ALKAWARIN JINI CHAPTER 9 BY _HAWWA MUH’D USMAN

ALKAWARIN JINI CHAPTER 9 BY _HAWWA MUH’D USMAN

                 Www.bankinhausanovels.com.ng 

*NEW YORK CITY..*

     Wani irin lafiyayyen sanyi ne daya gauraye da k’amshin dad’ad’an turaruka masu sanyaya ruhi suke tashi a cikin office d’in,ko ina ka kalla a tsaftace yake kamar ka yarda abu a gurin ka ci saboda yadda komai yake a zaune a muhallinsa,ko kad’an sanyin baiyi yawa ba bare ace zai cutar da ruhii,,cikin wani irin yanayi mai saukar da kasala k’amshin daya cakud’e da sanyin AC yake ci gaba da tashi d’auke da wasu irin yanayi daban² wanda su kad’ai ma sun isa su sanyayawa mutum zuciya tare da haifar masa da nutsuwa mai tattare da kwanciyar hankali,,yana zaune a saman had’ad’d’e kuma makeken table d’in dake cikin katafaren office d’in yana ta aikin binciken file’s da aka shigo masa da su babu jimawa,,a zahirin gaskiya duk wanda ya kalleshi tabbas zai yi masa kallon mutumin dake cikin nutsuwarsa,,sai dai ko kad’an idan da zaka bincika zuciyarsa ba haka abun yake ba,musamman idan ace shi da kansa zai tono maka k’asan ransa,wansa babu komai cikinsa face tunanuka da damuwoyi da suka taru suka yi masa jingim,,yayi zurfi cikin aikin da yake kan yi kiran Daddy ya shigo masa,da wani irin mutuwar jiki da yake fama da shi tun bayan dawowarsa daga 9ja ya d’ago kyawawan idanunsa ya zuba su akan fuskar wayar,kallo d’aya ya yiwa wayar da sunan da yake lilo akai gabansa yayi wani irin mummunan fad’uwa,kamar wanda bazai amsa kiran ba tunda ya fahimci Daddy’nsa ne nd yasan kuma dalilin da zaisa Dad d’in kiransa,kawai sai ya share yaci gaba da kallon fuskar wayar,daf da kiran yana shirin katsewa wata zuciyar tace masa

     “Kada yayi haka Hammad,ko dai ace babu komai Daddy mahaifinka ne,duk abunda zai maka bai cancanci wannan wulak’ancin ba,kai d’in kana da ilimi bai kamata kayi aiki irin na jahilan mutane ba,,kawai ka d’auka kaji mene ne yake faruwa da har ya sashi kiran naka..”

   Dakatawa yayi saurin yi da aikin da yake yayi answering call d’in,bakinsa k’unshe da cikakkiyar sallama.Muryan daddy kamar ba shi ba jin Hammad d’in ya d’auka kiran,bayan sun gaisa cikin hikima Daddy’n yayi ta d’an jansa da wasa,dole ba don ya shirya ba ya d’an saki jiki kad’an sai dai bai zarme ba,,a mafi yawan lokuta musamman irin wannan lokacin da yake cikin danuwa sosai al’amuran Daddy suke d’aure masa kai,sai dai duk da hakan ko kad’an baya tab’a nunawa,kuma hakan baya tab’a hana masa sakin jikinsa suyi magana ko wane iri ne duk da yadda yake tsananin jin haushin Dad d’in nasa musamman a yanzun da yake nuna son kansa.

    “Hammad! Duka na samu labarin abubuwan da suka gabata.. Saboda haka nema na yanke shawaran sanar da kai wani daddad’an albishir,,ina fatan kuma kaima zai faranta maka..!”

     Cije lip d’insa yayi kad’an zuciyarsa cike da bak’in ciki,a hankali ya maida idanunsa ya lumshe yana jin saukar wani abu kamar ruwa a cikin zuciyarsa,shi kam in dai ba k’addara ba ta ubangiji ya tabbata babubwani lokaci da rana zata fito ta gabas ta fad’i a yamma Daddy ya kira shi ya masa wani albishir,kuma a hakan ma wai har yana ik’irarin mai dad’i,,how comes Daddy zai bashi irin wannan albishir d’in..? Yaushe ne hakan zai faru..? Da wane lokaci.? Wata zuciyar ce tayi saurin bashi amsa da

      “Maybe a mafarkin ka daka saba yine hakan zai kasance.”

     Murmushi yayi mai ciwo tunawa da abubuwan da suka faru cikin satittikan da suka gabata,dama na can baya da suka faru a cikin rayuwarsa.Haka kawai sai yake jin zuciyarsa babu dad’i duk da dama ba’a cikin jin dad’in take ba,tabbas yayi abunda bai kamata ba a baya,duk abubuwan daya aikata da maganganun da ya fad’awa Mamma ko kad’an basu dace ace shine yayi su ba,kenan ba don Allah ya rufa asiri ba,Mamma’n bata tsaya biye masa ba mene ne kenan zai faru.? Sake matse idanunsa yayi while hannunsa a saman forehead d’insa yana murzawa a hankali² saboda ciwon da yake ji yaba shigarsa

      “Hope kana sauraren abunda nake cewa Hammad..!”

   A d’an firgice yayi saurin bud’e idanunsa da damuwa tasa su k’ank’ancewa

      “Ehh! Dad ina saurarenka..”

     Ya amsawa Dad d’in murya a shak’e

   “Good.! D’azun munyi magana da Mamma’nka ne sai take sanar da ni wata magana,to shine nake son yin confirming,,kuma kaima ina son ka fad’a min gaskiya,shin da gaske ne akwai wata wacce kake so…?”

    A bazata yaji kalaman Dad sun zo masa,cikin sauri ya gyara zamansa yana sake rarumo wayar ya rik’e ta sosai a kunnensa

    “Haka ne Dad..!”

    Sai da Daddy yayi jim sannan ya amsa masa

      “To da kyau..!”

       Shiru Dad ya d’an sake yi yana tunanin mafita,while shi kuma Hammad a lokacin ji yaje kamar ya bud’e baki ya tambayi Dad d’in abunda yake shiryawa,muryan Daddy ce ta katse masa hanzari inda yake sake tambayarsa

      “A wane gari/unguwar ne gidan nasu yake..?”

     Shiru yayi ya d’auke wuta zuciyarsa cike taf da fargabar abunda zai fad’awa Daddy kan wannan tambayar,bcos yasan duk abunda zai fad’a a yanzun zai fad’a ne kawai amma bawai dan ya san gaskiya ba ko kuma ya sani ba,sai dai zai fad’a ne kawai don tsoro da gudun kada yaje wani target ne Dad d’in ya shirya masa,,a zuci ya tsaya shawara da tambara kansa abunda ya dace yayi tun kafin Dad ya harbo jirginsa

   “What should i tell him..!? Shin na fad’a masa ban san inda suke ba yanzun ko kuwa na k’irk’iro wani abu daban na shaida masa..??”

      Wata zuciyar ce tayi saurin kwab’arsa ta hanyar bashi shawara

   “A’a Hammad kada ka sake kayi gaggawa,,ya kamata kafin kayi magana ka fara duba abunda zai iya faruwa a gaba,shin idan ka fad’awa Dad d’inka haka yazo yace tunda baka sani ba sai dai ka auri zab’insa fa..?? Ita shi kenan kun rabu..? Hakan na nufin ka hak’ura da neman burin zuciyar taka.?”

   Saurin girgiza kai yayi yana kiyastawa a zuciyarsa

   “Ko kad’an bazan tab’a rabuwa dake ba,,a ko wane irin lokaci,halinvtsanani ko farin ciki zuciyata taki ce ke kad’ai..”+

   “Good.! Hammad good.! To me zai hana baza ka iya b’oyewa Daddy ba,later sai ka sake tsananta bincike akan inda suke,,kaga kenan kafin duk wani hukunci da Dad zai yanke zai iya yuwuwa ka samo inda suka koma ko ba haka ba..?”

  

  “Yes! Wannan shawarar ita zan d’auka,tunda tayi min zanyi amfani da ita kawai.”

   Kamar yadda zuciyarsa tayi saurin kwab’arsa,haka nan sai ya tsinci kansa cikin in’inar da baisanma lokacin daya watsowa Dad d’in nasa tambayar

      “Dad mene ne za kayi haka da sauri kake neman gidansu..!?”

   

     Murmushi Daddy yayi cikin wani irin yanayi mai wahalar fassaruwa ya bashi amsa da cewa

      “Zanyi abunda ya dace ace nayi a matsayin mahaifi,,kamar yadda mahaifiyarka ta fad’a min tace kaina kad’ai na sani,bana duba matsalolin wad’anda suke k’ark’ashina.. Saboda haka na kira ka yanzun ba don komai ba,sai domin na shaida maka,tunda har Allah yasa kun nuna baku amince da zab’in da nayi ba,to ina so daga yanzun zuwa wata d’aya mai zuwa,four weeks kenan ko.? Ina so ka gabatar damu a gurin iyayen ita yarinyar da kake so d’in,,idan kuma ba haka ba,ko aka samu matsala koma dai yaya ne wani abu ya shigo tsakani ya nemi zarta k’aidar da na gindaya,tofa ina mai tabbatar maka sai dai kace ban fad’a maka ba,amma ko tantama babu dole kayi hak’uri kabi zab’in da nayi maka.. Ina fatan ka fahimci abunda nake nufi..?”

     Har Dad ya k’are maganar da yake yi Hammad bai daina mamakinsa ba,wanitunani zuciyarsa ta kawo masa har ya fara waswasi² akan anya ma Dad d’in bashi da masaniya akan abubuwan dake faruwa da shi da duk halin da yake ciki..? Katse masa tunani Dad ya sake yi ta hanyar tambayarsa

      “Ina fatan kaji abunda nace kuma ka rik’e..?”

     A sanyaye kamar mutumin da aka zarewa laka ya amsawa Dad da fad’in

      “Ehh! Daddy na fahimta..”

   

      “To! Me kace..? Shin hakan yayi maka ko bai maka ba mu canja wani tsarin..?”

   

     “A’a Dad yayi..?”

   

      “Ka tabbatar yayi maka..??”

   

      “Ehh! Dad,,yayi sosai..”

   

       “Idan bai yi bafa ka sanar da ni.. Tun kafin gaba a samu matsala,,ya kamata ka fito ka sanar da ni kai tsaye tunda ni na buk’aci ka sanar dani d’in..”

     Guri d’aya ya zubawa ido zuciyarsa cike da fargabar abunda zai iya faruwa ya sake amsawa da

     “A’a Dad in sha Allah babu abunda zai faru.. Hakan yayi..”

   

      “To shi kenan,saboda haka sai ka fara shiri,aurenka na riga na yanke lokaci nan da wata d’aya,idan kuma har kayi sake aka samu sab’ani sai dai kayi hak’uri,amma baka da yadda zaka yi,dole ka karb’i zab’in da nayi maka,,saboda haka sai ka fara shiri daga nan zuwa wata d’ayan..”

   

      “Toh! Dad.. Na gode sosai,,Allah ya k’ara girma..”

      Jikinsa a matuk’ar sanyaye yake maganar,,lokacin da suka gama magana da Dad bayan sunyi sallama,gaba d’aya ya kasa ajiye wayar daga hannunsa,damuwa mai girma ta sake zuwa ta rufe shi,wayar ya shiga jujjuyawa a hannunsa yana sake binta da kallo

      “Shin ta ina ne zan fara..!?”

       Ya watsawa kansa tambayar da a halin da ake ciki yana jin ba shi da amsarta nd bai san yadda zaiyi ya samo ta ba,duk wani hope da yake jin yana da shi a lokacin zuciyarsa taba sanar da shi ya rasa shi,,kalaman Dad d’insa na kusan k’arshe suka sake dawo masa a kwakwalwa

    _”Zanyi abunda ya dace ace nayi a matsayin mahaifi,,kamar yadda mahaifiyarka ta fad’a min tace kaina kad’ai na sani,bana duba matsalolin wad’anda suke k’ark’ashina.. Saboda haka na kira ka yanzun ba don komai ba,sai domin na shaida maka,tunda har Allah yasa kun nuna baku amince da zab’in da nayi ba,to ina so daga yanzun zuwa wata d’aya mai zuwa,four weeks kenan ko.? Ina so ka gabatar damu a gurin iyayen ita yarinyar da kake so d’in,,idan kuma ba haka ba,ko aka samu matsala koma dai yaya ne wani abu ya shigo tsakani ya nemi zarta k’aidar da na gindaya,tofa ina mai tabbatar maka sai dai kace ban fad’a maka ba,amma ko tantama babu dole kayi hak’uri kabi zab’in da nayi maka.. Ina fatan ka fahimci abunda nake nufi..?”_

      Duniyar tunani ya sake lulawa,yayin da maganganun da suka yi da Daddy gaba d’aya suke yi masa amsa kuwwa a cikin kunnensa

      “Lallai ne ya zame masa dole kafin wa’adin da Dad ya bashi yayi duk iya k’ok’arin da zaiyi ya samo inda suke,,idan kuwa ba haka ba,tofa ya sawa ransa salama komai da duk wani shirinsa zai lalace ne a lokacin da baiyi tsammani ba..”

    Cikin k’ank’anin lokaci gaba d’aya lissafinsa ya shiga k’wacewa,a hankali ya tattara duka file’s d’in daga gabansa ya tura su gefe,yadda yake jin jikinsa a wannan lokacin aikin gaba d’ayansa ya gama fita a ransa,hatta da zaman ma ji yayi ba zai iya ci gaba da yinsa ba,tsam ya mik’e tsaye bayan ya tattara wayoyinsa da keys d’insa ya fice daga office d’in,ko daya fito d’inma direct ya kama hanyar k’onawa gida ko sauraren su Sultan bai yiba bare ya tambaye su yaji idan sun kammala abunda suke su wuce tare,lokacin daya shigo cikin gidan ma kasa zama yayi,nan yayi ta zirga² daga nan zuwa can,ya jima cikin wannan halin kafin ya fara k’ok’arin kiran Mammansa,zuciyarsa sai azalzalarsa take akan son sanar mata abubuwan da suka faru tun bama tsakaninsa da Daddy ba,hatta da wad’anda suka faru a can baya.

      Kaf yadda suka yi da Daddy sai daya sanar mata bayan nan kuma ya d’ora da zayyana mata komai dangane da abunda ya faru da shi a can baya,bcos wancan lokacin data gwada taba son yi masa maganar k’in yarda suyi zancen yayi,sai yanzun da yayi ra’ayi dan kansa ya sanar da ita,yadda yake magana da damuwa kad’ai yasa Mamma ta fahimci irin girman damuwar da yake ciki,dan haka ko daya gama zayyana mata kaf abunda ya farun itama sai tayi amfani da wannan damar tayi ta bashi shawarwarin da zasu taimaka masa,had’e da k’ara masa k’arfin guiwan akan kada ya karaya yaci gaba da addu’ah sannan kuma yaci gaba da neman inda suka koma d’in,itama in sha Allah tayi masa *ALK’AWARIN* zata sa a bincika mata,tunda har Allah yasa ya fad’a mata inda ya tab’a ganin nata,bata kyale shi haka kawai ba sai data tabbatar ya d’an samu nutsuwa sannan suka yi sallama tana sake bashi hak’uri da shawaran kadafa ya fasa addu’ah,,yace mata

       “In sha Allah,,bazai fasa ba.”

  A haka har suka ajiye waya.

Cikin haka rayuwa taci gaba da yin nisa yayin da kwanakin da Dad ya d’iba suke zuwa suna wucewa tamkar zubar ruwa daga famfo,,sai dai har kawo wannan lokacin shiru ne babu wani labarin gano inda suke,,ata b’angaren Mamma na tun daya fad’a mata take bincike saboda tasan shi d’in ba lallai ne ya samu damar zuwa k’asar ba,sannan lokacin da suka yi maganar da yace mata zai d’auki hutu ya zo kawai,sai ya bincika da kansa ita tace masa ba sai yazo ba itama tana bincikawa,bcos bata so ya d’auki hutu yanzun lokacin auren kuma yazo yayi masa dai² da lokacin da zai koma bakin aiki,,ba don ya so ba sai don fad’in Mamma’n yasa yaci gaba da zama a k’asar,,ita kuma Mamma da take a 9ja ta baza masu mata bincike ta ko ina.

Tunda kwanakin suka fara tafiya hankalinsu duka ba a kwance yake ba,musamman Hammad da kullum cikin yiwa Mamma’n waya yake da tambayarta labarin an samu..?? Sai dai takan ce masa “A’a” idan ya sake kiran waya kuma ita take sanin yadda zata yi ta kwantar masa da hankali,a haka har suka kusan cinye sati uku daga wa’adin da Daddy ya d’ibar masa.Ranar da kwanaki suka cika sati uku dai² kuwa Daddy ya sake kiransa a lokacin yana gida kwance damuwa duk ta dabaibayeshi aikinma da kyar yaje ya dawo,,tun kafin wannan lokacin Daddy ya fahimci akwai matsala,sai dai ya b’oye ya nuna masa bai gane ba,sai tuni kawai da yayi masa akan maganarsu,nan kuwa Hammad ya rasa bakin da zai yi magana ya kare kansa da shi,a haka har Dad ya gaji ya kashe wayarsa coz ya gama fahimtar inda ya nufa sanar masa ne kawai bazai iya yi ba,,ko daya kira Mamma a lokacin itama bata iya sanar da shi ba,duk da a maganarta akwai damuwa,babu wanda ya takura a cikinsu akan lallai sai sun sanar masa ya rabu da su duka yaci gaba da shirinsa don yace aure babu fashi a wannan karon,dama² ma da ace sun sanar masa da damuwar daya saurara,amma tunda sunyi shiru shima bari yayi musu bakam.

   

*PENNSYLVANIA CITY..*

     Kwanaki kusan biyu kenan da take kwance jikinta yak’i dad’i,a y’an tsakanin duka kusan tana rayuwa ne amma cikin zuciyarta babu dad’i,tunda satin ya shiga ko wane yini da zai zo ya tafi kawai tana yinsa ne amma sam babu wadataccen lafiya a tare da ita,cikin skul d’inma idan sunje sai dai tayi ta bin komai da ido sai kwanciya kamar ruwa,magana idan ba ya zama dole ba ko ansaka da ita sai taga dama take amsawa,haka take shafe tsayin yini ba tare da tayi kwakwaran magana da kowa cikinsu ba,tun abun yana damun k’awayen nata har suka saba da halinta,sai dai su kansu suna tausaya mata musamman a lokacin da suka ga tayi rama,,yauma tun da suka dawo take kwance jikinta tun suna school ya sake rikicewa,wannan dalilin yasa ko da suka dawo su Badra ne kawai zaune,su uku kad’ai suke ta tattauna yadda zasu tafi 9ja,saboda halarta bikin Yah Hammad,kasancewar Daddy ya sanar mata da batun tun da suka yi waya kafin yanzun,shirin tafiyarsu 9ja kawai suke cike da zumud’i suna kuma hiran yadda bikin zai kasance da abubuwan da zasu yi idan sun koma,,kamar ancewa da Jannat ta d’ago haka nan tun data kallo inda take kwance idanunta rufe kamar mai bacci,cikin tausayawa ta sake kallonsu Badra,bayan tayi jim na wucewar wasu sa’o’i sannan tace

      “Y’an uwa nifa ina da shawara..!”

   Duka suka kalle ta suna sauraron suji abunda zata fad’a,shirun itama tayi tana tunanin abunda zata ce nd still tana kallonsu kamar yadda suke yi,cikin damuwa Zeeharis taja tsaki da fad’in

   “Wai ke mene ne zaki fad’a ne..? Kince kina da abun fad’a kuma kin yiwa mutane shiru..”

   Cikin jimami ta fara kad’a musu kai kafin tayi musu nuni da inda Sabina take kwance

   “A gaskiya ni dai ina tunanin,,me zaisa wai ba zamu tafi dukanmu bane,idan yaso ko gidane sai mu rakata taga mahaifanta ko ya kuka ce,nifa ina tunanin har da alhinin su yasa ta kwanciyar nan,,kunga idan mun tafi mu biyu mun barku a nan baza kuji dad’i ba gaskiya saboda sabo,amma idan muka tafi duka ganin mahaifan ma rahama ne ai ko..??”

   “Gaskiya ne Lady kin kawo shawara,nima dama tun ba yanzun ba nake wannan maganar,,dama kuma ko babu rashin lafiya yadda muke dai a cikin makarantar nan ya kamata ne ace mun tafi duka sai mu dawo idan an kammala hidimar biki ko ba haka ba..??”

   Jinjina kai Jannat tayi tana amsawa da

     “K’warai dear kinyi magana..”

  Murmushi kawai Zeeharis tayi tana fad’in

   “To ku da kuke wannan maganar haka akeyi.? Dan kawai kuna son zuwa biki sai kuce zaku janyemu duka mu tafi..??”

   “Ehh! Mana ai saboda mun san mun zama d’aya ne mu duka shi yasa zamu tafi taren..”

   “A’a gaskiya ba’a haka,kunga kawai ku tafi ku kad’ai kada mu tattara mu tafi wani abun ya faru a school.”

      Saurin tarar numfashin ta Badra tayi

   “A’a Malama,kinga kawai dai kice zaki k’i zuwa ne,amma mene batun wani abu da zai faru..?? Sufa nan ba kamar k’asar mu bace,da zaran munyi report babu abunda zai faru har muje mu dawo.. Kuma ma ai naga babu wanda bai sanmu ba,dan mun tafi cikin tak’aitaccen lokaci ne zamu dawo,kuma duka ma Allah sa muyi one week zamu dawo.. Bcos Daddy ma bazai barmu mu jima ba sosai a can..”

   “Haba friend ki fahimci abunda nake nufi mana,bikin nan fa na brother d’inki ne bawai naki ba,idan ace yau bikinki ake yi me zai hana baza muje ba duka,amma tunda biki ne na namiji ku d’in kuje mana ai ya wadatar mu sai mu zauna..”

   “Kinga kawai kice min baza kije ba,zaki tsaya b’oye² ni gara da kika fito ma kika nunamin matsayina a gurinku.. Dama tun farko na fahimta wollahi yadda muke zaune daku ba haka ku kuke zaune da mu ba,,shi kenan tunda haka ne,Allah ya had’a kowa da masoyinsa na gaskiya..”

    Yadda ta d’auki d’umi akan maganar yasa Zeeharis zuba mata idanu tana kallonta cike da tsantsar mamakinta

   “Haba friend mene ne yayi zafi haka,da zai sa ki fad’i irin wannan maganar..??”

   “Ai kema kin san ko mene zai janyo d’in..”

   Ajiyar zuciya Zee tayi tana rik’o hannunta

   “Allah ya huci zuciyarki k’awata,tunda kika fad’i haka Allah saina baki mamaki,in sha Allah daga wannan karon bazaki sake fad’ar makamanciyar wannan maganar ba,,zamu tafi tare amma ki sani bazan je gida ba,bcos nasan in dai Abbana ya san naje wollahi zai bani kashi ne,dan yana sane da abunda ke faruwa,zai ce me nazo yi al’halin ba lokacin hutu bane,,saboda haka ina so kiyi farin ciki ki kuma kore shakku akan zamanmu da ku,duka zamu tafi tare shi kenan hakan yayi miki dad’i..??”

   Hararar wasa tayi mata sannan ta rungume ta tana fad’in

  “Da kuwa naji dad’i wollahi mara misaltuwa..!”

   “Shi kenan ai babu sauran k’orafi ko..??”

“Babu kam..!”

  Duka suka yi dariya suna ci gaba da had’a kayan tafiyar tasu,juyi Sabina tayi a hankali cikin azabar damuwa ta kallesu duka,haka nan take ji a ranta inama ace tana da yalwataccen kuzari a jikinta da ta kasance a tsakaninsu itama anyi hiran da ita,sai dai babu yadda zata yi dole tasa ta keb’ance kanta a gefe guda kamar mai laifin dake tsoron kamu,,gefe guda kuma tunanin Innarta yana sukar zuciyarta,y’an siraran hawayen da suke sakkowa saman fuskarta tayi saurin gogewa tana sake shigewa cikin bedspread d’in data lullub’e jikinta had’e da sakin kuka mara sauti,,sai da tayi mai isarta sannan ta goge fuskarta ta fito a ciki,a hankali kuma ta mik’e ta nufi hanyar toilet da kyar²,dukansu suka sake binta da kallo mai cike da tausayawa.

*NIGERIA..*

    Duka kwanakin biki da suka rage yau baifi kwana hud’u ba,amma Daddy tuni har ya kamo hanya ya dawo Kano,lokacin daya iso gidan ya iske shi kamar yadda ya tafi ya barshi,amma daga zuwansa nan aka ci gaba da shirye² dan ita Mamma kusan gaba d’aya ta zare hannunta a sabgar,Daddy dai shi yake ta shirya komai sai taimakawar ma’aikatan dake gidan,,kasancewar yau laraba nd tun kafin ranar yake saka ran ganin Hammad amma sai yaji shiru ba tare daya ji wani gamsashen bayanin zai zo ko A’a ba yasa shi ci gaba da kiran wayarsa dan yaji zai taho d’in ne kamar yadda ya shaida masa ko kuwa dan ya fad’a masa lallai² kada ya bari Friday ta riske shi a can,,yana kira ya riski y’ar baturiyar nan tana shaida masa duka layukan nasa a kashewannan yasa sai yayi zaton wata k’ila ko yana cikin jirgi ne shi yasa sai ya hak’ura bai sake kiransa ba,yaci gaba da zuba ido yaga ta inda zai zo k’asar,,duka sauran y’an uwa da duka abokanan arzik’i Daddy shi yayi ta bada goronsu aka kai musu,dan haka shi yake matsayin uban ango kuma shi ne uwar,k’ark’arin Mamma da shiga harkokin sai ya kama dole,amma ta wasu b’angaren gaba d’aya ta tsame kanta gefe bcos tana taya d’anta jimamin wannan auren k’addarar.

*NEW YORK..*

        A can New York ma rikici ne ya b’alle tsakanin Hammad da su Sultan tun daren ranar talata suke ta abu guda har wayewar gari basu daina ba,kasancewar tun bayan da Daddy yaga Hammad yayi masa shiru da batun neman auren da yayi masa,ya kuma fahimci babu arzik’i a ciki,shi yasa kawai sai ya koma maganarsa da Sultan tunda shi angon yak’i bada had’in kai,duk wasu shirye² daga Sultan sai Sadeeq su kad’ai Daddy yake nema tun da kwanakin suka sake gabatowa ya ajiye Hammad gefe,,a cewarsa ya fahimci daga shi har Mamma’nsa so suke su saka wani ciwon ya kamashi shi yasa suka k’i amincewa su shiga sabgogin bikin,,rigima sosai suke tun da suka takura masa akan ya shirya su bar k’asar,yayin da shi d’in ya kafe kai da fata idan har ba’a gano masa inda his Lady take ba babu shi babu zuwa 9ja kuma aurenmu idan sunyi masa sa san inda zasu ajiye matar amma shi dai baya auren,sai dai koma mene ne zai faru ya faru,,rigima dai tak’i ci tak’i cinyewa tsakaninsu har sai da ta kai ga Sultan ya kira Daddy ya shaida masa a halin da suke ciki,bai nuna masa b’acin ransa ba har suka kammala wayar,,Daddy kuwa yana ajiye wayar ya shiga safa da marwa zuciyarsa cike da tunanin irin abubuwan da zasu faru idan har Hammad ya barbad’a masa k’asa a idanu,hanyar fita a d’akin ya kama har ya fita ko me ya tuna kuma sai ya dawo da sauri,waya ya d’aga cikin abunda bai wuce seconds talatin ba ya fara magana

         “Ina kike..??”

     Banji me aka ce daga d’ayan gefen ba sai dai naji Daddy ya sake yin magana cikin fushi da fad’a²

    “Lallai² kizo bedroom d’ina yanzun ina son ganinki,,kada kuma ki b’ata min lokaci.!”

    D’if sai ya kashe wayar yaci gaba da moving asides zuciyarsa tam da takaicin irin kunyar da Hammad yake k’ok’arin sashi yaji,,shigowar Mamma ce ta sashi dakatawa da sauri ya tare ta yana jifanta da wasu irin kallon da sai da taji jikinta ya bata babu lafiya,cikin dauriya bayan ta d’auke kanta daga kallonsa tace

    “Yallab’ai..! Gani Allah yasa dai lafiya kayi min irin wannan kiran na gaggawa..”

   Takaici maganarta ta k’arawa Daddy,nan ya shiga zazzaga mata ruwan bala’i ta inda ya shiga ba tanan yake fita ba,har sai daya tabbatar ya zazzage mata kaf b’acin ransa sannan ya d’ora da fad’in

“Awa d’aya kacal na baku daga yanzun zuwa lokacin da zata cika dake da yaronki wollahi ku tabbatar kunyi abunda nake so,idan ba haka ba wallahil’aziiym sai na b’ata muku ta yadda baku yi tsammani ba..”

  Yana gama fad’an ya wuce abunsa ya barta nan tsaye,,hankalin Mamma idan ya kai dubu a yau ya kai k’ololuwa wajen tashi,musamman yadda taga Daddy yana tada jijiyoyin wuya lamarin ya sake firgita ta,tabbas shekaru basa k’arya sai dai sanin da tayi masa a da shekaru kusan talatin da aurensu basu tab’a samun sab’anin da zaiyi mata irin wannan maganar ba,sai dai tunawa da hausar nan ta malam bahaushe da yake cewa “sabo da kaza baya hana a yankata”,,da kuma kasancewar yau da gobe wacce ke janyowa amarya tasha d’an banzan duka,take yasa ta sake gasgatawa tsayin zama baya hana a yiwa mutum rashin mutunci,addu’ah taci gaba da yi a zuciyarta akan Allah ya sauk’ak’a lamarin,dama kuma tun data shigo taga halin da yake ciki take yinta har ya fita bata fasa ba,da kyar² bayan ta gama saita nutsuwarta sannan ta d’aga k’afafunta ta baro d’akin gudunma kada ya sake dawowa ya tarar da ita tayi sauri ta nufi hanyar d’akin ta,cikin zuciyarta tana tunani akan lallai ne ya zamar mata wajibi ta kira Hammad ta rarrasheshi ya taho d’in dan idan har bata yi haka ba,tasan kanta komai zai koma,a hakanma kuma ba tsira zata yi ba indai a gurin mijin nata ne.

  Ko mintuna talatin bata yi da fitowa a d’akin Daddy ba tana shiga nata bedroom d’in tayi k’ok’arin kiransa sai dai abun mamakin duka wayoyinsa a rufe,wannan dalilin yasa itama sai tayi amfani da line Sultan,bayan sun gaisa ta buk’aci ya bata Hammad d’in a waya,sun d’auki lokaci mai tsayi suna magana a waya kafin ta ajiye ta nemi guri ta zauna had’e da buga uban tagumi.

    

*SOME HOURS LATER..*

Around 9pm jirginsu ya sauka a 9ja,daga airport kai tsaye bayan sun samu cab suka nufo Mayangu road gaba d’ayansu,saboda tun tahowarsu Badra ta kafe akan sai dai su fara zuwa can idan yaso daga baya sai su wuce su kaita gida,bisa dole badon ta soba ta amince musu suka taho taren sai dai tunda suka d’auko hanyar haka nan gabanta yake tsananta fad’uwa,,duk hiran da suke tunda tayi shiru bayan sun baro airport d’in bata sake magana ba har suka k’araso cikin unguwar ta Nassarawa G.R.A,a dai² bakin get d’in gidansu mai cab ya ajiye su da kayansu,suna gama sallamarsa suka wuce ciki Badra da Zee a gaba suna janye da luggage’s d’in kayansu,sai Jannat data rik’o hannunta su kuma suna biye da su,tun daga bakin get d’in gidan Sabina take bin ko ina da kallo,a iya tsayin zamansu duk da ta fahimci daga irin gidan da suka fito,ko kad’an bata tab’a sawa a ranta gidan da suka fito ya kai haka ba,daurewa kawai tayi taci gaba da binsu amma can k’asan zuciyarta tana sak’a dole ne ta d’an ja baya dasu matuk’ar sun koma lafiya,,tana tsaka da tunanin har suka k’araso k’ofar shiga parlor’n gidan.

Alamu Badra tayi musu da su wuce a hankali dan bata son Mamma ta gansu yanzun,a hakan duka suka lallab’a a hankali,sai da Badra ta fara lek’awa,ta tabbatar babu kowa a parlor’n dan haka duka suka wuce da sand’a duk dan suna so su bawa Mamma surprise,sanda suka gama shigewa da gudu² suka wuce Bedroom d’in Badran,,a gyare suka iske komai d’akin sai k’amshi yake had’e da sanyin AC dake busawa,tamkar tana gidan bata je ko ina ba,hakan yasa ta jin dad’i a hankali sai ta bud’e hannayenta tana shak’ar ni’imtacciyar isakar y’anci,sai data gama tukun tayi saurin juyowa ta kallesu tana dariya

  “Hey! Guy’s mene ne kuka wani tsaya kallo na ne..?? Ku nemi guri ku huta tukuna mana.”

Girgiza kai Sabina tayi saurin yi tana fad’in

“Noo! Dear ya kamata na wuce gida,,amma muje na gaisa da Mamma sai na tafi ko..??”

   Hararar ta Badra tayi tana fad’in

  “Kin manta..! Daga zuwan namu shi ne zaki ce zaki tafi..?? Kije ina to da wannan daren.? Uhhuumm.! Lallaima Princess,wai da a zatonki da nace mu taho saimu rakaki gida,kin d’auka da gaske nake..? Ai wollahi kima sa aranki ko zaki fita a gidan nan sai da safe dan Mamma ma ba zata bari ba,bare kuma Dad da idan yaji zai fad’a..”

  Tana maganar tana mata dariya k’asa² su Jannat suna taya ta,had’e rai tayi saurin yi tana kallonsu duka suna ta dariya,a hankali kuma sai ta kad’a kai kawai tana fad’in

  “Ku dai wollahi kuna da matsala,in banda abunku ai ba sai kunyi min haka ne zan gane bakwa so na tafi ba,,idan kuka ce min mu taho tarema ya isa,tunda kun san bazan baku kunya ba.. Amma shi ne har sai kun had’a da min wayo kamar wata y’ar goye..??”

  Dariya suka ci gaba dayi,itama sai ta samu damar darawa,,daga haka kuma sai suka fice duka zuwa bedroom d’in Mamma da niyyar gaida ita tunda basu same ta a parlor ba,,knocking suka fara,Mamma ta tambaya waye,amma sai suka yi shiru,izinin shigowa kawai ta bayar dan tasan wata k’ila d’an mulkin mijin nata ne shi yasa yak’i amsawa da yake yana kan fushi da ita itama sai bata damu ba da shirun da taji,bud’ewa sukayi suka shigo ciki,,tunda suka shigo cikin bedroom Sabina ta sake bud’e ido saboda daular dake shimfid’e cikin ko wane d’aki,duk dama dai d’akunan daga na Badra sai na Mamma kawai ta shiga.

  Baki bud’e Mamma take binsu da kallo tun da suka shigo har suka k’araso kusa da ita,sai da suka zauna a gabanta ne sannan ta fizgo maganar da kyar

  “My kiddo..! Saukar yaushe..!?”

Dariya suka saka dukansu dan yadda Mamma take kallonsu kad’ai ya isa ya basu tabbacin sun mata bazata

“Bamu dad’e ba Mamma..!”

“Uhhuumm.! Lallai yaran nan wato sai kuka kasa fad’a min zaku zo ko..!?”

Tsagaitawa suka yi da dariyar da suke yi Jannat tana cewa

  “Mamma wollahi Badra ta hanani fad’a miki,amma har na d’auki waya zan kira ki tace wai mu bari kawai muyi muku surprise..”

  Murmushin k’arfin hali Mamma tayi tana fad’in

  “Lallai..! Ai kuwa gashi nan kunyi.. Saura ita Hajiya Aminar,na ga ya zata ji idan ta ganku,dan nima tunda ba’a fad’a min ba bazan fada mata ba,sai dai kawai ta ganku..”

 

“Eyy! Wollahi Mamma kada ki fad’a,kowa kawai sai dai ya ganmu.”

  Sake yin murmushi tayi mai d’auke da ma’anoni daban² sannan suka gaisa dasu,lokacin da tazo kan Sabina haka nan tunda idanunta suka sauka akanta take jin kamar ana yaye mata wani irin duhu daya lullub’e mata zuciya,a hankali take sake kallonta suna ta hira da sauran yaran,,itama kanta Sabinar tunda suka shigo d’akin kallo d’aya ta yiwa matar taji jikinta ya d’auki rawa kamar wacce ake kad’awa gangi,sai dai ba kowa zai fahimci halin da take ciki ba sai mai tsananin sa ido,zuciyarta ta shiga cikin wani irin yanayi tun a kallon farko.

  Rashin sarkewar da Mamma taga tayi ne yasa ta yi murmushi sannan ta basu umarni da suje suci abinci idan sun gama kuma sai su kwanta saboda gajiyar hanya zuwa da safe sayi hiran,dukansu kuwa suka amsa sannan suka yi mata sallama,suna ficewa daga bedroom d’in dama Sabina ce akan gaba wajen fitowa,dan duka tun shigarsu take jinta a takure,ko gurin cin abincinma a gaggauce ta iya yin hak’uri suka zauna a dining daga nan kuma suka koma sama,shima d’in ta riga su komawa,tana shiga wanka ta shiga ta fara yi,tana fitowa bayan ta shirya tayi sallolin dake kanta ba tare data tsaya bi takan kowa cikinsu ba tabi lafiyar gado.

*03:00am GMT.*

      Jirginsu Hammad ya sauka a filin tashi da saukar jirgi na Malam Aminu Kano,su kansu basu yi zaton zasu zo basu haura haka ba kafin ace su iso d’in,kai tsaye suma koda suka fito gida suka nufo kasancewar dare yayi nisa sosai,da yake titin babu traffic a lokacin yasa cikin mintuna ashirin suka k’araso bakin get d’in gidan,baiyi k’ok’arin kiran kowa ba dan ransa duka a jagule yake tunda Mamma tasa shi tahowa bisa dole,,get man d’inma Sultan ne ya masa knocking bayan ya bud’e musu suka shige ko gaisuwar da yake musu bai amsa ba,,tunda ya sako k’afarsa a cikin gidan yaji yanayin isakar dake shiga cikin jikinsa ta sauya,a hankali damuwar dake tattare da shi ta fara k’ok’arin raguwa,fargaba ta sake tsananta a gare shi,,a hankali yake d’aga k’afarsa yana tafiya tun daga bakin get har suka k’arasa shigowa cikin gidan….._Tsayin shekarun dana d’auka daga fara rubutuna har zuwa yau,babu wanda ya tab’a yi min irin abunda kika min,duk da nasan an sadaukar min da pages na litattafai a baya da dama da ni kaina ban san adadin su ba,amma cikin hukuncin ubangiji babu wanda yayi min kwatankwacin abunda kika yi,,na gode sosai² *MY FENERH (Matar Soja)* kece mutum ta farko data sadaukar da littafinta guda akaina,,dole naji daban a wannan lokacin,kuma dole kuma nayi alfahari dake saboda karamcin da kika nuna min,bazan gaji ba wajen nuna miki tsantsar farin cikina,haka ba zan gaji da binki da addu’ah ba,har sai ranar da numfashi ya yanke min,,dole na ne ni *REAL SMASHER* nayi alfahari da littafin *Y’AY’AN GATA* saboda kasancewarsa kyauta mafi girma kuma mafi soyuwa a gareni,,na gode³ sosai da sosai,ubangiji ya saka miki da mafificin alkhairinsa dear,ya duba bayanki,ya hasakaka rayuwarki tare da yalwata farin ciki a tsakanin zuri’ar ki,,kin sani hawaye a lokacin dana ga kyautarki,yadda kika sa wannan bakwa farin ciki ina rok’on ubangiji daya dawwamar dake cikin farin ciki mara yankewa.🙏_

    *Fisabilillah.! Nake miki son so habibtiiy..* 💞+

       A kulle suka tarar da k’ofar shiga parlor’n gidan,duk wata hanya da suka san zata sada su da ciki sun duba amma duka babu wacce suka tarar a bud’e,gefe suka ja gaba d’aya suka tsaya kafin a fara Kallon-kallo tsakaninsu da Hammad da shima yaja gefen fuska a d’aure kamar bai tab’a sanin yadda ake dariya ba,sun d’auki tsayin mintuna a tsaye shiru kowa da abunda yake tunani aransa kafin ya d’ago ya kallesu duka yana tab’e baki

    “Dude’s.! Wai mene ne muke yi a tsaye ne..??”

  Fuskar Sultan da mugun mamaki ya kalle shi yana fad’in

   “Ban gane me kake son fad’a ba,,me kuwa zamu tsaya yi a nan idan ba jira ba.!”

    “Uhhuumm..! Jiran na mene ne..??”

   “Ban sani ba..! Da Allah malam kada ka b’atawa mutane rai mana,sai kace baka san me muke jiran ba..”

   Dariya ya d’anyi kad’an irin wacce ya jima baiyi irinta ba,cike da zolaya kuma ya fito da keys d’in dake tare da shi yana wasa da su a hannunsa yana ci gaba da dariya k’asa²

    “Uhhuumm..! Zaka sani ne yayin da kuka yi ta tsaiwa a nan..”

      Sarai Sultan ya jiyo me yace amma sai ya kasa fahimtar abunda yake nufi,bayan kamar mintuna biyar kuma da sauri ya dawo gabansa ya wafce keys d’in,,dariya Hammad ya sake yi yana jinjina kai,Sultan kuwa ko daya karb’e keys d’in a hannunsa kai tsaye ya nufi k’ofar shiga parlor,wad’anda yake tunanin ya fara gwadawa take k’ofar ta bud’e,juyowa yayi ya kalli Hammad da tsananin mamaki

      “Lallai ma mutumin nan ka raina mana hankali,,da kasan kana da keys d’in amma kasa mu zaman jira..??”

   

     “Hankalin naku nawa yake dama..?”

     Yana fad’ar haka yayi wucewarsa ciki ya barsu nan tsaye da mamakinsa,gaba d’aya suka biyo bayan shi,ko da suka shigo hanyar bedroom d’insa suka nufa yana gaba suna tafe suna binsa a baya,,kasancewar babu wanda yasan da zuwansu a lokacin bayan get man d’in gidan,shi yasa har suka isa cikinma babu wanda ya gansu,,suna shigowa ko zama bai jira yayi ba ya wuce bathroom,,sai daya watsawa jikinsa ruwa bayan ya d’auro alwala sannan ya fito,nan ya iskesu duka sun baje saman bed d’insa,dariyar mugunta kafin ya k’araso inda suke,yana zuwa bai jira komai ba ya bisu da duka,a firgice duka suka mik’e suka zauna suna binsa da kallon tuhuma

     “Haba dude,,wannan wane irin abune haka.? Kawai sai da kaga mun fara bacci zaka tada mu..”

      Juyawa yayi ya barsu a gurin k’asa² yace

     “Lokacin sallar ya kusa zaku kwanta..??”

   

     “Amma dai ai baiyi ba ko..??”

   

     “Uhhuumm.! Ku kuka sani,amma dai ku sani babu mai kwanciya wollahi sai anyi sallah damu a jam’i..”

   

     “Haba dude,,wannan wane irin tsari ne to,tun ba’ayi sallar ba kace sai mun jira..?”

     Ci gaba yayi da tafiyarsa ba tare daya juyo ba,Sultan cikin jin haushin dukan daya masa yace

     “To wai ina ruwanka da yin sallar mu a jam’i..?? Idan munyi ai kanmu za mu yiwa ko.!? Wannan ai shishshigi ne.. Ina ruwanka idan ba muyi a jam’i ba..?”

   

     “Uhhuumm.! Allah yasa ban ji me kuka fad’a ba..”

   

   “Kaji sarai.. D’an iska babu abunda baka ji ba..”

   Dariya yayi ba tare daya sake magana ba ya ci gaba da k’ok’arin saka jallabiyar dake ajiye saman resting chair,yana gamawa har yayi nufin kwaniya wani irin yunwa ya taso masa,a hankali ya fara tuna rabon daya sawa cikinsa wani abu tun safe daya sha coffee,cikinsa ya d’an tab’a a hankali daya fara damunsa bcos sosai yake jin yunwar a lokacin,tab’e baki ya d’anyi kad’an sannan a gaggauce ya kama hanyar fita daga room d’in,cike da nufin samawa cikinsa wani abu yaci kafin lokacin sallah ya riske shi,,har ya je bakin k’ofa Sadeeq ya d’ago ya kalleshi yana cewa

     “Man.. Ka taho da mu..”

      Bai juyo ba yace

    “Me zan taho da ku d’in..??”

   “Abunda duk zaka je nema,,ai mun san bazai wuce abinci zaka je nema ba..”

  

  “Uhhuumm..!  Da kun san kuna jin yunwa kuka kwanta za kuyi bacci..??”

   “Haba mana,,kaifa wasu lokutan ka cika matsaltsalu wollahi..Baka uzuri ne kai a rayuwa..?”

Ci gaba yayi da tafiya yana kad’a kai,ba tare da yayi magana ba ya kama handle d’in k’ofar zai fita

   “Dude! Muna jira fa..!”

   Sai da yayi murmushi ya girgiza kai sannan yasa kai ya fita while yana fad’in

“Ku ci gaba da jira..”

   Yana fita Sultan yayi saurin kallon Sadeeq yana cewa

   “Dude.! Wollahi gara ka tashi mu bishi,wannan d’an rainin wayon wata k’ila daga can yaci gaba,dan bana tunanin zai dawo yanzun,,tunda kaga lokacin Sallah ya sake gabatowa bama zai dawo ba..”

    Lumshe idanu Sadeeq yayi yana fad’in

      “Kai bashshi da Allah,ni dama ba wani sosai nake jin yunwa ba,idan safiya yayi maci,tunda Allah yasa ya fice ni kwanciya zan idan an kira sallah ka tashe ni.”

     Harararsa Sultan yayi yana fad’in

      “Ai ni d’in da yake gadinka zanyi ba,dole ka bani sallahu,,wollahi to nima kwanciya zan,Allah yasa dai daga can ya wuce kada ya dawo.”

      Yana maganar ya sake komawa yayi kwanciyarsa,shima Sadeeq d’in sake gyara kwanciyarsa yayi had’e da rufe idanunsa dake d’auke da bacci yana fad’in

   “Asubah ta gari abokin..!”

     (Ni da nake gefe na kallesu duka nace “asubah kuma ta yaushe banda wacce ke gabatowa..?”)

   

     Tunda ta kwanta bayan data idar da sallah ko k’wak’waran juyi ba ta iya yi saboda tsabar gajiyar dake bin cikin jikinta,hatta da shigowarsu Zee a d’akin da duk hirar da suka yi kafin baccin duka babu wanda ta sani bcos ta ruga su kwanciya,nd lokacin data kwanta ko mintuna goma bata d’iba ba bacci ya d’auke ta.

   Around 4:15am wani irin muguwar shak’uwa ta farka da ita,cikin tsananin mayen bacci ta sakko daga saman bed d’in ta nufi mini fridge dake gefe can a room d’in,a hankali ta bud’e dan ko motsima a sad’ad’e take yinsa,ta fara neman ruwan da zata sha,kaf ta gama bincike fridge d’in bata samu ruwa ba,dan gaba d’aya ma babu komai a cikinsa,Mamma duka tasa a fitar da komai tun bayan tafiyar Badra U.S,a sab’ule ta maida ta rufe sannan ta koma bakin gado ta zauna tana tunanin yadda zata yi.Ita dai tasan idan tana wannan yanayin matsawar ba ruwan ta samu ta sha ba bazata iya komawa bacci ba,nd gashi bata san takan gidan ba bare tace ga inda zata yi saurin samun ruwa,a hankali ta mik’e ta shiga zagaye d’akin saboda yadda ta takura da shak’uwar data addabeta,,bayan kamar mintuna biyar data shafe tana zagaye d’akin,ta sake neman guri ta zauna,ci gaba shak’uwar tayi da taso mata maimakon ace ya ragu sai dad’a k’aruwa yake,,rashin samun mafita yasa tayi saurin nufar inda Badra take kwance,har ta mik’a hannu zata tada ita ta tambayeta ruwa,haka nan sai taji zuciyarta tana fad’a mata kada tayi haka,komawa baya ta sake yi tana toshe bakinta saboda sound d’in sosai yake fita musamman daya had’u da talatainin dare tsaf zai iya tashin wasu cikinsu,damuwa sosai tayi saboda bata tab’a irin wannan shak’uwar ba tunda take,k’ark’ari idan ta jimawar duniya ta kai minti biyu zuwa uku ta daina,amma yau har tana neman wuce mintuna goma tana abu d’aya,shawarar fita kawai ta yanke tunda ta rasa dukkan wani mafita,cikin sand’a ta tashi daga inda take ta nufi hanyar fita daga d’akin,taimakon da Allah ma yayi mata a lokacin har ta fita ta rufe musu k’ofar babu wanda ya motsa cikinsu,a hankali taci gaba da tafiya tana haskawa da wayarta data fito da ita tabi hanyar staircase ta sauka k’asa,,bayan ta sakko d’in ta sai tasa yatsanta guda ta rufe saman fitilar saboda ta rage k’arfin hasken,bcos bata so hasken ya ja hankalin kowa a gidan,laluben hanya taci gaba dayi a hankali tana tafe tana waige² har ta iso k’ofar kitchen,shigewa tayi saurin yi ko k’ofar bata tsaya bi takan ta rufe ba,,gawurtacciyar ajiyar zuciya ta saki mai tafe da shak’uwa lokacin data tabbatar ta shigo tsakiya,da sauri kuma sai ta janye hannunta akan fitilar ta nufi k’aton fridge dake cikin kitchen d’in,sai data fara d’auko robar guda na ruwa ta ajiye saman cabinet sannan ta bud’e drawer ta d’auko glass cup,cikin sauri ta sake d’aga robber ruwan ta b’alle murfin ta soma tsiyayawa a cikin cup d’in,kamar wani yace ta fara mik’o masa haka ta d’aga cup d’in ta kaishi bakinta,cike da son jin ruwan ya isa makogoronta ta fara d’ad’akawa cikinta,sai data shanye ta kuma k’arawa sannan ta ajiye cup d’in tana sakin sanyayyar ajiyar zuciya had’e da yiwa Allah godiya a lokaci guda,stool d’in dake gurin ta ja ta haye samansa da nufin ta huta,sannan ta janyo wayarta ta fara latsawa coz tasan ko ta koma yanzun babu tabbacin ta iya komawa bacci,,tana zaune cikin nishad’i tana kallon pictures d’insu da kusan kullum suka fita sai sunyi ta jiyo alamar kamar ana tahowa inda take,dakatawa tayi saurin yi da abunda take ta kashe hasken wayar yayin da ta maida gaba d’ayan hankalinta da idanunta a kan hanyar shigowar tana jira taga waye yake tafe.

       Ko kad’an shi kansa Hammad tun daya baro bedroom d’insa ya iske cikin parlor’n bak’i k’irin babu alamun haske,baiyi gangancin kunna wutar ba yaci gaba da tafiyarsa tunda dai yasan kan gidan su,dalilin k’in kunnawar kuma shi ne baya son asan yazo a lokacin,kawai yafi so sai da safe kowa ya ganshi tunda dama yasan yanzun kam duka ahalin gidan suna bacci amma kuma yana ganin lokacin tashin su ya kusa,,haka nan zuciyarsa da tunaninsa duka basu bashi tsammanin samun wani a cikin gidan da yake idanunsa biyu ba,da k’arfinsa yaci gaba da takawa har ya gama sakkowa daga upstairs without ya kunna even torchlight da zai kalli hanya ya tunkari hanyar kitchen kansa tsaye,lokacin daya iso a bud’e ya iske k’ofar,dan haka shima sai ya shige cikin kitchen d’in,ba tare daya damu daya rufe k’ofar ba saboda dama a haka ya isketa kuma shima hakan yayi niyyar barinta,kai tsaye yaci gaba da nufar inda switch na lamps d’in kitchen suke,,k’aran da switch d’in suka bayar a tare sakamakon had’a yatsunsa da yayi guri guda ya danna a lokaci guda yasa ta d’an firgita tana dad’a fito da mayan idanunta nd ga kuma mamakin abunda ta gani,wanda shi a nasa gefen har lokacin bai ga alamun komai ba a gurin ba bare yaga mutum sukutum a kusa da shi,,juyowa yayi cike da gaggawa a niyyarsa ta samarwa kansa ko da coffee ne yayi sauri ya sha kafin a kira sallah idanunsa suka sauka kan fuskar da ko mashashshara yake aka tambayeshi bazai tab’a iya mantawa da ita ba,a mamakance duka suke kallon juna while idanunsu d’auke da wasu irin frightens suke kallon juna,sun d’auki tsayin mintuna suna kallon-kallo a tsakaninsu ba tare da an samu d’aya cikinsu ya iya furta komai ba sai nuna juna kawai da suke still sunk’i cewa komai,,da kasala a jikinta ta fara juya idanunta kafin tayi saurin lumshesu tana tsuke d’an k’aramin bakinta,hawayen da bata san lokacin da suka taho ba suka fara mata ambaliya a saman chicks,cikin muryar kuka² ta fara magana

   “I knew it’s not u.. Always am just looking at ur shade,,wannan mafarki ne kawai dana saba yinsa tun ba yanzun ba buh i knew it wasn’t happens genuineness,,na tabbata bazan tab’a ganinka ido da ido ba..!”

   A hankali kuma kuka ya kwace mata hawaye suka ci gaba da zuba daga idanunta,kifa kanta tayi saurin yi a saman cabinet yayin da take jin zuciyarta tana mata wani irin k’aik’ayin da tun da take bata tab’a jin kwatankwacin saba,ci gaba tayi da rera kukanta ba tare data bari sound ya fita ba gudunma kada ta tada kowa a gidan a sakamakon abunda take kallonsa a matsayin shirmen mafarki ko ta kira shi da tunani,,maganar da tayi dai² lokacin shiya bashi tabbacin lallai² itace a gabansa ba mafarki ko tunanin daya saba yiba,sai dai abunda yazo ya tsaya masa a rai kuma yake son sani shi ne

   “Ya akayi ya ganta a cikin gidansu..?? Mene ne kum yake zaune da ita a nan d’in..?”

    Yadda take gunjin kuka shi ya taimaka wajen dawo da shi duniyarsa nd ya kuma tabbatarwa da gasken ita yake gani ba shade ba,within a few seconds zuciyarsa ta bayyanar da shi a gabanta yana mai jera sakin sanyayyun ajiyar zuciya da bai san ta ina suke taso masa ba

  “My Lady..!”

       Ya fad’a yana sake twitching breath da kyar nd har lokacin mamakin ganinta a gabansa bai sake shi ba,saurin d’agowa tayi jin muryarsa a daf da ita,a hankali sai ta fara kalloshi tun daga kan k’afafunsa dake sanye cikin wani benassi slide sandals na maza mai kalar bak’i da fari har ta dire akan fuskarsa,still bata yarda da abunda idanunta suka gani ba ta sake binsa da kallon ta sake direwa a k’afarsa da take ta lek’awa,duka zaton ta da tunaninta a lokacin bai wuce ta hango kofato ba,coz tafi tsammanta ganinsa da gamo

“My Lady..! Mene ne kike yi a nan..?”

Ya sake yin maganar cike da shakkun irin kallon da take masa,y’ar dariya tayi wacce ta bayyana asalin sirrin kyaunta,sannan tasa hannu tana whipping hawayenta,mamakinta yake still yana tsaka da sake kallonta kawai sai ganinta yayi tsam ta mik’e zata fice,saurin tare ta yayi yana sauke mata narkakkun idanunsa

“Where do u think to go..? Ki sake tafiya ki barni ina bulayin neman ki..??”

  Saurin d’agowa tayi da kanta dake k’asa,duk da zuwa yanzun da take ganinsa a gabanta har numfashinsu yana had’uwa bata gama yarda shi d’in bane da gaske yake mata magana,,saurin tafiya tayi ta fad’a jikinsa tana sakin wani marayan kuka still mara sautin kamar na farko,cikin bin umarnin zuciyarta zuwa gangar jikinta da suke mata khud’ubar ko da ace gamo ne tayi ta rungume shi ko zata samu sassaucin yanayin da take ciki,,shi kansa wani irin mayen k’arfe ke fizgarsa tunda ya bayyana a gabanta cikin azama tana fad’owa jikinsa yayi saurin d’ora hannayensa a bayanta yayi holding d’inta tight ta yadda babu wani abu daya isa ya shiga tsaninsu,ba muryansa kad’ai data shak’e ba hatta da zuciyarsa gaba d’aya a lokacin jin komai yake daban a duniyar,komai ya gama rikid’ewa,cikin muryan kuka² ya bud’e baki da kyar yace…..Ina ne kika tafi My lady,,kinsa nayi nemanki har na kasa gano inda kika b’oye..? Me yasa zaki min irin wannan hukuncin..?? Shi kenan sai ki tafiyarki ki barni ina bulayi..??”

     Bata iya d’agowa ba bare yasa ran samun amsarta taci gaba rera kukanta a ciki,wanda idan ba shi da yake manne da ita ba babu yaddaa za’ayi mutum ya san tana yi,shi kansa hawayen da suka taru a gefen idanunsa na tsabar farin ciki a hankali suka biyo gefe suna d’iga saboda ya tabbatarwa ransa idan bai zubar da su ba,ba zai dai ci gaba da jin rad’ad’in dake damun zuciyarsa tsayin lokaci ba

       “Please gimbiyata..! Say something ko zan samu sassaucin abunda nake ji a zuciyata..! Shirunki yana sake sawa zuciyata shakku,da tunanin anya da gaske nake ganinki..?? Kin sa na kasa tabbatarwa kaina da gaske ne nake jinki a jikina,ko kuwa dai mafarkin dana saba yi ne har yanzun na kasa zuwa k’arshen sa..!?”

    Yadda yake maganar yana k’ok’arin d’agota yasa tayi saurin sake maida kanta ta kwantar,bcos har lokacin itama bata gama tabbatarwa shi ne da gaske ba tsaye a gabanta har ta jingina da shi,rabuwa yayi da ita ta sakewa lafewa a jikinsa sai dai zuwa lokacin ta d’an sassauta kukan da take yi,muryarta a sanyaye irin na mutumin da yayi kuka ya gaji bayan tayi gyaran murta tace

     “Kai zan tambaya ina ne ka tafi ka barni,,kasa na shafe tsayin lokaci inata jiran dawowarka.. Me yasa sai yanzun zaka dawo gare ni..?? Kasan tsayin lokacin dana d’auka ina jiran dawowar ka amma kak’i dawowa sai yanzun.??”

      Ajiyar zuciya yayi mai nauyi a hankali yana ci gaba da caressing bayanta kamar mai rarrashinta,d’agowa ta d’anyi ta kalleshi,za tayi magana yayi saurin tarar numfashinta ta hanyar sanya yatsansa a saman lips d’inta yana cewa

      “Shhhh! Ba yanzun ya kamata kiyi min duk wad’annan tambayoyin ba… Let us get some calmness Princess,sai ki tambaye ni duk abunda kike son sani,,kin ji.!?”

    Girgiza masa kai tayi cike da sakarci,a hankali kuma sai ta sake d’agowa tana satar kallon fuskarsa duk da ba duka take gani ba sakamakon d’ora fuskarsa da yayi a saman kanta

      “Yane My Lady.?? Ko nayi miki rowan ganin fuskar nawa ne.!?”

      Kanta tayi saurin sunkuyarwa tana b’oye fuskarta a jikinsa,k’asa² ta saki murmushin da ita kanta bata san lokacin daya taho mata ba,shima d’in murmushin yayi na samun sukuni,a hankali ya sake matseta a jikinsa,zafin matsar da yayi mata yasa ta d’an saki marayan ihu,da sauri ya sassauta rik’on da yayi mata yana dariya a ciki²

      “Yanzun kin tabbatar nine a kusa dake ba shade ba princess.??”

    B’ata rai tayi saurin yi cike da shagwab’a tace

      “To kuma dan kana so na tabbatar shi ne sai ka had’a da min mugunta..!?”+

   “Ohh! Sorry³.! Barin bari kada na jiwa y’ar amaryata ciwo ko..? Ko da yake ma ai idan naji miki ciwo ni zanyi jinyar ki ko.?”

   Saurin d’agowa tayi ta kalleshi,shima sai ya d’ago d’in yana sauke mata idanunsa masu cike da tuhumar abunda aka yi take nasa irin kallon

   “Uhhuumm.!” Tace a hankali ta fara ja da baya tana matsawa daga jikinsa,biyota ya fara yi while tana ci gaba da tafiya,a haka har sai da suka k’ure duka girman kitchen d’in,suna isa jikin cabinet ta dakata tana saurin kallonsa,kome ta tuna ta sake sauke kanta k’asa zuciyarta fal tsoro,tana tsaka da tunanin abunda ta aikata bayan ganinsa,without tayi tsammanin faruwar wani abu ta tsinto hannunsa a k’asan chin d’inta yana d’ago fuskarta,zuba mata idanunsa yayi,gaba d’aya yanayin da yake kallonta ya k’arasa saukar mata da kasala,still duk da idanunta na k’asa amma tana jin idanunsa akanta da suke k’ara yin tasiri akanta suna sawa tana dad’a daburce masa,gashi ta rasa abunda ya kamata tayi,,da gayya ya sake matsarta duk da ya fahimci a halin da take da abunda kallonta yake nufi,sai dai gaba d’aya yana ji a zuciyarsa bazai tab’a iya barinta tayi nisa da shi ba bcos yana ganin kamar wani abu zai sake ratsowa tsakaninsu har yayi nasarar rabasu ko kuma dai ya bud’e idanunsa ya tarar bacci yake yi

    “My lady..! Me yasa ba zaki kalle ni ba ne..?? Baki san ina missin..”

    Sai kuma yayi shiru ya kasa k’arasawa

      “To ai bazan iya bane,,shi yasa..”

   

      “Baza ki iya mene ne ba.??”

   

      “Kallon naka..!”

   

      “Uhhuumm.! Da gaske..??”

      Ya tambaya yana matso da fuskarsa saitin nata

         “Ehh..!”

     Tace cikin dashewar murya saboda yadda yake kusantota jikinta har ya fara rawar da bata san dalili ba

      “Me yasa to bakya iya bari mu had’a ido ne..?? Ina son haka..”

   

      “Nifa na fad’a maka,,bana iyawa ne kawai..”

   

       “Uhmmm.! Shi ne ai nima na tambayi dalilin.. Za ki iya sanar dani..?”

     Idanunta ta matse gam,a hankali bakinta ya motsa tace

      “Nifa haka kawai ne bana iyawa..”

     Murmushi yayi da gefe yana kallon kyakykyawar fuskarta sannan ya sake cewa

       “Sai dai ki kalle ni a sace ko..!?”

   K’irjinta ne ya d’aga da sauri sakamakon maganar da yayi wacce tasa ta jin tsoron gano lagonta da yayi,can daga k’asan zuciyarta tace

     “Dama yasan ina satar kallonsa ne..?”

    Ta tambayi kanta without tayi tsammanin samun fitowar amsar daga gareta

       “Am asking.. My Lady.!”

     Ya k’arasa maganar da wani irin yanayin daya sake sawa taji kasala yaci gaba da bin jinin jikinta yana k’ona ta,shiru tayi ta kasa magana hakan sai ya bashi damar yi mata rumfa har numfashin su yana had’uwa,,yadda ya kusantota fiye da baya yasa ta d’an turo bakinta kad’an har lokacin idanunta a rufe tace

    “To ni dai ka d’an matsa sai na fad’a maka..”

    “I can’t.. Kawai ki fad’a min a hakan,,idan ba so kike nayi miki..!”

    Da sauri ya sake rik’e kalmominsa bai bari sun k’arasa fitowa ba,sake d’agawa k’irjinta yayi da sauri cike da tsoro,idanunsa ya sauke a hankali yana kallon yadda k’irjinta ke sama da k’asa a lokaci guda

      “Please.. Ni dai kayi hak’uri ka matsa to na wuce,bacci ma nake ji..”

      Wani irin kallon sama da k’asa yayi mata kafin yace

     “Bacci..!? Yanzun ne kike jin baccin..??”

  Kai tayi saurin d’aga masa alamar “Ehhh”

   A hankali ya girgiza kai yana sake fad’in

   “Ke yanzun baki ji kunyata ba kike fad’a min kina jin bacci..??”

   “Ni ba wani kunyar da naji..Naga dai gaskiya na fad’a ai..!”

     “Really..!?”

      “Ehh. Mana..!”

   “Uhhuumm..! Yanzun idan nace jeki ki kwanta,zaki iya tafiya da gaske..??”

     Kai tayi saurin girgiza masa alamun “Ehh” murmushi yayi mai nuni da lallai ke yarinya ce,yadda yaga ta tsuke fuska lokaci guda yasa shi tab’e baki kafin ya matsa side d’inta ya jingina bayansa da cabinet d’in yana cewa

      “Ok.. U can move,,tunda haka kika zab’a.. Allah bamu alkhairi..!”

     Bata kalleshi ba,sai murmushin da tayi while a k’asan ranta tana cewa

      “Zaka san ni kayiwa gatse..”

    Bata tare data jira ya sake ceaa komai baduk da dagayya tayi maganar sai ta ja k’afafunta cikin zolaya zata bar wajen,ko dan taji me zai fad’a nema tayi masa hakan oho mata,,ko taku guda bai bari ta k’arasa yi ba ya fizgota da sauri ta fad’o jikinsa,a firgice ta d’ago idanunta ta kalleshi dan yadda yayi mata bata yi tunani ba shi yasa ta tsoratar,babu damuwan komai a saman fuskarsa yake kallon tsakiyar idanunta yana d’age mata gira

    “Uhhuumm.! Ban san idan nace ki tafi zaki iya lafiya ki barni ba..! Wannan shi ne kalar naki damuwar da zaki nuna akaina..?? Duk kukan da kike yi da jiran da kika ce kinyi min iya abunda zaki iya yi kenan..?”

     Janye idanunta tayi tana murgud’a masa baki,cikin rashin sani ya riga ya ganta,murmushi yayi ya sake matseta har sai da ta sake sakin y’ar k’ara,still hakan yayi masa dad’i har ya sake murmusawa,k’irjinsa ta kaiwa duka while cikin muryarta mai sanyi tana fad’in

     “Ni Allah ka daina min mugunta.. Idan ba haka ba ina tafiya bazan bari ka sake gano inda nake ba..!”

      Rik’e baki yayi yana fad’in

   “Me yayi zafi haka my Lady da zaki furta zaki guje ni..?”

   “To ba kai neba kake ta min mugunta.. Kuma ai ban san mene ne nayi ba kake min haka.”

       “Ohh! Sorry toh na daina,,ai kin hak’ura ko..?”

    Baki ta sake murgud’a masa sannan tayi masa alamar “Ehh” da ido,murmushi yayi a hankali ya nufo fuskarta ko me yake shirin yi ita dai bata gama fahimtar saba,abunda kawai zata iya cewa taga yana kallon lips d’inta,daf da fuskarta ya tsaya bisa kuskure kamar ance ya kalli k’ofa,yana d’agowa suka had’a ido da Sultan daya kafe su da idanu ko kyaftawa ba yayi,,had’e rai Hammad yayi cike da jin haushi yana tamke fuska ba tare daya kalli inda Sultan d’in yake ba yace

    “Mene ne kai kuma ka sawa mutane ido haka..?? Idan wani abu ka zo d’auka kayi sauri ka tafi mana ka tsaya kallon mutane kamar baka sansu ba..”

    Murmusawa Sultan yayi a hankali ya shigo cikin kitchen d’in yana binsu duka da kallon mamaki

   “Kai d’in mene ne kake yi a nan da wannan talatainin daren..??”

     Bai kalle shi ba bare yasan dashi yake ya samu damar ba shi amsa,sai dai ya sassauta rik’on da yayi mata,saurin zamewa tayi itama ko da taga ya cikata da nufin guduwa,yayi saurin yin magana

      “Ina ne zaki je kike sauri..!?”

   Da ido ta masa alamar tafiya zata yi,girgiza mata kai yayi alamun ba yanzun ba,ta sake narke masa idanunta tana masa alamun ita dai zata tafi,nuna mata yayi bai aminceba idan kuma ta tafi shi da ita ne idan har ta bari suka had’u,kamar za tayi kuka ta hak’ura ta tsaya sai dai ta sunkuyar da kanta a k’asa tak’i yarda su sake had’a ido,hankalinsa ya mayar kan Sultan daya rasa gano mene ne takamaiman abunda yake nema yana cewa

   “Wai kai da Allah malam mene ne kazo nema ne..!?”

   “Abunda duk ya kawo ka nima shine ya kawo ni,kuma shi nake nema..”

   Murmushi Hammad yayi yana tambayarsa

      “Kasan me nake yi ne..??”

  “Sai dai ka fad’awa wad’anda basu gani ba.”

   Still murmushin ya sake yi yana fad’in

    “D’an sa ido.. Zo ka fice da Allah..”

  Juyowa Sultan yayi yana sakin dariya mara sauti

   “D’an sa ido ko..?? Wollahi ka janyowa kankama na fasa zuwa ko ina,sai dai duk abunda za’ayi ayi shi a kan idanuna..”

  Harararsa Hammad yayi irin na kayi tsararo kaga wannan hark’allar,ba tare da yayi magana ba ya rik’o hannunta

    “Wuce muje my Lady.. Ina tsammanin idan mun bashi guri zai rasa wad’anda zai sama idon ko..?”

  

   “Ur Lady fa.!? Dama itace amaryar kake wani nok’ewa,sai cewa kake baka so,,ashe duk munafirci ne abun..”

   A fusace ya waiwayo yana kallonsa,yanayin kallon da Hammad d’in yayi masa da sauri yasa shi dakatawa iya haka bai ci gaba da magana ba

  “Uhhuumm.!” Shi ne kawai abunda ya fito daga bakinta lokacin da suke kallon-kallo wa juna,,dan ko da Sultan yayi maganar duk da bai karasa ba,kuma ko da ba’a fad’a mata ba a iya tunani da kaifin kwakwalwarta da Allah yayi mata,a mafi yawan lokuta tana iya fahimtar maganganun da aka fara ba tare da an k’arasa ba,bcos law take yi nd dole ne dama sai ta lak’anci irin wad’annan yaren idan ba haka ba tsaf sai a iya hallakar da rayuwarta ta wannan fuskar kuma a gabata ba tare data fahimta ba bare tasan abunda ake shiryawa,tana fad’in haka kai tsaye ba tare data jira ta k’ara ko minti guda ba tayi waje da saurinta tana had’awa da gudu²,,Hararar Sultan yayi sauri yi sannan ya bi bayanta da sauri,yana niyyar fitowa a kitchen d’in nan idanunsa suka hango masa Daddy yana sakkowa daga upstairs da alamun kamar zai fita ne zuwa masallaci,saurin komawa yayi da baya cikin tsananin jin haushin irin tab’argazar da Sultan d’in yayi masa duk da har lokacin bai gama tabbatarwa kansa dalilin tafiyar nata ba,amma yafi danganta hakan da ta fahimci abunda maganganun Sultan d’in suke nufi,,matsowa kusa da shi Sultan yayi yana dariya

   “Dude..! Wai wace ce ita wannan d’in.??”

   A fusace ya waiwayo ya kalleshi yana fad’in

      “Tambaya kake..!? To ka jira idan na nemo sani akan wace ce ita sau na fad’a maka..”

   Yadda ya d’auki d’umi yasa Sultan saurin fad’in

   “Allah baka hak’uri,,amma me yayi zafi har kake tada jijiyoyin wuya haka..!?”

Kallonsa ya d’anyi na tsayin lokaci kafin a fusace ya fice daga kitchen d’in ya bashi guri,,kiran sallar da yaji an fara yi shi ya dakatar da shi daga niyyarsa ta son duba inda tabi,da sauri kai tsaye ko jiransu bai yiba ya nufi masjeed.

  Lokacin da aka idar da sallah a masallaci a gaggauce ya dawo gida,yau ko zaman daya sabama bai iya jira yayi ba ya kamo hanya ya dawo,,tun daya shigo gidan yake ta dubawa ko zai ganta amma ina abu ya gagara duk inda zuciyarsa ta sak’a masa kaf ya duba bai ganta ba,plan d’in daya shiryama akan sai dai kawai a ganshi,wajen nemanta duk mutanen gidan sun gama ganinsa,,a parlor ya yanke shawaran zama,dan yasan nan ne kad’ai zai zauna yaga fitarta ko shigowarta matsawar tana cikin gidan,tun wajen k’arfe 6am da yayi zaune har 7am saura y’an mintuna ba tare daya motsa ba.Around 7:10am Daddy ya shigo gidan yana tafe yana addu’o’i da motsa yatsunsa dake nuna alamun yana yine da gab’b’ansa ba da wani abu ba,har ya gota inda yake zaune ya waiwayo cikin muryar zolaya yana fad’in

   “Babanah..! Barka da hutawa..”

Waiwayowa Hammad yayi saurin yi while yana rage tsayinsa duk da a zaune yake yace

  “Morning Dad..!”

“Ka tashi lafiya..? Ya hanya..?”

  “Alhamdulillah..!”

Yace daga haka ya sunkuyar da kansa k’asa gudunma kada garin bincike Dad ya fahimci wani abu na daga damuwar da yake ciki,,murmushin jin dad’i Dad yayi har ya juya ya fara tafiya ya dakata yana cewa

  “Hammad..! Ka sameni bedroom akwai maganar da nake so zamu yi da kai..”

 

  “Toh” ya amsa sannan ya mik’e jikinsa a salub’e,sai daya bari Dad ya wuce zuwa bedroom d’in sannan ya biyo bayansa,yana tafe yana mitar Dad zai hanashi gano inda ta shige a ransa.

  Tunda ta samu ta fice da gudu² bayan ta haura staircases d’in,tana fad’awa d’akinsu ko iya rufe k’ofar d’akin a hankaki bata yi ba saboda yadda kwakwalwarta ke tafarfasa,direct ta wuce toilet da kayan jikin nata da komai ba tare data tsaya cirewa ba ta shiga kwance kan shower ruwa ya fara sauka a jikinta

  “Me yasa za kayi min haka..!?”

  Shi ne kalmar daya fara zuwa bakinta cikin tsananin damuwa,dan har lokacin bata bar tuna maganar da Sultan ya fara fad’a ba,kenan hakan yana nufin ba bikin wani suka zo ba a gidan daya wuce nasa..? Wannan shi ne sakayyar da zai nuna mata..?? Hakan shine soyayyar da yake ik’irarin yana yi mata..? Bayan ta sgafe d’umbin shekaru tana jiransa,yanzun ace wannan shi ne tukuicinta..?? Lallai kuwa idan haka ne ta dad’e tana jahiltar kanta,tunda har tasa a ranta zai dawo gare ta,,ashe duk soyayyar ta bogi ce..?? Yake mata,bayan yasa ta rabu da duk masu zuwa gurinta ta hanyar shaida musu anyi mata miji a gida,,shi ne zai saka mata da wannan sakayyar..??

Hannayenta ta d’ago tana kallo zuwa jikinta daya gama rungumarta yanzun babu jimawa,duk wannan abun daya faru da ita dama ba itan yake so ba,romon baka kawai yake mata..??

Wani irin haske ta gani ya gilma a idanunta take ta fara k’ok’arin fad’uwa,taimakon da Allah yayi mata a lokacin tana daf da katangar toilet d’in,sai tayi saurin dafawa da duka hannayenta ta tsaya sosai,hawaye masu zafi suka fara tahowa da sauri²,,ta d’auki tsayin mintuna sama da sha biyar tana kuka a cikin toilet d’in ba tare data sassauta ba kafin tayi k’arfin halin yin addu’ah,bayan ta share hawayenta ta d’aura alwala sannan fito a lokacin idanunta har sun haura,,tana fitowa kai tsaye inda jakar kayanta take ta nufa bayan ta sauya kayan jikinta da doguwar riga sannan ta daidaita akan abun sallah,,tun tana sallah kafin ta idar dukansu d’aya bayan d’aya suka fara tashi suna k’ok’arin yin alwala.

Lokacin data idar kan kayanta ta koma,sai data tabbatar ta kimtsa komai nata sannan ta gyara jikinta,duka a lokacin ko bakwai bata k’arasa yi ba ta kallesu bayan taja luggage d’inta ta tsayar tana fad’in

  “Toh..! Guys nifa ina tunanin zan wuce ne zuwa gida gaskiya cos idan naci gaba da zama zan iya samun matsala,,,jikina yau duka babu k’wari sosai,ina ji a jikina kamar akwai wani abu da yake daf da faruwa dani.. So gara na hanzarta isa gaban Innata koda mutuwa zanyi na tafi a gabanta,,buh idan Allah yasa wannan shi ne had’uwar mu na k’arshe ina fatan duka zaku yafe min.. Ni dai na yafe muku gaba d’aya..”

   A sakarce duka suka bita da kallon mamaki,yadda take magana kamar mutumin dake bada wasiyya duka jikkunansu sai suja d’auki sanyi

  “Princess..! Ki sanar damu dan Allah,, wani abu ya faru kike irin wannan maganar.!? Wollahi kinsa duka jikin mu yayi sanyi.. Please.!”

  Kai ta kad’a musu a hankali tana sakin murmushin da kana kallo kasan bai kai zuci ba

  “Ko kad’an babu abunda akayi,,haka nan naji jikina yana bani.. So please mu yafi juna,,ban sani ba ko zan kai jimawa ko bazan kai ba..!”

Saurin b’oye hawayenta tayi sai kawai ta juya da sauri zata fita,Badra da nata hawayen har sun fara sauka tace

“Princess please.! Dan Allah na rok’e ki kada ki tafi.. Wollahi bana son tafiyarki,,ki jira mu shirya sai mu tafi duka please.. Yanzun ko kince zaki tafi ma Mamma bazata bari ba,bcos zaki tadawa jama’ar gidanku hankali ne.. Ki bari mu shirya please sai mu tafi taren kinga dama haka muka tsara..”

  Girgiza mata kai tayi a b’oye ta goge idanunta

  “I can’t wait anymore.. Tafiya ta shi ne masalaha,, Ku baza ku fahimci halin da nake ci ba,,kawai kuyi min fatan alkhairi,,na yi muku ALK’AWARI idan har na isa gida zan kira ku na fad’a muku duk yadda ake ciki da yardar Allah..”

  Tuburewa suma suka yi akan lallai bazata tafi ba,yayin da itama ta kafe kai da fata akan sai ta bar gidan a kuna lokacin,duk iya yadda suka so su murd’a ta abu yaci tura sun kasa tsayar da ita,ganin lamarin na neman zama rikici yasa Badra kiran Mamma a waya ta shaida mata abunda ke faruwa,a gaggauce Mamma ta baro kitchen wajen masu yi musu hidima ta nufo d’akin Badran wanda tun da safiyar Allah har k’aramin tsunami ya fara tasowa,,tana shigowa duka suka yi gurinta suna fad’in

  “Mamma dan Allah kisa baki ki hanata tafiya..please..!”

  Kallonsu tayi duka tana tambayar

  “Me kuka yi mata ne da yasa tace zata tafi da wannan safiyar da babu tabbacin wani gidanma sun tashi..?”

Gaba d’aya suka kaure da fad’in

  “Wollahi Mamma babu laifinmu a ciki,,muma haka nan muka ji tace zata tafi..”

  “A’a wollahi k’arya kuke,ku fad’a min wannan maganar na yarda.. Saboda Allah ina so ku duba girmansa ku sanar dani abunda ya faru,idan kuka b’oye min kun san baza ku b’oyewa ubangiji ba ko..??”

Rantse² suka mata akan basu sani ba,ganin haka yasa Mamma’n ta juya ga Sabina dake tsaye sunkuye da kai a k’asa tana fad’in

  *”Y’ata.!* Ina so ki fad’amin gaskiyar abunda suka yi miki kike son tafiya,,kin ji..!?”

*”Mammah.!* Wollahi ni dai babu wanda yayi min komai,,haka nan ne naji ina son tafiya yanzun..”

  Yadda ta kira sunanta da wani irin lafazi sai da yasa ta jin wani irin abu tun daga cikin kanta yabi ya sake tsirgawa ta cikin zuciyarta

  “Kin tabbatar basu yi miki komai ba,,amma kike k’ok’arin tafiya..??”

  Amsawa tayi da “Ehh babu” jinjina kai kawai Mamma tayi kafin ta juya zata bar wajen da fad’in

  “Am sorry to say dear,,tunda babu komai ina so ki zauna dasu tunda sun nuna basu yarda ki tafin ba.. Ina tunanin hakan shine masalaha ko..?”

  Saurin d’agowa tayi tana kallon bayan Mamma data kama hanyar fita ba tare data jira jin me zata ceba itan,,sannan ta dawo da kallonta kan su Jannat da suke ta ihun murna,ko kafin Mamma tayi wani k’wak’waran motsi a inda take tuni ta fashe da kuka mai tsanani,cikin kukan take cewa

  “Wollahi ni bazan zauna ba,,sai na tafi gurin Innata da Babana..!”

  Juyowa Mamma tayi saurin yi ta dawo inda take durk’ushe tana fad’in

  “Subhanallah..! Ni Asiya me zan gani haka..?? Daga hanaki tafiya sai abu ya zama matsala..?? Allah ya baki hak’uri ya kuma huci zuciyarki.. Maza ke Badra kuyi maza ku shirya sai driver ya kaiku,,kunji ko..?”

Da girmamawa duka suka amsa jikinsu duk ya sake yin sanyi da lamarin k’awar tasu,ba tare da sun tsaya tunanin yin wanka bama saboda damuwar da take ciki duka suka nemi kayansu suka shirya,,suna gamawa a lokacin Mamma har ta jima da fita suma suka d’unguma suka fito,,sai data yi musu nasiha sosai lokacin da suka je yi mata sallama dukansu sannan tayiwa Sabina alkhairi da kyaututtuka masu girma,bayan sun sake yin sallama ta rako su har bakin mota,ba ita ta juya ba sai da taga fitarsa a gidan sannan ta koma ciki zuciyarta cike da jimanta al’amarin yarinyar a ranta.

Tun da suka shiga bedroom d’in Dad sai daya shafe tsayin awanni biyu suna maganganu wanda duka suka ta’allak’a akan batun aurensa,kafin ya fito daga d’akin,, Allah yaso ma Dad bai cika tambayarsa ba akan maganar dan yasan da yanzun yaji haushinsa,bcos hankalinsa duka a lokacin da Dad d’in yake maganar ko kad’an baya tare da shi,,shi yasa har Dad yayi ya gama baya tunanin akwai k’wararan kalmomi biyu daya rik’e a zancen.

   Yana fitowa da k’aton wall clock ya fara katari wanda yake nuna masa 9:05am a lokacin,a gaggauce ya wuce zuwa bedroom d’insa ya sake kimtsawa,har lokacin duk da ya d’auki mintuna amma still Sultan da Sadeeq ko juyi basu yi ba tun da suka sake kwanciya bayan dawowarsu daga sallar asubah,wucewa yayi ya sake fita daga room d’in ba tare daya tashe su ba,,bedroom d’in Mamma ya nufa kai tsaye zuciyarsa cike taf da son yi mata albishir d’in yaga Tsuntsuwarsa…..*Daga dukkan alamu dai na samu mataya,,sai dai ina son yin jan hakali ne ga masu min maganar kada na tsawaita labari,amma am sorry to say,,labari ni nake rubutawa nd nina tsara shi tun kafin yanzun,saboda haka na san mene ne zanyi a gaba,,ko da maganar da zan fad’a baza tayi muku dad’i ba,shi yasa tun a farko nace kuyi hak’uri da abunda zaku ji,,i knew sak’on da nake son isarwa idan har ban kai k’arshe ba za’a samu matsala,sai dai tun yanzun wasun ku suna cewa ai na isar da sak’on da nake son isarwa,ta yaya ne za’a ce sak’on da bai kammala ba ya isa..?? Idan an kawo matsala ba’a warwareta ba,me kenan aka yi.? Dole sai na ce na gama ko na ajiye alk’alami na,sannan ne zaku kira cewa sak’ona ya kammala,ku da kanku zuwa yanzun ya kamatama ace kun shaida,tunda har kuka ga nazo nan ku fara tabbatarwa kawunanku labari ya taho gangara,ba sai kuna min maganar na tak’aita ba,labarina bashi da alak’a da True Life bare kuce na ajiye shi haka nan,idan batun hutu ne kuke nema min,nima zanso ne ace yau na kammala na samu hutun,bcos nasan typing ba abune mai sauk’i ba nd research too,kullum mutum cikin tunani da bincike akan abunda zai rubuta yake,kunga kuwa dole bawa yaso ya huta,,saboda haka don Allah masu maganar ku tak’aita please n please,a tsarina bana son karatun summary shi yasa nima ban fara yinsa ba,duka idan kunyi hak’uri bana tunanin zamu kai ko da 80 pages,,saboda haka wad’anda suke bina suka ga kuma zasu iya ci gaba da tafiya tare da ni basu gaji ba,ku taho mu ci gaba da shatar burtali,wad’anda kuma suka ce zasu daina karantawa ko ma nace sun daina har suka fad’a naji kuma na gani ina godiya sosai 🙏,Allah saka da khairan sai mun had’u a gaba,buh nasan ko iya hakan kuka tsaya kamar yadda kuka ce babu komai dan kuwa kun amfana da wasu daga cikin darussan da nake son ku fahimta d’in,,so Alhamdulillah.! Sai dai kuma nace ba haka aka so ba,wai k’anin miji yafi mijin kyau,,a k’arshe ina k’ara yi muku fatan alkhairi gaba d’aya masoyana,ban cire kowa a cikin ku ba..Real Smasher tana gaida ku all..🙏*+

💞

      Lokacin daya shiga bedroom d’in Mamma da kiranta ya fara while yana dubawa ya gano ta inda zai ganota,sai dai har ya k’araci lek’ensa bai tarar da ita a ciki ba,fitowa yayi da sauri yayi hanyar downstairs kasancewar safiya yasan da wahala ace bata kitchen,sanda ya sakko ta cikin parlor ya ratso nan ma bai tarar da ita ba,kai tsaye ya wuce ya nufi kitchen cike da k’warin guiwar zai sameta a can,sai daya fara lek’awa duk dan saboda ya tabbatar tana nan d’in ko a’a saboda ya gama d’ora tsammaninsa akan tana nan d’in,amma sai ya iske sai hadiman gidan kawai a ciki,,juyawa yayi ransa a d’an b’ace ba tare da yayi magana ba,har ya kama hanya zai bar wajen kuma ya saks dawowa yana tambayarsu inda Mamma’n ta shiga,kiran da aka mata a waya da futarta da tace tana dawowa suka shaida masa,ko gama saurarensu bai yi ba ya juya da sauri ya bar gurin dan shi a yau d’in nan tunda Allah ya nuna masa ita bazai yi sanya ba sai sunyi maganarta da Mamma’n,kuma idan ta kama ma da labarin ya isa ga Dad duka shi dai zaiyi dan a san yadda za’a yi da shi kafin ayi masa sakiyar da babu ruwa.

   Cikin parlor ya dawo ya zauna yana jiran ganin ta inda zata fito tunda duk inda yake tunanin samunta ya duba bata nan,a k’asan zuciyarsa yana k’issimawa duk tsayin lokacin da zata b’ata bazai gaji ba zai jira fitowarta,ba don komai ba sai don saboda Tsuntsuwarsa,ya tabbatar idan yayi sakaci a wannan karon ta sake tashi tofa baisan kuma a inda zai riskota ba.

    Ak’alla ya d’auki tsayin lokaci zaune shiru shi kad’ai kafin yaga fitowar Mamma kuma daga saman dai itama ta sakko,fuskarsa d’auke da mamakin ganinta ta wannan hanyar yaci gaba da kallon tahowarta har ta k’arasa sakkowa,,hanyar kitchen yaga tayi,cikin sauri ya kauda tunanin da yake a zuciyarsa ta hanyar maye gurbin sa da fad’in

      “Morning Mah.!”

     Dakatawa tayi da tafiya cos gaba d’aya ma ita bata san yana zaunen ba saboda tunanin abunda ya faru d’azun tsakaninsu Badra da Sabina daya d’auke mata hankali

      “Morning habibiiy.. Ka tashi lafiya ko..? Ya hanya.?”

      Murmushin yak’e yayi da fad’in

       “Alhamdulillah Mah..!”

    Murmushin itama ta mayar masa da fad’in

         “Ina zuwa ko..?”

   

       “Toh Mah.. A fito lafiya.”

     Juyawa tayi har ta fara tafiya yaji ya kasa nutsuwa da sauri ya d’ago ya sake yin shiru yana tunanin me zaiyi wanda zai bashi mafitar da yake nema.? Ya sake kallon hanyar data bi a lokacin har ta kai bakin k’ofar shiga kitchen,da sauri bakinsa yana b’ari yace

      “Mah..! Idan kin gama zanzo muyi magana..”

     Dakatawa tayi a bakin k’ofar tace

        “Shi kenan habibiiy..”

     Tana fad’ar haka ta shige ta barshi zaune a parlor.

   

*After some hours..*

      Tunda Mamma ta barshi zaune,yake kallon agogo,da yaji bazai iya zaman ba ya mik’e yayi sama,duk bayan mintuna sai ya fito ya duba ko ta fito,amma sai ya riski still tana cikin kitchen d’in,haka yayi ta safa da marwa tsakanin bedroom d’insa zuwa parlor,zuwa nata bedroom d’in amma sai ya tarar bata fito ba still,tun yana kallon agogo yana duba lokacin daya d’auka yana jira har abun ya kusan fara neman ya janyo masa damuwa,,ji yayi sam bazai iya ci gaba da jiranta ba,dan haka ko daya sauko a karo na k’arshe ya nufi kitchen d’in wajenta,aiki sosai ya tarar dasu suna yi,bayan ya d’an dakata a wajen a hankali ya furta

      “Shi wannan aikin baya k’arewa kenan.. Ko kuma dai dan ina son magana da ita ne yasa nake ganin tsayin lokacin..?”

     Katse zancen yayi da fad’in

      “Mah.! Mintuna kad’an please..!”

     Yana maganar yana rausayar da kai gefe

      “Ok.. Muje gani nan fitowa..”

     Kasa matsawa yayi a gurin har sai data ajiye abunda take yi,yana tsaye har ta wanke hannunta bayan ta tsane da mini towel sannan ta fito tana tafiya tana bada sallahu wa masu yi musu hidiman

      “Ina dawowa yanzun.. Amma kuci gaba kafin na dawo d’in,, ai kunga yadda na gwada muku ko..?”

    Suka amsa mata da “Ehh”

“To kuci gaban nima ina nan dawowa in sha Allah..”

      Sai da yaga fitowarta sannan ya iya juyawa a tare suka jero da ita,ganin da Mamma tayi ya kama hanyar staircase yasa ta kalleshi tana fad’in

      “Hammad..! Maganar bazai yiwu a nan bane da sai mun koma sama..?”

     Kai ya girgiza mata alamun A’a,amma kuma sai cewa yayi

     “Mah.! Zai fi mana zama secret ne,,bcos ban shiryawa kowa yasan mene ne zamu yi maganar akansa ba yanzun..!”

      Jinjina kai tayi itama sannan taci gaba da binsa suka wuce saman,bedroom d’inta suka shiga,bayan ya zaunar da ita saman resting chair ya d’an tsaya kad’an da hannayensa nad’e a k’irjinsa yace

      “Mah.. Ina son tambaya ne,akan su waye suka zo gidan nan..?”

    Fuskarta k’unshe da fara’a tace

      “Ga ku nan.! Mu ina muka ga wasu da zasu zo yanzun..?? Tunda ba’a fara biki ba,,ku kad’ai ne daga kai sai k’annenka kuka zo gidan nan..”

     D’an rufe idanunsa yayi yana girgiza mata kai

      “Noo Mah.! Ba wannan nake tambaya ba,bayan mu babu wasu da suka bak’unci gidan nan..?”

      D’an jim tayi bata yi magana ba,alamun kamar tana son tuna fuskokin da suka shigo musu daga jiyan zuwa yanzun da yake magana

       “Ki tuna Mah..!”

   

      “Babu fa,,ku kad’ai ne kuka shigo..”

   

      “A’a Mah..! Definitely akwai bakin fuskar da suka zo mana,,buh ya kamata ki tuna..”

   

     “Ohh! Na fad’a maka fa babu,,sai dai kuma ban sani ba ko friends d’in k’annenka kake nufi,,nasan dai bayan ku da kuka yi zuwan k’arshe cikin gidan nan sai su,,after wannan ban san kuma wanne ne kake magana ba..”

    Murmushi yayi kafin yace

        “Do u know them Mah..??”

     Kallon mamaki tayi masa tana cewa

     “Ban gane azancin na sansu ba..? Su suwa kenan na sani..?”

      Wani murmushin ya sake yi sannan yace

     “Yeah! Ina son tambayar wani abune fa..”

   

     “Ehh! Muna yawan gaisawa dasu tun suna U.S..”

   

      “Wacce ce kika fi sani a ciki..??”

     Kallon tuhuma Mamma ta fara masa bcos bata fahimci mene ne alak’ar tambayar da yake mata da kuma su kansu y’an matan da yake mata tambayoyin akansu ba

     “Duka mana..?? Kana da matsala da sanin da nayi musu ne..?”

   

     “Mah.! Can u help nd tell me..!”

   

      “Nd tell u what.!?”

    Ta fad’a da sauri tana binsa da kallon da yasa shi jin wani iri

      “Mah..! Sunan su kawai nake son ki fad’a min.. Please.”

   

      “I can’t..!”

      Shine abunda bakin Mamma ya furta,wani irin fad’uwa gabansa yayi daya tuna idan fa Mamma tak’i bashi had’in kai shi kenan bazai samu nasarar da yake nema ba tsayin shekaru

      “Please Mah.. Help me.!”

      Had’e rai tayi tana kallonsa

      “Bazan iya ba nace,,idan banda kai da abunka mene fa’idar shigo min da wannan maganar a dai² lokacin da hidindimu suka hau kanmu..?? Mene ne jin sunan su ko inda suka fito zai yi maka.? Ahh.!?”

    

     “Ni dai Mah please,,kawai ki taimaka ki sanar da ni,,daga haka nayi miki ALK’AWARI sanar dake ko mene ne ya faru,,please..!”

     Kanta ta kawar gefe nd fuskarta babu yabo bare fallasa tace

      “Shi kenan,,d’aya HAFSAT ne sunanta,d’ayar kuma ZAINAB,shi kenan kaji yanzun..?? Na gama ko..!? To matsa min na wuce ni,kada kasa ni b’ata lokaci a nan ga aiki can yana jiran mu..”

   

     “Wait Mah..!”

   

      “Zaman mene ne zanyi maka ne a nan d’in Hammad..??”

   

     “Mah..! Magana nefa za muyi,,kuma yana da matuk’ar muhimmanci ne a guri na,nd u too.!”

     Saurin kallonsa tayi sai dai bata yi magana ba

     “Nasan Mah baza ki manta labarin dana baki ba a baya can ba,,wanda cikin kwanakin da suka gabata ma munyi su a lokacin da nake U.S..”

   

     “Uhhuumm..! Sai aka yi mene ne yanzun kuma..??”

  Idanunsa ya matse da yatsu biyu kafin yace

   “Mah..! Duka komai daya faru akanta nefa,,itace yarinyar da kika sa a nemo lokacin da kika hana ni zuwa..! Shi ne bayanin da nake son yi miki..”

   Saurin mik’ewa Mamma tayi ta rik’o hannunsa,fuskarta cike taf da mamakin maganar

       “Ita wa kenan..!? Yaya akayi kuma ya zama ita..?”

 

   “Ohh! Mah..! HAFSAT d’in nake nufi.”

  Rik’e baki Mamma tayi fuskarta cike da mamakin faruwar al’amarin tace

     “Are u sure..!?”

    “Am very much sure Mah.. Ita ce wollahi.!”

    Sai kuma yayi shiru yana neman gurin zama dan yadda yaji lokaci guda kamar wanda aka hankad’a yana neman fad’uwa,saurin rik’o shi Mamma tayi tana fad’in

      “Bi a hankali Son..”

   Murmusawa yayi irin na babu komai fa yana sake girgiza mata kai

   “Nifa duk kasa na kasa fahimtar batun nan baby.. Ya kamata ka bani shi a bud’e,ta yadda zan fahimci komai..!”

     Kamo hannunta yayi shima ya zaunar da ita a kusa da shi sannan,a hankali ya d’ora kansa a join shoulders d’inta ya fara mata summary d’in labarin,,,fuskar Mamma lokacin daya gama mata bayani tsantsar mamakin dake shimfid’e samanta har ya wuce wanda za’a misalta,haka nan tunda tayi shiru ta tafi tunanin da neman mafita,yadda tayi shima haka yayi sai dai tunaninsu ya bambanta,duk da shima d’in tunanin hanyar da zai bi ya b’ullowa lamarin ta b’angaren Dad ya hana zuciyarsa ta samu sukuni,,kallonta ya d’an sake yi bayan ya sauke ajiyar zuciya,har lokacin bata yi magana ba nd babuma alamun tana cikin hayyacinta bcos duka alamu sun gama nuna tunaninta ya tafi wani wajen,tsintar kansa yayi yana fad’in

        “Mah.! I need ur help.. Can u.!”

     Da sauri ta d’ago tana amsa masa

   “Ina sauraronka Yarona.. Fad’i ko mene ne kake son cewa,,in sha Allah idan har baifi k’arfin ikona ba kuma zan iya nemo maka shi a duk inda yake,nayi *ALK’AWARI* zanyi iya k’ok’ari na naga na sama maka farin ciki..”

     “Promise Mah..!?”

     “Promised habibiiy..”

   “Thank u Mah.. Buh ina Badra take yanzun..??”

      Sai da tayi jimm sannan tace

    “Sunje su raka HAFSAT gida..”

  “What..!? Gida fa Mah..?? Ina kenan..!?”

       Ya tambaya yana zaro ido

   “Gidansu mana.. Akwai wani gidan da zasu bayan nasu..!?”

   Dafe kai yayi cikin sauri ya mik’e ya kama hanyar fita a bedroom d’in,sai dai bai ko k’arasa bakin k’ofa ba Mamma ta dakatar da shi

   “Ina ne zaka je kake sauri..? Bayan kasan bamu gama maganar ba shi ne zaka tafi..??”

   “Am sorry Mah,, yanzun zan dawo,,buh Mah zan rok’i alfarmar wani abu.”

     “Fad’i ina saurarenka..”

  Shiru yayi kamar bazai fad’a ba kuma sai cewa yayi

   “Please Mah..! Dama ina son ne nace ki gwada yiwa Dad maganar ta..”

   “A wannan lokacin Hammad..!?”

  “Ehh! Mah,,tunda ya bada dama ina tunanin ai har yanzun lokaci bai k’ure ba ko..?”

   “A’a ni kam ban sani ba,,buh zanyi masa in sha Allah..”

   “Amma fa Mamma please kada ya wuce yau,,ina son nayi fighting ne akan right d’ina cikin tak’aitaccen lokaci,,hope zaki taimaka min nayi winning over My Dad..?”

   Murmushi tayi masa wanda ya tabbatar masa da hundred percent tana tare da shi,da saurinsa sai ya juya yana fad’in

      “Thank u Mah.. I love u..”

      “Love u too habibiiy..”

     Da gudu² ya fice daga d’akin zuwa nasa,wayoyinsa ya fara bincikar a inda ya barsu,nan a saman drawer ya gansu kamar yadda tun dare ya zubesu,d’auka yayi ya fara k’ok’arin kiran line Badra,,cikin seekonni da shigar kiran aka amsa,lokacin data d’auka ko gaisuwarta bai iya jira ya amsa ba yace

      “Ina kike yanzun..!?”

    Can daga gefenta ta amsa masa da fad’in

    “Yaya bana gida nefa yanzun,mun d’an fita..”

  “I knew ai.. Amsar tambayan da nayi kawai nake son ji..”

    “Uhhuumm..! Ban san sunan unguwar ba Yah,,amma barin tambaya naji..”

      Juyawa tayi dai² lokacin tana kallon Sabina dake kwance gefe tayi kicin² tace

      “Friend.. Mene ne sunan unguwar nan please..??”

       Bata d’ago ba ko ta kalleta ta bata amsa,yana jiyo sautinta a lokacin da tace itama bata sani ba,,sai yayi saurin fad’in

      “Ba sai kin fad’a min abunda tace miki ba,just go nd ask someone.. Maza da sauri,,sannan ki turomin address da duk wani information d’in inda kuke,,yanzun da sauri kada ki b’atamin lokaci..”

  A ladabce ta amsa masa da toh,sannan ta mik’e tsam ta fita daga d’akin,,d’akin Inna ta nufa,bayan tayi sallama Inna daga ciki ta amsa tana fad’in

      “Shigo mana Bilkisu..”

       “Toh! Inna.”

     Da zata shigama bayan ta d’age curtains sai data sake yin sallamar,amsawa Innar ta sake yi fuskarta da fara’a,tana shiga ta nemi guri ta zauna da fad’in

   “Inna sannu da hutawa,,dama tambaya ne dani,na tambayi waccan matar tak’i fad’a min,,I dunno why tunda muka tashi da ita yau take wasu irin behaviours,wollahi duk mun kasa gane inda ta nufa..”

   “Allah sarki,,aifa sai dai kuyi ta hak’uri da Maman nan tawa,wani lokaci wuyar sha’ani gareta,,to amma akan mene ne zaki yi tambayar ko Allah yasa na sani..!?”

  

   “Amm! Dama Inna ba akan komai bane,sunan unguwar nan ne kawai nake son sani..!”

  Murmushi Inna tayi kafin tace

“Sunan unguwar nan dai kamar yadda naji tun zuwanmu ana ce mata *KAWO* to amma da yake kamar akwai b’angarori ne dai ko mene ne dai ban sani ba,mu dai nan b’angaren da muke suna cewa *KAWON MAI GARI..”*

Tiryan² Inna ta rattafa mata bayanin duk abunda take son ji,godiya tayiwa Inna sannan mik’e da niyyar fita a d’akin dai² nan sai taga wayarta tayi haske,murmushi tayi saboda ta san duk yaji komai so ba sai tayi wahalar tura masa ba,sannan ta k’arasa fita ta koma gurinsu.

   Yana kashe wayar shima shiri ya sake yi sosai,banda murmushi babu abunda yake ajiyewa karamar wanda aka yiwa kyakykyawan albishir,Sultan dake kwance tun shigowarsa yana kallon abunda yake da duk wayar da yayi ya jishi ya mik’e ya zauna yana tambayarsa

  “Dude..! Ina zaka jene da wannan ranar..??”

Bai juyo ba bare ya kalleshi yace

  “Ina ruwanka..?? Ko kuma dai ka aike nine da kake tuhuma ta.?”

  “Allah baka hak’uri jarumi.. A dawo lafiya.”

Bai sake kula shi ba yayi ficewarsa,,shoulders Sultan ya d’age da fad’in

  “Idan tayi wari zamu ji ai..”

Sannan ya sauka akan bed d’in yana mik’a saboda har lokacin gajiya bata bar jikinsa ba,bayan ya gama mik’ar ya shige toilet da nufin yin wanka.

  Lokacin daya fito bai iya tafiya ba,sai daya biya ta kitchen ya yiwa Mamma sallama,bayan tayi masa addu’ar fatan alkhairi da samun nasara sannan ya fita cikin sauri da farin ciki,,tiryan² yabi duk kwatancen da Inna ta bawa Badra,abu kamar wasa da tambaya da komai sai ganinsa yayi a line da Inna ta kwatanta d’in,sai abu guda daya kasa tantancewa,wato gidan daya b’ace masa dan bai san wanne ne ba a cikin gidajen,,line Badra ya sake kira tana d’auka tace

  “Yah Hammad..!”

  Ko gama fad’a bai jira tayi ba yace

  “Da Allah ni fito waje na kasa gane gidan..”

  Da mamaki a fuskarta tace

  “Yah..! Zuwa kayi ne.!?”

 

  “Ke bana son kinibibi,,da Allah fito da sauri kada ki b’atan rai..”

  “Toh” tace masa,cikin sauri taja mayafinta tayi waje,,tana fitowa da motarsa ta fara arba ashema a k’ofar gidan yake tsaye,shima d’in yana ganin fitowarta ya saki ajiyar zuciya,followed by sauke glasses na side d’insa

  “Ina ita k’awar taku..??”

    Abunda ya fara tambaya kenan,a zaton Badra ko da yayi mata tambayar duka ta d’auka Mamma ta bashi labarin abunda ya faru,shi ne ya biyo ba’asin abunda ya janyo tahowar tasu da gaggawa,da hannu tayi masa nuni da gidan data fito

     “Je ki kiramin ita,yanzun ku fito tare.”

  “Toh” ta sake cewa sannan ta juya ko k’arasowama inda yake bai bari tayi ba,,a yadda ta barsu shiru haka ta dawo ta riske su,tana shigowa ta tsaya daga bakin k’ofa fuskarta babu yabo kuma babu fallasa tace

       “Wai ance ki zo..!”

      A tare suka d’ago su duka ukun,ko da ganin idanunta akan Sabina sai duk suka d’auke kai suna dariya k’asa²

  “Inji waye..!?”

Ta tambaya babu damuwar komai akan fuskarta

  “Yah Hammad ke kiran ki..”

  “Kije ki fad’a masa bazan zo ba..!”

  Amsar ta matuk’ar bawa gaba d’ayansu mamaki,a tare suka kalli juna sannan suka kalleta

  “Baza kije ba kuma princess..!?”

Jannat da Zee suka ambata lokaci guda,kallonsu tayi tana kad’a idanu ta sake maimaitawa

  “Ehh! Haka nace bazan je ba..! Ko da wani abu..?”

“Uhhuumm.! Amma kin san wane ne shi d’in da zaki fad’i haka kice a sanar masa..?? Kin san kuma matsayinsa a gurin wacce kika bawa sak’on..??”

  “Ko wane ne shi,,i don’t care na fad’a nace bazan jeba.. Sai me..?”

Mamakinta sosai ya bayyana a saman duka fuskokinsu,,ba tare da Badra ta sake magana ba duk da taji haushin maganar da tayi tace ta fad’awa d’an uwanta haka ta juya kanta tsaye zata koma ta fad’a masa abunda tace d’in

  “Please dear,,kada kije ki fad’a masa dan Allah..”

    Cewar Zeeharis da Jannat,,a fusace ta juyo ta watso musu wani irin kallo da fad’in

   “Ban gane kada na fad’a masa ba..? Munafurtarsa kuke so nayi kenan..??”

    “A’a dear,,ki dai samu wani abu da zaki ce please,,amma wannan maganar tayi nauyi da yawa kinji..!?”

    Murmushin takaici tayi sannan ta juya tana fad’in

   “Banyi kama da munafukai ba dan haka babu abunda zai hana ni fad’a masa gaskiya..”

   Kusan k’aro suka yi da Inna dake k’ok’arin shigowa ranta a had’e,da sauri Badra ta ja gefe tana fad’in

   “Afuwaan Inna,, ban san kina tafe ba..”

  Hannu Inna ta d’aga mata alamar tayi shiru ba sai ta k’arasa ba,,gana d’aya suka d’ago jin Badra ta ambaci sunan Inna,jifanta Inna ta fara yu da wasu irin mugayen kallo har na tsayin lokaci,wanda suka sa ta tilas ta sauke kanta k’asa.

Fitar Hammad daga gidan babu jimawa sosai Daddy ya shigo,,a lokacin tuni har su Mamma sun kammala aikin duk da suke,tana jin wucewarsa zuwa sama tabi bayansa,dan itama dai a yau d’in tafi son ayi duk wacce za’ayi tsakaninta da Daddy,acewarta wannan mulkin mallakar ya fara isarta haka nan,gara tayi maganin matsalar,,a bedroom d’insa ta iske shi yana cire babbar rigar dake jikinsa,ko data riski inda yake tsaye bayan ya amsa mata sallamar da tayi sai tace

   “Barka da dawowa Yallab’ai..”

  Yana murmushi ya amsa mata da

  “Barka dai uwar gida.. Ya hidimomi..??”

  Tunda yaga yanzun kamar ta sake akan farkon maganar auren na Hammad

  “Alhamdulillah.. Yallab’ai ya hanya..??”

  “Hanya kam mun barwa wad’anda suka fita yanzun..”

  Sai suka yi musayar murmushi wa junansu,,bayan nan kuma ta taimaka masa ya rage kayan jikinsa,bata d’auko masa maganar a lokacin ba sai data bari ya samu nutsuwa nd ya huta gajiya,sannan ta kalle shi tana fad’in

  “Yallab’ai.. Ni kam akwai maganar da nake so muyi da kai fa..”

  Fuskarsa a sake bayan ya d’ago ya kalleta yace

“Uhhuumm.! Ina sauraronki ai..”

  Itanma sai data d’an kalleshi a nutse ta karanci yanayin da yake ciki kafin tace

  “Dama ina so ne muyi magana akan yarinyar nan da kwanakin baya Hammad ya fad’a maka yana sonta.!”

  Wani lafiyayyen murmushi Daddy yayi mata sannan yace

  “Wace yarinya kenan..? Ina tunanin wannan magannar ta mutu tun ba yanzun ba..??”

  “A’a ba mutuwa tayi ba.! Tana nan a raye..”

  Murmushi ya sake yi sannan yace

  “Toh! Ina sauraronki..”

    Gyara zama Mamma tayi ta bada duka nutsuwarta akan Dad sannan tace

   “Batun nema masa aurenta nake yi.. Ina ganin tunda akwai sauran lokaci har yanzun me zai hana kamar yadda yace min yana so a had’a auren lokaci guda,sai ayi masa hakan..?”

   “Dakata Asiya.. Wai wannan wane irin zance ne kike son yi ne..?? Kina so ki nuna min ni naje nemawa Hammad aure yanzun wai..?? Mata nawa kenan zai aura..??”

      “Biyu..!”

   Ta bashi amsa a tak’aice

      “Biyu fa..?? To ko ni da nake mahaifinsa ban zauna da mata biyu ba sai Hammad da yake yaro.?? Ina zai kai mata biyu idan ba wauta ba da rashin tunani..?”

 

    “Yallab’ai..! Nifa duka ba kan maganar zai iya ko bazai iya muke ba,all i want yanzun kawai shi ne amincewarka,,tunda shi ya nuna yana muradi mu mene ne namu a ciki idan har zai yi adalci Alhamdulillah..!”

   “A’a Asiya,,ya kamata dai ki bar yimin wannan maganar.. Ke kina ganin ko da na amince ma misali akwai iyayen da zasu yarda su bashi aure a kwanaki uku kacal..?? Kiyi tunani mana..”

    “K’warai baza’a rasa ba..”

    “Toh ban amince ba,,kuma ba da yahuna za’a jeba,,in banda ke da abunki nawa Hammad d’in yake da zaki biye masa akan batun auren mata biyu,,ina ma laifin ace yanzun yayi auren idan an kwana biyu ya b’illo da batun k’arawar, amma lokaci guda yace mata biyu..?! Biyu fa².!”

“To wai Yallab’ai mene ne matsalar ne..??”

  “Matsala kike tambaya ta..??”

   Girgiza kai Mamma tayi tana fad’in

   “Ehh! Matsalar da tasa kak’i amincewa nake nufi,,ni banga aibun auren bane,tunda shi ya nuna yana ra’ayi..”

   Kallon baki da wayo Daddy yayi mata sannan yace

   “Wato ke dai idan na fuskance ki,duk abunda yaron nan yace yana so shi kike k’ok’arin yi koh..? Kin fi so ko wane lokaci ki biye masa akan duk shirmen daya zo da shi.??”

   “A’a Yallab’ai wannan fa ba shirme bane,,magana ce akan *SO* da kuma *BIYAYYA* tsakani da Allah idan ka kalli al’amuran yaron nan ko ba’a fad’a ba,kaima kasan yana tsananin girmama maganarmu,to mu akan mene ne baza mu kyautata masa ba..?? Tunda ka zab’a masa mata kace sai ya aureta ya hak’ura yabi ra’ayin ka yanzun da yace ga wata wacce yake so,ya kamata ace ko bai ce ka aura masa ita ba,kayi k’ok’arin yi masa hakan,dan gaba ya samu k’warin guiwar da ko motsi kayi baka ce masa yayi maka kaza ba,yayi hanzarin biya maka buk’atar ka,,tsakani fa da girman Allah..”

    Kasak’e Daddy yayi yana kallonta har tayi shiru,hannayensa ya nad’e a k’irji ya zuba mata idanu sannan yace

   “To naji.. Amma dai batun aure ni kam nace ba yanzun ba..”

   Kallonsa Mamma tayi saurin yi da fad’in

  “Ban gane ba yanzu ba da kake ta fad’a.. Idan ba yanzun ba sai yaushe kenan..??”

   “Babu lokaci.. Ke nifa bari kiji ma k’arshen maganata,yarinyar nan da kuke maganarta,ko da zinare aka k’erata na haramtawa Hammad aurenta tunda har akanta ya nemi ya fara jayayya da ni..!”

   A mamakance Mamma ta kalloshi

   “Kace baka yarda ba..?? Sannan kace ka haramtawa Hammad aurenta..??”

  “K’warai haka nace,kuma haka nake nufi..”

   “Wollahi to bazai yiwu ba.. Saboda Allah don kawai wani ra’ayinka kace zaka hanawa yaro abunda yake so.. Idan kai baka da ra’ayin yin mata biyu,shi ka kashe masa muradinsa,,tsakani da Allah wannan maganar ai bama mai yiwuwa bace..”

  “Kika ce bazai yiwu ba..?? Wato zaki yi jayayya da maganata kenan..”

  “K’warai kuwa nima haka na fad’a..”

    “Ai shi kenan sai mu zuba mu gani,,ni dai nace ban amince ba,,idan kuma kina ganin zaki yi masa auren ne bismillah,,kin zab’a masa,nima kuma na zab’a,zanga da yadda za’ayi mace taje neman aure,dan ni dai babu k’afata a ciki…”

     “Ehh! Sai kasa ido ai,,wani abune dan baka jeba..?? Ni zanje kuma zan nemawa Hammad aurenta tunda har ita yake so,,in Allah ya yarda zaka sha mamaki..!”      Ran Inna idan yayi dubu ya gama b’aci dan tunda suka fara magana tana jinsu,kuma duka maganganunsu akan kunnenta aka yi a lokacin tana fitowa daga bayan gida,gaba d’aya a cikinsu babu wanda yayi zaton ta fito shi yasa ma suka ci gaba da maganar basu saurara ba,abunda kawai zasu d’orar shi ne sun ganta ta shigo d’akin,sannan ita kanta Sabinar lokacin da take maganar bata yi tunanin za’a samu matsala ba shi yasa,lokacin da Inna ta shigo d’akin tana kallonta take ta sha jinin jikinta musamman kuma da taga irin kallon da take mata sai duk yasa jikinta yayi sanyi,da sauri ta mik’e ta zauna tana sunkuyar da kai k’asa bcos ba zata iya jurar kallon Innar ba,,sai da Inna ta sake jifanta da mugayen kallo kafin ta kalli inda Badra ke tsaye da sunkuyayyen kai tana kallon k’asa

    “Bilkisu..! Wane ne yake kiranta ne ta bada wannan sak’on a fad’a masa..??”

      Jimm Badra tayi ta kasa bata amsa har sai da Innar ta maimaita mata tambayar

         “Yayana ne Inna..!”

    Ta bata amsa kanta har lokacin a k’asa,juyawa Inna tayi a fusace ta kalli inda take zaune

     “Ke yanzun dan baki da mutunci,,ko dai ace baki ji kunyar fad’ar maganar ba,ai kyaji kunyar ita wacce kika bawa sak’on,,idan ba rashin mutunci bama da iskanci har a aiko kiranki kice bakya zuwa..?? Zaman me zaki yi mana a nan d’in..? Ni dai kam *MAIRAMU* wollahi ban san ina kika aro wad’annan sababbin halayen ba,ace mutum shi kenan shi halayensa a murd’e..? To wollahi kiji ki kuma k’ara ji,ba dani zaki yi irin wannan halin rashin mutuncin ba,tun muna shaidar juna ma dake,sahunki a likaffa ki tashi ki fice kafin na b’atar miki..”

    Sai da Inna tayi mata tatas a gabansu kafin ta juya a fusace ta fice,,a hankali hawayen bak’in cikin fad’an da Inna tayi mata a kan idanunsu suka gangaro mata,iya tsayin tasowarta yau rana ta farko Inna ta bud’e wuta ta mata fad’a,a hakan ma kuma ba’a barta taji da haushin fad’an da akayi matan ba,sai da aka k’ara da bata takaicin yi mata a gaban k’awayenta,ita wannan abu dame yayi kama.? Ace a rasa inda za’a mata fad’a sai a tsakiyar k’awaye. Hawaye ta ci gaba da zubarwa tana jan zuciya babu sassauci,,gaba d’aya daga su Jannat dake zaune kusa da ita har Badra dake tsaye sai da lamarinta ya basu matuk’ar mamaki dan dai su basu ga abun da za’a ce tayi masa kuka ba a wannan y’ar maganar da Innar tayi,,shiru² da Inna ta gani bata da niyyar fitowa yasa ta rafka mata kira followed by fad’an zata zo ta fita ko sai ta taso,tsananin haushi gami da takaicin takurata ta fita yasa ta mik’e a fusace ta fizgo k’aton hijab d’inta dake gefen katifarta tayi waje ko takan Badra dake tsaye tana jiranta bata bi ba tayi wucewarta,,cike da mamakinta da har lokacin bai barsu ba Zee data dawo da idanunta daga rakiyar da tayi mata tace

     “Allah ya kyauta..”

  Jannat dake gefenta ta amshe da

    “Ameen dai y’ar uwa.”

  

   “Uhhuumm..!” Shi ne abunda Badra ta iya fad’a ba tare da tayi magana ba tabi bayanta da sauri,,a k’ofar gida ta isketa ko inda yake bata k’arasa ba ta coge a guri guda,,shi kuma gogan yana zaune cikin mota yana kallonta tun data fito yake kallonta amma yak’i fitowa,yadda ta tsaya rai b’ace yasa jin babu dad’i,duk da dama yasan za’a rina,,a hankali ya sauke glasses d’in dake gefensa ya yafito Badra da hannu,wuceta tayi ta isa inda yake bata ko kalli inda take ba,shima d’in tana k’arasowa ba tare daya kalleta ba yace

       “Mene ne ya faru.??”

   Tana kallonsa tace

      “Babu komai..”

   

      “Kin san bazan yarda ba ko..? Fad’a min gaskiya me aka yi mata.!”

       Sunkuyar da kai tayi k’asa tace

      “Inna ce tayi mata fad’a..”

   

      “Akan mene ne..??”

     Sake sunkuyar da kai tayi sannan tace

      “Cewa tayi baza ta zo ba.”

   

      “Shi ne sai aka yi mata fad’a akan wannan y’ar maganar..??”

   

      “Ehh.! Haka ne..”

   

      “Me yasa baki zo kin fad’a min ba to kika bari aka b’ata mata rai..?? Kina son ganin b’acin raina akan ki ko..?”

      Saurin d’agowa tayi tana kallonsa da fuskar damuwa

      “Yah Hammad..! Bafa haka bane..”

   

      “Uhhuumm.! Fad’a min yaya ne to..?”

   

      “Nifa bani na fad’awa Inna ba,,kawai taji maganar ne,kuma lokacin zan fito na fad’a maka sak’on shi ne Innar tayi mata magana..”

     Sai lokacin ya kalleta shima a kaikaice ya tab’e baki sannan yaci gaba da magana

      “Kin tabbatar bake kika fad’a aka mata fad’a ba..??”

     Dai² mak’ogoronta tayi saurin rik’owa tana sake marairaice masa kamar za tayi kuka tace

      “Na rantse Yah ni bance komai ba.. Ka yarda dani,wollahi ko su Jannat ma ka tambaya kaji zasu fad’a maka..!”

     Yadda idanunta suka fara tara ruwan hawaye ya sashi jinjina kai ba tare da damuwar hawayenta da yanayin da tayi maganar ba yace

      “Uhhuumm..! To da kyau.!”

      Daga haka kuma yayi shiru bai sake magana ba kuma bai kalli inda ita kanta Sabinar take tsaye ba,,tsaiwa Badra taci gaba da yi while shi kuma yana kallon tsuntsuwar tasa data mak’ale a guri guda ta wutsiyar idonsa,sai daya d’auki ak’alla mintuna biyar yana kallonta kafin ya juyo yana murmusawa ya kalli Badra data kasa tafiya

       “Tsaiwar me kike yi ne kuma..?”

  Fuskarta da damuwa ta kalle shi tace

     “Yah..! Naji ne kayi shiru baka ce na tafi ba ai..”

    Wani irin kallo yayi mata na ban gane me kike fad’a ba kafin ya ce

      “Sai kici gaba da tsaiwa ai,idan nace sai ki tafin..!”

     Yadda yayi maganar kamar da gatse yasa ta fahimci yanayin da yayi mata maganar,a hankali sai taja k’afafunta ta bar wajen,tana zuwa dai² inda Sabina ke tsaye ta kalleta sosai k’asa² tace

      “A nan zaki tsaya ne madam..?? Ko kuma dai saina shiga na fad’awa Inna har yanzun baki ji maganar ta bane..??”

      Saurin kallonta tayi ba tare da Badran ta tsaya jin abunda zata fad’a ba tayi cikin gidan da sauri gudun kada ta janyowa kanta fad’an Yayan nata da cikin k’ank’anin lokaci duk ya rikid’e ya koma wani masifaffe,,haushin yadda ake neman takurata tayi abunda bata so shi ne ya sake kamata,a hankali kuma maganar da Badran tayi kafin ta shige yayi mata reverse cikin kwakwalwa,gauron numfashi ta sauke bayan tayi tunanin idan har Inna taji labari zata sab’a mata,tayi saurin kawar da tunanin k’in zuwa inda yake a ranta,jiki babu k’wari ta d’ago ta sake kallon motar nasa sannan taja k’afafunta zuwa inda yake.

      Tunda ta fara tahowa yake kallonta,sai dai ba lallai ne ayi saurin fahimtar hakan ba bcos ba directly yake kallon nata ba,shi yasa babu yadda za’ayi mutum yayi saurin fahimtar hakan,sai dai ko shi da yasan siririn yin hakan a gurinsa,murmushi ya saki wanda yake sake bayyanar da asalin cikar kamalarsa a dai² lokacin data k’araso,sannan ya d’age glasses d’in zuwa sama bcos baya so ya bata fuskar da zata nemi ta jashi a k’asa,duk da yasan tana yi masa kallon mai laifi,,yadda yayi lokacin data k’araso sosai yasa ta d’agowa ta kalli motar,gaba d’aya glasses d’in jikinta tint ne,saboda haka ba lallai ne a iya gano wanda ke ciki ba bare kuma a iya gano abunda yake yi,,a gefe ta sake tsaiwa a tunanin ta ko zai fito,amma sai taga ya bud’e mata d’ayan side d’in na mai zaman banza,sai data gama jan class d’inta kafin ta zagaya ta shiga ta zauna,shi ya rufe k’ofar had’e da locking motar gaba d’aya ta yadda babu yanda za’ayi ta iya fita ko wani shigo har sai idan shi ya bada damar yin hakan,ba tare data kalleshi ba tace

    “Mene ne nufinka na zuwa gidan mu ne..?”

     Kallonta ya d’anyi bai ce komai ba yayi shiru,sake maimaitawa tayi still yak’i yin magana,haushin shirun da yayi mata yasa a fusace ta d’ago ta kalle shi,cikin azababben fad’a mai tafe da kishi tace

      “Wai me kake nufi da ni ne..??”

     Sai lokacin da tayi maganar sannan ya juyo ya kalleta fuskarsa d’auke da murmushin dake narka mata zuciya ya zuba mata idanunsa daya shanye

      “Me aka yi miki ne My Lady..?”

     Sosai tambayarsa ta bata haushi,sai dai ta daure bata tanka masa ba

     “Nayi tunanin ko da kika zo ya kamata ne ace kin nema min amincin Allah,amma kin shigo min babu sallama,nd kina tuhumata abunda nake nufi dake,without kin yimin kara kin gaishe ni.!”

       Ya k’are maganar dajifanta da hararar wasa,kunya ta d’an ji da yayi maganar,sai kawai ta juya masa k’eya da fad’in

      “Assalamu alaika.!”

     Sai da yayi murmushi mai sauti kafin ya amsa mata da

     “Wa’alaikis salaam warahmatullah wabarkatuh.!”

       Har lokacin bata juyo ba tana kallon waje tace

    “Ina yini.. Ya mutanen gida..??”

  Shiru yayi mata bai bata amsa ba shima akan lokaci sai daga baya yace mata

     “Komai lafiya.”

  Itama daga hakan sai tayi shirun bata sake ce masa komai ba,a haka har suka d’auki tsayin mintunan da su kansu basu san adadin su ba,gajiya yayi da zaman shirun yana kallonta yace

   “Wai ke haka ake yi ne,mutum yazo wajenki amma sai kiyi masa shiru.?? Me kike nufi ne Yallab’iya..?”

    Bata kalle shi ba k’asa² tace

     “Abunda duk kake nufi da ni nima shi nake nufi..”

   Kallonta yayi sosai jin yadda ta bashi amsa kai tsaye duk da bawai tayi don yaji ba

   “Wai mene ne matsalar ki ne Lady..?”+

   “Kafi kowa sanin matsalata ai.. Mene ne na saurin tambaya..?”

   Murmushi ya sake yi,cikin sanyin magana yace

  “I dunno Lady,,kinga ya kamata ki fad’a min sai na sani ko ba haka ba..??”

   Juyowa tayi ta kafe shi da kallon mamakin abunda yake fad’a,wai bai san abunda ke damunta ba yake cewa,bayan yafi kowa sanin abunda aka yi,ita zai rainawa hankali ya fad’a mata wannan maganar banda ma ya rainata,,maganar Sultan ce ta dawo mata kamar yanzun yake yi

  _”Ur Lady fa.!? Dama itace amaryar kake wani nok’ewa,sai cewa kake baka so,,ashe duk munafirci ne abun..”_

   Yanayin kallon da Hammad yayiwa Sultan  lokacin da yayi maganar shi ne abunda yafi komai d’aga mata hankali da tsaya mata a rai,dalilin da yasa tayi saurin fahimtar akwai wani abu a bayan maganar da yayi,dan haka da sauri ta fahimci komai duk da bai k’arasa ba

   “My Lady.. Kin daina magana ne..?”

   Tsabar haushinsa da take ji a lokacin bai hanata tambayar saba

      “Me ka gani..??”

   “Naji kinyi shiru ne,,kiyi min hira mana..”

  

   “Da baka nan waye yake maka ne..??”

   Murmushi yayi mata mai kwantar da hankali yana bata amsa a lokaci guda

  “Lokacin da bana nan,,aiki baya barina zama da kowa,,amma yanzun tunda gani ga ki kinga zaki d’ebe min kewa ko.??”

   “A’a’a.. Ni ban iya ba ai..”

    “Wane ne ya iya kenan..?”

   Ya tambaya yana kallonta

     “Amaryarka mana..!”

  Sosai maganar ta zo masa a bazata,gyara zamansa yayi yana fuskantar ta while ya kwantar da kansa jikin seat sai dai bai ce mata komai ba akan maganar da tayi,yayi k’ok’arin canja musu hiran da fad’in

    “Babah yana gida ne ko ya fita..?”

    Bata kalle shi ba tace

  “Mene ne zaka yi masa..??”

    “Ina ruwanki da abunda zanyi masa..?? Ko ke dana kira ki kika ce ace min baza ki zo ba wani ya tambayeki abunda ya had’a mu kika fad’i hakan.?” 

  Tab’e baki tayi alamun bata ji haushin maganar ba sannan kuma bata bashi amsar tambayar da yayi mata ba,haka tabarshi yayi ta magana duk da ba ma’abocin yinta bane,da ya gaji shi da kansa ya kyaleta,yana sake maimaita mata tambayar da yayi mata da fari game da Baba,still ta sake masa shiru bata kalle shi ba dan tana jin bata yi niyyar magana ba,d’agowa yayi daga jikin seat daya kwanta ya matso daf da ita

   “Wai mene ne yake faruwa dake ne..? Na kasa fahimtar inda kika nufa fa..??”

  “Ai kuwa bana tunanin zaka gane in dai haka ne.”

    “Me yasa haka to.!?”

  Kallonsa tayi a fakaice sannan tace

   “Babu amfanin nayi maka bayani bcos bana jin zaka fahimta..”

   Murmushi yayi mai sauti,kafin ya kyalkyale mata da dariya,irin wacce daga ji zaka fahimci shak’iyanci da rainin wayi yasa shi yin ta,a cikin dariyar yake mata magana

   “Ke yarinya ce ai har yanzun..”

  Saurin kallonsa tayi tana nuna kanta da fad’in

    “Ni ce yarinyar..!?*

   

      “To idan ba keba da waye nake..?”

  Baki ta murgud’a masa tace

  “Wollahi ni ba yarinya bace,,sai dai idan wannan mai bak’ar fuskar kake fad’awa haka..”

   Sake kyalkyalewa yayi da dariya ita kuma ta had’e rai a dole taji haushinsa,ganin ba shi da niyyar daina dariyar ya sake tunzurota,a fusace ta nemi bud’e motar ta fita,saboda haushi har ta manta ya rufe motar tun shigowarta,sai da tayi iya yinta ta bud’e ta kasa ta juyo tana kallonsa

    “Bud’e min ni na fita..”

      Dakatawa yayi da dariyar da yake mata yana tambaya

      “Ina ne zaki je..?”

   

     “Inda na fito.. Bud’e min ni dai na wuce..”

      Yana kallonta yace

      “Wai wace cema mai bak’ar fuskar ne.?”

      Harara ta wurga masa tace

      “Matar ka mana da zaka aura..”

     Murmushi yayi mai sanyi yana dafe saitin zuciyarsa,a hankali ya lumshe idanunsa yana fad’in

      “Bak’ar fuska ne dama dake..??”

   

   “Ban gane ba..??”

   “Dama baza ki gane ba ai.”

  “Saboda mene ne bazan gane ba to..?”

   “Ban fad’a domin ki gane ba.. Idan ni na fahimta ya wadatar..”

 

  “Uhhuumm.!” Tace ta sake jan baki tayi gum daga haka bata sake magana ba.

*Some hour’s leave…*

     Sai wajen Maghreb sannan Baba ya dawo gida,tun daga k’ofar gida da suka gaisa,Baba cikin tsananin mamakin ganinsa yasa ko tsayawa bai iya yiba,ya wuce cikin gida,a lokacin kuwa tuni su Badra har driver ya zo ya maida su gida,,shigarsa bai ko zauna ba ya kabartawa Ina wanda Allah ya nuna masa,murmushi tayi cikin zuciyarta tana mai yiwa Allah godiya had’e da yi masa tsarkaka kuma mafiya dad’in kirari, daga nan suka tsunduma hiran abunda suke ganin zai fishshesu.

   

     Gaba d’aya hirar tasu fiye da rabinta shiririta ne a cikinta,in banda tsokana da neman fitinannen babu abunda yayi ta mata,tun tana jin haushinsa ita da kanta ta sauke,,duk da a gefenta da farko idan ya fad’i magana ko ya tambayeta sai dai ta bashi amsa a tsaye,,a hankali cikin hikima yayi ta tsokanar ta yana watso mata tambayoyi cikin hikima,,duka basu wani jima sosai ba tuni ya gama fahimtar damuwarta,yinin ranar gaba d’ayan a unguwar yayi shi tare da ita.

    Dama zaman yayi shi ne ba don komai ba sai domin ya jira dawowar Babanta,coz yana maganar da yake son su tattauna sa shi tunda Allah ya dawo da shi,,a wannan ranar tunda Hammad yazo bai yarda ya tafi ba sai da tarihi ya maimaita kansa a gurin iyayenra,bayan an tuna baya ya basu labarin yadda rayuwa tayi masa bayan barinsu da yayi,da duk abubuwan da suka gabata a raguwarsu gaba d’aya,ciki kuwa harda Baffa zuwaa mutuwarsa,wacce tayi matuk’ar girgiza Hammad,,dattijon arzik’i mutum mai kamala da sanin ya kamata,ga daraja mutane ko da bai sansu ba,,bayan da k’ura ta lafa duk dama dai ba wani tashin-tashina suka yi ba,kasancewar suna sane da bayanin da baffan Inna yayi tun a wancan lokacin,shi yasa ko da yayi musu bayanin abunda ya faru basu ga laifinsa ba,suka dangantaka faruwar hakan a matsayin K’addarawa ta ubagiji.

      Bayan duk sun gama magabar suka ci gaba da hira irin wacce aka jima ba’ayi irin ta ba,,sai da dare ya riske shi sosai sannan yayi niyyar tafiya,bayan yayi musu sallama da alk’awarin dawowa gobe idan Allah ya kaimu,fatan alkhairi suka yi masa duka,sannan yayi hanyar fita yana sake yin sallama da su,,Inna ce ta kirata dan ita tuni ta k’ule a d’aki ta basu guri,lokacin da taji Inna na kiran nata hijab ta sake sakawa ta fito da fad’in

     “Inna gani..!”

    

   “Sai kije ai kuyi sallama,tunda ya fita ko.?”

  A sad’ad’e ta amsa mata jiki babu k’wari sannan ta wuce tabi shi,,a zaune ta tarar da shi a cikin mota ya zuro k’afarsa d’aya waje,d’ayar kuma da sauran gangar jikinsa a ciki,jikin motar ta samu ta jingina bayan tayi masa sallama,ya amsa yana d’an kallonta k’asa² har na tsayin mintuna biyu sannan yace

“My Lady.. Zan tafi,,sai munyi waya kenan.!?”

   Bata kalle shi ba tace

  “A ina ka samo number da zaka kira ni..?”

   “A gurinki zan samu..”

  “Ni bazan baka ba..!”

   “Da gaske..?”

   “Ehh! Bana bayar wa..”

    “Dole ne ki bani,ko da kin hana kowa.!”

   

      “Idan nak’i fa.? Zaka k’wata ne ta k’arfi..??”

    Sai da ya sakar mata wani murmushi sannan yace

      “Sosai ma..! Ko zaki gwada hanawa ne na nuna miki yadda zanyi dake.?”

     Shiru tayi bata amsa ba,shima sai ya kawar da batun ta hanyar mik’a mata wayar daya janyo a gefensa,k’in karb’a tayi akan lokaci har sai data janyo ya kusa fizgota,Allah ya dai rufa mata asiri duk da line babu kowa tayi saurin kaucewa amma da tuni ta fad’o jikinsa

     “Karb’i ni kina b’ata min lokaci,,kin san kuma na fad’a miki bana son kina min wannan jan ajin..”

      Kafad’a ta mak’ale masa alamun A’a,idanu yasa mata na tsayin wani lokaci kafin ya kalleta bayan ya maida wayarsa ya ajiye yace

      “Zaki iya tafiya.. Sai da safen ko kuma dai sai kinji muryana zaki iya yin bacci.!?”

   

     “Allah ya tashe mu lafiya,,ka gaida min Mammah.!”

     Murmushi yayi ganin bata kula wancan maganar ba da fad’in

      “Zata ji in sha Allah.. Sai munyi waya..!?”

   

     “Umm!” Tace masa sannan yace mata ta shiga gida,kamar baza ta tafi ba haka tayi ta jan jiki daga baya kuma ta shige,kai ya girgiza a hankali saboda tunawa da shiriritar da tayi ta masa a fili ya tsinci kansa da fad’in

      “Daddy.! Gani nan tafe,zuwa gare ka. “

    Yana fad’a yayi saurin juya kan motar ya bar unguwar da mugun gudu.

   

     A can gidansu ma,lokacin ko da Mamma ta cewa Dad

        _”Ehh! Sai kasa ido ai,,wani abune dan baka jeba..?? Ni zanje kuma zan nemawa Hammad aurenta tunda har ita yake so,,in Allah ya yarda zaka sha mamaki..!”_

      Takaicin maganar ne yasa Dad yin fushi,ba tare daya sake yi mata magana ba,a fusace ya fice ya bar mata d’akin,d’age kafad’a tayi itama alamun bata damu ba,sannan ta fita ta bar d’akin cikin zuciyarta tana tunanin mafita data rage nata duk duniya,nata d’akin tayi saurin nufa,kai tsaye ko da zuwa ta d’auki wayarta ta bazama cikin contact d’inta tana laluben numbersa,,dai² kan sunan daya bayyana *MALAM BABBA* ta tsaya a fili ta fara jera sakin ajiyar zuciya,bayan tayi y’an tunanin da take ganin zasu taimaka mata ta tura kiran ya tafi.

     Lokacin da wanda ta kira ya d’auka da sallama ta fara yin magana muryarta a sanyaye cike da girmamawa,har suka gaisa ya tambaye ta iyali da mai gidan nata,still jikinta yana a sanyaye ta amsa masa,daga nan kuma ta zayyana masa jawaban duk abubuwan da suke faruwa a gidan,saurarenta Malam d’in yake yi amma daga dukkan alamu cike da damuwa yake shima lokacin,daga bisani kuma ya k’are da bata hak’uri sannan ya ce ta bari zaizo gidan gobe da yardar Allah saboda maganar sam bata danganci wacce za’ayi a waya ba,,godiya tayi masa sosai kafin suka yi sallama,lokacin data gama wayar sanyayyar ajiyar zuciya tayi tana murmusawa saboda ko babu komai a yanzun kad’ai ta samu nutsuwar zuciya,while a gefe guda kuma tunanin zata tabbatarwa da Daddy yayi wasa d’an zaki ya girma yasa ta sake sakin k’ayataccen murmushi,a fili kuma bayan ta ajiye wayar haka nan ta rik’e waist tana kallon wall clock da fad’in

      “Uhhuumm..! Yallab’ai kenan,,kayi zaton kai kad’ai ne kake da iko da Hammad..? Hammad Yaro na ne da nake matuk’ar k’auna fiye da rayuwata,kuma kai kanka ka tabbatar da wannan k’aunar,saboda haka na d’aura d’amarar k’watar masa y’ancinsa a hannunka tunda kai da kake matsayin mahaifinsa ka kasa yi masa abunda ya kamata,,bazan tab’a bari ka wulak’anta min rayuwarsa ba,ta hanyar hana shi farin cikinsa,wannan yak’in na shirya yisa ne ba don kowa ba haka nan ba don komai ba,sai dan saboda farin cikin Yarona.. Idan kayi jayayya da mu na tabbata bazaka tab’a iya yin jayayya da Malam ba,shi yasa nayi tunanin saka shi a ciki,,idan kuma har ka iya yin jayayya da shi to na tabbata bazaka tab’a ja lamarin ubangiji ba,,amma kuma tunda ka tirje ni da hannuna zan zarge maka wuya da igiya na janyeka daga gefen hanya,tun kafin rabo ya kaika k’iyama..!”

       Numfasawa tayi a fili bayan kamar minti guda ta sake cewa

      “Yanzun wasan namu zai fara,,saboda haka ka shirya ga Malam nan tafe zuwa gare ka.!”

   

      Yana shigowa cikin parlor da Daddy ya fara arba zaune yana kallon news,inda yake ya k’araso da sallama,bayan ya gaisheshi bai zauna ba yayi hanyar staircase zaiyi sama,tun shigowarsa Dad baiyi magana ba kuma dama shi ya zauna jira a zaman da yayin,dan idan batun TV ne,ko wane d’aki akwaita sai dai da yake sunfi son zama a parlor’n idan suna nan,yasa na d’akunan suka zame musu kamar pictures sai lokaci² ake kunna su,har ya fara tsallakawa Daddy ya kirashi

      “Hammad..! Zo nan.!”

      Dawowa yayi kamar yadda Daddy’n ya buk’ata yana zuwa gabansa ya zauna saman rug da fad’in

      “Gani Dad..”

      Tambayar farko da Dad yayi masa ita ce

      “Yaya muka yi da kai d’azun..??”

     Sunkuyar da kansa yayi yana fad’in

      “Daddy.! Naje fa,yanzunma daga can nake..”

     Kallon rashin yarda yayi masa ba tare da yayi saurin k’aryatawa ba yace

      “Are u sure..!?”

     

      “Ehh.! Dad am very much sure.!”

   

      “Good.. Allah yayi maka albarka.”

      Amsawa yayi da fad’in “ameen” a fili kafin ya kalli Dad d’in daya mayar da hankali kan News yana fad’in

      “Daddy.! Shi kenan,zan iya tafiya..!?”

     Bai d’ago ba yace masa

     “U can go.. Ni ai na gama magana,tunda kaje aiken da nayi maka ai duk mai sauk’i ne,,jeka Alla ya tashe mu lafiya..?”

     Da sauri ya tashi ya bar wajen,dan ma kada Daddyn ya sake masa maganar yasa shi had’awa da tsallake matakalar benen da sauri² kafin kace me tuni ya b’ace a gurin,,sai daya tabbatar ya shige bedroom d’insa murmushin mugunta ya sub’uce masa a fili ya shiga magana da kansa

      “Dad.! Kenan,,me yasa tun farko zaka k’i amince min ne akan abunda zuciyata ke so..? Shin baka san hakan yana cutar da ruhi na ba..? Ko kuwa baka san a duk lokacin dana tuna kai kayi min silar rashinta a lokacin daya gabata ina ganin laifinka ba.??,,shi kenan ma dai duka wannan ya wuce,abar tuna baya,,kamar yadda kace nan da 1 month idan har nayi yadda kace zaka amince ka aura min burin zuciya ta,shin yanzun da na nemo inda ajiyata take,,zaka amince ka karb’i batun auren nawa ko kuwa..?” 🤔

   

     

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *