ABU-MALEEK CHAPTER 6 BY Nimcyluv
Www.bankinhausanovels.com.ng
Baƙin zanan dake saman ƙirjinsa, zuwa ƙasan cibiyar sa, gaba ɗaya zanan wanda akai da baƙin abu ya mamaye ilayin farar fatar cikinsa,
Sai ya zamana kamar anyi masa zanan Tattoo ne,
A duk lokacin daya buɗe idanunsa yaga zanan sai yaji zuciyarsa ta halba tare da buga masa da ƙarfi,
Yana samun kansa cikin ruɗu haɗi da fargaba,bai san lokacin da zanan ya kasance a jikinsa ba,
Shi dai ya buɗe idanunsa yaga zanan,
Menene shi? Wane yay masa gaba ɗaya bashi da masiyyar komai,
Amma yana ji a ransa Tabbas akwai Ɓoyayyan abu game da wannan zanan,
Shiyasa baya taɓa bari wani ya gani,
Duk da cewa baya son zafi da kuma manyan kaya amma yana ƙoƙarin ainun wajan ganin ya bawa zanan kariya,
Lumshe idanunsa yay tare da cafko laɓɓensa na ƙasa wanda ya gama jiƙewa da ruwa ya shiga tsotsa tare da cijawa,
Ƙuri yaywa zanan da gajiyayyun idanunsa masu kaifi da sanya mutum cikin firgici,
Shi kansa a wannan lokacin yana son ya fahimci zanan menene? Amma duk yadda yakai dan son fahimta baya gane komai na jikin zanan,
Sai kuma baƙin zanan ya ƙara haska farar jikinsa, ya zama kamar wani adoo ne a jikin masa musamman shi da yake tare da turawa,
Cikin nutsuwa haɗi da kamewa ya miƙa hannunsa tare da ɗaukan bathrobe ya sanya jikinsa tare da covering ƙirjinsa sosai,
Idanunsa a lumshe lashes ɗin nan zara-zara, sai ɗigar da ruwa suke ga girar a cike baƙa sosai da ita.
Yana fitowa ya nufi dressing mirror yana daga tsaye ya ɗauki wani lotion mai kyau da ƙamshi ya shafa, sabida garin sosai yake da sanyi,
Yana gamawa ya ɗauki body spray ya fesa saman fatarsa,
Sai kuma ya ɗauki handrayer ya shiga gyara sumar kansa, ya shafa oil a ƙwantaccen sajansa,
Nan da nan kyau da kuma haibarsa haɗi da cikar zatinsa suka bayyana yay wani mugun kyau like takeaway,
Wata red ɗin Armless ya ɗauka wacce take da zip daga gaba amma yay unzipping rigar, sai hula red daya ɗauka ya sanya saman sumar kan nasa,
Ta rufe iya saman gashin banda wanda ya kwanta can ƙasan wuyansa,
Yasubuhanallah! A.m ya zama wani damn cute are extremely ɗin nan,
Long wando sleeves ya sanya wanda ya kasance blue black,
Yana gamawa ya juya walking slowly ya nufi Parlo hannayensa sanye duk cikin aljihu, duk da cewa sanyin bai damunsa amma yana jin yadda tsigar jikinsa ke tashi,
A Parlo ya samu sweet kwance saman 3seater tana bacci duk ta cure waje guda,
Tattausan Murmushi ya saki wanda iya saman laɓɓansa ne kawai, gently kuma ya nufi wajan deep freezer ɗin dake Parlon ya ɗauki zallar madarar shanu mai ɗan zafi kasancewar yau setting ɗin freezer,
Yana ɗaukan madarar shanun ya cire tankar Inibi guda ɗaya a hankali cike takun ƙasaita ya juya ya zauna kusa da kitty ɗinsa.
Daɗi da garɗin madarar ya haddasa masa rufewar idanuna ba tare daya shirya ba, sosai yake son madarar shanu tana ƙara masa kuzari musamman idan ta kasance zallar ba haɗi.
Idanunsa ya rufe sabida murɗawar da cikinsa yay, a hankali ya shafa cikinsa wanda ya kusan haɗewa da bayansa,
Daga can outside kowa wanda maid ɗin hotel ɗin ce ta shiga danna blet ɗin door ɗin tana jiran permission,
Taɓe baki yay kana ya Marai-raice fuska kamar wanda aka tilastawa magana yace.
“Come in”
Tuni daman ya buɗe da remote a hankali take turo table breakfast ɗin nasa,
Ko inda take bai kalla ba, sai rufe idanunsa da yay ya haɗe rai sosai,
Ƙasa tayi da kanta tace.
“Sir! Breakfast is ready”
Shiru yay mata ita kuma ganin hakan ya sanya ta ƙara maimaita wa idanunsa a rufe yace.
“Out”
Da sauri ta juya zata fita Murya can ƙasa yace.
“Come and pick your jagwalgwalo”
Yana faɗin haka ya miƙe tare sanya hannunsa ya ɗauki sweet kai tsaye art room ɗinsa ya shiga,
Ya ɗauki pen da different colors a hankali ya fara zanan idanunsa a lumshe a haka yake zanan,
Yana gamawa ya buɗe idanunsa dai-dai lokacin sweet ta farka ƙuri yaywa zanan yana kwaɓe fuska ya ɗauki sweet ya rungome tare da faɗin.
“What I’m did? Mace na zana ko namiji? Why kai babu gashi but ƙirji yay the same dana mace mai…,”
Da sauri ya shiru yana ƙara kallon zanan shikam duk sanda ya rufe idanunsa yay zanan abinda yake zanawa kenan ya rasa wacce kalar halitta ce macace ko namiji kullum kuma idanun a rufe suke mikewi yayi tare da rungome sweet wacce take ƙara shigewa jikinsa.
Alaafi Kanzaf
(Masarautar Kanzaf)
Da sauri yake tafiya cike da tashin hankali, ko inda Barori da Fadawa suke baya kalla,
Bare ya samu zarafin amsa masu gaisuwar da suke masa,
Yana tafe sanye da baƙar Alƙyabba mai ratsin fari,
Idanunsa sun kaɗa sunyi jajir sabida tsananin tashin hankali da kuma damuwar da yake ciki,
Kai tsaye sashin Mai Babban ɗaki ya nufa,
Yana zuwa masu tsaron ƙofa suka buɗe masa, cikin sauri ya sanya kansa ciki,
A babban parlo ya sameta zaune saman wata haɗaɗɗiyar ladduma, an cika gabanta da kayan itatatuwa,
Yana zuwa ya zauna a gabanta tare da haɗe ƙafafuwansa waje guda fuskarsa nan tasa kamar hadari babu walwala sam ko guda a cikinta,
Ganin yanayin da Adams ke ciki yasa Mai Babban ɗaki fahimtar Tabbas akwai abinda yake damunsa, ko kuma ya samu wani labari akan Mahaifiyar sa Queen Roomana.
Cikin nutsuwa da kuma son kwantar masa da hankali tace.
“kiloshèle?” (Meke faruwa?)
A hankali ya ɗaga idanunsa da suka rine da jaa,
Ya kalli Grandma ɗin tasa cikin yanayin dakewar zuciya da son ɓoye mata abinda ke faruwa dashi,
Ɗan ƙasa yay da Muryarsa very slow yace.
“shè Oba wani Aàfin?” (King yana cikin Masarauta?”
Da mamakin tambayar rainin hankalinsu ta kallesa, ba tare kuma da tace komai ba taci gaba da duba azkar ɗin hannunta kasancewar ta mace mai tsananin riƙo da addini.
Ganin yadda Mai Babban ɗaki ta share tambayarsa yasa Adams yaji zuciyarsa ta ƙara gamsuwa da abinda yake shirin faruwa a cikin Alaafin ɗin,
Yau kimanin sati guda kenan babu King Tunde Muhammad Jalal a cikin fada, ko tirakar sa babu mai shiga,
Ga tsananin da aka ƙara a cikin Alaafin ɗin, ko ina ka zaga securitie’s ne ta ko ina, ba kuma iya cikin Alaafin ɗin abun ya tsaya ba,
A’a hadda cikin Kanzaf ɗin, abinda ya ƙara tada hankalin sa da kuma jama’ar dake cikin Kanzaf ɗin,
Domin babu wani bikin ODUN EGUN da aka taɓa yi aka shirya wannan tsaron sai na wannan shekarar,
Cikin nuna rashin damuwa yace.
“Wani abu na faruwa a cikin Alaafin ana ɓoye mana, menene wannan abun, wannan tsaron duk na menene? Shin mu baza mu iya kare Alaafin daga abin cutarwa bane sai an kawo wasu securitie’s? Mene yasa King Tunde baya fitowa? Ance MALEEK ya mutu mene yasa bamu ga gawarsa ba why all this happened?”
Ya ƙare maganar in a commanding tune.
A ɗan gigice Mai Babban ɗaki ta kalli Adams, cikin Zallar mamaki da kuma al’ajabi ina ya samu wannan maganar? Yaya akai yasan cewa MALEEK ya mutu?
Cikin haɗe gira sosai tace.
“Kilodé to fè má inkán ton shèlé Ni Aaafin? Omàda ti obálé gbágbé oró na, ko béré sini ronú ibi ti iya re Oloori Roomana wá, shé won ti ku tábi won wá layé? Lati ma inkán ton shélé Ni Aaafin ma soro gidigàn. Kodi dádán Kori gbogbo owùn to shélé Adams”
Abinda tace a hausance Shine “Mene yasa kake son sanin abinda yake faruwa a cikin Alaafin? Zai fi kyau ka manta da wannan zan can, ka fara tunanin inda Mahaifiyar ka Queen Roomana take, da gaske tana raye ko kuma ta mutu? Sanin abinda yake faruwa a Alaafin zai maka matuƙar wahala, kuma sai sanya baka son abinda ba lallai ka samesa ba Adams”
Kallon Mai Babban ɗaki yay yace. “I have the right to ask, ɗan uwana yay nesa dani, an wayi gari babu Mami, yanzu ana maganar jinin ɗan uwa na, yanzu kuma almost 1week babu King Tunde, then Aremo Sharefddeen shike Zama a madadin King Tunde a fada”
Jinjina kai Mai Babban ɗaki tayi, idan hankalinta yay dubu to ya tashi, ganin bata da niyyar magana yasa Adams ya miƙe a fusace tare da yin waje.
Da idanu ta bishi domin tuni ta fahimci zafin kishi ke damunsa na ganin Sharefddeen a kan kujerar karaga.
Adams na fita ya haɗu da Iyalode ( Jakadiya) a hanya tana tafe tana ƴan dube dube kamar mara gaskiya,
Kwallon yadda bakinta yake rawa yayi, alamar dai akwai abinda yake cin zuciyarta, washe baki tayi tare da suma yi masa kirari sosai, domin shi ne bai fiya sakar mata fuska ba, sabida kasancewar sa mutum bai jin kansa da kuma tarin izzar Sarauta,
Kallonta yayi fuska babu yabo ba fallasa yace.
“Tauraruwa mai wutsiya…, Kura kike ga tsoro ga ban tsoro”
Ya ƙare yana cije bakinsa tare da binta da kallo, for the frist time kenan da yaji yana son yaji salon nata gulman dan haka ya bata all his attention.
Murmushi tayi tana ƙara waigawa kafin ta numfasa tace “Gobara daga Teku maganinta sai Allah, wani kaya ne ya sauka nasan za kaji daɗin kayan, musamman idan kaga launin su, amma kada ka faɗawa kowa nice na fara sauke maka tallan kayan kaji ko?”
Jinjina kai yay tana shafa ƙwantaccen sajansa kafin yace.
“Kice yau dawa tayi nama kenan, ta ina kayan ya sauka? A kuma hannun waya sauka?”
Da sauri tace.
“Naji labarin cewa, Oba zaiyi murabus wannan dalilin ya sanya Aremo Sharefddeen yake zama a fada ma dadin King Tunde, Ni kowa nace wannan ai son zuciya ne, da nuna bambanci ko dan anga babu idanun uwar ɗaki na”
Sai kuma ta fashe da kuka,
Tare da kama bakin zani ta shiga sharce majina da gefen zaninta, kana tace.
“ALLAH sarki uwar ɗaki na, nifa sam ban yarda da ɓatan ta ba, ƙilama ƙuruciya akai mata sabida mugun nufi”
Nan take zuciyar Adams ta hau bugawa idanunsa ya ƙara yin jaa da sauri yace.
“Naji daɗin wannan labarin, akwai kyauta mai tsoka anjima zan nemeki, amma da Sharefddeen ya hau kujerar nan ƙwara ni dashi mubar duniyar”
Yana faɗin hakan yay gaba kamar shirwa, har wani duhu yake gani a cikin idanunsa,
Yana barin wajan Aremo Shakiru na zuwa tun daga nesa Iyalode ta saki kuka tana rafka salati,
Da mamaki Shakiru ya kalleta kafin yay magana tace.
“Muhammadur Rasulullah (S.A.W) ashe kowa mugu ne, wallahi mutumin nan ranka yake nema, nikam nace sam bazan yaudareka ba, yooo ina dalili fisabilillahi? Gashi dai fari tass dashi kamar nunanniyar kabewa amma baƙar zuciya garesa kamar yadda fuskarka take baƙa”
Cikin rashin fahimta Aremo Shakiru yace.
“Meke faruwa? Waye? Kamata ace za’a ga baya na? Never wallahi?”
Cikin ƙara matso ƙwallar idanunta tace.
“Abun ba daɗin ci, nikam nace ƙilan yau ba zaka iya bacci ba, yanzun nan Aremo Adams yake tambaya ta, wai Meke faruwa menene sirrinka domin yasan ni kaɗai na san komai naka”
Dariya Shakiru yay sosai kafin yace.
“Nasan hakan zai faru, dan haka babu wanda yasan abinda nake shiryawa rabo dashi kawai, komai yace maki ki faɗa min”
Kai ta ɗaga masa a zuciya take faɗin “ɗan banza da hanci kamar bushasshen kifin miya”
Yana faɗin haka ya yi gaba abinsa,
Dariya sosai Iyalode (Jakadiya) tayi tace.
“Me nayi yanzu? Na ƙara wuta fetur kenan? Yanzu aka fara wasan?”
*ABU_MALEEK PAID BOOK NE, BIYA KUƊIN KI, DOMIN KASANCEWA MUTUM TA FARKO WAJAN SHIGA VIP GA PROMO ƊIN DANA BAYAR, IT’S 500 VIA 0116886423 SULAIMAN NA’IMA S UNION BANK EVEDANCE OF PAYMENT 08119237616 ƳAN NIGER SUYI MAGANA TA WANNAN NUMBER 84506476*
Washe gari da maraice, Salimerh na zaune a lambu, iska mai daɗi tana kaɗa yalwaraccen ganin kanta,
Tana sanye da Black Silk short robe, La Perla company’s, hannunta riƙe da wani ƙaramin bowl mai kyau cikinsa cike da cin cin da Samosa, daga gefenta kuma wata duguwar kujera ce mai kyau, irin ta hutawa,
Gaba ɗaya lambun cike yake da shukoki.
Yanzu saura 1week bikin ODUN EGUN kuma shi ne mutumin daya dace ya fita matsayin Masquerade amma baya nan yay za tayi yanzu? Shine kaɗai zai iya dakatar da komai cikin sauƙi, wayarta ta ɗauka a hankali ta shiga dailing number sa, cikin Sa’a number ta fara ringing,
Kamar a mafarki taji yayi answering call ɗin, da sauri ta juya domin ta tabbatar cewa babu kowa, cikin farin ciki har hawaye na zubu mata tace.
“ZAKI!” Sai kuma tai Shiru saboda kukan da yaci ƙarfin ta, jin yana ƙoƙarin kashe kiran yasa da sauri tace.
“Akwai Matsala zaki, how long zaka kasance a inda kake? Shin zaka dauwama a inda kake ne? Mene yasa baka tunanin kabar ni, kamar Abba, kamar Mami? Please come back to us kaji Zaki”
Shiru tayi tana sauraran abinda yake cewa duk da ba wata magana yake mai tsayi ba, amma yadda yake Maganar kaɗai zaka san cewa bai saba dayin maganar ba, ga voice ɗin nan very slow kamar mara lafiya,
Kuka ta sanya masa sosai tana ɗan buga ƙafarta, can sai dabara ya faɗo mata da sauri tace.
“What? King Tunde ya mutu? Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un!”
Shiru tayi sabida jin yadda yaja wata wahalalliyar ajjiyar zuciya mai ƙarfi, cikin farin ciki tace.
“Ok Zaki, come back soon, but nan da 3days kaji”
Jin ya amsa da “ok” yasa ta kashe wayar tare da miƙewa tsaye, tana ɗan tsallan farin ciki, domin idan har Zaki yazo to tabbatas komai yazo ƙarshe (anya?).
Da sauri Junaid take bakin ƙofar shigowa yay sauri ya juya cike kuma da tashin hankali, ya nufi sashin Otun (Galadima).
Mai Babban ɗaki da Oumuu-Ayman zaune a saman dinning table suna yin dinner a hankali suke magana yadda babu mai jin abinda suke cewa, Oumuu-Ayman na Shirin yin magana su kaga Bola ta ƙarasu wajan ita da Hadimanta, kamar zata tashi Idanunta ya kumbura saboda kukan data sha,
Tana zuwa ta kalli Mai Babban ɗaki da Oumuu-Ayman kafin cikin kiɗima tace.
“Da gaske MALEEK ya mutu? Shin da gaske ne an zubawa King Tunde Muhammad Jalal Goba a cikin Abin shansa? Da gaske ne kuma MALEEK ɗin ba mutuwa yayi ba ɓoye sa akai?”
*FREE PAGES YA KUSA ƘAREWA🥱 via 0116886423 sulaiman Naima s union bank evidence of payment 08119237616*
Wata zufa ce ta shiga karyuwa musu, gaba ɗaya tashin hankali ya gama baiyana a fuskokinsu, kenan Hadima Zubaida ce ta yaɗa Wannan maganar ko mene? Ko kuma wani ne yake bibiyar su ya kejin abinda ke faruwa da kuma abinda suke shiryawa?
Oumuu-Ayman bata iya magana ba, sai sunkuyar da kanta tayi ƙasa tunu Jikinta ya fara rawa shikenan kashin su ya bushe, rayuwar MALEEK ta faɗa garari.
Mai Babban ɗaki cike da nutsuwa ta kalli Bola tace.
“Ina kika samu wannan labarin mai kama da almara fa?”
Nan take Bola ta zaro wayarta tare da danna wani vedio nan take fuskar Hadima Zubaida ta bayyana, a tare cikin kuma tashin hankali da kuma rashin Sanin abinyi suka miƙe tsaye tare da haɗa baki sukace.
“Hadima Zubaida!!!?”
*ABU MALEEK, IT’S 500 08119237616*
Rugar Mahinjo.
Tashin hankalin da Julde da Madibbo suka shiga ba’a magana,
Julde ta ƙara shiga rayuwar ƙunci da kuma baƙin ciki,
Yanzu bata da kowa mai sonta sai Madibbo,
Bukkar aka shigo Madibbo ne riƙe da ƙwarya wacce ya ciko ta da Madarar shanu,
Jikinta duk rawa yake saboda yunwar daya gama cinta,
Idanunta na zubar da hawaye ta kafa kanta a ƙwayar ta shanye Madarar shanun tass.
Da kallon tausayi Madibbo yabi Julde a ransa yake tunanin tabbas yanzu lokaci Yayi da Julde zata san komai,
Da sauri ya miƙe ya fita bayan bacci ya ɗauke Julde wacce yanzu ta koma namiji sanadiyyar askin da akai mata, tudun manyan ƙirjinta ne kaɗai zai tabbatar maka cewa Julde macace,
Sabida Allah ya albarka ce da manyan ƙirji so ma sha Allah!
A can wajan Bukkar kowa, Arɗo ne da Lamiɗo sai ɗan gidan Arɗo mai suna Barkido, Arɗo yace.
“Domin tabbatar da ƙudirinmu akan wannan yaron Julde dole sai ya zama Namiji”
Gaba ɗaya suka kalli Arɗo, Barkido yace.
“Arɗo Tayaya mace zai zama Namiji kamanta da kalar Halittar su da nono ne?”
Dariya Arɗo yayi yace.
“Wannan ba matsala bace, zamu sanya ƙwarya mu murje Nonon nata, yadda zasu koma ƙanana daga nan kuma zamu sanya igiya mai faɗi mu ɗaure sauran”
Lamiɗo yay dariya yace.
“Amma menene damar maida Julde namiji?”
Barkido ne ya cafki zan can da faɗin.
“Domin zamu turata kiwo tare da addini shanu guda ɗari, kasance wa har yanzu muna samun barazana ga mutanan da bamu san ko su wanene ba, to matsalar yanzu basa kashe mata, mu koma burin mu a kashe Julde, wannan dalilin ya sanya zamu maida Julde namiji”
A tare suka saki dariya kana Arɗo yace.
“Maza Lamiɗo jeka ka ɗauko mana Julde naga Madibbo ya fita yanzu, shima da sannu zan nemu abinda yake ɓoyewa”
Can jikin dare kowa ya kwanta bacci, Julde na kwance tana bacci sai sauke Ajjiyar zuciya take, ga kannan nata sai ƙyalli yake, can cikin baccinta taji an fara janta da sauri ta farka ta shiga lalubar sandanta cikin siririyar muryarta tace.
“Madibbo na?”
Shiru taji hakan ya sanya ta ƙara buɗe baki zatai magana taji anyi,,,,,