ALKAWARIN JINI CHAPTER 1 BY _HAWWA MUH’D USMAN

ALKAWARIN JINI CHAPTER 1 BY _HAWWA MUH’D USMAN

              Www.bankinhausanovels.com.ng 

TUSHEN LABARIN.*

       Yanayi da kuma tsarin gidajen dake arean kana kallo zaka tabbatar da ba’a cikin k’waryar gari ko nace birni kake ba,,RUGA ce irin ta Fulani mazauna yankuna daban² a cikin garuruwa,haka nan ita wannan ruga ta kasance ne a d’aya daga cikin k’auyukan *KANO*,a wani yanki  da ake kira *KAUSANI* dake a cikin k’aramar hukumar *WUDIL* a yankin  jihar *KANO* ta b’angaren northeast,ita dai wannan ruga a tun farkon kafuwarta ta kasance ana yi mata lak’abi ne da rugar *MALAM SHEHU MAI DARASU* ma’ana dai mutumin dake da yawaitar almajirai ko d’alibai ko kuma muce wanda ke bada karatu a tak’aice,,kusan zamu iya cewa wannan dattijo wanda tun a

shekaru da dama da suka gabata Allah yayi masa rasuwa,sannan ya kasance shi ne shugaba ga wad’annan al’ummah,sai dai a yanzun haka daya kasance baya raye sai y’ay’ansa daya rasu ya bari wanda har wannan lokacin suke cikin wannan yankin,amma kuma batun karantarwa tun bayan da Allah ya karb’i rayuwarsa sai AL’AMARIN ya tsaya saboda rashin wanda zai iya maida hankali ya gaje shi ta bangaren ci gaba da abunda *MALAM* d’in ya rasu akansa wato koyarwa a tafarkin addinin Islam,kasancewar shi ne mutum na farko daya fara zama a yankin ko muce shi ne asali da tushe na kafuwar wannan al’ummah dake rayuwa a wannan yankin,wannan dalilin yasa sai ya kasance shugaba ga wad’annan fulani dama wasu cikin k’abilunmu na Nigeria mazauna wannan d’an yankin sannan sai ya kasance anci gaba da kiran wannan yanki da sunan sa,duk da yankin garin ba wani girma ne da shi ba haka ko ta b’angaren tsarin gidajen dake gurin kad’ai da suka kasance cikin wani tsari mai birgewa,sannan a k’iyasin adadi na mazauna ko nace gidajen da ke wannan ruga duka baza su haura gidaje hamsin ba,idan kuwa har ace zasu haura haka to y’an tsirari ne zasu zama sun k’aru akan adadin farko.+

    Around 6:30am matashiyar y’ar budurwar da duka a shekaru bazata wuce shekaru goma sha hud’u ba,ta fito daga cikin wani gida wanda yake d’aya ne daga cikin gidajen da ke a castles na rugar wanda dukansa yake encircle with kinda traditional wall,a mafi yawan lokuta idan har mutum yaga irin wannan wall ko tsarin ginin gida makamancin wannan tofa tabbas zai kasance ne ga jama’a mazauna k’auyuka wanda su kanyi shi da karare,,she’s black in skin colour buh not dark in nature,she’s kinda American blacks,fatar jikinta mai kyau tana fidda wani irin sparkling mai d’aukan ido cike da burgewa kai baka ce zata kasance a irin wannan gidajen ba,sam baza’a a sata a jerin masu tsayi ba,haka ma baza’a ce mata gajera ba,dai² misali tana da d’an tsayin ta cif wanda ya sake k’awata gangar jikinta da Allah (S.W.T) ya hallice ta da shi,duk da tana sanye ne da hijab wanda tsayin sa duka yake saman knees d’inta,buh hakan baya hanawa idan har tayi taku d’aya next to go forward jikinta yayi wani irin girgizawa kamar tana sane ne take yin hakan,tana da round face mai d’auke da manyan idanu nd smaller mouth,haka nan da dogon hancinta,kyau dai² wanda duk wani bawa zaiyi fatan ya kasance yana da shi a tare da wannan baiwar Allah akwai shi sai muce “masha Allah da yadda duk ubangiji ya haliccemu sannan mu kasance masu yi masa godiya a kowane lokaci”,sannu a hankali take ci gaba da tafiya tamkar wata jinin sarauta nd deep kuma not minding cewa wani abu zai iya faruwa a time d’in kasancewar sanyin safiya da hanya yake shiru babu alamun mutane sun fara fitowa zuwa gonaki,a haka take ci gaba da tafiyarta cikin nutsuwa har ta k’araso bakin rafi.

    Zaune saman had’ad’d’en rocky mountain bicycle yake ta faman shek’a gudu abunsa  bisa saman bridge d’in dake saman ruwan garin na wudil,as usual idan har zai fita morning exercise,kansa yana d’auke da p-cap black colour daya kusan rufe fuskarsa,yayin da a ta gaban daga saman forehead d’insa a jikin cap d’in aka rubuta PUMA da yellow color,yana sanye cikin sport wear black nd yellow colour wanda duka shima yake d’auke da tambarin company puma,haka nan k’afafunsa suna sakaye cikin wani yellow nd black mens casual shoe shima dake d’auke da rubutun puma wanda ak’alla darajar takalmin kad’ai ya kai #33+k,fatarsa tana da haske haka nan fuskarsa daga ta gefe ya kasance nd yana d’auke ne da wani irin mustache dake fidda kyallin dake nuni da lallaifa yana samun kulawa da gyara,sai dai fuskarsa har a wannan lokacin bata kasance a bayyane yadda mutum zai iya zayyana asalin kyaun wannan matashin ba,,dai² yazo k’arshen bridge d’in a hankali ya fara yin k’asa yana gangarawa zuwa k’ark’ashin bridge d’in wanda k’orama tabi ta k’asansa,ak’alla zuwa wannan lokacin idan da ace za’a lissafa tafiyar da yayi daga cikin KUST (Kano state university of science and technology wudil) na tabbata zata iya kaiwa ak’alla ta mintuna 15 koma ta haura hakan zuwa arean Kausani da yake a wannan lokacin,,sai daya tabbatar ya tsaya sosai sannan ya sauka daga saman bike d’in yana zare p-cap dake saman kansa,bayan ya samu guri daga gefe ya ajiye bike d’in sannan ya tsuguna gaban ruwan yana janye hannun jacket d’insa zuwa sama ya fara d’iban ruwan yana wanke fuskansa,yanayin sanyin safiya da yasa ruwan ya kasance mai sanyi sai ya sashi yin sanyayyar ajiyar zuciya,kyakykyawa ne wanda irinsu ne tun a karon farko ake gane cewa su d’in ajin farko ne a komai na tsarin halittarsu ba sai an kuma na biyu ba,lissafa muku shi b’ata baki ne just imaging,,yana nan tsugune bayan ya gama abunda yake ya sake mik’ewa sannan ya nufi inda bike d’insa yake da niyyan barin gurin da niyyan komawa inda ya fito wato ya kama hanyansa na komawa zuwa campus.

     Har ya d’aga k’afarsa zai haye bisan bike d’in k’aran fad’uwar abu da fashewarsa yasa shi dakatawa,cikin nutsuwarsa ya d’aga madaidaitan idanunsa yana waigawa had’e da duba gurin daga nan inda yake tsaye,ko da yaga bai ga komai ba,sai kawai ya tab’e baki had’e da hayewa saman bike d’in ya juya abunsa cike da niyyansa na barin gurin.

   Cikin wani firgitattun ihu dake yawo a ilahin gurin,da kunnuwan duk wani mai ran dake gurin muryan bazai b’oye daga jinsa ba ta shiga amsa kuwwa a gurin

    “Wayyoo Allah! Taimako,, a taimaka min..! Babu kowa a nan ne,,ku rabu dani…Ku kyale ni..Me nayi muku.!?”

    Cikin hanzari ya dire daga saman bike d’in had’e da ci gaba da dube² wanda jin wannan ihun yasa shi tunanin definitely ne something must happen,dole ne akwai wani abu a bayan wannan ihun da yaji buh duk iya hangensa har lokacin bai ga ko da kwaro ya wuce ta wajen ba,haka nan ihun daya ji daga sau d’ayan nan sai yaji anyi shiru,sak’e² zuciyansa ta fara akan ya duba ko kuma yayi saurin barin gurin,,ya d’an shafe mintuna yana nan tsaye,can wajen kimanin mintuna biyu ba tare daya gama yanke hukunci ba,nd still yana waiwayawa asides ko zai ga wani alama da zai masa showing inda AL’AMARIN yake faruwa,,sannu a hankali ya kalli gurin sannan ya ajiye bike d’in ya fara ratsawa ta cikin gonakin dake gurin yana tafiya cikin sanyi da son kama koma mene ne a gurin,buh rashin wadataccen haske da yake har lokacin garin ba wai ya gama wayewa bane ga kuma duhun shuke² shi ne yafi komai bashi takaici,da sauri ya shiga laluba jikinsa ko zai samu abunda zai haska gudun kada ya had’u da wani halittar mai cutarwa amma sai bai samu ba wanda sai ma a lokacin ne ya tuna da ya bar phones d’in nasa a hostel,azama ya sake k’arawa yana ratsa tsakanin shuke²n.

    Kokawa sosai suke yi da su,k’artin maza har uku a kanta,amma a hakan sai son k’wace kanta daga gare su take ba tare da girma,yawansu ko k’arfinsu ya tsorata taba,illah mugun nufinsu a kanta da take hangowa,buh ta kasa saboda k’arfin namiji koda guda d’aya nema da mace bazai tab’a zama d’aya ba bare ita da suka had’un mata har su uku,dole ne ta kasa k’wacewa daga irin rik’on da suka mata,,ihu take son sake yi a karo na biyu ko zata samu ubangiji ya aiko mata mai ceton ta amma shima d’in basu bata wannan damar ba dan yadda suka d’aure mata baki da hijab d’inta,hakama sauran jikinta duk sun d’aure ta,,wanda zuwa wannan lokaci tuni har hawaye ya gama jik’a mata fuska kamar yadda take jin tsoron faruwar abunda suke shirin aikata mata haka zuciyarta cike take da fargabar rashin samun mai ceton ta,,dai² wannan lokacin ne d’aya cikin samarin dake kewaye da ita ya kalleta yana yi mata murmushi kafin ya furta

   *”SABINA.!* kenan wato kin d’auki magana ta wasa ko..? Shin kina ganin k’iyayyar da ke da mahaifinki kuke nunawa akan maganar aure na zai hana ni aiwatar da wani k’udurin na daban ne..?? Kina kallon kanki a mai wayo ko..?? Idan kuwa har kunyi wannan tunanin lallai kun jahilci kanku da har kuke tsammanin idan kunk’i amincewa da batun aure zan rabu da ku..Ni ba irin ku bane,kuma ba irin sauran mutane ba,da kuke d’ora yak’inin ku akan *HAK’URI* sam ni ban san shi ba,,kuma ban had’a hanya ta da shi ba,abunda kuka kasa fahimta ta da shi shine,,a duk lokacin dana ga abu na nuna ina so,to ko ta wane hanya saina na tabbatar na mallake shi,,dan haka a yau zan mallake ki,zan maida ke tawa,da duk wani abu da kike tak’ama da shi,,zan cimma burina a kanki,idan yaso kinga babu yadda tsoho zai yi dolensa ne ya bari a d’aura mana aure anjima tunda ya san babu wanda zai yarda ya auri *RAGOWA…!* ko ya kuka ce y’an hannuna..!?”

    Dariya dukansu uku suka shek’e da ita har suna buga k’afa irin ta tura haushi d’innan,ita kuwa Sabina dake yashe a gurin yunk’urin magana ta shiga yi a yayin da wasu hawayen bak’in ciki suke sake tunkud’owa,,dariya still duka suke yi mata,cikin wani irin murya wanda yayi magana ta farko ya kalleta yana rawa da girgizawa tamkar wani d’an iska kafin ya d’age kai da fad’in

  “Wai magana kike son yi ne..?? Naga kina kallona kina girgiza kai..wani abu zaki ce..??”

  Saurin girgiza masa kai tayi tana matse ido

  “Hhhh! Gayu kunji fa wai magana za tayi..! Yo maganar ya wuce tace nayi hak’uri na kyaleta,, Hhh Cikin ku ko akwai wanda zai taimaka mata ne tayi magana..??”

  Dariya suka sake shek’ewa da shi can daga gefensa na dama wanda ke kusa da shi d’in ya ce

   “Haba oga..! Waye zai bata wannan damar,,haka kawai muna ganin gara a gaban mu muje ta wuce mu..ai da zarar mun bud’e mata baki shi kenan asirin mu ya gama tonuwa,,dan haka kawai mu k’addamar mata..Amma fa oga kada ka manta nine a layi,,daga kai sai ni ko ya oga..!?”

   Dariya sosai suka sake fashewa da shi wanda aka kira da oga yace

   “Shege GOJE kace kai duk wannan batun naka hanya kake gyarawa kanka..”

   “Aaa..! Mai gida wa yak’i banza tunda ka lamunce mana yau d’aya dai..??”

 

    “Gaskiya fa sarki ina ganin kamar GOJE yayi gaskiya,garama kawai mu hanzarta tun kafin tsohon nan naku ya biyo sahu..Allah wallahi ka sanshi baya sanya akan wannan kadarar..”

  Duka suka kalleshi suna had’a baki da cewa

   “Shege a haka kamar baka magana amma kaji shi yanzun har cewa yake ayi sauri..!”

  Cewar GOJE kenan da yake dariya k’asa²,amma ga shi ogan nasu kuwa wani sabon had’e rai yayi yana kallonsa had’e da nannad’o wata uwar ashar yana fad’in

  “Kai dan uwarka waye tsohon namu..?? Kana nufin wannan rikitaccen dattijon nata ne ya zama nawa.??”

  “Sorry mai gida,,,ai gani nayi kai da ita duk yumb’unku iri d’aya ne..Shi yasa nace ehh haka..ka gane mana ba wani ehh abu daban bane nake nufi.. Ko yah kace GOJE.!?”

   Shi dai GOJE kallonsa yayi yana murmusawa kafin yace

“Ehh! Kuma fa kaima kace wani abu ILA..Amma dai kasan oga baya son irin wannan wargin..!”

  Kafinma ya kai aya tuni ogan nasu ya datse shi a maganar tasa da cewa

  “Amma dan uwarka kai wane irin kija(jaki) ne.? bance kada ka sake cewa wannan dattijon tsohona ba,alak’atar dake tsakanimu da shi daban,alak’ar dake tsakanina daku daban,dan haka ni bai haife niba,amma idan har ka sake Allah sai na cire maka hak’ori idan ma ban fafe kaba,,,,kawai²..!”

   Da yake duk sun san yaren nan take ILA ya shiga bashi hak’uri dan yasan ogan nasu akwai saurin d’aukan d’umi,bai tsaya sauraren ILA ba ya buga musu tsawa da cewa

  “Dallah kusa kai can ku jira ni..kai kuma ehh daga yau ka kiyaye harshenka,idan ba haka ba Allah zamu dunga samun sab’ani..”

 

   “Ayi masa afuwa mai gida,,zai kiyaye nan gaba..”

  Fad’in GOJE da yake wani bud’awa kamar wanda zai shiga filin dambe,,murmushin da mai gidan nasu yayi ne ya bawa ILA sukuni had’e da tabbacin sarki ya hak’ura dan haka ko da suka ankare da abunda yake nufi da yace kawai²,kuma yace su sa kai nan take suka juya had’e da d’an bada tazara tsakaninsu suna masu hangen hanya ko zasu ji motsin tahowar wani suyi alerting nasa.

     A kanta yake tsaye yayi severing legs yana mata dariya gami da fara untie na threads dake jikin trouser d’insa,,cikin zuciyar Sabina babu abunda take face sake kiran sunan Allah da neman taimakonsa akan ya ceceta daga sharrin wannan azzaluman bayin nasa,idanunta a rufe dan tunda ya tsaya a kanta ya fara k’ok’arin kwance mad’auran wandon ta sake shiga matsananciyar damuwa da fargabar abunda zai faru da ita,k’irjinta a lokacin banda matsanancin bugu babu abunda yake,gashi duka sun d’aure ta babu ta yadda zata iya tashi bare ta tseratar da kanta.

   Har lokacin bai yanke tsammani ba duk da dai yayi iya yinsa bai ga kowa a gurin ba haka yaci gaba da nausawa tsakanin duhun shuk’e²n cikin sand’a,,ya d’auki ak’alla mintuna sama da biyar yana kewaye gurin da yaji sautin ya fito ba tare daya ga even a needle ba bare yaga mai ihun,hakan sai yasa shi fara cire rai daga neman abunda ba shi da tabbacin gani ya kuma juyawa da niyyar tafiya,motsi da nishin mutum da yake ji daga gefensa kad’an yasa shi waiwayawa,cikin sauri kuma ya nufi gurin duk da irin takatsantsan da yake,yana shiga tsakanin shuke²n dake gurin da yake jin motsin nan sai ya tsinci kansa a d’an wani space wanda daga dukkan alamu shuke²n gurin aka cire aka barshi haka,,idanunsa ya kai dai² inda sautin groan d’in ke fita nan idanunsa suka yi mugun gani wanda yasa take jikinsa duka ya d’auki tsuma,,,addu’ah yayi na neman tsarin Allah daga mugun ji da mugun gani,haka zalika idanunsa a kulle ya juya saboda b’acin ran abunda ya gani bayan ya cije lips,cike da tsananin jin haushi da bak’in ciki ya juya zai bar wajen…

Har lokacin *SABINA* dake kwance cikin wannan mugun yanayin bata fasa kiran sunan mahaliccinmu ba da naiman taimakonsa,wanda izuwa wannan lokacin hankalinta ba k’aramin tashi ya sake yi ba,,buh jin shiru a lokaci guda da yayi yawa a gurin ba tare da sunyi mata komai ba sai ya bata k’warin guiwan fara k’ok’arin bud’e nauyayyun idanunta da zuwa lokacin suka gama hayewa,,a tunanin ta zuwa wannan lokacin ko data ji shiru duka tayi tsammanin sun hak’ura ne sun tafi ko kuma sun hango tahowar wani ne yasa suka gudu dan su b’uya,,sai dai me tana bud’e idanunta nan tayi arba da sarki wanda har lokacin yake tsaye akanta,nd still yana sake k’ok’arin untie na trouser sa,sao dai har lokacin bai kai ga kwance thread d’in ba alamun dake nuni da cewa ya d’aure sune ba yadda ya kamata ba,,ta gefen idanunta taga alamun giftawar mutum,hakan yasa cikin firgici mai had’e da tsoro tayi saurin karkata fuskarta zuwa side d’in da taga alamun an wuce d’in,,,a time d’in shi kam matashin tunda yaga wannan AL’AMARIN cikin matsanancin damuwa ya fara ratsawa ta cikin shuke²n yana tafiya zuciyarsa a cunkushe da tsananin bak’in ciki da b’acin ran dalilin da yasa tun farko bai tafi ba ya tsaya ganin k’wak’waf,,fuskarsa gaba d’aya tayi wani irin ja na zallar damuwa hakama idanunsa da suka kasance masu haske ganin wannan AL’AMARIN har yasa sun fara rikid’ewa,yana tafe sai maimaita kalmar

“Astagfirullah wa’atubu ilaik..”

Yake tun yana yi a zuciyarsa har kalmomin suka bayyana a fili amma still ci gaba yake da sake maimaitawa ba tare daya fasa ba,,,duk da Sabina ba wai ta ga fuskar ko waye ba ne at that time data hango shigewar tasa,haka nan sai taji ta amincewa ranta shi d’in bai kasance d’aya daga cikin su GOJE ba,,tun kafin ta kai ga gama tabbatarwa kanta baya d’aya daga cikin yaran d’an uwan nata da suke kan k’ok’arin keta mata haddi sai ta fara k’ok’arin bin umarnin da zuciyarta take bata,buh ganin da tayi ya juya baya alamun zai koma yasa sai hankalinta k’ara d’agawa,shure² ta fara da k’afafunta da sarki ke tsaye ya raba k’afafu a kai yana ta k’ok’arin cire long trouser dake jikinta bayan zani da take sanye da,,kamar wasa ta shiga shura k’afafun tana fad’in

“Uhmmm! Uhmmm! Uhmmm!”

Duk da bakinta yana k’unshe babu ta yadda za’ayi tayi magana,haka duk jikinta a d’aure yake bare tayi masa alaman da zai gane abunda take nufi sai yasa taci gaba da kallon hanyan daya bi d’in tana ci gaba da shura k’afafun,,,shi kansa matashin har ya fice a gurin haka nan sai ya tsaya kamar wanda aka dakatar,a hankali kwakwalwarsa ta fara nazarin abun daya gani,,tabbas idan har ba wai ace idanunsa sun kasa ganin dai² ba kuma ba k’arya suke son yi masa ba ai kamar yaso ganin yarinyar a d’aure,,shin kaamata guy d’in yayi kenan ko kuwa ita ta kawo kanta gare shi.? Tambayar daya fara zuwa masa kenan a zuciya,,duk da yasan halin wasu y’an matan ne shegen biye² buh ita wannan yanayin daya ganta ciki dole akwai abun tuhuma wamda shi kansa ya kasa tantance wanne yanayi ne d’aya a cikin biyu da yake tunanin.? Cikin azama kamar wanda aka tsikara yayi turning back zuwa gurin da AL’AMARIN yake kan faruwa wanda ya janyo har yana had’awa da d’an gudu.Dai² lokacin daya k’araso d’in ba tare daya tsaya tunani ko tambayar wani abu ba ya sanya hannunsa d’aya ya shak’o wuyan Sarki dake sunkuye a kan Sabina,cike da matsanancin sauri mai tattare da wani irin fushi ya shiga jansa a gurin har sai daya tabbatar ya janye shi akanta,,shi kansa sarki a nasa gefen da mahaukacin fushin ya shiga k’ok’arin juyawa dan yadda yaji an masa irin wannan shak’ar at once kuma ana jansa a k’asa,kokawa ne ya sark’e tsakaninsu sarki yana ta k’ok’arin ganin ya kwaci kansa daga mugun rik’on da aka yi masa wanda har a lokacin bai kaiga ganin fuskar ko waye ba bare ya san wane mai shishshigin ne wannan da har yayi masa katsalandan cikin lamarin sa.

Juyowarsa dai² lokacin daya k’wace daga rik’on tsaurin da matashin yayi masa idanunsa suka yi arba da kyakykyawan matashin dake tsaye akansa yana huci kamar idan yaga babu zai ci,,cike da gadara mai had’e da izgili sarki ya kalle shi kallon wulak’anci yana jinjina kai haka nan muryansa d’auke da wani irin yanayi mai kama dana mutumin da yayi shaye² ya furta

“Malam waye kai..kuma daga ina..??”

Marin daya tsinka masa ya sashi hantsilawa,cikin tsananin mamaki ya d’ago kai a fusace ya kalleshi

“Kan uba..! Kai har ka isa ka sa hannu ka mare ni..!? Waye kai nace..?? Dawa kake tak’ama da har zaka sa hannu ka mare ni..!?”

“Ubanka ne..!”

Ya bashi amsa muryansa d’auke da wani irin izzah yana sake zabga masa wani sabon marin,dafe chicks sarki yayi kafin ya sake d’ago fuskarsa dake cike da tsananin fusata,tabbas ko ba’a fad’a ba a wannan karon kam marin yafi na farko shigarsa,,magana yake son sake yi amma ina bai samu wannan damar ba,dan yadda ya sake d’auke shi da wani gigitaccen marin,yayin da a duk lokacin da yayi nufin yin magana kafinma ya kaiga yin maganar sai ya sake samun k’arin mari,,sai daya jera masa su sun kusa sha biyar amma sarki bai fasa ba,saboda masifar taurin zuciya irin nasa,dan kansa kuma ko da yaji azabar ta isheshi sai ya maze,,a karo na karshe kuma koda yaji saukar marin sai bai iya d’agowa ba,dan a duk lokacin da zai sake marin sa ji yake na biyun tamkar ya zarce na farko azaba,cikin hargagi sarki dake sunkuye kan babu yadda zai yi ya shiga magana cikin d’aga murya da hargowa

“Wai kai to waye ne..kuma ina ruwanka,me nayi maka ma da zaka zo kana duka na kamar wani dank’a..??”

Dundu ya sakar masa a tsakiyar bayansa wanda ya sa shi yin plat a k’asa had’e da canyara ihun azaba mai razanarwa wanda shi ne dalilin daya janyo hankalin su GOJE zuwa kansu,cikin sauri duka ai gasu sun nufo gurin da son duba abunda yake faruwa,sai dai ko da suka yi arba da sarki kwance a k’asa nan suka yi turus suna masu kallonsa had’e kuma da sake kallon Sabina da har lokacin itama tana nan a kwancen kamar yadda suka barta a d’aure tamkar hunhun goro,sake waigawa suka yi suna masu kai kallonsu akan matashin da suka gani wanda basu san ko waye ba nd kuma basu san mene ne actual abunda ya samu sarkin yake ihu ba

“Dallah dan uwarku me kuke yi a tsaye..?? Ku k’addamar mas..!”

Sarki ya fad’a yana share kwallar azaba data ziraro masa,,ba tare da sun ko tsaya tambayar sarki ba’asin abunda ya same shiba,coz su dai sun ganshi a baje a gurin,amma furucinsa kad’ai sai yasa suka yi kan matashin a guje suna fad’in

“Aaahh! K’arya ne wollahi..”

Murmushi ya saki mai ciwo sannan ya kallo inda take kwance,a hankali ta shiga mirgina masa kai gefe tana mai yi masa alama da “A’a”,amma bai ko saurareta ba saima sak’on harara daya aika mata sannan ya janye idanunsa akanta,tun kafin su kaiga k’arasowa inda yake tuni ya kai hannunsa had’e da fizgo wani ice dake kafe a gefe yana daidaita rik’on sa a hannunsa da jiran isowarsu,dai² kwaurin ILA ya kallo yana saitawa dan dama shi ne akan gaban,yana zuwa kusa da shi tunma kafin ya farga tuni ya ajiye masa shi akan k’ashin,ihu ya saki na azaba kafin ya dawo hayyacinsa ya sake d’ora masa a baya,birki GOJE yaja da yake bayan ILA cikin sauri ya juya aguje zai koma inda ya fito,nan take matashin shima ya take k’afarsa ya bishi suka shiga tsere a tsakanin gurin,,a hankali Sabina ta lumshe idanunta tana mai godiya ga Allah (S.W.T) daya kawo mata maceci,,dai² lokacin ne kuma ihun GOJE yasa ta saurin bud’e ido tana karkata kanta zuwa gefen data tsinkayo ihun nasa,kwance ta hango shi a k’asa yana birgima,haka nan matashin shima bai saurara masa ba sai shimfid’a masa icen yake a duk inda yaga dama,tun GOJE yana mirginawa da k’arfinsa yana bashi hak’uri har sai daya gagara,,a hankali ya d’ago kansa lokacin daya tabbatar GOJE yayi laushi sannan yasa hannu ya yafito su ILA da sarki da suka yi tsugune suna kallonsu tamkar monkeys (birrai),,ILA cikin tsoro dan yadda yaga anyiwa GOJE duka yasa shi k’ank’ame jikinsa yana fad’in

“Dan girman zatin Allah Yallab’ai kayi min rai,,wollahi ni dai babu ruwana..dama ni ban sansu ba yanzun na fara ganinsu..”

“A gidan uwarka..D’an shegiya,,wollahi tare muke duka mu uku Yallab’ai..”

Sarki ya fad’a shima cikin damuwa dan yasan matuk’ar suka samu hanyanr guduwa tofa shi zasu bari a tsaka mai wuya

“Ban tambaye ku wannan bayanin ba,,cewa kawai nayi ku zo..”

Matashin ya fad’a cikin husky voice d’insa daya sake firgita su ILA

“Dan girman Allah Yallab’ai wollahi mun san munyi KUSKURE,,,amma dan girman Allah kayi hak’uri,, munyi maka alk’awarin baza mu sake ba..”

Lower lip d’insa ya rik’o yana kallonsu

“Baza ku zoba kenan..??”

“A’a ranka ya dad’e,,wollahi zamu zo..”

“Ahaaa! Ku zo nan..!”

Ya fad’a yana nuna musu inda yake tsaye da icen hannunsa nd yana sake d’aure fuska,kasa tasowa sukayi kowanne jikinsa sai kyarma yake yana kallon d’an uwansa dan sun san matuk’ar suka kai kansu gare shi jibgarsu zaiyi kamar yadda yayiwa GOJE

“Baza ku zo ba kenan..? Ni kuke so na zo..??”

Ya sake tambaya cikin matuk’ar d’aure fuska

“A’a Yallab’ai wollahi bama saika zo ba..Zamu zo da kanmu..”

“Ok..! Maza kada ku b’ata min lokaci..”

Nok’ewa suka ci gaba da yi,nan ya jinjina kai yana nufar inda suke kai tsaye,suna niyyan sake guduwa shima yana binsu,a hakan ya shiga tafka musu icen sai da yayi musu duka dukansu,bayan ya tabbatar baza su moru ba,ya kalle su yana fad’in

“Maza ku kwance ta..!”

Basu bari ya gama fad’a ba suka yi wuf duka su ukun kowanne ya kama nasa b’angaren har sai da suka kwance ta daga mugun d’aurin da suka mata,,a hankali tasa hannu ta rik’e hijab d’inta bayan ta janye shi daga kan fuskarta,wanda sai a lokacin ne y’ar kyakykyawar fuskarta ta bayyana sosai a zahiri saboda yalwar haske dake bayyana hudowar rana,idanunsa akansu duka lokacin data kaiga zira hijab d’in a jikinta,idanunsa sukaa sauka a kanta,mummunan fad’uwa gabansa yayi wanda yasa shi saurin dafe chest yana fad’in

“Laa’ilaha illallah..!”

Idanunsa ya d’an lumshe a hankali sannan ya bud’e su still ya sake ajiye su akanta,itanma shi take kallo coz sai a yanzun ne itama ta samu damar kallonsa ba kamar a d’azun ba da take kwance kuma lokacinma bawai yana tsaye ne a guri guda ba nd hankalinta duka a time d’in baya tareda ita,,d’an murmushi tayi masa tana had’e hannayenta duka biyu yayin da hawaye suka fara ziraro mata,cikin melodious voice nata mai kama da ana busa sarewa ta furta

“Hak’ik’a na godewa ubangiji (S.W.T) bisa aiko ka da yayi a dai² lokacin daya cancanta,domin ka zama mace ci a gare ni,,tabbas na tabbatar ubangiji maji rok’on bayinsa ne shi yasa ya aikoka gareni,,a yau da ace baka zo ba Allah shi kad’ai ya barwa kansa sanin abunda zai iya faruwa da rayuwata,, na gode³ sosai Ubangiji ya saka maka da mafificin alkhairinsa..!”

A hankali take maganar amma yadda take ajiye kowane harafi tana bashi hak’k’in sa,kai baka ce za’a sameta a irin wannan yankin ba,,kallonta yake without yana blinking na eyes d’insa,har ta dasa aya a lokacin da kuka yaci k’arfinta,sheshshek’ar kukanta ne ya sashi dawowa duniyarsa,wanda nan take ya d’an sake lumshe idanunsa a hankali yana jin saukar wani irin yanayi a gaba d’ayan jikinsa,lokacin daya bud’esu kuwa akan su GOJE ya sake sauke su cike da tsantsar bak’in cikin irin d’abi’ar da suka so gwadawa kamar yarinya kamarta,haka nan muryarsa cike da bak’in ciki ya girgiza kai yana fad’in

“Ku yanzun baku ji kunya ba..?? Ace kunyi k’ok’arin ketawa yarinya kamar wannan haddi..?? Me kuke nema da baza ku samu a jikin manyan mata ba sai ita..?? Tayi muku wani abu ne..??”

“Yallab’ai wollahi Sarki ne ya samu tare mata hanya,,wai kawai dan ya nuna yana son aurenta,,to kawai sai aka yi rashin sa’a tsohonta yak’i yarda,,shi nefa ehh kawai mu kuma muka yi ehhh k’ok’arin k’addamar mata..!”

Fuska yayi squeeze cikin jimami ya maimaita

“Kuka yi k’ok’arin k’addamar mata..!? Kai baka ji kunyar fad’ar haka ba..??”

Kai ILA ya sunkuyar da yake dama a cikinsu duk ya fisu tsoro,cike da takaicinsu matashin ya d’an sake kallonta,har lokacin ita kuwa Sabina bata fasa kukan ba,cikin tausayawa ya jinjina kai sannan ya sake kallon su GOJE yana fad’in

“Tabbas kun ci sa’a a yau bana cikin mood d’in da zansa a kama ku a d’aure,,buh ku sani daga yau wannan shi ne zai zama na k’arshe matuk’ar kuka sake kwatantawa ba wai ina nufin a kanta ba,A’a akan koma waye lallai ne zansa a d’aure min ku,,,kun fuskanta ko..??”

“Wollahi Yallab’ai bama zamu sake ba in sha Allah..!”

Jinjina kai ya d’an yi sannan yace

“Maza kuje ku bata hak’uri,,nd make sure ta hak’ura idan kuma ba haka ba…!”

Bai gama rufe baki ba duka suka durkusa a gabanta fad’i suke

“Dan girman Allah Aunty Sabina ki yafe mana,,,mun tuba wollahi,bama za mu sake ba, idan kuma har muka yi miki ko da kallon banza nema mun yarda ki sanar masa a kaimu caji ofis a kulle..!”

A hankali Sabina dake gefe a tsaye ta kalli yadda suka zagayeta kamar zasu shige cikin k’asa dan ladabi,,idanunta ta d’an lumshe a hankali kuma ta saki d’an murmushi,,duk abunda ake akan idonsa yana tsaye a bayansu ya hard’e hannayensa bisa chest d’insa,yadda tayi murmushi sai yasa beautiful point d’inta lotsawa,shima lumshe idon ya tsinci kansa da yi sannan ya d’an yi murmushi,,aifa murmushin da Sabina tayi nan yasa ILA juyawa da sauri cikin murna ya furta

“Yallab’ai wollahi ta hak’ura kaga ma har murmushi tayi,,dan girman Allah,idan har kana k’aunar mahaifanka kaima ka yafe mana..!”

Saurin bud’e lumsassun idanunsa yayi,tabbas sai a lokacin tunanin sa ya dawo dai² saboda ambaton iyayensa da ILA yayi,a hankali kuma sai ya d’ago tsintsiyar hannunsa ya kafa idanunsa akan waterproof bluetooth smart anniversary watche d’insa,nan take a gogon ya nuna masa 7:40am,a hankali ya dafe kai yana fad’in

“Ya salaam..!”

Dan yadda ya tamawa lectures d’in yau amma sai gashi wannan uzurin ya gifta masa ba tare daya koma ba bare ya shirya ya shiga lecture d’in,d’an siririn tsaki yaja sannan ya kallesu da sauri yana fad’in

“Ku b’ace min a nan,,kada ku sake fuskokin ku su k’ara bayyana a idanuna,,idan ba haka ba zaku ga yadda zanyi da ku..!”

Rigegeniya suka fara yi wajen tashi,sai dai jikinsu duka yayi tsami buh a hakan sai da suka yi godiyar dole daya sake sasu suyi mata sannan kowannensu ya shiga jan jiki suka d’auki hanyar barin wajen,,,lokacin daya rage daga Sabina sai matashin nan ya d’an sake kallonta yana fad’in

“Ina kika nufa yanzun..??”

Duk da tambayan yazo mata a bazata dan ita kam tana can duniyar wasa da gefen hijab d’inta,amma sai bata amsa masa ba bare ta d’ago ta kalleshi,sai daya sake maimaitawa sannan ta d’ago kanta a hankali tana sauke idanunta idanunta can wani gurin daban,sannan cikin sanyin ta tace

“Gida zanje..!”

Sai daya jinjina kai yaja numfashi sannan ya ce

“Ok..! Muje na raka ki..”

“A’a ka barshi kawai bama saika jeba,,haka ma na gode sosai..!”

Kallonta ya d’anyi ya tab’e baki cikin husky voice d’insa ya sake furta

“Ba shawararki na nema ba,cewa nayi muje,,nd kiyi hankali kema,coz ba ko wane magana nake fad’a ake min musu ba..Saboda haka let’s go..!”

Ya k’arasa fad’a yana mai sake d’aure fuskar sa,,,saurin kallonsa tayi sai dai shi d’in bai ko kalli inda take ba,dan wani sabon d’aure fuskan da yayima nan take sai yasa gabanta ya shiga fad’uwa,,babu yadda ta iya haka nan bata da zab’in daya wuce bin umarnin sa,dan haka sai kawai ta wuce kan gaba shi kuma ya shiga binta a bayan ba tare da sun sake cewa ko a bane suka ci gaba da nausawa ta cikin shuke²n har zuwa lokacin da suka kai ga fita daga cikin gonakin suka sake d’aukan hanyar da zata sada su da rugar ta *MALAM SHEHU MAI DARASU.*

Sunyi tafiya mai d’an nisa kafin su isa ainihin castle d’in da rugar take,,tun daga nesa lokacin da suka nufo k’ofar gidansu,Sabina ta hango mahaifinta tsaye a k’ofar gidan kamar mai jiran k’arasowan su,sam bata kula da yanayin da yake ciki ba dan haka da murnarta taci gaba da nufar k’ofar gadan²,ko data isa daf da shi d’in kafin ta kai ga shigewa cikin gida nan sai ta furta

“Babanah.. Barka da safiya,an tashi lafiya..?”

At once kuma tana durk’usawa a k’asa fuskarta d’auke da yalwataccen fara’a,,sai a lokacin idanun baban Sabina suka sauka akan mutumin dake tsaye a bayanta d’in,ba tare da Sabina ko shi kansa matashin sun ankara ba sai kawai suka ji saukar mari wanda duka yasa su d’agowa suka bishi da kallon tsantsar mamaki…

*Tofa..wannan shi ne farawa da bismillah,,,, ko waye aka mara haka,,Allahu a’alaam..*Fuskarsa cike da tsantsar mamakin dalilin da yasa dattijon ya mare shi yake binsa da kallo,sai dai ya kasa bud’e baki yayi masa magana bare ya tambaye shi dalilin da yasa hakan ya faru,al’halin yasan bai masa laifin komai ba,hasalima dai yasan basu tab’a had’uwa ba bare yace ko yayi masa wani laifin before,nd a yanzun da suke tsaye shi ne farkon fara had’uwarsu da juna,,ita kanta Sabina ko data d’ago fuskarta wanda k’aran saukar marin ne yayi sanadin d’agowan nata cikin tsananin mamaki mai had’e da damuwa ta furta

     “Babah..!?”

  Sai dai ko kafin ta kaiga sake yin magana tuni baban nata ya d’aga mata hannu alamun tayi masa shiru kada tace da shi komai,cikin matsananciyar damuwa sai ta ja baki tayi shirun kamar yadda ya umarceta,amma kuma sai me? Sai taga Baban ya sake cak’umo saurayin yana niyyar sake marinsa a karo na biyu,,da saurinta ta matso jikin Baban ta rik’o gefen rigarsa,murya cike da tashin hankali take fad’in

   “A’a Babah kada ka dake shi..Dan girman Allah kayi hak’uri ka rabu da shi,,bai yifa laifin komai ba..!”

  Cikin tsananin mamaki ya waiwayawa yana  kallonta ba tare daya aikata abunda zuciyarsa take umartarsa dayi ba

      “Sabina wuce ki shiga gida..!”

   Baffanta dake tsaye a bayansu ya ambata yana hararan sBaban nata daya cakumo saurayin,a hankali ta shiga girgiza kai hawaye suna zirarowa daga idanunta cikin muryanta mai tattare da fargaba ta furta

    “A’a baffa,,bazan iya shiga ba,,dan Allah ka bawa Babanah hak’uri,,kace masa kada ya dake shi..Dan Allah.. Laifin me yayi !?”

  Yadda take yi yasa dukansu daga baban nata har baffanta d’in suka k’ame a gurin tamkar wad’anda akayi sculpturing nasu suna binsu da kallon mamaki.

   Kuka sosai sarki yake rusawa a tsakar gidan,yayin da matan gidan da y’an matasan samari kamarsa sai bashi baki suke da fad’ar maganganu marasa dad’i akan lamarin daya afkun,,daga can gefe kuwa ita kam y’ar dattijuwar dake zaune wacce duk abunda ake a gidan sam tak’i yarda ta kallesu bare har suyi tunanin zata tanka musu,hasalima ita ji tayi abun bai kwanta mata ba shi yasa ko kallo basu isheta yi ba,ta ci gaba da faman iza wuta abunta,,hak’uri suke ta bashi amma kamar wanda ake zugawa sam yak’i yin shirun,a haka dai da suka ga abun yafi k’arfinsu sai duk mutanen suka shiga fashewa d’aya bayan d’aya, har sai daya rage saura bai wuce su biyu ba,wato shi kad’ai da kuma wata mata dake rik’e da shi,wanda ta shiga jansa suka fara tafiya da niyyar barin gurin suna tafe tana yarwa da waccan matar magana cikin jin haushi,,har sun d’an matsa a gurin sai sarki ya faki idanun jama’a yayi wuf ya nufi hanyar fita daga gidan,a dai² k’ofar fita ya lab’e daga jikin dangar gidan yana lek’en waje fuskarsa da matsanancin farin cikin abunda ya fara hangowa,ba tare da tunanin komai ba ko AL’AMARIN zai canja yake lek’e abunsa,,lek’awarsa a dai² lokacin karaf sai suka had’a ido da shi,wanda yasa take k’irjinsa ya bada mugun sauti,haka nan ko da suka yi arba da matashin daya gama jibgarsu d’in bada jimawa ba,sai kuma ya ga Sabina tsaye tana kuka nan sai ya d’an saki murmushi dan yasan babu yadda za’ayi iyayen nasuma su yarda da abunda zata ce tunda yazo ya gama yi musu famfo,,wani killer smile matashin ya saki mai ciwo dan kuwa ko babu komai zuwa yanzun ya fahimci abunda ke kan faruwa,sai dai har lokacin yana rik’e a hannun baban Sabina dan kuwa bai sake shi ba,shima kuma baiyi k’ok’arin k’wace jikinsa daga gare shiba,yana nan tsayen still yana jiran ganin abunda zai sake biyo baya

   “Ke Sabina me kike son nuna mana ne..?? Ki wuce ki shiga gida nace..!”

  Kai taci gaba da girgizawa idanunta har lokacin suna zubar da hawaye,dan ita kam bata fahimci kan abunda yake faruwa ba,baffanta da yayi mata magana ko da yaga haka duk da yana cikin tsananin mamaki sai ya tsinci kansa da tambayarta

“Sabina shin kina nufin wannan ba shi ne wanda aka ce ya kama ki a bayan gari ba..??”

   Da matuk’ar mamaki ta juya ta kalli baffanta da yake maganar sannan tayi saurin sake kallon sarki da yake lab’e a bayan baffan ta kuma kalli Babanta daya saka kunne yana jiran yaji me zata ce

   “Me kace baffa..?? Wannan d’in aka ce ya kama ni..?? A ina aka yi haka..? Waye ya fad’a..!?”

   Ajere tayi ta sakin tambayoyin ba tare data jira baffan ya amsa mata d’aya ba tana kuma kallonsa fuskarta d’auke da matsanancin mamaki,,suma kallonta suke da mamakin kamar yadda take yi musu

  “Ke bana son shashancin banza,,ki fad’a mana abunda yayi miki yanzun nan,,shin gaskiya ne ya rik’e ki ko A’a..??”

   Bakinta ta toshe hawaye na sake mata tsere akan y’ar fuskarta tana kuma girgiza kai,Babanta kam da zuwa wannan lokacin ya gama k’ulewa cikin tsawa ya furta

  “Ki yiwa mutane bayanin abunda yayi miki kin tsaya mana shirme..Me kike jin tsoro ne..??”

  Kai taci gaba da girgizawa kamar wata wace ta samu matsalar ji da magana,buh duk da irin tsawar da baban yayi mata sam ta kasa magana,,baffanta daya fara fuskantar akwai matsala nan ya matso kusa da inda ya kama hannunta,cikin tausasa murya ya kalleta tare da cewa

  “Sabina ina so ki bud’e baki kiyi min magana,shin da gaske ne yayi miki wani abu..??”

   Kai ta girgiza alamun A’a,,Babanta kam tuni ya gama zuwa wuya da shirun ta a lokacin,ko da ganin ta sake girgiza kai cikin masifar fad’a mai tafe da b’acin rai yace

  “Dan ubanki baza ki yi magana shi ne baza ki iya ba,kike karkad’a mana kai,,mun zama sa’anninki ko..!?”+

    “Kayi hak’uri Baba..!”

   Muryanta cike da tsoro tayi furucin

    “Sabina kalle ni nan,,maza kiyi min bayanin abunda ya faru kinji ko,,ai ni na tambaye ki, dan haka kada ki ji tsoro kin ji ko..!?”

  A hankali ta sake furta

   “To baffa..!”

Kai ya kad’a mata sannan ya ce

  “Da gaske ne wani abu ya faru dake a bayan gari…!?”

    “Ehh baffa..!”

  Ta ambata tana sunkuyar da kai k’asa,a fusace Babanta ya d’aga hannu da niyyar marin saurayin,baffanta yayi saurin fad’in

   “A’a *AMINU* kada kayi haka,,me yasa kake son aiwatar da abunda zuciyarka ta umarce ka ne..?? Al’halin har yanzun baka tabbatar da gaskiyar abunda ya faru ba..?? Har kullum ina horonka da kafin ka yanke hukunci ka fara tsananta bincike akan komai,,ba daga an kawo maka magana kace zaka hau kayi hukunci ba,saboda na tabbatar ba ko wace magana ce ake fad’an ta take zama gaskiya ba..!”

   Huci kawai baban Sabina yake amma bai so aka ce d’an uwan nasa ya dakatar da shi ba,dan yadda yaji maganar nan a yanzun bashi da burin daya wuce ya hukunta duk wanda ya tab’a masa tilon y’arsa mace da yake ji da gani da ita,wacce a kullum cikin taka tsantsan yake da rayuwarta,haka nan cike da burin ganin ya aurar da ita ga mutumin k’warai kamar yadda addini yayi umarni da iyaye su zab’awa y’ay’ansu mazaje na gari

  “Kin tabbatar abunda kika fad’a min haka ne Sabina..?? Kuma abunda d’an uwanki yazo ya fad’a haka ne ya farun..??”

   Kanta ta d’aga ta kalli baffan idanunta da zuciyarta cike taf da alamomin tambaya akan mene ne sarki yazo gida ya fad’a..??

   “Dake nake Sabina da gaske ne wannan matashin yayi miki wani abu..??”

   Wahalallen yahu ta had’iye dan kuwa ko babu komai yanzun itama ta fara fahimtar abunda yake faruwa da dalilin da yasa shi lab’ewa yana lek’en su,,wanda a tak’aice ta gano cewa sarki yazo gida ya fad’a musu k’arya da gaskiya,duk da bata san mene actual d’in abunda ya fad’a d’in ba har yanzun,sai ta sake had’iye yahu,sannan a hankali ta girgiza kai ta bud’e baki da kyar tana cewa

   “A’a baffa ni babu abunda yayi min..Bai yi min komai ba face taimakona da yayi..”

  “Kin tabbatar babu abunda ya faru tsakaninki da shi..??”

   Ko kafin tayi magana Babanta cikin masifa ya tari numfashin baffan da cewa

  “K’arya take Yaya baka ga yadda take k’ik’k’ifta idanu ba,,wato kema kin zama munafuka ko..? Har kin samu damar da zaki dunga bin samari ko *HAFSATU..??* shi kenan ai,kije ki aikata duk abunda kika so,bazan tab’a hanaki ba,amma ki sani sai Allah yayi mana sakayya ni da mahaifiyarki,,irin wahalar da muke sha akan ganin mun inganta rayuwarki,,shi kenan kije ki aikata duk abunda kika so,ni ko mahaifiyar ki babu wanda zai hana ki,,kinji ko tunda haka kika gani yayi miki..”

  Cikin tsawa baffa ya kalle shi a fusace ya kira sunan sa

  “Aminu..! Ka dawo hayyacinka,ka kuma san irin maganganun da bakinka yake ambata,,kada kaje garin son ka farantawa wasu ka b’atawa wasu,sau nawa zan fad’a maka y’arka ba irin wacce za’ayi ta kawo maka tsaigumi akanta bace ka hau ka zauna..?? Me yasa baka jin magana ne kai kam,,yanzun idan da ace MALAM na raye ai babu yadda za’ayi nayi maka magana kaki saurarena,amma saboda yanzun bani da daraja shi yasa nake fad’a maka kana tsallakewa,shi kenan kaje kayi dukma abunda kaga dama kaji,karka fasa kaima..!”

  A hankali baban ya sauke kai k’asa alamun bai ji dad’in furucin yayan nasa akansa ba,cikin girmamawa da ladabi kuma ya furta

  “Kayi hak’uri yaya,amma ni gani nayi ai babu yadda za’ayi d’an uwanta ya k’irk’iro irin wannan maganar ya fad’a mana..”

  “Koma dai mene ai sai dana fad’a maka mu fara yin bincike muji ko..?? Amma saboda kafi kowa zuciya shi ne kake k’ok’arin aikata abunda kaga dama,shin zafin zuciyarka shi ne zaisa mu samu amsar da muke buk’ata daga gareta..??”

  “Kayi hak’uri Yaya..!”

Tsaki baffan yaja sannan ya maida hankalinsa kanta yana fad’in

  *”SHALELE* maza ki fad’a min komai kada kiji tsoron..Shin mene ne ya faru dake..??”

   Sai data kalli inda Babanta yake sannan ta fara zayyanawa baffan duk abunda ya faru tun daga fitowarta a gidan har zuwanta bakin rafi da abunda su sarki suka mata,haka nan taimakon da saurayin yayi mata,ba tare data rage ko wasali ba duka ta zayyana masa,,ko data gama fad’a musu abunda ya faru d’in wani mugun kallo baffan ya sakarwa Babanta cike da jin haushinsa yace

  “Sai dana fad’a maka ai,amma taurin kai ya hana ka bibiyi inda gaskiya take,,gashi nan ai ka kunyata kanka.. Sai ka saki d’an mutane ai yanzun tunda kaji gaskiyar abunda ya faru ko..!?”

    Cike da tsananin jin nauyin abunda ya aikata d’in shima baban nata ya sauke kai k’asa kafin ya saki matashin

      “Shi kenan *SHALELE* maza shiga gida kinji,,Allah yayi miki albarka..amma ki daina fita da irin wannan safiyar,sannan ko waye yace zai aikeki in dai mutane basu fara fitowa ba kice masa nace baza kije ba,,kinji ni ko..?”

      A hankali ta girgiza kai sannan tace

       “To baffa.!”

   

     “Maza wuce kije abunki kinji..!”

     Jikinta babu k’wari ta juya ta tafiya zuwa hanyan cikin gidan,har tayi taku biyu sai kuma ta tsaya had’e da waiwayowa,a hankali ta ajiye idanunta akansa had’e da yi masa murmushin ta,,shi kam a gare shi ajiyayyun numfashi ya sauke sannan ya lumshe idanunsa,dai² lokacin baffa ya k’arasa inda suke ya rik’o hannunsa

       “Samari muje ko..!?”

    Ya janye shi suka nufi hanyar cikin gidan tare,,da sauri Sabina tayi cikin gidan itama dan ganin sun taho,wanda shigowarta yayi dai² da lokacin da sarki ya juya shima zai bar wajen dan duk abunda akayi akan idanunsa ne,yana gurin har lokacin a lab’e yana saurare sai dai sam baiji dad’in yadda reshe ya juye da mujiya ba,,harara Sabina ta aika masa da ita mai d’auke da sak’on tsantsar k’iyayyarsa,cikin jin zafinsa kuma ta girgiza kai,sai dai bata ce masa komai ba ta wuce abunta,tsaki yayi shima zai bar wajen dan yadda yaci buri akanta sai gashi anyi rashin sa’a wani banza yazo ya rusa masa plan,girgiza kai shima yayi cikin kurari ya furta

      “Sai na cimma burina akanki Sabina,,sai nayi nasara..!”

      Yana fad’in haka ya saki murmushin mugunta sannan ya d’aga k’afarsa a gurin

      “Kaii! *LADO* zo nan dan uwa ka..!”

      Muryan baffa da shigowarsu kenan shi da matashin ta ambata,k’yam sarki yayi a gurin ya kasa matsawa,yadda hantar cikinsa take kad’awa kuwa da jim yadda baffan ya kira shi ba k’aramin tsoro ne ya sake shigarsa ba,amma kafin ya juyo saboda tantiranci sai ya dake kafin ya juya yana b’ata rai

      “Baffa gani..!”

     Kallonsa kawai baffan yayi ya girgiza kai,kome baffan ya tuna kuma sai kawai yace jeka zamu had’u anjima,,zan neme ka,saura kuma ka bar gidan kaji.!?”

    

     Daga haka baffan bai sake cewa komai ba ya wuce hannunsa rik’e da matashin suka nufi wata bukka dake gefe,wacce ita bata shiga ainihin tsakar gidan ba kamar sauran,,k’unk’uni sarki yayiwa baffan wanda shi baima kula ba dan ya riga ya wuce,sai dai matashin dake bayansa da yake ya juya ya,shi yaga abunda yayi d’in,girgiza kai yayi sannan ya wuce shima,zuciyarsa cike da mamakin halin wannan bawan Allah daya ji an kira da suna biyu a lokaci guda,coz a d’azun yaji ance SARKI yanzun kuma yaji dattijon da suka shigo tare ya ambaci LADO,to shin wanne ne d’aya a cikin biyu..?? Shi ne abunda har yanzun ya kasa ganewa,lokacin da suka shiga cikin bukkar,saman traditional mat dake shimfid’e awajen suka zauna,bayan sun gaisa sai baffa ya kalle shi yana murmusawa kafin ya ce

  “Samari shin daga ina ka fito haka..? kuma wane ne kai..?? Mene ne mak’asudin zuwanka nan garin,,sannan yaya ne asalin sunanka..??”

   Numfasawa yayi sannan yayi d’an murmushi da cewa

  “Ni dai baffa suna na *MUHAMMAD KABEER,* dalilin zuwana garin nan kuma ba komai bane face karatu daya kawo ni..!”

   Murmushi baffa yayi sannan ya ce

  “Masha Allah samari,shi kaima makarantar jami’a dake nan cikin wudil kazo ba..??”

    “Ehh! Baffa..nan ne..!”

  “Lallai zuwanka wannan garin alkhairi ne a garemu,,muna godiya sosai da alkhairin ka gare mu,muna kuma yi maka fatan alkhairi,ubangiji yayi maka kyakykyawan jagoranci akan abunda kazo nema,sannan yaci gaba da baka nasara har k’arshen rayuwa..”

   Da ameen ya amsa kansa a k’asa,shi kuwa baffa sai bai saurara ba yaci gaba

   “Abu na biyu ina mai sake baka hak’uri da abunda ya faru tsakaninka da d’an uwana,wato Aminu..Tabbas a wasu lokutan halinsa sai hak’uri,shi yasa kullum nake yawan yi masa fad’an ya daina saurin yanke hukunci,amma baya ji,saboda zuciyarsa ta banza,yanzun dubi abunsa ya aikata wanda sam bai dace ace yayi hakan ba..”

   Murmushi Muhammad yayi sannan ya ce

  “Babu komai baffa,,na tabbatar shima saboda bai san ainihin abunda ya faru bane,amma da bazai yi hakan ba,,kuma baffa ko da ni ne a matsayinsa aka zo aka bani labari kwatankwacin yadda aka fad’a muku,tofa zan iya yin abunda yafi nasa,saboda kare martaba da k’imar ahali na..amma babu komai baffa,sam ni banga laifin baba ba,abunda yayi shi ne dai²..!”

  Murmushi baffan yayi shima sannan yace

  “A’a fa samari,kada kace haka,ai yayi ba dai² ba,kuma nima zan same shi ne,ko dai ya canja wannan muguwar zuciyar tasa ko kuma zamu samu sab’ani a wannan lokacin..”

  Dai² nan baban Sabina ya shigo cikin d’akin bukkar da sallama hakama yanayin da fuskarsa ke d’auke da shi yana bayyanar da jin kunya k’arara,,ga baffa kuwa hararar d’an uwana nasa yayi sannan ya ce

   “Ai saika samu guri ka zauna ko muyi magana..!”

  Murmushi baban Sabina yayi sannan ya zauna k’asa² kuma yana kallon yayan nasa,shi kansa Muhammad da yake gefe abunda dattijon yayi sai daya bashi dariya,sai dai yayi murmushi kawai sannan ya basar,sai dai ko kafin yayi wani yunk’urin nan ya tsinto muryan baban Sabina yana cewa….Muryar baban Sabina d’auke da yanayin jin kunyar abunda ya aikata yake cewa

   “Yaro dan Allah kayi hak’uri bisa abunda na aikata maka,wollahi ban san haka abun yake ba,dan Allah ka gafarce ni,sharrin zuciya da kuma halin d’aukan magana irin nawa yasa ni yanke hukunci cikin fushi,amma dan Allah kayi hak’uri ka yafe min…!”

   Da sauri Muhammad ya kalleshi yana taran numfashinsa

   “Dan Allah baba kayi hak’uri wollahi babu komai,,na san ba don komai kayi haka ba sai dan ka kub’utar da iyalinka,kuma na tabbata duk abunda ka aikata kayi shi ne a bisa rashin sanin gaskiyar AL’AMARI,,amma ka d’auka babu abunda ya faru tsakanin mu,nima tamkar d’a nake a gurinka,kana da damar ka hukunta ni idan nayi maka badai²ba,,komai ya riga ya wuce da izinin Allah,baka yi min komai ba..”

    Cikin jin dad’i baffa ya kalli baban Sabina kafin ya ce

   “Alhamdulillah..! Shin Aminu ko kaga abunda nake yawan sanar da kai..?? A yau abunda ya kamata ace kai a matsayinka na babba kaine kayi,sai gashi ka kasa sai yaro k’arami ne ya gwada maka halin dattako,,shin yanzun kana da bakin magana..?? Me yasa a ko da yaushe baza mu dunga hak’uri da rayuwa ba,,me yasa muke yawan d’aukan al’amura da zafi.?? Wannan dalilin yasa nake yawan fad’a maka ka dunga danne zuciyarka akan abubuwa irin wad’annan,,idan ba haka ba wata rana zuciya zata saka aikata abunda bai kamata ba,,gashi nan ma tun daga yau ka fara ganin abunda nake yawan sanar da kai d’in ai.!”

   Girgiza kai baban Sabina yayi cike da jin dad’in nasihar da d’an uwan nasa yake yawan yi masa a lokuta da dama sannan ya ce

  “Tabbas Yaya yau kam na ga zahirin abunda kake yawan fad’a min,,kuma in sha Allah daga wannan karon nima ina mai tabbatar maka baza’a sake samun matsala makamanciyar wannan ba,,na gode sosai Yaya da yawan sanyani a hanya da kake,ubangiji ya jik’an magabatanmu kuma ya k’ara girma..”

  

  “Ameen” baffa da Muhammad da suke zaune suka fad’a suna d’an yin murmushi kafin baban Sabina ya sake juyawa ga Muhammad dake kusa da shi yana cewa

   “Nafa gode sosai d’an nan..Allah yayi maka albarka,yau gashi a sanadin ka abunda d’an uwana yake yawan nusar dani shekara da shekaru na kasa fahimta,lokaci guda zuwanka yasa na gane,tabbas kai alkhairi ne a tare damu,,zuwanka ya zama wani babban haske a gare mu,,har abada baza mu tab’a mantawa da wannan alkhairin naka gare muba..Allah ya tsare ka,ya shiryar da kai a hanya madaidaiciya..”

   Murmusawa ya sake yi yana fad’in “Ameen baba..”

   Sun d’an yi shiru na wani lokaci sannan baban yace

  “Amma har yanzun bamu san ainihin sunan kaba samari..!”

  

  “Ko kuma dai baka sani ba ko..??”

  Baffa ya fad’a yana murmusawa,,Fuskarsa d’auke da fara’a shima na jin abunda baffa ya fad’a ya amsawa baba da cewa

  “Babah ni suna na *MUHAMMAD KABEER..”*+

  “Masha Allah..! Cewa za kayi mai babban suna ne,,to ubangiji yasa ka kasance mai yin koyi da abunda mai asalin sunan ya bar mana kuma yayi umarni..!”

   Still ya sake yin murmushin kafin suka amsa da “ameen” shi da baffa dake zaune yana kallon su duka,zuciyarsa cike taf da farin ciki,,saurin mik’ewa baba yayi fuskarsa d’auke da fara’a wacce ta gaza boy’ewa ya ce

“Yaya bari naje na dawo,,ba jimawa zanyi ba amma..”

   “To Allah ya tsare,,sai ka dawo d’in..!”

  Murmushi yayi yana tafiya yace

  “Ai Yaya ba wani guri zanje ba,nan cikin gida ne zan shiga na dawo..”

  Murmushi duka suka yi,kafin baffa ya sake cewa

  “To..amma dai duk da haka ai fita za kayi,kuma kafin ka shiga cikin gida zaka wuce hanya ko..??”

  Bai tanka ba saima y’ar dariyar da yayi sannan ya fice,ya bar su baffa suna masa dariyar abunda yayi,,fitowar baban Sabina ke da wuya yana shirin zura takalmansa sai ga LADO yazo giftawa,fuskarsa a had’e ya kalle shi cikin nuna iko yana cewa

    “Kai LADO zo nan..!”

   Sai da LADO ya d’ago ya kalleshi sannan ya ce

   “Ni kake kira baffa..??”

  Maganar tayiwa baban Sabina wani iri,dan yadda ya ga kamar LADON yaso raina masa hankali

  “Shin idan har ba kai nake kira ba,akwai wani LADON na daban a wajen nan ne..??”

  “A’aaa! To baffa ai ni ban san dani kake bane shi yasa na tambaya..kada kaga laifina..shi matambayi ai hausawa sunce baya b’ata..!”.

  Cikin tsananin mamakinsa baffan wato mahaifin Sabina yake kallonsa

  “Kai LADO..Kai..! Yanzun ni kake fad’awa irin wannan maganar..??”

  Gunaguni LADO ya sauke kai k’asa yana yi,wanda sune suka sake tunzura baban Sabina, ba tare da LADO ya ankara da tahowarsa ba sai ji yayi kawai baban ya rik’o wuyan rigarsa dama a k’ule yake da shi tunda ya samu labarin abunda yaso aikatawa y’arsa,sannan kuma saboda ya raina musu hankali yazo ya juya labarin,wanda badon Allah ya tak’aice wahala ba da tuni yazo yana fama da kayan nadama da danasani ,,ko daya samu damar damk’an sa bai saurara ba ko tunanin abunda ya kamata yayi ya zabga masa wani shahararren mari wanda yasa LADO gigicewa ya saki ihun azaba,nan take ihun nasa sai ya janyo hankalin al’ummar gidan baki d’aya kwansu da k’wark’wata suka zagaye su duka

   “Kamar ni ina matsayin wa ga mahaifinka nayi maka magana sai ka tsaya kana min k’unk’uni,,uwaka kake cewa da kake min gunaguni..?? Dama baka sani ba a ciki nake da kai,duk iskancin da kake a garin nan ana zuwa ana fad’a min,dan ban tab’a yi maka magana ba shi yasa yau da iskancin naka ya motsa ka nemi sauke shi akaina da y’ata..?? Saboda nace bazan baka aurenta ba ko..?? Ai dama sam baku dace da juna ba,kana watsatstse da kai zan d’auki y’ata ne na baka..?? Mutumin da bai san darajar iyaye ba,ta ina ne zai san darajar mace..?? Sam halayen ku basu had’a hanya ba haka ma ayyukan ku,,,abisa abunda ka aikata a yau banda dai Allah ya tak’aita,wollahil aziiym da saina nuna maka kai d’in k’aramin shege ne..amma ka sani ba kai kad’ai ba,dukma wanda yake da mugun nufi akan yarinyar nan,wollahi ya shiga hankalinsa idan ba haka ba matuk’ar wani abu ya sake ya same ta sai inda k’arfina ya k’are tsakanina da koma waye,sai dai daga ranar ace zumunci ya lalace..!”

   “Uhmmm! Allah sarki,,kaji fa masu y’ay’a,wad’anda uwa ta haifa,ba kamar namu da muka tsinto a juji ba..To Allah na tuba har mene ne abun alfahari a game da y’a macen da kake ta mana wannan balok’ok’on akanta..?? Mu da muka haifi y’ay’a maza ai mu yafi kamata muyi alfahari ba ku da kuke da mace ba..!”

    Matar dake matsowa kusa da LADO ta fad’a tana yatsina fuska,ran baban Sabina a matuk’ar b’ace ya kalleta sai dai bai tanka mata ba ya girgiza kai kawai

    “Ke Tani shin waye yasa bakin ki a nan gurin..?? Ki kiyaye ni wollahi idan ba so kike na sab’a muku ba..Duk mutum mai hankali taya zai d’auki y’arsa ta cikinsa ya bawa mutun irin LADO..?? Wanda gaba d’ayansa bai kamata ayi alfahari da shi ba,wannan dalilin yasa ko da Aminu yace bazai aura masa ita ba nima nak’i saka bakina a maganar hana shi auren Sabinar,halayen su ba d’aya bane,ta yaya bayan muna jin irin abubuwan da suke aikatawa a gari mu d’auki yarinya kamila kamarta mu had’a ta aure da shi.?? Shin bamu cutar da ita ba idan muka bi son zuciyar mu..?? A yau nima na sake bada goyon baya,idan har Allah yayi mana tsayin rai ko dama ace mun mutu gabanin zuwan lokacin,ban amince a had’a aurensu ba,sannan daga yau kada na ji wani a cikin gidan nan ya sake zuwa min da maganar yana son auren ta,na soke wannan auren had’in aka kowa,dan haka ko wanne yaje ya duba mace a wani ahalin,amma batun auren dangi daga yau na raba shi tunda mun fara samun sab’ani daga wannan gara mu dakatar da abun haka nan,wanda akayi a baya ubangiji ya sanya musu albarka…”

   Muryar baffa dake tsaye a bayansu ya ambata,wanda hakan sai yasa su duka juyawa suka bi shi kallo,sai daifa babu wanda ya isa yace wani abu a game da hukuncin daya yanke d’in dan kuwa ya tabbata,saboda kasancewarsa babba a gaba d’aya ahalin gidan shi yasa maganarsa take kasancewa tamkar yankan wuk’a,,,kaf cikin ahalin babu wanda baiyi farin ciki da wannan batun na baffa ba,musamman samarin dake cikin gidan masu tasowa da wasu a cikinsu dama sun jima suna kyamatar auren had’in da ake yi musu,a dalilin ko wacce tayi maka ko bata yi maka ba haka idan har iyayen suka zauna suka yanke hukunci akan lamarin  babu yadda zaku yi gaba d’ayan ku dole ku hak’ura ku zauna da juna da dad’i ko babu.Lokacin da baffa ya gama maganar juyawa yayi ba tare daya tsaya sauraron cewar kowa ba zuwa cikin bukkar yana fad’in

  “Kai kuma LADO zamu had’u da kai,ba wai na kyaleka bane,zaka ci uwaka tunda dama ita take d’aure maka gindin ka dunga yiwa al’ummah d’iban albarka,zamu had’u ne dukanku zaku sani..!”

    Tani cikin k’unk’uni da yake shi baffa bata iya maida masa da magana gaba da gaba sai dai irin hakan ko kuma a bayan idonsa tayi ta harbin iska yasa yanzun ma tace

      “Sai dai mu san alkhairi,,kuma shi zamu gani..!”

   Bata jira komai ba itama ta janyo hannun LADO tana fad’in

     “Muje ciki kaji d’an albarka..”

   Harara LADO ya sakarwa Sabina da innarta da suka juya suma suka bar wajen,a ciki² kuma yayi k’wafa da cewa

   “Zaku san ni kuka hana aurenta,,aradun Allah dole ma na b’allo muku ruwan da baza ku tab’a iya kare kanku ba,,zan bar muku darasin da sai kunji dama ace kun aura min ita tuntuni,zaku gane KUSKUREN ku,ba dai ni aka tozartar ba,,da kanku zaku fuskanci ba’a tab’a ni a zauna lafiya..”

   Su kam su Sabina koda suka shige d’akin su,babu damuwar komai a ransu,suka zauna don cin abincin da Innar ta zuba musu kafin fitar su,wanda sai a lokacin ne Inna ta samu damar kallon SABINA kallo irin na tsanaki kana ta ce

   “Uwata.! Wai ni mene ne ya had’a ki da LADO kuma a wannan lokacin..??”

   A hankali ta d’ago kyawawan idanunta ta d’an kalli Inna had’e da sakar mata murmushi

   “Inna nima ban sani ba,ban san mene ne na tsare masa ba,ban san me yake nufi dani ba,kawai dai ni abunda na sani tun daya cewa Baba yana son ya bashi aurena yak’i amincewa shi kenan kullum yake takurani,kuma ko a yauma abunda ya faru ban san ya akayi yasan na fita ba har ya bini bakin rafin shi da abokansa..”

   Shiru Inna tayi tana saurarenta wanda ita kuma Sabinar sai taci gaba da zayyana mata abunda ya wakana a fitar tata har zuwa k’arshe,,dogon numfashi Innar ta sauke kana ta kalli tilon y’ar tata

   “Tabbas Sabina akwai wani wanda yasan da fitarki,haka nan ai bazai biki ba duk da kuna da matsala da juna,,amma bama wannan ba,shin mene ne dalilin da yasa ki fita da sassafe irin haka..?? bana ce dake kada ki sake fita a irin wannan lokacin ba..??”

   Shiru tayi tana sunkuyar da kai k’asa,muryanta cikin sanyi da rauni ta ce

  “Kiyi hak’uri Inna,nima ba’a son raina ne na fitan ba,illah gwaggo Tani data aike ni na samo mata ruwa..!”

  “Tani..!? Ta aikeki ki d’ebo mata ruwa..?? Shin bata san Malam ya hana ku fita da wannan lokacin bane..??”

  Cikin jimami da damuwa Innar ta fad’a tana kallon y’ar tata

   “Ai kuwa tayi kai..daga yau duk kawaicin da nake gwada mata akanki wollahi tunda d’anta yayi k’ok’arin haike miki kuma ta goya masa baya,,zata sani dani take zancen wollahi sai dai daga wannan lokacin mu raba dutse a hannun riga..Wato ma tasan ita ta aikeki amma shi ne zata dunga fad’awa mutane magana son ranta..?? Ai kuwa zata san ta tab’a min ahali,wollahi sai dai a daina zaman lafiyar,ai ba tsoronta ake ji ba,dan taga ana rabuwa da ita,shiru² ai ba hauka bane,,wane ne bai san daraja da k’imar ahalinsa ba..??”

     “Inna dan Allah kiyi hak’uri ki kyalesu,dama fa abunda suke so kenan ayi ta tashin hankali a gidan nan,Inna idan kika duba duka cikin gidan nan kowa baya kula lamuransu dan haka kawai mu barsu da Allah,tunda dai babu abunda ya far,mu barsu da Allah,duk muguntarsu in sha Allah wata rana zata koma kansu..”

  ‘Dan jimm Inna tayi kafin ta jinjina kai tana cewa

    “Shi kenan Sabina nayi hak’uri kamar yadda kika ce,zan kyale sune a wannan lokacin saboda kin bani baki,amma matuk’ar suka sake k’ok’arin tab’a min ke wollahi saina gwada musu fushi na,ki ajiye wannan a ranki ko mai dad’ewar lokacin da za’a d’auka idan har wani abu ya sake ratsowa wollahil aziym bazan lamunce shi ba…!”

  “To Inna in sha Allah ma babu abunda zai sake had’a mu da su d’in.”

  Cikin alamu dake nuna karaya Inna ta furta

    “Allah yasa..!”

  

    “Ameen Innata.. Muci abincin to..!”

  Sai lokacin Inna ta kalli kwanon dake gabansu da alamun kamar har ta manta ta d’anyi jim idanunta akan abincin har zuwa wucewar wani lokaci kafin tace

   “Ke bazan Ciba,ki ci abunki ke kad’ai..!”

  Marairaicewa Sabina tayi kamar zata yi kuka

  “Haba Innata yanzun duk akan wannan abun ne yasa baza ki ciba..?? Shi kenan to nima na k’oshi..”

   Ta mik’e daga gurin tana kumbura fuska,,saurin rik’o hannunta Inna tayi ta dawo da ita gabanta ta zaunar

  “Haba SHALELEN Baffa,,ta yaya za’ayi kice baza ki ci abinci ba..??”

  “To Inna ba dai ke bace kika ce bakya ci..!”

  “Shi kenan mu ci to,,kinyi farin ciki..??”

   Murmushi ta saki mai kyau wanda ya bawa fararen hak’oranta damar bayyana kafin ta girgiza kai tana fad’in

  “Ehh! Inna..ai dama u always make me feel happier,,ina alfahari dake..!”

   Sakin baki Inna tayi sororo tana kallon y’ar tata jin ta mata wani yaren na daban,a hankali kuma ta kamo kumatunta duka biyu tana sakin dariya da cewa

  “Ja’ira..! Wato nima sai an gwadamin yaren yahudawa ba..??”

  Dariya itama Sabinar tayi,suna cikin wannan yanayin sai ga Babanta ya shigo d’akin da sallama,tsagaitawa suka yi da dariyar da suke yi suka amsa masa,,shima fuskarsa da fara’a na jin dad’in yanayin daya iske su yayi murmushi kafin ya samu guri ya zauna

   “To..! Wane albishir kuka samu ne haka kuke ta dariya abunku..??”

  “Inafa albishir wannan y’ar taka idan tana nan ai kasan halinta bata tab’a zama bata sa mutum dariya ba..”

 

  “Aaa! Ai hakan yana da kyau,da ace wane ya saka kuka gara ace wane ne ya saka dariya ko ba haka SHALELEN baffanta..??”

   Murmushi ta saki tana matsawa kusa da baban

   “Ehh! Yawwa Baba na san dama kana bayana ai..!”

 

  “Sosai ma kuwa,mu kullum ai muna tare..Babar nan taki ce dai sai..!”

   Da sauri Inna ta tari numfashin sa

  “Nayi me ni kuma..??”

  “Aaahh! To bari dai mu bar kaza a cikin gashinta..Ko kuwa dai mu fige..??”

     “A’a baba a kyaleta..”

  Sabina ta fad’a tana dariya,Inna kam cewa take

  “Gwara dai a fige idan yaso sai mu ga wanda zaiji kunya..!”

  Dariya baban yayi shima ya ce

   “Aahhh! To mun fasa gwara a kyaleta kada mu wahalar da baiwar Allah..”

   Duka sai suka sake yin dariya,,Baban ne ya d’an tsaigaita cikin alamun na wanda yayi mantuwa ya furta

  “Ohh! Ni kam har kun sani zan manta abunda ya kawo ni..”

Inna ta kalleshi da mamaki a fuskarta

  “Malam me kuma muka saka mantawa haka..??”

  “Ehh! To dama na zo ne na shaida miki ki ya kamata a had’a abinci a kaiwa *MUHAMMADU..!”*

  Fuskarta d’auke da alamun tambaya taci gaba da kallonsa kafin tayi k’arfin halin tambaya

    “MALAM wane ne haka..??”

    Shima ita ya kalla yana murmusawa kafin ya bata amsa da

  “Yaron daya taimaki d’iyarki mana shi nake nufi ai..!”

   “Aihoo! To..Bari kuwa na hanzarta..!”

  Tana fad’a tayi saurin mik’ewa,shima baban fita yayi yana cewa

  “Idan kin gama ki bawa uwata ta kai masa yana can tare da Yaya..!”

  Da “to” ta amsa masa fuskarta sai murmushi take saki,tayi hanzarin d’auko wasu gidauniyoyinta sababbi dake ajiye ta fita,nan suka bar Sabina shiru tana tunani a ranta tana tambayar kanta

      “Dama sunansa kenan..??”

   Tun fitar Inna sai ta tsinci kanta da fara y’an tunanuka akan abunda ya faru d’azun,wani abu daya bata dariya lokaci guda shi ne tuna irin yadda yake bawa su LADO umarni tamkar wani fatherhood nasu,data tuna irin kallon da yayi mata sai ta sake sakin murmushi,tana cikin wannan halin sai ga Inna ta dawo d’auke da k’aton tray a hannunta tana fad’in

  “Yawwa uwata maza taso da sauri ki karb’a.. Kada a bar mutum da yunwa ko..??”

  “Toh” tace kafin ta d’auki wani hijab d’in tasa,tray d’in dake hannun Inna ta matsa ta karb’a kana ta fice a d’akin,Inna na bata sak’on ta gaishe shi idan taje,nan ma ta sai ta sake amsa mata da “toh” d’in,,,cikin nutsuwarta take tafiya har ta kawo bakin k’ofar bukkar da suke ciki,a dai² bakin k’ofar sai ta d’an tsaya shiru tana tunanin abunda zata yi,ko kafin tayi sallama nan kunnuwanta suka tsinkayi muryansa yana cewa baffa zai tafi,hakan sai yasa ta sake k’amewa a gurin tamkar wacce akayi sculpturing nata ba tare data motsa ba,haka nan sai ta shiga bin tray d’in hannunta da kallo,a zuciyarta tana jin rashin dad’in abunda ke shirin faruwa…..

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *