AMAREN BANA CHAPTER 2

AMAREN BANA CHAPTER 2

 Tana kwance a kan gadonta sai aikin karanta sakwannin Saleem takeyi a wayarta akwai wani wanda take jin dadinsa shi take sake karantawa “Lady with the red dress Kin san wani abun dariya? Duk da na barki a Abuja amma mafarkinki da tunaninki suna hanani bacci a Yola.” Nan tayi murmushi ta tuno lokacin da ya makala mata wannan sunan ta sa wasu kayane jajaye Anarkali suit, sukayi mata kyau sosai, shi kenan kullum sai ya dame ta wai bata taba masa kyau kamar na ranar ba. Dama gashi da maitan son abubuwan India. Kusan wannan lokacin akayi zabe, kullum hirar su yanzu akan siyasa ne kasancewar Daddy ya tsaya neman senata a Adamawa. Da ikon Allah kuwa ana gama zabe Daddy ya lashe wannan kujerar, ai murna ba a magana ranar har sai da su Momi suka ji saboda wani irin murna takeyi kowa ta samu sai ta rike hannunsa ta fada masa, Daddin Saleem yaci Senata. Duk da haka koman su na tafiya sumul da Saleem babu wani canji, sai ma wani kara ji da juna sukeyi domin har maganar aure yake mata wasu lokutan. Ko wani lokaci kuma ya samu to zata ga ya dire a Abuja saboda ya ganta, wataran da kanwarsa karima yake zuwa duk da ta san Rumaysah amma sai da suka sake wani shakuwa tukun. Haka nan duk ‘yan gidan ba wanda bai san Rumaysah ba, bare Mami kam da aka saka mata hotonta a screensaver wai tana kallon hoton surukarta. Ranar ya zo a irin haka ne yake mata hirar yanda dinner din aurensu zai kasance, “Kin san wani abu Rumy?”3 Kai ta kada masa yace “Ranar dinner din mu ba, high heel zaki saka saboda fuskarmu yayi daidai.” NAn da nan ta rufe fuskarta, “Ke kin faye kunya kaman wata bafulatana.” Tana murmushi tace” To ai kunya adon mace ne” “Haka ne kam, na yarda da ke.” ************ “Gaskiya likita wannan barna ne, wani irin abu ne haka Yaya Lamido suna gani zasu barshi? Wato ya raina wanda aka gina a ta bayan kenan, ka duba irin kudin da kuka tusa don ku musu gidaje. Da farko ya bada excuse gidan da yake haya yafi kusa da ofis dinsa, yanzu kuma me zai sa ya tusa miliyoyi yace ya sayi gida inbanda almubazarranci. Don shi yana ganin kansa bature bazai iya zama cikin mutane ba ko? Mu namu ‘ya’yan ai a ciki suke zaune, ko an fada masa daga yin shekaru hudu a turai ne mutum yake zama bature?” Abba yayi shiru yana ji har ta gama “Ke ina ruwanki? Ina ce baki so ki ganshi daga shi har uwarsa to ya miki nisa yanzu ba sai hankalinki ya kwanta ba? Idan abun alkhairi ya samu mutum idan bazaka masa murna ba sai ka ja baki kayi shiru don hassada yana cinye kyawawan ayyuka.”4 Jin haka Hajiya Atika ta san Dr. ya mata iyaka kenan sai ta ja bakinta tayi shiru. “Ni daman ba wannan bane ya kawoni, list ne ‘ya’yanka suka karasa yi, saboda a samu a gama komai ba sai lokaci ya karato ayi ta samun matsaloli ba. Nayi tunanin tunda za ayi nasu Khadija me za hana a hada gaba daya da na su Radiyya da Rumaysah, sai ayi gaba daya a huta.” Abba ya karewa littafin kallo, don yafi karfin takarda “Eh, ku huta ni kuma ku karni ko? Atika idan ba dai kawukan mutane kuke so na sayar na samo kudin nan ba, banga yanda kuke son nayi ba. Wani irin hauka ne wannan? Kinga ba zancen wani dogon bayani, duk wani abun da kika ga kin rubuta ki san yanda zaayi ki rage shi domin kashi daya bisa uku zan iya badawa, shi dinma tukun sai na duba na ga ko da hali, wannan fa ba a zo batun kayan sawansu ba da hidimar lokacin bikin na su abinci da sauransu, sannan ga kayan al’adu na gara da za ayi. Kasheni kuke son yi? Ko asibitin zan sayar na sama muku wannan kudin? Ni fa bana son karya a al’amurana don haka idan karya kuka sa gaba, bismillah kuje kuyi tayi. Ni dai na fada miki ehem. Kun iya cewa wasu suna almubazarranci.”5 STORY CONTINUES BELOW Jikinta a mace, rai a bace ta mike ta bar falon, “Mutum abu ya zama dolensa amma sai yayi ta mita a kai, a bisa wani dalili, dadin abun ma ba zaman haka nakeyi ba, ai nima zan iya wasu abubuwan. Kuma wannan dole ka bayar ko za kayi amansu ne” Haka ta ci gaba da sababi ta je daki ta ajiye takardar list din kayan dakin yaranta Khadija da Khamsa’u, a da harda Radiyya da Rumaysah amma yanzu ta soke nasu tukun. Tunda yanzu bikin manyan ta sa a gaba. Rumaysah ko tana ta gabzar karatu tunda masoyi yayi nisa, sai dai idan ta baro makaranta su sha soyayyarsu a waya, ta sha masa korafin tayi kewarsa. Hakuri yake bata kasncewar can ma karatun nasu yayi zafi. Ita kam Allah ya gani, bata bawa kowa fuska ba, ba wai don rashin manema ba sai dai kawai zuciyarta kacokam ta dauka ta damkawa Saleem1 Suna zaune a kan benci ne ita da su Firdausi sai ga su Umar sun nufo su aka gaisa sannan Umar yace “Firdausi zo ki min rakiya wurin cin abinci.” gaba daya akayo musu caa “Haba babana son kai haka? Sai ka manta Daughter wato yanzu Firdausi ake yayi ko?” “Tab na isa? Tunda kince haka kema taso muje ki zabi abunda ranki yakeso.” Da haka dai kaf din su suka rankwafa suka tafi, bayan sun fito ne kawai Rumaysah tayi arba da Saleem a gindin bishiya nesa da su kadan, tsabar farin ciki ta rasa me zatayi daya, kawai sai gani sukayi Saleem ya bude mata hannayensa alamar ta isa, nan suka sa musu tafi, kafin su ankara duka friends dinsu sun watse a wurin. Ashe su Umar sun san da zuwanshi plan sukayi don taje wurin. Cikin sassarfa ta karasa amma ta matsa gefe batayi yanda yake nufi ba.6 “Kin gwaleni ko kina so su Umar su min dariya.” Murmushi tayi sannan tace “Ashe daman kana hanya shine ko ka fada min.” “Hmm, kawai naji na maki bazata ne, idan kuma bakiyi murnar gani na ba sai na koma yanzun nan. Dama ke nazo gani.” “A’a yi hakuri me yayi zafi?” Nan suka ci gaba da tafiya har suka samu wuri sosai suka kafa hirarsu. Suna zaune da Saleem sai ga Faisal, wani dan Kano da ya nacewa Rumaysah, wai yana so suyi magana. Ya matsa gefe, don shi sam ya zaci ko karatu suke da Saleem don bai sanshi ba kasancewar yana gaba dasu a aji. Don ‘yan ajinsu kaf sun sansu musamman wanda suke tare tun rems. Cikin Ikon Allah sai taji Saleem ya damki hannunta ya daure fuska “Ina kike da niyyan zuwa?” “Ka sake min hannu na yi masa magana, kai ma ka san ban iya wulakanci ba.” “Wato daman haka kikeyi ko? Yau Allah ya nuna min.” Ranta ya baci don ita tunda ya tafi bata taba kula kowa da sunan soyayya ba. Cikin jin zafi ta fincike hannunta, ta isa wurin Faisal bayan sun gaisa ne tace “Don Allah kayi hakuri, ina da bako ne. Wani abune?” “A’a kawai kan maganarmu ce ta ranar amma naga kaman bakon naki baya son mu tauna, idan kin bani dama sai nazo gida muyi magana” Murmushi Rumaysah tayi sannan tace “Kaman yanda na fada maka kayi hakuri na riga nayi wa wani alkawari, idan bazaka damu ba.” “Ko shine wancan naga sai wani cin magani yakeyi yana muzurai sai cizgar kasa yakeyi.” Murmushi Rumaysah tayi Faisal yace “Shi kenan, zan baki lokaci kiyi tunani dai, sai anjima ki koma gun bakon ki kafin ya zo ya tada fada a nan.” Tana zama a gefen Saleem ya kawo hannu kaman zai bugeta sai kuma ya buga bencin. “Rumy, daga yau bana son na kara ganin ki da kowa, saboda wallahi ban san me zan iya yi ba idan na ga hakan, ke ma kin san bana so.” “NAji, kayi hakuri amma ka san sha’anin dan Adam idan ba ka bi da mutum a hankali ba sai kaga ana ta faman samun matsala.” “Ni dai na fada miki.” haka suka rabu baram baram, sai dai ya gagara hakuri washegari har gida yaje suka shirya. STORY CONTINUES BELOW BA abun da Rumaysah take so illa irin wadannan ziyara da Saleem ke kawo mata, da su da littafanta ne kawai masu bata karfin gwiwa su debe mata kewa. Kwarai take da nacin karatu, gashi kuma dama akwai kwanyar don haka tana kokari sosai. Son Saleem ya rufewa Rumaysah idanu ya kai ga idan tayi sallah bata da addu’ar da ta wuce “Allah ya Allah, kasa Saleem ne mijina, ka bani Saleem.” kullum addu’arta kenan bata taba neman zabin Allah.8 Wani lokaci yazo suna zaune suna hira ya tamabayeta “Rumy wai ni kam ki fada min me yasa kike so na alhalin ni ba kowa ba?” Murmushi tayi tace “Saleem, ka san abun da ake cewa unconditional love? To shi nake maka, saboda haka bana bukatar wani dalili da zai sa na soka.”1 Kwarai yaji dadin bayaninta domin ya gama yarda Rumaysah bata da kowa da ya fishi. haka suka sha hirar su cikin nishadi har ya koma Yola.1 Watarana Karima ta kira Rumaysah a waya take shaida mata Fatima yar Saleem bata da lafiya sosai don har ta bar gidan mijinta tana jinya a gidan Daddy, sickler ce. Don haka Rumaysah ta tuna wani lokaci da Uncle dinsu ya rasu musamman ya turo Karima ta dauketa taje ta gaida matan uncle din, wannan yasa Rumaysah ta samu Abba ta fada masa tana so taje ta dubo ta. Abba kuwa yayi na’am har ya hadata da Radiyya suka tafi tare. Nan suka hada sha tara ta arziki suka rike mata. Wannan ne karo na farko da Rumaysha taje gidan su Saleem, Mami kam dama ta santa a hoto. HAnnu bibbiyu aka tarbesu, suka gaida mai jiki sannan suka koma. Ko da sukayi waya bata fada masa taje gidan Daddy ba, suna cikin hira tace “Yaya Yola, hope dai karatun ake ba kallon babes?” “Tabdi, ke din ce har zaki ce kar na kalli babes bayan a gabana kike hira da samarinki?” Rumaysah na da zafin kishi don haka ta zage tayi ta kare kanta tace “wato kenan akwai babes din kenan.” “Hmm ke din nan naga alama kishi ma ya miki yawa, anya idan mukayi aure zaki barni na kara mata kuwa? Don gaskiya ni ina da sha’awan aure ba da ke kadai zan zauna ba.”2 “To akaina zasu zauna ne?” “Rumy kenan, wato ke dinnan ba, irin mata masu shiga rai din nan ne.” Murmushi tayi cikin jin dadi. Anayin hutu kawai sai Saleem ya taho da wata sabuwa, har gidan Abba yaje ya sameta ta inda yake shiga ba tanan yake fita ba wai akan dalilin me zata je gayar da yarsa? Abun ya bata mamaki kwarai a ganinta kyautatawa ne, “Na gode Allah don Shi nayi ba don kai ba da shikenan ka gwale ni a banza.”9 Abu guda da ta soma kula kawai da shi shine, Saleem ya fara mata tamkar ko don mukamin Daddy take son shi ko wani abu, bayan ya manta sai da suka dulmiya a soyayya sannan Daddy ya zama senata. Ta danne zuciyarta suka shirya, nan ne ta dago masa maganar aure. Dariya yayi yace “Ina ce munyi wannan maganar, yanzu yaya zan rikito maganar aure? Gaskiya na fi son na gama karatu Daddy ya sama min aiki, don bana son dogaro da komansa kin san sha’anin gidan namu.” Jin haka yasa ta daga masa kafa bata sake masa magana ba, amma ba wai abun baya damunta bane. Don haka ta dukufa kawai cikin istihara wanda ta taba gani a wani litafin addu’o’i.7 ************* Tana kallonsu sai shirye shiryen tafiya suke tayi, ita kuwa ranta a cunkushe don jiya sun bata da Saleem a waya, daga windon dakinta ta hango su suna shiga mota zasu airport saboda tafiyarsu Dubai. Bata ko raka su ba, tayi zamanta a daki sai bayan sun tafi ne ta ga kulewar motar tasu sai ta tafi falon Abba. A falon Abba take zaune fuskar nan a murtuke. Ya zauna a kasan kafet, yace “lafiya dai naga fuskar baby na a murtuke?” Sauka kasa tayi itama tace ” kowa baya so na ABba, kai kadai ne kake so na.” STORY CONTINUES BELOW “Hmm, an bata miki rai kenan, su waye da wannan laifin?” “Banda su Yaya Khans da Yaya Khadija, wai na daina shiga sabgarsu?” “hmm shi yasa ke bakiyi rakiya zuwa airport din ba? Rabu dasu abunki suna aure zan dauke ki ke da Radiyya da Ra’id mu je yawo idan ya warke idan kuma bai warke ba shi kenan.” Hannu ta kai masa suka tafa “Ashe ka gane, shhh kar Momi taji tayi min bakin ciki tace sai ta bimu na san zata aikata.”4 Dariya suka saka, sai kuwa gata ta shigo falon “meye ne kuke ta wani dariya ku biyun nan idan kuka hadu sai a hankali.” “Ba ruwanki, shawara mukeyi kema kije kuyi da su Yaya Khadija, wannan sirrine tsakani na da Abba.”3 “Kwaji dashi ai, naga aure zakiyi muga ta tsiyar.” Zumbura baki tayi tace “Wai sai kuyi ta cewa zan yi aure kaman na cinyewa wani space a gidannan, ni fa ba auren da zanyi ina nan daram.” Abba ya kalli momi domin ko jiya ma maganar da sukeyi kenan. “Kar ki damu ba inda zaki je abunki.” “Yawwa Abba, shi yasa kake burgeni, sai ka fadawa Baffa kar Goggo Shatu ta zuga shi don naji tana wani magana itama wai a hadani da su Yaya Khans a mana aure.” Dariya sukayi saboda shirmen Rumaysah. Ita kuwa Rumaysah tunanin Saleem ne turum a ranta don bata fadawa Abba abun da ake ciki ba asali ma basu san ta dagowa Saleem da zancen aure ba, haka take daurewa take abubuwanta normal. Sun fi sati a haka da kyar ya shawo kanta ta daina fushi. Ita abun da ya fi damunta Umar ya kai goron Firdausi har an sa rana, ga Naja’ah ma an kusa kai nata sai take ga kaman an barta a baya.1 Ganin suna kan seti kusan wata guda babu tashin hankali, yasa Rumaysah ta kara dagowa Saleem maganar. “Wai me yasa ne kam, kika fiye son janyo mana problems ki duba wancan karon irin abun da ya faru.”1 “Ni ba matsala nake so ba, na amince ka gama karatunka amma dai kawai bukata ta ka isa gida wurin Abba su san da kai, ayi duk wani abun da ya dace shine kawai fa. Ni ba auren nake so a yi yanzu ba.” Saboda ita har ga Allah ta soma damuwa da mutanen da suke matsa mata ciki kuwa harda wani lecturer din su, wannan taga ya kamata ace ta san Saleem da gaske yake, kar tayi ta koran mutane hakanan.2 Cikin damuwa yace “to naji, ki bani time zanyi tunani” Da tana jin haushinsa saboda yana yi kaman ita kadaice take son shi, amma da yayi wannan furucin sai ta hasala ranta yayi masifar baci, meye abun tunani akai? Shekarar su fiye da uku tare tun Remedials yanzu ko suna aji biyu amma wai Saleem sai yayi wani tunani? amma kuma tayi hakuri ta danne bacin ranta, ranar Talata suka yi maganar kasancewar yana gari yace mata alhamis zata ganshi in sha Allah. Da ikon Allah ranar Alhamis sai ga Ahmad nan abokin Saleem, har gida ya samu Rumaysah ya shaida mata Saleem wai ya tafi Kano kai kanwarsa asibiti. Tunani ne birjik a ranta shin Saleem bai da waya ne ko kuwa bazai iya zuwa da kanshi ya fada mata tafiya ta kamashi ba? Ahmad na tafiya ta nemi wayar Saleem a ranar, yayi ta ringing can sai wani cousin dinsa ya dauka. “Hello, madam da kanta yaya gida?” A sake ta amsa kasancewar sun saba ta dago muryarshi “Zunnu don Allah bawa Saleem wayar nan.” “Wallahi bacci yakeyi shi yasa ma na daga.” “Zunnurain, ka ta dashi kace ya zo ya karbi waya Rumaysah Umar Attahir na kan layi.”3 JIn yanda tayi magana a zaffafe ne yasa dan uwan yayi saurin tada Saleem. Ya taso ya karbi wayar “Hello, Rumy sorry wallahi bacci ne ya dauken yaya su Momi?” A dakile ta amsa “Lafiyan su kalau, yaya mai jikin naji kun tafi asibiti.” STORY CONTINUES BELOW “Da sauki, follow up takeyi a nan shine Daddy ya hada mu muka taho tare. Kinjini shiru ko?” “Eh, shi yasa na bugo naji dalili. Wai meye ne matsalar magana daya ka gagara fada min kai tsaye sai kayi tunani?” Saleem ya nisa yace “Kema kin san wannan maganar mun riga mun dade da yinta, maganar aure sai na gama school.”2 “Wai baka jina da kyau ne? ni fa bance mu daura aure yanzu ba, introduction kawai nake so.”4 “Abun da nake so ki gane, idan na fara dago wannan maganar Daddy cewa zanyi nayi committing kaina ga abu guda. Kinga kuwa bazaki sa na zabi ko ke ko karatuna ba ko kuwa?”1 NAn take abun nasu ya zamo ta fada ya fada, daga karshe taga kaman abun rainin hankali ya shigo kawai ta fara warware shi. “Daman ba sona kakeyi ba, kawai bata min lokaci kayi tayi. Macucci kawai, azzalumi dan iska mayaudari. Kaje can to ka nemi wata nikam bazan iya ba algungumi.” fashewa tayi da kuka ta rinka surfa masa zagi iri-iri wasun bata san ta sansu ba ma sai yau. Saleem ya runtse idanunsa yace “Rumaysah, me kike so? (what do you want from me?)” “Abun da nake so, shine ka fita daga rayuwata, daga yau bani ba kai, it’s over Saleem, kar ka sake nema na daga yau. Kuma na gode Allah da ban yarda na zubda mutumci na ba, yanda ka ganni haka zaka barni. Mugu! Ka fita daga rayuwata”4 NAn ta tsinke layin ta tsugunna a tsakar daki sai rusgar kuka takeyi, da ta san ita tafi son Saleem akan yanda yake sonta da bata yarda sunyi nisa haka ba, yanzu shekaru uku da tayi dashi duk ya tafi a banza? Haka ta wuni a daki banda aikin kuka ba abunda takeyi bata ci ba bata sha ba. Washegari Saleem yana barin Kano ya isa Abuja ba inda ya tsaya sai gidan su Umar, ya sameshi yana bacci wani irin wawan duka ya daka masa sai da ya firgita. “Wallahi ka tashi duniya ba lafiya”6 Nan da nan Umar ya watsake yace “A ina kuma aka sa bomb?”6 Saleem sai sintiri yakeyi a dakin “Da gaske ba Rumy na bace ta fada min wadancan maganganun, Rumaysah na ta na sona bazata taba zagina ba, Allah wannan Rumyn aljanu sun shigeta she is posessed.” Umar ya dakatar dashi “Wai me kake fada ne ni fa ban gane komai ba.” Nan Saleem ya zauna ya fada masa duk yanda sukayi, kuka kawai ya saka da ya tuna wai Rumaysah ce da bakinta ta ce su rabu, ba ita ba shi. Tabbas Umar ya tausaya masa “kalla, abokina ka kwantar da hankalinka in sha Allah komai zai wuce, ka bari idan ta sauko sai muje mu bata hakuri.” Da dare taje har falon Abba ta same shi, “Ah ah baby na me ya faru ne?” Zama tayi tana murmushi tace “Abba ba komai, dama ina son na fada maka ne na rabu da Saleem fa” Abun ya bawa Abba mamaki yace “rabuwa kuma me ya faru?”2 “Kawai dai Abba na duba naga wasu abubuwan Allah bai sa zasu kasance ba shi yasa naga gwamma mu hakura kawai da juna.” Abba ya kare mata kallo ya ga idanunta a bushe. “Kin tabbata ba wata matsala, naga fa ko kuka ba kyayi” Saboda shi ya san shakuwarsu yasa shi jin mamakin hakan. “Ba amfanin yin kuka akan abun da ya riga ya wuce ya kuma kare.” “To, Allah ya zabar miki miji mafi alkhairi.” “Ameeen Abba na gode.” Hankalinta bai tashi ba sai da aka kwana biyu ba wayar Saleem ba sakonninsa nan ne fa ta tabbatar sun rabu, ai sai wani sabon fage na tashin hankali. Rumaysah ta kade cikin kwanaki biyu banda kuka ba abunda takeyi, wannan abu ya dami Momi. Ko makaranta bata zuwa yanda take da kokarin zuwa. Abun ya basu mamaki. Momi na tsaye a kanta ta dage ta ci abinci ne sai ga su Firdausi da Naja’ah sunyi sallama cikin dakin.2 STORY CONTINUES BELOW Har kasa suka gaida Momi “Ku tashi ku zauna a sama, gwamma da Allah ya kawo ku ko Allah zai sa ta shiga hankalinta tayi wa kanta fada? Aikin kenan duk ta bi ta addabi kanta. ta san zata damu haka me zai sa tace su rabu tunda ta san bazata iya jure rabuwar ba. Ni na gagara gane wannan al’amari. Gata nan ni kam zan fita.” Momi ta kwashe kwanunkan tayi waje. Su Firdausi suka zauna a gefenta a bakin gado duk ta rame banda hanci da ido ba komai a fuskar. “Rumaysah, Momi fa gaskiya ta fada me zai daga miki hankali bayan kuma ke ki ka yanke hukuncin ku rabu? Ki sawa zuciyarki hakuri ki manta dashi” Idanunta a kafe wuri guda kawai take kallo, can sai hawaye suka gangaro mata. Naja’ah tace “A haka kike da shirin zana jarrabawa? Kin san dai karatu yayi zafi ko? Ki daure ki ajiye komai don ki lashe jarrabawar nan.” “Hmm, bazaku gane bane, baku san halin da nake ciki ba. Saleem shine zuciyata ya cuceni ya sa na bashi ita gaba daya ban san yanda zan fara karba ba.”2 “A hankali, ai bamu ce farad daya zaki manta ba, amma a hankali kiyi ta addu’a sai ki ga Allah ya yaye miki. Ki kawar da duk wani abu da kika san zai saki tunanin shi.” Idanun Firdausi suka kai ga kan Mulmulallen abun da ke gefen gadonta wanda Saleem ya bata kyauta. “Fara daga wannan” Nan tayi wurgi da shi jikin bango, amma yana nan daram bai fashe ba, ta karayi da kasa yana nan. Rumaysah tayi yake tace “Karfin soyayyata da Saleem ya wuce duka tunanin ki Firdausi.” Firdausi ta dubi kawarta duk tausayinta ya kamata. Hannunta ta janyo ta sauko da ita daga kan gado. Suka isa makeken wundon dake dakin Rumaysah ta mika mata tace “gashi wurga iya karfinki zuwa can kasa, idan bai fashe ba to na hakura.” Suna wurgawa kuwa abun ya yi Tas ya fashe. Nan take Firdausi da Naja’ah suka soma tafi, har suka sa Rumaysah murmushi sannan kuka ya biyo baya. Da kyar suka rarrasheta sannan suka tafi. Ran monday ta shirya zata tafi makaranta, Momi ta sameta har daki tace “Dubeni nan, Rumaysah. Ina so ki ajiye batun wani Saleem a gefe, kar ki kuskura ki samo carryover saboda wani can wanda bai cancance ki ba, don idan ki ka kuskura kikayi wasa zamu sa kafan wando daya dake a gidan nan, don haka maganar Saleem ya kare daga yau.” Daurewa tayi ta gyada kanta sannan ta fice, amma zuciyarta wani irin suya yake mata. A haka ne suka fara shirin bikin Firdausi da Umar abokin Saleem. Wannan ya dan dauke mata hankali kadan. Ranar dinner din Firdausi kawai sai ga Saleem ya samu Naja’ah ya jata gefe don kuwa kwata kwata Saleem ya ki bari su hadu da Rumaysah a wurin bikin. “Don Allah, Naja’ah ki tayani yiwa kawarku magana, na rasa me yake min dadi na san ko kiranta nayi bazata daga ba, shi yasa na sameki. Ni wallahi ba haka ne manufata ba, yaya za ayi na cutar da Rumy alhali ita ce ruhi na? Ni ban cuceta ba, ki bata hakuri please” Naja’ah ta nisa “Saleem, maganar gaskiya bazan boye maka ba, ka sa kawarmu a cikin kunci marar misaltuwa, zan dai mata magana amma banyi maka alkawarin samun goyon bayanta ba.” Tana fadan haka ya mata godiya sannan ya wuce, gaba daya shima ya lalace. Suna watse taro Rumaysah ta tattare duk soyayyarta ta makawa littafanta, sai dai da zaran ta bude littafi zatayi karatu to hawaye ke jika su cakwaf ba abunda yake damunta irin idan ta tuna alqawarin da tayi wa Momi na ganin ta yi kokari. Daga nan ta sha alwashin sai ta cinye duka papers dinta don ko guda ta fadi to tamkar Saleem yayi nasara a kanta ne. Haka ta dage har ta gama jarrabawarta suka samu hutu. AMma kaman ba Rumaysah ba ta rage walwala da tsokana da surutu haka su Radiyya zasu sata a gaba suyi ta bata baki. Ranar ta idar da sallar Maghriba a gida ta shafa addu’a kawai taji hankalinta ya tashi, taji har yanzu bata huce ba wani irin rudani ya dirar mata, da gudu ta tafi dakin momi ta samu tana zaune kan sallayarta, ta sallame kenan, a hankali ta rarrafa ta isa kan cinyarta ta kwantar da kai ta sa wani irin kuka mai rikitarwa. “Lafiyan ki Rumaysah?” Momi ta tambaya cikin tashin hankali. “Momi, Saleem ya gama dani, ya lalata min zuciya, ya tarwatsa min, banyi tsamman zan kara son wani yanda na so Saleem ba. Ya riga da ya kwace komai nawa.” Momi taji tausayin Rumaysah ta zaunar da ita tace “Look, zaki iya son wani, kuma ALlah zai kawo miki mijinki wanda yake miki matsanancin so. Wanda yafi Saleem komai, kuma a iya sani na Saleem ke da asara. Ki share hawayenki, bai cancanci ki zubar masa dasu ba, kinyi iya kukan da zakiyi dominshi, yanzu kam ya kare. Kina jina? Allah ya miki zabi mafi alkhairi.” Nan take ta goge hawayenta, wani irin tsanar Saleem ya darsu a zuciyarta. ********** Mami ta sashi a gaba sai kallo takeyi “to yanzu daka zuba min ido duk kayi ficifici da kai me kake so na maka? Bayan kai kayiwa kanka, me yasa bazaka nemi shawara ba sai da abu ya kwabe maka? Yanzu kam ya rage naka ai, amma zan fada maka abu guda shin kana tsamman zaka samu yarinyar da zata soka tamkar yanda Rumaysah ta so ka ne? Ai kayi asarar mace” Hankalin Saleem ya kara tashi, da kyar ya samu ya koma makaranta. Rumaysah ko yanzu duk wani addu’arta ya ta’allaka ne akan “Ya Allah ka min zabi na gari, Kasa duk wani nasara da daukaka na rayuwa da zan samu ka sa ina gaba da Saleem, ka daukakani fiye da shi.” Saboda zafin rabuwarsu da takeji. A hankali ta soma hucewa, nan ne ta fara tuno zagin da ta duddura masa, wani irin kunya ya kamata, sam bai dace ba abun da ta yi. Don haka ta kirashi a waya ta bashi hakuri ba don su koma ba sai don ya yafe mata zagin da ta masa ranar. Ana ta shirye-shiryen bikin su Khadija da Labeeb, Sajeeda da Ahmad, Khansa’u da Sa’ad sai kuma Muneerah da Abdullaahi. Shiri dai ba kama hannun yaro musamman Mama ta nemi izini don zuwa Dansadau tayi wasu shirye-shiryen a can sannan ta sanarwa ‘yan uwa da abokan arziki. Tana gidan yaya Hansai ne bayan ta gama duba katin tace “a’ah ni an raba hidimar bikin ke ko kuwa ranar bikin ne Sogiji?” “A’a yaya, har yanzu dai tare ne, hidimar ne dai kowa da nashi, wani abu ne?” “Naga jiya Atika ta kawo mana nata itama to sai na zaci zaku hada shirin tare ne don abubuwa su muku sauki.” Mama tace a ranta Atikan ce zasu hada abu da ita? Ai don ma kar shirinsu yayi daidai ta banbanta nata programs din. “Yaya Hansai hala dai tana so ta bayar da hannunta ne, kin san sha’anin mutune, wani idan ba kai da kanka ka bashi ba sai yace bayi da muhimmanci ko kuwa surutu ya soma tashi.”4 “To, Allah dai ya kawo gyara.” Saboda Yaya Hansai ta san ba wannan bane dalilin don ba wanda bai san irin gaban da Atika ta keyi da Sogiji ba. ******* Al’amarin Rumaysah kuwa kafin abokan Saleem su farga su san lalacewar abun tuni ta zuba shi a kwandon shara don haka ko da sukayi ta sintirin bada hakuri basu ma samu fuksa ba. Yana tsaye a gaban gate cikin motarsa yana jira a bude masa ne ya hangota yau ma a tsaye a jikin motar wani, kuma tabbas ba wanda ya gani bane kwanaki biyu da suka wuce. Shi bai san me yake damunsu ba ace mutum tara samari ya zamo masa ado? Sannan iyayen suna gani ba mai yi musu magana. Yarinya karama irin wannan banda iyayi bata san komai ba, sai tara mutanen banza suna ta zubar musu da mutumcin gida a gari. Tsaki ya ja sannan ya wuce ransa a bace. Bai wani dade ba Mama kawai ya gayar sannan ya koma. Wajen karfe Uku ya tuna ya kamata fa ya je wurin Meena, gaba daya ya sha’afa nan da nan ya danna lambarta.3 “Assalamu alaikum, gimbiya da kanta. Kin wuni lafiya?” Murmushi tayi sannan ta amsa “Lafiya kalau, yaya fama da ayyuka? Kar dai har ka fito” “Alhamdulillah, yaya naji kaman ma bakya gida?” “Wallahi, salon na fito a tunani na kafin lokacin zuwanka na kammala, sai kuma akayi rashin sa’a na samu layi.” “A ina salon din yake?” “K.City plaza ne a Wuse.” “To shikenan, bari na same ki a can, sai ma na zaba miki style din da za a miki.”4 Dariya tayi tace “Kaman da gaske kai din ne zaka shigo inda mata suke?” Murmushi yayi yace “To shi kenan naji, kice musu kar su jagwalgwala min kanki dama.” Cikin nishadi tace “To yallabai. Abun da za ayi me zai hana ka samen a gida kawai da dare?” “To shi kenan, karfe takwas ya miki?” “Takwas yayi, sai na ganka kenan?” “Sai kin ganni, a ajiye min abun dadi.” Nan sukayi sallama, take yaji shi cikin nishadi don kuwa shi kadai ya san me yakeji idan yana tare da Meena. STORY CONTINUES BELOW Yana sallar maghriba ya shirya, a masallacin unguwarsu Meena ya saurari Ta’alim sannan yayi isha’in sa domin karfe takwas a kofar gidan ya masa, an masa iso na girma da karamci, har falon baban aka shigar dashi, can sai ga ta ta fito, cikin shigen atamfa da mayafi, fara ce siririya tana da kyau mai daukan hankali. Cikin fara’a tace “Sannu da isowa.” “Yawwa, gimbiya sannunki da fitowa kema.” “yaya na ganka kai kadai ina Yaya Rayyan?” Murmushi yayi sannan yace “yau ya yayeni, yana can wai yau madam Aisha ta rike shi a gida.” Dariya tayi sannan tace “Maganin sa kenan ai.” Karewa fuskarta kallo yayi yace “Duk salon din ne haka naga har wani sheki kikeyi na daban? Gaskiya sun iya gyara ki rike su da kyau. Su zasu na miki ko munyi aure.” Fuskarta ta rufe cikin jin kunya “Gaskiya sun iya gyara.” ya sake nanatawa. Mikewa tayi ta zuba masa abubuwan da ta kawo kaman jira yakeyi ya dauki cup din ya fara. Yana sa spoon daya a bakinsa ya lumshe idanu “hmm, wannan kuma fa shi sunan sa meye?” “Watermelon granita” ta fada cikin jin dadi, ta san Fawzaan da santi da kuma yabawa sai dai bata masa abu ba to idan ya rinka kodawa sai ta ji kaman har da kari, sai dai ta san da wuya ya mata karya don wannan ba ya cikin dabi’arsa ita dai baya mata sai dai idan ya kama dole.4 “Gaskiya, idan munyi aure shi zaki fara mini, uhmm wannan dadi haka?” Meena tayi dariya. “Ko? ka sha kuruminka har sai ka ture.” “Yawwa wannan fa ya tuna min, yaya maganarmu ne ina ta kwana?” “Magana tana nan, Baba kawai nake jira ya dawo daga tafiyar da yayi na isar masa da maganar.” “To Shi kenan, Allah ya dawo mana dashi lafiya.” Nan ya rinka cika ta da hirar soyayya, kullum Fawzaan yana bata mamaki yanda komansa yake, musamman yanda take masa kallon ustaaz amma idan aka zo maganar soyayya to ita kanta ya sharce ta a guje. Saboda bata iya masa wasu lokutan.3 ****** *********** ********** ******* “Me yasa wasu lokutan kike abunki kaman karamar yarinya ne? Wani irin abune kuma yanzu zaki kawo min maganar kudin dinki? Bayan ankon da nayi wa kawayenki yanzu sai na bada kudin dinki? Banda wasu al’adu kuma da za ayi kar ki manta fa akwai shirye-shiryen bikin, na sa gyara a gaba sannan ga iyalina da wanne kike so naji ne?”4 Khansa’u ta kumbura kaman zata fashe “Me yasa kakeyi kaman ba sona kakeyi ba, duk wani abu idan nayi magana sai kace abubuwa sunyi maka yawa. Shi ankon nan ka dauka tamkar a cikin shirye shiryen auren ne mana. Amma ana magana sai kace iyali” Abun ya bata ran Sa’ad “Khans, look kar ki dauka ko zan aure ki zan bari ki ci min fuskar iyali. Ni na ganki na ce ina so ni kuma nake son aurenki, don haka idan har zamuyi aure ina son ki san da abu guda, kar ki dauka daidai da rana daya bana son iyalina ne yasa zan aureki, don haka kiyi respecting dinta haka kema ki rike girmanki, maganan kudin dinkin kawayenki kuma kiyi hakuri bazan iya badawa ba.” Ya kashe wayar, wani bakin haushi ne ya taso ya turnike ta. Tabdi!11 A daya bangaren kuma Sa’ad sai mita yakeyi haka kawai sai kace nine uban su, da suturar su ya zama min dole? Wallahi ba don zuciyata ta nace da son Khansa’u ba da na hakura saboda fi’ilinta sun soma isana. Haka dai zan yi hakuri tunda komai ya kusa karewa ta shigo hannu. Lokacin zan gwada mata yanda nake son nawa tsarin rayuwar.”6 Banka kofar tayi ta shigo don dama sallama ba wai ya ishesu bane, Momi ta juyo a razane tace “Khans, yaya dai na ganki haka?” “Bari kawai, Momi idan ba na kusa na fasa auren Sa’ad ba, ko an fada masa shine autan maza? Maza nawa na gwale na amince dashi shine zai zo yana fada min magana kaman wata wanda bata da gata.” STORY CONTINUES BELOW “To wai duk akan me ake ta wannan fadan haka ne?” “Kawai Momi fa don na masa maganar Ankon friends dina kudin dinkin zai bayar shine yake ta min kwana-kwana abu kadan yace Iyali.”5 Momi ta nisa tace “Shi kenan damuwar? kwantar da hankalinki nawa ne kudin dinkin ba sai na bada ba? Amma ai bazaki ce zaki fasa ba bayan saura sati uku aure ko an taba haka?” “Dubu dari biyu ne.”11 Momi ta zabura ta zauna daga kishingiden da tayi tace “dub… dubu dari biyu? kina haukane wani irin dinki ne haka?” “Momi su goma ne fa, kuma (dress maker) din telar ma ta mana sauki don dubu ashirin da biyar take dinkunnta tace zata min ragi a matsayin kyauta na aurena.”6 “Gaskiya ki bawa biyar hakuri. Ni bazan iya bada duka ba, don nima kudin hannuna sun yi kasa kina ganin yanda mukayi da Abbanku, kememe ya san abu dolensa ne amma ya zare hannunsa wai sai abun da ya dace zai yi don haka wasu souveniers din ma duk ni zanyi na share shi.” “Kiyi hakuri Momi ki daure ki bada duka, don Allah. Gashi na riga na fada musu za a musu dinki” “Gaskiya to ki canza mai dinki.” haka dai sukayi ta drama da kyar Momi ta yarda zata bada rabi. Don haka cikin account dinta ta je ta ciko sauran ta turawa kawayen nata tunda ta riga ta fada musu.11 Radiyya da Rumaysah sun shigo harabar gidan nan suka tadda Labeeb a kan kujeru shi da wani danuwansa MS, “A’a babban yaya ya na ganku a waje baku shiga ba ko Yaya Khadijan bata san kuna nan bane?” “Kar ki damu, yanzu zata fito munyi waya da ita.” “To shi kenan, da na dauka ko bata sani bane.” Nan suka gaisa sannan Rumaysah ta shiga ciki Radiyya zata wuce ne MS yace “Wai ni kanwar takun nan bata kula mutane ne?” Nan da nan Radiyya ta hada idanu da Labeeb suka kwashe da dariya, “Ai bari na fada maka idan dai Rumaysah ne danger zone, idan kana neman Balbalin bala’i to daya sunan ta kenan.” Ms, ya shafa fuskarsa yace “Ni kuwa ki ban contact dinta kiga ikon Allah, don sai ta saurareni.” Dariya sukayi sannan Radiyya tace “Allah ya baka sa’a” Daidai lokacin Khadija ta fito don haka Radiyya ma ta shige ciki. Tun a ranar Rumaysah ta samu wayar MS, suka gaisa tana tsume kaman an kawo mata labarin mutuwa, amma sai bai dago mata wani zance ba, asali kawai ya gama lakantar ko me take so don haka iyakan shi nan, nan da nan suka saba kullum yana gidan sai ka rantse a nan aka haife shi saboda karfi da yaji ya maida gidan wurin hirar sa. Cikin sati uku kawai amma ya saba da kowa. Haka za a zauna ayi ta hira ana wasa da dariya tun Rumaysha na gimtse masa fuska har ta sake. Shi kuwa MS ba abun da ya ke burge shi da ita irin kyaunta mai daukar hankali, gata dai bata kai sauran ‘yan uwanta fari ba, amma kyaunta na daban ne wanda muddin mutum ya hada ido da ita to sai ya daure.4 Saura sati biyu a kama azumin ramadan aka fara hidimar bikin. Ranar laraba su Khadija suke bridal shower din su yayinda Mama kuwa ta shirya Hafla wa su Sajeeda. Motoci manya-manya da kananu, masu tsada ne suke ta faman sintiri a cikin gidaje biyun, unguwar ma sun shaida abun na manya ne. Shiga ce ta alfarma a jikinta, ta fito fes da ita sai dai bata ga ta zama ba saboda ta gayyaci manyan mutane, daga dangi har makwabta ga kuma matan abokan mijinta, wanda daga matan senatoci ne sai matan tsoffin ministoci dama wanda ake damawa dasu yanzu. Yayinda Momi nata gayyar na class ne irin na ‘yan boko, a fadin kasar nan, wasu bakin tundaga lagas suka zo wasu ko daga turai. Duk dai don a taya su murna, ko mazan kansu basu nemi a hada shirin ba don sun san za ayi abun kunya a gaban baki. STORY CONTINUES BELOW An kawata filin taron gidan Abba da bakaken kujeru wanda akayiwa ado da kyallaaye masu ruwan hoda, ga wasu furanni masu kamshi da aka jera kan kowani tebur, kana ganin adon filin taron ka san ba karamin lokaci da kudi aka dauka wurin tsara shi ba hatta abun da za aci a wurin kalarsa kenan, ga wasu mini cakes da aka jera masu ban sha’awa ko wanne da farkon sunan amaren da angwayensu, kawayen amaren suna sanye ne da kaya ‘yan kanti duka kala iri daya ne wato pink da black sai dai kowanne da irin nashi kece mutumcin da aka masa, baga matan auren ba baga ‘yan matan cikin su ba, sai casu suke tayi an kure kida. Khansa’u da Khadija sun fito suma cikin ‘yar kanti doguwace har kasa amma ya kamasu, ruwan hoda ne aka masa ado da wani lace sharashara baki ta saman shi, sunyi kyau matuka ga fuskar nan ya sha kwalliya har da kyar ka gane su don shekin fuska.5 Mama taji shirun yayi yawa don haka ta shiga da kanta don duba amaren suyi su fito an riga an taru su ake jira a fara taron, sai dai me tana shiga ta samesu duk a mulke da kurkum basu ma shirya ba. “Ashe tuntuni baku shiga wankan ba? Kun sa na ajiye mutane sai jiranku sukeyi, idan baku gama kun fita ba nan da awa daya zan ce a fara kawai.” Munira magananniya tace “Mama, an taba taro ba amare? Ai ba a bude fili sai da mu don haka sai kun jira mu, yau muma ranar mu ce” Mama ta kada kai “Yau kuwa zaku ga yanda ake bude fili ba masu taron kar ku fito kuga ikon Allah.”6 “To munji, sorry ga mu nan fitowa idan baki tafi ba ta yaya zamu fara shirin?” Ta dube ta kawai ta girgiza kai, wai yanzu zata aurar da Muneeran ta. Ikon Allah. Wani kwalla ta share a gefen idanunta sannan ta koma gun bakinta. Amare sun fito fes cikin adon su na lafayu, iri daya suka saka kalan ja da ruwan gwal. Hafla dai ya kayatar don harda ‘yar drama aka shirya domin fadakarwa a nishadance. Ai ‘yan uwansu Baffa sai zulmiyewa sukeyi suna tafiya can a cewarsu bikin gidan Momi sai yara. Momi ko ranta ya baci ai tana sane da wandanda suka zauna sannan kuma ta san su waye makiyanta.5 Rumaysah dai duk wannan bidirin da akeyi, tana dale a saman (balcony) dinta tana hango komai, ita ko shiryawa batayi ba ma, normal kayan da ta saba amfani dasu ne a jikinta na wandon jeans da wata riga mai yalayala ya gama fito da kyaunta kanta ba dankwali, gashinta iska ne kawai ke wasa dashi, kafarta ma ba takalmi tana zaune kan kujera tana kallon ribibi. Fawzaan yana tsaye da Raa’id bayan ya fito daga cikin gidan Raa’id din don duba jikin shi. Nan ne ya hangota a tsaye a sama, wani irin mugun kallo yake mata “Wai me yasa bakuyi mata fadane, yarinya sam bata ji kun sake mata sai abun da ta ga dama takeyi…”4 Raa’id yabi idanunsa ya hango Rumaysah. “Ban san me yasa baku shiri ba sam, da hankalinta sarai bata bukatar fada yaya Fawzaan” Wani kallo ya watsowa Ra’id sannan yace “A hakan? Ni na rasa ma ta yaya take tsinana wani abu a makarantar naji ance wai Statistics take karantawa.” “Ai kuwa, Rumaysah ba daga nan ba kasan darajar 2-1 ma take ja yanzu haka? Ita dai kawai haka take daban, yanzu kaga dai hidima akeyi a gidan nan amma ta ware kanta a sama.” Juyawan da zatayi ne, suka hada idanu yana mata wannan kallon tsanar tashi, ita bata san me ta masa ba yake mata wani gani gani. Well, itama ta tsane shi idan bayi da labari. Banda fadin rai ba abunda ya iya, ta dauko wani tsaki ta ja.4 “Ni Raa’id bari na gudu, ban san meye matsalar mata da biki ba, kaga nan Meena nake jira ta gama na maidata gida, su Sajeeda suka matsa sai na kawo ta. Ba don haka ba ni yaushe zan tsaya wurin hidiman mata?” “Ai haka ne, duk inda mata suke to suna son kyale kyale da abun biki, yanzu ba ga ka nan ba har ka fara hidimanta tun kan ka aureta.” “Rabu da ita kawai ina biye mata ne yanzu idan mukayi aure duk bazan yarda da wannan shirmen ba.” Raa’id yayi dariyar yayan nasa.6 STORY CONTINUES BELOW Wuri yayi wuri a dakin taron da ake dinner dinsu Khansa’u. Nan suka fito suna haki kaman sunyi gudun fanfalake “Haba sai yanzu naji iskar duniya amma kawai a zaunar da mutum wuri guda wai ana hidima? I hate weddings” MS yayi murmushi yace “Ai na san gaba daya a takure kike, yanzu ko kinga hankalin mu kwance idan sun ga dama su kwana a ciki.” Rumaysah ta kwashe da dariya, shi kuwa ya tsaya yana kallonta ya matso daf da ita har tana jin hucin numfashinsa da ya fiye fidda warin taba, yana ganin yanda ta matsa baya yayi saurin dunkule hannunsa cikin jin haushi. “Kiyi hakuri, bazaki gane yanda kike da daukan hankali bane”5 Ita duk wanda zai ce yana sonta ma haushi yake bata bare kuma da ta dago manufar MS don haka tayi kaman zata koma ciki, amma ya kara bata hakuri. Can yace “Ki zo muje mu nemi wani abu muci.” “Ni bana jin yunwa sosai.” “Da gaske wani joint ne a Maitama, yana da kyau sosai yanzu zamu dawo baza mu zauna ba.” Rumaysah ta karkatar da kai tace “Gaskiya yanzu za a fara daukan hoto kar su nemeni su rasa” “Haba, ki rabu da mean sisters dinki ki zo mu je yawo mu more, ba mai sanin bakya nan.”3 Ba tare da wata damuwa ba, ta shiga kofar motarsa da ya bude mata. Nan take tayi pinging Radiyya hade da tura mata sako. “Na fita da MS, joint things.” Suna fita ne tace masa “Yaya karatun dai?” “Karatu ai sai ku mun bar muku wannan.” Rumaysah ta dube shi cikin al’ajabi “NI kana ban mamaki, yaya kana na miji zaka na kin karatu?” “Ba ana karatu don kawai mutum ya samu abunyi bane? To ni an tara an bar min me yasa zan wahala?” Mamaki ya kama Rumaysah amma ta boye murmushi tayi sannan tace “Yanzu ka gwammace ka dogara kan abun da za a na sammaka wanda baka da iko a kai, randa me baka baya nan fa ko kuwa suka kare sai kayi yaya?” Dariya yayi daidai nan suka isa tare suka sauka suka sayi abubuwan ciye-ciye a cikin Zavaati, basu tsaya ci ba suka koma mota, kaman yanda ya mata alkawari wurin event din zai maidata. Wata jaka ya bata Rumaysah ta dubeshi tace “Bazan ma duba abunda yake ciki ba, saboda na fada maka sai randa ka fara tara kudinka na kashin kanka kafin na karbi kyautar ka.” “Hmm, Rumy kina da abun mamaki, kin fita daban a cikin ‘yan mata amma kar ki damu. Zan nemo meye farashin ki (everybody has a price)” Caraf ta dago tace “Ba a kirana Rumy, ba na gutsire sunana. Idan Rumaysah ya maka tsawo to kar ka kirani da komai” Tana fadan haka ta tuna da sunan da wanda ya fara kirkiranshi duk ta tsane su, game da batun MS kuwa Rumaysah cewa tayi zaka mutu kana gwadawa ashe. Suna zuwa wurin parking ne ya kira sunanta, juyowan da zatayi maimakon ta fita a motar ne yayi daidai da haduwar fuskokinsu, tayi saurin matsar da kanta amma MS ya sa hannu ya riko kanta bayi da buri irin na yaga yayi kissing dinta ko zai daina tunanin labbanta masu kyaun gaske. “lafiyan ka, ka bari bana so.”3 NAn suka shiga kicin-kicin. Ai kuwa sai suka ji an bude kofar motar ta bangaren MS hannu yasa ya cafko shi wajen motar. Tana ajiye numfashi ta fito a kidime. Yaya Fawzaan! Me ya kawo shi wurin dinner?2 “Baka ji tace maka bata so ba? Ko kuwa baka fahimtar wannan yaren? Wato irinku ne masu daukan advantage din ‘yan mata a wurin biki ko? musamman idan kun hadu da wawaye.” Ya fada yana kallon Rumaysah daidai nan tayi saurin sadda kanta kasa ta hadiyi yawu.11 “Tun kafin wani yaji, kayi saurin bacewa a filin nan, don ban damu da auren danuwanka akeyi ba yanzu sai na sa guards su fitar da kai. Kar kuma na kara ganinka a ko ina kusa da ita, kaji na fada maka.” STORY CONTINUES BELOW Yana sake kwalar rigar MS ya shige motarsa rai a bace ya bar filin, Fincikan hannun Rumaysah yayi ya kaita motarsa ya ajiye ya buga marfin motar sannan ya zagaya bangarensa ya shiga. Hawaye ne kawai ke zuba a idanun Rumaysah “Seriously? me kike tunani zaki biyewa irin wannan? Ba ga irinta ba baku da aiki sai tara tarukucen samari kun dauka burgewa ne ace dan wane da wane saurayinku ne, Allah kadai ya san me zai faru da Allah bai sa na ganku a motar ba da nazo parking.” Kallonta yayi ta gefen idanunsa tana ta rusgar kuka, ya ja tsaki Allah kadai ya san ko wannan ne karo na farko ma. “Kayi hakuri Yaya Fawzaan” Ko kala bai ce mata ba har suka isa gida. Har cikin harabar gidan Abba ya shigar da ita. A sanyaye tace “Na gode” Idanunsa kawai ya lumshe mata ba tare da yace komai ba ya figi motar yayi gaba.5 Tana shiga gidan shiru kasancewar duk suna wurin dinner basu dawo ba. Dakinta ta haye da gudu ta kwanta sai kuka takeyi “Wato daman haka maza suke duka mayaudara? Allah ne kadai ya san me MS yake da shirin mun da Yaya Fawzaan bai hana shi ba.” Toilet ta fada da ta ga kukan bazai ficce ta ba, ta rinka brush har sai da ta gaji, har yanzu sai take ji kaman warin sigarin MS takeyi. Wajen sha daya tayi kwanciyarta. Amma ba abun da take tunani irin yanda Yaya Fawzaan ya taimake ta bayan babu abun alkhairi daya a tsakaninsu idan banda rainin da take masa ma.2 Da safe, sai wajen karfe goma tayi wanka sannan ta sauko, ta samu kowa da kowa a babban falo sun shimfida dogon ledar cin abinci kama daga ‘yan uwan momi da na Abba, da ma kawayen su Khansa’u gasu nan dai birjik. Tana sauka idanu sukayi mata caa “Ke kuma lafiya jiya aka neme ki aka rasa?” Maimunan Yaya Hansai ta tambaya. Khansa’u tace “kika san ko tayi wani catch ne kin san kanwar tawa ba da ga nan ba, tana shiga wuri take dauke hankulan jama’a tamkar magnet.” Radiyya ta ce “Ban ganki a wurin daukan hoton Tozali ba ma” Sai nan ne ta tuno sakonta don haka ta yi shiru. A sanyaye Rumaysah tace “Ban ji dadi bane shi yasa na dawo gida.” Maimuna tace “Baki tafi da motar ki ba, yaya akayi kika dawo?” “Yaya Fawzaan ne ya dawo dani.” Cak falon yayi tsit tamkar an dauke wutar NEPA kowa ya juyo yana dubanta. Khansa’u tace “Kanki daya kuwa? ko giyar wake kika soma sha? Wallahi to kiyi shiru tun kan Momi ta jiki me zai sa ki shiga motar Yaya Fawzaan wai ma yaushe kuka soma magana?”4 “Ya ganni cikin ciwo ya taimaka ya dawo dani shine wani abu?” ta fada ranta a bace da maganarsu.4 Mamaki ya dada rufesu don kaf cikin su idan ana zagin Fawzaan babu wanda ya kaita bada kaimi, gashi kuma yau tana kareshi.4 Bata sake bi ta kansu ba ta wuce kitchen, ta samu sunyi kaca kaca dashi, Yalwa da Laminde sai jidan kwanukan sukeyi suna fitarwa waje don wanke wanken ya fi karfin cikin gida. Ga biredi sunyi leda shida duk an bude an fara ci ba wanda a ka gama. Ta tsani kazanta a rayuwarta hakan yasa bata da ganda wurin kawardashi, sai da ta dan tattara sannan ta fito ta debi karyawarta tan.2 Karfe sha daya aka daura auren Su Khadija da su Sajeeda. Sajeeda Kano za a kaita, Khansa’u kuma Bauchi, Khadija da Munira ne a Abuja. Sajeeda na fitowa daga wanka ta ganta a zaune a bakin gado mamaki ne ya hanata magana da farko. Da ta samu muryarta ne tace “Rumaysah lafiya?” Tana murmushi tace “lafiya yaya Sajeeda, daman gifts dinku na kawo muku ke da Yaya Muneerah.” Dadi ne ya cika ran Sajeeda fal, “Mun gode sosai, amma Momi…” “Kar ki damu, shin kanwa bazata iya yiwa yarta kyauta ba sai maman su ta sani ne?”2 “To, Allah ya bar zumunci mun gode kwarai, bari na nunawa Mama” “a’a kar ki nuna mata yanzu, don Allah. Yanzu ma zan fita Allah ya kiyaye hanya ya kuma baku zaman lafiya” “Ameen, na gode” Rumaysa ta fita tana jin dadi a ranta. A ranar aka tafi da amare, sai dai Khansa’u ce sai washegari kasancewar har Bauchi za a tafi da ita. Zuwa litinin mutane da dama sun tafi, sauran wadanda ba za a rasa ba. Ya je daukar motarsa ne daga wurin wankewa sai Inusa yace “Yallabai ga wannan na samu a kasan carpet.” Fawzaan ya karba yana karewa abun hannun kallo, yaya akayi abun hannu a motarsa? Iya saninsa dai Meena kawai ya dauka a motarsa, kuma bai taba ganin wannan a tare da ita ba, sai dai ko Rumaysah. Ajiyar zuciya yayi sannan yace “Na gode Inusa.” Ya biyasa kudin wankin motar sannan ya tafi. Unguwarsu ya nufa kai tsaye gidan Abba ya shige, a wurin ajiye motoci ya adana tasa sannan ya shiga falon Abba. Audu yasa yayi wa wata ‘yar aiki magana a kira masa Rumaysah. Tana saukowa ta sameshi a falon Abba a tsaye, sanye yake da farar T-shirt ta polo da bakin wandon jeans tabbas kuwa ba kuskure akayi ba Yaya Fawzaan ke neman ta. Ko lafiya? Ko dai fada zai yi mata kan maganar ranar? “Ina wuni.” Ta fada a sanyaye yau ba tsiwar don nauyinsa take ji yanzu. “Lafiya kalau.” Hannu ya saka a aljihunsa ya ciro abun hannun “Na samu wannan a motata ina tsammanin naki ne ko?” Ya mika mata, ita kam kwata-kwata tashin hankali ma bai sa ta kula da ta batar da abun hannunta ba. “Na gode.” Har ya sa kai zai fice tayi saurin cewa “Yaya Fawzaan,” tsayawa yayi ya dan juyo da fuskarsa gareta , “Don Allah kayi hakuri a kan maganar ranar, kar ka fadawa kowa”5 Sauke idanunsa yayi ba tare da ya ce mata komai ba ya fice. Abba ya zo shiga gidan ne daidai nan ya ga Fawzaan na fita, don haka Fawzaan ya sauka suka gaisa sannan ya wuce. Yana sauka a mota ya ga Audu a bakin kofar gidan yace “Audu lafiya dai?” “Lafiya lau yallabai, sannu da dawowa.” “Yawwa sannu, wani abun ne?” “A’a babu, daman Barrister ne yasa nayiwa Laminde magana ta kira masa Rumaysah ya bata sako.” Abba yaji mamaki kwarai, sako kuma? “To shi kenan, sannu da aiki.” Me zai hada Fawzaan da Rumaysah har ya kawo mata sako, ko da yake sai ya tuno kwanaki uku da suka wuce shi ya sauketa a gida.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *