ALLURA CIKIN RUWA BOOK1 CHAPTER 6 BY BILKISU S. AHMAD FUNTUA
Bayan mun kimtsa.Muka doshi hanyar Kaduna, muna tafe muna hira har muka isa garin Kaduna,
ina ta ganin abubuwan mamaki. A inda muka bi hanyar gidan su Mama Inki na hango wani bututu ya yi sama yana ta fidda hayaki, tun daga nan hankalina ya
tashi, a cikin zuciyata na dauka gobara ce, amma sai na lura da su Mama da direba wannan wurin ma ko
kallo bai ishe suba balle ya firgita su. Nima sai na dake, zuciyata ta nasa mini cewa ba gobara bace Wannan kamfanin mai fitar da hayaki da na
hango kuwa ashe matatar man fetur, na NNPC ne da ke
a Kaduna. Mama Inki ta gaya, mini haka tana dariya. Da misalin karfe biyar saura minti biyar wani maigadin babbar kofa ya bude, mana, na ga wasu gidaje masu ban sha’awa wadanda aka zagaye su da badala. Muka shiga ciki muna zarce gidajen wasu har muka isa gidan su Mama Inki.
A nan yara suka fito suna tsalle ga Mama ga
Mama. Su Ummi suka kama ni suna mura,
“Lah! Har da Aunty Asiya”
Muka shiga ciki tare da kayanmu, daga gefe na hangi wani kasaitaccen falo wanda ban taba ganin ire-iren kayan alatu da aka zuba a cikinsa ba, ga duma- aka shirya mini,
an kunna na’urar sanyaya daki, ga
wani Katon gado da katifa lullube da lallausan bargo mai dan karan taushi.
Na dauko “yar tsohuwar rigar barcita zan sanya,sai ga Mama Inki da Ummi sun shigo, ta miko mini wata sabuwar rigar barci mai kyau, ta ce,Kiyi
amfani da wanna kafin mu je kasuwa gobe in karo miki wasu Na amsa na yi godiya.
Ummi kuma ta ce,Ita lallai da ni zata kwana
‘ Na ji dadi da Ummi ta ce haka.
Na saka sabuwar rigar barcina na tsaya gaban madubi ina kallon yadda dan lokaci kadan na kara
kyau. Sai na tufke gashina guda biyu ya sauko mini
har kafada na zama kamar *yar Fulanin daji da yake irin gashin mahaifina gare ni. Na hau bisa gado sai naji ya yi sama dani ya kuma yi kasa dani, wani sabon
dadi ya Kara kama ni har na kyalkyale da dariya.Sai Ummi ta ce,
“Anti Asiya kunna mana video mu yi kallo”.
• Da yake akwai video tare da T.V
da rikoda a dakin. Sai na yi shiru kamar ban ji abin da ta ce ba, har ta gaji ta nanata mini. Daga nan fa na yi ta maza na ce,
“TO”Na tashi
na je gaban video na yi karance-
karance nan take sai na gane yadda ake kunnawa, ta miko mini wani kaset na Indiya na saka na kunna, duk
da jikina na ta rawa zuciyata na dakan uku-uku. Cikin ikon Allah sai ga mutane sun fito. Na yi ajiyar zuciya na koma bisa gado muka kwanta na ware
mana bargo muka shige muka ci gaba da kallo. Ummi
na gaya mini yadda kaset din mai suna
“Nuri yake
tafiya, don ta saba ganin sa.
A cikin wannan kaset ne wata yarinya mai suna Ponam ta fito tana rawa tana waka, sai kawai Ummi cewa ta yi,.
‘Anti Asiya kina kama da wannan matar Sai na yi murmushi na ce,
“Haha Ummi ita
Indiya ni kuwa ‘yar kauye??
Sai tace Fari kawai ta fiki amma kin fita
hanci Da kaset din ya Kare Ummi har ta yi barci, ni kuwa dan Kwakwa sai da naga karshensa, abinka da
sabon shiga. Bayan na kashe na kuma kashe wuta, sai na shiga cikin kogin tunani, na fahimci cewa, lallai
mahaifina yana da gaskiya irin wannan jin dadi haka, ba duka mutum zai iya gani ba ya kau da kai, ya Ki son zama a irin wadannan wurare. Na nisa na ce, Nima
Allah ya sa wata ran mu ga iyayenmu da mu a irin wannan jin dadin, amin.
Kashe gari muka shirya za mu tafi kasuwa dani
da Mama Inki, na daura ‘yar atamfata ta ganin sarki wadda mahaifina ya dinka mini da sallah muka fito.
A zatona direba zai kai mu, sai kawai na ga
Mama Inki ta sa makulli ta bude mota tace dani in zauna gidan gaba,. Ta tuka mota babu tsoro babu komi ta fige ta muka shiga gari.
Misalin karfe goma da rabi na safe
bamu
tsaya ko in a ba sai salun inda ake gyara wa Mama Inki gashi. Ta ce tana so a yi mata wash and set. ni kuma ta ce dani, ko ina son a gyara mini gashina? Gudun
kada in yi kauyanci sai na ce eh
“. Na bude kaina
suka duba, suka ce,
“Gashina yana da yauki da yawa
sai dai kawai a wanke a gyara mini”
Ta ce musu,Suyi mini haka din’.
Bayan sun gama suka neme ni da in duba
madubi, ni kam a gaskiya ba don billena ba, sai in dauka bani ba ce,
komi nawa ya kara kyau,
idanuwana kamar an zuba masu
ruwan bula sai
walainiya suke yi, gashina yana kyalli. Gashina yana ta walkiya sun kasa mini shi gida biyu, rabi sun lankwashe mini shi ya sauka ta gefen kunnena, rabi
kuwa suka sauke mini shi har zuwa bayana: Kai Ummi fa ta yi gaskiya da tace ina kama da Ponam, lallai na yarda.
Mama Inki ta biya su muka tada mota muka
shiga kasuwa. Da muka isa Mama Inki tace dani in zabi duk abin da raina ke so. Kunya ta lullube ni, da Kyar na dauki dan kwali da riga ‘yar kanti. Na ce, “Na dauka Ta yi murmushi tace,”Asiya da sauran ki, ai ni
da yaya Aisha duk daya ne, ki saki jikinki idan ban yi
HMmm LABARI fa nata Tafiya shin KOYA ZATACI GABA da KAYAWA KUDAI KUCI GABA da kasancewa damu A koda Yaushe