AL-AMARIN ZUCI CHAPTER 3

AL-AMARIN ZUCI





CHAPTER 3









Ana gobe za a basu hutu ne Sagir ya dawo gida da albishir wa Aneesa. “Ki shirya zamuyi tafiya, wani aiki ya taso min a kasar Turkey, tunda kunyi hutu ai inaga ba amfanin ki zauna ko?”
Mamaki ne ya hanata cewa komai, wai yau ita Uwanin Inna ce zata kasar waje? Kasar wajen ma tare da Sagir da bayi da lokacin komai?


“Baki ce komai ba, ko bazaki je ba?”


Aneesa ta shiga rudani ta rasa me zata cewa Sagir “A’a ba haka bane, kawai dai…”

                              

“Kawai dai baza ki iya bin umurnin mijinki ba?”

                              

Ita tunaninta ya shallake nan ya tafi wata duniya daban da take matukar tsoro, tabbas idan wannan tsoro ya karasa shigarta ba tantama ta san zata samu babbar matsala. 

                              

“Zan iya, kuma a shirye nake”

                              

“Gobe bayan kin dawo makaranta zamuje a miki intabiyu na visa, tunda na karbi fasfo (passport) dinki wurin Daddy.”

                              

To kawai ta bishi da shi, ita dai ba daga nan take ba. 

                              

Bayan komai ya kammala ne cikin sati biyu suka hada jakkunan su ya kaita tayi wa Daddy sallama, sannan sukayi wa su Hajiya ma sallama. 

                              

Dawowarsu gida ne tace “Uncle Sagir, sai dai su Inna basu san da tafiyar tamu ba”

                              

Ya dubeta da kyau sannan yace “Ki kirasu a waya mana kuyi sallama, muna dawowa sai na kaiki in sha Allah”

                              

Ranta ba haka ya so ba, amma ba yanda ta iya ta amince ganin ba walwala a tare da ita yace “ko kin fi so ki basu labarin Istanbul a waya? Kinga idan kinje sai ki nuna musu har hotunan ki a can”

                              

Nan dadi ya kamata, ta masa godiya. Tana cikin karasa shirin akwatintane na trolley ya shigo dakin nata, yanzu ta rage jin tsoro idan ta ji shigowarshi don haka da wuri ta tambaya ko yana son wani abu ne?

                              

“A’a, ci gaba da shirin ki.” 

                              

kasancewr kwana biyar yace zasuyi yasa ta dauki kaya kala shida saboda sha’anin tafiya, da kayan bacci kala uku sai kayan ciki da ta diba, comb da brush da dan abun da ba a rasa ba”

                              

“Ki dau kaya masu nauyi don wannan lokacin a wurin su ana dan taba sanyi” Yana kallon yanda take nade komai take jera shi kaman wata mai aikin kirkire (artist).

                              

Baya gajiya da kallonta, duk da tsoronsa na sake barin zuciyarsa ta wahaltu yana ganin ya fara rasa ragamar yin hakan dangane da Aneesa shin kuwa zata iya samun wuri ta zauna? Sai yake jin tamkar ya gama wancan jinyar sai yana samun wani karfin zuciya da nishadi  a tare da Aneesa. Fatan shi daya Allah ya sa kar ya sake kuskure.

                                              

                        

Malam Hassan ne ya kaisu filin jirgi, har suka shiga jirgi Uncle Sagir ne ke rike da akwatinta ya bar mata ‘yar jakar hannun da take rike da ita. A hankali ta ke kula da duk inda suka tsaya me akeyi a wurin, don wannan ne karo na farko da zata shiga jirgi koma da tazo filin jirgi. Maimakon taga suna shiga inda mutane suke duruwa, sai taga sun haura ta sama inda daddaikun mutane ke shiga wurin. Nan Aneesa taga wata duniya a cikin jirgi. Tana kankame da jakar hannunta sai waige-waige takeyi cikin dabara tana kare wa komai kallo, kaman daga sama taji uncle Sagir yace mata . “Kinyi shiru da yawa me kike tunani?”

Sunkuyawa tayi cikin jin kunya “babu, kawai…”

“Kar kiji tsoro ba komai, ga wannan idan jirgin zai tashi ki tauna ba abunda zakiji” ya mika mata buttermint a hannunta, garin yin hakan hannunshi ya taba cikin tafin hannunta mai laushi. Nan take taji tamkar wacce akayiwa shokin. Sagir kuwa yana lura da canjin da ya gani a tare da ita, ya yi murmushi ya mayar da hannun shi ya zauna, har aka fara sanarwar daura damara. Ganin kar ya kara matsawa kusa a kuma ta dazu sai yace “ki duba” ya gwada mata yanda zatayi da nashi damarar kujerar. Da aka zo tashi ne ta damki kujerarta ta tauna mintin bakinta, amma duk da haka sai da taji a cikin ta. 

Filin jirgin Murtala Muhammed dake Legas suka fara zuwa inda zasu shiga jirgin da zai wuce kai tsaye dasu zuwa Istanbul, a wannan filin jirgin kam taga sun shiga bangaren da yafi girma fiye da wanda suka baro a Abuja, Sagir ya mata bayani ta wannan banagaren ake jigila tsakanin kasashe (international) wanda suka shiga kuwa a can Abuja na tsakanin garurwan gida ne Nijeriya (local flights). Sun shiga jirgin Turkish airlines inda zai dauke su ba tsayawa har babban birnin Istanbul.

Aneesa dai ba abun da ya fi damunta irin yanda kyawawan mata masu sintiri cikin jirgin nan suke ta kai kawo a kansu, a zuba wancan a kawo wannan, tana jin bacci amma bata son ta dauke idonta kan Sagir, don taga har wani murmushi yake musu tukun musamman wata da ta faye zuwa ta gurinsu, ta tambaya ko me Uncle Sagir yake so shi kuma ya juyo yace “Aneesa, a kawo miki tea?”

A hankali ta girgiza kanta, don bata son ta faye dura ruwa a cikinta, gudun kar taji fitsari bata san yaya zatayi ba, tunda bazata iya ce masa tana jin fitsari ba don haka ta kame bakinta. 

Duk maitarta na ganin kartayi bacci sai da ta runtsa saboda jiya bata samu isasshen bacci ba. 

A hankali taji muryar da tayi sanarwa dazu tana ce musu sun kusa iso (Istanbul Ataturk Aiport), a hankali ta bude idanunta taga kanta da rabin kafadanta gaba daya a jikin uncle Sagir yake, da sauri ta nemi dagawa amma sai ta samu ya mata kawanya da hannayensa karfafa. Ganin ta motsa ne yasa a hankali ya cire hannunsa daga bayanta suka hada ido, ya gyara zama ita kuwa ta gyara mayafinta. 

“kayi hakuri, nayi bacci ne ban san…”

Lumshe idanunsa yayi yace “ci gaba da baccinki saura minti ashirin a isa.” nan ta duba gefenta window ne taga abun mamaki gari kaman a mafarki ko ina wuta ne dau a kasansu. “a’a zan yi kallo”

Wajen awowinsu shida a jirgi nan take mutumin nan ya sake sanarwa akan sun iso masaukinsu, zasu fara sauka kowa ya daura damararsa. Ai duk da damarar da jirgi ya sunkumesu yayi kasa dasu Aneesa ba shiri ta cafko hannun Sagir, idanu rufe har saida suka taba kasa aka tsaya sannan ta kula da irin wawan rikon da tayi masa, da Sauri ta sake shi. Ya dubeta yace “Aneesa mai tsoron jirgi” nan da nan ta rufe fuskarta ai yau kam ta saya wa kanta abun zolaya.

Kasancewar ba su da wani kaya sosai, sun sauka da kayayyakinsu basu dade ba Sagir yayi waya, nan take suna fitowa suka samu motar otel tana jiran ta daukesu, kasancewar ya bukaci hakan. Cikin minti arba’in sun isa masaukin su, Aneesa kuwa kallo takeyi tun daga airport har suka shiga mota zuwa isarsu masaukinsu inda taga an rubuta Hilton Istanbul, sannan ta sararawa kallon titi. Da ikon Allah, wani shudin kati (blue card) kawai taga ya mika musu ba tare da ya biya kudi ba, ya bada wani shaida na takarda  da (password), suna shigarwa taji sunce “sannu da zuwa Mr. Daggash muna maraba da kai a otel din mu muna kuma maka fatan zaman jin dadi.” Nan da nan taga an hau hidimarsu ana karramasu, yanzu a wannan babbar kasar ma Sagir wani babba ne? 

                

                        

Nan dai taga wani mutumi mai sanye da inifom yazo ya kwashi jakkunan su. Aneesa dai duk inda Sagir ya jefa kafa ya daga nan take saka nata, kyaun garin ya wuce tunaninta kaf. otel din ma maza da mata sai kai komo sukeyi, sai da suka shiga kororon (corridor) da zai dangana su da dakin da aka basu ne tukun ta ga jama’a sun ragu. 

“Me kikace Aneesa? Ko dai da na barki a Abuja?” Sagir ya fada cikin zolaya. Da ta gane wasa yakeyi sai tayi murmushi, don ta gaji baza ta iya dariyar ma mai karfi ba, dadin dadawa tana jira taga yau yanda za a kwashe, don dai tun a falon da suka baro a can kasa (reception), ta kula da makullin kati na daki guda a ka bashi amma tana zaton ko zai kaita ne ya koma ya karbi nashi don haka sai bata damu ba, ganin mutumin nan da ya kwaso musu kaya ya ajiye duka jakukkunan su a dakin sai ta fara tsinkewa da al’amarin “yau akeyin ta yaya zan fara kwana a daki daya da uncle Sagir?” 

Sagir ya kunna mata ruwa yace “ki shiga ciki a toilet akwai ruwa ki watsa kiyi alwala kafin nan zan sauka na karbo wasu lambobi a kasa”

Ya fita ne saboda ya san bazata sake ba idan yana dakin. Sagir na fita ta karewa dakin kallo an kawata shi iya kawatawa gadone lafiyayye a bangare guda yayinda aka ajiye kujeru biyu kusa da wani makeken windon da ya bude zuwa waje, can ma wani gurin shakatawar ne. Bayan ta gama kallon dakin ne ta shiga bandakin tayi wanka tayi brush sannan tayi alwala, nan ne taji dadin jikinta, tana fitowa mai kawai ta shafa ta burma kayan baccinta ta fesa turare sannan ta maka hijabi, sai dai bata san ina ne alqiblar ba don haka ta samu bakin gado ta zauna tana jiran dawowar Uncle Sagir. 

Can sai gashi ya shigo, ganinta da yayi a zaune yace “sorry, na dade ko? ga alqibla nan” ya nuna mata hade da bude jakarsa ya fito mata da ‘yar sallayar da sai da ya ware ta sannan taga girmanta. sai da ta tada sallah sannan ya shiga. Ta biya sallolinta duka kasaru sai magriba ne ta yi shi cikakke. Tana sallame isha ne Sagir ya fito daga bandakin, kallo daya ta masa ta sunkuyar da kai saboda yanayin da ta ganshi da towel a jikinsa bata sake motsi ba sai da taji yace ta bashi sallayar.

Yau ita kam nata ya sameta a garin mutane, ba irin tunanin da batayi ba har ta gwammace tayi zamanta a Abuja da ta san haka masaukin su zai kasance. Yana idarwa aka buga kofar su, Aneesa taga ya mike ya tafi bakin kofar ganin wannan jallabiyar a jikinsa taga ya yi kyau. Sai kuma tace “ko wa ya san muna nan daga shigowar mu har yayi bako?” bata ida tunaninta ba sai taga ashe Sagir abinci yasa aka shigo musu dashi. Yace idan ta idar ta zo su ci abinci.

“Meeting dina gobe da jibi ne idan Allah ya kaimu, amma idan kina so zan wakilta miki wanda zasu raka ki ganin gari, a cikin hotel din nan ne zamuyi meeting din a dakin taron su, tare da wasu masu zane, (architects)”

Ita wa ta sani a garin nan da zai hadata da su? Sannan yaushe ta iya yaren su? Da wannan tunanin ne tace  “a’a ba komai zan zauna kawai idan ka gama taron sai mu fita tare.” 

“sarkin tsoro kawai” ya fada yana kallon abincinsa.

Aneesa tace “yaya akayi mutumin falon kasan nan ya san sunan ka bayan banji ka fada masa ba?”

Sagir yayi murmushi “Baki ga na mika masa wani kati ba?”

“eh,”

“Sunan shi Hilton hhonors, tun daga Abuja na biya komai, yanda ba zan yi tafiya da kudi mai yawa a hannuna ba, su kuma can suka turo musu sunana, da randa zan iso da kwanakin da zanyi da sauran abubuwa.”

“hmm shi yasa naga mutumin yana ta murna da zuwanka wato ya san kai babban bakon su ne kenan”‘

Ta bashi dariya yace “ni ba kowa bane, ko ke idan kina da wannan katin zasu kula dake sosai, musamman idan kina yawan sauka a otel din nasu”

Aneesa ta kama baki sannan tace “Tab, wane ni Uwanin Inna”

Sagir yayi dariyar da ya dade bai yi ba “wane ke Uwanin Inna? to ai Aneesan Sagir kam zata iya ko?”

                

                        

Yana fadan wannan kalmar dukkan su sukayi shiru, Aneesa na mamakin matsayin da Sagir ya bata a zuciyarsa yayin da shi kuma yana mamakin kansa da ya furta wannan kalami, amma ance magana zarar bunu. Don haka ba yanda za ayi ya mayar, jin dakin yayi shiru da yawa, yasa ya mike ya daura farantan a kan tebur din turo kwanuka ya ajiye wa room service a bakin kofa.

Aneesa kam yanda ya tashi a haka ya barta ta gagara motsa koda dan yatsa. “idan kin kammala zaki iya hawa kan gado ki kwanta ni zan kwanta nan kan kujera.”

Aneesa ta dubi kujerar ta dubi tsawon Sagir tasan ko idan ya kwana a kai da ciwon jiki zai tashi gashi suna da taro gobe, don haka tace “Ba zaka takura ba? ga nan gado a dakin?”

Dubanta yayi cikin shakku amma da ya ga bata damu ba sai ya rage wutan ya shiga kurkure baki ya dawo ya samu tana kwance a kasa ta sa pillow daya, har yanzu dai da wannan hijabin sallar tata.

“Ban gane kin kwanta a kasa ba?”

Aneesa ta hadiyi wani abu don tsoro sannan tace “kai baka san a kasa nafi yin bacci ba? duk randa na kwanta kan gado sai naji jikina yana min ciwo”

Sagir ya gane manufarta don ya saba ganinta tana kwana kan gado, jin haka sai bai ce mata komai ba, ya hau kan gado ya kashe fitilar dakin. “Amma kin san ko matan limamai ba su bacci da khimar ko?”

Ya bata dariya amma, tana tunanin yanda zata cire ta kwanta da rigar baccin jikinta kawai, da yaga bata motsa ba yasa yayi shiru ya barta. Aneesa tana jin yayi shiru ta zaci yayi bacci ne, ta mike ta cire lufayyar ta dauki abun rufuwa daya ta lullube jikinta, sannan tayi addu’ar bacci. 

Lumshe idanunsa yayi yana murmushi, shi zai ga karshen wannan kulafanci da akeyi.

Tsabar gajiya, bata ji tashin Sagir ba sai da ya idar da sallah ya tasheta. Zabura tayi “har Safiya tayi?”

“Eh, kin san harda canjin lokaci zai sa lissafin lokacin ya koma baya”

Mikewa tayi ta manta da ma wani wasan buya da takeyi ta wuce bandakin, sai da ta shiga ta ganta a madubi tukun ta tuna. haka ta makale a toilet. Sagir yajita shiru ne yasa yace “Aneesa lafiya?”

“Eh”

“Naji ki shiru ne lokacin sallah fa yana fita”

Ta rasa me zatayi can sai dabara ta fado mata tace “Don Allah dan miko min khimar dina uncle Sagir” ya san abun da ya boye ta kenan, yana dariyarta a ransa ya mika mata khimar din. Tana fitowa yace “in dai a haka zamuyi kwana biyar din  ashe kina da jan aiki” Ai shikenan abun da take jira kenan tsoro ya karasa bunne ta. Da kyar ta tattaro natsuwar ta tayi sallah, ta samu yana faman aikin sa na komfuta. Bai jira ya karya ba ya shirya cikin wasu 3-pieces suit mai ruwan toka yace mata “nayi magana karfe goma za a kawo abincin ki, ki leka tukun ki ga waye ne ki kuma tambaya, idan sun baki kika rufe kofa, kar ki budewa kowa sai kinji muryata.”

A sanyaye ta amsa, don ita ya kara tsorata ta da kyar ta tambaya “Suma a nan ana satan mutane?”

Ya mata kallon kasake “ko zaki gwada ki gani? Ana fada miki abun da zakiyi kina tambaya ko ana satan mutane, ina ne babu ta’addanci a duniya?” wannan Sagir din dai tana da matasala dashi har gwamma Sagir din jiya.

Haka sukayi kwanaki biyu kullum da safe idan ya shirya sai da yamma yake dawowa, kafin ya dawo kuwa akwai kofa ta cikin dakin su da yake hango waje anyi wurin zama, nan Aneesa take zama ta sha kallon ci gaban wannan babban birni, ga furanni masu sanyin kallo a cikin korayen lambuna, mutane kowa na sabgar gabanshi. Idan ta gaji da kallon waje ta dawo daki ta sha kallo a tv, duk da dai ba son kallon takeyi ba. Yana dawowa ya dauketa su fita gari. Aneesa dai ta bawa ido abinci, randa zasu fara fita ne ta gama shirin ta tsab, sai Sagir ya dubeta sama da kasa yace “Wannan wani irin kauyanci ne haka?”

                

                        

Nan da nan idanun Aneesa sukayi narai narai “Yaya zaki kama ki bunka wani hijabi kamar wa’azi zaki je?”

Ranta ya sosu amma sai ta danne tace “Uncle Sagir ni haka na saba shigata, suma baka ga suna saka nasu irin kayan ba?”

“To kema ba sai ki sa irin nasu ba?”

“Idan sun zo kasar mu irin nawa suke sawa ne?”

Jin haka Sagir yayi shiru, domin duk da kasancewarta mai karancin shekaru tunaninta mai zurfi ne, yana son mace mai tunani (he likes smart women). Haka ya hakura suka fita, idan ya juya ya ganta kamar zatayi swimming a cikin hijabin don rashin kaurin ta sai yayi dariya. 

Da suka fita ya kaita masallacin Sultan Ahmet, wanda aka fi sani da shudiyar masallaci (Blue mosque) saboda launin adon da akayi wa masallacin, musulmai da wanda ba musulmai ba duk ana bari su shiga ziyara sai dai an fi zuwa lokacin da ba na yin sallah ba saboda cunkoson jama’a. Abun da ya bata mamaki shine yanda taga wasu mata sun zo da wanduna kai ba dankwali amma taga da suka zo shiga ma’aikatn wannan masallacin sun basu dogin gyaluluwa suka rufe kansu da wuyansu sannan suka shiga. Bayan sun fita ne ta ke fadawa Uncle Sagir abun mamakin da ta gani shine ya mata bayani har wanda ba musulmai ba ana bari suyi ziyara a nan. 


Sunyi hotuna awurin kafin su wuce wani kayataccen wurin cin abinci. An dai ajiye abincin Aneesa kam sai kallon nata takeyi ta gagara tabawa, don wani abune kanana a cikin koko bata sanshi ba, amma taga Sagir ya daga ya kai baki ya cinye abun ya ajiye kokon. Ganin bata taba nata bane yasa      Sagir yace “Akwai dadi dai, ki ci mana”

Kai ta girgiza masa, tana ganin abu baki baki wani dadi zai yi? Nan yace “Bude bakinki”

Ta juya tana duba gefensu da bayan su yaya zata bude bakinta kowa yana ganinta? Sai da ya sake nanatawa sannan tayi yanda yace nan ya daga kokon ya sa mata a baki yace “Ki hadiye,” Abun mamaki sai taji abun ya wuce sulub, gashi yana da dandanon gishiri gishiri. Tissue ya dauka ya goge mata gefen bakin ta, hakan yasa Aneesa tayi saurin sunkuyar da kai cikin jin kunya, daga bisani tana jin dandanon abun da ya bata a bakinta, ashe dai yana da dan dadi sai da yaga ta dau dayan ta ci ne yace mata “Oysters kenan kika ci.” Tayi murmushi tana nanata sunan abun a bakinta, nan dai aka kawo musu green Salad aka kawo musu wani abincin kuma na Turkawa, har dai tace ta koshi. 

Daga nan hotel suka koma, sai washegari ne yace “akwai wurin da nake so ki gani, amma kuma a cikin ruwa za a kaimu kina tsoron ruwa?”

Aneesa ta zaro idanu, tana tunani yau har ina za a kaisu sai a ruwa? “A’a bana tsoro, a Kunuwal ina zuwa Rafi.”

Sagir murmushi yayi saboda wannan ruwan wane Kunuwal gaba daya bare rafin dake cikinsa. Waya taji yayi sannan yace ta shirya su tafi, wata doguwar riga ta saka mai ruwan daurawa ta nada farin gyale a kanta ta sa fararen takalman da basu da tsawo, a wajen dakin ta samu yana jiranta shi kuma T shirt ce marar nauyi a jikinsa sai wandon chinose da flat takalma. Suna fita wajen otel dinsu sai taga ya nuna mata abun da zasu shiga motar doki ne (luxury coach) ta daga idanu ta dubi Sagir, yayi mata murmushi, nan suka shiga mai musu bayani sai yi yakeyi, sun bi ta Golden Horn, wanda Sagir yace mata wannan shi ya raba garin kashi biyu, bangare daya na cikin Nahiyar Europe daya bangaren kuma yana nahiyar asiya. Abun ya bawa Aneesa mamaki matuka.

Haka suka ci gaba da tafiya lokaci lokaci Aneesa take satan kallon Sagir. An nuna musu wuraren tarihi da dama sannan suka je Bazaar wato kasuwar su ta gargajiya nan ne suka sauka a motar dokin nan, Sagir ya rike hannunta kamar karamar yarinya, sai shiga layi-layi na kasuwar sukeyi. Ba abun da babu, kama daga kayan kamshi, kayan yaji, da na abinci da na sakawa da duk wani abun da mutum zai bukata, domin kuwa makekiyar kasuwace, ita dai duk ta takura da rike mata hannu da Sagir yayi, amma ta kula shi ko a jikinsa. Wannan yasa ta dan saki jiki kadan.

                

                        

“Yaya sai tafiya mukeyi ban ga kin ce kina son komai ba.”

“Ni ba abunda nake so,” ta fada daidai lokacin da suka tsaya wurin kayan kwalliya na mata irin su dan kunne da sarka ta gargajiya. Sagir yace “Tunda ba abun da kike so ni ki zo na nuna miki me nake so.” Nan yayi cinikin wata sarka mai kyau tana da fararen duwatsu, yana dauka kuwa taga sarkar ta mata kyau don haka ta amince ya saya mata. Daga kasuwa kuma sun shiga dokin su inda ya kaisu bakin ruwa, suna isa wurin da zasu shiga motar ruwan, ta san wannan ruwan azimun ne ba zata hada shi da na Kunuwal ba.

Suna tafiya Sagir na mata bayanin sunan wurare, wasu ta rike wasu kuwa jinsa kawai takeyi, ita dai ta san yau tana ganin kyaun duniya. Suna iso wata gada ce ya nuna mata wani gini “Nan shi ake kira Rumeli fortress,” suna wuce kasan gadan kuma yace Kinga wannan, masarautu ne da aka gina su da zallar marble” Aneesa dai ta sha kallo, domin kusan awa uku sukayi ana yawo dasu a gari, har aka mai dasu bakin gaba inda abun hawansu ya maidasu Taksim square, ko da suka koma, hotunan da akayi ta daukanta da U. Sagir tayi ta kallo abunta.   

Ana washegari zasu koma ne suka fita sayayya, wani babban mall ya kaita Istanbul Cevahir, a nan suka shiga wani shago yace ta dauki duk abun da take so, sannan idan taga abun da zatayi tsaraba dashi ma ta dauka.

Sun shiga kantuna sunyi biyar. Amma har suka fito Aneesa bata ga Sagir da komai ba sai turare, ita kuwa sai da aka turo kayan da ta saya a keke, bayan sun ajiye kayan a masauki sauka sukayi wajen cin abincin otel din su suka ci abinci sannan suka koma masauki don kimtsa kayansu, don jirgin su da safe zai tashi tun cikin dare zasu tafi filin jirgi.

Tana shirya kayan a babban akwatin da suka saya ne Sagir yace mata “Har kina shirya kayan baki nuna min sayayyar taki ba?”

Murmushi tayi tace “Ni ban sayi komai ba”

ya dubeta ya dubi kayan dake gabanta “kina nufin duk wannan sayayyar baki daukawa kanki komai ba? To na su waye wannan kayan?”

“kaga na sayawa Aisha, Sameeha da su Khazeena, na sayawa Kamaal, da su Hamdiyya, wannan kuma na ‘yar kawuna ne wannan na Azhaan. Sai wannan na Abba da Daddy…” haka ta ci gaba da lissafa masa, hatta Musa mai musu shara da su Baba Saratu sun samu tsarabar Turkey amma Aneesa bata sayawa kanta komai ba. Abun ya bashi mamaki, a tunaninshi duk kayan da ta gani sun burgeta ne shi yasa tayi ta daukawa kanta, ashe ita duk jama’a ne a ranta yarinyar tana da kyakkayawar zuciya, zata mori zama da jama’a. Sagir yace “an taba haka mutum yayi tafiya bai sayawa kanshi komai ba?”

“wa yace maka ban sayi komai ba?”

Ta sa hannu a jakarta ta dauka masa kyamarar da sukayi ta daukar hoto tace “Ga babban kyautar da ta fi komai, a kullum na kalli wannan zan tuna zuwata nan garin amma, duk wadannan abubuwan zasu iya kodewa ko su bata ko na kyautar wata rana”

“Hakane kinyi gaskiya.”

Suna filin jirgi ne suna jiran a kirasu Sagir ya mike yace “ki jira ni a nan, ina zuwa yanzu kar ki motsa ko ina.”

A sanyaye ta amsa masa can sai gashi ya dawo, tana ganinsa tayi wata ajiyar zuciya wato dai duk yanda take jin tsoron Uncle Sagir shine komanta a kasar da bata san kowa ba sai shi, wani dadi taji ya lullubeta da ta ga ya dawo ya zauna a gefenta.

Bayan dawowarsu, Sagir ya ci gaba da al’amuran kasuwancinsa kaman yanda ya saba, Aneesa kuwa randa suka dawo washegari taje gidan Daddy ta bawa kowa tsarabarsa. Kowa yaji dadi yayi godiya, amma mummy yanda kasan kyautan kashi aka kawo mata, don yanzu kam ta daina boye kin Aneesa da takeyi kiri-kiri take kinta. Hatta Zaheeda da bata kula Aneesa sai da tayi murna da kyautar agogon da ta kawo mata mai dan karen kyau. Ko da Sagir ya zo daukanta su tafi Hajiya Juwairiya bata masa godiya ba. Sai da Daddy ya dawo ne suka nuna masa tsarabar ya kira yayi godiyar.

                

                        

Haka su Aisha duk sunji dadin tsarabar da Aneesa ta kawo musu duk da kuwa zuwa kasashe ba bakon abu bane a wurinsu, domin lokuta da dama acan suka fi yin hutun su, zata bada na Azhaan ne ta wurin Hajiya Sagir yace mata “ki bari cikin karshen mako na sama zamuje Kanon in sha Allah sai ki kai musu da kanki”

Aneesa tayi shiru saboda a tunaninta kafin hutunta ya kare zasu je Kunuwal, watakila ya sake shirin tafiyar ne ko kuma daga Kanon su wuce.

Ranar asabar sai ga Sameeha tazo gidan Aneesa, kwarai tayi mamaki amma kuma dadin ganin ‘yar uwarta ne yasa bata jima cikin mamakin ba, bayan sun gaisa ne Sameeha tace “yaushe zaku koma makaranta?”

Aneesa tace “saura sati daya hutun mu ya kare, wani abu ne?”

“A’a kawai daman ina so nazo ne na koyi wasu abubuwa a wurin ki,”

Maganar ta daurewa Aneesa kai, tace “Baba saratu bata nan ne?”

“Ta na nan, kawai zaman gidan ne ya isheni, kullum Daddy kara fita hanyata yakeyi, kuma mummy ta kasa shan kanshi, ban san me zanyi da rayuwata ba, hakan yasa naga ko auren ma nayi ban san yaya zanyi zaman auren ba tunda ban iya komai ba.”

Tausayin Sameeha ya kama Aneesa, “addu’a zakiyi tayi a hankali, hankalinsa zai kwanta, ya saurareki har ma ya koma miki kaman da. Kuma batun tunanin da kikayi ki koyi abubuwa wannan shine daidai. Amma kuma kinsan mutum bazai magance matsalarsa ba ta hanyar guje musu. Ki zauna a gida ki koyi komai ki canza shafin rayuwarki, abun da kikayi a baya kuskure ne kuma kin gane kuskurenki. Don haka ni na san idan daddy ya gamsu kin gane laifin ki, da kanshi zai mayar miki da rayuwarki. Idan kuma kina gani kin fi son ki yi ta gujewa rayuwar ki ba laifi sai nayi wa Uncle Sagir magana ki zo mu zauna”

Sameeha ji kawai tayi hawaye suna gangaro mata “Aneesa kiyi hakuri da duk abun da na miki, na nuna miki kaskanci ba sau daya ba, amma na san hakan ba daidai bane kiyi hakuri, sai dai bana tsamman daddy yana sona yanzu, kaman yanda Hamza ya gujeni haka kowa zai gujeni”

Aneesa ta jinjina maganar “kowa ai yana bukatan damar gyara abubuwa, don haka kiyi hakuri komai zai wuce, zan fadawa uncle Sagir ko zai bamu shawarar abunyi” 

Sun dan jima har zuwa azahar har ta taya Aneesa aiki kadan sannan ta ce zata koma. Tana fita kuwa sai ga Sagir sun shigo shi da Aadil, ta dawo suka gaisa sannan ta fita. 

Ta kawo musu ruwa ne Sagir yace “yau me yake damun kanwar taki naga ta yi sanyi?”

Aneesa tayi murmushi “maganarce dai ta kullum”

Aadil yace “Haba nima zance wannan ba ita bace Sameeha, sai dai naga wannan a natse”

“Uncle Aadil a ido na kake kiran ‘yaruwata haka?”

Aadil ya sa dariya ya daga hannayen sa “kiyi hakuri kar na rasa gidan zuwa cin buda baki, kin ga azumi ya kusa zagayowa”

Sagir yace “To laifi ne don ya fadi gaskiya? Nima ban taba ganin ta haka ba sai yau”

Aneesa ta hada rai ta tashi ta bar falon, tana kicin tana jiyo su suna tattauna wata kwangila don haka da ta gama kan tebur ta ajiye musu abincin ta wuce dakinta don ta huta, tana kwance tana tunanin al’amarin Sameeha ne Sagir ya shigo dakin, da hanzari ta nemi dankwalinta zata daura, ya zauna a bakin gadon yace “Aadil ya wuce, meye ne naga kin razana da na shigo?”

Hannu ta sa ta mutsuke idanunta “Nayi nisa ne a tunani shigowar kan ta sa ni firgita”

“hmm tunanin Sameeha? ko tunanina?”

Ta zaro idanuwa “ni kuma me zai kaini tunanin ka, bayan yanzu na barka lafiya a kasa”

“Don ina lafiya sai baza ayi tunani na ba? yau kam na san matsayina.” zatayi magana ne Sagir yace “To tunda ba tunani akeyi ba na Sameeha akeyi kenan, me ya faru?”

Nan dai Aneesa ta fada masa abun da ake ciki da yanda sukayi da Sameeha. “naji komai, kuma yanda kika fada mata gaskiya ne, abunyi ki ban kwana uku zan san meye abunyi zan kuma samu Daddy in sha Allah akan maganar”

Cikin fara’a ta rike hannun Sagir tana masa godiya a lokacin ne ta kula da dankwalinta da ke hannunta ashe bata daura ba.

Yana kula da ita don haka ya shafa gashinta yace “Haka kawai kina da gashi mai kyau sai ki k’i nunawa mijinki ya gani kullum kiyi ta maka lufaya kamar wata matar liman”

 Idanunta ta runtse tace “Uncle Sagir bana so.”

“wai ni yaushe aka yanka min ragon suna uncle ne a gidan nan, tun ina dauka kina kwaikwayar su Khazeena ne har abun ya zarce ya zama a ko ina ma haka ake ce min. so kikeyi wataran a ganmu tare ace wannan kam mijin ma ya mata tsufa da yawa har uncle take ce masa?”

girgiza kai tayi “to ai…”

“To ai meye? daga yau na soke uncle a gidan nan, sai dai wasu su fada amma ke kam Sagir kawai ya isheki.”

Yana shirin tashi ne tace “emm Uncle Sag…” kallon da ya mata yasa ta gagara karasa “to ai ni bazan iya fada bane”

“to shikenan ki sa min wani sunan banda uncle, meye maganarki?”

“Daman ina so na tuna maka ne batun tafiya Kunuwal din, sai mun dawo Kano ne zamuje ko kuwa kafin mu tafi?”

“ki dai saurara tukun”

Abin da yace kenan ya fita daga dakin.

Bayan ta kammala ayyukanta ne ta kulle ko ina, da yake Uncle S… oh Sagir ya fita inda yake zuwa kullum da har yau bai fada mata ba, sai tayi wanka ta dauko daya daga cikin english wears dinta, riga da siket ne wanda Khazeena ta rakata suka sassaya a wani plaza, bata cika sa su ba, saboda tafi jin dadin atamfa. Bata sauko kasa ba a falon sama ta zauna ta dauko hotunan su na Turkey tana kallo, tv kuma nata aikin watso labarai, ta dai kunna ne daman don ya taya ta hira. Kamshin turaren sa taji sannan ta gane yana tsaye a kanta ne, tana juyawa sukayi ido hudu.

“Banji shigowarka ba, sannu da dawowa”

“Wataran za asace ki, kin kure muryar t.v sannan kin rike wani aikin a hannu kina ta faman yi.”

“Tsoro nakeji shiyasa na kunna don ya tayani hira.”

“o, yanzu kam na dawo ki kashe komai sai ki sameni a daki”

Aneesa ta mike tsam ta fara tunanin yau kuma wani laifin tayi ta ga ta kanta. Tunda take bai taba cewa ta shiga dakinsa ba ko aikanta bayayi dakin, idan yana gida kuwa yafi so ya kadaice shi kadai a can don haka bai taba kiranta ba. Cikin fargaba ta maida hotunan dakin ta, ta adana a durowa sannan ta dauki mayafinta ta nufi dakin Sagir.

                      

Tana zaune a dakinta idan banda aikin kuka ba abin da takeyi, wanda da shi ta wuni dashi kuma ta kwana, ko kasa bata sauka ba wunin jiya kaf, babban matsalarta daya ba wanda zata iya fadawa kukanta a wannan yanayin. Bugu da kari wanda ya sata a wannan halin bai ma damu da ya san me take ciki ba, wai shi da kanshi ne ma yake fushi da ita. Shin yaya zatayi da rayuwarta ne? 

                      

Yana fitowa daga ofis, a mota yake tunanin abunyi, “lallai nayi mata alqawarin shiga cikin wannan magana na kuma warware matsalar Sameeha, saba alqawarin nan kuma ba daidai bane a gareni, idan Aneesa na da aibu ko kuma bata daukeni a matsayin komai ba, hakan ba shi zai sa nima na zama kamarta ba” don haka ne ya dauki hanyar gidan Alhaji Mahmoud, yaci sa’a kuwa ya sameshi a gida.

                      

Mummy ta shigo falo ganin Sagir suna magana da Daddy, kuma bata ga Aneesa ba sai ta raya wa kanta “hmm hali ya auku kenan, ta taba masa wani abun in banda haka me zai kawo shi cikin dare. Indai ‘yar Halima ce kam ka kulla da ganin bakin ciki” tayi kwafa ta koma daki.

                      

Suna gama tattaunawa da Daddy ya koma gida, yauma baiga alamar ta sauko ba, don kofar kicin na kulle yanda ya bari da safe. Ranshi a bace ya hau saman, a nan ya sameta a zube a kasan dakinta duk karfinta ya soma karewa. 

                      

“Aneesa (you are very stubborn) kin faye taurin kai” dagata yayi ya ajiye a kan gado, idanunta suna neman lumshewa, labbanta duk sun bushe. Da sauri ya koma dakinsa ya hado mata ruwan shayi mai kauri ya dawo dakin. A kan teburin gefen gado ya ajiye sannan ya zuba ruwa a kofi, ya dan sa yatsa ya jika mata labbanta dasu, cikin rashin karfin jiki ta kau da kanta. Haushinta ya kara kama Sagir “ki tashi ki sha tea,” ta so yin gardama, don haka ne yace “ki tashi ki sha ko na saba miki, wani irin rashin hankali ne za kiyi kwana biyu ba ci ba sha, so kikeyi ki kashe kanki?”

                      

A hankali ta zauna a kan gadon hawaye na bin fuskarta ta karbi kofin, ita kanta mamaki takeyi da taga har yanzu idanunta suna iya zubda ruwa bayan wanda ta zubar tsakanin jiya da yau.

                      

Yana zaune ta gama sha, ya umurceta da ta shiga tayi wanka ta zo ta kwanta, ba musu haka ta tashi ta shiga. Sannan ya mike ya bar mata dakin, tun daga cikin bandakin sai da taji karar buga kofar. “Yau ni kam nayi babban kuskure na jawo wa kaina damuwa a wurin Uncle Sagir” 

                      

****                *****                 ****                 ****

                      

Kwanaki uku da suka wuce ne Sagir yace ta sameshi a dakinsa idan ta kammala, Aneesa ta nufi dakin cikin fargaban laifin da tayi. Amma shigarta ta samu yana bandaki da alama wanka yakeyi don haka ta samu bakin gado ta zauna, can taji karar bude kofa ta ciri kai tace “gani Uncle Sagir” a karo na biyu ta kara cimmashi a yanayin da ta ganshi a Istanbul don haka ta sadda kai da sauri, “Dazu na gama ce miki Uncle ya kare a gidan nan ko?”

                      

“Na manta ne, bazan sake ba” idanunta suna kan yatsun kafarta da suke wasa da kafet . Yana cikin budadden ma’adanar kayan sawan shi ne yace mata “ki cire wannan hijabin ko ki koma dakinki”

                      

A hankali ta cire ta ajiye a gefe, ganinta a zaune, bayan ya juyo ne yasashi murmushi, ba tare da yace mata komai ba ya je gefen gadon shi ya kashe wutar dakin, ya rage guda na gefen gadon. Kallon shi tayi na rashin fahimta ko kuma kin fahimta yace “yanzu kuma kwanciyar ce take saki ciwon jiki ko kuma a zaune kika fi jin dadin bacci?” 

                      

“ni bana jin bacci” ta fada a sanyaye, 

                      

“Tunda bakya jin bacci je kiyi alwala ki zo muyi nafila. Bata masa gardama ba ta mike ta shiga bandakinsa ta yi kyakkyawar alwala sannan ta fito  sukayi sallar. Bayan sun idar ne ya juyo ya rike mata goshi taga yayi addu’a bata ce komai ba har ya kammala, ta mike ta je ta kwanta. Idanunta a rufe ruf, ganin ya kashe wutar dakin sai hankalinta ya kwanta a tunaninta bacci zaiyi amma kuma sai taji Sagir ya shiga yi mata wani salon da yake firgita mata tunani ya hautsina rayuwarta, yake jefa ilahirin jikinta a wani irin tashin hankalin da bai misaltuwa, a nan ta sandare kamar gawa a wannan lokaci idan za a tsaga jikinta kamar baza a samu jini ba don tsabar tsoron da ya shigeta. Tun tana daurewa  har ta gagara kore hoton da yake addabarta a kwakwalwarta, hakan yasa ta tattara duk wani karfinta ta hankada Sagir daga jikinta, har sai da yayi baya-baya. 

                                      

                        

A take yaji komai yana warware masa a kan idanunsa, wani irin bakin ciki marar misaltuwa ya rufe masa idanu, duk lokacin da ya dauka na ganin ya tabbatar da Aneesa wace irin mace ce, ya fahimceta ya tarbiyyartar da ita wajen cire tsoronsa a ranta, sannan hakan ya sake faruwa? Aneesa ta yaudare shi, ta kuma cutar da zuciyar sa. Bayan ya kumayi alkawari bazai sake bari mace ta masa hakan ba. A hankali ya kunna wutan gefen gadon, yace “ki tashi ki fita” cikin murya kasa-kasa.

Aneesa ko sai karkarwa takeyi “ki tashi ki fita min daga daki nace” sai shesshekar kuka takeyi tana bashi hakurin ture shi da tayi ba abun da takeyi. “nace ki tattara komai naki ki bar min daki tun kan ranki ya baci”

Tsabar bacin rai Sagir sai jin hawaye yayi a idanunsa. A sanyaye ta dauki hijabinta ta saka ta fita a dakin. Tana fita ya buga kofar dakin ya koma ciki, ranar haka ya kwana idanunsa biyu yana tunanin abunyi. Tunda gari ya waye ya fice a gidan bai sake dawowa ba har sai da ya tashi bacci, don haka bai san ma me take ciki ba. 

Washegari ne bai fita da wuri ba, amma bai ga fitowarta ba don haka ya duba kicin, amma ba alama anyi amfani dashi tun jiyan ma. Wannan ne yasa ya fahimci cewa takulle kanta ne a daki. Haushinta da yakeji a lokacin yana ga ko a ido ya saka ta zai iya mata lahani. Don haka bai nemeta ba har sai bayan shigowarshi a daren, ya sameta a wani irin yanayi.


Likita, Sagir ya kira ya daura mata ruwa tukun sannan zuwa safiya ta dawo hayyacinta. Cikin kwanaki biyu ta murmure don haka Sagir ya fita sha’aninta duka. Haka take zaune cikin kunci, ita daman ta san hakan na iya faruwa shi yasa tun farko taki amincewa zuciyarta ta so Sagir, gashi yanzu ya sa ta wulaqanta shi kuma yazo yana ganin laifinta. Ga mamakinta ranar Asabar da safe sai gashi ya tsaya a kofar dakinta “idan kun karasa shirin ku ni ina kasa, saboda yau nake son muje mu juyo”

Cikin daurewar kai tace “zamu wani wurine?”

Sagir ya mata wani irin kallo mai firgitarwa “kin mai dani shashashane, zan miki magana kiyi watsi da ita? Ko ban ce miki wannan Asabar din zamu tafi Kano ba?”

Sai da ta girgiza, jikinta ya dau karkarwa, idanunta suka firfito ganin yanda yake fada. Ita gaba daya ta manta da wani zancen tafiya, cikin wannan rudani da ta shiga na kwanaki uku, ina take tuna kanta bare wata magana da akayi ta a can wani lokaci da ya shude cikin wata duniya daban? Da sauri ta mike ta canza kayanta ta dauki khimar da wayarta, sannan ta dauki tsarabar Azhaan dama ta ajiye shi a kusa a karshe ta kulle kofar. Tsabar kidima ko minti goma bata dauka ba ta sauko, sai da ta sauka ta tuna bata dau takalmi ba, ta kara hawa. Tsaki yaja, don dai ya sanar da Ya Fanna zuwansu ne da ya bar wannan tafiyar. A mota ta same shi, ta zaci da Malam Hassan zasu tafi, amma sai ta ganshi a wajen zaman direba. Don haka ta bude gidan gaba ta zauna ba tare da tace masa komai ba, ya fizgi motar suka dau hanya “Allah dai ya kaimu lafiya, wannan irin tukin kaman da motar yake fushi” Aneesa tayi addu’arta ta shafa don bata tsammani fushi zai bari Sagir ya musu addu’ar.

Haka sukayi tafiyar nan kaf, amma Sagir bai ce mata uffan ba. Ganin hakan ta kudurta a ranta idan suna dawowa zata danne zuciyarta ta bashi hakuri. Sun shiga Kano wajen karfe Shadaya na safe, bai tsaya ko ina ba sai gidan goggon shi. Sunyi farin ciki da zuwan nashi, Anty Sameera ma tana nan, amma sai dai ganin Aneesa a tare da Sagir yasa ko wannen su ranshi ya baci. Don haka ruwa suka kawo musu, bayan an gaisa ne, Ya fanna ta tambayi dan uwanta. 

“ah duk lafiyarsu kalau, suna gaishe ku ma, ina Azhaan ne ban ganshi ba”

“Ai Azhaan ana makarantar islamiyya sai shabiyu zasu taso”

Sagir yace “yayi kyau, ai sha biyu kam sun kusa tasowa ma.”

Abun mamaki tunda suka gaisa da Anty Sameera sai ta samu gefen kujera ta zauna, tamkar bata taba ganin Aneesa ba bare ta ja ta da hira. Ya fanna ta shiga kicin, fitowarta sai ga ta da abinci a kula daya dan karami ta ajiye faranti da cokali a gaban Sagir. “sannun ku da hanya, ga dai abincin kuwa ba yawa, bamu san tare da amaryar zaka taho ba, sai dai bari na sa Atika ta dafa mata ko indomie ne.”  

                

                        

Daga Sagir har Aneesa maganar ta musu bambarakwai wai namiji da suna Hajara, amma suka boye mamakin su. Sagir yace “A’a mu kam ma sai da muka karya muka fito ki barshi kawai.”

“Allah, ko? Ai zaka dan taba dai musamman kanwartaka ta shirya shi kuwa”

Ya dubi Sameera yace “Sameera ai sai dai kiyi hakuri, amarya ta cika min ciki da girkinta, amma wani lokacin zan zo da yunwata”

Anty Sameera tayi murmushin da yafi kama da yake sannan tace “Yaya Sagir dai zaka hadani fada da Antina”

Aneesa dai sa musu ido kawai tayi tana murmushin da iyakan sa labbane, kusan anko da na Anty Sameera. Mamakin yanda Sagir ke nunawa kowa akan lafiya suke takeyi, gashi kuma sun taso takanas don zumunci amma an musu rowar abinci, ita dai gata nan ne kawai, da ma Kunuwal ya wuce da ita. Idan ya ga dama ya barta a can yayi tafiyarsa yafi mata akan wannan zaman da takeyi ana musu dariyar karya.

Sagir dai kaman ya fahimci takurar da Aneesa tayi da kuma yanda Ya Fanna ta musu, don haka yace “Mun gaishe ku a tsatsaye, don yau zamu koma in sha Allah kuma akwai gidaje biyu da zamu bi.” Ya duba gefen Aneesa ya daga ledar ya mikawa Sameera “wannan tsarabar Azhaan ce Aneesa ta kawo masa daga Turkey”

Ta karba “A’a lallai ashe Azhaan ya warke tsaraba tun daga Turkey, da fatan dai Antinmu ta dauko mana tsarabar Turkey itama” Sagir ya yi saurin kau da kanshi daga kallon Aneesa wanda ita ma tambayar ta daba mata gishiri kan ciwonta.

Sagir  yana mamakin irin hali na Yaa Fanna, idan dai don wata bukata tata bata  biya ba shine zata gwada wannan halin, tsabar rashin godiya, ba abunda Abba ya rage su dashi, hatta gidan da take ciki ita da mijinta da ‘ya’yanta Abba ne ya bata, sannan ‘ya’yanta basu rasa komai ba cikin rufin asiri suke wannan bai hana ta dage cewa sai ta samu ta kowani hanya ba, shi ya dade da sanin shirunsu na son ya maye gurbin Usman a wurin Sameera amma baya son yabawa abun muhimmanci shi yasa ya fita daga maganar.

Bayan sun bar gidan Ya Fanna haka dukan su biyun sukayi shiru a mota ba wanda yace uffam, gidan cin abinci taga ya kaisu ko da suka zauna shi ya fadi me za a kawo musu, da suka gama ne ya kaisu wani gida a Hotoro. Daga gaisuwar da sukayi ne Aneesa ta fahimci mai gidan abokin Sagir ne, matarsa mai fara’a da ita ta karbe su sosai Rabi’a sunan ta.

“lallai Sagir ka mana wayo, mu da muke shirin muzo muku sai gashi kun riga mu” Rabi’a ta fada cikin raha.

“A’a ke dai zaki kare mijinki, amma sau nawa Faruk yake shiga Abuja, sai dai yayi sabgar sa ya wuce, yanzu ma Aneesa na kawo miki ko ke zaki fi shi kokarin rike zumuncin tunda shi yaki”

“Ka dai kyauta, kuma mun amsa laifin mu, Anti Aneesa in sha Allah muma muna tafe kafun ku kara zuwa dai zaki ganmu da bataliyar mu”

Aneesa tayi murmushi tace “Allah ya nuna mana”.

Jifa-jifa dai Aneesa take sa musu baki a hirar su, don duk hirar da akeyi Sagir baya sata sai ko Faruk da Rabi’a. Sun dan fi dadewa a nan kafin suka kama hanya, Rabi’at ta hadota da kayan shafe-shafe masu kyau.

Wajen La’asar suka shiga Kaduna, nan ne yace mata “Zan ajiye ki gidan Hamdiyya kiyi sallah kafin na shiga gari sai nazo mu tafi, sai ki zauna cikin shiri”

“To” tace masa, a can Malali gidan Hamdiyyan yake ba karamin murna tayi ba da ganinsu. Bayan sun gaisa ne Sagir ya fita ya bar Aneesa, Hamdiyyan ma ta kusa sauka don haka ne Aneesa tace “Ashe dai lokacin biki da nauyinki”

Hamdiyya tayi dariya tace “Dake bai zo min da laulayi sosai ba, shi yasa mutane da yawa basu sani ba”

“to Allah ya budi ido lafiya”

“Ameen, saura namu bundle of joy din sai yaushe za a bamu?”

Aneesa tayi murmushi cikin rashin sakewa tace “ku taya mu addu’a Allah ya kawo masu albarka”

“Ameen, shine babba kam. Mun ga tsaraba fa ina ta cewa zan kira ban samu na kiraku ba shekaranjiya Yaya Kamaal ya bawa Darling ya kawo mun”

Aneesa kunya da mamaki suka kamata, tayi dariya. Hamdiyya tace “me ya baki dariya?”

“kawai naji sunan da kika kira Jamil da shine.”

“lah shine abun dariyar? ke baki cewa Yaya Sagir komai haka gaya kike kiranshi?”

Aneesa tace “uncle Sagir nake ce masa, amma kuma yace baya so wai sai dai na kirashi haka nan. Wai uncle ya dawo dashi tsoho.”

Hamdiyya tayi dariya sannan tace “kar ki yarda, idan ma zaki kira shi da sunanshi, wataran randa kuke dasawa ko kuwa ya burge ki ko zaki rarrashe shi sai ki kirashi da sunan da kika saka masa, zai na jin dadi a ransa”

“hmmm” kawai Aneesa ta iya cewa. 

“la kinga na tsaya surutu bakiyi sallar ba, kar ya dawo ya samu baki gama ba, bismillah shigo”

Nan Aneesa ta shiga cikin bangaren Hamdiyya, ba dai kudi ba aka narka a wurin tsara gidan da kuma kawata shi, babban gidane sosai mai kyau.

Tana idarwa kuwa sai ga Sagir ya dawo, don haka Hamdiyya ta bata kayan gyara fuska tace ta kara kwalliya sannan ta fito.

A falon maigidan suka same shi Hamdiyya tayi ta murna tana godiya. Da sauri ta koma dakinta ta hado abubuwa a leda tabawa Aneesa, tace mata sai sunyi waya. 

Tayi niyyar masa magana suna komawa amma ganin yanda ya hada fuska sai hakan bai taimaka ba don haka itama tayi shiru. karatun al-qurani kawai ke tashi a motar, har suka isa Abuja. Isarsu ta gaji likis don haka tana watsa ruwa, Sallah tayi ta daura taliya a wuta ta yanka su latas da tumatur tana da gyararren kirjin kazarta(chicken breast) don haka veitnamese pasta ta shirya wanda ta koya a wurin Paul. Da sauri ta shiryawa Sagir a kan table, a falo ta sameshi tace masa “na sa abinci a dining table” ko kallonta baiyi ba yace yaji.

Don haka ta debi nata taci ta kusa kammalawa yazo ya zauna zai fara don haka taki tashi a wurin. Yana sane da maganace a bakinta amma yaki bata fuskar yin hakan har ya kammala  ya sa ruwa yana sha.  

