AMAREN BANA
CHAPTER 3
GIDAN AMARYA KHANSA’U!
Juyi ta yi cikin jin dadin barcin da take kwasa. Wani mafarki take yi mai dadi wanda take jinta kamar tana wata duniya, kamar a cikin mafarki ta ji ana cewa. “Khans, Khans ki tashi”.
Juyi ta kara yi, domin ta zaci duk mafarki ne. Girgiza ta da aka fara yi ne, ya sa ta fara bude idanu, cikin lumsassun idanunta ta hango shi duru-duru. “Ki tashi za ki makara fa.”
“Ka bar ni na yi barci na”.
“Idan ki ka yi barcin kuma, ai za ki sa sauran jama’ar gidan su makara”. Sai a lokacin ta zabura da ta tuna yau za a tashi da azumi. Ba shiri ta wartsake. “Sa’ad ka manta ne ni ba na suhur fa.”
Murmushi ya yi ya-ce. “Na ji ke ba kya suhur, amma sauran jama’ar gida na yi, saboda haka ki tashi ki nemi abinda za ki shirya.”
Zaro idanu ta yi ta-ce. “Haba, yanzu fa barci na ke yi, karfe uku na dare zan fara shiga kicin yin girki? Gaskiya ka katse min barci na.”
“Ki yi hakuri, ko dan abu mai sauki ne, sai ki daura.” Baki ta zumbura, sannan ta sauka akan gadon ta dauki zani ta daura akan kayan barcinta, sannan ta nufi kicin.3
Tsayawa ta yi tana tunani. “Yanzu me zan fara shiryawa na mutum shida? Sa’ad, Bilkisu da yaranta ko da yake Zinah karama ce ba ta azumi.” Nan da nan ta fiddo Indomie ta jera akan Cupboard ta sa ruwa a tukunya, ta dafa. Tana gamawa, ta kai masu falon Sa’ad, sannan ta koma daki ta yi kwanciyarta.8
Da kyar Sa’ad ya tasheta ta yi sallar asuba. Amma har ya je masallaci ya dawo, nan ya sameta kwance ya kara tashinta.
Tana sallah, anan ta ci-gaba da barci ba ita ta tashi ba sai karfe goma na safe, ba ta ma san yaushe Mai-gidan ya fita zuwa wurin aiki ba.8
Sai wajen karfe daya ta yi wanka, ta fito falonta. Jin azumin take yi sosai, kamar ta fadi kasa, ba don kar ta ji kunya ba, da ta karya, sai kuma ta ga yaran suna azumi, a haka suka tafi makaranta, suka dawo, sannan karfe biyu su wuce Islamiyya, inda za su fara daura. Shigar ta kicin ne ta yi turus!4
Ta tsaya saboda ledojin cefane da ta ci karo da su. “Yanzu yaya zan fara yi da duk wadannan abubuwan?” Bude freezer ta yi kawai ta kwashi duka ledojin ta zuba a ciki ba tare da ta duba wanne ne na freezer din ba, ko kuwa ta gyara shi.6
Nan kuma ta shiga shirya abin da za ta yi na buda baki, dankali ta fere guda goma, sannan ta koma freezer din ta lalumo kayan miya, da kyar ta daura jallof din taliya da dankali. Lokacin ne ta shiga tunanin me za ta yi, na abin sha, don idan banda zobo ba ta iya hada ko wanne ba.7
Ta shiga Store ta duba ganyen zobo, amma ba ta samu ba, don haka ta fito ta-ce. “Yawwa Ummi tambayar min Mamanku inda ganyen zobo yake mana”. Ummi ta tafi tambaya ne, sai ga wayar Sa’ad. Ajiyar zuciya ta yi ta amsa. “Hello Madam, yaya azumin dai?”
“Alhamdulillah, yaya aiki?”
“Ga shi nan muna kan tabawa, da fatan dai ba wata damuwa ko?” Juya idanunta ta yi sannan ta-ce. “Babu.”
STORY CONTINUES BELOW
“Yawwa, don Allah ina son kosai irin mai kwai din nan a ciki, amma kar ya yi yaji sosai.”5
Khansa’u ta kasa yarda da abin da kunnuwanta suke jiye mata, karfe uku ne fa yanzu yaya za ta fara wani kosai yanzu? Ba yadda ta iya ta amsa masa, suka yi sallama.
Bilkisu ta shigo don ta ba ta zobon ne, ta ga ta zage sai dukan wake take yi a turmi, har ta farfasa shi. “Haa, ai ni Ummi cewa ta yi ki na son zobo ba ta ce min da wake ba, ai muna da surfaffen wake a store. Jikawa kawai za ki yi”.
Wani ajiyar zuciya Khamsa’u ta sake. “Na gode.” Nan ta karba, har Bilkisu ta zo fita ne ta juyo ta-ce. “Ehem, na manta ban fada miki ba. Baban Ummi fa baya cin indomie.”5
Ran Khansa’u ya baci, wato duk hanata barcin da aka yi, ta tashi tsakar dare ta dafa don ta burge shi, shi ne ma wato baya ci? Haka dai ta hakura ta ci-gaba da aiki. Har karfe shida tana kicin, lokacin ne Ummi ta shigo ta-ce.
“Anty kawo Fruits din na yanka miki.” Dadi ne fal! Ya cika Khansa’u, don kafafunta har bari suke yi, tiren sukutum! Ta mikawa Ummi, sannan ta ci-gaba da soya kosanta wanda ko wanne ya fi kama da hoton nahiyoyi (continents), don ko wanne da Shape dinsa.27
Sa’ad dai ya dawo gida shan ruwa da abokinsa, sun zauna cin abincin ne, tun daga budewa, hankalinsa ya tashi, amma ya matse ya mayar a ido ne kawai, don haka suka zuba suna fara ci ya-cewa abokin. “Wai ka ga nan sabuwar ‘yar aiki, muka yi ganin gidan ya karu, har yanzu ba ta gama gane kan aikin ba.”2
Da yake abokin magananne ne, sai ya-ce. “Haba, ai na ga alama, don dai na san Madam dai ba daga nan ba. Gobe dai Insha-Allahu za mu zo mu kwashi girkin amarya.” Sa’ad sai da ya kware da ruwan da ya kai bakinsa, wanda shi ne kusan abin da yake iya shayuwa cikin abincin kaf!6
Ba a maganar kosan nahiyoyin da ya sha mai, bare daskararren taliyar da aka dafa tun karfe biyu na rana, sai farfesun da ba laifi, ya yi dadi, amma sai dan karen yaji.11
Shi ya san zai samu matsala da ita, ta wannan bangaren, don tun kafin auren su ta fada masa ita hatta gadonta ba kullum take gyarawa a gida ba. Haka dai ranar abinci ya yi bojo. Sai Fruits ne kawai ya tafi.
**********
GIDAN AMARYA KHADIJA
“Hello”.
“Hello, my dear yaya gidan dai na bar ki ke kadai.”
“Alhamdulillah.”
“Kar ki damu, na yi magana da Nabila kanwata za ta zo ta tayaki aiki, ita da ‘yar yar mu za su zo.”
Khadija ta-ce. “To ba damuwa, idan sun iso, su dan jirani.”
“Su jiraki, kin fita wani wurin ne?” Ya tambaya cike da mamaki.
“Eh, na dan zo exclusive ne, zan dan sayi wasu abubuwan da ba mu da shi.”
Watakila abubuwan na da muhimmanci ne, idan banda haka yaushe ta je kasuwa?
“To ba matsala, zan fada masu.”
Tana dawowa, suka hadu suka shirya lafiyayyar buda baki, don daman kaf! Gidan Khadija da Rumaysah ne masu ra’ayin shiga kicin, lokacin shan ruwa aka jera abinci kala-kala. Labeeb na zaune sai zuba santi yake yi.2
“Eye, Malam aure ya yi ka ji. Idan banda a gidanka, yaushe za a jere maka kwanuka masu kyan gaske kala-kala masu dauke da nau’i-nau’i na abinci?” Abokinsa Sadiq banda dariya, ba abinda yake masa.
Ko da suka gama aiki, sai da su Nabila suka tayata kimtsa ko ina, saboda Khadija Allah ya yi ta da dan karan jan mutane a jiki har ta more su tas! Ba tare da sun san hakan ba. Nan ta sa suka kwana. Da safe da suka tashi tafiya kuwa, ta hada su da kayan kwalliya irin na ‘yan mata, sai godiya suke mata.
STORY CONTINUES BELOW
Labeeb dai yana jin dadin Khadija, domin akwai ta da iya kula da lamuransa, damuwarsa daya da ita shi ne tana nan kamar shanshani, ta faye dan karan yawo, ta maida kasuwa tamkar gidan makwabta.10
Daga aurensu sati biyu da ‘yan kai da suka wuce zuwa yanzu ta je kasuwa ya yi sau tara. Don haka washegari daya tashi fita, sai ya ki ya bar ko sisi, tunda dai kudin da take gani ne, take tafiya kashewa.4
Ai kuwa dawowar sa bai sameta a gida ba, ya kira wayarta, ta-ce masa tana wurin Tela. “Tela dai Khadija? Yanzu duk dinkunan ki sabbi, wane dinki za ki sake yi yanzu kuma?”7
Nan dai ta nuna masa ai wanann na shirin sallah take yi. Gaba daya ya rasa yadda zai yi da ita.7
*************
GIDAN AMARYA MUNIRA!
“Da gaske ban yarda ba, ka kara biyu nawa sun fi yawa”.
“Ke dai kawai kin iya coge.” Ya fada a gajiye. “Ni fa kaina ciwo yake min, zan je na kwanta.”
Tsumewa ta yi hade da sa hannu a kugu. “Ni kuma ba mutum bace, ai da na ke tsaye kan kafata, tun karfe daya.”
Murmushi ya yi. “Ki yi hakuri to, zan yanka miki, doyan ma ki bari zan soya. Ki yi (Pepper Soup) din kawai”.
“A’a zan soya, kai dai kawai ka taya ni yankawa.”
Nan suka ci-gaba da aikin su, lokacin sallah na yi suka bari, sai can suka ci-gaba.
Daidai lokacin da abokansa suka iso ne, suka samu ya fito daga kicin, nan suka shiga yi masa tsiya. “Yawwa, Muneera ai kin burge, daman ya faye son jiki, yanzu kin ga kin sa shi a hanya.”
Kallon su ta yi ta-ce. “Gobe duk wanda ya fara isowa, shi ma zai shiga daga ciki ya zamo Assistant ayi aikin da shi.” Nan suka sa dariya, ta gaishesu, sannan ta bar falon.
Ita ba abinda yake ba ta mamaki, irin yadda abokan Abdullaahi suka takarkare suka maida masu da gida wurin hira, idan ana shan ruwa, ba za su watse ba, wataran har sha dayan dare, wannan abu na damunta matuka.11
Sun jera kusan sati a haka, ranar ta-ce masa. “Wai ni abokan ka ba su da gidaje ne?”
Abdullaahi ya-ce. “Me ki ka gani?”
“Su kullum suna cikin yawon shan ruwa, ba za su zauna a gidajensu su sha ba?”
“Muneerah kenan, ai mutum rahama ne, sannan kar ki manta fa, za ki samu ladan da suka yi na azumi a dalilin ciyar da su da ki ka yi, suna azumi.”
“Na san da wannan, amma duk randa ka kuskura ka je wani gida shan ruwa, alhali na takarkare nai maka kayan buda baki, za mu yi kaca-kaca da kai.”4
“To ranki shi dade, mai da wukar, me ya yi zafi?”
“Hmm! Ai gaskiya ne, na san Yaya Sajeeda kam ta na can ba ruwanta, dama ko a gida aiki take yi kamar jaka.”
Abdullaahi ya yi dariya ya-ce. “Kin raina Yaya Sajeedan nan fa, sai ka ce ba a gaba take da ke ba.”
“Allah da gaske na ke yi, sam ba ta da kyuiya.”
“Hmm! Ke kuma Lazy Bones ba.”
Kallonsa ta yi cikin hararar so ta-ce. “Ni ka ke kira Lazy Bones? Idan na fara gwada maka nawa kalan kasalancin, za ka gane kurenka.”
“Wai yi hakuri, na ma fasa. Ayi hakuri. Yawwa ki shirya gobe. Insha-Allahu sai na kai ki gidan Baffa ki sha ruwa a can”.
Cikin Murna Muneera ta-ce. “Da gaske?”
Murmushi ya yi mata, haba ai take ta ji goben ya yi, ko za ta ga Mama ta more.4
************
STORY CONTINUES BELOW
Kallon kanin nasa yake yi tamkar ranar ce rana ta farko da ya fara ganinsa. “Uhm-uhm! Umaru, Uhm-uhm! Ba ka jira kanka ba, anya kuwa akwai gaskiya, ni ina hango gagarumar matsala a wannan batun naka.”3
“Yaya Lamido kar ka ji komai, na fada maka da idanuna sau biyu ina ganinsa da ita, nan ya sauketa, nan kuma ya zo wurinta. To tunda har su sun daidaita kansu, mu meye namu, baya ga mu bi su da fatan alkhairi?”14
“Ni duk ba wannan na ke ji ba, ka na gani Atika ba za ta daga hankalinta kan wanann al’amarin ba? Don ka san irin zaman da ake yi fa a gidan nan”.
“Na sani kwarai, kuma wannan ma bai wuci ya kawo wata hanya da za ta warware wannan takun sakar dake tsakanin su ba. Shi ya sa tunda na ga Fawzaan da Rumaysah, sai abin ya yi min dadi, domin kuwa faduwa ce ta zo daidai da zama.”
“Na ji batunka, duk da haka dai ba na son mu yi saurin yanke hukunci, har sai mun ji daga garesu, ka ga tunda kwanan nan aka yi bikin su Sajeeda, sai a dan ba su lokaci kafin a dago masu maganar.”
“To shi kenan, wannan magana ta yi dadi, kuma batun Atika ka bar ni kawai da ita.”1
Hajiya Sogiji ta yi shiru, tana sauraron Mai-gidan nata har ya kai aya, kan batun nasa. “To Alhaji ai wannan magana ai mai dadi ce, sai dai wani hanzari ba gudu ba, na san Atika kamar yunwar ciki na, zai yi wuya ta amince da wannan batun, na tabbata ba ta san me ‘yarta take ciki ba. Da ba za ta bari ya yi nisa haka ba.”
Shi ma dai Alhaji Lamido tunaninsa kenan, sai dai kamar yadda Umar ya fada masa, baida shakkar komai, yana da tabbacin hakan. “Ba wani abu Insha-Allahu, babban abin dai sun daidaita kansu.
Shi ne, zan yi magana da shi Fawzaan da kaina, don tabbatar da hakan. Sannan watakila wannan wani nufi ne na Allah da zai sa Atika ta rage wani abin nata.”
“To Allah ya sa, ya kuma zabar da abinda ya fi alkhairi.”
“Ameen, dan zubo min ruwan zafin nan, na sha ko ciki na zai dan warware.”
“To Alhaji”. Ta fada tare da mikewa ta tsiyayi ruwa daga flask din dake ajiye kan dan karamin tebur din dakin.2
********
Washegari a falon Baffa ya samesu suna zaune daga Baffan har Mama, murmushi ya yi ya-ce. “Baffa meeting ne haka?”
Shi dai mamaki ne ya cika shi, da ya ji kiran da Baffa yayi masa, sai dai da yake daman shi ma tafe yake da nasa bayanin a baki, sai ya zama faduwa ce ta zo daidai da zama.
“Har ka iso ne?.”
Zama ya yi suka gaisa, sannan Baffa ya-ce. “Kai kuma haka ake yi kawai, sai dai mu ji labarin ka samu mata ba mu da labari?”
Fawzaan ya sosa keya, yana dan murmushi. “Baffa, daman maganar da na zo maku da ita kenan. Saboda a wuce min gaba manya su sa baki.”
“To kai banda abinka, abinda duk daya ne, ai ba wata matsala. Allah ya sanya alkhairi ya kawar da duk wani sharri. Na ji dadin hakan kwarai”.7
Baffa ya dubi Mama suka yi wani murmushin su na manya. “Me na fada miki?”
Dadi ne fal! A zukatansu, haka Fawzaan ya fita tsabar murna, sai a hanyar gidansa ne ya yi tunanin to ta yaya Baffa ya san ‘yar gidan wa yake nema? Ko dai Ra’id ne ya fada masu don baya boye masa komai. To amma yaya ya san gidan su Meena? “Sai dai gobe Insha-Allahu, zan zo na ji duk yadda ake ciki.”3
Ranar laraba Rumaysah na dawowa daga makaranta, kai tsaye falon Abba ta wuce, saboda wannan al’adarta ce, sai ta gaida Abba, sannan take wucewa sama, sai dai idan ya tafi asibiti, to wannan daban.
Kasancewar ba ta same shi ba, kuma ga motarsa a waje ya ba ta tabbacin yana gidan, don haka kai tsaye dakin sa ta nufa, kwankwasawa ta yi, sannan ta bude kofar.
STORY CONTINUES BELOW
Sai dai ba shiri ta ja da sauri ta rufe a dalilin wata kwalbar da aka wullo setinta, ai kuwa tana rufe kofar sai Tush! kwalbar ta fashe, kafin ta fahimci me yake faruwa, ta sake jin karar ta biyu. Don haka kunnenta ta sa a jiki, don ta ji me yake faruwa.
“Ka sake min hannu na nace. Wallahi ka sake ni. Haka kawai!”
“Ki na hauka ne? Ni za ki jefa da kwalbar turare Atika?”
“An jefa din, nace an jefa din, ni da ka ci mutuncina fa, ka ke neman ka tona min asiri, idan ba za ayi mummunar tashin hankali ba. Ai wannan cin zarafi ne, idan banda haka ta yaya za ka fara tunanin hada min jini da na wancan jahilar matar? Wallahi za ayi tarzoma a unguwar nan, idan ba ka janye batun nan ba.”7
Abba cikin karaji ya-ce. “Idan kin ga dama ki tada World War 3, amma auren nan ba me fasa shi, da na yi tunanin sai na ji ta bakin Baby, kafin na yi komai, amma tunda ke ba ki da hankali, ba ki san ciwon kanki ba, har yanzu sai ki hana mu gani.”
“Ni kuwa zan gwada maka, jinina ba zai hadu da na Sogiji ba, domin kuwa ba ‘yar da na haifa da za ta amince da bukatarka. Gara na mutu da wannan abin ya faru”.
“Haka ki ka ce ko? Ni kuma zan gwada miki Baby ‘yar halas ce mai kuma yin biyayya ga mahaifinta. Akan wannan maganar ranki zai yi mummunar baci, idan ba ki maida hankali ba. Kuma sai dai ki mutun.”
Tashin hankali! Rumaysah nan jikin kofar ta fara sulalewa, wai me take shirin ji ne? Yaya ta ji Abba na ambaton Baby, da dan gidan Sogiji, da aure? Yaya ma za ayi wadannan kalmomi ukun su a hadu a jumla daya? Wace Baby din wai? Idan banda ita, duk gidaje biyun.Ba wanda ake kira haka, nan ma Abba ne kawai ke kiranta.
1
Yau ta shiga uku. Kuka ta soma yi wanda ba ta san yaushe ta fara ba, jakarta kuwa tuni tsabar tashin hankali ta wancakalar da ita a gefe, karan takun mutum da ta jiyo ne, ya sa ta mikewa da gudu ta bar kofar dakin, ba ta tsaya ba, sai tsakar dakinta.
“Me Abba yake shirin min? Ashe Abba baya so-na, zai min aure, ban sani ba? Sannan tukunna da wani dan Hajiya Sogiji yake shirin hada ni? Na san dai banda Yaya Fawzaan, don kuwa kwata-kwata baya ma cikin lissafi.
Yaya Bilaal kuwa ya faye fadin rai, baya ma kula mutane, kai yaushe ma aka gan shi a gidan? Yaya Sajjad kuwa na ji ance ma yana da wacce zai aura, ko ma waye ne a cikin su.
Abba ka jawo mini babban matsala, domin ba zan taba farin-ciki ba a rayuwa, da me zan ji? Kuncin da ke zuciyata ko kuwa wanda ku ke shirin haddasa min?”
Kwananta biyu a daki, wani irin zazzabi mai zafi ne ya rufeta. Abba ne ya shigo dakin a kidime. “Wai lafiyanki kuwa kwananki biyu a daki, ba ki je ko ina ba?”
“Abba, ba komai, kawai dai zazzabi ne, sai kuma ciwon kirji.”
Nan ne ya manna hannu a goshinta ya ji zafi radau! “Subhanallah, fever ce mai zafi Atika jiko tawul da ruwan sanyi ki kawo.” Ya kara duban Rumaysah ya-ce.
“Ba ki da lafiya, shi ne ki kai shiru ba za ki iya magana ba?” Hawaye ne kawai suka biyo gefen idanunta masu zafin gaske, saboda ita kadai ta san tashin hankalin da take ciki, karshe dai sai da Dr. Umar ya dora mata ruwa a gida tukun, ta samu dan dama-dama.
Wannan ya sa ya-ce ta rinka shiga mutane, ko za tafi saurin warkewa, haka ta daure ta sauka ranar, suna zaune a falon Abban har da Radiyya. Ta-ce. “Abba, ni ban san me yake faruwa ba, tsakaninka da Momi.”
Ya yi shiru kamar bai gane meye ba ya-ce. “Kamar me fa?”
“Abba mun ga ne, kwanan nan kun daina zama ku yi hira yadda ku ka saba, idan kun dawo daga aiki.”
“Babu komai, kun san ga azumi, ga kuma gajiyar bikin nan da ta sha, shi ya sa na ba ta dan lokaci ta samu ta huta.”
Yake kawai Rumaysah ta yi, saboda ta san ita ce silar wannan tashin hankalin da ya danno masu cikin gida.
**************
Kwanaki uku da yin maganar su da Baffa kullum sai sun yi waya da Meena, amma ba ta ce masa ga shi an iso batun tambaya ba, don Babanta ya dawo daga tafiyar da ya yi, hakan ya sa ya yi tunanin zuwa gida, ya yiwa Baffa tuni, bayan an sha ruwa.
Yana zaune da Mama suna tattaunawa ne a daki, ta dube shi ta-ce. “Gaskiya na ji dadin yadda ku ka yi tunanin ku hade kai cikin hikimar Ubangiji ku kawo karshen matsalar gidan nan.”
Fawzaan ya dubeta, ba tare da ya fahimci abu daya da take fadi ba. “Mama matsalar gidan nan kuma?”
“Kwarai kuwa, ni na san duk rawar kan Rumaysah, tana da zurfin tunani, kwarai na yaba da yadda tsoron abin da zai je ya dawo, bai hanaku nuna niyyarku na cimma kyakkyawar manufa ba. Ga shi sai Allah ya hada kanku ku ke son juna”.
“Tsaya tukun wai me na ke shirin ji ne? Mama ta dauka wai Rumaysah na ke so ne? Wannan yarinya mai tsegeranci? ‘Yar matar da na fi tsana duk duniya, yarinyar da maza suka gama jagwalgwalawa? Ina! Wato shi ya sa Baffa yake tunanin duk na gida ne. Hakan ya sa ba su je gidan su Meena ba”.7
Nan da nan wani tashin hankali ya sauka masa, ya ji zufa ya rufe shi ta ko ina. Yaya zai fara rayuwa da wannan yarinyar? Kai babbar matsalarsa ma, yaya zai yi da Meena, ai dole kawai ya samu Baffa yai masa bayanin komai. Idanunsa har rufewa suka soma yi, don tashin hankali, don haka bai tsaya jin sauran bayanin Mama ba. Ya mike ya fita yana gauraya hanya.
Mama ko murmushi ta yi ta-ce. “Fawzaan kenan. Sarkin kunya.”1
Ya dade a zaune a motar sa, don baya tsammanin zai iya tuna ina ne hanyar unguwar su bare ya kai kansa. Bai tashi sanin komai ba, sai ji ya yi hawaye suna zuba masa a idanu.
Dole ne ya samu mafita. Ranar bai runtsa ba, can da ya rasa abin yi, ajiye tunanin ya yi, ya shiga ya dauro alwala ya fara mika nafilfilu.
************ ****************
Ranar Juma’a yana fitowa daga masallaci. Gidan Dr. Umar ya nufa yana Parking ya wuce ciki, falon Abba dake nan ne wurin zuwansa kaf! Gidan. Yalwa ya gani tun daga karamin falo.
Ya sa ta kira masa Rumaysah idan tana gida. Ya kasa zama jira kawai yake yi, ta sauko ya ji dalili, yau sai ta raina kanta. Jikinsa hadaddiyar wagambari ne (Sky blue), ya sha hular zanna bukar, sai sintiri yake yi a falon.
A jirkice ta sauko daga Stairs din, doguwar riga ce (Peach Color) a jikinta har kasa, sai dai ya matseta gaba daya surarta a waje take. Cikin nan shafal! Kamar ba ta taba cin tuwo ba, rigar guntun hannu take da shi, gyalen da ke kanta kuwa, tsabar yanayin da take ciki na tashin hankali, rabinsa ne ya rufe mata rabin kai, yayin da sauran karshen yake tabo dunduniyar kafarta. A hankali ta karaso cikin falon, tabbas Yaya Fawzaan ne yake kiranta, domin kuwa ga shi nan a falon.
“Zauna”. Ya ba ta umarni, ita kuwa kamar wata mutum-mutumi ta yi yadda ya-ce din. Kare mata kallo kawai ya tsaya yana yi, can ya kau da kansa a ransa ya-ce. “Ina!”
Rumaysah dai kallon kurillan da Yaya Fawzaan ya sa ta a gaba da shi, tamkar wanda ya samu majigi na fim ne, ya soma ba ta haushi. “Yaya Fawzaan?”
“Wai ke dakikiyar ina ce? Ke wace irin mahaukaciya ce, ashe rashin sanin ciwon kan naki ya kai har haka? Abin naki kuma ya tashi akan kowa sai kaina zai dawo?”4
Dubansa take yi cikin bacin rai da kidima, saboda ba ta san dalilin wannan rashin mutuncin ba. “Me ya faru yaya Fawzaan?”
“Me… Me ya faru ki ke tambaya ta? Wane rashin hankalin ne ya shiga kwakwalwarki da har zai sa ki samu Abba ki fada masa cewa muna son juna? Wane irin wauta ke damun ki, da za ki yi wannan shirmen?”3
************
Oh, daman Yaya Fawzaan ne ake shirin hada ta da shi? Allah ya sawwaka, ranta ya yi masifar baci ta-ce. “Hmmm! Akan wane dalili zan je na yi karya akan hakan, bayan ni ko mafarki na yi wata wanda na sani za ta aure ka, zan farka naki barci, har tsawon sati guda saboda kar ma na kara ganin wannan mummunar mafarkin, ka auri wacce na sani ka bata mata rayuwa.
Idan ba ka sani ba, ka sani, me sonka zai amfane ni da shi? Kai ma ka san abin da ke tsakanin mu ba zai taba zama so ba. Ewww” Ta girgiza jikinta kamar ta sha daci ko ta ga abin kyama. “Da na aureka, gwamma na zauna ba miji”.2
Kwarai ya ji zafin maganganunta, amma shi ma yana cikin kuna. “Idan ba ki fada ba, to Uban wa ya je ya fada? Tunda daga wurinsu maganar ta fito.”
“Oho, wannan kai ya shafa, ni ba damuwata bace wannan. Saboda haka ka fita ka bar mana gidan mu.” Ji ya yi kamar ya tsinketa da mari, amma ya fasa, saboda bai taba dukan mace ba, sannan kuma azumi ne a bakinsu. Haka ya sa kai ya fice daga gidan, ba tare da ya cimma abin da ya kawo shi ba.
Yana fita, ta zube kan tumtum! din falon ta zage, iya karfinta tana risgar kuka, yanzu Abba ya fi son Yaya Fawzaan da ita? Har zai ce sai ta aure shi, ko tana so ko ba ta so?
A take anan ta-ce. “Na sha alwashin yadda ka sani ZUBAR KWALLA, a dalilin munanan kalaman da ka fada min, kai ma sai ka dandani bakin-ciki, sai na hana ka farin-cikinka kai ma.”7
********
Washegari da safe Raa’id ya shigo gidan ya samu Radiyya a falo. “To Sarkin kallo, kullum ke ba ki da aiki, sai rike Remote a hannu, wai ba ki gajiya ne?”
“Wai gajiya? Weekend din ne kawai mutum yake da lokaci, saboda daga litinin ya yi sai maganar aiki, kamar na bar aikin nan Wallahi, akwai wuya.”
“Kin iya cin kudi kuma ba. Ina Rumaysah ne, kwanan nan duk idan na shigo, ba na samunta a falo.”
“Hmm! Tana can sama hala, kwanan nan hakan ya fiye mata ne.”
“To ba ki tambayeta dalili ba?”
“Ba yadda ba mu yi da ita ba ta ki, to dole ne, mun rabu da ita, idan ta gaji da kanta za ta fada ai.”
“Kai, Radiyya, don me aka yi ‘Yan-uwa? (What are Sisters for?).4
Da kansa ya mike ya nufi dakin nata, yana bude kofar ya tsaya ya yi cak! Kwance take a kasan dakin, ta yi biji-biji da ita, kanta kamar na mahaukata, ga takardu tana karatu, amma fefofi sun yi goma a tsattsage, an dukunkuna an wurgar, dakin ya yi kaca-kaca da shi kamar ba dakinta ba.
“Rumaysah, me yake faruwa haka?” Tana ganin Ra’id, ai sai ta kara fashewa da kuka, cikin kukan ta-ce masa. “Ban san da me daya zan ji ba, na kasa gane wannan Assignment din.
An ba mu, na yi ya fi sau goma, na kasa samun amsa, sannan ba na gane karatun, sannan kuma zuciyata tana min zafi, ban san da me zan ji ba, sannan ga Yaya Fawzaan. Na yi hauka ko Yaya Ra’id ko dai ba ni da rai ne?”
A hankali ya isa gabanta, ya durkusa hade da rike hannunta. “Ki yi shiru Sister, ya isa haka, ba ki yi hauka ba, sannan da ranki, ki natsu ki fada min me yake faruwa? Wani abu Yaya Fawzaan din ya fada miki?”
“Oho, ya zo yana ta zagina yana fada min sunaye, sannan kuma wai meye ma?… Yawwa wai Abba ya-ce shi zan aura, idan na cika ‘yar halas. Momi kuma ta-ce sai dai ta mutu kafin ayi auren. Yaya Raa’id raba ni biyu za su yi?”
STORY CONTINUES BELOW
Kwarai ya tausaya mata ya-ce. “Ba mai rabaki biyu, za mu fada masu ba kya so, kuma dole su hakura, ji yadda ki ka dawo? Dubi dakinki? Ina tsabtarki? Har tsami dakin nan yake yi yuck!”
Ya fada hade da yamutsa fuska. “Yanzu abin da za ayi, ki tashi ki je ki yi wanka, zan turo Laminde ta gyara miki daki, ki ci adon ki, ki sauko kasa mu sha hirar mu.
Ki manta da wani wai shi Yaya Fawzaan. Hakan ko aka yi, ta yi fes! Da ita ta sauko tana yi kamar tana cikin farin-ciki, hatta Momi ranar tana gida, ta kuma ji dadin ganin ta haka.
Suna zaune wajen karfe sha biyu saura, sai ga sallama, sai wa za su gani? Yaya Shatu ce da Yaya Uwa tafe. Gaban Rumaysah ya yi mummunar faduwa, ta ji tamkar za ta saki fitsari, saboda idan ka ga Yaya Shatu ta zo, to wani gagarumin abu ya faru ko na ciwo, ko asara, ko mutuwa ko kuwa zancen aure.4
Ai ko ranar fuskarta cike da fara’a. Nan ta-ce “Ka ji wani batu mai albarka, kai yaran nan Allah ya saka maku da alkhairi, ya kara hada kawunanku, tuntuni abinda su Lamido ya kamata su yi kenan, amma suka tsaya wani abin daban. Gaskiya na ji dadi kwarai.”
Sanya albarka dai ya ki karewa, sai da aka gama gaisawa ne. Ashe wai nan su sun kawo kayan na gani ina so ne, musamman da suka ji labari a wurin Alhaji Lamido, suka hada kayan ya su ya su Goggoninsu wai na su gudumawar kenan.2
Sai ga shi an shiga jero kayan ana jibgewa, tamkar wani kayan lefe. Momi dai tafarfasa take yi, amma ba dama ta ce uffam, don sai Yaya Shatu ta zage ta tas! Ba abin da ya dame ta, don haka jira kawai take yi su tafi.
Ai kuwa suna wucewa, ta kira su Audu da su Mati. “Maza Audu ku kwashe wannan kayan ku mayar masu da tsiyarsu, can gidan Baffa za ku kai. Ko sun dauka mu matsiyata ne da za mu amshi abinsu? Za su wani sako Yaya Shatu a maganar.”
Nan take su Audu suka fara shirin jidan kaya, sai kawai suka ji Rumaysah dake tsaye a kusa da Stairs ta-ce. “Audu ku shigar da su wancan dakin kasan.”
Kallon ilahirin mutanen falon suka dawo kanta. Audu dai ya rasa me zai yi daya, ga Hajiya ta bada order ga shi ‘yar Hajiya ta take odan a gaban Hajiyar, ba tare da ta ce komai ba, don haka sai ya yi tsaye, ya rasa me zai yi daya.
Da hanzari Momi ta bi bayanta zuwa saman matakalar, inda ta kai mata damka, nan da nan su Audu suka watse. Su Radiyya ko tashin hankali ya bayyana a fuskokin su.
“Rumaysa, lafiyarki kuwa, kanki ne ya juye ko kuwa Tramol ki ka fara sha? Yaya zance a kwashi kaya a mayar? Sannan ki bude baki ki ce kar ayi hakan?”
Rumaysah ta shiga cikin tashin hankali, amma ta daure ta-ce. “Momi, ki yi hakuri, amma na amince zan auri Yaya Fawzaan.”19
Ba shiri Momi ta yi taga-taga kamar za ta fadi, kafin ta bude idanu Tas! suka ji saukar mari a fuskar Rumaysah. Su Yalwa dai rike baki suka yi, saboda kusan shekarar su goma sha a gidan kenan, amma ba su taba ganin Hajiyar ta daki ‘ya’yanta ba, sai yau.
“Ni Rumaysah, Ni za ki watsawa kasa a ido? Ina, kin yi kadan, ba za ki jawo min abin kunya ba. Daki auri jinin Sogiji, gwamma kin mutu ba aure”.
Mamakin kalaman mahaifiyarta ne, ya sa ta-ce. “Momi, don Allah ina neman alfarma daya, a daura min aure da Yaya Fawzaan, kafin ki kasheni, a kai masa gawata gidansa”.4
Hajiya Atika zamewa ta yi kawai kan landing din matakalar tana fadin. “Shi kenan, Sogiji ta asirce min ‘ya, shi kenan ta gama da ni, idan banda haka ba yadda za ayi jini na ya so sogiji bare zuri’arta.”6
Da sauri ta zabura ta tareta da gudu, ta sauka a stairs din, ko mayafi ba ta dauka ba, ta shiga sashin gidan Baffa, yayin da su Rai’d da Radiyya suka mara mata baya. Rumaysah anan ta zube tana kuka mai firgitarwa. “Momi ya zama min dole na yi wannan auren, saboda tabbas zuciyarki tana ba ni tsoro, dole na kawo gyara cikin al’amarinki da taimakon Allah.”7
STORY CONTINUES BELOW
“Ina Sogijin take, yau ki fito, duk abin da ki ke ji da shi, kin tara, kin samu.”
Mama ta fito tana jin murya, tabbas kuwa Atika ce ga ta a falonta na kasa, don tsabar masifa har dan-kwalinta ya karkace.
“Lafiya na ganki haka?”
“Dole ki tambaya mana, kin san me ki ka shirya ai. Ki bar ganin kin auri Yaya Lamido kin fito clean, za ki zo ki na yiwa mutane barazana ko an fada miki ba mu san daga Kofar Jange aka dauko ki ba a Dan-sadau?
Tsiya da talauci gadonku ne, a jininku yake, shi ne wato za ki yi iya kokarinki, don ki karkatar da hankalin ‘yata daga gareni ko ki shafa mata tsiyarki? To ko za ki mutu, jinina da naki ba za su hadu ba. Domin za ayi tashin hankali a gidan nan, hankula za su yi mummunar tashi.”
Hajiya Sogiji ta yi shiru tana ganin abin al’ajabi. “Hmm! Atika kenan sai dai hankula su tashi, domin kuwa da ba ni da niyyar sa kai a maganar nan, saboda sanin irin wannan hali da dabi’ar ta ki, sai dai kuma Rumaysah ba ke bace.
Don haka na sha alwashin Fawzaan baida mata, sai Rumaysah Bi’izinallah! Jininki sai ya hadu da jinina, sai dai idan ya hadu, ki zauna ki zuke jinin, ki ware na tsiya, ki bar na arziki.”9
Ran Momi ya yi masifar baci, ta juya za ta fita. Radiyya ta kai hannu don ta riko ta, da sauri ta fizge hannun cikin fushi sosai. Haka suka fita.
Fawzaan kuwa da ya shigo ta kofar baya, ya ji furucin mahaifiyarsa, nan da nan jikinsa ya dau bari, ya jinginu da jikin kofa, tun kafin ya sume. Da kyar ya samu karfi ya fita, sai dai ya sha fama, kafun ya tuno inda ya adana motarsa, zama ya yi a kujerar direba, ba tare da ya san me yake ciki daya ba.
Can ya tada mota, ya isa gida da kyar, kwanciya ya yi yana kallon silin din dakinsa, tamkar za su ba shi mafita, yana ji wayar tana ta ringing, bai dauka ba, ko bai daga ba ya san ita ce, mikewa ya yi ya shiga wanka. Fitowarsa still wayar tana kara. Ya san muddin bai amsa ba, za ta shiga damuwar rashin sanin halin da yake ciki, wannan ne ya sa shi daga wayar.
“Assalamu-alaikum.”
“Wa’alaikumussalam! Ya Allah. Fawzaan lafiya ka ke kuwa, me ya sameka?”
“Alhamdulillah! Me ki ka ji?”
“Na ji muryarka tamkar ba lafiya, ga shi sai waya na ke yi, ba a dagawa.”
“Gajiya ce kawai ta aiki.”
Ajiyar zuciya ta sauke. “To Alhamdulillah! Aiki kuwa ai dama sai hakuri, shi yana da wuya, kudi kuma da dadi ko?”
Dariya ya yi, wannan ne karo na farko da ya yi hakan, tunda ya tsinci labarin auren sa da Rumaysah. “Kin ce ki na nema na, me ya samu?”
“Kawai na ji ka shiru ne, kullum ka saba, kira mu gaisa, sannan cikin dare ka tada ni yin nafila, sai kuma na ji shiru jiya kaf!” Haka nan ya ji wani tausayin kansa, kwarai yake jin Meenarsa. Yaya za ayi ya auri wata baicinta?4
*************
“
Momi! Momi!! Don Allah ki bude ta, ki yi hakuri….” Cikin kuka Radiyya take bin Hajiya Atika, amma ba ta ko bi ta kanta ba, don haka da gudu ta sauka ta isa sashen Ra’id ta-ce. “Yaya Ra’id ka zo ka balla kofa. Momi ta kulle Rumaysah a (Toilet).”3
Da sauri suka dawo tare, sai dai Momi ta tsaya a gabansu ta-ce. “Duk wanda ya kuskura ya isa wurin kofar nan, sai nai masa mummunar baki.”
Haka suka tsaya cak! Radiyya ta lalubi wayar Abba, hankalinsa ya yi mummunar tashi jin abin da yake faruwa, cikin hanzari ya nemi wani Likita ya-ce, ya duba Patients dinsa yana da Emergency a gida.
STORY CONTINUES BELOW
Yana zuwa, ya kaiwa kofar bugu, sai da ta kusa rabewa biyu, a kwance ya sameta a kasan (Toilet), sai kakkarwa take yi, banda haka, ba ta ko iya kwakkwarar motsi, ta kusa sumewa. Tabbas ya san yanzu kam matarsa ta haukace, idan banda haka, bai taba ganin irin wannan gabar ba.
Dole Rumaysah ta shiga wannan yanayi. Kinkimarta ya yi, bai bi ta kan Momi ba, ya-ce. “Radiyya, dauko mata mayafi da takalma ki zo mu tafi.”
Suna isa asibitin, aka dora mata ruwa, don ta galabaita, ga ciwo ga sanyi ga yunwa. Nan da nan kwararrun Likitoci da Nurses suka rufu a kanta, kasancewarta ‘yar mai asibiti. Ransa a bace, haka suka yi zaman jinyar Rumaysah, wuni ta yi tas! Ba tare da ta san inda take ba.5
Baffa da Mama ne suka shigo asibitin a kidime, bayan Rai’d ya shiga, ya fada masu ga Rumaysah a asibiti. Momi ta kulleta a (Toilet) ta kwana.
Abba yana ganin su, suka gaisa suka jajanta abin da ya faru. “Umaru ka ga irin abinda na ke fada maka ko? Shi ya sa nace wannan abin da an hakura da shi tun farko. Tunda maganar auren nan ne ke kawo tashin hankali tun yanzu, ina ga idan an yi kuma fa?”
“Yaya Lamido, ba mai hakura da komai, aure kuma kamar anyi shi, an gama, sai dai ta hallakata. amma Rumaysah na farfadowa za a daura auren nan Insha-Allahu.”
Ganin kafiyar Dr. Umar ya sa Alhaji Lamido yin shiru, kan al’amarin.
**********
Kansa na cikin tafin hannunsa, ya shigo ofis din ya same shi. “Wai Fawzaan me yake damun ka ne kwana biyun nan, duk ba ka cikin hayyacinka, hatta aikinka ba ka maida hankali sosai?”
Dagowa ya yi cikin dimuwa ya-ce. “Dole na fada mata gaskiya. She deserves the truth”.
“Dakata me yake faruwa?”
“Rayyan ban san yadda zan fara fada maka ba. Ka dai san yadda na ke son Meena. Wallahi satin da ya wuce na samu kaina cikin wani irin tashin hankali marar misaltuwa.” Nan ya fada masa, duk abin da yake faruwa.
Tabbas Rayyan ya san Fawzaan ba zai taba yaudarar kanwarsa ba, a dalilinsa ya san Meena kuma shi zai bada shaidar, ba zai ha’inceta ba, don haka ya-ce.
“Kar ka damu, na fahimta amma ni ban ga damuwar ba anan, ka ga kai mijin mace hudu ne, ba sai ka auri wacce iyayenka suke so ba, sannan ka auri wacce ka ke so?”
Fawzaan ya yi murmushi, a ransa kuwa kwata-kwata ya tsani koda kwatanto sunan Rumaysah a matsayin matarsa ne ayi.
Daga Office gidan su Meena ya wuce, duk da yana tunanin yadda zai gabatar mata da wannan maganar, amma ya zamo masa dole. Kallonsa ta tsaya yi, bayan ya gama kwararo zance, ba ta san lokacin da hawaye suka shiga rigegeniya akan fuskarta ba.
“Meena, don Allah kar ki tada hankalinki kan maganar nan, da na san za ki tada hankali. Allah da ban fada miki ba, sai na warware matsalar, ganin wai Baba ya dawo ne daga tafiya, shi ya sa na fada miki abin da ake ciki, kar ya ji shiru, ya dauka ko wasa da hankalinki na ke yi. Insha-Allahu yau din nan zan je na yi wa su Baffa bayanin komai, na kuma kai masu maganarki.”
Goge hawayenta ta yi, ta daga idanun sama da niyyar ta shanye masu fitinar da suka ki tsayawa. “Ba komai, Fawzaan jarabawa ce, daman komai Dan-adam zai yi a rayuwa, sai Allah ya hada shi da jarabawa. Allah ya ba mu ikon cinyewa. Allah ya ba mu sa’a”.4
“Ameen, ko ke fa ki min alkawari don Allah za ki kwantar da hankalinki. Kin ji? Ba ki san hankali na yadda ya tashi ba, da na ga hawayenki.”
“Insha-Allahu ba zan damu ba.”
“Yawwa ko ke fa, dan yi murmushi na gani.” Nan ta hasko masa fararen hakoranta, sannan suka koma wata hirar daban kafin ya-ce mata. “Zan wuce na samu Baffan, duk yadda muka yi Insha-Allahu za ki ji ni.” Har jikin motarsa tai masa rakiya, amma hakikanin gaskiya, jikinta ya mutu.
STORY CONTINUES BELOW
A daren Fawzaan ya samu Mama akan shi fa gaskiya ba Rumaysah yake so ba, yana da wacce yake so. Duban shi ta yi tsab! Ta-ce.
“Ka na jin me na ke fada maka kuwa? Yarinyar nan saboda kai, uwarta ta kulleta a bandaki, amma ta jajirce ba za ta janye ba, kai take son aure, kai in takaice ma cewa ta yi ko uwar za ta kasheta.
To a daura maku aure kafin a kasheta, sai akai gawarta gidanka. Shi ne kai za ka zo min da wannan maganar? To karshen magana ma Likita ya-ce tana barin asibiti, za a daura aurenku, ni a gani na, ka bar komai a hannun Allah. Ka roke shi zabinsa kawai ya fi ma.”
“Don me ya sa zan auri jinin Momi Mama, bayan a idon mu ba abinda ba tai miki ba na keta da gaba?”
“Saboda iyayenku, wai daman dalilin dai don a gyara tsakani ne, yanzu jinka idan daya daga cikin Abba ko Baffa zai fadi. Atika ba za ta raba zumunci bane? Hikimar da iyayenku suka gani kenan a cikin wannan hadin”.
“Na ji Mama, zan yi tunani”.
Ya mike ya bar dakin ransa a cunkuse. tabbas ta san ba karamin takura Fawzaan aka yi ba, don tsakaninta da shi biyayya, amma yau bayan ya yi sa in sa da ita ma, har cewa ya yi zai yi tunani tukun, kan ya ba ta amsa. “Ya Allah ka kawo mana mafita a al’amarin gidan nan”.
Kwanan Rumaysah uku a asibiti, amma Momi ko lekau! Ran Abba ya yi masifar baci akan hakan. Daga asibiti gidan Baffa ya kai Rumaysah.
“Za ki zauna anan, har sai na shawo kan komai, idan ta ga dama ta biyo ki nan din, ta hallaka. Radiyya za ta kawo miki kayan da za ki bukata.”
Cikin tashin hankali take duban Abba, yanzu ita kuma me ya kai ta zama gidan Baffa? Yaya za ta fara zama a gidan? Amma ba ta da ikon yin wannan tambayar, don haka tana ji, tana gani. Abba ya damkata hannun Mama. Sashin gidan sa ya shiga kai tsaye dakin Momi ya wuce, ya sameta a ciki.
“Shi kenan, burinki ya cika, hankalinki sai ya kwanta, kin haddasawa ‘yarki ciwo, kin kusa kasheta.”
Furucin da ya fito a bakin Momi ne, ya razana Abba. “Gwamma da mutuwar ta yi ai, da ta janyo mini abin kunya.”
Salati ya sa, ya sanar da mai duka. “Atika anya akwai imani a cikin zuciyar ki? Wace irin gaba ce wannan da har ta wuce kowa ya tsallako ya shafi ‘yar cikin ki, da ki ka haifa?3
Menene amfanin sujjadarki da ruku’u, idan dai haka ki ke da muguwar zuciya. Gwamma kin daina wahalar da kanki wajen yunwa da kishin ruwa, domin ban yi tsammanin azuminki na da amfani ba.
Kin yi ta min abubuwa, ina dauke kaina, wannan ba yana nufin ba ni da ikon daukar mataaki bane a kanki, amma yanzu kin kureni, zan jurewa haukarki da shirme.
Amma Allah ya gani, ba zan iya zama da mai zuciyar kafirai ba, don haka idan kin ga dama, ki tafi Gusau. Idan kin ga dama ki yi zamanki, amma ni kam na sake ki, saki daya.”6
Yana fada mata haka, ya fice a dakin, anan kasan dakin ta durkushe ta fara risgar kuka. Yau ita Atika, ita Atika Likita ya fadawa kalmar saki? Ko a mafarki ba ta fatan ganin wannan ranar, sai ga shi ido na ganin ido a zahirce ta gani, duk saboda Sogiji. Wannan bakin-cikin ya sake sa ta dau kudurin, ba yadda za ayi auren nan.4
Har dare tana daki, ko abinci ba ta ci ba, sai aukin kuka, kafin daren kuwa labari ya bazu ilahirin gidan akan Abba ya saki Momi. Hankalin yaran idan ya yi dubu Ya tashi.
Saboda sun tashi sun ga iyayensu na matukar son juna da kula da juna, ga wata rayuwa da suke yi ta ban sha’awa. Ba su taba kawo rabuwa a tsakanin su ba, wannan ya sa duka yaran suka hadu da dare suka samu Abba.
Khadija ma ta taho daga gidanta. Rumaysah ma daga gidan Baffan ta fito. Khadija na ganinta ta banka mata harara. “Hankalinki ya kwanta kin kashe masu aure, to wai dole ne auren Yaya Fawzaan din, da ki ka kafe a kai?”
STORY CONTINUES BELOW
Tsawa Abba ya daka mata. “Ki yi shiru, ba na son jin wani abu. Idan akwai wani mai laifi a mutuwar auren uwarku, to Momin ce da kanta, saboda tun ba yau ba take min abubuwa na ke hakuri.
Amma kuma lokaci ya yi da za ta san ba zan lamunci duk wani shirirtarta ba, zama ne da ita ya kare. Don haka ku yi hakuri ku ci-gaba da al’amuranku, kar ku ce za ku bar wannan ya dameku.”
Gaba ki daya suka sa masa kuka. Ra’id ya-ce. “Abba, dole hankalinmu ya tashi, saboda mun tashi mun ganku tare, ta yaya za mu fara sabawa ta yaya za mu iya rayuwa, alhali ku na cikin kunci? Ka taimaka ka maida Momi dakinta. Shi ne kawai abinda za ka mana”.
Tausayinsu ya kama shi, amma gabaki daya shi ya san me yake ciki, don haka ya-ce “Ku je, zan duba na gani.”2
Jikinsu a sanyaye suka tashi. Abba ya-ce. “Khadija ki koma gidan ki dare ya yi, sannan ki kwantar da hankalinki, kin ji ko?”
Kai kawai ta daga masa, sannan ta wuce gida, ko da ta koma, ba ta bar kuka ba. A haka Labeeb ya shigo gidan ransa a bace, saboda ganin motarta da ya yi yanzu, don tun dazu ba ta gida. Hakan ya bata masa rai, don ya fara gajiya da fitar da take yi ba tare da izini ba, tamkar ta maida shi ba kowa ba, ko baida iko a kanta.
Amma ganin halin da take ciki, ya sa ya maida nasa fushin, ya isa gareta. Nan ta zayyane masa abin da ake ciki cikin kuka.5
“Ki yi hakuri, komai zai wuce. Insha-Allah za su shirya. Kin ji? Abin da za mu yi, shi ne mu taya su addu’a, kin ji?” Nan da nan ya jawota jikinsa, yana rarrashinta.5
************
Tana kwance akan doguwar kujera a falon sama na Mama, wani littafi take nazari. Kwatsam! Sai ga shi ya shigo falon, kanta ya nufa, da sauri ta zabura ta zauna.
“Wai ina son ki fada min, me yake damun ki ne, da za ki haddasa irin wannan fitina, sannan ki zauna lafiya, kamar ba abinda ya faru?”
Dubansa ta yi a sanyaye, sannan ta-ce. “Ina da dalilina.”
“Wane irin dalili ne, zai sa ki na ji, ki na gani auren iyayenki ya mutu? Idan banda irin gurguwar tunani irin naki? Ashe ki na da halin yin gyara a wannan al’amari, ba za ki yi ba?”
Mikewa ya yi daga kan kujerar zai tafi, da sauri ta kamo bakin rigarsa, ya tsaya, ganin zai saurareta, ya sa ta sakar masa riga.
“An fada maka ni ma ina jin dadin ganinsu da na ke yi a haka ne? Sam, ba son raina bane, amma na daure na kauda kaina, saboda mu kawar da gagarumar matsalar da ta fi wannan.
Na san halin Momi, tana da fada, tana da rashin son gaskiya, amma kuma haka tana da saurin nadama, na san za ta nemi afuwa, kuma Abba zai saurareta. Sai dai wannan tafiyar, dole ka taimaka ka ba ni goyon baya, don mu shawo kan al’amarin nan tare.”
Kallonta ya yi, ita ma duk ta jikkata, ta jejjeme ta zama wata iri, tabbas yadda take ji haka yake ji, koma fiye, don bayan baya sonta, ya tsani uwarta, sannan yana mutuwar son Meena.
“Ki yi hakuri, amma ba zan iya aurenki ba.”
Ranta ya baci kwarai, har ya juya zai fita ta-ce. “Saboda me ya sa ba za ka iya aure na ba? Saboda me ya sa ban kai matsayin na zamo matarka ba?”
“Ki fada min, ta yaya zan iya zama dake, alhali ki na matsayin ‘yar matar da na tashi da tsanarta a zuciyata?”
“Wane irin dalili zai sa maka tsanar mahaifiyata, har da zai sa ni ba za ka iya aurena ba?” Shiru ta yi don ta ji dalilin wannan tsanar.
Ajiyar zuciya ya yi, sannan ya-ce. “Akwai randa Mama ta tafi Kano wurin Goggo Uwa, an mata aiki tana kanta, daidai wannan lokacin ni kuma zan tafi makarantar kwana. Baffa ya gama min shirye-shirye na, ya-ce nayi wa Momi sallama, sai a kai ni. Budan bakinta da ta ganni, shi ne.
STORY CONTINUES BELOW
“Allah ya sa motarku ta kife a hanya, ka mutu kar ka sake dawowa, makirin yaro.” Yaya mutum wanda ya haihu zai iya kallon dan yaro mai shekara goma ya fada masa wannan kalmar.4
Bayan da iliminsa da komai, sai tsabar gabar da ya yi mata kanta? Don haka ba aure ba, ko meye ne, ba zai sa Momi ta shiryu ba. Sai dai wani ikon Allah din.”
Nisawa ta yi, don hakika ita ma ta kadu da ta ji dalilinsa, tabbas Momi za ta iya fadan komai idan tana cikin bacin rai, don mafadaciya ce ta karshe. “Shin idan za ka ki aure na don kiyayyar da ka ke yiwa Momi, ba za ka aureni don soyayyar da ka ke yi wa Mama ba?”6
Runtse idanunsa kawai ya yi, wadanda suka yi ja, ya wuce ya bar falon, ba tare da ya ce mata komai ba. Bin shi ta yi da kallo, ta yi murmushi, sannan ta daga littafinta ta-ci-gaba da karatu.
Ranar litinin sai ga ta cikin shirinta fes! Ta fito cikin wata doguwar riga mai launin koren ganye, ta yafa siririn bakin mayafi. “Mama ina so zan shiga makaranta, don na duba abubuwan da ake yi.”
“Dama ba ku yi hutu bane tuntuni?”
“A’a sai gobe za mu fara jarabawa Insha-Allah. Amma dai an turo min da (Time table), tuntuni yau din zan shiga na ga abin da ya tsere min ne.”
“To Allah ya bada sa’a. Ya taimaka, ki tafi a hankali dai.” Wata natsuwa Rumaysah ta samu, domin kulawar da Mama ta gwada mata. Ta rasa me ya sa Momi ta tsani Mama haka. Tana shiga makaranta. Firdausi ta fara nema.
“Wai har yanzu maganar ce haka? Kin ga yadda ki ka yi rama? Me ya sa ne?”
“Ke mu bar wannan maganar, yaya Mai-gidan?”
“Lafiyarshi lau, kin ki ki zo har yau.”
“Ke don Allah na gaji da zuwa gidanki kullum ba kya nan kamar wata shanshani, sai yawon masifa.”
“To wannan Week din Insha-Allahu zan zauna, bare ma sallah ta gabato ga mai rai, ayyuka kadai sun ishi mutum, don Allah na damu dake, ki fada min me yake faruwa?”
“Wasu lokutan rudani da matsanancin damuwa ya kan afkawa mutum a lokacin da bai tsammanince shi ba, har ya sa mutum a wani wuri mai duhu da kuma wuyar fita.
Bakin-ciki ne kawai a kewaye da mutum a wannan lokacin, wanda ko waje ba zan iya fita ba, na zabi na koma na zauna cikin wannan duhun, saboda nan ya fi min sauki akan kokawar fitowa. Ina fatan kin fahimta?”
Firdausi ta saki ajiyar zuciya, sannan ta-ce. “Ki dai kara min haske.”
“To ki jira sai na zo, yanzu kam bari na nemi su Naja’ah mu yi karatu, don kin ga kaina empty, ban san komai ba akan paper din da za mu rubuta gobe.”
“Ke ce ai, Einstein din mu, ba matsala Insha-Allahu”. Rumaysah ta dubi Firdausi a sanyaye, domin kuwa Saleem ne ya sa mata wannan sunan.
“Sorry, ban yi niyya..”
“Kar ki damu, ya wuce wannan wani shafi ne da ya shude a rayuwata, kuma ina shirin bude wani.”
Har yamma can tana makaranta, karatu kawai take yi, ba ji, ba gani, sai wajen shida saura ta bar Gwagwalada, ta kama hanyar cikin gari. Isarta an riga anyi sallah, kicin ta wuce kai tsaye ta samu Radiyya da Plate shake da Fruits, nan ta dauki daya ta-ce. “Ke za ki cika cikin ki dai, ki kasa cin abinci.”
“Hmm! Sis ba ki san yadda yau na gwaltu ba, ana cewa goma na wuya, gaskiya aka fada, don yau kam azumin ba laifi.”
“Sannu da kokari, ni da na wuni karatu fa, ya kwakwale min ciki? Allah dai ya amsa mana.”
Daga nan sama ta hau ta yi sallolinta, sannan ta yi wanka ta dawo falon Mama, anan suka baje suna cin abinci har da ita Maman, sai ga Fawzaan ya shigo gaisheta.
Radiyya ma ta gaida shi, amma Mama na kula ko kallon juna ba su yi ba, shi da Rumaysah bare magana, haka ya tashi ya fita. Yana fita Mama ta-ce. “Ahaf na manta, Rumaysah je ki kasa ki ce Yalwa ta ba ki Flask din Yayanku, sai ki sa masa a mota.”4
A sanyaye ta mike ta sauka kicin din, tana fita ta ga su Baffa da su Aasim, da mutane sosai a wajen, ta yi tunanin ta koma ne ta ajiye a kicin, ko kawai ta ajiye masa a cikin mota?
Don haka ta matse kawai, ta yi masu sannu, sannan ta nufi inda ya yi Parking. Kai tsaye ta je za ta bude motar, sai ta ji ta gam a rufe. Numfashi ta sauke da niyyar za ta juya, sai ta ji ya-ce. “Kar ki balla min mota, me za ki dauka a ciki?”
Juya idanunta ta yi, sannan ta-ce. “Mama ce ta-ce na ajiye maka Flask din abin suhur dinka a mota.”
Remote ya danna motar ta budu, sannan ta ajiye a kasan motar, ta gyara ta fito za ta rufe motar. Ashe shi ma zai rufe, don haka ya hada da nata ya manna shi da kofar, ai kuwa nan ta saki uban kara, sai da ilahirin jama’ar haraban gidan suka dawo da hankulansu can. “I’m so sorry, yi hakuri ban san hannunki na ciki ba na gani?”
Kin nuna masa ta yi, tana ta yarfe-yarfe ta-ce. “Shi kenan ba zan iya rubuta jarrabawana ba. wayyo ka cuceni.” Aasim ne ya iso da gudu ya-ce. “Lafiya me ya faru?”6
“Banda Yaya Fawzaan ne ya guntule min yatsun hannuna a kofar mota.” kada kansa ya yi ya rabu da ita.
Rumaysah ko ta koma cikin gida, sai raki take yi, wai ya sa ba za ta iya rubutu ba gobe jarrabawarta, alhali hannun dama ta matse, kuma da hagu take rubutu. Sai da Baffa ya sa shi a gaba, wai su tafi asibiti a duba yatsun nata.
Da ta san da shi za a hada ta, da ba ta langwame har haka ba, ran Fawzaan a bace kwarai ya figi mota. “Kawai ba ki saba da jin zafi ba, kin je ki na ta wani langwami, kamar yau ki ka fara jin ciwo, haka ake yi ne? Wa ya ce ki sa hannunki a wurin murfin mota, idan banda kauyanci?”
Haka ya yi ta surfa mata masifa, har suka isa, asibitin Dr. Umar, ya kai ta kai tsaye suna zuwa, matar ta shiga gaida Fawzaan, ta fito da Folder din su na family. Sai dai kam da gaske kan su isa asbiti, hannun ya kumbura suntum!1
Sai ya ji tausayinta, amma bai nuna fadan ya kare ba. Likitan da yake asibitin a lokacin, ya duba yatsun ya-ce. “Ba matsala, ga wannan cream din, na rubuta sai ku karba a shafa, na hada miki da maganin da zai taimaka da zafin ya sauke kumburin kuma.”
“Mun gode Dr. Williams.” Fawzaan ya fito ya yi gaba, nan ne Rumaysah ta zumbura baki ta-ce. “Yaya Fawzaan.”
Ya juyo ya dubeta. “Ba zan iya daukar jakata ba.” Ta rungume hannun da daya hannunta, jakar ko na ajiye saman tebur din Dr. Ya dawo rai a bace ya-ce. “Wani gulman da kinibibi ya sa ki dauko jaka yanzu? Me za ki yi da ita”1
Ya daga ya rataya mata a gefen kafada. Dr. Williams yana ta masu dariya ya-ce. “Barrister help her with the bag, please.” Tsaki ya ja, sannan ya wafce jakar ya rike mata, ya sa ta a gaba, ita ko dariya ya so ya kubce mata.7
Yana sauketa, ya mika mata magungunanta da jakarta, kafin ta gama sauka a motar, ya fizga, saura kadan ta fadi. Ta bankawa motar harara.
***********