ABU-MALEEK CHAPTER 8 BY Nimcyluv

ABU-MALEEK CHAPTER 8 BY Nimcyluv

                  Www.bankinhausanovels.com.ng 

Da wani irin firgici Adams ya runtse idanunsa, yana jin saukar maganar ta Queen Ayoola kamar saukar ruwan sama,

Tayaya JALALULDEEN zai ɗauke Mami?

Mene ya sanya ya aikata hakan?

Akan wanne dalili? Mene hujjar Jalaluldeen da zai sanya a ɗauke masa mahaifiya?

Tayaya akai ya faru? Bayan shi ɗin ba mazaunin gari bane?

Hannunsa ya sanya tare da share zufar data yanko masa,

Cikin Kaɗuwa da kuma tashin hankali Aremo Adams yace.

“Mumy! Ina kika samu wannan labarin wanda jinsa dai-dai yake da bugawar zuciyata, kada ki sanya na tsani jinina kuma ɗan uwa ne”

Ka faɗarsa ta dafa tare da ɗan matsawa ka ɗan tace.

“Haba Adams Tayaya kake tunanin zan sanya maka tsanar ɗan uwanka, na faɗa maka haka ne domin na isa na shaida maka abinda ke faruwa”

Kuka ta sanya masa tana ƙara faɗin.

“I’m just care about your mother ne, noting else dake da Jalaluldeen ai duk ɗaya ne, kasan Jalaluldeen he’s stubborn bazai taɓa tsayawa yaji abinda zan faɗa masa ba, 

Amma kai zaka iya tararsa kai tsaye ka faɗa masa, ko baya so dole ya saurare ka Tabbas zaiji maganarka Adams, ina cikin damuwa da tashin hankalin rashin Mahaifiyarku”

Jinjina kai yay cike kuma da son Queen Ayoola ya ɗan bata side hug tare da faɗin.

“I’ll talk to him Mumy, tabbas zan nuna masa kuransu dole duk inda ya kai min Mami ya fito da ita”

Kansa ta shafa kasancewar yau nrml shigar Yaruba yayi ko hula bai sanya ba bare wata Alƙyabba kafin tace.

“Let me have my way, kasan an fara shirin bikin ODUN EGUN”

Jinjina kai yayi domin baya jin zai iya magana a dai-dai wannan lokacin, tunani da kuma baƙin cikin abinda Jalaluldeen ya aikata wa mahaifiyar su,

Cikin damuwa yaja ƙafarsa tare da shigewa sashinsa, yana zuwa kayan jikinsa ya zame tare da faɗawa saman 3seater, tsaki yaja kana ya ƙara Miƙewa tsaye ya nufi fridge ya ɗauki ruwa mai sanyi yasha a hankali ya shiga sauke ajjiyar zuciya,

Sabida tafasar da zuciyarsa yake masa, a ransa yana kissima abinda zaiwa Jalaluldeen da zarar ya dawo, baya tunanin zai iya jiran dawowar sa dole yabi jirgi zuwa Madrid.

Da wannan tunanin Adams ya kwanta saman kujerar bayan ya gabatar da sallar Asar!

Da wani irin gudu ƙaramar motar ta shiga ta can bayan motarsa inda ƙofar baya take, wanda ba’a buɗe ta,

Daga ƙofar kuma zuwa sashinsa babu nisa, yana jin gine a bayan motar idanunsa a lumshe ya ringing sweet sosai wacce take ƙoƙarin kwacewa sabida mugun riƙon da yayi mata bana wasa bane,

Kwaɓe fuska yayi sabida wani irin bugawa da zuciyarsa take masa,

Kamar zata faso ƙirjinsa ta fito saboda yadda take harba masa,

Tafin hannunsa ya sanya ya ɗan tura cikin sumar kansa ya shiga hargitsa tulin sumar try to control his self,

Amma abinda ya kejin yafi ƙarfin ya samu nutsuwa,

Idanunsa a lumshe yaji anyi parking a motar, a hankali ya shiga buɗe idanunsa mutanan kuma daya gani yasa yayi saurin maida idanunsa ya rufe,

Ganin securitie’s ɗin ne kuma ƙara sanya shi gasgata zan can Salimerh, Tabbas akwai abinda ke faruwa a cikin Alaafin,

Bawai dan za’ai bikin ODUN EGUN ya sanya aka haɗa wannan tsaron ba,

Jin ƙarar buɗe murfin motar ne ya sanya ya ɗan ƙara buɗe idanunsa ganin Oumuu-Ayman ya sanya shi shagwaɓe fuska,

Cikin faɗaɗa fuskarta cike kuma da farin ciki ta miƙa masa fararan hannunta,

A karo na farko daya yayiwa wani murmushi kenan, cikin nuna jin daɗin ganin Oumuu-Ayman yasa A.M sakin lafiyayyiyan murmushi yana tsotsar laɓɓansa,

Tare da sanya tafin hannunsa cikin na Oumuu-Ayman, lumshe idanunsa yay lallai ya tabbatar yayi missed family nasa,

Yana fitowa daga cikin motar ya ɗan matsa kusan Oumuu-Ayman tare da shigewa Jikinta,

A hankali ya sauke Ajjiyar zuciya lallai Tabbas yayi rashin jikin uwa, jikin Oumuu-Ayman kaɗai yasa yaji nutsuwa inaga ya shiga jikin Miminsa?.

Kansa ta shafa tana ɗan Murmushi mai sauti tace.

“Wlcm back zakin zakuna”

Jinjina kai yay ba tare da yace komai ba, da sauri securitie’s ɗin suka shiga shimfiɗa masa wani farin carpet mai ɗauke da sunan JALALULDEEN TUNDE MUHAMMAD JALAL.

ganin ako wanne lokaci wani zai iya zuwa duk da cewa ba lallai ba, a hakan yasa Oumuu-Ayman sakinsa tare da yin gaba,

Cikin nutsuwa Abu_maleek ya sanya hannunsa tare da ɗaukan sweet,

Sarai yaga Salimerh yana sane kuma da kallon da take masa na ya naga guy ɗin nan ya zama Bature ne,

Carpet ɗin ya shiga takawa hakan yasa da ɗan sauri Salimerh tabi bayan A.m, yana gama shigewa sashin Salimerh ta shiga, securitie’s ɗin suka rufe da sauri tare da jan motar suka bar wajan,

Suna barin wajan Aremo Shakiru na zuwa kunansa maƙale da waya.

A.m kai tsaye sashinsa ya nufa ganin hakan yasa Salimerh yin gaba tare dabin wata hanya tabar sashin gaba ɗaya,

Domin babu wanda ya taɓa shiga sashin A.m dan haka ta rabu dashi sai ya huta sosai zata nemesa,

A gajiye ya shiga kutsawa cikin tafkeken sashin nasa wanda yake ɗauke da part biyu, amma da part 1 yake amfani,

Komai na sashin fari tass parlon farko wasu haɗaɗɗun kujerun ne farare dasu,

Sai fridge da ƙatuwar t.v ga a.c ta ko’ina sabida sam bai son zafin,

Tun daga ƙaramin parlonsa wanda daga shi sai bedroom ɗinsa ya fara zame kayan jikinsa, sweet kam tuni ta fara tsalle,

Yana zuwa bedroom ya faɗa bed ɗinsa tare da lumshe idanunsa yana cije bakinsa Wheel zuciyarsa na wani irin bugawa da ƙarfi wacce bai san dalili ba.

Turo baki yayi yana shafa sumar kansa tare da jan nippy ɗinsa a sanyaye cikin zazzaƙar Muryarsa yace.

“Yeah, i love my family but zaman Alaafin it’s difficult to me, ihu, surutai, hayaniya cai cai cai i hate Wannan Al’adun, Ya Rabb!”

Ya faɗa yana dafe goshinsa,

Miƙewa yayi tare da shigewa bathroom y sakarwa kansa shower ruwa mai sanyin gaske ya shiga sauka a saman farar jikinsa, da sauri ya shiga sauke ajjiyar zuciya so da ƙaunar ganin Maminsa ya saukar masa,

Uwa mahaifiya yau kam a jikin Maminsa zai kwana.

Murmushi ya saki yana tsotse ruwan dake saman lips ɗinsa a fili yace.

“She will be proud of me, nasan za tace na zama ƙatutu na zama saurayi big boy, and I’ll tell har faɗa zan iya tarewa kai na, bana faɗa ma Mimi cewa zanyi ƙarfi ba”

Ya faɗa yana jinjina kai irin saima wani ya taɓa sa ɗin nan.

A haka ya gama wankan ya fito sanye da bathrobe, jikinsa yana ɗigar ruwa ya ɗauki wata Armless mai shot hand ya sanya kana ya zuga zip ɗin,

Sai 3gauther daya sanya ya fesawa jikinsa turare,

Wani Vally’ Slippers ya sanyawa fararan sawayansa,

Kafin ya ɗauki ribbon ya tare sumar kansa waje guda ya ɗaure, murɗaɗɗan jikinsa ya bayyana sosai, ya zama ƙato mai cikar zati da haiba ga kuma tarin kwarjini,

Kai tsaye fita yayi daga sashin ya nufi main Parlo ɗan zaro idanunsa yayi saboda ganin Oumuu-Ayman zaune da table ɗin lunch yana ganinta ya shagwaɓe fuska,

Tare da ƙarasawa kusa da ita ya zauna ba tare da yace komai, ba tare da tace komai ba ta shiga haɗa masa lunch ɗin Yam-flour (Amala) sai Ofada rice with Efo riro (vegetable soup)  yana jin ƙamshin abincin ya lumshe idanunsa tare da matsawa sosai kusan Oumuu-Ayman ya matsu yaji abincin a bakinsa sosai yayi missed traditional food ɗin su.

Abincin ta ɗauka zata basa a baki, yace.

“No! Oumuu”

Kai ta girgiza masa tace.

“Yaushe rabon dana baka abinci a baki”

Lumshe idanunsa yay Lokacin daya buɗe ƙaramin bakinsa ta sanya masa abincinsa, daɗin abincin ya sanya ya lumshe idanunsa tare da ƙwace spoon ɗin a hannun Oumuu-Ayman yana faɗin.

“I’m 35 yrs Oumuu, so I’ll peed myself na girma yanzu”

Jinjin daɗin ganin Jalaluldeen yasa Oumuu-Ayman ta kasa ɗauke idanunta daga kansa, ya zama wani ƙatoto kamar basamude.

Duk kallan da take masa yana sane, a haka yaci abincin sosai kana yasha ruwa mai sanyi,

A hankali yayi hamdala kada ya kwanta jikin Oumuu-Ayman tare da juya mata bayansa ta gane abinda yake nufi, bayansa ta shiga shafawa har sai da yayi ƙyasa kamar jaririn da yasha Nono.

Miƙewa yayi zubbur da sauri itama Oumuu-Ayman ta Miƙe tare da faɗin.

“Ina zaka kuma, yana da kyau ka huta kasan babu wanda yasan ka dawo, kuma bana son a san ka dawo har sai bikin ODUN EGUN yazo”

Girgiza kai yayi a can ƙasan maƙoshinsa yace.

“Oumuu, Mami nake son gani, ina son naga how is she, then Dady wallahi i missed them sosai”

Zuciyar Oumuu-Ayman ta buga da ƙarfin gaske ta san cewa wannan surutan ita kawai zaiwa sai Mai Babban ɗaki da King Tunde da Mami, banda haka tari ma sai ya zama dole zai yisa, amma ya zama dole ta faɗa masa komai sabida sai yafi fahimta rashin gaya masan kuma babbar ilane, yanzu zai hauka Alaafin ta san halinsa tun yana Ƙarami har kawo lokacin daya bar Alaafin saboda ƙaddarar data faɗa masa, kama hannunsa tayi ta zaunar tashi cikin nutsuwa tace.

“Abu_maleek abubuwa da yawa sun faru, ina fatan zaka fahimta da kuma saurara, nasan baka shiga sabgar kowa amma a wannan lokacin dole ka sanya idanu a kan takun kowa, dole ka kwatarwa kanka ƴan ci da kuma ɗaukan mataki akan wanda suke son ganin bayanka”

Kallonta yayi da idanunsa wanda suka fara sauya kala kafin ya sauke numfashi ba tare da yace komai ya maida kansa ƙasa tare runtse idanunsa ya shiga taune leɓansa.

Cikin nutsuwa ta zayyana masa dukkan abinda yake faruwa, daga ɓatan Queen Roomana zuwa rashin lafiyar sarki, kawo ɓoye Maleek da sukai, zuwa Ɗaure Hadima Zubaida.

Tunda kafin ta gama magana jikinsa ya ɗauki ɓari jijiyoyin kansa suka miƙe tsaye,

Banda karkarwa babu abinda jikinsa da yake musamman kansa.

Ganin abinda ke shirin faruwa ya sanya ta riƙe sa sosai, tare da kama kansa ta shiga tofa masa addu’a, almost 10minute kafin ya shiga sauke ajjiyar zuciya a haka har bacci ya ɗauke sa.

Zamewa tayi ta kwantar dashi saman kujerar tare da ƙaro gudun a.cn kana ta fita.

 Rugar Mahinjo

Tun daga lokacin dasu Arɗo suna ganawa Julde azaba, basu ƙara waiwayar inda take suna jiran ranar da suka ɗaukan mata ya cika.

Julde kam kullum da wani irin azababban ciwon ƙirji take kwana, har lokacin kuma ta kasa faɗawa Madibbo abinda akai mata,

Har lokacin kuma igiyar da suka ɗaure mata nono tana jikinta dalilin daya sanya take kasa Numfashin yadda ya kamata. Rayuwa tai mata zafi da ƙuna duniya tai mata duhu sosai babu wanda take buƙata a yanzu face wanda zai taimake ta, ya ɗauke ta daga cikin Rugar baki ɗaya.

    *Gobe in sha zan gama free pages wanda suka kasance na farko wajan biya za’a sasu a vip, ma’ana inda za’a dinga posting biyu kullum kenan*

Tun daga wannan lokacin Abu_maleek ya daina fara’a bare walwala Hatta Oumuu-Ayman daina yi mata magana yayi,

Ya keɓe kansa shi ɗaya baya cin komai sai fruit sosai yake neman wanda zuciyarsa zata tattauna dashi amma ya kasa bawa Kowa wannan damar.

Ɓangaren Adams kam shirya yadda zai tafi Madrid yake domin yaje yaji dalilin daya sanya Abu Maleek ya sace masu uwa.

Kawo lokacin kuma babu wanda ya san da zuwan Abu Maleek ɗin.

Kwanci tashi babu wahala Yau ya kasance gobe ya kasance ranar da Za’ai bikin ODUN EGUN tun yammacin yau manyan sarakuna da kuma manyan mutane jirginsu ya dinga sauka a garin Benin.

Mutanan Kanzaf kowa ka gani yana cikin farin ciki musamman daya kasance zasu haɗu da nagartaccen Oba ɗinsu mai jin tausayin su.

Tun a Subhi tsaron Alaafi ya tsananta baka ganin komai sai securitie’s,

Shiri na musamman ake, har lokacin kuma babu wanda yasan cewa King Tunde Muhammad Jalal babu lafiya.

Biki yayi biki taron jama’a a cikin Alaafi ba’a magana, banda busa da sarewa haɗi da kide-kide babu abinda ake.

Wani mutum ne ya shigo filin wajan an rufe masa jiki ana kiɗa yana rawa wasu kuma suna Performance magic,

Bayan haka aka dafa doya aka bawa Kowa, sannan aka raba wa kowa emu (win) daga nan aka fara sanarwar ga King Tunde Muhammad Jalal ne zai fito yaywa jama’ar Kanzaf godiya ya kuma shaida masu yana mulki cikin jin daɗi da kwanciyar hankali.

A hankali ya shiga sauke sandar hannunsa a ƙasa yana taka ƙafafuwansa cike da zallar isa haɗi da kamewarsa, yayi shiga ta sarkin Yaruba, ya rufe fuskarsa,

Sai kirari ake masa ana buga tambura, Abu Maleek runtsa idanunsa yayi yana jin kansa kamar zai rabe gida biyu,

Idanunsa yayi jajurr saboda kiɗan dake hawar masa ka,

Da wani irin sauri kuma zuciyarsa ta shiga bugawa tashin hankalin ya ƙaro,

A hankali ya shiga ɗagawa jama’ar wajan hannu alamar gaisuwa har ya isa mazauninsa yana shirin zama, maimakon ya zauna sai aka ga ya zabura tare da yin.

   *DAN ALLAH ALLAH DAN ANNABI KADA KI SIYI LITTAFI NA DA NIYYAR YAƊA MIN SHI, KIJI TAUSAYI NA, KI DUBA GIRMAN ALLAH DA ZATINSA, IDAN KINA SO KI SIYA DOMIN ABINDA KAKE SO BAZAI TAƁA FIN ƘARFIN KA BA*

 Baya ya juya da sauri dafe da kansa ya juya masa yana jin kamar zai rabe gida biyu,

Da mamaki gaba ɗaya jama’ar wajan suka fara bin bayansa da kallo, sam ba haka King Tunde Muhammad Jalal ya zaba yin bikin  ODUN EGUN ɗinsa ba,

Abu Maleek kai tsaye part ɗinsa ya shige yana jin kamar duniyar zata kife dashi.

Yana shiga ya fara cilli da kayan jikinsa yana watsarwa,

Taune leɓansa yayi tare da sanya hannunsa ya dafe kansa dashi, cikin ƙasa da Murya yace.

“O’ohhhh”

Wannan alama ta cewa gab yake da shiga ɗaya duniyar tasa tunaninsa na neman juyewa.

Saman bed ya faɗa yana ƙanƙame jikinsa waje guda, ga wani irin ɓari da jikin nasa yake masa,  a haka bacci yay gaba dashi,

Da ƙyar yayi sallar Subhi, a lokacin ne kuma zan can rashin lafiyar King Tunde ya bazo a cikin Alaafi dama Kanzaf baki ɗaya, al’amarin daya tayar da hankalin jama’a kenan kuma an rasa ta yadda zan can ya fasu.

Misalin 11 na safe Abu Maleek na zaune saman kujera watching TV amma gaba ɗaya hankalinsa baya ga abinda yake kalla,

Tunanin sabuwar rayuwar daya tsinci kansa ya yanzu ita take masa yawo a zuciya shi kam sam bazai iya ba,

Madrid zai koma bazai iya zama cikin Alaafin ba abubuwan cikinta sun sama girma.

Da sauri ya miƙe ya shiga haɗa kayansa, yana shirin fita aka shigo Sashin nasa da sauri kallon juna sukai shida Salimerh wacce Idanunta ya kumbura saboda kuka cikin tashin hankali tace.

“Abu Maleek kazo inji Mai Babban ɗaki, jikin Dady ya tashi sunanka yake kira”

Wani irin dafe ƙirjinsa yayi saboda tsallan da zuciyarsa take masa,

Bata tsaya jiran komai ba  taja hannun Abu Maleek zuwa sashin King Tunde Muhammad Jalal.

Tun daga bakin babbar ƙofar yasan cewa Tabbas babu lafiya, idanunsa ya runtse tare da tura kansa ciki,

Gaba ɗaya kallo ya dawo kansa, idanun Kubraah da Bola ne suka firfito saboda tsananin mamakin ganin mijin nasu,

Sharefddeen, Shakiru, Adams, da kuma ɗan gidan Otun (Galadima) wato Junaid duk suka tsora masa idanu da Alhinin ganinsa, hakama Otun yabi Abu Maleek da kallo,

Babu kamar Queen Ayoola.

Babu wanda ya kalla a cikinsu ya nufi wajan mahaifin nasa tare da zuwa wajansa hankali tashe saboda ganin baya motsi sai kumfa dake fita a bakinsa, jikinsa yayi wani mahaukacin zafi.

Miƙewa yayi zai fita saboda sai a lokacin ya tuna shifa likita ne mai zaman kansa.

Otun ne yay gyaran murya da sauri Malamin dake duba Kinga Tunde Muhammad Jalal yace.

“Ciwonsa bana asibitin bane, domin samu maganin da zai warkar da King Tunde Muhammad Jalal dole ne aje BIRNIN BERA”

gaba ɗaya suka haɗa baki wajan faɗin “BERA??”

kai ya jinjina masu yace.

“Tabbas, a can ne kawai zai samu wani babban Malami ya bashi maganin da za’a bawa King Tunde,domin mutum shike ne kawai yake da wannan maganin, dan haka a cikin Aremos dole ɗaya zashi”

Adams najin haka ya miƙe tare da ficewa a hankali Shakiru ma ya miƙe alamar ba zasu wannan garin da ake cinye mutanan da ransu ba,

Kai tsaye Sharefddeen yace.

“Ga Abu Maleek nan I’m sure zashi, Daman shine yake son tafiyar nesa”

Kubraah da Bola suka shiga girgiza kai alamar ba zashi ba shima.

Oumuu-Ayman ce tace.

“Tayaya Abu Maleek zashi garin da babu wanda ya sani, kusan shin da ƙin yarda babban matsalar kuma kunfi kowa sanin ciwonsa lokacin da ciwon ya tashi Tayaya zai kare kansa? Waye zai taimaka masa?”

Kafin wani yay magana Abu Maleek yace.

“Zani, ku shirya tafiyar zuwa gobe”

Jinjina kai Malamin yayi yace.

“Domin zuwa Birnin Bera, dole ka zama mahaukaci, domin za kace kai kake fama da ciwon, dole za’a aske maka gashin kanka, za’a cire maka sumar fuskar ka, kuma dole za’a shafa maka baƙin fenti domin basa son farara mutane, idan ba haka ba kana zuwa sukai ido huɗu dakai suka kalli fatar jikin ka fara to Tabbas sai dai wani bakai ba…..

    *KUN SHIRYA…????? GUY’S U CAN START YOUR PAYMENT 500- VIA 0116886423 SULAIMAN NA’IMA S UNION BANK EVEDANCE OF PAYMENT 08119237616*

    SHARE FISABILILLAHI SABIDA ALLAH DA ANNABI👏🏻

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *