ALKAWARIN JINI CHAPTER 5 BY _HAWWA MUH’D USMAN
Www.bankinhausanovels.com.ng
A hankali Hammad dake kwance jikin Mamma ya d’ago kai ya kalleta,yadda tayi shiru tun shigowarta har yanzun ta kasa cewa komai,yanayin da ya ganta ciki sosai yasa shi jin damuwa dan yasan ko mene ne yake damunta a lokacin,tofa baya rasa nasaba da damuwarsa nd haka dama take idan har zata ga d’aya cikin yaranta a damuwa yanzun sai aga duk ta koma cikin damuwan itama,kansa ya sake mayarwa ya kwantar a saman cinyanta while yana facing fuskarta,a hankali cikin damuwa ya bud’e bakinsa da yake jin yayi masa nauyi ya furta
“Mah..! Me yasa Daddy zai min haka ne,,me yasa bazai fahimci halin da nake ciki ba..I have already know myself,me yasa daddy shi ya kasa fahimta,,anya Mamma Daddy yana son farin cikina..!? Ya kamata ki fahimtar da shi matsalar da zan iya shiga idan ya hana ni..Please Mah..!”
Sai data sauke dogon ajiyar zuciya while idanunta suna kansa tana kallon fuskarsa kafin ta nisa ta fara magana
“Kada kace haka Yarona,,mahaifinka na sonka kuma yana son farin cikin ka,ba iya kai kad’ai ba,dukanmu ya damu damu,,kamar yadda na san halayensa nasan kaima ka san wasu a ciki,dukan ku babu wanda ban san halayensa ba,saboda ina rayuwa a tsakaninku,,,na san halayen mahaifinka ba bak’on abu bane a gurin mu,ni da ku duka mun san shi,mun kuma san shi d’in mutum ne mai kafewa akan ra’ayinsa,dukkan maganar daya fad’a baya tab’a canjata,saboda haka bamu isa muce zamu ja da shi ba ko mu iya canja masa tsari,,sai dai abu d’aya ne zan fad’a maka a yanzun,kuma shi ne ,an ta maimaita muku,a duk halin da zaka tsinci kanka abu na farko da nake son ka fara tunawa shi ne Allah,,nasani kuma kaima ka sani matuk’ar ka kai kukanka gare shi bazai tab’a tab’ar da kai ba,idan har ka ambace shi da lafazin daya dace ka nemi k’ariy’arsa da taimakonsa na tabbar zai taimake akan ko wane irin AL’AMARI,sannan abu na biyu ahi ne ka kiyaye kanka da bawa shaid’an hanyar da zai gurb’ata maka rayuwa da tarbiyyar da muka yi shekaru muna ginawa,abu na uku shi ne duk runtsi duk wuya ka kasance mai biyayya akan maganar mahaifinka,matuk’ar bawai ya sab’a dokar ubangiji ba,in sha Allah da sannu alkhairi zai kwankwasa maka k’ofa,,idan har kana da damuwa kada ka gaza wajen kai kukanka ga mahaliccinmu,dan shi kad’ai ne zai yaye maka duk wani k’unci daka tsinci kanka a ciki,ta hanyar musanya maka shi zuwa sauk’i,,abu na k’arshe kuma shi ne ka kasance mai rik’o da addini a duk inda ka tsinci rayuwarka,ka zama mai kiyaye amana,sannan ka kasance mai cika *ALK’AWARI* idan har ka rik’e wad’annan a matsayin abokan rayuwa to ina tabbatar maka cewa za kayi rayuwa ba tare da samun wata matsala ba,idan kuwa har kaga wani damuwa ya same ka,to ka k’addara cewa ya faru ne ba don komai ba sai don saboda ubangiji (S.W.T) yana son ya jarrabi imaninka.!”
Doguwar ajiyar zuciya ya saki,,yayin da yake jin kalamanta suna masa yawo had’e da ratsawa ta cikin jini da b’argonsa,nd cikin k’ank’anin lokaci sai ya fara jin wani irin sanyi da rahama suna sauka a jikinsa,tabbas shawaran Mamma’nsa a irin wannan halin na damuwa abun so ne gare shi,a duk lokacin daya tsinci kansa a damuwa matuk’ar tana kusa da shi takan yi k’ok’arin tunatar da shi,haka nan takan sashi jin samun nutsuwa akan harma yayi kokarin mantawa da damuwarsa da irin wad’annan nasihohin nata,shin shi kuwa da wane irin abune ya kamata ya biya ta irin wannan alkhairin..? Tabbas babu,sai dai ya k’udurcewa ransa a kullum zai kasance mai yi mata addu’ah tare da fatan dacewa duniya da lahira.
Magana yake son sake yi,amma maganarta duka ta saukar masa da wani irin kasalan da har yasa shi jin bazai iya sake cewa komai ba,dan haka ko da yayi shiru,Mamma’n nasa bata fasa masa nasiha ba,tsayin lokaci suna tare ba tare data tafi ta barshi shi a halin damuwa ba,a hakan da suke tun shigowarta tana ta fad’a masa sanyayyun kalamai bacci mai nauyin gaske ya d’auke shi,lokacin data tabbatar yayi bacci,fuskarsa ta zubawa idanu tana kallonsa,yayin da zuciyarta take cike da tausayinsa.
A wannan lokacin ba ita ta tashi barin d’akin ba sai data tabbatar baccin sa yayi nisa sannan ta kwantar masa da kansa a saman pillow,mantle taja ta rufe shi half sannan tayi masa addu’ah had’e da d’ora masa peck a chicks ta kuma shafa kansa,hanyan fita a d’akin ta kama bayan ta tabbatar tayi masa deactivating na fluorescence ta fita,fitowarta tana k’ok’arin rufe masa k’ofan yayi dai² da lokacin da Daddy yazo wucewa,bai yi mata magana ba illa binta da kallo kawai da yayi,dan haka itama bata ce masa komai ba,nan kowa ya wuce ya nufi hanyar bedroom d’insa,cikin zuciyar Mamma kuwa ko da taga ya wuce,sai data rakashi da ido sannan ta sake binsa da fatan Allah ya ganar da shi gaskiya kafin ta shige ciki itama.+
Bisa al’adarta duk dare kafin ta kwanta takan yi shafa’i da wutri,dan haka kai yanzunma ko data shigo d’akin kai tsaye ta wuce toilet da niyyan d’aura alwala,sai da tayi wanka sannan ta d’auro alwala,tana fitowa bata tsaya shafe² ba,ta shirya cikin kayan baccinta masu taushi sannan tabi duka jikinta da sanyayyun turaruka masu sanyin dad’i,ta kuma yi shirin fuskantar mahaliccinmu,,ko bayan data idar da sallah ta jima tana addu’o’i kafin ta tattara hijab d’in da pray mat ta adana.Kana ta fita bisa al’adarta ta biyu a duk dare bayan tayi sallah idan har ta fita kafin ta wuce d’akin mai gidan nata sai ta duba duka yaran idan ta tabbatar duka suna d’akunansu sannan ne itama take tafiya ta kwantar da hak’ark’arinta,fitowar ta sai data fara duba d’akin Badra,nan ta isketa a kwance a lokacin tuni har tayi bacci,addu’ah tayi mata had’e da gyara mata kwanciyan sannan ta fita zuwa d’akin Bassam,shi kam zaune ta ganshi saman bed yana latse² a computer gefensa kuma litattafai ne yana ta aikin research,addu’ah tayi masa had’e da fatan alkhairi daga nan kuma ko data fito sai ta nufi d’akin Daddy.Da sallama a bakinta ta shigo sai dai fuskarta babu wani isashen walwala,zaune ta tarar da shi saman royal bed d’insa ya mik’e k’afafu,gefe da gefensa kuma tari takardu ne yana dubawa,k’arasawa tayi ciki ta nemawa kanta gurinzama a d’ayan side d’in na gadon sai dai bata yi magana ba har zuwa tsayin lokacin data tabbatar ya gama abunda yake,hannunta tasa ta taya shi tattara takardun while tana d’an kallon sa k’asa² sannan ta saki ajiyar zuciya
“Yallab’ai..! Ni kuwa tun d’azun nake son muyi magana da kai akan matsalar Hammad..!”
Yana gaban wooden vault d’insa yana jera takardun dake hannunsa tayi maganar,ba tare daya juyo ba bare tasa ran ya d’auki maganar da muhimmanci ya furta
“Idan kin san maganar da za kiyi ba shida amfani a gurina kadama ki fara yi min ita..”
Wani iri ta kalleshi saboda maganar daya fad’a ko kad’an baiyi mata dad’i ba,amma duk da hakan sai ta daure taci gaba da fad’in
“Amma fa Yallab’ai ya kamata ace kayi nazari akan maganar nan,sannan ka duba irin hukuncin daka yanke,yana da kyau ka saussauta wannan masa,a rayuwar nan da muke ciki a yanzun,kuma a matsayinka na babban alkali da k’asa ke alfahari da kai nasan da wuya ace ka iya k’ididdige adadin rape cases da ke wakana a cikin jihar nan ma,bare ace mun tafi lissafin na k’asa baki d’aya,baka san dalilin da yasa yaron nan ya fito kai tsaye ya nuna maka abunda yake ransa ba,ni dai har ga Allah ina jin tsoron faruwar wani AL’AMARI akan rayuwarsa…!”
“Asiya..! Me yasa ne bakya jin magana.? Tun da farko na shaida miki na gama yanke hukunci akan wannan maganar, saboda haka ki kyale ni da wannan magannar,aure ne banyi ra’ayin yi masa a yanzun ba,dan haka zan gargad’e ki akan tayar min da maganar,ko da wasa daga yanzun har zuwa lokacin da Hammad zai hattama karatunsa bana so na sake jin maganar nan ta sake tasowa..!”
Sakato tayi tana kallonsa har ya k’are maganar,duk da jikinta yayi sanyi da lamarin zuwa yanzun,dan a yadda take ganin yana nuna fushi akan maganar hakan kad’ai ya isa yasa ta fahimtar lallai ba zai tab’a canjawa ba,a jiyar zuciya ta sauke mai nauyi tana jinjina kai,cikin takaici gami da zullumin irin wannan baud’ad’d’en ra’ayin nasa ta sake kallonsa
“Shi kenan Yallab’ai.. Naji na kuma amince kamar yadda kace,in sha Allah bazan sake tada maka maganar ba,amma ina son ka san cewa,kamar yadda kace baka so maganar mun barta da izinin Allah,daga yanzun bazan kuma yi maka ita ba,haka shi kansa Hammad zanyi iyakar k’ok’arina nayi calming nasa akan maganar,,amma ina so kaji tsoron Allah,sannan ka tuna da lahira,kamar yadda ubangiji ya sanyaka ka zama shugaba a garemu baki d’aya,ka tuna da cewa ubangiji zai tambayeka akan hak’k’ok’inmu da suka rataya a wiyanka,sannan kada ka manta da hadisin Annabi (S.A.W) da yake cewa:”Dukkaninku masu kiwo ne,kuma dukanninku ababen tambaya ne abisa kiwon da aka baku,shugaba mai kiwo ne,za’a tambaye shi akan kiwon da aka bashi,namiji/miji mai kiwo ne abisa iyalinsa,haka kuma za’a tambaye shi akan kiwon da aka bashi,mace mai kiwo ce abisa gidan mijinta,haka nan itama za’a tambayeta abisa kiwon da aka bata,bawa mai kiwo ne abisa dukiyar uban gidansa,za kuma a tambaye shi akan abin kiwonsa” Sannan Annabi (S.A.W) ya sake cewa:”Ku saurara,dukan nin ku ababen tambaya ne akan kiwon da aka baku.!” Shin Yallab’ai wannan ba lamari ne da ya kamata ace munyi duba akansa ba a matsayin mu na mahaifa wad’anda Allah ya bawa kiwo ba.? Ya kamata ace muyi iya k’ok’arin mu wajen kiyaye tarbiyyar yaranmu fa,bai kamata ace kai da zaka tunatar da wani kayi k’ok’arin aiki da abunda ka san babu shi addini ba,kayi nazarin magana ta..”
Ajiyar zuciya ya sauke yana sake kallonta har zuwa lokacin da ta yi shiru
“Shi kenan na ji,na kuma gode,amma ki bani lokaci zan duba maganar ki..”
Daga haka ya rufe vault d’in sannan ya nufo gadon,inda ya tashi nan ya koma yanzun ma,sai dai wannan karon yana zuwa kwanciya yayi had’e da rufe idanunsa ya shiga jera addu’o’i,,Mamma kuwa jin abunda ya fad’a sai yasa hankalinta ya d’an fara kwanciya amma duk da hakan bawai ta sa rai hundred percent bane akan zai bi shawarar tata,sai dan kawai tana saka rai akan la’alla ubangiji zai karkatar da hankalinsa zuwa ga hanyar gaskiya,dan haka take ta sake k’udurcewa ranta zata sake jajircewa wajen yin addu’ah har zuwa lokacin da Allah zai sa ya yarda ya amince da abunda yaron nasu yazo da shi
“Yallab’ai.!”
Ta sake kiransa a lokacin daya kwanta,ba tare daya d’ago ba ya furta
“Dan Allah Asiya ki kyaleni haka nan da maganar nan,ya kamata ki san cewa dare fa yayi..Yanzun ba lokacin daya kamata ace muna wannan maganar bane..”
Sunkuyar da kanta ta d’anyi kad’an kafin tace
“Haka ne Yallab’ai.. Buh dama ba wani abu zance maka ba illa maganar fare da Hammad yayi maka d’azun,,ina son baka hak’uri ne dan Allah,kaga yazo matakin k’arshe,idan aka ce ka janye tallafin ka akan karatunsa,komai fa yana iya faruwa..”
“Uhhuumm..! Sai aka yi yaya kenan..!?”
“Ehh! Toh dama ina son ne nace maka..!”
“Asiya kenan,ni da Hammad ai mun gama magana,saboda haka babu ruwan ki a cikin wannan matsalar,magana ne tsakanina da shi,idan yaji maganar da nayi zai zo ya tuntub’e ni da zancen ko kuwa..!?”
“Haba ranka ya dad’e,, Kayi hak’uri mana, kamar yadda kace Hammad yaro ne,ni da kai duka mun san da hakan,amma ni abunda nake tsoro game da maganar nan,kadafa muje garin son gina rayuwarsa ya zama munyi k’ok’arin rusata da hannunmu,ka fahimci magana ta..”
Shiru ya sake yi yana jinjina kai sannan ya ce
“Shi kenan na fahimta,,amma dai ki bari nayi tunanin..”
“Toh Yallab’ai,, Allah yasa muji alkhairi..”
Da “ameen” ya amsa mata,daga haka yayi kwanciyarsa danma kada ta sake cewa wani abu sai ya juya mata baya,a lokaci guda d’akin yayi shiru yayin da zuciyar kowannensu take cike da tunanin abunda d’an uwansa ya fad’a,haka ma kowannensu tunanin da yake yi da hangen sa sai ya zama ya bambanta dana d’an uwansa.
A gefen Hammad kuwa tun gabanin asubah ya farka,nan fa ko daya duba baiga Mamma ba,a lokacin sai ya kalli agogo,yadda yaga lokaci yayi nisa ne sai ya gane cewa yayi bacci mai nisa,,zama yayi shiru yana sake tunani akan maganar daddy da yace masa zab’i ya rage nasa,idan zaiyi masa abunda yake so,shima zai masa abunda ya dace a matsayinsa na mahaifi,to shin idan ya sab’a hakan na nufin hukuncin Daddy yana nan na cewa da yayi zai zare hannunsa akan duk wani tallafin da yake bashi..!? Irin wad’annan tunanukan sune suka yita ma Hammad yawo a cikin kai,tun daya farka yake zaune shiru ba shi ya motsa ba sai daya fara jin ana kiran sallah sannan ya iya tashi a gurin,toilet ya wuce ya d’aura alwala sannan ya fita zuwa masallaci.
Lokacin da aka idar da sallah bai dawo gida a lokacin ba,sai da gari ya fara haske,ko daya shigo a lokacin gidan shiru,sai yayi shirin fita morning exercise,kamar ko wane lokaci ya fito cikin shirinsa sanye cikin sport wear na company *NIKE* yayin da k’afarsa ke sakaye cikin buffer running leisure sports shoe masu matuk’ar kyau da suke d’auke da tambarin dake nuni da cewa suma d’in sun fito ne daga company Nike,ficewa yayi a gidan yana riding abun sonsa wato bike na specialized allez,kai tsaye cikin race course ya nufa inda a kowane safiya idan har yana gida tofa ba shi da gurin daya wuce masa nan d’in,,almost two hours da wasu mintuna ya shafe sannan ya fito daga race course yayin da jikinsa yake jik’e da gumi,,shigowarsa cikin gidan ya iske babu kowa a parlor ko da yaga haka shima bai tsaya neman inda suke ba ya wuce hanyan staircase,direct bedroom d’insa ya isa ko da shigarsa nan ya fara k’ok’arin cire kayan dake jikinsa,lokacin daya rage daga shi sai boxer’s nan take duk wani suffar k’arfi ya bayyana a jikinsa,saman resting chair ya zauna yana ajiyar numfashi,sai daya samu ak’alla wasu mintuna yana zaune kafin ya tashi ya nufi bathroom da niyyar yin wanka.
D’aure da towel ya fito wanda ya tsaya masa iya waist yayin da hannunsa yake rik’e da mini towel da yake goge sumar kansa zuwa sauran sassan jikinsa,yana tafe yana fi gaba da goge jikinsan,har ya nufi gaban mirror kamar wanda akace ya dawo sai kuma ya nufi gefen bedside drawer inda ya zube wayoyinsa,a hankali ya mik’a hannu ya d’auko galaxy d’insa sannan ya shiga neman line Sultan dan a yau yake son su k’are magana da shi kan yadda zasu yi wajen komawa skul a goben,,kira kusan uku yayi masa ba tare da yayii answering ba,dan haka kawai sai ya yanke shawaran idan ya fita sai ya bi ta wajensa,mayar da phone d’in yayi ya ajiye yana d’an cije lip,har ya juya zai bar wajen ya sake dawowa,da sauri ya d’auko phone d’in yana sake dubawa,alamun sak’on daya gani ta inbox yasa shi saurin shiga da niyyar dubawa,sunan Mamma ya gani a guda while d’ayan kuma ko daya duba daga bank ne,sak’on Mammansa ya fara bud’ewa ya shiga duba abunda ta rubuto d’in
“Mrng Babynah..Na shigo ban ganka ba,buh nasan ka fita tun d’azun,, idan ka dawo ka same ni za muyi magana..”
Murmushi kad’ai yayi sannan ya fita ba tare daya duba d’ayan text message d’in ba da niyyar zuwa gurinta yaji maganar da tace masa za suyi d’in,lokacin da ko daya fito daga bedroom d’in d’akin ta ya fara dubawa sai dai bai ganta a nan ba,ganin haka yasa shi sauka downstairs,nd can d’inma bata nan,har kitchen duka sai daya duba ko da yaga bata nan wannan tasa shi komawa parlor kawai yayi zamansa,dan yasan duk inda ta shiga idan har ta fito zai ga shigowarta.
Kun san akan ce tsakanin mata da miji sai Allah,,kamar haka ne ya kasance ga Mamma da Daddy a wannan safiyar,,a kwanaki kusan uku da suka gabata sam idan ka gansu ba zaka tab’a zaton zasu d’inke a cikin k’ananun kwanaki kamar haka ba,amma a wannan safiyar dukda cewa da dare kafin wayeyar garin sun d’an samu sab’ani,amma a yanzun idan har ka kallesu lokacin da suka fito parlor kai baka ce sune suka samu sab’ani akan maganar Hammad ba,,ya samu ak’alla mintuna ashirin zaune kafin ya jiyo fitowarsu,suna tafe suna hira cike da shauk’i har suka k’araso cikin parlor’n,shi kansa Hammad lokacin da yaga fitowarsu sai da gabansa ya fad’i,amma kuma ko daya tuna alak’ar dake tsakaninsu da juna,sai kawai yaci gaba da addu’ah akan Allah ya taimake shi,duk da yasan abune mai wuyar gaske ace yayi winning over his Dad,a hankali ya janye idanunsa akansu sannan ya furta
“Barka da fitowa..”
Ko kad’an baiyi tunanin samun amsawar Daddy ba,amma sai ya ji shine ma ya fara amsa masa,mamaki fal zuciyarsa yake tambayar kansa
“Shin me hakan yake nufi..??” Tun kafin ya gama kokwanton da yake akan al’amarin tuni muryan Daddy ta dawo dashi daga mafarkin ido biyu daya tafi
“Son.. Ka tashi lafiya..”
Sake kallon Daddy yayi cike da tsananin mamaki,hakan sai yasa shi kasa amsawa saboda yadda yake ganin kamar ba Daddy’n ne da gaske yake masa magana ba,Mamma data farga da halin da yake ciki ne ta d’anyi magana da k’arfi ta hanyar kiran sunansa yadda tasan zai jita sosai,,a hankali ya waiwaya sashen da take ya kalleta,ido ta lumshe masa tayi masa alamun ya kwantar da hankalinsa,a hankali shima d’in sai yayi murmushin basarwa yana sosa k’eya
“Dad..! Barka da safiya..”
Da kulawa a maganar Daddy ya amsa masa da
“Ka tashi lafiya..? Ya sauk’in jiki..?”+
“Alhamdulillah Dad..!”
“Masha Allah,,haka muke fata a koda yaushe,ku kasance cikin k’oshin lafiya..”
Shi dai kam yana cikin rud’anin abunda Daddy yayi,sai dai ba tare daya sake magana ba daga gaisuwa yaja bakinsa ya tsuke,kallonsa Mamma ta sake yi da tambayar
“Ina wad’annan yaran suke..?? Kada dai ace duk magasannan nayi baisa sun fito ba.”
“Anya Mamma..? Bana tunanin sun sakko..”
Jinjina kai tayi cike da takaici sannan ta bashi umarnin ya kira su suyi break,cikin biyayya da nuna girmamawa ga maganarta ya mik’e ya nufi sama,bedroom d’in Bassam ya fara dubawa kasancewar shi ne daga farko,ko kafin ya shiga sai da yayi knocking sannan ya tura k’ofar ya shiga da sallama a bakinsa,kwance ya iske shi a saman bed yayi d’ai² yana ta zuba bacci abunsa cikin kwanciyar hankali,alamun da suka tabbatar masa da baima san ya shigo ba kenan,jinjina kai kawai yayi sannan ya nufe shi,duvet daya rufa ya janye sannan ya koma gefen windows ya yaye curtains d’in da suka sa d’akin yayi duhu,hasken rana daya hasko masa fuska sai yasa shi fara motsawa,kafin a hankali ya soma bud’e idanunsa da suka masa nauyi saboda azabar baccin dake kansa coz daren jiya bai samu ya kwanta da wuri ba yana ta aikin research,da Hammad ya fara arba yana tsaye a kusa da shi daga gefe fuskar nan kamar ba tasa ba,ya kafe shi da idanu nd hannayensa nad’e a chest d’insa
“Broahh..!”
Bassam ya fad’a cikin muryan bacci while yana mik’ewa ya zauna,hararansa Hammad yayi sannan ya juya ya kama hanyar fita a room d’in while yana fad’in
“Idan kaga dama ka sakko yanzun,if not kuma kaci gaba kasan ba dawowa zanyi na sake tashin ka ba..Tunda ita mamma ka rainata shi yasa za tayi ta zaryan zuwa tashinka.. “
K’ok’arin tashi ya fara dan yasan halin Hammad idan har ya fita bazai dawo d’in ba kamar yadda ya fad’a,haka nan yasan kansa zai cuta idan har bai sauka ba akan lokaci,,yana fita bedroom d’in BADRA ya sake lek’awa,lokacin ita kam tuni ta jima da tashi dan har tayi wanka ta shirya tana shirin fitowa shi kuma yana shigowa
“Hi Yah Hammad..”
Ta fad’a cikin y’ar siririyar muryanta tana masa waving,d’an murmushi yayi kafin ya amsa da
“Hello..! Daddy’s kiddo..”
Ganin da yayi ta gama abunda take yi ba tare da yayi mata magana ba ya juya zai fita,murmushi ta sake yi kafin ta gaida shi,yana tafiya yana amsa mata har ya fice,nan ta biyo shi suka sakko tare yana gaba tana biye da shi a baya har dining space,zaune suka tarar da Daddy da mamma tuni har sun fara break abunsu dan da dukkan alamuma Daddy yana niyyan fita ne da zaran ya kamalla abunda yake,sai da suka yi sallama kafin suka nemi guri suka zauna kowannensu ya shiga k’ok’arin bud’e plate dake rufe a gabansa sannan suka fara ci,babu wanda yake magana a gurin har zuwa sanda Bassam ya zo gurin a gaggauce,hararansa mamma tayi sai dai bata ce da shi komai ba taci gaba da cin abincinta har zuwa sanda ta kammala,ture plate d’in tayi gefe kad’an da fad’in
“Alhamdulillahillaziiy ad’a’amaniy haaza warazak’anihi min ghairi haulin minniy walak’uwwatiy..”
Daga haka sai bata sake yin magana ba har suka kammala sannan suka nufi cikin parlor dukansu,while daddy shi kuma yayi hanyar upstairs cikin sauri,mintuna biyar ya d’auka kafin ya sakko yana gyara zaman babbar rigarsa,sanda ya shigo tsakiyar parlor sannan ya kalli Hammad da fad’in
“Ehemm! Son yaushe ne zaka koma school..!?”
Kallon Mamma yayi sannan ya juya ga Daddy yana cewa
“Dad gobe ne zamu tafi..”
Jinjina kai Daddyn yayi kafin yaci gaba da tafiya yana fad’in
“Allah ya kaimu..”
K’asa² Mamma da Hammad suka amsa da “ameen”
“Toh.! Ni na tafi d’aurin aure,sai Allah ya dawo dani..”
“Allah ya tsare hanya Daddy..”
Cikin had’in baki dukansu suka fad’a,yayin da Mamma tabi bayansa suka fita tare dan yi masa rakiya,,a hankali Hammad ya maida idanunsa ya lumshe yana sakin ajiyar zuciya,deeply yake zancen zuci
“I know Dad zaka amincemin matuk’ar Mamma tasa baki,wannan dalilin yasa tun a farko na amincewa zuciyata na sanar da ita damuwata,,Thank u Mah..! Ba don keba da ban san adadin damuwan da zan shiga ba..Rabb ya biyaki da mafificin sakamako..”
Murmushin samun nutsuwa ya d’an saki sannan ya mik’e ya bar wajen..
*Monday TUSHEN aiki,ko bature na tsoronki.. Taken da bahaushe yayi kenan wa wannan rana.*
Tun asubah bayan da aka idar da sallah a masallaci bai tsaya ba ya nufo gida dan ya samu daman shirya sauran abubuwan da yasan zai buk’ata,around 7:00am ya gama packing kayansa a side,sannan ya shige bathroom,within 30 minutes cikin sauri har ya gama komai sai tafiya daya rage masa,lokacin daya tabbatar babu sauran wani abu daya rage masa ne ya d’auki phone da niyyar kiran Sultan,sai dai har yayi masa kira kusan uku duka bai d’auka ba,sai a kira na hud’u sannan Sultan d’in ya d’aga cikin muryan bacci
“Yane broah..!”
Ya fad’a yana murza idanunsa,shiru Hammad yayi bai tanka ba saboda takaicin jin sai yanzun nema ya tashi,kenan hakan yana nufin ko shiryawa Sultan d’inma baiyi ba kenan..??
“Hello..! Man..!?”
Ya sake fad’a yana mik’ewa tsaye,cikin matuk’ar jin haushi Hammad fara magana
“Amma dai kai wollahi anyi d’an iska,,banda ka rainawa kanka hankali sai yanzun ne zaka tashi a bacci..?”
“Sorry broah maa d’an kwanta ne bayan na dawo a masjeed sai bacci ya d’an d’auke ni..Buh lemme pack my luggage’s..”
Bai k’arasa ba Hammad ya tari numfashin sa da fad’in
“What..!? Ur luggage’s..? Kana nufin bakama had’a suba sai yanzun..? Wollahi to ba dani zaka tafi ba,,zanyi gaba idan ka gama shiryawa ka same ni a school..!”
“No! Broah..Ka bari mana yanzun zan kammala mu wuce,,ka san bamu saba tafiya mutum d’aya ba,ka bani minti ashirin ma,it’s ok for me na gama..!”
Tsaki yaja ba tare daya k’arasa jin zancen ba ya katse kiran,fuskarsa babu alamun wasa a samanta ya shiga jan luggage d’insa yayi waje ba tare daya bi ko takan ma’aikatan gidan ba bare yasa a fitar masa da su,,sai daya fitar da duka kayansa haraban gidan sannan ya koma ciki da sauri dan yiwa Mamma sallama,a kitchen ya isketa suna aikin shirya breakfast,bayan ya gaidata suka gaisa da housemaid’s d’insu cikin mutunci ya amsa musu babu wulak’anci kamar na wasu y’ay’an masu kud’in,daga haka suka fita tare da Mamma zuwa parlor,as usual idan har zaiyi irin wannan tafiyan na barin gida takan yi masa nasihohinta masu shiga jiki,yauma d’in sai data tabbatar ta sake yi masa nasihar ya kula da kansa sannan ya kasance mai takatsantsan da rayuwa a duk halin daya tsinci kansa,daga haka tayi maaa rakiya har bakin mota,ba ita ta koma ciki ba sai data ga ya kama hanyar fita a gidan sannan ta saki numfashi tana masa waving had’e da binsa da addu’o’i har zuwa lokacin daya fice a gidan.
Ko daya fito daga gida bai tsaya tunanin duba Sultan ba bare ya tuntub’e shi yaji ya gama d’in coz shi a tsarin rayuwarsa baya ta’ammali da mutumin da bai san muhimmancin lokaci ba,haka nan ya tsani jira,shi yasa da zaran yayi ALK’AWARI baya sab’awa k’a’idarsa,kai tsayen ko daya fito direct ya d’auki hanyarsa ta komawa garin na Wudil.
In less than an hour ya iso garin wudil,ko da yayi parking bayan ya zare seatbelt dake jikinsa yana k’ok’arin fita a motan kiran waya ya shigo masa,d’aukan wayan yayi ba tare daya tsaya dubawa ba,can daga d’ayan gefen muryan Sultan ya d’aki kunnensa
“Man..Wai ina ka mak’ale ne..? Tun d’azun fa na gama amma na jika shiru..”
“Da yake ai ka ajiye ni ne shi yasa zanyi zaman jiranka ba..??”
“Haba mana man,,duka fa ba wannan maganar bane,kana ina yanzun ni sai nazo na same ka..!?”
Jinjina kai yayi irin na ka rainawa kanka hankali kafin ya ce
“Ina school,,idan kayi sauri zaka iya tarar da ni acan.”
K’it ya sake katse kiran sannan ya shiga tattara sauran y’an kayansa ya nufi hanyan hostel..
*One week later..*
Cikin sauri ya fito ya nufi inda ya parker motansa,a lokacin Sultan ya biyo shi a baya cikin saurin yana tambayarsa inda zashi,bai kula shi ba ya shige cikin motan had’e da take ta,dai² isowar Sultan shi kuma ya d’aga a gurin,tsayawa kawai Sultan yayi rik’e da waist d’insa yabi shi da kaallo zuciyarsa cike fal da mamakin inda za shi cikin sauri haka,,ta mirror yake hango Sultan har ya b’acewa ganinsa,murmushi ya saki mai burgewa sannan a fili ya furta
“Ba zan tab’a bari ka san inda zani ba..”
(Tofa fan’s kunji wata sabuwa,ko mene ne dalilin Hammad na fad’in haka..?? Allah shi ne mafi sani,,amma bari muci gaba da binsa a baya,da sannu zamu gano dalilin)
Tun daya d’auki hanya yake shek’a gudu a bunsa,yayin da zuciyarsa take cike da wani irin shauk’i,cikin mafi k’ancin mintuna sai gashi ya iso dai² mararrabar daya saba tsayawa,bayan ya bar motan a gurin mutumin da yake bawa ajiya,sannan ya d’auka hanyan da zai kaishi cikin k’auyen nasu,yayi tafiya mai d’an tsayi kafin ya iso k’ofar gidan,tun a bakin zaure ya tsaya yayi sallama sannan ya koma gefe daga jikin bishiyar dake gurin ya jingina,bai wani jima sosai da tsaiwa a gurin ba Baban Sabina ya fito yana duba wanda yayi sallamar,ganin wanda ke tsaye a gurin sai ya sashi sakin fuska yana nufar gurinsa yake fad’in
“Maraba da takwara.. Yau a gari..??”
Murmushin shimaya mayar masa kafin ya durk’usa har k’asa ya gaida shi,cikin mutunci Baban ya amsa masa,sannan yayi masa jagaba suka isa cikin gidan,sun gaisa da jama’ar gidan kafin suka nufi turakar baffa da a lokacin yake k’ok’arin fitowa nan suka had’u a bakin k’ofa,ko da ganin Hammad tare da d’an uwansa take baffa ya saki fuska yana fad’in
“Maraba da mutanen Kano.. Kune tafe da wannan ranar..?? In ce dai ko har ka dawo makarantar..??”
Fuskarsa a sake ya amsawa baffa
“Na dawo baffa,,yau sati guda kenan,sai dai rashin lokaci da yasa ban zo ba..”
“Kayyahh.! Dama samun lokaci a gurin y’an makaranta ai da wahala,,musamman ku da kuke jami’a.. Fatan dai har kullum baya wuce ubangiji yasa ku kasance masu samun nasara..”
“K’warai kuwa Yaya,, ai sunama k’ok’ari a karatun,,mu kam da yake ba muyi ba bamu san dad’in saba,sai dai y’ay’a da jikoki da muke fatan ace su samu suyi..”
Daga haka duka sai suka d’unguma zuwa cikin d’akin dan su samu dama su tattauna musamman Hammad da yake tafe da magana a bakinsa zuwa ga baffa,lokacin da suka zauna,bayan sun sake gaisawa sannan ne Baban Sabina ya fita ya barsu su biyu a cikin d’akin,,bayan fitarsa a d’akin babu jimawa sai baffa ya juya ya kalli Hammad da kulawa yana fad’in
“Mai babban suna ya ka baro magabatan naka..?? Fatan duka suna lafiya..??”
Sai daya gyara zama sannan ya amsawa baffa da
“Suna nan lafiya k’alau baffa,sunce ayi muku godiya sosai,sunga abun sak’o,Allah ya saka da alkhairi..”
Murmushi baffa yayi sannan yayi shiru,, shima Hammad sai yayi shirun cikin zuciyarsa banda tunanin hanyar daya dace ya sanar da baffa abunda ke faruwa babu abunda yake yi,,yanayin yadda yayi shiru fuskarsa ta bayyanar da alamun damuwa yasa baffa kallonsa da kulawa kafin yayi magana
“Mai babban suna,,ince dai kana lafiya..Kuma babu wani abu da yake damunka..??”
D’ago kansa yayi dake sunkuye yana sakin ajiyar zuciya,kafin ya girgiza kai,cikin sanyin jiki da rashin hope ya fara magana
“A gaskiya baffa ba lafiya ba..”
Saurin gyara zama baffa yayi yana fad’in
“Subhanallahi..! Wani abu ya faru da kai,ko kuwa da wani naka..??”
Shima d’in gyara zaman ya sake yi kafin ya fara zayyanawa baffa duk abunda ya faru tun daga kan maganar da suka yi kwanakin da suka gabata akan Sabina,lokacin daya shaida masa zai sanar da magabatansa har zuwa duk yadda suka yi da Daddy’nsa,sai dai ya b’oye masa batun ra’ayin Daddy akansu,,fuskar baffa duk da yaji batun na Hammad kuma baiji dad’in hakan daya faru ba,amma kuma bai hana masa yin murmushi ba
“Mai baban suna,ina ganin wannan ba matsala bane da har zaisa ka shiga damuwa,tun da farko ko da kazo min da wannan batun nina amince maka ka nemi soyayyar yarinyar nan,saboda haka dan mahaifinka ya nuna cewa sai ka kammala karatu ai ba wani abu bane,kayi hak’uri da duk abunda yace akan maganar,sannan ka zama maiyi masa biyayya in sha Allah komai zaizo da sauk’i,, mu idan har ta b’angaren mune baka da matsala damu,da yardar Allah babu wani abu da zaisa mu canja ALK’AWARIN da muka yi maka,,sannan matuk’ar akan SHALELE ne ni da kaina na amince maka ka ci gaba da nemanta daga yanzun har zuwa lokacin da mahaifinka zai sakko ya tuntub’eka da batun..Amma kayi hak’uri da duk hukuncin da zasu zartar,in sha Allahu alkhairi yana nan zuwa..”
Maganar baffa sosai tasa Hammad jin tsananin farin ciki coz baiyi tunanin samun wata dama daga garesu ba akan batun,sai gashi a garab’asa ya samu amincewar baffa,har kuma yana bashi tabbacin yaci gaba da kafa gwamnatinsa,godiya sosai yayi masa had’e da addu’o’i na fatan samun tsawon rai,sun d’an tab’a hira kafin baffa ya fita ya barshi zaune shi d’aya da niyyar turo masa ita idan ya fita,ko daya fita a d’akin baffan da kansa yaje wajensu Sabina ya kira ta,bayan daya tabbatar ta tafi gurin Hammad d’in sannan ya fita daga gidan..
Lokaci ya ci gaba da tafiya yayin da shak’uwa,yarda da juna had’e da soyayya mai tsuma rai ta sake shiga tsakanin Hammad da Sabina,a duk lokacin da aka ce yau weekend ne cikin kwanakin bazaka tab’a samunsa a cikin skul ba,tun safe idan ya tafi k’auyen nasu tofa ba shi zai dawo ba sai yamma sosai,a haka rayuwa taci gaba da gangarawa,yayin da ta b’angaren karatunsa ya sake nutsuwa coz yana son cika burin mahaifinsa akansa,duk da soyayya daya tsinci kansa a ciki ko kad’an hakan bai hana masa mayar da akalar hankalinsa kan karantun ba,musamman daya kasance yanzun suna tsakiyar last semester nasu….Cikin wannan lokacin a hankali semester d’insu yaci gaba da yin nisa,yayin da bisa dole yasa Hammad jingine duk wasu al’amura nasa a gefe yaci gaba da fuskantar exam dake hararo shi,batun zuwansa k’auye kuwa a yanzun kasancewar baya samun wadataccen lokaci sosai na zirga² tsakanin k’auyensu da skul shima sai ya ajiye shi gefe,ya tattara hankalinsa kacokam a guri d’aya,ma’ana dai ya maida shi kan karatunsa,wanda a kullum addu’arsa,fatansa da kuma jajircewarsa baya wuce ace ya fita da sakamakon da Daddy’nsa zaiyi alfahari da shi,har ma da fatan ace Daddy ya yarje masa kan batun soyayyar sa duk da yasan abune mai wahalar gaske..+
*Some month leave…*
Lokaci ya tafi sosai,yayin da ta kowane b’angare ake samun ci gaba,,a gefen Hammad kam a wannan lokacin yana ta sake had’uwa da ci gaba a rayuwarsa,wanda a yanzun haka abunda ya rave masa ya kammala service nasa bai wuce y’an kwanaki ba,,wanda tun a wancan lokacin da yake shirin tafiya,kasancewar Daddy’nsa da yake sananne a k’asar nd ya shiga ya fita kan batunsa da yace baya son yin nisa da gida,yasa sai aka barshi a nan Kano,dan haka ko da aka tashi posting nasa shi da kansa ya zab’ama kanshi inda yake muradi watog garin WUDIL,coz a gurinsa yana ganin hakan shi ne hanya mafi sauk’i da zata sake bashi damar kusanta kansa zuwa ga soyayyar ta.
A b’angaren iyayen Sabima kuwa,tun lokacin da baffa suka yi magana da Hammad akan batun soyayyarsu,ko kad’an baffa bai sake tayar masa da batun zuwan mahaifansa ba,ko ya tambaye shi har tsawon wane lokaci ne zasu zo a tsayar da maganar auren su,duka tsakanin baffa da baban SABINA babu wanda ya tab’a tuntub’arsa da maganar har zuwa yanzun da shak’uwarsu ta sake yin k’arfi sosai,,duk da irin tsaigumin da yake yawo a cikin garin,akan al’amuran familyn a yanzun,wanda cikin wannan lokacin duk inda mutim zai zauna hiran da zaiji yana yawo kenan,haka nan babu wani majalisa da zata taru ta watse ba tare da an sako zancen family’n ba,nd haka nan ba zaka tab’a jin wani maganar kirki akansu ba sai dai akasin hakan duk da kasancewar sune asalin kafuwar garin,haka nan kowa da irin abunda zaka ji yana fitowa daga bakinsa,yayin da wasu ke fad’in alkhairi,wasu kuwa sharri ne zaka ji ya biyo bayan maganganun su,a lokacin da wasu ke cewa kwad’ayin abun duniya yasa su baffa bawa SABINA goyon bayan kula d’an binni,yayin ne kuma zaka ji wasu sunce su baffan suna son yin amfani ne da wannan damar ta hanyar tallata ahalinsu a gurin manyan masu kud’i,muaamman ma ita SABINA data kasance SHALELE a gurinsu duka,shi yasa suka k’i barin wani cikin samarin garin ya nemi aurenta,kamar yadda suka k’i had’a ta da LADO,ko wane lokaci suke cewa sun bada aurenta ga wani bare can a waje,,haka dai maganganu marasa dad’i suka ci gaba yawo,wanda basu tsaya iya kan su baffa kad’ai ba hatta da sauran yaran gidan dukansu suma basu tsiraba daga zage²n da ake yi d’in,buh duk da haka baffa sai ya sake toshe kunnensa bai kankama kowa ba,haka nan duka ahalinsu ya gargad’e su akan kada yaji ko ya gani,wani ciki ya tanka maganar duk da zaiji an fad’a.Cikin wannan yanayin rayuwa mai cike da nutsuwa gami da kwanciyar hankali taci gaba da gudana a tsakanin wad’annan ahali..
Cikin nutsuwa take tafiya kan hanyarta ta dawowa daga makaranta,duk da tare suke da su Hamudan amma ba lallai ne ayi saurin gano hakan ba,kasancewar tsakaninsu da ita akwai y’ar tazara sunyi d’an nisa da juna,da yake sunyi gaba da ita saboda guje²n da suke suna tafe suna tsokanar juna,a haka har suka k’araso k’ofar gida,,shigowarta a zauren gidan yayi dai² da lokacin da LADO ya sawo kai zai fito,ko da ganin ya riga ya shigo tsakiyar hanya babu kuma yadda za’ayi ta kaucewa had’uwa da shi sai yasa ta matsawa gefe ta bashi hanya tana jiran ya wuce,coz tasan idan tace zata wuce ba zai tab’a bata hanya ba,nd yana iya hankad’eta gefe ya kuma bi ta kanta,duk a dalilin k’in amincewar da tayi da shi,kamar ta san wani abu zai iya faruwa tun data kauce ta bashi hanya sai bata ko d’ago ba bare ta kalleshi taci gaba da jiran ya wuce ya bata hanya,,ga LADO kuwa tun tuni dama ya jima yana neman hanyar da zai b’ata mata duk kuwa da a yanzun tana matuk’ar k’ok’arin yin takatsantsan da duk wani abu da zai had’a su da juna tunda tasan ba mutunci ne da shi ba,haka nan baya ganin mutuncin kowa a gidan,dama² ace baffa yana nan duk da shima d’in bai tsiraba ba indai a gurin LADO ne,ci gaba yayi da tsaiwa a tsakiyar hanya shi bai koma cikin gidan ba haka nan shi bai bata hanya ta wuce ba,k da ganin ta fara gajiya da tsaiwar sai ta yankewa kanta shawaran yi masa magana,idanunta ta d’ago dake k’asa ta kalle shi sannan ta furta
“D’an matsa zan wuce..!”
Kamar mai jiran ta tanka masa ko gama rufe baki bai jira ta yi ba ya bata amsa
“Idan nak’i na matsa d’in fa..? Za’ayi min wani abu ne..?”
Shiru tayi bata tanka masa ba,ganin ta k’i sake tanka masa sai yasa shi jan mugun tsaki nd still yana tsayen bai motsa ba bare tasa rai da zai bata hanya ta wuce,saboda kalen bala’i nd dan ya b’ata mata rai nan take ya shiga jero bak’ak’en maganganun b’atanci akanta da Hammad,,sosai kalamansa suka soki zuciyarta,wanda yasa nan da nan ta fara jin babu dad’i musamman kalmomin da yake fad’a akan Hammad,amma duk da hakan sai taci gaba da rarrashin zuciyarta,yayin da idanunta ke cike taf da ruwan hawaye,still kuma tak’i yarda ta d’ago gudun kada ya gano weaknesses nata,haka suka ci gaba da tsaiwa har na wani lokaci,ba tare data d’ago ba haka nan tak’i yarda ta tanka masa,coz tasan akwai abunda yake damunsa musamman cikin wannan d’an lokacin daya san labarin soyayyar ta da Hammad d’in shi yasa yake son tononta da fad’a,wannaan dalilin shi yasa sai ta yiwa kanta ALK’AWARIN duk abunda zai mata ba zata tab’a biye masa ba,sanda yayi mai isarsa ganin tak’i kula shi yasa kan dole yaja bakinsa yayi shiru,kafin ya bita da wani irin kallon wulak’anci ya fara tafiya da niyyar barin gurin,tsaki yaja mai tattare da takaicin shirun da tayi masa yana sake fad’in
“Mutum dai ya gama zagayen duk da zaiyi,dan mu dai idan har yarinya ta kwaso mana ciwo babu ruwan mu eheee..! Mu dai a lokacin dariya ne namu,,idan kuma muka ji ba zamu iya hak’ura ba muce Allah ya k’ara..!”
Wannan kalaman sunfi komai k’ona mata zuciya dan yadda taji saukarsu ji tayi har sun zarta duk sauran maganganun daya fad’a abaya,,,shin me yake nufi ne da wannan maganar,yana nufin yace suna aikata wani abu ne a bayan idanun mutanen gidan su ko kuwa me yake son fad’a..?? Zuciyarta ta ambata mata,da k’una a ranta ta d’ago a fusace tana niyyan yin magana idanunta taf da hawayen bak’in ciki sai ganin Hammad tayi tsaye a bakin hanya yana sakin murmushi,a hankali ta janye idanunta a kansa,shi kuwa gogan sake gyara tsaiwa yayi had’e da sauke hannayensa dake nad’e a chest ya zubasu cikin aljihu kafin yaci gaba da takowa cikin zauren,duk kaifin baki irin na LADO kuwa ganin daya yiwa Hammad a wannan lokacin da babu zato sai da jikinsa yayi sanyi,tunaninsa da duk wani kuzarin da yake jin yana da su,nan take yaji sun gudu a jikinsa,a gabansa Hammad ya tsaya yana k’are masa kallo kamar mai tunanin abunda zai fad’a,zuwa wani lokaci kuma sai ya sake gyara tsaiwansa da fad’in
“Mun godefa sosai *YAYANMU,* sai dai ina ganin ya kamata ne ace ka koyi yadda zaka rik’e girmanka,hakan da kayi sam ba girmanka bane,,a matsayinka na babba ya kamata ne ace ka tsaya a matsayinka,irin haka yana janyo raini,saboda haka ka rik’e mutuncin ka kafin na… Ka fahimta ai..!?”
Sai daya sake yin k’asa da muryansa sosai ta yadda yasan babu yadda za’ayi SABINA dake tsaye gefensu ta ji,haka nan fuskarsa babu alamun wasa a samanta ya furta
“Idan ba haka ba,matukar ka sake shiga sabgar da ba naka ba,zan koya maka hankali ne,kamar yadda nayi a had’uwarmu na farko..Hope kana tunawa da ranar,,baka manta ba..!?”
Shiru LADO yayi ya kasa magana dan wani irin kunyan Hammad mai tattare da tsoro daya kama shi,sam baiyi tunanin yaji duk maganganun ba,dan haka ko da Hammad ya fad’a masa haka sum² ya silale zai fice a zauren,cikin salo Hammad daya matsa gefe ya furta
“Ohh! YAYANMU baka ji ba..”
Cike da tsoro LADO ya waiwayo ya kalleshi sai dai ya kasa had’a ido da shi
“Emm! Nace ba,,next time ko da ace kaji kana son yin irin wannan maganar,ba ita ya dace ka fad’awa ba,ka same ni kai tsaye ka sanar da ni…Kaa ji ba..!?”
Ya k’arasa maganar da yiwa LADO winking,,sum² LADO yayi kafin kace kobo tuni har ya b’ace a gurin,,da ido Hammad ya raka shi cikin wani matsiyacin kallo sannan ya tab’e baki,,cikin nutsuwarsa ya sake waiwayowa kanta dan tun daya shigo suka had’a ido ta sauke kanta k’asa,kallo d’aya yayi mata tuni ya fahimci yanayin da take ciki,,ganin ta sake sunkuyar da kai a hankali kuma tasa hannu tana wiping tears da suka sakko mata,sai kawai ya tsaya yana kallonta ba tare da yayi magana ba har ta gama goge²n fuskar,muryansa da takaici ya furta
“Wannan maganar har ya kai wanda za ace kinyi masa kuka..??”
Bata ce da shi komai ba haka nan bata d’ago ba saima sake sauke kai da tayi a k’asa kamar mai neman wani abu,shi kuwa ko da yaga bata da niyyan d’agowa cikin gatse bayan ya jinjina kai yana sake kallonta ya ce
“Ok..Wuce kije gida ko tunda ba kya iya magana..”
A hankali ta d’ago ta kalleshi cike da nazarin maganarsa,yanayinsa sam bai yi mata kama da irin wanda za’a ce tayi saurin gane abunda yake nufi bane,haka nan saman fuskarsa ba zaka tab’a iya rarrabe wane yanayi yake ciki ba,shin da gaske yake mata ta shiga gida ko kuwa akasin haka yake nufi? Ita kam ta kasa bambancewa dan haka sai taji ta kasa tafiya a gurin
“Ki shiga gida y’an mata..Ina shigowa yanzun..”
Sake kallonsa tayi sai dai wannan karon ko da yayi maganar ba ita yake kallo ba,sai data d’auki wasu mintuna tsaye da tunanin ko zai ce mata wani abu,amma sai yayi shiru,ma’ana dai yan mulkin sunzo kenan,cikin k’arfin hali ko da taga haka sai ta juya ta bar wajen,shigarta gida babu jimawa dan ko d’akinsu bata gama shigewa ba ta jiyo shi suna gaisawa da matan baffaninta,da sauri ta k’arasa ciki tana sakin sanyayyun ajiyar zuciya..
*A gurguje..*
Masu iya magana kance,sannu² bata hana zuwa,sai dai a dad’e ba’a jeba,haka nan dukkan abunda aka sakawa rana,dole ne wata rana zai zo harna ya wuce,,,kamar yau Hammad ya fara service,cikin hukuncin ubangiji sai gashi har lokacin kammalawarsa ya zo,,batun sakamako kuwa tuni ya jima da amsarsa,mafarkin daya jima yana yi akansa sai gashi addu’o’in daya jajirce yana yi,tare da taimakon addu’o’in Mammansa sun sa shi samun nasara ya fita da first class,,shi kansa mahaifinsa lokacin da yaga sakamakon duk da yasan waye yaron nasa da irin baiwar da yake da ita tun tasowarsa,a ranar a kuma dalilin irin sakamakon daya zo masa da shi sai yake jin wani sabon sonyayyarsa na sake ninkuwa a ransa,tabbas ya sani duk inda yake tunanin Hammad ya kai ya zarta,dan kuwa shi d’in abun alfahari ne a gurin ko wane irin iyaye,a wannan ranar daya rik’e result d’in nasa a hannunsa babu irin abunuwan da bai sak’a ba game da Hammad d’in akan ci gaban rayuwarsa,,,haka nan a ta b’angaren duk wani abokin arzik’i da yan uwa ga Hammas da duk wanda ya kasance makusanci gare shi babu wanda bai taya shi murna ba bisa wannan gagarumin abun farin cikin daya samu kansa a ciki,,ga uban gayyar kuwa a dai² wannan lokacin da yake ganin komai yazo masa k’arshe,shi duk ba wannan ne damuwarsa a yanzun ba,dan duk wani murnan da mutane ke taya shi idan har da ace zai bud’e musu sirrin zuciyarsa tofa lallai ne babu abunda zai hana basu adana farin cikinsu ba har zuwa wani lokaci..
Tun daya shigo gidan bayan rabuwarsu da Sultan ya shige bedroom d’insa,cikin kwanakin tun daya samu nutsuwarsa ta dawo masa da kyar yake iya saita nutsuwarsa,yanzunma ko kafin ya shiga wanka abunda ya faru da shi kenan,lokacin daya fito bayan ya gama shiryawa saman royar bed d’insa ya haye,maimakon ace a dai² wannan lokacin ya samu damar kwanciya ya huta gajiyarsa,sai kawai ya sake gyara zama had’e flexing legs,chin d’insa ya d’ora saman hannayensa daya sark’e guri guda yana mai nausawa zuwa duniyar tunani da neman mafita akan al’amuransa,,sai daya kusan raba dare yana tunanin hanyar da zai bi ya sanar da Daddy damuwarsa da yadda yake ganin had’uwarsu da Daddyn zai kasance idan har yayi masa batun kan ra’ayinsa,dan ya san dole ne ko ba gobe ba cikin kwanakin yayi maganar,coz ya san Daddy’nsa akwai shi da nuna matuk’ar jajircewa akan lamuransu musamman ma shi daya kasance babba,,,yana zaune yana ta tunanin abun yi,da hanyar daya kamata yabi wajen shaidawa Daddy SIRRIN ZUCIYARSA sai dai ya rasa mafita,a hakan da yakee har bacci ya fara fizgarsa ba tare daya shiryama yinsa ba,sai da baccin yaci k’arfinsa kafin ya hak’ura ya gyara kwanciya,addu’ah kam a wannan daren da kyar bakinsa ya iya motsawa har ya samu ya furta
“Bismikallahumma ahya wa’amuut..”
Daga haka yayi shiru bacci mai k’arfin gaske ya d’auke shi,,da asubah kusan makara yayi dan sai da Mamma tazo ta tada shi sannan ya iya fita masjeed,sanda aka idar ko tsayawa baiyi ba ya dawo ya sake kwanciya,ba shi ya farka ba sai after 10am.Cikin shirinsa ya fito duk da kasancewar yau ya sab’a k’aidarsa ta fita morning exercise,yadda yake tafiya fuska babu wani wadataccen annuri kad’ai ya isa ya bayyanama mutanen gidan akwai damuwa a tattare da shi,ko daya fito hanyan da zai sada shi da gym d’in Daddy ya wuce,duk da shi ba ma’abocin motsa jiki a gida bane amma kan dole yau ya hak’ura ya tsaya a gidan saboda rana daya fara d’agowa,,ak’alla sai daya samu kimanin awa guda a ciki kafin ya fito jikinsa duk a jik’e da gumi,bedroom d’insa ya sake komawa ya sille jikinsa kafin ya sake shiryawa cikin k’ananan kaya ya sakko downstairs,a parlor ya iske Mamma tana yiwa BADRA tsifar kai,saman kujeran dake opposite da wanda suke kai ya zauna fuska a d’aure kamar wanda wani cikin su Mamma’n yayi masa laifi ya furta
“Morning Mah..!”
Ya fad’a can k’asan mak’oshi,ba tare data d’ago ba ta amsa da
“Ka tashi lafiya..!?”
“Am cool.!”
Daga haka dukansu suka yi shiru,while yana jingina bayansa a jikin seat na armchair daya zauna kai had’e da lumshe idanunsa,d’agowa Mamma tayi jin yadda yayi shiru ta bishi da kallo kafin tayi magana
“Dear kaji sak’on Daddy..!?”
A hankali ya d’ago kansa yana kallonta kafin ya girgiza kai cikin sark’ewar baki da fad’in
“Mah.! Ya bada sak’o ne..!?”
“Ehh! Ya cene idan ka fito ka same shi za kuji magana..Nayi tunanin ko har kunyi maganar ma da shi.”
“A’a bamu had’u bama,tun a masjeed dai da muka gaisa,,buh barin je naji..”
Ko daya bar gurin a balcony ya riski Daddy zaune saman d’aya daga cikin kujerun gurin,bakinsa d’auke da sallama ya k’arasa kusa da shi yana rage tsayinsa,magazine d’in hannunsa ya sauke yana amsawa while fuskarsa cike da fara’a suka sake gaisawa,kafin yayi magana cikin sigar zolaya
“Son.! Ba dai sai yanzun ka tashi ba.!?”
D’an murmushi Hammad yayi da fad’in
“A’a Daddy yanzun dai na fito,sai kuma na ji Mamma tace kana nema na..”
“Ehh! Haka ne,nemi guri ka zauna,wani albishir nake son yi maka..”
Duk da Daddy ya kira maganar da albishir hakan bai hana masa jin fad’uwa gaba ba da jin furucin Daddy,a hakan kuma yaci gaba da k’ok’arin tattara nutsuwarsa waje guda yana sauraron jin abunda Daddy’n nasa zai fad’a,a hankali ya nemi guri ya zauna,ko da ganin haka sai yasa Daddy ya ajiye magazine d’in dake hannunsa shima ya tattara hankali akan Hammad d’in coz maganar da zai fad’a masa d’in tana da matuk’ar muhimmanci a gurinsa
“Ehmm! Dama son ina son shaida maka ne,kamar yadda kaji nace zan maka albishir,idan Allah ya nufa kamar yadda kuma na riga da na yanke hukuncin kan maganar,shi ne na zab’a maka inda zaka je kayi Master’s naka..Saboda haka ina son ka fara shiri,coz daga nan zuwa ko wane lokaci tafiyan tana iya tasowa..!”
Fuskarsa a cike da tsantsar mamaki ya kalli Daddy’n nasa
“Dad..! Tafiya karatu again..I thought daddy lokacin baiyi ba da zan sake komawa karatu.. Ina buk’atar hutu fa..”
“Hutu wane iri kake buk’ata Hammad.?? Banda wanda kake yi yanzun,har wani hutu kake so daban..!? Bana son shirmen banza,karatun ne baka shiryawa yi ba,shin kana da wani uzurin da zai hanaka tafiya a lokacin da nake so..??”
Kansa ya sauke k’asa da fad’in
“No dad..! Buh dama akwai maganar da nake son yi maka ne tuni..”
Kallonsa kad’ai Daddy yayi cikin muryan serious ya furta
“Ina saurarenka ai yanzun,kana iya fad’ar duk abunda kake ra’ayi amma ka sani bana son jin wani uzuri akan magana ta,dan ba zan tab’a karb’arsa ba..”
Sake sunkuyar da kai yayi,yayin da yake jin fargaba tana kawo masa farmaki
“Kai nake sauraro,idan ka shirya yin magana dani..If not kuma kana iya tashi ka bani guri..”
Sai da yayi namijin k’ok’ari kafin ya tattaro kalmomin bakinsa,nan ya fara magana da fad’in
“Daddy dama kan maganar da kuka yi da Mamma da jimawa nake son maka tuni,,shi ne nake ganin,tunda Allah yasa na kammala first degree d’ina,me zai hana Daddy yanzun ka amince min kan batun..”
Tun daya fara magana Daddy yake binsa da wani irin kallo har ya dasa aya
“Wane magana ne wannan kake magana akansa..??”
Daddy ya tambaye shi,sai da yayi jim kafin ya iya cewa
“Amm! Dad dama batun yarinyar nan ne nake nufi..”
“Aure kake son yi da wuri haka..!?”
Shiru yayi duk da yaji abunda Daddy’n ya fad’a,sake maimaita masa Daddy yayi cikin d’agawar sauti buh still ya kasa amsawa,jinjina kai Daddy’nsa yayi kafin ya furta
“Ka san Allah Hammad har a wannan lokacin ban shirya yi maka aure ba,ka san dalili..?? Saboda har yanzun kai yaro ne,idan kuma har kaga na amince maka kayi aure,to ka tabbata ka tsaya da k’afafunka,,amma matuk’ar kaga hakan bai kasance ba to kace bana raye ko kuma bani nayi maka ba..”
“Buh Daddy.. Ya kamata ne ace ko magana ne kuyi da iyayenta,gidansu su san cewa da gaske nake..!”
“Hammad..! Ka rufe min bakinka a nan,ni zaka fad’awa ya kamata..?? Na riga na gama yanke hukunci,saboda haka maza ka tashi ka bani guri,aurebne banga daman yi maka shi ba har a yanzun,idan kuma da wanda zaka fad’awa ne kaje duk gurin wanda kake tunani zai sani nayi maka..”
Jikinsa a matuk’ar sanyaye ya mik’e ya bar wajen,zuwa yanzun kam ya gama yanke tsammani da lamarin Daddy’n nasa,yasan tunda ya kafe abune mai wahala ace ya amince masa,ko daya baro gurin kai tsaye ya fice daga gidan gudun kada kada wani abu ya sake tasowa ko Mamma idan ta fahimci halin da yake ciki,yasan tana iya shiga damuwa akan batun,shi kuma abune da bazai so ba ace a dalilinsa iyayensa suna yawan samun sab’ani..
Kwanaki biyu tsakanin maganarsu da Daddy amma duk ya fice a hayyacinsa,duk inda yake tunanin zai samu mafita ya nema amma ya rasa,fita daga gidan idan har ba ya zamar masa dole ba cikin kwanakin duk ya daina,ko wane lokaci yana d’aki sai dai ya kulle kansa yayi ta tunani,,yauma d’in yana kwance saman armchair a parlor saboda zaman kad’aici daya fara damunsa yasa shi kan dole fitowa,dai² lokacin kuwa sai ga Daddy ya shigo gidan,a hankali ya d’ago ya masa barka da dawowa,yana harhad’e fuska yana komai ya amsa masa sannan ya nufi hanyan staircase,har ya fara haurawa ya dakata yana kiran Hanmad,yana daga kwancen ya jiyo Daddy na kiransa,da saurinsa ya mik’e yana amsawa,juyawa daddy yayi yana fad’in
“Ka same ni a bedroom yanzun nan..!”
“Toh Daddy..”
Amsa yana mik’ewa tsaye yabi bayansa,lokaci guda suka shiga bedroom d’in Daddy a gaba while Hammad na bayansa,sai daya zare cap dake kansa sannan ya kallo shi yana fad’in
“Na san dai babu wani shiri na musamman da zaka yi ko..?? Tunda har yanzun baka yi magana ba..”
Ya tambaye shi,kansa dake k’asa ya d’ago yana son tambayan Daddy wane irin shiri yake magana,sai dai ko kafin ya kai ga hakan,tuni har Daddy’n ya furta
“Ina nufin game da tafiyanka *FLORIDA,,* shin da akwai wani abun da za kayi..??”
Wani irin yahun tsoro ya had’iye kafin ya furta
“No Daddy..”
“Ok..! Tunda babu sai ka fara had’a kayanka,coz ina tunanin zuwa gobe zaka bar k’asar…Saboda haka ga sak’on ka nan ajiye ka d’auka za muyi magana zuwa da safe idan Allah ya kaimu..”
Cikin wani irin firgici ya d’ago kansa da zummar yin magana wa Daddy,amma me sai gani yayi Daddy ya wuce ya barshi nan tsaye shi d’aya…..
Kamar wanda aka sassak’a haka ya k’ame a gurin,zuciyarsa banda daka akan hukuncin Daddy babu abunda yake yi
“Shin Daddy yana nufin da gaske ban isa aure bane har yanzun,ko kuwa shi ne dai yake son tauye ni ta wannan gefen..?”
Ya tambayi kansa a dai² lokacin,kai yayi saurin girgizawa yayin da wata zuciyar take bashi amsa da
“Inaaa!! Ko kad’an ba haka bane,,kawai dai Daddy yafi son ganinka a damuwa ne,shi yasa ya yanke maka wannan hukunci,ba don komai ba sai don yasan kai d’in mai biyayya ne akan duk wani hukuncin da zai zartar,amma batun ace baka isa aure ba ai bai taso ba,shin nawa ne wad’anda basu kaika shekaru ba suke yin auren,ko iyayensu suyi musu..? Kawai dai ta iya yiwuwa Daddy yana da wata manufa ne na daban,shi yasa yak’i aminta da maganar ka..!”
Girgiza kai yayi saurin yi cikin yin na’am da batun na zuciyansa,ko tantama baya yi haka wannan maganar take,tabbas sai dai idan Daddy yana da wani k’uduri na daban shi yasa yak’i aminta da maganar,tun lokacin da Daddy ya juya ya barshi tsaye a gurin tunanin da yayi ta fama da shi kenan har na tsayin wasu mintuna kafin ya d’aga k’afafunsa da kyar ya bar wajen,banda gumin tashin hankali babu abunda yake fita a jikinsa,a haka ya nufo bedroom d’insa,yana shiga ya zauna a k’asa dirshen dafe da chicks d’insa da duka hannayensa biyu,kafin yayiwa duniyar tunani kutse,yayin ne kuma sabuwar damuwa tayi masa sallama zuciyarsa cike da wani irin pain wanda tun da yazo duniyar baya tunanin akwai lokaci daya tab’a shiga tashin hankali kwatankwacinsa,idanunsa sun canja launi,haka fatar bakinsa gaba d’ayanta zuwa lokacin ta gama bushewa,da taimakon ubangiji a lokacin ya fara k’ok’arin kamo kalmomin
“Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un.. Allahumma ajirniy fiiy musibatin wa’aklufniiy khairan minha..Laa’ilaha illa anta subhanaka inniiy kuntu minaz’zalumiiyn..”
Yajima yana maimaitawa har bai san adadin sau nawa ya karanta ba tsabar tashin hankalin da yake jinsa a ciki,a daddafe ya k’ok’arta ya mik’e ya nufi toilet,alwala ya d’auro bayan daya dawo ya shimfid’a pray mat sannan ya shiga jero nafilfili na neman sauk’i daga gurin rabba,shi kansa a wannan lokacin da ace za’a tambaye shi raka’o’in da yayi ba lallai ne ace ya iya tantance adadin suba,abunda kawai zai iya fad’a shine ya san yayi nafila ta neman sauk’i daga gurin ubangijin talikai,amma bai san ko raka’a nawa bane yayi,a wannan daren kwata² Hammad bai samu damar runtsawa ba,yadda yaga rana haka darenma ya zo masa ya wuce,da asubah kuwa tun kafin mutanen gidan su fara fitowa a d’akunansu tuni har ya fice a gidan ya nufi masallaci,lokacin ko da aka idar da sallah k’in shigowa gidan yayi har around 7:00am,a lokacin ne kuma ya nufo gidan,yana shigowa suka had’u da Daddy shima a lokacin yana nufar gym,tun kafin ya motsa a gurin da niyyar komawa tuni har Daddy ya ganshi,a niyyarsa lokacin shi ne ya koma baya,sai akayi rashin sa’a tun shigowarsa daddyn ya riga ya ganshi,kan dole a ba yadda zai yi ya k’araso ciki yana fad’in
“Morning Dad..!”+
“Morning son..Ka tashi lafiya..??”
K’asa² ya amsa da
“Alhamdulillah..!”
“Ina fatan ka fara parking kayanka,duk dama dai jirgin dare ne zaku bi..?”
“No Daddy,,buh yanzun zanyi idan na shiga..”
“Yayi to..Sai ka hanzarta ba sai lokaci yayi sannan kace zaka had’a abunda kake buk’ata ba,kasan dai jirgi ba zaiyi jiranka ba ko..??”
Shiru yayi yana sunkuyar da kai k’asa,deeply a lokacin ji yake inama ace yana da k’warin guiwa da babu abunda zai hana bai cewa da Daddy a fasa tafiyar ba yanzun ba sai ya gama shirinsa zuwa gaba,buh saboda yasan bai isa yayi masa musu ba yasa sai ya amsa masa da “Toh” yana sake sunkuyar da kai cike da biyayya,Daddy ne ya fara barin gurin kafin shima ya wuce zuwa bedroom d’insa da niyyar had’a duk wasu muhimman kayan da yasan zai amfani da su,a gaban closet d’insa ya tsaya bayan ya janye murfin gefe ya tsaya rik’e da waist looking to his outfits yana nazari kamar wanda bai san abunda ya tsaiwa shi a gurin ba,tun daya tsaya a gurin gaba d’aya sai ya rasa abunda zai fara d’aukowa saboda duka shi ba abunda yake ransa ba kenan,ya shafe ak’alla sama da mintuna goma sha biyar yana k’arewa siturun nasa kallo kafin ya fara zaro su d’aya bayan d’aya yana ajiyewa saman resting chair,sai daya cire ak’alla sama da 30 set sannan ya dakata yana sake rik’e waist da tunani fal zuciyarsa na abunda ya dace yayi kafin lokacin tafiyarsa yayi,kamar wanda aka tsirawa wani abu sai kawai ya juya cikin saurin yana barin gurin,bathroom ya nufa cikin gaggawa yana sakin ajiyar zuciya dan a lokacin gani yake zai iya kamo bakin zaren,,ba tare daya b’ata lokaci ba yayi wanka yana fitowa ya hau shiri cikin sauri²,within a few minutes sai gashi ya fito cikin shiri tamkar ba shi ne wannan da damuwa yayiwa yawa ba,har wani shining da sparkling ke fita a fuskarsa mai d’aukar idanu,cikin sauri² ya sake tattara phones,car keys d’insa da envelope da Daddy ya bashi a daren jiya yayi waje,bai zame ko ina ba bayan fitowarsa sai wudil dan yadda yake jin zuciyarsa na azalzalarsa a lokacin idan har baiyi abunda take sak’a masa ba tabbas za’a iya samun gagarumar matsala.
Lokacin daya shigo cikin k’auyen ko daya isa cikin gidan,a nan ne kuma sak’on tafiyar da su baffa suka yi ya riske shi,inda aka sanar da shi sunje d’aurin aure can a wani k’auye da ake kira *INDABO* sannan ba lallai ne su dawo da wuri ba,gaba d’aya guiwoyinsa ne suka sanyaya lokacin da labarin ya iso shi,yayin da damuwa ta sake lullub’e shi bcos a lokacin gani yake daga wannan lokacin ba lallai ne ya sake samun wani chance ba,haka nan zuciyarsa sai shaida masa take shi kenan idan bai samu damar ganin baffa ba a wannan lokacin ba yayi loosing duk wani hope,,wannan shi ake kira samu da rashi,,ya taho da tunanin da zaran yazo ga baffa komai zai zai zo masa da sauk’i sai gashi ya iske baffan baya garin,shin har tsawon wane lokaci ne zasu d’auka kafin su dawo..?? Ya tambayi kansa,yana ganin shi da a yau jirginsu zai bar k’asar,gashi ko kayanma bai had’a ba ya fito daga gidan,saboda kasa samun nutsuwar zuciya da yayi sai kuma ya riski wannan abu,sake kallon agogon dake d’aure a tsintsiyar hannunsa yayi a karo na sau babu adadi,a yinin ranar gaba d’aya gani yake lokacin kamar wanda ake zuk’ewa da wani abu dan yadda yake fella gudu,dai² yana sauke hannunsa a k’asa ta shigo d’akin da sallama kanta a k’asa,tunda ya d’ago ya sauke idanunsa akanta ya kasa janyesu har sai data ajiye tray d’in dake hannunta,d’an nesa kad’an ta zauna har lokacin bata d’ago ba ta gaishe shi,sai daya saki ajiyar zuciya kafin ya iya amsa mata yana ci gaba da kallonta,dan yadda yake ji a zuciyarsa game da ita ji yake a lokacin tamkar ya had’iyeta ko zai samu sassaucin abunda yake ji d’in game da ita,,,duka sunyi shiru tun zamansu,yayin da kowanne da tunanin da yake a k’asan ransa,hiran ma da suka saba duka a yau sun gagara yinta sai kallon kallo da suke,ga Hammad kuwa a wannan lokacin rashin samun nutsuwa yasa shi kasa magana gashi har lokacin baiga baffa ba bare ya warware masa damuwarsa,shi yasa duk wasu kalmomin da yake tunanin yana da su suka tsere,ita kuwa Sabina ba komai ya hana mata yin magana ba sai tsabar kunyarsa da take ji,musamman daya kasance idanunsa suna kanta.
5:00pm agogon hannunsa ya nuna masa,zuwa wannan lokacin tuni ya gama fidda rai da samun damar ganin Baffa,dan haka kawai sai ya yankewa kansa hukuncin komawa inda ya fito yayin da yake jin babu dad’i a k’asan zuciyarsa,kallonta yayi ba tare daya samu damar fad’an komai ba ya mik’e,sai daya dai²ta tsaiwarsa sannan da kyar yayi k’ok’arin tattara kalmomin da suka masa saura a bakinsa ya furta
“My Lady..! Zan koma,,amma ina so idan baffa ya dawo,ki sanar da shi na zo muyi sallama ban same shi ba..Tafiyar gaggawa ta tasomin yau da dare zamu tafi idan Allah ya kaimu..”
Muguwar fad’uwa gabanta yayi lokacin da taji abunda yake fad’a,cikin sauri ta d’ago kanta ta zuba masa manyan idanunta,so take tayi magana amma ta kasa furta komai sai girgiza kai kawai data samu damar yi
“My Lady..!”
Ya kirata cikin wani sanyayyar murya,kasa amsawa tayi saboda wasu masifaffun hawaye da suka kunno mata kai,bai damu da rashin amsawar da tayi ba ya ci gaba da magana while yana tunkaro inda take tsayen
“My Lady.. Ina neman alfarma a gurinki..Ina fatan zan samu hakan daga gare ki..!”
Girgiza masa kai tayi sai dai tak’i yarda ta kalleshi haka tak’i yarda tayi magana dan tasan tana bud’e baki kuka ne zai fara fitowa,,murmushin k’arfin hali ya saki dai² lokacin daya tsaya nearer to her
“Da gaske kina so na..?? Kuma zaki iya aurena..??”
Maganar ta fito daga bakinsa,kai tayi saurin sake girgizawa tana murmusawa duk da tana jin damuwa,d’an murmushi jin dad’i shima ya saki sannan ya sake fad’in
“Zaki iya rik’e min amanar kanki..??”
Nanma ta kuma girgiza masa kai
“Shin zaki iya jiran dawowa na ko da zan kai tsayin shekaru ban dawo ba..??”
Wannan karon sai data d’ago ta kalleshi wanda yin hakan ya taimakawa hawayen da take b’oyewa damar sakkowa saman fuskarta sai dai tayi saurin k’unshe bakinta gudun kada sautin kukanta ya bayyana,tasan da zaran an jiyota jama’ar gidan suyi zaton ko wani abu yayi mata,sai ta sake girgiza masa kai,kai shima ya shiga girgiza mata alamun kada tayi kuka amma ina tuni hawaye sun gama wanke mata fuska
“Don’t cry my lady..Kina son ki karya min zuciya ne.? Kukanki a irin wannan lokacin dai² yake da yasa ni fasa tafiya,duk da umarni ne na mahaifina,,Kiyi hak’uri ki daina min asarar hawayen ki, in sha Allah kamar yanzun zanje na dawo gare ki,,I promised..!”
Tana sheshshek’ar kuka take fad’in
“Har tsayin wane lokaci ne zaka tafi ka barni..??”
“Bana tunanin zan wuce shekara guda..!”
Shiru tayi bata sake cewa komai ba sai hawaye da take sharcewa a zuciyarta kuwa fad’i take
“Shekara guda..Kenan zai d’auke mu tsayin lokaci ba tare da mun had’u da juna ba..?? Waya sanima ko shi kenan ba zamu sake had’uwa ba..!”
“Am really sorry my Lady,,haka k’addarar mu yake,dole ne ko muna so ko bama so sai hakan ya kasance,buh idan muka yi addu’ah komai zai zo har wata rana ya wuce..Amma dan Allah ina so kada ki manta da cewar wata rana zan dawo gare ki kamar yanzun..!”
Zuwa yanzun kam tuni kuka yaci k’arfinta,durk’usawa tayi a k’asa taci gaba da kuka sai dai babu sauti a cikinsa sai zallar hawayen da yake zirara daga idanunta,saboda toshe bakinta da tayi,shi kansa Hammad kasa jurewa tsayawa yayi nan ya durk’usa a gabanta yana girgiza mata kai nd yana jin kamar ya rik’o ta zuwa jikinsa ya rarrasheta
“Please my lady..ya kamata kiyi shiru haka nan,kada ki sawa kanki damuwa,,ko kina son wani ciwon ya shige ki..?”
Saurin girgiza masa kai tayi
“Ok..! To ya isa haka,idan ba so kike ki karyamin zuciya nima nayi kuka ba..Shin kina son ganin hawaye na..??”
Sai ta girgiza masa a hankali cike da sakarci
“Ok..ya isa to kinji..ki bar kuka.”
Hannu tasa ta fara sharce hawayen tana sakin ajiyar zuciya,zuwa lokacin idanunta har sun fara rikid’ewa,Hammad kuwa ganin yadda take sauke ajiyar zuciya akai² da yadda damuwa ya lullub’e fuskarta sai yasa shi kasa cewa zai tafi duk da lokaci ya tafi sosai,a haka yayi ta fad’a mata kalmomin da yasan zasu taimaka mata wajen samun nutsuwa,,sai daya tabbatar ta samu nutsuwa kafin da kyar suka hak’ura suka sake yin sallama,ba dan taso ba sai dan ya nuna baya son ganin kukanta yasa wannan karon tayi ta had’iye kukan,tafiya suke kamar marasa laka a jika har suka fito zauren gidan,suna daf da fitowa kwatsam sai ga su baffa sun sawo kai cikin zauren,lokaci guda wani gagarumin farin ciki ya ziyarce shi har bai san lokacin daya furta
“Alhamdulillahillaziiy bii ni’imatihi tatimmus’salihaat..!”
A fili yana mai sakin k’ayataccen murmushi,ita kanta Sabina ganin murmushin dake fuskarsa sai daya bata nutsuwa,,cikin tsananin farin ciki da dawowarsu tun bai kai ga tafiya ba ya shiga yiwa musu barka da dawowa,da fara’a a fuskar dattijan uku suka amsa masa ma’ana baffa,baban SABINA sai kuma baban LADO,bayan sun gaisa da su baffa yake fad’in
“Mai babban suna..! Yau kuma sai kazo ka iske bama nan ko..!?”
Murmushin k’arfin hali yayi sannan ya amsa
“Wollahi kuwa baffa,ai har na fidda rai zamu had’u,sai kuma kuka dawo..”
“Allah sarki..Wollahi fa da yake munje INDABO d’aurin auren y’ar aminina ne,to kasan harkar jama’a shi yasa bamu samu tahowa da wuri ba sai yanzun..”
Sun sake gaisawa,sannan sun d’an tab’a hira a hakan,kafin su baffan suka bishi da fatan alkhairi tunda sunga ya fito yana shirin tafiya,sun san dai zai yi wahala ace ya tsaya,,amsawa yayi kansa a k’asa,zuwa can kuma har su baffa suna niyyar wucewa cikin gida Hammad yayi ta maza da cewa
“Baffa..Dama na zo ne muyi magana,sannan nayi muku sallama,sai kuma na iske bakwa garin…”
Dakatawa baffa yayi da tafiya sannan ya kalle shi yana fad’in
“Eyyaahh..! To ko zamu bari zuwa wani lokaci,tunda yanzun lokaci ya k’ure ko..??”
A hankali ya sosa k’eya dan yasan baffan bai fahimci abunda yake nufi ba sannan yace
“Baffa idan babu damuwa yanzun muyi maganar,saboda idan na tafi babu lallai na sake dawowa kwana kusa..Dan ina akwai tafiya a gabana yau da dare..”
Murmushi baffan yayi sannan ya bashi izinin su shiga daga ciki idan magannar tana da tsayi daga nan suka wuce yayin da shi da Sabina suma suka bi bayansu,suna shiga ta wuce tayi ciki ta barshi nan ya k’arasa d’akin da baffan ya shiga,sun sake gaisawa bayan nan shiru ya biyo baya har na wani lokaci kafin baffa ya magantu
“Mai babban suna.. Shin wane magana ne kake son sanar dani ne..??”
Sai daya gyara zama sannan ya d’ago kansa dake sunkuye a k’asa yayi d’an murmushi nan ya fara zayyanawa baffa duk abunda ke faruwa da tafiyar da zaiyi a yau d’in,tabbas ba don kasancewar baffa mutum mai ilimi ba gami da kaifin basira da har ya iya gano damuwar dake kwance saman fuskar Hammad sannan ya gano adadin k’aunar dake tsakaninsa da Sabina tabbas da sai yace dama can k’arya yake yi,nd yazo ne kawai da niyyar yaudararsu,sai da yayi jimm na tsayin lokaci yana tunani kafin ya jinjina kai ya fara magana
“Tabbas wannan magana taka,wani AL’AMARI ne wanda Allah (S.W.T) ya hukunta faruwarsa,wanda dabararmu ko k’arfinmu bai isa ya hana afkuwarsa ba,hak’ik’a Ubangiji shi kad’ai ya barwa kansa sanin dalilin da yasa wad’annan al’amura suke faruwa,dan haka bamu da bakin yin wata magana ko yanke hukunci har sai mun jira ganin ikonsa akanmu,dan gaka sai muci gaba da addu’ah Allah yasa hakan ya zame mana alkhairi mu da ku baki d’aya,,,batun tafiya kuma da zaka yi,in sha Allah zamu yi ta maka addu’ah har Allah ya dawo da kai lafiya,ALK’AWARI ne mun riga mun d’auka dan haka kada kayi tunanin faruwar wannan lamari zai sa mu karya ALK’AWARIN mu gare ka..Muna yi maka fatan alkhairi da fatan Ubangiji ya bada sa’a kan abunda akaje nema..”
Duk da yaji matuk’ar dad’i da furucin baffa,sai dai a gare shi a kuma nasa hasashen sam ba haka yake muradin yaji ba,a nasa ra’ayin da kuma son ransa yaso ne kawai ace baffa yace idan har da gaske yake sonta to kawai zai d’aura musu aure,idan yaso bayan dawowarsu sai su san yadda za suyi da lamarin Daddy,amma sai yaji ya tsaya iya kan maganar har yanzun suna nan akan batun zasu jira dawowarsa,duk da bawai ya raina hakan bane yaso ace kawai baffa ya yanke hukuncin aura masa ita daga nan sai ya tafi da abarsa zuwa sanda zasu dawo,yasan Daddy’nsa zai sauka ya kuma karb’i batun tunda yana sa rai zuwa lokacin ma tuni har da rabo zasu dawo masa.
D’agowa yayi saurin yi ya kalli baffa,zuciyarsa da taraddadin abunda zaice idan har yaji maganar da zai fad’a yanzun,daurewa yayi a hakan bayan ya sake sunkuyar da kansa k’asa sannan ya furta
“Amma baffa..! Shin babu yadda za’ayi ku aura min ita.!?”
Shiru baffa yayi yana kallon Hammad har ya dasa aya kafin ya murmusa da fad’in
“Haba mai babban suna.. Ta ina ka tab’a ji anyi irin wannan auren babu sa albarkar iyaye,,sannan kasan matakan aure da abubuwan da suke hallata shi,dole ne idan za’ayi aure sai da waliyyai,sadaki sannan shaidu,to mu da babu ko d’aya daga ciki a tare damu sai muce zamu yanke hukunci..?? Ina ganin ya kamata ace muyi hak’urin har zuwa lokacin da Allah zai dawo da kai,in sha Allah zuwa lokacin komai ya daidaita..”
Sam ba haka Hammad yake son ji daga bakin baffa ba,dan shifa har ga Allah idan har da ace a yanzun zai ce ya amince masa to a shirya yake ya nemo komai da baffan ya ambata,dan haka kai tsaye sai ya sake fad’in
“Baffa ina ganin wannan duka ba abun damuwa bane ba,zamu iya samunsu a duk lokacin da muka buk’ata,fatana shi ne amincewarka,nayi maka ALK’AWARIN ni da kaina zan nemo sauran a duk inda ya dace..”
Murmushi baffa ya sake yi masa kafin ya ce……
*Kyal Kyal.. Lallai Hammad ka deb’o da zafi aradu.. Aaa! Abu yayi soyayya ta k’arfafa,,irin wannan yanke hukunci haka da gaggawa…To dai fan’s kunji hukuncin da Mutumin ya yankewa kansa,,amma kuna ganin baffa zai amince ya aura masa ita kamar yadda yake muradi..?? Shin yaya matsayin hakan zai kasance ga Daddy’n Hammad idan har hakan ta faru,anya kuna ganin zai amince ya karb’i auren nasu a nan gaba..??*