ALLURA CIKIN RUWA BOOK 1 CHAPTER 13 BY BILKISU S. AHMAD FUNTUA
motarsa, na mai da hannuwana bisa kirji na goye su na zuba wa Aliyu ido.
Cikin murtuke fuska Aliyu ya ce,Tsakanina
da ke abin da-zai biyo baya ke nan ko? Wato kin daukeni wani iri shine kika shawo ado kika fito wajen wadannan
“yan karyar, amma jiya daga na yi miki
maganar hoto kika mai dani ko oho, dubi wani ya fidda ke waje kun bata lokaci mai yawa kuna hira. Shima an tsara shi kamar yadda aka tsara ni ko?” Na yi shiru ina sauraronsa, domin babu wani abin da zan gaya masa ya saurare ni, tunda naga ya harzuka. Sai kawai na juya ba tare da na ce uffan ba na nufi gida.
Can na ji ya kara kwalla mini kira, na yi biris
da shi, sai na bude gida na shiga. Zuwa can na ji ya ja mota ya ta fi, na shiga dakina na kulle na fada bisa gado na fara kuka.
Na yi kukan kusan tsawon awa uku, sannan na
ji kaina ya fara sarawa, na daure na tashi na sanya kayan barcina, na duba agogo na ga karfe daya da rabi,
na koma bisa gado na kwanta hawaye na ta bi bayan kunnena yayin da filona ya jike sharkaf.
Ina jin tunda na fara rayuwa a duniya ban taba
ganin bacin rai irin wannan ba, saboda ni dai ba ni fada balle malami ya doke ni ko mahaifina, haka ba a taba kawo karata wajen mahaifina daidai da rana daya
balle har su bata mini rai ba. Ina murna inzo Kaduna hutu, amma a wannan
dare Kadunan ta fita raina, babu abin da nake so irin na ganni a gidanmu. Da mahaifina bai barni zuwa wannan hutu ba, da ban zo Kaduna har na gamu da Aliyu harna shiga wannan tarko na soyayya ba, da har ina gani zaya wahalar dani haka.
Bisa zance na hakika ina ganin son da nake
yiwa Aliyu ba zan iya rabuwa da shi ba, in har ba shi ya buda baki ya ce in rabu da shi ba, to kuma ina da wahala, tun da yau duka-duka haduwarmu da Aliyu kwana nawa; amma ya fara Bullo mini da irin wannan hali. Ko ni da kaina na je wurin Kabir, ai Aliyu bai
kamata ya yi min fada irin na yau ba, amma babu komi don ya ga ina sonsa ne.
Da safe bayan mun yi kalaci mun gama kintse-
kintse, muna zaune a falo tare da Mama Inki, a nan ta sami damar tambaya ta wanda ya ba Ummi wadannan makudan kudi, na shaida mata Kabir ne. A ra’ayina ban yi niyyar gaya wa kowa ba abin da ke tsakanina da Aliyu, amma da Mama Inki ta yi
maganar wadannan kudi da Kabir ya ba da bai yi daidai ba sun yi yawa, sai na tsinci kaina ina share kwalla ta gefen idona da hannuna na dama.
Mama Inki ta nemi da in gaya mata abin da
yake bata mini rai, nace Babu komi, ina dai son
komawa gida ne gobe” Sai nan da nan na ga ranta ya baci, tace
‘Amma sanda na dauko ki ba haka muka yi da
mahaifinki ba, a bisa lissafi yau sauran kwana biyar ki koma, kuma ma duk abin da ya dame ki ai ni ya kamata ki gayawa ba Yaya Aisha ba, ko ba a nan kike ba. Haba Asiya ina ganin ki mai hankali ya ya za ki bullo mini da wani hali na daban?”Sai nasa gefen zanina na share *yan kwallan da suka fito mini, sannan na zayyana mata yadda muka
kwashe da Kabir, har zuwa yadda muka yi da Aliyu.Sai ta yi dariya ta ce,Asiya guda nawa kike balle har ki san halin maza? Aliyu saboda zafin son da yake yi miki dole hankalinsa ya tashi ran da duk ya ganki da wani, kuma daman mai suna Aliyu zuciya ne
da shi sai dai idan ba sunansa ba ne. kuma lokacin da ya ce miki bai kamata ki saurari irin su Kabir ba, abin da ya kamata ki ce masa shine, kin bar wuka da nama
a hannunsa ya yi miki maganin al’amarin.
Kina nan kina bata ranki, shi yanzu duk inda
yake hankalinsa ba ya kwance, gani yake yi Kabir zaiyi kokari ya juyar miki da kai. Ban da Aliyu daga ganin Sarkin Fawa sai miya ta yi zaki”Na ce,Wallahi Mama ko magana bai bari nayi ba ya hau ni da fada Ta Ce,
“Namiji ya fi mace kishi, amma sai a
rika cewa mun fi maza kishi nan” Mama Inki ta dinga gaya mini maganganu
masu kwantar da hankali, sai na ji kwata-kwata na manta da bacin ran da ya faru dani.
Da azuhur muna zaune ina tare da yara muna karatun Alkur’ani, sai aka kira in zo an yo mini waya, na san dai kila Aliyu ne ko Kabir. Ina dauka sai na ji muryar Aliyu. Ya ce, “Asiya?” nace,Ina wuni?”Ya ce,
“Lafiya lau, don Allah ki shirya ke da su
Maryam zan z0 in kai ku gidan wani abokin aikina, matarsa na son ganin ki”
Sai na yi sauri na ce,Kash! Sai dai ko su
Maryam ni ba zan sami dama ba Kafin ya ce wani abu sai na ce,Sai anjima”
Na aje wayar abina na koma muka cì gaba da karatu. Da la’asar aka sake bugowa, na tabbatar Aliyu ne dai, ina dauka na ce, “Uhm!”
YaCe,Asiya wai me ke damun kanki ne?”
Na ce,Shi ke nan ko”. A nan take na katse
wayar na tafi abina.Haka ta kasance wannan ranar ya dinga bugo
waya, tun da na dauka sau biyu ban Kara dauka ba. Wani abu da yake damuna shine, duk da na san Aliyu ya damu, to ni ma zuciyata ba kwance take ba,
saboda tsananin son da nake wa Aliyu sai karuwa yakeyi.
Lokacin da na ji muryarsa sai na ji kamar in
rufe ido in jini makale da shi, amma dole ta sa na dake gudun gaba. Yadda na ji muryarsa na san lalle yadda ban yi barcin kirki ba, shima bai yi shi sosai ba.
Na ci gaba da tunanin idan Aliyu ya yi fushi ya
rabu dani har abada ya ya zan yi ke nan? Kai ai ko naga so mai dimbin yawa cikin idon Aliyu wanda yakeyi mini, kuma ma ai Mama Inki tace, zafin son da yake yi mini ne ya kawo wannan fadan da ya yi mini, to in haka ne ai ko ba zaiqi zuwa inda nake ba.
Sai dai kuma duk son da nake masa tun da nike da gaskiya ba zan taba wulakanta kaina in neme shiba, idan na yi masa haka ina ganin na ba da kai bori ya hau ke nan, zan daure har sai ya zo inda nake ya gane kuskurensa, kamar yadda ya zo inda nake ya bata mini
rai.A wannan dare na yi tunani iri-iri sa’ar da na kwanta bisa gado, da misalin sha biyun dare na kasa barci, babu abin da nake so in gani sai fuskar Aliyu ya rinka yi mini wasannin da ya saba kamar in na yi
magana ya kwaikwaye ni, ko kuma ya kara shagwabar dani yana kirana bebin Aliyu.
Kai a duniya kuwa akwai abin da ya fi so dadi?
Babu shi, lalle yanzu na gane abin da yawancin kawayena na makaranta suke ji, a lokacin na dauke su mahaukata, yanzu na gane abinda ke sa masu kuna a
zuciya, na yi zumbur na tashi na kunna kaset din Aliyu ina kalon sa, idan ya yi murmushi sai in ji kamar dani yake yi.
Hmmm LABARI fa nata Tafiya shin KOYA ZATACI GABA da KAYAWA KUDAI KUCI GABA da kasancewa damu A koda Yaushe