AHUMAGGAH CHAPTER 1
Misalin karfe 6 na safe ne,Juyi nake ina kikkiftawa salon kwace baccin gajiyar da har yanzu yake bibiyan idanu na. “Yau ma Daga inda nafi kwanciya a chan dungun daki na tattaro karfi na duka nayi mika don na watseke,da kyar na waro idanuna dan kuwa Bibbiyu nake gani har wani jiri ke deba na,hakan kuwa bai hana ni daddagewa na zauna tsam ina muzurai ba sai dai duk da haka idanuna sunyi dishi dishi kamar wata mai kallon gajimare. sanda na dauki mintuna uku da hannun dama na ina yarfe su kafin suka dawo min normal sai dai har yanzu Basu nuna min abbu na ba. ‘Wani irin faduwar gaba ne ya taso min”Innalillahi wa inna ilaihi rajiun! Na furta acikin zuciya na.Wani mugun fargaba ne naji ya rufe ni atake,a hujajan na mike tsaye ina dube dube dan bansan sanda sanyin sautin murya na ya fidda sautin sunan sa ba’..cike da damuwa na fito ina cewa ABBUH…! …jiya cikin dare Abbu ne akwance kusa dani kamar gawar da yaki kabarin sa. Dan Daga ni har shi bansan ya akayi safiyan yau ta riske mu ba. duba shi na shigayi sai dai ina dora kafata bakin dakin daya raba jingar karar dake tsakar gida sai na hango rayawar karan masara har an sakaye kofar bayi dashi alama nacewa da mutum aciki yana zagaye. ‘Bayin nadan bi da ido na dan wani lokaci domin na tabbatar ko shine aciki,bayan kamar minti biyu nayi ajiyan zuciyan tare da sauke boyayyen nishi nan na juya na koma cikin dakin dana fito. “…Yagaggen Tabarman kajinjinin dabinon da muke kwana akai na dora hannu na akai na jawo shi batare da na nade ba na karkade duk kasan dake kai na fito dashi waje. A jikin dangar kara daya suturce mana asirin jimammiyar muhallin mu na tsaya,sanda na zare kararen da suka rage mana na hura wuta sannan na yarfa tabarman akai na juyo tsakar gida. Daga nan A Gaban wata dakilalliyar ramin murhu nayi tsugune,Hura wuta na shiga yi da gaske domin sanyin safiyar mu ta sha banban dana kowa a yankin mu. “Sunana Bahiyyah Ahmadu Alba. ni Bansan daga ina muka fito ba bare nace na san asalin mu amma yanzu haka a wata katafaren yankin jeji mai tsananin sanyi da duhun itacuwa muke zaune nida iyaye na da jinsin zuriar wasu fulani wanda su ba bakake ba kuma su ba farare ba. Nan din Yanki ne Daya tsaga tsinin kahon nahiyar africa,Kenan mu ba acikin wata kasa muke ba. A cikin kasashen afurka da suke zageye damu kuwa sun hada da ethiopia,somalia,djoubuti da cibiyar bahohin ruwa guda biyu wato quardafui da somalian sea,sai kasar kenya dake gudu maso gabas. Shiyasa ma idan anka duba yankin mu da kyau sai inaga kamar muna cikin wani tsauni ne a chan Cikin dajin daya ya raba gulf of eden da kuma bahar maliyar(red sea). Tsawon shekaru na a duniya na dauka acikin wannan yanki aka haife ni,Sai dai nasha mamaki sosai a lokacin da ammu wato mahaifiya ta tazo gaban ta na mutuwa. Anan ta take sanar da ni cewa ita cikakkiyar yar kasar somalia ce. A somalia jinsin yare biyu ne,ko ka kasance arab ko dan somali. Toh Ammu na balarabiya ce tar dan cemin tayi bata ma jin yaren su na somali a duk dama larabci da somalin suka dai ne yaren da ake yi a kasar.. Tace min Abbuh wato mahaifina kuma dan yankin ethopia ne gaba da baya,A wajen cin kasuwanci a boader chan mahadan su dake wajen kasar djibouti ta hadu dashi. soyayya mai tsananin karfi yayi sanadiyar auren su. Daga nan A takaice Iyaye na sukayi zaman aure a kasar ethiopia wato garin mahaifina sai dai Rayuwa na shudewa dangi suna ta mutuwa,kafin a hankara rayuwar iyaye na ta koma garin mogadishu wato state capital na kasar somalia nan inda aka haifeni. Anan ma Ko shekara guda banyi ba Koluluwar Yunwa Da jarabar tsiyan talauci irin na kasar somalia ya sa akayi wata karamar yakin daya rabamu da kowa da komai namu a duniya. Dan haka muka yi hijira muka bar somalia,dan tun ina Jaririya hijirar ya kawo mu wannan dajin inda muka hadu da jinsin zuriar fataken fulani mu kayi zaunen mu a cikin su muna rayuwa. Gashi har Yau shekara ta goma sha hudu bamu bar nan ba. A shekaran daya gabata ciwon daji yayi sanadiyar mutuwar Ammuh kuma tun mutuwar ammun Abbu ya kamo da mummun ciwon zuciya wanda nikaina na rasa gane wata irin tsaninin so da shakuwa ne ke tsakanin su,my dad cannot live without my mum1 shakuwar su tasha banban da irin shakuwar masoyan zamanin yanzu. A da chan,Allah ya bama abbu na baiwar magance cututtuka da sanin warakan ciwo ko da sanadiyar mutum ne koko na aljani. Abbu na yana da baiwar shiga jeji yayi farauta kuma ya tsinko ganyayyaki,itacuwa da saiwa kala kala,yana kuma iya sarrafa su ta yadda yake so domin a samu sauki,da waraka akan kusan ko wani irin cuta. Tsawon shekaru yana taimakawa amma yau Sai gashi har Abbu na yakasa gano itace ko wani ganyen da zai masa maganin Ciwon son ammu na dake damun zuciyar sa. Mutuwar Ammuh kamar faduwar wata danga ce agare mu gashi abbu yasa abun aransa sosai fiye ma dani. “Sai Gaba daya ya dena fita ko ina,tun lokacin ya tsayar da duk wani harkan sa ta siyar da magani gashi har ciwon zuciyar yayi tsanani ya kama shi ta inda bazai ma ji maganin gargajiya akan lokaci ba. A Yanzu Buri na na sami taikamakon da zai wadatar dani har na kaishi ganin likitar bature a chan yankin kasar egypts inda nake karatu dan naga suma suna shigowa kasuwanci a yankin mu kuma bamu da wani nisa sosai. Ko da nayi yunkuri sai naga Jikin abbu yaki sam,A kullum tsoro na kar abbu shima ya mutu ya barni dan bansan ina zanje ba. ………. A haka Ina zaune gaban murhun,idanuna sun yi lufu lufu da hayakin danyen karar dake ci Da kyar wutar murhun ta kama tana ci bal bal tashi nayi na jawo kwaryan dake gefe na,don kafin nan na dan tsaftace wajen danake zaune,sai kawai na dora sauran gasashen namar rago da muka ci jiya domin shima ya turara musamu na sawa a bakin salati. Asali dai Bamu cika cin abincin da ya shafi ganye ko itacuwa ba,,dani da iyaye na gaba daya We are not much of vegetarians. Dana zo daga baya ma na san asalin tarihin ammu sai na dena bata lokaci na wajen nazarin yanayin cin abincin mu. Ammuh tace min a chan somalia haka nan suka saba iyaye da kakanni,suna nomar turmeric wato(kurkurm) curry da kuma corriander,abincin su kuma daga namar rago, namar shanu kaza da tinkiya, Sai basmati rice. Hakan ya dada bayyana min tasirin halin talaucin da kasar somaliar take ciki,amma tunda muka dawo nan alhamdullhi zamu ce,duk dama munsaban amma Abbu wata rana yakan sa muci zallan yayan itacuwa ko ganyen alaihu,tufa,cerely,gurji,karas,ibini da dabino da kuma ganyen lettuce. Mukuma mukan bashi hadin kai ne A matsayin sa na masanin kariyar cuta sai muke biye mashi mafi akasarin lokuta muke sauya abinci. “Ina zaune gaban murhun,Daga baya na na Ji karar sautin takun sa,mikewa nayi na juyo ta inda zan ganshi da kyau as usuall tsaye yake cikin dakakkiyar rigar jumfa wacce take suluk babu shape,rigar ya dan tsuufa amma fari ne tass wandon kuma kalar kasa ne,he is looking neat babu lifo,don a duk dama ni karama ce bai hanani tsaftace abbu na ba. Tsaye yayi hannun sa rike da buta ya tsura min hasken fararen idanun shi yana kakalo murmushi kamar bashi bane mai sani kukan tausayin kaina ko wani dare. Domin son yaga nayi murmushi sai ya yabani da kalman larabci yana mai cewa Saiiqah…yah noori…! Nikuwa Yadda ya furta kalaman nan naga kuma yana kallo na yana murmushi sai ya sani naji wani tsananin kaunar sa da tausayin sa ya tsuma ni…a take na mike tsaye ina kallon shi Hannun shi naga ya ware duka biyu ya buda min,ni kaina Bansan sanda na taho kusa da shi na rungume sa ba..gam ya dada matso ni tamlar wanda zai maidani cikin sa”wani sanyin hawaye mai shiga rai shi ya kufce min ayayin dana kankame sa nima jiki na dik yayi weak a haka na furta ABBUH ban karasa ba….sai naji ya shafa kai na,A hankali na kuma furta ABBUH NA, HAMMAM dina, Wano Dada kankame ni yayi jikin sa sai rawa yake alaman shi kadai yasan meya keji ajikin nasa,a haka ya dago fuska ta zuwa nashi yana min murmushi mai taba zuciya da sa sanyin rai… Yace yata shin waya koya miki kalmar “hammam” bacin nasan ke baki iya larabci ba?..hakika kalman tayi min dadi…bayan matata zaynah,a duniya ke kadaice zaki iya gayamin wannan kalma mai dadi kuma naji dadin shi. Share guntun hawaye na nayi ina murmushi sai Na sunkuyar da kaina na seconds biyu.. Cikin farin cikin da bansan na meye bane na furta. “Abbu,ranar a kasuwar kofar gidan modibbo naji wani balabaren egypts yana fada ma sarki ‘hammam” shikuma sarki yaji dadi sosai har ya masa kyautar azurfa. Shine Sai na tambaye shi ma’anan kalman shine yake cemin kalma ce ta girma kuma ba’a cewa kowa hammam sai mutumin da ya cika abun Alfahari,abun koyi,abun kauna kuma abun tinkaho..2 Hannun shi na kama fiska ta na sake wasu irin disasshun murmushi: nace Abbbu..kai ne abun alfahari na Allah ya baka lpya abbu na. Dan Shiru abbu yayi,Sai Na lura tsaban farincikin abun da nace yanzun yasa abbu na baice komai ba. Nidai karamar ajiyan zuciya nayi Hannun shi dake famar sacewa da tsaninin sanyin dake busowa na riko cikin idonshi na furta …wai shin yaushe zaka warke muje jeji ne,..?abbu na Ina so na raka ka deban magani kaga kwana biyu kudin mu duk sun kare..ko ka mance lokacin da kake dauko ni akafada muna tsintar ganyen mu?ko dan ammu ta barmu shikenan kai zaka dena rayuwan ka dani?. Kokarin Sake kiran sunan shin zanyi amma ban ko karasa kalmar ba ya rufe min baki na da yatsun sa..cike da sanyin jiki ya jawo ni jikin shi Tsam sai naji ya sake rungume ni.. Wani Ajiyan zuciya na sauke Nima sai na lafe ina mai sauke ajiyayyan numfashi. Wani shiru ne ya ratsa tsakanin mu Tsawon lokaci sannan abbu ya dago ni yana mai kallon fuskata,nima kallon sa na tsaya yi dan daga ka ganshi kasan maganar dana furta ne yayi tasiri a zuciyar sa sosai. But Maybe am too young to understand what love is shiyasa bazan fahimce rashin dauriyar sa akan soyayyar sa da ammuh ba. Anma kuma Ba sai an fada min ba nasan abbu yana nadaman sakani cikin halin da nake ciki yanzu sosai. Sai da ya kure ni da ido Kafin ya numfasa da dai Kamar wani magana zai min sai naga ya sake min hannu na da sauri ya juya dubar sa kan abunda na daura akan murhu.. Ashe namar dana daura a wutar ne ke famar babbakewa nikuwa tsaban shaukin kasancewa tare da abbu na yasa ban ma ji ba,da azaman sa ya sauke namar yana yarfa hannu… Da sauri na matso,ina cewa mugani…tafin hannun shin na riko inda ya kone ina furawa da iskan baki na inai masa sannu cike da so da kulawa.. Ina Cikin haka Kwasam sai naga dison Hawayen shi ya digo akan hannu na daya ke cikin nashi,sai dai bai ma bari na daga ido na kalle shi ba ya goge idanun shi da sauri ya kuma zaunar da ni kan dutsin dake wajen baice uffan ba ya juya abunshi Nidai Ina ta kallon shi Har ya gama tsatsame naman ya aje agabana,sai ya dauki kwara guda Yace yi bisimillahi Inayi kuwa ya kaimin namar bakina. Mahaifi na kkyawar mutum ne sosai duk dama wahala ya tsufar dashi amma kuma farin fata,bakin gashi da manyan dim eyes dinsa su suke yawan sani Lumshe ido a hankali ina kuma sake budewa Cikin sauki Yake sakamin ina taunawa a tsanake. Sai da nakai kusan sau hudu kafin nima na yanka bari guda na kai mashi bakin sa.. Ya na kan ci..sai na kirashi nace “Abbu cikin son na sa shi dariya..sai kuwa ya amsa ni da na’am noor! Sai nace wai Meyasa ka daina kira na da asalin suna na?ko ya dena maka dadi ne.. Faffadan Murmushi kawai yayi yace,ai ko bayan raina ne, nasan kuwa akwai mutane dayawa a doron kasa da zasu kira ki da asalin sunan ki BAHIYYAH ta. Amma kinga ni? Dole na girmama ki da sunayi da yawa.. Dariya mai sanyi kawai nayi ganin murmushin karfin halin da yake min yana kuma maganan cikin raha pretending to be ok bayan nasan ba yajin dadin. Sai ya dafe tsakar kaina with much serious tone kamar wanda zai yimin wata muhimmin addua..Yace bahiyyah kincancaci a kira ki saiiqa..sabida ke alheri ce kuma akan hanyar alheri zaki dawwama har abada. Kece ..noor wato haske,hasken rayuwar iyayen ta…sai yayi murmushi.. Hawayen dake hargowa a idanu na na tare cikin karfin hali nayi murmushi nace ..abbu dayan fa? Baice min komai ba Hannun shi ya sauke kawai yana murmushin sa,sai da ya sake yankar namar zai kai min baki kafi yace Almass?(diamond)kar ki damu dashi.4 Nidai Kiyi hakuri bahiyya tah,nasan Abbu sam baya kyautawa yar sa. “Ina kan tauna na baki na, sai nace hakuri akan me kuma abbuh na?bai amsa ni ba sai yace min nayi miki Alkwari bazan sake sakaki cikin wani hali ba. Kisani nafi kowa son ki rayu cikin farin ciki ba kunci ba. Tirrr da mahaifin da zai jefa yarsa cikin kunci..dan juya kansa yayi dan da wani irin remorseful feeling ya karashe kalman. …atake sai naga yanayin sa ya fara sauyawa. Hankali na adan tashe nace abbuh?wai akan me kake furta irin wayannan kalaman,nayi maka wani abu ne? Yace ah,a Bahiyya…ai ko kin min laifi ma na yafe miki har abada,dada riko hanu na yayi yace min Amma bansan ko ke zaki yafe min ba,bar ganin ina cikin zafin ciwo a jiya ina sane dake araina,kina wahala dani sosai naga har firgita kikeyi cikin dare kina kirayen sunana….ina tausaya miki sosai. Kuma Tin A lokacin na fara jin dole na na rayu ko dan farin cikin ki bahiyyah kinyafe min…? “Dan Shiru nayi dan banma san me zance masa ba Cikin farin cikin da bansan dashi ba na gyada kai ina goge idanuna da suka dan sauya kalar su Yauce rana ta farko danaji abbuh ya furta min hakan kai tsaye..,har abbu ne yau ya iya mance jimamin mutuwar ammuh yake cewa zai rayu dani?wani Murna ne ya mamaye kirji na sosai wanda babu misalin shi. ****** Tun daga wannan rana har cikin makon,a gaba dayan ta a haka rayuwa ta sauya mana, duk dama abbu baya fita ko ina amma bai taba kwanciya ciwo ba tun wannan rana. Muna cikin wannan yanayi Wata ranar Alhamis na fito nayi wanka na fes,ganin abbu ya warware yana kwance shiru sai na nemi izinin sa na bar shi a gidan shikadai,ni kuma na Fito cikin garin kallon wasa a chan yankin sarkin fulani domin ziyartar babban kawata wanda ake kira da JUNNUT.. Junnut ma marainiya ce,sai dai ta rasa uwa da uba ne baki daya,ayanzu a hannun yar uwan mahaifin ta wato ummah Surbajo take zama. Mahaifin junnut da sister sa ummah surbajo asalin jinsin zuriar fulanin yankin ne. Don haka junnut asalin bafulata ne maiji da kyau baiwa da kuma buri mai kyau na rayuwa. Kawancen mu da ita ya samu nasaba ne tun daga kan iyayen mu,Don kuwa mahaifiya ta itace babban kawar mahaifiyar junnut Ammuh tace min da ada chan damu ka shigo garin bamu san kowa ba mahaifiyar junnut su ne jinsin fulanina farko da suka bada iyayen nawa mafaka acikin wannan yanki har aka karbe mu.. Iyayen junnut duka sun rasu tun kafin ammuh na ta bar duniya Sam rasuwar sun baiyi mana dadi ba,gashi sun tafi sun bar dukiya mai tarin yawa da shike su masu arzikin dabbobi da kudin hadadan kasuwanci da larabawan egytps da china ne toh bayan mutuwar su sai ya kasance yarsu da suka bari wato junnut bata cikin irin halin maraicin danake ciki. …gashi a duk tsaunin wajen ummah surbajo ce kawai tayi karatu mai zurfi,tun asali ma ta dalilin ta iyayen mu suka yarda muke zuwa makarantar bature a chan kusa da egypt dama da yankin ethiopia har muka sami ilimin bature nida junnut yanzu munkai matakin ss1.. Wanda a yanzun Mutuwar ammu na da ciwon abbu ya dan dakatar da ni daga halarta kwana biyu banje ba. Ummah surbajo tana matikar kula da junnut dan haka Ko meye junnut take so ana mata shi. Rayuwar ta take yi cike da buri da son kawo mana cigaba… Tun Muna yan Shekaru 4 shakuwar mu ya wuce yadda hankali zai iya dauka,ayanzu duk wani sirrin ta na sani haka itama kuma tasan nawa. tsaban yadda muke da ita wani bin ko ciwon kai nakeyi zaka ga itama ta fara yinshi kuma bata samun sauki har sai na samu Gashi kusan siffar fatar jikin mu da tsarin jikin mu daya, duk wani halayen mu na yaranta ma iri daya ne,banbacin mu shine ita tafi ni iya magana da mutane sabida awani wajen ni shiru shiru ne. GAshi har munkai shekaru sha hudu,Da shike al’adan fulanin su muma muke bi,mutuwar ammu ne ya hana ayi min aure,ita kuma junnut burin ta na rayuwa ya hana ayi mata musamman data samu goyon baya daga antyn ta ummah surbajo. Junnut tana matukar kaunar rayuwa,mace ce maison taga ta yi ilimin bature mai zurfi tayi kudi tana kwalliya tayi kyau,tana tuka motoci. Above all babban burin junnut ne ta ga tayi aure nan gaba kuma ta auri Babban soja ko wani iri ne kuwa bata damu ba. A hanyar mu na kasuwa Yau ma hirar data zo min da shi kenan. Sai dariya muke fuskokin mu dauke da annuri Hannun mu sarkafe da juna. Chan sai Tace min baahi?batare da na dago ba Nace naam “Daga Gobe Buri na zai iya cikawa amma kwata kwata bana jin farin ciki sabida nasan kwanan nan zamu rabu. Nace ko?..wanne daga cikin burin naki ne zai raba mu junnut.. Tayi dariya tace min buri na koyan turanci. Kinsan ko wanda anty surbajo take dan koya mana bazai ishe ni na wanku har na auro soja na ba ko? Murmushi kawai nayi cikin nuna mata rashin fahimta nace To wanne kenan?ai Nima sai inbiki ko? Junnut idan kika tafi kika barni bansan ya zanyi ba.. Dan Kallo na junnut tayi,dan Salon danayi maganan ya sata taji wani iri. jawo ni tayi muka koma gefe muka jingina da bayan mu. Wani Ajiyan zuciya tayi,Tace ashe babu dadi? …,bahiyyah kinsan me naji kuwa a lokacin da abbu yake ciwo kika daina fitowa muje karatu kwata kwata ma na daina ganin ki? To Walhy ji nayi kamar nikadai ce a duniyan nan.. Ni Gashi ina nan Bansan wani halin kuke ciki ba gashi umma surbajo ta hanani zuwa yankin ku…wai its too far”cikin rigimammen gurgun turancin ta takarashe maganan Duk dama Damuwa ne sosai akan fuskarta. Sai nayi Murmushi nace ai babu komai junnut,nasan bazaki barni cikin wani hali ba,ba gashi abbun ma ya warware ba Dan karamin Nishi junnut ta sauke tace eh,Mungode ma Allah.. Amma kinsan me?nace mata a’ah.. Tace “inada yaqinin cewa bazamu taba rabuwa ba bahiyya, nidake shakuwa ce na har abada na Amana,soyayya na rai da rai..ina matukar kaunar ki kawata. Anan muka juyo duka muna fuskan tar juna cikin shauki mai nuna kaunar gaskiya dake tafe da kalaman zuciyar mu Nidai Bance komai ba don tausayin ta da nake ji,junnut is kind of emotional don ko ni nasan nafita karfin xuciya da jarumta. Cikin sanyin murya tace bahiyyya . Na dube ta nace naam junnut Tace dama naji umma surbajo ne tana cewa gobe zasu zo su dauke ni.. Hannun ta na sake garan gatsau Cikin tashin hankali Nace su waye kuma junnut?wai Ina za kije ne? Ita ma shiru tayi ta kure ni da idon don kuwa a Ba zata naji kirji na ya buga. Nan ta fara min bayani a tsanake don kuwa yau babu fuskan wasa a tattare da ita. Tace”Yan uwan mama na ne daga chan wata kasar zasu zo,ummah surbajo tace awajen su zan koma zama na har abada, bahiyyah ance suna da dukiya da duk wani abunda zaisa buri na na rayuwa ya cika kinga bama sai na tafi da gado na ba,wai dama jira suke na kai sha hudu ko sha biyar sai suzo su tafi dani.. Ruwan daya taru min a idanuna na sake cikin sanyin jiki nace dagaske kike yi junnut? Gyada min kai kawai tayi Wasu zafafan hawayen Junnut ta fashe dashi ta rungumeni, sai gashi jikin ta duk yasaki yana neman fara rawa nima Bansan sanda na kankame ta na fashe da kuka ba. Rungume da juna Sai da mukayi mai isar mu kafin muka rarrashe juna,nan junnut tayi min alkwari cewa ko ta tafi bazata taba mancewa da rayuwar da muka gina tare ba Don sanadiyar burirrika irin na junnut nima naji ina son nayi karatun baturen nan ko dan na taimaki abbu na, a duk dama bani da buri masu yawa irin na junnut,Nima Alkawari nayi mata cewa bazan mance ta ba,haka ma nace ni zan zamto mata mafaka na farko wajen ganin ta cimma burin ta duk rintsi duk wuya. Tsananin amintar dake tsakanin mu yasa nake jin kamar duk wani cigaba ko karuwa da duk wani al’amarin rayuwar junnut nima nawa ne. Gani nake kamar mani zataje tayi sabuwar rayuwar data samu achan din. Haka dai muka waske da kyar muka goge hawayen mu cikin karfafa ma juna gwiwa har muka isa kofar filin wasan samari da yan mata da aka saba yi.. Da mamaki sai ba muga kowa ba don yamma ya fara rufawa sosai waje yana neman yin duhu Junnut ce ta yi tambayar meya faru taga nabu kowa a fili yau,sai ake sanar da mu cewa ai yau din nan sarki modibbo ya sake SABBIN samarin AHUMAGGAH a daji don haka ne yasa kowa ma ya shiga gida da wuri.. Tabe baki kawai mukayi muka juya muka dauki hanyar komawa gidan su. Muna tafe muna hira,nake cewa junnut ni Sam al’adan nan bata burge ni. Sai Tayi dariya cikin raha tace akan me? don sosai muke da samari kala kala masu crushing akan kyawun halitar mu,junnut farar fata ce,sai dai ita tana da pale brown eyes ba irin nawa daya kasance grey ba!..,sosai tsarin halittar mu ya kere idanun dul wani maigani,dan tun tasowar mu samari ke buga kansu akan mu wai suna son mu. musamman ma ni da ban cika son abun ba,muna cikin hirar ta mu sai junnut tace mon “kodai kin dade baki fito dandali ba ne gashi yau kin fito gayu basu nan ko? ….hade rai kawai nayi sai naga tayi dariya Tun kan na amsa tace kar ki damu tunda bamu samu wasa ba sai muje gidan ku na yi sallama da abbu halan gobe bazan samu zuwa ba. Dadin jin hakan da tace yasa ni murmushi kawai Sai Muka dora niyyar tafiya wajen abbu Hiran burrrikan ta take min nima Ina kan jadadda mata yadda raina yaki jinin al’adan Ahumaggah akan haka kuma dariya kawai take yi min.1 Wato shi AHUMAGGAH wani babban al’adace ta wasu jinsin fulani. wanda zaka ga yaro namiji tun yana jinjiri ba za’a mishi aski ko kaciya ba sai ya kai sha biyar ko sha hudu,ko ma sha shida. Nan sarkin gari,da matsafa da aljanun sa zasu tara wayannan samaruka a tsuma su da tsumin aljanu, sannan akai su jeji abasu jawadin tsawon kwana bakwai batare da sun fito gari ba.1 To Cikin wannan kwana bakwai din ake saka ran duk wani yaranta dake kansu zasu aje shi ajejin. Da zaran kwanaki bakwai ya cika sun fito sai ayi musu aski kaciya da aure.1 Sai dai kuma mummunan abu da samarukan AHUMAGGAH shine kwana bakwai ajejin nan da sukeyi babu abunda suke ayyanawa sai rayuwa iri na dabbobi da jahilai. Da rana zasuyi fashi ma duk wanda suka ci karo da shi. Idan budurwace haka zasu yi layi su kwanta da ita suyi mata fyade. Haka ma idan matar aure ce zasu zabi daya daga cikin su yayi zina da ita. Bayan nan yankin ance Akwai masu wannan al’adan Achan kasar nigeria cikin wani kauye a garin alkaleri a bauchi state. sai dai su al’adan su basu hade shi da dokokin tsafi da aljanu ba. a wannan jinsin fulanin kuma aljanu da bokaye kusan sune ma hukumar al’adan. Dan kuwa akwai doka mai tsanani na cewa. “Duk budurwan da ta ci karo da Ahumaggah har yayi mata fyade toh za’a shafe ta daga zuriar,a kuma a jefe ta da baqin cursed na aljanu. Thy believe idan saurayi bai fita a kwanakin Ahumaggan sa ba ya sadu dakai tamkar bada jinin ka ne ma shedanun aljanu ne. Matan aure da abun ya shafa ma jefe su akeyi ko akashe mahaifin ta a shafe ta a zuria..2 ****** Ahakan Har muka iso gidan mu bamu bar musun hakan da junnut din ba. Ita kam ma abun bai dame ta sabanin nikam dana kejin da ina da iko da na sa an dena yin shi a doron kasa. Gani nake wannan jahilci ne da rashin tsoron Allah. No wonder sarki modibbo da bokayen sa,gaba dayan su basu shiri da iyayen mu, haka ma naga sun tsani umma surbajo sosai..har wani suna wai kadangariyar bariki suke kiranta da shi Sabida shi sarki modibbo babban jahili ne babu arabi babu boko sai tsafi da neman arziki wajen aljanu dan bunkasa mulkin sa da kasuwancin garin sa. amma iyayen mu sun nemi addini da ilimin bature dai dai misali a wajen larabawan egypts da kuma yan china dake shigowa kasuwanci ta boader somalia. Dan haka ne ma rayuwa ta nida junnut ba dai dai yake dana kowa ba.. Wayewar mu basira da ilimin mu a fili yake nuna kansa. Tun daga bakin kofa muka doka tagwayen sallama Muka shigo Amma sai Shiru kakeji tsakar gidan gaba daya babu bakowa,sai nace junnut ki shiga daki ki same abbu ni zan sa mana ruwan alwala Tace min toh ta saka kai Niyyata su gaisa idan tayi sallah Nake son na rakata bakin hanya ta koma gida Ina sane da cewa Umma surbajo bata son ta cika dadewa a waje musanman ma da naga har waje ya yi duhu yanzu magrib kuma ya shigo. Shigar junnut dakin keda wuya na kafa kai Ina famar hakar ruwa a tulun bakin rijiya.. Ko ajiyan numfashi ban yi ba wani irin firgitaccen karar ta ya dake kunne na wanda ya sani sake butar danake shirin kai hannu na na shigo cikin dakin mun aguje. Junnut lpya? Bata amsa ni ba A durkufe agaban abbu na same ta ‘Abbu..abbuuu…. Abbbuhhhh..cikin firgicewa ta riko rigar shi tana fada kamar zata cire ranta da kuka,sai yanzu na na lura aman jini yake,duk yayi malala a a hannun ta tana famar jijjgashi Nima durkushewar nayi gaban ta muka shiga jijjgashi muna tallafoshi ba shakka ciwon zuciyar sa ne ya tashi gadan gadan. Kukan rudani duka muka farayi musamman ma junnut da shike tafi ni sanyin zuciya. da naga hakan bazai ficce mu ba,sake mata shi nayi daga bisani na mike tsaye na fito tsakar gidan neman maganin shi daya hada yake sha a kwana biyun nan. Kwaryan shan na rarumo Sai dai kashhsssss maganin dake ciki bai kai ko rabin cokali ba. Haka ma Duk iya bin cike munyi nida junnut amma ba muga ragowar sa ba. Haka muka yi cirko cirko akansa muna neman mafita,ga shi dare ya rufa ga shi Hankalin mu a matukar tashe yake ganin halin da abbu yake ciki dan aduk sanda yayi tari gudan jini ke fashewa yana kuma fetsowa.. Karshen ta barin san nayi da junnut adaki tana ta kuka sai nayi kokari na sulale a zuciye na fito na bar gidan na kama hanyar jeji. Tafiya kawai nake buri na naje cikin dajin ko zan samu na kalato magani abbuna ya sha ya rayu. Karewar Maghriba ya shiga sosai donko gaba na bana gani sosai danake tafiyar But I was so dertemined,ko ajiki na zuciya ta arufe take kuma duk wata alaman tsoro na kau dashi. Sai dai Ko rabin jejin ban tsaga ba naji takun mutum abaya na ina kuwa daga ido naga aminiyata junnut faca faca alaman biyo ni tayi. Abun ya bani mamaki,tambayar kaima nake anya junnut tasan hatsarin dake cikin wannan lokaci kuwa?.. A zuciye Nace junnut?baki da hankali ne zaki shigo jejin nan cikin dare?Idan wani abu ya same ki fa me zaki ce.. A take Tace min oho Share ta nayi na taho zan maidata gida ta fauce hannun ta Kallo na take yi Don Tsaban zuciyar ta ya karaya Cikin wani birkitaccen kuka Ta tsare numfashi na da cewa wai ena ruwan ki dan nazo,wato so kike na barshi ya mutu ko bahiyya? Abbu mahaifina na ne nima kuma Bazan zauna ina kallon shi cikin wannan azaba ba.. Kuma Dole ne na zo na taimake ki mune masa magani..hada ranta tayi ta kame Bance komai ba,dan Hawaye ne suka sauko minbina sharewa dana ganta ahakan sai naji na damu da safetyn ta sosai I wish dat bata zo gidan mu yau din ba ma,a haka ma ban bari ba duk iya musu munyi akan ta koma gida kan abbu Amma haka fir junuut taki. A haka na hakura mukaje cikin jeji neman maganin tare. Bamu samu irin ganyen da wuri ba dan munkai kusan rabin awa muna dubawa.. Sai da mukayi nisa bamu sani ba,Finally junnut ce ta gano shi ta nuna min,dan kwazazzabi ne yabi wajen sai na mika hannu ina tsinkawa tana tara min a fallen rigar ta “Mun ko debo isasshen a Kai hannu na na karshe sai naji an chapke ni,a tsorace na shiga fixgewa sai dai kuma lyaki sakowa.. Wani kara nasake Cikin radadin murdamin hannun da akayi Kafin Junnut tayo kaina,nadaga ido sai charaf mukayi ido hudu da saurayi AHUMAGGAH.. Wani uban Ihu na tsala nace junnut ki gudu ga Ahumaggah..cikin rudani da rawan murya tace Ahumaggah?3 Wani ihun na sake tsalawa..ko da junnut zata firgita ta gudu amma ina sai naga batayi hakan ba Kokawar jawo ni Ma Ta shigayi cikin dauriya dukan mu muna ihun neman ceto Ahaka Har ta ci nasaran kwace ni a hannun sa muka fado kasa tare A hargitse muka mike ai tun kafin Ahumaggan yace zai zago na tura junnut kan hanya nikuma na kwaso maganin da muka debo a hannu na,..wani uban Gudu muke cikin jeji da dukan karfin da Allah ya bamu. Gudu yaki ci yaki karewa dan Bamu san munyi nisan kiwo ba sai da hakan ya faru damu tsaga ciyawa kawai mukeyi babu iyaka… Ayayin da shima Ahumaggahn ya haukace yana biye da mu aguje da dukan karfin sa ko kiran yan uwnsa baiyi ba…. Bana so mu rabu da junnut dan haka muka rike hannu muna falfalawa back to back.. Gashi Idon mu duk ya rufe da tsoro,sao A Chan bakin wani tsaunin itace daya fado kasa junnut bata lura ba tayi tuntube ta fadi gashi ta gaji sosai sai haki take..nayi kokarin janta amma wani Ihu tayi cikin radadin zafi wanda ya tabbatar min da cewa taji mumunnan ciwo a kafarta A tsorace na zube gaban ta nayi kokarin dagata don jin sautin tahowar Ahummagan ya gama jefamu cikin rudani. Agurguce dai na tallafo ta Da kyar na dago muka tsaya tana dingishi kafarta na dama har ya farke ya na zubar jini sosai. Munajin sautin iska alaman Ahumaggan na gaf da mu anan tsananin tsoro ya sa muka sake juna Ita Junnut tayi gabas ni kuma nayi arewa.. Gudu kawai muke yi har na samu na tsira sai na buya bayan bishiyar kuka ina ta haki ina neman dai daita hankali na. Anan Nakai wasu mintuna goma banga wullowar Ahumaggan ba haka ma banga junnut ba Atake naji Kirji na ya buga,kaina yayi mummunan sara,gashi ina so na kwalla ma junnut kira amma ina tsoron dada jefa mu cikin fitina. Nasan tabbas sauran Ahumaggan ma suna nan,kuma muddin suka ji muryan mace zasu fito dukan su kuma nasan bazamu taba tsira ba. Cikin jarumta na fito a sadade ina neman junnut ajejin. Tafiya nake ina duban gaba da baya,har na naci kusan rabin awa banganta ba,sai da nakai chan ciki wajen gonar masarar sarki modibbo kafin naji dafff an dafa ni. A hargitse na waiwayo dan tsoro sai kuwa muka hade ido da junnut tana tsaye kamar kungi hawaye taff kan fuskan ta. Wani irin daskararren Kallo muka tsaya yiwa juna cikin mu babu wanda ya iya furta komai Gaba daya Ji nayi Jiki na ya dau sanyi dan Yanayin da take kallo na sam bangane mashi ba… idanun ta sunyi jajir kuma ta riko rigarta ta cukuikuyo shi da dukan hannayen ta tana nuna alaman tsana ma yanayin da take ciki. Innalihhihi wa inna ilahi rajiun Murya na tsananin na rawa nace” Junnuut…jun.. Ai Bata bari na karasa ba tasake min Kukan ta mai dauke da tsumayi wanda ya dakatar da ni. Atake naji wasu mahaukatan hawayen sun bulbulo min Cikin firgici Nace meye ne? Nan ta riko ni tana mai dada fashewa da kuka Tana boye fuskanta ajiki na,kai kawai take girgizawa Anan Zuciya ta tuni ta bani cewa wani abu mummuna ya faru da ita dan haka nima nabu jira na fashe da azabbaben kuka mai fitar da sautin ciwon daya fi nata ciwon zafi Wani Kankkame juna mukayi cikin dajin muna kuka sosai da kuma dukan zuciyar mu,..batare da ta furta min ba Na gane cewa Ahumaggan nan ya cimma burin sa ne akan budurcin junnut. Da kyar muka rarrashe kanmu Mukayi zaman mu cikin tsakiyar gonan bamu damu da komai ba muna tsananin jimami. Cikin disashiyar sautin kuka Nace shikenan yau na shiga uku junnut,..maganganu nake yi cikin rudani da Har zan fara bada kaina laifin jawo ta cikin wannan matsala Sai naji tace”kar kice haka bahiyya,ai duk abunda zanyi akan Abbu tamkar nayi ma mahaifina na ne..+ Ni Damuwata yanzu ummah surbajo da cikar buri na! Kinsan yadda nake so nayi rayuwata ko?wallhy Ina matukar son na Zama mace a duniyan nan bahiyya bazan iya jure duk wani abunda zai ranani da hakan ba! Yau idan akaji abunda ya same ni nasan ko ummah surbajo bazata kula ni ba bare adanka ni wajen dangin mahaifiya ta. Sai bata sake cewa komi ba dan Kuka mai ban tausayi junnut take yi cikin zafin rai da rikicewa Gashi ba karamin zafi jikin ta yake mata ba,nikaina kukan nake yi kuma nasan dauriya junnut take yi ayayin da take min maganan ayanzu. Damuwa sai ta mamaye zuciya ta,don Bayan tinanin hukunci da za’ayi ma junnut awajen sarki Babban fargaba shine burin ta na rayuwa da take sa shi a ran zai fara daga gobe. Sai naji kawai banyi mata adalci musanman da naji cikin kukan nata kamar tafi damuwa da Cewa za’a shafe ta a zuria ayi cursing dinta inda ko umma surbajo bazata so ta hada hanya da ita ba bare taje birni ta cimma burin tan. Dan a al’adan yace muddin aka shafe ka babu wanda zai sake so ya hada zuria dakai,don gani za’ayi kamar kaidin ba alheri bane kuma darajar ka ta gushe kenan har abada Tausayin ta sai ya kamani sosai Junnut tayi min hallaci sosai,yau ta dauki qaddarar biyo ni neman magani ma mahaifi na rayuwar ta kuma ya shiga matsalan da bansan mafitar sa ba. Tunani nakeyi sosai Dan haka kawai nake jin cewa dole nima nayi mata hallacin da zai dawo mata da martaban rayuwar ta cikin gaggawa. Nace junnut idan zaki iya kawai muje gida yanzu mu samu abbu mu fada masa nasan shi zai nema mana mafita ko?. Junnut Gyada kanta kawai tayi ta kwantar da kanta akan kafada ta cikin jimami dan kwata kwata rasa budurcin nata bai wani dara ta chan chan kamar tunanin cikar burin ta ba sai tace. Bahiyyah ki rufa min asiri mana kinji?… Sai na dan langwafo na kalle ta,dan ban fahimce ta ba …mikewa tayi ta zauna tare da riko hannu na.. Tace Kinsan a duniya bani da kamar ki ko Bahiyya!Toh dan Allah Ki rufa min asiri mu binne maganan nan tsakani na dake bana so kowa yaji. Cikin mamaki na ware ido ,a marairaice tace Kinga tunda naji ciwo jini na bina ai ummah surbajo bazata gane abunda nake ciki ba har sai na bar garin nan gobe ko?.toj Dan Allah bahiyya kimin wannan Alfarman, hawaye na zubo mata sai ta marairaice min sosai gwanin tausayi Nikuwa Cike da zakuwa Nace zan yi miki komai a duniyan nan junnut ..ina dai baki so kowa yasani ne? Amma toh baki tsoro aljanu su tona mana asiri.. Ahumaggan nan zai fada ma aljanun su cewa yayi fyade ma budurwa,a gidan sarki kuma zasu jira mu har kwana uku idan bamu kai kanmu ba kinsan zaki iya mutuwa ko? Da sauri Tace eh..nasani Anma ai basu sanin ko wacece akayi ma fyaden ba har sai takai kanta ko? Ba tare da wani shakka ba Nace eh Wani ajiyan ziciya Junnut ta sauke cikin sanyin tace “bahiyyah,Shiyasa nake so ki taimakeni…sai kuma tayi shiru alaman kalman ya mata nauyi abaki Nace inajin ki junnut.. Nan ma sai ta kafe ni da ido tayi shiru abun ta Da kyar sanda na dinga takura ta da cewa dare na dada yi mana ajejin,gashi tashin hankali ya gama mamaye zuciyar mu kafin ta shirya furta min. Anan junnut ta nemi alfarma ta tana cewa “Domin cikar burin rayuwa na nake rokon ki da ki sadaukar min da darajar ki wajen sarki Cikin kukan da bansan dashi ba Ta dada ruko hannu na tace “Ina nufin kice masa kece akayi miki fyaden bani ba.. Zu je tare amma ke zaki dauki laifin Inyaso koda an wanzar da hukunci akanki sai mu hada hannu mu dauko abbu mu kaishi chan inda ummah surbajo zata koma kasar nigeria sai ayi jinyar sa da dukiyata. Cike da mamaki Nace junnut?kinsan me kike cewa kuwa Tsaye ta mike tana dingishi,dan tun kafin na kawo korafi na tace toh nidai wallahy zan kashe kaina,daga yau muyi bankwanan a duniya bahiyya…kinsani Idan bazan cika buri na ba gwara na mutu. Nima tashi nayi a rikice nakai mata dan karamin mari a fuska,a zuciye nace zaki kashe kanki baki da hankali ne… Cikin kukan bakim ciki ta sulale ta tsuguna gaba na tana mai tana kafafu na a kaskance tace bahiyya dan Allah ki taimake ni,wallhy nayi miki Alkawari zan dawo miki bazan rabu dake ba …zamu yi rayuwar mu mai tsafta ni dake har abada..Alkawari ne. Wani irin Tausayin ta ne naji ya shige ni sosai domin Wani Kuka mai shiga rai takeyi ayayin da nima na fashe da kukan na tsuguna na rungumo ta jiki na muka dunkule munayo tare.. Cikin tsananin son naga na yaye mata damuwar ta nace mata na Amince zan dauki alhakin yin mata haka.. Sai dai sharadi na shine wannan maganan ya kasance wata babban SIRRI l mai girma a tsakanin mu wanda ko abbu bana son yasan dashi. Junnut ta dada rungume ni tana kuka tana min godiya Tare da min Alkwarin duk dukiyar ta na wajen ummah surbajo zai dawo na jinyar abbu na. Haka na dauka wannan kayan alkwarin makaina Ni sam Bandamu da wani curses din da za’ayi min gobe agidan sarki ba. Sannan a tunanina na yaranta na bana kawo cewa akwai abunda zai tsare ni wajen nema mahaifina gamsashen lapya,wani tsafi da aljanu duk gani nake sun yi kadan su kara da ikon Allah.. Iya kaci ne ace inhar da ummah surbajo zamu zauna a inda zata koma gobe a birni to zan iya rabuwa da abbu na. Toh Wannan shine kadai babban abun daya yake damu na yanzu.. Ta ya zan fara ma abbu bayanin haka?gashi Bantaba boye mishi komai ba sai yau da nake shirin zan boye mishi sirri na da kawata junnut.. Shin ko akwai abun da ya fi dadi a duniya kamar kasan kana da iyayen ka a raye koda kuwa baku tare?. Cikin daren A daddafe muka iso gida,samu mukayi abbu ya riga ya dauke motsi amma kuma numfashin sa bai dauke ba. A gefe na ajiye maganin sa duka muka zube gwiwar mu agaban sa muna jimanta yanayin sa he is kind of stable now nan na fita na shiga hade ruwan magani tare da ruwan zafin da junnut zata dan tsaftace jikin ta ita kuma tana dakin tare da abbu tana tallafa masa. Babu abunda junnut take yi sai hawaye. Abbu yayi luiii da shike ma bayada karfin magana sai ido yake binmu da shi har muka gama duk abunda zamuyi. Anan Bamu kama hanyar gari ba sai da na tabbata junnut tayi wanka ta dan kimtsa kanta kafin na gyara na abbu kwanciya na fito na rakata har layin gidan su sannan na dawo. Cikin wani irin yanayin tunani nake tafiya,babu abunda nake tunowa sai alkawarin mu da junnut da yadda komai zai zamto min daga gobe.. Shekara ta goma sha hudu ne kawai a duniya dan haka bansan ko hukuncin dana yanke dai dai bane ko ba dai dai ba. Washe gari Da safe Bayan na hada ma abbu na maganin sa na bashi ya sha,sai nayi zamana gaban sa na tsura masa idanu na bance uffan ba…,na dade a haka ina tunani dan a daren jiya ma ko tunanin kiftawa baizo min ba,yanzu ma kallon shi kawai nake ina tuno irin rayuwar farin cikin dasuka bani shida ammuh a lokacin da bankai haka ba Tabbas ummah surbajo tana da ilimin da zata sama min mafita game da rashin lpyar Abbu.. So nake abbu na ya warke sosai ya rayu koda babu ni atare dashi… Sanyin safiya na kan busowa na fito nayi alwala nazo kan abbu nayi masa karatun qur’ani dai dai inda na kama.. Chan naga Abbun Ya farka ya bude idanun sa amma ko tashi da kyau bazai iyayi ba. A Yadda na saba wanke shi nayi masa alwala haka nayi ta taimaka masa har yayi sallah… Dan kadan ya sake shan maganin sannan ya kwanta yana kallo na,sosai yanayin sa ya dada rikita ni.. Gani nake idan ya kwanta baccin hala bazaima tashi ba tsaban wahalar dayake sha da jikin nasa. Dana ga kallon nasa yayi yawa Chan sai abun ya fara bani a kwakwalwata ko dai wani abun yake bukata ne?sai nima bance komai ba,inda yabi da ido nake bi sai banga me yake kallo ba face ni,sai na tashi tsaye Ina dan dube dube ko zanga ya min alama.. Murmushi kawai yaso yayi amma Wani tari sai ya shake shi,karasowa jikin sa nayi a dame nace sannu abbuh… Tarin bai tsagaita ba sai naga abbu ya ruko duka hannaye na Yace bahiyyah,jiya a ina kikaje kika samu magani? KAllon sa nayi A hankali na furta “jeji”,wani runtse ido naga yayi alaman baiso yaji hakan ba amma baya da karfin da zai yi scolding dina.. Yace ke da junnut kuka je ko? Toh meya faru da ku naga jini a rigar ta,ke kuma har yau idanun ki basu washe ba..shin bazaki fada ma mahaifinki damuwar ki ba bahiyyah? Yadda yayi maganan sautin muryansa na karkarwa yasa Sai nayi shiruuu tsawon lokaci kaina a kasa bance komai ba. Muna cikin haka aka yi sallamah agidan mikewa nayi na fita abbu na bina da kallo mai dauke da alaman tambaya. Dogaren sarki nagani,yace Aika ne daga gidan sarki modibbo akan cewa naje cikin gaggawa Abbu dai bai sake tanka ni ba Nan na shirya kaina na nufi gidan su junnut. Junnut ce take gayamin cewa a jiya data shigo gida cikin dare ta cikaro da tashin hankalin ummah surbajo sai ta tutsiye ta da fada har da mari har sai da tayi mata karya akan abunda ya faru sai dai ta juya kan labari ya koma kaina kamar yadda muka shirya. Kenan ummah surbajo ta rike cewa nice akayi wa fyade ba junnut ba, kwata kwata batason abunda zai shiga rayuwar junnut anan gaba dan haka ta sata agaba akan maganar. Dan akan junnut umma surbajo bata da sani bata da sabo. ummah surbajo gani take idan ta kyale maganan har ta bada junnut goyon baya ta boye ma sarki,toh hala wani abu zai iya biyo baya. junnut tace min yau din ma ita tasaka ta agaba akan dole sai taje ta fada a gaban sarki modibbo,da taki data so haka har magana yaje gaban sarki shine aka aiko a dauko ni. Daga nan Bamu wani bata lokaci ba muka kai kanmu gidan sarki modibbo muka aiwatar da plan din mu na cewa ni Bahiyya nice Ahummaga suke riske ni ba junnut ba.. Sai muka juya kan labari muka shirya duk yadda zamu samu hadin kansu. Toh Kamar yadda aka saba jama’a sun taru sarkin matsafan da aljanun sa duk sun hallara za’ayi min hukunci. Ganin mun yi tsuru tsuru muna rarraba idanu salon marasa gaskiya ga idanun mu kuma cike suke da hawayen tsoro sai yasa basu kulaba,tashin hanklin mu yasha masu sarki modibbo kai har yasa ba a bata lokaci wajen zurfafa bincike akan lamarin ba aka yanke hukunci. A wannan lokaci koni bana kuka da jimamin da kawata junnut keyi,Abbu na chan gida bai ma sanda haka ba. Anan fada kuma Sabida babu mahaifina awajen sai aka bani sharadin awowi biyu da cewa na tattara kaya na na bar garin an shafe ni a zuriar su,sannan ina gani boka da aljanun sa suka gama tsubuce tsubacen su akaina ina jin su bance uffan ba. A Duk ilahirin jinsin zuriar fulani dake fadin jejin Nan basu kai kimanin dubu daya da dan dori ba dan haka kusan kowa yaji abunda ya faru dani Wasu sunji bakin ciki sosai,wasu kuma Sunyi murna musamman yan mata sa’oin mu da suke ganin nice matoshiyar sa’ar su wajen samun mijin aure. Junnut kam gaba daya sai ta birkice,itakadai ke rike dani tana jimami har muka kai kofar gidan su. Muna Isa kuwa na samu har bakin nasu sun zo wanda zasu tafi da ita chan birni.. Dana shigo gidan ma,sanda Ummah surbajo tayi min fada sosai akan abun da ya faru damu jiya nida junnut din Tace duk gangancin mu ne ya jawo mana. Don junnut bata manta marin da ta karba ajiyan data dawo cikin dare jikin ta duk wani iri ba…sai nayi tunani wai don ma junnut batace ma ita akayi ma fyaden ajiyan ba kenan?ashe kuwa da ta fada gaskiya hala ummah surbajo ma kawai zata iya kashe ta har lahira da fada. Haka mukayi tsuru tsuru muna bata hakuri,da shike ma ummah surbajo tana da ilimin bature da yelwatan tunani Daga baya Sai ta shiga tausaya mana gaba dayan mu. Dataga inata kuka sai da tayi kusan sani zazzabi da nasihan ta,aganin ta duk tsumayin rabuwa da aminiyata ne ya kawo ni gidan nasu a yanzu da bani da wata rayuwa mai daraja a idon kowa agarin. Hakuri ta bani sosai tana cemin Allah ya qaddara nan ne karshen gabar kawancen ki da junnut. Kema yau zaki bar cikin wannan jinsin ga Junnut itama zataje chan nahiyar da ta dubi kudu wato chan persian empire asalin cikin kasar iran wajen dangin mahaifiyar ta. A Cewar ummah surbajo,asalin mahaifiyar junnut jinin sarauta ce ta wani babban daula zuriar sarauniya DAWLAT KHATOON dan haka su kayi alkawari zasu rike rayuwar junnut a matsayin yarsu ta har abada gashi kuma yau sunzo cika alkwarin su. Ita kuma ummah surbajon zata koma da zama na dindin a kasar nigeria chan cikin jahar kaduna. Muna cikin saurarar ummah sai ga umaru dan mashayin garim ya taho gigice ya zube gaba na. Yace baahi,ki taho,baba ahmadu mai magani…yana magana yana hako yana nuna hanya A take naji yawu na ya dauke chak kaina yana wani iri bugu… Nace mene ne,ina abbuh? Su umma da junnut duk sukayi tsaye suna kallon shi da fuskan razana kamar yadda na ke binshi da kallon nima Nan umaru ya sanar dani cewa ai yana tahowa ne yaga abbu na akasa kan hanya yana ta aman jini Runtse idanu na nayi,dama saida jiki na ya bani cewa abbu zai iya cewa zai biyo ni yaga me na ke cikii Ban tsaya sauraran komai ba,na sa gudu na fita agidan junnut zata bi baya nah ummah surbajo tayi sauri ta finciko ta tana cewa ke wai ina zakije? Bakijin magana ko Maza wuce kije ki shirya yanzu zaki tafi, tace ummah zanbi bahiyya ne,sai bata kulata ba kuka junnut ta fashe da shi tace ummah Abbu baida lpya sosai dan Allah ki barni naje amma haka ummah surbajo taki sam tayi mata shiru junnut kuwa ta cigaba da kuka har saida ummah surbajo dan kanta ta gaji tace toh taje ciki tayi shirin ita zata bi bayana taga meke gudana kafin nan junnut ta amince ta motsa. Nikuwa ina isa na haura kan abbu duk yayi wani iri,ga datti da kuran kan hanya ya shafu akan rigar sa yana ta habon jini. Umaru ne ya taimake ni muka koma da abbu na gida,shima bai wani tsaya ba yayi tafiyar sa ya barni da Abbun a hannu a tsakar gida. Zama nayi a gabansa shi yana daga kwance,har ya dan dawo hayyacin sa ya bude idanun sa ya kalle ni..,nan ya shiga yana tanbayata meya kaini gidan sarki. Nikuwa a Duk tunani na nabari cewa yau komai yazo mana karshe tun da zan damka shi a hannun ummah surbajo akaishi birni ayi masa jinya,hakan yasa kawai na cije na fada masa abunda ya faru batare da yasan gaskiyan sirrina da junnut ba Sai dai Har nagama nayi shiru banji ya ce uffan ba,hasali ma Idan ina maganan abbu kallo na kawai yake yana kada kan sa slowly nikaina bansan meyake tunani ba. Sai chan naji Abbun Ya sake nanata min tambayar sa yana cewa bahiyyah Ahumaggahn ne suke riske adaren jiya? Cikin dauriya da fargaba nace mashi eh.. Juya kanshi gefe yayi,ya barni cikin zullumi na tsawon mintuna ashirin Chan Yace min yata bahiyya! …kiyi hakuri da rayuwar duniya ki zama macen kan ki…,kar ki taba zubda kimar ki da darajar ki,sannan kar ki ci amanan kowa. Mamakin kansa yasa na dago kaina na dube shi sai naga bama kallo na yake yi ba Yace Ni ahmadu yau naso ace qaddarar mu ta saba haka don kuwa har cikin raina nake jin ke din wata ce a duniyan nan kuna bazan taba yarda da sabanin haka ba. Da Ahumuggah, sarki modibbo da aljanun sa duk sunyi karya su salwanta ikon ubangiji acikin rayuwar ki. Kije inda zakije aduniyan na kuna kiyi aikin ki na kwarai,halal dinki kawai zaki nema bahiyyah,duk abinda ya saba haka kibar shi har abada.. Wani fat fat Zuciya ke bugu dan Dagowa nayi na kalle shi cikin sanyin jiki nace toh abbuh … “Kallo na shima yake yayi sai TAri ya dan turke shi duk da haka bai fasa ba yace Kinji abunda na fada miki ko? Nace ehhh naji Abbu,mikewa tsaye nayi da sauri ina shiri shiga daki zan dauko masa magani.. Sai naga ya ware Hannun sa ya mika min,sai nima na riko shi tarin na dada hauhawan sa a hankali…sai naji ya dada rike ni dam dam duk yunkuri da zaiyii kuma tarin sai ya kara karfi kamar yadda ya ke kara karfin riko ni. Idanun mu a take suke rine ni dashi sukayi jajir muna kallon juna anan abbu Yace min bahiyyah,muryana na rawa sosai nace naam abbuh …yace baki taba min komai na bacin rai ba a duniya ,shin haka zamu rabu bazaki fada min gaskiyar lamarin ki ba?…murya na na dada rawa na firgita kadan sai Nace abbu?man take ya lura da cewa maganan ne yayi min nauyi abaki Sai Yace toh shikenan bahiyyah ta Na hakura Allah ya miki albarka daga nan,..bai sake kallo na ba ba sai aman jini daya shiga yi. Kuka mai sanyi na fashe dashi,nikadai ina kanyi kamar wacce aka ma bishira da mutuwa,abbu sai ya kau da kansa bai ce dani uffan ba Sai chan danayi zuciya ta tayi sanyi sai naga kamar bazan iya ba kawai sai na fara bashi asalin labarin abunda ya faru tsakani na da junnut ajiya cikin dare Tun da na fara abbu yake wasu irin silent hawaye sai yayi shiru ya tsura min idanun shi labbansa dauke da karamin murmushi.. Hannun shi daya ya saka ya a shafo kaina dik jikin sa na rawa sosai Yace ai dama nasani, Allah bazai taba bani kunya ba domin kuwa Allah baya tozarta bawar shi mai masa biyayya bahiyyah. Da ace Jiki na ya bani cewa dagske Ahumaggah sun salwantar da rayuwar ki sabida ni da tun bayau ba na bar duniya nan.. Hakan bai faru ba shi yasa najira naji gaskiyan lamarin ki daga bakinki ki. Abbu yace”Kinyi sadaukarwa mai girma bahiyyah ta” Junnut ma yata ce bazan so ace hakan ya same ta ba,kuma naji dadi daya kasance babban burin ki ne masamu lpya na rayu awani wajen koda baki tare dani. ,…Allah ya sa sadaukarwan ki ya zamto sanadiyar wanke hakkin junnut akaina wanda halin rashin lpyata ne ya jawo mata wannan mummunan qaddarar a cikin rayuwar ta. Allah ya bata abunda za taje nema.. Nikam babu abunda nakeyi sai kuka,zuciya cike da kaunar mahaifi na da kyar na iya tsagaitawa har nace ameen.! Yau Ji nake kamar nafi kowa sa’ar uba a duniya , dan kuwa abbu is the most simple and most understanding father a duniyn nan..Duk da haka hakuri na shiga bashi ,amma sai ya jawo ni jikin shi ya rungume ni Sosai. Tarin ne ya sake Addaban sa amma bai sake ni ba. Yace na barki da duniya bahiyyah ta amanan kanki yana hannun ubangiji na Albarka ta na tare dake Kar ki manta da wannan “Kar ki ci amanan kowa don nasan da tarbiyan dana baki zaki iya zama da kowa..! ke da junnut tamkar wani haske ne,dan haka kar ki sake ki bada fili ma shaidan har babban aminiyar ki ta dawo abokiyar gaban ki”.. Karshen maganan abbu na kenan sai yayi kalman shahadar sa ya bar duniyan mai gaba dayan ta..2 Naji bakin ciki marar misaltuwa sai dai Ban iyayin wani kuka ba sai hawaye da dan addu’oin dana koya a chan islamiyar su ummah surbajo Rabuwa da mahaifi irin nawa da zafi,anma Hakuri da juriya na wajen Allah na mika gaba daya,na kuma roke shi sai na samu sauki. A daddafe naje na fada aka zo aka suturta abbu aka kaishi gidan sa gaskiya.mafi akasari daga mutanen garin mu sun dada jin tausayi na aransu Tsegerun jiki kowa sai cewa sukeyi nayi na bar garin,acewar su tsinuwar aljanu dake kaina shiya kashe abbu na. Ina daga tsakar gidan su junnut na rafka uban tagumi ina hawaye,sai naga an shiga daki da ita,anan suka gama duk wani maganan su banji komai daga ciki A Ciki har da maganan cewa ummah surbajo zata tafi da ni kasar nigeria nan da cikar awa biyun da sarki suka bani akan na bar garin. Junnut ne ta sa ta dole ta aminta da hakan,Sai dai sanin halin sarki modibbo ya sa surbajo ta shiga fargaban rike ni Damuwar ta ba dukiyar da zata bayar ba,kar muje dani na zamto mata fitina tunda anriga an jefe ni da bakin aljanu. To lokaci ya kure kuma Babu wa’adin warware maganan sosai don haka,naa amince da shawaran ummah surbajo Buri na kawai ta fitar dani daga nan yankin lami lpya Toh da su junnut suka tafi Umma surbajo sai da ta dada jadaddain cewa a zamu tafi taree amma ni bazan zauna da ita ba sai dai na nayi gaba na kana rayuwa ta nikadai acikin garin kaduna nikadai Haka rayuwa ta tsara min wannan ranar kuwa bana taba mancewa da ita a kundin tarihin rayuwa ta Rana ce da na rabu da abbu da junnut,nayi karya ma abbu kuma na bar garin da gawar mahaifiya ta yake shinfide na har abada. Tin da muka dauko hanya sai nayi shiru,har wani kwalalan zazzabi sai da ya kama ni. . Ummah surbajo ma tausayi na take ji sosai azuciyan ta shiysa har ta fara tunanin zata kyale ni nayi kwana ukun zaman makokin mahaifi nah agidan ta.. Araina nikuma nasan junnut zata yafe min tunda ma abbu kawai na gaya ma sirrin mu kuma shima gashi ya bar duniyan nan Yau daga ni sai ita sai Allah muka san gaskiyar labarin rayuwar mu akan Ahumaggah Daga nan Ni kaina bansan yaushe muka iso nigeria ba. Har muka iska sauke mu a garin kadunan ban ma lura ba sai da naga mutane suna hulda da junan su gwanin ban sha’awa Kasar kuwa akwai kyaun tsari da yelwatan arziki, uwa uba ga kabilu masu kyau da al’adu na ban mamaki. Haka kawai naji iskan kasar ta amshi zuciya ta tafiya ta nakeyi ina bin ummah surbajo kamar dama kasata ce nigeriar. Nan inda muka sauka anace ma sunan anguwan badarawa,gidan ummah surbajo irin duplex din nan ne mai tsafta dashike ma bata da miji mukadai ne kawai agidan babu kowa.. Yau kwana hudu da isowar mu dan Ban bar gidan ummah ba tukun sabida jikina yaki ya sake ni,a kullum na kwanta sai nayi mafarkin abbuh yana min murmushi. Ummah surbajo kuwa a shirye take,. dan naga ta cika min alkawari na data dauka ma junnut na kulawa dani ,dan tun zuwar mu naga ta sa an kira likita dan nigeria agaggauce har gida kuma yake zuwa kaina yana duba ni Gashi a kullum jikina sai ya tashi Wani bin idan abun ya dame ni sai,har nakanji kamar na fada ma ummah gaskiyan lamari Amma kuma bana iyawa dan nakance Toh meye amfanin fasa kawai tunda nasan bazan iya dawo da abbu na duniya ba?kuma ga junnut dina zata cika burin rayuwar ta. Iyakaci ace na rabu da garin mu ne kuma an tsine min..besides garin sarki modibbo ba asali na bane kuma ba zuria ta ba. A Yau safiyar liitinin sai Na farka da fargaba da wani irin bugun zuciya,domin kuwa tun asubah ummah surbajo ta fito fili tana cemin nayi na bar mata gida kar curse dina ya shafe daya daga cikiin dangin ta.. Nikam ban wani damu ba sai na roke ta wa’adin kwana biyu tace min babu komai. Munyi ne akan sharadin zanje na nemi sana’a mai kyau a cikin garin koda kuwa wanke wanke ne a kasuwa kafin na bar mata gidan ta… Dan haka ko zama banyi ba na fita neman abunyi sai dai bnci sa’a ba Da safen washe gari ma haka na shirya na fita bansan kowa ba Haka na dinga tsagawa cikin garin kaduna ina neman aikin da zai rufa min asiri, Mutanen kasar kuwa akwai su da tausayi,ko da bazasu baka aikin ba su fiye wulkankta mutum ba nakai yamma ina zagaye ga yunwa ga gajiya har sai da na iso bayan gari inda karuwai ke zama kafin,Da kyar na ci karo da wata mata wanda na lura kyau na ne kawai ya dauke mata ido ba abunda nazo nema ba. Dana mata bayanin kaina sai Tace min zata koyar dani sana’ar saida abinci (sales girl) idan na kware kuma ta ga zata iya zama dani zata barni ina kwana a shago da sauran masu aikin ta. Naji dadi sosai sai Nayi mata godiya nace mata akan gobe zan fara zuwa aikin.. Dana zo gida na fada ummah surbajo tayi murna sosai,har tayin yunkurin bani kudin gadon junnut datamin alkwari akan jinyar abbuh amma hakan naki karban ko sisin ta nayi tafiya ta. Bayan watanni biyu,lokacin har mun rabu da ummah surbajo na kama gaba na aiki nake yi gadan gadan wajen anty hanne a restaurant din ta na bayan gari. Ni ba wata cikakkiyar wayayyya bace amma bazaka ga hakan da sauri atattre dani ba ba sabida ina da mugun mugun kyaun fuska da abun da ake kira kyaun jiki.. As young as i am,a shagon anty hanne idan akwai musun da aka tabayi jar aka zuba kudi mai yawa to akan banbance kamanni na Dan wasu sunce kamanni na da pop artist Ariana grande kamar an tsaga kara ne musamman idan nayo murmushi wasu kuma suka ce nice ma indian movie star wato aishwairiya rai sabida kalar idanuna.2 sai dai ni ba farar kalar fatan turawa nake dashi ba,fari na dai dai yake da na asalin iyamuran kudancin nigeria irin bright yellow skin mulmulalle mai haske da laushi irin marar fidda kurji ko tabo din nan. “Dama Abbu da ammu na farare ne,dan haka na dauko yalalen gashi mai tsayi irin na ammuh, tsayin ta da dirin jikin ta ma kai komai nata na halittar jiki ban bari ba. Idanu na ne kuma na dauko na abbu na dan shima kwayar idansa kalar ruwan tokace irin na aishwryr,gashi thy are well rounded and sunken su dai basu yi girma sosai ba, dan madaidai ta ne Wanda tsayi da cikowar eyelashes dina ya dada kawata su ya bani wani shegen fierce look. Nidai Na kasance wata madubin dubawa dan ko babu kwalliya nasan ni mai kyau ce. Anan kuma kyauna ya jawo na sama mana kasuwa sosai kamar ba nice aka ce aljanu sun Tsine min ba. sai dai bana da son cika magana, hasali ma Tsaban yawan shiru na da kamun kai yasa anty hanne ta yarda dani sosai,yanzu awajen ta nake samun kariya da cikakken tsaro daga komai, har da maza yan iska da kuma kawayen ta karuwai yan madigo. Anty hanne ba musulma bace anma tana da dabiar daraja dan adam, akalla dai she is in her late 40s tana da dan shegen data haifa sunan sa chris,to tunda ta haihun sai ta bar sana’ar karuwancin kwata kwata sabida tasa tunanin rayuwar dantan anan gaba. Amma sai bata bar bayan garin ba sabida sana’ar da ta bude na saida abincin domin anty hanne karshe ce wajen iya dafe dafen abinci,wani salon girkin abincin ma koya take yi a online kuma duk iya wahalar yinsa Sai ta koya kuma kaga ta iya tsaf Sana ‘ar ya karbe ta,dan Akallah itake da babban shagunan dake ciyar da kowani mahaluki da zaizo wajen Dama chan Kowa yakan so abinci ta,Toh tunda nazo sai abun ya dada bunkasa,har daga wajaje daban daban ana shigowa neman abinci wajen ta,” Tana mutun ta kowa amma Da zaran ka nuna kai mayen mata ne sai ta bata rai ta kora ka. dan kuwa har yau anty hanne bata gaya ma kowa cewa ni ba kowa bace illah marainiya. Asali ma cewa take ni yar uwan ta ne nazo daga kauyen su.. Itama tana da kyau dan kuwa cikakiyar shuwa arab ce daga maiduguri amma mahaifiyar ta yar garin katsina ce. Kamar uwa haka ta zame min,girki da sarrafe sarrafen abinci babu wanda take koyarwa fiye kamar ni. Idan muna aiki tare sai Tace min kar nayi samari har sai na tara kudi na nemi ilimi mai zurfi.. Hakan kuwa har fara saka wa araina sai na zage sosai ina aiki,ita kuma tana aje min kudin har na koma wanu makarantar gwamnati ina dan cigaba da karatu na. A ss1 suka sake maida ni,amma danayi term daya aka gane ina da hazaka sai aka cilla ni aji biyu na Kafin ace shekara ta zago na waye tar har turancin broken din nan na iyashi sosai kamar dashi aka haife ni1 Sai dai a rayuwa nafi bada aikin anty hanne muhimmanci dan ko makarantar na shirya zanje, inta aikin saisa abinci ta kama nakan iya ajiyewa na rana guda don kawai na kula mata da business din ta, Sosai ta rike ni kamar jinin ta,itace tayi sanadiyar kwace fuskan maraici da damuwa acikin zuciya ta Sai nake ganin to meye a duniya nan wanda bazan iya mata ba?. Gashi Yanzu Na kanje wajaje dayawa aika,banki, kasuwa da sauran tsabgogin business, domin a shekara guda danayi anan kasuwan cin anty hanne ya dada habakan da yasa ta bude shagon saloon na mata ana mata service din pedicure and manicure. Tsaban gatan da tayi min sai ta barni ina zuwa chan ina raba kafa ina tayata aikin manicure idan na kammala saida abinci na,musamman wekends da bani da makaranta Kuma duka aiki biyu tana biya na. At 15years jiki na ya dada bayyana kyaun sa na ban mamaki… Girman da ya dan bayyana a kirji na ya shiga ruda mazan banza har na fitan hankali A ciki kuwa harda saurayin anty hanne wanda ta kama da kyar kwara daya akan shi zai aure ta ya rufa mata asiri. Shikuwa brother felix tunda yaga na habaka sai ya samin kahon zuka. Tun abun baiyi tsamari ba har masu jin haushi na suka dauki wannan daman suna kai mata gulman cewa na fara girma zan kwace mata manemi. Kwance tashi har anty hanne ta fara sauya min fuska, .nikuma sai na dauke wuta ma saurayin nata dan ko gaishe sa banayi Yanzu Duk da haka ban tsira ba,don a ranar da ta gane cewa asali ma baiya da niyyar auren ta dan Kudin ta yake so yaci sai taji haushin sa har sukayi kaca kaca yaje ya sha giya ya bugu sosai.. Gashi dama shima a gidan mu yake kwana tare da anty.. To daya shigo Maimakon yaje ya bata hakuri sai ya taho dakina ya farmin da niyyar yimin fyade. Ihu nayi masa ina kwarwa Ita kuwa anty hanne data fito sai ta hada har da kishi da rudewar tunani ta hada harda ni ta kora mu a rayuwar ta. Ranar Nayi kuka sosai,dan kuwa na fahimce ta itama sosai ba a son ranta tayi min haka ba sai du su arna dama basu cika daukar qaddara mai muni a rayuwar su ba. Tasan babu laifi na,amma sai tasa aranta nice sanadiyar rabata da mijin data sha wahalan samo shi don ya rufa mata asiri ya aure ta Ni kaina na fahinta wato samun miji Ba abu ne mai sauki wajen tubbiyar karuwa ba Dan haka na yi tafiya ta uwa duniya a duk dama bansan ina zanje ba. Kaya na da kudin aiki na da anty hanne tabani sune kawai a hannu na danko wayar salula bani da shi. “Kwaryan Garin kaduna na shiga ina browsing ko ina da idanu na,Tun bana son kashe kudina har nafara tabawa Daga inci wannan sai inci wannan Wani abin ma da kudi na amma da kyar na samun wajen kwana mai mutunci.1 Kwana biyu kacal nayi ina gantalin neman mafita makaina kwasam ranar sai nayi dare a wani hanya.. Dama wani hanyar nake bi idan zan shigo gari to bansan cewa ana fashi awajen ba sanda nayi kuskuren shiga cikin su har hukumar tsaro suka kama ni cikin rundunar yan fashi..1 Naci kuka kamar zan fidda raina amma babu wanda ma ya saurare ni Haka aka kulle ni har tsawon kwana 10 Wanda Da kyar da wahala na fitar da kaina,Anan kayana da kudi na suka salwanta suka bace na dawo daga ni sai ikon ubangiji na. Gefen wani dakali na zauna Damuwa sosai ya fara shiga raina Gashi Tunda aka sake ni a station ban ci komai ba ga yunwa ga tashin hankali gashi gaba daya na rasa gane ina zanje guda daya domin ataimaka min ko da na kwana koda zuwa gobe na nemi mafita.1 Haka na ta zaga garin kaduna da kafata ta karshen ta a wani babban masallaci mai site din mata da maza na dan rabe Juyi kawai nakeyi,kalar tausayi inda yunwa da bakar gajiya ya riga ya galabaita ni kwance tashi nake kamar taliyar dayaji ruwa, gashi ni sam ban iya roko ba. Duk sai na rasa meke min dadi A duniyan nan,baccin ma yaki zuwa sai dai nasha ruwa nayi sallah. Chan dai da yamma yayi sosai inata murkusu su saiga wata mata kanar daga sana ta taho da awarar ta leda mai zafi yana buso qamshin dadi sai kuma Tayi min tayi da fara’ar ta.. Ni kaina nasha mamakin kaina dan ko irin Ja din nan banyi ba n tsoma mata hannu na fara deba bibbiyu ina kaiwa bakina cikina dayaji saukar abu mai dumi har wani kugi yake shi kadai daga bisani matar sai ta tsura min idanu kawai tana min kallon anya lpya kuwan.. “Ban ma lura ba sai da na farga daga abun dana keyi,sikini na sauke kaina kasa cikin jin kunyar ta har Hawaye naji na neman kufce min,sai na maida su dai na yi controlling kaina cikin dabara na tsame hannu na pretending to be ok! Matar Ba yadda batayi dani nacinye ba amma haka naki fir harda mata karyan cewa zanje gida dama jiran lokaci nake yi.. Sai nayi mata godiya Tace toh bakomai hakan yasa na tattara kafata bayan isha’i na tsaga dare na cigaba da tafiya.. A Duk sanda na tuno da abun da ya faru dani a hannun polisawa da barayi sai naji tsoro ya taba ni sai nayi sauri na nemi gefe na zauna, Chan kuma sai na tashi na cigaba da tafiya kamar na mance Acikin daren har Wani unguwa na kai kaina bansani ba,wajen kuwa shiru ne babu hayaniya daga ji kasan anguwan manya ne. Normally nabi kan shimfidddiyar titin na dan sauka cikin wata siririyar hanyar data bi bayan anguwan ni kadai ina tsagawa kamar wata mayyyah don ko fargaba bana ji buri na na samu wajen da zan dan fake zuwa gobe amma har yanzu ban gani ba sai ma dada zilma kaina cikin ciyawa nake yi Ina dada kaiwa ciki bayan wani anguwa,sai naga duhun dake gabana ya dadu yayi yawa,tsoro sai yasa ni kawai na tsaya ina tunanin kar nabi hanyar nasake jefa kaina cikin wata masifa. Gefen wani old abandoned mtn stall na zauna na rafka uban tagumi.. Anan Ko minti biyu banyi wani rudadden kara ya firgitar da ni sai da na fada kasa na toshe kunne na. Karar kamar na bindiga ne amma banga kowa ba tukuna Wani rawa jiki na yakeyi shikadan sa Da kyar na dawo hayyacina anan ne ma na fara jin sautin Maganganu sama sama a kusa da ni,da wani uban speed kirji na ya kara bugun shi Sai nayi saurin labewa da kyau jikin shagon,nasa ido ina kalle kallen hanyar da zanbi na arce na bar wajen acikin hanzari Ina kuwa saka kafata zan gudu sai naji an dafa ni… Numfashi na ne ya dauke chak, Daga juyawa ta sai naga mutumin daya dafa nin ya sulale kasa ya fadi jikin shi da gefen kansa duk jini.. Da sauri na tsunguna akansa ‘na tsura masa ido sai naga yana kwace idanunsa da kyar yana min alaman na taimaka mashi. Daga gani yasha tsere dan haki yake yi irin na gajiyyau Kafin ma ya bide baki yamin magana sai na ji maganganun wasu mutane,a iya turancin dana iya wajen anty hanne yasa na gane cewa kashe shi suke neman yi shiyasa suka biyo sa nan Sai na yi sauri nima na dauke numfashi na,na ruufe shi da ciyawan wajen nikuma nayi gefe da shi ina lekowa haka na jira har saida mutanen suka bar wajen. Nan na shiga duba mutumin nan har nagane cewa.An harbe shi a gefen kafada ne Ne toh jini na zuba sosai sai kawai na yage dankwali na na daure wajen.. He looks very healthy and rich kaya masu shegen yau da tsada ne ajikin sa sai naga kuma ya tsufa sosai akalla zai kai shekaru saba’in ko tamanin a duniya. NAsan bazan iya daukar sa ko motsa shi ba,dan haka na shiga jejin wajen na shiga nemo mana hanyen mafita.. Karshe dai akan bola na tsaya na taho da sauran tsimammen giyar da aka sha ala watsar da broken botles da aka jefar kan wata open dump daukowa na yi na zauna na goge na kimtsa,da shi nayi jinyar sa duk dama yaban wahala sosai, mutumin nan yayi dauriya iya dauriya sa shure shure da komai har Allah ya bani sa’ar cire masa harsashin bindigar agafen kafadar sa.. Babu magani mai kyau ko wani mafita dan haka sai mutumin nan ya sume min Daga nan Mutumin nan bai farfado ba har sai da gari ya waye ni kuma ban yi bacci ba don tsoro haka na tsaya gadin sa. Da ya dago lunsamshun idanunsa ya kalle ni sai yace meye sunana nikuma nace mashi suna na bahiyyah. Yace min ya gode sosai da na ceto rayuwar sa amma nataimake Shi mubar nan wajen dan yasan za’a sake dawowa neman sa. Banyi musu ba na tallafa masa da kyar dan kuwa bantaba ganin dauriya da gwarjini irin nashi ba. Haka muka dafa juna muka shiga wani waje chan bayan garin inda babu mutane sai go naki da shukoki. Sai dai na lura raunukan jikin sa ya takura masa sosai kuma yana shan wahala. Muna kaiwa wani waje naga ya sake ni ya dan kwanta,yana dan dauke numfashi. Tausayinsa duk sai ya kamani dan Ji nayi kamar wani mutuwar zan sake gani agaba na, dan haka na shiga hade haden ganyen kusa dana nesa mai amfani da marar amfani har naci sa’a na gogga ma mutumin nan ya dan ji dama dama ya farfado. Sai Yace min na fita bakin hanya na nemo masa aron waya zai kira azo adauke sa Cikin mamakin ta ina zan fara nema Nace eh? Bai kula ba Yace kije kiyi sauri..kinji yata..? “Yanayin da yayi maganan yasa ni na mike tsaye Bansan meyasa ba sai naga kawai naje bakin hanya..da shike wajen baya ne sosai babu kowa Nikaina Na kai wajen minti 10 kafin naga wani saurayi akan machine roba yazo wucewa. I know i have to be smart sai na sa masa hannu na tsare shi a nitse. Cike da wayo da iya magana nace mashi dan Allah ya taimaka min nace dani da mahaifina ne muka zo wucewa sai mukayi hatsari kuma wanda ya buge shi ya gudu gashi babu wayar da zan kira gida. Naga fargaba a idanun saurayin amma dashike I look very cool and innocent gashi ina da kyau mai jan hankali, a haka har ya biyo ni na nuna mashi mutumin a matsayin mahaifi na .. Saurayin ya jimanta har da cewa zai taimaka mana amma mutumin sam yaki,shidai kawai yafi damuwa da yayi kirar da wayar sa. Bayan ya gama kirar sai Yace masa ya tafi babu damuwa za’a zo adauke mu. Nima Godiya na masa kamar da gaske Shikuwa haka yaki tafiya shima sai ya zauna damu har kusan mintuna ashirin duk ya dauka ko mahaifina na gaskiya ne dan kuwa sosai mu kayi pretendingn hakan “chan bada dadewa ba sai naga wasu kerarrun motoci har guda biyu manya manyan jeep daya an rubuta GMC YUKON daya kuma TOYOTA RAV4. A rayuwata inba a tv na ni bantaba ganin irin su ba.. Motocin Suna gama parking agaban mu Sai naga Wata kyakywar hmsahkiyar mace ta fito da sauri tayo kan sa Salati ta fara yi sannan ta rusuna gabansa Tana jajantawa,shima da kyar yake mayar mata magana, Ashe ma wani secret meeting ya fito da shugaban sojojin nigeria shine saii yan ta adda suka biyo sa sai naga sauran sojojin da suka fito daga toyotar sun tsaya sunyi jungum jungum anan dan dole aka sallame Saurayin nan aka karbe sunan shi da lambar sa,har soja guda daya ya raka shi har inda zaije Mukuma a cikin motar matan nan aka tafi damu. Nidai sun bani mamaki sosai Don A tunani na asibiti zamuje sai naga kuma an dau wani hanya Anbi damu wata sabon anguwa Cikin wani boyayyen gida mai azabban kyau muka sauka Sunan matar nan begham sahiba. Tana da taushin hali ga yawan murmushi.tunda mutumin ya bata labari na take ta min murmushi da saukin hali Anan naci abinci mai mugun dadi, nayi wanka na kwanta akan gado mai laushi Har sai washe gari Kafin matar take tambaya na labarin meya faru,ban damu ba nayi mata bayani. Kamar yadda shima mutumin ya gaya mata anan tace min nayi kokari sosai dan kuwa bansan waye na taimaka a jiyan ba. Tace nayi hakuri nadan zauna anan dan Babban hatsari ne su kyale ni na fita bare shikuma mai jinyar. Dan haka ne tace ba zamu je asibiti ba sai an tabbatar da safetyn mu anga komai is set ba mai kuma bibiyar mu Nikam bance komai ba nasan ko ansake ni ma bansan ina zan dosa ba,but Ni kaina Na fahimce cewa wannan din wani babban mutum ne,dan kuwa tsaro mai karfin bala’i aka saka acikin gidan Da muke Wanda ya kasance daga ni sai shi sai wannan hamshakiyar mata. Duk da ana bashi kulawa amma nima ina bada taimako na dai dai gwargwado Wasa wasa har Sati biyu mai kyau mu kayi anan kafin har Allah yasa mutumin yawarke ya tashi akan kafar san. Nan yasa aka kawo ni,muka gaisa sai yake tambaya ta tarihi na da inda za’a same iyaye na da gidan mu. A wajen sa is a matter of my security shiyasa suka ajiye ni nikuwa ban boye mishi komai ba na fadi masa komai daga inda na fito. Mutumin Yaji tausayi na sosai,sai ya aika aka kira begham sahiba. Banji dai yace mata uffan daga abunda na fada mashi ba dai, sai ya danka mata ni amana A hannun ta,yace mata gani nan sai ta kula dani,na lura cewa Mutanen suna da kirki sosai dan har hakuri sukayi ta bani Toh Tun Daga nan sai bansake ganin sa ba. Da safiyar ranar aka saka shi awasu motocin kirarar bakaken Mecerdes maybech wanda kamannin su iri daya ne har bazaka gane wanne yake ciki ba. Bansan ina za akaishi ba kuma ban tambaya ba. Nima Chan cikin dare bayan nayi isha’i na dan kwanta sai ga begahm sahiba,.. Kallo na tayi,sai na mike na zauna ina mai gaishe ta Batare da wani dogon bayani ba tace min na biyo ta mu tafi Sum sum na bita muka fita har waje, wata bakar jeep kirar nissan aka bude min tasha tinted babu tunanin zaka iya gane komawa ne daga ciki tare da begahm a seat din baya nayi zugum ana jan mu. Tsawon awowi uku muna tafiya har bacci ya kwashe ni,sanda na bude ido na na ganni a wani gari wanda bansan inane ba. Cikin wata katafaren gate aka bude aka shigar damu A duk da bacci da gajiyan dake idanu na bai hanani kalle kalle ba dan kuwa rudewa ne kawai banyi ba. Begham tace min sauko bahiyya ai mun iso ko. Baki na dana wangale ina kallo na rufe Nace toh na sauko cikin ladabi da sanyin jiki na iso gare ta Dan tafiya kadan mukayi zuwa wani shashi, A hannun wata mata sanye da kayan aiki ta damka ni sai aka kaini wani waje Aka bude min wata daki na shiga nikadai.2 Juye juye nake yi ina tunani iri iri Anan Har bacci ya dauke ni ban sake ganin begahm ba! Qarar da wooden door din ya saki ayayin da ake budewa shi ya daga ni a dan baccin bayan sallajn fajr dana keyi. ‘begham sahiba ce ta shigo Wato kyakyawar matar nan da Aka danka ni hannun ta jiya da daddare. “..Tun Bata karasa sake handle din door din ba ta kafe ni da ido sai dai batace uffan ba anan nima Sai na dan dago na kalle ta Wani haske da taushin murmushi nagani akan cikakken dattijuwar fuskan ta daya sa naji duk baccin dake idanuna sun washe. Gyaran murya tayi tare da cewa sallam Na ansa ta a nitse na mike na karbi kayan dake hannun ta cikin ladabi na gaishe ta da “ina kwana” sai ta amsa min tare da miko min package din dake hannun nata Tace min Open!.babu bata lokaci Sai na bude. Wasu jajayen doguyen Riga ne da dan kwalin su nagani ba ayi musu adon komai ba dana warware sai naga size dinsu dai dai kamar gwada ni akayi.1 Begham Tace baccin ya ishe ki kuwa bahiyya? Nayi saurin gyada mata kai to ina waje Maza ki shirya da kayan hannun ki sai ki taho ki same ni. Nace toh cikin mikakkiyar yanayi na tashi tsaye da kayan a hannu na kamar ba wacce ta taso daga baccin gajiyan ba. nan na shiga toilet na wanke idanuna na fito na shirya cikin kayan Data zo Min da shin din tsaf na fito na biyo bayan ta muka fara tafiya. Akan Wata shimfidadiyar titi muke takawa cikin wata katotuwar black and golden gate wanda bazan iya misalta tsawon shi Ba muka dosa. Ba shakka shi nagani ajiyan da muka shigo cikin dare sai dai ayanzun nafi ganin girman sa,..tunda muka hau tafiyar nake raba ido nidai sai kalle kalle na keyi begham tana a gaba na tafiyar ta Cikin nitsuwa Wanda Daga ganin ta kasan ita din babban Mace ce ..,duk dama a jiyan cikin dare muka shigo wani Mamaki ne ya cika ni ganin yawan mutanen dake haraban gidan ana ta kaikawo kowa cikin samfurin kayar aikin sa. Tun Daga tsarin kofar wannan katoton golden gate zaka iya cewa gidan wani babban mashahurin mayakin soja ne tsaban yalwataccen security armed forces dake kare gidan ta kowani fuska. masu aikin tsaron gidan suna da yawa Wanda akallah uniform din jikin su ne ya banbance su da sauran tarin ma’aikatan dake shawagi wasu sunsa clayed brown uniforms wasu day wears,kowa na hidiman gaban sa. Ina dauke idanu Na a kansu na ci karo da wasu irin dirarrun storey buildings guda biyu masu kama da ancient building of rustic architecture,to be honest,gidan babu maraban shi da gidan sarauta its huge, 8000 to 10000 times bigger than gidan dana fito. …kuma kowane storey buiding yana da personal golden door dinsa wanda suka kere tsayin na farko dana fara gani yanzu Da aka bude mana gate din farko wata haddadiyar parking lot na fara gani,acikin ta babu mota kwara daya da za’a baka wanda bazai fidda ka talauci na har abada ba. Bayan manyan driveways dake wajen, a Kusa da shi akwai katoton horse stalls wanda zai iya daukan dokuna dari zuwa dari biyu wajen is kind of grassy its like masu lura dasu ne kawai ke shawagi anan wajen. View din ginin gidan gaba dayan ta is just like that of a royal kingdom amma Kuma ba haka bane kai tsaye,sai ina ga kamar tsantsar tarin dukiya ce kawai take ambaliya bana wani sarauta ko Mulki ba . anan Shashin ma gani nayi kowani ma’aikaci na yawo cikin specific tsarin uniform din aikin sa Wata tsaftatacciyar iskan dana shaqo Ta ramin hanci na yasa ni noticing reference to nature dake zagaye da dogon Shararren streets din daya bada Undulating contours da layout din gidan cikakken tsari,its a Cool decorative greeny vegatation of palm trees sun jeru sunyi liff kamar da hannu aka zana su. Gefe da wannan waje akwai jerarrun pebles back splashes wanda suka Dada fallasa tsafta da nitsuwa Da kuma kwanciyar hankali dake muhallin wajen a karshe dai Wasu manyan multi purpose wood /metal furnitures zaka gani inda aka sarrafa su a wani open space kamar lambun shakatawa AHakan ma ba a bar cikin wajen haka ba sai da aka saka royal ottoman walls da relaxing benches hala ko dan Organisational functions. Gidan dai duniya ce Ido na ya gaji ne dan Bazan iya daukar komai da komai ba, dana bayyana muku tsarin,basket ball and handball court,swimming pools,arch statues,water splashes,da luxurios garages and gym din dana gani.1 Domin kuwa iya kallo nayi,amma Ni kaina bazan iya Fadan komai tsala tsala ba har muka shiga wata hall way daya miko mu wata tsaleliyar royal palour,kai wannan ya wuce nace dashi palor bari akira shi da royal hall kawai Wata mata ce ta shigo ta same mu nan suka gaisa, begham tace mune baqin albarkarciya jahan Aarah Allah ya sa bamu iso mata cikin takurawa ba”… Matar tayi mana murmushi da gefen idonta ta kalle ni sannan Tace”barkan ku da zuwa begham ai dama ku take jira amma kujira ni anan ina zuwa.. sai ta koma ciki Babu bata lokaci.. Nikam cigaba da kallon duniya nayi,..duk kauyanci na yau saida ya fallasa kansa design din cikin gidan ya wuce mahadar Da za’ace dashi luxury Meets royal elegance. Domin kuwa an hado tarin lush materials in bold colours like turquoise and ornate patterns chairs and sofas anyi sune da wani irin design din silk and velvet. Sannan an hada tsadaddun setin gadgets and kuma daidaita marching textures kamar su velvet couches din,metal light fixtures,wood tablets and glass decors. A takaice dai duka Furnitures Dake Ilahirin gidan an kera su ne da elm, marble,hickory and chery,sannan dukan handles din furnitures din su anyi shi ne da Tsadaddun brass knobs wanda ya hada da hannun drawers,cabinets da tuff boards ga kuma airmores.2 A gefe dani kadan akayi ma zaunin wasu shegun hand crafted brass and copper lanterns dake fidda wasu irin launin haske daya dada kara ma wajen touch of royal sophiscation and warm elegance. Ban san Sanda na karkato wuya na leka Sauran hallways din ba its like A saman kowani hall Dake gidan akwai crystal chandellier Mai mugun dauke ido Then finally The wall scounces. Shigowar wannan matar ya dakatar dani Daga duban wani Iri ne,as expected da murmushi kan fuskan ta tace mana ki shigo bismillalh sannan tayi gaba Muka fara binta abaya.2 Tun Kafin muyi nisa begahm ta dan dube ni, wani Kallon gyara kimtsi tayi min wanda ya jefa ni cikin nemowa kaina nitsuwa Da kama kai. dan haka Ne ma ban kara kallon sunnah ma komai ba har muka iske wata amazing royal palour Bazan iya Fadan me ya kumsa ba Tsabar haduwan shi.1 Tuni matar da ta kawo mu ciki tayi gefe ta tsaya Ni kuwa alokacin Wata kyakkwiyar mata ce ta dauke min ido, i bet she is in her early fifties azaune agaban full size screen tv take xaune tana amsa waya tana dariyar ta mai cike da nuna kasaita da aji. Kallo daya zaka mata kace sarauniya ce domin kuwa jikin ta sanye yake da wani tsadadden grey gown mai dauke da ratsin black diamond stones kanta tamke da Nadin turban Shi kuma baki. Haka muka jira ta gama amsa wayar ta,data juyo ta kalle ni wani Murmushin dana gani shimfide a angelic face dinta yasani naji ciki na yayi kugi har gabana yana dif dif shi kadai A duniya Bayan mahaifiya ta wannan mata to me She Is the most beautiful creature anyone can think of. Ido kawai tayi ma dayan matan ta fice ta bar mu da ita MU ukU. Sai naga begahm sahiba ta rusuna da sauri cikin girmamawa tana cewa, Allah ya ja zamanin ki jahaniyah mai Tarin albarka ga nan yarinyar da aka bani na kawo ta wajen ki. A Nan ma murmushi kawai matar tayi mikewa tsaye tayi cikin Salon kwarjini da kasaita ta iso gareni. Wani nitsatsen Kallo ta bini dashi A sanda take faman daidaita Kasaitacciyar tsayuwar ta agaba na Karkwawa hannu na ya fara yi dakanshi duk Tsoro da fargaban inuwan ta ya cika min mara tam da fitsari sai Zaro ido waje nake ina sadda kai. Da shike batace mjn uffan ba Wajen wani shiru ya dauka kamar an kashe maraya,nidai ko da ba’a gaya min ba a irin wannan kallo Nata Nagane Cewa ta takarance ni tsaf daga sama har kasa Babu ragi ..sai da taja sight relieve kafin tace min “Ure most welcome”..ta na fada Da sauri na dago Na dan kalle ta dan kuwa sautin muryan ta mai mugun tsada ce sai dai barin baki ya hana ni amsata Tace Begham ki kira min adama kuzo tare In 5minutes. Begham Tace toh angama ranki shi dade sai tayi waje ta barmu Atake. Matar Bata sake kallo na ba ta Juya ta koma kusa da tsakiyar hall din,Sai da ta dan bani Rata tukun ta juyo tace yarinya Meye sunan ki? Ban bata lokaci ba na dago Cike da dauriya Nace”sunana …bah…i..yyah Bahiyyah… Sai Tayi Shiru Bata sake cemin uffan ba But She was looking at me closely like a true royal queen of dynasty yadda ta nade hannayen ta da su kaji jan qunshi da kwalagwalai yasa naji tamkar ina gaban wata sarauniyar matan duniya ne Gaba daya Ita kuwa kallo na takeyi har Sai da ta lura na natsu kafin ta sake sauke ajiyan nunfashi Cikin nitsuwa da sanyin kalami ta fara min magana. Tace sunana jahan Aarah nice matar wanda kika taimaka a wancan daren da baiyi da manufar alheri a cikin rayuwar mu,miji na Ya fada min sunan ki bahiyyah But na sake tambayar ki ne sabida waka daga bakin Maishi yafi dadi… Anan Wani nitsuwa maganan nata ya sakamin dan cikin kasaitaccen yanayi ta karashe shi,sai Nayi shiru na bata full attention Sai ta cigaba Da cewa Mijina ya fadamin komai Game dake,dan haka Zaki zauna anan gidan tare dani kafin nan ya kammala sauran jinyar shi ya dawo. Fatan kin fahimce ni? Da sauri na gyada kai na tari numfashin fargaba dake neman shake min wuya na da beam smiles Shigowar su begham kenan jahan Aarah,tayi nuni da Matar da ta shigo Damu mai suna adama Wanda kowa A gidan yake kiran da Sunah ammuh,Anan Jahan tace Mim wannan zata nuna miki duk abunda ya kamata ki sani. Wani kawataccen box naga ta sa adaman ta dauko mata,ba bata lokaci naga ta miko shi ma begham Ita kuma ta rusuna tana godiya …a haka har tayi mana sallama ta bar gidan mu uku aka barmu a faloun Inda Nan din gidan sarauta ne Da zan iya Cewa Adama ce jakadiyar jahan Aarah but no. data dan dube ni sai Tace Ranki shi dade fatan zamu iya tafiya Ko akwai wani bayani Ne? Kawai sai naga matar ta min hannu Alaman na matso,murmushin data keyi yasa na dada tahowa a sanyaye na tsaya daf da ita. She knew im nervous and soo scared,hannu na ta fara kamawa sai tace godiya ta tabbata ga yarinya mai jin kai irin ki. Karki razana da mu babu abunda zamu miki,kwance tashi ai baya hana ruwan rijiya sabawa da guga ko!just relax ..u will get use to this place Its ur home now. A hankali na dago na dube ta naga murmushi ma takeyi still,Kirjina ne ya shiga bugawa Amma dana samu na kauce ma hasken idanun ta da kyar na iya furta mata nagode. Tace zaki iya aiki agidan nan? Nace eh na kuma na gyada kai a ladabce Tace toh adama gata nan Zan gaya miki Sauran details din aikin ta anjima. I think she will fit in best ma aikin dana zabar mata. Hannun matar Naji A kafadata Ta dafa ni sai na dago kai Amma Nakasa hade ido da ita,But i can feel it while smiling at me tace Daga yanzu Zaki zama mai kula Min da dana shima yana nan agidan nan2 ..Yadda tayi maganan nasan This statement is neva a request Bare na samu filin MUhawwara da zuciya Ta akan ina so ko bana so Nidai Wani irin faduwar gaba naji tun kafin ma na ce Komai,naji ammuh Adama ta yi korafi tanacewa amma ranki shi dade,anya bata kasa a matsayin personal maid din khaldun ba? Dan karamin miskilallan murmushi matar tayi tace mata a’ah, I think shes 15 ko?Ta dube ni Sama da kasa in a quick body inspection nikuwa nayi saurin sauke kai na kasa Nayi Shiru. Sai Tace zata iya mana,beside a matsayin alfarman da tayi mana ta wuce wanda zan bata aikin kula da dawainiyar dana. Adama Da saurii adama tadan rusuna kai tace yes jahan Just Do one thing,teach her everything and everywhere. Idan kuka kammala nida kaina zan gaya mata dokokin aikin ta Adama ta dube ni tace kinji ko? Cikin barin baki mai dada bayyana innocent heart dina na amsa da eh naji. Nagode Nan Jahan din tayi murmushi ta sallame mu hannu na adama ta kama muka nufi wani site. Nidai bin ta kawai nake yi amma Bansan cewa jahan din tafada ma adama akan Gwajin hali ta daura ni Shiyasa tabani wannan aikin ba. Chan da yamma Bayan waje yayi liff ana ta shirin himman kirayen sallahr magriba Matar ce a kwance akan wata sculpted black tuned soffa a wani purple tinted mini palour Har ta sauya Kayanta zuwa royal orange arabian jallabiya. waje yayi shiru sosai don kuwa nan waje ne da ta saba amsa wayar mijin ta wato retired,navy admiral 5 stared army general,a reknwn political beurocrat,and the 39th chief security adviser to the united states legis. Rtr adm gen alhj hamood mufaddal clive sunan shi.. Shi mutum ne karfaffa mai tsayi da jiki curently in his late 70s. Duk da wayannan matsayin na shi He Is still a son from an ancient royal palace of iran anan ma wata sarauniyace ce ta haife shi.2 Da tarihin Zuria yabi zuria a nan asalin tarihin sa ya bayyana cewa ajinsin dawlat khatun ya fito karkashin jinin wasu bi-Queens of the persian empire paticularly jinin sarauniya badi’atul jamal waccce ta fara kafa tarihi nadaban a labarin sarki sayful maluku tun a lokacin kasar iran yana amsa sunan sa na land of aryans a duniya. A yanzu inda ta kwanta babu abunda take Tunani kamar maganan da su kayi da mijin ta akaina tun kafin nazo,shiru tayi cikin wani nazarin daya sake jefa ta cikin jimamin abunda ya faru da shi a cikin kwanakin nan yare da lunshe idanun ta ta sauke wani sassayan ajiyan zuciya. Asalin sunan ta Aarah,amma ana kiran ta da Jahan Aarah itace matar sa na farko,duk dama ita ba daga dangin shi bane amma Soyayya sosai su kayi kafin sukayi aure …rtr hamood ya kasance Shine hasken zuciyan ta cikar burin ranta,farin cikin ta da duk wani sadaukar wan ta,sai dai inta Tuno cewa badon yarinyar nan bahiyya ba da babu shi a duniyan yau Sai taji kamar ta sa a kira mata bahiyan tayi declaring dinta yar cikin ta kawai dan nuna godiyan su,. Da dai Sun tsara hakan tun a farkon jin labarin ta,sun fahimci cewa ita abun a tausayawa ne, yarinya karama Marar uwa da uba ne a duniyan nan. Sai dai she can’t Do That just yet,bazasu iya aikata haka agagauce ba domin kuwa su manyan mutane ne wanda rayuwar su ke tafiya da tsari da dokoki wanda dole ne su bishi ko dan samun tabbatcen tsira daga makiyan su. Bayan mutuwan iyaye,ayanzu abu mafi daraja arayuwan jahan Aara shine Mjin ta Daga shi kuma sai yayan ta Guda biyu mace da namiji Gashi Haka kawai Bahiyyar ta shiga ranta,har ta Kuma furta hakan ma gen hamood M tun ma bata ganta ba Toh Lokacin ne suka hadu sukayi nazarin rayuwa Mai zurfi akaina harda hadun bakin yar uwan sa begahm sahiba acewar su tunda an tabbata bani da kowa a duniya toh Kafin su maida ni official adopted child zan zauna a matsayin mai aiki da hidama da dansu Wanda Duk cikin zuria suke ganin kamar babu irinsa a wajen wahalar zama,shi mutum ne mai murdadden yanayi,muddin har na iya zama dashi to babu tantama zan iya zama da kowa. Kuma Ahakan suke saran sanin wacece ni kuma da Wacce irin zuciya nazo Musu dashi. Cikin su jahan tafi kowa Fatan na Kasance ta gari Inda zatayi saurin yanta ni ta dawo da ni tamkar yar cikin ta domin ita mace ce mai tsananin tausayin nakasa da ita Ga son maida Ladan alheri akan lokaci..tunda ta ganni yau take faman tausayi na aranta. She is already thinking of so many ways to repay my kindness. Ni kuwa tun Ranar da muka fita a shashin jahan Aarahn ba a sake bada izinin dawowa dani ba Achan wani sashi muke Jibge,tare da sauran dattijan mata Su hudu wanda suka kasance manyan masu lura da ma’aikatan gidan kowa dana shi fannin Daya kware. Ammuh adama itace general Chief maid Na gidan,Sai mami fatima tana kula da harkokin siyayya Da harkokin Kowani irin store Inde nagidan ne, Mami hafsa Itace mai Lura da duk wani shige da ficen kowa dan haka tana da Masifa Sosai. …Mami jamila Kuma Itace kunne da idon gidan babu karya Wajen Aikin ta na gano munafukai da warware matsala Tsakanin Mutane. Sam basu da matsala domin kuwa akwai wadatacciyar arzikin da komin Salalan Tsiyar mutum dole zaiji shi ajikin sa. Yanayin Tsarin dokan da aka shimfide ake bi da ma’aikatan gidan Shi yake nuna sakewar su da dattako da girmamawan su wajen Aiwatar da dutyn su. Kwanaki goma sha biyu kacal Ammuh adama ta dauka tana saita ni Farko sai da ta zagaya dani kowani sashi lungu Da sako na gidan kafin muka dawo muka fara daga kan koyar salon magana girmama Nagaba kwajin tsafta,iya tafiya,Kayan Amfani da girki,hatta yadda ake serving da yanayin gyaran gadon su duk ta nuna min hazaka da kaifin basirah ta yasa yanzu zaka sha mamakin yadda adama ta sake dani,dan sau daya zata fadi abu na dauka,daga ta koyar dani tofa za taga nayi dai dai koma fiye Da hakan, kuma bana da saurin mantuwa.2 Ammuh Dai ta dawo min kamar wata uwar daki don kuwa tun zuwa na ba wanda ya taba daure min fuskan sa Agidan.. Yanzi har na Saba a gidan Karfe 7.00 Na kowani rana ake bude gate Din waje gaba dayan ta sannan babu mai fita agidan har sai karfe 9. Anan inda nake Kwana kuma 6.oopm na safiya ake buga musu workers alarm Daga jikin wata katuwar agogo dake Chan sama tsakiyar gidan dan haka kowa lokacin yake tashi ya shiga hidiman aikin sa Yau Ina zaune akan sallaya Ammu adama ta tada ni nayi wanka na fito na saka wata riga da zani ruwan madara Da simple flat shoe na biyo ta. Ni dai bakowa bace amma a yadda naga suke min nasan indai karamci ne to ana yimin. Site din jahan Aarah muka nufa da shike babu hayaniya har muka shiga banga kowa ba Sai ita a Zaune Akan Beige rug Wanda yaji Floral patterns Rusunawar Gaisuwa ammu tayi Bayan ammun ta mike Nima tuni sai Na bi sawon ta na rusuna.”Nace Allah ya taimake ki ina kwana? Jahan tace lpya bahiyyah ko!. Nace eh nice…sai dai bandago kai na ba Yadda na gaishe Da Jahan din cikin ladabi da girmawa ya matukar burge Ammuh adaman barin Ma aje kan jahan Din dake sake min faffadan murmushin ta mai Saurin Tausasa yanayi Daga ganin kalar biyayya ta,She’s now very sure that zan iya aikin da suka daura ni akai Duk dama tasan Task ne mai matikar wuya. Gashi dama ban san cewa begham sahiba kafin ta tafi ranar Har ta fada mata na iya girki kala kala ba. Im just a teenager but with lots of focus and energy ni bana son saibi bare sanyin jiki ayadda naga mahaifiyata na Kazar Kazar Akan aiki Nima haka na taso da spirit din. Jahan Aarah tace ki saurare ni kiji abunda zan fada miki duk abunda baki gane ba call my attention ok? Kaina a tsunkuye nace yess Jahan. Tayi murmushi Tace’..aikin ki na farko karatu ne zaki zauna a koyar dake domin ki samu good secondry school cert,duk wanda kika gani agidan nan yana aiki toh yana da abun da zai nuna na matsayin matakin karatun sa, but yours is gonna be afternoon sessions a site din maids Thats in kin kammala duk wani aikin ki. Game da ayyukan ki kuma Ya kamata kisan cewa. Dana Shi kadai yake cin Break fast dinshi dan haka akan lokaci zaki na kasancewa a kitchen din dake section dinsa Wanda ke Kusa da dakin kwanan sa… Adama tafada miki kitchen din nashi ne shi kadai ko? A Dan Sanyaye Nace eh. Tace good to Kar ki sake Kiyi masa abinci awani wajen inba A nashi kItchen din ba Doka ce Cikin gamsuwa Nace yess maam Tace By 7.30Am na Ko wani Safiya zaki shiga bedroom dinshi,do not wake him up kedai ki tabbata kin aje mishi fresh mint tea,and dont forget No Sugar honey Za kisa Masa 2teaspoon. Zakiga oak side table anan zaki bari sannan sai ki fita Inya tashi Zai fito karfe 8.00 Dai dai dan haka kiyi kokari Yana bada baya ki shiga dakin ki canza bedings Dinsa ki tsaftace dakin,kar ki manta zallan dakin baccin sa ne aikin ki,sauran part din san akwai masu kula dashi. Sannan Karfe 9 zai taho dinning dinsa cin breakfast. Sai ki tsaya ki yi serving dinshi ki Zuba mashi ko wani nauin abincin da akwai ba tare da kin tambaye shi mai yake so ba Bayan kin kammala da nan sai ki koma ki hada mashi ruwan wanka akwai instrument so set it at exctly 39 degrees,yana wanka ke kuma kina tsaftace kitchen din sa. Kar ki damu da serving dinshi abincin rana a wajena yake ci. sai dai Idan ya dawo zaki kawo abincin daren shi dining dinsa da misalin karfe 8.00,sauran lokacin da kike free zaki iya amfani da shi kiyi sauran ayyukan Daya dace Nidai kallon bakin ta kawai nake,nace Ikon Allah!shikuma hakan rayuwar sa yake?Hmm tabb di. “Baahi…adama ta dakatar da tunani na da kiran ta Afirgit na amsa da naam.. Tace Kinji abunda aka ce miki ko? A dan birkice nace naji insha Allah zanyi Duka.. Nan Jahan ta sallame ni Fuskar Ta dauke da Wani irin Weak smiles. Dana fice Adama ce ta matso cikin saukar da kai tace ranki shi dade jahan. kiyi hakuri da shisshigi na amma sai naga kamar daman Da kika bata yayi yawa khaldun sa’ood bazai so ace….. Bata karasa ba jahan ta daga mata hannu..Tace Karki damu Da wannan adama Nina haife shi kuma Nasan menakeyi sarai Shin ya kike ganin hankalin yarinyar a yanzu?ko akwai abunda kika gano game da ita wanda zan iya sani ne? Nidai Nayi nazarin Mai zurfi Akan tarihin rayuwar Ta dana jiyo Muddin Yarinyar nan ta wuce wannan jarabawar dana dora ta to ba shakka zan kaita wani matsayi mai kyau arayuwa… Ajiyan zuciya adama ta saki tace a’ah babu komai Jahan she’s perfect sai dai bamusan nn gaba ba…nidai Ki barmin komai A hannu na ni zan kula ..Adaman tace. Jahan tace Toh kiyi kokari… Daga nan sukayi sallama kowa ya shiga hidiman rayuwan sa. washe gari da safe Ammu adama ta taso ni agaba tace min Yau fa zaki fara aikin ki bahiiyyah gaba naKe Yawan faduwa sabida gani nake kamar Bazan Saba ba cikin nitsuwa da jan kunne Ammuh adama ta Zaunar dani tace kina ji na? Nace eh Tace to kar ki sake ki shiga bangaren shi Gatsau,bare Kuma dakinshi in har ba akan aikin ki ba and most impotantly babu ruwan ki dayi masa magana inba shi yayi miki ba Ki nitsu ki ji duk abunda zaice miki batare da kin sa ido kina kallon nashi idanun ba,in yana tsaye kar ki zauna domin shi ba mutum bane mai son raini zakiyi hankali dashi sosai. Cikin nazarin abun Na kuma cewa toh naji Ammuh Tace Tashi muje na kaiki sabon dakin ki Zaman ki anan ya kare ..da sauri na dago nace sabon daki Na kuma?Tare zamu kuma kenan ko ammuh? Dan Allah kar ki rabu dani .. Ammuh Adama tayi murmushi cikin son kwantar min da hankali tace Bahiyyah kenan, Daga nan dai batace uffan ba,Hannu ta mika min na taso jiki a sanyaye na fara biyo ta. Bamu tsaya ba sai a cikin wani sashi Ta cikin gidan Mai kamar four duplex apartment Amma bashi din bane design Ne kawai Sai da ta nuna min Wani zigzag stairs da zan bi ya Sada ni da wajen aiki na kafin muka sauko Wani daki sai ta bude min Muka shiga ciki Tare. Its a very Exotic sleek style bedroom So simple and elegant. gadaje Yan madaidaita har guda biyu aka bar min Ga brass lanterns Masu fararen haske,komina design din Sa fari ne kar gwanin sha’awa. This is ur personal room. AmmU tafada tana Bude Min wardrob dan na ga kayan sawaN da aka aje Min,tace Min zaki iya muamala da kowa amma aikin ki baya bukatar ki sake da sauran ma’aikatan gidan nan If posible Just stay alone shi Zai Fi miki. Tace babuu wanda jahan ta karramashi da wannan matsayi saike dan haka kar ki bani kunya bahiyya. Sai na dan kalle ta dan Sosai na kejin wani iri araina,sai naji na Bi na damu tsoro na neman shiga ta sosai..all this rules..oohh ya rabbi Haka har adama tayi min sallama ta fice,tin daga ranar kuma ban sake ganin ta ba. Nikuwa Ba jira Da safassafe na tashi na haura site din sa,i think A rana na farko i was a bit early sabida danaje kitchen din shin sai da nayi tsayuwan minti talatin ina jiran lokaci ya daidaita kafin na hado Masa steamy mint tea na dora akan italian tea sets farare kal Na fito dasu A hankali nake bin ta hallway da yakai ni har bakin kofar dakin shi,cikin kula natura kofar tsoro na kar na dago shi a bacci Dama A raina na bari cewa He must be a demigod tunda kula da shi ma yazama abun aiki Irin haka.2 Dana shigo Fully na kare ma ko ina kallo Sai naga Dakin yafi karfin Ma ace dashi normal daki don yana da girma sosai its like an apartment on its own Har da palours. A kusa da tsakiyar dakin aka kafe Wani sharbaben king sized royal bed,mutum ne a kwance fuskan sa gaba daya a rufe Take da duvet Ba Aganin komai daga siffar sa Ban tsaya kalle kalle ba na aje tea din akan oak Oriented table na juya na fita kamar yadda aka fada min Dinning hall Nayi da sauri naje na shiga jera mashi warmers din abincin shi Akan dinning table. Haka na dinga bin lokacin aikina daki daki har naci nasaran gyara mashi daki na sauya bedsheet na jejjera pillows komai akan tsari Saura minti kadan lokacin cin abincin shi yayi dan haka na fita naje dinning area din nayi tsaye ina jiran shi ya dawo Daga inda yaje don nayi serving dinshi ..But ganin 9 yayi dot bai shigo ba nayi himma na shiga serving Duk abincin dake wajen yadda aka koya min. Ina gamawa nayi sauri na koma dakin shi Nan na shiga dayan kofar da nake tunanin bayan gidan sa ne,to tunda nike da alhakin hada mashi ruwan wanka that means tsaftace bayin sa ma aiki na ne. Haka na gama kare ma wajen kallo,Kirji na ne ya biga ganin girman complicated bathrum din da ko a mafarki ma babu kaman sa, na dan dafe kaina na taho domin fara abun daya kawoni A cikin bayin Wata katoton mirror ce mai dauke da handler na kayan duniya. Gefe dashi akwai bath tub wanda ajikin shi drawers ne masu yawa da Wata full sized jaccuzi da kuma site din wata striated rectangular glass shower Tana wani kyalli kamar ba ataba taba shi ba shima gefen sa da akwai fixtures masu dauke hankali Komai Dai a bayin Royal purple And black ne girmanshi mutane fiye da talatin zasu iya shiga ciki Nidai Tabe baki nayi kawai na shiga hada mashi ruwan wanka at exctly 39 degres din”,wai shin wani dan adam ne a duniya Wanda har yake da specific tempureture na ruwan wankan sa? rike da themometar dake bayin a hannu na nake wannan tunani ina tabe baki.1 Finally i did whats right minti sha biyar kawai na dauka na fito daga dakin walking quietly Down stairs zuwa dining area dan naga ko ya taho Luckly enough Bayan shi kawai na hango alaman yana cin abincin amma Koda wasa banga ya kammanin shi yake ba,leke nake ina daddafa pillar Ko zanci sa’a sai dai ko 1scnd ban yi ba naga ya mike alaman zai tashi,wani uban tsoro yasa Ni back turn da gudu na yi hanyar kitchen na dauko food dismisal tray Kafin na Dawo Nan ban ganshi ba Kallo nabi abincin dashi wanda yake kamar ma ba ataba shi Ba,i was like did he even touched It? Sai ido na yafada kan half stained spoon wanda ya isar min da amsa ta haka Kawai na Shiga tattara Komai nakai kitchen na Kuma tsaftace su Haka Najira har ya fita kafin na je loundry dan ance mani za’a dinga bada gogaggun kayan shi ina aje masa a closet dinsa. Tun Daga ranar Haka nake yi kullum babu abunda ya sauya, Nakan dai gaida jahan dik lokacin da naga sarari dan ba ko yaushe ake ganin ta ba Tun ina dar dar da gidan har na sake na jajirce na shiga bin dokokin aiki na tsaff inayin shi Sai dai fa har yau ban taba ganin fuskan sa da kyau ba Idan na kawo mint tea yawanci fuskan sa a arufe yake cikin comfoters ko ma ya juya fuskan sa gefe Ko da ina serving dinshi baya zuwa har sai na kammala na tafi, bare ma nace nagan sa Rana daya dana ci sa’a ya zauna ina zuba mashi abincin idanun sa da dukan hankalin sa nakan wayar sa. kyakkwar motsin nunfashin sa banaji bare naga ya kamannin sa yake. All i know is he is fair,fari ne tass irin caribean white din nan kalar jikin shi kamar ana goge shi da madara kullum, shi baiyi dau ba amma sheqin dayake yi ya wuce misali yana da tsayi da ginannen jiki da duk da namijin da ya mallaka zaiyi tinkaho da shi Domin Kuwa babu maraban tsarin sa dana Indian actor john abraham..1 Yau sati biyu kenan amma sau daya na taba jin muryan shi ranar dana ce muku na yana latsa Waya hakan ma Cemin Yayi “leave”2 Muryan nashi ko akwai dadi,Its husky,deep yet very appealing domin kuwa har yau ban mance sautin shi A kunne na ba. One fateful friday morning na taho da safe domin aje mishi shayin Sa as usual nayi komai daki daki sai dai Ina juyawa zan fita naji tsadadden sautin muryan shi cikin dakewa da gadara Ya furta stop!!!? Wai wacece ke Kike shigo min daki na?