ABDULKADIR CHAPTER 3

ABDULKADIR




CHAPTER 3






Zaune take gaban mudubi badan zatai kwalliya ba, tunda ta fito daga wanka ta sakama jikinta riga da wando na Pakistan, ta dauko hula ta ajiye kan mudubin, anan ta shafa mai ta zauna batare da tasan asalin abinda take tunani ba. A hankali ta dauki farar hular ta saka a saman kanta, tana gyara zamanta, hasken hular na saka nata hasken kara fitowa. A hankali cikin sanyin yanayinta tayi baya da kujerar da take sama tana mikewa tsaye. Madai-daicin tsayin da take dashi bai hana sirantakarta fitowa ba, duk da girman kayan jikinta. 6

Falo ta fito tana ganin Mami a tsaye hannunta riqe da hijab 2

“Ke ba dake za’aje kun shin ba?”

Mami ta bukata, tana kallon Waheedah data girgiza mata kai, girman yarinyar na bata mamaki, yanda shekaru suke gudu na tsoratar da ita, yanzun Waheedah din tace a aji shidda sakandire, Waheedar tace take shirin zana jarabawar gama aji shidda, ko Amatullah ta gitta sai taita kallon su, tana mamakin lokacin da rayuwa ta kawota inda take, da gaske haihuwa kyauta ce mai girma, kyauta ce da take ma fatan duk wani wanda Allah bai nufa da samu ba ya samu ko zaiji abinda ake ji. 1

“Jikina yamun nauyi Mami, suje abinsu, nace Amatu zata sakamun jan lalle idan zamu kwanta…”

Waheedah tai maganar tana katse wa Mami tunanin da take.

“Allah ya kaimu… Zamu fita kasuwa da Haj. Halima”

Kai Waheedah ta jinjina tana fadin

“Saikun dawo…”

Tsaye tayi har saida taga Mami ta fita daga dakin tukunna, daga nan cikin dakin tana jiyo hayaniyar mutane da yake nuna alamun bikin da zasu sha a cikin gidan, tun da satin ya kama ake hidima, babu kuma ranar da kanta baya mata ciwo, dan bawai tana son hayaniya bane, amman biki yara uku ita kanta tasan saidai suyi hakuri, Muhsin, Khadija da Babangida, da shi Babangida ma za’a daga, dan ginin shi ko rabi baikai ba, sai Kawu Hamisu ya bashi gida mai daki biyu ya zauna har Allah ya hore mishi ya kammala nashi.

Ita duk ba wannan bane a ranta, Abdulkadir ne manne da zuciyarta, zata iya cewa tun tafiyar shi da rana daya bai taba barin tunaninta ba. Lokutta da dama tana tashi daga bacci takanji kirjinta yai mata nauyi da tunanin halin da yake ciki, shekara daya akace zaiyi yazo gida, amman yanzun shekaru biyu kenan. Watannin baya kasa hakuri tayi, batasan lokacin da tambayar ko yana lafiya ta subuce mata a gaban Abba ba, shine ma yace mata yaje ya duba shi sau daya. Yana lafiya, tukunna taji tadan samu nutsuwa ta wasu fannonin.

Kan kujera ta zauna, niyyar kwanciya take, tunanin Suratul-Kahf da bata karanta ba na sauko mata, kasancewar ranar juma’a. Ta rigada ta saba data idar da sallar asuba take karantawa, yau din bata samu wannan lokacin ba, saboda ta taya Mami gyaran gidan da aka bata, dan duk wanda ya kwana, ana sallah suke ficewa su koma sashin Hajja. Tunanin taje ta dauko Qur’an din takeyi, Aminu ya shigo da sallamar data amsa mishi cikin sanyin murya

“Commander an diro…” 1

Ya fadi yana dariya, hadi da wucewa kitchen, muryar shi Waheedah take ji ta dira kunnuwanta da wani irin yanayi, kafin ma’anar kalaman nashi su zauna mata, zuciyarta taji ta fara tsalle-tsalle da take tunanin kashedi ne, dan yanda ta fara doka mata, in bata miqe ba, tanajin tsaf zata fito daga kirjinta tayi kafafuwan kanta ta fice daga dakin dan neman duk inda Aminu yace Abdulkadir din yake. Mikewa Waheedah tayi tana saka hannu ta dafe kirjinta, inda take jin zuciyarta na kara gudu da duk daqiqa. A bakin kofa ta zira takalman bandaki da batasan ya akai suka zo wajen ba. Manya-manya ne, karamar kafarta na yawo a ciki, amman bata ma kula ba. 7

Tafiya kawai take kamar wadda aka sakawa batira, kafafuwanta take takawa tana nufar bangarensu, badan sun taba doguwar maganar da tsayinta ya wuce mintina biyar ba, amman tanajin wata irin sanayya da tai mishi da take tunanin sai dai su goga da Hajja in akazo maganar sanin halayen shi. Abdulkadir din data sani bazai shiga cikin gida ba, idan wani ne daban ya shekara biyu baya gida, yana zuwa bangarensu zai wuce yaga mahaifiyar shi, banda Abdulkadir, zai iya jira, daya shiga hayaniyar da take bangaren Hajja gara ya jira. Tana da tabbacin yana bangaren su.

STORY CONTINUES BELOW


Nan kuwa kafafuwanta suke daukarta, bayan shi ta fara hangowa, zata rantse da Allah ba girma kawai ya kara ba, harda tsayi, jakace rataye kan kafadar shi, rigar jikinshi ta kamashi kamar zata bude, damtsen hannun shi tabi da kallo daya kusa yar siririyar cinyarta. Sosai take takawa, bugun zuciyarta na karuwa, wani irin dumi taje ji jikinta ya dauka kamar zazzabi na shirin kamata. Tsaye tayi a bayan shi tana kasa motsa labbanta, hannunta daya na kan kirjinta kamar maison kare zuciyarta da take tunanin zata iya fitowa kowanne lokaci. 5

Hannun shi Abdulkadir yakai yana sake kwankwasa kofar, yana jiyo kidan da suka kunna har nan inda yake tsaye. Tsaki yaja yana addu’ar wanda zaizo ya bude kofar ya kasance kasa yake dashi, yanda zai zabga mishi marin tsayuwar da yasha a bakin kofa, in ba wulakanci ba, ya zasu kunna kida su kuma kulle kofa daga ciki. Yana shigowa gidan ya fara dana sanin zuwa. Baisan meye a maganganun Yassar da sukanyi tasiri akan shi haka ba, amman saiya sauke mishi sakashi zuwan da yayi. Bayason hayaniya irin haka, saboda yasan dole sai wani ya bata mishi rai, ga hannun shi yana saurin tashi, yanzun abin harya fi nada. 3

Yana sane yaqi zuwa hutun sallar da sukan zo na kwana biyu ko uku in yayi tsayi. Bawai dan baiyi kewar gida ba, sosai yake jin kewarsu, musamman Hajja da Zahra, babu wanda yagani tunda ya tafi daga Abba da sai Yassar. Dan shi kusan duk wata biyu sai yaje ya duba shi, kafin ya tafi kuma duk zuwan da zaiyi sau sunyi fada. Saida yaja dogon tsaki tukunna ya kara kwankwasa kofar da karfi wannan karin. Alama yaji ta cewar akwai mutum a bayan shi, kafin ya tsayar da hankalin shi waje daya, yanajin shiga da fitar numfashin Waheedah da takeyin shi a tsorace.

Juyawa yayi gabaki daya, yana tsorata Waheedah da take tsaye, ta kuwa yi baya gabaki daya, cikin zafin nama ya riqo hannunta, saida yaga ta tsaya da kafafuwanta tana ware mishi idanuwanta da suke cike da tsoro tukunna ya saki hannunta, yana mamakin yarinyar daya bari ce a gaban shi, komai ya canza tattare da ita banda farinta, runtsa idanuwan shi yayi yana sake bude su akanta, tayi wani irin girma naban mamaki, farin da rashin kibar yana nan, sai dai za’a iya kiranta da budurwa, duk da a idanuwan shi tana nan a yar yarinyarta. 2

Waheedah kuwa dayan hannunta ta saka tana kama wanda Abdulkadir ya saki, zuciyarta naci gaba da lugude a cikin kirjinta, numfashinta ma kokawa take dashi cikin yanayin da kusanci dashi haka kadai yake bayyanawa, sosai ya canza mata, kuma ba askin kanshi kadai bane yasa fuskar shi canza mata, dan ya aske shi qasa sosai, Abdulkadir da yake tara suma, fuskar shi tai mata fayau da askin da akan kira buzz a turance. Ga tabbai qananu a fuskar da batasan yanda akai yaji su ba. Tabon da yake gefen goshin shine kawai tsohon abu a fuskar shi, dan tasan dashi tun kafin ya tashi.

Idanuwanta ta sauke zuwa wuyan shi, inda yake da wani dogon tabo daga gefen mummuqen shi zuwa wuyan, yana bace ma ganinta daga inda rigarshi ta lullube, wani abu na matsewa a zuciyarta, hannunta takejin yana mata kaikayi haka kawai, so take ta kaishi kan tabon da alamu suka nuna sabone sosai, ta kuma kirga duka qananun da take gani kan fuskarshi, yanda inya sake dawowa zata ga ko yaji wani sabon ciwon ko baiji ba. Kofar da Abdulkadir yaji an bude yasa shi dan juyawa, kafin ya sake juyowa yana mayar da hankalin shi kan Waheedah.

Yana mamakin yanda ta tsaya tana kallon shi, kamar tana son bude har tsokar jikin shi taga ko yana boye wani abu cikin kasusuwan shi, yana kuma mamakin tsoron da yake cikin idanuwanta bai hanata kare mishi kallo haka kamar ta aike shi ba, batun yanzun yake kula da ita ba. Ko abu su Zahra suke son tambayar shi ita din suke sakawa, haka zata kalle shi cike da tsoron shi da baya hanata yi mishi tambayar, karfin halinta bazai gaji da bashi mamaki ba. Baisan dariya mai sauti ta kubce mishi ba, saida yaga yanda ta hadiye wani abu da yafi karfin yawu

“Hamma…”

Ta furta, muryarta can kasan makoshi, idanuwa Abdulkadir ya kafeta dasu, yana sata sake hadiye wani abu da take ji tokare da makoshin ta. Zata rantse tanajin zuciyarta ta yunkuro mata da tambayar da ta jima tana ma iska a dakin su, tunda shidin da take son tambaya baya nan.

STORY CONTINUES BELOW


“Shekara daya akace Hamma…. Shekara daya akace zakayi kazo… Me yasa ka dade?” 1

Wata gajerar dariyar Abdulkadir ya tsinci kanshi da sakeyi

“Shine gaisuwar?”

Ya bukata, muryar shi na nutsar da gudun zuciyarta. Ta dauka girman shi zaisa muryar shi ta canza ko ta kara budewa, tana nan yanda tasanta, shidinne kawai ya canza a bayyane. Dan murmushi taji ya kwace mata

“Ina wuni…”

Kai Abdulkadir ya girgiza kawai

“Ki kawomun abinci”

Ya fadi maimakon amsa gaisuwarta, ya juya yana sa hannu ya tura kofar, akan ce idan ka girma, rana da abubuwa nasa haskenka yadan dishe. Bayajin ko wahala zatasa Waheedah dishewa, da tunanin farinta da yakeji cikin idanuwan shi har lokacin ya shiga dakin yana fadin

“Uban waye ya kunna kida ya kuma kulle kofa daga ciki?” 2

Ya karasa maganar yana kare musu kallo, dakin kusan cike yake da mutane, bakin fuskar da bazai wuce dukan su ahalin Bugaje bane ba, dan ga kamannin nan yana gani, wasu kuma ya gane su.

“Ubanka ne, nace ubanka ne ya kunna”

Abdulkadir yaji muryar Yassar cikin kunnuwan shi, kafin yaji hannun Yassar din kan wuyan shi dayai ma wani irin riqo da yasa Abdulkadir din riqo hannun Yassar daya kasa banbarewa 1

“Hamma zaka kasheni…me yasa kakemun hakane a gaban yara… Ka sakeni dan Allah”

Abdulkadir yake fadi, yana raina karfin shi da yake tunanin ya karu saboda yanayin horon daya samu a makaranta.

“Daga zuwan ka, shisa babu wanda yai kewar ka” 3

Cewar Yassar daya saki wuyan Abdulkadir din yana tallabe mishi bayan kai

“Dan banzan yaro kawai”

Idanuwa Abdulkadir ya sauke kan Salim da yake kallon shi yana murmushi

“Idan na karaso saina tabbatar labbanka sunyi kumburin da zaka kwana biyu bakai murmushi dasu ba” 5

Mikewa Salim yayi yana wucewa dakinsu, ba akan shi Abdulkadir zai fara sauke kurar NDA daya kwaso ya shigo da ita ba. Dariya Yassar yakeyi, Abdulkadir din ya wuce bayan ya watsama duk wani da suka hada ido dashi a cikin dakin harara. Dakin shi ya wuce yana murda kofar yaga ta bude. Shiga yayi da takalman shi, dakin a share yake, sai dai akwai kaya kan gadon, juyowa Abdulkadir yayi da nufin zuro kai yaji wanda ya shigo mishi daki ya zuba mishi kaya akan gado. 1

“Nine, ni nake kwana a dakin da aka fara hidimar biki…”

Yassar ya fadi muryar shi dauke da gajiya da rikicin Abdulkadir da baya karewa. Yana yawan zuwa dubo shi a makarantane, tun ranar farko da yaje yaga halin da yake ciki, yasha wani irin duka ga zazzabin da yake da tabbacin dukanne yasa mishi shi, gashi ya rame sosai, daya dawo gida har kuka yaima Abba da fadin yaje ya dawo da Abdulkadir din, tunda zama sojan ba wahayin shi aka saukar mishi ba. Dan yana da tabbacin rashin kunya da bakin shi zaisa su mishi dukan da zai ajalin shi wata rana. Abba yace shi yaji zai iya, abar shi, kilan sanadin sojan yasashi fara ganin kan mutane da gashi.

Amman hankalin Yassar din ba’a kwance yake ba, bazaiki ace kullum yaje ya duba halin da yake ciki ba, yaji dadi ma yanzun da wayar hannu ya yawaita, ko bakaje kaga mutum ba, zakaji muryar shi, amman zai karya idan yace baya addu’ar kar Abdulkadir yai abinda zasuyi mishi dukan mutuwa a NDA din nan, dan yaga alama abin babu sauqi.

“Kaine mutum na farko da zan kulle ko kwana biyune Hamma, saboda kana mun abinda kake so a gaban yara” 2

Abdulkadir ya fada babu alamar wasa a muryarshi, hannu yaga Yassar ya kawo, da sauri ya rufe kofar yana dariyar daya manta rabon da yayi irin ta. Kan gadon ya karasa yana kwanciya, kafafuwan shi a kasa, duk da ba takalman bane suka hana shi dora kafafuwan kan gadon, ra’ayin kwanciyar a haka kawai yake ji. Iskar gida kanta daban take data NDA, gyara kanshi ya sakeyi, farar rigar Yassar dake gefe nasa Waheedah fado mishi, badan kalar nata farin iri dayane da rigar ba, ko kusa basuda alaqa, kawai ya tsinceta a ranshi ne, yafi alaqanta hakan da jiran da yake ta kawo mishi abinci, dan yunwa yake ji ta fitar hankali.

STORY CONTINUES BELOW


**

Kitchen ta koma, tana jinta kamar akan iska take tafiya, tanajin yanda zuciyarta ta lullube mata wani nishadi da idan tabari ya fito fili tsalle-tsalle zata fara kamar karamar yarinya, ba tana cikin kunci bane a shekaru biyun nan, sosai take zagaye da yan uwanta da suke sakata farin ciki, amman nishadin da take ji yanzun ganin Abdulkadir dinne kawai yake bayyana shi. A litattafan Hausar data karanta taga soyayya kala daban-daban, shisa ta sakama kusancin da takeji da Abdulkadir ayar tambaya, dan har yanzun batajin yana da suna a zuciyarta. Dan abinda takeji akan shi yasha banban da duk wata soyayya da take gani a litattafai.

Abinda takeji akan Abdulkadir batasan tun yaushe ya fara ba, kawai bude idanuwa tayi a kusa dashi taji zuciyarta na wata irin dokawa, idan sone ya kamata ta fara tunanin koshi yanajin kalar kusancin da takeji akan shi, amman har kasan zuciyarta bata damu dako yanaji ko bayaji ba, asalima tanajin yanda nata ya ishesu su biyun. Kuma tana jin tsoron shi kamar yanda su Zahra suke jin tsoron shi. sai dai akwai wani karfi da yake tasowa daga zuciyarta koda yaushe yana danne tsoron in tana son magana dashi.

Da murmushin daya kasa barin fuskarta take zuba mishi shinkafa da miyar da Mami ta girka, ta kuma san saboda Amatullah ta dafa, dan ba zataci abincin da batasan waya dafa ba, haka zata wuni tana shan shayi, kyankyamin da yarinyar take dashi har mamaki yake bama Waheedah. Salak ta zuba mishi a gefe da su tumatiri da ta yayyanka harda kokomba. Batasan waye da waye baici abinci ba, amman naman dake miyar kusan fiye da rabi ta zuba ma Abdulkadir din. 1

“Tunda shi baqone…” 3

Ta furta ma kanta, Allah kadai yasan kalar abincin da suke ci acan, gara yau yasan yazo gida. Babban faranti ta samu ta dora karamin a ciki tana rufewa, tukunna tasa cokali a gefe. Ruwa ta daukar mishi da kofi duk tasa cikin farantin tukunna ta dauka tana ficewa zuwa bangaren su Abdulkadir din, saida ta kwankwasa suka ce ta shiga tukunna ta cire takalmanta a wajen ta shiga.

“Ina Hamma Abdulkadir?”

Tai tambayar tana kallon Naziru daya nuna mata dakin Abdulkadir din da dan yatsan shi, yana mayar da hankalin shi kan kallon da yake, dan shi kadai ta samu a falon ma, da alama kowa ya fice hidimar gaban shi. Abinda bata sani ba shine Abdulkadir ya fito ya zare wayoyin speakers din da suka kunna kidan dashi, da yaji bai hana kidan yi ba, yaje ya raba extension din da kayayyakin suke jone da socket din dakin gabaki daya yana zubarwa a kasa ya juya ya koma daki baice ma kowa komai ba. Yassar ne yace su hakura kawai su kyale shi, shisa kowa ya fice daga dakin, shi kanshi Nazir din sai gaban tv din ya koma sosai dan ya rage maganar tayi kasa yanda kunnuwan shine kawai zasuji.

Wucewa Waheedah tayi, tana kwankwasa dakin

“Shigo…”

Abdulkadir din ya fadi, a hankali ta tura kofar tana shiga hadi dayin sallama, tashi zaune Abdulkadir yayi yana kasa hakuri data ajiye mishi farantin, yasa hannu ya karba, a kan cinyar shi ya dora yana budewa hadi da saka cokali a ciki ya fara cakuda gefe, tukunna ya diba yana zubawa a bakin shi. Yanda ya sauke numfashi nasa Waheedah jin da tana da iko kullum saita aika mishi abinci Kaduna. Tasan ya kamata ta tafi, amman kafafuwanta kamar an dasasu a wajen, bayanta ma ta jingina da bangon dakin tana kallon yanda yake cin abincin da sauri-sauri. Abinci ya mishi dadi sosai, bai damu da tsayuwar da Waheedah din tayi ba, ko kofar dakin data bar mishi a hangame. Haka kawai yaji ya kasa ce mata tsayuwar me take mishi a dakin har lokacin.

Batasan meyasa takejin son mishi magana haka ba, jikinta har dumi yake dauka da yanayin son mishi maganar

“Dame kaji ciwo Hamma?”

Ta tambaya, yanda yadan tsaya, kafin yakai cokalin abincin bakin shi yana juyowa ya sauke mata kananun idanuwan shi yasa zuciyarta dokawa cike da tsoron shi da bai hanata sake fadin

STORY CONTINUES BELOW


“Yaushe zaka tafi?”

Abincin Abdulkadir yake taunawa a nutse, inda wani ne ba ita ba, zaiji kamar ya raina shi da yawa da har zai tsaye yana jero mishi tambayoyi, amman a muryarta yake jin yanda tsakaninta da Allah tayi tambayar, babu raini kowani abu, kawai tana son sani din, amman daga haka raini yake farawa, shiru yayi ya kyaleta yana cigaba da cin abincin shi

“Sune basa barin ku zuwa? Ko kaine kawai kaqi zuwa? Hamma kaga wani tabon fa har a gefen kuncinka… Dame kaji ciwuka haka dan Allah?” 3

Waheedah taci gaba da jero mishi tambayoyin da take jin suna fito mata a sauqaqe, kamar sun shekaru masu yawa a tare dashi, kamar tayi sabon da zatayi labari dashi mai tsayi batare da fargabar komai ba haka take jinta, duk da a kasan zuciyarta wani abu yake fada mata ba amsa zata samu ba, itama ba tana tambayar shin bane dan ya amsata, tana tambayar ne kawai saboda tana son magana dashi ko da bazai amsa ba, indai yana jinta ya isheta.

“Ko kun fara fita aikin soja ne?”

Ta bukata, tana ware idanuwanta, zuciyarta cike da wani sabon tsoro da tunanin abinda hakan yake nufi

“Hamma kun fara zuwa yaqi ko? Inalillahi wa ina ilaihi raji’un…oh Allah na… Ko harbine tabon wuyanka? Oh Allah na” 4

Cokalin Abdulkadir ya ajiye cikin abincin shi yana fadin 1

“Fitar mun daga daki Waheedah…” 3

A daburce tace

“Na’am…”

Dan tunaninta yayi nisa cikin kalar tashin hankalin da take gani a fina-finan sojojin da take cikin kallo yanzun duk idan ta samu lokaci. Yazid kanbar mata laptop dinshi inya samo, saita kalla a ciki.

“Ki fitar mun daga daki kafin in watsa miki mari” 2

Abdulkadir ya fadi can kasan makoshi, saboda dariya na gab da kwace mishi, yana kallon tsoron da ya cika idanuwanta kafin ta fice da sauri kamar zata fadi, saida ya tura kofar tukunna wata irin dariya ta kwace mishi, yana mamakin yanda Waheedah ta kasance mai hankali kuma marar hankali duk a lokaci daya. Hannu yasa ya shafi tabon da haukanta yake mata tunanin na bindiga ne. 5

“Wai yaqi…”

Ya fadi yana karayin dariya

“Wallahi Waheedah bata da hankali… Yaqi fa” 3

Abdulkadir din yake maimaitawa har lokacin yana dariyar da yakejin fitowarta tun daga zuciyar shi. Abincin shi ya karasa cinyewa tas yasha ruwa, tukunna ya ajiye farantin a kasa, gani yai uku da kusan rabi, hakan yasa shi mikewa ya kwance takalman kafar shi, tukunna ya shiga bandaki dan ya dauro alwala, fuskar shi ya kalla a mudubi, murmushin da yake bayyane a jikinta nasa shi janye idanuwan shi daga kan mudubin, dan yanayine da ya zame mishi baqo, ya kwana biyu baiyi nishadi irin nayau ba. Tsintar kanshi yai da murmushin har ya idar da alwala ya fito, waje ya samu ya zauna yana jira a kira sallah dan ya wuce masallaci.

*

Dinner zasuyi da daren ranar, duk da Abba ya nuna duk wannan bidi’ar bason ta yakeyi ba, haka ya hakura ya kyalesu ganin sun kafe. Dogayen riguna ne sukai anko iya su yan cikin gidan, material din wine color, yayi matuqar kyau. Mami tai ma Nuriyya ankon da duk sauran dinkunan da taima Waheedah. Yanzun ma tare duk suka fito da za’a tafi, yanayin dinkin ya zauna ma Nuriyya sosai, da wahala ta gitta baka sake kallonta ba, ko dan kwalliyat data sha, kusan duka yan gidansu Waheedah din Nuriyya tai musu kwalliyar su, ga kunshi ansha, kamar sune amaren. Nuriyya ta rataya mayafinta a kafada, yanda su Zahra ma sukayi. 4

Itakam Waheedah fuskarta fayau take, banda hoda data murza sai Vaseline data shafa ma labbanta, daurin dankwalinta ma mai sauqi tayi, saidai kalar kayan ta amshi farar fatarta, ta yafa qaton mayafinta a kafadunta duka biyun, duk da haka wani iri takeji, wuyanta da yake a bude, itakam wannan mayafin asarar kudine, dan tasan ana gama bikin zata ajiye shi, tafi gane hijabanta. Motar da za’a dauke su ciki ta cika tsaf, bata samu waje ba. 1

“Yanzun dan Allah saiku tafi kubarni?”

Waheedah ta fadi cikin sanyin murya, tana dorawa da

“Nuriyya dan Allah ki rungumeni…”

Dariya Nuriyya tayi

“Ki yamutsemun riga? Wallahi bazai yiwu ba” 2

Sake marairaicewa Waheedah tayi

“Toni ki tashi in rungumeki”

Maryam, yar yayan Abba dake zaune gefen Nuriyya ta kwashe da dariya.

“A wacce cinyar zaki rungumeta? Mansur muje dan Allah…” 1

Maryam ta karashe maganar tana miqa hannu ta ja murfin motar dan taga alamar in suka biyema Waheedah zasu kara bata lokaci, ba zata rasa wanda zata biyo ya kawota ba. Kuma za’a daddawo daukar sauran mutane dole daman. Waheedah din kanta tasan hakan, kawai dai taso ta bisu dinne tunda duk sa’anninta na cikin motar, ga Nuriyya kuma, kafin dai ta gama sanyin jiki duk sun shige, tsaye tayi a wajen tana jin idanuwanta sun cika da hawaye.

“Waheedah ke baki tafi ba?”

Taji muryar Yazid, juyowa tayi, kwalla cike da idanuwanta

“Wai ba waje…”

Dariya Yazid yayi, yarinyar bata da wahalar kuka ya kula, sai dai akwai wani abu tattare da sanyin halinta da yake ji har kasan zuciyar shi. 4

“Yanzun Abdulkadir zai fito, saiku wuce tare…ina zuwa zanyi abu”

Yazid ya karasa yana wucewa da sauri, aikam Abdulkadir dinne ya fito, jikin shi da shadda ruwan toka mai cizawa, ta manta ranar karshe data ganshi da manyan kaya, sosai taga yai mata kyawun da taji yasa zuciyarta ta matse waje daya. Sai kamshi yake zabgawa, hular da take hannun shi ya saka saman kan shi yana karasowa inda take, ya miqa mata wallet din shi da agogo yana da links din hannuwan rigar

“Riqe mun…” 2

Hannuwanta biyu ta ware mishi ya saka a ciki, yana daukar link guda daya ya fara sakawa a jikin hannun rigar yana zabga tsaki

“Meyasa Hamma zaimun wannan hannun shirmen?”

Da sauri Waheedah tace

“Kawo in sa maka?”

Kananun idanuwan shi ya kara kankance mata

“Kin iya?”

Kai ta daga mishi, kayan hannunta ya karba, yana miqa mata dayan hannun shi, kamawa tayi tana dan rausayar da kanta gefe

“Saika dago hannun ka”

Ta fadi a hankali, gyara mata hannun Abdulkadir yayi yana kallon yanda ta nutsu tana saka mishi link din, sai yaga kamar tafi dazun yi mishi haske, ko dan kwan fitilar da ya haske mata fuskane, bai sani ba.

“Dayan hannun…”

Cewar Waheedah tana jin wani gajimare na mata yawo a kanta. Miqa mata Abdulkadir yayi yana ware mata tafin hannun shi ta dauki link din. Saka mishi tayi, sai ya tsinci kanshi da miqa mata agogon, karba tayi ta daura mishi, wallet din ya miqa mata, yasan yana da aljihu a wando da rigar kayan da suke jikin shi, kawai yanajin bata ta riqe mishi ne. 4

“Kin shirya? Muje?”

Ya tambaya, tana daga mishi kai, harya numfasa yai mata maganar ta bude bakinta ta amsa shi, saiya tuna Waheedah ce, ta saba amsa mishi magana da kai, saboda shiya saba kyaleta duk idan tayi. Wucewa kawai yayi tana bin bayan shi, saida suka karasa tukunna taga dayar motar Abba ce zasu fita a ciki, zagayawa Abdulkadir yayi yana bude motar ya shiga, harya kunna baiga alamar Waheedah zata shigo ba, numfashi ya sauke yana rasa kalar Waheedah, kafin ya miqa hannu ta ciki ya bude kofar, yana ganin tayi baya tana murza hannunta da alamar ya bugeta.

“Sai nace ki shigo?” 1

Ya bukata a fadace, yanajin gajiyar da baisan daga inda ta fito ba. Idanuwanta take ware mishi, dan taji ba cayai ta shiga din ba, tambayar ta yayi, kai ta girgiza mishi a hankali, da alama tana jiran ya bata umarni ta shiga din tukunna, numfashi ya sake saukewa a karo na farko, bayajin zai iya masifa 2

“Shigo Waheedah…”

Ya fadi da gajiya a muryarshi, shigowar tayi, tana rufe murfin kofar, tana jin yanda kamshin da yake ya cika motar…!Idan akwai abinda yakeyi a nutse a rayuwar shi bai wuce tuqi ba, ko Yassar daya koya mishi tuqin idan zasuje wani waje yakan ce mishi +

‘Abdulkadir kana taka mota kaman zata cijeka. Dan Allah ka kara gudu’

Shikam baiga saurin da yake ba. Yanzun ma a nutse yake tuqin shi, kamar yanada duka lokacin da yake bukata. Waheedah kuwa ta nutsu a gefe tana wasa da wallet din shi da take hannunta, zuciyarta na doka mata a kirjinta kamar zata fito waje. Ga shirun da yake cikin motar da take jin kaurin shi kamar tasa hannu ta dangwalo yai mata yawa. Rasa abin yi yasata balle maballin da yake jikin wallet din tana wasa dashi. 2

“In kika lalata mun saina zane jikin ki” 1

Abdulkadir yai maganar hankalin shi nakan tuqin da yakeyi, dan yanajin yanda maballin yake bas bas duk idan ta bude ta sake rufewa, yasan wasa take dashi. Badan ba zaiyi abinda yace din ba, ya zaneta tasan ba wani abu bane, ba zai zama ma farko ba, bata dai san dalilin da yasa maganar shi ta bata dariya ba.

“Na zama sa’anki ko?”

Ya buqata jin sautin dariyarta, bata amsa ba, bai kalleta ba kuma har lokacin, amman yasan kai take girgiza mishi. Bata mayar da maballin jikin wallet din ba, hakan yasata budewa tana sa hannu ta shafa wajen da taga alamar I.D card dinshi ne, hannu tasa ta janyo tana kokarin ganin hoton da yake jiki, sai lokacin Abdulkadir yadan juya ya kalleta, yana mayar da hankalin kan tuqin da yakeyi, yaga yanda take daga I.D card din wajen gilas din kofar dan tagani, hannu ya miqa ya kunna fitilar dake cikin motar yana sata rufe idanuwanta ta sake budesu da wani yanayi dayake nuna bata tsammaci hasken daya gauraye gaban motar ba. 1

Tukunna ta kalli Abdulkadir din da idanuwan shi suke kafe kan titi, numfashin da batasan dalilin shi ba ta sauke tana mayar da hankalinta kan ID card din da yake hannunta taci gaba da dubawa, dan yatsanta babba na shafa kan hoton shi da yake manne a gefe. Mayar mishi da ID card din zatayi wajen data ciro shi taga dan qaramin hoto a wajen tasa hannu ta zaro tana karema hoton da alamu suka nuna bai jima da daukar shi ba, dan askin da yake kanshi yanzun shine a jikin hoton. Wani abu dayai mata tsaye a makoshinta take kokarin hadiye wa amman yaki tafiya 2

“Hamma…”

Ta kira muryarta can kasan makoshi, saida tai tunanin bazai amsa ba tukunna yace

“Menene?”

Dan yaji ta kira sunan shi, bai amsa bane yana jiran taci gaba da magana, jin tayi shiru yasa shi amsawa, yasan zasu iya kaiwa inda zasu kai batai maganar ba tana jiran saiya amsa ta. Dan gyara zamanta tayi tana kallon Abdulkadir din, gudun zuciyarta na karuwa da tambayar da take shirin yi mishi, kafin ta tattaro duk wani kwarin gwiwar da zata iya tace

“In dauka?” 3

Dan daquna fuska yayi duk da bai kalleta ba, yanayin nasa idanuwan shi qara kankancewa

“Meye?”

Numfashi taja a hankali tana sauke shi da fadin

“Wannan hoton?”

Sake rage gudun motar yayi yana dan kallon hoton da ta nuna mishi, dan yasan akwai qananun hotuna da yawa a cikin wallet din tashi, baisan kowanne take cewa ta dauka ba, hoton ya kalla, da alamu a kafadarshi da yake nuna yana therma III yanzun a NDA, hoton bai dade ba, kafin ya taho din nan ne ya dauka, shine hoton shi na karshe dayai zuwa yanzun. Fuskar shi har lokacin a daqune take, kan titi ya mayar da hankalin shi yana kara gudun motar yanda yake da kafin ya rage. Ba tambayarta bace ta bashi mamaki, baiga me zatayi da passport din shi bane ba, hoton dako kyau baiyi ba.

Zuciyarta take ji ta dawo makoshi saboda gudun da take, amsar shi take jira, in yace karta dauka zata mayar ta ajiye mishi, tun da daga farko ma batasan meyasa ta tambaye shi ta dauka din ba, ta ciro hoton kuma taji tana son kasancewa dashi, tana son samun wani abu daga wajen shi kafin ya sake tafiya, tunda ba ranar dawowa gare shi ba. Wani abu da zai riqeta harya sake dawowa. Batasan kalaman da zatai amfani dasu su fassara dalilinta ba, kusan hakan dai shine abinda take ji.

STORY CONTINUES BELOW


“Kaji Hamma… In dauka?”

Ta tsinci kanta da sake fadi, dan daga mata kafada Abdulkadir yayi yana juya steering wheel din ya sha round din dake gaban shi, jitai wani abu na narkewa a zuciyarta da batasan akwai shi ba, yanayin shi da abinda yai da kafada nasa numfashin ta yi mata barazana. Dakyar ta iya cewa 1

“In dauka?” 1

Wannan karin Abdulkadir dinne ya sauke numfashi

“Komai ne sai nayi surutu?”

Dan murmushi tayi

“Baka ce in dauka ba ai…haka kayi da kafadun ka”

Ta karasa tana daga nata cikin son nuna yanda yai da nashin. Kai kawai Abdulkadir ya girgiza dan sun karaso wajen da Yazid din yai mishi kwatance za’ayi dinner. Baiyi tunanin zai gane ba, sai dai yawon da suke sha a garin Kano ba dan kadan bane ba. Waje ya samu yayi parking yana bude motar ya fice. Hoton Waheedah ta mayar inda ta dauko shi, tukunna ta bude murfin motar itama tana ficewa. Sai da yaga ta fito tukunna ya rufe motar ya soma tafiya, bin bayan shi Waheedah tayi dan gani tai yana sauri sosai

“Kaji Hamma, in dauka?” 2

Take fadi tana mayar da numfashin daya sashi juyawa ya kalleta, sauri take kamar zata fadi tana kai hannu daya ta dafe mayafin dake jikinta, dayan riqe da wallet dinshi tana kokarin tattare doguwar rigarta ko zata kara sauri, juyawa yayi yanajin murmushi na shirin kwace mishi, bai taba ganin kalar Waheedah ba, baisan meyasa yaji yana so ya kure rashin hankalinta ba. Sauri ya kara yana bi ta duk inda yaga turmutsun jama’a duk da ga hanya nan dazai iya wucewa, sai da yai wajen mintina biyar a hakan har yana hango kofar wajen tukunna ya tsaya yana juyawa, hangota yai can cikin jama’a an matse ta, sai kokarin turmutsowa take da hannuwanta da suke mishi kama da sandar siririn rake. 1

Murmushin da yake ta dannewa ne ya kwace mishi, kai ya girgiza

“Wallahi yarinyar nan bata da hankali…” 1

Abdulkadir ya fadi yanajin nishadin da ya rasa daga inda yake fitowa, komawa yayi baya dan yaga alamar mutane na gab da ture Waheedah ta fadi kasa, in wani ya takata yana da tabbacin karyewa zatai bal, hannunta ya kama yana janta, banda maida numfashi babu abinda takeyi, hanyar da babu mutane yabi da ita, dakyar take tafiya saboda batasan wahala irin wannan a rayuwarta, dakyar ta iya cewa

“Hamma sauri kake kamar zaka tashi sama wallahi….”

Dariya yaji ta kubce mishi

“Lalaci ne yai miki yawa”

Ya fadi yana ci gaba da janta, binshi take da duk saurin da zata iya har suka shiga wajen daya qawatu babu laifi tukunna Abdulkadir din ya rage saurin da yakeyi yana sakin hannunta, numfashi ta mayar tana fifita fuskarta da wallet din shi saboda zufar wahalar da take jin tanayi. Kankance idanuwan shi yayi a kanta, kafin ya mayar da hankalin shi kan harabar wajen yana nemo tebir din da yaga babu kowa da kuma kujerar mutum hudu tukunna yaja hannun Waheedah batare daya damu da mutanen dake binsu da kallo ba suka karasa wajen, kujera daya yadan ja baya yana jan hannunta ya zagaya da ita, zama tayi dan tagaji kam.

Ta gefenta Abdulkadir ya zagaya ya zauna yana kallon yanda take mayar da numfashi. Hannunta Waheedah ta sauke kasan tebir din tana murzawa da dayan, tana jin kamaf Abdulkadir yabar mata shatin nashi hannun a wajen da yanayin dayai mata tsaye a zuciya.

“Bakace in dauka bafa” 3

Ta fadi tana kallon Abdulkadir daya dauki robar ruwan da take ajiye a wajen yana murzawa da nufin budewa da alama. Kananun idanuwan shi ya kafeta dasu da yasata sauke nata idanuwan, zuciyarta naci gaba da tsalle a cikin kirjinta. Ruwan shi Abdulkadir ya kwance, yana son ganin yanda tsoro kan cika idanuwanta, kai robar yai bakin shi yana shan ruwan sosai tukunna ya mika robar kusa da Waheedah yana fadin

STORY CONTINUES BELOW


“Ki sha ruwa…”

Hannu tasa ta dauki robar ta cire murfin dabai daure ba sosai tana kaiwa bakinta ta kurbi ruwan tukunna ta mayar ta rufe, ba kishi take ji ba, tasha ne kawai dan yace tasha, dan shine ya bata bazata iya ce mishi batajin kishi ba. A hankali ta ajiye robar tana soma kalle-kalle ko zata hango su Nuriyya. Amman ko alamun su bata gani ba. Yazid ne ya karaso wajen yana jan kujera ya zauna hadi da fadin

“Kai jama’a, wallahi jikina ciwo yake mun”

Kallon shi Waheedah tayi cike da tausayawa, abinda yafi ciwon jiki ma tasan zaiyi, tunda hidimar bikin ta fara shi yake zirga-zirga. Cikin sanyin muryarta tace

“Sannu… Kaine baka huta ba ai Hamma…”

Murmushi yayi yana sauke idanuwan shi akanta, tun dazun ya kula da yanayin fuskarta kafin su taho, baisan lokacin da abinda yake ji ya fara ba, kawai ta gitta ta gaban shi ya tsinci zuciyar shi da doka mata. Tunda yazo wajen yake cin karo da yan mata kala daban-daban, dukkan su fuskokinsu dauke suke da kwalliya taban mamaki. Yanda tata take fayau ya mishi, lokaci zuwa lokaci taken sake gyara zaman mayafinta a kafadarta, ya kula da a takure take jinta saboda rashin hijab dinta 8

“Me yasa baki saka hijab ba?”

Ya bukata, bayason ganin yanda take a takure, dan murmushi tai mishi cikin yanayin sanyinta, baisan koshi kadai yake ganin kyanta ba, da dan bakinta da yasan mata da yawa zasu shafa abubuwa da dama dan kalar labbansu tayi ruwan hoda haka kamar nata, idanuwanta sunfi komai daukar hankalin shi a fuskarta, yanda suke maiqo kamar da hawaye a cikin su koda yaushe kan saka shi murmushi koshi kadai ne. 1

“Su Zahra zasu dameni”

Kai Yazid ya jinjina

“Ki daina yin abinda zaki takura saboda mutane…”

Kai Waheedah ta rausayar gefe, bazai fahimta ba, bata takura kanta bane saboda su, idan ta saka hijab din yanda zasu takurata zaifi yanda take a takure yanzun, ta zabi abinda yafi mata sauqi ne kawai. Abdulkadir hankalin shi ya mayar kan hidimar da ake wajen dinner din, ganin hirar Yazid din da Waheedah ta fara dakushe mishi nishadin da yake ciki. 6

*

Dan mudubin da ta saka a cikin yar jakar hannunta ta dauko tana saka shi ta karkashin teburin wajen ta duba fuskarta, kowa yace mata tayi kyau, daga yan gidansu Waheedah zuwa abokan wasan su da suka zo bikin, sai dai kamar koda yaushe akwai murya a kasan ranta da take fada mata kyawunta bai kaiba, kyawunta bazai tana isa ba, kamar yanda bazai cike mata gurbin abubuwa da yawa da bata dashi a rayuwarta ba. Ta jima tana tsara kwalliyarta yau, amman Waheedah na fitowa saita raina duk wani kyau da take tunanin tayi. Batasan menene a tattare da fuskar Waheedah din dako hodar kirki bataji ba. 8

Tana da tabbacin ba ita kadai take ganin wani sanyi da yake cikin idanuwan Waheedah a koda yaushe ba, yau dinma batare da wani yunkuri ba taga Waheedah din tayi kyau, da pink lips dinta da take jin kamar ta cire ta mayar a tata fuskar, duk da inta kalli yanda zubin kirarta yake takan ji sanyi ta wani fannin, duk kyan Waheedah da hasken fatarta ba zata nuna mata dirin jiki ba, duk da itama a sirantakarta Allah yai mata wadattacen cikar kirji da Nuriyya take jin bai kamace taba, yanda take siririya yakamata komai nata ya zamana a shafe, ta fito a asalin zanen lamba dayanta. 8

Tunda suka zo takan tashi ta yawata a cikin wajen ko zata ga Waheedah din, amman ko alamunta bata gani ba, yanzun ma zagayawar take tana dube-dube, kafin idanuwanta su sauka kan Waheedah din da take murmushi cikin yanayin da yakan kara mata kyau. Karamin tsaki Nuriyya taja, tana jin wani daci har a kasan zuciyarta da batasan daga inda yake taso mata ba. A hankali take karasawa, idanuwan mazan duk data gitta yana kanta, amman ko kadan bata kula dasu ba, gabaki daya hankalinta yana kan Waheedah da Yazid da alamu ya nuna hira sukeyi, akwai wani namijin tare dasu da batasan kowaye ba, saboda ya bata baya. 4

STORY CONTINUES BELOW


Takawa tayi harta karasa inda teburin yake tana fadin

“Inata neman ki tun dazun”

Saukar maganar Abdulkadir yaji saman kanshi, dan a bayan shi Nuriyya ta tsaya, gyara zaman shi yayi tukunna ya juya a hankali dan yaga wacce marar tunanin ce take mishi magana tsakiyar kai, batare dako sallama tayi musu na ballantana ta gaishe su tukunna tai maganar da zatayi, idanuwan shi ya fara saukewa kan fuskarta, kafin ya kankance su yana kare mata kallo, wani abu yake ji yana dokawa cikin kunnuwan shi daya rasa daga inda yake jin sautin shi, dan bashida alaqa ko kadan da kidan da yake tashi a wajen. 1

Zai karya idan yace bai manta da wata Nuriyya a shekarun nan ba, saurarawa yayi dan gane inda yake jiyo sautin, kafin yagane zuciya shi ce take dokawa a kirjin shi, alaqanta hakan yake da mamakin girman da yarinyar tayi.

“Baki iya sallama ba?”

Abdulkadir ya fadi har lokacin yana rasa dalilin da zaisa zuciyar shi ba zata daina bugawar da take ba. Ware idanuwanta Nuriyya take akan Abdulkadir din, batasan yazo ba, Waheedah batace mata yazo ba, duk da a shekarun nan biyu daya tafi, ta tabbatar babu wanda Waheedah take damu da zancen shi idan ba ita ba. Bata taba ganin shi cikin manyan kaya ba tunda take, ba tun yanzun yake mata kyau ba, hankalin data kara yasa kyawun nashi bayannar mata sosai yanzun. Gashi yayi wani irin girma. 1

“Hamma…”

Nuriyya ta fadi tana murmushin da Abdulkadir din yaji zuciyarshi ta kara gudun dokawar da take. 1

‘Tana da kyau’ 5

Wata murya ta fada a cikin kanshi. Sake kankance idanuwan shi yayi kamar zata iya karantar abinda yake tunanin akan fuskar shi, idan akwai abinda ya tsana a rayuwar shi bai wuce raini ba, yara kuma a shekarun su Nuriyya sukafi jin tashen raini, saboda kuruciyar girma na dibarsu, shi bai saba yima kanshi karya bane kawai, yaga tana da kyau, ya kuma yi acknowledging kyan nata a ranshi.

“Sannu da dawowa”

Nuriyya ta fadi tana shirin dorawa da

‘Yaushe kazo’

Yanda Abdulkadir din ya daure fuska ya hanata fito da maganar a fili, juyawa yayi batare daya amsa Nuriyyar ba hadi da gyara zaman shi, tukunna kamar an mishi dole yace

“Yawwa”

Wani abu Nuriyya taji ya tsaya mata a makoshi, har ranta taji dadin ganin nashi, ya tuna mata yanda yake mata kyau naban mamaki, a lokaci daya kuma ya tuna mata yanda daga kawar Waheedah da suke gaisawa kan dole bata wuce nan ba, bakuma zata taba wuce nan ba, batasan meyasa yanayin yai mata ciwo na gaske ba. Waheedah kuma Abdulkadir din take kallo, yanayin shi na nuna alamar gajiyar da yai da zaman wajen.

Inda idanuwan Waheedah suke Yazid yabi da kallo, kafin ya sake mayar da kallon shi kan fuskarta, yana runtsa idanuwan shi ya bude su hadi da kauda tunanin da yake shirin dirar mishi

‘Duka nawa Waheedah din take’ 2

Ya fadi a ranshi yana mikewa

“Ina zaka je? Yanzun fa kake fadin kagaji”

Waheedah tai maganar tana dauke idanuwanta daga kan Abdulkadir din

“Zan huta Waheedah…bari inzo”

Yazid ya karasa dan yaga ba’a fara rarraba abin ci a wajen ba, dare nayi, sunce kuma ba zasu jima ba sosai, ya kamata ayi abinda za’ayi a tashi kowa ya kama gabanshi.

“Wai ta ina kuka zauna, nima inata duba ku”

Waheedah ta tambaya, hararta Nuriyya tayi tana matsawa ta zauna inda Yazid ya tashi taja kujerar kusa da Waheedah sosai, dai-dai kunnenta tace

STORY CONTINUES BELOW


“Ko ko fadamun Hamma ya dawo”

Dan murmushi Waheedah din tayi, muryarta can kasa ta amsa Nuriyyar

“Bamu zauna bane shisa, kuma dawowar bazata yayi”

Dan tabe baki Nuriyya tayi, kamar rashin zaman su na hana Waheedah din mata zancen Abdulkadir, ba tun yanzun tagane Waheedah nason Abdulkadir din ba, ita daice har yanzun take son raina mata hankali kamar yanda ta saba, take nuna kamar bata san abinda take ji akan Abdulkadir din so bane. Ko dan tasan ba samun shi zatayi ba shisa take son nuna kamar batasan tana sonshi ba oho. Duk idan Nuriyya tai wannan tunanin takanji sanyi a ranta, a karo na farko Waheedah bata samu abinda take so ba, wannan karin itama zataji yanda zafin rashin samun komai da kake so yake. 9

Abdulkadir zaice ya kwana biyu wani abu bai gwada karfin halin shi irin yau ba, kokawa yake da idanuwan shi karsu kalli inda Nuriyya take zaune amman hakan na neman gagarar shi. Ita kanta Nuriyyan ta kasan idanuwanta take kare mishi kallo tana ganin yanda fuskarshi take a daqune babu alamar wasa ko kadan akanta. Zungurin Waheedah tayi da alamar su tashi subar wajen. Dan kallon Abdulkadir tayi itama, tana son zama dashi din ko ba zasuyi magana ba, tana kuma son zagayawa ta zauna cikin su Zahra dan nan ne kawai zatafi more bikin, wannan ne karonta na farko da ta taba zuwa wata hidimar biki.

Duk da anayi a dangin Abbah sosai, su Amatullah kanje harsu kwana, ita kam tana zama gida, duk da ko a fuska babu wanda ya taba nuna mata banbanci, kawai dai hayaniyar ce bata cika so ba. Mikewa Nuriyya tayi tana kara taba kafadar Waheedah din data mike itama, hakan naba Abdulkadir damar da yake nema ta kallon su biyun, sai dai idanuwan shi nakan Waheedah.

“Zamuje wajen su Amatu…”

Ta fadi tana kallon shi, kai Abdulkadir ya girgiza mata yana fadin

“Idan na tashi tafiya wallet dina fa?”

Sai lokacin Waheedah ma ta tuna wallet din shice a hannunta, bin hannun nata da kallo Nuriyya tayi wani abu na tokare mata kahon zuciya dan alamu sun nuna tare suka zo da Abdulkadir din.

‘Allah ya rabaki da naci Waheedah’

Nuriyya ta fadi kasan zuciyarta. Wallet din Waheedah take shirin mika mishi, yanda ya kafeta da kananun idanuwan shi nasata kasa motsa hannunta, kallonta Abdulkadir yake har saida ta koma ta zauna. Baisan dalilin shi na hanata tafiya ba, kawai yanda yakejin zuciyarshi na dokawa har lokacin cikin bakon yanayin daya kasa fahimta yasa bayason ya zauna shi kadai. Ganin ta Waheedah ta koma ta zauna yasa Nuriyya din fara shirin zama itama.

“Ki wuce inda zakije”

Abdulkadir ya fadi yana watsa mata wani kallo dayasa ta barin wajen batare data ko yima Waheedah sallama ba, ta tsorata sosai, ranta kuma inyai dubu ya gama baci, meyasa zaima Waheedah magana kamar tana da muhimmanci a wajen shi, ita kuma yai mata magana kamar ita din bakomai bace, yana nuna kamar Waheedah yar uwarshi ce, bayan babu wanda baisan agola bace a gidan nasu, itama din bakomai bace a wajen shi. Harta koma inda ta fito ta zauna ranta a bace take jinshi, bikin gabaki daya yagama fita daga ranta. 5

*

Numfashi Abdulkadir ya sauke da barin Nuriyya wajen, gabaki daya abinda yakeji baqone a wajen shi, bakuma zai yiwu yar mitsitsiyar yarinya kamar Nuriyya ta saka zuciyarshi wannan gudun ba, kawai dan tana da kyau. Baya son raini, komai tattare da Nuriyya na nuna mishi idan ta samu fuska zata raina shi.

“Sai muzo tare ki tafi kibarni…”

Yai maganar yana kallonta, a lokaci daya yana rasa yanda akai ita kadai take ganin bangaren shi haka, yanda yakejin ita kadai zai iya nuna ma bangaren shi haka batare da tunanin zata raina shi ba. Dan kallon shi Waheedah tayi tana sauke idanuwan ta dan akwai wani abu tattare da nashi idanuwan da yake karya duk wata garkuwa ta jikinta, komai tattare da Abdulkadir daban take ganin shi. Batasan me zatace mishi ba, dan haka shiru tayi kawai tana lafewa cikin kujerar da take zaune a wajen.

STORY CONTINUES BELOW


Abinci aka kawo aka ajiye kan teburin da suke zaune, abincine wajen kala uku a cikin faranti daya, sai tsire a tsinke, harda hadin salad a gefe, a koshe Abdulkadir yake jin shi dan yaci abinci kafin ya fito, tsiren kawai ya dauka yana ci, kallon shi Waheedah takeyi harya cinye, nata tsiren ta dauka daga cikin plate dinta ta sake dorawa a nashi batare da tace komai ba, kallonta Abdulkadir yayi, ba dokawa zuciyar shi tayi ba, dumi yaji ta dauka wannan karin, hannu yasa ya dauki tsiren baice komai ba ya fara ci. 12

Lemo Waheedah ta dauka na roba da aka ajiye musu guda biyu, bata taba ganin shi da coca-cola ba tunda take, hakan yasa ta sanin ba zabin shi bane, dan haka ta bude mishi sprite din tana daukar abin zuqa ta saka a ciki tana turawa gaban shi. Dauka Abdulkadir yayi, banda Hajja da Yassar, babu wanda ya taba mishi abinda Waheedah din take mishi yanzun. Kowa a gida yana daukar baya bukatar kulawa, ko Hajja takan yi wannan tunanin wasu lokuttan. Sosai zuciyar shi ta sake daukar dumi, baice komai ba. Tsiren ya cinye, yana ganin Waheedah ta dauki abin goge hannu tana mika mishi, karba yayi ya goge hannun shi tukunna ya dauki robar lemon yasha kusan rabi ya ajiye

“Ruwa fa?” 1

Ta bukata, kai ya girgiza mata a hankali, yana kallon ta gyara zamanta kamar shi din dayaci wani abu kawai ya isheta, ita ba saitaci ba, numfashi ya sauke, yana kallon yanda fitilar wajen ta karama fuskarta haske. Haka suka zauna shiru, ita tunanin shine fal cikin ranta, shikuma bazaice ga abinda yake tunani ba har mutane suka fara hada-hadar fita, da alamu anyi abinda za’ayi an fara shirin tashi. Yazid ne yazo yana jansu biyun a cewar shi za’ayi hotuna, binshi sukayi akayi hotuna sosai dasu tukunna Abdulkadir din ya damqi hannunta yana fara janta. Binshi take tana kallon hannun shi da yake rike da nata, zuciyarta kamar zata fito waje take jinta.

Su duka biyun basu kula da Nuriyya da take bin bayansu tanajin kamar zuciyarta zata fado, karshen abinda zai faru shine Waheedah ta samu abinda take so, fuskar Abdulkadir din take kallo ko zata ga alamun so, kamar yanda yake bayyane a fuskar Waheedah, amman bataga komai ba, asalima kamar ranshi a bace yake. Ita dai komai zai faru kar Waheedah ta taba samun Abdulkadir din. Tana jin zatayi komai dan kar hakan ya faru. Wajen motar shi suka karasa tukunna ya saki hannun Waheedah din, yana bude motar da mukullin, har lokacin basu ga Nuriyya da take tsaye a gefe ba. 2

Zagayawa Abdulkadir yayi ya shiga motar, ya miqa hannu ya budema Waheedah daga ciki, jikinta babu karfi ta shiga cikin motar tana rufe murfin, su dukansu juyawa sukayi ita da Abdulkadir din ganin an bude murfin bayan motar.

“Nuriyya…” 4

Waheedah ta fadi cike da mamaki tana dorawa

“Banganki ba”

Cikin takaici Nuriyya tace

“Ya zakiyi kiganni daman” 2

Saida taji sautin muryarta tukunna tasan a fili tayi maganar da tayi. Yanayin muryarta Abdulkadir yaji bayaso, yanda tai maganar kamar Waheedah ta mata wani laifi ya mishi wani iri, saboda yana tare da Waheedah din bai kuma ga abinda tai mata ba. Baisan dalilin da yasa ta bude mishi mota tana shirin shigowa ba, shisa yake da tabbacin idan ta samu fuska zata raina shi, ga zuciyar shi da yaji tana shirin ci gaba da dokawa.

“Ki rufe mun mota…”

Ya fadi a tsawace, yana saka Nuriyya mayar da kafarta data dago, tana jin wasu hawayen bakin ciki sun tarar mata lokacin data rufe mishi kofar tana matsawa gefe ganin ya fisgi motar kamar zai bigeta. Cike da rashin jin dadi Waheedah tace 1

“Hamma…”

Saida yai baya da motar sosai yai kwana tukunna ya kalli Waheedah din idanuwan shi cike da rikici

“Tare nazo da ita? Meyasa zata budemun mota? Sa’anta ne ni?” 3

Kai Waheedah take girgiza mishi idanuwanta cike da tsoro, batason fada, musamman nashi

“Meyasa zaki kirani kamar ban kyauta ba then? Sa’ankine ni da zaki kira sunana kina tsareni da idanuwa kamar ban kyauta miki ba?”

Kai Waheedah ta sake girgiza mishi, yanda take jin ranshi ya baci nasa idanuwanta cika da hawaye. Tsaki Abdulkadir yaja, shi kanshi idan za’a tambaye shi asalin abinda ya bata mishi rai bazai ce gashi ba. Yasan Nuriyya na da hannu a cikin bacin ran nashi, baisan tayaya bane kawai. Tunda Waheedah ta lafe cikin kujerar motar ko motsin kirki batayi, ta gefen idanuwan shi yake kallon tana goge fuska, yasan kuka take. Inyai magana ta amsa yaji kuka take tabbas zai watsa mata mari ya bata dalilin da zata saka shi a gaba tana mishi kuka, shisa baice mata komai ha har suka karasa gida.

Ita ta fara fita daga motar, tukunna ya fito shima, zagayawa yayi ta gefen da take, cikin sanyinta ta dago da hannu tana mika mishi wallet din shi, karba yayi yanajin shi wani iri. Bude wallet din yayi tukunna ya sa hannu yana zaro duka kananun hotunan da suke cikinta, sosai ya matsa daf da Waheedah din ya kamo hannunta yana ware tafin ya saka mata hotunan a ciki tukunna yasa dayan hannun shi yana rufe yatsunta akan hotunan ya saki hannunta yana juyawa abinshi…!Washegarin ranar a kwance ya wuni, tunda yai wanka, karin safe ma baiyi ba sai wajen karfe sha daya na safe. Ko daya fita yai sallah a masallaci wajen karfe daya, yana dawowa daki ya cire dogon wandon ya mayar da iya gwiwar shi, kwanciya ya koma yayi. Idan abu ya riga ya wuce baya tunanin shi, baya wannan asarar, shisa baisan dalilin da Nuriyya zata manne mishi cikin kai haka ba, ko idanuwan shi ya rufe ita yake gani, ta addabe shi, ta hanashi sakat, ya riga da ya fadama kanshi tana da kyau, baiyi ma kanshi karya ba tun farko, amman taki barin shi, wani in yagani saiya rantse da Allah hotonta ya dauka ya samu waje ya rataye cikin kanshi. 12

A hankali yaja karamin tsaki yana juya kwanciyar shi, yunwa yaji ta fara mishi sallama, duk da bai karya da wuri ba, saboda shi mutum ne da baya wasa da abincin kwata-kwata. In har baici ba, to damar hakan ne bai samu ba. Ya mike yasa wani ya kawo mishi dinne yake mishi wahala yau, lumshe kananun idanuwan shi yayi, har lokacin Nuriyya na manne cikin kanshi, bacci ne ya fara fisgarshi a hankali. Cikin kunnen shi yaji an turo kofar hadi dayin sallama a hankali 2

“Hamma…”

Muryar dayai tunanin Nazir ne ta dirar mishi. Shiru yayi bai amsa ba, yana fatan shirun tasa kowaye ya tafi.

“Hamma kazo inji Hajja…”

Nazir ya fadi yana riqe da kofar ko da almatsutsan Abdulkadir din zasu tashi. Bazai tsaya ya sauke su akan shi ba

“Kaina namun ciwo” 7

Abdulkadir ya fadi batare daya bude idanuwan shi ba, baisan kiran me Hajjon take mishi ba, bangaren ta yasan a cike yake da mutane, ta kuma san bason hayaniyar yake ba, zata fara sakawa a kira shi. Ba kanshi yake ciwo ba, jikin shine bayajin dadin shi. Turo baki Nazir yayi dan saida Hajja ta balbale shi da fada tukunna yazo kiran Abdulkadir din 3

“Tace kazo…”

Sake runtsa idanuwan shi Abdulkadir yayi

“Zanci ubanka idan na bude idanuwana kana cikin dakin nan” 6

Yanajin karar rufe kofa, batare daya bude idanuwan shi ba ya gyara kwanciyar shi yana kwantawa kan bayan shi hadi da dora hannuwan shi duka biyun kan cikin shi, bacci ne mai karfi ya dauke shi wannan karin duk da yunwar da yake ji. Ba zaice ga lokacin daya dauka ba, baccin kuma yau yayi karfin da baiji turo kofar ba sai bubbuga mishi kafa da yaji anayi, a tunanin shi Nazir dinne ya sake dawowa, raini yasa shi harda bubbuga mishi kafa wannan karin. 2

Cikin zafin nama yai amfani da inda yake jin hannun na bubbuga shi ya hasaso inda fuskar yake tunanin fuskar Nazir din zata kasance yakai mishi wani barin makauniya. 4

“Umm um um umm…”

Yassar ya fadi yanajin wani yawu da yake tunanin jinine na tattarowa yana cika mishi baki, dan a mummuke Abdulkadir ya same shi 5

“Ba zaka fita ba kenan dan uban ka?” 1

Abdulkadir ya fadi jin gurnanin da Yassar din yayi yana bude idanuwan shi hadi da mikewa ta sauke su kan Yassar dake dangwalo mummuken shi yana dubawa, ware kananun idanuwan shi Abdulkadir yayi

“Inalillahi… Hamma… Wallahi na dauka Nazir ne…” 5

Hannu Yassar ya daga mishi kawai yana wucewa bandaki ya kuskure bakin shi yana zuwa saitin mudubi, wajen harya tara jini daga waje, bude bakin shi yayi yana zira dan yatsa ya tana hakorin shi na sama da yaji kamar ya fara girgidi, sosai ya tattaba hakoran duk da yake tunanin sun fara girgidi yaji suna zaune dam, dubawa ya sakeyi yaga babu jini tukunna ya fito daga bandakin yana samu waje gefen gadon ya zauna, bazai karya ba, ya maku yanda ya kamata. 6

“Hamma…”

Abdulkadir ya kira da alamun dariya a muryarshi ganin yanda Yassar din ya nutsu. Gabaki daya fuskar shi Yassar yake ji ta dauki dumi kamar tana zazzabi ita kadai. Saida ya tabbatar idan yai magana muryarshi ba zatai rawa ba tukunna yace 6

STORY CONTINUES BELOW


“Dan ubanka ba zaka bude idon ka ba? Daka cire mun hakori me zaka fadamun?” 2

Sosai Abdulkadir yake son danne dariyar shi amman ya kasa, sauka yayi daga kan gadon yana mikewa tsaye, sosai yake dariya

“Inda Nazir dinne haka zaka kai mishi wannan dukan? Saboda kai baka da tausayi?” 2

Dariya Abdulkadir yakeyi

“Wallahi bansan kai bane ba”

Kai Yassar ya jinjina yana yin qwafa kawai. Gabaki daya duk wani karfin gwiwa daya shigo dashi dakin ya gama sacewa. Bandaki Abdulkadir ya wuce yana wanko fuskar shi ya fito, nesa da Yassar din ya zauna, dan yasan in ya yanke hukuncin rama dukan shi zaiji jiki. Tukunna yace 1

“Menene kake tashi na?”

Sai da Yassar ya watsa mishi wani kallo tukunna yace

“Hajja tace zaka dauki mutanen da zasu kai Khadija, saika tabbatar ka tattaro su Zahra dan kar suce zasu kwana…”

Dakuna fuska Abdulkadir din yayi

“Gaskiya babu inda zance…bari in kira su Zahra din in musu kashedi kawai” 19

Tsare shi da idanuwa Yassar yayi cikin yanayin daya sashi qara daquna fuska yana fadin

“An shiga rayuwa ta wallahi… An takurani gaskiya” 5

Kallon shi dai Yassar yaci gaba dayi batare da yace komai ba. Abdulkadir din bayason yana kallon shi haka, bayaso yana kallon shi kamar yayi wani laifi. Meyasa za’ace ya fara kai mutane wani waje, Hajja tasan a gidan in ba ita ba sai Abba, ko yara ba’a sakawa yakai makaranta. Balle yazo ya fara dibar wasu mutane kamar direba. 1

“Ba zaka je ba kace Abdulkadir? Kai tsaye ba zakaje ba? Ince maka Hajja tace kayi abu kana fadamun ba zakaje ba? Dan Ubanka ba zaka shiryu ba, ba zaka gane girma kakeyi ba ko?” 3

Yassar yake fadi ranshi a bace, baisan lokacin da Abdulkadir din zai gyara wannan muguwar dabi’ar ta rashin ganin kan kowa da gashi ba. Kicin-kicin Abdulkadir din yayi da fuska 1

“Nidai an shiga rayuwata gaskiya”

Ya sake maimaitawa yana saka Yassar fadin

“Yayi kyau…”

Yaja kafafuwan shi yana dorawa kan gadon, wayar shi kirar blackberry curve 2 ya zaro daga aljihu yana ci gaba da dannawa. Sake daquna fuska Abdulkadir yayi yana kallon Yassar din, yasan ranshi ne ya baci, bayan Abba a gidan babu wanda yake kokarin gujema fushin shi irin Yassar, fiye da Hajja dan yasan ita da wuri take sakkowa

“Wanne unguwa ne?”

Ya bukata muryar shi can kasan makoshi, inda yake Yassar bai kalla ba, ballantana yai kokarin kula shi.

“Hamma kaji… Wacce unguwa? Karfe nawa za’a tafi? 1

Shirun Yassar ya sake mishi

“Bana so ina magana ana mun shiru, kasani kuma, ina tambayarka kayi banza ka kyaleni” 1

Yanayin yanda yai maganar yana sa Yassar fadin

“Fada zakai mun Abdulkadir?”

Kankance idanuwa Abdulkadir ya sakeyi

“Magana nake maka kai shiru ka kyaleni”

Kai kawai Yassar ya jinjina

“Ya maka kyau”

Ya karasa maganar yana mikewa ya fice daga dakin, Abdulkadir nabin shi da fadin

“Kaifa kaqi bani amsa, banyi fushi nabar maka dakin ba kaine zaka fita? Hamma bana son irin haka… Hamma… Ok ya maka kyau” 8

STORY CONTINUES BELOW


Wucewa Yassar yayi, yana jin ‘Ya maka kyau’ din da Abdulkadir din ya fadi da tasa shi jin son komawa yasa belt ya zane jikin Abdulkadir din, sai dai alkawari yaima kanshi bazai biyema Abdulkadir din ba, dan idan akwai mashi a kusa, tsaf takaicin dazai qunsa maka zai saka soka mishi batare daka sani ba. Idan ya biyema Abdulkadir zai dake shi saiya karya shi, yana kuma da tabbacin duk da bazai rama ba, bakin shi bazai shiru ba. Addu’ar shiriya yai mishi kamar ko da yaushe. 1

*

Saida ya dauro alwala tukunna ya fito daga dakin da nufin zuwa masallaci dan yaga la’asar ta kusan qarasawa, yana da tabbacin ana gab da kiran sallah.

“Zahra…”

Ya kira daya hango ta taho, tun jiya yake mamakin girman yarinyar, wai har ta gama sakandire, Yassar ne yake fada mishi ta nemi gurbin karatu a jami’ar Bayero dake nan Kano din ma da yake mishi zancen girmanta. Duk da ta tsallake aji uku, kasancewar tana da kokari sosai. Takowa take a hankali tana nufo inda Abdulkadir din yake

“Yanga zaki tsaya mun?”

Ya fadi yana kallon ta, kai ta girgiza mishi tana saurin fadin

“A’a…”

Ta karasa inda yake tsaye da sauri. Kallon ta Abdulkadir yayi, dankwalin lace din dake jikinta ne ta dora saman kanta batare data daura ba, indai Zahra ce ba zata taba yin abu irin na mutane ba yasani, ko makaranta zataje hijab dinta in baya hannu lokacin zakaga tana saka shi.

“Ki kawomun abinci…da ruwa, kikai mun dakina a bude yake…”

Amsa shi tayi tana shirin juyawa Abdulkadir yace

“Ki fada musu ni zan dawo daku daga wajen kai Adda… Duk wanda na nema sai yaji a jikin shi”

Ware idanuwa Zahra tayi, gabanta yana faduwa, kafin ta dakuna fuska

“Baki jini ba saina watsa miki mari”

Sake dakuna fuska tayi, da gaske Hajja take ba zasu kwana ba din dai, bayan Adda Khadee din da kanta tace musu zasu kwana tun kafin bikin.

“Zan fada musu”

Zahra ta amsa tana wucewa, yana kallonta tasha kwana, tunawa yayi baima tambayeta wacce unguwa ko kuma karfe nawa ba, bin bayanta yayi tunda ta rigada tasha kwana ko kwala mata kira yayi ba lallai taji shi ba, gashi yau bayajin hayaniya kwata-kwata. Zahra kuwa tana shan kwana taci karo da Amatullah

“Kinsan Hajja tasa Commander ne yakai mu?”

Dafe kirji Amatullah tayi

“Kice mun wasa kike? Haba dai Commander… Ina ce Hamma Yazid zamu bi”

Kai Zahra ta girgiza ma Amatullah din

“Yanzun yaimun magana da kanshi, wai karma mu bari ya neme mu idan an kaita din”

Buga kafafuwa Amatullah tayi cike da rashin jin dadi

“Allah dai ya hadamu da jarabu da qwai…”

Turo baki Amatullah tayi tana fadin

“Ai gara Jarabu da qwai akan Hamma A…”

Hadiye maganar tayi ganin Abdulkadir din a tsaye ya diro musu kamar mikiya. Yanda ya tsareta da idanuwa yana tabbatar mata da maganar yake so ta karasa, wani abu da taji ya tsaya mata a wuya ta hadiye, a daburce tace 4

“Hamma A… Hamma Aminu” 1

Zahra da yanayin Amatullah din ya tabbatar mata da Abdulkadir din ne ya karaso wajen yasa ta juyawa ta kuma matsa kamar zata hade da bangon wajen, da yanayin fuskarshi ya tabbatar mata da yajita.

“Yaushe Aminun ya zama Hamman ki?”

Abdulkadir ya fadi yana tsare su da idanuwa. Alamun motsi yayi su biyun suka kwasa da gudu, kai ya girgiza murmushi na kwace mishi 1

STORY CONTINUES BELOW


‘Jarabu da qwai’

Ya maimaita cikin zuciyar shi wani murmushin mai sauti na kwace mishi

“Sai naci uban yaran nan Allah…” 1

Yai maganar a fili yana juyawa. Masallaci ya fita abin shi. Sanda ya dawo hanjin shi har nadewa suke waje daya. Dakin shi ya nufa kai tsaye yana tunanin ganin abinci baiga komai ba, tabbas saiya zane jikin Zahra. Fita yake shirin yi yaji an kwankwasa kofar hadi dayin sallama cikin sanyin muryar daya tabbatar mishi da Waheedah ce.

“Shigo…”

Ya fadi

Da kafa ta tura kofar saboda farantin da yake hannunta, tukunna ta shiga dakin. Zahra ta sameta tace Commander yace ta kai mishi abinci. Hakan yai mata dadi, tun safe take jin ganin shi, ta fito yafi a qirga amman bataga giccin shi ba, batason fito da hotunan daya bata jiya daga inda ta adana su, saboda gidan cike yake da mutane. Farantin ta ajiye mishi a kasa tana mayar da hannunta daya baya kamar mai boye wani abu

“Ina wuni”

Ta gaishe dashi

“Lafiya…”

Ya amsata a taqaice yana jan farantin gaban shi

“Akwai wainar shinkafa, ban saka maka ba saboda nasan baka ci” 1

Da mamaki Abdulkadir ya dago yana sauke mata kananun idanuwan shi. Baya tunanin ko Hajja tasan bayacin wainar shinkafa, dan da bakin shi bai taba cewa kowa yana cin abu kaza ko bayaci ba, idan yaje ya duba yaga ita akayi ficewa yake ya nemi wani abin daban yaci. Ganin kallon da yake mata yasa tajin zuciyarta na bugawa, tana mamakin yanda idanuwan shi suke birkita mata lissafi, duk kankantar su.

“Ban taba gani kaci ba, idan ka shigo anyi baka diba kake fita”

Waheedah tai mishi bayani, Idanuwan shi ya dauke daga kanta, yana jin jikin shi ya dauki dumi na daban. Abune da bai taba tunanin wani yai damuwar dazai kula ba. Plate din shinkafa da miya harda lettuce data zubo mishi ya dago yana dora shi kan cinyar shi, yanda yake motsa abincin a nutse take bi da kallo, kafin ya diba abincin yana fara kaiwa bakin shi. Idanuwanta Waheedah ta dauke daga kanshi, tana dan sa hannu ta dafe kirjinta da yake dukan uku-uku. Passport dinta ne data gama bincika duk wasu da take dasu tana dauko wanda tai tunanin tayi kyau a ciki ta ke riqe dashi a hannunta. 5

Tun jiya da tunanin ta bashi yazo mata zuciyarta take dukan uku-uku da tunanin abinda zai iya biyo baya. Tasan babban cikin su bazai wuce tasha mari yace ta raina shi ba, amman son ya tafi da wani abu da nata ne yafi karfin duk wani tunani da takeyi, yanda yabar mata wani abu nashi duk da ko baiyi ba tasan zai kasance manne a zuciyarta harya dawo, haka take so ko yayane itama ya tuna da ita, ta gama tattaro karfin gwiwarta amman ganin shin da tayi ya tuna mata yanda a kasan komai akwai tsoron shi a shimfide. Kalle-kalle take cikin dakin, a drawer din gefen gadon ta hango wallet din shi, karasawa tayi wajen tana zama.

Sai lokacin Abdulkadir ya dauke idanuwan shi daga kan abincin da yake ci ya kalleta, ganin wallet din shi yayi a hannunta ta bude

“Kin ban ajiya ne?”

Ya bukata yana tsareta da idanuwa, tunda ta shigo yake tunanin ta kara haske, sai lokacin ya kula da lace dinta farine da ratsin ja ko stones din jikine ja bazai tantance ba, shiya kara fito da haskenta dayai mishi yawa a ido. Kai Waheedah ta girgiza mishi zuciyarta take ji ta dawo wuyanta, idanuwan shi ya dauke daga kanta yana ci gaba dacin abincin shi, hakan ya bata damar saka mishi hoton cikin karamin wajen da zaka iya ajiye hoto tukunna ta balle wallet din tana ajiye mishi inda taganta. Sosai zuciyarta take dokawa har wani zazzabin faduwar gaba take ji a jikinta. 4

Ga zufa da tafukan hannunta sukeyi, mikewa tayi

“Ina zakije?”

Abdulkadir ya tambaya, bai jira amsarta ba ya dora da

STORY CONTINUES BELOW


“Ki jira in gama ki tafi da kwanonin”

Komawa Waheedah tayi ta zauna, idanuwanta kafe a kasa, shirunta Abdulkadir yaji ya mishi yawa, hakan yasa shi kallon ta, kanta a kasa yake

“Waheedah?”

Ya kira cike da alamun tambaya, ta dago tana sauke mishi manyan idanuwanta da yake da yakinin za’a cire hudun nashi a ciki har a samu ragowa, har mamakin yanda za’a ce idanuwan mutum ne da wannan girman yake, yana son ganin tsoron shi cikin su saboda girman da sukan qara yi mishi. 1

“Lafiyar ki?”

Ya tambaya, tambayar shi kanshi tana bashi mamaki, haka kawai yana son jin tana lafiya, da bata mishi surutunta yau. Kai Waheedah ta iya daga mishi, yanda ya kira sunanta nasa har lokacin zuciyarta dokawa take har cikin kunnuwanta. Numfashi ya sauke, ita kadai take amsa mishi magana haka, surutun nata yake son ji, tana amsa mishi magana da kai. Abincin shi ya karasa ci yana cire robar ruwan daga kan farantin ya dago dashi ya miqama Waheedah data miqe tsaye, gara ta fita, kan shi yake jin ya mishi nauyi yau din nan, Nuriyya taki ficewa daga cikin shi, bazai kara da tunanin ko lafiyar Waheedah kalau shisa take mishi shiru-shiru ba.

*

Tsaye yake jikin mota Abba yana jiran wanda zaikai din su fito, ance mishi sharada ne, yagane ta wajen dan akwai abokin shi a gurin unguwar. Waheedah ya hango tana takowa inda yake, tafiyarta yake kallo kamar batason taka kasar dakyau karta tsage ta rufta da ita. Hijab ce mai hannuwa a jikinta har kasa. Yana son hijab, dan matar shi ba zata saka mayafi ta fita wani qaton banza na kallonta ba, kwalliyarta a cikin gida zatayi iya idanuwan shi. Kalar hijab din ruwan kasa mai cizawa, a ranshi yake tunanin ko Waheedah batasan tana da gaske bane, duk kayan da zatasa kara mata haske suke suna saka ta shigar mishi ido. Yana son mace mai duhu

‘Kamar Nuriyya’ 7

Wata murya cikin kanshi ta furta mishi tana saka shi sauke numfashi, duk da ba karya ta fadi ba, yanayin kalar Nuriyya haka yake son macen shi ta kasance. 3

‘Har yanayin jikinta da komai nata’ 2

Muryar ta sake fada mishi tana saka shi girgiza kai, kamar yana son fada mata kartai musu haka shi da ita, karta ja musu raini. Karasowa Waheedah tayi tana fadin

‘Hamma baka shirya ba, yanzun fa za’a tafi, dangin su Angon har sun zo”

Sosai yaji dadin saukar muryarta da ta katse mishi tunanin da yake da yake da tabbacin babu abinda zai ja mishi sai rainin dayafi tsana a rayuwar shi. Kafin maganganub Waheedah din su zauna mishi suna saka shi kallon ta cike da rashin fahimta

“Wanne irin shiri?”

Dan kallon shi Waheedah tayi tana rausayar dakai, tagan shi da wando iya gwiwa sai riga blue mai haske datai mishi kyau naban mamaki a idanuwanta, amman duka cikin abokan angon da suka zo da motocin da kuma yan gidan nasu da zasu taya hidimar daukar amaryar manyan kaya ne a jikin su.

“Baka sa kaya ba”

Ta fadi, tana saka shi kankance mata idanuwan shi. Haka Yassar yai mishi maganar sake kaya dazai fito, itama tazo tana mishi yanzun

“Tsirara kika ganni? Meya sami kayan da suke jikina? Me yasa bazan je da wannan din ba? Su ba kaya bane”

Kallon shi Waheedah take yanda ya kankance ido yana mata masifa kamar jiranta yakeyi daman, ita bada tunanin komai tai mishi magana ba, idanuwanta taji sun cika da hawaye. Batare da tunanin komai ba ta sake cewa

“Allah ya baka hakuri…”

Wani murmushi Abdulkadir yayi mai sautin dake fassara ya kasa yarda shi Waheedah tace ma ‘Allah ya baka hakuri’. Duk da baiji raini a muryarta ba, baqar magana ce ta fada mishi saboda yana magana mai tsayi da ita 2

STORY CONTINUES BELOW


“Bakar magana zaki fadamun? Saboda kinga hakorina? Maganar da nake dake tasa zaki fara rainani ko?”

Hawayen da take tarbewa ne suka zubowa, yana kara harzuqa Abdulkadir din saboda bayason kuka marar dalili, idan zaka saka shi a gaba kana mishi guga gara ya tabbatar ya baka dalili me karfi nayin kukan

“Me nai miki?”

Kai Waheedah ta girgiza mishi, hawayenta na sake zuba, fadan shi take ji har kasan zuciyarta, inda tasan zai mata fadan ba zata soma mishi maganar kayan da yasa ba.

“Raini ne yasa kike mun kuka?”

Abdulkadir ya sake tambaya yana tsareta da qananun idanuwan shi. Kafin yaja tsaki yana wucewa ya nufi bangaren su, kayan da Yassar din ya fito mishi dashi dan ya saka yaqi ya dauka hadi da jan wani karamin tsakin, dan baisan dalilin da yasa shi yake sake kayan jikin shin ba, tunda baiga abinda sukai ba. Ko motsi Waheedah batayi ba daga inda yabarta, hannu take sakawa tana share kwallar da taqi daina zubar mata har lokacin, fuskarta tayi wani irin ja, abinka da farar fata. Anan Nuriyya da tun jiya da suka dawo ta kwanta batare da tace mata komai ba ta sameta.

Tunda aka fara hidimar a gidansu Waheedah din take kwana, duk da ko babu hidima tana kwana wasu lokuttan, kusan rabin da kwata na rayuwarta tare dasu takeyin ta a gidan. Yau da safe data tashi ma bata kula Waheedah din ba, saboda haushinta take ji, haushin kowa da komai take ji, data isheta catai mata kanta ke mata ciwo, harda bata paracetamol din rainin hankali.

“Ke kuma lafiya? Me akai miki?”

Nuriyyan ta tambaya tana tabe baki, hannu Waheedah tasa tana share kwallarta, muryarta a dishe tace

“Hamma Abdulkadir ne ya sauke mun fadan shi”

Dariya Nuriyya tayi saboda har ranta taji dadi, Abdulkadir din ya tabbatar mata da Waheedah kamar kowa ce a wajen shi, babu wani special treatment da take samu 3

“Abin dariya ya baki ko?”

Waheedah take fadi tana hararar Nuriyyan data sake yin wata dariya tana riqo Waheedah din hadi da dora kanta kan kafadar Waheedar

“Sorry kawata. Halin Hamma wanne ne baki sani ba?”

Jinjina kai Waheedah tayi, tasan shi fiye da zaton kowa, fadan shine ba zata taba sabawa dashi ba, duk yanda take da tsoron duka gara ya daketa dayai mata fadan shin nan mai tsaya mata a rai.

“Nasani Nuriyya, bana son fadan shine kawai”

Tabe baki Nuriyya tayi

“Nidai muje…”

Ta karasa tana kama hannun Waheedah din dan su samu mota, cikin abokan angon wani ya leqo kai yana ma Nuriyya murmushi

“Ya zaku wuce direban naku?”

Ya fadi yana dan daga mata gira, dariya Nuriyya tayi ganin baiko kalli inda Waheedah take ba. Murfin motar zata bude dan ta shiga, kamar daga sama taji ance 1

“Ina zaki je?”

Juyawa tayi zuciyar ta na dawowa makoshinta, kamshin turaren shi na cika mata hanci, shaddar jikin shi tayi matuqar amsar shi, jikinta har wani bari yake, kafin ta kula da idanuwan shi tsaye suke kan Waheedah. Wani tuquqi taji ya taso daga dan yatsan kafarta yana samun wajen zama a makoshinta. Yana fitowa bai ganta wajen motar ba, hijab dinta ya hango, ranshi a bace yake har lokacin, baima san wayace tabar wajen ba. 1

“Nace ki bar wajen ne?”

Ya tambaya, kai Waheedah ta girgiza mishi, kalar fadan da yake ji yau na bata mamaki, tunda daman bashi ya kirata ba, ita ta same shi a wajen, yanda ya kafeta da ido yasa ta wucewa ta gaban shi kamar qwai ta fashe mata. Wani kallo ya watsa mata mukullin motar dake hannun shi na subucewa ya fadi, kafin ya yunkura Nuriyya ta tsugunna ta dauko mishi tana sauke idanuwan shi cikin nata, wani irin abu na tsirga mishi dayasa gashin dake bayan wuyan shi miqewa. Hannu ya miqa mata ta saka mishi mukullin a ciki. Yana duk wani kokari dazai iya karya riqe hannunta ya jujjuya shi yaga kunshin ta dakyau.

STORY CONTINUES BELOW


Idan akwai abinda yake kara burgeshi bai wuce kunshi ba, ko baisan yarinya ba yaga hannuwanta dauke da kunshi saiya sake kallo, musamman na Nuriyyan da yake baqi da ja. Gashi yan yatsun nata jan lallen ya kama. Wani abu ya hadiye a dakyar yana tsintar kan shi da fadin

“Wa yai miki kunshi?” 3

Murmushi Nuriyya tayi saboda shine karo na farko da yai mata wata magana da ba amsa gaisuwa bace, banda jiya da yace ta rufe mishi kofa.

“Wata mata ce”

Ta amsa tana saka shi ware kananun idanuwan shi da ya tabbatar a waje yai maganar, kai yadan daga mata yana juyawa. Takun tafiyar da yakeji ya tabbatar mishi da Nuriyyan na biye dashi. Zuciyar shi dokawa take sosai, ga tsikar jikin shi da yake ji tana miqewa, bayaso ya juya ya sake fadin wata maganar da bai niyya ba, shisa ya kyaleta. A tsaye wajen motar ya samu Waheedah. Zagayawa yayi ya bude motar ya shiga, wannan karin baice ma Waheedah ta shigo ba, da kanta ta bude kofar ta shiga. Bata kula da hararar da Nuriyya ta watsa mata ba, dan ita taso ta shiga gaban motar. 5

Babu yanda zatayi haka ta bude bayan ta shiga, duk da gabanta na faduwa kar ya koreta, baice mata komai ba, zuciyarta har wani tsallen murna take, murmushi yaki barin fuskarta har lokacin. Dan tashi Abdulkadir yayi yana saka hannun shi a aljihu ya ciro links din dake cikin aljihun tukunna ya zauna. Waheedah ya mikama links din, batace komai ba ta karba tana gyara zamanta dan ta saka mishi a hannun da ya miqo mata din. Cikin yanayin dayasa murmushin da Nuriyya take ya bace bat daga fuskarta, kallon su takeyi har Waheedah din ta daura mishi link din, ya janye yana miqa mata dayan hannun nashi, saka mishi tai tukunna ta gyara zamanta batare da tace komai ba. 1

‘links ne kawai, kema dan bazai yiwu ya baki bane kisa mishi shisa ya bata’ 2

Nuriyya take fada ma kanta duk da wata murya na gaya mata

‘Ita ma din ai ba kanwar shi bace, babu abinda ta hada dashi, agolar gidan su ce’ 3

A karo na farko da taji daman Waheedah tazo a kanwar Abdulkadir din da hakan zaifi mata, saboda babu wani chance na soyayya a tsakanin su. Kirjinta take jin yana mata zafi da abinda take jin kishi ne na fitar hankali, tasan Abdulkadir ya mata nisan da bazai misaltu ba, shisa duk kyan da yake mata, da yanda yake sak da zabin mijin da take burin samu bata taba daga burinta akan shi ba. Haka take so yaima Waheedah nisa, ko kadan bata son wanni kusanci daya banbanta da wanda yake nunawa tsakanin shi da kowa. Idan ba zata same shi ba, Waheedah din ma ba zata same shi ba. 2

Abdulkadir kuwa kokawa yake da yanda komai na jikin shi yake son juyawa ya sake kallon Nuriyyan, kafin kanwar Abba ta bude motar ta shigo tana fadin 1

“Abdulkadir…”

Damar yai amfani da ita ya juyo

“Anty… Ina wuni”

Dan ware idanuwa Anty Maryama tayi, duk da taga Abdulkadir din ya girma, tana tunanin hankali ne yazo mishi har yau take samun arziqin gaisuwa 1

“Lallai Abdulkadir an girma…” 1

Ta fadi tana saka shi daquna fuskar shi. Irin abinda bayaso kenan, saika gaishe da mata saita dinga nuna maka kamar an haifeka a gabanta, ko Hajja da ta haifeshi bayaso tana ce mishi yaro a gaban kannen shi. Nuriyya ya dan kalla yana sata sauke idanuwanta daga kanshi babu shiri. Juyawa yayi yana gyara zaman shi. Anty Hafsatu ce ta shigo itama yanajin motar tai qasa saboda nauyin da sukai mata. Tayar da motar Abdulkadir yayi

“Ka tsaya Hajiya Hassana ta karaso, gata can ta taho”

Anty Hafsatu ta fadi tana sa Abdulkadir fadin

“Inba saman motar zata shiga ba nan dai ai ya cika” 3

Abdulkadir yace yana yin baya da motar, ganin da gaske tafiyar zaiyi yasa Anty Hafsatu rufo murfin motar

“Mutum nawa suke zama a baya? Ka jira tazo Abdulkadir”

Daquna fuska yayi yana fadin

“Gaskiya ta shiga wata motar. Bakiji yanda motar tai kasa ba da kika shigo… Inba so kike muna tafiya muna gurzar titi ba” 5

Bude baki Anty Hafsatu tayi cike da mamaki

“Kaci uwaka Abdulkadir, kana jina…” 1

Daquna fuska Abdulkadir din yayi, yana shirin yin magana Waheedah tace

“Hamma…”

Yanda tai maganar cike da roqo yasa shi harararta cike da alkawarin sauke mata wata masifar. Bata damu ba indai zaiyi shiru, bata so su Anty Hafsatu suce ya musu rashin kunya, kuma tasan idan maganar tai tsayi ba a iya rashin kunya zai tsaya ba, Abdulkadir zai iya fita yabarsu a motar ko su su fita subar shi a ciki. Batason hakan ya faru, Nuriyya dake gefe tana kallon su ta tabe baki. 2

‘Allah yai miki baqin shishigi’ 3

Ta fadi a ranta, koma menene din bata ga matsalar Waheedah ba tunda dai su Anty Hafsatun jinin shine, ita kuma bare ce, amman ji yanda tai mishi magana kamar tana da wani muhimmanci a wajen shi. Tun su Anty Hafsat suna mita har sukai shiru, saboda radio din da Abdulkadir ya kunna yana qure maganar, basu ce ya kashe ba, tunda babu wanda inhar yana zuwa gidan baisan halin Abdulkadir ba. A haka suka isa gidan Adda Khadija din, da duk da ba babba bane yanayin ginin yaima Abdulkadir kyau. A cikin motar ya zauna bayan ya fadama Waheedah inta shiga cikin gidan tace ma su Zahra su fito su tafi…!

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *