Ina zaune gefe guda muna hira da Yaya Aminu, amma irin kallon da yake mani yana damuna, sai ya rika tambaya ta karatuna dana Hadiza.
•Na ce, “Hadiza ta kammala karatun aikin
Jinya, yanzu ta fara na angozoma, inda za ta fito da mukami biyu ke nan’.
Shi kuma ya ce mani, “Ya karanto fannin likita ne wato medical doctor, sai dai na fi bayar da karfi a fannin mata da yara da sauran manyan cututtuka”
Na yi ajiyar zuciya na ce, “Lalle Yaya dole ka dade, ashe ba dan karamin karatu ka yi ba, da a nan Najeriya ne sai ka saba abin da ya fi shekaru goma baya”
Ya ce, “Ai don haka na ki zuwa hutu na bari in taho gaba daya”. Muna cikin hirarmu mai dadi sai ga Lari ta katse mu, ta ce, “Wai in zo in ji Ibrahim”: Na amsa da kyar na dauko gyalena zan fita, sai Yaya Aminu yana dariya ya ce, “Asiya ba ki shafa hoda da jan baki ba, ko wannan saurayin ba a yi da shine?”
Na ja gyale na rufe fuska na nuna alamun jin kunya a kan abin da ya fada, amma sai ya ci gaba da tsokana ta har na ce, “Ai ba saurayi na bane, muna dai gaisawar mutunci ne”. Na juya na nufi zaure sai na ci karo da mahaifina, na rabe jikin bango sai da ya wuce sannan na fice.
Ibrahim ya yi mani gaisuwar’ mutuwar kakana, sannan muka fara hira. Sai ya ce, “To Asiya iyakar tika-tika-tik, yau na ji an ce Yayanmu na Rasha ya sauka, yanzu sai mu Kara matse dantse wajen rokon Allah”
Na yi ajiyar zuciya na ce, “Har ka ji zuwansa?”
Ya ce, “To ba ga shi na gaya miki ba, yanzu ma zuwa na yi in gai da shi ko zan sami ganinsa?” Na ce, “Me zai hana, ai shi Yaya Aminu mutum ne mai saukin kai”. Ya ce, “Yaushe za ki koma Zariya?”Na ce,
“Gobe za mu tafi tare da Yaya Aminu,
amma sai na raka shi Kuka-Sheka”. Ibrahim ya yi murmushi yace, “Yar gatan yayan ba’
Na ce, “Ibrahim baka gajiya da tsokana, mene na na gatanci?” Sai na hangi Yaya Aminu a zaure zai shiga dakin Yaya Abubakar, da alama kila shirin bacci yake yi, sai na nemi Ibrahim da mu karasa zauren don su gaisa.Na koma gefe guda na barsu suna hira irin ta tsakanin maza. Bayan sun gama na raka Ibrahim har gindin motarsa. Na zo zan shiga gida na ji motsin Yaya
Aminu a cikin dakin Abubakar, na leka don in masa sai da safe in kuma ji ko yana son wani abu, sai ya ce, “Ba kya shigowa ko bacci kike ji ne?”
Na ce, “Eh, da baccin ma, amma ina son yin bitar wani littafi ne ka san aski in ya zo gaban goshi ya fi zafi, kuma kai ma ya dace ka huta saboda surutun da ka sha yau wajen jama’a ‘yan sannu da zuwa”
Ya ce, “Ai lalle kam, saboda dazun har kaina ya rika sarawa, na ko san surutu ne da jama’a”.
Na ce, “To shi ke nan sai da safe Yaya ko akwai abin da zan kawo maka?”
Ya ce, “Yana bukatar shayi kofi daya”.
Na hado shayi na kawo masa, ya dube ni ya ce, “Na gode”Na yi murmushi na ce, “Babu komi
yi ma kai ne”Sai ya dan yo mani wani murmushi na musamman, ya ce, “In zauna”. Sai na zauna bakin hannun kujera, ya bude ‘yar Karamar jaka ya fiddo mani hotunansa ina kallo, yawanci shi da abokansa ne, sai wani wanda suka fi dauka da wani jar fata, ya ce mani abokinsa ne na Kut da kut sumansa El-Bashir, mutum ne mai arzikin gaske, in na ce maki kudi ina nufin irin mahaukatan kudin nan, yana da kamfanonin magunguna da asibitoci, karatu iri daya muka yi da El-Bashir, saboda haka a kamfanin Babansa na rika aiki tamfirari idan mun sami hutun makaranta.
Bayan na gama makaranta sai da mahaifin El-Bashir ya matsa mani da in masa aiki a wani sabon asibiti da ya bude, na tsaya na fara aiki, haka kawai wannan shekarar sai na ji babu inda nake so sai gida Nijeriya, na ta da hankalina ainun, sanan ya barni na taho.
Sai na ce, “Ai gara da ka dawo ka ga yanzu hankalin Inna Hafsatu ya kwanta, kuma dama rashin dawowarka ya takurawa su Hadiza da Mukhtar
•Sai na nuna masa hoton wata Baturiya da ke rungume bisa kirjinsa, na ce, “Yaya Aminu wannan
‘yar makarantarku ce?”Sai ya dube ni tare da shigar da idanuwansa, sannan ya yi murmushi ya ” ce,
“Bayar makarantarmu ba ce yarinyata ce”
Na ce, “Ashe wata ran za mu yi bakuwar Baturiya”
Yace,Haba tuni muka manta da juna, da dai
na amince mata da na auro ta mun taho tare, to ba ni da ra’ayin auren jar fata, ba su burge ni, na fi son in dawo gida in yi aure irin yadda muka gada, a kuma bisa yadda addininmu ya shimfida mana” Na yi doguwar hamma, sai na tashi na kwashe kayan shayi na yi masa sallama sai da safe na shiga gida.
Ranar lahadi da safe bayan na gama bai wa kowva kalaci, mun shirya tsaf na zuba wata bakar. hijab mai adon kyalli a gaba, na rufe kaina da dan Karamin bakin gyale, da farin takalmi da farar jaka, ina tsaye a tsakar gida ina sallama da mahaifina, shi kuma Yaya Aminu na tsaye yana daura agogon hannunsa.
Ashe duk tsawon lokacin da muke magana da
Babana Yaya Aminu babu abin da yake yi sai aikin kallona. Zuwa can na waiga na dube shi, sai ya yi firgigit ya kawar da fuskarsa gefe guda.
Muka shiga motar da Yaya Aminu ya zo da ita ta wani abokinsa, muna tafe muna labari ina ba shi labarin bayan rabuwa, shi kuma yana tukin mota, wani zubi ya dan waigo ya dube ni mu yi murmushi har muka iso Kuka-Sheka. Ya tsaya kofar gida yana yiwa jama’a gaisuwa, yayin ne na fada cikin gida da gudu, wanda har ya sa mutanen cikin gida suka yi min ca da ido.
A nan ne na firgita Mama Inki, ita kuwa Inna Aisha na gindin rijiya tana gyaran kayan miya, ta saki wuta tana kallo na. Inna Hafsatu kuma na zaune kusa da kakata tana shafa mai, sai na fada bisa
Hmmm