ALLURA CIKIN RUWA BOOK 2  CHAPTER 25 BY BILKISU S. AHMAD FUNTUA

Na ce, “Matar wai ita Doctor Mairo wadda tace a halin yanzu tana aiki ne a Kano. ko Baba Suraj ya taba baki labarinta?”

Jamila ta ce, “Ke ko ina kika san ta?**

Na yi mata bayanin abin da na sani, sai ta ce,

“Suraj bai bani labarinta ba, amma shi Aliyu yana gaya mini yadda ta zame masa Karfen kafa’

Nan da nan zuciyata ta fara bugawa a kai a kai da kuma sauri da sauri, sai na yi tagumi na dubi Zahra’u na Kara neman bayani wajen Jamila

Doctor Mairo, ‘yar wani babban soja ce aminin mahaifin Aliyu na Kut da Kut, tun tana

“jami ‘a take masifar son Aliyu amma shi ta yi rashin.! sa’a bai amince mata ba. Ana cikin haka ran nan sai.

Allah ya hada ku da shi, yanzu kusan shékara shida ke nan tana aiki ta ki aure ita sai dai Aliyu, shi kuma”ya yi rantsuwa ba zai aure ta ba.

A da nan Kaduna take aiki a asibitin Dutse, komawarsa Kano ita ma ta nemi canji zuwa asibitin

Murtala” Bayan Jamila ta yi shiru’ sai na dubi ‘agogon hannuna nace Bari mu tafi Zariya za mu koma yanzu, don Allah kada ki gaya ma ‘Baba Suraj cewa mun zo, kuma ki yi mini alkawari ba za ki gayawa”

Aliyu mun yi zancen Doctor Mairo da ke ba”Ta ce, “Asiya mene ne idan na gaya masa, kuma.ma ai ya 

Ya daga mata hannu na nuna alamar dakatar

-da ita daga magana, na ce, “A’a, Jamila shi ya kamata ya sanar dani, amma tunda ya ga bai son in sani, to a bar ta a hakan”.

Mun iso makaranta da misalin shida na maraice, muka ci abinci sannan muka yi wanka tare da ba da farali, sai na saka rigar baccina. Zahra’u ta dube ni tace”Asiya na yi zaton karatu za mu yi’*

Na ce,Gaskiya Zahra’u kije ki yi karatunkI,

amma ni yau yadda zuciya ta yi mini kunci bana jin kona yi karatu zan fahimci abin da na karanta”.

Zahra’u ta zauna daf dani ta kamo hannuna ta rike tana dubana, ta ce, “Asiya har sau nawa zan . gaya miki ne, ni kam bana bai wa Aliyu laifi kamar yadda kike ba shi, Mairo na son sa, shi kuma bai son ta, to mene ne?”

Na dubi Zahra’u na ce, “Ke kuma kin yadda da hakan, idan haka ne to mene ne na boye mani? Ni gaskiya Zahra’u na fara saka shakka a kan sha’ anin aurenmu da Aliyu, dan an ce bai son Mairo to ni da yake son wane mataki ya dauka na son ya kai ni gidansa. Idan an buga an raya ai duk jirgi daya ya dauko muni da ita”. Haka dai Zahra,u ta rika kawo mani misalai daban-daban har daga bisani na hakura, na ci gabada harkar karatuna. Shi kuma Aliyu ban nuna masa komi ba.Ranar wata alhamis na tashi bani da darasi, sai na rika jin raina babu: dadi ko kadan a inda na raya ma raina ko ma gida za nine? Sai kawai na fara shirya kayana zani Malumfashi, na rubuta ma Zahra’ u wasika ma aje mata a daki kamar haka

Zahra u

Na san za ki yi mamakin wangan tafiyar tawa, gaskiya bana jin dadin zuciyata saboda haka zan je dubo lafiyar gida, abin da yasa ban tsaya jiranki ba, saboda nasan yau darussanku za su dauke ku har zuwa bayan azuhur, kuma gobe da jibi kuna da gwadawa. In Allah ya yarda zan  dawo ranar asabar ko lahadi, sai na dawo, Allah ya bamu sa’a.

Taki har abada Asiya Yusuf

Ina isa gida Malumfashi sai na samu Yusuf shi kadai a gida, na tambaye shi su Inna fa? Ya ce,

“Ai duk suna Kuka-Sheka”. Na ce, “Lafiya dai ko?” Ya Bh, sai dai jiya ne Allah ya yi ma Malam Audu mahaifin su Inna rasuwa”Na ce, “Innalillahi wa’inna ilaihir rahi’un!

Bana Malam Audu an cimma shekara, Allah ya rahama masa, Allah ya gafarta masa, amin

Sai muka ci gaba da juyayin mutuwar da kuma tuna tsawon lokacin da ya dauka a kwance yana faman jinya, na yi sallar azuhur na ci abinci, sannan Yusuf ya raka ni na nemi motar zuwa Kuka-Sheka.

Na sami mutane jingim a kofar gida, cikin su har da Babana da mijin Mama Inki, na durkusa na yi musu gaisuwa, na shige cikin gida. Na sami iyaye da

‘yan’uwa da abokan arziki cike da gida, na bi kowa daki-daki ina yi masu ta’aziyya, sannan na koma kusa da kakata na zauna.

Ta Kara gaya mini yadda al’amura suka rika aukuwa da lokacin mutuwarsa tazo Na tausaya masa na kuma tausaya ma kaina, saboda. dai duk mai rai mamaci ne, mutum kuma bai san lokacin da za ta cin masa ba.

Inna Hafsatu tazo ta zauna kusa dani tace

“Asiya wa ya gaya miki rasuwar Baba?” Nace

“Wallahi Inna haka nan zuciyata ta rika raya mini da inzo gida, to ashe abin da zan tarar ke nan. Allah yayi rahama masa Sukace, “Amin”. Inna Hafsatu ta dama mani fura ta hado tare da tuwon shinkafa ta kawo mani 

Ban sami yin magana da Innata ba sai da ta shiga dakin kishiyar tsohuwarta domin yin sallar la ‘asar, nima na yi alwala sai da muka idar da sallah muka yi addu a ga marigayi kakana, sannan na sake gaida ita nayi mata gaisuwar mahaifinta. 

A gaskiya banyi baccin kirki ba saboda yawan jama’a. Da misalin Karfe hudu na sulusin dare, a lokacin sayin asuba ya sauka bacci mai karfi ya dauke ni, har na shiga mafarki barkatai wanda ya sanya Inna Hafsatu tata dani.• Ta ce, “Ina kuka a cikin bacci ina fadin bana so bana so”

Na ce, “Eh, wani mutum ne ya dame ni na ce masa bana sonsa amma ya makale mani

Sai ta ce, “Babu komi alheri ne, in yi sadakar

Kosai da safe Da azuhur ne Yusuf ya rinka shigowa da buhun shinkafa da garewanin mai, ya durkusa gaban kakanmu yana yi mata bayani daga Alhaji Ibrahim kuma tare suka zo yana kofar gida.

Bayan an kintsa an shimfida masu tabarmi aka ce Yusuf ha shiga dasu cikin gida. Su uku ne shi

Hmmmm