ABDURRAHIM MATUKIN JIRGIN RUWA NE CHAPTER 5 BY FADDY BABY

ABDURRAHIM MATUKIN JIRGIN RUWA NE CHAPTER 5 BY FADDY BABY

 

 

 

Banda salati da kuka ba’abinda Na’ima ke iyayi. ”

Shugaban jirgin ruwan (captain) ya bada rigar ruwa (rain coat) yace”

Aba duk matan dake jirgin susa. ”

Munaso dan Allah kowa ya kwantar da hankalin sa, ba abinda zai faru dan mun kai sanarwa (report) ababbar headquarter tamu, za akawomana agaji yanzun nan, cewar” captain d’in jirgin.”

Duk maganar da yake cikin speaker yake yinta, in bahaka ba, bakowa zai ji shiba, dan jirgin nada girma sosai balefi.”

Bak’aramin razana mutanan dake cikin jirgin nan sukayiba, ganin jirgin nasu saura k’iris ya nutse, gashi har yanzu basuga alamun masu ceto ba. ”

Shikan shi captain d’in jirgin yagama sadakarwa. ”

B’ak’aramin rud’ani captain d’in ya shigaba, ganin b’angaran matuk’an, masu control d’in jirgin gabad’ayan shi ya nutse cikin ruwan . ”

Gudu muta nan kusa da b’angaran da ya rufta suketayi suna dawowa b’angaran da yake da dama -dama. ”

Allah sarki kusan baka ganin muta ne, sai kawu nan su. ”

Bindiga carptin d’in ya ciro ya harbi kan shi, dan bazai jure ganin ruftawar jirgina gabad’ayaba.”

Rabin jirgin duk ya nutse, duk wata hayaniya da muta ne keyi duk sun baryi, banda mutun uku daga cikin matuk’an jirgin da sukai saura, duk dasu tsabar amanace irin tasu turawa, amma su sun iya ruwan da zasu iya taimakon kansu, tom amma su turawa sunada amana duk runtsi duk wuya sai dai amutu tare badai su gudu ba, dan duk sun iya ruwa sannan ga rigar ruwa amma sai sukak’isawa suka ba matan sukasa, Allah sarki su kansu mutum ukun da sukai saura sunriga sun gama galabaita, suna ji suna gani haka suka sadaukar da rayuwar su, tsabar alk’awari irin nasu. Matun daya ne da shima yagama galabaita, hannu yake ta d’agawa sakamakon k’arar jirgin da yake ji yana nufo su, dan koba afad’aba yasan su akakawo ma taimako.”

Jin jirgin nata shawagi yasa ya lalibo usir d’insa yahura yasan k’arar zata ankarar da su dan yasan sakamakom ruwan da yasha kansu ne yahana masu kawo masu agajin sugan su. ”

Tunk’arfin shi yahura usir din. ”

Daya daga cikin masu kawo agajin ne( first air) yajiyo k’arar husird’in. ”

nuna ma sauran abokan tafiyar yayi inda yajiyo k’arar . ”

Da saurin su suka karaso in da sukejiyo k’arar hura usir d’in. ”

Shiko azera da yajiyo alamun tahowar su, cigaba da hura usir d’in yayi yana bubbuga hannun shi aruwan da d’an sauran k’arfin da yarage mai.”

take suka gane inda al’amarin yafaru, kara sawa sukai. ”

Cikin ikon Allah sukai ta fito da muta ne, daga cikin jirgin da had’arin (accident) yafaru, basuyi wani wa halar fito da muta ne ba, k’asan cewar yawancin matan duk asaman ruwa suke, saboda rigar ruwa (rain coat) da akabasu sukasa.”

Sun d’au dogon lokaci suna fito da muta ne acikin ruwan, inda duk Wanda aka ciro asibiti (hospital ) ake wucewa da su,

Ikon Allah duk iya sa idona danayi banga Na’ima ba cikin muta nan da aka ciro, har suka gama cirowa, ban ga alamu da sauran mutum b, dan har na’urorin su saida suka haska, basuga komai ba, suka nufi da wa inda aka ciro asibiti (hospital)

Tafe yake cikin d’an ma dai-dai cin jirjin sa, matashi ne Wanda dagani kud’i da kwanciyar hankalin sun wadatai dan dagani ba sai an fad’aba kallo d’aya za kai mai kagane hakan, Sauri yake yak’osa yaje gida, saboda uzirin da yake da shi agidan, wani tudu -tudu yake gani na tun karo shi da alama koma meye igiyar ruwa ce ta jawo shi. ”

Tunkafin abun ya iso kusa da shi ya tabbatar da mutun ne, parking yayi da jirgin nasa acikin ruwan, sannan yasa, wata sanda dake cikin jirgin yarika jawo abun nan ahankali, saidai tun kafin ya iso wajan shi ya tabbatar da mutum ne, dan yaga rigar ruwa (rain coat) ce ajikin mutum d’in shine da lilin da be nutseba acikin ruwan.

Cikin jirgin sa ya sata sannan ya tub’e mata rigar ruwan da ke jikin ta. ”

Al’ajabi ne ya ishe sa, ikon Allah tom wannan kuma daga ina mutum cikin ruwa kuma mace. ”

Tafiya yake yana sake- saken yadda zaiyi da ita, kai kodai in yadda tane? tom in kuma fa nayarda ta kuma bata mutu bafa?. ”

Nan dai yayan kema kan shi shawara, akan ya kaita gidan sa alabashi yakira alheri ta dubata ta tagani ko tanada rai.”

Bashi ya isa gida ba sai 6 pm lokacin garin yafara duhu. ”

Yana shiga gidan ya d’akko ta daga mota kasan cewar yana fita gab’ar ruwan yayi parking a inda suke aje jiragan su. Ya d’auki drop d’in mota har gidan sa.”

Bayan ya kwantar da ita ne nalura she Na’ima ce😉. ”

Waya ya d’auka ya turama alheri sako (text massage) tazo yanzu yana son ganin ta. ”

Cikin mintina kad’an alheri ta iso gidan. ”

Alheri kallan shi tayi damamki tace”.

ABDULRRAHIM wannan fa ina kasamota?. ”

Banza yayi da ita kamar bazai amsa mata ba, sannan yace “ahankali kamar anmasa dole, tsintarta nayi, kidubata mana. ”

Alheri da mamaki take kallan sa so take tak’ara tambayar shi amma bataga fuskar hakan ba, dan haka taja bakin ta tayi shiru, tayi ai kin da yakawota.”

Tad’an kwashi mintina tana dubata, sannan takalli Abdurrahim tace”.

ABDURRAHIM normal take tension ne yasata cikin wannan yanayin amma bari ina zuwa akwai allurar (injection) dazan mata yanzu”.

Cikin k’ank’anin lokaci alheri tadawo da allurar, tayima Na’ima, sannan tace” mai zata tafi gida, ok thanks yace” mata, sannan yazaro kud’i dayawa yabata, kai Abdurrahim ai kawuce haka aguna, kodai kana kokwanton matsayin kane aguna? ”

Kai ya girgiza mata alamun a’a tom Nagoge yace “mata ahankali cikin natsuwar shi da rashin son hayaniya.”

Abdurrahim tun da yaba Na’ima awa d’aya (hour) bata farkaba kamar yadda alheri tace mai, tashi yayi ya shiga d’akin dake kusa da nata, yayi sallah ya shiga kitchen yayi makan shi abu mai saukin ci, sannan yakoma d’akin da ya kwantar da ita ya shiga d’akin shi. ”

Cikin tsakiyar dare Na’ima ta farka, da wata irin k’ara mai rud’arwa ihu take tana salati sai tangal tangal take ita kad’ai akan gadon.”

Abdurrahim yaji k’arar mutum cikin furgici yafito dan shi harga Allah ya manta da wata yarinya aginsa.”

Keeeeee! Ke wata irin dabba ce yace” ma Na’ima da batason abinda takeyiba dan har yanzu bawai tadawo normal bane. ”

Na’ima kuwa jin tsawar da Abdurrahim yayi mata ai kararud’ata yayi wani uban k’aratasake saki Wanda yasa Abdurrahim rufe kunnuwan sa da sauri, yana ja baya. ”

Lura dayayi kamar ba ahayyacin ta yasa shi, Sau rin barin gurin. Dan shi mutum ne Wanda baya son hayaniya kallo d’aya zakai mai kagano hakan. ”

Ruwa mai sanyi ya d’akko ya watsa mata, wata irin ajiyar zuciya ta sauke wadda ko ba afad’amaba kasan tadawo ahayyacin ta. ”

Hmmmmm tace” da karfinta taja wani ubannun fashi. ”

Abdurrahim ta k’ure da ido tana kallo, can kuma tace”.

Bawan Allah dan Allah inane nan? ”

Bazan da da ita yayi yajuya zai koma d’akin shi, tayi saurin sakko daga gadon da take tace dan Allah Bawan Allah aduniya nake ko lahira? Harga Allah takemai tambayar, duk da tambayar tata taso sashi dariya, cigaba yayi da tafiyar shi, itako tacigaba da tambayoyi ta. bawan Allah dan Allah ya akai nafita daga cikin ruwan nan?.”

Agogon hannun shi ya nuna mata, sannan ya kwantar da fuskar shi akan hannuna shi yanuna mata gadon da ya ajeta taje ta kwanta duk da Hannu yake mata kwatancan, kamar dai yadda kurame keyi. ”

bayadda ta iya haka takoma gadon ta kwanta,da tunanina yadda za tayi magana da kurma in gari ya waye, kai Allah dai kasa a Nigeria nake ma, shikenan yanzu inaji ina gani zan kwanta d’aki daya da namiji tom ai kamar d’aki d’ayan ne inda daga yafito zai ganni aiko bazanyi bacci bama, dan ba’abinda natsana kamar namiji yaga kwanciyata, duk ita kadai ke maganar ta cikin zuciya, ahaka bacci ya kwasheta ga wata bala in tattar yunwa da takeji. ”

Washe gari Abdurrahim yagama duk abinda zaiyi amma bata farkaba. ”

alokacinda Na’ima tafarka lokacin shi kuma Abdurrahim yagama abinda zaiyi har yafita aikin shima, gidan shi ko rufe abin shi yayi kamar yadda yasaba in zai fita aiki. ”

Da wata irin yunwa Na’ima ta farka dan cikin tama har gefe daya na rike mata, zama tacigaba dayi akan gadon tun tana tunanin fitowar Wanda tagani jiya har ta kasa jurewa ta tashi taje kusa da k’ofar sai dai da alama yamafita saboda tatura k’, ofar taji arufe take. ”

Kasa daurewa tayi ta fita daga d’akin kitchen tashiga Allah ya tai maketa tasamu wani tea da yasha ya rage sai dai ya huce sai wai nar kwai itama da alama yaci yarage ne, d’auka tayi tacinye tass sanna tadanji saukin yunwar, saidai me tana gama ci amai ya biyo baya aiko taita kwarashi agun. ”
Rasa abinda zata kwashe aman tayi tolailet d’in d’akin ta tashiga nan ma bata ga awani alamun abunda Zata goge ba ko ta share, komawa tayi tazauna duk da duk atsorace take agidan dan bata saba zama guri ita ka daiba. ”

Sai can kusan 5 Abdurrahim yadawo gidan har ga Allah ya manta da wata Na’ima sai da ya tunkaro gidan ya tuna. ”

Zaune take duk tata kure jikin ta kallo d’aya zakai mata kagano duk atsorace take. ”

Tanajin bud’e k’ofa dayi zumbur ta mike daga zaunan da take tana zare ido. ”

Kallo daya Abdurrahim yayi mata ya dauke kan shi, kitchen yanufa dan haka tabi arshi take daga yadawo aiki bazaiyi komai ba har sai yasamar ma kanshi abinda zaici dan shi bai iyacin abincin siyeba tsabar kyankyami irin nashi🤔. ”

Bawan Allah dan Allah ina kasamoni tana mai maganane tana nuni da hannu kamar tana magana da kurma dan ita duk atunanin ta kurma ne. ”

Wani banzan kallo abdurrahim yayi mata dan shi tsantsar raini yake gani maganar da take mai da kurame, banza yayi da ita ya shiga kitchen dan samarma kanshi abinda zai ci. ”

Yana shiga kitchen d’in yaci karo da aman da Na’ima tayi mai aciki tarasa abin kwashewa tab’ar shi agun. ”

Da sauri yadod’e hancinsa yadawo baya da sauri, kallanta yake rai abace yace”wai meyasa talaka baya da hankali ne? Keko ko atalakan bagidajiyar talaka ce, nuna ta yayi da hannu yacigaba da cewa wallahi nabaki minti daya ka cal kigoge min wan can k’azantar sannan kuma kizo kibar min gidana yanzu yanzun nan….. ”

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *