ALKAWARIN JINI CHAPTER 7 BY _HAWWA MUH’D USMAN
Www.bankinhausanovels.com.ng
Yana zaune saman bed yayin da bayansa ke jingine a jikin pillow saboda gajiyar da yayi da kwanciya,Sultan ya shigo da sallama,d’aga kansa yayi ya bishi da kallo har ya k’araso kusa da shi ba tare daya samu damar bud’e baki yayi masa magana ba,sai dai ya amsa sallamar a k’asa²,,zama Sultan yayi daga gefensa ta wajen k’afafunsa yana kallon yadda cikin y’an kwanaki duk ya zama wani pale
“Dude..! Ashe ka farka..!”+
“Ummmhh!” Yace yana motsa k’afarsa kamar zai tashi,kallonsa Sultan d’in ya sake yi da hanzari yana tambaya
“Tashi za kayi ne..!?”
Wannan karon da kai ya amsa masa alamun “Ehh”,Taimaka masa Sultan yayi har ya sauka daga saman bed d’in,a hankali sai ya furta
“Thanks dude..!”
Murmushi Sultan yayi masa yana girgiza kai alamun babu komai,sannan ya juya yana tafiya a hanakli har ya isa bathroom,alwala ya d’auro bayan ya wanke bakinsa ya fito, pray mat ya shimfid’a sannan ya daidaita a kai,ya kabbara sallah,duk da bawai lokacin sallah ne yayi ba dan duka a lokacin bazai wuce 11am ba na safe,raka’a biyu yayi a daddafe masu sauk’i,sannan yayi tahiya ya sallame,ya d’auki lokaci yana addu’ah,yayin da Sultan ya zuba masa idanu kawai yana kallonsa da tsantsar tausayawa irin rayuwar da yake
ciki,,,idanunsa da hawaye kwance a cikinsu,sai dai basu samu damar saukowa ba,,ya shafe tsawon mintuna kafin ya mik’e a gurin,bayan ya maida pray mat d’in muhallinta ya koma ainihin inda ya taso,har lokacin bakinsa na motsawa alamun yana ci gaba da addu’ah hannunsa rik’e da counter,,fuskar serious Sultan yayi wearing yana kallonsa
“Dude..! Ina da magana fa..”
Ba tare daya kalleshi ba,muryansa cikin sanyin da kana ji kasan tsabar jin jikin da yake yine yasa ta koma haka
“Uhhuumm..! Kana iya fad’in duk abunda ka so..”
“A’a broah..! Ba haka nake so naji ka fad’a ba,,idan har dan zan iya fad’ar duk abunda na so ne,ai da ba saina tambayi izininka ba..”
“Kada ka damu,,kai dai ka fad’a kawai ina sauraron ka..”
“Uhhuumm” Sultan yace kafin ya sake kallonsa yana fad’in
“Barshi ma kawai..”
D’agowa yayi da idanunsa ya kalleshi kafin ya tab’e baki
“Ok..good..”
Sake kallonsa Sultan d’in yayi jin abunda ya fad’a
“Baka son ji kenan..!?”
“Tunda baka yi niyyar na sani ba,mene amfanin na takura ka fad’a..!?”
Murmushi Sultan yayi yana jinjina kai
“Kai dai kam wollahi zanga ranar da zaka chanja..”
“Baza ka tab’a ganinta ba kuwa..Idan har ita kake jiran gani,,bana tunanin zata zo..”
Surin taron numfashin sa sultan yayi da cewa
“Zata zo..Kuma zaka ce na fad’a maka..Da idanunka zaka ganta..!”
Shima Sultan d’in yayi saurin katse masa maganar,sake tab’e baki yayi while yana fad’in
“I don’t think so..”
“Ok.. Ni dai naji a jikina kuma nasan zai zo,,buh bama wannan ba,,,tun wancan ranar da muka baro Wudil naso yi maka maganar,to kuma dai yanayin da kake ciki sai yasa na kasa yi maka bayanin abunda naji tun a ranar..”
“Akan mene ne..?”
“Labarin abunda ya faru da mutanen garin mana ai shi naso sanar maka lokacin..”
Idanunsa ya zuba akan Sultan yana jiran yaji abunda zai fad’a,yadda yaga alamunsa take ya fahimci lallai akwai labari a tare da shi,sai dai baya jin zai iya fahimtarsa,a hakan kuma sai ya bada nutsuwarsa akan Sultan d’in bawai dan ya damu da son jin abunda zai fad’a masa ba,ga Sultan kuwa ko da yaga yasa nutsuwa a lamarin take ya kwashe kaf yadda suka yi da dattijon nan ya sanar da shi,,tun daya fara bashi labarin banda gumi na tsabar tashin hankali babu abunda Hammad keyi,bakinsa yana fad’in “Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un,,Laa ilaha illah anta subhanaka inniiy kuntu minaz’zalumiiyn”,har zuwa lokacin da Sultan ya rufe labarin da fad’in
“A gaskiya d’an uwa ina ganin *AL’AMARIN* soyayyarkan nan sai Allah,then muci gaba da addu’ah,,idan har Allah yasa kuna da rabon ganin juna to..Amma duk ta yadda kake zato wollahi lamarin nan naku ya wuce haka,ni kaina ban tab’a tsammanin *AL’AMARIN* ya kai nan ba..”
Idanunsa da suka fara rikid’ewa ya sauke k’asa daga kallon da yake jifan Sultan da shi na jin irin fatan da yake masa,,a k’asan zuciyarsa kuma yana ci gaba da tasbihi ga Allah da yi masa kirari akan ya jib’inci *AL’AMARINSA* idan har da rabon su ga juna a rayuwa ya had’a su da gaggawa
“Bana tunanin akwai wani da zamu samu wanda yasan inda suke rayuwa gaskiya a yanzun,tunda nayi tambaya nd nayi bincike amma har yanzun shiru bamu samu wani gamsashiyar amsa ba..”
Lumshe idanun dai ya sake yi,yana gyara kwanciyarsa yayin da yake jin zuciyarsa na masa wani iri,sam babu dad’i a yanayin da yake ciki yanzun,,kula da Sultan yayi da halin da yake neman shiga shi yasa shi yin shiru daga maganar da yake
“Dude..! Kana lafiya dai ko..??”
Idanunsa ya d’an bud’e a hankali ya kalli Sultan ba tare daya amsa ba
“Dan Allah broah..! Kada kasa damuwar wannan *AL’AMARIN* a zuciyarka,,ya kamata ace zuwa yanzun komai ya canja,ka cirewa kanka damuwa,idan fa wani abu ya sameka Mamma da mu dukanmu zamu shiga damuwa,,,idan muka maida lamuranmu gurin Ubangiji zai isar mana,amma damuwa babu abunda zai haifar sai k’aruwar ciwo.”
Murmushin takaici ya saki,ba tare daya iya cewa da shi komai ba ya sake maida idanunsa ya kulle,har Sultan ya gama fad’ar abunda zai fad’a bai sake daga ido ya kallkalle shi ba,sai daya tashi tafiya da yayi masa sallama sannan ya bud’e idanunsan suka yi sallama ya tafi.
Tunda Sultan ya saka k’afa ya fita ya barshi a gidanyake cikin damuwa a dalilin jin irin iftila’in daya cafkawa al’ummar garin wanda shi ne dalilin daya sake d’aga masa hankali,,musamman kuma da yaji ance bayan nan sama da mutum ashirin sun rasu,duk sai zuciyarsa ta kasa samun sukuni,tunanuka da dama suna sake bijiro masa,tayin da zuciyarsa ke hasko masa wasu faruwar lamarin tamkar a gaban idanunsa ne suke kan faruwar,,wayer garin ya tashi jikinsan da sauk’i sosai amma zuwa yanzun tsananin tashin hankali yana neman ya maida komai baya,ciwo yana neman dawowa sabo,da taimakon addu’o’in da yake yi Ubangiji ya taimake shi tun kafin ciwon yaci k’arfin jikinsa ya janyo drawer da magungunansa ke ciki,bai jima sosai da shan maganin ba bacci ya d’auke shi.
Kwanaki sun dad’a tafiya har lokacin Hammad yana cikin wannan mawuyacin halin,,jinyar da duka yayi ta ne a cikin y’an satittika amma idan ka ganshi sai kayi zaton ya shafe tsayin shekara a kwance,,wanda cikin wannan lokacin bisa taimakon ubangiji da yawan kai masa kuka da yake yi,baya ga addu’ar mahaifa gami data y’an uwa zuwa abokan arzik’i ya fara samun sauk’i har ya fara iya fita da kansa,sai d’an abunda ba’a rasa ba,ragowar b’urb’ushin ciwo,wannan kuma mun san dama sai a hankali sannan komai zai koma dai²,,,tun daga wannan jinyar gaba d’aya sai ya sake komawa tamkar wani hearing impaired,magana idan ba da wani na jikinsa ba shi d’inma shak’ik’i gaba d’aya ya daina yinta,kuma ko da tambayarsa kayi idsn bai so ba ko d’aga idanu bazai yi ba bare kasa ran zai kalleka ko samun damar amsa maka,,ya daina zaman hira da kowa,dariya ko murmushi duka ya daina yinsu ga kowa,yayin da ya koma tamkar wani namijin zaki,,a kowane lokaci ya gwammace ya zauna shi kad’ai yayi shiru yana tunanin,idan ya gaji kuma ya koma tuna irin moment da suka yi sharing a tsakanisu,,idan kuma yaji kewarta ya dame shi sosai haka zai d’auko head tie d’in data d’aure masa hannu yayi ta kallo yana sauke wahalallun ajiyar zuciya,,takardar da baffa ya rubutama lokaci zuwa lokaci yakan d’auko ta yayi ta kallo,idan hakan bai masa ba kuma sai ya koma karantawa,yana bin ko wane harafi dai² kamar lokacin da baffa ke karanta musu.
Yana zaune yayi zurfi cikin duniyar tunani wayansa dake ajiye gefensa tayi k’ara,a hankali ya kalleta sannan ya kauda kansa zuwa gefe,,duka idan yana cikin irin wannan mood d’in ko kad’an baya son wani abu ya shigo masa,,,dan haka nema ko daya kalla saboda baiyi niyyar d’auka ba sai ya d’auke kansa daga kallon wayar,har ta katse aka kuma kira bai yi attempting d’auka ba,tsaki yaja cikin fushi a karo na uku ya d’auka wayar ba tare daya kula da sunan dake kan wayar ba cikin fad’a² ya furta
“Bance bana son a dameni ba ne..!?”
“Sorry..! Sir..!!”
Muryan Mamma ya katse shi,saurin bud’e ido yayi yana duba screen d’in wayan,tabbas sai yanzun idanunsa suka ga abunda ke rubuce,surprisingly yace
“Mah..!?”
“Ranka ya dad’e..!”
Itama ta fad’a while tana sakin murmushi
“Am sorry Mah,, buh banyi zaton kiranki bane shi yasa..! Amma kiyi hak’uri..”
“I knew..! Ai yallab’ai..”
Katse kiran yayi saurin yi,yana sauke ajiyar zuciya had’e da matse forehead d’insa dan duka baiyi tsammanin Mammansa ce take kira ba tun farko da ko kad’an bai yi abunda yayi ba,tashi yayi ya fita da sauri dan yasan da kamar wuya ace ba nemansa take yi ba tunda ta kira shi,ta bedroom d’inta ya fara dubawa bcos yasan a irin wannan lokacin bazata wuce can ba,a nan d’in kuwa ya isketa lokacin daya bud’e k’ofa,tana zaune saman pray mat,k’arasawa yayi ciki ya zauna yana jira ta idar da addu’ar daya isketa tana yi,,itama Mamma ko da taga ya shigowa nan da nan sai ta tak’aita,bayan ta idar ta juyo tana kallonsa fuskarta babu yabo bare fallasa,sannan ta fara masa magana cikin muryan lallami
“Son..! Dama gani nayi tunda Allah yasa yanzun kaji sauk’i,, shine nake so muyi wata magana da kai..”
Sunkuyar da kai yayi k’asa a hankali kuma ya amsa mata da
“Toh Mah..!”
“Ina fatan ka san akan abunda zanyi maganar..!?”
Ta tambaye shi al’halin tana mai tsare shi da idanuwanta,sai daya girgiza kai kafin ya amsa da
“A’a Mah..”
“Ok.. Da kyau toh..”
Saurin kallonta yayi cikin sark’ewar baki yana fad’in
“Buh Mah.. Why baza ki sanar da niba,,da gaske nake ban san akan mene ne zaki yi magana ba. I swear..”
Idanu ta lumshe masa alamun shi kenan nd ya kwantar da hankali,,shiru yayi yana kallonta da had’iye yahu,ita kuma Mamma taci gaba da magana
“Na san baka sani ba,,nd duka abunda nake magana akansa ba wani abu bane face akan rashin tafiyarka,,dan ni dai har yau ina zaune ne cikin duhu,ba tare dana san takamaiman dalilin faruwar al’amarin ba,sannan ku duka babu wanda yayi k’ok’arin sanar dani daga kai har shi Sultan d’in da na ganku tare,,na tambaye shi kuma ya nuna min shima bai sani ba,to abunda dai ban sani ba shi ne mene ne abunda kuke ta b’oyewar tsayin wannan lokacin..??”
“Mah..! Bafa wani abune,,kawaifa dama damuwa ce ta haifar da ciwon..Amma bayan nan babu komai..”
Tsare shi ta sake yi da idanunta tana jifanshi da kallon ban yarda ba kafin ta magantu
“Ni wai kake fad’awa wannan shirmen..?? Nd kana so na yarda ko..!?”
Marairaicewa yayi yana fad’in
“Da gaske Mammana babu komaifa,,ki yarda dani..Kin san ban saba yi miki k’arya ba..”
Yadda yayi da fuskarsa nd tasan har yanzun yana kan matakin shan magani,yasa sai kawai ta jinjina masa kai badon ta amince ba,sai don kawai tana tsoron abunda takurashi ya fad’a mata gaskiya zai haifar,,bayan ta gama kallonsa tace yaje ta sallame shi,a sad’ad’e ya tashi ya bar d’akin dan tuni ya gama karanto rashin yarda afuskarta,bayan yayi mata sallama yayi saurin ficewa a d’akin danma kada tace ya dawo,a hankali Mamma ta girgiza kai bayan taga fitarsa tausayinsa fal zuciyarta.
Washe gari tun da safe kiran wayar Daddy ya shigowa Mamma,bayan ta d’auka sun gaisa,ya tambayeta yaransu da gida,itama ta tambayi aiki,sun gama gaishe² Daddy yake sanar da ita labarin skul d’in da su Hammad suka yi *UNIVERSITY OF NORTH FLORIDA* tana neman mutum goma daga cikinsu,nd gudun ma kada a samu sab’ani wasu daban da basu ake buk’ata ba suje,yasa suka yi specifying sunayen wad’anda suke buk’atar,,Mamma dai kam ko da taga bata fahimci inda maganar Daddy ta nufa ba tayi caraf ba tare da tayi k’waron baki ba ta tambaya
“To amma Daddy,, mu mene ne had’in mu da wannan labarin..!?”
“Haba Asiya..! Yanzun duk baki fahimci komai ba daga cikin maganar da nayi..!?”
“Wollahi alhaji ni kam dai ban fuskanta ba..”
Takaitaccen murmushi yayi mata
“Ai matsalar da aka samu dama tun farko baki tsaida hankalinki kan yadda za’ayi ki gane ba,al’halin kuma ko a cikin magabata na fad’a miki mak’asudin kiran..”
“Me kace to..!? Ina tunanin ban jiba kam gaskiya..”
Sai daya sake murmusawa kafin cikin zolaya ya furta
“Idan na maimaita mene ne tukuici na..!?”
Murmushin itama tayi tana fad’in
“Ka fad’a tukuna,,idan dan tukuici ne ai sai ka zab’a..!”
“Sure.!?”
“Ehh! Da gaske..”
Still ya sake yin murmushi sannan yace
“Toh shi kenan,,ki duba wayarki zaki ga amsar tambayar ki a ciki..”
“Haba Daddy..! Maimakon ka fad’a min da bakinka shi ne sai an bani aiki..!?”
“Ba aiki bane,,ki duba d’in dai da kanki ina ganin zaifi miki sauk’i ma..”
“Toh..! Shi kenan,bari na duba d’in, tunda so ake dai a wahalar da Shari’a..”
Dariya Daddy yayi mai sauti yana fad’in
“Wace shari’ar..??”
Sai bayan Daddy ya maimaita sannan Mamma ta fahimci abunda yake nufi,dariyar itama ta sake yi kafin ta rufe maganar da fad’in
“Irin wacce yallab’ai yake yi..”
Tana fad’in haka tayi saurin katse wayan tana darawa,shima Daddy a b’angaren sa ko da yaji ta katse kiran dariyar yayi a fili kuma yana fad’in
“Asiya kenan,,Shari’a irin wacce muke yi,ai ba dai² take da sauran shari’ar da kike ji a labari ba..”
Can a gefen Mamma kuwa,lokacin data katse kiran email d’inta ta shiga dan ta duba sak’on da Daddyn yace zata gani,da short video tayi arba wanda daga dukkan alamu kuma kana gani kasan a tsakiyar abu ne akayi cutting d’insa,murmushi tayi kafin tayi playing nasa,,,tsaf ta gama kallon videon yayin da fuskarta ke bayyanar da wani irin sihirtaccen murmushi.Ko bayan data gama dubawa ms ita ta fara neman Daddy suka yi magana akan lamarin,a nan tsakaninsu suka gama tattauna duk yadda tafiyar Hammad zata kasance,kafin suka yi sallama yana sake tabbatar mata da lallai ne nan da zuwa dare zasu sake yin magana bayan ya tuntub’i Hammad d’in,daga nan duka suka ajiye wayar.
A wannan daren saboda maganar da Mamma ta yiwa Hammad akan abunda yake damunsa kuwa tun daya fita gaba d’aya sai ya kashe wayoyinsa,dan haka ko da Daddy ya kira shi yaji a kashe sai ya sake kiran Mamma’n yana mata complain na jin wayoyin Hammad da yayi a rufe,hak’uri ta bashi dan itanma a lokacin bata san dalilin aikata hakan ba,,wanda a b’angarensa shi kuma gogan,wasa² tun daga ranar da tayi masa tambayar dalilin kwanciyarsa rashin lafiya ya koma wasan b’uya da ita kamar wasu surukai,duk inda yasan zai ganta baya tab’a bari yaje bare su had’u,yayin da a gefe guda kuma wayoyinsa suke kashe babu ta yadda za’ayi tayi saurin binciko shi,tun tana kiran cikin kwanciyar hankali har lamarin ya fara bata tsoro²,tayi kiran tayi jiran ganinsa amma duka bata sauya zani ba,a hakan kuma har lamarin ya fara neman fin k’arfinta,dan haka ko da taga zata jefa kanta a damuwa sai ta hak’ura ta fawwala lamatin wa ubangiji,duk da zuwa lokacin da abun ya fara damunta sai ta k’udurce tarfa shi a dai² lokacin da bai zato ba.A ranar kuwa tayi sa’a dan gaba d’aya ma baya gidan,dan haka bayan data bincike d’akinsa bata same shiba,ta koma parlor cikin shirin zaman jiran shigowarsa.
A bangaren Hammad kuwa dai² wanman lokaci da Mamma ta kafa tarkon son ganinsa,suna kan hanya suma d’in a tsakiyar traffic,,yayin da Sultan d’in ke driving kan hanyarsu ta dawowa daga *Y’AN KABA,,* k’addararsa ta kira shi,yayin da tasa su biyowa ta hanyar *MAIDUGURI ROAD.*
Dai² lokacin suna tsaye tsakiyar traffic,,tsabar tsokana irin ta Sultan dake driving a hankali sai ya juya bayan ya d’an kalle shi fuskar da murmushin zolaya kwance samanta,sai dai baiyi magana ba,,a lokacin kuma ba komai ya ja shi ba illa ganin da yayi,Hammad yayi shiru kamar baya cikin motar,,juyawa Hammad yayi daga kallon ginin gidan *INDOMIE* da yake na dai² kwanar maggi,wacce itace idan mutum yabi ta d’od’ar zata sada shi har cikin *UNGUWAR KAWO,,,* wani mahaukacin kallo ya watsa masa a dalilin dariyar da yake yi,wacce ta dad’a assasa jin tsaiwar da suke yi,,dama kuma gaahi tun bayan daya tashi daga jinya abu kad’an yanzun sai yasa yaji haushinka,,,sai daya ja tsaki fuskarsa a had’e babu alamun fara’a,har ya bud’e baki da niyyar tambayarsa abunda ya gani na dariya ,dan shi gaba d’aya haushinsa d’aya yaji ana dariya a kusa da shi baya ga takaicin mak’alewar da sukayi a traffic d’in daya dame shi,abu goma da ashirin sun had’ar masa,d’aga idanunsa daya zuba Sultan yayi cike da son shafe fushin da yake yi na ganin shima Sultan d’in ya had’iye dariyar,idanunsa suka masa bazata can daga d’ayan hannun nasu..Fuskarta ya hango zaune ita kad’ai sanye da uniform farin hijab nd light blue d’in riga da wando a cikin keke napep,banda murmishi abunda take ta zabga abunta alamun dake bayyanar da tana cikin farin ciki,fuskarta a lokacin tana kallon wani gefen daban,,Idanunsa ya dasa a gurin yaci gaba da kallon kyakykyawar fuskarta dake cike da fara’a ba tare da yana blinking idanunsa ba,,yadda take cikin farin ciki a lokacin haka nan shima sai ya tsinci kansa da mugun farin cikin daya jima bai yi irinsa ba,wanda sakamakon ganinta a dai² lokacin da baiyi zato ba ya haifar masa
“Shukhraan ya k’adiiyr..”
Ya fad’a k’asa² yayin da yaci gaba da yiwa Allah godiya a zuciyarsa daya had’a shi da farin cikin rayuwarsa a lokacin da yake tsananin buk’atar hakan,,hannun da abun hawansu yake aka fara bawa hannu,ko kafin yayi magana da Sultan tuni har Napep d’in da take ciki ya fara tafiya,suna baro wancan hannun sun shigo dai² kwanar gidan maggi yaga napep d’in ya sake tsayawa,maza ne guda biyu a gurin tsaye wanda da dukkan alamun su suka tsayar da shi,idanunsa ya sake d’orawa a gurin yana jiran ganin ta inda zasu bi su shiga sai ganinta yayi ta fito a ciki su kuma sun shige,a lokacin guda ta sake yin murmushi bayan ta d’anyi magana da mazan da suka tsayar da napep d’in nasu fuskarta da wannan uban murmushin,wani mahaukacin kishi ne ya fara rufe masa ido,nan da nan ya fara ganin duhu na mamayarsa,lokaci guda fara’ar dake saman fuskarsa ta fara disashewa,gashi su d’in har lokacin ank’i basu hannu,zazzafar iska ya fesar yana sake kallon side d’in da napep d’insun yake tsaye sai dai a lokacin har sun bar gurin,kallon Sultan yayi yana fad’in
“Dude..! Ka bi wannan hanyar..”
Yana maganar yana kallon napep d’insu da yayi nisa,kallonsa Sultan yayi saurin yi da mamaki a fuskarsa
“Me yasa..!?”
“Cewa nayi kawai ka bi nan,,ban ce ka tambayeni ba..”
Harararsa Sultan yayi yana tab’e baki
“Idan nak’i kuma fa..!?”
Da sauri ya juyo a fusace ya kalleshi
“Idan ka k’i kace..!?”
D’age masa gira Sultan yayi alamun haka yake nufi,,girgiza kai kawai Hammad yayi kafin ya nuna masa waje da fad’in
“Fita..!”
“Idan na fita ina kake tsammanin zanje..!?”
A tsawace ya sake magana yana cewa
“I said,,get out..!”
Murmushin yak’e Sultan yayi masa yana fad’in
“Kai yanzun idan nace zan fita a tsakiyar traffic d’innan sai ka bari..!?”
Tsaki yayi yana kallon hanyar da suka bi
“Ooh! Shet..!”
Ya fad’a yana runtse idanunsa dan a lokacin tuni suka yi mugun nisa,,juyowa yayi idanunsa jajir ya kalli Sultan a dai² lokacin da fitilar bada hannu ta sake su,take motar Sultan yayi kafin ya karkata ya d’ebi hanyar data shiga Kwanar maggi
“Dallah malam idan bazaka iya tuk’inba ka fita ka bani guri,kana abu kamar baka da kuzari..”
Kallonsa Sultan yayi ya masa murmushi sannan ya sake bada wuta suka bi hanyar da mahaukacin gudu.
A gefen su Sabina kuwa,lokacin da mai napep d’insu ya tsaya,kasancewar ita kad’ai ce a ciki,ko da ganin zai d’auki mutum biyun nan duk da bata ji dad’in had’a ta cikin abun hawa d’aya da maza da mai napep d’in yake shirin yi ba,sai bata yi magana ba tayi shiru,har suka gama daidaitawa,suna niyyar shiga ta d’an kallesu fuskarta da fara’ar dole
“D’an uwa dan Allah ko zaku shiga ciki,inda zan sauka babu nisa sosai,dan ina ganin kamar zan riga ku sauka..”
Kai d’aya daga ciki yayi saurin girgiza mata yana murmushin shima sannan ya ce mata
“Babu komai..”
Fitowa tayi saurin yi daga ciki suka fara shigewa,a dai² lokacin ta sake yin murmushi tana fad’in
“Na gode..”
Sannan ta koma ta zauna a takure daga gefe,tana kallon waje ranta duk babu dad’i
“Aikin banza kawai,su masu abun hawan nan sam basu san hak’k’in wad’anda suke d’auka ba,,in banda tsabar wulak’anci ina dalilin had’a mace da namiji a cikin abun hawa d’aya..Sai kace ba musulmi ba.!? Kawai dan suna tak’amar abun hawansu ne sai suyi ta wulak’anta passenger.! Wollahi duk ranar da wani ya sake min haka Allah sai ya yabawa aya zak’in ta..”
Na kusa da ita ne jin tana mita duk da ba jin abunda take fad’a yake yi ba ya d’an kalleta yana murmushi
“Hajiya magana kike yi ne..!?”
Saurin juyowa tayi ta kalle shi,cikin zuciyarta tana addu’ar Allah yasa baiji me tace ba,,murmushin yak’e tayi masa tana girgiza kai
“A’a’a..! Babu komai..”+
“Uhhuumm..! Na zata kince wani abu ne..!”
“A’a..!”
Sake juyawa tayi tana kallon waje,cikin mitar abun tana fad’in
“Kaji min mutum,,sai kace wanda na kasa da shi,har da wani tambayata abunda nace..Kamar nayi magana da shi..”
“Uhumm! Hajiya nace ba..!?”
Saurin waiwayowa tayi tana murmusawa
“Meya faru kuma..!?”
Ta tambaya cikin rashin sanin abunda zai sake cewa
“Sunanki nake so ki fad’a min idan babu damuwa..”
“Me jin suna na zai amfana maka kuma..!?”
Tana fada tana murmusawa
“Babu komai,,kawai na tambaya ne,idan babu damuwa a taimaka a fad’a min..”
“HAFSAH..”
Ta fad’a a tak’aice, murmushi yayi da fad’in
“Suna mai dad’i..”
Bata juyo ba bare yasa ran zata kalleshi ta furta
“Na gode..”
Sai ta kuma yin shiru tana sake karkata kanta gefe
“Ranki ya dad’e..!”
Runtse idanunta tayi cikin zuciyarta ta furta
“D’an anace kenan..Me kuma zan maka..!?”
“Idan babu damuwa zan iya sanin inda zaki.!?”
“Gida..!”
Ta fad’a cikin yanayin gajiya da amsa masa,girgiza kai yayi yana fad’in
“Da kyau..”
Sai kuma yayi shiru shima bai sake magana ba,,sunyi tafiya mai d’an tsayi daga kwanar maggi zuwa *KAWON MAI GARI* sannan Sabina tayi magana
“Malam idan ka samu guri zan sauka..”
“Toh..! Hajiya”,ya fad’a yana tsayawa a gefen hanya,jakarta dake rataye saman kafad’arta ta nemi saukewa ta sallami mai napep d’in,mutumin da yayi ta mata surutu d’azun ya lek’o daga ciki yana fad’in
“Hajiya..!”
A sad’ad’e ta d’ago dan ita kam zuwa lokacin Allah ya sani kuma har zuciyarta ta fara tsoron yin magana dashi,haka nan take jin fargabar tsaiwar da take bare kuma maganarsa da a duk kalma d’aya da zai tambayeta takejin zuciyarta tana tsananta bugu,baya ga gargad’i da wani sashi na zuciyarta ke yi mata
“Nace ba..!?”
Idanunta akansa ba tare data samu damar amsawa ba,irin kallon da take masa ne ya sashi yin murmushi kafin yace
“Zaki iya tafiya..”
“Me yasa zan tafi,bayan ban sallami mutum ba..!?”
“Ki barshi kawai..”
Kallon rashin fahimta taci gaba da binsa da shi,murmushin still ya sake yi,sai dai bai ce mata komai ba,kallon mai napep tayi da shima yake murmushi lokacin,za tayi magana yayi saurin taron numfashinta
“Hajiya kinga kawai kije tunda ya fad’a miki..”
Fuskarta cike da mamakin kalaman mai napep ta sake yunk’urin yin magana again ya tare ta
“Hajiya an riga an biya miki,kije kawai Allah ya sanya alkhairi..”
Maganganunsu duk a hard’e taje jin suna shiga kwakwalwarta,tana tsaye ba tare data tafi ba suka ja napep suka yi gaba abunsu,tsaiwa taci gaba da yi a gurin tana mai bin hanyar da suka bi da kallo,sai da taga sunyi mata nisa sosai kafin ta juya ta kama hanyar da zata kaita line gidansu,a zuciyarta tana tunanin kalaman mai napep da suka tsaya mata a rai in da yace
_”Hajiya an riga an biya miki,kije kawai Allah ya sanya alkhairi..”_
To itafa wannan Allah ya sanya alkhairin ne ta kasa fahimtar abunda ake nufi da shi,har ta shiga gida bata daina tunani da juya maganar a ranta ba.Shigowarta kenan ta iske Inna sunkuye a bakin rijiya tana janyo ruwa,sallama tayi jikinta a d’an sanyaye sannan ta k’araso ciki,d’agowa Inna tayi bayan ta amsa tana fad’in
“Sannu Uwata..”
D’an murmushi tayi tana amsawa,kafin ta durk’usa tana fad’in
“Inna barka da gida..”
“Yawwa y’ar nan,,yanzun nan na gama zancenki ashema kina tafe..”
“Ehh! Inna ai yau jarabawar ce bamu yi da wuri ba,shi yasa ban dawo tun d’azu ba..”
“Toh! Allah dai ya fito muku da kyakykyawan sakamako..”
Da “ameen” ta amsa sannan Inna tayi mata izinin ta shiga ta cire kayanta ta huta,amsawa tayi cikin ladabi sannan ta mik’e ta shige cikin d’aki.
Iya k’urewar gudun daya kamata ace mutum yayi musamman inda yasan ba hanyar motoci bane kawai Sultan yake yi amma cikin wani hukunci na Ubangiji duk iya kar dubawarsa da hangawa ya duba sai dai ya nemi napep d’in daya d’auko ta ya rasa,,gashi sai ci gaba suke da tafiya kamar zasu k’ure malejin hanya,sabon tashin hankali ya sake ziyartarsa,yayin da gumin tsananin tashin hankali ya shiga keto masa,bai juyo ba bare ya kalli Sultan ya ce
“Tsayar da mota.!”
Kallonsa Sultan yayi da rashin fahimta dan shi bai san me yake faruwa ba har lokacin
“Kamar yaya na tsaida mota..!?”
“Cewa nayi ka tsaya..Idan baza kayi ba zan fita.”
Mahaukacin brake Sultan ya taka,ko gama tsaiwa motar bata yi ba tuni har ya bud’e murfin ya fice,lek’owa Sultan yayi ganin ya tafi baice masa komai ba
“Malam..Wai me yake damunka ne..!? Da fari kace mubi hanya,yanzun kuma ka fice baka cemin komai ba…Me yake faruwa ne wai..!?”
Bai juyo ba nd still yana ci gaba da tafiya,cikin muryan jin haushi yace
“Zaka iya tafiya..”
Saurin fitowa yayi ya biyo shi a baya
“Kamar yaya zan iya tafiya..!? Idan na tafi naje ina..!?”
Tsaki yaja ba tare daya kalle shi ba yaci gaba da tafiya,while yana kallon napep da suke yawo a arean ko zaiga mai number da yaga ya d’auke ta.
Tun misalin k’arfe 5:00pm har aka fara kiran sallar Maghreb suna cikin arean Kwanar maggi,ba tare da sun ga abunda suke nema ba har aka idar da sallah,lokacin bayan sunyi sallah a wani masallaci dake gefen hanya,Sultan ya koma mota ya zauna dan shi dai Allah ya gani ba zai iya wannan zagayen azabar ba,,wasa² har k’arfe 9pm tayi suna cikin unguwar,,kuma har a that time Hammad yak’i yarda ya shigo su tafi gida tunda dai haifa abunda yake nema ba,gajiya Sultan yayi da masa maganar su tafi kawai ya d’auki waya ya kira Mamma dan yana sa yak’inin duk duniya itace mutum ta farko da zata cewa Hammad yayi,haka nan idan tace bari ba saita k’arasa ba zai bari d’in,,bayan sun gaisa da Mamma kai tsaye ya fad’a mata abunda ke faruwa,,suna gama maganar tace ya bata Hammad d’in suyi magana,lek’owa yayi a motar ya kirashi amma gogan yak’i yarda ya amsa masa,har sai da yace masa gavMamma akan line tana son magana da shi sannan ya juyo da sauri ya karb’i wayar,a kunnensa yasa tun kafin yayi magana ta furta
“Hammad..! Duk inda kuke yanzun ina son ganin ku..”
“Buh Mah..!”
“Bance ka bani ko wane irin excuse ba,abunda kawai nace shi ne,i want see u now.!”
“Ok.! Mah..Gamu nan dawowa..”
Katse wayar tayi,cikin jin haushi shima ya cillawa Sultan wayarsa sannan ya bud’e motar ya shiga,tun daya zauna bai sake magana ba har Sultan yayi reverse suka d’auki hanyar komawa gida.
Tana zaune a tsakar gida da littafin physics a gabanta,a zahiri duk wanda ya kalleta tabbas zaiyi zaton karatu take,sai dai a wannan lokacin sam zuciyarta bata tare da abunda idanunta ke kallo,,daga d’ayan gefen kuma Babanta da Innarta ne bisa tabarma suna hira,yayin da radio take nata b’ab’atun a kusa da Baba,,zuciyarta tayi nisa da gangar jikinta,zuwa cikin tunanin abunda a kowane rana shi ne aikinta,sai dai tunanin a yau ya sha bamban da sauran ranaku,tayi zurfi a duniyar tunanin dalilin rashi dawowarsa gare ta,,yaro ya shigo gidan da sallama,Inna da Baba ne suka amsa masa,yaro ya durk’usa har k’asa yana fad’in
“Wani ne yace yana sallama a k’ofar gida..!”
Baba ya kalli Inna yayin da itama take kallonsa dukansu fuskokinsu da mamaki,hankalin Baba akan Inna ya amsawa yaron ya tambayo wa ake nema,juyawa yaro yayi ya fita bayan y’an mintuna ya dawo yace
“Wai yace HAFSAH yake nema..”
Sake kallonsa Inna tayi shima ya kalleta kafin ya juya ga Sabina data k’ure littafi da ido
“Uwata..!”
Ya kira sunanta,sai dai sam bata ji ba,har kusan sau biyu yana maimaita kiranta duka bata ji shi ba
“SHALELE..!!”
Ya sake kira,firgigit tayi tana amsawa sannan ta ajiye littafin ta taso da sauri,girgiza kai kawai Inna tayi dan ita kam da jimawa ta gama fahimtar inda hankalinta ya tafi
“Kije ki duba k’ofar gida ana sallama..”
Amsawa tayicikin girmama maganar Baba ba tare data tsaya tambayar da waye ake sallama ko wa ake nema ba,ta zira hijab d’inta ta fita cike da son cika umarninsa,,a k’ofar gida kuwa lokacin data fita tsaye ta iske mutum ya jingina jikin mota,sai da tayi addu’ah bayan ta gama k’are masa kallo ko zata iya gane waye daga inda take,rashin wadataccen haske a gurin shi ne babban abunda ya hana mata ganin fuskarsa tun daga nesa,kai tsaye bisa umarnin zuciyarta ta fara takawa ta nufi inda yake tsaye…..Lokacin da suka shigo gida a parlor suka tarar da Mamma tana jiransu,suna shigowa bayan sun gaisa da Sultan,ya nemi guri ya zauna,yayin da shi kuma gogan ya nufi hanyar barin gurin bcos duka yana jin ransa yana yi masa babu dad’i,so yana tunanin ba zai iya zama ba
“Hammad..!”
Mamma ta kira sunan sa dai² lokacin da yake d’aga k’afarsa d’aya,a bakin staircase ya tsaya yana runtse idanunsa ba tare daya amsa ba,ya d’auki kusan mintuna biyu a tsayen kafin ya iya juyowa,yafito shi tayi da hannu alamun yazo,guiwoyinsa a sanyaye ya dawo sannan ya nemi guri ya zauna d’an nesa dasu kad’an buh not far
“Mene ne matsalar kane..!?”
Tayi maganar tana kallonsu duka duk da a zahiri tana magana ne da Hammad,gyara zama Sultan yayi bayan ya kalle shi da niyyar bata amsa
“Mamma..! Wollahi nima abunda yake damuna kenan,,tun kafin yanzun na so ya sanar dani abunda yake damunsa,sai dai har yau bai bani damar sanin damuwarsa ba..Buh ban sani ba ko zuwa gaba idan zuciyarsa ta aminta daya sanar min..”
Kallonsa Mamma tayi da fuskar serious
“Baby..! Me yake damunka ne..!? Kasan ba tun yanzun kake b’oyemin damuwarka ba ko..!?”
Shiru yayi ya kasa magana,itama bata wani damu da shirun da yayi ba taci gaba da magana
“Baby.. Zaka sanar dani damuwarka ko kuma zaka jira Daddy ya dawo,,kaga sai ka sanar masa ko.!?”
Saurin d’agowa yayi ya kalleta,jinjina masa kai tayi alamun abunda ta fad’a d’in haka take nufi,marairaicewa ya fara yi
“Mamma.. Daddy fa..!?”+
“Ehh! Mana ba haka kake so ba..!?”
“No Mah.. Duka fa ba yadda kike zato bane..!”
“Ba sai ka ce min wani abuba,,bcos na jima da sanin abunda yake damunka..So kawai dai na sa maka ido ne ina jiran ganin ranar da zaka sanar da ni,,ko dan kaga ban takura maka ba wannan karon,shi yasa kake tunanin b’oye min..!?”
“Mah..!”
“Yaro² ne,,tunanin k’in fad’a min da kayi zai sa na kasa fahimtar damuwarka..?? Bari to ni na fad’a maka dalilin rashin lafiyar ka yasa ni rabuwa da kai,ba don komai ba sai don bana son na haifar muku da damuwa,shi yasa na saka maka idanu,amma yanzhn lokaci yayi daya kamata ace munyi maganar..! Shin da gasks ne a dalilin *SO* ne kayi rashin lafiya..!?”
Saurin kallon Sultan yayi da fuskar tuhumakafad’a ya d’age masa alamun bashi da sani akan abunda yake son tuhumarsa
“Tambayarka nayi ba’ayi haka ba..!?”
“Mammah amma fa..!”
“Just answers..! Anyi ko ba’ayi ba..!?”
“Anyi Mah.”
“Good..! Me yasa to ka kasa fahimtar duk boy’ewar da zaka yi ni d’in zan sani..!? Ko baka yi wannan tunanin ba..!?”
Shiru yayi bai amsa mata ba
“Shi kenan tunda ka maida ni surukarka,,shi yasa ma ka fara wasan b’uya dani ko..!?”
Dafe k’eyarsa yayi yana kallon k’asa dan yadda kalaman Mamma’n yasa jikinsa fara yin sanyi
“Bari mubar wannan maganar tunda naga kamar baka shirya yinta da ni ba..Kun san dalilin kiran da nake muku..!?”
Sultan yayi k’arfin halin amsawa da “A’a”,bayani komai dake faruwa tayi musu nd kamar yadda idanunta suka gane mata videon da Daddy ya aiko mata,,bayan ta gama kuma tayi musu fatan alkhairi da samun nasara,Sosai Sultan ya nuna jin dad’i a fili da kasancewarsu masu nasara a cikin dubbanin wad’anda suka yi karatu tare,tabbas yana jin alamun nasararsu ne ya fara baytana,,kafin su rufe babin wancan maganar na farko suka fad’a kan batun yadda tafiyar tasu zai kasance,tun da suka fara magana ko “ehemm” Hammad bai furta ba har suka yi suka gama sannan Sultan yayi musu sallama ya tafi gida,hankalin Mamma akansa bayan fitar Sultan ta juyo tana kallonsa
“Baby..! Yanzun yaushe ne kuka yanke za kuyi tafiyar..!?”
D’agowa yayi saurin yi ya kalleta
“Mah! Ina zamu..!?”
Mamaki sosai akan fuskarta take kallonsa
“Ban gane ina zaku jeba..!? Baka san maganar da nake yi bane..!?”
“Banji ba Mah..! Buh me yake faruwa ne..!?”
Jinjina kai ta shiga yi tana kallonsa da mugun mamaki shimfid’e a saman fuskarta
“Baka ji komai ba kace.!?”
“Mamma da gaske fa ban san mene ne kuka ce ba..”
Sake jinjina kai tayi tana k’arewa fuskarsa kallo,tabbas daga dukkan alamu iya gaskiyar sa yake fad’a mata,nd shi ne abunda ta hango a cikin idanunsa,to amma idan har ace duk maganganun da suka yi da Sultan bai ji komai ba,ina hankalinsa yake a lokacin..!?
“Mah..! Baki ce komai ba..”
Magannar da yayi ita ta dawo da ita hayyacinta
“No..! Ba saina sake maimaitawa ba,ka jira idan Daddy ya kiraka zaka ji komai a bakinsa,,ehmm! Dama yace min yana kiran wayoyinka a kashe..Shin akwai dalilin da yasa ka kashe waya..!?”
“Babu Mah,kawai dai..”
Sai yayi shiru kuma yana sunkuyar da kai k’asa
“Kawai dai me..!?”
D’agowa yayi ya d’an saci kallonta
“Nothing Mah..”
“Uhhuumm..!” Tace daga haka kuma sai bata sake magana ba,shima d’in shiru yayi a zatonsa zata sake yin maganar amma sai yaga gaba d’aya ma bata da niyyar cewa wani abu,hak’ura yayi da yaga bata da niyyar yin ko da kwakwkwaran motsi yayi mata sallama sannan ya wuce bedroom.
Har ta k’arasa kusa da inda yake bata gane ko fuskar waye a tsaye a gurin ba,sallama tayi a daf da shi cikin sanyin muryanta tana sake watsa idanunta a kansa
“Barka da fitowa ranki ya dad’e..”
Muryansa ya daki kunnenta,tunanin inda tasan muryan kwakwalwarta ta tafi yi,a lokacin da zuciyarta kuma take tambayarta
“Shin ia nasan mai irin wannan muryan..!?”
Tayi furucin cikin salon son ganowa,shirun da tayi bata tanka ba yasa shi juyowa sosai yana fuskantar ta
“Ranki ya dad’e fatan kina lafiya,,ya mutanen gida..!? Nd ya kika dawo gida..?”
Damm.! Taji k’irjinta ya buga a sakamon muryan da taji a karo na biyu,wanda shi ne ya bata damar tuno ko muryan waye
“Mutumin da muka had’u d’azun,,shi ne yanzu yazo gidan mu kuma..?? Ta yaya aka yi ya san gidan mu..!?”
Kamar yasan abunda take tunani yana murmushi yake fad’in
“Kiyi hak’uri fa,,da fari dai barin gabatar miki da kaina ko..!?”
“Ba buk’atar haka..!”
Tayi saurin katse shi ba tare data ko kalli inda yake ba,da mamaki shi kam yake kallonta cikin salon nuna damuwa ya furta
“Why not *My Lady..!?”*
K’irjinta ne ya sake bugawa sakamakon sunan da taji ya ambata,nan da nan taji kwakwalwarta tana sake tuno mata da ainihin wanda yake fad’ar sunan,dana tunaninsa take kan yi aka tura kiranta
“Kayi hak’uri..”
Ta fad’a tana kauda kai gefe saboda wani mugun haushinsa da tsayuwarta gaban wani ba shi ba ya haddasa mata
“Amm! Babu damuwa..Amma me yasa kike bani hak’uri..?”
Sai data ja dogon numfashi kafin ta iya furta
“Saboda a gidan mu an riga anyi min miji..!”
Wani wawan kallo ya mata cikin kid’imewa
“Ke d’in,, aka yiwa miji a gida..!?”
Kallonsa tayi itama tana sake tsuke fuska
“Ehh! Ko ban isa bane..!?”
“A’a..! Ni ina na isa na fad’i haka..!?”
“Ka isa mana,,tunda ai bakin kane,, kaga kenan kana da damar yarda ko ka k’aryata..”
“A’a..! Ranki ya dad’e mene ne abun rashin yarda,,tunda har kin fad’a kinga ai ban isa nace ba haka bane,,sai dai gaskiya bazan b’oye miki ba,Allah ya sani da gaske nake sonki shi yasa ko d’azun da muka had’u a abun hawa har munyi nisa naji bazan iya daurewa ba,kawai sai nabi umarnin zuciya ta akan na bi bayanki dan naga inda zaki je,,buh tun da Allah ya k’addara al’amarin yazo da haka,sannan Annabi (S.A.W) yayi mana hani akan nema cikin nema,,kinga kenan dole na hak’ura,saboda haka ina yi muku fatan alkhairi,,Allah yasa albarka,sannan idan lokaci yayi da fatan baza’a manta damu ba..”
Saurin kallonta tayi,not minded shima ya kalleta fuskarsa da murmushi
“Kada ki damu fa,,ni yanzun ina matsayin kamar yayan ki ne,ko ba haka ba..!? Kinga kenan idan babu soyayya ai ina ganin sai muyi zumunci ko..!?”
Murmushin k’arfin hali tayi masa a lokaci guda kuma tana girgiza masa kai duk da dai ba haka taso ba,sun d’an jima tsaye yana ta mata hira sai dai ita kam a gareta daga “Ehhh” sai “A’a” iya amsanta kenan idan yayi mata magana,har ya gaji dan kansa yayi mata sallama,bcos ya fahimci hankalinta duka baya kansa,sai da yaga shigarta gida sannan ya shige mota ya tafi.
Tun daga shigarta gida yanayin kallon da taga Inna da Baba suna binta da shi yasa kunya ta fara neman rufeta,sallamar tata ma a sad’ad’e tayi,bata jira kuma amsawarsu ba sum² ta wuce ciki,girgiza kai Inna tayi tana murmushi,kafin ta juyo ta kalli Baba da shirin yin magana yayi saurin taron numfashinta bcos ya fahimci akan abunda za tayi maganar
“Mairo..! Ba sai kince komai ba,in dai akan wannan maganar ne..”
“Amma Malam..! Me yasa za kace haka..!?”
Gyara zama Baban Sabina yayi daga kishingid’a zuwa zama sosai ya sake fuskantar ta
“Na san dai kisan da *ALK’AWARIN* dake kanmu..? Bayan nan kuma kin san ko waye ya k’ulla,,to dan haka idan har kin manta,ni ban manta ba saboda haka bari na sake tuna miki,,idan har baki manta ba Yaya Allah yayi masa rahama,kafin ya rasu shi ya bada auren Uwata ga Muhammadu,sannan wannan abu ba wai kai tsaye muka yi shi ba,saboda haka dan baya raye a yanzun,ba shi yake nuna zan gaza da cika masa *ALK’AWARIN* daya d’auka ba..Amma bari nayi miki y’ar tunatarwa game da muhimmancin rik’on amana da cika *ALKAWARI* la’alla ki sake fahimtar dalilin,a masulunce ko nace kamar yadda Allahu (S.W.T) yace acikin surutun-nisa’a (ayata 58):”Lallai ne Allah (S.W.T) yana umarninku da ku bayar da amanoni zuwa ga masu su.Kuma idan zaku yi hukunci a tsakanin mutane,ku yi hukunci da adalci. Lallai ne,Allah madalla da abunda yake yi muku wa’azi da shi.Lallai ne Allah ya kasance mai ji ne,kuma mai gani”.Dalilin saukan wannan aya kuwa shine,kafin ayi fathu makkah,ya kasance key (wato makullin) d’akin Ka’abah,yana wajen Uthman Ibn Talha.To a lokacin da akayi fathu Makkah kuma sai Manzon Allah ya cewa Uthman Ibn Talha ya bashi key d’in d’akin Allah mai alfarma(Ka’abah),sai ya bashi yana mai cewa ‘AMANA’ na baka,sai manzon Allah ya bud’e d’akin Ka’abah sannan ya fidda dukkan gumakan dake ciki.A dai² wannan lokacin kuma baffansa Abbas da Aliyyu (R.A) sai suka buk’aci makullin ya kasance a hannunsu,amma sai Annabi yak’i basu.Kamar yadda sayyadina Umar ya rawaito (R.A) yace Manzon Allah ya fito daga Ka’abah yana karanta wannan aya ta surutun-nisa’a kamar yadda fassaran ayan ya gabata,sannan sai ya mayarwa Uthman Ibn Talha makullin,wannan abun ya baiwa Uthman mamaki da sha’awa sosai,ya kuma sa masa k’aimi na ya karb’i addinin musulunci,tunda a matsayin manzon Allah (S.A.W) na wanda ya samu nasara akansu ya cika wannan amanan,ya nuna addinin na gaskiya ne,wannan dalilin yasa Uthman Ibn Talha yaji dad’in hakan sosai kuma anan take ya shiga musulunci,ma’ana ya karb’i kalmar shahada..Anas (R.A) ya rawaito cewa ba kasafai manzon Allah yake khud’ubah ba,face sai ya ambaci cika *ALK’AWARI* da rik’on *AMANA*..”
Kabbara Inna tayi cikin jin dad’in k’issar da Baba ya bata,ko kafin ta kaiga sake yin magana nan ya d’ora da fad’in
“Saboda haka nake son ki k’ara sani akan wanda kika yi,matsawar kika ga an fasa auren yaran nan ko bai yuwu ba kamar yadda Yaya yayi buri,to ki tabbatar cikin biyu aka samu d’aya,ko dai ace yaron nan da kansa yazo yace ya fasa,ko kuma ya zama bana raye..Tabbas wad’annan dalilan su kad’ai ne nake tunanin zasu sa kiji an fasa wannan auren..”
Jikin Inna a sanyaye ta kalle shi duk da k’issar daya bata ta tab’a mata zuciya,sannan kuma tana jin akwai maganganu sosai a bakinta,sai dai hujjar daya kafa mata tasa taji jijiyon jikinta duk sun sake d’aure ta,harma taji baza ta iya sake cewa komai ba.
Yana shiga bedroom kayan jikinsa yayi k’ok’arin cirewa,d’aure da towel daya tsaya masa iya waist ya zauna gefen bed,yana tunano yadda AL’AMARIN ya faru,tabbas badon sab’anin da aka samu ba,yasan babu yadda za’ayi ya kasa had’uwa da ita,yayi nisa cikin tunaninta hoton fuskarta ya sake dawo masa kamar yanzun ne take gabansa,fuskar nan cike da fara’a,runtse idanunsa yayi saurin yi yana cusa yatsunsa duka a cikin sumar kansa,lokacin guda kuma tuna ko waye take ma murmushin ya sake haddasa masa jin babu dad’i,tsaki yaja mai sauti a lokaci d’aya ya kaiwa iska bugu
“Lallai akwai matsala duk ranar da na sake ganin kin sake yima wani makamancin wannan murmushin..”
Ya fad’a a fili lokacin da yake mik’ewa ya nufi hanyar bathroom,after some minutes ya fito jikinsa jik’e da ruwa alamun dake nuna wanka yayi,slowly yake tafiya jikinsa na motsawa,sai dai ba kowa zai gane hakan ba bcos motsawa ne yake yi irin ba sosai ba d’in nan yanayin dai cike yake da bada sha’awa,tamkar wani gawurtaccen jarumi,,a gurguje yayi shirin bacci saboda yadda zuciyarsa take a cunkushe,yana gama murza lotions ya feshe jikinsa da turarukan sa yabi lafiyar bed,damuwa na sake masa barazana,ba tare daya bi ko takan pyjamas d’insa daya ajiye ba,yayi kwanciyarsa daga shi sai boxes da armless,idanunsa a kulle damuwoyin da yake ta k’ok’arin kaucema suka fara kawo masa ziyara,baccinma ba dan kasancewarsa b’arawo ba,da sai yace bai san lokacin da yayi shi ba.
Wasa² tun daga wannan ranar ak’alla sai daya d’auki tsawon kwanaki uku yana zagaye a cikin unguwar *KWANAR MAGGI* ba tare da yaga wani daya san su ba,ko even su d’inma,,kullum ta Allah kuma idan yaje bai samu gano inda suke ba,baya tab’a hak’ura gobe ma haka zai sake d’aukan jiki ya tafi,sai dai kullum amsan d’aya ne,baya had’uwa da even a single man da yasan su,a haka har aka kwana uku.
A b’angaren Daddy kuwa tun bayan da suka yi magana da Mamma lokacin daya tambayeta dalilin da yasa Hammad ya kashe waya,tace masa bata sani ba sai dai tayi magana itama akan matsalar,sannan ta sanar da shi sak’onsa,wanda shi ne dalilin da yasa Daddy’n yake ta tsammanin ganin ya kira shi tunda shi idan ya kira baya samunsa,sai dai shiru har yanzun kamar an shuka dusa,nd itan kuma suk lokacin da yayi magana da ita tace ta sanar masa,saboda haka ne sai ya kasa gane waye mai gaskiyar a tsakaninsu,sh baiji daga gare shi ba,ita kuma tana sake tabbatar masa ta fad’i sak’onsa,wannan dalilin yasa ko daya sake kiranta,yadda Mamma bata zato haka yayi ta mata fad’an da bata san dalilinsa ba,shiru tayi masa sai da ta bari yayi ya gama sannan ta bashi hak’uri,,katse kiran yayi dan yadda tayi masa magana wisely nd calmly yasa shi jin bazai iya jurewa hakan ba,,yana kashe wayan itama Mamma a nata gefen,ajiyar zuciya ta saki,sannan ta k’udurce a ranta yau ko mene ne zai faru dole ne ta gwadawa Hammad jan ido,bcos tana ganin zai fi fahimtar abunda take son sanar da shi…..Washe gari da safe a parlor Mamma ta zauna gudun kada ya fice a gidan bata sani ba yasa ta zauna dakon fitowarsa,ko cikakkun mintuna biyar bata d’auka da zamanta a gurin ba sai gashi cikin sauri² yana shirin fita,a tsaitsaye ya gaida ita ba tare daya zauna ba ya kama hanyar fita da sauri,tana kallonsa tak’i yin magana har sai data bari yaje daf da k’ofa zai fita sannan ta kira sunansa,tsayawa yayi cak a inda yake kafin ya juyo a hankali cikin mutuwar jiki ya kalleta fuskarsa da alamun damuwa
“Mah.! Na zo ne..!?”
Kai ta girgiza masa,cikin sanyi ya dawo ya nemi saman armchair ya zauna yana fuskantarta da jiran jin me zata fad’a,duk jinsa yayi masa wani iri haka nan ya kasa d’aga kai ya kalleta
“Ina zaka je by this time around kake sauri..!?”
Maganarta ta katse masa tunanin da yake yi,saurin d’agowa yayi ya kalleta,sai dai ko inda yake bata d’aga kai ba bare yasa ran zata kalle shi,saima sake had’e rai da tayi coz bata son bashi fuska
“Kai nake sauraro,,ka tsaya kallo na..!”
Had’iye yahu ya fara yi da kyar sannan cikin sanyi ya furta
“Mamma..! Unguwa zamu je..!?”+
“Kai da waye..!?”
“Amm! Tare da Sultan ne..”
“Uhmmm..! Ina ne unguwar da zaku je d’in..!?”
Shiru yayi yana nazarin inda zai ce,zuwa can dabara ta fad’o masa a rai
“Mah..! Gidan su Sadeeq nefa zamu je..”
Kallon rashin yarda da abunda ya fad’a tayi masa kana tace
“Ka tabbatar abunda ka fad’a haka ne..!?”
Shiru ya sake yi sannan ya d’an girgiza kai followed by
“Ehh Mah..”
“Ok..Allah ya tsare hanya,buh make sure ka kunna wayoyinka,idan kuma ba haka ba wollahi thumma billahi,kaji dai rantsuwa nayi ko..?”
“Ehh.! Mah”
“Shi kenan jeka,Allah ya dawo da ku lafiya..”
A sab’ule ya amsa da “ameen” har ya tashi zai tafi ya sake waiwayowa ya kalle ta,canjin da ya gani a fuskarta shi ya bashi tabbacin rantsuwar da tayi ba k’alau ba,nd dole ne akwai dalilin da yasa tayi masa hakan,,take yaji zuciyarsa ta fara raya masa fasa fita har sai daya koma ya d’auko wayoyin,,har lokacin tana zaune bata motsa ba ya zo ya fita,itama Mamma koda taga fitarsa da wayoyi a hannu a hankali ta saki ajiyar zuciya a fili kuma tana fad’in
“Allah ya taimake ka,,amma da yau na gwada maka fushin da baka tab’a ganin nayi ba..”
Yana fitowa daga cikin gida mota ya shige ya bar unguwar da mugun gudu,ba tare daya nemi rakiyar Sultan ba ya kama hanyarsa shi kad’ai though ma dai wannan ba shi ne karo na farko daya fara tafiya shi d’aya ba,,tsayin kwanakin da suka gabata shi kansa yasan bulayi kawai yake,amma tabbas baiji ajikinsa zai had’u da itaba tunda har gashi yana neman shafe yini na hud’u kan neman inda suke,amma amsar iri d’aya yake maimaita samu da wanda ya samu a baya
“Waii! Haka kullum zanyi ta yawon neman ki ba tare da na samu inda kike ba..?? Har ina kika b’oye ne.?? Ya kamata ace kin gwadamin inda kike rayuwa,tun gabanin zuciyata ta tsaya..”
A fili yayi maganar yana mai had’awa da sakin wahalalliyar ajiyar zuciya,,dai² yana karkata kan motan zai shiga cikin Kwanar Maggi a hankali d’aya a cikin wayoyinsa ta fara kuka,slow yayi da tafiyar gangancin daya d’auko sannan ya rik’o wayan,unexpectedly sunan Daddy yayi appear,da hanzarin sa yayi answering kiran ya jingina ta a kunnensa bakinsa har shaking suke gurin yin sallama.
Ga Daddy kuwa ko kafin ya kira Hammad sai daya fara kiran Mamma dan ya tabbatar Hammad d’in ya kunna wayoyin kamar yadda ya bada sak’o ko kuwa,yana samun tabbaci akan ya bud’e wayoyin kuwa daga gurin Mamma kai tsaye ko da suka gama maganar ya kira shi dai² lokacin
“Sannu ubana..!”
Cikin muryan fad’a² Daddy yayi furucin yana jiran yaji me Hammad zai fad’a
“Barka da safiya Dad..”
Kalmar tayi escaped a bakinsa ba tare daya tsara fitarta a lokacin ba,,ajiyar numfashi Daddy yayi,ba tare daya amsawa gaisuwarsa ba ya ci gaba da fad’an sa
“Hammad..! Raini ne yasa ka kashe wayoyinka ko mene ne dalilin yin hakan..?!”
“A’a Dad,, bana jin dad’i ne kwanakin nan..”
“Jin dad’i kace..?? Yo yanzun waye zai ce maka yana jin dad’i dama..??”
Shiru yayi bai iya magana ba,jin haka yasa Daddy ya rufe shi da fad’a ta inda ya shiga ba tanan yake fita ba,sai da yayi masa tas²,bayan daya gama balbala ruwan fad’an then ya watso masa jawabin abunda yake faruwa da fad’in lallai² su shirya shi da Sultan a gobe su kama hanya,zai turo musu da sak’o bada jimawa ba,a yau duk abunda suke buk’ata suyi su gama,duk shirye²n da zasu yi su zuwa gobe su tabbatar sun tafi baya son a b’ata lokaci,,ba don Hammad yaji dad’in hukuncin da Daddy ya zartar ba,sai dan kawai son yayi masa biyayya ya amshi umarnin nasa,sannan suka yi sallama duka maganar Daddy kadaram kadahan (babu yabo bare fallasa).
Gefen route (hanya) ya gangara yayi parking,tunani iri daban² suka ci gaba da kawowa kwakwalwarsa ziyara,a hankali yake tunani kan maganar da suka gama da Daddy yanzun bada b’ata lokaci ba,,ya d’auki lokaci shiru ba tare daya san abunda ya kamata yayi ba kawai dai yana tsaye ne a gurin kamar wanda aka tilastawa yin hakan,,kansa ya d’ago daga jikin seat daya kwantar ya d’ora saman steering wheel had’e da rufe idanunsa,a fili yayi magana mai nuni da yana buk’atar taimako
“Why so soon.. Zan sake tafiya al’halin ban ganki ba..!? Yah Allah ka taimaki wannan gajiyayyen bawan naka..”
Tun daya tsaya a gurin bai iya fita a motan ba,sai dai idan yaga mutane sunzo wucewa ya d’ago kai zuciyarsa cike da fatan ganinta,haka napep ma dake shige da fice a unguwar sai dai idan baiga zasu gifta shi ba amma sai ya duba,haka yayi ta kalle² ko Allah zaisa yayi dacen ganinta kamar rannan,,har yamma yana tsaye a gurin da yayi parking ya kasa motsawa,ba shi ya bar unguwar ba har sai da akayi salatul asr,shima d’in sanadin kiran da Sultan yayi masa ne akan maganar tafiyarsu goben nd yace zai shigo gidan yanzun,dalili kenan da yasa shi kamo hanyar dawowa cikin sauri tun da ya riga yace da Mamma tare zasu fita da Sultan,,yanzun idan ta ganshi shi kad’ai ta d’auke shi matsayin me..? Dama yaga yanayinta tun a d’azun,so hakan yaba nuni da komai zai iya faruwa da shi matuk’ar ya bari Sultan ya riga shi zuwa gidan.
Tuk’in ganganci,tuk’in jeka ka mutu ya shiga shek’awa,daga kwanar maggi zuwa Mayangu road ko minti sha biyar baiyi ba ya k’araso,a dai² ALU avenue ya tsaya,bayan yayi parking ya shiga k’ok’arin kira line Sultan d’in cike da fatan Allah yasa bai riga ya fita daga gida ba
“Dude.! Kana ina ne..??”
Abunda ya iya fad’a kenan zuciyarsa na daka
“Gani a gida..Wani abu ne..?”
Ajiyar zuciya Hamma ya sauke cikin samun nutsuwa yayi hamdala a zuciyarsa,while a fiki kuma ya furta
“Yi sauri ka fito gani bakin line ku..”
“Ok” Sultan yace sannan ya ajiye wayar,shima d’in duka tsakanin yi masa waya da fitowarsa ko mintuna biyar baiyi ba ya k’araso inda yayi parking,daga nan suka d’auki hanyar gida.
Shirin duk daya kamata ace sunyi saboda tafiyar dake gabansu sunyi bisa tsari,kamar yadda Daddy ya shaida masa,hatta Sadeeq ma da suka yi waya da shi ya sanar musu shima ya kamalla komai suna dai jira ne wa’adinsu ya cika,nd sun ajiye batun akan kawai zasu had’u da juna a airport goben idan rabb ya nufa,daga nan suka bi juna da fatan alkhairi kana suka ajiye waya,bayan nan shima Sultan yayi sallama da shi ya wuce gida dan k’arasa sauran y’an abubuwan da suka yi masa saura.
Washe gari tun misalin k’arfe 6:30am suka bar gida,tare da ahalinsu duka suka yi musu rakiya,wannan karonma cikin masu raka Hammad sam babu Daddy kamar lokacin tafiyarsa na farko,duk da bai so yin tafiyar ba musamman a irin wannan lokacin haka nan ya sawa ransa dauriya,ba don komai ba sai dan yana so ya farantawa Daddy a matsayinsa na mahaifi,shi yasa komai zai ce masa baya tab’a yi masa musu,,da misalin k’arfe 7am da y’an mintuna bayan sun gama sallama da dangi,jirginsu ya bak’unci sararin samaniya,,,sunyi tafiya ta ak’alla awanni goma sha uku da mintuna daga 9ja zuwa k’asar Amuruka kafin jirginsu ya samu damar sauka,,kai tsaye bayan saukar su cab suka nema da zai kaisu cikin Florida,bayan isowarsu Jacksonville kasancewar a gajiya suke duka yasa a ranar ba su samu damar shiga UNIVERSITY ba,sun dai bari akan sai zuwa washe gari idan sun huce gajiya,sannan su tunkari mak’asudin abunda ya kawo su.
*NIGERIA..*
Duka tunda satin ya kama take jin jikinta babu dad’i,ga exam da kullum idan ta fita bata samun dawowa da wuri,nd idan ta dawo d’inma sai dai ta had’a da neman medicine saboda headache daya takura mata,a gefe guda kuma tunanin sa daya addabeta fiye da lokacin baya.
Tun data fito daga exam take zaune ita d’aya yayin da ta buga uban tagumi a bakin class d’in ta zubawa hanya ido,yadda take jin zuciyarta ta cika taf da tunaninsa yasa hawaye gangaro mata,sam bata san abunda ke faruwa da ita ba,sai dai ta jiyo saukar abu ajikinta,a hankali tasa hannu ta gogo fuskarta,sosai abunda ke faruwa ya bata mamaki ganin tana kuka without sound sai zallar hawayen dake sauka,jakarta ta bud’e ta zaro handkey d’insa daya bata tun karon farko kafin suyi sabo,gently ta fara goge fuskarta yayin da wasu hawayen ke sake sakkowa kamar ana tunkud’osu,bata fasa gogewa ba taci gaba har sai da tayi mai isarta dan kanta kuma ta rarrashi ranta sannan ta tattara y’an kayayyakin ta tayi hanyar fita a school d’in ba tare data jira wad’anda suke area d’aya ba ta kama hanyar komawa gida.
Kwanaki sun dad’a turawa a b’angaren ta,sai dai kullum babu wani ci gaba ta da take gani dangane da damuwarta,a kullum idan ta zauna bata da aikin daya wuce tunani da zubar da hawaye,cikin k’ank’anin lokaci fuskarta ta saje yin pale (fayau) saboda rashin wadataccen nutsuwa,,Inna kanta a cikin wannan y’an kwanakin lamarin ya fara damunta,duk da tasan damuwarta amma idan ta tambaye ta sai dai tace mata stress ne yayi mata yawa,,sai dai kawai tasa mata ido,amma abun yana damun zuciyarta,a duk sanda zata kalleta ta kan ji babu dad’i saboda yadda take zaman shiru,ko aiki idan za tayi sam babu wadataccen kuzari a tare da ita kamar da can baya,itan data kasance mai kazar² soyayya da damuwa yasa ta koma kamar ba ita ba,irin kunyar nanma da aka san d’iyan Fulani da shi duka shima a yanzun ta ajiye gefe saboda yadda damuwarta yake bayyane a fili.
Ganin lamarin bana k’are bane yasa Inna yanke shawaran neman mafita ta hanyar bin umarnin da zuciyarta take bata,lokacin da suke maganar da Baban Sabina kawai ta bar shine akan tana son yi tafiya buh shima d’in bata fito fili ta sanar da shi dalilin tafiyar ba,ko daya takura ta da son jin dalilin da zai kaita,kawai tace masa tana son taje ganin gida ne sannan ta samu ta d’an zaga danginta kasancewar ta jima sosai bata je ba,besides kuma anyi mutuwa babu adadi a family’n nata,bukukuwa da haihuwa duka ba tare data samu damar zuwa ba,sai dai a gefe d’aya duk da tana son zuwan tayi gaishe²,can k’asan ranta zuwan nata ya ta’allak’a ne akan lamarin yarinyar tata,tana son karb’o mata taimako a gurin baffanta ko Allah zai sa ta dangana (sawa ranta hak’urin rashinsa),idan kuma Allah ya nufa suna da rabon ganawa,tofa tabbas zata fi kowa farin ciki da faruwar al’amarin,,duka a cikin tak’aitattun kwanaki Inna ta yankewa ranta shawaran tafiyar sai dai ta barshi akan nan da zuwa k’arshen sati,ma’ana weekend idan ya zagayo,duk inda akace ta tafi Friday zuwa Sunday sai ta kamo hanyar dawowa.
*FLORIDA STATE (U.S.A).*
Cike da samun gagarumar nasara,ya fito daga k’aton theater,hannunsa d’auke da had’ad’d’en briefcase nasa mai d’auke da jimillar takardunsa,sai dai fuskar nan a had’e take cif babu alamun farin ciki,k’arasowar sa a gurin ita tasa Sadeeq dake zaune dafe da chin d’agowa ya kalleshi,saboda sanin halinsa da suka yi bai cika magana akan minor things ba shi yasa yanzunma da yake su nsan idan har ba tanbayarsa suka yi ba babu tabbacin ya iya fad’a musu abunda ke faruwa a ciki,wannan dalilin yasa ko da suka kalleshi a tare suka ambaci
“Dude..! Ya ake ciki..?!”
D’auke kai yayi kamar bai jisu ba,bayan ya zauna a seat d’in dake kusa da su,cikin nuna halin ko in kula da maganar da suke yi ya furta
“Idan kun shiga zaku san komai..”
Kallon juna suka yi,ko kafin Sultan yayi kwakwkwaran magana wani bature ya lek’o yana tambayansu *ALIYU MUKHTAR*,karkata kai suka yi su biyun jin an kira sunan Sultan,a hankali kuma sai ya mik’e bayan ya kallesu duka bakinsa d’auke da addu’ah yayi gaba Sadeeq ya bishi da fatan samun nasara amma gogan ko d’aga kai baiba,murmushin k’arfin hali Sultan yayi sannan ya wuce ciki,baturen ya maida k’ofa ya rufe,nan gurin ya rage daga Sadeeq sai Hammad sai kuma sauran abokan karatunsu da aka kiransu tare,amma magana ta fatar baki ko d’aya bata sake had’a su ba,bayan Sultan ya shafe ak’alla tsayin mintuna talatin ya fito yana murmusawa,canjin da Sadeeq ya gani tun daga kan fuskarsa yasa shi ambaton
“Alhamdulillah alaa kulli halin..!”
Duk da bai san mak’asudin sauyin da aka samu d’inba,a kusa da shi Sultan ya zauna,kamar wasu yara ya sak’ala hannunsa a saman wuyar Sadeeq d’in cikin tsananin farin ciki yana fad’in
“Dude..! Gaskiya Allah kad’ai ya isa abun godiya..Tabbas mu d’in masu nasara ne tun daga haihuwa.”
Murmushin gefe Sadeeq yayi cikin salon nuna farin cikinsa yace
“Allah mutumina..!?”
“Sosai ma..Amma dai bari ka fito mayi maganar,kasan yanzun babu lokacin yinta..Idan mun koma zamu tattauna..”
Dariya suka yi suka bawa juna hannu,sannan Sadeeq ya mik’e yana fad’in
“Sai na fito y’an uwa..?”
“All the best dude..!”
Sultan ya fad’a yana masa murmushi,kafin ya wuce shima sai daya kalli Hammad sannan ya juya ya tunkari k’ofar shiga zauren ganawar.
Shima d’in kamar su,dai² adadin lokacin da suka b’ata a ciki haka shima ya d’iba kafin ya fito fuskarsa k’unshe da fara’a mara misaltuwa,yana zuwa dai² inda suke ya sake bud’e baki cikin tsantsar farin ciki ya rungume Sultan yana fad’in
“Kaii! Dude..Gaskiyar ka daka ce mun tabbata masu sa’a,,lallai wannan ba k’aramin abun farin ciki bane a garemu.”
Murmushi Sultan yayi masa yana shirin yin magana suka ga Hammad ya mik’e,kallonsa duka suka yi yanayin yadda suke jinsu cikin farin ciki amma shi duka fuskarsa bata gwada komai ba,farin ciki ko akasin haka ba zaka tab’a ganewa ba,magana suke shirin yi sai dai babu wanda yasan actual abunda d’aya zai furta a taren sai suka furta
“DUDE..! Are u happy..!?”
Ba zata suka ji ya amsa musu da
“Am not..!”
Da mugun mamaki shimfid’e a fuskokinsu suka matso kusa da shi,bakunansu har sark’ewa suke wajen tambayarsa
“Me yasa haka..!?”
Bai tanka musu ba ya wuce yana tafiya nd yana sassauta d’aurin tie d’in dake wuyansa
“Baza ku gane ba.”
Yayi furucin k’asa² ba tare daya basu damar jin abunda ya fad’a d’in ba,,da sauri² suke binsa yayin da kowanne ke watso masa tambayar dalilin da yasa baya farin ciki da samun gagarumar dama irin wannan da kowa ke burin samu,sai dai tun daya ce musu baya farin ciki bai k’ara magana ba har suka dawo masaukinsu,,yadda yaga duk sun nufo inda yake yasa shi saurin mik’ewa fuska babu alamun fara’a ya wuce ya barsu nan a tsaye,ya d’auki tsayin lokaci a bathroom kafin ya fito sanye da bathrobe yana sake had’e fuska,saboda ko kad’an bai shirya yi musu bayanin dalilin da yasa shi fad’ar haka ba
“Dude..Wai me yasa kake haka ne..?”
Sultan daya gaji da shirunsa ya fad’a,yana daga tsaye a bakin mirror yayi saurin waiwayowa yana kallonsu
“Me akayi ne..!?”
Ya tambaya fuska da alamun neman k’arin bayani
“Kafi kowa sanin abunda akayi ai,,mun tambaya ka kasa bamu amsa ba,nd ka wuce ka barmu tsaye..Me kake nufi ne..?”
Murmushin gefe yayi sannan ya juya ya sake barinsu a tsayen ba tare daya ce komai ba,shirun da yayi musu har ya gama abunda zaiyi yana niyyar fita sannan ya juya kallesu,kamar zaiyi magana kuma sai ya fasa ya fice abunsa,,matuk’ar haushi Sultan yaji akan lamarin a hankali shima ya juya ya fice,nan d’akin ya rage sai Sadeeq kawai,shi kam tsabar d’aure masa kai da lamarin Hammad yayi zama yayi agurin ya had’e hannayensa duka ya d’ora chin d’insa akai yana tunanin halayen Hammad masu matuk’ar d’aure kai.
*NIGERIA..*
Juyowa Daddy yayi daga tsayen da yake yana cire wayarsa daga jikin kunnensa,a hankali kuma ya saki siririn tsaki kafin ya sake daddannawa ya maida ita kunnensa,kusan minti guda ya d’auka kafin yaji wayan ta fara fitar da sound na alamun kiran da yake yi ya tafi,ajiyar zuciya ya saki kafin ya maida wayan hands free
“Assalamu alaikum warahmatullah..!”
Muryan Hammad ya ambata cikin sanyi mai tattare da nuna damuwa
“Wa’alaikas salaam warahmatullah..!”
Daddy ya amsa,yanayin yadda yaji muryar Hammad cikin sauri ya fara tambayar lafiyarsa saboda yadda yaji yana magana kamar yana cikin wani yanayi sab’anin farin ciki,ko daya tabbatarwa Daddy lafiyarsa k’alau nan Daddy’n ya sake watso masa wani tambayar
“Ina fatan anyi nasara..!?”
Numfashi ya shak’i sannan ya furta
“Ehh! Dad..Munyi nasara..”
“Alhamdulillah..!”
Daddy ya fad’a cikin yanayin nuna tsantsar farin ciki
“Yanzun zaku dawo kwana kusa,ko kuwa sai nan gaba..!?”
“A’a Dad,, sunce mu jira nan da two days,duk yadda ake ciki zasu sanar damu..”
“Toh.! Babu damuwa,,ai sai ku jira d’in ku gani ko.!? Amma sun sanar da ku wane irin aiki ne zasu yi da ku..!?”
Ajiyar zuciya ya sake yi sannan ya amsa
“Ehh! Dad sun sanar mana,sunce ne za muyi aiki da hukumar binciken manyan laifuka ta *FBI* (Federal Bureau of Investigation)..”
“Masha Allah..!³ Ubangiji yayi muku kyakykyawan jagoranci.”
“Ameen” ya amsa a sanyaye dan shi har ga Allah bai shiryawa zama a k’asar ba,duka tunaninsa akan zai juyo 9ja ne a kwanakin,sai dai yadda yaji Dad yana farin ciki dole jikinsa ya sake yin sanyi
“Shi kenan kace mu da kai yanzun sai da ziyara ko..??”
Daddy yayi furucin cikin yanayin barkwanci,murmusawa yayi bisa dole
“Haka dai suke nufi Dad,,amma..!”
Sai kuma yayi shiru ya kasa k’arasawa dan yasan muddin ya fad’i abunda yake zuciyarsa yanzun Daddy zai rufe shi da fad’a,shi kuma abunda yak’i jini kenan,shi yasa ma yayi shirun
“Amma mene..!? Naji kayi shiru baka k’arasa ba.”
“Nothing Dad,,buh dama zance ne a gaida min kowa..”
Murmushi Daddy yayi sannan suka yi sallama…..