AJALIN SO CHAPTER 7

AJALIN SO CHAPTER 7

Hannun ta ajiye daf da nasa zuciyan ta cike da fargaban dalilin da ya da ta kawo kan ta nan din+ But she cant help it kwana tayi tana tunanin sa acikin mafarkin ta sai taga kamar wani abu mummana zai same sa jin karamin nunfashin ta data kasa boyewa yasa shi bude idanun sa slowly ya kalle ta bata sani ba dan karamin murmushi ya sake … at same time ta mike kawai zata tafi taji ya riko hannun ta wani irin bugu kirjin ta yayi ta sake nishi mai dauke da tsoro ta juya taga dai har yanzu bai jiya ba calmy yake a shimfede kamar yada ta same sa Lpya dai ko ?..yafirta sannan ya bude ido da kyau Ya jawo ta kusa da shi a dan firgice ta zauna tana kauce ma idanun sa Shanyayun idanun sa Ya kure ta da shi zai sake magana tace ni xan tafi..bai kula ba ya jawo ta da dan karfi ta fada jikin sa gaba daya Yace noo.. Sai kin fada min kafin ki tafi meya kawo ki nan?ko sun sake biyo ki ne..ya dage mata gira so cute Zatayi magana amma ta kasa sabida yadda taji ta gam ajikin sa har wani nade ta yayi da hannun sa kamar ya sami teddy bear yana sane da hakan ya dada jawo ta ta hauro sama da kirjin sa lips dinsa dake saitin kunne ta yasa take shako zautatun numfashin sa tuni ta lunshe ido ta lafe tana jin dumin jikin sa rigar sa ta kankame da hanun ta kirjin ta na bugu shikansa baisan meyasa yaji yana bukatar hakan ba ba shhaka da ita ya kwana azuciyan sa Yace Say somthing “comon …banafsha? Mafarki nayi.. Im just scared …Da kyar ta furta muryan har na rawa kalar kuka Yayi shiru chan yace look ure just scared.. Amma ba wanda zai sake damunki evrything is been taking care off sai ki cire aranki ko Ta dan gyada kai Tayi shiru itama sai ya lumshe idanun sa..chan ta zame ajikin sa ta dan dube kafar nasa har yanzu daure da white bandage Ganin bai bude idon ba ya sa ta karasa ta dan taba yace shhh …dont touch it unless u wanna help me massage …yadda yayi magana yasa taji kunya ta dan sadda kanta kasa sai ta taho daf ta daura kafar nasa acinyar ta ta shiga shafawa slowly tana dannawa haka ta cigaba da massaging har sai da taji shiru ya koma bacci Ajiyan zuciya tayi cike da rudanin zuci ta bar dakin ta wuce kan gadon ta koma bacci itama tun bayar haka ta sake lumewa cikin blanket bata sake motsawa ba.. Ga lokaci nata tafiya Ba yadda hjy mamah bata yi da ita kan ta tashi ta tafi makaranta ba amma haka taki fir.. Sai ma ta nace da cewa ai mohan yace yau bazata je ba.. Dan dole Hjy ta dago ta tace mohan dinne yace bazaki makaranta ba.. Tace eh..tace akan me fa..shine principal dinku ko me? Dan ya saki makarantar sai akace shine me iko dake..tace a’a a nannnah ai bai da lpya ne..sai ta dan turoi baki ta kumayin shiru tana inda inda.. Hjy tabi da kallo tace ikon Allah…mohan baida lpya sai akace banafsha bazata je makrnta ba..? Ke sauko nan anya lpyar ki kuwa.. Ta dan sauko har ta soma taro ruwa a idunun ta tace Allah nannah shi ya ce kar na je yau.. Ai zaki iya tambayar sa ko.. Kallon ta hyj mamah tayi tace wato kina boye min wani abu ko?…tayi saurin girgixa kai alaman bata gaskiya..hajy ta sake matsowa daf da ita tace meya same shi jiya to..meyasa kukaje asibiti kuka zauna har dare..kifada min.. Ta dan yi shiru ta sunkuyar da kai gaba daya sakalcin nata abun dariya.. Hjy tace watoh bazaki fada ba kenan ko banafshah..shi yace kar ki gaya min ko? Dai dai nanya tsaya bakin kofar yana jin su.. Tace ba shi bane nannah..kawai fa yaji ciwo ne ai kema baka gani ba jini yayi ta zuba ..ta dan da fuksn damuwa.. Yana ji hjy tana neman kawo maganan garin yaya sai kawai ya juya ya bar wajen. Haka suka ci zaman su anan banafsha tana juya ma hjy mamah zance gaba daya ta ksa gane me take cewa Har sai da ta saa ta mata alkwarin xata bada zuma ma mohan sabida ciwon sa ya warke da wuri.. Duk tayi hakan ne sabida su tsaya da hirar akan ciwon kafar nasa bata zan hjy mamah dagaske take yi ba.. Shikuwa tun da ya fita bai sake dawowa ba sai chan bayan isha’i.. Komai ya shirya daga tafiyar sa don haka yayi bankwana da asibitin sa. Sanye take da material mai kamar lace purple mai aikin silver stones an mata riga da skirt fitted sosai ya nuna kykywan shape din pre maturity din ta. hjy mamah ne agefen ta suna kallon wani indian series “the cross road” Yana sallamma suka maida kallon su kansa Sanye yake da jumfar getzner royal blue da hular matching vine simple armani half shoes ya dakaya ma kafar sa wanda ba tantama sabida ciwon ne.. har ya zo ya zauna basu dena jin qamshin daddan turaren sa dake gauraye musu cikin.. Yana gaisawa da hjy mamahn ita kam ta kasa zama waje daya duk kunya da fargaban sa take ji ko da ta kare masa kallo sai ta sabule zata mike tsaye ta bar wajen hjy tace baki gaisuwa ko.. Ya kauda kansa adan daburce ta rusuna tace sannu da dawowa… Kamar bazai amsa ba yace sannu..kamar walkiya ta bace bat sai ji sukayi ta rufe kofa acahn sama.. hju ta dago y dube sa tace hankain ka yana kwance sai shinfide mulki kake kamar kasamu ajiyayyen bayi..1 Ya dan juyo carelesly yace hjya shine zaki kai kara na har wajen sa meyey ne bazaki iya fada min ba.. Ya dan daure fuskan sa sounding serious. Tace me kuwa zan maka ai ka fi karfi na mohan ka raina ni sabida bani na haifeka ba dana ne.. Ka duba kaga yadda yarinyar nan take tsorata ma inuwan ka wai sai yaushe zaka dawo mutum har afara rabarka….kai kenan kullum kamar dutse ni dai bazan zuba maka ido ba har ga Allah ka ishe ni.. Yayi mata shiru still fuskan sa daure yace kin gaji dani sai ki yadaa ni ai.. Ai nace miki ban sani bane.. dana san zata tsorata zan ajiye ta anan ne…? Nafa baki hakuri wai meyasa hakan ne hjya. yanzunvkinsan anyi min fada shikenan hankalin ki ya kwanta ko Kasar makoshin sa yace Dama za’ayi tamin abh amma ni idan nayi kuskure daya sai a haura min.. Ta sani sarai ba hakan yake so ya fada ba sai ta sa muryan kuka.. Toh Ka fito fili kace ka gaji da rike mana yarinya ba dai kana wulkanta ta ba.. Dama wa ya isa da kai..kowa yana binka..kuma kafi son har ni ma kana juya ni kamar masa” ka cire iyayen ka daka ke ganin idan sun maka zai bika Kenan ni bani da darajar da zan sa ka zauna da wata ka zauna da ita lpya? Mohan meye na maka a duniya katsaneni ?gashi yau har yar marainiyan Allah ka sa’a gaba. Yace plesse stop it hjya Ni bana son kina fadan haka u know is not true. Ke fa kinsan ina daurewa kawai baki so ki fada ne. Meye kikace na rika mata wanda bana yi’ Har fa daki na nake bari bata zo.. Tace to sai me..ai matar ka ce ko dan yanzu bata da amfani wajen ka kake ganin takurawn ta.. Ni dai wllhy nasan matsayi na wajen ka… shiysa daga yau kasake min bazan jira ba wajen uban ka dakake darajwa nan zan kai bazan bari ka kashe yaarinya marainiya ba…marar tausayi kawai ta waysa masa harara.. auren nan kuma dole kayi xaman saa don baka isa ba.kai din banza ciki duk kashi? Idan kuma har ka tunxira ni zaka ga abunda zan yi maka .. Yayi shiru ya daure fuskan sosai kamar abun ya mugun damun sa amma ba hakan bane har wani sosai aransa… Amma ai tafi kowa sani yana kokarin akan banafsha..sai yace ki gama sabida zanje nayi bacci.. Hakan daya gada ma ya dada kular da ita haka ta zauna yana matse idon munafurci tana satan kallon sa.. .aransa ya tabe baki yace hjy mamah kunun barkwano..kana sha kana kuka amma idan yakai ciiki dole yayi maka magani.. Nasan duk zaki aikata abunda kika lissafa amma nasan magananin ki Tana ji tana gani yayi shiru ya tsaime ko dan rarrshin ta ko ya bada hakuri ma duk barazanar datayi masa akan auren haka yayi shiru ya mike ya nufi part dinsa. Da guntun masifa ta shiga ta same banafsha itama .. Kusan kalar borin data mata kenan akan tana wasa da alkwarin da suka kulla akantaa na zaman auren Har tayi kuka amma hjy bata daddara ba.. Duk dama yau ta bata hakuri sosai ta nuna mata zata yi mata biyayya ko da nan gaba mohan din cinye ta zaiyi.. A haka bacci ya dauke ta.. Ita dama Zuciyan ta cike yake da shrye shiryen zaman diris da shi..badai kawai bayason raini da rashin kunya bane ai zan dena masa..haka ta sa aranta tayi bacci. shikuwa anan kayan sa ya dan tarkata adan karamin trolley sai gadgets din sa… Ya riga yayi magana da iyayen sa sun fahince shi.. Yanzu haka saura nimrah. Sai da ya gama komai sannan ya dawo ya kwanta ya kira wayar ta. A rigima kowa yana jan qamshi..don duk iya kisisinan datake saka masa baiya kulawa sai ya sauya topic din Ko da ta tuhume sa rashin kira akai akai ya gaya mata projec ke saka sa agaba.. Gashi dama bata san ya dawo nan gidan su da zama ba a tunanin ta yana zaman sa gidan su shi kadai.. Tasan yaddaa ya tsani arainasa do hala ma yanzu basu magana kwata kwata da yariinyar..bata daddara ba kuwa sai da ta tambaye sa kwailar matar sa…da kamar zai amsa sai ya kaucar da magana da cewa yazo ta same sa a russia nan da sati guda yana missing din ta.. Duk irin wayannan kalaman idan yana fada sai taji ta a sama tsaban dadi…don ita har yau bata cire tsammanin mohan yasan sirrin su ba kawai pretending yake sai tana ganin kamar asirin bai wani kama shi ba tasan bai wani damu da ita ba..amma hakan take daurewa ta tsula tsiyar ta don duk bacin rai da zata sa shi bai taba daga hannu ya taba ta ba wani bin ma sai tayimasa mai cin rai..kuma tayi borin kunya kuma idan yazo kwakumar ta haka zai lallabata.. But is not enough har yanzu so take taga ta sauke amsa girman nan nashi..tana so idan yazo jikin ta ya zama weak baida mafita sai inda tayi da shi. But that has neva happen ko da na rana daya ne.. Idan yayi mata shiru ya barta tana shagaliin masifan ta toh tasna tarata yake kuma idan ya fashe bata jin dadi…but she loves him dearly duk wannan a prt of life din su ta dauke sa. Haka suka kare wayar akan zata zo ta same sa anan russia tayi masa kwana biyu… Tun 3na safe ya tashi ya dauro alwala yayi tahujjud cike da tauhidi da neman nasara akan abunda zai sa gaban sa daga yau din.. Karshe yayi zaman addua ma iyalin sa. Yana neman alkhairin dake cikin auren sa musamman wanda yake tsakanin sa da marainiyar Allah banafsha har ransa yasan bazai iya bata duk wani hakkin aure yanzu ba amma yana rokin Allah ya sa ya cire komai aransa ya bada matan sa hakkin su sabida darajar auren ba don yanayin da aka daura masa auren nasu ba… Haka ya gama ya mike ya shiga wanka.. Da asubahin fari ana neman karfe shida saura.. Banafsha na kitchen tana so ta dama ma hjy mamah kunun daka mai tsamiya.. …nan ya shigo ya same ta zaune kana dadauma tana lazimi.. Bai sa kayan sa ba tukun so simple tshirt na marks and spencer mai layin fari fari ya sa akan dark brown wando.. Kamar wani na daban ya zo kusan daf da ita ya zauna… Jikin ta ne ya bata ba lpya ba.. Tana ajiye charbin ta juyo ta kalle sa.. Yayi murmushi sai kanta ya dada daurewa …yace kin tashi lpya ko? Ta dai sa ido tana duban sa ya dan kamo hannun ta yace comn hjy ta,ni wllhy bana son kina yawan fada dani wata rana fa zamu rabu… Lokaci guda taji tayi sanyi tace yau kuma tanan zaka fara min.. Ya dada gyara zaman sa yace ah ah..jiya fa ke kikayi maganan ki nima yau sai ki bari nayi nawa.. Tayi shiru tana binsa da ido..cikin hikima da wayo ya fara kawo mata tadin project dinsa har da yadda ya samu yayi komai ko kafin ya gama ta riga ta dago cewa tafiyar sa zaiyi.. Gaba daya sai taji hankalin ta ya tashi.. Tace yaushe ka warke ciwon kafar da zaka laka makan ka tafiya karatu.. Yana shouru yayi tsuru tsuru gaban ta alladbce Yau ko borin bata iya ba bare masifa sabida sosai ya sauke kansa yana lallabata don ta fahimce shi.. Yace’bamu taba rabuwa ba kema kinsan haifa na kaeai sukayi amma jinin ki ne kawai ajiki na” A duk lokacin da kike so nayi miki ai zaki iya fada min ko” Bata so tayi masa hawayen gaskiya sabida taga shima danne nasa ya saba yi tun yana yaro.. Ta dan shagwabe yana rike da kafadun ta tace’ Kana gama wa zaka dawo gida ko?…ya gyada kai kamar karamin yaro..tayi shiru kamar ta sake tunowa tace toh matar kan kuma mani zaka sake bari ko me?. Ita yaushe zaka fada mata,ai hakkin ta ne ta san da wannan tafiyar ai ba komai ne zan na maka ba.. Yace kiyi hakuri ki taimaka min dai…kar ki damu zan gaya mata komai kafin na bar gidan nan i promise.. Tace ok,amma kana dawo zaka dauke abun ka kam.. Batare dayayi dogon tunani ba ya amsa da cewa eh..haka suka dinga alkwarin nasu kala kala har da na shirme bai damu ba god knws he loves her soo much….tanayi tana saka masa albarka..ko dan cikin ta bata maza son data keyi ma mohan ba..shiyasa ya dawo abokin gabar ta ako ina don idan da zata nuna son afili sosai tasan zata gurbata masa rayuwan sa. Banafshan tana shigowa ya mike tare da cewa zan je na shirya.. Ita kuwa Tana ajiye dan karamin silver tray din Tacee ina kwana… Ya amsa ba yabo ba fallasa ya tsaya kallo She looks very sexy in trouser yau wando da riga ne dai dai kugun ta an zana katoton elepahnt ta gaban sai dai daga gani Sa kasan baida nauyi all in light pink colour har da dan mayafin da ta rife kanta wanda shima pink din ema amma ya shiga dark duhun suman kanta kawai ake gani aciki … Hjy mamah tace me za akawo maka..ko zaka sha wannnan toh banafsha ki kaimasa daki.. Yace nnooo..bazan iya sha ba ya dan taba cikin sa ta wani harde rai yace to shikenan amma bayan zu ba idan nagama zan aiko sai ta kawo min.. Tace toh.. Itakam ko kulasa bata sake ba bayan sun gama shan nasu ta shiga tayi wanka ta shirya tsaff cikin uniform din ta.. Hjy mamah tace kar ki manta ki kai masa ..tace nannah ba cewa yayi zai aiko Ko rufe baki bayai ba sai ga aika akan taje ta same sa.. Turaren ta dan fetsa sama sama na humran ta ta kamo hanyar dauke da da royal jug din kunun nasa.. Ita bata taba ganin ya sha ba gani take idan takai ma zai iya koro ta da shi.. Tana biga sallama da daddan qamshin humrah ya soma tuamali..hakan ya sa ya juyo da kyau yana bin kofar da ido har ta shigo ciki.. Wani irin sunkuyar da kai tayi gaban ta na dan faduwa,gamshin turaren ta da nata sai ya hadu ya gamutsa yanayin atmosphere dakin..bazata iya dage ido sosai ba Cos He looks so dashing Complete set na black men suit ya saka na Calvin klein.. Hannun sa dauke da wata shakikiyar tai wang men skeleton watch.. Sai yai fresh kamar wanda duniyar gaba daya zai bari.. Tana ajiyeewa ta kasa zama tana so ta fita yace …banafsha” Chak ta dakata irin yau kuma in ka ajiye “ke” din tasan dai kafin ya kira ta hakan sai da dalilli.. Tayi ajiyan zuciya a hankali ta amsa da naam ta juyo ta samesa.. Zama yayi abakin gado yasha mamaki daya ga ta rusina a kasa agefen sa.. she’s really diffrnt now Ko duk tsorn ne..Yace ina abunda hjy ta baki kawo min nan.. Ba musu ta mike ta dauko tray din ta ta kawo gaban sa.. Baice komai ba ya tsaya kallon ta tana zubawa ko rabin cul din bata kai ba yace enough” Ta ajiye ta dauko ta mika masa idanin sa take kaucewa don sosai take jin fargaba aduk sanda suke inuwa daya.. Barin ma yanzi dakomai ya sauya gani take she owe him alots. Wanda hakan Ma damuwa yake kara mata aranta shes still feeeling tied Down har yanzu Sai da ya kai kurbi daya bakin sa sannan ya dago ya dube ta yace” Dauko min wancen ya mata nuno da envelope ba musu taje ta dawo.. Kasan makoshi yace good girl..ita dai bata ce komai ba Sai ya ajiye cup din wani madaidaicin envelope ne Ya mika mata yace idan kin tashi anan ki kaima hjy mamah…tace toh..yayi shoru Kamar bazai sake furta komai ba yace” zanyi tafiya mai dan tsayi…bazan dawo ba Da wuri ba ..idan akwai matsala ki gaya musu zasu fada min.. Tayi shoru daga bisani tace Allah ya kiyaye hanya..yace ok.. Maganan schl idan baki son wannan zan sa sauya miki…tace ah’ah Yace are you sure Ta gyada kai bata so ta kawo maganan Yace toh Ayi karatu lpya ,i have ur securities set….so please behave ban son rawar kan nan” kinsan hjy bazata ji dadi ba kika sake shiga irin wancan rigimar ko… Tace uhmm zan kiyaye.. Yace good! Toh dauke abun ku ki fita da shi.. Ta mike jiki ba kwari tattara tayi waje.. Sauke ajiyan zuciya yayi Ya jawo dan karamin troleyn sa ya fito gaba daya daga dakin ya sa mata security lock. Wani rin damuwa ke dawiniya da zuciyan ta amma ta kasa bari ya fito fili Tana ji suna sallam da hjy mamah ta noke a bathrum kamar fitsari ya kaita.. Har sai da taji ya rufe kofar sannan ta fito.. Kudi ya zare ya bada nusaiba itama tana daf da fita agidan har da masa kuka amma bai ko kula ta ba.. Yana tsaye sai gata ta fito kallo daya yayi mata ya dauke kansa..lokacin yana kokarin shiga back seat don jan sa za’ayi..tayi saurin karasowa Tana zuwa gaban sa tayi shiri abinda ke hannun ta yakare ma kallo.. Gora ne mai kyau cike da honey..amma sai yaga kamar idanun ta acike suke da Hawaye Yace yaya ne kam? Batace uffan ba ta mika masa tace hjy ce tace na kawo maka… Yace whats that? Ta dan shagwabe tace nima bansani ba yayi tsaki yace toh ki rike na baki…tace no no… Emmmm…bata so ta kira sunan sa sai tayi shiru Sai ya dan dake yace hey whats my name”?chak ta yanke nunfashin ta Ta dago ta sakalce masa fuska kamar wacce zata fashe masa da kukan shagwaba yace answer me..muryan sa yau kamar wani sauti na daban takejin sa acikin dodon kunnen ta. its make her skip a beat so weak haka take jin kanta idan yana mata magana ita kadai tasan daurewa take yi Ta dan sauke hawaye tana sharewa wasu suna tohowa.. Ya tabe baki yace aikin banza…duk ki gama sai kin fada min abunda na tambaye ki anan yau din Wani yace miki ki aure ni? Ko kunya ta kike ji arent you alwys hugging me..dagangan yayi maganan don ya sata budi baki ta amsa shi. Sai dai yau kam bata da gwarin gwiwa ita tun jiya data san babu laifin sa akan mutuwar iyayen ta ta karaya da komai..amma sai ta daure Tace ni bance in son auren ba.. yace ok amma shine kika yarda aka laka min ke ko?ba damuwa tin da kin nace sai ni din i have accept,Kallon sa tayi …ya wani lumshe ido so sexy ya sake bude wa I just hate pretence aduk lokacin da kike tare dai just act like my wife na yafe ki.. .. Forget abot evrything ..kinga nima ba so nake ba cos i have my wife… Ta mitsuka fuska wani irin sasanyar kuka ta fashe masa da shi ta tana turo baki.. Tace to ni ina ruwa na ai ai…sai ta kasa cewa komai da shike ysan bata kallon sa direct sai yayi murmushi yace ohon miki,ni dai nasan aure ba a dole ma mutum gashi ke kinje kinyi dani, nidai nima na taba yin shi. Idan da gaske baki son zama da ni gwara ma ki ce musu baki so.. don mata na ma kawai zata koya maki hankali…kuma ni? babu ruwa na.. Ta dada sake sautin kukan nata gwanin tausayi gwanin dariya… Yace toh zaki fada abunda na tambaye ki ko sai na cigaba ?cikin dan karamin shekshar kukan Tace toh me kace? Yace meye wannnan a hannun ki..ta dago tace honey ne fa.. Ai cewa tayi kana sha sabida ciwon kafar ka ya warke da wuri.. Yace ooh wai magani ne … Are you sure bake kika kawo min dan nasha na fara like miki ba.. Oya open it lets see… She neva tot he can be this playful…haushin maganganun nasa take ji amma haka kawai taji baiya affecting din ta.. Sai take ganin kamar ma gaskiya yake fada tund bata zabin da yawuce ta zauna da shi ai dole yace an lika masa ita..kuma tasan matar sa akwai masifa daga jin yadda suke mata tun wancan lokacin tasan akwai rikici Toh ni ya zanyi take tambayat kanta amma bata samu amsa ba Idanun ta duk sunyi ja daga kukan daya sata tayi yanzun amma sai ta dago ta share hawayen ta shiga bude murfin zuman tana gamawa tace heere na bude… Yyi maya kallon ok me kike jira taste it manah…” A sanyaye ta kai kan bakin ta yana sha da wani irin susuttccem kallo yake binta wanda ya sa ta kasa hadiyewa akan lokaci.. Kadan ne ya wuce dan karamin bakin nata saura sun mannu kadan agefe.. Yana kan bata piecing looks din Yace ok…to ruffe abunki ai dama na baki kyauta ko.. Ta dan girgiza kai sai ya matso kusa da ita daf kamar zai rungume ta.. Hijabin ya dada gyarawa zama tana dan satar kallon sa kamar zatayi exploding tsaban bugun zuciya.. Shima haka kawai yake jin y kasa controlin kansa in his own little way yasan zaiyi kewar fitinar ta.. Tallafo sukutaccen fuskan ta yayi da hannun sa duka biyu kamar wanda zaiyi mata kiss” Wani irin sweet husky and vibrating voice yasa yace i really love honey..kinga ciwo na bai warke ba Zamuyi kyautar dan wuta ko na hakura.. Tayi shiru sabida bazata iya bari yaji rawan da muryan ta yake yi ba.. Yace silence? I hate silence kan ta hankara sai ga sasaanyar lips dinsa a dai dai saitin shatin bakin ta inda sauran digon zuman sauka.. Wani irin damke arms din sa tayi batare da tasan tayi haka ba..ta rufe idanun ta A hankali ya shiga lashe wajen yana making wani irin moves da lips dinsa Teasing her da feeling din kisses din sa duk dama tasan bazai yi ba.. Shes alredy in heaven ta kara lumshe idanun ta wanda ke tafe hawayen sabon yanayin data tsinci kanta Yana gamawa ya bita da sassanyar kallo kamar baisan me yayi ba..yace ok now what my name.. Ta dan sake hawaye sai ya fauce zuman yace zan sake miki irin wancan..tayi saurin daga masa kafada alaman bata so.. Yace to say it.. Tayi masa shiru..yace ohhhhh wato har ma dadi kike ji ko? Sai ya jawo ta kusa da shi again ..cikin ido ya dube ta sannan ya sauke mata light peg a lips din ta yace and worst is coming… Cike da dauriya ta bude idanun ta tace ai zan fada…yace oya say it. Tayi shiru..ya sa arms din sa awaists din ta ya dago ta daf da shi kamar zasu goge fuskan juna da tako da ta so haka ya dasa mata cool grey eyes din aciikin nata.. Yace toh fada miin… Tace..yayyy..a.yayyah.. Yaya mohan ta runtse idanu kamar irin tafadi babban kalmar fbomb… Murmushi ne ya kufce masa bazata… Yace good duk dama banji sosai ba.. Bazata iya daure numfsahin sa dake watsowa akan fuskan ta ba don haka ta dan yi suppot da hannun ta akan kirjin sa kadan.. Ya bita da kallo ya tabe baki..yace no male friends Tace ai kafada min ranar yace ba irin wancan nake nufi ba irin wanda suka biyo ki ke ki bare ma mutane baki..me makike cewa min ma.. Tayi saurin cewa seniorre mohan” Ya dan fashe da dariya ya sake ta… Yanzun kam tasan dagan gan yake mata duk abunda yake yi yanzu….amma tasha mamaki sosai Kodan yasn bazata sake ganin sa bane ai taji hji mamah tace shekara biyu zaiyi achan. Ta dan zumburo baki Yace”senioree? Whats that ur one in town intelct dakike zagin mutane dashi ?ya tabe baki kamar irin zaki sani Kallom shi tayi Komin shi na yaudare na sai yau ta soma gane salon sa he’s a chronic heart controller sai ya sa kayi abu baka san ka aikata ba A shagwabe tace ni bana zagi..yace lie” What about that day in the dark me ma sunan yaren…tace spanish.. Yace huhhh? Dan anace miki dr senoritte shine nima zaki laka min wani yare…no i dont want ki bari matata ta tayi min haka.. Tayi saurin zumburoo baki ta dan juya kanta.. Bai kula ta ba ya juya ya ajiye zumar akan seat dinsa na baya.. Yace comn now kije a kaiki makatanta zakiyi latti..yanzu taga ya dawo da normal face dinsa.. Sai ta gyada kai tace yess.. Yace yes what? Ta makale wuya gwanin shawa tace yaya mohan.. Yayi murmushi yace not this one dayan..tace senoirre mohan.. Yace ok..meaning.. Ta daure tace sir,mohan. Baice uffan ba ya gyada kai yace ok .. Ya juya ya shiga motar kamar bai damu ba ya ja ya rufe .. ana juyawa da shi ya sa ido yana kallon ta har sai da ta lume sannnan ya dawo ya sauke ajiyan zuciya,.. Dakin hjy mamahn ta nufa tana jin wani iri aranta she’s missing him alredy.. she cant belive that its aching her.. it hurting,..wani zafi ne azuciyan ta wanda itama bata san na miye bane kar dai tace ta fasa zuwa makarantar me hjy ta damu. Haka ta daure fito falo ..Ta shigo ta same hjy tana zaune da damin kudi agefen ta da wasu card har guda biyu.. Da tayi tunanin kawai ta bata abubuwan ta amma tasan halin mohan sarai akwai dalilin daya sa bao mika mata dirct ba ya boye a envelope yace abata.. Tace har ya tafi ko? Ta gyada kai adan sanyaye tace kema sai ki sa himma yanzu zaki tafi kafin nan dauko min ruwan zuma na akan table.. Tace toh ta fita.. Waya ta dauka ta danna amsa kira yanagani amma bai dauka ba sai datayi sau uku Kamar basu ne daxu suke tarairayar juna ma ta shiga masa masifa.. Yace ina daf da airport jjy ki fadi abunda zaki gaya min.. Tace naga atm da credit cards ga kudi baka ce min komai ba Yace ehm irin ya manta nan ..yace dama atm din banafsha ne kuma naga bai dace na bata ahanunn a haka kawai ba shine na ce ta kawo miki..jiya nayi mata activating savings . duk scholl fees din ta da sauran abunda take so zan na saka mata kudi a wata sai tana cirewa.. Tace yayi..shikuma credi card da kudin fa yayi shiri don yasan zata iya cewa ya raina ma arzkin ta ko dan ya sace masa gwiwa Yace duk naku ne ai hjy mamah na”yarkin ai matata ce ko?..tace iyyeeeeh,irin marar kunyan nan Ya sauke wani irin amiable grin yace ke fa kika cewa na bar ki da aiki,so no complains now… duk abunda kuke so akwai…ki kula min da kanki ok? Tayi murmushin mai dauke da jin dadin abinda yayi tace saura kayi ta musu kiriniya duk agaban idaona zaka zo ka same ni.. Yayi dariya mai dan sautii..yace bye ya katse wayar sa.Tin kafin jirgin sa ya tashi yake waya da dr aliyu Da shike yau baya cikin mood din daure fuskan sai ya yi masa wayo yana tanbayar sa a ina ya koyi yaren spanish ai yaji su sunayi da banafshan ranan Dr Aliyun yasha mamakin tambayar amma da shike yasan mohan da wiya yayi tambaya a banza ko cikin wasa sai yace masa shima bai iya ba kawai bai wice few words din dai dayayi grabing wajen kallon football ba cos most of the big teams are from spain.. yace ok shikenan”kasan makoshii yace makansa i will find another way “sabida shi baiya kallon football a rayuwan sa kwata kwata. 1 Jirgin 9.45am ya daga da shi zuwa dubai daganan zai sake kafa hanyaar sa zuwa russia. Da yamma kowa ya dawo gidan but The house feels so empty witout him musamman wajen baby wife din sa Barin ma yanzu da take Kan fighting da tunanin sa musamman last moment din da sukayi sharing jiya. Yayi mata murmushi har sau biyu har da dariya shock of all his lips againts hers.. Amma hakan bai hanata rike maganan da yadafa mata nacewa an like masa ita ba.. tana cikin wannnan yanayin its arnnd 10.30 in the night sai ga hjy mamah da waya tana zuwa ta makel mata a kunne.. Tace yi magana mohan ne.. Sai yanzu ta tuno ashe dazun tace ya bayar da acct na kudin schll fees din ta da duk abunda take bukata gashi hjy ta nace lallai sai tayi masa godiya.. Dan shiru tayi daga bisani tace asalam Ina wuni…jin bai amsa ba tayi saurin cike gaisuwar da yaya mohan.. Kamar yana jira ta cika kuwa Yace lpya.. Ance zaki min magana oya quick go on..bana so a sake kirana aji busy mata ta tana jira”… ko da ba ace ba tasan fuskan sa daure yayi maganan..amma ba hakan bane Sai ta dan turo baki irin to ni ina ruwa na.. Tace dama ..uhmmm cewa zanyi nagode.. Sai da ya lumshe ido yana jiwo uneseness dake tafiya da nufashin ta Yace ok bazaki tambaye ni na isa lpya ba? Nace idan baki son auren nan fa gwara ki san yadda zakiyi da shi kafin na dawo ta dan shagwabe kamar zatayi kuka tace kayi hakuri..sai ta kasa cewa komai tana pouting lips dadi yaji aransa..tayi shiru kadan cahn tace ka isa lpya? Yace uhmm..ina shikenan kin gama? Ta gyada kai tare da cewa uhmmm itama.. Yace toh kashe wayar ki.. Ta dan dago tace ba waya ta bane zan kai mata ..yace ok bye.. Tayi shiru yace me nace tace “ok,bye…dama abunda yake jira tace masa kenan yay karamin murmushi Ya katse wayar sa.. Haka rayuwar ta cigaba yau dadi a zuciyan ta gobe babu Tana dada girma Wani abu daban take ji a zuciyar ta game da kanta.. Wani bin gani take kamar bazata iya soyayya da mohan ba soyayya ya riga ya wuce a rywar ta an yi ajalin so a duniyar ta tun anar da iyayen ta suka tafi But with the way she thinks about him musamman duk ranar da taji hjy mamah na hirar matar sa nimrah sai taji wani irin azuciyan ta sosai..ai taji sarai ana cewa tana zuwa wajen sa a inda yake tana masa hutu. Sometimes Haka zata wuni tana tuno sa a makrnta ma aikin kenan har su fazila sun soma gane wa amma sai tace musu ita auren ne ya takura ta sukuwa tausayin ta suke ji tunda tace musu tana da kishiya.. gashi tun ranar basu sake yin waya bare taji muryan sa yau kusan wata goma sha daya kenan da tafiyar sa Har su hjy mahnoor suka dawo nigeria. Dai dai gwargwado itama tana kulawa da ita amma har yau kallon karamar yarinya take mata.. Hjy mamah kuwa sam taki yarda ta raine ta a wannnan fannin Dadin karin abin ma da girman banafshan yake dada samun improvement daga gabobin jikin ta,tun daga kan hips inta take tasowa tana cika shekara sha biyar nono suka dada cikowa a kirjin ta duk dama ba manyan sosai bane amma bakaramin kara mata kwarjini sukayi ba… Haka take karatun ta yanzu haka tana neman shiga ss3 sune zasu zana waeec bana ita da su maryama din ta fazilah ma shirin aure take yi za hada ta da dan wani air mashal auren hadi a kasar waje bazata.. Su suke dan forcing din ta itama tana siyan wasu abubuwan na amfanin matan aure kamar tirare da simple hade haden mayakun kamshi great traditonal scents,altho basu kai kansu wajen neman maganin mata ba musamman na jin dadin jima’i sabida kunya da nauyin yariinta da ke damun su. Amma kafin kace wani abi banafsha ta tara abubuwan sosai a wadrob drawer ta..don duk abunda aka bada fazilah tayi using takan kawo ma banafshan itama da shike yanzu kusan layi daya suke kuma tamkar yan uwan juna haka suka dauke kansu yanzu. Maryam dake son auren ne Allah bai kawo ba sabida sosai take son yaya ameer din su fazila amma har yau bai nuna interest din sa ba tukun.. Bangaren mohan kuwa Aikin karatun sa kawai yake daga gidan idan aka cire nimrah to dad dinsa ne kawai yake ganin za ido da ido a saukake.. Hjy mahnoor da hju mamah ma sai dai suyi kuma baya son magana yayi nisa sai ya katse Abun sa.. To a Karshen shekaran da alhj Muamar ya dawo sai ya shigo da maganan auren anty rawiya don har ta samu miji anan abujan sannnan nan Da sati biyu zaayi bikin ta sai shirye shirye ake Hakan ya sa banafsha cikin farin ciki amma bai kai da akace mata hjyn birni wato step sister hjy kuma babban aminiyar mamah na niger itama zata dawo nigeria da zama ba.. Itace mahaifiyar su sadik ahmd da mufeeda da suka zo bikin ta.. Dama tana ta so ta samu yan uwa wanda zasu debe mata kewa da damuwar ta..don tzakanin ta da nusaiba har yau sai gyaran Allah. Sai gashi Allah ya sa komai ya gyaru at once ga anty rawiya gasu mufeeda.. A cahn cikin anguwan jaba gidan su da hjy mamah yake na asali wanda dan su ya gina musu .. Kuma har sun sa rana akan ana gama bikin secndry graduation din zu nusaiba da banafsha year din su hjy mamah zasu tare suma. Ba tan tama duka cahn zasu koma da zama nan kuma zai zama daga hjjy mahnoor sai nusaiba. Toh zaman banafshan ne basu da tabbas sabida auren dake kanta Kwance tashi abubuwan dayawa suka wakana lokaci ya shude” After 20 months da tafiyar sa ana saura just 4 months ya kammala ya dawo gida. Su banafsha an ciika 16years cas cas..sun dawo yan mata tarwal an kare secondry schol Ranar ba yadda hjy mamah batayi da mohan yayi magana da banafshan ba amma haka yaki firrr shi sam baya so.. Ita kuwa ta zuba ido taga ko hjy mahnoor zata barta tana rike waya tunda sun kammala schll amma haka taki firr. Musamman ma da nimrah ta sa ido tana lura da komai Sometimes idan tana zuga hjy mahnoor sai kace ita ta haife banafshah Har a bikin anty rawiya Wannan kam na gida ne bata nemi izinin sa ba ta shiga hidima akayi har aka gama. Ita bata san dacewa hjy mamah da nimrah basu wani shiri ba sai ranar sabida Tana ji tana mata masifan akan maganan haihuwa ita sam bata ga amfanin uban gayen data ke ci haka kawai ba aure na nemn shiga shekara hudu amma babu ko cas Ita ko nimrah dama daurewa take amma da abin ya ishe ta ta maida maganan cikin habaicci Cewar ta ai gashi an sama masa mata ita ta haifa masa mana. Hjy mama kowa ta rike abun aranta yaaan idan tayi amsa surutu shiru zaiyi mata, don haka ta sharing damuwar ta ma hajyn birni Ita ko banafsha Babu ruwan ta,kullum tana jikin nannahn ta ko inta samu sarari akai su gidan anty rawiya. Toh Da bikin fazila yazo ne ya dawo mata matsala.. Ranar da kyar ta iya budan baki tace tana so tayi magana da shi Gashi ana shirye shiryen gyaran gida da gagarumin waliman komawar gidan su hjyn birni da hjy mamah. Komin su na cahn yanzu kuma ana sa rai gobe za’a bude sabida schl su mufeeda basu samu zuwa ba ance sai ma da wata guda ko biyu idan suka samu hutu. Tsakanin hjy mamah da yar uwan ta Kusan halin su daya ne sai Ita hjyn birni ta wani fanni tafi hjy mamah sakalta yara.. Bisa munafurcin nimrah Hjy mahnoor ce ta yanke hukuncin banafsha ta zauna da ita amma Ko da taga banafshan na kukan rabuwa da hjy mamah bakaramin daga hankali tayo akan sai dai tafi da ita sabon gida ba Amma haka taki firrr tace sai mohan ya Bada izini Ita kuwa banafsha tasan kunya da nauyi ba barin ta zaiyi tana sakewa da hjjy mahmoor ba bare kuma aje ga nusaiba Toh da haushin haka ranar gaba daya ta sakalce ma hjy mamah, akan ta kira mata shi zata tanbayee sa dakan ta.. Ko da aka kira sa Gaban ta ne ke faduwa Bata yi magama da shi ba amma sai gashi hjy mahnoor ta katse hanzari da nata hidiman karshe ma ita ta gaya masa bukatun banafshan na hidiman auren kawarta da kuma dawosar ta gidan su hjy mamah.. Da shike mum din sa ta sa baki duka ya amince.. Hjyn birni ke tutsiyeshi akan lallai sai ya kawo kudin anko da sauran su wani irin dogon list suka hada masa wasu abubwan ma baitaba jin su .. Shidai yasan idan suka hadu waje guda damuwa ne awajen sa duk dama hjyn birni bata boye nata son datake masa ba kamar hjy mamah ba. Don arabu lpya duk ya turo musu abunda suka bukata da sunan kudin hidiman bikin.. Itakam banafshan bata damu ba tunda dai ya amince mata shikenan Aranar da ta dawo zaman gidan hjy birni ta raba kudi gashi uku. Ta bata isassau wanda zata yi har da gudumawa Sannan ta ce nata sauran zasu mata amfani da shi Sabida itama kwanan zata tare gidan miji.. Gaba daya idan aka fadi hakan sai taji ta shiga wani hali.. Ita fa gani take har yanzu kamar bazata iya zama da mohan ba. Ga matsalan matar sa nimrah abubuwan dayawa sun sa taji fargaba .. Har yau a Karaman yarinya suke kallon ta Kwanaki da suka hadu wajen bikin anty rawiya kamar zata shake ta haka take daka mata tsawa irin gata babba ita kuma yarinya Kuma ta lura hjy mahnoor bata cewa komai sai ma ta rika ce mata ai nimrah babban antyn ta dole tayi mata biyayya tunda ta girme ta sosai Gashi babu labarin nanny lalah babu labarim ta.. Ana saura wata uku dawowaar mohan su hjyn birni da hjyn mamah sungama hade duk wani shirin su na gyaran da suke da niyyar mata.. Sukam suna so aranar da ya dawo washe gari ayi komai akaita gidan ta.. Don haka suka fara sata agaba,da yi nan bar nan Idan ana bata abi taci kamar yarinya suke daukar ta wani nin dayawawa wani bn dan kadan Wasu ma sai daya a sati ake tsuma ta da shi.. Ita dai bata so amma bazata iya furta komai ba…duk ta rike damuwr ta sai ta maida kanta shiru shiru Ganin hakan ya sa anty rawiya itama tayi mata shiru tasn dole idan akayi nisa zata fada…sam bata so ta cika takura mata akan harkokin rayuwar ta duk dama yanzum ba wacce tafi zuwa gidan ta kamar ita. Ana cikin haka ya rage saura wata guda mohan ya dawo haka su mufeeda amma sun iso tun watan baya su dai suna kano ne basu iso abuja ba,ranar kwatsam sai ga maryam ta kawo mata ziyara tare da albishir cewa yaya ameer ya zama nata suma zasuyi tryinh luck din su idan aka dace suyi aure Ga fazila har ta samu schl acahn uk tare da mijin ta Taji farin ciki kam amma ko da maryam take nuna murna da farinciki ta tana zagewa akan cikan burin ta sai taji wani iri sosai arnta.. Tasan bazata taba samun irin wannan rayuwar ba so bayan tafiyar ta tayi tagumi cike da tunanin me zai zo mata nan gaba.. Haka kawai ta fashe da kuka.. Sai da tayi mai isar ta danna ta lura da anty rawiya dake bakin dooor tana kallon ta tuntuni Dama yau akayi zata kawo dulka da morocan bath din da ake hada na musamman wanda zasu fara mata.. Tsarin abubwan sun dada zafafa ita sam bata ma jin dadin jikin ta. Yanzu tana wanka za fara cewa tsugunna anan tashi akan wannann rufe kanki da wannan Wani bin da masifa suke karewa da su hjy sai ta ce musu qamshin yayi mata yawa kuma yana sata murar dare duk dama basu tana gani ba.. Amma basu daukar maganan ta serious su dai sun sa rai lallai banafsha zata je gidan mijin ta kuma ita zata share musu hawaye su samu jika. Koda anty rawiya ta Shigo Kasa ta koma ta dan rakube.. Tasan zata fahimce ta to meyasa bazata fada mata damuwar ta.. Hakan kuwa akayi cikin lallami tace banafsha Idan akwai abunda ke damun ki ko akeyi miki baki so ki gaya min Ni zan gaya ma abban mohan ai idan ya sa baki komai zaki ga anyi miki shi ko menene Ta yi shuri tana taro tears din ta ta rasa taya zata fara fitar da damuwar ta bayan sun tarun sun yi yawa yanzu Anty rawiya Su hjya mamah ne ko? Tayi saurin girgiza Kai alaman ah’a Tace to waye ne.. Ni ne?ko hjy mahnoor.. Tace ah’a fa anty.. Tace to meye ne damuwan ki? ko akan komawar ki gidan miji ke damun kanki.. Ta dan daure ta shere hawayen ta tace ah’a anty idan akace naje gidan sa ai zanje.. Ni dai kawai bana son shi ne kuma shima fa baso na yake yi ba..anty,wai dole ne sai shi zan aura a rayuwa ta? Ta da fashewa da kuka mai dan sauti Anty tayi shoru tana dan sassaita ta kadan kadan chan ta shiga mata nasiha.. Tace kiyi hakuri banafsha,nasan lamarinki akwai wahalan rikewa ammaa ai auren ki fa yanzu its 2years wa zai yarda ace za’a raba shi haka kaawai don baku son juna… ai kinga za’a ce baki ma zauna da shi ba bare agani… kinga shi aure bayin kowa ba ne sai Allah, kema baki san alherin dake ciki ba Idan kuma kina ganin damuwar ki da yawan kukan ki zai iya sa ki samu mafita ashe bazaki je ko ina ba.. Tace yanzu saura wata guda ne ya dawo ko? Tace eh..anty Tace toh Ni dai shawata shine cikin kwanakin nan Ki dage da yin addua Ina kinsan yadda ake istikahra… Ta dan gyada kai daga bisani tace bazan iya yi da kaina ba sai na gani.. Tace ok gobe zan aiko miki da littafin husnul muslim sai ki duba ciki Ki zauna ki koya da kyau a daren Ranar juma’a ko litinin sunfi falala sai ki tsaya ki mika bukatar ki wajen Allah Daga nan Sai kija bakin ki kiyi shiru..idan alheri ne auren ki da yay mohan zaki ga sakamako idan kuma ba mijin ki bane duk zaki ga aikin zabin Allah.. Ke dai kiyi kokari kiyi kinji? Sai yanzu taji dan relieve aranta tace insha Allahu zanyi hakan anty nagode.. Washe garin bayan anty rawiya tayi mata muhimman bayanin komai game da istikhara Zama tayi sosai ta bada hankali tana kokarin haddace adua’ar dake cikin littafin…+ Don haka acikin dare misalin karfe daya saura ta dauro alwala ta shirya tsaf tare da daura kyakywan niyya aranta da imanin cewa yau Matsalan ta yaxo karshe.. Ba wani shakku.. Cike da kamala da nitsuwa ta mika sakon ta wa ubangijin ta bata damu ba Cos tasan Is not necessary sai kaga result a mafarki kamar yadda yawanci ilahiran musalmai suka dauka Yakan xo ma wasu dai dai kun kam amma mafi akasari Baiya nunawa sai dai ya afku acikin hidimomin rayuwa. Haka rayuwan ta kasance mata tunda tayu shiru kake ji ba abunda taji ya sauya azuciyan ta game da fargaban xaman ta da mohan Sai dai yanzu babu damuwa sosai aranta,deep inside her tanajin sabon salon karfin gwiwa da kwarjini amma bata san akan miye ba. Zuciyar ta kamar ya rusuna yayi shiru ya kuma dakatar makansa daga wasu tunanin Ita kanta kokwanto take yadda takejin sauyin yanayi… Its feels like shes ready to face anything amma bata san ko hakan take ji ba Ita dai ta sa aranta Allah bazai taba barin ta ba,sannan bazata cire hope ba har sai mohan ya dawo taga ya dauke ta ya kaita gidan sa suna zaman aure. Tana da yaqinin cewa duk abunda xai faru nan gaba sakamakon soyayyar ubangijin ta ne Sai ta ajiye komai agefe duk abunda ake yi bata kawo musu Gashi an tsananta shirye shirye. Bata Taba tunanin su hjy mamah zasu dauki abun da tsauri kamar hakan ba Don Tamkar wance za’a sabon auren ta haka suke jibge kudi ana siyar abubuwan da zasu kaita da shi na zamani.. Har ya kasance Yau saura sati guda mohan ya iso Nigeria alhj muamar da babban aminin sa alhj yakubu sune suke shirin zuwa badge and honour partyn gamawar sa don suga achivements din da mohan din ya samo Bangaren hjy mahnoor kuwaa tunda su hjy suka kawo maganan tarewar banafshan dama take kaucewa amma yau da Dika aka taro anan gida akayi magana bata iya daurewa ba ta nuna rashin jin dadin ta sosai Hakan ya jawo hatsaniya tasakanin ta da tsoffi biyu… Cewar hjy mamah ai dama bata mata alkwarin cewa sai banafsha ta kai wani shekaru ba kafin ta xauna da mijin ta dama cahn sabida rashin lpya ne akayi jinkiri…tafiyar mohan ya dada karasawa Hjyn birni ma ta goya baya cewar ai yanzu kam ma yarinya takai tunda ta riga tayi 16 a gida.. Zaman gidan miji kamar ta kama Sosai hjy mahnoor tayi fushi aranfa,tunanin ta auren nan gaba dayan sa cin zarafin yarinya ce hadi da yadda nimrah take bata salon karfin gwiwa kullum akan abar ta tacika 18 amma ba yadda ta iya yanzu Yanzu dai an tsaya acewa mohan yana dawowa da kwana biyu banafsha zata tare da shi gidan sa. Da kyar alhj yayi sulhu tsakanin su aka samu daidaituwa… Don Sosai ran hjy mahnoor ya baci fiye da yadda ake zato ita sam gani take idan banafshan bata kai 18yrs ba bata mallake hankalin kanta ba .. And she hates to think that danta ne zai yi sha’anin aure da premature girl. Ita dai bawai ta gamsu bane ta amsa ne kawai don bayadda ta iya da mijin ta da iyayen sa Tsimewa tayi ta bar musu wajen Don ko sallama mai kyau bata yi musu ba Shikam alhj tabe baki kawai yayi a tsakiyan su.. Ranar A duk rigima da facts din da hjy mahnoor ta baje masa bai ce komai ba sai dai nasihan ta hakura ta yi abunda ya dace ma danta tasan kuma gaskiya yake fada idan ta sa pressure akan maganan auren mohan bazai ji dadi ba tunda ya riga Ya amince… Daurewa tayi ta shiga hidimar shiri bikin kamar yadda suke so. Gashi ba wani sakewa da ita banafsha take yi ba amma Kullum idan ta xo sai ta jawo maganan da zai sa banafshan taji a ranta cewa bata kai na aure ba. On the other hand kuma su anty rawiya ..hjy mamah da hjyn birni ba hakan suke rainon ta akai ba. nuna mata suke ta kai kuma dole ta zauna a dakin ta Duk dama ba damuwar ta bane auren amma Tafi daukar nasu Musamman data ga fazilah na zaman ta shiru gidan miji gwanin shawa’a so why not her… Tana zaune tayi tagumi Ajiyan zuciya tayi a kasale tace no no no..ni ta dabance ba kamar fazilah ba.. Im sure her husband loves her kuma sun fahimci juna ni kuma fa….sai tayi shiru ta sadda kai kasa tana taro hawayen ta da suka cike mata idanu.. 2minute silence tayi tana calming kanta sannnan ta mike ta shige bathrum ta dauro alwala. Bayan kwana biyu. _medical college russia rwsk_ . Cross wall building ta ciki dan karamin luxury apartment ne all white mai dauke da tambarin zanen damisa a dark lead plate dake jikin entry. Fararen curtain ne ke yawo dakansu cikin sanyin iska mai dadi da sa nitsuwa sunyi yale yale suna bayyana marvelous view na blue beach din dake shimfeda a resort din ta waje.. Remote din tv ne agefen sa yayi kwance da baya idanun sa a lunshe baya ko motsi Sanye yake da simple armless shirt bright yellow na dolce and gabana mai dauke da wandon sa iya gwiwa He’s 31-32yrs now.. bayan dada bayyanan sirrin kyaun sa da fuskan sa yayi har a jikin sa sai daya sake nuna sabon nitsuwa da sauyawar yanayi.. Yau burin sa ya cika he is the best in works and character An bashi girmamawan kwarewa na musamman tare da membership award na babban kungiyar likitoti dake india da germany in respect of world health org da united nations organisations. ajiyan ba zallan Alhj muamar ba hatta su dr aliyu da suka hallacin taro sun nuna masa kyakkwan jinjina da yabo.. They were all proud of him musamman iyayen na sa yana daya daga cikin abun daya sa shi gode ma Allah .. Duk dama ya dauka ko nasaran zai iya sha masa kai ne amma sai yake jin ba hakan ba aransa.. Burin sa yanzu bai wuce ya sanya albarkan karatun ta yadda zaa amfana ba.. A matsayin da yake yasan wasu masu kudin ma ba lallai su iya daukar sa jinya ba.. he’s a world class doc Samun Lokacin sa da aikin sa a fadin kasashen is worth a huge amount of money bare kuma aje ga dawainiyar jinya a zai dauka. Akan Hakan ya yanke hukunci kawo generic medicines a asibitin sa a as of major project din da zai kawo na cigaba Wanda zai tallafo marasa karfin da galihu.. A wannan tsarin duk wani kudin magani zai sauke farashin su suyi kasa sosai inda al’umma zasu fi amfana.. Sannan masu fama da cututtuka wanda samun saukin su yake da wuya da tsada kamar cancer da sickle cell shi kadai yasan tana di mai kyau dayake shirin yi musu idan ya dawo bakin asibitin sa. A ido bawani banbancin sauyawar yanayi amma a zuciyar sa Yanxu mohan ba kamar da yake ba Domin kuwa abubuwa dayawa na ban tausayi da taba xuciya sun faru da mata da yara kanana babu wanda bai gani ba Yanzu Gani yake rayuwar ma nawa take? imani ne ya shige ransa sosai Can cikin zuciyan sa All he wants now is a simple and peaceful life baya son yaga ya sa kansa aikata ba dai dai ba musamman ma wani na kasa da shi.. Nimrah tasha zuwa nan wajen sa , Sai dai har yau bata samu fuskan daga masa hankali ba Mamaki yake bata matuka yau shine gobe ba shi bane Har ta gaji ita dakanta ta dena zuwa wajen sa ta this week ta koma lagos da zama don next year ake shirin fara sabon election a nigeria lady bata zama. Gashi tunda taji anyi maganan banafsha xata tare da su bata sake dawowa abuja ba bare ta kira hjy mahnoor. Borin nata agaban mahaifiyar ta tayi,don tayi masifan tayi kuka har ta yi ma mohan barazanan bazata taba yarda banafsha ta xauna agidan ba aamma ba abunda ya sauya Haushin sabon dabiun shirun da yake mata take ji..musamman idan Tana masifa He only say’s what he had to say sannan bazai yi musu ko muhawwara da ita ba…she really hates that Bata hakura ba sai da lady xineta tayi mata fada akan ta kyale su Don lady tana sane da idan nimrah tana fushi bata iya hakura sai tayi kisan kai kashe banafsha kuma tamkar karewar rayuwar su ne Sai Tayi mata huduban cewa tunda hjy mahnoor tana da ja akan zancen gaba daya da ita kawai zasu yi amfani su daga musu hankali Tarasa meyasa har banafshan ta yadda zata dawo despite plan din su da sukayi akanta sai ta soma tunanin ko anga mijin ta kyakkwa ne son kowa ana so a like masa Who wudnt love mohan ?ita da ta kashe rai akansa ma Of cous wata ma zata iya mancewa da shi ya kshe iyayen ta bare ma karya ne Duk hakan na ci mata rai ko bacci bata iyayi Da jiji da kai da kuma karfin ikon mallakan cewa zata baza mugun ta da fadin rai ma banafsha tayi shiri Tayi tayi tagane ta wajen sa ko tsanan ne kawai a tsakanin su basu shiri. Amma inna Sai wani bori da yauqi take yi amma sam yaki daga kansa akan maganan. A daren ranar ya tattara komin sa ya shigo dubai hotel ya kama ya zauna akan washe gari zai bi jirgin nigeria ya dawo. Hjy mamah da hjyn birnin Dun dade da masa bayanin komai amma bai sa kansa tunanin matan sa ba tukun. Abu daya ke cinsa arai Don ko ya mance idan suka gama waya sai ta sake maimaita masa Ko yanzu ma abunda ta fada masa kenan “mohan ka tuna alkwarin mu,please let the girl be for now…kaji.? Kabari ta mallake hankalin kanta kafin ta zama matarki atlesat let her be 18..kayi min alkwari.. He noticed much more tension in her voice tasa abun a ranta sosai..gani yake kamar tana tausayin banafshan ne. Of cous aure is not a small issure,amma meyasa ta damu hakan shine bai sani ba Kawai sai ya amsa mata da emmm…amma bai cewa komai bayan hakan. Anan kuma angama shiri tsaf Su mufidah da su sadeek ma suna faman shirin kammala jaraabwan su su iso abuja.. Haushin banafsha kenan gashi bata da waya tasan baza su same ta anan ba sabida taji ance gobe mohan zai dawo kuma jibi zata tare gidan sa.. Hjyn birni kanta tana shan mamakin yadda suka saba lokaci guda duk dama sun girme ta kadan.. Yanzu mufida tana 2oolevel a univsty.. Amma da shike bata da girman kai hatta maryam idan tazo ma banafshan sai sun gaisa Washe gari da safe Angama komai an kintsa ko ina kowa na zumudin dawowar mohan itakam ma ciwon cikin period ya hanata sakat Da sassafen ranar nimrah ta dawo Abuja itama.. Wani masifa take ji da shi tasan dole za akawo banafsha but bata yi alkwarin saukin kai daga wajen ta. Kishin na damun ta fiye da yadda ake gani a kwayar idanun ta Sai take ganin in har kishi ya sa tayi kisa akan son mohan How can she eva cope wit a teenager a matsayin kishiyar ta . She wished it was aysha again.. Yarinyar da bata san komai ba.. so innocent and pure hearted kullum cikin murmushi..haka duk muguntan mugu bata judging dinsa da sharrin sa sai alherin sa. Amma hakan ta kashe ta amma banafsha? Gani take cin ubanta kawai yakamata tayi da kyau agidan ba sassauci tunda lady bazata amince ta kashe ta ba.. Tuno da irin wayannan maganganun yasa ta kasa samun kwnaciyar hankali.. wanka ta fada ta shirya kanta tsaf cikin gayu..tasha fleeky make ups dark brows and smoky eyes takalmin 5inches heel na gucci iri daya da kayan ta take takowa mostly tafison saka dogayen riguna na kanta masu fadi sabida girman nonuwar ta dake dan bata mata shape.. Dark red Loose braid ne akanta dogaye tayi kyau amma sallon ta wuce wajen kawar ta jamila don ta rage zafin da kirjin ta yake mata . Tasan dai Ita kadaice zata tula mata kasa sam bata ce mata batayi dai dai ba sabida gulma da hada waje duk abunda nimrah tayi ko ta fada dai dai ne.. Da chan ita ta soma bata shawaran ta kwace mohan daga wajen iyayen sa ta rike sa makanta ita kadai.. Amma tunda tayi masa yayi mummunan fushi ta sha bakar wahalan shwo kansa ta soma kama kanta akan tsoma bakin ta akan iyayen sa Amma yanzu she dont care idon ta arufe yake da guguwar kishi ji take ma ta tsane kowa agidan nasu.. Musamman su hajy mamah Tun da taje cahn saloon din suke hiran auren har kiran sa bata daga ba,tasan maybe ya dawo ne Kuma zai iya cewa suje gidan iyayen sa anan zai sauka. Ita sam tayi rantsuwa bazata shiga hidiman dawowar wata shegiyar yarinya gidan ta ba. Karshe Haka shima ya share ta ya isa gida Hjy mamah da hjy birni tuni suka hallora banafshan ne kawai agida bata iya motsawa. Duk dama baison maganan da yawan dariya amma yau din ta dabance domin kowa ya nuna masa gata da kewa yadda baiyi zato ba.. su nusaiba an kara girma Ana kan shirin fara registration a university of nigeria nssuka inda ta zaba karanta business administration.. Sabowar desiner box ya bata na watches da turare masu tsada aciki pink ….duk daga clothing brand and collection na kamfanin mawakiya nicki minaj…kamar an tsoma ta a aljanna haka taji She was soo hapy ita duk dama baya sake mata amma sosai take kaunar sa aranta. Da kyar suka barsa yayi bacci ,. Musamman su hjy mamah da ke jaddada masa cewa gobe yazo ya dauke matar sa ya kuma ga sabon gidan su.. Yasha albarka har ya gaji sai dai da safen ba wanda ya gansa don kuwa tunda ya shirya ya fice ya shiga gari harkokin gaban sa bai kO yi tunanin hutawa ba… Anan kuma hjy mamah sun shigo ma bata sani ba don tayi bacci Da safe ne anty rawiya ta biya gida itama don ta masa maraba amma baya nan sai ta taho gidan su hjy mamahn itama Duk wani nasiha da waazantarwa sunyi mata Angama tatttara komai by 10am har ansa profesionals sunje sun tsala ma banafshan dakin ta.. Wani irin gata su alhj sukayi mata tamkar wance akayi auren huce haushi da ita Gaba dayan kayan ta daga QATAR aka yo su.. Set din structures na huge wardrobe…princess sized mirror …kana shigowa kuma Akwai lallusaan small size chinese carpet mai touch din black da burgendy da Royal king-size bed da cushions dinsa mai dauke da lallausan puffy matress an cike ta da designs masu kyau na trow pillows da bead warmers Tsaf cikin Tsadadden linen da duvet mai taushi aka shinfedata all complete in pure burgendy sai kyalli ko ina yake.. Akwatunan ta 36 din nan tun na aure komai dai ya samu maxauna ras ras tubrkallah Nimrah bata nan yau ma don haka bata san lokacin da suka shigo sukayi aikin ba. By 6pm maryam ta koma gida sukayi bankwana gwanin tausayi fazilah ma dake uk tanace sosai akan sam zata zo suyi mata wunin tare amma hakan baiyuwa ba . Bayan isha’i tana fitowa daga wanka suka ci karo da hjyn birni Dan daure fuska tayi tana shagwabewa musamman dataga me ta shigo dashi ahannun ta.. Itakam ma Bata kula ta ajiye kaskon wutar akasa tace oya… Kiyi da jikin ki lokaci ya tafi… Tana turo bakin amma haka ta amsa da toh ta taho kusa kamar yadda ta saba tayi tsuguno daf da hayakin kan kaskon ya tirare ko ina towel ne ajikin ta babu komai bayan nan don haka Har wani zufe ke keto mata Ita sam wannann abun ya dade yana takura ta amm Ba yadda ta iya a Cewar su hjyn birni”mace zinariya ce sarauniya yar gwalisa ado da kwalliya sune tsaftar ta bata na zama kamar lami ba komin tsufan mace kwalliya da kwalisa yana fito da ita… Cewar hjy mamah kuwa komin arziki da ilimin mace idan bata cika mace a gadon namiji ba banza ce a rayuwa… Haka suke rudin ta da kalaman su wanda bata ma gane wasu ma’anan Of cous tasan bazasu fito fili suce ga abunda suke nufi ba amma ita ta fahince su sosai. Sun kashe kudi iya kudi wajen tsala ta tayi kyau tayi tsantsi duk jikin ta yayi smooth.. Olive green material mai kamar lace da designs kamar na manyan dark emirald stones riga da skirt fitted mai bazuwan da fadi sosai akasa. Hour glass shape din ta ne ya bata wani irin sirrin kyaun shape yanzu nonowar ta sun ciko fiye da da cahn girma ya dan nuna sosai ajikin ta but her face dosnt hide her age. Couple with light make up din da aka mata sai ya haska kyakyanwan flawless and impeccable caramel skin tone din ta her lips appears natural and shiny with nude picht lipgloss yadda tayi kyau sai kace ita kanwar Mowgli ce ko ita ta haife sa. Normal dauri akayi mata mayafin mai dan kauri aka yafa mata suna daki sau kuka take zuba musu suna rarashin ta.. Bata dassauta ba sai da antu rawiya ta tafi ya rage ita da su hjy mamahn ne agidan.. Ta daga hankali sosai haka suma amma sai suke dannewa a ransu sabida ta samu tayi shiru.. Sosai take jin zafin rabuwa da su ba irin borin da batayi musu ba Wani bin suyi hawaye wani bin suyi mata fada.. Don su kwantar mata da hannkli ba abunda basu ce ba, Cewar su idan mohan yayi mata wani abu bazasu barsa ba.. Don kuwa awajen sun baifi karfin duka ba.. Duk dama taga shirmen nasu amma sosai ta sa abubuwan da suke cewa aranta . A duniya idan ta cire familynn ta bata da kamar su su biyun Ko A littafin novel akace mata za asame irin wayannan mata masu riko da amana da gaskiya bazata yarda ba..1 Gurbi na musamman ta ajiye a zuciyan ta na kaunar su da girmamama su Yau tasan ko da iyayen ta na raye its obvious bazata samu irin wannnan kyakkwan tabbacin kulawar da suke bata ba. Suma hakan ne aransu don tuni suke dauke ta jinin su abun alfaharin su…. Gaba daya sun dauki so da burin duniya sun daura akanta.. Gani suke itace dai dai jikan su kuma shm maybe ita zata share musu hawayen su tunda zata ji magana su ba kamar nimrah ba.. Shikuwa mohan By 8.30pm ya bar site din mahaifin sa ya dawo dakin sa yana kimtswa dan kayan aikin sa ya hade gaba daya adan karamin trolley ya yi musu sallama ya kama hanyar gidan su hjy mamahn… Wani daddaar Qamshin 30 ocean lavender scent ke tashi ajikin sa Yasha yadin shadda mai laushi sosai cool sky blue colour da hula zanna bukar wanda ta mugun dacewa da aikin zaren kayan sa. Hannun sa manne yake da wacht din Daniell welingtong matte black yana murxa stairyn sa majestically.. fuskan sa Normal and calm yake tukin sa shiru ba abunda ke tashi sai sasaayanr muryan sheik abdl rasheed minshary ta suratul ibrahim cikin motar sa kiran bentley GT ba mai kaman benz din ba dukulalliyar jeep waccce take tafiya kamar bata taba kan hanyar.. Yana isa gidan bai yi wata wata ba yayi parking ya shigo.. A falon ya dakata yana kallon ko ina yana tabe baki a kasale Komai ya burge sa Tsarin gidan a yelwace take babu takuri.. Cikin hakan saiga mai aiki ta wulga tana gaishe sa amma bai amsaa ba yace tace musu ya iso. anan ne ma daya jingine kansa ya soma kawo tunanin yadda idanun sa zaiga banafshan.. Shi sam baya son tuna ta amma he cant deny it In his own little way he misees her alot. He’s just wondering how she will look now…yaji nace ta gama secondry schl few months ago Shin Ta dena shagwaba sakalaci da yawan kuka? Ko ko fitinan ta har hau bai kare ba..? Murmushin gefen baki yayi,ayayin da ya gyra azama jin motsin shigowar mutum inda yake. Su biyu ne suka dosu shi cikin shigar su na atampa super holland in matching colour alaman ankon su kenan… Gyara zama Yayi ya tabe baki yana duban su har suka iso suka zauna a dogin kujera ayayin da ya dan rusuna ya gaida su kamar ba shi ba.. Mamaki sosai yake bada hjy mamah cikin ranta ta kasa gane wani irin jinsi ne dan jikan nata ya fito… Ko alaman wasa ko murmushi babu tattare da fuskan sa shiyasa ma basu samu daman jan magana yayi tsayi da shi ba.. Sunyi masa nasiha tare da jan kunne akan matar nasa musamman ma banfshan da suje gargadi da kuma masa tunin cewa ita marainiyace gaba da baya.. Sarai yaji abunda suje fada amma sai Yayi shiru yana binsu da ido.. mamaki suke basa musamman hjya mamh dake faman kurin cewa baifi karfin duka awajen ta ba… Bayan kamar minti 30 sukayi sallama inda hjyn birni ta shiga dauko masa matar sa domin su tafi.. Gashi” kije ki same shi yana jiran ki..hjyn birni ta fada tana mika mata handbag dinta tana kuma gyara mata lullubi this time around fuskan ta kawai ta bar mata a bude inda colourn kayan ya dada haska alluarance din beautyn ta.. Kirjin ta ne ke bugu A shagwabe Tace hjy kunce zaku zo toh yaushe ne zaku xo din… Ta kure ta da ido gwanin tausayi Sai yanzu hjyn birnin ta lura da cikowar da idanun ta sukayi da hawaye… Duk rawa jikin take yi ammma kafin ta amsa hjy mamah ne ta shigo da akwatuna biyu babba da karami da wani.. Cike da dauriya da karfin hali tace ke zaki fara kenan ko? Ki zo ki wuce ku tafi babu inda zamuzo.. Tana fada tana mika ma mai aaiki kayan suna kaiwa waje inda motar mohan yake.. Tuni ta sake hawayen ta Ta dan sunkuyar da kai alaman bata ji dadi ba.. Hjyn birni tace ya zakice bazamu zo ba gashi duk kinsa ta kuka.. Yoh ai sai tayi ta kukan tunda na hana ta taki ji me kuma zamuzo mu mata.. Tana shiru ta shiga share hawayen ..dukan su su biyun suka taho gefe da ita…suka ce”ki kwantar da hankalin ki auta .. kin daiji abunda na fada miki ko?..idan kukan zakiyi kuma ba sake ganin mu zakiyi ba. Tace “toh nannah. Bazanyi kukan ba..Ta dada share hawayen ta gwanin tausayi “mu Je toh ki same shi..cike da so da kauna Hjyn birni ta shafa mata fuska gently ta riko ta suka fito tare.. Inda hjy mamah ta sulale akan gefen gado ta kasa binsu don har cikin ranta tana jin zafin rabuwar nasu.. Ruwa ya kai bakin sa amma sabon sauyin yanayin atmosphere dakin yasa ya dan sauke kasa kadan yana duban su.. Dama shikam ya fada shes a “maysun”beautiful face and body. Altho bai yi tunanin zata kara girma haka.. Ba abunda ya fado masa sai To meyasa mum take ganin kankantar ta aransa sai ya soma tunanin mata nawa yagani wanda suka kasa ta a gidajen miji? Har hjy ta xaunar da ita a kujeran dake kallon sa bai ce uffan ba. Tace toh gata nan kadaiji abun da muka fada maka . Batayi tsammani ba taji Yace naji hjya sai da safe kuma ko.. Murmushi tayi cike da mamaki ta gyada kai ta shiga ciki tana kukkuni.. Wani irin dukan uku uku kirjin ta yake qamshin mixed turaren ta na damun ta amma bai kai yadda take shako wanda dake jikin sa ba.. He’s faultless in looks and personality…maybe shiyasa yanzun kirjin ta ya tabbatar mata da cewa bazata iya dena jin tsoron sa ba. Shiru ne ya ratsaa wajen yana kare ma hallitar ta kallo da gafen ido yana yabawa.. Kafin ya hankara yaji sautin prety crack voice din ta mai cike da dauriya tace”ina wuni …sannu da dawowa ..tayi shiru..chan ta sauke boyayyen nunfashi a hankali ta furta”yah mohan.. Murmushi ne ya so ya kufce masa haka kawai amma ba halin sa bane sai ya dake ya dan kau da kansa… “yace Thanks..toh Ya kike…”sai yau kika san na dawo ko?bai bari Ta amsa ba yace ok get up lets go…yana wasa da wayar sa slowly kamar ba shi ya furta ba don ko motsawa baiyi ba Tayi shiru ta sunkuyar da kai feeling her Broken eye lashes idanun ta har suna mai mai..Ta naji yadda ko inan ta ya amsa jin sassanyar muryan dayasa ya furta hakan.. zatayi magana amma ta kasa sabida hawayen dake so ya fetso kuma bata san na miye bane Yana lura sai ya dago da kyau don su hade ido..hakan na faruwa kuwa ta sake hawayen suka gangaro zirrr Yayi karamar smirking irin”Wow…anfara sana’a ..i ques crying is her hoby now.. A zuciyan sa ya firta ya na dada kure ta da wani irin piercing looks ita ma ba abunda take sai bulbulo da hawayen.. Ya tabe baki haka kawai don yaji dadi aransa.. Yace me akayi miki kike kuka ko kin raina ne ni zaki min? Ta dan girgiza kai.. Sai ya matso kusa da ita kadan gently yace uhmm toh Meyasa baki zo kin gaishe ni jiya ba? Tace yaya.. ai bani da lpya ne.. Kamar zai tambaye ta meke damun ta sai yayi shiru yace “lie” Kuna shirin aure ko? So u really wanna come with me?Kin yarda kina so na kenan.. Zaki zauna da ni da matata? Lokaci guda ta yanke hawayen Tayi shiru tare da bata ranta Ya dada sake sirrin murmushi yace i hate silence.. Abun na cin mata rai wato shi baya ko sauyawa..it feels like yadda suka rabu haka ya yadawo mata. cikin kalar shagwaban da bata san tayi ba tace ni bance ina so ai…ai…bani da lpya ne Ta dan murkuda baki kasa kasa. “ok ciwon ke saki min kuka..?inche ni na saka miki ciwon? Ta dan girgiiza kai..yayi murmushi adan bayyane yace ok tashi muje.. Atleast 2years is enouhg for you to make ur decisions dama na fada miki ya mike ..ya tattara wayar sa zuwa aljihu ayangace yace”idan kin gama sai ki fito ko? Ni zan kai inda kika zaba makanki zama. Ta dada sake hawayen ya sauko mata yana fita ta mike tana duban bakin dakin su hjy ko ina shiru sai taji ta dada karaya a sukwane ta zare jiki ta biyo bayan sa.. Wanda ya shirya kayan ta a booth din shi ya bude mata kofar mota ta zauna.. Baice ufffan ba haka yayi driving dinsu har har anguwan dake only 25minutes ya raba su da nan . Simple mansion mai kyau 2 storey building amma yadda aka tsara super structures din shi ya hadu sosai. Babu abunda bata gani ba..cars ..pools …garages points kaka kala masu fauke hankali Lokacin ana neman karfe 9.30pm Yana tafe tana boyo sa sai dai yayi mata jisa kadan sakamakon kalle kallen da ta ke danyi.. Ita dai tanajin labarin gidan sa amma bata taba zuwa nan din ba sai yau Suna shawa step dai dai corridor ya tsaya ya hude wata kofar yana kallon ta tana tahowa ” This is your room ya furta …tana shiga Ya sake mata kofar yayi gaba.. Kayan ta da aka shigo da shi ne kawai anan tsakiyar dakin Ba abunda baiyi mata kyau ba she felt so blessed that dan damuwar da ta shigo da shi aranta duka suka dan washe.. But still waje ta samu ta zauna akan couch ta tare da nade kafafun ta .. rungume kanta tayi ta lunshe ido ta sauke wani irin ajiyan zuciya.. Me zai faru dani? Ya zama na zai kasance agidan nan…?wani in nanauyan yanayi ke so ya fizgeta amma Sai ta yi saurin kaucewa .. Lets pray first..ta furta Ta mike tare da jawo kayan da aka shigo da su yanzun Kananan kayan ta ne da sauran wanda su hjy mamah suka mata sabbi masu shegen tsada cewar su akwatin yar gata.. Sai dan karamin ciki wanda anty rawiya ta bata ne dama shine bata bude taga meye aciki ba. Don haka ta yaye mayafin ta zauna ta jawo sa gaban ta ta zuge zip din.. Daga chan bangeren hagu sama kadan da inda yake gangarowa da view din step din dakin banafsha ..nimrah ce a ciki sanye da riga da skirt na atamfa ta chahhko daurin dankwali gaba tana famar jeka ka dawo…. Dazu da ta shigo ta shiga sarai ta ga dakin banafshan kirjin ta ne ke ci da wuta anya zata iya jurewa ta bar wata ta shaki numfashi a matsayin matar mohan bayan ita ‘wato mutanen nan da gaske sukeyi ” sai taji komai ya tsaya mata arai “huci take tana tuno abubuwan da suka tattauna dazu da su jamila”tace Yes…dole na dauki wannan salon basu isa su zauna lpya ba Tayi wuf ta bude kofar dakin ta ta fito Ita ko banafsha ta shagala tana famar duban abubuwan dake ciki don ta sha mamaki Turare biyun dake ciki kawai ta iya ganewa duk sauran kayan a package suke Tunani take ko ta bude ko karta bude sai ta dauki turaren kawai tana dubawa. Labe da kofa nimrah har ta turo ta shigo bata sani ba yatsine take tana kallon ta tana maganaganun xuci sosai take ji kamar ta kama ta ta shake mata wiya ta mutu.. Ganin banafshan bata hankara ba Dan gyara tsayuwa tayi zata fara azalzalan ta da masifa sai charaf idanun ta suka sauka akan gwalaben turaren dake hannun ta men sexual arousing perfumes Wani irin shocking ne ya debata tayi wani irin firgitaccen nunfashi daya fargan da banafshan Suka hade ido a dan tsorace ta mike tsaye… ita kuma tuni ta tunziira ta iso ta fauce kwalaben turaren ta shiga karantawa da dan karfi.” The scent of doughnut and black licorise? Ta dago a haukace ta dube banafshan?Tace lily of the valley… Tayi mata kallon sama da kasa in total disguist irin yar karama dake? Huhhhn? ta sakewani wawan gurnani tayi watsi da su akan kujera ” baya banafsha ta ja ta kasa cewa komai amma ina sai tayi saurin jawo ta da karfi..tace toh karuwa Allah ya tono asirin ki ..zo nan ki yi waje”Allah ya tuno asirin ko yar iska karuwa.. Watsaistiya kaeai Nan banafshan Tayi saurin kufce hannun ta tana shirin calming tsoro dake cin ta amma ko hawaye bata ji shaukin saukewa ba Nimrahn ne ta dada kamo tace Ki fice min agidana nan ba gidan karuwai bane kije cahn kiyi isknci..ta hankoda ta bakin kofa da karfi..ta zaro mata furios an angry face din ta.. Tace bari kiji wllhy i wll neva allow you in herre.. gidan matsiya tan iyaye ki zaki koma su nema maki admission abayan gari.. Anan kuka ya subuce mata marar sauti ko uffan batace ba don sosai tsoro yake damun ta. Nimrah kuwa kayan ta hado baki daya tanayi tana masifa,abu daya ne banafshan bata gane ba its seems like duk turaren yafi daga ma nimrah hankali Wani iriin jefa tayi mata da akwatunan Sannan ta dauko dan karamin shima ta wurga mata Tuni ya sauko daga kan qado yana daukowa cikin sauri don tun yana sauyya kaya yake jin sautin hayaniyar Ita dai banafshan shuru tayi tana hawaye tana jin yadda nimrah ke azalzala mata masifa tana hankade ta… Ita bata ga amfanin sa ba ma don awajen ta babu amafanin kishi tsakanin su Yana zuwa kuwa tana fincikota tace bazaki fice ba ko nan gidan uban ki ne? Inda ta rike ya mata zafi sai tayi dan kara tare da kwace hannun ta da karfi tace ni ki kyale ni..i hate this pls leave me alone ki kyalee ni Tace In kyale kii ki kawo kin karuwan ci da badala gidana?… Hannu ta daura zata sake cahkumo ta tayi taurin kai ta fixge jikin ta..ta sauke mata harata da tsaki Wanda ya dada hatsala nimrah har ta daga hannu zata sharara mata mari Mohan ne ya shiga tsakani da wuri..ko ajikin ta don gaba daya idanun ta sun rife.. Yace meye hakan whats all this nimrah?me kukeyi anan ya dubi kayan dake waje anan. Itako banafshan Gefe ta dan zame tana kallon yadda nimrah take haukar cewa sai dai yace ta bar mata gida.. Anata yarintar ta so ace ya tsawatar ma nimrah fada ko ya mata wani abu tunda tasan duk wanda ya xo wajen yasan ita aka ciwa mutunci” Sai taga baice komai Ba hasali ma ko kallon ta baiyi ba Ya jawo hannun matar sa suka haura sama suka barta anan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *