da abokansa, bayan an gama gaisawa sai kakata tace, “Ina angon nawa?”
Abokan suka nuna shi, bayan sun dan jima suka tashi suka tafi. Da aka yi ‘sallar magariba mahaifina ya shigo yiwa su Inna sallama, sai na ce,
‘Zan bi shi”. Saboda direban su Mama Inki zai mai da shi. Na yi sallama na ce ran lahadi zan dawo.
ranar Asabar mahaifina ina ya koma
Kuka. Sheka, ni kuma ban yi wanka ba sai azuhur, saboda ramuwar baccin da ke kaina. Bayan nayi sallar la’ asar na dora abincin dare wato birabiskon alkama domin yana daya daga cikin abincin da babana yafiso, na yi shimfidar tabarma a gaban dakina, na fiddo littafi ina tilawa saboda ranar talata muna da gwadawa.
Can sai ga Larai yar makwabtanmu wadda kan shigo wajen Inna tana aiken ta, saboda rashin Zainab. Na ce, “Yauwa Larai zoki sawo mani karan rake” tace,
“To’. Sai ta ci gaba da cewa tana murmushi, “Yaya Asiya ina zaki na, ga kin yi gayu?”
Na ce, “Ke Larai wannan shine gayu?” Ta ce, “Kin ga yadda kika yiwa gashinki ado kuwa sai ka ce Baturiya, kuma dinkin atamfar ya yi kyau da ke
Na ce, “Uhm! Larai kuruciya na dibar ki, idan kin je makarantarmu ta Zariya ashe sai ki lalace wajen kallon yadda ake kwalliyar gashi’ Na mika mata kudin rake nace, “Maza ki sawo mani”
Bayan ta dawo na gutsura mata yanka, sai na ce, “Ashe raken arha ya ke yi?” Tace, “Don dai na ce masa ke ce kika aiko ni shi ne dalilin da ya baki da yawa”.
Na ce, “Ai ko na gode, shin Larai ina za ki yau?”
Ta ce,Ba ni zuwa ko ina, aike na za ki
*Na ce, “A’a, alayyahu za ki yanka mini ga shi
can a kicin”. Na ci gaba da shan rakena.
Kusan in ce na yarda da aka ce mani mai shan karan rake hankalinsa kadan ne, domin ana tsaye bakin Kofa ana sallama, amma Allah bai ishe ni ba har Larai daga kicin ta fito ta zo ta tada ni, sannan ne na daga kaina a hankali na dubi kofa, na aje rakena na mike na nufi wajen wannan bako, ‘mai kyan gaske, sai wani annuri ke fita a fuskarsa, ga kwarjini na musamman wanda ba duk maza ne da shi ba, kwakwalwata ta nemi rikitar dani a kan ina ne na san wannan mutumin?
Duk yadda aka yi wannan wushiryar tasa ta sha gilmawa ta gaban idona, amma kuma a ina ne?
Har na isa inda yake tsaye ban gano inda na san shi ba, sai shine ya daure ya ce, “Shin wai ko Asiya ce ne?”Na ce, “Eh, ita tace Ya ce, “Su Inna basu nan ne?” Na amsa, “Eh”Ya dai tabbatar ban gane shi ba, sai yace, Asiya nine Yayanku Aminu”
Haba ban san lokacin da na kama shi
Kamkam ba, na ce, “Wallahi Yaya Aminu ban gane kaba’. Ina tsalle da murna gaba daya.
Ya ce, “Ai na lura, ko da yake nima ba domin dan fetalinki ba sai ki wuce in ban iya gane ki ba”
Na fiddo kujerar karfe daga dakin Babana na sanya masa a tsakar gida ya zauna, ina ta rawar jiki da shi na kawo masa ruwan sha da lemu, na zauna yana tambaya ta labarin gida ina gaya masa, har da mutuwar da ta kai su Inna Kuka-Sheka.Na ce,
, “Ga shi babu abinci, amma na dare ya
kusan sauka Ya ce, “Bani tare da yunwa na ci abinci a Kano, sai dai rakenki za ki sammani”.
Na ji kunya, na ce, “Ko a sawo maka wani?’
Ya ce, Wannan dai nake so”. Yana
murmushi na mika masa. Ya ce, “Asiya na ji dadin ganin yadda su Baba suka barku kuke makaranta”
Na ce, “Ai ka san halin Baba da son ilimi, amma gaskiya Yaya idan a bisa hanya muka hadu da an yi abin kunya, domin ba zan gane ka ba” Ya ce, “Saboda me?” Na ce, “Ka yi kiba, ka kara tsawo, ga haskenka ya fi na da”Ya yi murmushi ya ce, “Kin san kasashen
Turai ba kamar namu ba, kema ina ganin fetalinki kawai yasa na gane ki, amma hatta sautin muryarki ta canza mani, ke wadda na bari tana daura zani hagu a dama yau ga shi kin iya gyara irin na mutanen zamani”
Muka kyalkyale da dariya. A daidai wannan lokacin mahaifina ya shigo, ya tsaya yana kallona yana kallon Yaya Aminu, sai na ce, “Baba Yaya Aminu ne fa”
Ya bude baki yana mamaki tare da salati, yayin da Yaya Aminu ya mike ya nufi Baba yana mai cike da fara’a, suka zauna ana gaisawa, ni kuma na yi amfani da wannan damar na shiga daki na daura dankwali na nufi kicin na samu na kubce ma irin kallon da Yaya Aminu ke mani.
Baba ya bai wa Yusuf kudi ya sayo kaji nan da nan ya gyara su, ni kuma na yi ma Yaya Aminu
farfesu.Karfe takwas na dare na yi masu shimfidar tabarmi a tsakar gida, shi kuma Yusuf ya gyara masa dakin Yaya Abubakar domin gyaran nasa dakin sai a hankali.
Hmmm