ALLURA CIKIN RUWA BOOK 1 CHAPTER 34 BY BILKISU S. AHMAD FUNTUA

ALLURA CIKIN RUWA BOOK 1 CHAPTER 34 BY BILKISU S. AHMAD FUNTUA

 

Mun tsaya

Ya yi dariya ya ce,Koke kika rada mini sunan nan kin ci a yaba miki don tsananin iya kiran sunan, kada ki so ki ji irin dadin da ke kama ni cikin raina idan kika kira sunana. Wai da kika ce in je cikin iyalina, ai ke ma rabin iyalina ce, saboda haka ba aibu don na kashe lokaci

 

mai tsawo da amarya ta Da irin wadannan surutan muka yi sallama, muka rabu a kan gobe Asabar za shi Katsina, idan ya dawo da

wuri zan gan shi, idan bai dawo ba in sanya ido Lahadi.

Ranar asabar da misalin karfe goma na dare muna zaune a dakin Yaya Abubakar ni da Aliyu, ya dube ni da kyau ya ce,Asiya jikin ne ko garin na

ga duk kin canza mini, ko don na rabu da ganin ki?” Na Ce,Wallahi Aliyu babu wanda babu, daga

garin har jikin ya yi zafi”. Ya ce,Kamar ya ya fa?”

Na ce,Na farko mun sha wuyar karatu, na biyu har yanzu muna cikin karatun, sannan muna cike

da zullumin yadda sakamako zai kaya, sai kuma

azumin da nake yi jiya da yau”Ya yi dariya ya ce,

“Azumi ai na jin dadi ne,tunda wani tanadi ne kike yi wa kanki ranar gobe kiyama. Maganar sakamakon jarrabawa wannan ya daina damun ki, insha Allah kin haye kin gama, ai ance alamun Karfi yana ga mai kiba” Ya ci gaba da fadin, “Shin Asiya ba ki tambaye ni dalilin rashin zuwa na wancan satin ba Na ce,Bari na yi sai in na ji ba ka gaya mini ba kana in tambaya, ka san saurin tambaya wani lokacin ba shi da amfani”

Ya ce,Eh, haka ne, saboda hankalinki nake

Kara son ki Asiya. Abin daya hana ni zuwa na je Lagos ne sai jiya na dawo, kuma neman da aka yi mini a Lagos alheri ya tabbata a kiran

Na yi war da idona na dube shi, duba irin na

neman bayani cikin gaggawa. Ya Ce,

“Asiya sun tura ni Amerika zan yi kwas na wata shida ko tara”Na yi zugum, sannan na ja dogon lumfashi na dago ido na dube shi na ce,

“Allah ya sa alheri, Allah ya kai ka lafiya ya dawo da kai lafiya” Na yi yar dariyar yake da hakora, na sunkuyar da kaina kasa. Sai shi ma ya yi shiru yana juyayin wani abu a ransa.

Ya dade idonsa a Qasa, mun sami kimanin

kusan minti hudu ba tare da wani ya ce uffan ba, sai can Aliyu ya kira sunana a hankali cikin yar damuwa,na dan jima sannan na ce,Na’am”

. Ba tare da na daga kaina ba.Ya ce,

«Na san dalilin da ya sa na ga ba ki yi

farin cikin wannan tafiya tawa ba, saboda za mu dade ba mu sadu da juna ba, ki yi hakuri nimana yi tunanin haka din, na kuma so a ce kin gama karatun ki mun yi aure wannan tafiya ta samu, to amma Allah ba haka ya shirya mana ba “.

Na yi shiru saboda ni wannan ba shine dalilin

damuwa ta ba kadai, amma sai na ci gaba

da sauraronsa ko Allah ya sa in ji ya yi maganar abin da yafi ci mini tuwo a kwarya. Maimakon in ji abin da nake so, a’a, sai ma ya bullo da cewa,

“Asiya gobe idan zan koma sai mu tafi

tare da ke da Hadiza ko?”Na yi masa wani irin kallo nace A bisa wane dalilin kuma? Mu da za mu koma makaranta ranar Lahadi yau sauran kwana shida” Yayi murmushi ya ce,A bisa dalilina, don muyi sallama saboda ni ranar Laraba zan tafi”

Na Ce,Idan mun yi a nan ma ta isa ba dole ba

ne sai mun je Kaduna Ya yi yar dariya ya ce,

“Asiya ko dai wani ya fara yi mini barna ne ban sani ba? Amma yadda kike gaya mini magana da walakin goro cikin miya” Sai ya taso tsam daga inda yake zaune, ya zo ya zauna bisa hannun kujerar da nake zaune, sai na dora

kaina bisa ciyata ina mai kallon Kafafuna ina cike da bakin cikin rashin gane abin da ke damuna, na cewa Aliyu ya ki ya gane abin da nake nufi, wai ni ya ya zanyi da raina. Ga dai mutane masu sona na neman su matsa mini, ga iyayena sun zura mini ido kullum suka ga Aliyu ya z0 so suke yi su ji magana mai karfi, shi kuma Aliyu ya ki ya ba ni haske a kan maganar aurenmu, sai ma wani Karin bacin rai wai zai yi tafiya mai tsawo ba tare da an zartar da komi ba.

Dubi Alhaji Ibrahim a shire yake in ba shi Karfin gwiwa in ji dadin tunkaho da shi kamar yadda Hadiza ke yi da Mukhtar.Sai zuwa can ya dora hannunsa bisa bayana, nan take na ji tsigar jikina ta tashi, ya kira sunana na amsa da kyar.

Ya ce,Don Allah ki yi hakuri mu je Kadunan

nan tare da ku, don Allah, na san kina cikin damuwa a kan wannan tafiyar tawa, amma wallahi Asiya na fi ki damuwa, saboda ku mata rauni gare ku, ina iya tafiya cikin dan kankani lokaci wani ya zo ya hure miki kunne, in dawo in same ki gidan wani, ni kuwa babu yadda za ayi in yi miki haka” Na ce,Eh, haka za ka dauka kai ma ai ina iya zama in jiranka, amma idan ka ga dama ka yi auren ka a can ba za ka Kara tunawa da wata can Asiya ba, idan hakan ya dame ka ai kana iya zartar da komi kafin ka tafi

Ya yi shiru wanda na tabbatar da ya san abin da

nake nufi da fadar haka, amma maimakon ya bani amsa a bayyane sai ma ya yarfar da maganar yace,Ke idan da kin san abin da ke damuna game da ke wallah da sai na zama abin tausayi a gare ki, amma babu komi lokaci na zuwa wanda insha Allah komi zai Wanzu” Haka ya rinka yi mini zantuka masu dadì, sai dai ni a gaskiya haushi nake ji nasa saboda yaqi fitowa sarari ya yi wa mahaifina magana, sai dai ni yake nuna wa tsabar so. Na yi masa hannunka mai

sanda ya ki ya fayyace mini komi, ga shi yana matsa mini a kan mu je Kaduna ni kuma ban ga amfanin zuwa na ba, ban da in Kara bacin rai.

– Ina kuma so in gaya masa maganar Ibrahim,

ganin muna wannan rigimar na san lalle in na sanar dashi abin da zai kawo wa ransa daban, saboda haka sai na ja bakina’ na tsuke.

Ya ce,To ya ya maganar tafiya?”Na ce,duk yaddah muka yanke Sai goben idan ka z0 ka ji shawaran da A nan fa ya fara yi mini wasu wasanni yana kokarin ya sumbaci hannuna, na ce,Ni kuwa Aliyu ba ni son irin wadannan abubuwa Ya ce, “Kai lalle ban yarda ba, akwai abin dake faruwa wanda kike Boye mini. Don Allah ki gaya mini na san ba kan maganar tafiya ba

ne kawai wannan tunzuri Ai kai ma namiji ne, ka yi kokarin ka gane mana Sai ya ce,Na san ba wani abu, wani ne dai keson ya raba ni da ke, kuma ko wane me ya yi kadan,kuma ki sanar da Hadiza a kan maganar tafiyar gobe da karfe sha biyu insha Allah za mu tafi, in kuma ba ki zuwa na san matsayina yanzu Na ce, “Ni ban san yadda zan cewa Baba ba”

Hmmm LABARI fa nata Tafiya shin KOYA ZATACI GABA da KAYAWA KUDAI KUCI GABA da kasancewa damu A koda Yaushe

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *