AL-AMARIN ZUCI CHAPTER 5 KARSHE

AL-AMARIN ZUCI




CHAPTER 5 KARSHE





Komawarsu gida da kusan Sati Inna ta kula Aneesa bata da shirin komawa sannan kuma direban da ya kawota ma ta sallameshi, hakan ya kara ankarar da Inna tun zuwan Aneesa bata kula tana waya da mijinta ba sai dai tace yana mika gaisuwa. Don haka ne ta kirata tace “Uwani, ina fata dai ba matsala kika samu ba da mai gidan naki?” +

Sai da gaban Aneesa ya fadi yaya akayi Inna ta gano ta? 3

Shirun da tayi yasa Inna ta hada daya da biyu. “Yanzu uwani ashe baki dauki duk abun da nake fada miki ba? Mutumin nan yana iyaka kokarin sa akan ki shine har zaki iya daga kafafu da sunan yaji ki bar gidansa? sannan ki shafe kwanaki ba tare da sanar da mu abun da kike ciki ba?”

“Inna ba yaji nayi ba, gidansu na koma kuma Hajiyarsa ta san nan na taho ita tace ma na zauna na huta tukun.”

“Ita Hajiyartaku tace ki zauna ki huta? Haka ake aure? Ashe baza kiyi hakuri ki zauna a dakinki ba? Mu kinga muna kokawa kowa damuwarmu ne? ko kina tsamman kowa zaman lafiya takeyi da mijinta? Wannan ai rashin hankali ne kin kwashi kafa kinje kin zube a gidansu, an fada miki ita Hajiyar bata son danta ne, da zaki budi baki kiyi ta fada mata laifinsa?”

Aneesa taji ranta ya fara baci yaya Inna zata mata fada maimakon ta goyi bayanta?

“Inna fa ni ban fada ba, itace ta dage lallai sai ta san me yake faruwa”

“Da kinyi zamanki a dakinki, akwai wanda zai san kin samu matsala da mijinki bare har a so jin meye matsalar? watakila ma war haka da kun shirya komai ya wuce”

“Inna fa baki san me ya hada mu ba, har mari na sai da yayi fa”

“Sagir din ya mareki?” hankalin Inna ya tashi amma ta danne tace “Ba dole ya mara ba, tunda ke kowace magana aka fada kina da amsarta.” 2

“Inna ke dai kawai kina goyon bayansa ne, amma yaya za ayi nayi shiru bayan yana zargin cewa wai ni da abokinsa muna soyayya.”

Inna ta sa salati ta sanar da ubangiji “Uwani! me nake ji haka? me zai bashi wannan tunanin da har zai dau mataki a kai?”

Nan Aneesa ta bata labari tun daga zuwan Mummy gidansu abun da ya faru.

“Ashsha, komai ai dan bincike ne da bin diddigi, kafin a yanke hukunci ko a zartar da tunani.” Ita dai Aneesa maimakon ta zo gaisuwa ta koma ta kara jibgawa marar lafiya damuwa. Shigowar malam Habu Inna Halima ta masa bayanin abun da a ke ciki, wannan yasa ya kira Aneesa yace “Innarki ta min bayanin komai, amma ina son ki san cewa kece kasa da mijinki, hakuri zakiyi ki koma idan yaso a dakinki sai ayi muku sulhu, amma tahowarki gida ba shi zai yi maganin matsalarki da mijinki ba, don haka kiyi hakuri ki shirya ni da kaina zan maidake sai a zauna ayi magana”

Aneesa ta hada rai tana tuno duk abun da Sagir ya fada hade da marin da ya wanka mata, nan ta tuno zaman yunwan da Innarta tayi a hannun Daddy a ladabce tace “Baba, kayi hakuri amma ni kam bazan koma gidan Sagir ba har sai ya zo da kanshi.”

STORY CONTINUES BELOW


Inna ta kama baki tace “lallai kuwa kina da aiki, da wannan taurin kan naki kike so kiyi zaman lafiya da miji? An gaya miki mu abokanan wasan ki ne? ko kuwa so kikeyi kema ki zauna ki haihu a gaban mu sunan mu ya sake baci a gari?”

“Inna naga halin rayuwa da kika fuskanta, kin kuma ban labarin wanda ban gani ba wannan yasa na dau alqawarin bazan bari na miji ya wulaqantani yanda ya faru dake ba, don haka idan har na bar gidan nan to cikin kima da daraja Sagir zai zo ya daukeni.”

Inna Halima ta zabura zata kai wa Aneesa duka malam Habu yayi saurin riketa “Halima kar ki taba ta mana, ai abun baiyi zafi haka ba sai ki illata abunda ke jikinta. Tunda tace haka sai a saurara a ga zuwan shi Sagir din.” ya juya kan Aneesa yace “Amma ina son ki san da cewa muddin nan da kwana hudu Sagir bai zo ba kafarki kafata zan maidake gidanki.” Cikin tashin hankali Aneesa ta dago kanta amma da taga bata da wani zabi sai ta amince.

Dadinta daya shine Mama tana jin abun da ya faru ta tirje kasa tace ba abunda zai sa Uwani ta koma “Ina Haliman? Wato ita har ta manta wuyar da ta ciwo wurin namiji ko to ai kuwa mudddin ina raye sai na ji dalili, haka kawai yarinyar kirki ita ayi ta wulaqanta ta. Yi zamanki Uwani naga wanda ya saki komawa a garin nan”

Hankalin Aneesa yayi matukar kwanciya jin maganar mama ko ba komai ta san zata kwatar mata ‘yancin ta, amma haka kawai Inna ta dau zafi, ita bata ga laifinta ba a wannan lamari shi yasa taji zuciyarta ta kara kissima mata jin haushin Sagir, gashi karatu yana ta wuceta. 1

Har tayi niyyar komawa gidan Mama saboda tana goyon bayanta sai kuma Mama tace mata “kiyi zaman ki a can, ni dai ina garin nan sai naji dalili ai kudi ba hauka bane, kema kina da gata wannan irin kazafi da me yayi kama?”

Hakan yasa Aneesa ta koma gidan Inna, tana shiru abunta, jira takeyi su Innan su mata maganar komawa ta tattara inata inata ta koma gidan Mama abunta, don ko baban Halima bai ce komai kan lamarin ba.

Har dai Abba ya dawo yaji abun da ya faru da farko ransa ya baci kan abun da Sagir yayi, amma sai Hajiya ta bashi hakuri tace ita ta san maganin abun.

Sagir dai yana kwance a kan kujerar falon gidanshi amma gabaki daya ba wai dadin rayuwar yakeji ba. ko ina ya duba bakin ciki ne a rayuwarsa. Ba abun da yafi damunshi irin yanda su Hajiya suka matsa masa kan maganar Aneesa, a hakikanin gaskiya shima yayi kewarta amma da zaran ya tuno furucinta na ranar sai yaji ta sane masa kwata-kwata. Ya rabu da Ummi ya saba amma ya rasa me ya sa Aneesa na nesa dashi amma yake jinta a duniyar da take kusa tamkar tana cikin jikinsa.

Idan ya tsaya tunani sai ya ga ta ina ya kuskuro, sai da ya bari ya fuskanci ko wacece Aneesa, amma hakan ya faru ko da yake wannan mai sauki ne, tunda amininshi da ya dade da saninshi ya san komai game da shi ya gagara gano cewa yana son matar da zai aura har ma ya aureta bai gano me yake ji game da ita ba, tabbas yayi babban kuskure. Sallama yaji a kofa ya mike yaje don ya duba ko waye.

Aadil ya gani a bakin kofar, lalle wannan shi a cikin marasa kunyar ma na gaban layi ne shi. Sagir bai ce komai ba ya maida kofa zai rufe, Aadil ya sa hannu ya tare. Sameeha ta fito daga bayan Aadil ganin su tare yasa ya bude musu kofar suka shigo ko kallo Aadil bai isheshi ba.

“Sameeha, sorry gidan ba mata ban san me zan kawo miki ba I hope you don’t mind” Aadil ya kalli Sameeha duka sunga yanda damuwa ta bayyana karara a tare da Sagir. Duk da dai a bayyane bai bari hakan ya nuna ba amma da ya bude baki zai yi magana zaka fahimci yana cikin kuna da bacin rai.

“Uncle Sagir meye ne yake faruwa na samu labarin cewa Aneesa bata nan”

“Ina tsamman mijinki yana da amsar komai, ko kuwa shi ya turo ki ki tamabaya masa inda rabin ranshi take?” 5

Aadil yace “Sagir, me yasa kake hakane, maganar nan gudace ka tsaya ayi ta a tsanake mu fahimci juna amma baka bada hanyar yin hakan ba. Ta yaya kake tsamanin za a warware wannan matsalar?”

STORY CONTINUES BELOW


Sagir ya gyara zaman shi hade da harde hannayensa cikin juna tamkar yana sauraren Aadil.

“Naji na gode.” ya amsa a karshe bayan Aadil ya kai aya.

Sameeha ta dubi mijinta sannan ta dubi Sagir “Uncle Sagir tabbas nice babbar silar wannan fitina da ta auku, kuma na gane kuskuren yin hakan da nayi da na rike sirrina da mijina mun zauna mun maganace wannan matsalar shin kana ga har wani zai san cewa a da Aadil ya taba son Aneesa? kar mu manta fa zuciya bata da kashi kuma ba yi da ikon juya AL’AMARIN ZUCIyarsa. Wai meye laifin Aneesa a wannan maganar? Ita da bata san hawa ba bata san sauka ba da zaka juye dukkan laifi ka daura mata? A ganina ya kamata ka kara tunani kan wannan maganar.” Aadil ya mike Sameeha ta bi bayansa suka bar Sagir a zaune, ko kala bai ce musu ba.

Suna fita Sameeha tace “Kana ganin zai sauko?”

“hmm ni na san Sagir aje-aje zai sauko sai dai kuma wannan lokacin ne ban sani ba. kar ki damu gobe zan sake masa magana kafin nan abun da kika fada masa yau hala ya masa tasiri.”

“to Allah ya kaimu”

Washegari Sagir na ofis tare da wani ma’aikacin sa “Yaya zaka yi min wannan shirmen, haka ake rubuta report, ina sauran bayanin? idan baza ka iya aikin ba akwai dubbai da suke nema, saboda haka ko ka gyara aikin ka ko kuwa na nemi wani” ya fada hade ta buga file din hannun shi a kan teburin, yana huci. shigowar Aadil ofis din ne ya sa ya sallami ma’aikacin, ya daga ido ya dubeshi. “Akan meye zaka zo kana huce haushinka akan wanda bayi da laifi?” 2

Sagir yayi kwafa “Ziyara biyu a awa ashirin? da fatan dai komai kalau”

Aadil yayi murmushi sannan ya ja kujera ya zauna “Sagir kana bani mamaki idan har na duba naga wai abu daya da bai dameka ba a rayuwa shi ne zai yi sanadin shiga tsakani na da kai”

“hmmm direct to the point ina son haka.” Sagir ya fada hade da ajiye biron hannunshi mai dauke da logon kamfaninsa.

“Wai shin kana ga da na so Aneesa wa kaina Sagir, kuma tana cikin qaddarata kasan da cewa ko saninta baza kayi ba?”

“Hakan kuwa zai fi dacewa kaga duka zaku fi fahimtar juna tunda kauye kuka fito tunaninku iri daya ne, ko kuwa?” 5

“Ai ina tsamman babu wanda tushen sa birni ne tunda haduwa akayi aka tada birnin. Maganar dai ba daga nan take ba. Maganar da nake so ka fahimta a nan itace Aneesa bata da laifi. Tabbas na so ta, amma tunda aka sanya maganar auren ku na san dole na tsayar da kaina don kai ne mutum daya a duniya da zan iya rabuwa da komai saboda tsakanin mu ya kai haka. Nayi mamaki kwarai da har zaka bari son mace ya shiga tsakani na da kai. Ka bari karamar yarinya tana juya maka tunani yanda take so bayan ka taki matsayin juya mata daban-daban a sako-sako na kasar nan dama wajen ta. Me akayi akayi Aneesa da zata shiga tsakanin Aadil da Sagir?”

Sagir ya mike a fusace ya daga hannu tamkar zai kai wa Aadil mari sai kuma ya fasa “Ya isa haka bazaka shigo har inda nake kana fada min abun da yadace ba, ko kuma wace mata ya kamata na aura, idan kana da matsala da matata wannan damuwarka ce amma ina son ka san matsayarka a kan Aneesa zan iya fada da kowa don haka ka tashi ka fita min daga ofis.” 3

Aadil yayi murmushi yace “Exactly, abun da nake so ka gane kenan Sagir, Aneesa itace rayuwarka shin kana ganin zaka iya bari wani fada kalilan tsakanin ka da tsohon aboki ya raba ka da abun son ka, jigon rayuwarka? Macen da kake tunanin ta zamo uwar ‘ya’yan ka? ni dai Sagir Mustapha Daggash da na sani ba daga nan yake ba. Don me yasa zaka bari kuskuren da kayi a rayuwa guda daya yayi ta juya al’amuran sauran rayuwarka. Idan Ummi ta yaudareka ta ci amanarka wannan ba shi yake nufi duka mata haka suka taru suka zama ba”

“Aadil bana so ka sako min maganar Ummi”

“Don me yasa baka son na sako maka maganar Ummi, ka san da cewa ta dade da tafiya a rayuwarka amma har yau ita ce matsalarka a rayuwa, me yasa kullum kake kauce magana akanta? Idan har da gaske ka wuce shafinta a rayuwa me yasa kake making decisions saboda abun da ta maka a baya? Kar ka bari ta ci galaba a kanka. Duk da ban san me ta maka ba amma na san da cewa idan baka mance ba ka ci gaba da rayuwa tabbas zata hanaka gina kyakkyawar rayuwa da iyalinka da suka fi kowa muhimmanci a gareka”

STORY CONTINUES BELOW


Sagir ya zauna jiki a sanyaye kanshi a cikin tafukan hannunsa. A cikin ransa yace “Ya Allah, me na yiwa Aneesa me zata daukeni? Na rabu da ita da karamin ciki, Allah kadai yasan me take ciki a yanzu ko a wani hali take, tsorona daya kar ta kauracewa abinci na san ba karamin aikinta bane…” dago idanunsa da yayi ya hada da na Aadil yasa, yaji tamkar an zare masa tausayin Aneesa a ransa wani fushi ya kara harzuka sa abunka da AL’AMARIN ZUCI yana huci yace “Naji abun da kace, don Allah idan bazaka damu ba ina aiki.”

Yana fada ya mike ya bude kofar ofis alamar Aadil ya fice. Ba tare da cewa komai ba Aadil ya fita daga ofis din.

Aadil yana fita Sagir ya dauki makullai da wayoyinsa ya fice daga ofis din, saboda a wannan lokacin bayi da natsuwar yin aikin ma gaba daya, komai ya ishe shi na rayuwar. Main house ya wuce bai tsaya ko ina ba sai dakin Hajiya, amma ya tadda shi a rufe.

“Yaa Sagir?”

“Aisha, ina Hajiya take?”

Aisha dai da ganin yanayin yayanta ta san yana cikin damuwa kwarai “Dazu ta fita zuwa asibiti gaisuwa.”

Shafa kansa yayi cikin damuwa ya fita ba tare da cewa komai ba, Hajiya kawai yake son ya yi magana da ita ko zai samu saukin damuwar da yake ciki. Gida ya koma yayi shirin masallaci tunda ko ya fita bai koma gida ba, sai da aka ce masa za a rufe masallacin.

Kai halin da zuciyarsa ke ciki a wannan lokacin baya ji zai iya jira har zuwa washegari ba tare da ya sata a idanu ba, domin ya rasa natsuwarsa gaba daya. Madaidaiciyar jakarsa ya dauka ya sa kaya kala uku a ciki da abubuwan da zai bukata na amfani, domin ya yanke shawara zai je ya taho da Aneesa.

Har ya daga waya ya kira Malam Hassan saboda ya shaida masa batun tafiyar sai kuma ya fasa saboda bai san iya lokacin da zai dauka ba. Kamar gari bazai waye ba yake ji, daga sallar asuba ya kama hanya.

****** **********

Tana kwance a daki duk duniya ba abun da yake mata dadi, gashi a daren jiya ta fara jin cikin jikinta ya fara motsi, duk sanda ya motsa sai ta tuna Sagir, wai shin me ya hana shi zuwa? Har yanzu fushin yake yi da ita? Yanzu ashe da gaske Sagir yakeyi yana tunanin zata iya son wani da na miji musamman abokinsa? Mamakinsa kwarai takeyi idan tana tuna kalamansa. Idan yana tunanin ya iya fushi ya tsaya tukun yaga nata kalan fushin, zai ga HUKUNCIN ‘YA MACE. Duk randa yazo ko kallon shi bazatayi ba, idan ya ga dama ya koma ba ita amma ba ruwanta dashi. Haka kawai ya hadata fada da Innarta sannan ya hanata zuwa makaranta. 5

Ita kadai sai kunkuni takeyi da zuciyarta sai ga Muhammad ya shigo da gudu cikin dakin. Yana shigowa ta tashi da niyyar yayyafa masa fada amma yace mata “Adda Uwani, ga nan Uncle Sagir yazo yana dakin bakin Baba”

Kaman a mafarki taji kanta, ta bude idanu ta lumshe alamar kawar da tunanin da ya zo mata, sai taji Muhammadu yace “Naje nace kina zuwa?”

Da sauri ta rike hannun shi tace “Kaje kace ka samu ina bacci.”

Muhammadu yaje ya dawo yace “Wai to yaji nace miki ki kunna wayarki”

Aneesa ta riko hannunshi tace “Me kace masa?”

“Cewa nayi kince kina bacci” 14

Aneesa taji kaman ta make keyarsa “wa ya ce maka haka ake aika? ka tafi kaje kayi karatunka.” Tana zaune tana auna zuwanta da zamanta ne Inna ta dago labulen dakin nata tace “Ashe ba tun dazu nake jin Muhammadu yana ta sintiri a dakin nan ba? Ko ba mijinki bane yazo? Ni zan kai masa ruwa kina kwance bayan ya taso daga nesa?”

Jin Inna zata tada hankalinta yasa Aneesa ta tashi ta dauki mayafinta ta nufi dan karamin falon Malam Habu.

Idanun Sagir suna kan kofa yana sauraron shigowarta gaba daya ya kagauta da son ganinta har yake ji da zata kara wasu mintoci bata fito ba zai iya shiga cikin gidan. 5

STORY CONTINUES BELOW


Tana shigowa ta samu wuri ta zauna, amma abun mamaki ta nemi duk abun da ta shirya fadawa Sagir ta manta don tsabar fushi da haushinsa da take ji komai ya shallake tunaninta. Taki cewa komai gudun kar garin magana ta fadi asalin abun da take ji a wannan lokacin.

“Uwanin Inna yau ko gaisuwa Uncle Sagir bazai samu bane?” 3

Aneesa ta kara hada rai ganin bata da niyyar magana yace “Da alama dai yawan yin fushina ya shafe ki, amma amin afuwa. yaya kike da baby?”

lalle ma wannan ya ma gama raina mata hankali ya dauka zai dauko kafafunsa ya cika ta da surutu sannan tace ta amince dashi ta bishi zooo kamar wata rakuma?

“Babyn ka lafiya kalau, idan ka gama zan iya shiga? Dama Inna ce ta sani kawo maka ruwa.”

Sagir shiru yayi ya koma cikin kujera yana kare mata kallo. Wannan ya nuna masa Aneesa ba yanzu zata sauko ba, amma sannu a hankali ya san zata bude cikinta. Don haka yace “to ba laifi tunda bakya son muyi magana zamu karasa idan munje gida, baki san da zuwana ba don haka zan barki ki gama kimtsawa da safe zan dawo sai mu tafi.”

Aneesa tace “oh, ni na ce maka zan bika? ina tsamman baka fahimceni ba tukun ba da kai nazo ba haka ba da kai zan koma ba don haka zaka iya tafiya”

Ta mike zata bar falon Sagir yayi saurin mikewa ya rike hannunta ba shiri ta juyo ta hadu da jikinsa.

“Tunda har na taho kina tsamman zan koma ni kadai ne? lalle yarinya har yau baki san waye Sagir ba”

Aneesa tayi kokarin kwace hannunta da ta kasa tace “Ni kuwa na san waye Sagir da abun da zai iya yi don haka bana buqatar kasancewata tare da shi.”

Murmushi yayi sannan ya riko fuskarta zuwa nashi. Ya mata abun da ya saba yi idan ya so rikitar da ita. Yana saketa ta juyar da fuskarta cikin jin haushi. “Sai da safe ki zauna cikin shiri karfe takwas ina hanya.”

Abun da ya mata ya bata haushi matuka hakan yasa ta gagara ce masa komai, haka ta koma cikin gida.

Bata cewa Inna komai ba har sai bayan isha ana zaune ana hira a tsakar gida, Inna tace “Ni Uwani banga kin gama shiri ba, Malam yace sunyi da maigidan ki zaku koma da safe ko”

Aneesa tace “Inna fa ba haka mukayi dashi ba”

Inna Halima ta fusata tace “Sagir din ne zai yi karya ko malam? Bana son shashanci idan zaki mike ki je ki karasa shiryawa gwamma kin mike idan ba haka ba kuwa gobe yana zuwa ko da kayan jikin ki ne kawai haka zaki bishi ku tafi. Kaji min shirmen banza.” 2

Jiki a sanyaye Aneesa ta shiga daki ta fara hada kayanta, can kuma ta wurga zani a akwatin ta zauna ta sa kuka, sai da tayi son ranta sannan ta hakura don kanta. Sannan su Inna ko su dan hora shi suce sai daga baya zata koma, amma daga zuwan shi harda amincewa ta bishi, gobe kam likida ta zai yi da duka tunda yaga ba a daukar mata fansa, dadin karawa kuma ta rasa me yasa Sagir yake dawainiya da rayuwarta? Idan tana tare dashi taji babu wanda ya kaita sa’a idan ta rasa shi taji babu wanda ya kaita asara.

Gashi Falmata tayi mata nisa da taje sunyi shawara, da sassafe ta faki idon Inna ta hada duk abunda zata bukata ta fice daga gidan bata tsaya a ko ina ba sai wurin da ya zame mata abokin hira lokacin da abokai suka mata karanci, wurin da ta kan samu kwanciyar hankali da nishadi, sai dai kuma tana isa wurin ba abin da ta tuna illa zuwanta da Uncle Sagir inda ya lallabata saboda ta bishi su koma. Ya zauna a bakin gaba a lokacin, Rafin kukanta ke nan. Nan tayi zamanta a gindin wata bishiya, me yasa duk inda taje a rayuwarta sai Uncle Sagir ya bita ne? Nan ta zauna ta bude jakarta, idan taji lokacin sallah ta bude jakarta ta fito da abin sallah, ta debi ruwa tayi alwala, idan ta ji yunwa kuwa daman da guzurin biredinta. Ta gama shirya plan dinta tsab cikin dare, don da ta koma da Uncle Sagir ya dake ta ko ya zage ta ya kala mata son abokinsa gwamma ta zauna a rafin Kukanta. 2

STORY CONTINUES BELOW


Karfe takwas a Kunuwal yayi wa Sagir, kai tsaye ya yi sallama gidan malam Habu. Kasancewar Inna ta san da zuwanshi ta tanada masa abun karyawa Amina ta kai masa, sai dai fa hankalin Inna ne ya tashi da ta shiga daki bata ga Aneesa ba. Ta duba bayi nan ma babu ita ba labari, don haka tayi tunanin tana gidan mama.

Sai da suka gaisa da Sagir ne tace “Ina ga Uwanin tana gidan Mama na sa Amina ta kirata.”

“Ah, ba komai Inna zan karasa can saboda ta can na gaida su maman.”

“To ba laifi, sai kun dawo.”

Sai dai abu mai daure kai canma da yaje su mama sukace basu ga Aneesa ba tun wayewar garin yau. Da Inna ta samu labari sai abun ya dameta “To ina Uwani zata je? Ke Amina je gidansu Falmata ki duba Adda Uwani, kice mata maza-maza ta taho nan mai gidanta ya zo.”

Suna zaman jira ne sai ga Amina ta dawo tana haki “Inna wai inji Innar Falmata wai itama bata je gidansu ba”

Inna ta kama haba cikin damuwa “Yau ina Uwani ta shiga zata jawo min magana, ban san wani irin taurin kai bane yake damun yarinyar nan.”

Hankalin Sagir ya fara tashi ganin duk inda ya dace a je neman Uwani anje ba a sameta ba.

Wasa wasa har yamma ba labarin Uwani, don haka Malam Habu yaje ya samu mai gari ya fada masa abun da ake ciki, nan ne yace zai sa yara su dubata.

Aneesa kuwa tana ganin yamma ya kawo kai ta san cewa zama a rafin kukanta ya kare dole ta nemi wurin kwana. Don ta san har yanzu sarkin nacin nan bai tafi ba. Kai tsaye ta san inda zata je kuma ba wanda zai neme ta a can, ta kama hanya fuskarta a lullube bata tsaya ko ina ba sai gidan Fatu kanwar Na Ta’ala. 3

Hankalinsu Inna kam yanzu ya gama tashi, saboda harda Sagir a yawon nema amma sam ba sa’a, don haka malam Habu ya same shi yace “Ina ga ya kamata, kaje haka ka huta zuwa safiya mu san abunyi in sha Allah. Tunda mai gari ya sani to in sha Allah za a sameta cikin gaggawa” 2

Sagir ai baya jin zai iya barin Kunuwal ba Aneesa don hankalinshi dubu ya tashi , Ina zata je? Duk ni na jawo, girman laifina yasa ta gujeni har ta gwammace tasa Innarta a damuwa saboda ni. saboda bata son ta bini mu koma. Please Aneesa where are you?” Nan abun ya fado masa, rafin Kukanta, yes!

Tana ganin kafa ya lafa gari ya soma shiru, nan ne tsoro ya kamata, a hankali ta lallaba tana tafiya ba abunda take tunani sai irin abun da yake faruwa a gida, don tunda take bata taba guduwa ba sai yau.

Fatu na daya daga cikin mutanen da suka goyi bayanta lokacin gurminta da Na Ta’ala har ta so ganar dashi amma yaki saurarenta. Aneesa ta san mijin Fatu matukin mota ne saboda haka ba ko yaushe bane yake gari, don haka fatan ta daya shine ya kasance yau ma baya gari. A sace ta shiga cikin gidan

Motsi taji ta leko tana cewa “Waye ne?”

Aneesa ta bude lullubin da tayi wa fuskarta, Fatu tana ganinta ta zaro idanu. Ta sake rage su sannan tace “Waye kaman Uwanin Inna?”

Aneesa ta gyada mata kai gami da rage murya tace “Fatu nice”

A razane Fatu ta saki labulen dakinta ta fito tsakar gida “Lafiya na ganki cikin dare? yaushe kika zo?”

“Fatu taimakon ki nake nema”

Fatu ta dubeta cike da mamaki, yanda ta samu labarin Uwani ta zama babbar mutum wani taimako zata nema a wurinta yanzu?

“fada min Uwani wani taimako zan miki? don idan bai fi karfina ba zan miki in sha Allah, lokacin da ya kamata na taimake ki ban taimake ki ba.”

Nan Aneesa tace so takeyi ta bata makwanci. kuma kar kowa ya sani.

“”Gidan Inna fa?”

“Ina cikin wata damuwa Fatu da ba inda zan tsira sai nan, ba wanda zai yi tunanin zuwa nan ya nemeni.”

STORY CONTINUES BELOW


“To shikenan, ba komai, bari na miki shimfidi.”

Aneesa tayi ajiyar zuciya sai dai Sagir ya tattara muguntar shi ya koma amma bazata bishi ba.

Yana zuwa zuciyarsa ce ta kame saboda bai ga abun da yake tsammani ba, don kuwa wayam ya samu wurin, sai dai yaga wani abu a dunkule a gindin bishiya, da taimakon hasken da ke hannunshi ya haska sai ya ga sallaya ce nadaddiya. Ajiyar zuciya yayi “Alhamdulillah, Aneesa me yasa kike bani wahala?” Sai dai ya duba ko ina bai sameta ba. Don haka ya koma gidan Malam Habu a falon yayi zamanshi da niyyar asuba na fari can zai koma yasan zata je neman kayanta da ta bari.

Ai kuwa sai da hankalinta ya kwanta ne ta tuno da kayanta da ta bari a gindin bishiya, abubuwanta da dama suna ciki, sai dai yanzu dare yayi sai da asuban fari zata je ta dauko kafin ta san abin yi.

Tana sallah tace “Fatu ba abinda zance miki sai godiya, baki san irin taimako na da kikayi ba, Allah ya biyaki” 1

“Ameen, ai Uwani munyi zaman mutumci dake, kar ki fadi haka. Amma don Allah zan san me yasa kika bar gida har su inna bakya son ta san inda kike?”

“Hmm, ke dai kawai wasu matsaloline na samu yanzu shine suka matsa min wai sai dai na koma ni kuma bazan iya ba.”

“To, ai wannan babban magana ce, ki tsaya mana a warware koma menene amma guduwa ba shi bane, ina zaki je idan kin gudu? Dole ki koma gida ki fuskanci komai.” nan ta tuno abunda ta fadawa Sameeha kenan da ta samu matsala da Daddy.

“Tawa matsalar daban ce, bazan bari nayi irin rayuwar da Inna tayi ba Fatu.” 1

“To amma ni kuwa sai nake ga kamar ke kike sa kanki a wannan halin, yanzu kina wahalar da kanki ga ciki a jikinki, ina zaki shiga wanda ya wuce ki komawa mutanen da suka fi kowa kaunarki, kowa da kika gani hakuri yakeyi sai dai na wani yafi na wani.”

Aneesa dai jin Fatu takeyi “Na gode Fatu, Allah ya saka da alheri. Sai kin ganni in sha Allah idan komai ya daidaita” 2

“Don Allah ki koma gida Uwani, na san da mijinki ne kika samu matsala ko?”

Aneesa taji mamakin yanda fatu ta dago ta “ke kam ki bar maganar kawai.”

“Allah yana son ki, don yanda Nata’ala ya ban labarin mutumin na san haka, ya fada min yanda ya damu da al’amarinki sosai. Hakan yasa yace ya san zai kula da ke sosai.”

Fatu bata san me take fada ba sannan bata san matsalarta ba, mutumin da yake son ka ne zai fadi abubuwa a kanka wanda basu dace ba? “Shi kenan zan duba maganarki, ni na wuce”

Nan sukayi sallama ta koma rafin saboda ta kwaso abubuwanta tayi zamanta a wurin ta san zuwa yamma zai koma idan bai sameta ba, tunda lokacinsa na da matukar muhimmanci a kamfaninsa. Tana isa gindin bishiyar ta sunkuya zata dau jakarta sai ta ga wayam, ta juya bayan bishiyar nan ma bata ga komai ba sai hankalinta ya tashi, wa yazo nan cikin dare ya dauke mata abubuwanta?

“Wannan kike nema?”

Muryar da taji ne ya matukar razana ta ta juyo tana kallon shi, jikinta na rawa tamkar taga zaki. “Uncle Sagir?”

“Kina tsamman akwai inda zaki shiga a garin nan na gagara samoki ne?”

“Ni ba guduwa nayi ba” Ta fada a dake tare da dauke fuskarta. Ga wani dan karen sanyin da ake zubawa.

“To idan ba guduwa kikayi ba, ki zo mu tafi. Don na gaji gida nake son na koma”

cikin haushi ta kalleshi “oh ka daina yawo a jirgin ne yanzu?” 3

“Tunda ina tare da sarauniya kam ai sai yanda tace za ayi, idan bata son shatar jirgi ai dole na na hakura.”

“Na zaci saboda zaka iya ne ya sa kake yawo a jirgi me ya canza? Ni bazan bika ba”

STORY CONTINUES BELOW


“Kiyi hakuri ki zo mu tafi, kin san kin gajiyar dani jiya ba wanda yayi bacci a gida, Inna ma jiranki takeyi don haka kizo muje ta gama miki fada mu tafi.” 10

Idanu ta zare a hankali tace “Mugu!” 9

“Me kika ce?”

“Babu, ni fa ba inda zan bika muje, gwamma ka kama hanya ka tafi.”

“Duk abun da zaki ce dai ki bari sai munje gidan Inna tukun.”

Ta dago idanunta dasuka kumbura sukayi ja sannan tace “oh saboda ka samu masu tayaka fada ko? Ai na san ba abun da zai gagari the rich SD, haka nan rayuwar kowa a matsayin wasa take a wurinka, saboda haka ba amfanin ja da kai a wannan maganar”

“Naji kawo hannunki” Hararar sa tayi sannan ta juya idanunta.

Ya sabi jakar tata, sai dai jinta yayi kamar dutse tsabar cika ta da akayi da kaya, ya dubeta ‘yar ficila da ita “yaya akayi kika dauki jakar nan bata ka dake ba?”

Ko kulashi bata yi ba suka ci gaba da tafiya; tayi gaba yana bin bayanta, sai surutu yakeyi “Na fada miki ki bar daukan abu mai nauyi shine zaki kinkimi wannan jakar ki tafi da ita har rabin gari ko?” Bata ce masa komai ba sai tafiya sukeyi amma kafin ya ankara tayi wani wurin ta bace masa. Hannu yasa a goshi cikin damuwa. 3

Aneesa bata tsaya ko ina ba sai gidan mama, “Uwani ina kika shiga tun jiya kin daga hankalin kowa?”

“Mama guduwa nayi” 2

Salati Mama ta sa tana taba hannu, “Uwani guduwa fa kika ce?”

“Ni dai Mama da na koma gidan sa sai dai ku kasheni, amma ba inda zan je. Mugu ne kasheni zai yi wataran” 5

Ai ko nan da nan hankalin mama ya tashi ta jawo Aneesa jiki “ki kwantar da hankalin ki, Uwani. Ba inda zaki je kiyi zaman ki a nan bari shi Sangirun ya zo ya same ni haka kawai zai halaka miki rayuwa? an fada masa mu bamu son ki ne? Duk Halima ce ta biye masa” 4

Nan ta sha zamanta ta manta da anyi ruwan Sagir bare ma kuma ta san da shi a cikin garin Kunuwal, da azahar sai ga Inna ta sabo gyalenta, tun daga kofa take sababi “Ina uwanin yau sai ta gwada min wanda ta haifeta tunda ni ban isa ba.”

Mama ta tari numfashin ta “A’a dakata Halima, meye kike ta wani tada jijiyoyin wuya?”

Inna dai ko daki bata karasa ba nan bakin tabarma ta dire, Aneesa ko na daki taki fitowa saboda ta san Inna zata tusa ta a gaba. “yanzu ke kin gwammace, ‘yar ki tayi ta rayuwar wuya, irin wanda kika ciwo a gidan mijinki na da? To bari na fada miki ba inda zataje. Idan kuma dole ne to sai ya zo ya dauketa a gabana na gani. Kaji min kokari dai, haka kawai yarinya da juna biyu ya kama lillisa mata mari kaman an aiko shi? Har yau fuskar fa bata sabe ba.” 12

Inna idanu kawai ta zuba kan tsohuwarta tasan tana biyewa Uwani ne kawai, har zata sa suji kunya yanzu wani abun zata je ta fada masa fisabilillahi?

“Mama, don Allah kiyi hakuri, ai bamu ce bai yi kuskure ba amma tunda ya gane har yazo don tafiya da matarsa ai inaga bamu masa adalci ba idan munce bazai dauke ta ba.”

“Oh, so kikeyi mu masa adalci shi ya tozarta mu ko? idan yaje ya mata lahanin da yafi wannan fa? Ba inda zata koma, wani irin miji ne zai daki fuskar matarsa?” 2

Haka Inna tana ji, Mama ta gama bayanai kala-kala akan ita ba inda Uwani zata je, don haka ta koma gida ta fadawa Malam Habu yanda sukayi.

Hakuri ya bawa Sagir yace yaje ya huta, zasu shawo kan komai zuwa yamma in sha Allah duk yanda ake ciki da safe sai yazo ya dauki matarsa kafin nan sun mata nasiha.

Sagir yana mamakin kafiya irin ta Aneesa, yanzu a yanda taken nan duk taje tana wahalar da kanta, bata ma zauna ta huta wa ranta ba wai duk don tana gudun shi. Shin zai sake samun wuri a ranta bayan furucin da yayi mata?

STORY CONTINUES BELOW


Wunin ranar ne ya kunna wayoyinsa, haka yayi ta fama da jama’a amma sam hankalinsa baya jikinsa, yana gidanshi na Gombe don ya huta amma ya gagara sukuni, bare ya saurari wayewar gari. Gashi har dare Malam Habu bai neme shi a waya ba, don gajiya na tare dashi ne yasa yana wanka bacci ya daukeshi, amma can cikin dare ya farka, tunanin Aneesa ya hanashi sukuni. Alwala ya shiga yayi sannan ya soma nafilfilu. 1

Musamman Malam Habu ya tafi gidan Baba, domin dai wannan maganar sai ya gwada sa baki a ciki idan dai ta Mama ne to Aneesa tayi bye bye da gidan Sagir sai ko idan ita ce tayi amanna tana so ta koma. Tana jin sallamar, malam Habu ta gyara mayafinta tace da Aneesa “Uwani koma ciki.”

Ai kaman dama jira takeyi ya iso tayi wuf ta mike. Bayan sun gaisane Malam Habu cikin tattausar murya ya bawa mama hakuri, akan duk abun da ya faru ya wuce tayi hakuri ta bar Aneesa.

Cikin irin jin nauyin dake tsakanin surukai ba don ta so ba mama tace “Shi kenan tunda kace, amma dai ina son ya barta ta huta tukun sannan ya dauke ta, sannan idan ya zo ina son ganinsa.”

“To ba komai, Mama Allah ya kara girma, in sha Allah zamuyi waya. Ina ita Uwanin?”

Sumui sumui ta fito daga daki, ta gaishe shi, ganin haka Mama ta mike ta basu wuri. Wannan ne karo na farko da ta ga bacin ran Malam Habu sosai “Yanzu Uwani ashe haka kike da kafiya da son zuciya?”

Shiru tayi tana wurli-wurli da idanu. “Abun da bai kai ya kawo ba, kin tada hankalin kowa da kowa saboda wani dalili naki na daban? Kin azalzali ran innarki tana cikin bacin rai don haka nake son ki zabi abun da kika ga ya dace, domin dai muddin kika kashe aurenki to sai dai ki nemi wani wurin zuwa ba gidana ba, don bazan bari ki saka Halima cikin wani kunci ba a rayuwa.”

Kuka takeyi sharbe sharbe har da majina yana gamawa ya kama hanya ya tafi. Haka dai ta kwana cikin juyi sai wani sarawa da taji kanta na yi.

Ai kuwa da safe tara bai rufa ba sai ga Sagir a gidan saboda ya samu sammacin Mama, tabarmanta sabuwa ta shimfida masa ta bashi abun kari mai kyau sannan ta zauna, Uwani na zaune a kan kujerar tsugunno dake bakin kofar dakin Mama, banda kunkuni ba abun da takeyi, ita a dole mai fushi.

“Kai malam Sangiru haka akeyi ne? kuma daga baka kawata sai kaje kana bata wahala don kishi ya maka yawa?” 10

Jikin Sagir a sanyaye yace “Mama, tabbas anyi kuskure kuma an samu sabani sosai, amma dai kam in sha Allah hakan bazai kuma faruwa ba. Kin san AL’AMARIN ZUCI mutum baya iya juyasa sai bayan ya aikata yake da na sani, amma na miki alkawari in sha Allah bazaki kuma jin makamancin hakan ya sake faruwa ba.”

Mama ta nisa sannan tace “To, naji dadin hakan, don ta ni kam da yanda ka ga Uwani to haka zaka juya ka tafi bazan baka ita ba. Amma yanzun ma bazan amince ba sai kunyi magana ta yarda da bakinta sannan.”

Sagir dai mamakin karfin halin tsohuwar yakeyi, amma sai yaji ta burgeshi. Daki ta ce su shiga su tattauna, Aneesa ranta a cunkushe ta kare masa kallo sai shine ya soma magana.

“Anee, ban san ta inda zan fara ba. Na san duk abun da zance yanzu bazai miki wani tasiri ba kasancewar kina cikin hali na fushi. Kin cancanci kiyi fushi dani, amma ina son ki san cewa na amince da kuskure na, kuma hakan bazai sake faruwa ba da yardar Allah. kiyi hakuri ki bini mu tafi.” 2

Kanta na kasa har ya gama, ba tare da ta tankawa batun sa ba. Sai da yayi shiru tace “Ina son ka san zan bika ne saboda abubuwa guda biyu, na farko nayi alwqawari wa Hajiya cewa zan koma idan naga jikin Inna ya lafa. sannan na biyu kuma na kudurta a raina bazan sake barin Inna ta shiga wani kunci ba idan har ina da ikon kawar da hakan, idan banda haka ba inda zanje. Sannan abu na karshe bazan bika ba sai ka amince da sharadi guda” 2

Sagir yayi shiru shi dai yau yana ganin ikon Allah “Naji ina saurarenki, menene sharadin? kusan cikin zakuwa yake tambayar, don ba abunda yafi masa dadi a maganarta illa ta amince zata bishi.

STORY CONTINUES BELOW


“Duk randa ka sake daga hannu ka taba lafiyar jiki na ko Abuja ka kawo Kunuwal bazan bika ba, na dawo kenan” 15

“Na amince, amin afuwa wancan ma idanu na ne suka rufe…”

Dakatar dashi tayi tace “Mu tafi kan na canza ra’ayi na” 9

“To rankishi dade” 10

Ya fito ya samu Mama a fafarandar ta, gefe ya samu ya zauna, sai ga Aneesa ta fito da mayafinta tace “Mama na amince zan bishi mu tafi.”

Mama ta kama baki cikin al’ajabi, “Ke dadi miji ko? To Allah ya sauke ku lafiya, nan gaba ki nemi gidan zuwa, daga zuwanshi har ya miki dadin baki zaki tafi ki barni.” 5

Sagir yace “Mama, gani dai a zaune ki daina min bakin ciki mana, bayan ke baki taho ba sai kuma ki hana ta tafiya?” 4

“Ku dai kuka jiyo, Allah ya raka taki gona.”

Aneesa dai jin su takeyi batare da ta tanka ba. Sagir ya sallami Mama sannan suka wuce gidan Inna tare da Aneesa.

Suna zuwa cikin gida Inna ta dauko muciya ta bita dashi, Malam Habu yace “Halima kyaleta, ba ta dawo ba me ya saura kuma? Ina shekaran jiya wuni kikayi kukan rashinta?” 4

Inna na tsuma ta hau Aneesa da balbalin bala’i. Ta mata fada har ta gode Allah sannan ta bawa Malam Habu fage, shima dai jan kunnen ta yayi akan duk rintsi kar su kara ganin ta zo gida saboda wani rikici tsakaninta da mijinta.

Tana ji tana gani Sagir ya rabata da gida, Allah kadai ya san me ya tanada mata idan ta koma, a mota suka tafi bata cewa uhm ko uhm-uhm bai nemi ya isheta da surutu ba. Ko sun tsaya cin abinci sama-sama ta taba ya nemi ya mata magana ta hade rai, haka dai yayi shiru suka ci gaba da tafiya.

Suna isa ta haura dakinta ta karkade kura ta wanke bandaki sannan ta shiga wanka. Sai da ta kammala shirinta sannan ta sauka zuwa kicin, tana kokarin hada abinci ne ya shigo kicin din ya sameta, “Yanzu duk gajiyar hanya da kika dauko me zai sa ki shiga kicin?”

Bata ce masa komai ba ta ci gaba da aikin ta zuwa yayi ya kashe gas cooker din ya riko hannunta “Magana nake miki, kuma idan ina magana saurarona akeyi saboda haka ki saurareni.” 6

Duk da cikin tsattsaurar murya Sagir yayi maganar amma Aneesa tayi kwafa tace “Don kowa yana sauraronka sai kayi tsammani nima zan saurareka? Kar ka manta kudi fa ba shi bane kiman dan adam.”

“kina stressing kanki, na fada miki ki kwantar da hankalinki. Yanzu ba lokacin da zamuyi magana bane”

“Ni bance maka zanyi magana da kai ba, kalen ka min mummunar fassara?”

Aneesa ta sa kai ta bar kicin din, Sagir yayi ajiyar zuciya yana binta da idanu. Tana barin kicin din daki ta koma ta kama sana’ar kuka, ga wani matsanancin ciwon kai dake addabarta kwanaki hudu kenan a jere. A daddafe ta sauko kasa wurin da suke ajiye magunguna saboda ta samu ta sha ko zata ji saukin juyawar da kanta ke yi. Tana tsakiyar falon Sagir ne taji wani jiri ya kwasheta, ba shiri ta zube kasa. Ta dauki kusan minti ashirin a gurin kafin Sagir ya zo kashe wuta, nan ya sameta a zube. Hankalinsa ne yayi mummunar tashi

“Inna lillahi wa inna ilaihirraji’un, Aneesa!” ya fada yana taba kuncinta, amma bata motsa ba. Da sauri ya nemi ruwa ya watsa mata a fuska, wayarsa kawai ya dauka da makullin mota ya zuba a aljihu sannan ya dauko hijabinta ya zura mata, ba tare da ya jira ta karasa farfadowa ba ya sunkumeta sai mota.

Kallon likitan yakeyi kamar wanda ya rikide zuwa fatalwa, “Yanzu likita kana so kace min jinin Aneesa ne ya hau sosai har ya haddasa mata faduwa?”

“Eh, kwarai kuwa. An yi sa’a ma da bai taba dan cikinta ba kasancewar bayi da kwari sosai yanzu. Saboda haka sai an kula sosai. Yanzu mun saka mata ruwan allura a cikin drip dinta, zuwa safiya dai zata samu isasshen hutu sannan mu sake gwadawa mu gani. Ina sa rai magungunan da na bata zasu saukar da BP din.” 2

Hannu bibbiyu Sagir ya sa ya dafe kanshi cikin dimuwa yanzu shi ya haddasawa Aneesa hawan jini? Wai me yake tunani ne da har zai iya cutar da dan adam haka, bayan kasancewarta mutum ma macen da yafi so bayaga Hajiyarsa?

Shi ya kwana a kanta, ga gajiya shima da yake fama dashi amma haka ya mance da tashi gajiyar, fatansa Allah ya bawa Aneesansa lafiya.

Da safe sai ga wayar Hajiya, Sagir ya daga suka gaisa. Hajiya tace “Kana lafiya?

“Lafiya, alhamdulillah.” ya fada a raunane.

Hajiya taso ta karanci damuwa a muryarsa amma tasan ba a rabe dayan biyu, yanzu haka baya wuce kan maganar Aneesa ne.

“yanzu Sagir fi sabilillah, ashe bazaka hakura da fushin kan nan ka dauko yarinyar nan ba, gashi lokacin awunta na karatowa ta samu kula ta musamman, amma ka zauna sai fushi kakeyi na wofi wanda bansan ka dashi ba. Ka ga hakan da kakeyi ya dace kenan?”

Sagir yayi ajiyar zuciya yau kam bai san yanda zasu karke da Hajiya ba, “Hajiya ai na daukota jiya da dare muka shigo gari.”

“Ah to abu yayi kyau, sai dai na san tana cikin wahala ga gajiyar hanya, me zai hana ka kawota nan ta dan kwana biyu kafin nan ta karasa warwarewa sai ta dawo”

“Ai hajiya gamu nan a asibiti ma bata ji dadi ba, tun jiya likita ya bata gado amma dai da sauki.”

Cikin damuwa Hajiya tace “Aneesan take asibiti tun jiya, shine sai yanzu da na kira zaka fada min? Wai kai me kake shirin dawowa ne Sagir? ” HAjiya ta ja tsaki domin bazata tsaya bata lokacinta a kan Sagir ba, domin taga alama ya riga yayi nisa, cikin hanzari ta shirya ta sa direba ya kaita asibitin da su Sagir din suke zuwa. 2

Ai tun kafin ta iso ya shaidawa likitan baya son kowa ya san abun da yake damun Aneesa.

“Gaskiya, kana ban mamaki, kaga yanda fuskar yarinya ta canza a dare daya kacal wai shine zaka ce da sauki?”

“Hajiya kiyi hakuri cikin dare muka taho asibitin, na zaci ma duba ta kawai likitan zaiyi to sai yace, bata da karfi sosai shi yasa ya daura mata ruwa.”

can sai ga Aisha ta taho da abinci zuwa lokacin Aneesa ta tashi daga baccin da ta kwana tana yi. Da ikon Allah ciwon kan ya daina, sai tsamin jiki. Batayi mamakin ganinta a asibiti ba saboda ta san azabar da ta sha a jiyan. Ta yunkura zata gaida Hajiya da Abba da ya iso a lokacin ne Hajiya tayi saurin kwantar da ita.

“Sannu, ki rinka yi a hankali kinji ko?”

Kai ta gyada sannan suka gaisa. Likitan ya shigo ya sake dubata, nan ne ya shaida musu zuwa yamma zata iya komawa gida matukar zata samu isasshen hutu, amma kafin nan sai ta karasa drip din da ya daura mata da safen.

Daddy ya iso asibitin bayan Sagir ya shaida masa Aneesa na kwance, sai da suka rage su biyu a dakin yake cewa “Aneesa, wato abun da yake faruwa shine banda labari? Ashe idan kina da matsala bazaki sameni ba?” cikin jin nauyi tace “Daddy fa ba haka bane.”

“To yaya ne? Sameeha ta fada min komai ai. Daga yau duk wani abun da zai tashi maza maza ki fadi damuwarki kar ki kara cewa zaki tafi.”

Kai ta daga masa kawai tana shiru.

Sagir kuwa yana ta sunne kai, tsoron kar a gano karyarsa. Jin Hajiya tana ta bawa Aneesa shawarwarin da ya kamata tabi tunda ga halin da take ciki yasa hankalinsa ya kwanta. Banda sintiri ba abunda yakeyi har zuwa dare aka sallamesu.

Suna shirin fita daga dakin ne, Hajiya tace “Ai ina ganin tunda ga yanayin jikin nata, me zai hana ta koma Main house ta dan kara murmurewa kafin nan?”

Sagir yana tunanin abun fada ne yaji Hajiya tace “Aisha, saka jakarta a motar Jibrila, kice su shirya komai da kyau.” Aisha ta amshi ‘yar jakar da ta je ta shiryowa Aneesa, tayi waje da ita. Aneesa ko dadi fal ne a ranta ganin Hajiya tace ta koma wurinsu. Saboda ko yawan shigowarsa dakin da take a asibitin ma haushinsa yake kara mata duk da tana jin tausayin yanda ya kwazarbabi kansa ya damu da ciwonta amma haushinsa da take ji sai ya rinjayi tausayin, saboda haka tamkar ta zuba ruwa a kasa tasha taji da Hajiya ta saka ta a motar gidan Abba sukayi gaba. 5

Sagir dai cikin sanyin jiki aka barshi, yanzu yana tare da Aneesan ma yana samun matsala wurin shawo kanta bare an sake nesanta su kam ai sai ta Allah. Ba yanda ya iya Hajiya ta riga tayi magana. yana ji yana gani suka tafi masa da mata ba yanda ya iya, amma ta wani bangaren suna da gaskiya, don ciwonta ya tsorata shi, idan nisantarsa zai sa ta murmure to zai daure har sai randa ta sauko su fahimci juna.Sagir ya tafi ofis, Aisha da Aneesa suka je suka dauki kayanta, ta hada kayanta sosai a babban akwati ta kwashi takardun da zata bukata. Sannan sukayi gaba, Sagir kuwa tun safe ya rasa me daya yake masa dadi. +

Komawarta da kwana biyu Sagir ya je makaratarsu, yayi magana da principal a kan Aneesa kasancewar hukumar makarantar sUn san da aurenta, gashi tana fama da laulayi hakan ya sa yace zata bar zuwa har sai lokacin jarabawa ya karato tazo ta zana.

Lesson teacher ya sama mata, tana zuwa har main house suyi karatu.

Hajiya da kanta ta sa Aneesa a mota suka wuce asibiti ta mata booking antenatal. Aneesa ba abun da yafi mata haka kwanciyar hankali.

Washegarin randa suka dawo daga asibiti ne Sagir ya shiga dakin Hajiya, nan ya sameta tana kwance tana jin shigowar Sagir dakin amma tayi kaman tayi bacci don haka ya kyaleta.

Kullum Sagir sai yazo gidan da dare a nan yake hira sannan ya koma gida amma ko fuska baya samu a wurin Hajiya bare ya samu ganin Aneesa, kullum suna manne bare ya samu ya mata magana. An dauki sati a haka, wannan yasa Sagir ya samu Abba.

“Abba daman maganar Aneesa ne, tunda na ga ta dan samu karfin jikinta batun komawarta gida” Duk sabon shi da sakewarsa da Abba ta maza kawai yayi ya yi magana. 2

Abba yayi kamar bai fahimce shi ba “Ah, har sun gama jarabawar ne?”

Sagir yayi tunanin daman wai suna shirin rike masa mata har sai tayi jarabawa ne? 2

“Abba jarrabawa kuma?”

“Ka san a wannan yanayin nata tana bukatar hutu sannan ga karatu a gabanta, duk da akwai mai tayata aiki idan ta koma ina ga stress zai mata yawa, saboda haka inaga ka dan kara barinta a nan ta kara hutawa.” 7

Cikin jin nauyi Sagir yace “To shi kenan Abba.”

Ya kula kaman wani hadin baki sukayi masa ga uwa uba kwata-kwata wayar Aneesa a kashe ya rasa me yake masa dadi.

Ranar ya gaisa da Hajiya a daki fitowarsa falonta ya samu Aneesa ita kadai ce a nan tana karatu don haka yayi tunanin amfani da wannan damar don ya mata magana, amma cikin ikon Allah ya zauna kenan sai Hajiya ta sa baki ta kira Aneesa wai ta tayata sa kaya a wardrobe, ran Sagir ya baci ita da tazo hutawa bata da lafiya kuma wani aiki kuma za a sakata, sannan mutum da matarsa an haramta musu ko da magana ne bare su kebe. Haka ya mike ya bar gidan jiki ba kwari. 8

Randa Aneesa ta cika sati biyu a main house ne Sagir ya yanke abun yi don ya kula idan ba ya dau mataki ba abubuwan sa gaba daya zasu daina ci gaba, don yanzu haka ma ya daga tafiya zuwa kasashe biyu saboda rashin sanin madafa. 4

Aneesa ta gama hira da su Aisha da Hajiya ranar Kamaal ma yana gida sai wajen karfe goma tace musu sai da safe.

Shigarta bangarenta taji mamaki kasancewar a kashe ta bar wutan cikin daki gashi kuma ta same shi a kunne. Don haka sai ta bari akan ta manta ne bata kashe ba ta fita. Ta nufi jikin wardrobe don daukar kayan baccinta ne sukayi ido hudu dashi, da sauri taja da baya tsabar tsoron da taji.

STORY CONTINUES BELOW


“Subhaanallah. Ka ban tsoro, me kakeyi a nan baka tafi ba?” 3

“Yaya za ayi na tafi matata tana nan.” Ya fada yana duba wani littafinta da ya dauka a durowar gefen gado.

“Idan su Hajiya suka san kana nan…”

Nan ne ya dago kan shi yana dubanta “wai me kika fadawa Hajiya ne take goyon bayan ki haka, me yasa baza kiyi hakuri ba, ban san meyasa kike hukuntani haka ba. Please ya kamata yanzu ki bari haka nan ya isa”

Aneesa ta kankance idanunta, abun da Sagir ya mata laifin sa daban, amma ya rinka daukar laifin ba a matsayar komai ba shi yafi cusguna mata rai. Don haka tace “Ni kuma me nayi? A gaban ka Hajiya tace na taho nan na huta kafin na samu kwarin jiki, har zuwa lokacin da zan gama jarabawata.”

“Amma idan kika nuna zaki iya zama a gidanki ba me cewa ai ki zauna a nan, me yasa zaki biye musu?”

Ranta ya gama kai kololuwa wajen baci, cikin kankance murya kasa da nashi tace “Biye musu? kasan me kake fada kuwa, kana magana tamkar ka manta komai. Ko don kana tunanin ka boyewa su Hajiya abun da yake damuna ni zai buya a wurina? So kakeyi na bika ka karasani da hawan jini ko kuwa ciwon zuciya kake son ka bani wanann karon?” 3

“yaya za ayi ka manta irin zargin da ka min Uncle Sagir? Ko bakayi tunanin illar da hakan zai haifar a rayuwata ba? Na sakankance na yarda da kai na baka soyayyata, na amince da kai koda kuwa yin hakan ba karamin abu bane a gareni ka nuna min kana tare dani bai kamata naji tsoron rayuwa ba… lokaci daya ka rusa komai ka nuna min bani da wani matsayi ko daraja a rayuwarka, Sagir kana sane da halin da nake ciki ka dauki hannu ka mareni, cikinka ne a jikina ka taba lafiyata, da wani abun ya same ni kai kam ba ruwanka tunda bani a bakin komai a rayuwarka. baka da asara. 3

Nayi wa kaina alqawarin bazan auri mijin da yake daga hannu a kan matarsa ba sai dai ka sauya dare daya ka canza kamanni ka sa na maimaita kuskuren da Innata tayi. Akan me yasa kake tunanin zan saurare ka? Ka san yanda mutum yake ji kuwa idan an masa mummunar zato? Baka sani ba ni zan fada maka. Gari guda sun juya min baya akan mummunar zato kai Sagir kaine ka fiddo ni daga wannan ramin da na fada na firgici da tsoro da kin rayuwa. Ka fada min yanda zanji lokacin da wanda ya bani SABUWAR RAYUWA ya kwace a lokaci guda?” Aneesa ta karasa maganarta cikin kuka mai shiga rai hawayenta suna zuba ba kakkautawa. Sagir ya matso kusa da ita a hankali yasa kanta a kirjinsa yana shafawa. 10

“Hakika ni mai laifine sosai a gareki, laifin da ko ni bana iya kallon kaina idan na tuna shi. Na san na muzanta sunan yarda, nayi miki mummunar zato sannan na yanke hukunci cikin fushi. Amma duk abubuwan da nayin nan Aneesa ina son ki san daidai da rana daya zuciyata bata amince da zargin da take miki ba, wani fushi marar amfani ya kaini ga aikata abun da na aikata. Rashinki a gareni ba karamin gibi ne a rayuwata ba. Duk son aikina bana jin dadin yinsa, idan ina dakin taro banda kuncin rashinki ba abun da yake gabana. I lost my essence, ina matukar bukatarki a tare dani Aneesa please come home.” 6

Aneesa ta kara sa kanta a jikin Sagir tana kuka, ya dago kanta hawaye ne shar shar a hankali ya sa baki ya sumbaci fuskarta dai dai inda hawayenta ke zuba, ya goge mata su.

“Ki daina kuka haka, ya isa, Sagir ya daina sa Aneesa kuka in sha Allah”

Murmushi tayi cikin wani annashuwa mai tarin yawa. Tace “Har yanzu kana sonta?”

“Ina sonki Aneesa” Kanta ta girgiza alamar ba ita take nufi ba, ya dubeta cikin rashin fahimtar me take nufi “Ummi, har yanzu kana sonta? Na san zafin abunda tayi da gudan kar abun ya sake faruwa ya janyo mana matsalar mu, da kuma duk wani janyewa dakayi daga gareni tun farkon auren mu. Shin sonta ke saka…”

“Aneesa, ban taba tunanin bayan auren mu zan canza sosai ba kamar yanda na canza, da har sonki zai zame min jiki ya kuma juya min al’amurana, wanda har zai sa bazan iya rayuwa ba tare da ke ba face cikin kunci. Ina so ki manta da Ummi kaman yanda na zabi na mance da ita a rayuwata, KE NAKE SO kuma wannan bazai taba canzawa ba”

STORY CONTINUES BELOW


Murmushi tayi mai dauke da nishadin jin maganganun Sagir. “Me tayi maka ya haddasa maka wani abu a rayuwarka?”

Sagir ya nisa ganin Aneesa ta sa shi a gaba yace “Ta canza, ta soni kafin auren mu, ko kuwa abun da nayi zato kenan, sai dai kuma bayan ta aureni ta ga irin dukiyar da nake dashi dani da iyayena, sai suka canzata, ta sa buri a rayuwarta ya zamana ba abun da take so illa kyale-kyale, ta canza kawayenta da yanayin shigarta abun har ya kai ga…”

Sagir yayi shiru kaman yana fafutukar fadin abun da yake ransa, Aneesa ta sa hannunta ta rike nashi hannun. “ya zamana ko auratayya bazatayi dani ba sai ta san akwai abun da zata samu a ciki, daga baya ta daina kulani duk juyin duniyar da zanyi, ga bin wasu kawaye da takeyi marassa kan gado, duk a tsawon wata nawa da aure, mamakin ta ya kamani, abu na karshe da tayi naji zaman mu ya kare shine kwana ta komayi da wuka saboda kar na zo kusa da ita. Ta nemi rayuwata saboda ba ni take so ba kudina take so. Wannan yasa na ji tsoron sake son wata ‘ya mace na ji tsoron sake aqalar rayuwata a hannun kowa, har nake ganin kowace mata haka take, amma kuma kasancewata da ke kin nuna min kaman yanda ba duka aka zama mata na gari ba haka ba kowace mace bace take da makarkashiya a tare da ita. Kin gwada min menene hakikanin so, you made me believe again” 2

Aneesa tayi ajiyar zuciya cike da tausayawa rayuwar da Sagir ya gani na rashin so daga matarsa ta sunna, wato dama da dalilinsa na kin sakewa da ita tun farko, a tunaninta jijji da kaine yake gwada mata. “shi ke nan komai ya wuce”

“ko ba komai yau an kirani Sagir, ba uncle.” Tayi murmushi, shi kuwa ya kara janta jikin sa kafin ya rike hannunta ya zaunar da ita a bakin gado, “yaya babyn mu, kina ta fushi dani ko labarin baby an daina bani.” ya shafo cikinta.

“Lafiya lau. Ya fara motsi”

“Da gaske?” ya fada hade da kawo kunnen shi kan cikin.

“Ai ba za ka ji ba sai ya dade yakeyi.”

Ya daga ya dubi fuskarta sannan yace “I am so sorry, yaushe zamu koma gida? Nayi kewarki sosai, gidan mu ma na bukatar ki”

“uhmm sai Hajiya tasa min rana na koma”

“Don Allah ki yi mun rai kice mata kin fara jin karfin jikin ki.” 4

Sagir yaso ya bata dariya, “yaya zan fara ce mata ina so na koma bayan tana ganin yanda kake sintiri a gidannan ta san meye kake so, amma bata ce min na tafi ba.”

“Ni dai ki san yanda zakiyi idan ba haka ba kuma zan tattaro na dawo dakin nan.” 15

“Ka rufa min asiri, ba ruwana.”

“Ba ruwanki? Ba ke kika jawo mana ba, da kika fada mata komai.”

Ta kwantar da kai sannan tace “Ina kake so naje to?”

Yayi murmushi yace “Gida, wurin mijinki”

Aneesa tana cikin jin dadin hirarsu kenan ta ankara da agogo da sauri ta mike “lah, karfe sha biyu fa, ka tashi ka tafi gida”

Sagir ya jawo hannyenta zuwa gareshi yace “Gani ga gidana ina zanje? yau a nan zan kwana.” 5

Ta kama baki hade da zaro idanu “Ka rufa min asiri ka tafi don Allah” ta firfito da idanu har ta so ta bashi dariya.

Abun da Sagir ya shiga yi mata ne ya nuna mata cewa tabbas zama yazo yi ba tafiya ba.

Ana kiran sallah ta farka, gani tayi yayi alwala ya fito daga bandaki. “yanzu yaya za ayi ka tafi masallaci? Idan ka hadu da Abba ko Kamaal fa ko wani dan gidan nan ya ganka?” 4

“Sai meye suma sun san sun rike min mata. Na zo tayata hira ne.”

“Don Allah kayi hakuri kayi sallarka a gida don na yau kawai, yaya zanyi zaka sani jin kunya.”

STORY CONTINUES BELOW


Dariya yayi yace “Na nawa kuma sun riga sunga motata a waje, don haka ki kwantar da hankalinki ba komai”

“Zaka hanani zuwa gaida Abba kenan.”

“A’a, na sama mana hanyar komawarki cikin sauki ne, tunda kince ke baza ki iya ba. Kinga idan suka ga na fara kwana a nan ai zasu tattaraki ki koma.” ya sauke hannun jallabiyarsa ya fice daga dakin, tamkar a gidansa yake.

Aneesa ta rike kai ta jabe zaune, sai da taji an tada sallah a masallaci ta iya mikewa tayi alwala.

Da safe bayan Abba ya gama cin abinci ne ya dubi Hajiya Khadija yace “wai ni kam me yasa baza ki bar yaron nan ya dauki matarsa bane?”

“Ah, Abba shi fa da kanshi yace a barta sai randa ta huce ta koma da kanta, kaga kenan ai bai damu ba don haka kyaleni dashi” 4

Alhaji Mustapha ya girgiza kai yace “ke ma dai kina tayata fushin kenan, amma ni banga me zai hana ta koma ba tunda ba a kwance take ba. Aiki kuwa basu rasa masu yi musu shi ba, don haka ni ban goyi bayan zamanta ba” 7

“To, tunda kace haka. Amma ai abun da yayi wa ‘yar mutane bai kyauta ba, idan aka barshi kuma ya sake maimaita hakan fa? Gwamma dai ya gane banbancin rashinta da kuma muhimmancinta ina ga zai gyara al’amuran sa.”

“Shin ba kya kula da sintirin da ya faye yi tun da kika dauko masa mata? ki dai barsu suje can su daidaita kan su amma idan kika takura su kuma to sai shima kiyi masa masauki don dai yau nan gidan motarsa ta kwana.” 9

Hajiya tayi shiru tana jinjina maganar Abba, tabbas ba tun yau ba ta kula da yawan sintirin da Sagir yakeyi a gidan, amma ta ki ta bashi sararin ganin Aneesa idan dai har magana ta kai haka kam dole ta tattara masa iyalinsa ta koma.

Bayan kwana biyu Sagir ya tafi da matarsa gida, ko da suka koma Aneesa sai mita take masa na cewar ya janyo har taji kunyar su Hajiya. “To yanzu ke hakan bai fi miki ba akan kina ta kame-kame ke da mijinki?” Sagir ya fada mata cikin rashin damuwa da maganarta.

Zama dai ya mike gadan-gadan tsakanin Aneesa da Sagir hakan ya janyo kyakkyawar canji a tare da natsuwarsu duk. Aneesa dai sun fara jarabawa, Sagir kuwa ya mai da hankalinsa ga kula da kasuwancinsa da iyalinsa sai dai matsalar har yau dai alaqa tsakaninsa da abokinsa Aadil bata gyaru ba, yaki bashi fuska iyaka suyi aikin ofis shi kenan.

Ana saura Sati daya Aneesa ta rubuta jarabawarta ta karshe a NECO ne haihuwa ya taso mata gadan-gadan. Tunda ta shiga watanta daddy ya turo Baba Saratu domin ta zauna da ita, don haka ta samu kula sosai, nakuda na tashi Baba saratu ta fadawa Hajiya da mummy sannan suka nufi asibiti domin Sagir yana South Africa a lokacin. Yana samun labarin abun da ake ciki hankalinsa gaba daya yayi gida, nan yasa Aisha ta hada shi da Aneesa a video call, amma ina tana ta kanta bata san ma me yake cewa ba. Ganinta a wannan halin yasa Sagir ya kara tausaya mata yaji kuma kaunarta ya karu a zuciyarsa.

Tana kwance a gado a dakin da aka shirya mata da zatayi zaman jego cikin dakunan kasa, taga baby na motsi don haka ta dagata tana girgizawa, a hankali ta tsinkayi kamshin Sagir daga idanun da zatayi sai ko ta ganshi a dakin.

“Maa sha Allah, Aneesa sannu da kokari.” ya durkusa a gaban gadon yana kallon baby a hannunta, a hankali ta mika masa. Tana kallon yanda yake kallon baby cike da so da kauna, ya tofa mata addu’o’i. Ya sa ta a jikinsa sannan ya dubi Aneesa ya hada ya rungume su. “Ba ki san irin farin cikin da kika damka min ba, Allah ya raya mana ita cikin tafarkin addinin musulunci ya kare mana ita daga dukkan sharri”

Aneesa ta share dan kwallan da ya fito mata sannan tace “Ameen.”

Ya kara dubanta yace “yaya kikeji, ba dai wani problem ko?”

“A’a lafiyata kalau.”

“To alhamdulillah, Allah ya raya mana Khadija Khairiyya” 3

Aneesa tayi murmushi sannan tace “Ameen, Allah kuma yasa ta dauko halayyar masu sunan.”

STORY CONTINUES BELOW


A nan Sagir ya zauna suna ta hira sai da Baba Saratu ta shigo tace lokacin wankan su yayi. Sagir ya mika baby shima ya mike yayi nasa dakin domin ya dan rage gajiya.

Tana fitowa daga wanka ta je ta samu Iyatu suka shirya abincin Sagir a kan table, amma bayan awa daya sai gashi ya shigo dakin da plate din abincin shi.

“Da kayi magana ai sai a kawo maka baby, na san dai ita ake ta faman bibiya”

Sagir yayi dariya, yace “ba ruwanki damu.”

Shi wai a dole ranar a dakin zai kwana, amma ba shiri tun karfe sha biyu yace su kwana lafiya domin kuwa lokacin ne garin Khairiyya ya waye. Aneesa tana dariyarsa ya fita a dakin ya koma dakinshi.

Bayan kwana uku da haihuwar Aneesa ne sukayi manyan baki daga Kano, Rabi’at ne da mijinta Faruk. Aneesa tayi farin cikin zuwansu, nan da nan ta shirya musu tarba ta musamman. Sun dade suna hira Aneesa ta tambaye ta labarin su Maryam yaran Rabi’at, kafin suka ce zasu wuce Rabi’at tace “kiyi hakuri bazamu samu halartar suna ba, kasancewar zamuyi tafiya gobe. Amma in sha Allah zaki ganni idan na dawo.”

Aneesa tace “ba komai, yanzun ma kun kyauta sosai da kuka zo. Allah ya bar zumunci ya kuma kare muku hanya.”

“Ameen, Allah ya raya mana pretty Khairiyya” Da suka tashi tafiya Rabi’at ta bata wasu lesuka masu kyaun gaske guda biyu da ‘kananan ‘yan kunnayen gwal na baby. Shi kuwa mai gidanta kudi ya bata a envelope. Sai bayan tafiyarsu ta ga bandir din ‘yan dubu-dubu ne. Duk ta ajiye su a dakin Sagir sai ya dawo zata nuna masa.

An daga taron suna kasancewar ranar Aneesa zata rubuta paper dinta na karshe, Anty FAtima ce ta shirya duk wani abu na tarban bakin sunan Aneesa.

Ana saura kwana biyu suna ne sai ga su Mama a Abuja, musamman Sagir ya aika mota Kunuwal yace wadanda zasu zo suna su biyo motar a kawo su. RAnar murna a wurin Aneesa ba a cewa komai, haka ta raba dare suna hira da mama. Amma wai ita fushi takeyi don me yasa Inna bata zo ba. Sai a waya suke magana tun haihuwar, ta dai shiryo mata kayan kauri an taho mata dashi.

Nan Sagir ya shigo dakin da Mama take yace “Ke tsohuwa, me ya kawo ki bayan da kin hana ni dauko matata?”

Mama tayi dariya tace “Ai sa’a kayi, ina zan bari kana min sintiri a gida ku a dole soyayya? Gata nan na tarkato maka ita kuyi ta fama, da ‘yarku mai shegen kukan nan”

Ya dade suna hira a dakin sannan ya musu sai da safe.

Ranar suna da safe Sagir yayiwa Aneesa wata kayatacciyar kyauta, dakinsa ya kirata. Sai da ya gama hirar sa da Khairiyya ya fito da wani dan karamin akwati ya daura a kan gadon ya bude mata yace “Wannan kyautace ta musamman da na tanadar don wannan ranar. Ba abinda zan baki ya biya wani kyautatawa ko kuma wannan farin cikin da na samu ta dalilinki, please accept this” 9

Aneesa ta tsaya tana kallon abubuwan cikin akwatin tana kallon Sagir. “ki dauka naki ne.” Makullin mota ta gani da wasu takardu sai wata sarka mai dan karan kyau, ita kanta bata taba ganin abu mai kyau irin sa ba.

Sagir ya mata bayanin takardun wai na gidanta ne. Gidan da suka taba sauka a Gombe wai dama da sunanta ya saya amma bai fada mata ba sai lokacin da ya dace yazo. Sarkar kuwa ya tuna mata lokacin da ya barta a airpot a Turkey yace ta jirashi, abunda ya sayo mata kenan. Aneesa kam ta rasa bakin magana sai hawaye taji suna bi mata idanu. Da taga bazata iya magana ba mikewa tayi ta rungume shi cikin yabawa da gode masa. Baby kuwa cika mata daki yayi da sayayyarta har ta rasa inda zata sa wasu.

A filin gidan Sagir aka shirya kayatacciyar walima, taron yaga jama’a da dama daga kowani bangare kawayen Aneesa na makarantarsu ma duk sun hallara. An ci an sha an rarraba kyaututtuka ga duk wanda ya halarci wannan taro. Mai jego ta shiryu cikin kaya na alfarma. Akwatuna tirim aka ciko daga gidan Daddy wai duk nata ne da na baby. Haka takwararta bata rage su da komai ba, har da turarrukan na musamman ta aiko wa Aneesa domin gyaran jiki, Aneesa har ta rasa bakin magana.

STORY CONTINUES BELOW


Wuni sukayi bayan suna da su Khazeena suna shirge kayan sunan a dakin tsakiya da bata amfani dashi sosai, ta ware wasu zannuwan ta bawa su Zahida da Khazeena wasu kuwa ta aikawa Aisha da Hamdiyya, ta daukawa Innarta da Amina ma.

Anty Sameera ma tazo sunan, don a wannan lokaci dai ta sawa kanta salama ta amince tana sauraron wani dan majalisa da ya dade yana sonta, matansa biyu. Ganin Sagir ya zakalkale baya tunanin wata sai Aneesan sa ita ma ta hakura domin zaman hakan ya soma damunta. 6

Kamaal ya kammala karatunsa na Masters har ya fara aiki a Kaduna.

Tun bayan haihuwarta Baba Saratu take ta aikin shirya ta, ba wasa. Ta hanata yawo ba takalma kullum kuma tana cikin sata zama cikin ruwan bagaruwa. Ga aukin turarata da takeyi. kullum kuwa tana cin romo da shayi mai kauri har saida Aneesa tayi wani bulbul tana sheki tukun. Kafin su gama jego dai har wani kamshi na musamman ya zauna a jikin Aneesa. Daga wannan lokacin kuwa Baba Saratu ta rakashe a gidan Aneesa.

Ranar wata laraba ne sukayi waya da Innarta, take shaida mata Malam Habu ya samu koyarwa a babban secondary a cikin Gombe don haka yanzu aikin sa ya koma can. Aneesa murna ya kamata marar misaltuwa.

Da dare suna cin abinci da Sagir take fada masa abun da ya faru. Yayi murna da jin labarin kwarai a lokacin ya kira malam Habu suka taya shi murna. Bayan sun gama wayar ne yace “Mun kammala shirye-shiryen da mukeyi fa na bude kamfanin mu na south Africa ina ga cikin wata mai kamawa za a bude kamfanin, in sha Allah.”

Aneesa tana murmushin jin dadi tace “Lallai abu yayi kyau, Allah ya sa a bude lafiya ya kuma yi albarka kaman yanda sauran suke dashi.”

“Ameen, sai dai zai dan bukaci lokaci sai na tabbatar da cewa komai ya daidaita sannan na dawo, za a min rakiya ko kuwa Khairiyya tayi kankanta?”

Aneesa tace “me zai hana. Itama dai yanzu kam ta kunsu da yawa kullum ita kenan daga daki sai falo? ko kuma idan za aje danna mata allura.”

Yayi dariya yace “To shi kenan sai ku shirya wani sati sai muje Kunuwal ku musu sallama suga Khairiyya kafin mu tafi.”

Aneesa ta amsa masa sannan ta shiga kwashe kwanukan zuwa kicin, a falo ta same su da ta dawo. Sagir yace “Tashi ki kwantar da Khairiyya inaga baccin ta yayi nisa yanzu kam.” Ta karbi jinjirar tasa a dan karamin cot din ta mai laushi. Sai da aka gama labaru tukun tace “mu kam mun shiga sai da safe,” Sagir ya kalleta yace “Ban gane sai da safe ba, ai yau kam kun koma sama ki je ki kwantar da ita ina haurowa yanzu nima.” Jin haka Aneesa ta sha jinin jikinta don haka dakinta ta shiga ta kimtsa tukun sannan ta amsa kiran mai gidan nata.

Wannan zuwan nasu gidan su na Gombe suka fara sauka, a wancan zuwan nasu Aneesa bata kula da gidan da kyau ba kasancewar shigan dare sukayi. sai a wannan zuwan ta kula duk kayan da Daddy ya mata da wanda Innarta ta mata a nan aka shirya mata su. Nan taji wani dadi ya lullubeta, ta kara jin son Sagir a tare da ita. Suna isa tamkar su Amina ita suke jira, kowa sai son karban Khairiyya yakeyi Inna tace “kaji min yara dai sai kun tumurmutsa ta ne tukun na? ku bari sai ta tashi a bacci sai duka ku dauketa.” 2

Sagir ya shigo suka gaisa da Inna tace “Aneesa ta fada mana ci gaban da aka kara samu Allah ya sanya alheri ya kuma kara daukaka. Yayi kyau”

“Ameen, Ameen ina Muhammad ne yau ya samu baby bai zo mun gaisa ba”

“Hmm gasu can sai fada sukeyi akan wanda zai riga dauka.”

“Ina ruwan Muhammad, Inna ni zan shige akwai inda zamuje da Malam zan same shi a makaranta”

“Ayya, to ba laifi. sai kun dawo”

Inna tana komawa ciki tace “ki tashi kije ko da abun da zai ce miki, wai zasu fita da malam.”

Tana shiga yace “zamu anguwa da Malam zakiyi rakiya?”

“A’a ku dai sauka lafiya sai kun dawo”

“Ina khairiyya?”

Aneesa tace “tana wurin Inna, zaku dade ne?”

“A’a akwai abokina Haruna kin tuna shi ai,” Aneesa ta gyada kai “zamu je ganin sa ne akwai abunda zamu tattauna”

Aneesa tayi murmushi tace “to Allah ya dawo daku lafiya.”

**********

Da yamma sai ga Malam Habu ya shigo gida yana farin ciki sai kira yakeyi “Halima, ina Haliman ne?”

Inna ta fito da sauri daga daki don dai ta san wannan kira ta dabance “lafiya malam?”

Malam Habu ya zauna a bakin tabarma yace bude ki ga wannan”

Inna ta sa hannu ta karbi takarda tana dubawa “Malam wannan fa?”

“Kin san yaron nan Sagir muna tafiya muka samu wani abokinsa daga can muka wuce wani gida sai ya shiga suka gama dubawa sannan ya maida abokin a nan ne ya fito da takardar nan yace “Malam wannan naka ne, inaga tunda yanzu aikin ka ya dawo Gombe wahalar shiga da fita kar tayi maka yawa zaku iya dawowa da su Inna”

“Inna tasa salati tace “Amma lallai ba abun da zame cewa Sagir sai Allah ya biyashi da madaukakiyar gida a aljanna Allah ya saka da alheri.”

Nan Inna ta sa baki ta kira Uwani suka shaida mata a abunda mijinta yayi, mamaki da dadi da farin ciki ya cika ta fal ta rasa bakin magana.

Sai da dare ta nemi wayarta ta kira Sagir.

“Ba kiyi bacci ba?”

“a’a, yanzu dai nake da shirin yi na samu Khairiyya tayi.”

“lalle kin ci sa’a. Allah yasa anjima kar ta tashi miki”

Aneesa ta yi shiru sannan tace “Sagir akwai abun da zan yi maka don na nuna maka godiyata kan dawainiyar da kake dauka akan iyayena da ni kaina?”

“Aneesa kasancewar ki tare dani ya isheni komai”

Lumshe idanu tayi tace “Na gode Allah ya kara rufa asiri, ya sa ka gama da duniya lafiya. bakina bazai iya furta maka iya farin cikin da nake ciki ba”

“Ni na san abun da zai iya nuna min, ko na zo na daukeki ne?”

Aneesa ta rufe fuska tamkar yana ganinta tace “A’a wannan karon kam kayi mana afuwa mu kammala kwanakin da muka zo yi.”

“To shi kenan, amma dai ki dawo da shirin ki sosai.”

Haka dai suka sha hira mai shiga rai kafin sukayi sallama.
BAYAN SHEKARA UKU +

“Khairiyya dawo ki zauna, kinga yana kwaikwayon abun da kikeyi ko?”

Aneesa ta mike ta kamo hannun Sabir yaro dan shekara daya. “Zo ka zauna ka rabu da Adda Khairiyya” 1

“Ammie ni ma gyara min na zauna a cinyarki.” Khairiyya ta fada cike da fitina ta yara. 1

“Kai zaku karya ni ne? Ni kin mini katuwa, kuma kun dameni ina karatu”

Yarinyar ta shagwabe fuska tace “shi kenan kuma Abbie zai dawo shi zai daukeni, tunda ke kinki.”

Bude kofar falon da akayi ne ya jawo hankulansu da gudu Khairiyya taje ta dale jikinsa tana “Abbiena oyoyo, kaga Ammie wai bazata sani a cinyarta ba wai zan karyata. Ni motace Abbie?”

Sagir ya daga ‘yarsa mai shekara uku yace “A’a ke ba mota bace, ki rabu da Ammie zamu tafi yawon mu muma” Sabir ma sai murna yakeyi daga inda yake yana tashi cikin koyan tafiya yana faduwa suna masa dariya kasancewar yayi lattin yin tafiya. Sagir ya daga su duka su biyun. Aneesa tayi murmushi sannan tace “Sannu da dawowa”

“Yawwa, sannunki da gida na ga alama wadannan sun hana ki karatu a haka zaki zana jarabawar gobe?”

Ta daga takardar a gajiye sannan tace “Kai dai ka bari Abbie gaba daya na rasa ta inda zan fara, da na kaisu wurin Baba Saratu sai su dawo wai su nan suke so”

Yayi murmushi yace “Duk da dai na gaji, amma bari na je miki dasu na one hour kafin nan kin samu kin dan kara duba wani abun.”

“Na gode, you are a life saver.”

“komai don ke my dear, Khairiyya mu tafi mu bar Ammie tayi karatu ko? kar taci zero a school”

Yarinyar ta tuntsure da dariya. Aneesa ta bi bayansu da kallo cikin sha’awar yanda mahaifinsu yake mu’amala da su duk da karancin lokacinsa. 3

Ya kasance mai gudanar da rayuwarsa cikin fifita iyalinsa sama da komai, duk aikin da yakeyi to asabar dai ba fashi yana gida cikin iyalinsa idan kuwa tafiya ta kamashi wanda zai kwana biyu haka yake tarkata su su tafi musamman idan Aneesan tana hutu kasancewar tana karatun digirinta a nan jami’ar Cape Town dake South Africa. A cikin shekarun ya samu ci gaba masu tarin yawa a bangaren kasuwancinsa, wanda har kamfaninsu ya samu lambar yabo da dama. 4

Aneesa ta rufe littafinta kenan sai wayarta ta shiga kara Tana dubawa taga Aisha ce “Maman Abba sai yanzu zaki kira? Nayi fushi”

“don Allah kiyi hakuri, baza ki gane bane sam ban samu zama ba, gashi Abba baya bari na samu baccin dare da safe idan na bige kamar wata bugaggiya”

“Tab kya dandana haka Khairiyya ta min, yaya Yola?”

“Yola lafiya sai zafi, kaman na gudu.”

“A da kenan, ina Rufa’i yana ji kike cewa zaki gudu?”

“ke dai bari shi din ma don garinsu ne da ya riga ni, yaya jarabawar dai da Cape town?”

“Gashi nan muna ta kai na kusa gamawa ma, Cape Town lafiya kowa yayi wishing dina banda ke”

STORY CONTINUES BELOW


Aisha tayi dariya tace “Tunda kin samu fatan alkhairi daga babban yaya me kuma zaki nema? ni a su wa?”

“Ke dai bakya rabo da zolaya. ki shafa kan Abba.”

“Zai ji in sha Allah, ina ‘yan yarana naji su shiru”

“Hmm dazu na samu Abbinsu ya fita dasu sun hana min sakat, amma na ga lokacin baccinsu ya kusa yanzu zanje na karbe su ko shima ya huta”

Nan sukayi sallama da Aisha, sai da tayi wanka tukun sannan ta nufi falon mai gidan. Ai kuwa nan ta samu duk yaran sunyi bacci. Murmushi tayi sannan ta dauke su duka ta je ta kwantar, ta hado tea ta dawo dashi falon.

“Sai yanzu kika kare karatun ne daga awa daya.”

“hmm waya na tsaya yi da Aisha, tana gaishe ku ma”

Sagir ya karbi kofin hannunta sannan ya zaunar da ita a gefen shi “Muna amsawa, shine zaki je ki zauna ki manta damu?”

“Ayi mun afuwa.”

“Naji, ayi dai a gama jarabawar nan ko za a samu lokaci na, don naga alama hatta Sabir ya fi ni samun lokacin yanzu.”

“kai kuwa zaka hada Sabir da kanka, ubana na kaina ne fa shi, kai kuma fa?”

Sagir ya ajiye kofin hannun shi yace “oh ni kuma fa? zan nuna miki ko ni waye kuwa.”

Aneesa ta kyalkyale da dariya.

Tana gama jarrabawa suka tattara duka sukayi gida, ba wanda ya kai Aneesa dauki kasancewar tun haihuwar Sabir rabonta da gida, ba wanda ta fi kewa irin Innarta da Mama. Gashi tana daukin zuwa ganin ‘yar wajen Sameeha wacce ta haifa watanni hudu da suka shige.

Zuwanta gidan Daddy ta tarad da wani abun mamaki abun al’ajabi, Farid din Anty Fatima ta gani hannun Mummy tana masa rawa da wasa, wunin ranar kaf da tayi gidan Mummy ce abincinsa da fitsarinsa da kashinsa. Ta kalli Sameeha da tazo wuni ita ma ta dubi Mummy, Sameeha ta kwashe da dariya tace “Long story”

Ai kuwa ta sha labari, Sameeha ke fada mata “Ina lokacin da na fada miki mummy tana asibiti abun sai addu’a? To tunda mummy tayi wannan ciwo tana dawowa gida ta tara mu tace wai ta hango mutuwa, kuma wallahi duk abunda tayi kadan ne na abun alfahari cikinsa kuwa shine haihuwarmu da tayi amma da ta duba sai taga zata yi asarar abun alfaharin saboda kin bamu lokacin da tayi ta tarbiyyantar damu. Har ta so ta rasa daman da akace mutumin da Allah ya bashi ‘ya’ya mata har ya tarbiyyantar dasu to ya samu rabo. Don haka ta tuba kuma tana kwaban mu da duk wanda ya dauko halinta to ya shiga uku. Nan ta dage wai sai dai Daddy ya kaita Gombe ta ga Innar ki.” 6

“Haba, shi yasa naji mamaki da Inna tace min su Daddy sunje, ai bata fada min abun da ya kai su ba, kai Alhamdulillah, naji dadin wannan abun. Allah mai yanda ya so kenan, dama kowa da hanyar shiruwarsa Allah ya bamu kyakkyawar karshe don mutum karshen sa shine komai, idan yayi kyau to ya samu rabo.”

“Haka ne Aneesa, yaya labarin Uncle Sagir?”

“Lafiyar shi kalau, anjima zai zo ai. Ji yanda Mufida ta girma masha Allah”

“Kinga kamanninta da Khairiyya ko?”

“Ai kuwa, ina nunawa Baba saratu hotonta tace wannan kam Khairiyya sak. Yaya babanta?”

“Lafiyar shi kalau.”

Da dare Daddy ya zauna cikin y’ayanshi da jikokinsa, banda farin ciki ba abunda yake ji. Ya kara godewa Allah kan ni’imonin da ya masa. Gashi hakurin da yayi da Juwairiyya ya sa ta koma kan hanya wannan yasa ya ji fusshin da yakeyi ya sauka, musamman da suka je har inda Halima take ta nemi gafarar ta, ko ba komai haka Allah ya kaddari gutsurarriyar rayuwa a tare dasu, ga kuma rabon yaran da zata haifa da Malam Habu. Ko da yake yanzu kam Alhaji Habu ne daga bara.

STORY CONTINUES BELOW


Aneesa tana ganin yanda Sagir yake sama sama da Aadil abun ya sosa mata zuciya, don haka ta kudiri yi masa magana.

Randa suka shiga Gombe ranta ya mata dadi, taga kannenta duk sun girma kamar ana jansu, gashi suna karatunsu gwanin sha’wa, Innarta kuwa shagon saka ya bunkasa don yanzu ta debi matan da suke koyarwa ne tana gida abunta sai lokaci-lokaci take lekasu. Washegari taje gidan Falmata murna kaman zasu yi yaya. Ta sa yaran Aneesa tana ta kallonsu yara kyau kaman ‘ya’yan larabawa. Falmata ma ta samu ci gaba sosai, hankalinta a kwance da mijinta, sun samu da kyar Innarsa ta dawo Gombe tare dasu.

Kasancewar Sagir da Malam Hassan ya turo su sun zagaya sosai kan ‘yan uwa. Kwanan su uku a Kunuwal gidan mama. Musamman ta kaiwa Fatu wuni ta duba lafiyarta da na yara, kayan arziki sosai ta kai mata.

Ta samu labari Munkaila na kwance ba lafiya shame shame, ana ta jita jita dai wai ciwon zamani ne ya kwantar dashi. A ranta kuwa fata takeyi Allah yasa bai kakabawa wata wanda bata ji ba bata gani ba.

********

Ta dago kai daga rubutun da takeyi a komfutar laptop dinta, saboda hannun Uncle Sagir dake mulmula mata kafada, “To, madam blogger ai yanzu kam za a hakura da rubutun a kula dani ko yaya?”

“Wai, afuwa my dear wallahi ban kula da yanda lokaci ya tafi ba. Na zauna ina amsa tambayoyin makaranta shafin ne”

“Hmm, na ga alama fa shafin ya samu karbuwa. Sannan kuma mutane suna bude cikinsu. Sai dai kin san yawanci masu amfani da komfuta ba sune maudu’in naki ya shafa ba, me zai hana ki nemi wata hanyar da sakonki zai isa kunnen wadanda wannan al’amari yafi shafansu?”

Aneesa tayi murmushi dole Sagir ya zama mai nasara a babban kamfani irin Daggash-Adebayor saboda baya rabuwa da hikimomi na bunkasa abu da kawata shi “Tabbas ka fadi gaskiya, nima ina tunanin ko mujalla mai saukin kudi wanda zai isa hannun kowa da kowa da kuma samun fage cikin jaridunmu?”

“uhmm, hakan yafi. Its a good idea, akwai wadanda na sani suke wannan harkar zan hadaki da su sai ku fara tsara (strategy) din in sha Allah, amma kafin nan taso kizo.”

“My dear ni ko dai ina da abun cewa game da wani batu.”

“uhum ina jinki? wani abu ne mai muhimmanci haka? Kin san nayi kewarki sati guda da nayi ba na nan.”

Shawagwabe fuska tayi cikin raki tace “Ayi min afuwa, amma ni sai bana jin dadin irin yanda kake rike da fushin abun da ya riga ya wuce a ranka.”

Sagir gyara zama yayi tare da dauke hannunsa daga kafadun Aneesa saboda ya san maganar da zata yi “Idan dai har da gaske ka hakura da furucin da kayi a kaina me ya hanaka yafewa amininka? Ka duba abun nan shekaru hudu kenan amma ka ki ka koma masa kamar da, wai ace mutumin da ka fi kowa shiri da shi yake kuma sonka da alkhairi sama da shekaru goma sha tara shine kake fushi dashi akan abun da bayi da laifi? Ba wai ina justifying abun da yayi bane, amma ka duba mana ka gani shi ya maka hira fa? meye lafin zuciyarsa don ta masa sha’awar wani abun da ba nashi ba?”

Sagir ya danna mata wani irin kallo “Da gaske nakeyi, eh ya ce yana sona amma wannan duk a baya ne, yanzu yana da iyalinsa da yake matukar so kuma kuskure ne da ya yi ya kuma gane laifinsa, amma sai a ce kai har yanzu ka gagara yafe masa? A cikin ku waye ya kamata yaji kunya? Shi da ya bar maka abun son shi saboda kaunar da yake maka ko kai da ka bar shi saboda aabun da kake so?”

Ajiyar zuciya yayi “Aneesa, baki san yanda nake jin ki a raina bane, ko kallon shi nayi sai na tuna lokacin da yayi admitting cewa yana sonki.”

“And then? Kai ka san yanzu kam wutsiyar rakumi tayi nesa da kasa, ni takace amma fa kar ka manta AL’AMARIN ZUCI abu ne mai rikitarwa. Ka yafe masa don Allah. Allah ma yana yi mana gafara ballantana ma nawa rayuwar duniyar take? Yau mune gobe ba mu ba, ba amfanin gaba da musulmi dan uwanka, bare kuma ga munin rabewar zumuncin da ke tsakani.”

STORY CONTINUES BELOW


“Ni na yafe masa, kawai dai bana son na sake sakar masa ne yana kalla min mata.” 6

Murmushi tayi sannan tace “Ho, Uncle Sagir. Aneesa taka ce ba mai sace maka ni, shi yasa ka hana ni yin aiki a waje sai daga gida ko? Nima ina maka kishin kaina ba zan taba bari na keta wannan haddin ba don haka, don Allah ka gyara tsakaninka da abokinka.”

“Naji In sha Allah zan same shi muyi magana.”

“Yauwa, na gode sosai.” Nan ta maida kanta zuwa kirjinsa.

*********

Khazeena ce tazo mata da wani abun al’ajabi “Da gaske nake, Ammie. Ni gaskiya aure nake so nayi kafin naci gaba da karatuna.”

“Wai ni me ya sameki ne? duk nacin karatunkin nan, kice ke sai dai aure kike so? Kin san ma tukun zaman auren yanda yake da wuya? ki bari ki kara ko shekaru biyu ne kafin kin kara wayo.”

“Ammien Khairiyya, shekaruna sha bakwai fa yanzu kuma ai ba yanzu za ayi auren ba, ni dai yaje yaga Daddy suyi magana, idan yasa ko zuwa next year ne ba sai ayi ba? Ni gaskiya shi nake so, kuma aure yake so muyi to don me yasa zan rasa shi bayan ko wani lokaci idan na tashi zan yi karatuna.” 4

“Uhm-uhm to shikenan , ni dai abun da nake jiye miki kar ki zo dadi miji ya hana ki ci gaba. Ilimi yana da matukar muhimmanci, amma aure yana gaba dashi tunda kince haka ki ci gaba da neman zabin Allah. Sai ki ga komai yazo cikin sauki, tukun na ma waye ne ya daukewa ‘yar kanwata hankali haka?”

Khazeena tayi murmushi cikin jin kunya. “KIn sanshi sai dai don Allah kar ki min dariya.”

Aneesa ta dubi Khazeena cikin mamaki “Oh, wai Khazeena ce take soyayya yanzu har ma ana boye min sunan shi to shikenan zan tayaki adddu’a idan ta rika ai zata fito. Ina Farouk ne dan gidan abokin Daddy?”

Khazeena ta tsume tace “Ya faye surutu da papa daga yazo banda hirar abun da yake dashi da matsayin da ya taka sai ki rantse ba wanda ya kai shi haduwa duk garin nan. Ni yanzu Ammie Uncle Kamaal ne muka daidaita dashi” 4

Nan take Aneesa ta fiddo idanu tana mamaki “Khazeena, kin ga ta kanki a ina kuka hadu da Kamaal da har kuka kulla wannan irin soyayyar?” 5

“Tun shekaru biyu da suka wuce a bikin Anty Aisha ya soma min magana, amma dai ban fara kula shi ba sai shakarar da ta wuce.” 6

Aneesa dadi fal a zuciyarta, domin kuwa ta san Kamaal mutumne mai hankali da kamun kai, tabbas ta san Khazeena tayi sa’a haka nan shima yayi sa’ar mata ta gari idan har abun nasu ya daure. Ai ko bata yi wani jinkiri ba ta sanar da Sagir abun da yake faruwa.

“Wato kai kam dai daga abokan ka sai ‘yan gidanku zasu kwashe min ‘yan kanne na ko? Zaheeda dai bare zata aura, mun gaji daku haka nan.” 6

Sagir yayi dariya yace “Ko an ki ko an so dai an shige mu, kuma mun rike gam. Allah ya sanya alkhairi, ki rabu da ita ta gabatar dashi, tunda ta kammala sakandirinta kuma ta fito tace ga abun da take so ba shi kenan ba, wannan kuma tsakaninta da mijinta sai ya barta tayi karatun don na san shima yana son karatun bazai hanata ba. Da wani wanda ba a sani bane sai a ji tsoron ta zauna haka. Bare ma zamani na sana’o’i daban daban ai bazata zauna ba abunyi ba. Don nima na tsani zaman banza, shi yake haddasa fade fade a tsakanin ma’aurata.”

“Hakane, to Allah ya shige mana gaba.”

Da gudu ta banke kofar dakin ta shigo a tsakar gudun tayi sallama da mujalla a hannunta “Baabar Ammiena duba, kinga ansa hoton Ammie a jikin wanann magazine din. Kiga bata miki kyau ba?”

Baba Saratu ta karbi littafin suna dubawa da Khairiyya “Ah, lallai ko Ammien ki ta fito radas da ita, a ina kika samu?”

“Abbie ne ya kawo ya nuna min wai ga aikin Ammiena tana koyawa mutane abu a magazine. Nima idan na girma zance ta dinka min irin hijab dinta, kinsan yanda take kyau kuwa idan ta saka?”

“Kai Khairyya, nima fa mamana ta fi Ammienki kyau. Ba ke kadai bace Ammienki mai kyau.”

Khairiyya ta zaro idanu tana nuna yatsa cikin al’ajabi tace “Kema kina da mama? Ki ganki fa tsohuwa dake yaya za ayi kiyi mama?” 6

BAba Saratu tayi dariya sosai su ka ci gaba da shirmensu. Kafin Aneesa ta zo ta musu sai da safe, don Khairiyya kam ta kauro dakin baba saratu Sabir ne dan Ammie.

********

Suna zaune da yara a falon Sagir bai wuce awansu uku da shigowa gidan ba bayan sun dawo daga kai amarya Khazeena gidan mijinta da yake kaduna. Don kuwa da magana da biki kaf bai wuce wata takwas ba sai gashi an kaita gidan Kamaal a matsayin matarsa. Sabir ne ya miko mata remote “Ammie sha katuuu” 3

Ta karbi remote din tace “Haba Sabir, bazaka bar mutane su huta ba kullum abu guda kenan. Ba ka san yanda na gaji ba, tamkar anmin duka kazo ka ishi mutum da katuu”

Sagir da yake zaune ne yace “A to ba ku kuka sabar masa ba, abunda kwata kwata ba a son yaro ya wuce awa biyu yana kallo amma idan kuka bar musu tv shi kenan kaman kun sama musu nanny.”

“Abbie, kai kanka ka san kallo bai dameni ba, wai dai once in a while ka dan barsu su kalla shi kenan ya dawo musu jiki.”

“Aiki ya same ki ai, sai kiyi ta sama musu masu amfani da karin ilimi, ki kuma kayyade iya lokacin kallo idan ba haka ba yaro sai ya tashi kaman dolo rainon TV ba wasa bare kwakwalwa tayi kaifi.”

Dariya tayi ganin yana mayar da agogonshi da alamun shirin fita ne ta gagara hakuri, “Wai don Allah my dear na tambayeka wani abu man.”

Kallonta yayi yace “Ina sauraronki sarauniyar blackmail, meye kuma yanzu?” 10

“NI dai kana min sharri, ba dama nace maka haka sai ka tuna min randa na fara. Ni dama ba komai bane akwai abu guda da kullum kakeyi muddin kana kasarnan kuma baka daina ba har yau, ni kuwa ban taba sanin meye bane. Nayi shiru saboda bana son shiga rayuwarka. Amma dai yanzu baka ganin ya cancanta na san inda mijina yake a ko da yaushe?”

Murmushi yayi ya rike hannayenta, “Aneesa kenan, ina ruwanki da wurin zuwa na?”

“Babu ruwana hakan yasa ban taba tambaya ba, kasan AL’AMARIN ZUCI, ba wai hakuri ne da zuciyar mutum ba, wannan yasani tunanin yanzu idan aka sa min wuka na fadi ina kake zuwa bayan isha bazan sani ba.”

“Naji zan fada miki, amma idan kin sani me zakiyi da sanin?”

“Babu, kawai dai…”

“Gidan Abba nake zuwa bayan na dawo daga wurin karatu.”

Kallonshi tayi cikin mamaki. “Karatu!”

“Eh, karatu.”

“Wani irin karatu kuma?”

“Wanda zai amfane ni duniya da lahira. Ko kuwa nayi babba da daukan ilimi ne?” 6

“A’a ni bance ba, naji mamaki ne kawai. Ban taba tsammani wai kai SD zaka zauna daukan karatu a yanda abubuwan ka suke babu sarari da lokaci ba. Gaskiya kayi kokari domin ilimin addini yayi karanci a rayuwar yanzu hakan yasa ake ta shirme a rayuwa, amma da za a sauke girman kai a koya da abubuwa zasu yi sauki musamman na mu’amala tsakanin mutane, ko miji da mata.” 3

“To madam journalist, idan kin gama tambayoyin zan tafi kar nayi latti.”

caraf Khairiyya tace “Abbie kaima idan kayi latti za a maka bulala.”

Dariya sukayi duka sannan yace “Ba a dukan Abbie Khairiyya.”

Ya shafa fuskarta sannan ya kalli Aneesa “Sai na dawo.”

“To a dawo lafiya, Allah ya bada sa’a.” Ta fada hade da shafo saman cikinta mai watanni bakwai wanda ya taso tamkar yanzu zata haifo shi…

Alhamdulillah.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *