ALLURA CIKIN RUWA BOOK 2 CHAPTER 35 BY BILKISU S. AHMAD FUNTUA

Haka muka yi ta yi su fada in fada. Dak kokarinsu basu shawo kaina ba, ni dai na dage bazan taba auren Aliyu ba sai da yardar mahaifisa Zahra’u ta ce,

“In hakura ya tura kakanninsa na wajen uwa”.

•. Na ce, “Na hakura sai na yi tunani”. Dole dai aka kyale ni. Bayan mun ci abinci muka tashi tafiya, aka ce

Aliyu ne zai mai damu, a nan na toge ni ba zan shiga motarsa ba. Da kyar dai na shiga baya muka tafi.

Ina ganin lalle wata na shiga cikin damuwa, amma da na dubi Aliyu sai na ga ni kamar ma babu abin da ke damuna. Da muka isa makaranta ya sauke mu ya nemi in tsaya na nuna masa ba fuska, sai ya biyo mu yana kokarin kama mani hannu na tsaya.

Na dube shi na rike kugu na ce, “Kada ka Kara neman taba ni, ko ka ce za ka kama mani hannu. Wallahi! Wallahi!! Ba ni ba kai har abada” Ya yi sakake yana kallona, sai kwalla ta cika masa ido. Ya yi karfin hali ya mai dasu, ya mika mini bandir din kudi, na dube shi a sakarce na ce,Don Allah ka daina bani abin hannunka kada mu tashi biya bill ya yi mana yawa, ka san abin matsiyata Aliyu yasa hannu ya dafe kansa, da alama ya rasa hanyar bi, wato dabara ta fara Karewa a gare shi. Ita kanta Zahra°u abin da nake yi ya fara damunta,

sai kawai ta sa hannu ta amshi kudin hannun Aliyu, idonta cike da kwalla ta kasa ma Aliyu sallama.

Muka kwanta ruf da ciki bisa gadonmu kowacce na ta rasgas kuka kamar ranmu zai fita. Can Zahra’u ta ce, “Yanzu Asiya ki tuna fa Aliyu tafiyar dare zai yi in ya yi hatsari alhaki bisa wa?”

Na ce, “Bisa kan mahaifinsa Zahra’u, ni yanzu so nake Kawun Anti Wasila ya dawo in sanya ya yi mani rokon Allah ya fidda Aliyu a raina”.

Amma Zahra’u ki sani fa duk wulakancin da akà yi mana sai ma yanzu wani sabon so ke saukar mani a zuciya, kuma kina ganin kamar ina ma Aliyu cin fuska ya zama dole, tun da su abin da “yan ‘uwansa suka dauka, nice na manne wa Aliyu”. Sai na Kara fashewa da kuka.

Harkokin makaranta sunata tafiya, yanzu shirin tafiya gida muke yi, inda ita Zahra°u tana cike da dokin za ta London wajen mijinta, tana kuma cike da bacin rai saboda ba ta san yadda rigimarmu za ta kasance ba.

Muna sauran kwana uku rak mu je hutu gida, ina kwance ni kadai a daki, ita kuma Zahra°u ta je saloon domin a gyara mata kafa da kumba, gashi da. inda ya dace. Bayan na tashi na yi sallar la’asar, Zahra’u kuma ta dawo sai ta bude jaka ta miko mani wasika, na duba na ga ba rubutun da na sani bane, sai na aje na ci gaba da ‘yan gyare-gyarena.Can na tuna na dauko wasika na fara karantawa, haba ban san lokacin da na fara ashariyar zagi ba, na barke da kuka na ce, “Ni wallahi ban yarda ba, wannan ma kashe ni ake so ayi”

. Zahra’u ta kasa magana, sai ta amshi takardar tana karantawa ta ga abin da ya firgita ni. Daga ofishin Babban likita Steel Rolling, Katsina.

Hello Asiya

Yaya karatu ya Zahra’u ki ce ina gaishe ta.

Asiya na san wannan wasikar ta razana ki ainu..

Amma ki kwantar da hankalinki ki yi mata

‘yakkyawar fahinta, insha Allah babu abin da zai biyo sai alheri. A tun lokacin da na dawo gida Nijeriya na yi arba da ke, to wallahi tun a ranar soyayyarki take azalzalata a zuci, kullum ina Kokarin danne ta, amma tana Kara tsananta a gare ni, na bi duk hanyar da ya kamata in nuna miki da ido a cikin wani launin harshe, , amma na ga kinqi fahimta, ba kuma ganewa ne ba ki yi ba, illa kin riga kin sa son wani a zuciyarki. Asiya ki bani hadin kai saboda na san da wuya ki mika min wuya gaba daya, to duk matsalar da kike shirin saka ni, wallahi a shire nake in shiga a ciki Asiya ki daure ki amshi soyayyata wadda ita ce ta kafa iyayenmu har suka zama ‘yan uwa, to sai mu karasa masu ita, samar masu abin cikin kwan wanda ya fi Kwan dadi.

Na yi imani har ga Allah ban yi miki shisshigi ba, a bisa abin da ke tsakaninki da samarinki, illa ma ince a bari ya huce shi ke kawo rabon wani. Kuma ina ji a jikina akwai wani abu da Allah ya shirya mana a tsakanina da ke, ga misali yadda Allah ya Karfafa zumun ci mai Karfi a tsakanin mahaifanmu.

Kuma ina sanar miki da cewa, mi mutum ne mai zafin nama a bisa abin da zuciyata ke so, saboda haka kada ki yi mamaki in na ce miki ina gama rubuto miki wannan wasikar zan je gida in sanar musu, sannan in je Danja in tura magabatanmu zuwa wajen magabatanki na Katsina. Yanzu abin da ya rage sai kunzo hutu, idan na sami karbuwa zan zama daya daga cikin maza masu sa’a da farin ciki a duk abin da suka zuciyarsu. Idan ke ban sami masauki ba a zuciyarki, sai in yi shirin daukar borin da za ayi mini, wanda ba zai taba razana ni ba balle har in ja da baya, tun da zuciyata ta riga ta yi cinikin Kaunarki, saboda haka bazata taba ganin laifinki ba saima duk abinda kikayi ta kara dokanta a kanta.

Dr. Aminu Ibrahim

Bayan Zahra’u ta gama karanta wanna takarda, sai muka rankaya zuwa gidan Anti Wasila.

Ita ma da ganinmu ta san babu lafiya, nan da nan hankalinta ya tashi.

Ta ce, “Wohoho! Asiya idan kan maganar aure ne lalle ruwan idonki zai kare kanki, me kuma ya faru?”

Zahra’u na shardar hawaye ta mika mata wasikar Yaya Aminu, sai da ta gama karantawa ta nisa ta ce, “Wannan fa shine ana kukan targade ga karaya ta samu, lalle idan iyayenki suka san abin da ke gudana a gidan su Aliyu za su yi gaggawar bawa Aminu ke. Wannan ma ko shakka babu, kutashi muje Kusfa”.

Mun yi sa’a Malam ya dawo amma saboda yawan mutanen da ke son ganinsa ba mu sami ganinsa ba sai da muka kwashe awa uku. Anti Wasila ita ta zayyana masa lamarina tun farko, ya injina kansa ya ce, “Asiya share idonki daina kuka, sha’anin aure na Allah ne, ba a ja da ikon Allah,

Hmmm