ALKAWARIN JINI CHAPTER 2 BY _HAWWA MUH’D USMAN
Www.bankinhausanovels.com.ng
Muryan Baffa ta jiyo yana cewa
“A’a mai babban suna baza muyi haka da kai ba,,ai tunda ka shigo gidan nan yau kam ba zaka tafi ba har sai ka ci wani abu..!”
Murmushi yayi mai sauti kafin ya bawa baffa amsa
“Baffa..! Wollahi sauri nake yi ne na koma makaranta saboda ina da aji yanzun,duk da ma dai nayi latti,tun d’azun ya kamata ace na koma makaranta na shirya.!”+
“Ehh to.! Duk da haka nima bank’i ka tafi ba amma dai tabbas sai ka sawa cikinka wani abu kafin ka wuce d’in,ai kai yanzun ba bak’o bane,kaima d’aya ne daga cikin ahalinmu kaga kuwa babu ta yadda za’ayi mu barka ka tafi ba tare da ka ci wani abuba..!”
Murmushin dai still ya sake yi ba tare daya iya cewa komai ba bare yayiwa baffan musu yaja bakinsa yayi gum,,har lokacin Sabina tana tsaye a bakin k’ofar cikin rashin jin dad’in abunda taji yana fad’a sai dai ko da taji amsar da baffa ya bayar nan take sai ta saki siririyar ajiyar zuciya kana ta bud’e bakinta da ada yayi mata nauyi tana rangad’a sallama,dukansu ne suka amsa mata kafin baffa yace
“Shigo mana SHALELE kika tsaya a waje..!”
A hankali ta matsa jikin k’ofar had’e da janye jigataccen labulen dake k’ofar kana ta shiga tana sake yin wata sallamar
“Yawwa y’ar albarka kamar kuwa kin san maganar da muke yi kenan,ai gara da kika yi hanzarin zuwa..”
Murmushi ta d’anyi sannan ta matsa gabansa ta ajiye tray d’in,,muryan baffa taji yana fad’in
“Uwata..! Ki zauna tare da shi ni zan d’an fita na dawo yanzun nan,kada ki barshi shi d’aya yana jira kinji ko..??”
“Toh baffa..Allah ya tsare hanya..!”
“Ameen uwata..Allah yayi muku albarka..!”
Baffan ya fad’a yana dafa kanta,sannan ya juya ga MUHAMMAD yana cewa
“To mai babban suna zan fita na dawo amma ba jimawa zanyi ba,in sha Allah yanzun zan dawo..”
A hankali ya d’ago kansa ya kalli baffan yana murmusawa shima ya amsa masa da cewa
“To baffa Allah ya kiyaye hanya..A sauka lafiya..!”
Nan baffan ya fita yana amsa musu,,bayan fitar baffa a d’akin sai Sabina ta bud’e babban kofin silver dake saman tray d’in wanda ta shigo da shi,,kyakykyawan damu ne na fura daya ji nono tayi haske,banda k’amshin kayan yaji babu abunda take,ba tare data kalle shi ba ko ta tambaye shi taji zaima sha ko a’a kawai tasa masa ludayi kawai sai ta ajiye masa a gabansa,tana gama abunda zata yi sai ta koma d’an nesa da shi kad’an ta zauna tana wasa da gefen hijab d’inta kanta a k’asa ba tare data sake waiwayarsa ba bare taga abunda yake yi,,d’agowa yayi a hankali lokacin da yaga ta koma gefe ba tare data yi magana ba kana ya tab’e baki,ba tare daya ce mata ko ci kanki ba shima,ya d’auki mug d’in ya fara shan furan,lokacin daya fara shan furan tun a karon farko sanyayyan dad’i irin na furan daya ratsashi sai yasa a hankali ya shiga lumshe idanunsa,while yana yabawa wanda yayi furan a ransa,nd yana ci gaba da kaiwa cikinsa ba tare daya saurara ba,,har ya gama bai yi magana ba,haka itama tana zaune bata ce masa komai ba,ajiye mug d’in yayi dai² lokacin data d’ago kanta dan yadda zaman ya fara damunta gashi duk ta kasa sakewa a gurin,,shi kuwa a gare shi duk motsinta tana yi ne akan idanunsa,dan haka duk abunda take yi yana kula da harma da yadda take yawan yamutse fuska,akai² kuma ta sauya yanayin zamanta,lokacin kuwa ko data d’ago a karo na sau babu adadi karaf sai idanunsu suka had’u,buh ga Sabina sai tayi saurin janye idanunta tana sake sunkuyar da kanta a k’asa,,sake tab’e baki yayi can kuma kamar wanda akace dole sai yayi mata magana,muryansa cike da mulki kamar wani d’an sarki ya furta
“Mene ne dalilin da yasa kike fita da safe.? Ina nufin a irin wannan lokacin da ba kowa ne ya fito ba..??”
Yadda taji yayi maganar haka nan sai taji k’irjinta ya tsananta bugawa,within few secs duk sai ta fara neman nutsuwarta ta rasa,nd bakinta nan take sai yayi mata nauyi ta kasa amsa masa,,yana kula duk da yanayinta dan haka ko da yaga bata amsa ba sai kawai ya share bai sake tambayarta ba,duk da ya gama abunda yake zuwa lokacin amma sai bai musu sallama ba ya ci gaba da zaman jiran dawowar baffa kamar yadda yace ba jimawa zai yiba,,,sun sake shafe tsayin lokaci a hakan ba tare da wani a cikinsu yace da d’an uwansa ci kanka ba,,wanda shi kansa Muhammad d’in a da zuwa lokacin ya gama gajiya da zaman sannan lokaci bayan lokaci tunda yaji shiru baffan bai dawo ba sai ya d’ago hannunsa ya duba lokaci,haka nan kuma sai ya kalli k’ofar shigowa yaga ko baffan yana kan hanyan shigowa,,ko da dai yaga shirun na neman yin yawa sai ya sake kallon sashin da take cikin isa yana sake d’aure fuska
“Daga yau kada ki sake fita idan har baki ji alamun mutane sun fara fitowa ba ko kuma ba tare da wasu zaki fita ba,idan har dan ke kad’ai ce ki hak’ura da fitan,,sannan abu na biyu idan ina magana bana so naji anyi min shiru al’halin ana jina,,dole ne idan har nayi tambaya a nemo amsar daya dace da tambaya na,,,bana son shirme ko wasa a lokacin da nake serious magana da mutum..Hope kin fuskanta..??”
Sai data d’ago kanta jin yadda yake bata command tamkar wani Babanta ko Innarta,zuciyarta cike fal da mamakinsa dan yadda yake nuna mata isa,al’halin tasan basu had’a wata alak’a da juna ba,,sannan abun daya ke sake bata mamaki da shi kuma ta kasa fuskanta a maganarsa shi ne shin idan ya tafi ba shi kenan ba..?? Duk wani abu kuma daya had’asu zai wuce tunda dai taimakonta yayi idan ya tafi ai shi kenan kuma babu tabbacin acema su sake had’uwa,,to amma taji yana cewa idan yayi magana dole ta nemo amsan bashi,shin da ita yake ko kuwa dai kawai yana nufin ga kowama da wani alak’a ya had’a su haka yake..? Ita dai duk ta kasa gane mene ne actual abunda yake nufin,,,yadda tayi shiru ya sashi sakin wani slender breathe kafin yaci gaba da watso mata tambaya
“Mene ne alak’ar ki da wannan guys d’in..??”
Sai data sake damk’an gefen hijab d’inta kafin tayi karfin halin yin magana
“Wanne a ciki..??”
Cikin salon sake had’e rai ya kalleta yace
“What do you want me to do..? Na maimaita miki tambayar..??”
D’agowa ta sake yi ta d’an kalleshi,a hankali tayi k’wafa dan ita dai wannan nuna ikon da isar nasa ya fara hawa mata kai,sam a rayuwarta bata son d’abi’a irin wannan ga koma waye idan har ba wai ace iyayenta ba,had’e rai tayi itama sannan tace
“D’an uwa nane..!”
A ransa yace “ashe taji abunda na tambaya,take son kuma na maimaita mata” amma a fili sai ya d’an harareta yace
“Shi wanne kenan a ciki..??”
Kamar bazata bashi amsa ba can kuma sai ta ce
“Wanda suke cema sarki..”
Jinjina kai yayi kafin ya sake jefo mata wani tambayan
“Sunansa kenan shi d’in..?? Ko kuwa wannan ne sunansa kad’ai..??”
“A’a ba sunansa ba ne,kawai dai su d’in ne a tsakaninsu ne suke fad’a masa hakan,buh i think kamar dai sunan sune dai can na kangararru kuma fitinannu..!”
Jinjina kai ya sake yi yana sakin murmushin irin amsan data bashi
“Okay..! Wannan dai kina nufin kamar sunan ne da su a waje suke amfani da shi..?? Nd akwai wani sunan nasa kuma daban da kuke kiransa dashi a gida ba..??”
“Ehh! Akwai..!”
Ta fad’a a k’agauce dan ita tambayoyin nasa sun fara isarta,jinjina kai yayi cikin gamsuwa sannan cikin salon son takurata ya sake cewa
“Yayi kyau..! Amma yaya kusancinki da shi yake..?? Uhmm! saifa kinyi hak’uri da ni,haka nake da yawan son tambaya..!”
“Babu komai..”
Ta fad’a duk da ta gajin kamar yadda ya fahimta da kansa,amma kuma sai taci gaba da bashi amsar a hakan
“Shi d’in d’an k’anin Babanah ne..!”
“Ohh! Kenan family’n ku d’aya da shi..!?”
“Ehh! Haka ne..”
Jinjina lamarin yake a ransa nd yana kuma hasashen dalilin da yasa d’an uwa na jini zaiyi k’ok’arin zaluntar d’an zuwansa,kamar dai yadda ya kusa faruwa da ita a yau banda dai Allah ya kiyaye,,buh duk iya tunanin sa da son binciko ainihin gaskiyar dalilin da zai sa LADO aikata hakan iya hangensa da k’ulluwarsa ya kasa fahimtar komai,,ba tare daya kalleta ba sai dai ta jiyo muryansa yana magana
“Ina mamakin yadda za’a ce duk alak’ar dake tsakaninku da kusancin ku amma ace yayi k’ok’arin cutar dake,,buh shin kun tab’a samun wani sab’ani da shi ne..?? I mean something haka like kunyi fad’a akan wani abu da zaisa ya rik’e abun a ransa ko kuma dai wani matsala haka na cikin gida ya had’a ku..??”
A hankali ta d’an cije lip d’inta,bayan ta numfasa sannan tace
“Ehh! To nima dai gaskiya ban san wane irin dalilin ne zaisa shi yin hakan ba,buh all i knew dai ba zai wuce kan maganar aurenmu ba da aka k’i amincewa da shi..!”
With much marvel yake kallonta kafin ya maimaita
“Aure..!? Wane iri kenan..??”
Duk da maganarsa ta bata mamaki amma hakan bai hanata yin murmushi ba dan gani take kamar baya fahimtar hausa sosai ko kuma dai me yake nufi ne bata sani ba
“Aure dai irin wanda ake yi a kowane k’abila da jinsi na mutane..!”
Ta fad’a ba tare data kalleshi ba dan dama duk tambayan da yake mata tana daga yadda take tun zamanta take bashi amsa sai dai idan ya fad’i wani abu da taji shi wani iri sai ta d’ago ta kalle shi,jinjina kai ya sake yi yana tab’e baki ba tare daya sake tambayan ta komai ba duka suka sake yin shiru,,kusan mintuna biyar sun sake shud’ewa ita harma ta manta da sunyi batun aurenta da LADO sai ji tayi ya ce
“Kuma kina sonsa dama can..!?”
Idanunta ta d’ago ta tsare shi da su tana nazarinsa tana kuma nazarin amsar daya kamata ta bashi,jin yadda tayi shiru bata ce komai ba gashi ta kafe shi da ido kamar mai neman amsar a kan fuskarsa sai ya mata waving had’e da fad’in
“Hello..!!”
D’an firgita tayi kafin ta saita nutsuwarta tana jan dogon ajiyar zuciya,kana ta girgiza kai da cewa
“A’a..! Kawai dai shi ne ya samu Babanah da maganar,buh shi kuma baba sai yak’i amincewa shi ne dai ina jin sai abun bai musu dad’i ba,acewarsu wai me yasa Babanah ba zai aura masa niba tunda dama haka ake yi a gidan,shi ne sai shida Innarsa suke ta fad’an maganganu tun daga lokacin,kuma kullum cikin neman fad’a suke da Innata,amma ita bata kula su,Babanah ma da baffa sai suka ce mata duk abunda za suyi kada ta kula,shi yasa ko suna maganarma bata tsayawa a gurinsu..!”
Tun data fara maganarbyake kallonta yadda take yi tana gesturing face sai ya tsinci kansa da yin murmushi a b’oye ba tare daya bari taga hakan ba
“Ehmm! Amma me yasa d’azun dana tambayeki baki bani amsa ba..?”
Jim ta d’anyi tana son tuna mema ya tambaya,sai aka yi sa’a a lokacin yace
“Akan dalilin da yasa ki fita da safe nake nufi..!”
“Ohh!”
Ta fad’a kafin ta tab’e baki tana cewa
“Uhmmm! Goggo Tani ce ta aike ni na samo mata ruwa wai zata yi girkin safe bata da ruwa..!”
“Dama ba Inna ta aikeki ba..??”
“A’a ba ita bace..!”
“To ita d’in wace ce d’inki a gidan nan..??”
Sake kallonsa tayi sannan tace
“Itace Innar LADO..”
Shiru yayi yana nazarin sunan a ransa a fili kuma sai cewa yayi
“Babar wanda kika cemin d’an uwanki ne shi..??”
“Ehh! Shi..”
Ta fad’a tana sake gimtse bakinta daga haka ba tare data sake cewa komai ba
“Ok..na fahimta..!”
Abunda kawai shima yace kenan sai shima d’in yayi shiru yana nazarin abun a ransa da dalilin da yasa Gwaggon nata zata aiketa a safiyar nan al’halin tana da d’a namiji
“Shin me yasa bata aike shi ba shi daya kasance namiji kuma wanda take da ikon aikashi ko ina nema ta so,sai y’a mace kuma ma yarinya kamar Sabina..??”
Zuciyarsa ta watso masa tambayar
“Dole ne tana da wani dalilin da yasa ta aike ta..!”
Wani sashi na zuciyarsa ya bashi amsa a take,buh duk da haka tunanin sa har yanzun ya kasa kaiwa inda yake da buk’ata duk da yadda yake son sake takura kansa da son lallai shifa sai ya gano dalilin Gwaggon nata na aikenta a irin wannan lokacin,,dai² lokacin baffa yayi sallama wacce itace ta taimaka wajen dawo da shi daga duniyar tunanin daya nausa,,dukansu suka amsa masa,nan baffan ya shigo yana murmushi had’e da fad’in
“Kuyi hak’uri ko,na tafi na barku kuna jira na..!”
Shi kansa duk da ya gaji da zaman da fari kasancewar zaman shirun da suka yi a bayan fitar baffan,sai kuma daga baya daya dunga tambayarta tana bashi amsa sai zaman duk da yayi kuma bai wani sake damun shi ba sosai kamar da farkon,,haka nan itama gare ta,,,duka suka had’a baki a tare shi yana cewa baffan “babu komai” while ita kuma Sabina tana yi masa barka da dawowa,,one after d other duka ya amsa musu sannan ya nemi gurin zama yana kuma yi musu sannu dan yasan ya barsu sun jira shi sosai,,koda taga baffan ya dawo sai ta fara tashi,a hankali ta mik’e ta shiga tattara kwanukanta duk da dai bai tab’a abincin ba iya furar kad’ai yasha,sannan tayi hanyar k’ofa zata fita ba tare data ce komai ba,da idanu ya bita har ta fice,,yana ganin fitar ta nan sai yayi saurin kallon baffa yana cewa
“Baffa ni zan tafi..naga lokaci har ya tafi sosai..!”
“Toh..! Zaka tafin..??”
“Ehh! baffa zan koma makaranta saboda akwai wasu ayyukan a gabana,duk da dai yau nayi latti bazan samu shiga aji ba..!!”
“Toh to..! Allah sarki Ubangiji ya tsare ya kuma maida kai lafiya,,mun gode sosai da alkhairin ka gare mu,Allah kaima ya dubi lamuranka..”
“Ameen baffa..nima na gode sosai,,Allah ya k’ara girma..”
Baffa yana murmushi ya amsa masa da “ameen”,sannan suka mik’e tare baffan yana cewa
“Ince dai ko zaka dunga kawo mana ziyara idan ka samu sarari..?? Tunda Allah har ya had’a mu ko..Ba wai ace shi kenan mun rabu ba..??”
“In sha Allah baffa zan dunga lek’owa idan al’amura sunyi min sauk’i a makaranta..!”
“Toh..! Masha Allah,, Allah ya bada iko..”
“Ameen” ya fad’a yana juyawa da niyyan fita while baffa na biye da shi a baya suka fito daga cikin d’akin,fitowarsu tayi dai² da lokacin data matsa a bakin k’ofar d’akin tana tafiya cikin sanyi kamar kazar da k’wai ya fashewa a ciki,,sunkuyawa yayi ya fara k’ok’arin saka takalmansa while yana bin bayanta da kallo had’e da mamakinta,,har tayi nisa da su sai ta jiyo muryar baffa yana cewa
“Uwata yi maza ki ajiye kwanukan mana kizo kuyi sallama ko..?”
Da sauri ta waiwayo ta kallo bayanta inda suke tsaye da niyyar amsawa baffa,karaf sai ta tsinci idanunsa akanta yana kallonta,,yadda ya zuba mata idanunsa duk sai taji jijiyon jikinta sun saki hakama harshenta yayi mata wani irin nauyi,,bata iya amsawa ba sai kai data kad’a sannan ta juya taci gaba da tafiya buh wannan lokacin cikin d’an sauri² take yinta har ta isa d’akin su,,a tsakar d’akin ta dire tray d’in,sai dai ko data duba bata ga Inna ba nd tana son shaida mata zata je suyi sallama,dan haka ko data ajiye d’in sai kawai ta juya cike da niyyar komawa kamar yadda baffan ya bata izini….. Cikin nutsuwarta take takowa kamar ko wane lokaci idan tana tafiya,,tun daga nesa daya hango tahowarta yake kallonta buh idan ba nutsuwa mutum yayi ba babu ta yadda za’ayi ya fahimci hakan dan yadda yayi kamar ba itan yake kallo ba,nd yana ci gaba da saka takalmamsa,deeply kuma yana mamakin yadda halayenta suke,gata dai karamar yarinya amma sosai Allah yayi mata baiwar nutsuwa da hankali,,iya yau kad’ai daya fara ganinta,amma har ya gama fahimtar halayenta,iya zuwa yanzun gaba d’aya a cikin d’abi’unta babu wanda bai fahimta ba cikin d’an k’ank’anin lokaci da suka zauna tare,,,har ta k’araso inda ta barsun,a lokacin tuni har ya gama abunda yake yana tsaye kusa da baffa suna ta hira kamar dama can sun jima da sanin juna,ko data k’araso inda suke da niyyan suyi sallama da shi nan baffan ya kallesu duka yana fad’in
“Muje ko uwata mu masa rakiya..!?”
Murmushi tayi sannan tace
“Toh baffa..!”
Daga haka bata sake cewa wani abuba suka kama hanyar fita daga gidan tare su ukun,,a bakin k’ofar gida suka iske baban Sabina yana k’ok’arin shigowa gidan,ko daya gansu fuskarsa d’auke da fara’a ya tare su yana fad’in
“Takwara tafiyar ce ta taso..??”
Fuska a sake Muhammad ya amsa masa da
“Ehh! Baba zan koma makaranta ne nasan anata nema na yanzun..!”
“To Allah ya tsare hanya,,mun gode sosai² ubangiji ya mai da kai lafiya..”
“Ameen ya Allah,, na gode sosai nima..”
“Yawwa to a sauka lafiya,,sai gani na gaba ko..??”
Murmushi yayi a zuciyarsa yana fad’in
“Allah kenan mai had’a zumunci a tsakanin bayinsa..”
Amma a zahiri sai ya amsa masa da cewa
“In sha Allah baba idan har na samu sarari zan dunga lek’owa mu gaisawa..!”
“Toh to..! Allah ya nufa..Allah kuma ya kaika lafiya..Mun gode k’warai ubangiji ya dafa maka..Amma dai ka k’ara hak’uri da abunda ya faru d’innan..”
Sai daya kalli dattijon yayi murmushi zuciyarsa cike da mamakin wannan ban hak’uri haka da yake ta maimaitawa,sannan ya ce
“Babu komai baba in sha Allah,,komai ya riga ya wuce..”
Da kyar suka bar wajen baban Sabina dan yadda yake ci gaba da bashi hak’uri abun sai ya koma bashi kunya,daga nan kuma kai tsaye hanyar da zai fitar dasu zuwa ainihin babban titi suka nufa a sauk’ak’e,suna tafe baffa da Muhammad suna d’an tab’a hira musamman akan yadda harkar noma da kiwo yake a yanzun,,a cikin hiran ne baffa yake tsokanarsa yana cewa bazai iya noma ba,while shi kuma yana fad’awa baffa ai babu abunda zai gagare shi in dai a harkar noma ne,dariya baffa yayi kana yace
“Haba..! Mai babban suna,,kana kalloka nan ko fartanya ina jin baka tab’a rik’ewa ba bare ka gwada noma kunya guda,bare akai ga gona guda..Ai kai d’in bakayi kama da wanda suka san wahala ba..”
Murmushi yayi sannan ya ce
“Baffa ai duk abunda ake buk’ata ga cikakken namiji shi ne juriya da jajircewa akan duk abunda yasa a gabansa,haka nan duk wani abu sawa ne a rai,idan mutum dama ya riga yasa a ransa bazai iya ba,tofa babu yadda za’ayi ya iya,,amma ni kam baffa ina ganin babu abunda zai gagare ni matsawar nasa shi a raina kuma naji ina so..”
“Aaa! Da kyau sosai..! Haka ya kamata ace mu maza dama mun gina zuk’atanmu,a koda yaushe muji cewa duk abunda yazo mana zamu iya yinsa ba tare da fargaba ba,,amma abun haushin shi ne a wasu lokutan wai sai kaga namiji ya kwanta a gida yana jiran a dafa a bashi,,musamman ku can a maraya an fi samun irin wannan,,amma mu nan kam babu yadda za’ayi kaga namiji bai fita gona ba tunda mu har matan muma sukan fita zuwa gon.!”
“Haka ne dama baffa,,rayuwarce ta yanzun sai addu’ah kawai da fatan Ubangiji yasa mu cika da imani..”
“Ameen..! Wannan kam shi ne babban fatan da muke har kullum..”
Dai² nan suka iso bakin titin,,wanda ga Muhammad sai a lokacin ne ya tuna da bike d’insa daya bari a can gurin daya ga Sabina buh yasani kam zuwa yanzun babu tabbacin ace zai ganshi shi yasama bai ko yi nufin dubawa ba,,haka nan sai a lokacin daya sake laluba jikinsa ya tuna da cewar bai fito da ko anini ba,jim ya d’anyi yana tunanin yadda za’ayi ya koma skul,nd ga shi ko phone babu a jikinsa bare yayi kira a zo a d’auke shi,,,gefe ya juya can daga d’ayan gefen na bridge d’in,yana y’an tunanuka na neman hanyan da zai bi ya tafin,can daga tsallake ya hango wani d’an k’aramin shop dake da alamun daban² irin na masu sai da recharge card,ko daya hango gurin a bud’e sai yayiwa Allah godiya sannan ya kalli baffa yana fad’in
“Baffa da kun koma haka kada nayi ta janku da nisa,tunda mun fito hanya nima yanzun zan samu abun hawa ya maidani buh zan tsallaka can na kira waya kafin na wuce…”
“Toh mai babban suna,mun gode sosai ubangiji ya saukeka lafiya..”
“Ameen baffa sai kun sake gani na..”
“Toh Allahu ya kawo ka da alkhairi..”
Da “ameen” ya amsa masa sannan ya d’an kalle gefen ta yana cewa
“To *K’ANWATA* ni zan tafi ko,,amma ki dunga kula da lokacin daya dace ace kina fita,,ba kowane lokaci ake so y’ay’a mata su dunga fita ba,saboda hatsarin da zai iya samun su.. kinji ko..??”
Sai data d’ago ta kalleshi idanunta suna fidda k’yallin hawaye sannan ta girgiza masa kai tana cewa
“In sha Allah zan kiyaye..!”
“Yawwa to ni zan tafi,,sai na sake dawowa..”
Cike da rashin kuzari sai ta amsa masa da “toh” sannan ta bishi da fatan kiyayewar Ubangiji,,suna nan tsaye ita da baffa a gurin har ya tsallaka zuwa d’ayan side d’in ya nufi gurin shop d’in,,bayan da suka ga ya wuce d’in sannan baffa yace mata su koma haka nan,a lokacin rana har ta fara d’agawa,nan suka kama hanyar su ta komawa gida.
Kai tsaye bakin d’an k’aramin shop d’in ya nufa,yana yiwa mutanen daya iske a gurin sallama had’e da mik’a musu hannu suka yi musabaha,,a hankali ya juya ya kallo cikin shop d’in dan a zatonsa zai iske mai gurin a ciki,sai dai yaga babu kowa,ko da yaga babu mutum a ciki,da fari sai yayi kamar bazai magana ba,can kuma dai da yaga shirun bazai amfana masa da komai ba,nd zai sake b’atawa kansa lokaci,sai ya kalli na farkon dake zaune a saman bench d’in da fad’in
“D’an uwa dan Allah ina tambaya ne..??”
Da mamaki suka kalle shi kafin ya amsa masa
“To Allah yasa na san abunda zaka tambaya..!”
Jim ya d’an sake yi kafin yace
“Dan Allah ina mai wannan shop d’in..!?”
Sai da suka kalle shi duka,after sun tabbatar ba wani abu ne yasa shi neman mai shop d’in ba sai ya amsa masa da cewa
“Gani..! Amma lafiya MALAM kake tambaya.??”
“Ehh! To lafiya k’alau zance maka,,buh ina neman waya ne zanyi kira idan kuna bada rent..”
“Okay..! Babu matsala akwai,ammafa duk minti d’aya zaka bada naira #100..”
Sai da yayi murmushi nd yana fad’in
“Babu matsala,,damuwata dama nayi kiran..”
Sannan ya karb’i wayan da ake mik’o masa,a hankali ya d’an matsa gefe kad’an da su yana clicking phone d’in,bayan ya loda number ya danna kira had’e da k’urawa screen d’in idanu yana nazarin tafiyar kiran,,sai da wayan ya kusa katsewa sannan aka d’auki kiran,da sauri yasa wayan a kunnensa dai² lokacin da ya furta
“Hello.. Man..!”
Can daga d’ayan side d’in wanda aka kira d’in ya furta
“Man..! What’s up..?? Kafa tada mana da hankali da yawa,tun safe sai nemanka muke a cikin skul amma bamu ganka ba..Where have u been ne..?? Gashi har prof ya shigo ya fita baka nan..Ina ka shiga ne..??”
Sanyayyar ajiyar zuciya ya sauke sannan ya furta
“Yeah! Ina nan wajen bridge kazo ka d’auke ni yanzun..Ban fito da phone ba..”
“Ok.. Gani nan a hanya..”
Yana fad’in haka ya katse wayan sannan ya koma kusa da masu shop d’in ya mik’a musu wayan kana yace ma mai shop d’in yayi masa hak’uri babu kud’i ne a jikinsa idan anzo d’aukansa sai ya sallame shi,amsawa yayi da babu komai sannan yace
“Amma fa Yallab’ai zaka yi mana k’arin kan abunda muka yi da kai,,tunda sai mun jira,sannan lokacin daka ci minti d’aya ne da sakan ashirin da uku (1m 23secs)..”
Murmushi yayi masa kana ya amsa masa da
“Babu damuwa,,bari wanda nake jira ya k’araso..”
Daga haka sai basu sake yin magana ba suka bashi guri ya zauna,,almost 10 minutes ya kwashe yana zaman jira,time to time kuma yana kallon hanya,buh still shiru bai ga zuwansa ba,haka nan idan yaga babu alamun zuwansa sai ya d’anyi tsaki,still wasu mintuna biyu suka sake shud’ewa,,har ya mik’e tsaye cikin yanayi na fara hasala kuma ya hango tahowar motan.
Da mugun gudu motan k’irar toyota tundra fara sol mai duhun glasses ta zo ta gifta su,,har motan ya wuce shi,a hankali kuma matuk’in yayi slow sannan ya fara k’ok’arin yin reverse zuwa hannun da Muhammad d’in yake,komawa yayi ya zauna yana jiran ya k’araso fuskar nan a had’e irin na mai jiran k’iris,lokacin daya iso inda suke zaune bayan ya gyara parking sai ya sauke glasses d’in side na mai zaman banza ya d’an sunkuyo da niyyan yin magana,,kyakyatawan matashi ne wanda duka bazai haura tsaran Muhammad a shekaru ba da komansa,,a hankali ya kallo inda yake ganin bai motsa ba yana fad’in
“Am sorry friend,,na d’an samu matsala ne wajen fitowa daga skul..”
D’agowa yayi ya zabga masa wani mugun kallo kafin ya mik’e yana tura hannayensa a cikin aljihun jacket d’insa,sannan ya nufi inda motan yake,bai bud’e ba ya d’an sunkuya ta window d’in yana fad’in
“Bani ni na sallame su..!”
Sai daya kalleshi yayi murmushi sannan ya furta
“Me kuma..!?”
Wani malalacin kallo ya watsa masa sannan yace
“MALAM idan zaka bani ka bani..I think na fad’a maka ban fito da kud’i ba..”
“Ehh! Ka fad’a min..Sai akayi yaya to..??”
Shahararren tsaki yaja cikin jin haushi yana fad’in
“Dan Allah malam bana son rainin hankali,,ai ka san bada wayana na kira kaba,,shi ne ina tambayan ka kana rainamin hankali,idan ka zone dan ka b’ata min lokaci kaja motan ka wuce..zan dawo da kaina ko baka zo ba..!”
Y’ar dariya matuk’in motan yayi sannan ya d’auko wallet d’insa yana dubawa da niyyan d’auko masa kud’in,fizgewa Muhammad yayi yana harararsa sannan ya matsa inda yabar su zaune,bai wani tsaya duba meye a ciki ba ya zare 5k ya mik’a musu after ya musu godiya ya juya ya barsu sai godiya suke masa shima,,bai tsaya kulawa ba kawai ya bud’e motan ya shige,sannan suka d’auki hanyan campus..
A b’angaren Sabina kuwa da baffa tunda suka kama hanyar komawa basu wani tsaya ba,abunka da mutumin daya saba da zuwa gona,haka nan tafiyar k’afa duk nisanta da yake ba jinta suke yi ba,nan da nan sai gasu har sun dawo gida,,a k’ofar gida baffa ya tsaya gurin abokansa dake zaune k’asan awning dake k’ofar gidan,Sabina kuwa suna zuwa bayan ta gaishe su sai ta wuce abunta zuwa cikin gida kamar yadda baffan ya bata umarni,,shigowarta a lokacin yayi dai² da lokacin da LADO yake k’ok’arin fitowa,nan a bakin k’ofa sai suka kusa yin karo da juna,,yadda ya taho kamar zai fad’o kanta sai yasa tayi baya da sauri tana fad’in
“A’uzhubillahi minashshaid’anir rajiim.!”
Wani wulak’antaccen kallo ya sauke mata cikin fusata yana fad’in
“Ke dan uwarki waye kike cewa shaid’anin.!?”
Bata tanka masa ba sai dai ta tab’e baki gami da juya idanunta,abunda Sabina bata sani ba shi ne a wannan lokacin wannan abu biyun da tayi ba k’aramin k’onawa LADO rai yayi ba,nan take ya taso kanta kamar zai dake ta,da sauri ta sake ja da baya har tana yi kamar zata fad’i,,shi kuma yaci gaba da binta har ta kai jikin bango,ganin yadda yake ci gaba da nufo ta duk da hakan sai yasa itama ta fara hasala duk da a tsorace take da lamuransa,amma sai tayi jarumta cikin d’aga murya ta yadda tasan za’a iya jiyota ko da a cikin gidane a kawo mata agaji,bayan ta watsa masa mugun kallo sannan ta ce
“Wai kai LADO dan Allah ni me nayi maka ne da kake son takuramin..?? Naga dai ni wani abu bai tab’a had’a ni da kai ba bare kace ko na ci maka bashi,,,so let me be..! Ka fita a hanyata,,idan ba haka ba kuma Allah zan maka rashin mutunci ai ba tsoranka ake jiba..”
Jinjina kai yayi cikin k’asa da murya hakama fuskarsa a daf da nata yake fad’in
“Ai wollahi yarinya kinyi kad’an na kyaleki,,dan kin ga yau kin tsallake wannan tarkon,aka ce miki zaki iya tsallake na gaba ne..? Wollahi tunda nayi niyya,,na lashi takobin had’e da yin *ALK’AWARIN* sai na d’and’anaki matuk’ar muuna raye nine zan fara d’and’anar zumanki,,idanma old man d’inki yana ganin yafi k’arfina ta wani hanyar to ni nan gagara badau nake…Allah wollah…!”
Bai kai ga k’arasowa ba yaji saukar lafiyayyen mari a both chicks d’insa,,cikin wani irin mugun mamaki ya d’ago had’e da fad’in
“Kan uban can..!? Ke har ni zaki mara..!? Kamar ni LADO..!? Kina mace kisa hannu ki mare ni..!?”
Cikin hucin masifa kamar wacce take filin yak’i itama cikin k’arajin masifa ta furta
“Na mare ka d’in.. Idan kuma kana ganin zaka iya ramawa bismillah,,shege ka fasa a tsakaninmu..!”
Hannu LADO ya ware zai tafka mata a fuska muryar baffa daya jiyo kamar ana haniya a zauren gidan ya lek’o ya furta
“Kada ka kuskura ka tab’a ta..Idan kuwa ka sake ko da gefen hijabinta ka tab’a yau zaka ga yadda zanyi da kai a gidan nan..”
Da sauri ya juya yana kallon inda ya jiyo muryan baffan,nan take kuwa suka yi ido hud’u da shi,k’wafa LADO yayi cikin gunagunin b’acin rai ya furta
“Ai dama duk kuke d’aure mata gindin ta dunga raina mutane..Amma wollahi bazan bazan fasa ba tunda na lashi takobin yi sai nayi..”
Sai dai fa bawai yayi ne ta yadda baffan zai jiyo shiba coz yasan gamuwarsu da juna ba zata tab’a masa kyau ba matuk’ar ya jishi
“Sha³n banza..zo ka wuce daga nan kafin na shigo na riske ka..!”
Sum² LADO ya bar kusa da ita bayan ya watsa mata kallon zamu had’u next time,sai kin raina kanki,,,itama gareta mugun kallon ta watsa masa had’e da yin tsaki sannan ta bar wajen zuciyarta k’al dan murnan yadda tayi jarumta wajen marin LADON,,wanda dama muryan su baffa da take ji ne a kusa da k’ofar shigowa shi ne dalilin daya bata k’warin guiwan d’aga muryan a sonta ko babu komai idan baffa ya jiyo zai masa fad’a,sai ga shi a b’agas ta samu damar marinsa,yadda take cike da jin haushinsa a yau d’in take sai taji wani gefe na zuciyarta ya cika da tsantsar farin ciki,,baffa da har lokacin yana tsaye ya juya kanta lokacin tana niyyar shigewa yana fad’in
“Uwata abunda zan fad’a miki shi ne daga yau kada ki sake wani abu ya kuma had’a ki da shi,,kin jini ko..?? Kinga dai abunda suka kusa yi miki d’azun shi da wannan kangararrun abokan nasa,saboda haka sai kin kiyaye kanki daga shiga duk wani abu da zai had’a ku..kin ji ko..??”
“To baffa..In sha Allah zan kiyaye..”
“Yawwa to..Maza jeki gida..Allah yayi miki albarka..”
Da “ameen ta amsa masa kana ta wuce cikin gida abunta..
A b’angaren Muhammad kuwa tun da suka d’auki hanyan komawa skul bayan ya mik’awa friend d’in nasa wallet d’insa bai ko sake kallonsa ba,yayi shiru yana kwantar da kansa a jikin seat,duk da yadda yake ta masa magana da tambayarsa inda yaje da safen amma ko kallo bai is he shi yi ba,,hasalima shi haushi ne ya kama shi jin yadda duk ya dame shi da surutu nd a time d’in duka ba abunda ya dame shi kenan ba,cikin alamun nuna gajiya da surutun da yake masa ya d’ago kai yana sauke masa wasu awful looks kafin ya furta
“Sultan..! Please dan Allah kaja bakinka ka rufe haka nan,kai wai baka gane lokacin da mutum yake cikin yanayin da zai saurari wannan zantukan naka..?? Ka kyale ni naji da damuwata mana,,amma kazo sai k’ok’arin k’ara min wani kake..!”
Murmushi sultan ya saki mai sauti,cikin alamun zolaya kuma ya ce
“Ohh! Friend kaifa matsalar ka kenan,,baka rabuwa da damuwa,nd idan za’a tambayeka kuma a banza,ba fad’a za kayi ba,,,ai sai kaje kayi ta fama da kayan damuwarka..”
Sake kallonsa Muhammad yayi sai dai bai ce masa komai ba ya juyar da kansa zuwa side yana kallon hanya had’e da sakin long crack,wanda yasa sultan yin murmushi sai dai bai sake ce masa komai ba a haka har suka shiga cikin campus.
*2 days leave…*
A gefen Sabina kam zuwa yanzun tun bayan tafiyarsa hankalinta a kwance yake,dan tun daga ranar da AL’AMARIN ya faru,bata sake barin wani abu ya shiga tsakaninta da LADO ba haka ma Innarsa wato Tani,,a yanzun kullum cikin taka tsantsan take dasu,hakama duk wani abu da tasan zai had’a su ko ya janyo a samu sab’ani,sosai sai ta shiga k’ok’arin guje masa,ga Innarta ma itama ta fita a lamuransu Tani d’in,sai dai wani abun mamaki kuma da yakr faruwa shi ne tun da baffa yace zasu had’u da LADO,gaba d’aya sai aka nemi LADON a gidan aka rasa ya gudu daga gidan,hakan sai yayiwa jama’ar gidan dad’i dan dama kullum cikin neman magana yake a garin.
Ga baffa da baban Sabina kuwa tun suna neman LADO dan yi masa hukunci akan abunda ya aikata har suka gaji suka watsar,dan kuwa sun san duk daren dad’ewa wata rana dole ne zai kawo kansa gare su idan ya gama guje²n,nd dama kuma baffa yasan za’a rina shi yasa ma a ranar da AL’AMARIN ya faru yace masa saura su nemeshi su rasa d’in.
Shigowarsa kenan cikin gidan da yammacin ranar yana tafe yana fito kamar wani d’an farauta,,ko da yake ina maraba tsakanin d’an shaye² da mafarauci..?? A wasu lokutan ai halayensu suna d’an kama da juna,,da baffa ya fara katari a hanyarsa ta shigowa gidan,,sai ya d’auke kai yayi kamar bai ganshi ba zai wuce,baffa da mamaki a fuskarsa ya bishi da kallo kafin ya ce
“Kai LADO kai..!? Zo nan dan uwaka..Ja’iri mai siffar jinnu..!”
K’eyarsa ya shafa yana sunkuyar da kai k’asa had’e da gunguni k’asa² ya d’an rage tsayin sa kad’an,wanda da kad’an yafi ace mutum yana tsaye da fad’in
“Aaa! Baffa barka da yamma..!”
Malalacin kallo baffa ya bishi da shi kafin ya girgiza kai cikin jimami da cewa
“Ka gama guje²n naka..??”
“Aaa! Baffa nifa babu inda naje,,kawai dai..”
“Kawai dai me..!? Ai tambayarka nayi ka gama guje²n yau ka dawo gida..??”
Bai iya bashi amsa ba,nan kuwa baffa ya juya yana fad’in
“Biyo ni to muje ciki,,,yau zaka ci uwaka wannan mai fuskar kamar faifai…”
Ba don LADO ya so ba sai don babu yadda za’ayi ace ya sake guduwa nd kuma sun riga sun had’u da baffan shi yasa kawai ya shiga binsa a baya,,a tsakar gida baffa yaja tunga ya tsaya,cikin d’aga murya yana kallon mutanen gidan da cewa
“Kuna ina ne kai..! Duk ku fito ina son ganin ku..!”
D’aya bayan d’aya suka fara fitowa daga d’akunansu wad’anda kuma suke tsakar gidan nan suka shiga matsowa gaba dan jin dalilin baffa na son tara su dukan…..Saman traditional chair dake ajiye a gefen rumfar baffa ya zauna,yayin da su kuma gaba d’aya ahalin kowannensu ya nemi guri ya zauna duka suna zagaye da shi had’e da kasa kunnuwansu ga abunda zai fad’a,,kaf gurin sai da baffa ya kallesu bayan ya tabbatar da su wane ne a gurin da kuma su waye basa nan sannan ya juya ga y’an yara² dake wasa a gurin yana fad’in
“Kai Sule kai,,,zo nan maza kaje ka kiramin babanku Aminu a k’ofar gida..Kai kuma Hamudan je ciki kacewa Tani tunda ban isa na ce tazo ta amsa akan lokaci ba,,to taci gaba da zama,,amma ta kiyayi gamonmu da ita..!”
Da gudu yaran biyu kowannensu ya bar gurin cikin sauri duka suka nufi inda aka aike sun cike da son isar da sak’on baffa akan lokaci,mintuna biyu da aiken baban Sabina ya shigo gidan cikin sauri,yana zuwa bayan yabi ilahirinsu da kallo kuma sai ya nemi guri nan a kusa da baffa ya zauna saman d’aya kujeran da babu kowa akai,yana fad’in
“Yaya wannan taron fa..?? Ince dai ko lafiya aka taru duka gida a nan..!?”
“Lafiya k’alau..!”
Baffan ya fad’a yana mai kallon hanya da sauraren isowar Tani,,sai da d’an aiken baffa ya kwashe ak’alla mintuna biyar da dawowa,amma shiru babu ko alamunta,girgiza kai baffa yayi cikin takaici kana ya kalli inda LADO yake yana fad’in
“Kai LADO..! Ina son yanzun nan maza ka sanar damu gaskiyar abunda ya faru a shekaran jiya..!”
Ba tare da LADO ya d’ago ba haka nan k’asa² ya furta
“Toh..Baffa ai naga kun riga kun san komai,,mene ne amfanin na maimaita kuma..”
Da mamaki duka mutanen gurin suke kallonsa,dan a iya tsayin wad’annan shekarun da aka kwashe tun bayan mutuwar MALAM,kaf a gidan baffa shi ne ya koma lamba d’aya,duk wani hukunci ko al’amuran da suka shafi gidan gaba d’aya da hukuncinsa ake aiki,hakama duk lokacin daya zartar da magana tofa ba’a tab’a samun wani ya musawa maganar tasa,ko kuma a mayar masa da magana kai tsaye,, buh yau karon farko lado ya fad’i irin wannan maganar mai tattare da rashin d’a’a ga baffan,ba ga mutanen gurin kad’ai ba hatta da shi kansa baffa sai da maganar LADO ta bashi matuk’ar mamaki,sai dai sanin halin LADON a yanzun na rashin mutunci wanda kowa ma bai kyale ba sai yasa baffa jinjina kai kawai,ba tare daya sake bi takansa ba ya kalli jama’ar gidan duka yana cewa
“Alal hak’ik’a na san da yawan ku a shekaran jiya lokacin da LADO yazo da wannan magana game da Sabina,kun yarda da shi,sai dai wani abun ban haushi,takaici da kuma Allah wadai shi me,ko da yazo yace wani ya kamata yana k’ok’arin haike mata,,a gaba d’ayan wannan magana babu gaskiya a ciki,dan kuwa ba haka take ba..”
Nan take baffa ya shiha warware musu duka abunda ya farun,after kuma ya umarci SABINA data sake maimaita musu abunda ya had’ata da su LADON,,nan itama ta shiga zayyana musu komai kamar yadda ya faru,,ko data gama basu labarin take gurin duka suka d’auki salati,,yayin da wasu a ciki suka hau fad’in
“Ya kamata a hunkuta shi kada gaba ya sake maimaitawa..”+
Dai² lokacin anata hayaniya Tani ta k’araso gurin tana yatsina fuska da kallon mutane d’aya da d’aya,,babu wanda ya kalli inda take bare ya kula da abunda take tambaya game da hayaniyar da ake,dan haka ko da taga babu mai tanka matan sai ta nemi guri ta zauna kamar sauran tana maida kunnuwanta ga abunda ake tattaunawa akai,,Baban Sabina ne ya kalli inda LADO yake cikin jin zafinsa kamar zai yi magana,ko me ya tuna kuma sai ya fasa ya rabu da shi,musamman ma dan gudun kada ace dan akan y’arsa ne abun ya faru shi yasa yake hakan,,baffa ne ya kalli LADO yana cewa
“Kai LADO shin yanzun zaka sanar damu dalilinka na gayyato abokanka ku tare ta a hanya ko kuwa..??”
Tsam Tani tayi wacce duka zuwanta gurinkenan bata wani jima ba,cikin hargowa ta fara fad’in duk abunda yazo bakinta
“MALAM wannan wane irin magana ce kuma haka kake yi..!? In ce wannan maganar ya riga da ya wuce tun a shekaran jiya..amma kuma shi ne har yau abu yak’i ci yak’i cinyewa sai kwan gaba kwan baya ake akan wannan y’ar maganar..!”
Zuba mata idanu duka suka yi har ta dasa aya kafin baffan cikin takaici ya ce
“Tani..! Shin da kika zo nan na baki damar kiyi magana..!? Ko kuwa kinga na ware wani na tambayeshi..!?”
“A’aahh! Toh ai MALAM gani nayi yau kwana biyu amma har yanzun maganar tak’i wucewa a gurinku,, ko kuwa dan an tab’o y’ar lelenku ne,,shi yasa zancen ya gagara wucewa..!?”
Babu wanda baiyi mamakin kalamanta ba,buh da yake duk sun san hali kowa sai ya shiga tofa albarkacin bakinsa akan rashin dacewar abunda tayin
“Kin kyauta Tani.. Kuma wannan ya sake tabbatar mana cewa kece silar lalacewar rayuwar yaron nan,,wanda dalilin yasa sam baya ganin kowa da mutunci a cikin garin nan baki d’aya,,baga mutanen waje ba,hatta muma da muke gida d’aya duk ya raina mu,babu wanda ya isa yace masa yi wannan ko kuma bari wancan,duka babu wani babba a idanunsa,,to amma abunda nake so dake shi ne,tun da har kina ganin y’ar lelenmu kika ce an tab’a ko..? Tabbas baki yi k’arya ba,dan haka nake son ku kwana da shirin ku,daga rana mai kamar ta yau idan har ana son zaman lafiya damu a gidan nan,tunda gida dai namu ne ko..?? Kuma mune muke da iko da shi ko..?? Mutanen duk dake cikin gidan nan babba da yaro duka k’ark’ashin mu suke ba,,matsawar daga yau na sake ji an sake kawo mana k’arar d’anki,tofa ki kwana da sanin ni da kaina nayi alk’awarin zan d’auke shi na kaishi Maiduguri almajiranci..Idan yaso muma bakinmu ya huta da ban hak’uri,da kuma neman maganar da yake yi..”
Ba Tani ba hatta LADO ko da jin furucin baffa sai daya tsorota a dalilin yasan tunda baffan ya furta,tofa lallai ne yana iya aikatawa dan yadda yake kaifi d’aya,amma duk da haka saboda duniyanci irin na Tani bata fasa magana ba
“Ahayyeeh..! Cas..! Allah nawa! Yo Allah na tuba dan an fad’i haka shine me,,nifa wollahi na k’una bana tsoron k’auri,,zancen almajiranci kuma wollahi ba dai akan d’ana ba,,idan har za’a kai kowa a gidan nan wollahi banda nawa,,,haifarsa fa nayi bawai tsinto shi nayi a juji ba,dan haka sai dai asan wanda za’a kai amma ba LAD..!”
Marin da ya d’auke ta dashi ne ya datse k’arshen maganar tata,cikin tsananin mamaki mai had’e da takaicin tsinkata da akayi a gaban jama’ar gidan ta d’ago da niyyar ganin wane ne ya mareta haka,ido hud’u suka yi da Mijinta wato mahaifin LADO,ya sake d’aga hannu da niyyan sake wanketa da wani marin sai aka yi rashin sa’a baffa cikin hanzari yayi masa tsawa yana fad’in
“Ashsha..! Isiyaku bana sonka da saurin fushi,,me yasa zaka biye mata kaima ka aikata haka a gaban yara,,da ka bari anbi komai a sannu,saurin hannu bai kamaceka ba..”
Haushin Tani fal idanunsa ya sake watsa mata mugun kallo kana yana amsawa baffa
“Yaya ai daka kyaleni da ita,,wollahi wannan matar na rasa wace irin shaid’aniya ce ita,,duka gida tak’i zaman lafiya da kowa,sannan kai da muke kallo a matsayin babban wa kuma uba a gurinmu,ta tsaya a gabanmu tana fad’a maka magana son ranta,,wollahi Yaya dama tuni na gaji da zama da ita,hak’uri kawai nake yi tun tuni,bawai dan ina jin dad’in zama da ita ba,amma yau tunda ta fito da halinta kowa ya ganj shi kenan tayi kai,sai ta tafi gidansu dan ni dai banga dalilin da zaisa ni ci gaba da zama da matar da bata san darajarku ba..Yau d’innan aradun Allah zata tattara,sai ta barmin gida na..”
“A’a a’a..! Isiyaku baza ayi haka ba,,hakur’in dai shi za’a ci gaba da yi,,,nemi guri ka zauna tukuna muyi maganar a tsanake ko..!?”
Komawa yayi ya zauna yana zub’awa Tani mugayen kallo,ita kam har lokacin tana nan tsaye dafe kumatumta kamar mutum-mutumi,a lokacin ba komai yafi b’ata mata rai ba illa irin maganar sakin ta da yayi,wacce ko zafin marin da yayi mata a nata ganin bata ji shi ba,kamar yadda taji saukar kalamansa,a ranta tayi k’wafa mai ciwo kana ta nemi guri itama ta zauna sakamakon magana da baffa yayi mata akan idan bazata zauna ba tana iya barin gurin,,ci gaba aka yi da maganganu akan matsalar da aka samu d’in yayin da a b’angaren Tani tayi shiru tamkar bata gurin aketa maganar,a nan ne kuma baban LADO da baffa sai suka sake tsayar da magana akan duk abunda zai samu Sabina daga lokacin zuwa nan gaba dai² da k’wayar zarra aka ce musu yau ga wani abu ya sameta tofa kafin su tuhumi kowa zasu fara ne ta kan LADO tunda an faro da shi daga haka,gaba basu san me kuma zai sake yi mata ba,,after kuma aka musu tsakani,nd babansa yace ko kallon banza idan yayi KUSKUREN yi mata taji bata gamsu sa shi ba tazo ta sanar masa,shi da kansa zai d’auki matakin daya dace,,nd idan har ya sake ta kawo k’ara akan shi ko abokansa sunyi mata wani abu,tofa ya kuka da kansa,,,bayan duk an gama da waccan maganar sai baffa ya sake jaddada musu hukuncin sa na soke batun auren gida da yayi,inda yace daga yau kowannensu ya fita waje ya nemo matar da tayi dai² da ra’ayinsa,,ko da aka gama baban LADO sai hak’uri yake bawasu baffa dan shi kam ji yake duka ya muzanta a idanun y’an uwan nasa,sai da baban Sabina ya nuna masa jan ido sannan suka samu kansa yayi shiru amma kana kallonsa zaka tabbatar abun ya tab’a shi Sosai.Ko da baffa ya tabbatar babu wani mai k’orafi nan take duka ya sallame su ba tare daya nemi shawaran wani a cikin k’annen nasa ba,duk dama dai ya san halinsu akan duk hukuncinsa bazasu tab’a jaba sak dai suyi na’am,,a hankali duk yawan su suka shiga watsewa kowa ya nufi harkokin dake gabansa,kafin kace me tuni sai ga gurin ya dawo fayau babu kowa sai su baffan da suka yi saura su uku,suna sake tattaunawa akan matsalolin da suke fuskanta game da LADON..
A can campus kuwa tun bayan da Muhammad suka dawo hankalinsa kacokam sai ya maida shi kan karatunsa kasancewarsa mutum mai k’wazo,nd duk wasu al’amura da basu shafi harkar skul ba duka ya tattara su ya maida gefe,nd yaci gaba da tunkaran exam dake gabatowa kasancewar semester da suke tazo ending,,while a gefe guda kuma kullum zuciyarsa tana kan tunatar da shi *ALK’AWARIN* da yayi ma baffa na kai musu ziyara idan har ya samu sarari.
*Almost 2 weeks leave…*
A duk tsayin wad’annan kwanakin da suka gabata,kullum cikin sa rai yake akan zai samu chance na zuwa,buh maimakon ace lamura sunyi masa sauk’i sai ma sake cakud’e masa suke,,duk da kullum cikin son zuwan yake amma daya motsa can nan wani uzurin zai sake gifto masa da zai hana masa zuwan kamar yadda yayi niyya,deeply kuma a kullum da tunanin zuwan yake tashi yake kuma yini sai dai babu wani isashen lokaci a gare shi.
Yau ranar ya kasance Friday,,ganin ba wani jimawa za suyi a skul d’inba sosai sai yasa shi fitowa cikin shiri,a zuciyarsa yana saka ran zuwa ya gaida dattijan,,da misalin 10am suka fito a lectures wanda kuma daga shi d’in sai ya zama basu da wani sauran abu daya rage musu a skul d’in,banda su zauna tutorial (ma’ana su k’arawa juna sani akan abubuwan da suka shigewa wasu cikinsu duhu) lokacin kam ko da yaga prof ya tattara kayansa zai fice daga lecture hall d’in da sauri shima ya mik’e yabi bayansa kamar wanda yake shirin tambayarsa wani abu,buh suna fitowan sai kawai ya kama hanya abunsa ya bar gurin,kai tsaye motan da Sultan ya d’auko shi wancan ranar da suka fara had’uwa ya d’auka sannan ya fice a skul d’in,kasancewar shi kad’ai ne a cikin motar shi yasa sai ya shiga fella gudu abunsa a saman kwaltar ba tare da damuwar komai a ransa ba,,within 10 minutes ya iso dai² bakin hanyar da suka rako shi wancan had’uwar,can daga d’ayan side dai² inda ya tsaya ya kira sultan a waya yazo ya d’auke wancan ranar yayi parking kana yayi sallama wa mutumin daya gani zaune kana ya barma masa ajiyan motan a gurin mutumin,duk da ba wancan mutumin ya tatar ba,,sannan ya tsallaka titin yana nufar hanyan da zai shigar da shi cikin d’an k’auyen nasu Sabina,,yayi tafiya mai d’an tsayi kafin ya iso inda castle na rugar yake,kai tsaye k’ofar gidan ya yunk’ura kana ya samu guri ya tsaya yana tunanin yadda zaiyi ya samu wanda zai aika,ko da ya tsaya a k’ofar gidan kuwa bai yi mamakin yadda aka yi ya iya dawowa ba duk da uban jejin daya yake tsakaninsu da titi nd sai mutum ya wuce shi kafin ya riski inda gidajen nasu suke,ya kwashe ak’alla mintuna sama da biyar a tsaye a k’ofar gidan shi bai lek’a yayi sallama ba kuma shi bai tafi bazhaka nan ba tare daya samu d’an aike ba,,a haka mintuna biyu suka sake zuwa suka wuce kafin ya hango wasu yara can nesa da shi suna tahowa,sai daya jira har suka k’araso inda yake sannan ya musu magana akan suyi masa sallama da masu gidan…..Shigar yaron zuwa cikin gidan da fitowarsa duka ko minti uku ba’a d’auka ba,sai ga baffa ya fito da mamakin wanda yake sallama da shi,,a tsaye ya iske Muhammad ya jingina a jikin k’atuwar bishiyar maina dake k’ofar gidan,fuskarsa cike da fara’a ya k’araso inda yake yana fad’in
“Lale marhaban..!”
Shima murmushin yayi yana nufar baffa dake tahowa,nan suka had’u a tsakiyar awning na k’ofar gidan,durk’usawa yayi har k’asa da niyyar gaida baffan yayin da shi kuma baffa yake mik’a masa hannu alamun su gaisa yana kuma fad’in
“A’a! Mai babban suna ba haka addini ya nuna mana ba,,mik’e tsaye mu gaisa a haka..Wannan ai al’ada ne.”
Kunya ce ta kama shi dan shi a ganinsa idan har yace zai gaida baffan a tsaye ba k’aramar rashin kunya yayi ba,,amma kuma saboda baffan ne yace masa ya mik’e d’in,ganin babu yadda zaiyi sai ya mik’e tsayen yana mik’awa baffa hannu cike da matsananciyar kunyarsa,musabaha suka yi while still yana rage tsayinsa had’e da kallon k’asa,sun gaisa da baffa cikin mutunci da girmama juna kafin baffan ya sake kallonsa,kallo irin na tsanaki,duk da bawai baffa ya san tsadar kaya ba da sauran ababen more rayuwa ba,amma daga tsarin shigarsa zuwa yanayin fatar jikinsa kad’ai sun sake tabbatarwa da baffan cewa lallai ne daga gidan masu da shi ya fito,buh kasancewar ba abunda ke ran sa ba kenan sai ya ce
“Yanzu mai babban suna banda abunka ai kai ka zama d’an gida,mene ne abun tsayawa a waje ka nemi d’an aike..!?”
Murmushin dai still yake sake yi sannan ya amsawa maganar baffan
“Baffa gara dai nayi hakan,shiga gidan mutane kai tsaye ai ba addini bane,dole ne duk mutum mai hankali kuma wanda yasan ya kamata,sannan ya fahimci addini dole ne ya tsaya ya nemi izini gudun fad’awa halaka,kamar yadda Allah (S.W.T) ya bayyana mana a cikin littafinsa mai tsarki cikin suratun nur (verses 27-28) game da shiga gidan mutane
“Ya ku wad’anda suka yi imani.! Kada ku shiga gidaje wad’anda ba gidajen ku ba har sai kun sami izni,kuma kun yi sallama a kan ma’abotansu (ma’ana mammalaka daga gidan).Wannan ne mafi alkhairi gare ku,tsammaninku,za ku tuna.To,idan ba ku samu kowa a cikinsu ba,to kada ku shige su,har sai an yi muku izni.Kuma idan an ce muku,”Ku koma.” Sai ku koma,wannan shi ne mafi tsarkaka a gare ku.Kuma Allah game da abin da kuke aikatawa,Masani ne..”
To kaga kuwa baffa wannan hujjar itace tasa ni tsayawa a nan,saboda kada na sab’a dokar da mahaliccinmu ya shimfid’a a gare mu..”
Tun daya fara janyo masa ayoyin baffa yake bin tafsirinsu har ya dasa aya a bayanin nasa,kallon tsanaki baffa ya sake binsa da shi fuskarsa cike da tsantsar farin ciki,cikin gamsuwa da abunda Muhammad ya fad’a d’in ya sake rik’o hannunsa sosai yana fad’in
“Lallai kayi gaskiya,kuma hak’ik’a nayi matuk’ar farin cikin had’uwa da mutum kamar ka,,a iya tsayin shekaruna a wannan k’auyen tunda nake ban tab’a ganin matashi daya had’a nagarta kamar ka ba,kai abun alfahari ne a cikin duk wani ahalin da suka same ka,ta ko wane fanni halayenka abun ayi koyi da sune,,ka godewa Allah da irin baiwar da yayi maka,sannan kaci gaba da kiyaye abunda ka riga ka sani..Allah yayi maka baiwa mai girma,ka kuma godewa mahaifanka domin sunyi matuk’ar k’ok’ari wajen gina rayuwarka da ilimi,,fatan Allah yayi musu tukuici da gidan aljannah,dan nasan jajircewarsu ce ta kaika ga zama abunda ka zama a yau..”
Da “ameen” ya amsawa baffa yana mai jin dad’in irin yabawa iyayensa da baffan yayi bisa jajircewarsu akan tarbiyyarsa,,,nan baffa yaja shi suka shiga ciki,suna tafiya baffa yana sake jadadda masa kan cewa,nan gaba ko da yazo kada ya sake tsayawa a k’ofar gidan wannan umarnin sa ne gare shi,kuma shi ya bashi damar shigowa kai tsayen,,godiya yayiwa masa dai² lokacin da suka shiga d’akin da baffa ya saukar bak’inshi,sun sake gaisawa a mutunce da tambayarsa karatu zuwa sauran harkokinsa,kafin baffa yayi niyyar fita yana fad’in
“Bari na nemo Aminu yazo ku gaisa ko..!?”
Godiya ya sake yiwa baffan,after kuma ya fita ya barshi shi kad’ai,sai ya d’auko phones d’insa dake cikin aljihunsa ya zube su a gabansa,d’aya daga ciki wacce ta kasance k’irar samsung galaxy s10 plus ya d’auka ya fara clicking cikin kwanciyar hankali,kira ne ya shigo masa dai² lokacin yayin da sunan *SULTAN* ya shiga lilo akan screen d’in,tuna dalilin da zaisa ya kira shi sai yasa shi ajiye wani slender breathe,daf da kiran zai katse ya d’auka had’e da sa wayan a hands free,,muryan sultan kamar zai Faso wayan yake fad’in
“Hello..Man ina ka shige ne..!? Duka class sai neman ka ake,,ka sanfa kai ake jira,shi ne zaka shanya bayin Allah,me hakan yake nufi..!?”
Sai daya bari sultan ya dasa aya kafin ya bashi amsa
“Ka aike nine da kake tambayata inda na je..!?”
Da mamaki a cikin muryan sultan yake fad’in
“Bala’i..! Ba dai ace ka fice a skul ba..!?”
Siririn tsaki yaja kana yace
“Ehenn.! Dafa.?”+
“Tabbb’ amma dai mutumin nan ka cika d’an rainin sense wollahi,banda tsabar wulak’anci kasan bayin Allah nan sun saba jiranka,kawai sai ka fice ka barsu a nan,without taking excuses..??”
“Hey! Man..Mene ne abun wulak’ancin a nan..? Shi kenan sai aka ce ni ba zanyi nawa uzurin ba,sai dai kullum naita aiki bani da lokacin hutu..!? An fad’a maka agogo ne ni da bazan huta ba..!?”
“A’a..! Ni kam ban ceba,,amma dai da kasan zaka fita,sai ka sanar dasu kaga ba sai sunyita jiranka ba..!”
“Ok..good.! Buh why don’t u expiate me..kaga kenan zai zama basu yi jiran banza ko..!?”
Murmushi sultan yayi kafin ya ce
“No man..! Kafa san bana iya tsayawa gaban jama’a haka nayi magana kamar kai…Kawai dai ka san yadda za kayi da su,,suna nan suna jira..Nd zanma sanar dasu nan da 10 minutes zaka dawo..!”
Cikin sauri ya tari numfashin sultan d’in yana fad’in
“Tabbb’ wollahi kada ma ka soma,dan ni nan da ka ganni bana kusa,nd yanzun ma banga lokacin dawowa ba..Idan ka sasu jira kai ka sani,ni bance kowa ya jira ni ba..”
Murmushi sultan yayi cikin tsokana kafin ya sake cewa
“To wai kai ina kaje ne haka da wannan safiyar ma.!?”
“Ina ruwanka da inda naje..ko kuwa dai salon sa idonka ya motsa..!?”
“Aaa! To Allah ya bada hak’uri,,, amma dai da alamun ko..!”
“Ko me..!?”
Ya sake tarar numfashinsa,,dariya sultan yayi yana fad’in
“No..! Babu komai,kawai dai sai ka dawo d’in.. Buh when ma zaka dawo ne..!?”
“Wai kai ina ruwanka ne da inda naje,ko sanin lokacin da zan dawo,,ka aiki ni ne..!?”
“Allah baka hak’uri.. Sai na ganka.”
Daga haka sultan ya katse kiran yana murmusawa,while a fili kuma yana furta
“Idan tayi wari dai zamu ji..!”
A can gefen Muhammad kuwa koda yaji sultan ya katse kiran wayan,tab’e baki yayi kana yaci gaba da abunda yake yi a phone d’in nasa,yana kuma jiran ganin dawowarsu baffa.
Cikin nutsuwarta take takowa,sannu a hankali har ta zo bakin k’ofar d’akin,,dai² ta cire takalmanta tana niyyar yin magana his uniquely perfumes aroma suka kaiwa hancinta ziyara,a hankali ta maida kyawawan idanunta ta lumshe yayin da k’irjinta yake tsananta bugawa,while kyam ta mak’ale a gurin ta kasa koda motsa even bakinta bare ta iya yin sallama,,duk da bawai ta ganshi bane,ko kuma ace ta ga even a clue da zai bata tabbacin ya zo gidan,amma haka nan zuciyarta take shaida mata yana nan a kusa² da ita,,sai data shafe ak’alla mintuna uku cikin mugun yanayin zurfafa a tunani kafin taja dogon ajiyar zuciya,sai data gama saita nutsuwarta sannan ta motsa harshenta da kyar tana furta kalmar sallama,,yana zaune a cikin d’akin yayin da yayi flexing legs d’insa tamkar basarake muryanta ya doko shi,sai daya d’ago kansa daga kan wayan sannan ya amsa mata da wannan husky voice d’in nasa a lokacin Sabina tuni har ta shigo ciki hannunta d’auke da mug na robber mai kyau,,kallonta ya d’anyi a fakaice kafin ya janye idanunsa akanta yaci gaba da abunda yake yi akan wayansa,,itanma ko data shigo nd taji wani muryan daban ya amsa mata sab’anin na baffanta da take tsammanin yana cikin d’akin,duk da ta fahimci ko waye ya amsa d’in sai data waiwaya ta kalli inda yake,a nan tayi arba da shi a zaune kamar yadda baffa ya fita ya barshi,cikin shigar kayan mu na hausawa,shadda ne zubin feitex material getzner fara sol sanye a jikinsa wacce darajarta ya kai 58k+ ta sha d’inkin zamani,haka nan kansa sakaye cikin hular zanna wacce ta b’oye suman kansa,haka nan ta k’ara masa kwarjini da k’ima,banda haske da k’amshi babu abunda yake bazawa tamkar wanda ya juye tandun turare a jikinsa,,da kyar ta samu tajanye idanunta akansa kana ta matsa daf da shi ta ajiye mug d’in a gabansa,kallonta ya sake d’agowa yayi musamman ganin ta ajiye a kofin a gabansa,ba tare data sake kallonsa ba cikin zazzak’ar muryanta bayan ta nemi guri ta zauna ta furta
“Barka da safiya..!”
Kamar bazai amsa taba dan yadda yake sake binta da kallo,wanda itama kanta Sabina a lokacin tayi tsammanin ko bai jita bane,hakan sai yasa ta d’ago kad’an ta d’an kalle shi,nan take kuma sai taji ya amsa mata da
“Kin tashi lafiya..!?”
Kad’an ta sake sunkuyar da kanta k’asa zuciyarta na skipped buh cikin dakewa itama ta amsa masa
“Lafiya k’alau.. Ya ka koma gida..!?”
D’agowa ya sake yi ya kalleta,while yana d’age one eyebrow d’insa kamar mai son nemo amsa ya amsa mata a tak’aice
“Lafiya Alhamdullah..!”
Shiru tayi daga haka bata sake magana ba dan duka iya kalaman da taji zuciyarta zata iya furtawa kenan a lokacin,,shima gogan shiru yayi sannan ya d’auke kai,daga hakan still sai yayi kamar bai san tana gurin ba,yayin da zaman shiru ya ratsa tsakaninsu,sun shafe ak’alla mintuna goma a haka zuwa can ko daya gaji dan kansa sai ya ajiye wayan hannunsa,unexpectedly Sabina taji muryansa a cikin kunnuwanta yana fad’in
“Bakya zuwa skul ne..!?”
Kai ta d’am girgiza kad’an kafin tace
“A’a,, ai tun d’azun muka taso..”
“Ok..! Good..!”
Abunda kad’ai yace kenan daga haka kuma bai sake magana ba dan jin sallamar su baffa a k’ofar d’akin,saurin mik’ewa Sabina tayi zata fita nd tana amsa sallamar su baffan,shima d’in sallamar ya amsa kuma yana binta da ido ganin tana shirin fita,kamar zaiyi mata magana kuma sai ya fasa,a tare su baffa suka shigo da Babanta,bayan sun musu barka da dawowa Sabina ta fice ta nufi cikin gida,a lokacin baffa ya kalle shi yana murmusawa da cewa
“Mai babban suna ince dai baka gaji da jira ba ko,da kaji mu shiru.!?
Fad’in baffa da yake neman gurin zama
“A’a baffa babu komai..”
A mutunce suka gaisa da Baban Sabina,inda baffa yake yiwa Muhammad bayanin sai daya dangana da zuwa gona sannan ya samo Aminu d’in,murmushi ya sake yi daga haka suka ci gaba d’an tab’a hira da su,,sai daya samu ak’alla awa guda a k’auyen yana tare da su suna ta hira sannan yayi musu sallama da niyyan komawa,,wannan karon ma har bakin titi suka tako shi buh wannan lokacin baffa da Babanta suka raki shi suna ta masa godiyan ziyara daya kawo musu,sai da suka ga ya tsallaka sannan suka kama hanyar komawa,shi kuma nan ya nufi inda ya bada ajiyar motansa yayiwa mutumin godiya,bayan yayi masa alkhairi kuma ya d’auki hanyan komawa skul..
Wasa² rayuwa ta fara yin nisa a tsakani,yayin da zuwa wannan lokacin tsakanin iyayen *SABINA* da *MUHAMMAD* zumunci mai k’arfin gaske ya sake k’ulluwa,,yayin da a b’angaren Muhammad kuwa a iya tsayin wannan lokacin ya kasance yana yawan kai musu ziyara lokaci zuwa lokaci idan ya samu dama,,,suma kansu dattijan biyu a tun bayan had’uwarsu da shi duk lokacin da zai zo d’in suna jin dad’in hakan sosai,haka shima a duk lokacin da yazo d’in har ya koma yakan tsinci kansa cikin tsantsar farin ciki da jin kamar yana tare da wani b’angare na ahalinsa,,a haka ne lokaci ya gangaro dan kuwa har sun yi exam sum gama sai dai tunda ya fara bai samu dama ya lek’a suba,ko da suka kammala exam d’in a lokacin da sun samu break irin na tsakanin semesters,sai yayi shirin komawa zuwa gida,sai dai ko kafin ya tafi d’in sai daya je k’auyen domin yayi musu sallama dan yasan zai kwana biyu acan,a nan ne yake shaida musu ya samu hutu zai tafi gida saboda ya jima bai jeba,kuma hutun zai d’auke shi tsayin lokaci kafin su sake had’uwa,,ko kafin suyi sallama da shi d’in tuni su baffa suka shiga hada-hadar had’a masa tsaraba,sosai suka cika shi da alkhairi had’e da tsaraba mai yawa,duk da a gurinsa bai so tafiya da komai ba dan gudun kada yaje gida a tuhume shi,buh yadda su baffa suka nuna rashin jin dad’i akan k’in amsar kyautar tasu sai yasa shi amsa kana yayi musu godiya,sannan suka sake yin sallama yana sake jaddada musu shi da dawowa sai ya k’are hutunsa.
Lokacin ko da suka fito daga d’akin da baffa yake saukar sa nan suka tsaya a tsakar gidan suna sake yin bankwana duka zuciyoyinsu babu dad’i saboda sabo da suka yi da shi a cikin d’an tak’aitaccen lokacin,,,ni kuwa dai cewa nayi kuji tsofaffi da son a sani,sai kace wani jininsu duk sun damu dan kawai zai tafi..Tunma kafin su raka shi kenan,ina kuma ga sun rabu gaba d’aya..?
D’an kalle² ya shiga yi a tsakar gidan kamar mai neman wani abun,kafin ya maida kallonsa ga baffa da yake masa magana,,shi kansa a lokacin tambayar baffan yake son yi game da inda Sabina take,amma kuma sai yayi shiru dan ya rasa me zai ce masa,,a haka duka suka yi sallama da sauran mutanen gidan suna tayi masa addu’ar Allah ya tsare hanya,cikin masu sallamar kuwa harda Innarta amma itan ta gagara ganuwa,,,a iya tsayin lokacin da suka shafe a tun bayan had’uwarsu da yake zuwa gidan bai tab’a zuwa ya tafi bai ganta ba sai yau,wannan dalilin sai yasa shi shiga wani irin yanayin nd karo na farko kenan a yau daya tsinci kansa da jin rashin dad’in faruwar hakan.A hakan ba tare daya sa ran ganinta ba suka tasamma k’ofar fita daga gidan,sai dai ga dukkan wanda ya sanshi ko ya kalleshi a wannan lokacin dole ne ya fahimci akwai damuwa a tattare da shi.
Ganin yadda yake tafiya kamar baya so yasa baffa yayi saurin kallonsa yana tambayarsa
“Mai babban suna ince dai ko lafiya kake..!?”
Da sauri ya d’ago kansa dake sunkuye a k’asa ya kalli baffa yana masa murmushi,kafin ya d’an girgiza kai kad’an yana cewa…..