Shidai Usman baice mata komai ba, dan bata ita yake ba, bawai baya jin haushin abunda take mishi ba, “a’a yana ji but Yadai shareta ne kawai, bai son yaita biye mata, yaita bata ranshi a banza da hofi
Kai tsaye cikin gidan ya shiga da motar, bayan sun fita Usman ya bud’e kofar motar sannan yaje ya bud’e ma Amal kofar ta fito
Kallonshi tayi tun daka sama har k’asa sannan tace poor tare da sakan tsaki tayi gaba abunta
Duk abunda Amal tayi alh Sulaiman mahaifinta yana sama yana kallonta, kai ya girgiza lallai y’arsa tayi nisa gaba d’aya bata ganin darajan Talaka, shima da kanshi abun yana damunshi Sosai, sai yasa a kullum yake mata addu’a tare da nusar da ita
Alh Sulaiman ya bu’kaci Usman ya dawo cikin tawagar masu binshi, wanda yace Amal ta bashi Aron Usman na wata biyu ya dinga tuk’ashi Kafin ya dawo yaci gaban mata da aiki
Amal bata soba, domin tasan muddin ya fara bin Dad, toh zaiji dad’i kuma zai samu hutu, amma babu yanda ta iya dole ta yarda, yanda ta Gode Allah ma wata biyu Dad d’in nata yace Mata
Usman ya fara bin Alh Sulaiman wanda Alh Sulaiman yana Lura da yaron yasha bashi kud’i yace ya ajiye Mai tare da fad’in bai san ko nawa bane, bayan kuma yasan yawan kud’in, “kawai yana son gwada Usman dinne ya gani, kuma koda yace ya bashi kud’in inya k’irga sai yaga dai dai.
Koda Alh Sulaiman yaga haka saiya canza salo, saiya zubar da kud’i a mota da gangan amma Usman bai taba d’auka ba, wata rana saiya d’auka ma yaba Alh Sulaiman din yace ya yarda kud’i a k’asa
Alh Sulaiman ya gwada Usman ta hanyoyi da dama Wanda kuma Usman bai taba cin amana ba,” Alh Sulaiman yayi mamaki musamman da yaga Usman yaro ne, amma yana da ri’ke Amana, yasha gwada drivers d’inshi amma saisu fad’i jarabawan
Abunda yasa Alh Sulaiman har yayi sha’awan ya gwada Usman saboda yana ganin irin yanda yakeyi shida Amal, inta mishi Abu yanda yake hakuri baya ramawa
Sannan yana bukatar yaron da zai dinga tayashi kula da wasu harkokinshi na kusa dashi, wanda yana bukatar yaro Mai Amana Sosai, sai yasa harya bu’kaci ya gwada Usman din
Nan Alh Sulaiman yace OK Ina son ka Kawo min takardan ka..
Usman yace OK cikin jin dad’i
Koda suka koma Abuja, bayan kwana biyu Alh Sulaiman shiya k’ara yima Usman maganan takardun shi….
Wanda Usman ya kawo mishi Washe garin ranan, koda usman ya kawo Kai tsaye falon gidan ya shiga inda yaga Alh Sulaiman da iyalanshi, Amal wani irin kallo ta watsa mishi cikin tsana tare dajan tsaki, abincin da takeci saboda ganin Usman da tayi taji gaba d’aya zuciyarta ya tashi, domin ita a duniya Talaka kyama yake bata..
Tashi tayi da gudu ta haura Sama, tare da d’auko chew gum, tasa a bakinta ta faraci
Usman bama Alh Sulaiman takardun shi yayi Bayan ya gaidashi cikin girmamawa, sannan ya gaida hjy Rabi itama,”amsawa tayi da lafiya cikin sakin fuska
Story continues below

Usman fita yayi daka falon wanda dai dai lokacin Amal ta sauko
Kallon Dad d’inta tayi tare da fad’in “Dad mai yasa zaka bashi izinin shigowa falon nan? Bayan muna cin abinci, gaba d’aya yasa mun tashin zuciya kaman zanyi amai, wlh Dad bana son ganin Talaka irinshi ko kad’an m….
Hjy Rabi tace Yimin shuru sha sha sha, mara hankali, wai Mai yasa gaba d’aya baki da tunani ne? Kina mantawa da Mai arziki da lafiya Talaka duka bayin Allah ne, kuma Allah duka ya haliccesu, karki manta bawai dan Allah baya sonsu bane yayi su a talakawa ba, haka kuma bawai dan Allah yana sonki bane yayi ki Mai kud’i, a’a gaba d’aya arziki da talauci jarabawa ne, Allah yana bama mutum arziki domin ya jarabashi, haka Yana bama mutum talauci domin ya jarabashi ya gwada imaninsa, “Amma ina mamaki ke gaba d’aya kin d’auki duniya da zafi, bakya gane hakan, shifa Allah bawai dan baya son bayinsa bane yake jarabtansu, kika sani koya fiki a wajan Allah?
Dan haka in zaki canza gwara ki canza, domin Kema Allah saiya jarabceki ya kwace dukiyar take, sai muga yanda zakiyi, tunda ke kin maida komai kaman Kece kika fi kowa
Amal tace nidai Mum karya k’ara shigowa falon nan, Indai inacin abinci gaskiya bana so, “sannan ai tunda shi Mai mana bauta ne dole yabi umarnin abunda muka sashi
Hjy Rabi zata K’ara magana amma Alh Sulaiman yayi mata alama da tayi shuru ta barta kawai
Alh Sulaiman kallon Amal yayi da fad’in zo nan Amal
Zuwa tayi tana fad’in dad wlh na rasa mai yasa Mum gaba d’aya bata d’aukan abunda nace mata, kwata kwata bata sona
Alh Sulaiman yace Amal ina son ki sani mum d’inki na sonki, kawai halinki ne bata so, amma tafi kowa sonki karki manta ita ta haifeki, baki da wata uwa data wuce ta,karki k’ara fad’in cewa bata sonki, domin mutum bazai haifi abunda zaice baya soba
Amal tace Dad yanzu ni Mai nayi? Kawai gaba d’aya Mum komai Nayi saita nuna ita bata so, duk abunda nake so ita mum bata sonshi
Dad yace ba haka bane amal, inda zaki dinga yin abunda tace toh da zaki gane cewa tana sonki fiye da kowa da kuma komai
Amal dai bata k’ara cewa komai ba, ganin haka yasa Alh Sulaiman tashi tare da fad’in ki fad’ama Mum d’inki inada meeting na fita gashi time ya kusa
Amal tace toh Dad
Tashi yayi ya fita.
Ganin haka Amal ta kalli takardun daya kawo ma Dad d’inta har zata kauda kanta sai kuma ta k’ara kallo dan taga kaman cv d’inshi ne ya kawo, d’auka tayi da sauri ta bud’e tashi tayi tana fad’in dama yayi har degree?
Hmmm gaskiya yanzu degree ya zama ruwan dare, kowa Wanda yakai da wanda bai kaiba saiku ganshi da degree, Hmmm Fara yaga takardun tayi tare da fad’in zaka iyayin degree amma bazaka samu aiki ba, har kana tunanin samun aiki wajan Dad? Hmmm you are wrong.
Shima Dad mai yasa ya amshi takardun Usman din? Kenan Dad ne yace ya kawo mai koya Abun yake? I have to find it, inma Dad ne yace ya kawo mai takardun wlh bazan bari ba, bazan taba bari Dad ya bashi aiki ba, a driver d’ina zai dauwama har karshen rayuwarshi, Talakan banza da hofi Sai shegen fad’in rai da mugun girman kai, Allah yaga abunda ya gani ya barshi cikin tsiya, dan haka a cikinta zaka dauwama wlh, kaida arziki sai dai kaga wasu Nayi amma Kai kam har abada
Tashi tayi taje ta watsar da takardun da tayi gutsi gutsi dasu a bola, sannan ta dawo falon ta zauna tana ta surutai kaman Usman din yana gabanta.
Lokaci d’aya ta tashi ta haura Sama inda ta nufi d’akin Mum din nata
Story continues below

Ganin hjy Rabi tayi tana waya dole yasa amal zama tana jira ta gama wayan sannan ta fad’a mata abunda Dad yace
Bayan hjy Rabi ta gama wayan ta kalli amal dake ta faman danna wayarta tace ya akayi Amal?
Tace Mum dad yace in fad’a miki ya fita, yana da meeting
Hjy Rabi tace OK
Amal tashi tayi zata fita hjy Rabi ta kira sunanta da Amal
Tsayawa Amal tayi tare da fad’in inaji Mum
Hjy Rabi tace zoki zauna ina son muyi magana ni dake
Dan yamutsa fuska Amal tayi tare da zuwa tazo ta zauna akan gadon d’akin kusa da Mum din tata
Mum ta kalli amal tace amal wai gaba d’aya naji ko ince ban taba ganin wani yazo Wajanki da sunan fira ba, sannan duk Wanda Dad d’inki suke mishi magana sai kice basuyi miki ba, sannan ni ban taba ganin wani yazo Wajanki zance ba, ko inji kina magana da wani a waya ba da Sunan kuna soyayya ba…
Amal ta katse hjy Rabi da fad’in Mum Wai kodai kin gaji da zama dani ne wai?
Hjy Rabi tace Kinga ban son shirme tambaya nakeyi miki
Amal ta turo baki tare da fad’in Toni mum ni yanzu kwata kwata kwaya nawa nake? Kofa 18yrs ban kaiba sai wannan year din Zan cika, shine kike min wani maganan aure.
Hjy Rabi tace kin iya fad’in ke yarinya ce amma kin iya rashin mutuncin dako babba wacce take da shekaru sai an samu mara kunya Kafin tayi abunda kikeyi, wlh amal ina rabaki da wulakanta dan Adam, baki San yanda Allah zaiyi damu gaba ba, shifa komai na rayuwa baya dauwama….
Amal tace Toni yanzu Mum Mai Nayi kuma??
Hjy Rabi tace ke yanzu baki ga abunda kikayi ba? Koma ince kike kan aikatawa ba?
Amal tace nidai ban sani ba
Mum tace shikenan nidai a matsayina na mahaifiyarki bazan daina fad’a miki gaskiya ba, sannan wlh bazan fasa fad’a miki ba, in kinji kin gyara kanki inma baki gyara ba kanki, domin ke macece kuma gidan wani zaki, baki San mai zaki tarar ba, kuma bakowa zai iya d’aukan abunda kikeyi ba, kowa ki mishi gori
Amal kuka tasa tare da fad’in hjy Rabi na mata baki, dan tace ita macece, shine amal ke fad’in wai baki take mata, tana Mata fatan wahala
Hjy Rabi ita Abun takaici ya bata, tace Amal taya zan miki baki? Kawai Ina k’okarin nuna miki ki gyara halinki ne, domin baki San gobe ba
Amal tace Mum karki manta wacece ni, sannan karki manta Waye Dad, Dad mutum ne dan kasuwa Mai tarin dukiya, sannan ni d’aya ya mallaka, kodan abunda nake dashi babu wani namijin da zaiyi min iko ko gadara, wlh Mum ni nasan ni millionaire Amal nafi karfin wulakancin namiji
Hjy Rabi sakan baki tayi tana kallonta, lokaci d’aya kuma tayi murmushin takaici tare da fad’in au dama ke abunda ke rudanki kenan?
Hmm yaro man kaza, gaskiya Amal baki San mai duniya ke ciki ba, inda kin San halinda duniya ke ciki da baki fad’i haka ba
Namiji kike tunanin zai raga miki saboda dukiyar mahaifinki? Hmm lallai kam, Toh wani namijin koda Dad d’inki ne yake bama duka family d’inshi abinci da kud’in kashewa bai hana inya aureki, kika Mai Abu yaci miki mutunci in bakiyi wasa ba ya zaneki, ya sa’ko ki
Amal tace tab, wlh Mum da ranan ya gane waya taba, ni lallai kam
hjy Rabi tace Allah dai ya kyauta, nidai Ina baki shawara a matsayina na Uwa kiji tsoran Allah ki daina raina dan Adam, domin rayuwa takan iya canza ma mutum at any time, sannan shi wannan arzikin da kike takama dashi Allah zai iya rabaki dashi, inma ya barki dashi Akwai mutuwa, sannan waje d’aya ake birne Talaka damai kud’i, sannan karshen mutun kabari daka shi sai farin kyalle wato likafani abunda aka sama Talaka shine ake sama Mai kud’i, Kinga kenan duk d’aya muke wajan Allah, babu wanda yafi wani wajan Allah sai Wanda yafi tsoransa
Abunda nake son ki fahimta anan damai arziki da Talaka duka bayin Allah ne
Amal tashi tayi tana fad’in nidai Mum bari in tafi Dan naga kaman baki da wani abun fad’a, taya zaki had’a Mai arziki da Talaka? Bayan akwai banbanci Sosai, yau koda mutuwa mai kud’i yayi zo kiga yawan mutane, amma Talaka fah? Wama ya damu da yaje….
Hjy Rabi salati ta saki tare da fad’in lallai amal Abun naki ya girmama, wato ke bazaki gane yanda rayuwa take bako?”Hmmm Allah ya kyauta ya kuma shirya
Amal tace Ameen tare da fita tana fad’in ai gaskiya na fad’a, taya za’a had’a Mai arziki da Talaka, ai kowa yasan akwai banbanci, nesa ba kusa ba.
Yau Saturday Usman ne zaune a cikin wani falo Mai kyau duk da bashi da wani girma Sosai, amma an kashe mishi dukiya domin kayan dake cikin falon kadai zai tabbatar da hakan, danko kujeran falon kasan masu shegen tsada ne
Gabanshi an ajiye Mai kayan ciye ciye, yana zaune cikin riga da wando k’ananan kaya, sunyi mishi kyau, domin Usman kaya suna amsan shi, kuma uwa uba ga tsafta, sannan k’arya ne kace baya kamshi, “Amma dai ita millionaire amal tace yana wari lol
Sadiya ce ta fito cikin wata doguwar rigan atamfa tare da fad’in ya naga bakaci komai ba?
Usman murmushi yayi tare da fad’in ina jira kizo ne
Sadiya tayi dariya tare da fad’in Toh gani nazo sai kasha drinks da kuma snack din
Usman yace a’a sai naji dalilin wannan kiran na gaggawa
Sadiya tace uhm, wai inata kiranka kullum amma ka kasa Bari mu had’u, kullum kace aiki aiki
Usman yace Toh ya za’ayi, tunda ban tara ba, ai dole in nema
Sadiya tayi murmushi tare da fad’in ina son in fad’a maka wani abune, kasan mahaifina soja ne, kuma yana da alfarma, shine nake son in ganka kasan an fara saida Abun army, inaso kaje cafe ka cika, saika tafi NDA short service
Indai kana son aikin soja, toh ka saka a ranka ka samu ka gama
Usman shuru yayi yana nazari, dan son aikin yanayi, kuma a halinda yake ciki ko wani aiki yazo Mai zai amsa, Indai ba haram bane Wanda ya sabama Shari’a, toh sai dai wani abu d’aya shine yaba Alh Sulaiman takardun shi, yanzu inya nemi soja Alh Sulaiman bazaiji dad’i ba….. Hmmm masu karatu kunji fah Usman abunda yake tunani, muje zuwa.
Sadiya tace Usman ya naji kayi shuru kuma? Kodai baka son aikin soja ne??
Usman yace a’a ba haka bane, Aini bani da wani zabi a halinda nake ciki yanzu, amma ina son kiban daka yau zuwa gobe zan kiraki muyi magana
Nan suka canza wata firan inda take fad’a mishi baici komai ba
Yace Alhmdlh, tare da fad’in a Ina kike aiki yanzu?
Sadiya tace ina lecturing ne a university of Abuja
Usman yace kai Allah ya taimaka
Ta amsa da Ameen tare da fad’in ina fatan dai an ajiye iyali?
USMAN yayi y’ar murmushi tare da fad’in har yanzu dai, domin aiki bai samu ba, kwakwara taya zamu ajiye iyali??
Sadiya tace Aiba daga nan take ba
Usman tashi yayi tare da fad’in Bari in gudu, sai na kiraki
Sadiya ta amsa da kadai k’i cin komai a gidan nan
Usman yace in nazo next time zanci insha Allah
Har waje ta rakashi inda yahau taxi ya wuce, kai tsaye gidan mahaifiyarshi ya nufa, inda motar ta tsaya a dai dai kusa da kwatar kofar gidansu
Fita yayi yaba ma Mai taxi din kud’i sannan ya shiga cikin gidan Kai tsaye tare da sallama
Amsawa mama tayi wacce take zaune tana yanka alaiyahu, tace a’a har an dawo??..
Yace eh wlh, da wajan aiki ma zan koma, amma nace dole sai nazo na ganki munyi magana
Mama tace maiya faru? Allah yasa dai tafiya?
Murmushi yayi tare da fad’in lafiya, dama akan maganan takarduna dana kaima Alhaji ne, toh yau na had’u da wacce nake baki labari rannan, wacce mukai karatu tare, toh shine tace in nema soja zan samu insha Allah, toh bandai amsa mata ba, saboda Kinga Alh Sulaiman ya amshi takarduna
Mama tace in banda abunka USMAN danya amshi takardun ka AI shima nata bai kamata kakiyi ba, domin raba k’afa akeyi, duk Wanda mutum ya samu, amma idan mutum yace zai zauna waje d’aya ai yana da aiki
Inaga shima ka nemi soja din duk Wanda ka samu shikenan, ni Wlh hankalina ma yafi kwanciya da aikin soja din Domim ban son yawan fushin nan naka, musamman yanda kake nunawa zaka iyayi ma y’ar Alh Sulaiman iyaka, kar wata rana zuciya ta d’ibeka kaje ka illata musu y’a ka janyomin bala’i ina zaman zama na
USMAN yayi murmushi tare da fad’in haba mama sai kace mara hankali, ai yanzu wlh komai tayi baya damuna ko kad’an hasali ma ni yanzu tausayi take bani, domin irin rayuwar data d’aukan ma kanta Abun a tausaya mata ne
Mama tace hakane, Allah ya ganar da ita
USMAN ya amsa da Ameen tare da fad’in yana….. K’aran wayarshi ne alaman Shigowan message wayarshi yasa yayi shuru da abunda yayi niyan fad’a tare da d’auko wayarshi ya fara duba message din kamar haka
Story continues below

You are invited to and interview on Monday tare dasa mishi date da time, kuma a company din Alh Sulaiman
Wani irin murmushi ya saki tare da fad’ama Mama abunda aka turo mai
Mama taji dad’i Sosai tare da taya dan nata murna, tace Kai Allah yasa a dace ya bada Sa’a Wlh naji dad’i Sosai
Usman ya amsa da Ameen
Nan mama ta tashi ta d’auko Mai abinci tare da fad’in yau dai abunda kakeso Nayi.
Usman bud’ewa yayi yaga danwake ne, dariya yayi tare da fad’in kai naji dad’i Wlh, Ina son danwake Sosai, ci ya farayi Bayan ya kammala ya tashi tare da fad’in Bari in koma
Mama tayi mishi addu’a tare da fatan alkairi
Amal ce zaune a bukkan dake gidansu tana danna wayarta, daka duka alama chatting takeyi, yanda take murmushi kadai zai nuna maka Tana fira da wani ko wata sannan duk da Wanda take firan dasu daka gani suna sata nishad’i Sosai
Lokaci d’aya naji wayar ta Fara K’ara alaman an kirata a wayar, d’auka tayi tare da sawa a kunne tace harka kirani daka baka number
Ta gefenshi yayi murmushi tare da fad’in Toh ya zanyi am in love, dole in kira inji muryan youngest millionaire
Amal murmushi tayi tare da fad’in amma naga kaman bada number din k’asar nan ka kirani ba
Yace yeah Ina China I just go for some important work, but dana kira kince harna kira Bayan you don’t know my number
Amal dariya tayi tare da fad’in haba am Amal fah, ina gane Abu da sauri
Murmushi yayi tare da fad’in am eager to see you, zan dawo cikin week dinnan kawai just to see you
Amal tace oh really Mr lover guy
Dariya yayi tare da fad’in yeah
Sunyi sallama akan zaizo danya ganta
Amal ta had’u da guy dinnan ne a instagram, inda ya nace mata, tun Tana d’an shareshi harta Fara kulashi, domin tana ganin yanda yake wasa da naira a video din da yake sawa, ga motoci na alfarma da yake shiga, wannan Abunne yasa amal harta yarda ta bashi number dinta domin bayan kud’i da yake dashi taga yana dakyau, har take ganin Sun dace
Tana nan zaune a wajan, lokaci d’aya ta tashi danta koma ciki, inda taga Usman yana shigowa cikin gidan, wani irin kallo ta watsa Mai har zata wuce ta tsaya tare da d’aga hannu dayi mishi alama akan yazo
Usman yi yayi kaman bai ganta ba, dan haka ya nufi d’akin da aka tanada na masu aikin Gidan
Amal baki ta saki cikin mamaki, lokaci d’aya kuma ta nufi d’akin inda ta iskeshi harya kwanta shi d’aya a d’akin
Amal tace samun waje, baka ga Ina kiranka bane? Nasan kana gani amma ka wuce, wai Mai yasa kana Talaka sai shegen girman kai Mai yasa kasa ma kanka girman kai da shegen fad’in rai m….
Usman yace eh ni Talaka ne amma gumina nake ci ba maula ba.
Amal tace miye maraba? Aida abunda kake da maula babu maraba, dama shifa Talaka bai iya samun waje ba, wlh Kai inda Allah ya baka kud’i Tab Allah yaga abunda ya gani insha Allah a haka zaka k’are
USMAN murmushi yayi tare da fad’in Alhmdlh, ni nasan aiki nake muku kuke biyana, ba rokanku Nayi ba, sannan ni bana gudun talauci domin na godema Allah da yanda yayi ni, sannan Indai haka arziki yake, irin yanda kike raina Dan Adam toh Wlh gwara in mutu Banyi arziki ba, gwara in koma ga Allah cikin talauci na, sannan kina fad’in a haka zan dauwama, murmushi yayi tare da fad’in Alhmdlh ai duk yanda nake na gode Allah domin gumina nake ci, sannan rabon bawa da arziki mutuwa, idan Allah yasa zanyi ko Ana ha Maza ha mata sai Nayi, sannan ki daina takama da dukiyar mahaifinki, kiyi dana gidan mijinki, ki samu kiyi aure sai muga dukiyar mijin taki yana fad’in haka ya rufe kofar d’akin garam
Rufe ido tayi domin taji tsoran yanda ya buga kofar, a hankali tace what? Ni yake fad’ama haka?
How dare him, ni Amal yake fad’ama haka? Lokaci d’aya kuma ta saki murmushi tare da fad’in zanyi maganin shi zansa a koya mishi hankali yanda nan gaba bazai k’ara k’okarin fad’ama wata magana ba, balle ni…. Fuuuu tayi cikin gidan cikin bacin rai
Usman yaje yayi interview kuma yaci 90% out of 100 inda ya zama ma’aikaci a company din Alh Sulaiman
Duk wannan abunda ake amal bata Sani ba, domin tun sanda sukai wannan Abun bata K’ara sashi a idonta ba, da Farko taso tasa a Kama mata shi a mishi duka daka baya saita fasa akan ita zata horar dashi da kanta
Saurayin amal yazo Wanda suka had’u a instagram, inda aka saukeshi a tafkeken falon ba’ki
Hjy rabi tayi murna domin ganin anzo tad’i wajan y’ar tata, sai farin ciki take, musamman da taga Amal din itama Tana d’auki
Amal ce ta fito cikin riga da skirt na atamfa dinkin yayi mata mugun kyau, domin saurayinta yace in zaizo atamfa yake son ganinta dashi, dan haka yasa ta saka mishi domin yace kullum a hoto da English wear yake ganinta
Amal fita tayi ta nufi falon ba’ki wanda yau shine rana na Farko da zasu had’u dashi ido da ido
Bayan ta shiga falon ba’ki ta ganshi zaune akan kujera yasha k’ananan kaya, ganin amal ta shigo d’akin yasa ya tashi tare dayin hugging dinta yana fad’in wow beautiful princess is hare
Amal dan tureshi tayi domin batai expecting hakan ba
Murmushi yayi tare da sakinta yace oh sorry baki son inyi hugging d’inki koh? Duk cikin turanci yake mata maganan
Amal murmushi tayi tare da fad’in ka zauna mana
Kamo hannunta yayi tare da zaunar da ita kusa dashi yana fad’in Bari in d’auki hota da millionaire amal
Murmushi amal tayi domin a duniya Tana son a dinga nuna ita fah ta isa, hakan yasa ta saki jiki dashi
Nikam kallon guy din Nayi fari ne shima amma ba Sosai ba, sannan nidai a idona ba wani irin haduwar nan yayi ba, amma a idon millionaire amal taga haduwarshi har take fad’i cikin ranta a fili yafi kyau
Sunyi hoto Sosai inda ya janyota jikinshi tare da matseta yana son su d’auki hoto, amal ta dan tureshi tare da fad’in no bana son haka
Yace am so sorry my young princess millionaire
Murmushi tayi tare da fad’in kaci wani abu, yanda take magana tanayi ne tare da isa, itafa wata ce, ya Lura da ita dan haka ya d’auki Ruwa kawai yasha tare da tashi yace zai tafi, kiran sunanshi tayi da fad’in fahad so soon you don’t even tell me who you are what are you doing for a living
Murmushi yayi tare da fad’in saukana a Nigeria kenan nazo inda kike, I have to go Zan dawo
Fita sukayi inda taje rabashi ya d’auko wani zobe cikin dankareriyar motarshi ya kamo hannunta ya saka mata zoban diamond Wanda kullutun diamond din kawai zai iyayin 10mil amal ido ta dan bud’e alamar kyautar tashi ta bata mamaki Sosai
Tace wow what a nice gift
Murmushi yayi tare da fad’in don’t insult me, is just a small tin
Amal wani irin murmushi tayi alaman ta samu dai dai da ita
Yace bye my millionaire princess I will call you
Tace OK tare da d’aga mishi hannu
Duk wannan abunda suke USMAN na kallonsu bai taba jin haushin abuba irin yau, lallai ya tabbatar ma kanshi yana jin wani abu akan Amal domin sanda yaga wannan guy din ya kamo hannunta dakyar ya samu yayi controlling kanshi…..
,
Amal cikin gida ta koma Kai tsaye, da gudu ta k’arasa falon gidan inda ta iske hjy rabi a falon, cikin murna take fad’in Mum mum kalli irin kyautar daya bani
Hjy Rabi kallon zoben da yaba Amal tayi Wanda kallo d’aya tasan zoben ya haura Million 8, tace amal dan Waye ne yaron??
Amal tace Wlh Mum ban sani ba, yadai bani kyauta, sannan abunda na sani shidai Dan kasuwa ne, bai cika zama a Nigeria ba, domin business d’inshi gaba d’aya a waje yafi yi
Mum tace ikon Allah, amma wannan kyautar daka had’uwa baki gama sanin koshi waye ba
Amal tace kai mum koni da kaina zan iya siya fah, ni a wajena ba komai bane danya bani zoban nan ba, hakan da yayi ya nuna yana sona, tunda kalli fa irin kyautar da yayi min…..
Shigowan USMAN falon tare da sallama yasa amal yin shuru tare da kallonshi cikin shiga Mai Kyau wanda ya bata mamaki.
USMAN gaida hjy rabi yayi tare da fad’in nazo amsan file din
Alh Sulaiman ne ya aikoshi amsan file wajan hjy Rabi wanda ya manta dashi a gida which is very important, gashi yanzu zasu shiga meeting an nemi file din an rasa, shine ya tuna Ashe yana gida bai d’auko ba, shine ya Aiko USMAN yazo ya amsa
Hjy rabi Bayan ta amsa gaisuwar tace OK Bari inje in d’auko maka
USMAN ya amsa da Toh
Tashi hjy rabi tayi tare da nufa sama danta d’auko mishi
Amal tunda ya shigo ta watsa mishi wani irin kallon tsana, ita a nata tunanin yana tu’ka dad ne kaman yanda yace ta bashi Aron shi,
USMAN kam gaba d’aya Satan kallonta yake, yana jin wani irin Abu a kanta wanda bai taba jiba sai yau, da sauri ya Fara kwaban zuciyarshi akan ta daina yaudaranshi domin har abada Amal ba sa’arshi bace tafi karfinshi nesa ba kusa ba
Fitowan hjy rabi ne yasa ya dawo daka duniyar tunanin da yake ciki, inda ta mi’ka mishi file din tare da fad’in gashi ka kai mishi USMAN
Amsa yayi tare da fita, tuk’i yake yana kallon fuskan Amal da sanda guy dinnan ya kamo mata hannu yasa mata zobe da sauri ya taka burki ya tsaya tare da ajiyan zuciya…
Usman ya dad’e a tsaye Kafin yaja motar yayi gaba, lallai ya kamata ya cire ma ranshi wannan tunanin, hanya d’aya ya kamata yabi shine ya amsa ma Sadiya domin dai ta cire kunya ta fad’ama Usman kudirinta, tun daka lokacin ya danja baya da ita domin Baya Sonta, inda ya kawo uzuri da fad’in baida aiki, har tace ita shi takeso sannan in baya son aikin soja zata sama mishi wani, Toh daka baya kuma ya samu aikin company din Alh Sulaiman inda ta k’ara mishi magana Yadai nuna mata tayi hakuri, amma still tana kiranshi akai akai suna magana
Usman yana tuk’i harya k’arasa office inda yakai ma alh Sulaiman file din aka shiga meeting
Bayan sun fito daka meeting inda Usman ya koma nashi office din, zama yayi yana tunani tabbas ya kamata ya auri sadiya, zaisa aje a nema mishi aurenta
Hakan ko akayi usman yama k’anin mahaifinshi magana inda aka tura gidansu sadiya an kuma amince an bashi ita
Usman ganin Idan yayi aure zai manta da amal amma kullum kaman kara Sonta yake, Abun yana matukar damunshi Sosai, sai dai in yana waya da sadiya yakan manta da amal din, domin tana mishi kalamai masu dadi daka sun gama wayar kuma saiya fara tunanin amal
Story continues below

Fahad ya dawo gidansu amal inda harya gaisa da hjy Rabi, inda take tambayan shi d’an gidan Waye shi??
Yace su y’an Kogi state ne anan mahaifinshi yake, amma mum d’inshi bata tare suna zaune a nan abuja shida dad d’inshi, amma ni ban cika zama ba coz nike kula da kasuwancin Dad d’ina
Hjy rabi tace eyya Allah ya taimaka
Soyayya Mai zafi ta shiga tsakanin amal da fahad, tun yana tabata Tana hanashi harta Fara barinshi domin yanda yake nuna fushin shi Idan ta hanashi har ya Kawo mata uzuri dashi ne wanda zai aureta miye danya taba ta
Amal Tana mamakin irin yanda yake mata, kuma sai tayi hakuri, tun Tana mamaki harta daina domin tasan tana sonshi kuma uwa uba bata son ganin bacin ranshi ko kad’an
Yau suna zaune a falon baki fahad yana danna wayarshi, lokaci d’aya ya ajiye tare da fad’in Amal wai yaushe za muyi aure ne? Ina son in haifi baby dake very soon, ko yanzu zan baki baby na ko sai munyi aure??
Amal kallonshi tayi cikin so da k’auna tace Idan mukai aure dai I….. Bakinshi ya saka cikin Nata yana kissing d’inta tare da tsotsan harshenta Sosai….
Amal gaba d’aya koda ya cire bakinshi cikin Nata sumar zaune tayi domin ta kasa koda motsawa domin wannan shine first time dana miji yayi kissing d’inta…..
Shima kaman ya Lura da hakan yace Amal kar kice min wannan shine farkon kissing d’inki da akayi???
Amal ko motsi ta kasa balle magana, hura Mata iska yayi tare da fad’in how far
Firgit tayi tana kallonshi..
Yace wannan ne first time right
Kaita d’aga mishi cikin wani yanayi
Fahad yace oh I see gaskiya inada aiki, my young millionaire saina koya miki abubuwa da dama Kafin aure, domin bazan bari insha wuya ba Idan mukai aure, ina son daka munyi aure inga love, kinga I have to teach you now before the wedding
Amal shuru tayi tana sauraranshi, lokaci d’aya yasa hannunshi akan nononta yana taba mata su tare da shafa mata su, Amal gaba d’aya bata son abunda yake mata but sai dai takan rasa bakin hanashi, komai zai mata bata iya hanashi ko kad’an
Fahad wasa yake mata da nononta Sosai yana shafa mata su, lokaci d’aya ya janyota tare da maida bakinshi cikin Nata yana tsotsa tare da shafa mata nononta
Amal gaba d’aya jikinta har rawa yake saboda tsoro, gashi ta kasa hanashi
Usman ne ya shigo falon yaga abunda ke faruwa, wani irin ja idonshi yayi tare da nufansu inda ya watsar da file din dake hannunsa yaje yaja fahad yayi wurgi dashi k’asa
Amal tashi tayi jikinta na faman Mata rawa
USMAN Marin fahad ya farayi tare da dukanshi yana fad’in Dan iska kazo Zaka bata ma yarinya rayuwa koh?….
Amal ganin Usman na dukan fahad yasa ta nufi USMAN da sauri ta tureshi tare da fad’in how dare you? Lokaci d’aya ta d’aga hannunta zata mareshi….
Jin muryan alh sulaiman tayi yana fad’in ke amal karki Fara..
Amal tace Dad Kalli abunda yama fahad, muna zaune yazo ya fara dukanshi..
Alh Sulaiman kallon fahad yayi wanda labarinshi yaji wajan hjy Rabi amma bai taba ganinshi ba, bakinshi a fashe domin USMAN ya fasa mishi
Alh Sulaiman ya kalli USMAN tare da fad’in USMAN ya zakai haka??
USMAN shuru yayi lokaci d’aya yace Alhaji kayi hakuri bazan iya fad’a maka dalili ba, domin ba abun fad’a bane
Amal tace ai dama taya zaka iya fad’a matsiyaci wanda bai gada arziki ba, ina ruwanka, dama kai naga take taken ka kana ba’kin ciki damai arziki, sai yasa Allah ya Barka a tsiyace Talakan Banza dana h….
Tsawa Alh Sulaiman ya daka mata tare da fad’in Yimin shuru nace, abunda bai taba yi mata ba gashi yau yayi mata
Kallon fahad yayi tare da fad’in ina Mai baka hakuri akan abunda ya faru, sannan Idan kana son Amal inaso ka turo iyayenka muyi magana dasu
Fahad yace Toh tare da fita fuuuu yana ma Usman wani irin kallo
Amal tace Dad shikenan abunda zaka ce? Bayan kana kallon irin dukan da yayi mishi? Wlh Dad sai nasa an kulleshi fita tayi da sauri Dan taje taga fahad Kafin ya tafi
Bayan fitan amal Alh Sulaiman ya kalli Sulaiman tare da kiran sunanshi yace Dan Allah ya fad’a mishi abunda ya faru, kar yaji shakka ko tsoro ya fad’a mishi abunda yasa yayi hakan, tare da fad’in Wlh usamn na yarda dakai sai yasa ban maka iyaka dako ina a cikin gidana ba
Na tabbata abunda ka gani ba k’arami bane ina rokanka akan ka fad’amin abunda ka gani..
Usamn yace kayi hakuri alh amma abunda ka yanke shine dai dai ya turo iyayensa, sannan ina Mai bada shawara akan in za suyi zance su daina kebewa su biyu domin na ukunsu shaidan ne…..
Usman na fad’in haka yace bari inje in shigo da ba’kin tare da fita
Alh Sulaiman da ido ya bishi, maganan USMAN da yayi ya tabbatar mishi a wani yanayi mara kyau ya gansu, lallai usamn Dan arziki ne, shima da kanshi Alh Sulaiman fahad bai kwanta mishi a rai ba, lallai zai yanke hukunci akan amal wanda ya tabbata bazata so hakan ba, kuma a wannan lokacin zai nuna mata shike da iko da ita, domin bazai bari tasa rayuwarta cikin halaka ba……