“My dear!” ta fada a sanyaye cikin fargaban abun da zai biyo baya, amma ganin Sagir ya tsai da kofin tumblan da ke hannun shi tsakanin hannun shi da bakin sa yasa taci gaba kanta a kasa “Don Allah, ka min afuwa akan duk abun da na maka, ko cikin sanina ko wanda ban sani ba. Hankalina sam yaki ya kwanta ganin fushinka, na rasa me yake min dadi. Haka mukayi tafiyar awa kusan bakwai amma ace baka furta min wata kalma ba? Ban san yaya zanyi da raina ba, don Allah kayi hakuri”

Tana kai aya ya kurbe ruwan hannun shi ya dubeta “Sunan da aka zaba min kenan? lovely, yafi Uncle dadi na gode. Ni kuma me kika min?” Ya fada yana murmushi, sannan ya dau tissue ya goge bakin sa, ya tura kujerar baya zai mike. Da sauri Aneesa ta durkusa kasa hannunta kan gwiwar sa tana kuka a hankali tace “idan ba abin da nayi maka, me yasa ka canza min? ka daina hira dani? ka daina ce min sai dasafe, ko fita zakayi bana sanin ka fita. kayi hakuri ka fada min laifina”

Kallo ya kare mata tas, lallai yarinyar nan ta wuce duka tunaninsa, wai tambayarsa ma takeyi me ta mishi? Yana daukarta a bakauyiya mai karancin shekaru ashe ta dama sauran ta shanye, harda wani my dear! yarinya kinyi kadan. 

Sunkuyawa yayi ya dagota daga kafafunsa yace “Ba na son wannan kukan, nace miki ba abun da kika min, tunda ai kema baki san laifin ba ko? Don haka me yasa zaki damu? sannan kin dauka idan zan je wani wuri har sai na sanar dake? wannan ba lallai bane don haka idan kinga hakan ya faru ba wai yana nufin wani abu bane. Tashi kije ki”

Aneesa tana kallon shi cikin idanunta da suka canza launi daga farare tas suka koma jajaye, amma ta rasa me yasa ta kasa gaskata abun da ya fada mata.

“Na gode.” ta fada sannan ta fara tattara kwanukan kan table din, Sagir ya mai da murmushin sa a hankali ya rufe fuskarsa ruf, ya san me ya kamata yayi.
                      

Facal! Facal! ta wurga ta sake dauko wani ta jefa “Wallahi ban yarda ba sai kin sake, wancan bai shiga da kyau ba”

                      

“Falmata, ke dai kawai kin faye cogel. Nawa ya riga naki, ko ba haka ba Abulle?”

                      

Abulle tace “Uwani, kullum ke kike ci. Gaskiya a sake.”

                      

Uwani tana dariya tace “Hmm, gwamma ku Falmata yau bazaki makaranta bane? Ni kam nayi gida zan shirya kar Inna ta min fada.”

                      

Abulle tace “Ai makaranta sai ke, Innar Falmata ta cire ta. Ke ma ban san me zakiyi da bokon nan ba kaman wani jaraba, kin bi kin nannace masa duk sa’o’in mu ke kadai kika nace.”

                      

“Ku zauna nan dai baku san dadin iya karatu bane shi yasa. Kuma bazan bari ba. Sai anjima” Tana fada ta juya cikin sauri ta bar bakin rafin. 

                      

Tana tafiya taji ana binta a baya  don haka ta rage sauri ta dan juya kadan, ai tana ganin shi ta kara sauri.

                      

“Uwani, Uwani ki tsaya mana muyi magana me yasa kike gudu na ne?”

                      

Wayyo, yaya zatayi da wannan sarkin nacin nan ne? “Na ce maka ka daina bi na, bata lokacinka kakeyi.”

                      

“Haba Uwani, ki fada min yaushe zan same ki a gida muyi magana.”

                      

“Idan na shirya zan neme ka yanzu karatu nakeyi don Allah ka daina bina.”

                      

“Naji Allah ya baki hakuri, sai anjima.”

                      

Ta wuce tana sauri kaman zata kife ta shiga gida, kai tsaye dakinta ta wuce ta fidda kayan makarantarta sannan ta shiga wanka, tana shiryawa ta samu Inna a madafi. 

                      

“Yau ma sai da kika kara lattin ko? Ni na rasa wannan wasa naku na fama da kullum sai an yi shi, sai nayi magana da malam ya sa a rinka wassafa ki a makarantar tukun.”

                      

“Inna kiyi hakuri, bazan sake ba.”

                      

Nan ta dauki kular abincinta tayi waje da sauri, tana fita ta wuce su Sheyido suna wasa a gindin bishiyar kofar gidan su, “Uwani yanzu ke kadai a cikin maza zaki koma ajinku wannan shekarar?”

                      

Murmushi tayi cikin rashin damuwa tace “Je ki dauko takardunki mu tafi.”

                      

“Tab, Baffa zai min duka. Sai kin dawo.” Tana juyawa taji sun tafa suna dariyarta, ko a kwalar rigarta ta tafi makaranta.  Idan an tashi ma bata tafiya sai da Malam Habu saboda ‘yan mazan tsokanarta sukeyi. Don ita kadaice mace a ajinsu, sai gwamma daya ajin ma akwai mata biyu. 

                      

“Baba kana gani yau ma sai da su Tukur suka tsokane ni ko?”

                      

Malam Habu ya ce “Ki rabu dasu, abunki da suka tsokane ki ai baki manta me aka koya muku a aji ba ko?”

                      

Kai ta daga masa sannan suka ci gaba da tafiya har suka koma gida.

                      

Tana isa gida ta tarar Inna Halima ta daura sanwa, hakan yasa ta maida kayan gidanta jikinta ta shiga yi mata wanke-wanke.  

                      

Hakan ya kasance mata al’adarta kullum, ranar da yamma bayan ta gama ayyukanta ganin ba makarantar Muhammadiyya tace “Inna ina son na je na duba Mama tun shekaranjiya banje ba.”

                      

“Ki gaishe su, ki tafi a hankali don Allah. Ba ruwanki kuma da yara daman.”

                      

Uwani ta fita sai sauri takeyi, domin duk inda ta wuce gulmarta akeyi wai ta ki barin boko alhali sauran kawayenta duk basuyi. Don Falmata ma aure za a mata da kaaka. 

                      

Kaman wani hadin baki tana fitowa daga gidan Mama sai ta tarar da Nata’ala a bakin kofa, “Uwani yau kam don ALlah ki tsaya, ban san me na miki ba kike wulaqanta ni haka.”

                                      

                        

“Na ce maka ka rabu dani.”

“Uwani ina sonki, ki taimakeni ki amince muyi aure. Ke kanki kinsan ba tun yau ba nake binki da wannan maganar da bana sonki da na hakura, kina sane har mata Inna ta zaba min saboda na kara aure amma nace idan zanyi aure to fa sai dai Uwanin Inna. Idan baki amince ba inaga mutuwa zanyi kullum bana bacci saboda tunanin ki wayyo Uwaniyo na, ki taimakeni.”

Batayi aune ba taga Nata’ala ya sa kuka, yau ta shige su zai tara mata jama’a “Naji naji, kayi shiru don Allah kar kayi kuka. Ni dai ina so kayi hakuri, kaga ina karatu kuma da zaran su Baba sunga ina kula wani to fa zasu cireni a makaranta dama surutai yayi yawa.”

“Ni na amince zan na zuwa idan har kin yarda zaki aure ni to zan bari ki yi karatunki, amma don Allah ki soni kema.”

Ya bata tausayi sosai amma kuma ita gaskiya tana tsoron yin aure ta bar karatunta don kawai ya mata alkawarin makaranta.

“sai nayi shawara gaskiya.”

“To na dawo yaushe kenan?” 

“Zan fadawa Fatun ku.” Haba nan fuskar Nata’ala ta washe, murna ba a cewa komai ko da ya koma majalisa ma su Iro sun san dai da wani abun a kasa don yau farin cikin Nata’ala daban ne.

 “Tashin hankali, yau zai shigo gidan nan ya sameni, wato dama munafurcin da yake min kenan ko?”

Tume matar baffan Nata’ala ta dube ta tace “Rabi, daina tada jijiyoyin wuya, kema fa kin san ba tun yau ba Nata’ala yake so ya yi aure meye ne a ciki kuma don lokacin yin yazo, kin san fa matsalarku ta rashin haihuwa.”

“Na sani, tuntuni muke tare bai san bana haihuwaba sai yanzu?”

“Lokaci ne fa komai, to ina laifi don ya gwada neman aure.”

“Ni kuma na mutu kenan.” hayaniyarsu yasa basu ma ji shigowarsa ba, da yaji abunda suke fada yace “Haba Rabi, sau nawa zan miki bayani, komai fa lokaci ne. Kuma kin san na dade ina son Uwani meye abun tada hankali? Kinsan bazan taba wulaqantaki ba, don haka ki kwantar da hankalinki har Allah ya kawo lokaci don ni kam ban cire rai ba.”

Jin maganar Nata’ala yasa ta bar tsuma. 

Wasa gaske tun Nata’ala yana zuwa Uwani taki kula shi har ya zamana ta fara dan saurarenshi, ranar kwastsam sai ga Baba ya dawo daga kasuwa suna tsaye a soron gidan shi. 

“Ikon Allah, Uwani? Daman abun da ake fada min gaskiya ne? kin sa ina ta fada da mutane?”

“Ina wuni Baba?” Nata’ala ya durkusa ya kwashi gaisuwa.

“Lafiya kalau, ha’a kai ba Nata’ala ba. Me kakeyi a wurin Uwani?”

Cikin jin nauyi ya hau sosa keya, “Baba aurenta nake so nayi.”

Baba ya juya ya dubi Uwani “Bata ce maka karatu takeyi ba?”

“Ta fada, amma ni na amince ko bayan auren mu idan tana so tayi karatunta.”

“To to to, magana tayi kwarai ai sai kayi magana magabatanka su iso a san lalle auren kake nema, amma ganin tana makaranta a yawaita ganinku bayan kana da iyali ina ga hakan bai dace ba ko me kace?”

Nan take fuskar Nata’ala ta washe. Uwani ko da gudu ta wuce cikin gida. 

Shi kenan ai abunda take gudu ya faru, yanzu Baba zai sa ayi mata aure, hakan ya sa tayi fushi da Nata’ala ko ya zo sai su Falmata su shiga bata hakuri, ranar tsabar haushin da ya bata tsallaka danga tayi ta gudu ta bayan gidan Mama. Daga can rafin kukanta ta wuce ba ita ta koma gida ba sai daf maghriba. 

Watarana tana komawa gida ta samu Inna na jiranta tunda taga kallon da take mata ta sha jinin jikinta. 

“Inna, lafiya na ganki haka?”

                

                        

“Lafiya na kalau, zauna muyi magana.”

Jikin uwani a sanyaye ta samu wuri ta zauna “Ina so ki saurareni a tsanake kan abun da zan fada miki, komai yana da lokaci a rayuwar nan da kike gani.”

Ganin tashin hankalin fuskar Inna uwani tace “Inna, wa ya mutu?”

Inna Halima ta daure tace “ba wanda ya mutu, Baba ya fada min an kammala maganar auren ki da Nata’ala wannan juma’ar za a daura…”

Iyaka abun da taji kenan ta sulale ta zauna, yau shikenan an katse mata karatunta. Duk da tana son Nata’ala ba karamin haushinsa ta ji ba, haka taci kuka Inna na yi tana yi ba mai rarrashin dan uwansa, saboda Inna ta ci buri uwaninta tayi karatu amma gashi rana tsaka an katse wannan mafarki da ta gani. 

Ranar Alhamis aka saka ta a lalle, Juma’a da safe kuwa aka daura auren ta da Nata’ala. Shekarunta goma sha uku a duniya lokacin. Abokansa ko murna suke masa ya samu mata son kowa kin wanda ya rasa, don a cikin ‘yan matan garin ma Uwani tana tashen kyau a lokacin, sai gashi ita da take cewa bazatayi aure ba karatu zatayi ta buge da riga duk kawayen nata shiga daki. 

Sati guda suka dauka Nata’ala na aikin rarrashi, amma wataran har da cizo ya fito. Rabi dai da sassafe take wucewa gaban dakin su taji gumun da ake tabkawa a tunanin ta duk ihun dadi ne sai kawai taga ya fito rike da hannu yana jini, nan fa ta san akwai matsala.

“Lafiya Nata’ala? Me ya sameka kake ihu?”

Cikin jin kunyar kansa yace “A ina kika jiyo ihu ke kuma da safen nan mafarki kikayi hala.”

“Ah, ba mafarki nake yi ba idanuna a ware ras na fito fitsari naji ihu a dakin Uwani na jira banji komai ba sai gaka ka fito.” nan ne idanunta suka kai kan hannunsa “la ila, cizonka tayi? ji fa har jini yana bulbula, ni ban taba jin ana maita a zuri’arsu ba. Kai ma maganinka ka dauko ‘yar boko, gashi ta dauko maita ta zo maka dashi gida tana cinye ka tun da ranka.”

Da sauri Nata’ala yace “Ke yi min shiru, bana son sakarci, wani irin maganace hakan kuma? madubi ne ya fashe ya ji min ciwo.”

“Madubi? Jefe jefe kukeyi a dakin kuka fasa madubi?” ta riko hannun tana kallon shatin ciwon “shine ya karkace, ni ko sai nace aradu kamar hakora” Fizge hannunsa yayi ya sabi buta yayi waje.

 Uwani na fita girki Falmata ta zo mata wuni, don ba abunda yake tsikararta idan ba gulma ba. Tana zuwa da ta fara dagowa Uwani zancen sai tace mata “Ke ni rabani ai haushi ma yake bani, kinaga ya sa Baba ya cireni a makaranta bayan ba haka mukayi dashi ba. Wai shi a dole lallabi kullum sai ya kawo min tsire da balangu, harda taliyar nan ta wurin mai shayi indomi sai kiga ya sayo ya kawo wai nayi hakuri na yafe masa.”

“Haba Uwani, Nata’ala fa yana sonki me yasa zaki masa wulakanci?”

“Karya yakeyi ya daina sona, bayan mugu ne shekaranjiya sai da na gintsa masa cizo.”

“Lalala cizo dai Uwani? baki da hankali ko? ke baki ji me Dije ta fada bane? haka fa akeyi daman ba mugu bane.”

“Ba wanin nan, ni yaushe naje gidan Dije? Malam ya hana mu yawon gidan kawaye idan anyi aurensu yace ba kyau.”

“To shi kenan kina nufin na tafi kenan.”

“A’a ke ai babban kawatace, kuma na fada miki damuwata ne wannan ba wani sirri bane ban san me zanyi ba. kuma abun kunyan yana fita najisa da Rabi a tsakar gida ta gane cizon shi nayi tun shekaranjiya take min kallon wulakanci.”

“Kinga abun da kika jawo ko? Wallahi ingaya miki ki lallabashi tun yana ji dake, kin ga Garbana yace zamu sha soyayya idan munyi aure shi yasa ingaya miki ba wani takura zan zage na kula dashi, har a baki sai na bashi abinci dan soyayya.”

Uwani ta rufe baki tana dariyar Falmata. Can dai sukayi sallama ta tafi. Tun daga ranar Uwani ta sassauto ta daina yiwa Nata’ala mugunta, idan ta tashi da safe bata bacci sai ta tabbatar yana cikin wadatuwar duk wani abun da yake bukata. Ummansa dake daya sashin dake manne da nasu kuwa kullum sai Uwani ta sa mata abinci ko abun marmari tayi sai ta kai mata, wannan yasa kullum take yabon Uwani. shi Maigidan kuwa  haka zata zauna tana masa fifita yana cin abinci. “Kai Uwaniyo, wallahi kina sakaltani da yawa, kin san yanda bana son fita ko zuwa gona ne ko kasuwa saboda yanda kike tarairayata da zaran na fita to burina shine na dawo gida na ganki, naci daddadan abincin ki. Gaskiya Inna ta iya kiwo.” Kullum idan suka zauna aikin shi kenan na yabonta.

                

                        

 Rayuwarta ko gwanin dadi, don idan Rabi ta so tada tsiya Nata’ala taka mata birki yakeyi. Ba a dade ba Uwani ta samu ciki, ai murna wurin Nata’ala da jama’ar gidansu ba acewa komai, ririta kuma ai wani sabon salo aka bude.

Yana zaune a gindin bishiya hankalinsa yayi nisa wurin tunani iska ya zuka ya  fesar sannan ya gabtari sandar raken hannunshi yana tauna yana saka abunyi, ai shi bai san tafiyarsa Jos zata kawo masa babban asara ba haka, jibi wani garabasa da Nata’ala ya samu don kawai baya gari, da me zatayi da tsoho irin shi? Gaskiya yarinyar tayi, gata da iya daukar wanka. Kanshi kawai ya jinjina, ya gama tauna rakensa ya zagaya gindin dalbejiya inda abokansa marassa aikin yi suke taruwa a bata lokaci. Suna ganinshi suka dau shewa ga dan birni ya dawo. Nan ya zauna suka ci gaba da surutu. 

Hankalin Inna ya kwanta game da Uwani ganin tana zaune a dakinta lafiya, gashi daga shiganta har ta samu rabo. “oh ni Halima wai Uwani ce zata haifi danta itama. Allah abun godiya.” Malam Habu ya ajiye buta hannunsa yace “Ai akwan a tashi ba wuya, haka dama rayuwar take. Kinga rabon wannan cikin ne yasa akayi auren cikin gaggawa, gashi ta kwantar da hankalinta. Sai dai a bisu da addu’ar zaman lafiya.”

“Ameen malam, amma na so a ce tayi zurfi a karatun boko da na Muhammadiyya, duk da dai alhamdulillah ta samu na arabin daidai gwargwado.”

“KOwa da rabonshi, idan da rabon ta samu a gaba sai ki ga tazo tayi ne a dakinta.” Nan suka ci gaba da hirar su ta mata da miji bayan Inna ta shimfidawa malam Habu tabarmar ene. 

Kullum ita da Rabi ne suke sawa Munkaila abinci ganin yanzu Umman su bata girki sun dauke mata, don haka wataran har cikin gidan yake zuwa ya dauka. Ranar da yamma Uwani na sharar kofarta  sai gashi ya shigo, har ta tsorata kasancewar bai yi sallama ba. 

“Ai na bawa yara abincinka sun kai maka.”

“Hmm, Uwani kenan. Tuni na cinye, ni ba abinci bane ya kawoni daman Nata’ala ne ya turo ni yace na kiraki yana soro zai baki sako.”

Murmushi tayi ta gyara tsintsiyar hannunta ta jingina shi da bango sannan ta dauki mayafi ta bi bayanshi, Nata’ala dai baya gajiya da tarairayarta yanzun kuma ko meye zai ce mata oho. 

Sai dai suna isa zauren ba Nata’ala ba labarin shi to kodai ya dade ne a wurin har ya gaji ya tafi? Bata ankara ba kawai taji Munkaila ya hankada kofar dakinsa ya tura ta ciki. Ta dubeshi cikin tsoro, “Lafiyanka kuwa me yake damunka zaka turo ni nan? Ina Nata’alan yake?”

Munkaila yayi wata munafukar murmushi yace “Au wai ke kin dauka da gaske mijinki kiranki yakeyi, wannan kiran nawa ne don haka kar ki nemi ki bata min lokaci.”

“Lafiyan ka kuwa me zakayi, ka matsa min na fita.”

“Ai yau ba inda zakije, haka kawai kiyi ta yi wa mutane sintiri a cikin gida kina cin gayu sannan kice kar a more?” Idanunta ta zaro cikin kidima da tashin hankali. Kafin tayi tunanin abunyi ya aunata da bango. TUn tana iya ihu da magiya har tayi suman tsaye. 

Nata’ala ko yana sauri ya taho gida saboda ya kawo wa Uwani hantarta tun da duminsa don bata son cin abinci mai sanyi. Yana shigowa gidan yaji wani irin nishi kaman yara suna kuka, nan ya tsaya cak don yaji ta inda yake jin sautin sai ya gano daga dakin kaninsa ne, don haka ya tura kofar a hankali don ya ga waye ne.  Amma abunda ya gani yayi masifar tayar masa da hankali. Don ko bazai so ganin kaninsa a haka ba da koma waye bare ace matarsa. Nan yayi wurgi da ledar hannunshi ya rarumi sanda a soron ya koma dakin, wanda duk shigowarsa da motsi bai sa sun shiga hankalinsu ba. Kaninsa Munkaila ya gani kan matarsa Uwani. Duka yakeyi ba ji ba gani, da kyar Munkaila ya samu setin kofa yayi waje da gudu, yayinda uwani tayi shame-shame bata iya motsa ko da yatsa,  wannan ba karamin haushi ya bawa Nata’ala ba ya sunkuma mata sanda ko ta ina, da kyar tayi wani wawan juyi sai gata a lungun dakin. shi kuwa fadi yake yi yana duka “Uwani abun da zaki min kenan? irin zaman da mukeyi kenan? Kin cuceni Uwani ban yafe miki ba kanina shakiki?” Wani irin kara ta sake tana mukurkusu sai da ilahirin jama’ar gidan suka nufi dakin da gudu. 

Tume ce ta fara wabce sandar hannun Nata’ala tana fadin “Me yake faruwa? lafiya kake kuwa? “

Nan daya matar tace taimaka mu daga ta bata motsi fa”

Ai suna daga ta sai ga jini yana biyo kafafunta. Idanunta kuwa a kafe kikam ko ruwa sun gagara zubdawa. “Lah, Tume tayi bari. Nata’ala cikin Uwani.”

“Can mata, ai dama natane ita kadai. NI Nata’ala bana haihuwa ita ta san inda ta dauko abunta, tunda ya fita ko can mata. KUma a daren nan ki tattara ki bar mini gidana, na sake ki, na sake ki na sake ki, na sake ki saki uku kar kuma ki kuskura ki kara nuna min fuskarki bake ba ni HAR GABAN ABADA”

Mamaki ne ya kama gaba daya mutanen gidan, hatta Rabi sai da ta tsorata, yanda yake ji da Uwani yau yayi mata kaca kaca haka. Nan ne wanda suka riga isowa kowa ta bada bayaninta, daga karshe suka kinkimeta zuwa sashinta suka kimtsata, abunka da karamin gari Inna harta ji labari “Na ta’ala yayiwa Uwani duka cikin jikinta ya bare, kaman ma ance ko ta suma ne ko ta mutu ne oho.” Cikin tashin hankali Inna ta sabi gyalenta  tayi gidan ‘yarta a karo na farko tunda ta aurar da ita. Tana zuwa kuwa ta tadda mummunar labarin mutuwar aure har saki uku, ga ‘yarta a kwance rai a hannun Allah bata uhm bare uhm uhm. Da sauri ta nemi Malam Habu ya samo musu tasin first lady saboda halin da Uwani take ciki sai asibiti. Ita kanta Inna da ta ganta ta gagara gane ko tana da rai ko ta mace. 

Sai da suka kwana biyu a asibiti bayan an mata wanki ciki tukun sannan Uwani ta farfado nan ma dai kallon mutane kawai takeyi bata iya magana sai hawaye. Inna ta tausaya mata matuka musamman bayan taji abunda taji ance ya hadata da mijinta fada, don ita kam ta san ‘yarta ta kuma san tarbiyyar da ta mata, jira kawai takeyi ta warke ta fadi komai don ta fidda kanta daga zargin mutane.

Ko da aka sallamesu, sati guda sukayi basu samun bacci don cikin dare sai ta firgita ta sa wani ihu tamkar mahaukaciya sabon kamu, dole Inna ta koma dakin Uwani saboda ta kula da ita, cikin natsuwa tace “Uwani, kalleni nan nifa mahaifiyarki ce, shin duk duniya kinada wacce ta fini?”

Uwani ta girgiza kanta “To idan kuwa haka ne kin san cewa koma me zai faru ni bazan guje ki ba, ina so ki fada min abun da ya faru ranar.”

Uwani kuka kawai ta fashe dashi, da kyar ta soma magana amma kuka ya hanata fadin komai, Inna ta barta sai washegari, amma duk da haka bata sauya zani ba. Sai da suka shafe wata guda a haka, Uwani ta dake zuciyarta, ta dau alwashin zata fadi komai kuma zata manta da komai sai dai ita kam ba ita ba da namiji, domin sun cuceta sun hallaka mata rayuwa. Lokacin ne Uwani ta fadawa Falmata komai, nan ta samu Inna suka sa Uwani a gaba da nasiha. “Kar ki tayar da hankalin ki in sha Allah kaman yanda kika fada mana komai, wataran haka duniya zata gane ke mai gaskiya ce, ki kwantar da hankalinki mu muna tare da ke ko ma me zai faru, domin kuwa ke ‘yata ce kuma na san zafin ki, addu’a ce kawai mafita tunda kowa yaki yarda kan cewa kina da gaskiya.”

Wannan ranaku sune mafi muni a rayuwar Uwani, wanda har zuwa wannan rana kwakwalwarta taki manta wannan tashin hankali da ta fuskanta. 

Nata’ala labari ya sha samunshi akan Uwani ta rantse danneta Munkaila yayi, shi kuwa tunaninsa a wancan lokacin shine me ya kaita dakin kaninshi? Ansa daya ke ziyartar kwakwalwarshi ai Uwani ce tajawo hankalin Munkaila gareta tunda ta san irin kyaun da take dashi. 

Watanni ta dauka bata fita, don da zaran ta fita yara zasu fara mata ele da waka, ana haka sai ga ‘yar gidan Malam Sunusi ta zo da kwatankwacin karar abunda ya faru da Uwani, to nan ne fa zance ya canza alkibla kafin ayi haka da haka Munkaila ya arce da gudu ya bar Kunuwal. 

Nata’ala yayi kuka da idanuwanshi, yayi ciwo har kaman bazai tashi ba akan rabuwarsa da Uwani kan abunda bai yi bincike ba ko ya bata daman bayani. Ya bita har ya gaji duk da yasan shima shirme yakeyi domin kuwa aure a tsakanin su ya kare. 
                      

Aneesa dai sun koma makaranta, satin su uku kenan da komawa, amma bata ga wani canji daga Sagir ba. Asalin zancen ma dai wataran sukanyi kwana biyu basu hadu ba, don kafin ta fita daga gida zuwa makaranta ya tashi ko yana wajen motsa jiki ko kuma ya fita. Wataran kuma kafin ya dawo ta riga tayi bacci, tasha ta shirya abinci sai dai ta bawa su Musa a waje. Abun ne ya dameta matuka ta nemi abunyi. Nan ne ta yanke shawarar neman Aadil a waya inda ta nemi ganinshi.

                      

“Amarya bata laifi ko ta kashe dan masu gida.” Aadil ya fada yayin da ya zauna a kujerar falon Sagir.

                      

Aneesa tayi kwafa tace “Ni dai ban kashe dan masu gida ba, amma laifina har ya kusa ya karni”

                      

“A’a haba, muna nan wa ya isa ya taba ki?”

                      

“Maganar gaskiya Uncle Aadil akwai abun da nake son na tamabayeka ne ya daure min kai matuka game da abokinka. kuma bani da wanda naga ya dace zai kuma iya warware min wannan tambaya sai kai”

                      

Aadil yayi shiru yana sauraron Aneesa, can ya gyara zama yace “ina jinki kanwata, menene tambayar ki?”

                      

“Don Allah ina son ka fada min tsakanin ka da Allah, shin akwai watace a rayuwar uncle Sagir kafin na shigota?

                      

Tambayar bata bashi mamaki ba tunda ya san taqaddamar da sukayi da Sagir a lokacin da ya fahimci ko Aneesa wacece.

                      

“Sam, babu wannan ni dai a iya sanina ma ya dade bai tunkari wata ‘ya mace ba da sunan so tun kafin ya hadu dake ma bare zancen aure”

                      

Tana son ta masa bayanin dalilinta na yi masa wannan tambayar amma bata son tono cikinta don haka tace “To, Amma ba wani abu na rayuwar uncle Sagir da ya dace na sani? A hakikanin gaskiya na san yanda tsakaninka da shi yake kuma hakan yasa na nemi shawararka don haka bazan boye maka ba na janyo wani babban laifi ne, kuma nayi duka iya kokarin naga na shawo kan wannan matsalar na gagara.”

                      

Aadil ya gano me take nufi don haka ya amsa mata tambayar da ya sha dambe tsakanin zuciyarsa da kwakwalwarsa wajen furta shi tun ba yau ba.

                      

“Na gane, Aneesa idan har akwai abu guda da yakamata ki sani kuwa to shine Sagir ya taba yin aure!”

                      

A take zuciyar Aneesa ta hau dukan uku-uku, nan take taji tafukan hannunta sunyi zufa, idanunta suka fito ba don kishi ba sai don tsantsan mamakin da amsar Aadil ya haddasa mata.

                      

“Tun yaushe? yaya akayi ba wanda ya sani?”

                      

Aadil ya nisa yace “da dadewa, tun farkon fara aikin sa a matsayin me tsara zane na gine-gine, munje Bauchi dangane da wani aiki a nan suka hadu. Karfin yiwuwar abun ma abokin mu ne ya karfafa shi kasancewar a gidansu Sagir ya ganta. Abu kamar wasa, muna komawa Abuja ba da dadewa ba zance ya kankama, kusan ko wani karshen wata muna Bauchi wurin Ummi. Har Allah yasa akayi auren cikin matukar kaunar junansu”

                      

Aneesa tace “to me ya faru?”

                      

Aadil yace “kin san komai akace da wa’adinsa anyi auren su da wata hudu kowa ya tsinci mummunar labarin mutuwar wannan auren wani abun mamaki shine har yau Sagir bai taba fadawa kowa takamammen dalilin rabuwarsa da Ummi ba. Abun da ya fada kawai shine, bata da lafiya ya bata abin da zata bukata ita da iyayenta don su nema mata magani”

                      

Aneesa tayi shiru cikin alamun damuwa, kafin tace “Na gode uncle Aadil, Allah ya bar zumunci”

                      

“kar ki damu komai zai daidaita in sha Allah, mutumin nawa ne sai a hankali zaman tare da ma sai an hada da hakuri da lallabi, kin san sabon shiga ne, ki bashi lokaci”

                      

Aneesa kwafa tayi a ranta tace wanda ya zauna da matar so na tsawon watanni hudu da wacce bata san meye soyayyar da na miji ba waye sabon shiga a cikin su oho.

                                      

                        

“To ni zan gudu, Allah ya bada zaman lafiya”

Aneesa cikin sanyin jiki ta mike ta bar falon. Ranar zama tayi a falon kasa da niyyar sai ta ga dawowar Sagir gidan, suyi magana. Amma abin mamaki shiru har sha biyun dare bai shigo ba, nan dai ta bige da yin bacci.

Kiran fari ne ya tada Aneesa, ta tashi ta ganta a kan kujerar falon Sagir. Hakan ya tabbatar mata dai nan ta kwana tana jiran dawowar mijinta. Lafiya dai Sagir bai dawo ba? Nan take hankalinta ya tashi, ta haura sama ta murda kofar dakinsa a hankali amma baya ciki, haka bandaki ma. Kafin kira na biyu dai Aneesa ta duba ko ina a gidan ba labarin mijinta. Don haka ta daure tayi sallar asuba, sai da ta kare sallar ta daga wayarta, don ta kira shi. Sai ta samu text a wayar “Tafiya ta kamani, zuwa gobe in sha Allah zan dawo. Ki kula da gidan”

Ta duba lokacin da ya turo sakon tun jiya da yamma. Yanzu laifinta har ya kai ga Sagir yayi tafiya bai zo sunyi sallama ba? ko da yake sai ta tuno abun da ya fada mata dawowarsu daga Kano ba lallai bane ya sanar da ita komai idan kuwa ta ga hakan ya faru to ba wai yana nufin wani abu bane. To amma yanzu dai ta fara tantamar hakan.

Nan da nan ta nemi lambar amma ta rinka jinta a kashe don haka ta hakura, ta zauna jiran tsammani.

Kaman an tsikareta ta zabura “yau ina da gwaji a makaranta, gashi ko karatu banyi ba.” Ruwan zafi kawai ta sa a cikinta ta yi wanka, ta fito ta shaidawa Malam Hassan yau da sassafe zasu tafi.

Tana zuwa ta fara karatu, tana yi tana gwada lambar Sagir har dai ta fahimci ba daukan karatun takeyi ba, don haka ta hakura. Sai da ‘yan ajinsu suka fara zuwa ta zauna tana bin bayanin da sukeyi a cikin jam’i (group discussion). Shigowar malamin darasin farko ne ya sa dole ta kashe wayarta. 

A bangaren Sagir kuwa ya rasa me daya yake ciki ransa ya kai makura wurin baci, sai dai yakan rasa me yasa duk da bacin ran da yake ciki, duk sanda ya ga Aneesa sai yaji tausayinta, yaji zuciyarsa ta shiga wani yanayi na son ya yafe mata abun da tayi, yakan ji kunci idan ya tuno hawayen da ta zubar a dalilinsa, wannan yasa ya fuskanci abun da ya dade yana gudu a ransa, wanda shi ya sani sai dai kin amincewa hakan ne babbar matsalarsa. 


Wannan abu kuwa ba komai bane illa tsananin son Aneesa da yakeyi a cikin ransa. Ba abun da yake so illa yaga ya samu dalilin da yasa Aneesa tayi masa abun da tayi saboda yanda yake matukar kwadayin yaga banbancin tsakaninta da Ummi tsohuwar matarsa. Wannan dalilin yasa ya tuno abu guda ya kuma sa ya yanke shawarar gano gaskiya da kanshi ba tare da Aneesa ta san hakan ba.

Karfe Biyu Sagir ya dauki hanya ba tare da ya fadawa kowa ba, don hatta sakataranshi ce masa yayi idan an neme shi yace bazai samu ba zuwa nan da gobe. Bai tsaya ko ina ba har sai da ya isa Gombe, a nan yayi masauki ya huta kafin washegari da safe wurin karfe takwas ya karasa Kunuwal. “Sagir ko me kake tunanin yi?” wata zuciyar tace “gwamma ka san komai ko za ka san matsayar rayuwarka da Aneesa”. Gaba ki daya zuciyarsa ta gagara samun natsuwa akan Aneesa, kuma idan ba sanin komai yayi game da ita ba ba yanda za ayi ya warware abun da ke kawo musu matsala. Yana zuwa ne ya samu wani matashi a hanya kafin ya isa gidan malam Habu, don haka ya tsaya ya fito daga motar.

“Assalamu alaikum,” ya fada tare da mika masa hannu matashin ya amsa Sagir yace “Don Allah tambaya nakeyi”

“To Allah yasa na sani.” matashin nan ya dubi Sagir da kuma abun hawansa ya san dai bako ne, koma daga ina yake kuma attajiri ne.

“Sako ne nazo dashi zuwa ga tsohon mijin Uwanin gidan malam Habu ko za ka fada min inda gidan shi yake?”

Matashin nan yace “Tab, ai war haka Nata’ala ya tafi gona, sai dai a kaika wurin”

” Don Allah ko zaka taimaka ka kaini?”

“Ba laifi muje na kaika”

Ya zauna a cikin mota mai raba da aukin kamshi yana nuna hanya har suka zo bakin gonakin, ya sauka ya kirawo Na Ta’ala. Sai gasu sun dawo tare

                

                        

“Na gode ko, Allah ya saka da alheri.” ya sa hannu a aljihu ya ciro wallet dinsa ya ciro ‘yan dubu-dubu guda biyar sabbi kar yace “ga wannan ayi aski”

Matashin nan ya zaro idanu yana kallon makudan kudin hannunsa, ai wannan sai su masa aure ya tafi yana ta godiya yana farin ciki. 

Na Ta’ala, ya dan durkusa yana fadin “Sannu yallabai, ance kana nemana sai dai ban dau fuskar ba”

Sagir ya mika masa hannu cikin fara’a yace “Assalamu alaikum”

Nata’ala ya amsa. “Ni sunana Sagir Daggash, kuma daga Abuja nazo domin muyi magana idan bazaka damu ba ko akwai wurin da zamu tattauna ba a idon mutane ba”

“To yallabai, bismillah.” nan Nata’ala ya nunawa Sagir wani gefe can suka gangara. “Kaine mijin Uwani ko?”

“Eh nine, kuna lafiya ko?”

“Alhamdulilah, sai dai ince ko komai lafiya dai da Uwanin?”

Sagir ya dan ji mamakin yanda Nata’ala ya damu ko kuma yayi tunanin wani abu ne ya samu Aneesa?

“Lafiyarta kalau, ina son sanin ko tsawon wani lokaci ka san Uwani, na fahimci kaman har yanzu tana ranka”

“A’a yallabai ba haka bane…”

“Kar kaji komai ina da dalilina na maka wannar tambayar.”

“Na san Uwani tun tana ‘yar yarinya, sannan an daura mana aure tana da shekaru goma sha uku, ta kuma yi wata shida a gidana”

“Idan bazaka damu ba, don Allah zaka iya fada min dalilin da yasa kuka rabu cikin karancin lokaci haka?” Sagir ya sa masa idanu yana ganin yanayin fuskarsa.

Sai da ya nisa ya zayyanawa Sagir labarin duk abunda ya faru tsakaninsa da Aneesa cikin takaici da da na sani yake wannan bayanin. 

“Yallabai, kanina shakikina shi yayi sanadin rabuwata da matata, ni kuwa na dau mataki cikin zafin rai da gaggawa, kaji dalilin rabuwarmu.”

“Don Allah, yallabai kar ka wulaqanta Uwani, saboda bata cancanci kaskanci a rayuwa ba, mace ce ta gari wacce al’amarin wani bai dameta ba, kyautatawa nata kuma shine a gabanta, sannan taga rayuwa kuma tayi hakuri duk da karancin shekarunta”

“Naji Na Ta’ala, na gode da bayanin da ka min ka taimaka kwarai Allah ya baka yaran da zasu maka addu’a, masu jin kai”

“Ameen, na gode. Ai ma mai dakin nawa ta samu haihuwa shekaru hudu da suka wuce”

“Ah, yayi kyau Allah ya raya su.” Sagir ya dauki kudi mai yawa ya bashi “Ga wannan a saya musu biskit” sunyi sallama sannan ya wuce. Daga nan gidan Malam Habu ya nufa.

Inna taji mamaki da yara suka shigo suka ce mata wai ga mijin Uwani a waje, da sauri ta tashi a kan sakar da takeyi ta dauki mayafi, falon Malam Habu ta bude masa tayi masa shimfidi.

“Sannu, da isowa”

“Sannu Inna, mun sameku kalau?”

“Lafiya kalau, ai yara suka shigo suka ce wai ga nan maigidan Uwani, nace anya kuwa? Amma suka dage shi yasa nace to lallai kuwa hakan ne, ikon Allah”

“Ai na zo duba wasu al’amura ne, shi yasa nace bari na karaso mu gaisa”

“ji kuwa uwani bata kira ta shaida mana kana hanya ba,”

“A’a aikin tasowa yayi shi yasa itama sai da na kama hanya na shaida mata, amma duk lafiyansu kalau”

“To yayi kyau maraba.”

Inna ta mike ta zubo masa nono da dambu, ta hado da ruwan randa mai sanyi a kofin silba ta kawo masa tace “bari na tura yara su kirawo Malam Habu a makaranta sai ku gaisa.”

“A’a ba damuwa yanzu zan wuce, zan bi makarantar kawai sai mu gaisa, itama Uwanin ina shirin idan suka samu hutun tsakiyar zango sai tazo taga gida.”

“Ayya yayi kyau Allah ya nuna mana lafiya”

“Ameen, ni zan wuce kenan”

“Da wuri-wuri haka? ko ruwa baka sha ba”

“Da yake na bar ayyuka Abujan yau nake son na koma”

“Allah ya kiyaye, hanya. Idan kaje a gaishe dasu Hajiyar duka”

Sagir ya matsa kusa da Inna ya mika mata bandir din kudi ‘yan dari biyar.” Ga wannan ban tsaya a hanya na sayi tsaraba ba”

“A’a za ayi haka, kai da kazo aiki kuma sai ka shiga dawainiya? mun gode amma ka rike ai kai matafiyi ne kafi buqatarsu”

“Inna, ku rike dai, ai mu albarkarku muke nema”

Jin hakan yasa Inna ta karba a kunyace, tana ta zuba addu’o’i, sukayi sallama ya nemi Malam Habu suka gaisa sannan ya kama hanya. Sai da ya bar garin Kunuwal yayi ajiyar Zuciya, sannan ya fito da wayoyin sa ya duba, shi ya manta fedes da cewa tun safe bai kunna su ba.

Yana kunnawa sakonni sukayi ta shigowa, amma bai samu na Aneesa ko daya ba, don haka layinta ya fara nema, amma sai ya jita a kashe. Nan ne yayi tunanin hala tana aji ne yasa ta kashe wayar. Ya kira Aadil “Hello, Sagir. Lafiya wayoyinka basu aiki tun da safe?”

“wallahi lafiya, na tafi Gombe ne amma yanzu ma ina hanyar dawowa, mantawa nayi ban kunna su ba”

“Gombe? lafiya dai?”

“Lafiya kalau, kawai wasu (personal issues) ne”

“Idan dai ka dawo ina da magana da kai.”

Sagir ya dubi agogon cikin motarsa sannan yace “To, inaga zan shigo can da yamma, kaga yanzu karfe sha daya muke nema”

“To Allah ya kaimu, kai kadai ka tafi ne?”

“Eh, malam Hassan zai kai Aneesa makaranta ni kuma ba wai na yarda da tukin Nuhu bane”

“To shi kenan sai ka iso din kenan, ka neme ni kafin ka isa gida dai”

Sagir yace “kasan dai akwai gajiya sai na huta tukun.”

“Ai, muhimmin abun dai shine ka san yanda zaka tunkari gidan, don jiya naje.”

 Sagir ya canza hannun da yake waya da ita “Me ya faru? me ya samu Aneesan?” Sagir ya fada cikin tashin hankali.

“Ba komai kana tuki, amma abun da zan fada maka kawai shine ta san maganar Ummi”

Suna gama wayar Aneesa ya sake nema, yaci sa’a kuwa sun fita tara a lokacin don haka ta kunna wayarta, itama neman nashi takeyi sai ga kiransa ya shigo.

“Hello, Aneesa?”

“Na’am, kana ina ne? ina fatan dai lafiya? Tun safe nake nemanka bana samu, hankalina ya tashi gashi munyi gwaji amma ban iya rubuta komai ba don Allah ina kake?”

“Ki kwantar da hankalin ki, nayi tafiya ne, amma ina kan hanyar dawowa kinji?”

“To, don Allah kayi hakuri ka dawo da wuri. Idan ka dawo zamuyi magana na gane laifina.”

“Kar ki damu, nima ina son na ganki, ina hanya. Nan da awa biyar in sha Allah don yanzu na kusa shiga Bauchi”

“Allah ya kiyaye maka hanya.”

Bayan sun gama magana ne Aneesa taji wani sanyi a ranta saboda bata ji alamar fushi ba a tare da muryar Sagir, maimakon haka ma wani kula ta tsinkaya daga gareshi. A darare ta zauna har akayi sauran darrusan, tana Allah-Allah ta koma gida ta shirya tarban Sagir.

                      

Iskar dada karfi takeyi, irin ruwa mai nacin nan ne, lokaci daya ya tsuge sai dai karfin shi ya ragu ya karu. Aneesa ta dubi agogon da ke makale kan siririn hannun ta yafi a kirga, yayin da take kokarin gyara jakar da ke hannunta , wanda a yanzu ya kusa zamewa daga jikin ta gaba daya, Saboda tashin hankali.

                      

“Amma ko ina Uncle Aadil ya tsaya? Yasan halin da nake ciki kuwa? Me zai sa yace na jira shi bayan ya san baya kusa?. Ga shi ba inda zan shiga na rabe kafin ruwan nan ya tsagaita! ko dai na koma cikin makarantane?” Tambayoyin da suke cikin kwanyarta kenan. 

                      

Ta daga kanta tana duban titin da kusan babu kowa sai motoci jifa-jifa da suke ficewa daga makarantar ko shigar ta. Ga ‘yan tasi amma tana jin tsoron shiga, saboda ba wai ta san gari bane sosai. Sannan wane ita ta taka cikin wannan yanayi. Ga uwa uba wani dan karen nauyin da yake dankare a zuciyar ta idan ta tuno abun da ya faru. Kai… tsaya shin ta ma san me ya faru kuwa? Me ake boye mata? Tayi saurin girgiza kan ta sai a lokacin ta kula da safa da marwan da take tayi a kan layi.

                      

Saura kiris ta juya zuwa inda ta fito dai-dai nan ne taji karar tsayuwar mota a gefen ta. Mai tuka motar yayi saurin bude mata kofar gaba, yayin da tayi saurin shigewa ciki. Sai da ta natsa ne ta goge ruwan fuskar ta sannan ta dube shi a cikin kagara amma ganin yanayin fuskarsa yasa ta dan sassauta.

                      

“kiyi hakuri da barin ki da nayi a cikin ruwa, (traffic jam) na samu kan hanyata ta zuwa nan, ina fatan dai bakiyi fushi ba?” Aadil ya fada yana kallonta ta gefen idon shi.

                      

“Uncle Aadil, banyi fushi ba fada min me ya samu  Uncle Sagir dina?”

                      

“Kar ki tada hankalinki, daga can nake yanzu, kuma Alhmadulillah. Saboda haka ki kwantar da hankalinki kinji?” ya fada yana kallonta  “Subhaanallah, duk kin jike”

                      

Aneesa sai kada kafafunta takeyi labbanta suna bari, ji takeyi kamar Aadil baya ma tafiya a motar. 

                      

“Na sani, me yasa malam Hassan bai zo dauka na ba?”

                      

“Ni nace masa ya tsaya a asibitin, tare da Kamaal koda wani abu zai taso, kuma na fi son na fada miki da kaina.”

                      

Cikin kidima ta juyo ta dube shi “Uncle Aadil ba mutuwa Sagir yayi ba kuke boye min ko?” ta dube shi da idanu masu dimbin bada tausayi, da raunana zuciyar mai kallonsu.

                      

“Sagir yana lafiya kalau da ranshi, kaman yanda na fada miki hatsarin mota kawai yayi, ya dan samu rauni amma yanzu haka na bari likitoci suna dubashi ma, sunce anjima zasu shiga dashi dakin tiyata”

                      

Ai Aneesa shiru kawai tayi, ta jingina da kujera tana zubda kwalla, don sai taji bata jin sautin kukan ma, can ta furta “Duk ni na jawo, ni nace masa yayi sauri ina son muyi magana.”

                      

Aadil ya dubeta hade da cewa “Aneesa ki daina wannan maganar, kiyi shiru addu’a zakiyi.”

                      

Ya sa hannu ya kunna na’urar duma motar, domin ya kula ta fara barin sanyi. Ya san ko ya ce subi gidanta ta canza kaya bazata amince ba don haka kai tsaye ya kaisu asibitin. A filin Adana motoci na shahararren asibitin Aadil ya tsaya.

                      

Yana tsayawa Aneesa ta balle kofar motar ta fita cikin sauri.

                      

“Aneesa!” Aadil ya kirata yana kara sauri, “ga wannan” ya mika mata lema. 

                      

“A’a ka barshi”

                      

Tare suka shiga asibitin, suna karasa shiga ciki zuciyar Aneesa na kara bugawa. A bakin kofar ta ja ta tsaya, tana tunanin ko ta shiga ne ko ta juya, wata zuciyar tace mata  “Aneesa Sagir ne fa a kwance a ciki.”

                      

Nan taji wani karfin gwiwa ta samu ta karasa ciki. Dole ta shiga ta ganshi koda kuwa bayan hakan bata san yanda zata rayu  ba, tunda dai itace sanadin abun da ya faru da shi ranar.

                                      

                        

A hankali ta bude kofar, yana kwance a kan bayan shi, da kyar yake numfashi, wasu igiyoyi da wayoyi ne a mammanne a jikin kirjinsa zuwa bayansa, wasu suna fita wasu suna shiga. na’urar gefen shi kuwa yana ta kara a hankali, amma abun da Aneesa ta gani ya girgiza ta; Wai yau Sagir Daggash ne yake kwance bayi da masaniyar me yake faruwa dashi bare ya san inda lokacinsa mai tsantsan muhimmanci a gareshi suka tafi, tabbas dan Adam ba komai bane. Ta karasa bakin gadon nashi ta zauna a bakin kujerar da ke kusa da gadon. A hankali ta dauki hannunshi daya da baya ko iya motsawa ta rike a nata lallausar hannun, hawaye sai zuba sukeyi a idanunta suna gangarowa.

“Ka yafe min uncle Sagir, duk laifina ne. ka yi min duk abun da kake so, ka daina min magana amma ka kokarta ka tashi ka warke, ina matukar bukatarka.” yanda take wannan magiyar ya taba zuciyar Aadil, har yaji shima idanuwan nasa sun ciko da hawaye. 

“Ya isa Aneesa, kar ki zargi kanki da faruwar hakan, shin baki yarda da qaddara bane? hakan Allah yasa zai faru don haka ki daina magana irin wannan addu’a zamuyi Allah ya bashi lafiya cikin gaggawa”

Aadil ya fada yana tsaye a gefenta.

Shigowar nurse ce tace ya kamata su fita waje saboda basu son wani infection ya shiga ciwon majinyacin. Hakan yasa suka fita Aneesa ta zauna a kujerar bakin kofar dakin. 

A zaune a haka take ba tare da ta motsa nan da can ba  isowar su Hajiya ne yasa tayi saurin mikewa don ta kimtsa kanta amma duk wanda ya ganta a wannan lokacin ya san ta girgiza.

“Ina wuni Hajiya?” ta fada cikin girmamawa

“lafiya, Aneesa, me nake gani haka?” Hajiya Khadija ta rike kafadun Aneesa ta zaunar da ita. “ki duba, yanzu nake son naga kin goge wadannan hawayen. Meye amfanin kukan? shin zai sa ya warke da wuri? kiyi ta addu’a sai ki ga komai yazo da sauki. “Kiyi hakuri ki zama mai juriya kinji?”

Aneesa ta yi saurin amsawa amma hawaye sun ki daina zuba.

Haka suka zauna a nan ba tare da matsawa ba, sai yin sallah. Wajen karfe tara na darene Hajiya tace “Aneesa, kinga kina bukatar hutu ya kamata ki tafi gida. Direbana yana waje. Kamaal da Aadil zasu zauna nan koda za a bukaci wani abun” bata so tafiya ba amma kuma idan Hajiya ta fadi abu ba zata iya musawa ba. 

A bayan kujerar direba ta zauna yayin da Hajiya take owners. Amma sam hankalin Aneesa baya cikin motar gaba daya, ya tafi wata uwa duniya ce daban ba abun da take tunowa sai maganarsu da Sagir da safen, yace shima yana son ganinta. 

Sun gama waya ta koma aji lafiya, bayan an tashi ne taji shiru malam Hassan bai zo ba, ta nemi Aadil sai yace ta jira shi a makarantar. Ashe tuni an musu waya kan cewa Sagir yayi hatsari tsakanin Bauchi da Jos, su kuma suna ta kokarin a taho dashi Abuja, shi yasa sai yamma Aadil ya zo daukanta. 

Da ta sake kiran Aadil taji ko lafiya taji shiru shine ya fada mata “Sagir ne, yana tahowa ya samu hatsarin mota… dauko shi… asibiti…” bata ma karasa fahimtar me yake fada ba, can taji yace “ki tsaya a makarntar zan zo na dauke ki yanzu, in sha Allah”. Shi kenan daga nan duniyarta ta juya .

A cikin motar a hankali take Addu’ar “Ya Allah ka bawa uncle Sagir dina lafiya, ka bawa uncle Sagir lafiya”

Sun bi gidanta ta dauki kaya sannan suka koma main house. Hajiya ta kawo mata abinci, amma haka ta manta yunwanta bare dandanon bakinta. Bata iya bacci ba , tana ta addu’ar samun lafiya wa Sagir, da sassafe ta bar gidan Hajiya ta nufi asibiti tare da Aisha a motar Aishan. Har yanzu bacci yakeyi, sun samu an mayar dashi wani daki daban na kula ta musamman. Likitan yace ya samu karaya a cinyar dama, sunji tsoron zubewar jini a cikin jikinsa (internal bleeding) amma sun duba babu hakan, wannan yasa suka fada musu cewa Sagir yayi sa’a sosai duba da yanayin hatsarin da yayi don ba me cewa rai ya fita a cikin motar, duk da haka zasu ci gaba da bincike don a tabbatar da cewa ba a yi kuskuren komai ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *