ABU-MALEEK CHAPTER 3 BY Nimcyluv

ABU-MALEEK CHAPTER 3 BY Nimcyluv

                   Www.bankinhausanovels.com.ng 

Robar ta faɗi ƙasa, cikin sauri kuma ta ɗauka tare da mayarwa saman fuskarta tana sauke ajjiyar zuciya.

A hankali kuma cikin son tunanin abinda zai faru gaba shiga yawo cikin kwanyar kanta.

Tabbas rashin lafiyar King Tunde tai matuƙar faranta ranta sosai fiye da sosai ma.

Kawo lokacin harshashen kasancewar ta Sarauniyar Kanzaf take.

Cike da farin ciki da kuma jin daɗin,

Sabuwar nasarar dake shirin tunkaro ta, ta tsirawa mirror’n idanu tana hango zallar kyau da kuma tarin haibar dake saman fuskarta,

Lallai Tabbas Hadima Zubaida tana da amana da kuma riƙo da gaskiya wannan dalilin ya sanya ta zama Amintacciyar Hadimar King Tunde.

Baya tayi kaɗan tana watsa hannayenta sama cikin dakakkiyar murya ta mai cike da isa da kuma gadara tace.

“Easy! Easy! Wannan lokacin tunani ne bawai shirme ba, wanne dalili ya sanya Oumuu-Ayman da Mai Babban ɗaki suke son ɓoye MALEEK? Har suke laƙaba masa kalmar mutuwa kalmar da ita a rayuwa ma mancewa take da ita, idan har ba gani tayi wani ya faɗi ya mutu ba”

Shiru tayi da zan can,

Ta shiga kewaye cikin ma dai-dai cin Parlon nata,

Murmushi tayi kana ta ɗura hannayenta duk biyun ta bugi tsakiyar kanta tace.

“Perfect idea, dole Tabbas ya kamata MALEEK yayi mutuwar gaskiya, domin shi kaɗai zai hanani zama sarauniyar Kanzaf”

Ta faɗi hakan tana mai faɗawa saman kujera 3seater tare da sauke gwauron numfashi.

Misalin 11:30 na safe Salimerh ta fito sanye da wani tattausan farin voyal na mata.

Wanda yake ɗauke da red torches, masu kyau da kuma walwali suna ɗaukan idanu,

A ƙalla voyal ɗin Jikinta zai kai adadin kuɗi kimanin 1500k (dubu ɗari da hamsin).

Sai milk ɗin Alƙyabba data sanya a saman voyal ɗin,

Wanda ta haddasa fitowar a salin kyanta kuma ta ƙara shaidawa jama’a Tabbas, ita ɗin jinin Alaafi ce,

Salimerh tana da sanyayyan kyau bata sa jiki sosai sai tsayi da take da shi,

Ga kuma fara’a da kyautatawa, amma tana son nuna cewa iya ɗin da gaske jinin sarauta ce,

Wanda ko da ace bata nuna ba to zallar jin kanta da kuma isarta haɗi da Izzarta ka ɗai zai shaidawa mutane cewa ita ɗin jinin King Tunde Muhammad Jalal ce.

Hannunta riƙe da wayarta mai ƙirar Iphone 12pro max,

Kanta a ƙasa take taka Fararan sahunta wanda suke sanye cikin wani takalmin fata,

Mai tsananin kyau ga wani gashi gashi dake a jikinsa,

Daga bayanta kuma Hadimanta ne suke riƙe da school bag ɗinta da kuma Iphone system ɗinta,

Duk inda ta gilma bayi ne ke zubewa suna gaida ta, duk da cewa abinda take dubawa yana da matuƙar muhimmanci amma haka take daurewa tana ɗaga masu hannu,

Sabida wulaƙanci bana ta bane, infact ma bata iya sa ba.

Wani babban dogari ne ya ƙara su da sauri ya buɗe mata back seat na motar mai ƙirar  Mahindra XUV7000 ash color!

Da sauri ta faɗa mota tana mai gyara zaman farin iphone bluetooth ɗin ta,

Driver na ƙoƙarin jan motar, taji an buɗe ƙofar left hand side ɗin ta an shigo,

A hankali ta saki numfashi tana mai ɗan taune laɓɓanta, tuni ƙamshin perfume ɗinsa ya shaida mata ko wanene,

Ba tare kuma da tayi magana ba taci gaba da searching ɗin dake na *Criminology*

Kasancewar yau ne First time da zata halarci *Dean Of Law* (University of Benin) a hankali kuma ta shiga typing ɗin “Define Criminology¿”

Cikin abinda bazai wuce wasu daƙiƙo ba goggle ɗin suka watso mata amsar.

_Criminology is a_ _multidisciplinary science that studies a diverse set of information related to criminal activities such as individual and group criminal activities, perpetrator psychology and effective means of rehabilitation._ _Criminology degrees examine social reaction to crime, methods and procedures to prevent and combat crime and social protection from crime. Criminology combines theories from other disciplines like psychology, sociology and law_

Anya zata iya wannan karatun mai wahalar gaske da kuma tarin hatsari,

Wata zuciyar ta bata amsa da.

“Dole za kiyi, kada ki mata wannan karatun shi ne hope ɗin ki, kuma shine abinda kike so kiyi Achieving a rayuwa, kuma yin wannan karatun shi ne zai baki damar tsare jama’ar Alaafi da kuma al’ummar Kanzaf,

Wannan karatun shine zai baki damar fahimtar mugwaye kuma azzaluman da suka jima suna zuluntar ɗan uwanki, wanda har kawo yazo babu wanda yasan ko suwane bare yasan plan ɗinsu na gaba”

Fesar da iska tayi a hankali kuma ta juya ta kalli wanda yake kusa da ita.

Tattausan Murmushi ya sakar mata, a hankali kuma yace.

“Ina kiranki baki picked mene dalili  my princess?”

Kauda kai tayi dan sam ko sau ɗaya bata jure kallon sa,

Domin yana da cikar haiba ƙwarai da gaske, jan numfashi tayi dai-dai kuma lokacin,

Da driver yaywa motar key suka fara tafiya tace.

“Bro! Nayi busy sosai ne”

Ta faɗa tana yin baya tare da kwanciya a jikin kujerar motar.

A lokacin ne kuma drivern ya cilla motar saman titin masarautar ya nufi babban gate.

Junaid ya fidda wani emotional sound mai ɗauke da manufofi da dama,

Kana ya shigayiwa Salimerh wani kallo wanda yake nuni da zallar so da kuma ƙauna kafin ya numfasa cike da jarumta da nuna cewa shima ɗin jinin sarauta ne, domin Junaid ɗane a wajan Otun (Galadima) yace.

“Nawa Abba magana akan abinda yake tsakanin mu, seriously bana son wani long time, please my princess help me”

Idanunta a lumshe sam a wannan lokacin bawai tunanin Junaid ɗin take ba,

Gaba ɗaya tunaninta ya tafi akan brother nata, wanda yake ɗaukan damuwar ta a matsayin tasa,

Amma yay mata nisa mai yawa yaya za’ai ta dawo dashi Nigeria zuwa Kanzaf, domin ya ziyarci bikin ODUN EGUN na wannan shekarar?

Ganin tai nisa sosai cikin tunaninta yasa Junaid miƙa hannu a taushashe ya kama nata hannun yace.

“Look! My princess love me or hate me is not my problem, amma dan Allah ki aminci da auran mu please dear”

Cikin rashin sanin abinyi kawai da jinjina masa kanta,

Cike da farin ciki ya zame hannunsa a nata yana faɗin.

“Ohh Wow! Junaid you’re the best thank you My princess”

Murmushi kawai tayi tana ci gaba da duba courses ɗin da zata karanta onder criminology justice kamar su.

Introduction to Criminology.

Theories of Crime Causation.

Human Behavior and Victimology.

Professional Conduct and Ethical Standards.

Juvenile Delinquency and the Juvenile Justice System.

Dispute Resolution and Incidents Management.

Criminological Research.

      *🇪🇸SPAIN/ MADRID*

Only you hotel atocha!

Babban hotel ne, wanda kana ganinsa kan cewa bana ƴan zauni gari banza bane.

Musamman yadda tun farkon titin da zai sadaka da hotel ɗin yake ɗauke da manyan jami’an tsaro (Securitie’s).

Haka kuma cikin hotel ɗin tun kafin ka shiga sai na’ura ta cajeka tsaf ta tabbatar babu abin cutarwa jikinka sannan za’a baka damar shiga.

Tun a reception na fara ganin manyan ƴan wasan Madrid sanye da farar riga wacce a gaban rigar aka sanya (Emirates fly).

Kowa na ɗauke da small bag a bayansa sai gorar ruwa mai sanyi.

Sai fitowa suke daga cikin room ɗin su gasu nan irin su ALABA, LUNIN, MARCELO, KROOS, ISCO.

BENZEMA ne ya ɗan ja Sirrin tsaki yana mai juyar da kansa gefe cikin harshen turanci yace.

“What the fuck”

Ya faɗa yana fesar da iska,

Sarai sauran sun fahimci dalilin daya sanya Benzema yace haka, amma no one’s talk dole su jira domin umarnin coach.

A can cikin room 212 kowa baka jin komai sai ƙarar gudun A.C da kuma ƙarar gudan ruwan dake zuba daga cikin shower, alamar dai wani ke wanka a ciki.

A hankali ya sauke wata zazzafar iska tare da sanya fararan teeths ɗinsa ya datse jajayen laɓɓansa da haƙoran,

Hakan ya samu asali ne sabida sanyin ruwan showern daya sauka saman ƙwantaccen gashin kansa wanda yake da tsayi sosai ainun domin ya sauka har ƙasan wuyansa,

Gashin baƙi ne siɗik amma daga ƙarshen gashin wanda ya samu nasarar kwanciya a bayan wuyansa ya kasance coffee,

Da sauri da sauri kuma ya shiga sauke ajjiyar zuciya yake ya ɗaga kansa sama ruwan da dukan fuskarsa yana sauke saman faffaɗan ƙirjinsa wanda yake cike da baƙin gashi,

Sun manne da farar fatar sa,

Idanunsa da sukai jajirr kuma yaja ya rufe bayan ruwa ya gama dukansu,

Yana da ƙirar sosai ga tsayi da kuma faɗin ƙirji ƙwayar idanunsa blue ce kana ganinsa zaka tabbatar cewa shi ɗin half-caste ne (ruwa biyu)

Gaba ɗaya jikinsa yana ɗauke da gargasa hakan yasa yake da yawan jin zafi,

Wannan dalilin yasa bai fiya zama da complete dress ba idan yana cikin room ɗin nasa,

A kasalance ya miƙa hannunsa tare da kashe shower,

Kana ya shiga wanke bakinsa da brush da yana gamawa kuma ya ɗauki bathrobe fara tas ya saka cikinsa,

Ya fito daga cikin bathroom ɗin kai tsaye kuma ya tsaya gaban dressing mirror,

Bai wani shafa komai ba sabida weather garin is too high!

Farin wando ya sanya wanda ya kasance 3gauther sai farar singlet,

A hankali ya sanya hannunsa ya ɗauki wani perfume Tom-ford ya fesa a jikinsa a saman singlet ɗin,

Duk wannan abinda yake kansa yaƙi tsayawa waje guda, sabida tsananin zafi da kuma azabar da yake masa,

Ga wani irin nauyi yau da kan yay masa yana jin komai ya tsaya masa sai wani shuuuuuu ya keji a cikin kunnuwansa!

IWC Schaffhausen Rolex ɗin dake tsintsiyar hanunsa ya duba yaga 3:48 gajeran tsaki yaja yana taune leɓansa tare da tsotsar na ƙasa ya shiga ganawa kansa a zaba,

Ƙara sauke numfashi yay yana mai tsitsyaya win a cikin glass cup kana ya kafa a saman bakinsa ya shanye tass,

Idan ta sabon shan win ya riga daya saba domin ya ɗauke ta kamar ruwa ne,

Amma duk da hakan tasbihi baya barin bakinsa yanzu ma cikin ransa yake faɗin.

“Astagafirullah wa’atubu ilaik!”

Ƙara duban agogon yay yaga 3:50 dai-dai kuma 4:00 za’a dake wasa wanda ya kasance wasan cikin gida, ma’ana zasu buga wasa tsakanin Madrid da Chelsea.

Bayan ya gama shan win ɗin ne kuma ya ɗauki farar rigar Madrid ya sanya a jikinsa nan take harafin A.M ya bayyana a bayan rigar,

Da sauri kuma ya ɗauki bag ɗin ɗinsa da lemon power horse energy ya fita zuwa reception ƙafarsa sanye cikin combust.

A can reception kowa gaba ɗaya ƴan wasan sun yi gaba kaɗan ya rage, cikin nutsuwa yake tafiya idanunsa yay jajir jijiyoyin kansa sun fito sunyi raɗa raɗa gaba ɗaya jikinsa tsuma yake,

Shi kaɗai yasan yadda ya keji, sosai naman jikinsa yake rawa kamar zai zame daga jikin ƙashi ya faɗo.

Coach ɗin Madrid mai suna Carlo Ancelotti, yana ganin fitowar sa yay saurin kama hannunsa cikin harshen turanci yace.

“ABU_MALEEK time is not our side, kasancewa kai ne ma dadin Christiano Ronaldo, kawo lokacin da muka rasa Ronaldo matsayin ɗan wasan Madrid muka fara samun matsala, amma daga lokacin daka dawo club ɗin mu komai ya dai-dai-ta, da buga ƙwallonka dana Ronaldo babu bambancin sam, But why are you doing this? Kana behavior like wani mental problem”

Ya ƙare maganar yana jan hannun wanda aka kira da ABU_MALEEK ɗin wanda a taƙaice mutane suke cewa A.M

Abu_maleek sam bai fahimtar zan can Coach ɗin nasu,

Banda duhu babu abinda yake gani dan haka kawai yake biye da Coach ɗin har zuwa cikin wata babbar mota lafiyayyiya,

Kai tsaye kuma suka nufi  *Santiago Bernabèu Stadium*

Lokacin tuni ƴan wasan Chelsea sun gama zuwa kowa yana riƙe da hannun yaronsa,

A.M na zuwa Coach ya ɗauki wani yaro sai bawa Abu_maleek da sauri kuma cikin tsananin a zabar daya keji yay gaba abinsa,

Dan a duniya ko kaɗan bai son ganin yaro musamman Namiji, hakan na tayar masa da tsohun tsumin dake zuciyarsa,

Kai tsaye kuma ƴan wasan suna fara shiga cike da ƙwarin qwiwwa musamman yanzu da suka san cewa Abu_maleek yana tare dasu, domin shine hope ɗinsu a wasan.

Yana gab da shiga tsakiyar filin wasanne kuma yaji kansa ya tsara nan take yaga wasu stars a cikin idanunsa a hankali kuma wani majic na shekara da shekaru suka fara gilmawa ta cikin blue eyes ball ɗinsa,

Nan da nan kuma jikinsa ya ɗauki rawa idanunsa suka firfito sosai,

Coach da tsoro ya kamasa zuciyarsa cike da fargaba ya ƙarasa inda Abu_maleek yake cikin rashin sanin abinda ke damun A.M ɗin ne kuma yasa Coach ɗin faɗin.

“Abu_maleek my champion what happened to you?”

Banza Abu_maleek yay masa a zahira ma sam baiji mai yace ba domin yanzu yana ɗaya cikin duniyar tasa ya fita daga asalin

Abu_maleek ɗin da suka sani,

Ganin hakan ne kuma yasa Coach cikin ɗaga Murya yace.

“Abu_maleek It’s 4:15 Already an take wasa me kake haka? Meye ya shiga cikin tunaninka ne? Ko kuma wasan ne baka so”

Abu_maeek ya juya da sauri sabida bazai jure ihun da Coach ɗin yake masa ba, yana ɗaga ƙafa da niyyar shiga cikin Stadium ɗin ne kuma yaji gaba ɗaya ya gama shiga ɗaya duniyar tasa a hankali ya ɗan dafe kansa yana taune leɓansa tare da furzar da iska daga cikin bakinsa cikin zafin harshe kuma yace.

“O’ohhhh”

Coach da ransa ya gama ɓaci ya ɗaga hannu zai riƙe A.m da wani irin zafin nama irin na ƴan ball da kuma juyewar tunani Abu_maleek ya sanya hannunsa ya shaƙe wuyan Coach tare da yin sama dashi.

    *SHARE FISABILILLAHI SABIDA ALLAH*

 _Bana sauri acikin tafiyar rubutun nan nawa, dan haka karatu za kuyi cikin farin ciki da kuma kwanciyar hankali, fatana kuci gaba da bin littafin *ABU_MALEEK* domin tafiya ce mai cike da ƙaddara za kuji sabbin abubuwa wanda dole za kuyi mamakin su amma babu mamaki a ikon Ubangiji, a next page ne kuma za kuji wani sabon part mai tarwatsa zuciya, ku nutsu ko fahimta sosai🥰☺️_

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *