ALKAWARIN JINI CHAPTER 8 BY _HAWWA MUH’D USMAN

ALKAWARIN JINI CHAPTER 8 BY _HAWWA MUH’D USMAN

                     Www.bankinhausanovels.com.ng 

Can k’asan ranta ta yiwa kanta tambayar,buh babu wani a kusa da ita da yake jinta bare ya fidda ita daga duhun data shiga,,jin yadda Inna tayi shiru take ya haddasawa Sabina mummunar fad’uwar gaba mai tsanani,still duk da hakan ta mak’alawa ranta dauriya gami da k’arfin hali,yadda Inna tayi zugum tana kallonta ba tare data ce mata komai ba yasa jikinta sake yin sanyi,a hankali ta sake d’ago kanta ta kalli Innar muryarta cike da fargaba

    “Inna..! Dan Allah kiyi hak’uri,, wollahi ban san ranki zai b’aci akan maganar nan ba,tun farko ma da ban fara bada takarduna ba,,dama ni ban riga na sawa raina zanje ba,kawai dai dalilin da yasa na kai takardun ina da sa rai ne akan ko da ban samu an tura ni wata k’asar ba,ace na samu dama gwamnati ta d’auki nauyin karatuna a cikin k’asata,kinga kenan zanci gaba da zama tare da ku ba tare da fargabar wani abu zai faru da ni ba,,nd kuma hankalinku zaifi kwanciya akan ace nayi nisa.!”+

   “Waye yace miki baza mu amince ba..? Mamana karatu a duk inda kake sunan shi karatu,imma a cikin k’asa ko a wajenta duka d’aya ne,,a duk inda kake Allah shi yake karewa kuma yake tsarewa,dabarar mutum ko k’arfinsa bai isa ya hana Allah ikonsa ba,tsakaninmu da ke addu’ah ce da fatan Allah ya baki ikon kiyaye dokokinsa akanki.. Sabnan tarbiyyar da muka yi shekaru muna gina rayuwarki akai,muna fatan babu wani kyale²n duniya da zai rud’e ki har ya lalata mana ita,,in dan Allah ya tsara tafiyarki mu bamu isa mu hana hakan kasancewa ba,,kada kiyi tunanin baza mu iya yarje miki tafiya ba tare damu ba,a duk inda kike addu’ar mu zata ci gaba da riskarki,mun yarda dake kamar yadda muka tabbatarwa kawunanmu baza ki tab’a bamu kunya ba..Idan wannan damar ta samu muma masu yin alfahari ne da duk abunda zaki zama a nan gaba,,kiyi tafiyarki kinji ko,,kada ki ce saboda wani dalili zaki fasa,da yardar Allah zaki kasance cikin masu nasara..!”

     Kuka ne ya fara taho mata da sauri ta sakko daga gefen rijiya tayi zaman dirshen a k’asa

   “Na gode Innata,,Ubangiji ya dubi bayanku,,in sha Allah kamar yadda kuka d’auki yarda kuka bani,da yardar Allah ba zan tab’a baku kunya ba.. Zan kasance mai kulawa,tare da takatsantsan da duk inda na samu kaina..”

   “Allahu ya baki iko.. Ya kuma karemin ke a duk inda kike..”

  

   “Ameen Innata.. Ina rok’on ubangiji yayi muku tsayin rai,,domin kuyi alfari da samuna matsayin y’a..”

    “To Ubangiji ya amince..”

   Da “ameen” ta amsa sannan ta mik’e daga inda take zaune ta koma saman gefen rijiya tana sharce hawayenta,sauri² tayi ta d’aura alwala,sannan ta nufi hanyar d’aki.

      Duka da yin maganar kwanaki biyu,gwamnati ta fara neman duk wad’anda suka kai takardunsu domin tantancewa,kasancewar Sabina bata saba sauraron radio ba yasa ko da aka sabar sai bata samu labarin ba,,yadda tak’i jinin sauraren radio yasa a mafi yawan lokaci ko Baba ya kunna matuk’ar tana zaune barin wajen take,shi yasa sai bata sani ba,Inna kuma ko da taji lokacin da Baba ya kunna radio dare ya riga ya fara nisa,nd lokacin tana da yak’inin a Sabina ta jima da yin bacci,shi yasa ma ko tunanin sanar da ita tun a daren bata yi ba,ta bari akan zuwa da safe suyi maganar,,lokacin bayan sun gama sauraren labarai,Baba yana shirin kwanciya Inna ta kalle shi,duk da tana fargabar fad’a masa,amma wani sashi daga zuciyarta yana fad’a mata ta sanar masa,ba tare data yi jinkiri ba tayi amfani da damar data samu tayi masa bayanin duk abunda yake faruwa,,da fari an so kai ruwa rana dan Babah,dan ya gwada k’in amincewarsa da tafiyar Sabina wata k’asa da sunan karatu,,amma ko da Inna ta fayyace masa yadda suka yi da Baffanta,sai yayi shiru bai sake yin magana ba har tsayin wani lokaci,,Inna kuwa ko da taga haka gaba d’aya cikin zuciyarta sai taci gaba da addu’ah akan Allah yasa kada ya kafe akan maganar da yayi na farko,,tana cikin tunanin maganganun baffa,ta jiyo maganarsa yana amsawa akan ta fara zuwa goben taji kiran da ake musun,zuwa dare idan ya dawo zai zauna dasu duka bayan yayi shawara akan tafiyar ko akasin haka,,sosai Inna ta fara murna bcos ta san tunda yayi wannan maganar baza’a sha wahala ba sosai gurin amincewarsa,wannan dalilin yasa ta k’udurce jajircewa wajen ci gaba da addu’ah har Allah yasa ya amince.

      Ga Baba kuwa deeply tunda ta sanar dashi yake sak’a abubuwa da dama akan maganar,buh abunda yafi kwanta masa a rai gane da naganar shi ne furucin baffa,kan haka shima ya k’udurce a ransa zai jajirce yayi istikara domin nema musu mafi alkhairin zab’i agurin ubangiji,wannan yasa shi jinkirtawa bai riga ya yanke hukunci kai tsaye ba.

     Washe gari da safe tana kwance tana bacci Inna ta lek’o d’akin da niyyar sanar da ita abunda ke faruwa,tana shigowa ta tarar da ita kamar yadda tayi zato,tashinta ta fara yi cikin farin ciki ta bata umarnin tayi maza ta shirya,kallon Inna ta tsaya yi,tunani daban² suna kawo mata farmaki a rai

   “Mamana lafiya kike min irin wannan kallon..?”

    A hankali ta janye idanunta tana kallon gefe

    “Inna ina zanje da wannan safiya kike cewa na shirya..??”

    Murmushi Inna tayi mata mai kyau

     “Ya Allah..! Ashe fa baki san da batun ba ko..? To maza dai kiyi sauri kada lokaci ya tafi,ana can ana neman ku..”

   

    “Inna neman mufa kika ce..?? Waye yake neman namu..??”

     Lokacin har Inna ta juya zata fita ta dawo inda ta barta tsaye,hannunta ta rik’o sosai suka zauna a gefen k’atuwar katifarta da Baba ya siya mata tun bayan fara aikinsa a wani textile company

     “Rannan ba kince min kinje kai takardu ba..?? Kuma har muka yi magana dake..?”

   

     “Ehh! Inna.. Amma ai..!”

   

      “Ba sai kince komai ba Mamana,,kamar yadda na fad’a ne yanzun kiyi maza ki shirya sai kije kiji kiran da ake muku ko..??

   

   “Kiyi hak’uri Inna,,ba sai na koma ba,ni dai tuni na hak’ura,,gashi Baba bai sani ba har yanzun,shi yasa duk jikina yayi sanyi da al’amarin.. Ina tunanin kawai na fasa zuwan..!”

   “Kul..! Na sake ji kinyi irin wannan maganar,tafiya idan har Allah ya nufa babu fashi zaki je da yardarsa,,toma banda abunki tunda har mu da muke matsayin mahaifanki kike fargabar zamu k’i amincewa ya zama mun amince,mene ne dalilin da zaisa kiji kin fasa..!?”

  Saurin kallon Inna tayi baki bud’e da mugun mamaki

   “Da gaske Inna.. Yanzun kina nufin Baba ma ya amince min.!?”

     “K’warai kuwa,,ya amince..”

    Tsantsar mamakin yadda akayi Baba yayi saurin amincewa ne yasa ta rik’e Inna ta k’ank’ame,fuskarta cike da fara’ar da bata san ta yadda zata misalta ba ta fara jerowa Inna surutu

  “Wollahi Inna duka fargabata da damuwa akan amincewar Baba ne,,nasan ba lallai ya yarda naje wata k’asar ba,,shi yasa tun farko na kasa sanar masa..”

   “To ai kinji yanzun na fad’a miki ya amince,,saboda haka sai kiyi maza ki tashi kafin ki makara kuma ki makarar damu,,daga yau in sha Allah babu sauran fargaba.. Ayi maza a shirya a tafi..”

   Murmushi tayi ma Inna cikin sauri ta mik’e tabi ta a baya

   “Ai Inna yanzunma kuwa zanyi sauri na tafi kada na b’ata lokaci..”

    In less than 1 hour ta gama shiryawa,file d’in takardunta da duk abunda tasan zata tafi dashi Inna ta tattara mata guri guda,tana kammalawa ta d’auka sannan ta yima Inna sallama,banda addu’ah babu abunda Inna take yi mata.

   Tunda ta fita daga gida har ta isa cikin *AUDU BAK’O SECRETARIAT* bata fasa kiran sunan Allah ba da addu’o’i,,da tambaya da komai ta samu ta iso wanjen da aka ce su je d’in,lokacin data iso ta iske jama’a sosai,amma yawansu sam bai bata tsoro ba,duka addu’ar ta har lokacin bai wuce ace tayi nasara ba,sai da suka wuce awa guda tsaitsaye suna jira kafin motocin gidan gwamnati suka fara isowa,bayan anyi musu bayani da abunda ake buk’ata suyi,sannan aka fara raba musu forms da zasu cike,,then kuma aka sake karb’ar takardunsu da passport guda biyu,tana gama cikewa ta mayarwa da secretary d’in gidan gwamnati,bayan kowa ya mayar da form d’in da aka bashi aka sake musu bayanin daga yanzun zuwa k’arshen sati zasu iya jin kira,saboda haka sai kowa ya kasance ya fara shiri,,godiya suka yi duka after an tab’a siyasa aka sallame su,tunda ta fito take jin zuciyarta cike taf da farin ciki tana tafe tana ci gaba da addu’ah har ta fito titi,napep ta samu da zai mai da ita gida,tana dawowa ta shiga bawa Inna labarin abunda aka shaida musu,daga wannan lokavin bata sake zama ba ta zage taci gaba da addu’ah,babu dare babu rana addu’ah take all the day akan Allah ya basu sa’a,,Inna ma a gefe guda ba’a barta baya ba ta dage sai addu’o’i take musu.

   Batun Baba kuwa tunda ya bada izinin taje taji kiran yayi shiru bai sake magana ba,da dare bayan ya dawo ya kirata,tambayoyi yayi mata cikin nutsuwarta tayi masa bayani yadda ya kamata,shima ,addu’ar dai yayi dan tun a daren da Inna ta sanar masa batun ya fara istikara,haka nan kuma tunda ya fara addu’ar neman zab’in Allah sai yaji al’amarin ya shiga zuciyarsa.

*NEW YORK STATE..*

Zuwa yanzun kam Hammad yana aiki ne kawai amma badon ra’ayin kansa ba,,buh still duk da irin nasarorin da yake samu ta fannin aikin ko kad’an baya jin dad’in zamansa a k’asar haka duka baya kallonsu a matsayin abun alfahari,kawai dai yana rayuwa ne saboda yadda Daddy yake son zaman nasa a can amma ruhinsa tuni ya jima da barinsa a 9ja,,a wasu lokutan kuwa idan tsumin soyayya ya tayar masa sai dai ya tafi park yayi zamansa,ranar yini zaiyi baya gida,sai yaga dare yayi ko ya d’an ji dama sannan zai kamo hanya ya dawo.

Shirye²n zuwansa 9ja kuwa a kullum sake k’aruwa yake,sai dai aiki da a kullum yake sake toshe masa k’ofofin damar da yake samu yake,wannan dalilin yasa babu halin ya motsa,bcos yasan yanzun za’a fara nemansa,a wasu lokutan kuwa saboda haushin da yake ji idan aka kirashi cikin takaici zai amsa kiran bcos har yanzun aikin bawai ya gama shiga ransa ba ne.

Sultan da Sadeeq kuwa cikin wannan d’an tsukin idan har ba ranar aiki bane,zaka same su tare,amintar dake tsakaninsu kamar dama can tare suka fara zuwa k’asar,,cikin rayuwarsu a kullum canji ta ko ina a y’an wattani sai sake samuwa yake,yayin da suke ta yin sama a kullum ta fannin aiki.

*NIGERIA..*

     Tana kwance kanta a saman cinyar Inna suna fira,while Inna nayi mata tsifar kai,,a hankali y’ar Nokia Inna dake gefen kanta tayi k’ara alamun shigowar sak’o,kamar baza ta kula ba sai Inna ta d’auka ta mik’a mata

  “Mamana! Duba min nan ki gani,sak’on mene ne aka turo..?”

  

  “Toh.!” Tace then kuma ta ansa,sai data fara cire key sannan ta fara dubawa,cikin ihun murna ta fara kwararo addu’ah

   “Alhamdulillahillaziiy bii ni’imatihi tatimmus salihaat..!”

    Tana kaiwa k’arshe ta janyo Head tie d’inta ta yafa a jikinta,sannan tayi sujuda hawayen farin ciki na sakkowa saman fuskarta

    “Mamana..! Mene ne..??”

   Inna ta tambaya tana jiran taji k’arin bayani,ta jima tana addu’ah kafin ta d’ago tana maimaita

    “Alhamdulillah ya Allah..! Alhamdulillah.!³”

   “Wai Mamana ki fad’a min abunda yake faruwa kink’i..?”

   Sai data gama addu’o’in sannan ta kalli  Inna fuskarta har lokacin cike da hawaye

“Inna..! Tabbas Allah maji rok’on bayinsa ne..”

“Haka ne Mamana.. Amma me ya faru ne..?? Sanar dani..”

“Inna batun tafiya karatu ne ya taso,sunce zuwa ranar alhamis mu kasance cikin shiri..”

 

  “Alhamdulillah alaa kulli halin..! Lokaci yayi kenan..?”

“Ehh! Inna..”

  “Toh..! Mamana,Ubangiji ya bada sa’a ya kare ki sharrin mutum da aljan.. Ya rufe idanun mak’iya akanki..”

  Nasiha sosai Inna tayi mata mai ratsa zuciya a lokacin kamar yaune zata bar k’asar,, a ranar kuwa saboda tsananin farin ciki kasa bacci duka gidan suka yi,washe gari da yake ranar talata ne 2 days before tafiyarsu Inna tasa ta shiryawa taje gurin baffanta,da yamma sai tabi motar da zai kaita garin had’ejia (GINSAU BIRNIN DOKI),,duka kwananta d’aya a garin ta juyo cike da alkhairin baffa gare ta.

 

Babanta ma yayi mata y’an siye² dai² k’arfinsa ba tare daya zafafa ba dan har waya ya siya mata da zasu dunga jin yadda take,,ta b’angaren Inna ma ta d’an yi mata siyayya dai² aljihunta,,tun da batun tafiyar ya taso,gaba d’aya suka fara alhini,bacci kuwa sai dai da yake ana cewa b’arawo ne,amma sam basa wani samun isasshen bacci,,a daren data dawo daga had’ejia alhinin tafiyarta yaci gaba da k’aruwa,ita tana jin babu dad’i saboda rabuwar da zata yi da iyayenta a dai² lokacin da bata zata ba,suma suna alhinin tafiyar nata,a haka dai da taimakon Inna da Baba ta samu ta harhad’a y’an kayan tafiyarta.

Washe gari da safe misalin karfe 7:00am suka d’unguma gaba d’aya da niyyan yi mata rakiya zuwa airport,kasancewar tun dare suka gama sallama,amma ko da suka fito daga gida suna tafe a hanya cikin napep sai da Baba ya sake mata nasiha sosai,,Inna kuwa tunda suka taho da tayi shiru bata k’ara magana ba har suka iso airport,,,a gabansu akayi mata komai,har zuwa lokacin da aka fara kiransu,,cikin rashin kuzari ta mik’e tana musu kallon bankwana,sabbin luggage’s d’inta da Baba ya siya mata akan tafiyar ta bi da kallo sannan ta sunkuyar da kanta hawaye yana bin kumatunta,juyawa tayi ta fara tafiya bayan sunyi sallama,jikinta duka a sanyaye taci gaba da jan akwatinta hawaye yana ci gaba da sakko mata,har ta d’anyi nisa dasu sai ta juyo a hankali tana kallonsu,su kansu jikinsu duka a lokacin ya sake yin mugun sanyi bare kuma itan da take jin kamar ta fasa,sakin jakunkunan tayi a k’asa ta dawo inda suke da gudun ta,tana zuwa ta rungume su tana sakin kuka mai sauti.

     Daga ita har Inna zuciyoyinsu sun gama karyewa,banda kuka babu abunda suke,tun baba yana lallashinsu har sai da suka sa ya fara fusata,da kyar da kuma fad’a² nasiha² yayi k’arfin halin rarrashinsu,shima d’in sai daya bud’e musu ido sosai,bcos da fari hak’uri yayi ta basu suka k’i sauraronsa sai da suka ga yayi fushi ne sannan suka hak’uran,,sallama ta sake yi musu sannan ta juya a hankali tana tafiya daga nan bata sake dawowa ba kuma bata sake waiwaye ba kai tsaye ta wuce abunta tana goge hawayen dake sakko mata…..

    Sai data b’acewa ganinsu sannan suka ja k’afafunsu da sanyayyen jiki,cike da niyyar komawa gida,yayin da zuciyoyinsu suka cika da damuwar rabuwa da ita,,suna fitowa daga airport cab suka d’auka da zai maida su gida,tunda suka kamo hamya duka suka yi shiru ba tare da wani yayi magana ba har suka k’araso gida,haka nan tunda suka dawo suke sake ci gaba da binta da addu’o’in fatan sauka lafiya.

    Dai² lokacin data juya tafiya kawai take amma duk wani k’warin guiwarta yana tare da mahaifanta,tabbas yadda take ganin damuwa shimfid’e saman fuskokinsu,yana k’ara tafiyar mata da sauran kuzarinta,sosai hakan yasa ta fara ji aranta ba don tafiyar da zata yi saboda ci gabansu bane gaba d’aya lallai ne da babu wani dalilin da zaisa ta tafi ta barsu da kewarta,,wannan dalilin yasa tunda ta juya taji bazata iya sake juyawa ta kallesu ba,bcos tana tana ji a ranta yin hakan a gareta yana dai² ne da rugujewar muradinta.

     Har ta shiga cikin jirgi bata daina hawaye ba haka nan bata fasa addu’ah ba,a hakan ta fara kokarin duba seat d’inta,lokacin da taga seat d’inta daga gefen window hamdala tayi sannan ta wuce ta zauna,a hankali kuma sai ta lumshe idanunta,karo na farko kenan data tsinci kanta a jirgi,sai duk take jin wani iri buh ba lallaine mutanen dake cikin gurin suyi saurin fahimta ba,bcos kowa aikin gabansa yake,kallon mutane ta d’anyi sama² taga yadda suke ta gaishe² da juna abunsu kowa yana ta murna,wasu kuma data kallesu sai taga kamar sun san juna,,tana zaune tayi shiru bcos har lokacin akwai wad’anda basu gama shigowa ba nd babu wanda ta gani data sani,kowa a gurina bak’on fuska ne,yasa ta d’auko y’ar wayarta kirar techno camon ta shiga ciki da d’an dubawa saboda ba komai ta sani ba,kasancewar wannan shi ne karo na farko data fara rik’e waya,camera ta shiga kamar yadda taga mutane suna ta d’aukan photo,da nufin d’aukan kanta saboda ta ajiye tarihi,buh bata san yadda za tayi ta d’auka d’in ba,jigum tayi tana kallon mutane,zuwa wani lokacin kuma ta sake d’ago wayar tana kallo,so take ta gano inda damuwar yake amma abu ya gagari saninta

       “Lemme help u..!”

     Sanyayyar muryar ta ambata,a hankali ta d’ago kyawawan idanunta ta sauke su akan kyawawan y’an matan biyu dake tsaye suna mata murmushi,murmushin itama tayi musu sannan ta d’aga hannunta biyu 🙏

       “Assalam alaikum warahmatullah.!”

   Fahimtar abunda take nufi yasa su yin murmushi sannan suka yi mata sallama had’e da bata hak’uri,tana amsawa tana musu murmushin ta mai kyau,a mutunce suka gaisa da su sannan d’ayar data fara magana ta karb’i phone d’in nata ta fara yi mata pictures masu kyau,tana ganawa ta mik’a mata wayar da fad’in

    “Gashi ko..? Amma fa gaskiya sunyi kyau sosai..”

  D’ayar da suka zo tare itama tayi murmushi

    “Haba dear kema banda ke,ai itan mai kyau ce,so kinga kuwa pic d’inma dole su yi kyau.. Bcos kyau ya had’u da kyau.. So.! What will it be kenan..??”

     

         “Most beautiful..!”

    Dariya suka yi dukansu biyu,sannan Sabina ta karb’i phone d’inta da take mik’a mata tana ganin pictures d’inta,,sanye take cikin Arabian gown black colour mai adon red a jiki,yadda tayi rolling vail d’in ba k’aramin kyau yayi mata ba,kayan sunyi matuk’ar dacewa da jikinta tamkar dama can daga united Arab ta fito,musamman kuma daya kasance ta k’awata y’ar fuskarta da light make-up,powder kawai da tasa sai lip gloss da d’an kajol data zizarawa idanunta,amma shi ne suke ta zuzuta kyaunta haka,ita har mamaki suka so bata dan yadda suke ta kod’ata,sai dai bata ce komai ba,tana gama kallon pictures d’in ta d’ago tana murmushi tace

        “Thanks Sis..”

  

  “Never mind princesse.. Buh can we be friends..!?”

       “Why not..?”

  A kusa da ita suka zauna suna fad’in

      “Thanks once again..”

      “U are welcome..”

    Still ta farkon ta sake cewa

    “Am BILKISU ALIYU (BADRA).. Ke fa.??”

  Sai da tayi murmushi ta amsa da

   “Hafsat Al’amin Usman..buh u can call me *SABINA..”*

      “Wahh.! What a nice name..”

      Murmushi ta sake yi tana fad’in

  “Thank u,,buh friend d’inki fa..??”

      Itama Sabinar ta tambaya,murmushi d’ayar tayi mata tana fad’in

    “Ismiy.! JANNAT MUKHTAR BABANGIDA..”

    Dariya suka yi jin ta fad’a da larabci,Sabina cikin tsokana tace

      “Gashi kuma ni anyi rashin sa’a..”

    Da sauri Jannat ta tari numfashinta

      “Ohh.! Friend na mene ne fa..??”

   

     “Bana jin Arab..”

 

   “Ahh haba.. Yanzun waye zai kalle ki ya yarda bakya ji..??”

   “Serious ban san mene kika fad’a ba,,ki fassara min…”

  

   “Uhmm! I think dai ba ni kike fad’awa ba..?”

  Dariya suka yi daga haka suka ci gaba da hira kamar sun jima tare,,suna ta fira Badra ta kalli Sabina

   “Princess.! Na tambaye ki wani abu mana..”

       “Allah yasa na sani..”

     Za tayi magana kenan staff d’in jirgi suka fara yiwa wad’anda ke d’auke²n photo magana da su kashe wayoyi,,wayarta ta d’auko tayi switching nata off,sannan ta mayar cikin handbag d’inta,,taimakonta d’aya a lokacin duk da bata tab’a shiga jirgi ba ta kula da yadda y’an matan suka d’aura seatbelt,nan itama tayi k’ok’arin d’aurawa,a hankali jirgi ya fara k’ok’arin tashi,idanunta ta mayar ta rufe bakinta d’auke da addu’ah har suka lula cikin sararin samaniya.

               _(Safe trip our princess).._

*NEW YORK CITY..*

      A gaggauce ya shirya kasancewar daren jiya bai samu isashen bacci ba,saboda damuwar daya sawa ransa,yana gama shirin ko tsayawa baiyi ba ya fito da sassarfa bcos yana daf da makara a aiki,,har ya fito zai shiga mota ya tuna wayoyinsa daya bari,siririn tsaki yaja before ya sake komawa,yana shiga ya tarar da wayan da alamun kira ya katse,bai tsaya duba waye ya kira shi ba ya d’auka yayi waje,,har yayi nisa sosai a hanya kiran Sultan ya sake shigowa,hands free ya maida ita cikin isa da mulki yana fad’in

      “Dude.. Ya aikin..!?”

   

      “Normal man.. Buh ka tayani murna,,yau na shiga aka bani takardar canjin gurin aiki.. Yanzun hakama ina kan shiryawa zan baro Las Vegas,,dama duk bana jin dad’i da nayi nisa da ku,ni kad’ai kamar bani da relatives..”

   

      “Ina suka maida ka kenan..?”

   

       “Nan kusa daku ne..”

   

      “Uhhuumm..! Kaji dad’in ka,dama yanda kake dawowa ka tare a nan gara da suka maka canjin kaga zirga² ya ragu,,kaima ka samu ka maida hankali sosai akan aikin..”

   

     “Nufinka dai kace bana bawa aikina muhimmanci ko..??”

   

      “Nop.! Buh kusan hakan nake nufi..”

   

      “Ok.. Good,,idan na iso zan nemeka..”

   

       “Ok.. Sai naji kan.”

    Suna gama wayan ya sake bawa motan wuta dan yana son ya k’arasa before 8 tayi masa,,har lokacin daya isa gurin aikinsa sannan ya sassauta gudun sa.

   

*PENNSYLVANIA CITY (U.S.A).*

      Cikin katafaren filin tashi da saukar jirage na *Philadelphia International Airport* jirginsu SABINA yayi dirar mikiya,a kuma cikin garin na Pennsylvania,,zuwa lokacin tuni jikin kowa dake a cikin jirgin ya gama yin tilis dan gajiyar zama,saboda tafiya da suka kwaso mai d’an karen nisa from 9ja to U.S hours d’in akwai nisa,,jiki duk yayi tsami masu bacci sunyi sun gaji,haka masu hira ma sunyi sun bari,yayin da kowa ka duba fuskarsa ya gama k’osawa jira kawai yake a iso.

   Lokacin da aka fara sanarwar mintunan da suka rage a sauka kada kuso ganin k’auyenci a gurin mutanenmu,tun ana sama kafin jirgi ya gama sauka,mazauna gefen windows suke lek’en k’asa,hatta da na tsakiya suma ba’a barsu a baya ba,,k’asar kam akwai ci gaba sosai tun a haka da muke hangota,a raina nace wani abun kam sai ma mun sauka,,har jirgi ya sauka suka fara fitowa basu fasa nuna hali ba,kowa sai bud’e baki yake anata kalle² munga tsari ba kamar mu nan ba,duk dai nasan 9ja ma ba baya ba akan wasu k’asashen duk da yadda na raina ci gabanmu da naga U.S nasan muma a aljannar wasu muke hakan sai yasa ni godewa Allah bisa ni’imar da yayi a gare mu,,a nan suka iske wakilan gidan gwamnati da zasu jagoranci ragamar nemawa d’aliban admission a mabambanta schoolsa cikin k’asar da zasu yi karatu,bayan kowa ya shiga mota aka sake d’aukan hanyar da zai kai su *VILLANOVA UNIVERSITY* dan su Sabina kam can aka nema musu.

      Kowa inda yake so nan aka ajiye shi,Sabina kam da yake dama ita b’angaren *LAW* take so,saboda shi ne muradin ranta,,sai aka yi sa’a a nan d’inma suka sake had’uwa da k’awayenta na cikin jirgi (Badra da Jannat),cos dukansu a k’ark’ashin school d’aya ne zasu yi karatu,ma’ana dai *villanova school of law* lamarin sosai yayi musu dad’i daya kasance suna cikin faculty d’aya nd kuma dama tun kafin su baro 9ja zumunci ya fara k’ulluwa a tsakaninsu.

    An raba kowa zuwa school d’insa,yayin da ya kasance musu zasu zauna a hostel,,wajen rabon d’akunan kwana sai ya zama an kusa samun sab’ani,inda aka so rabasu da juna,,Jannat na zaune kan seat Badra ta sameta sai had’e rai take

      “Heeyy lady..! What’s up..?? Naga kina had’e rai,,mene aka miki ne..??”

      D’agowa tayi ta kalleta fuska babu walwala

     “Ba d’aki d’aya zan zauna daku ba..”

     Teasingly Badra ta ci gaba da kallonta

      “So..! Sai kuma aka yi yaya..??”

   

      “I don’t wanna leave ur side..!*

      Dariya ta kyalkyale da shi tana fad’in

      “Kaii..Lady kina da ban dariya.. Me yasa bakiyi musu complaining ba to..??”

   

     “Haba mana ki gane abunda yake faruwa,ni ban san mene ne zance ayi saurin canjani zuwa room naku ba..”

   

     “Good.. Kinga kenan zaki zauna a duk inda aka kaiki tunda baki sani ba..”

   

      “Ohh! Dear.. Kizo muje nasan zaki yimin k’ok’ari ai,Allah bana son wancan room d’in duka fa ba y’an nahiyarmu bane..”

   

      “So what..? Ba sai ki zauna tare da su ba,tunda ke baki da baki..”

   

    “Please dear.. Muje to tare kinji..?”

   Kallonta tayi from head to toe ta tab’e baki,Sabina dake zaune gefensu tana kallon damar su yanayin yadda Badra tayi sai ya fara k’ok’arin tuna mata wani fuska,buh saboda ta d’an rud’e kad’an a time d’in sai yasa bata yi saurin ganowa ba

    “Kinga idanma zaki jene ki dawo to,if not kuma mu zamu yi tafiyarmu..”

  

    “Haba friend ke kuwa ai ya kamata ki rakata,, babu dad’i ace kunzo tare wajen kwananku ya bambanta.. Ko kema baza ki so hakan ba..”

      Sabina da tun da suke magana bata ce dasu komai ba ta fad’a tana kallon Badra

    “Ni kam babu inda zani,ko ina sai dai ni na zama bakinta,idan bata iyawa ta zauna da sababbin fuska..”

   

      “Ok.. Shi kenan,muje friend na raka ki kinji..”

     Sabina ta fad’a tana mik’ewa tsaye,fuskar Jannat da fara’a ta rungume Sabina tana cewa

      “Thank u.! thank u³.!! Princess.”

     Murmushi tayi suka kama hanya su biyun,,basu jima sosai ba suka dawo suna tafe suna hira sama² har suka k’araso inda suka barta,kallonsu tayi ta ce

       “An canja d’in..!?”

    Harararta Jannat tayi tana cewa

       “Ba’a sani ba..!”

    Not minded ta ce

       “Ok.. Let’s go ko..?”

     Luggage’s d’insu duka suka ja daga nan suka kama hanyan hostel.

*NIGERIA..*

    Tunda Badra suka tashi akan idon Mamma,bayan ta dawo gida take ta k’ok’arin kiran line d’insa dan ta sanar da shi ya dunga sa ido akansu,buh bata samunsa,,a gefe guda kuma batun da Daddy yazo mata da shi wanda sam zuciyarta bata aminta da batun nasa ba,shi yasa take ta nemansa cikin kwanakin dan suyi maganar amma sam ta kasa samunsa.

     Har dare ya fara rabawa hankalinta yana kan taga ta same shi amma abu ya faskara,,bisa dole ta hak’ura,ko data duba time taga zuwa lokacin zaiyi ace su Badra sun sauka,sai tayi k’ok’arin kiran nata don taji ko sun isa lafiya,cikin sa’a nata line d’in tana gwada kiran ya shiga.

    Su kuwa a b’angaren bak’in k’asar turawan a dai² lokacin a nasu k’asar lokacin tsakar rana ne,tun da suka iso room kowa cikinsu sai hada²r shirya kayansa yake,kiran Mamma ne ya shigo wayarta a time d’in suna ta hayaniya ita da Jannat,special ring d’in dake tashi cikin wayar ya tabbatar mata da Mamma’nta ce take nemanta,tsalle tayi daga inda take ta rarumo wayarta,dai² lokacin da take d’aukan wayan da fad’in

    “Amincin Allah ya tabbata ga mahaifiyar da tafi kowace irin uwa a duniyata..!”

    Murmushin jin dad’i Mamma tayi sannan ta amsa da

  “My little kiddo,,fatan kun sauka lafiya..?”

    “Lafiya k’alau Mammana..!”

   Sunyi hira sosai da Mamma,dukansu suna cikin farin ciki da kasancewar kowannensu cikin aminci sannan suka yi sallama,har Mamma zata ajiye wayan Badra cikin ihu ta ce

   “Mamma..! Pleasee! Kada ki ajiye waya,,ga sabuwar k’awata da nayi ku gaisa.. Mah! U know what..?”

    “Ohhh.! My Kiddo yanzun daga isarku har kin fara k’awaye..??”

   

      “No.. Mah.! Wannan she’s so special,, tun a jirgi muka had’u,kuma itama y’ar Kano ce..”

   

      “Ok.. Toh dai ku kula,ba kowa nake so kuyi abota da shi ba,,kinji ko baby..?”

   

     “Toh! Mah,,in sha Allah,zamu kiyaye..”

   

      “Yawwa to bani itan mu gaisa..”

      Tana fad’in haka,Badra ta juyo inda su Sabina suke kowa da kaya a gabansa

      “Hey..! Princess.. Ga Mamma na zaku gaisa..”

     D’agowa Jannat tayi saurin yi daga kan kayanta tana fad’in

      “Kaji rinto wai Mammanki,, Mamman Yah Hammad dai..”

     B’ata fuska Badra tayi

     “Allah babu wani nan,ai kowa yasan Mamma tawa ce,kuma nima tata ce..”

   

     “Noo.! Madam da dai kince ke ta Daddy ce,zan yarda amma idan kince ke ta Mamma ce,fashi kawai zaki yiwa Yah Hammad..”

   

      “Ke kika sani.. Ni ban san wannan ba..”

      Ta mik’awa Sabina waya ta juya daga kusa dasu,,tunda ta karb’i wayan haka nan jikinta yake wani irin karkarwa kamar wacce ta kama wuta,muryarta tana b’ari tasa wayar a kunnenta tayi sallama,,a ladabce ta gaida Mamma,itanma ta amsa mata cikin sakin fuska da mutuntawa,har suka yi sallama sannan Mamma tace ta bawa Jannat waya jikinta bai daina rawa ba,tunda ta mik’a mata haka nan muryar Mamma sai amsa kuwa yake mata cikin kunne,tunaninta,kwakwalwarta da zuciyarta gaba d’aya suka tafi yajin aikin son tuno mata da muryan waye magabar wannan matar suke yi mata yanayi.

     Bayan Mamma ta gama waya dasu tana cikin farin ciki sosai,haka nan itama tunda ta tuno shirmen Badra sai taji muryar yarinyar da suka yi magana ya tsaya mata a zuciya,tunani daban² suka fara zuwa mata a rai sai dai ta kasa bambance mene ne hakan yake nufi.

   

*NEW YORK CITY..*

     Tunda ya shigo gidan a matuk’ar gajiye yake,cikin kwanakin gaba d’aya nutsuwar sa bata jikinsa saboda wani mugun bincike da suke kanyi na wani aikin da suke ta bincikensa.

   Yana shigowa ya kunna wutar gidan sannan ya ajiye suit d’insa saman armchair ya nufi hanyar bedroom d’insa,,gidan flat ne sai dai tsarinsa akwai masifar kyau dan ya matuk’ar had’uwa kasancewar ginin turai ne,komai yana nan a muhallinsa,,bai d’auki dogon lokaci ba ya fito sanye cikin wani black d’in 3quarter sai short-sleeved t-shirt dake jikinsa,a ta gaban rigar anyi rubutu da white nd red colour da manyan harufa, *JUST DO IT* shi ne rubutun dake gaban rigar ya nuna,sai tick daya ratsa tsakiyar rubutu ma’ana btwn just nd do it,sosai yayi kyau a cikin kayan musamman daya kasancewar fari tas,,k’afarsa sanye cikin benassi slide sandals na maza yake takowa,kai tsaye ya wuce hanyan kitchen zuciyansa cike da nufin nemawa kansa abunda zai d’umama uwar hanjinsa.

     Coffee kad’ai yayi ma kansa preparing sannan ya fito hannunsa da cup yana tafe yana sipping,har ya dawo parlor inda ya bar laptop d’insa da wayoyinsa,saman mini table dake gurin ya d’ora cup d’in sannan yayi operating na computer yana sake zurfafa bincikensa kan evidence da yake tarawa,gefe guda kuma yana ci gaba da had’iyan coffee har ya shanye tas,sannan ya sake maida hankali sosai kan aikin da yake yi d’in.

      A hankali door bell yayi k’ara,d’agowa yayi da sauri ya kalli k’ofar kafin ya mik’e ya nufi k’ofan da shirin bud’ewa,,Sultan ya gani tsaye da uban luggage’s d’insa,a hankali ya kauce ya bashi hanya,murmushi Sultan yayi sannan ya wuce ciki yana yin sallama,k’asa² ya amsa sannan ya sake binsa while yana tambayarsa bcos yana mamakin abunda ya gani

      “Dude.. Wai dama nan suka dawo da kai..??”

   Yana murmushi yake fad’in

  “Ko kuma na nemi a dawo dani ba..!”

  Fuskarsa da mamaki fal samanta ya kalleshi

   “Ohh! Kai kace adawo da kai dama..??”

   “Ehh! Na gaji da zaman kad’aici ne,shi yasa na nemi transfer.”

  “Ok.. Amma ni d’azun ai ba haka ka sanar dani ba.”

   “Yanzun kuma na fad’a maka yadda akayi ai.”

   K’wafa Hammad yayi sannan ya nemi guri ya zauna ba tare daya sake yin magana ba yaci gaba da aikinsa,,kallon gurin Sultan yayi sannan ya sake kallon shi

   “Dude.. Wai babu wani abun ci ne a nan..?”

     “Gashi nan ka fad’a..”

     Slowly Sultan yayi tsaki sannan ya mik’e yayi hanyar fita,d’agowa yayi ya kalleshi sai dai bai ce masa komai ba har ya fice,shi kuma ya sake maida hankalinsa kan aikinsa.

   

*PENNSYLVANIA CITY..*

     Tana daga kwance saman gadonta wayarta a hannunta tana y’an tunanukanta,bacci ya fara kawo mata ziyara,dama a gajiye take sosai,hakan yasa sai ta yanke shawaran yin baccin ko yaya ne tasan zata ji dad’i,a gefenta Badra ta zauna

      “Princess..! Tashi muyi hira..”

  “Sorry friend,,am already falling a sleep.. Bazan iya wani hira ba yanzun,,idan nace zan takura kaiba kuma shirmen ne kawai zanta fad’a..”

“D’azun baki yi bacci ba ne..??”

“Yeah..! Ai bana iya bacci a abun hawa..”

  “Ok..! Yi baccin ki,,idan kin tashi ina da bashi akanki.. Kin yarda zaki biya..??”

Murmushi tayi mata idanunta a lumshen tace

“Yeah..! Na amince..”

  “Ok..! Shi kenan,a tashi lafiya..”

   Still ta sake yin murmushi sai dai bata ce komai ba saboda baccin da take ji,gashi zuwa lokacin har ya fara neman sa mata headache.

    Mintuna sha biyar tsakani tuni bacci ya d’auke ta,kallonta Badra tayi fuskarta da murmushi ta juya tana kallon Jannat

      “Dear.. Ki duba min nan..”

   Wayan dake hannunta ta k’awar gefe da fad’in

        “Mene ne..??”

 

    “Ohhh..! Ke matsalar ki bakya saurin gane magana dole sai an yi miki fashin baki..”

    Murmushi tayi cikin dariyar zolaya tace

      “Kamar ke ba.?”  

   Harararta tayi za tayi magana Jannat ta dire akan gado ta nufi hanyar toilet,k’wafa tayi cikin k’unk’uni tace

   “Zaki san dani kike,,kuma saina fad’awa Yah Sultan..”

Ita kam Jannat dariyama maganar ta bata,tana daga tsaye a bakin k’ofar toilet take fad’in

   “Ohoo! Dai nima zan fad’awa Yah Hammad ya rad’amin..”

  Jifanta tayi da flat sandal d’in k’afarta,suna cikin shirmen jifan juna akayi knocking k’ofar room d’in,a tare suka juya suna kallon k’ofar kafin su bada izinin shigowa…..      Sai da aka fara bud’e k’ofar d’akin,ko kafin mai shigowar ta bayyana sai data d’auki y’an mintuna sannan ta shigo cikin takun isa,kallon-kallo aka fara tsakaninsu da ita,ta d’auki lokaci tana kallonsu suma suna kallon ta,sannan tayi magana cikin wani yanayin da na kasa ganewa

      “Hello..!”

   Shi ne abunda ta fad’a,maimakon sallama da aka san duk wani musulmin k’warai da ita,daga haka bata sake cewa komai ba ta wuce tana jaye da luggage’s d’inta da backpack goye a both shoulders d’inta,wani irin kallon raini Badra ta jefeta da shi ta kama waist

     “Heeyy! Malama da Allah fita kiyi ma mutane cikakkiyar sallama,,ko an fad’a miki nan duka christians ne..? Zaki shigowa mutane guri da wani hello,,hello d’inki na banza,da kinsan baki yi ba ai kin shigo kai tsaye..!”

   Dakatawa tayi da tafiyar da take tana sakin luggage’s d’in,a hankali kuma ta waiwayo tana kallon Jannat data tsareta da ido,tunaninta duka a lokacin ya gama bata ita tayi maganar,muryan fad’a tayi wearing kan nata itama cikin masifa ta hayayyak’o mata kamar yadda taji anyi magana tun farko

    “Bazan yi ba d’in,, sallama ko..?? Haka naga daman yi idan zaku amsa ne ku amsa,if not kuma kuyi shiru,ba lallai ne sai kun amsa ba,,nd daga yanzun duk lokacin dana shigo zanyi abunda naga dama ne,sai inga ta tsiya,,tunda ba a kan mutum zan zauna ba,sai ku samin ido..”

     “Haka kika ce..??”

   Juyawa tayi saurin yi zuwa inda ta jiyo maganar sannaan ta furta

      “K’warai fa..”

   

    “Fita to.. Ba’a nan room d’in zaki zauna ba..”

     Kallon shek’ek’e ta yiwa Badra cike da rainin wayo tace

      “Allah ko..?? Kece zaki hana ni zaman,ko kuma kinga an kafe hakan a allon sanarwa ne..??”

   

     “Malama idan fa ba zaki mana sallama ba,wollah yanzun zamu watsaki waje da kayanki..”

    “Da gaske..??”

  

     “Ya isa haka Dear,,kyaleta kawai,bai kamata ma ace kin biye mata ba,duk da yin sallama ba wajibi bane,amma mu nan tunda ta shigo kallo d’aya zai bata amsar daga ina ne muka fito..”

    Jannat da tunda bak’uwar ta shigo bata ce komai ba ta tofa nata

      “Haba Lady..wannan ai iskanci ne ace mutumin da yake muslim,kuma cikaakken bahaushe ya shigowa mutane guri da wani hello,,ke dan Allah baki ji kunyar tozarta addininki bama..??”

   

     “Kamar yaya kenan..?? Kinga nifa bana son shishshigi,, daga zuwa na zaki fara kawon k’abli da ba’adi,rayuwa ne kowa da irin nasa,so kowa yayi abunda ke gabansa,ina ruwanki da rayuwata..??”

     Gyad’a kai Badra tayi cikin jin zafin maganar ta tace

      “Amma dai kinji kunya wollahi,indai haka wannan tsarin kika zab’ar ma rayuwarki,kina cikin wani hali,,a matsayinki na muslim,har ayi miki gyara,amma ki danne ki shigo da son rai..?? Idan baki sani ba zan sanar da ke,idan kuma mantawa kika yi ni zan tunantar dake,,Annabi (S.A.W) cewa yayi a hadis:”Baza ku shiga aljannah ba har sai kunyi imani,kuma baza kuyi imani ba har sai kun so juna..Shin bana nuna muku wani abu da idan kun yi shi zaku so juna ba.? Kin san mene ne yace..??”

     

    “Ku yad’a sallama a tsakaninku..”

      Duka suka kalli juna da mamakin amsawar da tayi,,jinjina kai Badra tayi sannan taci gaba

     “Sannan Ammar (R.A) yace:’abubuwa guda uku (3),wanda duk ya had’a su ya had’a imani..”

     Kafin ta sake yin magana ta karb’a mata

     “1-Mutum yayi adalci ga kansa,2-yad’a sallama a cikin jama’a,3-yin kyauta a cikin rashin wadata..”

   

    “Sannan an karb’o hadisi daga Abdullahi Ibn Umar (R.A) yace:’wani mutum ya tambayi manzon Allah (S.A.W) wane abu ne a cikin musulunci ya fi alheri..?”

     

    “Sai manzon Allah (S.A.W) yace:”Ka ciyar da abinci,sannan kuma ka yad’a sallama ga wanda ka sani da wanda baka sani ba..”

   Badra cikin tsananin mamakinta ta fara tafa hannayenta

    “Da kyau..! Wato da duk kin sani amma kika take..?? Shin mene ne fa’idar ki na shigowa ba tare da sallama ba.?? Kuma a mazaunin kina cikakkiyar musulma..??”

     Kallon Badra ta d’anyi sai kuma ta sauke dogon numfashi,da fari yadda taji Badran na fad’in zasu watsata waje da kayanta har ta fara hasala,sai dai jin ta fara kawo mata hadisai take yasa jikinta yayi wani irin mutuwa,kallonta ta sake yi muryar ta cike da sanyi ta furta

   “Am really sorry Sis.. Gaskiya ni kaina na ji kunyan abunda na aikata,buh na gode sosai da tunatarwan da kika min,,in sha Allah hakan bazai k’ara faruwa b..”

      “Better..!”

   Daga haka Badran ta juya tana tab’e baki ta nufi gefen bed d’inta,tana shirin zama bak’uwar tasu ta koma da baya,can bakin k’ofa ta tsaya,bayan ta kallesu duka ta furta

  “Assalam alaikum warahmatullah wabarkatuh..!”

   Ba tare data kalli inda take ba ta amsa tana had’e rai kamar wacce aka aikowa da sak’on mutuwa,kusa da ita ta k’araso cikin sauri tana mik’a mata hannu

    “Am ZAINAB HARIS,,buh zaku iya kirana Zeeharis kamar yadda sauran k’awayena na secondary suke kira na..”

   Sanin wulak’anci babu dad’i da fad’an da Mamma take yawan yi musu yasa Badra ta d’ago bayan sunyi shaking hand ta furta

      “U are welcome..”

   Har lokacin bata saki fuska sosai ba,yanayin ta yasa Zeeharis ta d’an tsaya jimm kafin ta furta

   “Sister..! Kiyi hak’uri fa da abunda ya faru,naga kamar har yanzun duk da na gane KUSKURE NA,kamar baki karb’i hakan a matsayin KUSKURE ba..”

    D’agowa tayi da kanta ta kalleta tana yamutse fuska

   “Noo! Kada ki damu,,ya riga ya wuce,shi d’an adam ai aajizi ne,so.. Sai mu kiyaye faruwar hakan a gaba..”

   “Yeah.! Haka ne,,na gode sosai da nunamin KUSKUREN na da kika yi..”

     “Babu komai..!”

   Murmushi tayi mai kyau har ta juya zata bar wajen kuma ta d’an dakata

   “Buh..! Sis zan iya tambayar ki wani abu,Please..??”

  “Babu damuwa,,ina sauraronki..”

   “Daga wane k’asa kuke please..?”

     “9ja..”

  “Ohh! Kuma daga Kano kuke ne.??”

    “Ehh..”

   

      “Alhamdulillah..! Na samu y’an uwa,,amma zan iya sake tambaya..?? Idan babu damuwa.?”

   

      “Babu..”

     Duka amsoshin nata a tak’aice take yinsu kamar ana mata dole,amma sam basu sa Zeeharis jin babu dad’i ba

      “Please..! Nace k’ark’ashin wane school za kuyi karatu ne..??”

   

      “Law school..”

   Ihun murna tayi wanda a sanadin yinsa ya farkar da Sabina dake bacci

   “Ohhh! Yah Allah.. Kinga kin tashi baiwar Allah tana tsaka da bacci..”

   Badra dake harhad’e rai ta fad’a tana kallon Sabina data gyara zama tana kallonsu,saurin juyawa Zeeharis tayi ta kallo inda Badran ke kallo,ido hud’u suka yi da ita tana kallonsu,a hankali sai ta kama kunnenta tana fad’in

   “Yi hak’uri y’ar uwa,,ban sani bane,buh mujhe maaf karte..”

  

  “Tofa.. Har da bak’in indiyawa muke da kuma.??”

    Jannat tayi maganar tana jinjina kai

   “Ke kam dai Lady yau gulma kike ji wollah,tun d’azun kina nan tsaye ke baki yi abunda za kiyi ba,nd baki bawa mutane guri ba..”

   “Bazan yiba d’in,, ina ruwanki da ni..??”

  Har ta juya zata shige wayar ta dake gefen gadonta ta fara kuka,duka ring d’in yasa su dakatawa daga musayan maganar da suke,a hankali ta dawo ta tsaya kusa da wayar,sai data fara lek’a fuskar wayar kafin ta d’auko tana fad’in

      “Hello.. Yah Sultan na..”

   Ko gaisawa basu kai ga yi ba,Badra dake zaune taji an ambaci Sultan ta taso a sad’ad’e tana zuwa dai² gurinta bata tsaya jira ba ta wafce wayan daga hannun Jannat ta bar gurin da sauri

   “Hello.. Yah Sultan nah..! Hope kana cikin k’oshin lafiya.. Ya aiki..??”

  Daga gefen Sultan jin muryan Badra a waya ya sashi dakatawa da tafiyar da yake,lokacin duka fitowarsa kenan daga gidan Hammad yana son zuwa gurin Sadeeq

    “My angel.. Kina kusa dama..?”

  “Ehh! Ai tare muke da Lady..”

   “Ok..! Ni ai ban san kuna hanya ba,sai yanzun da mukayi waya da Mamy take sanar dani kun riga kun taho,,amma a wane location kuke cikin U.S d’in..??”

    “Muna nan cikin Pennsylvania ne..”

   

     “Ok.. Kusa damu kenan.. Wane school ne..??”

  “Yah Sultan.! Muna fa VILLANOVA UNIVERSITY ne.. When zaka zo mana ziyara..??”

   Tayi maganar cike da shagwab’a

“Ohh! Angel,, zan lek’o muku ziyara,amma ku maida hankali kuyi karatu kinji my angel..??”

   

     “Toh Yah..in sha Allah za muyi..”

   

      “Yawwa daddy’s kiddo.. Bani Jannat d’in mu gaisa ko..!?”

      Sallama tayi masa tana murmusawa sannan ta mik’a mata wayar fuskarta da murmushin tsokana

      “Ai da kinsan baki bani ba,,y’ar rainin wayo kawai.”

      Gwalo ta mata sannan tayi gaba abunta,girgiza kai Sabina tayi tana d’an murmushi sannan a hankali ta sauka daga saman bed tayi hanyar toilet.

*NEW YORK CITY..*

Cikin y’an kwanaki da dawowar Sultan New York da aiki,al’amura a gefen Hammad komaai ya tsaya masa cak,ba’a gurin aiki ba,haka nan ba’a gida ba,,duk da cikin y’an watannin k’ok’arin kawai yake saboda investigation da suke kan wani case,nd burinsa har kullum shi ne ya kai inda yake so amma ina zuciyarsa da kwakwalwarsa a cikin wannan tak’aitaccen lokacin ta gagara sarrafuwa,ji yake komai ya kafe masa a guri guda tamkar tsohon k’arfe,ba don ya so ba haka nan bisa dole yake tattara komai ya ajiye a duk lokacin daya tsinci kansa cikin damuwa,sai dai har yanzun babu mafita,,ko yanzun yana zaune akan computer yana aiki,zuciyarsa tayi wani irin harbawa,still bai ajiye aikin ba yaci gaba,a hankali rubutun dake saman screen d’in suka fara watsewa wasu kuma suka shiga juya kansu zuwa upsidedown,dakatawa yayi ya shafo sumar kansa har ya gangaro kan kyakykyawa kuma gyararren mustache d’insa,sake k’urawa screen d’in idanu yayi amma still sai yake ganin komai yana sake juyewa,duk wani rubutun dake kai ya koma masa baya gane komai sai *MY LADY*,tab’a computer yaci gaba dayi yana ta k’ok’arin saitawa,amma yayi iya yinsa rubutun sai sake nuna masa shirme suke,a hankali ya zame ya kwanta saman armchair tare da rufe idanunsa,cikin k’ank’anin lokaci labarin ya fara sauya salo,yayin da komai yake dawo masa farko,idanunsa yayi saurin bud’ewa ya zubawa rufin kayataccen parlor’n kallo,tunaninta gami da soyayyarta masu girma dake mak’ale cikin zuciyarsa tsayin shekaru suka sake taso masa

   “My Lady..!”

  Ya furta a fili yana jera sakin wahalallun ajiyar zuciya kamar wanda ya ganta a gabansa,saurin mik’ewa yayi tsaye,kamar walk’iya ya shige bedroom d’insa,duka da shigarsa da fitowarsa ko cikakken mintuna ashirin bai ba,ya fito sanye da wasu kayan,a gaggauce ya kwashe duk wasu tarkacen kayansa masu muhimmanci da wayoyinsa bayan ya kashe computer ya fice a gidan cikin sassarfa,fitowarsa a lokacin yayi dai² da dawowar motar su Sadeeq,yana niyyar shigewa nasa motan suka k’araso kusa da shi,basu ko gama gyara parking ba Sultan yayi hanzarin fitowa a d’an hanzarce yana fad’in

  “Dude..! Sai ina kuma kai da muka bari kana aiki..??”

   “Zanyi tafiya ne..”

Kallon juna suka yi cikin had’in baki kuma suka furta

  “Zuwa ina kenan..??”

Ba tare daya kallesu ba ya ce

    “9ja..”

  “What..!? 9ja fa kace,,ana tsakiyar aikin zaka yi tafiya..?? Uhhuumm! Wasa kake yi guy..”

“Uhhuumm..!” Shi ne kad’ai abunda yace dan ya fahimci suna d’auka da wasa yake yi,daga haka bai k’ara magana ba yayi shigewarsa mota ya bar arean tamkar zai tashi sama,bcos a lokacin ji yake gaba d’aya zuciyarsa ta gama kiransa,nd yana jin matuk’ar bai kwana a 9ja ba a wannan lokacin komai zai iya faruwa da rayuwarsa,,tafiya kuwa tunda yayi niyya yana jin babu dalilin da zai hana shi fasawa tunda ya shirya yinta,shi yasa ko daya fito babu wanda ya kira bare ya fad’awa yana hanya,yafi so ne kawai su ganshi kai tsayen,ya san babu wanda zai ce masa saboda mene ne ya taho.

*PENNSYLVANIA CITY..*

     Wasa² zamansu cikin d’aki guda su hud’un ya zama gwanin sha’awa,zuwansu k’asar da fara karatunsu duka ba’a d’auki lokaci ba amma har sunyi sabo sosai da juna,shak’uwa da mutunta juna kuwa har ba’a cewa komai,idan ka gansu matuk’ar bawai ace ka san su ba tun farko,sai kayi tunanin dama can taren suke,saboda k’ullaliyar alak’ar su mai k’arfi da ko a class basa zama daban²,a ko ina zaka same su tare da juna,cikin makaranta ko wajen ta,,wannan dalilin yasa tsananin aminci da shak’uwarsu jama’a da dama ba iya kad’ai wad’anda suka fito k’asa d’aya da su ba,hatta da farar fata suke sha’awar zama dasu.Ta b’angaren karatu kuwa a ko wane lokaci suna sahun gaba,haka ma idan aka dawo b’angaren barkwanci da tsokana suna nan,,mutum ko waye matuk’ar kun had’o hanya,yanzun kana yin abu ko da cikin kuskure ne,indak gabansu ne zasu sako ka gaba da tsokana,tun jama’a basu fahimce su ba,har salon nasu ya fasu kowa ya fahimci yanayinsu,,dai² gwargwado ta fuskar girmamawa shima suna k’ok’arin bawa duk wanda wani alak’ar mutunci ta had’a su da shi,shi yasa ko farar fatar suke jinjina musu ta wannan fannin,nd wannan dalilin yasa suma suke samun karramawa daga gurin abokan karatunsu har ta b’angaren malamai.

   

     Tana kwance bayan dawowarsu a skul yayin da Zeeharis,Jannat da Badra suke ta hiran gida da y’an uwansu,,tayi shiru yayin sa hankalinta tuni yayi gaba,tayi nisa cikin duniyar tunanin rayuwarta

      “Princess,, taso kiga wani abu dan Allah a nan..!”

  Cikin ihu su Jannat suke mata magana,yadda tayi shiru bata ce komai ba yasa Badra tasowa ta dawo kusa da ita,a hankali ta dafa shoulder d’inta

   “Me yake damunki ne..?? Kwanakin nan duka na kula da kefa kina yawan b’oye mana wani sirri.. Shin har yanzun ba muyi jimawar da zaki sanar damu damuwar ki ba ne..??”

    Idanunta ta d’ago dake cike taf da hawaye tana kallon Badra,a hankali kuma ta maida su ta lumshe hawayen dake kwance ciki suka samu damar gangarowa,,a kid’ime Jannat da Zeeharis suma suka dawo gefenta

      “What’s going wrong princess..?? Me zai saki kuka ke kuwa a dai² lokacin da kike rayuwar farin ciki.??”

    Cikin muryar kuka tace

     “Sam ba yadda kuke zato bane..”

    

    “Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un.. Dan Allah kiyi hak’uri ki bar kuka,bai kamace ki bafa,,kuma kema kin sani..”

   

     “Ba haka bane.. In dan damuwa ne,na jima a cikinta,kawai dai baku tab’a fahimta bane,amma tun zuwa na k’asar nan da abuna na zo,,nasan kuma da shi zan koma ga mahaliccinmu,matukar ban ganshi ba…”

   

    Shiru suka yi gaba d’aya kowa cikinsu da abunda yake sak’awa a zuci

     “Dan Allah to princess ki bar kuka,,in sha Allah,ubangiji zai kawo mafita..”

   

     Sai data ja numfashi sannan ta ce

      “Allah yasa.. Amma ni kam ina ji a jikina,wannan ranar bazai zo…!”

     Saurin rufe mata Badra tayi tana girgiza kai

      “Zai zo da yardar Allah,,kuma zaki ce na fad’a miki,in sha Allah duk abunda ke damunki ubangiji zai miki maganinsa,,kin sani fa,kuma ke musulma ce,saboda haka ki daina yanke tsammani,sannan ki bar munanawa Allah zato,wata rana komai zai zama tarihi..”

    

     “Dear.. Tsayin shekaru nawa zan d’auka kenan ina jiransa..?? Kullum fa cikin tsumayinsa nake,,yaushe zai dawo,a ina zan ganshi..?? Wad’annan sune damuwata a kullum.. Amma ban sani ba,bani da amsa kuma bani da wanda zai fad’a min inda zan ganshi..”

     Idanu suka ware akanta suna kallon yadda take sharce hawaye,cikin tsananin mamakinta da damuwa dukansu suka sake had’a baki

      “Wa kike jira ne princess..??”

     Sai lokacin ta fahimci abunda damuwa tasa ta aikatawa,sam bata shirya sanar da kowa damuwarta ba a dai² wannan lokacin,da sauri ta shiga goge fuskarta ta mik’e a gurin,har ta fara tafiya ta waiwayo fuskarta da wani irin tsoro ta ce

     “Mene ne wai kuka wani sakani gaba haka..??”

     Kallonta suka ci gaba da yi har ta fara zargin kanta

     “Wai ku dan Allah mene haka ne,kun samin ido ina magana duk kunyi shiru,,ku bani amsa mana..??”

     Ajiyar zuciya suka yi duka,kowa da mamakinta fal zuciyarsa mace kamar ba ita ba,yanzun tayi abu kuma ta sake birkicewa

     “Uhhuumm..! Labari fa kike bamu,shi ne zaki wani nuna kamar baki sani ba.. Dillah dawo ki k’arasa mana mu..!”

   

     “Labari..!? Na waye..? Akan mene nake baku labarin..??”

   

      “Ur Prince mana.. King of ur heart..”

     Zaro ido tayi hannunta dafe da k’irjinta dake duka da sauri²,tana ci gaba da kallonsu taci gaba

      “Da gaske na fara baku labarinsa..??”

     Ta tambaya tana raba ido,,Zeeharis ce taci gaba da magana,dama kuma tunda ta tashi da itan suke maganar

      “Ehh! Mana,to wai ina ya tafi ya barki ne,mu kin samu a duhu.. Nd kukan ki ya tada mana hankali sosai..”

     Fuskarta da damuwa mai girma ta dawo kusa dasu ta zauna

     “Da gaske na baku wannan labarin..??”

    Tayi tambayar cikin rashin yarda

     “To banda abunki idan ba kin fad’a mana ba,ta yaya za’ayi mu sani mu..??”

   

     “Haka ne,,amma ni ai ban san yaushe ne nayi maganar ba..”

   “Uhhuumm..! Ai shi kenan tunda baki yarda ba,amma dama ta yaya zaki sani tunda kina b’oye mana,mu kam bamu sam matsayin da kika d’auke muba,,amma na tabbatar duk cikinmu nan babu wanda yake tare dake da wani zuciyar na daban.. Ko akwai..?? Idan akwai ku fad’a mata gata nan..!”

   Duka suka tabbatarwa Zeeharis babu,kallonta tayi fuska fal damuwa

  “Kin gani ko princess.. Wollahi gaba d’ayanmu nan,da zuciya d’aya muke tare dake,na tabbata idan ace a cikinmu ne,wani yake tare da damuwa zai sanar kuma har muyi sharing nasa wa juna,,amma me yasa zaki mana haka..?? Ya kamata ki sanar damu matsayinmu a gurinki.. Ko ba haka ba guys..??”

   Tamkar had’in baki duka suka rud’e da cewa

     “Gaskiya ki sanar damu..!”

   Kunnuwanta tasa hannu ta toshe,dan yadda suke maganar ihunsu sake hawa mata kai yake,su kuma da basu san me yake faruwa ba maimakon su dakata sai suka ci gaba

   “Ehh! Ki sanar damu,,kawai ki fada mana..! Mu dai ki fad’a.!!”

   Yadda taga basu da alamar dainawa yasa cikin tsawa tace

     “Yaa isaaa..! Enough..!!”

  D’if sukayi duka lokaci guda suna masu binta da kallon mamaki,cikin sheshshek’ar kuka mai tafe da damuwa ta fara magana

   “Zatonku na d’auke ku wani matsayi ne na daban.. Ko ba haka kuke tunani ba..??”

   “K’warai kuwa,haka muka gani,kuma haka kika nuna mana..”

       Kanta ta shiga girgizawa

    “Baza ku tab’a fahimtata ba,haka nan baza ku tab’a fahimtar dalilin da yasa na kasa sanar daku ba,,kuna tunanin saboda ban yarda daku bane yasa nak’i sanar daku damuwa ta..?? Shi kenan na amince nayi laifi,na kuma karb’i duk wani abu da za kuce matuk’ar akai nane,,shi kenan zan sanar daku,komai ya wuce..??”

    Ci gaba suka yi da kallonta sai dai wannan karon kallon nasu yana k’unshe ne da ma’anoni da dama,a hankali ta maida idanunta ta rufe kana ta fara zayyano musu labarin soyayyarta tun daga farkon had’uwarsu tamkar yanzun ne komai yake wakana,har ta dasa aya babu wanda ya iya yin ko da tari,tana yin shiru ta bud’e idanunta sannan ta fashe da wani irin kuka mai tsuma zuciya,,d’akin gaba d’aya ya d’auki shiru baka jin komai face sheshshek’ar kukanta cikin tsananin damuwa.

     Yayin da gaba d’ayansu dake saurarenta jikinsu yayi wani irin sanyi,tausayin ta gami da jinjinawa k’ok’arin ta yasa suke mata wani irin kallo na daban,,kafad’arta Jannat ta dafa cikin tausasa murya tace

   “Princess.. Amma shin kina ganin laifinsa ne cikin abunda ya faru..??”

   Sai data goge fuskarta sannan ta gyad’a mata kai

   “Idan banga laifinsa ba,shin laifin waye kike zaton zan gani..??”

   Caraf Badra tayi ta amshe zancen

   “A gaskiya princess,, ni kam duka cikin labarin nan,laifin mutum d’aya na gani..”

   Waiwayawa duka suka yi kanta suna kallo

     “Waye kike nufi..??”

  A hankali tana k’ik’k’ifta idanu tace

   “Dad d’insa.. Gaskiya shi ya janyo rabuwarku,idan ba don haka ba,ai da duk ba’a zo wannan matsayar ba..”

   (Uhhuumm.! Lallai Badra zaki tafka KUSKURE idan kika ci gaba da magana.. Fan’s ya kamata ku bata shawara tayi shiru hakan nan,dan kada allura ta tono garma)

   Saurin kallonta Zeeharis tayi tana cewa

    “A’a Badra.. Kada kiyi saurin yanke hukunci..!”

  “Haba friend,idan ba shi bane ba to waye ne za’a kira mai laifin..??”

   “I knew,,yayi ba dai² ba daya k’i zuwa nema masa aurenta,bayan nan kuma ya tura shi MUHAMMAD d’in karatu.. Amma kada ki manta da cewar,ita rayuwa da muke yi gaba d’ayan ta ubangiji ya tarawa kowane bawa yadda yake son nasa ya kasance,nd kuma daya tashi duk da hakan ya tsara rayuwarmu  ta tafi ne a bisan doron *K’ADDARA* komai tsarin Allah ne,so kinga kenan idan yaso ko a yanzun sai ya had’a su,tunda tun da fari shi yaso rabuwarsu ko ba haka ba..??”

  Shiru ta d’anyi kafin ta gyad’a kai

     “Yeah..! Haka ne maganar ki..”

   “Kun gani ba,,sannan idan kuka duba ko cikin labarin data bamu yanzun tace sun samu matsala a garinsufa,after kuma suka samu canjin gurin zama,kunga kenan idan kun duba nan ba tsarinsa bane kuma bana Daddy’nsa ba,akwai dalilin da yasa Ubangiji yayi haka,,ni ina ganin lokacin had’uwarsu ne bai yi ba,amma idan har lokacin yayi ba kamar yadda ubangiji ya raba su babu shawaran d’aya daga cikinsu,zai had’a su ba tare da d’aya a cikinsu ya sani ba.. Kuyi nazari mana..!”

“Yeah! Kin fad’i gaskiya..”

Duka abunda suke fad’a kenan,ita kanta da take tunanin kamar ya ajiyeta jiransa sai duk jikinta yayi sanyi,cikin k’ank’anin lokaci tauhidi ya sake shiga zuciyarta

   “Tabbas.! Kunyi gaskiya,, ubangiji shiya raba tsakaninmu,,amma dole akwai Sila.. Shin waye ne silar a nan..??”

  Shiru tayi da yake a zuci tayi maganar,nan wani gefe daga zuciyarta ya bata amsa da

  “His Dad..!”

   Idanunta ta lumshe a hankali tana sake zurfafa tunani cikin zuciyarta,ta d’auki lokaci mai tsayi sannan ta fara addu’ah

    “Yah rabb..! Kai ne magani da abunda ke b’oye kuma kai ne masanin abunda ke sarari,ya ubangijin samman bakwai,da kuma k’assan bakwai,,ya ubangijin al’arshi mad’aukakiya,tabbas kai kad’ai ka barwa kanka sanin dalilin da yasa ka raba wad’annan zuk’ata,,yah Allah..! idan har kayi nufin had’a wad’annan gajiyayyun bayi naka,ina rok’on ka yah Allah,daka had’a fuskokinmu da alkhainka..!”

K’aran thunderstorm daya ratsa kunnuwanta yasa ta saurin bud’e idanunta tana kallon windows d’insu

  “Heeyy! Guys muyi maza mu rufe windows kada ruwa ya jik’e mana room..”

  A gurguje duka suka watse a gurin,itama Sabinar sai ta mik’e tana nufar hanyan toilet zuciyarta cike da nufin yin alwala.

*NIGERIA..*

Cikin aminci da nutsuwar rai,bayan dogon hanyar da suka kwaso jirginsu ya sauka a katafaren filin saukar jirage na Malam Aminu Kano,shi kad’ansa kamar yadda ya fito haka ya sauka daga shi sai halinsa sai kuma wayoyinsa,,hire cab ya d’auka daga airport d’in har k’ofar gidansu,,bayan ya sallami mai cab,ya tasarma k’ofar shiga gidan kai tsaye,,babu wanda ya san da zuwansa a lokacin,buh ya k’udurce dama sai dai kawai su ganshi tunda duk lokacin daya sanar yace zaizo sai an samu matsala,shi yasa ko da yayi niyyar zuwan yak’i sanarwa,,Mamma ita kad’ai zaune a parlour tana watching TV ya shigo da sallama,,cikin tsananin mamakin ganinsa lokacin da yake shigowar take fad’in

  “Hammad..!? Kai ne..??”      Kai ya gyad’a mata fuskarsa k’unshe da kyakykyawan murmushi har ya shigo cikin parlor’n,lokacin daya k’araso daf da ita still Mamma bata daina binsa da kallon tsantsar mamaki ba,gaba d’aya gani take kamar ba da gaske take ganinsa a kusa da itan ba,,murmushi ya sake yi ganin irin kallon da take masa,har yayi niyyar zama sai kuma ya fasa ya k’arasa inda take,warm hug ya bata da yasa ta sauke doguwar ajiyar zuciya,da kyar tana k’ik’k’ifta idanu ta dago hannunta ta shafa kansa,har k’asan ranta tana mai jin dad’in ganinsa

   “Baby.. Yaushe ka taho ne..? Amma baka sanar min kana hanya ba..!?”

   Murmushi yayi mata yana k’ifta idanunsa

  “Mamma..! Nayi nufin baku surprise ne,shi yasa ban sanar ba..Amma ayi min afuwa..”+

  “Uhhuumm! Aifa kam gashi nan ni kam ka bani,, ya gurin aikin naku..?”

  “Alhamdulillah..! Mah ina mutanen gidan suka yi ne..?”

     Harararsa tayi kafin ta amsa masa

   “Sau nawa ne zan fad’a maka ni kad’ai na rage a gidan..??”

    Sai daya dafe bakinsa yana mata murmushi sannan yace

   “Ohh! Am sorry Mah,, na manta ne munyi wannan maganar tuni..”

   Still yana shafa sumar kansa

     “Kai dai ka sani..”

  Murmushin k’arfin hali ya sake yi mata sannan ya nemi guri ya zauna yana fad’in

   “Wahh! Mah Daddy fa.. Yana gari..?”

    Jimm Mamma’n tayi cikin wani irin yanayi na b’oyayyen tashin hankali ta kad’a masa kai,tunda yayi tambayar yasa mata ido yana kula da duk wani motsinta,yadda tayi reaction lokacin da take masa response yasa take ya fahimci akwai damuwa,kusa da ita ya dawo ya kwantar da kansa a jikin shoulder d’inta

    “Mah.. Did something went wrong..??”

   Still bata yi magana ba saima kanta data kawar gefe,saurin mik’ewa yayi ya zauna

  “Please.! Ki fad’a min abunda yake faruwa,,u know bazan iya juran ganinki a damuwa ba.. Please Mah.!”

   “Hammad.. Akwai damuwa ne,,idan na fad’a maka babu abunda zai k’are mu da shi daga ni har kai,haka ma idan na b’oye bazai yi mana maganin komai ba,bcos dole ne nan da d’an lokaci nasan zaka san komai..”

   “Haka ne Mah. Buh ki sanar dani damuwan..”

    Kallonsa tayi idanunta taf hawaye,a hankali tasa hannunta a saman kansa tana shafawa kamar mai rarrashin sa

“Baby ina cikin damuwar hukuncin Daddy’nku ne a wannan karon,saboda ya sanar dani a kowane irin lokaci zai yi maka aure..!”

    Bai tsaya jiran mene ne zata sake fad’a ba ya rungume ta cikin tsananin murna

    “Thank u Mah,buh wannan ai ba abun damuwa bane.. Ya kamata ne ace kinyi farin ciki,coz nima ina cikin farin ciki.”

      Kallonsa kawai take yadda taga yana zumud’i akan maganar da take yi d’in,without ya jira yaji k’arshen inda maganar zata tsayaya hau murna

   “Thank u Mah.. Da kika bani wannan kyakykyawan albishir d’in.. I love u Mah..I love u ³..! Mu’aaahh.!”

    Ya d’ora mata peck a chicks,nd cikin sauri ya mik’e a gurin yayi sama itan kuma ya barta tana aikin binsa da idanu,a gurguje ya watsawa jikinsa ruwa sannan ya fito cikin shirinsa,ko tsayawa ya fad’a mata inda zashi a time d’in bai yiba ya fita da sauri,a baya ta biyo shi tana kira don ta k’arasa sanar masa inda k’arshen zancen yake amma ina har yayi mata nisa,kiransa ta shiga yi sai dai kash nan d’inma bata yi nasara ba don kuqa hannu kad’ai ya d’aga mata da alamar yana dawowa yanzun,,tun kafin ta k’arasa inda yake tuni har ya fizgo mota yayi waje,dafe kai tayi cikin takaicin rashin samunsa tana fad’in

        “Yah rabb..!”

    Shi kam cikin ziciyarsa gaba d’aya farin ciki yake da jin maganar aurensa da Daddy ya yanke yanzun,ba tare daya damu da tambayar Mamma wace ce ko y’ar waye ba,bare a inda take yasa kai ya fice nd without tunanin abunda zai biyo baya,,haka nan kuma bayan fitowarsa daga gidan sai yake jin zuciyarsa ta kasu kashi²,yayin da yake jin wani sashin ya cika da zumud’in ganin lokacin ya gabato,d’ayan gefen kuma sai yake jinsa cike da damuwa,sai dai farin cikin da yake cikinta yafi k’arfi ta yadda har yake neman danne damuwar sa,d’an dafe gefen chest d’insa yayi,dai² saitin inda zuciyarsa take k’aik’ayi,a hankali ya d’an cije lips d’insa ya fara magana

    “Me yasa ke kuwa zaki shiga damuwa al’halin mammalakin ki yana cikin tsananin farin ciki..??”

      Kamar wanda yake magana da mutum ko yake sauraron amsa,sai yayi jimm shi kad’ai yana sakin numfashi,ya d’auki y’an mintuna shiru sannan a hankali ya lumshe idanunsa da fad’in

     “Haba ke kuwa,,ki kasance cikin farin ciki mana,,yanzun fa ba lokacin shiga k’unci da damuwa bane,,ya kamata kiyi farin ciki kamar yadda mammallakin ki yake yi.. Let’s cheer up.! Lokacin farin ciki ne,so muyi farin ciki gaba d’aya..”

      A hankali kuma ya saki sihirtaccen murmushi,cikin tsananin gudu ya ci gaba da cin taya,dai² lokacin yana shiga kwanar gidan maggi,ya samu gefe yayi parking a inda ya saba tsayawa,sai dai wannan karonma bai fito ba ya zauna cikin motar yana tunanin hanyar daya kamata yabi,shin zai fita ne yayi tambaya ko kuwa haka zai ta zama cikin motan da saka ran zai ganta..?? 

   

      A kan idanun Mamma ya fita a gidan,duk da taso tsayar da shi bcos tana son ya sanar mata inda zashi,buh abu ya gagara har ya fice ba tare daya saurareta ba,cikin tsananin damuwa bayan taga fitarsa ta koma parlor ta zauna tana mai buga tagumi da duka hannayenta biyu,lokaci guda zuciyarta ta kasu da mugayen tunanuka,cikin tsananin tashin hankali kuma suka fara tafka muhawara

       “Shin yanzun tunda ya iso k’asar zan sanar masa hukuncin Daddy ne ko kuwa zan b’oye masa zuwa nan gaba sannan na fad’a masa..??”

      Ta yiwa kanta tambayar,,saurin girgiza kai tayi alamun “A’a” sannan ta sake zurfafawa cikin tunani yayin da wani sashin na zuciyarta yake cewa

      “Kada kiyi haka,,gara kawai ki fad’a Masan,bcos duk abunda zai faru a yanzun na d’an lokaci ne,daga kin sanar masa komai zai wuce,,kema kin huta da ganin tashin hankali a gaba..!”

   

     “To amma idan yak’i amincewa fa sai nayi yaya kenan..??”

     Bijirarriyar zuciyarta ta saje watso mata amsa

     “Shi kenan.. Sai ki sanarwa Daddy’nsa,,dan Hammad yak’i amincewama da zab’insa ai ba wani abun damuwa ba ne..!”

   

      “A’a bazai yiwu ba,,dole ne nayi k’ok’arin rarrashinsa,,bai saba yiwa mahaifinsa musu ba kan duk hukuncin daya yanke masa,,so yanzunma dole ne yayi hak’uri yabi maganarsa..”

   

      “Babu dole..! Kawai dai kiyi k’ok’arin lallab’a shi idan ya amince shi kenan,,idan kuma ya nuna baya so..!”

   

      “A’a ba haka ba,,dole nayi k’ok’arin fahimtar da shi,wannan umarnin mahaifinsa ne,ya kamata ne ace ko yana so ko baya so ya karb’e shi da dukkan zuciyarsa.”

   

     “To wai da kike batun dole³! Ke haka aka miki.?? Ko kuwa shi Daddy’n anyi masa dole wajen aurenki..?? Shin ku bakwa tunanin jefa rayuwar yaron ku ahalaka ne..??”

      Shiru tayi tana jan ajiyar zuciya

     “Yeah! It’s true,,dole ne na lallab’a shin kafin ya koma.. Buh ina jin tsoron kada yak’i amincewa fa..”

   

     “Uhhuumm..! Kina wasa ne kema.. Ta yaya ne kike zaton zai amince d’in.? Al’halin ke da kanki kin sani tun a can baya ya shaida miki akwai yarinyar da yake so..!”

     D’if tayi tana tuna irinbmaganganun da suka yi a bayan wanda a dalilin hakan har sai data kaishi da kwanciya jinya,da kyar² ta fara twitching breathe had’e da goge zufar dake karyo mata tamkar wacce tayi tseren gudu

     “Shin yaya kenan za ayi idan yaji wannan batun..?? Hakan yana nufin akwai damuwa kena..? Yah rabb! Ka kawomin tallafi wannan lamarin yana neman juyarmin da tunani..”

    Kamar za tayi kuka haka reaction d’in dake shimfid’e saman fuskarta ya nuna,amma saboda dauriya irin nata da k’arfin halinta ko silin hawaye bata bashi damar sauko mata ba.

*PENNSYLVANIA CITY..*

        Tana fitowa a toilet saman bed d’inta ta koma ta zauna ba tare data yiwa kowa cikinsu magana ba,daga can k’asan zuciyarta kuma tana ci gaba da kai kukanta gurin ubangiji,har gabanin lokacin sallar magrib tana zaune bata motsa ba,duk da irin ihun da suke yi a room d’in,a haka har lokaci ya shiga ta mik’e tayi sallah,bayan ta idar ta ci gaba da zama a gurin tana addu’o’i,ba ita ta shi a gurin ba sai data tabbatar tayi sallar isha’a sannan ta sake d’orawa da addu’o’i,tana idarwa sai ta d’auke abun sallah ta koma saman gadonta,yadda garin yayi sanyi sakamakon ruwan saman da suka samu da yunwan dake sasikar cikinta yasa ko da su Jannat suka gama shiryawa zasu fita tace su jirata,da mamaki duka suka tsaya kallonta,Jannat kam ko da taga baza ta iya yin shiru ba tace

   “Amma! Princess kefa kika ce baza ki fita ba..!? Why kuma yanzun zamu jira ki..??”

   Baka kalleta ba taci gaba da shirinta cikin sauri²

       “Ra’ayi na canja..”

   Tana fad’ar haka ta mik’e,bayan ta gyara fuskarta ta d’auko pencil trouser na mata da long sleeve na mata ta saka,after kuma taja blazer d’inta dake ajiye a gefenta,bayan ta sakaye k’afarta cikin wani had’ad’d’en women’s chunky heels mai zip ta gaban,tana mik’ewa ta sab’a blazer d’inta ta rufata a saman kananan kayan dake jikinta,tana takowa kusa da su ci gaba da rolling vail a saman kanta,cikin sauri² duk tayi komai ta gama

    “Wah..! Princess..!! Gaskiya da kinyi zamanki,kinga kuwa yadda kika yi kyau..!?”

      Murmushi kad’ai tayi ta kuma tab’e baki ba tare data ce dasu komai ba ta wuce ta barsu tsaye a gurin

    “Ni kam gaskiya ina kishi princess,, wannan ai sai kisa masu jan kunne suyi ta biyo mu.. Kunga fa dan Allah,ni kam gaskiya duka yau bazan jera dake ba,salon ace masu Aikinki ne mu..”

       Cewar Zeeharis da take kallon Badra,dariya suka yi mata suna fad’in

      “Gara miki ma ki wuce muje kawai,,idan ta wannan matar zaki biya ina jin daga yau baza ki sake fita ba..”

   

    “Haba sisters,, kuna kallo fa,matar nan da fari kamar bata san komai ba amma yanzun fa..? Ku duba uban gayun data d’auka.. Ni dai ina kishi..”

 

    “O’o! Kada ki damu mana sisi,maybe da tsarinta ne haka,yanzun kuma ta canja,so muje kawai kada mu b’ata lokaci..”

    Hararar wasa tayi musu sannan suka fice daga room d’in,cike da tsokana Badra da suke binta ta kallo ta tana dariya

    “Nifa Sisi tuni nayima Yayanah kamu..”

  Bata juyo ba bare ta kalleta ko tasan da ita take magana suke tafiyar,duk inda suka wuce sai dai suga ana binsu da kallo,tun basu wani damu ba,har suka fara tsarguwa.

   Wani had’ad’d’en eatery suka shiga dake kusa² da skul d’insu ne dana kuma basu cika yin nisa ba idan sun fito gudun samun matsala,bayan sunyi order abunda suke ganin zasu iya ci,Badra ta sake yin magana

   “Princess nayi magana d’azun amma shi ne kika share kamar ba dake nake yi ba..!”

    Bata kalleta ba tace

   “Mene ne kika ce..??”

  Kallon sauran tayi tana murmushi sannan tace

    “Cewa nayi nayi ma big Bross nah kamu,,sai kuma kika share ni..”

 

     “Na meye ne kamun..?? Biki za kuyi ne..??”

   Cike da rashin fahimta duka suka bita da wani irin kallo

      “Kamar yaya..??”

  Idanunta ta d’ago ta kallesu

    “Ehh! Mana tambaya ne nayi ai,kamun na mene ne..? I thought sai ana bikin aure ake cewa ana kamu.!”

   

      “Uhhuumm..!” Suka ce daga haka kuma kowa yaja baki yayi shiru,kallonsu ta sake yi bayan ta saki murmushin basarwa sannan ta juyar da kanta gefe itama daga barin kallonsu,sarai ta fahimci abunda suke nufi buh bata so maganar yayi nisa ne shi yasa tayi cutting d’insa,bata so suji ace ta dalilinta mutanen da suka d’auketa matsayin y’ar uwa ita kuma ta saka musu da jin rashin dad’i ta hanyar nuna k’in ahalinsu a zahiri,bcos ta jima da sanin bata da ikon sarrafa zuciyarta,dukan wani motsi ko soyayyarta wa mutum d’aya kad’ai ta mallakasu,nd tana ji a jikinta har numfashin ta na k’arshe ya risketa baza ta k’ara iya yiwa wani halitta kwatankwacin son da take masa ba indai har a wannan gefen ne.

    Har suka gama abunda ya kawo su gurin babu wanda ya sake magana a cikinsu,sun tashi tafiya kenan zasu biya adadin kud’in da aka musu bailing waiter d’in yake sanar musu an biya musu,fuskokinsu k’unshe da mamaki suka kalleshi zasu tambaya sai dai tuni har ya riga ya bar wajen suma d’in ganin babu wanda zai tsaya yayi musu bayani kawai sai suka fice a gurin suka kama hanyar komawa hostel.

*NIGERIA..*

       Yinin ranar gaba d’aya ya tafiyar da shi wajen zagaye cikin location d’in da bai sani ba,nd duka ma kusan zai iya cewa babu wanda ya sani a gurin bare ya nemi rakiyarsa ko taimakonsa wajen gano inda suke zaune,,zuciyarsa cike da wani irin k’uncin da lokaci guda ya sakko ya mamaye ilahirin farin cikin daya tsinci kansa a ciki,bayan ya gama gararin sannan ya hak’ura ya juya akalar motar da niyyar komawa gida.

      Da kyar ya dawo da kansa gida saboda matsanancin headache da yayi masa mugun kamu,,ko daya iso mayangu road d’in ma a nan bakin get ya tsaya ba tare daya iya shiga da motar ba ya nufi k’aramar k’ofar shiga gidan,a haraba ya iske drivern gidan,ko kallonsa bai iya yiba yace

      “Kaje ka shigo min da mota.”

  Yana fad’ar maganar yana tafiya da kyar

      “Sir.. Buh key fa.?”

     “Idan ka duba zaka ganshi.”

    Kai tsaye ya wuce cikin parlor,lokacin daya shigo babu kowa a parlor’n,direct ya wuce bedroom,alwala ya fara d’aurawa a daddafe sannan ya kabbara sallah a nan cikin d’akin.

    Mamma kuwa da duka tashinta a gurin ko mintuna sha biyar cikakku bata yi ba ta shiga ciki da niyyar yin sallah ta jiyo motsin dawowar motarsa,ita kanta a gaggaucen tayi addu’o’i bayan ta idar da sallar sannan ta nufo d’akin nasa,zuciyarta na sake sanar mata kawai ta fad’a masa idan yaso tun kafin Daddy ya iske shi suyi wacce za suyi da shi,, a kwance ta iske shi idanunsa a rufe yana facing sama,sai dai yadda ya d’ora hannunsa d’aya a saman forehead ya isa mutum ya tabbatar ba bacci yake yi ba,kusa da shi ta samawa kanta gurin zama bayan ta k’araso sai dai bata yi magana ba ta tsaya ne kawai don tana son karantar yanayinsa

   “Baby..! Tashi ka zauna ina son muyi magana da kai yanzun..!”

   Idanunsa ya bud’e kad’an cikin damuwa yace

   “Mah.. Lallai ne sai Yanzun kuma..?”

  “Ehh! Yanzun ne nake tunanin yafi na sanar maka..”

    Had’iye yahun bak’in ciki yayi sannan ya tashi ya zauna buh ya jingina bayansa jikin pillow,,kallon sa tayi cikin tsanaki kamar yadda yake kallonta sai dai itan bata wani d’auki lokaci ba ta janye idanunta akansa,cike da sanyin jiki ita kanta ta fara masa magana

   “I knew Hammad tun daga haihuwarka kai yaro ne mai tsananin biyayya,,nd ko wane irin magana muka zo maka da shi kana yin iya k’ok’arin ka kaga kafaranta mana cikin bin umarnin mu.. Amm..!”

   Sai kuma ta d’an dakata kad’an tana tunanin abunda zata sake cewa next,tun data fara maganar yake jin gabansa na tsananta fad’uwa buh sam bai san mene ne alak’ar hakan da yake ji da kuma maganar Mamma’n nasa ba,d’agowa yayi kad’an ya sake kallonta,tun da tayi shiru har lokacin ta kasa ta sake cewa komai,cikin yanayin kwantarwa mutum hankali ya gyara zamansa bayan ya rik’o hannunta duka yana kallonta ya ce

    “Mah.. Duka wad’annan abubuwan da kika riga kika sani ne akaina,so kada ki sama kanki damuwar komai,,ki fad’i duk abunda kike son cewa,i promised zan saurare shi ko da zuciyata bata so,barinma nasan bazaki tab’a yin abunda ni bana k’aunarsa ba..”

   Kai ta rausayar gefe da alamun gasgata maganarsa,nd ta zame hannunta d’aya daga cikin nasa

   “Kayi min *ALK’AWARI* habibiiy,, ko mene ne nace zaka yi min shi babu musu..!”

    Haka nan tunda yaji ta furta kalmar *ALK’AWARI* gabansa yaci gaba da fad’uwa a kai² kuma zuciyarsa tana tsananta harbawa da sauri²,kansa kad’ai ya iya gyad’a mata cikin sanyi ya furta

   “Mah..! No need nayi miki wani *ALK’AWARI* kin riga kin san waye dank’i,, so don’t think lokaci guda zan canja daga yadda kika sanni,,ki fad’i duk abunda kike so,i knew my self,ko da *ALK’AWARI* ko babu u know zanyi duk abunda kike so matuk’ar kin sa ni yinsa..”

   Chicks d’insa ta shafa da hunnunta wanda ta cire daga rik’on da yayi mata tun a farko

   “Noo! Baby.. Nafi so ne ka tabbatar min ko mene ne zan fad’a baraka yi min musu ba..”

    Zuwa yanzun kam jikinsa ya wuce ace yayi sanyi bcos yana jin matuk’ar bata yi gaggawa sanar da shi ba tofa gangar jikinsa tana gargarar mutuwa,haka dukkan kalaman da taje furtawa jinsu yake sukar zuciyarsa,a hakan ya daure bayan ya runtse idanunsa daga rad’ad’in da yake jin kwakwalwarsa nayi masa yace

      “Shi kenan Mah.. Babu damuwa..! Ki fad’a kawai,in sha Allah zaki same ni mai biyayya akan dukkan maganar ki..!”

   

    “Good..! Buh.!! Ina fatan ka rik’e maganar da muka yi da kai d’azun kafin ka fita..!?”

     Kai ya gyad’a mata,itanma sai ta jinjina masa kai

    “Idan har baka manta ba,nace maka Daddy’nku ya fara maganar aurenka ko..??”

   

     “Ehh! Mah.. Kin sanar dani wannan maganar,,amma Mamma mene alak’ar wancan maganar da wannan ne..??”

   

     “Uhhuumm..! Saboda dukansu abu guda suke nufi..”

    

     “Kai.! Mamma to amma ni ai duka kinsa hankalina ya tashi ne,,nd nayi tunanin wani abu ne daban kike son sanar min.”

   

    “Hammad kenan,tabbas na yarda har yanzun kai yaro ne,,shi yasa gaba d’aya ka kasa fahimtar abunda nake son sanar da kai,,amma tunda baka fahimce niba,barin sanar da kai,kaga kenan sauran hukunci ya rage naka,,tunda dukkan wuk’a da nama yana hannunka sai yadda kaso za kayi da su.”

  “Yawwa Mah.. Tell me nasan labarin ki,ba mai haddasa damuwa bane..”

   Yana d’an murmushi yayi maganar

   “Hammad batun da nake son yi maka,bafa abun wasa bane,saboda haka ina son ka maida hankalinka jikin ka,,batune muke yinsa ni da kai akan aurenka..”

  “I knew Mah,, shi yasa ai na fad’a nima,saboda nasan babu abunda ya had’a batun aure da damuwa..”

   “Uhhuumm..! Shi kenan ai tunda haka ka d’auki batun,,amma kasan wace yarinya ce Daddy’n zai had’a ka aure da ita..??”

  Fuskarsa da fara’a sosai yake kallon Mamma,har zai ce mata “Ehh” sai kuma kawai yaji bazai iyaba nan take ya sauya da fad’in

   “Noo! Mah..!!”

“Ka gani ba,shi yasa ai na fad’a maka tun da farko ka cire batun wasa,muyi maganar serious amma kake ganin A’a,, to ba kowa bace face y’ar gidan amininsa *ALHAJI ISHAQ BUNAWA…!”*

  

      “Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un..”

   Shine kad’ai abunda ke iya fita daga bakin Hammad a dai² wannan lokacin da dukkan damuwa ta lullub’e shi,banda wasu irin mahaukatan gumi da suka fara tsere a cikin jikinsa gaba d’aya a lokacin shi kansa babu lallai ya iya gane a duniyar da yake…..

“Mah.! Me yasa Daddy zai yimin haka..?? Please ki fad’a min..? Har sau nawa ne Daddy zai dunga yanke min hukunci ba tare da yaji ra’ayi na ba..? Anya Mah.! Daddy yana yiwa rayuwata adalci..??”
     Shiru Mamma tayi ta kasa magana saboda yanayin da taga ya shiga ba k’aramin so yayi ya tada mata hankali ba,totally he’s out of control bare ta iya lallab’a shi ya saisaita kalamansa bcos sunyi kaishi da yawa
   “Please.! Mah kiyi min magana,did he do..?? Wannan fa rashin adalci ne,me yasa sai ni kad’ai Dad zai yima haka..?? Duk dan ina iya hak’ura da abunda zuciyata ke so akan nasa,shi yasa anytime yayi ra’ayi sai ya murd’a min nawa tsarin..??”+
    “Ya isa haka Hammad,,ya kamata ace ka iya tauna lagazin bakinka,sannan ka san irin words d’in da bakinka zai furta akan mahaifinka,ko mene ne zai yi maka mahaifinka ne yana da right yayi maka koma mene ne..”
   “Amma Mah saboda kawai yana matsayin mahaifina sai ya dunga yanke min hukunci kan rayuwata..?? Me yasa bazai yimin adalci ba.?”
   “Hammad.! Idan baka maida nutsuwarka a jikinka ba zan nuna maka KUSKUREN da harshenka yake k’ok’arin yi yanzun..”
    Murmushi ya saki irin wanda da gani kasan da kad’an yafi kuka ciwo
   “Uhumm! Good. Mah.! Da kyau.! Saboda na fad’i gaskiya shi yasa zaki bi bayan Daddy..? Me yasa tun farko kika kasa fahimtar da Daddy wannan gaskiyar..?”
   Kallonsa tayi tana girgiza kai dan tasan matuk’ar ta biye masa a irin wannan halin da yake ciki komai zai iya faruwa,shi yasa ta ga gara kawai tayi shirun coz zai fiye musu alkhairi,dariya ya saki mai sauti idanunsa na fitar da hawayen bak’in ciki
    “Why Dad..!? Why.? I dunno why things suke tafiya min so hardly,,kullum rayuwata sai juyi yake kamar waina,da farko yak’i zuwa nema min aurenta,nd he says ban kai matsayin rik’e gida ba,,after ya sani tafiya karatu duk da bana so nayi hak’uri na tafi,next k’addara ta shiga tsakaninmu yeah! Wannan kam na yarda Ubangiji ya tsara faruwarsa buh saura kam Dad shi ne ya janyo min faruwarsu,still now kuma yana preparing yi min aure without na san da maganar sai da lokaci ya k’ure..?? Uhmmm! What a surprise things,,Mah mene ne kenan Dad zai yi a gaba.? I know kin san duk tsarin Dad a kaina.. Please Mah ki sanar da ni kawai.”
    Wani dariyar sake fashewa da shi kamar zararre,hawaye naci gaba da sauka a saman chicks d’insa
       “Mah..! U know what.?? Tun yanzun gara fa ki sanarma da Dad bana son auren san nan da zai yi min.. If yak’i ya fasa kuma i must fleeing..”
      Kallonsa ta tsaya yi fuskarta taf da damuwa
      “Son.! Baka jin magana ko..?? Yaushe ka koyo fitsaran da zaka kalle ni kana min wad’annan maganganun ne..??”
   
      “Mah..! Serious fa ki sanarma mijinki this time around ba zan tab’a yi masa biyayya akan abunda yake so ba,matuk’ar ya dage sai dai..!”
      Lafiyayyen mari ta sauke masa a chicks d’insa na hagu,sai dai duk da hakan da tayi ko kad’an bai sa Hammad ya damu ba,saima dariya daya sake sawa kuma itama sam bai ji haushin abunda tayi masa ba,kallonta yaci gaba da yi da jajayen idanunsa da suka k’ank’ance yana shafa gurin data mare shi
       “Thank u Mah.! Saboda na fad’i gaskiyar abunda yake raina shi yasa zaku tarun min kan abunda babu shi a zuciyata..? Shi kenan zan koma inda na fito tunda bakwa buk’atar zamana a kusa daku,buh kada kusa rai a kusa ko nesa zan yi muku biyayya kan wannan hukuncin,,ko da kuwa ace zaku nemi a d’aura min aure ne da thousands Ladies a rana guda,ku sani bazan tab’a son ko d’aya daga cikinsu ba,matuk’ar ba *ABUNDA RAINA KE SO* bane,zan hak’ura da yin auren gaba d’aya kowa ya huta..”
     Yana gama fad’ar abunda duk yazo masa cikin kwakwalwarsa ya dire k’afafunsa daga saman bed d’in zuciyarsa na tafasa,direct inda ya ajiye muhimman kayansa daya zo dasu ya nufa yana zuwa ya tattara komai nasa cikin gaggawa,sannan ya sauya pyjamas d’in dake jikinsa da wani suit mai kalar red wine daya fitar a cikin closet d’insa,sai daya tabbatar ya gama komai sannan ya nufo inda take zaune shiru kamar wacce aka sassak’a,a hankali ya tsuguna gabanta yana d’ora hannayensa asaman laps d’inta
         “Please Mah forgive me..! Duk abunda nayi miki ki yafe min,hakan bazai sake faruwa ba da izinin Allah..”
     Dogon ajiyar zuciya taja,duk wannan abun da ake ita kam bata ma san ya tashi a kusa da ita ba,sai ganinsa tayi cikin shirin da ta kasa tuna yaushe yayi shi
    “Son..! Mene ne haka..?? Ina kake shirin zuwa da wannan daren..??”
    Kansa a k’asa without ya d’ago bare ya kalli fuskarta yaga irin yanayin da take ciki ya ce
   “Zan koma inda na fito ne.. Bcos idan naci gaba da zama nan zuciyata zata iya samun damuwa.. Nd na baro aiki a gabana..”
   “Ba yanzun ba son,,ka bari ko da zaka koma zuwa da safe sai ka tafi..”
    Shiru yayi bai bata amsa ba,ya juyar da kansa gefe,can k’asan zuciyarsa shi kad’ai yasan abunda yake sak’awa
   “Mah.! Ai idan kika ga ban koma a yau ba,sai dai idan na samo labarin inda suka koma ne,amma idan ba haka ba mene ne zai zaunar dani a inda ake fatan ganin rayuwata tazo k’arshe..??”
   “Son.! Baka ce komai ba.. Naji kayi shiru..!”
   “Allah ya kaimu Mah,, yau da gobe duka d’aya ne..”
    Kansa ta shafa a hankali kafin ta ce
   “Taso kazo muyi magana to tunda ka dawowa nutsuwarka..”
   D’an kallonta yayi kad’an fuska babu wani alamun annuri,da farko kamar kada ya tashi bcoz ita kanta Mamma’n ya fara ganin laifinta akan maganar da take yi na umarni daddy akan san,ko me ya tuna kuma sai ya mik’e ya zauna a gefentan
    “Baby..! Mene yasa baza ka bi maganar mahaifinka ba..?? Shin baka so kaima naka yaran da zaka samu nan gaba suyi maka biyayya..??”
    “Noo.! Mah! Buh ya kamata ne ace Dad ya gane zamanin daya wuce yana da Bambanci da wanda muke ciki,,idan har ace da anyi auren dole yanzun fa..?? Ko mata fa an daina yi musu dole,bare ni da nake namiji,,ki fahimtar dashi Mah nima ina da nawa Zab’in,me zaisa ko wane lokaci sai shi ne zai zab’a min yadda zanyi..?? I have my own lifestyle fa.”
   Hannu tayi saurin d’aga masa alamun ya isa haka,shiru yayi yana ci gaba da binta da kallon mamaki
   “Hammad.! I have already told u ya kamata kasan irin maganganun da zasu na fita a bakinka game da mahaifinka,amma baka ji ko..??”
  “Sorry Mah.. Buh..!”
   “Bana son jin komai daga bakinka yanzun,,maganar da nake yi maka ba wai cewa yayi na nemi shawarar kaba,,umarni ne ya bani,dan haka ko kana so ko baka so abunda ya tsara shi zai yi ba wai wanda kake so ba,,hope ka fahimce ni..??”
   “Mah.. Me yasa ne to lallai sai ni kad’ai Dad zai yima irin wannan tsarin,me yasa ba zai gwada yima Bassam ba..? Gaskiya Mah am tired,, fisabilillah nayi masa biyayya fa,,ya kamata ya bari na zab’i abunda nake muradi bawai shi ya dage kan lallai sai shi ne zai zab’a min abokiyar zama ba,,nifa zan zauna da ita ba Dad ba.. Gaskiya Mah idan Dad ya takurani a wannan lokacin wollahi komai na iya faruwa..!”
    Sabon mari ta k’ara sauke masa a chicks d’insa,dafe da gefen ya sake d’agowa yana kallonta cike da mamakinta
    “Kada ka fad’a min zancen banza Hammad,, ko dan kaga ina binka ne yasa kake fad’ar duk abunda ranka yaso,dan kaga nayi maka shiru ko..?? To barin fad’a maka,ko kaji ko kada kaji,aure babu fashi,duk inda zaka shiga kaje kada ka fasa,,dan kawai kaga ina lallab’a ka,soyayya ba hauka bane da zaka nemi ka jani a k’asa,, kada Allah yasa ka yarda d’in ka tafi duk ma gidan uwar da za kaje mana wata tsiyar ce..??”
   “Mah..! Yau kece kika sa hannu kika mare ni.?? Akan kawai nak’i amincewa da wannan maganar shi yasa kema zaki juya min baya.? Shi kenan Mah! saboda na fad’i gaskiyar abunda yake zuciyata sai kema ki ga laifina.? Me yasa ba zaku duba halin da zan iya shiga bane.? U know idan da ace bani da wacce zuciyata ke muradi zanyi hak’uri na karb’i zab’in ku,buh tunda na riga na shaida muku ina da wacce nake muradi ya kamata ace kunyi hak’uri,,shi kenan Mah,na fahimta..”
     Saurin mik’ewa yayi daga inda yake cikin fushi zai bar wajen tayi saurin rik’o hannunsa
   “Ko kad’an son ban so na d’ora hannuna akan kaba,kai ka sani aikata haka,nd saboda bani da yadda zanyi ne,dole tasa ni dakatar da kai daga KUSKUREN da kake k’ok’arin aikatawa,bani da wani zab’i sai nayi hakan,,ya kamata ka tausasa zuciyarka ka karb’i zab’in mahaifinka..”
    “Me yasa ne Mah baza ku fahimci abunda zai iya faruwa ba..? Ko kuwa dan iyayenta sun kasance talakawa ne Daddy baya son alak’ata da ita..?? Ita kad’ai nake so,kuma da ita bake son k’are rayuwa..”
    “Bana son ka aikata abunda zai janyo maka fushin ubangiji Hammad,,rashin bin umarnin mahaifinka zai iya haddasa maka shiga matsala,kayi k’ok’arin bud’e idanunka ka kalli gaskiya.”
     Murmushi yayi mai ciwo yana kallonta
       “Shi kenan Mah,,buh *ALK’AWARIN* dana d’aukar musu fa,na kai shi ina.?? Ita,iyayenta da sauran relatives nata duka nayi musu alk’awarin zan dawo,idan ban koma ba,mene ne ubangiji zai yimin a matsayin hukunci..?? U know umarnin ubangiji ne cika ALK’AWARI,idan banyi k’ok’arin sauke nauyin da yake kaina ba ubangiji ma bazai kyale niba..”
      Jinjina kai tayi cikin sanyin jiki ta ce
      “Na sani Hammad,buh yaushe ne kayi musu ALK’AWARIN.?? Kasan dai Daddy’nku ba zai fasa abunda yayi niyya ba ko..??”
          Kai ya jinjina mata ba tare da yayi magana ba
   “Shi yasa nake so kayi hak’uri kaci gaba da yiwa mahaifinka biyayya,wata rana sai labari..”
    
    “Uhhuumm.!” Yace k’asa² ba tare daya sake magana ba yaja bakinsa ya b’ame bcos yasan duk abunda zai fito a bakinsa a irin situation d’in da yake ciki ba zai yi dad’i ba,ganin haka yasa Mamma taci gaba da lallab’a shi sai dai tunda yayi shiru,bai ko sake d’aga kai ba,itama sai kawai tayi shirun,bayan sun shafe tsayin lokaci a hakan tayi masa sallama ta bar bedroom d’in,,tana fita a d’akin ya mik’e cikin sauri ya had’a nasa ya nasa ya ajiye gefe,after kamar awa guda da tafiyarta a lokacin wajen 11pm har ya wuce,yana gama tabbatarwa kansa babu yadda za’ayi ta dawo ya tattara ya kama hanyar barin gidan.
Daga gida direct airport ya nufa,cikin gaggawa yayi bucking night flight,a daren wajen 12am jirginsu ya d’aga zuwa U.S,tun daya fito daga gida gaba d’aya zuciyarsa ta kasa samun nutsuwa bcos maganar duka ya tsaye masa arai,gani yake kamar Daddy baya son farin cikinsa ne shi yasa yake masa irin wannan karan tsayen.Sama da awa goma sha uku suka d’auka cikin gajimare suna tafiya amma dai² da sau d’aya gyangyad’i bai kama shi ba bare yayi bacci,tsayin awannin idanunsa biyu sai dai yayi wani irin shiru,zuciyarsa cike da fargabar abunda zai iya faruwa,,a haka suka sauka a New York.
     Tun daya bar garin,shirun da suka ji babu alamunsa yasa da daren Sultan yayi ta kiransa a waya amma duka ya kasa samunsa,tun suna d’aukan maganar daya fad’a wasa har dai abu ya fara neman zama serious,,ga shi yau tsayin kwana biyu kenan amma shiru kake ji babu shi babu labarinsa,sunyi jiran,sunyi kiran duka a banza coz amsa d’aya suke samu wayoyinsa a rufe suke,wannan dalilin yasa Sultan yanke shawaran ya kira gida Nigeria yaji ko yana can d’in kamar yadda ya fad’a musu,duk da sun d’auki maganar tasa a wasa.
    Gama yanke shawaran yin hakan babu jimawa yana niyyar kira,kiran Daddy ya shigo wayar Sultan d’in cikin hanzari ya d’auka,bayan sun gaisa Daddy yake tambayarsa ko lafiya yaji wayoyin Hammad a rufe..? Sai daya saita nutsuwarsa shi kansa sannan ya yiwa Daddy bayanin abunda yake faruwa,cikin tsananin mamaki bayan sun gama maganar suka yi sallama.
     A gida Nigeria kuwa lokacin da Daddy suka gama magana da Sultan line Hammad na nan k’asar ya kira amma sai ya ji shima d’in ana shaida masa a rufe,ya sake trying line da yake amfani da shi a U.S shima d’in same abunda yaji kenan,line Mamma ya kira ya ji ko gaskiya ne Hammad d’in yana nan,a lokacin fitowarta kenan babu jimawa tana sauri zata je office kiransa ya shigo mata,da sallama a bakinta ta d’auka bayan ya amsa mata ya d’ora da fad’in
    “Yaushe Hammad ya zo k’asar..!?”
     Amsa masa tayi da “jiya ya zo ranka ya dad’e..”
   
     “Toh amma mene ne ya samu wayoyinsa duka suke a rufe..?? Ko kunyi magana da shi ne..!?”
   
     “Ehh! Munyi magana daren jiyan,, sai dai yak’i saurarena,ban san yaya ne zanyi masa ba..”
   
     “Haba Asiya,,wannan ai zancen banza ne kike yi,ta yaya ne zaki fad’a min wai yak’i saurarenki..?? Duk yadda za ayi ina so kiyi,bcos dole ne Hammad yaso abunda nake so..”
   
    Gauron numfashi ta saki da fad’in
       “Ni kam gaskiya Yallab’ai am tired, ta yaya zaku sani tsakiya kai kana fad’a min dole ya saurareka nd shi d’in ina fad’a yana gaya min bazai yi ba..?? Gaskiya nima k’ok’ari na ya gaza,wannan karon kam na kasa yin nasara,saboda haka ka neme shi kuyi maganar,bazan iya ba gaskiya..”
   
      “Asiya ni kike fad’a ma baza ki iya ba..?? Kada Allah yasa ki iya d’in, aure ne babu fashi, ko HAMMAD na so ko baya so sai ya karb’i zab’in da nayi masa..”
   
     “To shi kenan ai,,in dai wanna maganar ne,gaka nan ga kuma Hammad d’in, kuyi a tsakanin ku ni kam ba sai na sake shiga ba,zan zama y’ar kallo ne kawai a tsakaninku.. Amma gaskiya alhaji wannan lamarin yayi yawa,fisabilillahi ta yaya ne zaka takura yaron nan akan zab’in ka,ba zaka tambaye shi ba ko yana da wacce yake so,shi kenan ko wane lokaci sai abunda kake so ne za’ayi..? Sai kace saukar wahayi..”
   
     “Asiya ki saurara min da wad’annan maganganun naki,,kada ki fusata ni,,umarni na bayar kuma dole ne ayi min biyayya akan dukkan abunda nake so.. Kinji na fad’a miki,ba wai Hammad kawai ba akan kowa naso yanke hukunci haka zanyi..”
   
      “Shi kenan ai,,Allah ya bada sa’a,, kuma ni kaina na fahimta,kanka kad’ai kake so,dole Hammad ya fad’a dan kuwa baka yi masa adalci wollahi,yaron nan yana yi maka biyayya iya kar iyawarsa,amma yau har ta kai kasa shi fad’in maganar da bai dace ajita daga bakinsa ba,,ya kamata ka sauya shawara gaskiya..!”
   
     “Ni kike fad’awa magana Asiya..?? Da kyau kinji ba,,yayi miki kyau..”
      K’it ya kashe wayar yana furzar da zazzafar iska, zuciyarsa banda tiriri babu abunda take yi bcos kalaman Mamma sun k’ona shi da yawa.
      Itama Mamma a nata gefen wahalallen ajiyar zuciya ta sauke,a hankali kuma ta tab’e baki sannan ta shige mota ko gaisuwar da ma’aikatan gidan suke mata bata iya amsawa ba,tasa driver yaja suka bar gidan.Tafiya suke amma gaba d’aya hankalinta yana kan maganganun da suka gama da Daddy,cikin zuciyarta zuciyarta sai sak’awa da kwancewa take kan lamuran Daddy,tabbas ko ita zata shaida da maganar Hammad Daddy’nsu ya cika son kansa da yawa,idan ba haka ba wane dalili ne zaisa ya dage akan zab’awa Hammad d’in matar da shi zai zauna da ita ba shiba..? Har sun sauka daga kan mayangu road sun d’auki hanyar state road zuciyarta ta kasa nutsuwa a fili ta furta
      “Idan nayi maka haka yaro na banyi maka adalci ba,,tabbas ba tun yanzun ba ka fad’a min kana da wacce kake so.? Shin me zaisa ne ma Daddy’nka yace sai shi zai zab’a maka mata..?? Ya zama dole nayi wani abu idan ba haka ba lallai ne na tabbata wacce take son kanta da yawa..”
   Lokaci guda ciwon Hammad da bayanin likita a wancan lokacin ya sake dawo mata,da sauri ta ce
      “Tsayar da mota..!”
     Saurin taka brake driver yayi yana fad’in
      “Hajiya..!”
      Ko kafin ya fad’i abunda yake ransa tuni ta riga shi
     “Maza mu koma gida da sauri..”
   
      “Hajiya gurin aikin fa..??”
   
     “Cewa nayi ka maida ni gida.. Na fasa zuwa.”
     Cikin girmamawa ya amsa sannan ya juya kan mota suka kama hanyar gida,,suna isowa bayan ta shiga ciki direct d’akin Hammad ta nufa a gurguje, ko knocking bata yi ba saboda yadda gabanta yake tsananta fad’uwa da sauri ta tura k’ofar d’akin,yadda tayi tunanin haka ce ta faru sai dai bata kula ba tun farko,a hankali taci gaba da dubawa amma shiru babu ko alamar yana nan,fitowa tayi ta tambaya ko ya fita ne,gaba d’aya ma’aikatan gidan suka tabbatar mata da basu ga fitarsa ba,duk yadda Mamma take tunanin al’amarin sai ya nemi shallake tunaninta.Line Dad tayi k’ok’arin kira amma wani abun mamaki yak’i amsawa,sai daya masa miss call ak’alla sama da goma a lokaci guda sai dai ko guda bai d’auka ba,bare tasa ran zata ji magana mai dad’i daga gare shi,bisa dole ta sawa ranta hak’uri ta daina kiransa bcos bata da yadda zata yi masa.
     Wasa² al’amari ya tsananta,tsakanin Mamma da Daddy an daina zaman dad’i duka akan tayi magana akan ta gaji itama bazata iya ba,tun daga ranar gaba d’aya sai kawai ya share ta bama ita kad’ai ba duka gidan yak’i kiran kowa kuma yak’i zuwa garin,shi kansa Hammad a bangarensa bai sake bi takan saba,dan ma kada suyi tunanin ya hak’ura ne da maganar,shi yasa har aka shafe tsayin satittika bai kuma tuntub’ar kowa cikinsu ba.
     Ita kanta Mamma a nata b’angaren zuwa wannan lokacin gaba d’aya ta gama tabbatarwa zuciyarta ya hak’ura ya janye k’udurin nasa ne,amma abun mamakin cikin satin sai ga labari ya isketa next month auren,,cikin gaggawa ta kira line Daddy wanda har ta manta rabon da suyi waya ma,bayan ya d’auka sun gaisa duk da a sharce yake amsa mata tace
    “Yallab’ai.! Wai mene ne kake k’ok’arin yi ne.?? I thought ka hak’ura da wannan batun tun ba yanzun ba,na rigafa na sanar maka Hammad yana da wacce yake so..!”
     Banza ya mata bai bata amsa ba,jin haka yasa ta fad’in
      “Hello..! Yallab’ai.!”
   
      “Ina saurarenki Asiya..!”
   
     “Uhhuumm..! Naji kayi shiru ne baka ce komai ba..!”
     Murmushi yayi yana fad’in
       “Me kike so nace ne Asiya..?? Nace na janye ko kuwa me kike nufi.!?”
     Shiru Mamma tayi bata amsa ba,bcos maganarsa ya tabbatar mata da bai janye ba d’in,a hankali ta saki ajiyar zuciya tana fad’in
       “Shi kenan Yallab’ai,, amma dai ina son ka kasance mai duba matsalolin wad’anda Allah ya d’ora alhakin kula dasu a hannunka,idan kana ganin ka kyautatawa wasu mu da muke makusantanka ka munana mana,Allah fa bazai bar hak’k’in mu akanka ba,,ka tuna da cewa Ubangiji (S.A.W) da kansa ya kyamaci zalunci sannan ya saka shi a tsananinmu a bun haramtawa,ina so kafin ka yanke hukunci kayi tunanin halin da za’a shiga,idan har ka takura shi akan abunda baya so to ina son shaida maka ka tsammanta ganin abunda baka yi tunanin faruwarsa ba a gaba…”
     Tana gama fad’ar abunda take so itama bata jira taji me zai fad’a ba ta kashe wayarta,,ga Daddy kuwa tana kashewa baki bud’e yabi wayar da kallo,tabbas yasan gaskiya ta fad’a to amma idan har ya yarda yace zai janye lokaci guda,kai tsaye sai ya fito yace da aminin nasa ya janye batun auren daya nemawa Hammad d’in..?? Kai ina,ko kad’an bazai iya aikata haka ba,dole dai yayi wani abu akan matsalar,har yayi shiru kuma wani tunanin ya fad’o masa
   Lallai ne ya kamata yayi wani abu akan wannan matsalar,,to amma tunda haka nema mai zai sa bazai jarraba yaga idan har da gaske ne akwai wacce Hammad d’in yake so ba,idan yaso sai ya sanar dashi ya amince,sannan ya sashi gabatar dasu gurin iyayenta kawai,idan yaso dai² lokacin da yayi niyya sai ayi komai a gama bcos ya gama shaidawa makusantansa nan da 1 month auren Hammad d’in,saboda haka ne baya son a sab’a daga yadda ya tsara,,idan kuma har aka samu sab’ani daga hakan ko yaya yake shi kenan sai kawai ya soke uzurinsu a gurinsa,kunga kenan faruwar hakan dole dai yasa abi nasa,ko ana so ko ba’a so,tunda har ya bada dama dole dai ayi hak’uri a karb’i hukuncinsa.
   Murmushi yayi lokacin da wannan shawaran yazo masa,yana gama yanke hukuncin kai tsaye sai ya fara k’ok’arin kiran Hammad cike da son yi masa albishir.
   
   

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *