Da na lura na gane wannan ita ce siyasa, yana fushi dani amma yana kokarin nuna wa abokansa ai komi lafiya lau, sai na dake nima na nuna masa na iya siyasar.
Na rinka sunkuyar da kaina kAsa ina murmushi ina dan duban gefensa ina mai muna alamu wata magana yake mani wadda na ji dadinta tare da jin kunya. Domin su Lawal da matarsa na zaune a karkashin wata dalbejiya, a haka muka isa inda suke. Nan take suka mike tsaye suka tarbe mu.
Matar Lawal ta ce, “Aliyu masu sarauniya, an, rike mata hannu ga jaka an rike mata, wannan idan an barka a wuya za ka sagalata”
Aka fashe da dariya. Shi kuma Lawal ya ce,
“Na sara maka mutumina, ban ga laifinka ba, domin ka iya zabe dole ne ka rude a kan Asiya, shi ne dalilin da yasa na ce ni dai a kawo mani ke in ganki.
To nima na yaba
Aliyu ya ce, “Don Allah ku daina fasa mata kai tana mani yanga, yanzu ma sai da ta yi mani yanga muka taho”Na dube shi na yi murmushi tare da rausaya da ido, sannan na ce masu, “Don Allah kada ka biye ma Aliya, ina bacci ya ta dani”
Muka zauna muka fara gaisawa tare da bayyana kai, sannan uwargida Laura ta yafito wani
Lawal na son Aliyu Kwarai dole ransa ya baci, kamar ni da Zahra’u ne, a ce bai kula da ita ba na san lalle raina zai baci. Na tuna yadda ya bani ta rihin rayuwarsu, sun hadu a Kwalejin Barewa ta Zariya ne, abota ta Kullu tsakaninsu har suka gama babu wanda ya taba jin kansu, ya zamanto kowanne da sha’awarsa a zuciyarsa, inda shi Aliyu ya dauki fannin tukin jirgin sama, shi kuma Lawal ya nufi soja. Duk dai da haka kaunar nan sai ma abin da ya ci gaba. To shi Lawal tun yana soja ya fara neman auren Lauratu.
Ni ina ta tunanin zuci yayin da Aliyu ya lankwashe cikin kujerar yana ta aikin kallona yana lumnshe ido, har dai Lawal ya gaji ya ce, “Ashe dai Aliyu ba karamin daga maka hankali Asiya tayi ba, haka kake matsa mata da kallo sai ka ce a yau ka fara ganin ta. Haba Aliyu baka da hakuri ko kadan” Ni dai na sunkuyar da kai kasa na yi murmushi. Ita kuma Lauratu tace,
“To kai ma Lawal kana damun Aliyu ka hana shi sakat”. Ta kamo hannuna ta ce, “Zo muje ciki mu yi hirarmu”
Bayan sallar magariba muka isa bisa tebur
din cin abinci, Lawal ya ce,Asiya ya ya ba kya cin
abin kirki? Ki fa saba tun yanzu da nan da gidan
Aliyu duk daya ne”
Aliyu ya ce, “Ba wani abu ba ne illa shagwada ce, ta riga ta saba in dai muna tare sai na ba ta a baki, to yau ta yi mani laifi ta ga bani da niyyar ba ta, shine la kasa ci”Na harare shi na ce, “Aliyu da neman magana
kake”.
Lawal ya yi murmushi ya ce, “Asiya ba ki da dama ashe ke kike tsokanarsa
Muna zaune ana Kara hira Aliyu ya yi mani wani irin kallo, ni kuma na duba agogona sannan na dube shi ina nuna masa alamar dare ya yi, sai ma ya dauke kansa, ni kuma na ci gaba da tsare shi da kallo, har Lawal ya ce, “Aliyu fuskar Asiya Da magana da kai fa
Aliyu yace, “Rabu da ita Lawal tana nuna wai dare ya yi ai ina kallonta kyaleta nayi
Sai na gyara zama na ce, “Wallahi Lawal na ga dare ya fara, kuma ka san gobe za mu gida shi ne nake son shiga gidan ‘yan’uwa sallama”
Lawal ya ce, “Aliyu Asiya na da gaskiya, ka san halin jama’armu idan ta shiga wani gidan ba ta shiga wani ba Karshe ka ji abin ya zama tsegumi”
Sai na ce, “Idan ma zan matsa masa bai gama hira ba, kana iya sanya direbanka Lawal ya mai dani
Lawal ya duba Aliyu ya ce, “To ka ji Aliyu ko hakan za ayi? Aliyu ya yi shiru, sannan ya cc. “A ‘a, bari in
mai da ita Lauratu ta bani kayan shafe-shafe da hotunansu da na dansu Aliyu, shi kuma Lawal ya bani naira dari biyar ya ce sai na ga tsarabar Indiya in Allah ya maido su lafiya.
Na yi godiya mai tarin yawa, sannan muka tafi. Mun yi nisa da tafiya babu wanda ya yi magana, sai na daure na ce “Aliyu abotarku da Lawal ta dace, domin na ga harta zama zumunci”
Bai tayar da kai ya dube ni ba, kuma ko sakin fuska, sai ya amsa da cewa, “Ko!” Ransa ya baci. Na ce a zuciyata, har yanzu fushin yana nan ke nan? Shi ke nan mu zuba ni da shi.
Sai da muka zo wani babban shagon sayar da littattafai sannan ya rage gudun motarsa, ya ce,
“Yaya mu tsaya za ki sayi littattafan da kika ce za ki saya?”
Na ce, “A ‘a, ba zan saya ba”
Ya ce, “To gobe fa ba zamu tsaya ba, gara ki saya yanzu’
Na ce, “Na fasa idan na je Zariya na saya”.
Ya yi shiru, sannan ya ja mota ya doshi wani lungu ya yi fakin din motar ya kashe wuta.
Na ce, “Lafiya?”
Sai ya ce, “A’a, ina son sanin dalilin fushin saboda ni da kika batawa rai ban yi fushi ba sai ke ce da shi”
Na ce, “Dalili sai ka tambayi kanka tunda kai ka fara fushi ba dole in taba ka ba
Ya gyara zama ya sagala hannu daya bisa sitiyari, yayin da ya saka daya hannun ya rungumo bayan kujerar da yake zaune yana mai fuskantata, ni kuma na sunkuyar da kai kasa na yi tagumi.
Ya ce, “Kinga da farko da nayi miki maganer zuwa gidan Lawal bai dace ki kawo mani maganar Zabra’u ba, idan kece kika neman mu je gidan wata kawarki na nuna rashio sha’awata na san lalle ranki zai baci, tunda bani da dalili mai karfi, wannan ke nan. Sai na biyu
Hmmm