harga ita bacci takeso tayi.
” kin warke ai naga.”
Yana kan tafiyar ya bata amsa atak’aice.
Ita kuwa haushi ne ya cikata daman ba barinta zaiyi ta huta ba shine ya hana zama a school?
Cewa Baabah Lami tayi ta zuba su acikin fridge ita kuma tafice daga kitchen d’in.
Gurin mummy ta koma dan sanar da ita akan sun dawo amma koda taje sai bata tarar da mummyn ba hakan yasa ta wuce d’akinta ta sauya kaya kafin ta dawo kitchen d’in dan had’a masa abinda yasata.
*****
Acikin kwana ukun daya rage wa Abbas ya tafi ba k’aramar sakewa da Teemah yayi ba hakan kuma shi ya kawo shak’uwa mai k’arfin gaske atsakaninsu yakan 6ata lokaci yana mata hira da labarai na ban dariya, wani lokaci ya k’ira mata Mahmud awaya suyi ta hira dashi Abbas yana jinsu sai dai yayi ta murmushi in kuma sunyi abin dariya shima sai ya dara, yawo sukanje kusan kullum dashi hakanan yakan kaita islamiyah da boko ya kuma dawo da ita gida hatta muhibbat sai da suka kai mata ziyara tare da Teemah, anan ne ta fahimci ashe ma ba budurwarsa bace wacce abokinsa zai aura ne wato Saleem.
Ita kanta wani lokaci takanyi mamakin al’amarin takance ashe dama Yah Abbas ya na da fara’a da sakewa haka?, amma mai yasa bai ta6a gwada min asalin halinsa ba sai ya ari wani hali ya ya6awa kansa, kodan shi soja ne shiyasa yake mugun hali oho.
Mummy kanta taji dad’in wannan sauyin domin dama can bata son wancen d’abi’ar tasu ta rashin jituwan nan, kawai dai bata da yadda zatayi ne, kuma ganin hakan ne yasa ta manta da fushin datakeyi da Teemahn akan abinda tayiwa Abbas d’in saboda sosai hakan ya 6ata ran mummy aganinta raini ne kawai ke damun Teeman tunda shi Abbas d’in ai ba abokin wasanta bane.
Cikin wannan kwanakin ne kuma Fauzee ta takura Teemah akan al’amarin Abbas d’in yayinda abin yake matuk’ar k’ona ran Teemah fiye da zaton mai karatu, tun daga ranar da Abbas yakai Teemah school har suka gaisa shikenan kullum sai sun rakota in sun tshi zata koma dan kawai su ganshi, wani lokaci har 6uya take yi dan kar su ganta, hakan bazai hana washegari su kuma tambayanta abu akansa ba most especially fauzee tafi damuwa dashi sosai.
Bata kula ta haka take danne ranta har sai inta dawo gida sannan ta yi ta masa mita da fitina akan hakan shikuwa da bama sanin kirki yayi musu ba yadai san sun ta6a gaisawa da k’awayenta amma yanzu koya gansu he can not even recognize them amma duk da haka dan ya k’ara bata haushi sai yace ” wai har yanzu bata daina damunki ba, jiya fah da mukayi waya nace mata karta na sakoki akan maganar amma bataji, kiyi hak’uri lil sis ki barni da ita zanyi maganinta”
Hakan kuma bazai hana washe gari taji sabon salo daga Fauzeen ba sai duk suka bi suka d’aure mata kai gaba d’aya tarasa waye ne mai gaskiya acikinsu.
Akullum Fauzeen zancenta ita a had’ata da Abbas tana so ne dan Allah ko phone number d’insa ne Teemah ta bata yayin da shi kuma yake nunawa akan ai suna waya ma da ita kawai fooling d’in Teemah takeyi tana wasa da hankalinta.
Dataga inaah so suke su caza mata kai kawai sai watsar da al’amarin gaba d’aya tama daina kulawa koda Fauzeen tamata magana.
Lokacin da Abbas yafara shiryen-shiryen komawa da Teemah suke komai duk wani abu daya dangamci tafiyarsa da ita akayi shi kansa yana yabawa da k’ok’arinta akan hakan sai dai deep down yana matuk’ar jin tausayinta har aransa domin shak’uwar da sukayi ba irin shak’uwar da za’ace anyi ta ankuma manta ta bane tana mat’uk’ar tsaywa azuciya, dakansa yafahimci irin yanda take ji da nuna kishinsa wanda yanada tabbacin ita kanta bata san ma’anar hakan data keyi ba.
+
Wani lokaci yakanyi danasanin hakan daya mata yasan zai cutar da zuciyarta ne ba kad’an ba dan yana da tabbacin da bai sake da ita har haka ba da bazata ji zafin rabuwa dashi ba kokad’an koda kuwa yabar garin, duk da yake shi ya shirya hakan a matsayin hukuncin rashin jin data tayi masa da kuma rashin kunya amma shida kansa yanzu yasan bai kyauta mata ba.
Ana gobe zai tafin da k’yar ta tafi ta kwanta amma kuma sam bacci yagagara d’aukanta haka ta kwana idanunta biyu tana ta tunanin rabuwa da yayanta.
Kusan sallar asubah ne ta tashi ta dauko jakar makarantar ta ta fitar paper ta yagi d’an k’arami da biro tayi rubutu akai, ajiye shi tayi bayan ta gama rubutawa, sannan ta sake yagan wani the same size da wancan takuma yin wani rubutun shima ta ajiye, wasa wasa sai da tayi kusan kala biyar duk ta tarasu agefe ta d’ora kanta akai.
Har akayi sallar asuban tana kwance idanunta a rufe gaba d’aya sai takejin babu dad’i, dakyar ta tashi ta d’auro alwala tazo tayi sallar asbah d’in, sai dai tana idarwa bacci ya d’auke ta akan sallayar datayi sallan.
Dayake bata yi bacci da dare ba sai wannan baccin yamata nauyi sosai har gari ya waye ma bata sani ba har kusan 7:00 tana bacci.
Abbas kuwa dama fitan wuri yake so yayi shiyasa yayi shirinsa da wuri yayi zaman jiranta dan sun rabu ne akan cewa da sassafe zata zo ta tashe shi daga bacci dan kar ya makara ganin lokaci na tafiya ita kuma shiru sai ya fito ya nufi d’akin nata dan ba mamaki ma mantawa tayi da batun tafiyar tasa acewarsa.
Ahankali ya tura k’ofar ya shigo bayan bugun da yayi yaji shiru yana shigowa kuwa sai idanunsa ya sauk’a akan gadon ta dayafi zaton tana kwance akai tana bacci amma kuma sai bai ganta akan gadon ba sai yaganta ak’asa akan sallaya, murmushii yayi kana yace ” daga sallah sai bacci kenan” .
Takardun dayagani agefen gadon ya nufi wajensu aransa yake tunani k’ilan kwanan karatu tayi shiyasa take baccin yanzu.
Hannu yasa ya d’auko takardan dayaga k’ananun papers akai sai yaga anyi rubutu kamar haka……..
_People are like_ _stained-glass_ _windows_ .
_They sparkle and_ _shine when the sun_ _is out_ ,
_but when the_ _darkness sets in,_
_their true beauty is_ _revealed_
_only if there is a_ _light from within_ .
Kauda wannan yayi ya je ga na k’asa shima yaga ta rubuta…..
_Hold on to what you_ _must do,_
_even if it’s a long_ _way from here_ .
_Hold on to your life_ ,
_Even if it’s easier to_ _let go_ .
_Hold on to my hand,_
_even if someday_
_I’ll be gone away_ _from you. __I’m_ _going to miss u _so_ very much yayah_
Sosai jikinsa yayi sanyi dayaga papers d’in haka yadinga d’aga wa yana gani tare da k’ara maimaitawa har kusan sau uku.
Daga k’arshe sai ya zare guda d’aya wanda yafi sanyaya mashi rai ya ninke yasaka abayan condom (cover) d’in wayarsa sauran kuma ya mayar mata abinta ya ajiye mata.
Inda take kwancen yaje ya tsaya yana kallonta yanda take baccin ba k’aramin birgesa tayi ba ” she’s innocent while sleeping.
Wayarsa ya ciro ya kashe hasken camera d’in sai ya d’auke ta a photo daganan yajuya ya tafi abinsa.
Koda ya fito d’in sai yabiya ta kitchen dayake yasan mummy kullum dasafe in kana son ganinta toh a kitchen zaka same ta har sai taga ta sallami kowa kafin hankalinta yake kwanciya.
Da sallama ya shiga kitchen d’in tana juyawa ta amsa sallamar tareda fad’in ” bade harka shirya ba”?
Murmushi yai mata sannan yace “nagama shiri mummy inaso inje dawuri ne dan akwai abinda nakeso nayi acikin maidugurin kafin nawuce.
Jinjina kanta tayi alamar gamsuwa, sai sannan kuma suka gaisa tare dayi mata sallama gaba d’aya, itama mummyn fatan alkhai alkhairi tayi masa da kuma d’umbin godiya bisa ga karamcin daya nuna musu wata guda cif na hutun daya samu awajen aikinsa yabar mahaifansa ya taho dominsu saboda zumunci.
+
Sai yau ne zashi Gombe kuma acan ne zasu had’u da daddyn Teemah dayake shima yanacan yaje gaida ‘yan uwa da mahaifiyarsu.
Amma shi Abbas d’in gobe zai wuce dayake bawani yawane da ‘yan uwansu nacan d’inba kusan kowa yanufi inda zashi Daddyn ma goben zai taho watak’ila ma su fito tare da shi gaba d’aya.
Dayake saturday ne sai Teemah tayi tashan baccinta tana baza mafarki ba ita tatashi ba sai ba sai kusan 9:am balle yanda baccin yayimata dad’i kwata-kwata sai ta manta da batun tafiyar yayan nata.
Tana farkawa kuwa shi fad’o ranta
sai kuma idanta ya hango window gani tayi hasken rana gal ya haske ko’ina, wani mik’ewan datayi arazane harta ni sai dana tsorata da hakan.Da gudu tafito ta nufi d’akinsa tana zuwa, k’ofar d’akin ma a6ud’e yake hakan yasa bata sha wahala mr bugu ba kawai ta fad’a ciki.
Yanayin d’akin ne ya tabbatar mata da cewa yatafi d’in ne dagaske domin ko’ina shau tagani babu wani sauran abubuwan amfaninsa a d’akin.
Take kawai taji jikinta yayi sanyi har gwiwoyinta na barazanar kasa rik’e ta a tsayen data ke.
Sai ta k’arasa kan gadon dake d’akin ta kwanta gaba sai ta rasa mai ke mata dad’i, tasan bazata ta6a iya hana shi tafiya ba amma atleast taso ko sallama ne suyi, taso tamasa kallon k’arshe dan bata tunanin akwai chance d’in sake kallonsa kwana kusa.
Ta kai a k’alla kusan mintina talatin ad’akin kafin ta lalla6a tafito.
Zuwa lokacin kuma wani zazzafan ciwon kai ne ya ziyarceta sanadiyar bugun da zuciyarta keyi akai-akai.
Tana fitowa sai ta had’u da mummy cikin shiri ga dukkan alamu ma fita zatayi.
Ai tana ganin mummyn sai ta yafi da sauri ta rungumeta take sai hawaye ya gangaro mata zirrrr.
Mummyn ma dayake ta fahimci damuwarta musamman dataganta tafito daga 6angaren d’akinsa sai ta fahimci cewa shi taje dubawa tunda tasan basuyi sallama ba.
Hakan yasa tafara bubbuga bayanta cikin tausayin ‘yarta ta amma sai bata nuna tasan damuwarta ba illah tambaya data jefa mata nacewa “meyafaru,? meke damunta?”.
Temah ‘kinyin magana tayi sai da mummyn tayi kamar ranta yasoma 6aci ta hasalo tare da maimaita tambayar da d’an tsawa sannan ne Teemahn tace mata ” mummy yayah yah yatafi abinsa kuma yak’i yatasheni abaccin yatafi kayansa………
Tsaki mummyn taja tare da fad’in ” zamanki yake ne da har sai yatashi kafin yayi tafiya.
Shiru Teemah tayi dan zuwa yamzun kalamanta sun fara mata nauyi, tafara gwammace yinshiru fiye da yin maganar ma gaba d’aya.
Hakan yasa tabar jikin mummyn tawuce d’akinta yayin da mummy ma tayi tafiyarta tana mai gyara rik’on jakarta batare da ko waiwaye tayi ba.
Haka cikin sanyi tayi dukkan abinda zatayi tagama ta shirya tafito sannan ta had’a tea tayi zaman sha kallon kofin tayi sai take Yayanta ya fad’o mata arai ta tuna a d’an zaman sun da sukayi dashi irin abubuwan walwala dayake sada ta dasu, ta tuna ranar daya sata ta masa alk’awarin daidaita kominta yadda kowa keyi, tadaina rashin ji da rashin kunya wa babba kuma taringa cin abincinta akan lokaci yace inhar tayi hakan toh ya mata alk’awarin wani abu amma sai ta gama secondary school kafin ya gaya mata, tayi tayi dashi akan yasanar da ita yak’I sam yace bayanzu ba shi dai fatan shi tayi masa alk’awari, duk da tana son sani koma menene abun amma haka ta hak’ura ta d’auka masa al’kawari.
Sake kallon kofin data had’a tea d’in tayi ahanakali sai ta kai hannun ta d’auko kofin takai bakinta, tunda takafa shi akai bata cire ba har sai data shanye shi ras kafin ta dire kofin dai-dai da mik’ewarta dan tana dire kofin ta bara arean dinning d’in takaoma d’akinta.
Gidan shiru bakowa bakuma motsin komai dayake ba yara k’anana ne agidan ba ballantana aji hayaniyarsu kuma mummy ma bata nan balle ko k’aran TV ne taji, sai kawai tata shi itama ta fito agidan da niytar fita amma harta kai k’ofar fitan kuma sai taji ranta na 6a ci da fitan kuma ma taka mammiyan inda zataje ma bata sani ba, sai kawai tajuyo ta dawo gida.
She feels like tayi kuka amm bata son ta 6ata hawayenta abanza tunda shima yayan bai damu da ita ba so no need ta ta zubda hawayenta akansa duk da tana ganin idan ba kukan tayi ba sam bazata ji ta normal ba, baza ta ji kanta daidai ba.
*****
Hak’ik’a sabo baida dad’I kokad’an kuma Abbas bak’aramin nasara yaci ba akan Teemah dan wannan tafiyarsa tasa ta matuk’ar jijjiga ta, sosai yashiga jikinta har tana jin kamar tunda take bata ta6a missing d’in wani abu kamar haka ba.
+
Mummy kanta abin har yaso yafara damunta ganin yanda Teemahn nata ta dawo, kwata-kwata ta canja gaba d’aya kamar ba ita ba, zakayi mamakin inda rashin jin Teemah yatafi wata kalar shiru-shiru tadawo, dayake abin ya had’u mata da girma sai suka had’u da kewar yayanta da kuma girman data yi sai ya haifar mata da wata natsuwa taban mamaki.
Duk wanda yasan Teemah ada idan yaganta yanzu tokuwa yasan ta canja gaba d’aya, bata fiya magana ba yanzun takan zauna tayi shiru na fin awa biyu batare da ko kyaky-kyawan motsi tayi ba.
Wani lokaci mummy tayi ta mata magana amma bazama tasan tanayi ba, makaranta kuwa tsakaninsu sai dai ido idan kaga tayi doguwar magana toh kuwa sai dai in abin yazama dolene sannan takeyi, ko ma menene akeyi ko akayi her only answer is “ehh ko a’a” wani lokaci kuma tayi anfani da wani sassa na jikinta domin tabbatar da abinda takeso agane.
Sabon salon miskilancin nata har classmates d’inta suna mamaki da hakan dan Teemah sune irin class disturbance d’innan amma cikin k’ank’anin lokaci duk wancan halayyar ta kau.
Yanzun kam takan zauna taci abinci 3square meal d’innan baya wuceta ,takan ci dai koda babu yawa ma musamman idan ta tuna da alk’awarin data yiwa Yayan nata sai take daurewa tana d’an kiyaye abubuwan daya sa ta alk’awarta masa akan zata nayi, tunda tasan matsayi da kuma girman alk’awari duk da yanzun tanaji kamar ta tsani yayan nata har zuciyanta amma hakan bazai hana ta kasa cika masa alk’awarin data d’aukar masa ba.
Abbas kuwa suna waya da mummy ko ranar daya bar damaturu ma bayan ya isa gombe yak’ira ta haka dazai wuce ma saida ya k’irata kusan ma kullum sai sunyi waya da mummyn nata inda mummy a kullum take binsa da addu’ar sa’a da kuma kariya aduk inda yake tana kuma k’ara masa tuni akan addininsa da kuma rk’o da gaskiya da amana tare da kwatanta adalci aduk inda rayuwa tajefashi.
Babban dalilin daya sa Abbas ke yawan k’iran mummy kenan saboda baya so akullum yayi missing d’in addu’ar data ke yi masa, sosai hakan ke masa dad’i amma abin mamaki bai ta6a tambayar Teemah ba koda wasa, ita kuwa hakan sai yake k’ara bata haushi, daga baya ma inta ga suna wayar sai ta tashi tayi wucewarta indai tana tare da mummy alokacin inkuwa bata wajen ma shikenan.
Koda Daddyn ta yadawo shikansa yayi mamakin canjawarta dayake bai samu yadawo a washegarin ranar da Abbas d’in yaje Gomben ba saboda wani issue daya rik’esa kusan 3days yak’ara bayan sunyi sallama da Abbas d’in.
Shi da kansa ya jawo Teemahn jikinsa ahankali da lallami yake tambayarta ko wani abu ke damunta dan yanda yaganta d’in bak’ara min mamaki yayi ba, amma tace masa ba komai yayi tambayar har ya gaji amma bai samu gamsashiyar amsa daga gareta.Daga baya ne bayan sun ke6e da mummy yake sake tambayarta me yasamu Angel d’insa yaganta bakamar yanda yasaba ganinta ba, sai mummy bata 6oye masa ba ta sanar dashi cewa Teemahn tadawo hakane tun bayan komawar Abbas wajen aikinsa.
Dariya daddyn yayi sannan yace ” ta gaji mamanta kenan”
Cike da mamaki mummyn ta d’aga kai ta kalle sa, sai ya jinjina mata kai alamar tabbatarwa.
Yakuma k’ara da fad’in kin manta da k’yar nasamu kika dawo hayyacinki lokacin rabuwarku da Alh.Yusuf?”
“Murmushi kawai mummyn tayi masa dan kokad’an bata so ta tuna baya shiyasa bata k’ara furta wata kalmah ba ta basar da maganar kawai.
Babu wanda yakuma kulata akan maganar kowa sai ya k’yaleta dan sun san na lokaci k’ank’ani ne zata warware dakanta.
Ita kuwa hakan yafi mata tagi so kowa yabarta yanda yaganta bataso ake yawan tambayarta akan hakan dan bata sanin amsar bayarwa sai dai ma taji haushinka kai mai tambayar abinda yasame tan.
Kwanan Abbas shida da tafiyah sai ga Mahmud ma ya dawo, aranar dasuka fita daga camp, Teemah kam bazata ce batayi murna da dawowar tashi ba saboda shima tayi kewarsa amma tagagara bayyana murnarta afili.
Shikansa yayi mamikn inda rawar kan Teemah yatafi amma sai yabar hakan amatsayin girman data san yasameta ayanzun,duk da yake yasan sun fara shiri da Abbas kafin yatafi amma bai ta6a zaton shak’uwar dake tsakaninsu har takai matsayin da rabuwarsu zai ta6ata har haka ba shiyasa ma sam wannan dalilin bai zo kansa ba.
Sai kawai yayi ta tsokananta wai ad’an tafiyan daya yin neh harta yi wayo haka?, ko kuma idan tayi wani abin yace ” iyeh irin angirman andaina yarinta” murmushi kawai takeyi masa shikuwa daman dayake akwai wasa atsakaninsu sai baya ta6a gajiya da tsokanan nata koda bazata kulashin ba sai yayi.
Mahmud yaso yayi zamansa a damaturun kafin yafara aikin bautar k’asan amma Anty ta rink’a damunsa da k’ira akan wai yadawo gida tana son magana dashi.
Dafarko yaso ya share ta yak’i zuwa saboda babu wani anfani zuwan nashin, gani yake gufin yayi nisa sosai kuma idan yaje d’in ko 1week mai kyau bazaiyi ba zai dawo toh ina amfanin zuwan nashi.
Data matsa masa sai kawai yace mata shi bashida kud’in transport d’in dazai kaishi lagos manufarsa intaji ta hak’ura da tafiyar amma abin mamaki sai yaji Bank alert tamasa transfer d’in kud’i isassu daza su kaishi su kuma dawo dashi, ko k’ira bai yi yamata godiya ba, sai kuwa k’iranta yabiyo baya inda take cewa yabi flight maza yataho.
“Toh” kawai yace mata tare da yanke wayar aransa yake mamakin fitina da kafiya irin na mahaifiyar tasa.
Dabara ce ta fad’o masa na k’iran Abbansa yagaya masa amma shima abin mamaki sai yace masa wai yatahi d’in kawai wai ai suma sunyi missing d’insa musamman Antyn nasa acewar Abban wai sosai take damuwa da rashin Mahmud d’in akusa dasu.
Tsaki ne yaji na shirin kubce masa yayinda yake shirin yanke k’iran amma sai ya danne yayita acikin ransa.
Haka ransa baiso ba ya shirya yayi sallama dasu mummyn yatafi maiduguri daganan yabi jirgi yawuce Lagos d’in.
Abin takaici ma ba komai zai mata ba kawai a fahimtarsa fitina ce ke damunta bataso yad’an zauna tare da mummyn in an barta nan wai ita mai dabara.
Washegarin zuwansa wata tazo gidan mai suna Munira, mahaifiyarta ce ta aiko wajen Antyn, lokacin data zo kuma Antyn bata nan sai Mahmud tasamu kwance akan kujera.
Wani fi’ili da salo tafara yi masa ita adole tana yanga, shikuwa haushi yabi ya cikashi da k’yar ya bata amsar tabayar data yi masa na cewa ina mum d’in sa take?
Zata sake magana ya tare ta cikin k’osawa da kasancewarta akusa da shi d’in ga kuma haushin uzura masa da Anty tayi inda azafafe yace mata ” contact her mana karki dameni ni dallah”
Jan bakinta tai tayi shiru tana k’are masa kallo, shikuwa yana da kwancen yaga ta kasa d’auke idonta akansa da farko yabata chance saboda yanayin kallon na d’an lokaci ne zata ‘auke idanun ta amma sai yaga ina bata da niyyar dainawa, sai yatashi ya zauna da sauri yana kallonta idonta acikin nashi yace mata “naci miki bashi ne?
Jijjiga masa kai kai tayi alamar “a’a” +
” so why the eyes?”
Yasake fad’i sai sannan ta kauda idonta gefe cikin jin d’an nauyi.
Tsaki yaja kana yakoma ya sake kwanciya amma ko 2mins bai k’araba ya tashi ya bar parlourn yayinda munira ma ta raka shi da idanu.Ajiyar zuciya Munira ta sauk’e lokacin da Mahmud ya6acewa ganinta, take kuma sai murmushi ya d’an k’wace mata data tuno da mahaifiyarta tasan bata da wata matsala matuk’ar ta furta cewa yamata.
5minutes me kyau Munira bata k’ara ad’akin ba ta fito itama, dan ji tayi zaman ya gundureta tun bayan da Mahmud yabar d’akin hakan yasa ta mik’e tafito itama.
Azaton ta zata ganshi a harabar gidan ne, amma ga mamakinta ko kalar rigarshi ma bata gani ba ballanatana shi da kansa jitayi datasan inda yayi da babu abinda zai hanata zuwa kodan ta k’ara ganinsa ma kawai koda bazaiyi mata magana ba .
Haka ta taka ahankali taje ga motarta ta tayar tayi gaba zuciyarta fal farin ciki da ganin Mahmud d’in da tayi for the first time arayuwarta domin basu ta6a had’uwa ba sai yau d’in gashi kuma akayi sa’a shid’in ya mata 100%.
Shikuwa yana fita 6angarensa ya nufa ransa a matuk’ar 6ace dan tun ganinsa da yarinyar yaji yatsaneta sam bata birge shi ba, balle data k’ura masa idanun nan nata ji yayi kamar ya hauta da duka ma sa’anta d’aya shi ba mai saurin hannu bane inbahaka ba yace da mari zata sha d’azun dan yanda tabashi haushi.
Tsaki yaja lokacin daya isa d’akin nasa ji yake kamar ta shiga rayuwarsa ne dan yana cikin hutawansa tasa ya tashi ba shiri ya fito sai ya zauna abakin gadonsa yana wani jijjiga k’afa kai kace wani abin 6acin rai irin sosai d’innan akayi masa.
Nan kuwa bahaka bane ko tsanan Muniran dayaji yanayi ya samo asali ne daga tsanar daya yiwa duk wani wanda yake huld’a da Antynsa domin acewarsa duk ba alkhairi bane yahad’a su.
Munira bata jima da barin gidan ba Anty ta dawo kuma koda da dawo d’in da bataga Mahmud ba bata wani neme shi ba sai tayi zamanta apalournta ta hakimce kamar wata sarauniya.
Tunowa datayi da sak’on da sukayi za’a kawo mata saboda abinda yasa tadawo gidan dawuri ma kenan dan kar azo ba’a sameta ba gashi har sun shiga lokacin yanzu, dayake daman sun saka lokaci koda ta dawo d’in kuma sai bata tadda kowa ba agidan da alamun kuma sak’on ma bai iso ba har yanzu .
Wayarta ta lalu6o ta nemi numbern me aiko sakon ta kirata dan taji dalilin jinkirin da aka samu d’in.
Bayan sun gaisa ne matar take ce mata ai ta aiko ma already ‘yarta ta taho zata kawo mata sak’on tad’an jirata kad’an bari ta sake ta6ota awaya taji inda ta tsaya.
“Ok” kawai Antyn tace tare da cire wayar daga kunnanta numbern Mahmud tasake k’ira tabashi umarnin zuwa yasameta a palourn sannan ta ajiye wayar a gefenta.
Mahmud kamar bazashi k’iran Antyn ba amma dai ya daure yatashi yaje wayar tasan ma ad’akin yabarta domin bayyi zaton zai jima awurin Antyn ba.
Da sallamarsa ya shiga d’akin yayinda Antyn ta amsa ciki-ciki kamar bata so ta amsa sallamar ko kuma kamat dole akayi mata ta amsa inba ka lura bama bazaka gane ta amsa d’in ba.
Jijjiga kansa yayi cikin takaici, sai da ya isa gefenta ya zauna kafin yace mata ” wani lokaci kina abu kamar bada hausawa kika tashi ba Anty”
Ido ta zubashi mishi alamar tambaya take mishi batare data furta tambayar tata da bakinta ba.
Shikuwa sai yaci gaba da fad’in ” yanzu fi sabilillahi tsabar isa sallamar ma sai kin ga dama kike amsata Anty?”
Azafafe Antyn ta amshe maganar tasa da fad’in ” toh d’an ayi,ubana malam Muhammadu, kadawo kuma ko zaka fara takur min, nagade ni ce na haifeka kuma tun kan ahaifeka nasan ana sallama aduniya ko kai zaka koyamin yanda akeyi yanzu?
Murmushi yayi dan ganin yanda Antyn ta hayyak’o masa kwata kwata ya rasa matsalar matannan sam bata son gaskiya ita.
daga magana kuma Anty sai ki hau………
+
Kar6e maganan tayi da fad’in ehh banaso.
Kawai sai ya bata hak’uri yana murmushi dan ya shatantar da zancen, sai yace tunatarwa ce fa kawai nayi Anty kinsan ni bakina baya shiru idan naga abu shiyasa.
Kauda kanta tayi cike da jin haushi ganin hakan yasa shima yaja bakinsa yayi shiru.
Haka sukayi zaman kurame kusan na mintina goma babu wanda yasake yiwa wani magana illah Anty dake d’an jan tsaki time to time wanda yake da harshen damo domin haushin nata biyu yazama, gana mahmud gana Matar da tasata jiran sak’o kuma tasa6a lokaci.
Harji takeyi ai badan tana matuk’an buk’atar abinba da cewa zatayi tafasa su bari kawai.
Daga k’arshe sai Mahmud ya mik’a hannunsa yajawo remote ya kunna T.V domin katse zaman shirun da sukeyi dashi da Antyn tasa.
Jiyake kamar ya bud’i baki ya tambayeta dalilin k’iran datayi masa amma ganin yanda tasha mur sai ya hak’ura da tambayar, yana matuk’ar so kuma ya tafi yabar d’akin domin akwai inda yake son zuwa sai dai ayanda yasan halin Antyn yasan bori zata masa kar kuma tace ta k’ira shi yak’i ya saurareta saboda ya rainata…….wannan dalilin ne yahanashi barin d’akin kawai ya kunna T.V duk da ransa ba son kallon yake ba amma dan dolensa ya kurawa T.V d’in idanu dukda baya wani fahimta sosai, jira yake yaji ta anbatoshi amma shiru.
Sun kai 20 minutes zaune agurin sannan yaji anturo k’ofar parlourn tare da fad’in “ex…….cuse me………”
Da tura k’ofar da yin maganan da kuma shigowan duk sun faru ne adaidai lokaci d’aya.
Da mamaki Mahmud yasake juyawa ya kallo k’ofar dan ganin waye mai wannan rainin hankalin, kawai sai idanunsa suka sauk’a akan yarinyar daya gani d’azu, shi harya manta ma da ita bacin yanzu da ya sake ganinta.
Kallon inda Anty take yayi sai yaga yanda take 6are baki tana dariya wa yarinyar kamar ba ita ce mai uban fushi da tsaki ad’an wasu takaitattun lokutan da suka gabata ba, ga dukkan alamu bak’aramin farin ciki tayi da zuwan yarinyar ba.
Mahmud sai ya jijjiga kansa kawai yakuma maida dubansa ga T.V d’in tare da fad’in ” ALLAH YAH SHIRYAH”.
Munira kuwa zuwa tayi ta zauna akusa da Antyn tana murmushi suka gaisa da juna bayan sun gaisa d’in ne Munira tace harfa nakusan isa gida ma sai mummyna ta k’irani tace wai kindawo in sake komowa.
” kardai kice min kin zo bana nan”?
Cewar Antyn ta fad’a da kulawa
” ehh nazo mana wannan be sanar miki ba” Munira ce ta fad’a tare da nuna inda Mahmud yake zaune da idanu tana d’an satan kallonsa.
“Humm zai fad’a min ne wannan me mugun halin ?”
Antyn tafad’a tare da ta6e bakinta gefe.
Shikuwa ko kallonsu ma baiyi ba sai yayi kamar irin bai san ma dashi sukeyi d’innan ba.Amma acikin ransa bak’aramin haushin Kalmar mugun hali da Anty ta ambace shi da shi agaban yarinyar nan yajiba.
Yana gani Munira ta ciro sak’on Antyn tabata a leda bak’i, bama wani abu me yawa bane amma yaga duk farin ciki da walwalar Anty ya k’aru alokacin datayi arba da sak’on a hannunta.
Haka kawae yaji zuciyarsa taraya masa ba abun kirki bane aka kawo mata bana arziki bane abin.
Koda Munira ta mik’e da niyyar komawa inda ta fito sai Anty ta mik’e da fara’arta take tambayarta wae da abun hawa tazo ne?
Da ” ehh”
Muniran ta amsa mata.
Sai Antyn tace dama wae ko Mahmud zai sauk’e tane amma tunda da mota tazo shikenan.
Yana ganin yanayin canjin fuska atake agurin Munira amma sai ta d’an basar tace ” bakomai akwai wataran ai”
Amma aranta bak’aramin haushi taji ba na missing wannan damar datayi.
Acewarta aida tasan abinda Antyn zata ce kenan da bazata ce da mota tazo ba….,,..,,….(nikuwa nace ai danasani k’eyace Munirah)😜.
Anty dakanta tarakata har wurin motar tata suna takunsu kamar wasu k’awaye.
Lokacin data dawo daga rakiyar kuma bata sami Mahmud a palourn ba shima tafiyarsa yayi dayake daman hanya yake nema shima.
Koda ya koma d’akin nasa misscalleds yatarar awayarsa kusan 5 , ciki kuwa harda na Abbas guda d’aya da sauran abokanshi da kuma wanda suka yi dashi akan zasu had’u yau.
+
Saida yasamu yazauna duk ya bisu da k’ira kafin yayi shirin fita inda zashi d’in.
Mayafi Anty ta k’ara d’auka ta nufi gidan k’awarta Anty chideh.
Lokacin da Anty tashiga gidan shiru taji ba motsin kowa koda tata knoking sai taga ba’a amsa mata ba sai kawai tabata uzurin ko Anty chidehn na wanka ne shiyasa.
Saita turo k’ofar tashigo ciki kanta tsaye,
amma saidai me…….. wani gani da Anty tayi har sai da takusan kwara amai a inda take d’in take tayi fatan kar Allah yasake nuna mata irin wannan abin har abada.
tana k’ok’arin juyawa sai Anty chidehn ta hango ta, yunkurawa tayi da niyyar tashi ta zauna sai hakan yabawa abokiyar masha’artata dama tafahimci meke faruwa dalilin d’ago kan datayi.
Sai jiyo muryar Anty chidehn tayi tana fad’in ” ah’ ah mum Mamud why did u stand there”?
Hankalinta akwance tayi maganar kamar ba wacce aka ganta ta ke ayyakata babban sa6o ba.
Anty kamar bazata juyoba sai ta daure ahankali ta juyo sukayi 4eyes da Anty chidehn, murmushi tayi mata yayinda Anty tasha mur sosai dan kokad’an bata ta6a kawowa aranta Anty chidehn na irin wannan harkar ba.
Tashi Anty chiden tayi ta zauna tana ‘ko’karin lullu6e jikinta tace ” k’araso mana “
Daurewa Antyn tayi ta k’araso chiki yayinda takasa d’auke idanunta daga kan house maid d’in Anty chidehn wacce zuwa yanzu tafahimci ba house maid kad’ai yarinyar ta tsaya ba harda……..
Koda ta iso ma dakyar tasamu guri ta zauna jikinta duk yayi sanyi.
Anty chidehn ne tace mata Wai ita tafiya tsoro dayawa miye ma abin yin shocked anan sai kace yau ne tasan aka fara yin lesbian?
Tambayar ta bawa Anty mamaki sosai har hakan yasa ta d’ago idanu ta kalli Anty chidehn sosai.
Sam Anty takasa daina mamakinsu dan ganin datayi su kwata kwata abin bai wani damesu ba kamar ba abin jin kunya tasame su sunayi ba.
Dariyah kad’an Anty chidehn tasaki ganin yanda Anty ta kasa daina yi mata kallon tuhuma.
Sai ta mik’a hannu ta d’an kamo hannun Antyn atake kuwa Anty ta wafce hannunta da k’arfi domin zuwa yanzu in akwai abinda tafi kyama toh itace babbar aminiyar shawaran tata wato Anty chideh.
” come on, feel free mana mum mamud bakomai fah”
Tafad’i da dukkan gaskiyarta tana kallon Antyn ita adole in anbarta ba abin damuwa vane hakan, ganin Antyn bata kulata ba sai ta k’ara da fad’in ” sucking kawai nake sata tamin when I’m in need but nothing else”.
“hmm”
kawai Antyn tace tare da mik’ewa daga kan kujeran datake tace tatafi gida.
Magana taso suyi akan maganin da aka kawo mata d’azu amma wannan 6oyayyen halin Antyn chidehn data gani yau yasata fasa yin maganar ma gaba d’aya kawai ta koma gidanta.
Anty chidehn ma batawani damu ba dan tasan damuwar na yanzu ne kawai dakanta ma zata dawo kodan wani dalilin na daban.
Anty kuwa koda takoma gida tunanin abun yakasa barinta sam bata ta6a kawo hakan ga k’awartanba duk da yake ahlul kitabi ce ita amma sam bata kawo cewa rashin imanin Antyn yakai har haka ba.
Wannan dalilin ne yasa tad’an d’aukewa Anty chidehn k’afa na kusan kwana biyu, yayin da Anty chidehn tabata chance itama akan ta huce tukunna tasan cewa akan hakan bazasu rabu ba sai dai akan wani dalili daban domin bak’aramin sanin sirrin juna sukayi ba, ko wannan d’inma Anty Chidehn ta 6oye mata ne dan ganin kamar ita ba ra’ayinta bane yin hakan shiyasa bata ma bayyana mata ba.Shima Mahmud zuwan Munira da kwana biyu yace shikan zai koma ana nemansa Daddynsa ma baya gari amma ya tattara yakoma yobe state d’in abinsa domin jiyayi sam zaman chan d’in yadaina yimasa dad’i. +
Da farko Anty taso ta hanashi komawa dan ita afad’anta wai sai ya jira Abbansa yadawo tukunna.
Mahmud kuwa yak’I amincewa da batun nata don dolenta ta kyaleshi yatafi badan ranta yasoba.
A week d’in daya koma ne Munira tasake dawowa gidan amma wannan karon tafiyar kanta ce ba aike ba ne, koda tazo suka gaisa da Anty kamar yanda suka saba suka d’an zauna suna ta tad’i tsawon mintina bataga Mahmud ba bakuma taji Anty ta ambace shi ba a maganar dasukeyi d’in.
Kasa hak’uri tayi sai da ta tambaya tace ” Anty ina yaronki”?
Dariya Antyn tasaki kad’an sannan tace kardai kice min tafiyar batawa bace ta Mahmud ce”?
” murmushi Muniran ma tayi tare da fad’in haba shikuma ?
” kedai fad’i gaskiya yarinya”
Yanda Antyn ta ke sakewa suyi hira da kuma yanda tayi mata magana ayanzun yasata ko shakkun Antyn ma bataji sosai ba dukda yake son d’anta yakama zuciya amma tasan dole sai dasa hannunta sannan zata sameshi inba haka ba kam tasan samunshi zai d’an mata wahala.
Sai batayi k’auran baki ba tafara sosa kanta tana sussun kuyar da kai kamar wata mumina, take sai Antyn ta gama ganota aikuwa sai tayi murmushin da kana ganinta kasan farin ciki taji har zuciyarta.
Tashin farko sai takamo hannun muniran sannan ta bata assurance akan cewa karta damu indai Mahmud ne kamar tasameshi tagama tadaina ma damun kanta.”
Wannan albishir d’in ne yasa Munira ta rungume Antyn da k’arfi tana murna da godiya kamar bazata daina ba, tana sake Antyn kuwa ta tashi ta zari key d’in ta da gudu ko kunya bataji tayi waje wai bari takaiwa mummynta albishir mai dad’i.
Da murmushi Anty ma tarakata yayinda tana fita itama Anty ta zari mayafi ta tafi gidan aminiyar ta Anty chideh shab ta manta da batun lesbian d’in tsabar farin cikin datake ciki.
Kuyi hak’urin rashin jin update da dawuri da bakuyi ba pls abubuwane suka min yawa.Koda Anty chideh taganta murmushi kawai tayi, daman tasan dolene zata dawo kodan yanda sukayi sabo sosai ma.
+
Haka Anty ta kora mata bayanin abinda yafaru tare da nuna tsantsar farin cikinta afili.
Dama tun asali tafison ita taza6awa Mahmud matar aure da kanta sai kuma akayi sa’a fad’uwa tazo mata daidai da zama Munira ta nuna tana ra’ayinsa.
Munira y’ar k’awar Anty ce dasuka had’u sanadiyyar maganin mata.
Domin duk wani nau’i na magani da suke anfani dashi ita da Anty chideh Mahaifiyar Munira ke musu order daga sokoto kuma sunajin dad’in maganin shiyasa suke shiri sosai.
Anty tana gani kamar samun Munirah amatsayin matar d’anta wata dama zata samu dazai sa zumuncinsu da mahaifiyar Muniran ya d’ore sosai.
Anty chideh ma sai tayata murna tare da k’arfafa mata gwiwa akan hakan.
*****
Mahmud kuwa koda yakoma bai wani dad’e agidan ba yawuche inda aka turashi awani d’an k’auye ne zaiyi bautar k’asan.
Da farko Teemah murna takeyi sosai data ga yadawo d’in dan azatonta yanzun agida zai zauna amma sai yace mata ai shi tafiya zaiyi take sai murnar tata ta koma ciki.
Dayaga haka sai ya mata alk’awarin zuwa duk weekend yana dubata sai da taji haka kafin tad’an sake fuska.
Haka sukayi ta dashi aranar daya sauk’a d’in kuma duk hirar bata wuce ta Abbas ba.
Shima sai ya ringa biyeta ganin hakan tafi buk’ata.
Harda yayi niyyar k’ira mata Abbas d’in su gaisa amma sai ya fasa daya tuno cewa Abbas d’in yanzu yana bakin aiki ne.
Haka suka gama hirarsu suka rabu, yana komawa d’akinsa kamar Abbas d’in yasani sai ga k’iran sa ya shigo.
D’auka Mahmud yayi yana murmushi yace ” d’an halak”
“Allah ko”?
Cewar Abbas d’in slowly
Mahmud ne yaci gaba da fad’in wallahi nake gaya ma yanzu muka gama hirarka da lil sis harfa da zan k’ira layinka in had’a ku sai kuma nayi tunanin ko kana aiki ne”
” hmm ai gara ma baka k’ira ba, bayanzu zanyi magana da ita ba tukunna da sauran lokaci”
Mahmud na dariya yace
“Kai oga Abbas hukunci ne wannan ko kuma ra’ayine?
” duka biyun” Abbas ma yafad’a atakaice.
Kafin Mahmud yasakeyin wata magana sai Abbas d’in ya k’ara fad’in yaushe ma kadawo ne bansani Mahmud
” Yau-yau d’in nan na iso amma inajin gobe ko jibi ma zan shiga wani k’auye”
” owk Allah ya kaimu”
da ” Ameen” Mahmud ya fufe maganar sannan sukayi sallama da juna.
Washegari da yamma Mahmud yawuche yabar Teemah da kewa.
Amma wannan karon bata wani damu sosai ba dan zuwa yanzun tafara sabo da irin hakan. Tafar gane cewa dole ne irin hakan sai ya faru tunda suna da ‘yan uwa kuma dole a ziyarci juna.
Bazai yiwu ace kowa yazo sai ta yi kewarsu ba saboda ba kowane zai zo yakuma zauna mata agida ba dolene atafi tunda kowa nada muhallinsa koma badan hakan ba kowa nada abinyi.
Haka tacigaba da zuwa makarantar ta harsun kusa kammala S S 2 d’in sai Daddynta yace waec zata rubuta kawai bazatayi SS3 ba.
Itama dataji datayi farin ciki sosai dan dama tagaji da zaryar zuwa makarantar nan.
Shikuwa Daddyn ganin girman data ke k’arawa ne yasashi yanke wannan hukuncin, dan Teemahn akullum kamar hurata akeyi haka ta k’ara k’iba dukta cicciko.
Yayinda Mummy sam hakan bai mata ba, inda asonta taso Teemahn ta kammala gaba d’aya kafin sai ta rubuta waec d’in, amma koda ta gwada sanar da daddyn Teemah k’i yayi ya amince dan acewarsa bata da hujhan da zai sa dole sai anyi hakan, dolenta ta hak’ura ta zuba musu idanu.
Ana cikin hakan ne wani matashi yabi ya uzzura ma rayuwarta yahanata sakat.
Akullum inta fita zuwa islamiyah sai ta ganshi yasha gabanta da niyyar yimata magana.
Itakuwa kokad’an bata so daya takurata ma sai ta daina zuwa da k’afan datake zuwa dayake dama itace tace zata na zuwa dakanta bama sai ankaita ba, amma dataga matsin yayin yawa sai ta ce Habibun yaci gaba dakaita kawai.Amma me…..gudun gara take ganin kawai tayi domin tana fitowa zata ganshi tsaye ajikin motarsa yana rarraba idanun ta inda zai ganta.
+
Rashin sa’an datasake yi kuma shine wani lokaci Habibu baya isowa da wuri har sai an d’an fara watsewa yayinda wasu lokuta kuma har jiranta yakeyi tatashi kafin su wuce gidan.
Aduk ranar da Habibun bai iso dawuri ba haushi sosai Teemah keji kamar tayi fiffike yayinda ga matashin kuma abin farin ciki ne dan yana samun chance d’in zuwa kusa da ita harma yayi mata magana, dukda bawani kulashi takeyi ba amma dai yana jin dad’in hakan sosai.
Ranar kuwa da bai samu daman mata magana ba yakan bisu abaya har sai sun shiga kafin yake wuchewa shima.
Sai dai bai ta6a gangancin shiga musu gida ba yakanzo ya tsaya na tsawon wasu lokuta a k’ofar gidan daga d’an nesa batare daya nemi kowa ba shidai akullum burinsa yaganta koda sau d’aya ne.
Yau ma takama ranar Sunday, koda Habibun ya sauk’eta gida yakoma suka fita da mummy kuma basu dawo dawuri ba har aka tashi a islamiyar dan siyayyar mummy baya k’arewa matuk’ar tashiga kasuwa shiyasa suka 6ata lokaci sosai.
Tsaye take ak’ofar makarantar tana ganin duk kowa na tafiya amma ita sam ba Habibu babu alamarsa, zuciyarta nagaya mata cewa tabi ayarin masu wucewan itama suwuce tare sai dai tana tsoron kar kuma waccen mayen yabiyo su abaya abinda ta tsana kenan.
Kafin ta ankara sai taga har ankusa watsewa gaba d’aya domin d’ai d’aiku ne kawai suka rage dan dolenta tafara tafiyah da niyyar cimmah way’anda suke gabanta su had’a hanya amma taku biyar me kyau batayi ba sai kawai taga mutun tsaye agabanta yana murmushi, kallonsa ta tsaya yi da mamaki hankalinta kuma yana ga wad’anda takeso su tafi taren daya fahimci haka sai ya d’an k’ara matsowa kusa da ita hakan da yayi sai ya hanata ganinsu ma gaba d’aya sanasiyyar katangan ta yayi musu.
” kiyi hak’uri ya kad’ai nakaiki gida”
Yafad’a yana kallon fuskarta.
Muryarta na rawa tace” awani dalili”.
” masoyi”
yabata amsa atakaice.
Da mqmaki ta d’ago kanta ta kalleshi.
“Koba haka bane?
Yasake tambayar ta.
Bata bashi amsa ba illah hanya da fara k’ok’arin nema dan ta myi wucewarta.
Amma mutumin ya hanata wucewa domin duk wani motsin da zatayi sai shima ya motsa ya kuma tare gabanta.
Dan dole tasake tsayawa ta wurga masa harara tare da fad’in ” wai me kake buk’ata ne”?
” ki saurareni”!
Kauda kai tayi gefe cikin fushi ranta inyayi dubu toh yau jitake ya6aci saboda mutumin nan sam ta tsami hakan dayayi mata ko tace yake kanyi mata.
Shikuwa ganin hakan da k’warin gwiwarsa yaci gaba da fad’in………….
Kamar yanda na ta6a fad’a miki sunana Imran dan nasan kin manta tunda ba damuwa akayi dani ba.
Kuma ni ba a unguwar nan nake da zama ba, nazo ne duba wani fili sai Allah yasa naganki kuma kika kwanta min araina duba da yanayin nutsuwarki.Dafatan zan sami kar6uwa kodan mu k’ara fahimtar juna da kyau dan ni ji nake nasamu matar aure nagama………
Murmushin takaici Teemah tayi wanda ya tsaya mata a kan le6e kawai….aranta tace su matar aure manya!
Horn sukaji daga gefensu take dukkansu suka kallo gurin, Teemah naganin motar gidansu ne tatafi da sauri tana hamdala wa mahallici.
Bata kula da mummy acikin motar ba sai da ta shiga ta ja marfin motar ta rufe kafin ta lura da mummyn.
Innalillahi wa innah ilaihir raji’un tafad’a azuciyarta dan yau kam tasan me rabata da mummy sai Allah.
Baki ta bud’e da niyyar yin magana sai mummy ta dakatar da ita da fad’in ” waye shi “?
” nima fah ban san shi ba mummy”
K’ura mata idanu mummyn tayi tana karantar yanayinta afili zaka fahimci rashin sabo da hakan da batayi ba ga dukkan alamu tilasta ta tsayuwan akayi kodan ganin yanda ta taho da sauri daga jin horn d’in mota duk da bata ma san wake cikin motar ba balle tace danta ganta ne, amma hakan bazaisa takasa yi mata fad’a ba ko dan saboda ta k’ara tsare mutuncinta a matsayinta na ‘ya mace. Wannan dalilin ne yasa mummyn ta d’ago hannunta tare da ware yatsa d’aya ta nuna Teemahn dashi kana tafara magana.
” kinsan Allah Teemah ki shiga hankalinki banason rashin hankali da rashin wayo, baki san mutun ba shine harda tsaywa dashi a k’ofar makaranta?
Owk nagane, saboda ki nuna ke kin isa ko me?
Hawaye Teemahn tafara tare da jijjiga kanta Allah mummy bansan shi ba yau ne fah yafara……….
Hannu mummyn ta d’aga tare da dakatar da ita daga cigaba da maganan, sai kawai ta sunkuyar da kanta k’asa tana zubda hawaye, bata so kokad’an mummy tayi fushi da ita akan hakan taso ta yi mata bayanin komai amma mummy takasa tsayawa ma ta saurareta ballantana taji abinda ke faruwa.
Takaicin ta d’aya shine akan wanda bata ma ta6ajin zata so shiba mummyn ta na shirin yi mata fushi.
Motar shiru baka jin k’arar komai sai na shashekan kukan Teemah har suka iso gida.
Koda suka iso gidanma mummy ko kulata batayi ba suka fiffita a motan suka barta, kayayyakin data siyo d’inma Habibu ne da ita suka kwashi abinsu kota kan Teemahn batabi ba.
Sai da Habibu yafito ne yazo gurin motar ya d’an bata baki akan tayi hak’uri ta shiga ta bata hak’uri zata sauk’o ai.
Da jajayen idanu ta kalleshi tace Mummy tana fushi sosai dani ko ?
Yace a’a zata hak’ura ki shiga ki bata hak’uri.
Da k’yar ta daure ta fito a motar ta shiga ciki lokacin ma har maghrib ya k’arato, ganin haka kawai sai ta wuce bayi ta d’auro alwala ta zo ta tada sallah.
Ba ita ta tashi agurin ba har sai da tayi sallahr isha’i.
Addu’a sosai tayi kafin ta tashi ta nad’e abin sallahr.
Ko hijabin datayi sallan dashi bata cire ba ta nufi d’akin mummyn ahaka.
Da sallama ta shiga d’akin sai ta sami mummyn na shirin kwanciya.
Zama tayi ak’asa kanta ak’asa tajira har mummyn ta gama shirin baccin kafin taje gareta da muryar kuka take bata hak’uri.
Mumnyn yi tayi kamar batasan da ita a d’akin ba domin kwanciyarta tayi ta juya mata baya, sai da taga kukan da Teemahn keyi kamar zaiyi yawa kar kuma yasata ciwon kai.
Koda tayi tunanin nan d’inma sai da k’ara minti guda akai kafin ta tashi ta zauna ta fuskanci Teemahn tare da fad’in
” inajinki yah akayi?