ALLURA CIKIN RUWA BOOK 2 CHAPTER 4 BY BILKISU S. AHMAD FUNTUA

Mun isa Malumfashi gab da magariba, bayan

mun gaisa da Inna ba abin da na fara tambayarta sai ya ya Hadiza fa? Ta shaida mani ta tafi school of Nursing Katsina kwana biyu da suka wuce. Na yi dariya na ce, “Kai Hadiza na kwakwar aikin _jinya, ni ko ‘yar

hularsu ke burge ni?”‘ Inna ta ce,

“Ra’ayi ne dai kawai”• Bayan sallar isha’i Babanmu ya shigo yana gyaran saitin talabijin, na bi shi har falo muka gaisa, na nemi waje na zauna Inna ita ma ta shigo, amma sai ta zarce uwar daki.

Mun fara hira da mahaifina a kan fitowar admision dina, ya yi shiru sannan ya ce,To Uwani

yanzu ina zaki ke nan?”

Na amsa “Baba na fi son Zaria

Ya ce, “Inda Abubakar yake ke nan?” Na ce, “Eh Baba .

A daidai lokacin ne Inna ta fito da goro a hannunta tana ci, sai Baba ya ce, “Samman goron nan Aisha”. Ta koma daki da sauri ta dauko masa gwangwanin goron baki daya tana dubawa, har ta isa gabansa ta mika masa. Ta ce,

, “Ga shi duba ka gani, goron ne babu

fari sai dai daushe ne, irin wanda ka fi so”.

Ya amsa ya dauki daya ya mika mata gwangwanin, bayan ta sami waje ta zauna sai ta ce,

“Ni dai Malam ba don wanda ake so bai shirya ba, na fi sha’awar ta shiga jami’a da daurin auren ta, saboda yanzu ba ka ji yadda mutanen unguwar nan suka fara tsegumi a kan Uwani da Hadiza ba, wai muna nan muna ruwan ido sai amsar dukiyar jama’a sun ga wanda za mu bai wa wannan yara. To ni ka ji irin maganganun da suka fi damuna”

Mahaifina ya yi shiru ya daga kansa sama, sai

Zuwa can ya sauke kan nasa kasa ya nisa ya ce, “Kin ji irin abin da ke hada ni da ku mata tsegumi, ina amfanin sauraren wadannan maganganu, har yaushe za ki tsaya ana gaya maki ita Aisha?”

Sai Inna ta ce, “Amma Malam kai ma za ka shaide ni a kan rashin son shige-shige da rashin son sauran tsegumi, abin da hatta ‘Yar Zaina idan aka ganta sun dinga tambayarta ke nan, wai ina Uwani?

An ce masu mai kudi ke son ta ko? Haka dai za kai ta jin suruta barkatai.

Ban da ma a tare yaro bisa hanya ana lambaya, rannan sai ga Hajiya ta Babban gida, bayan mun gaisa kamar abin arziki sai cewa ta yi “Uwar su «Yar Zainab ba ki nuna mani irin ruwan arzikin ba na

wajen masu son Uwani”

Sai na yi shiru na ma rasa amsar da zan ba ta, sai kawai na ce, “Uhm! To me kake so in ce

Malam?”

Sai Babana ya yi tsaki ya ce, “Allah ya raba

mu da mutane masu sanya ido a kan harkar gidan

wasu, ba sai su bari ba idan auren yaran ya tashi sun

ga an kai mu gaban. Alkali an tsare mu a bisa mun ci

dukiyar wasu, sannan a ji dadin yi mana dariya.

Abin da zan gaya maki kada ki kuskura ki

mai da martani ga kowa, to kin ji. Ke kuma Uwani

kada ki bamu kunya kin ga mun ba ki wannan

damar, ki zo ki jawo mana abin da ya fi karfinmu.

Ki kama kanki don Allah, saboda sharrin ‘ya mace

yawa gare shi, ki fiddo littafin addu”o’ inki zan kara

maki addu’o’i na tsari, saboda yanzu za ki shiga

jama’a kala-kala, wani in yana son ka wani ba shi ko

kaunar bude ido ya ganka Na ce,

«To Baba A tsakanin kwana biyu da na je ina shirin

tafiya jami’ar Zariya, Inna ta amsar mani maganin

gargajiya na tsarin jiki, kamar na sha da na wanka da

makamantansu, ta tabbatar mani kada in ji bakin ciki da kowa, to insha Allah, Allah na tare dani.Na ce,

. “Haka ne Inna Ita ma kakata wadda take a Kuka Sheka ba a barta a baya ba wajen hada mani maganin tsarin jiki, wanda kuma ban yi mamaki ba ganin ta Kara matsawa wannan karon, tun ina ‘yar Karama in na je hutu wajen ta aikinta ke nan, magungunan da ake ba ni ma har sun fara isa ta, sai ka ce wadda zata yakin duniya. Dalilin da ya sa duk abin da suke ba ni ba na musun sha shi ne, Alkur’ani an ga ba ki da sihiri kuma an ga halas ne, a nemi magani.

Ana gobe zan tafi Zariya Ibrahim ya kawo mani su Zubaida da Zaliha yini, wato ‘ya’ yansa. A tsarabar da na yi masu daga Kaduna har da su ribon da riguna da “yar bebi, wannan tsaraba ta Kara mani kwarjini a wajen wadannan yara, na kuma tsefe masu kansu nasa masu shamfu na warke, na zauna na rangada musu kitso ya sauka bisa bayan wuyansu gwanin ban sha’awa. Allah ya yiwa wadannan ‘ya’ya na Ibrahim baiwar gashi mai tsawo. Na yi masu wanka na saka musu sababbin rigunansu. A nan fa ‘yar Karamarsu Zubaida ta ce, “Don Allah Yaya Asiya ki barni in kwana a wajen ki Na yi murmushi na ce, “To Zubaida idan

Babanki ya zo na tambayar maki” Muna zaune muna cin tuwon dare sai Zaliha ta ce, “Yaya Asiya a Kara mani miya da man shanu” Na ce, “To”

Na gama wanke masu hannu na cika ma ko wacce hannu da cingam, sai Ibrahim ya aiko ga shi ya zo. Muka fita gaba daya ina dauke da Zubaida

‘yar shekara uku, ta Kara makale wa cikin jikina, wannan abu ya yi ma Ibrahim dadi, na lura da yana da iko da nima ya dauke ni ya rungume kamar yadda na rungume ‘yarsa.

Suka fara gaya masa abubuwan da na yi masu, sannan na rokar ma Zubaida a barta ta kwana.

Ya ce,Babu damuwa”

. Na zuba su Momi cikin

mota ina rarrashinsu.

Na ce, “Zaliha ki gai da Mami da Mamanku” Ta amsa ciki-ciki, na rika shafa mata kai nace,

“Insha Allah idan nazo hutu kwana biyu zan daukoku ku yi mani yini kin ji?”

Sannan suka dan saki ransu, na ce, “Idan har ba ku yi dariya ba to na fasa”. Suka Kyalkyale da dariya.

Direba ya ja su suka tafi aka. barni ni da

Ibrahim da Zubaida, muka koma bisa dakalin gidan su Hadiza a cikin baranda na kashe lantarkin kofar gidan.

Hmmm

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *