ALLURA CIKIN RUWA BOOK1 CHAPTER 5 BY BILKISU S. AHMAD FUNTUA
idan kun lura ku dubi yadda wasu ke wulakanta ‘ya’ya mata sanadiyar aure-aure. Abin da yasa na ce ana wulakanta su kuwa daya ne, dubi yadda almajirai ke
yawon banza alhali da iyayensu,
wani dalilin almajiranci ya rabu da iyayensa ke nan, wasu kuma sune ake samu sun zama barayi ko ‘yan fashi da makami,
a yayin da yanzu su ne ke bullo mana da addini kala-kala suna ta da zaune tsaye a cikin Kasa. Idan kana da matarka daya, kuma Allah bai hore maka dukiya ba, to ina ganin ko
‘ya ya goma kuka haifa za ku iya kula dasu. idan matanka biyu ne, sannan Allah ya wadataka da arziki, sai ka iya
kula da yawan ‘ya ‘yan da suka haifa maka ba tare da ana shiga damuwa ba. Ayi aure a haifi ‘ya’ya daidai karfin ma'”aurata, daidai Kurji daidai ruwansa, kadaran-kadahan.
Da ake fadin a haifi ya’ya da yawa, ba ka san
wanda zai ji kan ba! To wa ya san gawar fari? Kila ka haifi “ya ‘ya da yawa kazo ka kwanta ka mutu, kila
kuma ‘ya’yan nan duk cima zaune ne, ka ga rayuwar wadannan yara sai kuma gyaran Ubangiji kenan.Annabi S.A.W) yaCe,
“Ku yi aure ku
hayayyafa, ni mai alfahari ne da yawan al’ummata a ranar tashin kiyama. Ba yana nufin ku yi ta aure bisa kaucewa ka’ida har ku haifi *ya yan da ba za ku iya
daukar nauyinsu ba Kuma idan mun koma Bangaren ba da ilimi da
tarbiyya, a wannan zamani masu ‘ya ya kadan sunfi samun saukin yin hakan. Zamani yana canzawa, komi
ya yi tsaye, mutane kuma yanzu babba da yaro kowa
hutu yake so, babu mai son wahala a duniya ballantana
ya tashi ya nemi na kansa. Wadannan kadan kenan daga cikin irin hujjojin da na bayar.
Nan take makarantarmu
ta lashe wannan
mahawara. Jarrabawar farko ta aji biyar dinmu Allah
ya bani sa’a na yi ta daya, wanda ban taba yi ba tunda na fara ilimina.
A nan mahaifina ya nuna mani murnarsa ya
kuma shaidawa mahaifiyata cewa, lokaci ya yi da idan
Mama Inki ta aiko in je Kaduna hutu, za a ba ni dama. A wannan rana nayi mura wadda ba ta
misaltuwa, na kwanta barci raina ya yi fari fes, na yi tunani a raina ko ya ya Kaduna take? Tunda Allah ya halicceni ban san ko ina ba, baya ga Katsina sai
Malumfashi, sai ko Funtuwa da na taba raka Inna Hafsatu dani da Hadiza biki muka kwana biyar. Inda
dai nake yawan zuwa sai kauyen su
tsohuwa Kuka-Sheka, wannan fa duk hutu dole ne inje in gai da su. Na yi tunanin yadda kawayena ke bani labarin ‘yan Kaduna
da yadda aka kawata ta tun
zamanin su Sardauna da irin manyan ma’aikatun da ke
cikinta. Yadda zuciyata ta dauki zuwa in yi wannan
hutu a Kaduna kamar zuwa kasashen waje ne. Mama Inki kuwa tasan wannan lokaci su
Uwani na cikin hutun zangon farko, sai ta aiko tana rokon arziki a barta su wuce tare tunda ga shi harta shiga aji biyar.
llai kuwa mahaifina ya cika alkawari ya barni
inje Kaduna. Da yamma aka yi wannan magana da
dare ya yi na kagu da gari ya waye, amma sai. na tsinci jikina yana min ciwo saboda yawan mirgine-mirgine
da na kwana yi a musabbabin rashin barcina.
Da gari ya waye na yi sallah na gai
da mahaifina, ban zarce ko ina ba sai na fara da wankin kayana, suka bushe na dauki dutsen gugar Yaya
‘Abubakar na goge su tass A lokacin shirye-shiryen nawa duk inda na
sa kafa Zainab na biye dani, tana ce mani “Don Allah
Yaya Asiya ki sayo mini “yan bebi a Kaduna”
Na ce,To *yar kanwa insha Allah zan sawo
miki?
• Da misalin Karfe sha biyu sai ga Abubakar ya
shigo da fara”a, ya ce mini
“Asiya ki shirya ga su
Mama Inki can sun wuce Kuka-Sheka, ta ce tana biyowa nan gidan don ku wuce tareda ita zuwa Kaduna Daga nan Abubakar ya ci gaba da cewa Inna
-ki taya ni murna na sami shiga A.B.U Zaria, kun ga jaridar da naga sunana ya fito” Na yi sauri na amshi jaridar ina dubawa, sai na ga
sunansa Abubakar Yusuf da kuma kwas din da zai yi, wato Akawuntun. Ai sai a ji dadi, na dinga murna da
ganin sunansa ne na farko, na kama hannun zainab muka
sheka sai gidan su hadiza, na shaida masu yau ne lafiya ta zuwa Kaduna, kuma in anjima kadan, sannan
kuma na basu labarin makarantar da Abuhakar ya samu zai tafi.
Sai Hadiza tace. “Ke Asiya yanzu tafiya za kiyi
ki barni? Na Ce,
“Haba hadiza har sau nawa kikeyi mini
gwalo ki yi tafiyarki Kano ki barni, har don yau nima zan rama tsiyar da kike mini sai- kice haka?” Muka Kyalkyale da dariya, sai na lura da hankalin
Inna Hafsatu ba ya tare damu, tayi tagumi ta shiga wani hali na dogon tunani.
Zuwa can nace
“Inna lafiya ko mun fadi wani
abin da ya bata miki rai ne?” Sai tayi ajiyar zuciya tace” A’a,
Asiya samun
makarantar Abubakar ya tsaya mini a rai, shine na shiga tunanin haka. Bature yaso ya je wannan makarantar ta
Zaria, a shekarar da mahaifinsa ya rasu Allah bai yi ba,ga shi ya shiga Kasashen Turai ko hutu ma ya ki zuwa Sai ta fara
Zubar da hawaye, na rika bata
magana. Hafiza tace,
“Gaskiya Inna ina ganin auren da kika yi ne yaga Malam Adamu na shigowa•nan gida
shine abin da ya fi ta da masa da hankali. Akwai ma wata rana da ya Kirani dakinsa yace mini.Hafiza kina son zaman mal adamu a gidannan nace masa a,a yace duk sanda yazo gidannan saiiiiiii////////////////////////////////////////////////
Inna tace hadiza dakin gayamin wannan maganar tun a wancan lokacin taci gaba da cewa tsakaninmu da malam adamu saidai Allah yayi mana sakayyah haka kurum ya yaudareni ya aureni don kawai yaci dukiyar marayu gashi yayi sanadiyyar tafiyar bature rasha yaqi ko zuwa hutu mu ganshi
Hadiza tace ai ni tun lokacin da mukazo hutu muna aji biyu naga ya daina zuwa sai dadi ya kamani nasan lallai kun rabu dashi
Ita dai inna hafsatu tanata share kwallah da gefen zaninta hadiza ta gama girki ta zubo mana mukaci mukayi daidai sannan mukayi sallar azahar saiga yaya abubakar ya shigo bayan ya gaida inna hafsatu sai yace asiya gasu mama inki sunzo nayi zumbur na miki muka tafi gida muna shiga gida nace mama inki sannu da zuwa tace yauwa asiya hadiza inayinnku muka amsa tare lfy qalau daga nan na kama hannun abbah dan shekara uku na wajen mama inki inayi masa wasa ita kuma mahaifiyata bata zirga zirgar kawo musu abinci mama inki ta dauki buta tayi alwara ta fara sallah