AMAL
CHAPTER 5
A haka har suka k’arasa gida inda Mum din sadiya keta faman mita akan ita wannan aure gaba d’aya ya fitar Mata a rai, tare da fad’in munanan kalamai akan USMAN ….
Sadiya dai kuka take tayi inda daga karshe taga Abun yayi yawa yasa ta fara fad’in Mum karki manta shifa wannan arzikin na Allah ne, sannan irin namijin da kike so in aura tun tuni ban samu ba, gashi garin biye ma shawaranki har yanzu Banyi aure ba, karki manta na girma a gida,kuma kwata kwata usman shekara nawa ya bani?? Ya kamata ki jinjina masa domin aurena da zaiyi…….
Rufe min baki mara hankali, ke yanzu har kina ganin baki da wanda zai aureki in usman ya fasa???
Toh Bari kiji Idan kina tunanin wannan shirmen Toh ki daina, domin a yau yace ya fasa zan had’aki da irin mijin da kike so, ba sabon kud’i ba irin wannan saurayin naki ba.
Sadiya tashi tayi Fuuuuu tayi cikin d’akinta domin bazata iya sauraran wannan Abun ba ko kad’an, domin har cikin ranta takejin abunda Mum d’inta take fad’a akan Usman din
An fara hidiman bikin Usman da sadiya Wanda Mum d’inta gaba d’aya ta cire hannunta a ciki, Ma’ana bata wani sakin jiki sosai tana hidiman bikin, Abu d’aya takeyi shine dinner din data had’a wanda wannan tasan dole kawayenta suzo shine kawai take aikin shi dakyau
Usman gaba d’aya hidima yakeyi inda Alh Sulaiman ya bashi gudun nawa Mai tsokan gaske, har usman saida yayi mamakin wannan kud’in
Sanda aka Kai akwati, ranan wanda suka kai akwati sun ga wulakanci, sai dai ma an dan raga musu wai nan tunda Anga yasa kaya masu kyau da tsada…..
Duk yawan kayan da suka kai, domin akwati biyar yayi dai dai karfinshi, amma ya zuba kaya masu tsada, dubu biyu Mum din sadiya tace a basu, wai ai matsiyata ne, komai aka basu za suyi murna, haka aka basu 2k babu irin kayan ciye ciyen da ake badawa na kai kayan akwati
Koda y’an kai akwati suka koma Gida, Wata matar dan uwan mahaifin usman take fad’ama Mama irin abunda akai musu
Murmushi mama tayi tare da fad’in suyi hakuri ai dama shi aure a gaji haka, dole sai Anga abunda ba’a so, sai anyi hakuri
Wannan maganan da mama tayi shine ya kashe bakin kowa
Biki ya rage sauran kwana biyu akayi hadaddiyar dinner daya tara manyan mutane, wanda suka amsa sunansu, ciki harda Alh Sulaiman da hjy rabi , ita kam Amal ban tunanin tasan zaiyi aure domin ita dashi da babu duk d’aya ne, ita burinta a kullum shine ma Dad d’inta ya koreshi taga ya wulakanta a duniya
Anci ansha inda ango da Amarya suka sha kyau, sai dai ango yanda yake kaman dariyan Ya’ke yakeyi, domin shi gaba d’aya ya rasa Mai yasa baya jin dad’i ko kad’an, haka dai har kowa ya watse
USMAN shine ya Kai sadiya gida, inda bayan sun k’arasa take cemai naga kaman wani abu yana damunka koh??
Kallonta yayi tare da fad’in kaman ya?? Mai kika gani??
Tace banga komai ba, kawai dai haka jiki na yake bani
Murmushi ya sakar mata tare da fad’in babu komai , sometimes ina tunanin skul ne, sanda kike zuwa kice in koya miki Abu
Story continues below

Dariya tayi Sosai tare da fad’in oh rayuwa kenan, ashe zamu zama Mata da miji ikon Allah kenan
Murmushi yayi tare da fad’in hakane, tabbas ikon Allah ya wuce wasa, sai kayi ta zama da mutum ashe da matarka kake baka sani ba, sai dai in lokaci yayi
Wani irin dariya tayi tare da fad’in Aida Nasan kaine zaka zama mijina, da wa innan y’an matan masu zuwa suna fakewa da ka koya musu Abu dana hanasu su dinga min magana da miji
Dariya yayi tare da fad’in ikon Allah, fakewa suke kenan??
Sadiya tace kwarai kuwa, Usman ko nima Ina cikin su lokacin, na Fara Sonka tun Ina skul, sai dai abunda na lura a lokacin kai mata basa gabanka sannan baka da lokacinsu, sannan abunda yasa ban matsa ba lokacin Nasan iyayena ba za suyi min aure ba, dole inna Gama degree saina k’aro karatu Wanda kuma gashi nan, amma da yake Allah yasan irin son da nake maka sai gashi ya had’a mu sanda na cire Abun a raina, ranan dana ganka kaida wannan yarinyar Wlh ba k’aramin kishi naji ba, amma da tace ita ba matarka bace saina ji dad’in hakan….
USMAN yace lallai kam, ashe an dad’e ana so na??
Ido ta rufe tana dariya
Sun dad’e suna fira Kafin yace ta shiga cikin Gida dare yayi
Sallama tayi mishi sannan ta fita tayi cikin gidan kai tsaye , tana shiga ta tarar da Mum dinta zaune a falo..
Sadiya tace mum baki kwanta ba??
Mum din ta balla mata wani shegen harara tare da fad’in sai yanzu kuka gama ya barki kika shigo??
Sadiya tace ban gane ba?
Mum din tace taya zaki gane, tunda kin zama Wawiya mara hankali, kin zama Mara wayau, ke har yanzu kina kan bakanki koh
Tace Mum ki fad’amin Mai hakan ke nufi domin ni Wlh ban gane ba
Mum din tace sadiya ke yarinya ce, koda kin Kai shekara d’ari Toh a wajena ke k’araman yarinya ce, sannan bazaki taba hango abunda ni zan hango miki ba, wlh babu wanda zai so yaga nashi cikin wuya, ni nafi kowa sanin zafinki duk wani wanda zai soki Toh a baya na yake…… Dan shuru tayi sannan taci gaba da fad’in, kin d’auki son duniya kin d’aura ma wannan yaron, gaba d’aya bakya gane dai dai da kuma abunda ba dai dai ba, wlh Ina hango miki irin halin da zaki shiga nan gaba, sannan karki manta Talaka duk kud’in da yayi wannan tsiyar tashi tana nan a cikin ransa……
Tashi sadiya tayi tare da fad’in haba Mum haba Mum, Waye ake haifa da arziki?? Kowa da kike gani saida yazo duniya ya samu, karki manta duk masu kud’i da kike gani yanzu da yawa talakawa ne, babu abunda basuyi ba na wahala Kafin daga baya Allah ya basu dukiya, sannan mum shifa arziki da talauci duk na Allah ne, wlh zan iya zama da usman koda baida komai, dan Allah Mum ki barni naji na gani zan zauna dashi komai zaiyi min bazan ce komai ba…..
Mum din tace haka kika fad’a?? Kenan ya fini a Wajanki koh!?? Har Kike fad’amin magana sabo dashi, lallai sadiya Wlh na tabbata nan gaba za kiyi dana Sani sai yasa nake guje miki hakan, har yanzu lokaci bai k’ure miki ba, za’a iya fasa wannan auren a maida mishi da kayan tsiyar shi….
Sadiya tace Mum wannan kayan da kike kira kayan tsiya yafi min komai da nake dashi….. Sai kuma ta saki kuka Tana fad’in Wlh Mum zan zauna dashi koda baida komai Nasan Allah shine mai azurtawa, kuma insha Allah bazanyi dana sani ba, domin da zuciya d’aya nayi wannan auren, karki manta yanzu koda Mai mugun kud’i na aura Allah zai iya kwace dukiyar daga hannunshi ya Mai dashi Talaka, shi kuma wannan Mai zaki ce?
Mum Dan Allah Kimin fatan alkhairi tare da addu’an zaman lafiya, shi nake bukata daga gareki
Mum din dariya tayi tare da fad’in lallai soyayya ta rufe miki ido, bakya gane komai, toh Bari kiji tunda haka kika fad’a shikenan badai auren Talaka ba wanda ya fara samu yanzu ba? Gaki gashi ina mai tabbatar miki idan kud’i suka gama jik’ashi zaki gane abunda nake fad’a miki
In bakiyi wasa ba saiya k’aro miki kishiya in bakiyi wasa ba Ya sakeki ya Mai daki bazawara, amma tunda kince kinji kin gani in wani abu ya faru babu ruwana
Sadiya d’akinta ta nufa Domin bata jin zata iya magana, tunda taji an kira zai K’ara aure in batai wasa ba, lallai sadiya tana da mugun kishi, ba zata iya bud’e ido yau taga usman ya k’ara aure ba, ido ta lumshe tare da fad’in hakan bazai taba faruwa ba, domin bazan jure ba, lallai USMAN nawa ne shi d’aya, sai yasa Allah ya bani shi bayan mun d’auki lokaci bamu had’u ba, kuma gashi baiyi aure ba, wannan tunanin da tayi shine yasa harta iya samun nutsuwa ta fad’a toilet tayi wanka sannan ta kwanta
Shi kam usman hotel ya nufa domin gidansu akwai ba’ki sannan babu inda zai kwanta, tunda harta d’akinshi akwai mutane
Koda ya isa wanka yayi tare da saka wata jallabiya sannan ya kwanta tare da lumshe ido, gaba d’aya tunanin amal ke damunshi, har tausayin sadiya yakeyi domin irin son daya lura tana mishi, gashi shi kuma zuciyarshi Tana kaishi inda bai dace ta kaishi ba….. Da sauri ya bud’e ido domin baya son wannan tunanin amma gashi ya kasa dainawa
Duk yanda yaso ya tura ma ranshi tsanar Amal domin ya daina tunaninta amma Ya kasa…..
Amal ce zaune tana danna wayarta daga gani chatting takeyi kuma da duka alamu tana fira da fahad ne, domin yanda take wani irin murmushi
Lokaci d’aya wayarta tayi K’ara
D’auka tayi da sauri Tana dariya tare da fad’in kai my dear wlh kasa sai dariya nake tayi……
Daga gefenshi yace haka nake so my princess always inga kina dariya
Tace ngd
Yace baby I miss your lips, I want to kiss you
Murmushi tayi tare da fad’in really
Yace yeah, zanyi tafiya cikin week dinnan
Da sauri tace ina zaka??..
Yace Dubai, sannan zan biya China shima, ina son in siyo miki kayan akwatin ki, guda nawa kike so
Amal wani irin murmushi ta saki tare da fad’in wow my dear, da wuri haka zaka Fara siyayya
Yace eh gwara in siya da wuri saboda a kawo da wuri, kiga abunda bai miki ba
Wani irin murmushi tayi mai cike dajin dad’i sannan tace hakane, ina son akwati guda 36 kaga ko wanne dozen kenan sha biyu sau uku, sannan with car Ina son a rubuta sunana a number din motar a saka millionaire Amal
Dariya yayi tare da fad’in an Gama my princess always as you wish
Ido ta lumshe tana murmushi cikin jin dad’i Sosai
Fahad yace kina ina
Tace home
Yace plz come and see me ina Gidan nan nawa
Amal tace OK gani nan
Bayan ta kashe wayar tashi tayi lokaci d’aya ta shiga cikin gidan tare da d’auko key din mota inda ta fita
Kai tsaye gidan ta nufa inda tayi horn Mai gadi ya bud’e sannan ta shiga
Bayan ta fito ta fad’a cikin gidan kai tsaye domin kofar falon a bud’e yake ma, akan kujeran falon ta ganshi a kwance daga shi sai boxer babu ko riga a jikinsa
Amal wani iri taji amma da yake so sone saita shiga tana fad’in bacci akan kujera.
Jin muryanta yasa ya tashi tare da nufanta ya rungumota yana fad’in baby I miss you alot
Ido ta lumshe domin yanda taji banana dinsa yana dan taba ta alaman a mi’ke take
Fahad yace baby I….. Sai kuma yayi shuru tare da sakinta ya kamo fuskanta yana fad’in always kina k’ara kyau my young millionaire baby
Murmushi ta danyi
Lokaci d’aya yakai bakinshi cikin Nata ya fara kissing d’inta…..
Gaba d’aya Amal wani irin dum taji tare da mutuwar jiki, in fahad yana taba ta sai ta tsinci kanta da kasa hanashi duk da Tana ji a jikinta basa ban dai dai, tana cikin wannan tunanin taji ya kamo hannunta yakai wajan banana d’inshi dake tsaye kyam……….
Ku dunga hakuri da Typing error coz bana editing
Hannunta yasa akan banana d’inshi ya fara shafawa……
Amal hannunta ta Fara k’okarin ja, amma ta kasa domin ba ri’kon wasa yayi ma hannun ba, gabanta sai faman fad’i yake tare da jin tsoro, tunda take bata taba jin tsoro irin na yau ba a rayuwarta…..
Fahad kissing d’inta yake yana shafa banana d’inshi da hannunta….. Lokaci d’aya ya fara k’okarin kai hannunshi kan breast d’inta…..
Wani irin tureshi tayi da karfi, wanda ya matsa baya
Idonshi ya canza launi, domin yana matukar sha’awa Sosai
Amal kuka takeyi tare da fad’in dama haka kake??
Yana k’okarin yin magana tace ban son jin komai, tare da K’okarin fita daga falon
Kamota yayi tare da rungumota yana fad’in am so sorry Amal, sonki yamin yawa sai yasa indai na ganki bana iya controlling kaina, plz forgive me, in kikai fushi dani bazan samu sukuni ba
Kukan da takeyi ya fara raguwa wanda hakan ya tabbatar mishi data Fara sauka… Wannan ne ya bashi daman ci gaba da fad’in Amal Ina sonki da yawa, bazan taba son inga nayi miki abunda zai bata miki rai ba, muddin ina tare dake Indai zan ganki sai inji gaba d’aya bana iya samun nutsuwa wlh sonki ya kamani da yawa, am crazy about you…..
K’asa ya tsugunna tare da kamo hannunta ya ri’ke yana fad’in plz forgive me my young millionaire baby….
Murmushi ta sakar mishi
Hakan yasa ya gane ta huce
Amal tace plz ka tashi
Fahad yace taya zan tashi kina fushi dani
Tace bana fushi dakai, am sorry koda yaushe Ina maka wrong fahimta, ya kamata in yarda kana sona bazaka taba cutar dani ba
Fahad I really love you, sai yasa nake son mu kiyaye har sai munyi aure
Fahad murmushi yayi tare da fad’in hakane baby, zamu kiyaye tare daja mata kumata yana dariya
Itama dariyan ta Fara Sosai
Fahad yace Mai zaki ci??
Tace nothing just kawai Ina Son zuwa Gida I…….
K’aran wayan fahad yasa tayi shuru, inda ya nufi wayan tare da d’auka yasa a kunne ya fara magana kaman haka hello
Ban San mai ake fad’a mishi ba, naji yace what??
Lokaci d’aya kuma ya saki wayar tare da zama ya zauna tare da sakin wayar
Amal kallonshi tayi cikin damuwa tare da fad’in maiya faru??
Kallonta yayi sannan yace nothing muje in rakaki ki wuce din
Kallonshi tayi cikin mamaki, tare da fad’in lafiya kuwa?? Plz fahad tell me maike faruwa??
Fahad yace nothing baby, let go tare da janta sukai waje, har mota ya rakata tare da k’okarin kwantar mata da rai akan babu komai daya faru
Story continues below

Koda Amal ta tafi fahad gidan ya koma yana murmushi wanda nidai ban San kona miye ba kuma…..
A yau dubban mutane suka taru inda aka d’aura auren Usman da amaryarsa sadiya inda aketa San Barka
Kaman yanda al’ada takeyi anyi komai ranan daurin auren sannan a ka zo d’aukan amarya da yamma domin zuwa gidan mijinta
Koda aka Kai sadiya Domin mum d’inta tayi mata fad’a ce mata tayi jiki magayi ai, taje zata gani
Sadiya kuka take so Sosai, domin wannan Kalman ta mahaifiyarta ta k’ona Mata rai, dan babu maraba da tace mata na yayeki ko tace babu albarka na a ciki, sadiya taci kuka Sosai sannan tayi kudirin zama da mijinta lafiya, tare da jure duk wani abu dazai taso domin ita da kanta tasan ko harshe da hakori ana sabawa, balle su da suke matsayin miji da mata
Mahaifinta yayi mata nasiha Sosai tare da tunatar da ita hakurin zaman aure, domin aure gaba d’aya hakuri ne, inda daga karshe yaita saka mata albarka…..
Bayan ankai sadiya gidanta Wanda an zuba Mata kaya na Kece raini, domin an narkan mata da dukiya a wajan kayan dak’i Sosai
Bayan an kaita wanda suka kaita suka fara shirin tafiya, domin ita ba wasu kawaye bane da ita, domin mate d’inta sunyi aure
Aka tafi aka barta ita d’aya daga ita sai halinta, inda kowa ya watse
Usman bai shigo gidan ba sai wajan 10 inda ya shigo da kaza da drinks kaman yanda ko wani ango yake ma amarya a daren farko, wanda ake cema kazan ci in ci hhhhhh, wasu kuma suce ci ki Biyani
Usman da sallama ya shigo cikin d’akin inda ya Tarar da ita ido sun kumbura domin kuka, ba komai take tunawa ba sai Kalman da mahaifiyarta tace Mata wanda Abun ya tsaya Mata cikin rai
USMAN kallonta yayi tare dayin murmushi yace banyi zaton ganin haka ba
Da sauri ta kalleshi
Murmushi ya saki tare da fad’in yeah, I mean kina tare dani kukan Mai kikeyi
Lokaci d’aya ta girgiza kai alaman magananshi ya bata mamaki, domin duk wata amarya tana Wannan kukan indai za’a kawo ta gidan miji, toh amma ita kukan kalaman mahaifiyarta take wanda Abun ya tsaya Mata cikin rai
Lokaci d’aya kuma tayi murmushi tare da cire komai, domin tana burin ta faranta ma mijinta cikin wannan rana, kuma cikin wannan daren wanda ko wani namiji da mace suke buri wato daren farko, first night kenan
Usman yace Kinga gaba d’aya idonki ya kumbura, ya kamata kije kiyi wanka sai kiyi alwaya muyi sallah
Tashi tayi Kai tsaye ta fad’a toilet inda tayi wanka sannan ta fito, koda ta fito bata ganshi a d’akin ba, dan haka ta shafe ko ina da turare a cikin jikinta sannan tasa rigan bacci Shara Shara sannan ta d’aura hijab akai tare da saka zani ta d’aura, Shigowan usman yasa ta kalli kofar
Yace yauwa muyi sallah inda suka fara sallah raka’a biyu domin nuna godiya ga Allah, Bayan sun idar
Yace suje suci abinci
Binshi tayi inda suka nufi falon gidan domin dama yunwa takeji, sunci abinci sunsha, sannan suka dawo, a daren wannan ranan sadiya ta zama cikakkiyar mace inda Usman ya raya sunna da ita
Usman shima ya zama Cikakken mutum domin ya ajiye iyali shima…..
Amal koda ta tafi gida wani irin yanayi ta shiga domin gaba d’aya abunda fahad yayi mata shike mata yawo a Kai, ita yanzu bama ta tunanin halinda ya shiga sanda aka kirashi, ita dai abunda ya mata shike dawo mata
Ido ta lumshe tare da fad’in Ina son fahad amma bazan Bari ya keta haddi na Kafin muyi aure ba, dole in tsare kaina har zuwa sanda za muyi aure….
Story continues below

*2 WEEK LATER*
Alh Sulaiman ne keta sintiri a falon gidanshi, kallo d’aya zaka masa ka gane yana cikin damuwa Sosai.
Shigowan usman yasa ya nemi waje ya zauna tare da fad’in Usman zo ka zauna
Bayan Usman ya zauna, inda Alh Sulaiman gaba d’aya zufa ce ke keto mishi a jiki domin yana cikin mugun Tashin hankali Sosai
Yace Usman gaba d’aya Sun tafi da duk wani muhimman abubuwa na, y’an damfara ne USMAN
Salati usman ya saki tare da tashi cikin tashin hankali inda yake fad’in ka samesu a waya ne??
Alh Sulaiman yace ban samesu ba, wani abokina nake fadama wa, shine yake bani labari, wlh ban taba tunanin haka ba, tunda Nasan company d’insu ashe duk scam ne, a cikin dukiya ta na basu kashi 90 Innalillahi’wa inna ilaihirajiun……
USMAN gaba d’aya kasa furta komai yayi,….. In Mai karatu bai manta ba, akwai sanda Usman yayi fad’a da fahad har yaje ya shigo da wasu ba’ki, wanda fahad ya boye daya gansu, a ranan sun kulla business da Alh Sulaiman Toh sune suka gudan mishi da dukiya ya daina samun su a waya
USMAN sauke ajiyan zuciya yayi tare da fad’in amma wa innan mutanan basa tsoran Allah, amma kayi hakuri Alh insha Allah komai naka zai dawo, nayi maka wannan alkawarin akwai abubuwan da zamu tsara
Alh Sulaiman kallon mamaki yake ma USMAN domin shidai yasan kud’inshi sunsha ruwa kenan har abada
Gaba d’aya Alh Sulaiman ya shiga cikin damuwa, Indai kud’i ne yasan ya rasa amma yana da saura, sannan yana da k’adara Wanda bai taba tunanin zai saida ba
Gaba d’aya duniya ta samu labarin karayan arzikin alh Sulaiman inda ya fad’o daga cikin masu jerin kud’in Africa aka cireshi daga cikin layi
Gaba d’aya company d’inshi wasu har sun daina aiki domin Suna tsoro Kar tun ana biyan salary azo a daina, gwara su Bari kawai su nemi wani duk da Sun San cewa aiki yana wahala, cikin ma’aikatan kalilan ne suka rage
Alh Sulaiman hankalinshi a tashe yake Sosai, kullum yana cikin tunani, usman ne yake kulan mishi da harkokinshi yanzu
Gashi bikinsu Wanda kowa ya sani bai fi sati d’aya da wani abu ba, hjy rabi itace ke gyara amarya, inda take tambayan Amal Wai ina fahad ne?
Amal tace Nima kwana biyu bana samunshi a waya
Hjy rabi tace kaman ya??
Amal tace Nima ban sani ba
Shuru hjy rabi tayi tana nazari domin ita bata gane wannan Abun ba, tasan dai sun biya kudin sadaki gaisuwa sa rana, amma ya kamata ace by now Susan Mai ango ke shiryawa, Anya Wannam auren kuwa??
Gashi bata son yima Alh Sulaiman magana Domin yana cikin wani hali, uwa uba ba wani lafiya gareshi ba, domin yawan tunani ya taba mishi zuciya, Allah sarki, lallai karayan arziki babu dad’i, just imagine ko kaine ka ajiye kud’i aka sace how will you feel??
Balle shi daya saba ri’ke manyan kud’ade amma yau babu saura kad’an, wanda ana gab da a Fara saida k’adara tunda baya fita balle business yaci gaba, sai dai usman da yake dan tayashi, wanda shima ba komai ya sani akan business din duka ba, gashi wanda suka shiga cikin company din domin zuba hannun Jari sun ce suna bukatar kud’insu…..
Gaba d’aya dai Alh Sulaiman ya shiga cikin wani hali, wanda haka dole saida Ya fara saida wasu kaddaranshi a kasuwa
Yau su hjy rabi na zaune sai ga kayan akwati wanda daga hjy rabi har amal babu wanda yasan za’a kawo
Nan hjy rabi ta Fara kame kame Mai zata basu, wata daga cikin masu kawo kayan akwatin tace gashi mun Kawo bama bukatar komai, dan tafiya za muyi
Hjy rabi tace toh Ina zuwa
Matar tace a’a nace bama bukatar komai
Haka suka tafi, hjy rabi kam mamaki abun ya bata wannan wani irin Abu ne?
Za’a kawo kayan akwati basu sani ba, Hmmm Allah dai ya kyauta, ko bud’e kayan batayi ba, saida Amal tazo a nan aka fara bud’e kayan
Akwatin guda 36 ne kaman yanda dai ta fad’a mishi
Amal Sai dariya take gashi an zuba kaya masu tsadan gaske a ciki ga sarkan gwal d’inta dangare, harta a warwaro harda na zinari aka sa mata
Hjy rabi duk da ranta ya baci akan abunda sukayi na rashin fad’a musu, amma ta daure inda aka fara hidiman bikin
USMAN ne zaune a falo yana danna laptop
Saiga sadiya ta fito tana kallonshi tare da fad’in yanzu gaba d’aya baka da lokaci na saina wannan mutumin shida iyalanshi gaba d’aya su kake ma bauta, kazo kaima ka canza aiki
USMAN kallonta yayi tare da fad’in komai nayi ma Alh Sulaiman ban fad’i Ba, sannan ban biya shiba
Mutumin yayi min hallaci wanda bazan taba mantawa dashi ba, yayi min abunda ba kowa zai iyamin ba, wlh bazan taba gudansa ba
Kuma komai zanyi mishi ban biya shiba
Tabe baki tayi tare da fad’in Allah ya taimaka, ita gaba d’aya bata son yana hulda da Alh Sulaiman ko dan saboda wannan Amal din data tsana
Alh Sulaiman duk da baida lafiya ya daure domin shirin bikin amal, inda aka mata siyayyan kayan dak’i masu tsada domin ya nuna ma y’ar tasa Yana Sonta, komai aka siya ba’a kai ba domin basu San Gidan amarya ba, saita tare gashi fahad baya d’aukan waya, ranan data kira ya d’auka shine yake fad’a mata iyayenshi sune za suyi komai shi yana China wajan business d’inshi, akwai matsala Sosai sai yasa baya d’aukan waya
Nan dai taji hankalinta ya dan kwanta, sai yasa bata damuwa yanzu
Ranan daurin aure wanda za’a d’aura a central mosque Wanda mutane suka taru Bayan an idar da sallah aka fara d’aura auren wasu sannan nasu Amal amma babu wakilin ango,
Gaba d’aya Alh Sulaiman ya shiga damuwa, suna nan zaune saiga fahad yazo inda ya shigo cikin masallacin
Alh Sulaiman yace number din…..
Dakatar da Alh Sulaiman yayi tare da fad’in ya isa basai kace komai ba, nazo nan ne domin in fad’a bazan auri y’arka ba, dan na fasa mace Mai nutsuwa nake so Mai kamun kai, sannan daga ranan daka bar wannan driver din ya dukeni baka ce komai ba yasa na gane kai ba mutumin arzi…..
Usman wani Mari ya sakar mishi…..
Nan fahad ya tashi yana shirin ramawa mutane suka rikesu tare da fad’in cikin masallaci ne fah nan
Usman jin haka yasa ya nutsu fahad kam sai fitar dashi akayi yanda yake fusge fusge zai rama
Alh Sulaiman hawaye ya tsinci kanshi dayi
Lokaci d’aya ya kamo hannun Usamn tare da fad’in ya bashi Amal halak malak basai yayi komai ba, Indai ya amince
Usman kallon mutanan wajan yayi wanda suke kallonsu, yace ya amince cikin tausayin mahaifin amal din
Nan aka d’aura aure wanda k’anin mahaifin Usman din da yazo bikin amal da fahad ya amshi auren Bayan Usman ya ciro kud’i cikin aljihu har duba hamsin a matsayin sadaki…….. Hmmm yanzu labarin ya fara………
Bayan an gama d’aura aure nan aka fara taya usman murna, tare da Alh Sulaiman
Bayan sun fita Kai tsaye gidan Alh Sulaiman suka nufa inda akwai mutane y’an biki da suka cika gidan Anata hidiman biki, wanda duk mata ne a cikin gidan ba maza ba, duka sunzo taya su murnan biki
Alh Sulaiman haka ya ratsa ya shiga cikin gidan shida usman wanda sukai d’akinsa kai tsaye, Bayan sun shiga k’iran hjy Rabi yayi a waya tare da fad’in tazo ita da Amal
Ba’a dad’e ba saiga hjy Rabi ta shigo ita da Amal wacce take murna Domin tasan by now ta zama matar fahad, duk da ta kirashi yana ta danna mata busy
Amal ganin Usman cikin d’akin Dad d’inta yasa duk wani annuri dake fuskanta ya dauk’e
Lokaci d’aya tace Dad mai wannan yakeyi a nan??
Alh Sulaiman yace ki sami waje ki zauna
Amal cikin bacin rai tace Dad bazan zauna wajan da wannan ya zauna ba, Dad karka manta ko Waye shi, dahar ka bari Ya shigo maka cikin bedroom only god knows mai zai aikata, tayu harda had’in bakinsa mutanan nan suka cucek…..
Tas ya sauke mata Mari a fuska cikin zafin rai….
Kallon mahaifin nata tayi cikin mamaki tare da fad’in Dad nika mara akan wannan kaskantaccen, akan wannan Talakan ka mareni??
Alh Sulaiman yana K’okarin k’ara marinta usman ya tare shi tare da bashi hakuri akan ya barta yarinya ce
Amal tace ai dole kace haka, tunda ka mallake min Dad, sai abunda kace mishi
Alh Sulaiman wani siririn hawaye ne ya zubo a fuskanshi
Ganin haka yasa jikin amal yayi sanyi bakinta Ya mutu ganin hawaye a fuskan mahaifin nata
Alh Sulaiman yace Amal ban taba tunanin halinki yakai haka ba, har zan baki umarni kiyi shuru amma k’iki yi, nuna Usman yayi tare da fad’in shidai wannan da kike kira Talaka yayi miki rana, sannan wannan da kike kira hala harda had’in bakinsa aka cuceni bazan taba yarda ba, domin na yarda da Usman fiye da kaina.
Usman ya cinye jarabawata da dama Wanda ban taba tunanin zai cinye ba, domin irin jarabawan dana mishi ba kowa zai iya cinyewa ba, amma sai gashi Abun mamaki ya cinye jarabawan cikin sau’ki
Yau fahad yaci min mutunci a bainan dubban jama’a, inda ya tozarta ni, tare da kin aurenki…..
Amal wani irin kuka tasa tare da fad’in Dad anya fahad ne kuwa??
Alh Sulaiman yaci gaba da fad’in amal yau inda kina wajan na tabbata da kin gane Waye shi
Nan ya fad’a musu irin rashin mutuncin da fahad din yayi mishi
Sannan ya k’ara da fad’in Amal daga lokacin da fahad yayi min tujara na tabbata ina Raye ne domin inga aurenki…..
Dan shuru yayi sannan yaci gaba da fad’in Amal nasan ba wani lokaci zan k’ara a cikin wannan duniyar ba, na tabbata ko yanzu na mutu bazaki wulakanta ba domin na bada ke inda za’a ga darajan ki sannan a mutunta ki, Amal ko Bayan raina ban yarda ki saba ma mijinki ba, ina son ki zamo mace Mai biyayya wannan kad’ai za kiyi ki nuna min ke y’ata ce
Story continues below

Hjy Rabi cikin kuka take fad’in haba Alh wannan wani irin magana ne kakeyi haka??
Dan Allah ka daina irin wannan maganan kana tayar mana da hankali
Ita kam amal kasa magana tayi domin gaba d’aya inta fahimci mahaifinta yana nufin ya aura mata aure da wani ba fahad ba, toh Waye wanda aka bama aurenta???
Alh Sulaiman yace rabi kiyi hakuri amma wannan maganan ta zama dole muyi ta
Hjy Rabi kuka take wi wi wi, kaman karaman yarinya
Alh Sulaiman kallon Amal yayi tare da fad’in Amal Ina son kiyi biyayya ga mijinki, sannan ki tuna komai Ya faru da bawa kaddara ne, kana naka Allah na nashi.
Naba ma USMAN aurenki…..
Da sauri ta tashi tsaye tare da fad’in Dad wani usman din???
Mahaifinta yace samu waje ki zauna
Zama tayi tana kallon mahaifinta domin tana son jin wani usman din aka aura ma ita
Mahaifinta yaci gaba da fad’in Usman ga shinan shine mijinki……
Amal gaba d’aya wani irin yanayi ta shiga wanda zan iya cewa bata jin abunda mahaifin Nata yake fad’a, babu abunda take fad’a cikin ranta sai Kalman Usman shine mijinki…… Wani hawaye ne ya silalo mata alaman takaici Wai driver d’inta shine mijinta
Hjy Rabi tace amma wannan fahad din badan arziki bane, Amma babu komai kansa ya cuta, bamu ba, Allah kad’ai yasan mai zai faru inda anyi wannan auren, gwara daya fito ya nuna mana irin halinshi
Alh Sulaiman murmushi yayi tare da kallon usman yace akwai wani gida na, dake aso rock, 3 bedroom ne akwai komai, zaku zauna a can
Usman yace a’ah ranka ya dad’e, ka barshi zata zauna a gida na…..
Amal tashi tayi da sauri tayi bedroom d’inta tana kuka Sosai kaman ranta zai fita, wai driver aka aura mata a matsayin miji
Alh Sulaiman binta sukai da ido sanda ta fita, sannan ya kalli Usman yace Aida can kuka zauna, sai akai kayanta can, duk da akwai kaya cikin gidan
Usman yace a’a ranka ya dad’e zansa a gyara gidan da nake sai a ware mata dak’i d’aya, Usman ya fad’i hakane domin gudun gorin Amal, domin ya tabbata indai ya yarda suka koma gidan da mahaifinta ya basu ya shiga uku
Alh Sulaiman ganin Usman din ya nuna yafi son su zauna a gidan nashi, yasa ya amince tare da fad’in yaushe za’a kawo ta??
Usman kanshi na k’asa yace zuwa jibi, gobe za’a gyara mata d’akin da zata zauna a ciki
Nan Alh Sulaiman ya furta Allah ya kaimu, inda Usman da Hjy rabi suka amsa da Ameen sannan ya musu sallama…..
Har zai fita Alh Sulaiman ya kirashi tare da fad’in Usman dakata
Usman tsayawa yayi tare da komawa ya zauna inda suke zaune
Alh Sulaiman yace usman ina so ka d’auki matarka ka tafi da ita
Usman na k’okarin magana…..
Alh Sulaiman ya dakatar dashi tare da fad’in kar kace komai, kana da gidan iyaye zaka iya kaita, sannan zaka iya zama da ita a gidan da nace na kwana biyu
USMAN shuru yayi lokaci d’aya yace Toh domin baya son musu da Alh Sulaiman dan haka yace zasu tafi tare din, inda yace zai ajiyeta a gidan alh Sulaiman na wani lokaci
Alh Sulaiman jin haka yasa yayi murmushi tare da saka ma usman albarka
Inda yace ya tafi za’a kawo amarya gidan Bayan ya fad’a mishi address din gidan, nan usman ya tafi kai tsaye gidan mahaifiyarshi ya nufa duk da yasan k’anin mahaifinshi ya mata bayanin abunda ya faru
Koda ya isa da sallama ya shiga cikin gidan
Inda mahaifiyarshi ta amsa tare da fad’in Usman ne??
Yace eh mama nine
Shiga yayi tare da zama ya gaidata cikin girmamawa
Amsawa tayi tare da fad’in a kawo maka abinci ne??
Yace a’ah Alhmdlh, tare da sakin wani nishi sannan yace, mama Nasan an fad’a miki abunda ya faru??
Tace eh an fad’a min, tun d’azu nake ta mamaki, kaida bakwa shiri da yarinyar taya zaku zauna matsayin miji da mata??
Duk da na lura Kai kana Sonta. ……
Da sauri ya dago yana kallon mahaifiyar tashi ya akayi ta gane yana son amal
Mama murmushi tayi alaman duk yanda yakai da boye Abu itafa ta haifeshi tafi kowa sanin halinsa, tafi kowa sanin Waye shi, kaf duniya babu wanda zai iya fad’a mata Waye Usman ya fad’a dai dai kaman ita
Kallonshi tayi tace ita sadiya din ta sani??
Yace a’a bata sani ba, nake tunani
Mama tace ya kamata kaje ka fad’a mata abunda ke faruwa, domin inaga gwara ta faraji a bakinka akan wani ya fad’a mata
Yace Toh mama
Inda mama ta fara mishi nasiha akan yayi adalci sannan yaji tsoran Allah
Inda ta nuna mishi komai na duniya dan hakuri ne, na tabbata Amal bata Sonka amma ina son komai zatai maka kayi hakuri tare da tuna halaccin mahaifinta a gareka
Yace insha Allah mama tashi yayi ya mata sallama inda ya isa Gida Kai tsaye…..
Koda ya shiga a falo ya tarar da sadiya tana kallo, tasha riga da wando fuskanta tayi makeup tayi kyau dai dai misali
Ganin Usman ya shigo yasa ta tashi da sauri tayi hugging dinsa tare da fad’in tun d’azu nake kira baka d’auka ba
Yace au Wlh wayata a silent yake, gaba d’aya tun sanda na shiga masallaci nasa a silent ashe ban cire ba
Tace haba nayi mamaki, ince kodai wani abu ya faru ne, ashe lafiya
USMAN hannunta ya kama tare da zaunar da ita akan kujeran falon, kallonshi tayi tace my dear muje kayi wanka sai kaci abinci
Yace a’a Ina son muyi magana ne akan wani abu mai muhimmanci
Tace lafiya kuwa?? Idonshi na kanta cikin damuwa take tanbayar shi
Yace sadiya Ina son Kimin uzuri, sannan ki d’auka komai ya faru da bawa haka Allah ya tsara, karki manta Komai da d’an Adam yakeyi a rayuwa Allah ya riga ya tsara …..
Sadiya cikin damuwa tace hakane, Nasan haka dan Allah fad’amin mai ya faru?
Nan usman ya fara bata Labarin abunda ya faru boye mata komai ba…..
Tashi tayi tsaye Tana mishi wani irin kallo
Ganin haka yasa ya tashi shima tare da kamo hannunta yana k’okarin janyo ta jikinshi
Da sauri Taja jikinta tana fad’in dama na sani, dama na sani , abunda nake tunani dama kenan, gashi ya tabbata, sai yasa suke janka a jiki, wlh bazan yarda ba sai kuma ta saki kuka tana fad’in ka cuceni
Lokaci d’aya kuma tasa dariya Tana fad’in nasan wasa kakemin bazaka k’ara aure ba tare da sani na ba
Kamo mishi hannu tayi tana fad’in plz karka k’aramin irin wannan Wasan kaji my dear
USMAN gaba d’aya tausayin sadiya ne ya kamashi Sosai, lallai sadiya Tana sonshi da yawa
Kamo hannunta ya kar’ayi tare da matse su yana fad’in sadiya abunda nake fad’a gaskiya ne, dan Allah ki fahinceni….
Da karfi taja hannunta tayi ciki da gudu tare da rufe kofar d’akinta ta Fara jefar da kayan d’akin tana kuka…..
Usman jin haka yasa ya nufi kofar yana buga mata alaman ta bud’e amma ina bama jinshi take ba sai jifa takeyi da kayan d’akin, gaba d’aya maganan mamanta ne yake mata yawo a Kai, lallai namiji bad’an goyo bane, lallai usman yaci amanarta……