AMAL
CHAPTER 4
Koda amal ta fita ganin fahad tayi yana k’okarin shiga mota, da sauri ta nufeshi tare da kiran sunanshi amma Banza da ita yayi alaman ranshi ya baci, da gudunta ta isa gareshi tare da riko Mai hannu ta fuska key din motar da yake kokarin yasa danya tadar da motar
Kallon ta yayi tare da fad’in amal give me the key
Amal tace am so sorry fahad, plz kayi hakuri akan abunda wancan driver din yayi maka, and I…..
Yace what?? Driver?? You mean driver d’inku ne??
Amal tace eh he is our driver
Fahad yace how dare him, yana driver zai saka hannu ya bugeni and you did not say anything, I thought wani cousin d’inki ne or dan uwanki na can nesa
Amal tace a’a plz am sorry zan d’auki mataki akansa, taya zan bari ya taba ka ba tare dana dau mataki ba…..
Zuwan USMAN ne wanda yazo zai fita waje Domin ya shigo da ba’ki wanda Alh Sulaiman zai zauna dasu suyi meeting, ganin USMAN din yasa ta fad’in…. Kai driver tare da matsawa kusa dashi ta shiga gabansa Wanda hakan yasa dole ya tsaya cak dan ta shiga gabansa
Wani irin kallo ta watsa mishi, sannan tace mishi Kai Waye?? Who are you da zaka saka wannan k’azamin hannun naka akan wanda zan aura? Karka manta you are my driver, my driver my servant, inaso Kai apologising d’inshi right now or else….
Usman da yake sauraranta yace or else what?? Amal wannan ba sonki yake da gaske ba, inda sonki yake da gaske bazai taba jikin kiba ba tare da kunyi aure ba, yaudaranki kawai ya…..
Tace enough, don’t try to say anything, I don’t want to hear anything from you, am big enough to do whatever I want, infact who are you to try to lecture me?? Dan shuru tayi amma kana kallonta kasan ranta a bace yake…. Sannan taci gaba da fad’in whatever I did is non of your business, is my life I have d right to do whatever I want, and no one will say why or should stop me, you have cross your limit today, you forget who you are, but let me reman you of something you are my driver, my driver….. Dan shuru tayi sannan tace just apologize him
USMAN wani irin kallo ya mata
Fahad yace baby you see?? Wannan mutumin yana da girman kai, kince driver d’inki ne, but kalla irin kallon da yake miki, and gaba d’aya baya jin maganan da kika fad’a, tunda baibi umarninki ba…..
USMAN yayi murmushi tare da fad’in yes am her driver, gaskiya ka fad’a but Alhmdlh Gumi na nake ci, sannan ba maula nayi ba, sannan…… Shuru yayi tare da furzar da wata iska sannan yaci gaba da fad’in kaji tsoran Allah, domin duk abunda kayi da yar wani kaima za’ayi da naka, yana fad’in haka ya wuce ya Barsu
Fahad kallon amal yayi tare da fad’in give me my car key
Amal kallonshi tayi ganin yanda ya tamke fuska, alaman bada wasa yake ba
Tace fahad, miye haka?? Ya naga kaman kayi fushi….
Yace amal anci min mutunci a gabanki tunda nake wani Talaka bai taba fad’amin magana ba sai yau, na yarda talaka najin haushin Mai kud’i but is not his fault…. Shuru yayi lokaci d’aya ya k’ara mi’ka mishi hannunta tare da fad’in I said give me my car key
Story continues below

Amal tace fahad Mai kake son inyi mishi, just tell me komai kace I promise zanyi, just tell me mai zan masa, just to show him his mistake
Fahad wani irin murmushi yayi ganin USMAN na zuwa Lokaci d’aya ya janyo amal tare da bata fake kiss a goshi
USMAN wani abu yaji ya tsaya mai a wuya amma ya basar domin ba’ki ne zasu shigo
Ganin Mai gadin gidan yazo yana k’okarin bud’e gate yasa fahad sakin amal tare da fad’in baby if you love me and care for me just fire him, I don’t want to see him again in this house
Kafin amal ta bashi amsa aka shigo da mota wanda mutanan motar suka fito, fahad dake zaune a mota hango mutanan cikin motar yasa yai k’asa dakai tare da rufe fuska
Amal tace lafiya
Yace amal just enter d car plz
Amal da sauri ta bud’e kofar motar ta shiga
Fahad yace ta rufe kofar
Da sauri ta rufe tare da mi’ka mata hannu ya amsa key din ya tada motar tare da kunna motar ya kunna AC
Kanshi ya juya yana kallon Amal
Saida yaga ba’kin Sun wuce sannan ya sauke wani ajiyan zuciya
Amal tace fahad ka sansu ne
Kai ya girgiza tare da fad’in a’a Mai kika gani??
Tace is seem lyk you scare daka gansu…
Yace haba scare of what?? Hannunta ya kamo tare da fad’in baby in Ina tare dake why will I scare of anyone
Murmushi ta saki kawai ba tare da tace komai ba
Ganin is like kaman bata bata yarda da abun da yace ba, yasa yace baby I will send my parents suzo Ayi maganan bikin mu, zan nuna ma wancan driver din koni wanene after my parents come, ya k’arasa maganan cikin bacin rai
Amal jin yace zai turo parent d’inshi Ayi maganan aurensu hakan yasa ta saki wani irin murmushi cikin jin dad’i, domin ita Tana son fahad Sosai, ko dan shine first love d’inta oho
Fahad ganin ta saki yasa ya janyota kusa dashi ta matso da yake taba kujeran baya shi kuma yana ta gaba, fuskansu ya had’e suna shakan numfashin juna, Lura da yanda amal din take kaman a tsorace yasa yayi dariya tare da fad’in baby let me go sai munyi Waya..
Furgit tayi tare da lumshe ido, lokaci d’aya ta bud’e idon tare da k’ago murmushi tace OK
Yace tomorrow I will take you for shopping get ready by 4
Tace wow really??
Kai ya d’aga alaman yeah tare da fad’in I will do anything just to make my youngest millionaire baby happy
Ido ta lumshe alaman jin dad’i
Sallama ya mata sannan ya fita tayi cikin Gida
USMAN kam meeting suke da Alh Sulaiman da bakinshi wanda suke san fara hulda da company din Alh Sulaiman din, gaba d’aya abunda fahad yayi ma amal ke tama USMAN yawo a ido, gaba d’aya baya sauraran abunda suke fad’i danshi baya gane komai yanzu
Haka har suka gama meeting din inda Alh Sulaiman ya yarda suka kulla halaka ta business da mutanan domin yaga akwai samu Sosai
Koda zasu fita Alh Sulaiman tashi yayi ya kalli Usman tare da kiran sunanshi ya d’ago a tsorace alaman ya firgita da kiran da yayi mishi
Alh Sulaiman yace muje mu raka su wajan mota
Tashi USMAN yayi suka fita inda suka raka mutanan har wajan mota, USMAN koda suka fita baiga motar fahad ba hakan yasa hankalinshi ya kwanta
Bayan mutanan sun wuce Alh Sulaiman yace USMAN shima yaje za suyi magana a office
USMAN tafiya yayi cikin motarshi da company ta basu wanda za’a dinga cirewa cikin albashinsu kad’an kad’an har su gama biya, motar sabuwa fil da ita k’iran Benz
Kai tsaye wajan sadiya ya nufa domin yasan indai har yaje wajanta zata kwantar mishi da hankali da magana Mai dad’i
Bayan ya k’arasa gidansu sadiya din ta saukeshi a falon ba’ki inda ta cika mishi gaba da kayan ciye ciye
Kallonshi tayi tare da fad’in my dear kaci wani abu mana plz
Usman kallonta yayi wanda ya saki murmushi tare da fad’in am OK
Tace haba my dear Mai yasa kakemin haka a kullum baka son cin abunda na kawo maka sai Anci Sa’a, in baka cin abunda na baka nawa zaka ci?? Plz kasha koda drinks dinne
Usman ganin yanda ta marai raice yasa yasha ruwan goran Faro tare da fad’in nasha hankalinki ya kwanta
Tace Sosai
Yace ya shirye shirye
Tace Alhmdlh sai dai dama ina son maka magana, tunda kace Kai baka son bidi’a mum d’ina ta had’a mana dinner wanda tace in maka magana tana son kaima ka hallara, sannan ta bani kayan da ake bukata kasa ranan in baka, domin ana so ya zama Kala d’aya da Wanda zansa da kuma naka
USMAN yace gaskiya kaman yanda na fad’a miki tun farko bana son bidi’a inda za kuyi hakuri da kun barshi domin ni bana bukatar wannan Abun burina shine kawai Ayi biki lafiya tare da fatan zaman lafiya, ni mutum ne wanda bana son irin wannan Abun sai yasa na fad’a miki bazanyi ba
Sannan kiba mum hakuri dan Allah
Sadiya tace haba my dear Mai yasa zaka fad’i haka, dan Allah kayi hakuri Wlh bazan iya fad’ama mum haka ba, domin kace Kai baza kayi ba, shine ita tace Bari ta mana, Kaga bai kamata ince mata kai baka so ba….
USMAN yace sadiya koda za kuyi bazan hana kuba, amma maganan gaskiya bazan samu zuwa ba, tashi yayi tare da fad’in Bari inje, ranan Usman shi d’aya ya fita ba tare da ta raka shiba, USMAN hakan bai dameshi ba, domin shi baya son Ayi mishi Komai a hidimar bikinsa saga dangin sadiyar gudun abunda za’a goranta mishi nan gaba
Koda sadiya ta shiga ciki ta fad’ama mum d’inta yanda sukai da USMAN inda ta Fara bala’i Tana fad’in AI komai ya fad’a Kece kika ja, kin tashi kin d’auki son duniya kin d’aura Mai, ai dole yace haka, ni taimako zanyi miki domin Nasan baida kud’i ne yasa yace babu abunda zaiyi amma yanzu saboda tsiya yace Wai baza shiba, wlh wannan yaron yana da girman kai, In kika biye mishi zaki sha wahala gaba d’aya kina wani nuna mishi mugun so wanda ya zarce misali ke ga Wawiya…..
Sadiya babu abunda take sai kuka……
Usman gida ya nufa kai tsaye inda ya Tarar da mahaifiyarshi tana aikin dafa abinci, zama yayi tare da fad’in mama sannu da gida
Mama ta amsa tare da fad’in har an shigo? Ya aikin?
Yace Alhmdlh, ya kamata dai ki Fara shiri domin mu koma gidana, inda so samu ne ina son ki riga komawa Kafin Ayi biki
Mama tace a’a Usman bazan zauna a gidanka ba, domin ina jin tsoran zama da Sirika, gwara in zauna a nan, yafi min
Usman yace mama haba, Indai bazaki zauna a inda nake ba, miye amfanin samu na?? Dan Allah ki Fara shiri mu koma
Mama tace uhm USMAN bazaka fahimta ba, amma ina son kabar wannan maganan kawai
Usman shuru yayi domin yasan wacece mahaifiyar tashi, Indai ta dage akan Abu, sannan ita mutum ce wacce bata son shiga sabgar kowa, mace ce mai hakuri ga saukin Kai, sai dai fah tana son usman kaman ranta bata had’ashi da kowa
Amal kam koda Dad ya shiga ciki a falo ya ganta Tana ta sintiri wanda hakan ya nuna mishi daka duka alama shi take jira
Aiko tana hango mahaifin Nata ta nufeshi tare da fad’in Dad yanzu akan wannan banzan driver din kake ganin kaman Fahad shike da laifi? Dad Ina son ka koreshi daka aiki domin bana bukatar ya tuk’ani haka kaima Dad naga kana da dri…
Alh Sulaiman ya dakatar da ita tare da fad’in ya isa haka amal, Usman yanzu ba driver d’ina bane, haka Kema yabar miki aiki domin kuwa yana aiki a company d’ina as my PA personal assistants
Amal tace what?? Dad your PA that poor guy, my driver become ur PA how…. Shuru tayi tana jimami tare da nanata Kalman PA lokaci d’aya kuma ta zauna akan kujeran dake falon sannan tace Dad mai yasa zaka bashi wannan muk’amin Dad karka manta shifa Talaka ne inya samu dama he can do anything, Dad karka taba barin Talaka ya rabeka ka barshi yaita shan wahala ta yanda zai gane banbancin Mai arziki da Talaka
Dad plz just for my happiness ka koreshi plz Dad I hate him….
Dad yace amal inaso ki san wani abu d’aya, Usman ya zama yaron dana yarda dashi, domin na gwadashi na gane ba macuci bane, dan haka na yarda dashi yau koda bana Raye na tabbata zai iya ri’ke mun ku tare da kular muku da abunda na bari duk da bani da tabbacin Kafin in mutu ko zan bar wani abu, duba da irin yanda rayuwa take tafiya, babu yanda Allah bayayi sai kiga mai kud’i ya tsiyace Talaka yayi arziki, Allah kenan babu yanda bayayi, saika tara dukiyar daka karshe ciwo ya kama ka, haka za’ayi ta nema maka lafiya cikin abunda ka tara, in bakai Sa’a ba aita neman maganin Ka’ki warkewa har abun daka tara ya k’are
Toh Kinga shi Allah babu yanda ba yayi, dan haka Ina So ki sani Amal ke d’aya ce y’ata dana mallaka, da yawa zasu zo Wajanki ne saboda abunda na tara, ke yarinya ce baki San mai duniya ke ciki ba, ni mahaifinki ne zan iya sadaukar da komai just for your happiness, amma ina son ki sani ya kamata kima kanki karatun ta nutsu ki gane Allah shine mai azurtawa shine mai hanawa, sannan zai iya kwacewa daka hannun wanda yaba, sai kiga ya azurta Wanda bashi dashi, damai arziki da Talaka duka bayin Allah ne, wajan Allah duk d’aya muke babu banbanci
Story continues below

Amal tace Dad ka daina had’amu da Talaka, domin ba d’aya muke ba, shifa komai na duniya guda biyu ne, kuma ko wanne akwai banbanci, misali yes no, in out, Kaga wannan kalma ce Mai zaman kanta, haka shima Talaka da mai kud’i, rich poor…. Kaga akwai banbanci ko wajan fad’a, Mai arziki matsiyaci, Dad even skin dinmu da nasu are not the same, jikinmu yana da kyau, amma su fah??
Dad Talaka Talaka ne, mai kud’i Mai kud’i ne, inda inada iko da wajan da mai kud’i ya shiga Talaka bazai taka k’afa yaje wajan ba, amma Dad yanzu for god sake ka biye ma Mum an kaini skul d’in da Akwai yaran talakawa, wanda zan iya cewa yanda kasan saboda su akai skul d’in, haba Dad wannan Abun kunya ne ace y’arka Dad your only daughter Tana karatu a wannan k’asar……
Dad murmushi yayi tare da girgiza kai, yace Amal, ni a wajena Abun alfahari ne ace y’ata tana karatu a cikin k’asata duk irin dukiyar da nake dashi, wannan Abun alfahari ne, kuma zanso duk wani mai hali yayi irin abunda Nayi
Amal tace Dad forget ol this tin, yanzu ina son ka kori that driver coz I hate to see him, wlh Dad ban San inga ko kad’an yana cikin farin ciki, not even him Talaka ma ban son in ganshi cikin hutu, domin bashi da hutu sai bauta, bautan ma namu mu masu arziki……
Dad ya dakatar da ita tare da fad’in kina da hankali kuwa amal??
Turo baki tayi alaman taji haushi
Dad tsaki yayi tare da tafiya ya barta, domin ya lura komai zai ce mata bazata gane ba
ita kam amal gaba d’aya ranta a jagule yake, akan mai zai sa ace driver d’inta shine ya koma aiki a company d’in Dad dinta, kenan ya samu ci gaba, ita da take son ta ganshi a kaskance, amma sai gashi ya samu mugun ci gaba, har ya zama PA din mahaifinta, yau Idan Dad baya nan shine zaiyi magana da yawun Dad d’inta,…. Da sauri ta tashi tsaye tare da fad’in impossible dad must fire him
No wander naga yanzu yana saka kaya masu kyau, nan taita tunanin yanda za tayi domin Dad ya koreshi
Washe gari kaman yanda fahad yace Mata ta shirya su fita hakan koh akayi
Yazo ya d’auketa suka fita inda ya kaita wani super market yayi mata siyayya sosai
Amal taji dad’in irin siyayyan da yayi mata, inda daka nan ya nufi Da ita wani gida Bayan yayi horn Mai gadi ya bud’e ya shigar da motar inda yace Mata let go
Tace inane nan???..
Yace Gida na
Fita tayi daka motar inda suka shiga, kallon gidan takeyi gidan yana da kyau sai dai bashi da girma
Fahad ciki ya shiga inda ya barta a nan zaune cikin falon
Jim kad’an sai gashi da drinks ya kawo mata, Bayan ya ajiye ya nufi inda take tare da kamo hannunta biyu ya matse Mata su yana fad’in na k’osa muyi aure ki zama tawa…..
Amal wani irin murmushi ta saki tare da fad’in really
Gira ya d’aga mata alaman eh
Tace banga kowa ba, ko kai d’aya kake zama a nan??
Yace ban dad’e da siyan gidan ba, just kawai ganin abunda ya faru yasa Nayi deciding mu dinga firanmu a nan ta yanda babu Mai takura mana
Amal ta zaro ido tare da fad’in sai gaskiya Idan Dad ya sani ranshi zai baci
Fahad yace yanzu zaki fad’a mishi muna zuwa nan ne??
Tace a’a mutane nake ts…..
Janyota yayi jikinshi wanda hakan yasa dole tayi shuru, wani irin runguma yayi mata tare da matseta yana fad’in come on amal dnt be scare, nine Zan aureki and babu abunda Dad zai Sani, just trust me we are safe hare Kinga abunda akamin a gidanku, inda badan ina sonki ba, bazan k’ara nemanki ba
Story continues below

Amal gaba d’aya ita dai ta kasa saki, domin ita dai hankalinta bai kwanta da su dinga zuwa nan zance ba, amma tana son fahad, babu yanda za tayi and shi zata aura…..
Dan cireta yayi daka jikinsa yana fad’in baby is like kaman you are not comfortable hare right??
Kai ta girgiza alaman a’a.
Fahad yace so feel like you are at home my young princess millionaire
Amal murmushi ta saki
Tashi yayi tare da zuba Mata drinks ya bata tare da fad’in kisha naga kaman you are sweating
Amal tace Nop tare da taba goshinta Wanda taji zufa, murmushi tayi tare da amsan cup din hannunshi ta Fara sha
Bayan ta gama sha ta kalleshi tare da fad’in I have to go
Tashi yayi tare da d’agota ya matseta a jikinsa yana fad’in baby is like you don’t trust me?? Ok let go
Jin haka yasa amal fadin no fahad is not like that, I trust you more than my self
Kawai Ina son zuwa Gida ne, coz ban fad’ama Mum zan fita ba
Fahad yace OK tare da sakinta yace muje, domin ya lura da ita kaman tsoro takeji sosai
Binshi tayi a baya har mota suka fita inda ya tsaya a kofar gidansu, kallonta yayi yace are you happy now??
Kallonshi tayi
Gira ya d’aga mata yace you are at home now Kinji dad’i
Wani irin son fahad din taji tanayi domin ganin harya kaita gidanshi baiyi yunkurin yi mata Komai ba, lallai yana Sonta tunda abunda tayi zato ba haka ta gani ba, tunda gashi ya kawo ta gida……
Katse mata tunani yayi tare da fad’in hey why are you staring at me lyk that???
Murmushi tayi tare da fad’in fahad I love you…..
Kallonta yayi tare da matsawa kusa da fuskanta har suna jiyo numfashin juna ya fara magana da amal I really love you too, lokaci d’aya ya fara k’okarin ya mata kiss k’aran wayarta yasa yaja baya ba tare da yayi mata ba
Ita kam harta lumshe ido, jin k’aran wayar Nata itama yasa ta bud’e ido, tare da d’aukan wayar taga Mum ce
D’auka tayi Mum tace amal kina ina?? Kizo ina nemanki yanzu
Tace OK mum tare da kashe wayan, ta kalli fahad yace zan shiga gida mum na son ganina
Nan sukai sallama bayan ta d’iba kayan daya sai Mata harda security suka taya ta d’auka domin kayan Nada yawa
Kai tsaye amal Bayan ta shiga gida, dakin mum ta nufa inda taga Mum a zaune ta zabga tagumi
Shigowan amal yasa Mum tashi Tana fad’in amal Mai yasa bakya zuwa skul yanzu??
Tace waya fad’a miki Mum??
Hjy rabi tace am asking you??..
Amal ta turo baki tare da fad’in saboda bazan iya karatu inda yaran Talaka keyi ba, saboda naga ba mutunci na bane, tunda bakwa son in fita waje in nayi aure zanyi a China fahad yace in Bari in munyi aure sai inyi a China ko wata k’asar da nake so…..
Hjy rabi cikin bacin rai tace ashe baki da hankali amal?? Yanzu saboda wani wanda ko iyayensa bamu sani ba, shine zaki daina karatu?? Toh Wlh kinyi k’arya dole kici gaba, ko kinki ko kinso….. Yaron da baki da tabbacin zai aureki?? Inda gaske yake ya turo iyayenshi mana su zo, amma saiya hanaki zuwa skul ki hanu, saboda ke baki da hankali idonki ya rufe
Tace look mum plz ya isa haka dan Allah, nifa tun Farko na fad’a bana son skul d’in da yaran talakawa zasu iya zuwa, taya za’a gane banbancin Talaka damai arziki, Indai har zamu dinga cudanya dasu?? Mum mu dasu ba d’aya bane, bazan iya ba, bazan iya hulda da y’ay’an talakawa ba even for a minute, baki ga yanda nake jiba inna zauna lecture gaba d’aya ji nake jikina yana kaikayi yanda kika san suna goga min jikinsu…… Mum Talaka damai kud’i bai kamata su zauna Inuwa daya ba Mai arziki mutum ne mai girma Mai daraja, shi kam Talaka mutum ne wulakantacce Mara daraj……
Daka mata tsawa mum tayi tare da fad’in Yimin shuru mara hankali shasha, baki da hankali sannan baki da tunani, ke gaba d’aya baki San Allah shine mai komai ba?? Wannan arzikin da kike takama dashi Allah zai iya kwacewa yaba wani, wlh amal ko kina so ko bakya so dole ki koma skul, cikin yaran talakawan da baki so nan zaki zauna kiyi karatu sha sha sha, mara tunani, wannan bakin naki Wlh in bakiyi wasa ba sai Allah ya jarabceki Wlh….
Amal kuka ta saki Tana fad’in AI dama na sani Wlh bakya so na, inda kina so na wlh ba zaki barni in dinga had’aka da y’ay’an talakawa ba
Mum tace eh naji bana sonki, indai akan wannan Abun kike cewa bana sonki Toh Wlh bana sonki din, kuma ina guje miki Randa Allah zai jarabceki domin wannan mugun bakin naki da baya sanin abunda zai fad’a wata rana sai kince Mai yasa na fad’i hakan indai bakiyi wasa ba, yau masu kud’i nawa suka samu karayan arziki?? Talaka nawa yayi arziki???
Amal cikin kuka tace ai mum duk mai kud’in daya samu karayan arziki in kika duba zaki ga yana hulda da Talaka shine suka goga Mai kashin tsiya…. Ga Dad ya tashi ya d’auko wancan driver din ya bashi aiki, wlh Mum baki ji yanda nake jiba idan na tuna driver Talaka kankantacce shine Wai yau dad yaba PA d’inshi haba Wlh Dad must fire him
Mum tace idan company d’inki ne AI saiki koreshi Mara hankali kawai
Amal tace na Dad ne kuma wlh yanda Dad ya bashi aiki haka zansa Dad ya koreshi, wannan alkawari ne inko hakan bai faru ba daka ranan zan canza suna……..
Hjy rabi tace Aiko zaki canza suna, domin ina Mai tabbatar miki babu inda zashi….
Amal na k’okarin yin magana hjy rabi ta daga mata tsawa tare da fad’in Yimin shuru Mara hankali kawai fitar min a d’aki
Amal Fuuuuu ta fita kai tsaye d’akinta ta nufa inda taita sintiri kaman Mai parade, ba komai take sakawa ba sai yanda Usman zai bar office din Dad d’inta, k’aran wayarta ne yasa ta nufi wayar tare da dauka, fahad ne dan haka yasa ta saki wani murmushi tare da daukan wayar tasa a kunnenta……
Fahad yace my young millionaire kin San wani abu??
Murmushi tayi tare da fad’in a’a saika fad’a
Yace Dad d’ina zaizo ganin Dad d’inki, domin Ayi maganan aurena dake
Amal tace wow really
Fahad yace yes, kin San ina sonki, so bani da wani fata face in aureki
Amal cikin jin dad’i tace Nima Nasan haka, sai yasa koda yaushe nake son ka
Murmushi yayi tare da fad’in I will call you later, tare da kashe wayan….
Amal wani irin ihu ta saki tare dayin tsalle na Murna domin burinta zai cika, zata samu abunda take so….
Sadiya ce zaune a cikin bedroom d’inta, ba komai take tunani ba sai yanda zata shawo kan Usman ya amince ya amshi kayan da Mum d’inta ta bata wanda tace shi zai saka in za’ayi event din…
Lokaci d’aya ta d’auki wayarta tare da kiran Layin usman din, bugu uku ya d’auka yana fad’in amarya bakya laifi…..
Ajiyan zuciya tayi tare da fad’in my dear ina cikin wani hali…
Yace maiya faru???
Tace dan Allah ina son ganinka, ka taimaka kazo muyi magana dan Allah
Usman yace ok Zanzo karki damu gani nan tafe
Kashe wayar yayi
Sadiya babu tashi tayi inda ta fad’a toilet tayi wanka shap shap, sannan ta fito ta saka wata doguwar riga bayan ta feshe jikinta da turare Mai kamshi….
Zama tayi tana jiran zuwan nashi, wayarta ce ta Fara K’ara inda ta d’auka taga usman dinne
Bayan ta d’auka yace nazo, ina kofar gidanku, ki fito….
Tace ka shigo mana
Yace a’ah basai na shigo ba, kizo muyi magana a nan kawai
Tashi tayi ta fita, inda ta sameshi cikin motarshi, kai tsaye ta shiga cikin motar inda ta zauna a gaba…. Kallonshi tayi ta saki murmushi tare da fad’in amma dai yau ga dukan alamu bakaje office ba
Yace Mai kika gani
Tace gashi yau ka amsa kirana da wuri..
Dariya yayi tare da fad’in dole in amsa domin yanda naji muryanki kaman kina cikin damuwa
Sadiya tace Sosai kuwa, wlh my dear ina cikin wani hali, dan Allah karka k’i amincewa da abunda zan fad’a, koda yake mum tana son ganinka….
Yace lafiya kuwa?? Maiya faru??
Story continues below

Tace babu komai, kazo muje kaga mum..
Yace OK muje
Fita yayi inda suka shiga cikin gidan, har babban falon su, ta kaishi, sannan tasa aka kawo mai abun ciye ciye, inda ta nufi part din Mum din tata, jim kad’an sai ga sadiya da Mum dinta Sun fito
Usman cikin girmamawa yake gaida mahaifiyar sadiya, inda ta amsa cikin sakin fuska, tare da fad’in ya aiki
Yace Alhmdlh
Mahaifiyar sadiya tace, Usman nace ta kiraka ne domin tamin bayani akan yanda kukayi kaida ita, akan maganan event din da nace zan had’a muku, usman kaida sadiya duk Abu d’aya ne a waje na, yanda take y’ata kaima haka kake a waje na, sannan ina son ka sani sadiya ita d’aya garemu, komai zamu iyayi Mata Dan farin cikinta
Ina son a matsayina na uwa, kayi hakuri kazo wannan event din, wanda na had’a muku kaida ita
Usman nauyin mahaifiyar sadiya din yaji dan haka yace Mata zai zo insha Allah, kaman yanda suke bukata
Sadiya wani dad’i taji ya rufeta, inda yayi ma mahaifiyar sadiya din sallama ya fita, shida sadiya din
Bayan sun fita ya kalli sadiya tare da fad’in zan gudu, tunda kinsa mama tayi magana
Sadiya murmushi tayi tare da fad’in babu ruwana, yanzu bari in d’auko Maka kayan da zaka saka, sai ka bada d’inki
USMAN yace a’a, ki fad’amin colour din kayan da ake bukata insa zan siya
Tace haba my dear, miye amfanin siya kuma, tunda gashi an sai maka, dan Allah ka amsa, karka manta ni dakai yanzu mun zama Abu d’aya, idan kana irin haka sai kasa in dinga wani irin tunani.. ..
Usman yace Toh shikenan naji, a bani
Da sauri tayi cikin Gida ta d’auko Mai kayan tare da bud’e motarshi tasa Mai, sannan ta rufe tana fad’in nasan ranan zakai kyau, domin my dear tubarkallah
Murmushi yayi tare da fad’in AI ban Kai rabin kiba
Ido ta Dan zaro alaman ni din
Usman sallama yayi mata tare da fad’in aiki ya baro saboda kiran da tayi mishi
Mahaifin fahad yazo yaga Alh Sulaiman, inda suka tattauna, akan batun auren y’ay’ansu, mahaifin amal yana ma mahaifin fahad kaman kallon sani amma Ya manta inda ya sanshi……
Alh Sulaiman yayi na’am da batun domin yanda mahaifin Fahad ya nuna kamala, tare da mutunci, inda ya yarda yaba fahad y’arshi tare da fad’in baya son bikin yaja lokaci Mai tsawo
Koda Alh Sulaiman yake fad’a ma Usman domin a halin da ake ciki yanzu usman ya zama Kaman shine mai bama alh Sulaiman shawara akan abubuwa da dama, domin alh Sulaiman yakan tambayeshi akan Abu, inya bashi shawara sai yaga abun yayi kyau
Usman ya shiga cikin damuwa Sosai, wani irin ciwon kai yaji ya kamashi lokaci d’aya, har Alh Sulaiman ya lura da Kaman ya canza
Yace Usman lafiya kuwa? Ko baka jin dad’i ne??
Usman yace kaina kemin ciwo Sosai
Nan take alh Sulaiman yace yaje yaga Dr ya duba shi, domin a bashi Magani tare da cewa Allah ya k’ara sauk’i, ya kamata ma ka d’auki hutu tun yanzu tunda bikin ka ya matso
Nan Usman ya wuce Kai tsaye gidan mahaifiyarshi ya nufa wanda yasa an gyara gidan, an rufe wannan kwatar anyi suminti a wajan, sai yasa akama gidan fenti tare da gyare gyare harta d’akinsu yanzu tiles ne aka saka
Yana shiga da sallama d’akinshi ya nufa inda ya kwanta, domin kanshi ke mishi wani irin ciwo, kwanciya yayi tare da lullube jikinsa
Mama da sanda yayi sallama tana sallah lokacin Bayan ta idar d’akin dan nata ta nufa inda ta ganshi yana kwance ya lullube jikinsa
Story continues below

Mama tace Usman lafiya kuwa?? Da wannan ranan ka rufe jiki, kodai baka jin dad’i ne??..
Dakyar ya fara magana wanda idonshi ya rune yayi ja, yace mama bana jin dad’in jikina, gaba d’aya Ina tunanin gajiya ne, ga bacci inaji
Mama tace toh in banda abunka aida asibiti kaje aka baka magani, saika kwanta in kasha, amma ka kwanta da cuta babu magani
A hankali yace Idan na tashi zani asibiti yanzu bacci nakeji sosai
Nan mama tace toh Bari in d’auko Maka paracetamol kasha, dan naga kaman zazzabi kake, tayu kafin ka tashi kaji ya dan sake ka….
USMAN cikin ransa yace lallai ina son Amal, ban taba tunanin sonda nake Mata yakai haka ba, ido ya lumshe yana tunanin irin abubuwan da suka faru tsakaninshi da amal din, wanda gaba d’aya take nuna kyamarshi da tsana a kanshi, lallai zuciya batai mishi adalci ba, data fad’a son wacce bazata samu ba, dole in cire tunanin amal a cikin raina domin Nasan ba Kala ta bace har abada tafi karfina, niba kowa bane, face Talaka wanda take kira da bawa, uwa uba ni driver d’inta ne…..
Mama ce ta katse Mai tunani tare da bashi maganin tana fad’in tashi kasha Kafin kayi baccin
Amsa yayi yasha domin baya son magana Sosai, domin baiyi niyan shaba, danshi yasan maike damunshi, amma yasan In baisha ba mama zata matsa
Bayan yasha maganin ya kwanta tare da lumshe ido, amma baccin Ya’ki zuwa, ji yake idonshi na mishi zafi Sosai ga kanshi dake faman sarawa kaman zai fashe dan azaba
Wasa wasa usman yau kwananshi uku baya fita, mama tayi tayi yaje asibti ya’ki sai yace jikin da sauk’i, kuma kullum yana kwance Indai ya tashi Toh sallah yaje
Usman duk yanda yaso ya cire tunanin amal ya kasa, gaba d’aya shida kanshi yana mamakin yaushe ya fara son yarinyar da bazai taba samu ko a mafarki ba haka?? Ya tabbata koda mutuwa zaiyi amal tafi karfinsa har abada, wlh koda zaiyi kud’i Sosai ya tabba kallon driver zata dinga mishi, ido ya lumshe tare da fad’in lallai Talaka akwai sama kanshi abunda yafi karfinshi , inko ban cire wannan Abun ba zan mutu ba’a San na mutu ba kam, yayi k’okarin ya cire abun amma yaki ciruwa ga bikinshi dake gaba towa, shi har tausayin Sadiya yake Sosai yanda take masifar sonshi, kullum ta kirashi kuka takeyi akan ya’ki bari taxo ta ganshi, yau dai ya amince zata zo, shima saida Mum d’inta tayi magana akan tare zasu zo
Wajan k’arfe 2 motarsu ta tsaya kofar gidansu Usman inda mum din sadiya tun daga kofar gidan ta Fara sarewa tare da fad’in y’arta ta kwaso tsiya
Wani abu saida suka shiga, duk da an gyara gidan bata ga wannan kwatar ta da d’inba, inda ta gani saiya??
Mum din sadiya gaba d’aya ji tayi bata son zama amma dai ta daure ta zauna
Inda suka Kawo mai kayan fruit da yawa tare dasu abinci
Mama ta tarbesu hannu bibbiyu, tare da Kawo musu abinci amma Mum din sadiya ko kallo kayan da aka kawo basu isheta ba, inda Usman ya fito tamai ya jiki sannan tayi musu sallama ta fita Mota
Ita dai sadiya taci abincin zuciya daya tare da damuwa da yanda taga usman ya rame yayi duhu lokaci d’aya
Kallon mama tayi tare da fad’in mama ya kamata yaje asibiti, yace baije ba, Nayi Nayi yaje ya’ki
Mama tace ai yana da kafiya, saiya zauna ciwo yaita cinshi ai jiki magayi, amma mutun ya zauna da ciwo bazai je yaga likita ba
USMAN yace mama nafa warke gobe zan fara fita inna Fara fita zaku tabbatar na warke
K’aran wayar Sadiya ya hanata magana, ganin Mum d’inta ce yasa ta d’aga
Mum din tace bazaki fito daga wannan kangon ba kizo mu tafi……
Sadiya murmushin Ya’ke tayi dan kar su gane, tare da fad’in Bari mu tafi
Zan zo da Dr in ba zaki hspt ba, sadiya sallama tama mama cikin girmamawa tare da fita USMAN ya rakata
Mama gaba d’aya abunda mahaifiyar sadiya tayi ta lura, inda taji gaba d’aya jikinta yayi sanyi da lamarin, domin tasan ba komai yasa tayi hakan ba sai dai kyama da kuma ganin yanda suke rayuwa
Bayan sun fita sadiya ta shiga mota Bayan Usman yayi ma Mum dinta godiya
Bata kulashi ba sukai gaba
Inda Mum din sadiya ta Fara fad’in yanzu a wannan gidan dama yake Yaron??..
Wlh sadiya kinyi Asara Indai kika auri wanda ya fito daga wannan kangon Dan bazan kirashi gida ba, kina kyakyawa gaki da aiki Mai Kyau lecturer amma ki k’are da dan gidan malam wance saboda Asara da rashin mafad’i……
Sadiya tace haba Mum ni Ina sonshi g…..
Fat takai mata duka a baki tare da fad’in Yimin shuru sha sha sha mara hankali, ai jiki magayi za kiga so wlh Indai aure gidan tsiya ne gaki gashi nan ai, kalli gidansu?? Ga shegen mak’o yana aiki a company d’in alh Sulaiman Ltd amma kalli gidan da suke zaune, dama sabon Fara samun kud’i ne dole Ayi tsimil mila…
Sadiya babu abunda take sai kuka domin har cikin ranta tana jin zafin abunda mahaifiyarta take fad’i a game da usman din…….