AMAREN BANA CHAPTER 8 KARSHE

AMAREN BANA CHAPTER 8 KARSHE

Bayan kwana biyu da faruwar hakan ne. Meena ta fada masa Baba ya tsaida rana, nan da wata daya, akan ya fadawa su Baffa ko hakan yayi masu. Duk da ya dade yana jiran hakan, wannan ne burinsu su biyun, sai ya samu kansa da cewa.4 “Meena zan yi tunani akai, saboda a halin yanzu Rumaysah ba ta jin dadi, ina son a ba ni lokaci ta dan kara samun lafiya, sannan na sanar da ita, kin san na fada miki Heart problem ne da ita.”2 Meena shiru ta yi tana jinsa har ya gama. “To shi kenan. Allah ya ba ta lafiya”. Yana tafiya, ta samu Hajiyarta ta fada mata yadda suka yi da Fawzaan. Ran Hajiyar ya baci kwarai. Ta-ce. “Na rasa me ya sa ki ka nanewa Fawzaan din nan, da yana son ki, zai yi ta miki wasa da hankali haka? Kafin ayi tambaya haka ya yi ta yi, sannan yanzu batun sa ranar ma yawo zai yi da hankalin mu?” “Hajiya ki yi hakuri, don ya bada uzuri ai.” “Ki min shiru, auren ki zai hana matarsa rashin lafiya?” Haka dai Ameena ta yi shiru. Ranar juma’a ne aka yi waya Yaya Shatu ba lafiya, don haka Fawzaan ya-ce zai tafi, don ya dubo jikin nata. Rumaysah ma ta-ce za ta je. Ya-ce. “Ke da ko gidan ki ba ki koma ba. Yaya za ki fara batun wani tafiya zuwa wani gari?” “Don Allah ka yi hakuri, ka bar ni na je. Wallahi raina na son ganinta.” Jin hakan ya sa ya yi shiru, abinka da ciwo, mutum baya ciwo ma, ba ka sa ran sake haduwarku, bare ba lafiya kuma ya san irin shakuwarsu. Bugu da kari baya son wata damuwa a tare da ita. Don haka ya amince ta shirya. Tare da Aasim za su wuce, don Baffa da Abba kam sun yi gaba. Sai da suka zo shiga mota ta-ce. “Amma don Allah ina fata yau kam ka sha mai me kyau, don gaskiya ba za a sake juyar da ni ba, a wata motar.” Dariyarta ya yi da ya tuno ranar. Sun sameta a asibiti, jikin dai ba laifi da dan sauki, amma daga gani ta wahala cikin kwanaki biyun da ta yi a kwance. Kasancewar gidan Yaya Shatu babban gida ne. Rumaysah a nan ta sauka cikin Cousins din su, yayin da Aasim da Fawzaan suka sauka a bangaren mazan. Sai da magriba, sannan suka koma gida. Rumaysah kuwa tunda ta tafi da Yaya Isyaka da matarsa, ba su sake haduwa da Fawzaan ba, da Issha ya shigo har dakin da take ya sameta. Daf! Da ita ya isa ya zauna ya-ce. “Ya kamata fa ki huta, kin san lafiya ba ta isheki ba, tun dazu ina ki ka shiga ne?” “Ina side din Yaya Isyaka, kai ma ba sabgarka ka tafi ba.” Ta fada hade da nade hannayenta a saman kirjinta, cikin fushi. Murmushi ya yi yana kallonta, sannan ya lumshe idanu ya-ce. “Ke ‘yar daru ce Wallahi, Sai ki ka ci sa’a kuwa yana miki kyau. Shi ya sa na ke sonki…”23 Yana fadan haka. Rumaysah ta yi saurin juyowa suka hada idanu, shi ma ita yake kallo sun dauki lokaci a haka, kamar ya wayance ya-ce kuskure ya yi, amma ya ji ya gaji da wannan wasan buyon da suke yi. Fuskarta ya tallafo cikin hannunsa, yana shafa gefen kuncinta ya sake cewa. STORY CONTINUES BELOW “I love you Rumaysah.” Gudun bugun zuciyarta ne ya karu har take tunanin zai fasa mata kirji. Ba ta san yaushe hawaye suka zubo daga idanunta ba. Hannu ya sa a hankali yana share mata su, ita kanta ba ta san na meye ba. Farin-ciki ne ko kuwa haushin rufeta da ya yi ya bar ta tana ta wahala ita kadai?7 Can ta nisa ta-ce. “Me ya faru da maganganun da ka fada na cewa ni matar kaddara ce a gareka? Ko kuwa sai da ka zo Kaduna ne, za ka ce min ka na so-na?” Kansa ya sauke cikin jin nauyin abin da ya yi. “Rumaysah, ina son ki mance da duk wani abin da ya gabata na batanci tsakanin mu, wannan a baya ne ya shige. Ina sonki, kuma ke kyakkyawar qaddara ce a gareni, wannan ya sa na ke godewa Allah.” Wani hawayen farin-ciki ne ya sulalo mata. “Shi ne sai yanzu za ka fada min?” Ta fada a shagwabe. Harararta ya yi cikin wata siga ya-ce. “Yaushe ki ka ba ni damar na fada miki?”4 “Ni kuma sau nawa ina fada maka, ka kasa fahimta, shi ne sai yanzu ka ga daman fadi?” “Kodai Rumaysah dari na ke da a rayuwata? A iya sani na, ba hanyar da ban bi ba wajen nuna miki”. “Ina za ka iya da Rumaysah dari, bayan guda ma ta gagare ka?” Hannu ya sa ya rike kunnensa, sannan ya-ce. “Ina neman afuwa. I’m sorry da na sa ki cikin kunci na munana miki. I’m sorry da ya kai ni yanzu kafin na fahimci cewa ina matukar sonki”. “Ni ma ka yi hakuri da duk abin da na taba maka, daga yau na daina yi maka musu”.5 “A’a kar ki daina, ki na min dan kadan, karfe shida zuwa bakwai na dare.” Ya fada hade da kashe mata ido daya.6 Dariya suka yi ya lakaci hancinta, ba tare da idanunsa sun bar nata ba, ya duka zai sumbaci labbanta masu dimauta shi ne, sai ga su Maryam da Hajara sun shigo dakin. Da sauri ya janye daga Rumaysah, hade da dunkule hannunsa cikin jin zafi. Rumaysah kuwa ta yi murmushi, tana kallon sa. “To mai mata, sai ka fita ‘Yan-uwanka na nemanka, ka zo ka wani matsa mata”. “Ba za ku gane bane, tana bukatar hutu ne, shi ya sa na zo don ta samu ta kwanta, kun san ba ta iya barci, sai ina gefenta.”4 “To da ka zo din tausa za ka mata ne?” Dole suka sa ya fita, ya bar masu dakin, don sun yi masa caa! Yana fita, suka sa dariya. Yayin da zuciyar Rumaysah ko dadi fal Ne baya misaltuwa. Da kyar idan ta yi kwakkwarar barci ranar, sai tuno abinda Yaya Fawzaan ya fada kawai take yi.4 ***** Da safe tana shiga karamin falon Yaya Shatu, kawai ta ji an jawo ta gefe. Yaya Fawzaan ne. “La! Yaya Fawzaan me ka ke yi?” “Good morning, haka kawai an hana ni ganin matata.” “Yaya ka san ni zan shigo falon yanzu?” Ta fada tana waige-waige. “Saboda na san kamshinki.” Ya rada mata a kunne. Ture shi ta yi ta matsa gefe sannan ta-ce. “Kawai daga fadin ka na so-na kuma sai ka zake?”6 “To me ki ke so na jira?” Yana fadin haka, sai ga Hajara ta shigo falon. “Oh! Ku dai sha’anin ku sai ku, mutum kamar za a sace masa mata, ko ina sai gadi? Lallai Rumaysah ana shan Love.” Kunya duk ta rufe Rumaysah. Da sauri ta fice daga falon ta yi kicin din cikin gidan, can ya bi-ta ya zo daf kunnenta ya-ce. “Na ga alama danginmu sun sa mana ido, ki shirya mu duba Goggo Shatu a asibiti, za mu koma Abujan mu, ko zan samu sakewa, ba takura.” Murmushi ta yi masa, sannan ta bar kitchen din. STORY CONTINUES BELOW Sun duba jikin Yaya Shatu gaskiya da sauki, don akwai bambanci tsakanin jiya da yau. Yaya Shatu ta dubi Fawzaan ta-ce. “Ina fata dai ba ka sake ajiye mata kayan budurwarka ba a gida?” Kunya ta kama Rumaysah, suka shiga yi mata dariya, sauran jama’ar dake dakin kuwa, ba su gane me Yaya Shatu take nufi ba, su kai mata fatan samun lafiya, sannan suka fito. Yana cewa. “Duk ke ki ka jawo”. “Ni na jawo ko kai, waye ya ki bayani tun farko?” Tun daga asibiti ya bude mata kofar dake bayan na mai tuki, ya-ce ta shiga nan. Ya san sarai me ya shirya, domin kuwa suna tafe, sai kallon matarsa yake yi. Can Aasim ya gaji ya-ce. “Yaya Fawzaan titin a gaba yake dai.” Fawzaan ya make keyarsa ya-ce. “Me ruwanka, ka kalli gabanka.”5 Rumaysah kam ba ta tanka ba, sai aukin murmushi take yi. Suna isa, ita ya ajiye a gida, sannan ya wuce gidan Baffa. Fawzaan na fita ta wuce gidan Anty Safiyya, tun daga bakin kofa ta fara ihun murna. Anty Safiya ta bude kofa tana fadin. “Lafiya Rumaysah, me ya faru?” Wuceta ta yi kawai, ta shige ciki tana fadin. “Anty Safiyya, ba za ki yarda da abinda zan fada miki ba.” “Dole na yarda, wannan irin farin-ciki haka? Sai ka ce Fawzaan ya mance da Meena?” “Wannan labarin ya fi wancan dadi, domin kuwa ya yi Confessing, ya-ce yana so-na.” Sai ga Anty Safiyya ma da ihun murna, sai kuma suka koma cewa Alhamdulillah! “Kin ga ikon Allah ai, na fada miki a hankali zai fahimci muhimmancinki, kuma idan Allah ya so, zai so-ki kamar yadda ki ke son sa, tsakani da Allah. Amma dai ke ce ba ki gane ba. Yaya Fawzaan ya dade yana sonki, saboda da baya sonki, ba yadda za ayi al’amuranki su dame shi. Kin ga idan ba ki da lafiya, yadda hankalinsa yake tashi kuwa?” “Hmm! Haka ya-ce wai ya yi ta nuna min, ni ce naki fahimta. Ai kuwa har yanzu na kasa amincewa.” Lokacin ne ta bawa Anty Safiyya labarin tafiyarsu Kaduna dubiya. “Wai, ki ce yau amarya ki ke sabuwa dal!” Murmushi ta yi ta rufe fuskarta, sannan ta-ce “Anty Safiyya, wace amarya kuma yanzu fa watannin mu kusan bakwai da aure.” “Ah to ana tsufa ne, kin ga ko ni nan amarya ce, domin kuwa komai na sabo dal! Ne, har sai na fi wata amaryar wata dayan ma. Ai sai yadda mace ta ga dama za ta zama a gidan ta ko ta zama amarya ko uwargida, ko kuwa ma ta zamo uwargida kuma amarya, tunda idan mutum yana da dattaku da kamun kai. Sanin ya kamata da hakuri, to dole a dora mata mukamin uwargida. Idan ko ki ka hada da kwalliya, iya tarairaya, sabbin girke-girke, raki da sauransu, sai ki zamo uwargida kuma amarya a wurin mijinki. Koda da wasu kuwa tauraronki, sai ya fi shanawa.”4 “Wai, har kin sa na ji aiki ja ne a gaba na.” “Ai ke na yarda da ke ba ni da haufi, yanzu dai wuce mu je ki sha gyara, don yau har kunshi sai an miki, yanzu zan kira Anty Hauwan Katsina, don tana gari. Yanzu ta zo ta sauya miki kammani. Karfe nawa zai dawo?” “Ban sani ba, may be ya kai maghriba, don gidan Baffa ya tafi, idan ya-ce don shi na zo, na yi gayu fa?” “Da bai san ki da gayu bane ko me? Kuma idan ya san don ki faranta masa ma ki ka yi, ai sai ya kara jin dadi.” Nan take Anty Safiyya ta danna wayar Anty Hauwa mai lalle. An ci sa’a kuwa ta kammala wani aiki kenan, ga shi sun saba da Anty Safiyya. Zuwa karfe biyu sai ga ta ta zo. Nan suka shiga aiki. Kafin biyar Rumaysah, sai wani kyalli da kamshi take yi, ga lalle an zizara mata. Inji Anty Safiyya sak! AMAREN BANA! Suna gamawa, suka ce sai Anty Hauwa ta tsaya ta ci abinci, tana ci, tana zuba masu hira. Ba laifi akwai ta da son mutane matar. Rumaysah ta yi saurin komawa gida ta yi wanka, sannan ta sa wata atamfa (Light Blue) mai ado da farin zane, ya yi mata kyau matuka. STORY CONTINUES BELOW Ta gama shirinta, ta daura lafiyayye abinci, sannan ta yi maghriba. Har ta kammala girkinta, bai shigo ba, don haka ta yi tunanin masallaci ya tsaya. Sai dai da ta idar da Issha’i, ta ji shirun ya yi yawa, don haka ta gwada wayarsa. Amma haka ta yi ta ringing bai dauka ba. Daga karshe dai ta gaji da jiransa ta wuce daki ta yi kwanciyarta, nan ta bar masa abincin da ta dafa. Shigowarsa ya ji gidan ya yi masa shiru da yawa, don haka ya san ta kwanta. Wanka ya yi sannan ya sauko. A hankali ya leka dakin nata, ya samu ta yi barci, shiga ya yi ya cire takalmansa ya kwanta a gefenta. Kallonta yake yi tana barci, hankalinta a kwance, sai wani sansanyar kamshi dake fita daga jikinta. Hatta gashinta kamshi yake yi. Yayin da shi kuma zuciyarsa take cike da rudani, a bangare guda ya furta mata sirrin zuciyarsa, a dayan bangaren kuma ya rasa abu mai muhimmanci a gare shi. Gyara mata rufuwarta ya yi, ya sumbaci saman kanta, sannan ya mike don barin dakin, daidai lokacin ta yi juyi kan hannunsa. A hankali ya zare hannunsa. Amma nan da nan ta bude idanu, ta gan shi a samanta. Da sauri ta zauna cikin yanayin barci, ta-ce. “Yaya Fawzaan yaushe ka shigo?” “Koma barcin ki, yanzu shigowata.” “Abincinka, yana falo.” “Ki bar shi kawai, ni ma na gaji, kyau ni ma na samu hutu”. Dubansa ta yi sannan ta-ce. “Ka san aikin da na ci wajen shirya maka abincin nan kuwa?” “Naci abinci yanzu na kai shi ina Rumaysah? Karfe sha daya fa.” “Kai dai kawai ka ce ka ci daga inda ka fito.” Ta mike ta nufi kofa, domin ta je ta adana abincin kar ya lalace. Daga yau za ta ma daina damuwa da al’amarinsa, saboda ta lura sai ta sake komai zai daidaita, sai ya tsiro da wani abin. Har ta gama tattarawa, ta sa a fridge. Sannan ta koma dakinta, ta samu yana zaune kansa cikin hannu, sai kuma ta yi tunanin koda i wani abin ya faru ne, ya hana shi shigowa gida? Ba ta tambaye shi ba, ta fassara shi. A gefensa kadan ta zauna ta-ce. “Yaya Fawzaan, kanka ne yake ciwo?” “A’a ba komai, kawai dai wani abu ne kuma ya riga ya wuce, koma ki kwanta sai da safe.” Zai mike ta riko hannunsa ta-ce. “Ko ni ba za ka fada min ba?” Wani irin abu ne ke yawo masa a cikin jikinsa, Yana matukar son ya kasance da ita amma, sam baya son hakan ya faru a cikin yanayin da yake ciki na bacin rai don haka, ya fita daga dakin hade da ja mata kofa. Zama ta yi tana tunanin ko me ke damun Yaya Fawzaan? Da ta ga ba ta da amsa, ya sa ta yi kwanciyarta. Fawzaan kuwa yana kwance, yana tuna maganarsu ta dazu da Meena. “Fawzaan ka yi hakuri. Amma Hajiya ta-ce kawai mu hakura, ka kula da lafiyar matarka idan har Allah ya sa muna da rabo da juna, sai Allah ya daidaita tsakanin mu a gaba.”4 Mamakin kalamanta ya ji, ga shi tana gama fada masa ta fashe da kuka. Ya rasa yadda zai yi, ji ya yi kamar ta zare masa wani bangare na jikinsa, ga sabo da sonta da ya yi na tsawon shekaru, bai taba kallon kowa ba a matsayin matarsa, kamar yadda yake kwatantota. Duk da ya amince yana son Rumaysah, amma ya riga ya san Meena ya ajiye a matsayin wacce ko ba jima, ko ba dade zai aura. Sai ga shi an datse masu tsakani. Koda ya nuna mata shi da kansa zai yi wa Hajiyar magana ta-ce. “A’a ka bari kawai ta riga ta gama magana, ko ka ce wani abu, ba za ta saurareka ba, don na samu Baba da maganar. Shi ma din abin da ya-ce kenan.” “Yanzu Meena ki na nufin shi kenan dangantaka tsakanin mu ta kare?” Cikin kuka ta tashi ta koma cikin gida, wannan ya ba shi amsar tambayarsa, ya dade a zaune a wurin kafin, ya mike ya koma gidan Baffa. Sai dai har suka gama hira, bai fada masa akan cewa an warware maganarsa da Ameena ba.2 STORY CONTINUES BELOW Tun Issha yana son ya dawo gida, amma sam baya son ya komawa Rumaysah da bacin rai. Da ikon Allah nafila ya yi raka’a biyu, ya godewa Allah bisa zabin da yayi masa, hakan ya ba shi sukuni ya samu ya dawo gida. Da safe sai ga wayar Rayyan, yana tambayarsa. “Me ke faruwa ne? Meena yanzu ta kirani tana kuka.” “Ba ta fada maka abin da ya faru bane?” “Ina, kawai dai kuka ta tsaya yi min, na fahimci dai dalilinka ne.” “Ba komai kawai ba wani abu bane, yadda Allah ya hada mu, haka nan shi ya yi ikonsa ya yi sanadin rabuwarmu. Allah bai sa za ta zama matata bane, domin kuwa iyayenta sun ba ta umarnin rabuwa da ni.” “Har da Kawun? Amma bisa wane dalili, zan je …” “Ka bari Rayyan, duk iya karamci ka yi min shi, tun da ka shige min gaba a wannan al’amarin, tunda kuwa haka ta kasance, ba na so ka bata tsakaninka da Kawunka. Allah ya ba ta miji na-gari wanda zai so ta fiye da yadda na so ta.” “Gaskiya ban ji dadin wannan abin ba, na san kawai an samu Misunderstanding ne.” Fawzaan ya yi shiru. Misunderstanding? Uzuri ya ba su na su bari matar sa ta warware, sannan ayi biki, shi ne zai zamo silar da zai sa su janye magana da manya sun riga sun shiga ciki? Ko baya son matarsa, ai ita mutum ce kuma ta cancanci adalci da sassauci. Bare kuma yana son matarsa matukar so. Idan ba tsoron karya ba ma, yadda yake ji game da Rumaysa a ‘yan watannin nan, bai tsammanin ya taba jin makamancin hakan game da Meena, sai dai kawai sha’anin sabo da ita da ya yi. Ya samu tana shan Tea gaishe shi ta yi kawai ta ja baki ta yi shiru, saboda gani take yi kamar daga shekaranjiya zuwa jiya. Mafarki ta yi kuma ta tashi a barcin. Kamar yadda a cewarsa ya-ce. “Dream is over.” Shi ma Tea din kawai ya hada, sannan ya-ce. “Yau ba abinci ne?” “Babu”. Ta fada a takaice. Haka ya shanye shayinsa a tsanake, daga bisani ya-ce. “Zan fita zan leka ofis, ina da sauran ayyuka, kin ga ran Juma’a ban samu zuwa ba, ga shi gobe litinin.” “Sai ka dawo”. Kawai ta furta, domin ba ta da abin cewa. Yana fita, ta duba lallen hannunta da ya yi jazur! Da shi a kan fatarta, kawai sai ta fashe da kuka. Haka ta wuni sur!4 Bayan Maghriba ta yi wankanta, ta zauna a daki kan sallaya, har aka yi Issha, domin ta hakura da kukan, zama ta yi tana karatun Alqur’ani, sai dai duk Ayar da ta karanta, sai ta tuna Yaya Fawzaan ne ya koya mata. Daga karshe kawai fashewa ta yi da kuka, tana cikin hakan ne, ba ta ji motsi ba, kawai sai jin hannu ta yi a saman bayanta, a hankali ta dago suka yi ido hudu. “Ya-Salam! Rumaysah me yake damunki?” Ai sai ta rushe gaba daya, nan da nan Fawzaan ya tallafota jikinsa. “Wani abu ne ya faru?Please fada min, me ya saki irin wannan kuka haka?” “Ka daina tambayata abinda ya faru, bayan kai ka fi kowa sani, ka daina wahalar da ni ka na sa min zuciya a rudani, ba zan iya dauka ba. Akan me ya sa za ka ce ka na so-na bayan na san ba haka bane. Na dade ina bawa zuciyata hakuri a kanka, har ta soma samun salama, kwatsam! Ka furta min kalmar da ta fi komai dadi da muhimmanci a rayuwata, sannan kuma za ka cutar da ita, ka zagaya wurin abin da ka fi so, ka mance da ni. Me ya sa Yaya Fawzaan. Nace Why?” Hawayenta ta share ta tsayar da kukan ta-ce. “Yau ina son na san matsayina a gidan nan, ina son na san matsayina a rayuwarka, ina kuma son na san matsayina a zuciyarka? Don na gaji ba zan iya fafutuka ba kuma.” STORY CONTINUES BELOW “Rumaysah!” Ya fada cikin wata irin murya mai rikitarwa, wani irin sanyata ya yi a jikinsa tamkar zai tsaga kashinsa ya cusata a ciki. Sannan ya saketa ya-ce. “Ke ki ke da kowace dama da ki yi ikoda zuciyata, ke ce kuma rayuwata kuma KE NA KE SO. Abin da ke tsakanin mu, kuma wani AL’AMARIN ZUCCI ne da yake boyayye, sai mu, muka san sirrin sa. Ki kwantar da hankalinki, domin da ni da zuciyata da dukiyata da duk wani abin da na mallaka, a karkashin ikon ki suke, sai yadda ki ka yi da ni.”8 Wani dadi ne ya kara cika mata zuciya, nan take ya riko fuskarta, ya aika mata sakon da yake nufi. Bada bata lokaci ba, kuma suka bar magana da baki, suka shiga fayyacewa juna kauna zalla, wacce ba algus cikinta, a zahirance. Sun dau tsawon lokaci a cikin wani yanayi da sai su kadai suka san abin su.5 Na barwa mai karatu ya kwatanto farin-cikin masoya biyun a wannan lokaci. Na hango matan fada, sai kokarin leken zukatan Rumaysa da Fawzaan suke yi, amma ina, sun kasa. Saboda Masoya biyun sun yi katanga da duniyar waje, bare su bar jama’ar Fadar mata zalla su leka. Fawzaan dai dadi da mamaki ne suka kama shi, saboda irin yanayin da ya samu matarsa abin sonsa, wato dai tuntuni mummunar zato yake ta mata, na batun cewa ta bar kanta wa samari,4 Ko kuwa cewa da ya yi maza sun gama jagwalgwalata, domin kuwa Intact ya samu amaryarsa. Ai sai ya dada dimaucewa, cikin kaunarta da shaukin sonta.5 Rumaysah dai ba ta san yaushe ta koma kan gado ba, farkawa ta yi a hankali ta ganta a jikin mijinta, ta yi saurin motsawa, don ta tashi, sai ta ji ya kara kwantar da ita. Duk da cikin barci ya rikota, don haka ta koma ta kwanta ta daga idanu tana kallonsa, yana barci cikin natsuwa. Wani irin dadi ne ya ci-gaba da ratsa mata zuciya. Tabbas ta san Yaya Fawzaan asalin kaunarta yake yi. Saboda zahiri ta ga hakan. A hankali ya bude idanu, ya ganta “Liar, idan anyi magana, sai ki ce ba kya satar kallo na.” Murmushi ta yi, ta kau da fuskarta. “Na kashe maka sauro ne fa”. “Uhm! To ga wani a nan kara kashewa”. Ya mika mata kuncin sa. Dariya ta yi ta rufe fuskarta, sannan ta-ce. “Gwamma kai, ni kam zan shirya na tafi makaranta.” Janyo hannunta ya yi ya-ce. “Za ki je ina?” “Makaranta”. “Na ji ki sarai. Ba inda za ki je, saboda ni ma yau ba ni da lafiya, yanzu ma waya zan yi na fada a ofis.” “Ka san Oga Mike sarai, sai ya kamo hanya ya zo dubiya.” “To ba shi kenan ba, karya na masa ne? Ciwon so ya kamani farad daya, irin mummunar kamun nan na bazata. Saurara fa ki ji, har bugun zuciyata ta canza. (Very lethal) ina fada miki”.2 Ya fada hade da nuna mata gurbin zuciyarsa, yana shafawa a hankali da hannunta dake cikin tafin hannunsa, fuskarsa kuma ya nuna alamun yana cikin jin radadi. “Uhm! Ni na san maganin wannan.” Ture hannunsa ta yi, ta mike da sauri, tana tashi ta shige wanka, don ta shirya, ya bi-ta da dariya. Tun da suka yi sallah da suka maida barci, sai yanzu kawai ta ankara har bakwai da rabi, kuma tana da aji karfe goma.5 Ta gama abin karyawa, ta ajiye a Table ne, sai ga shi ya fito sanye da Suit dinsa kalar shudi mai duhu (Midnight Blue). Ya sha Tie din sa mai layin ja da Blue, a saman farar rigar da take kasan Suit din nasa. Ga shi ya amshe shi, tamkar an gwada shi tsab! Aka dinka kayan. Ya yi matukar kyau. Murmushi ta yi masa sannan ta-ce. “Na dauka ka kira Oga Mike din ai.” “Hmm! Na kira shi, ki min wayo ki tafi ki bar ni a gida?” Lakace hancinta ya yi, sannan ya zauna kan kujerar. A tsanake ta zuba masa abin karyawa, tana shirin zuba nata ne ya tsaya kallonta. “Me ki ke nufi? Come on, zauna mu ci wannan”. STORY CONTINUES BELOW Murmushi ta yi. Fawzaan ko ya jawo ta kan ciyarsa ya shiga ba ta a baki. Shi ma yana ci, lomarsa daya ya-ce. “To, babbar magana. Shi kuma wannan meye sunan girkin nan?”2 “Sweet Potatoes Made-Over.”4 “Wannan din dankalin hausawa ne?” “Ehem”. “To yaya aka yi na ji baya shake mutum?” “Ka na so ka koyi yadda ake yi? Sai na dauko maka littafin (My Kitchen Essentials), na Sister Azizah Idris (UmmYasmeen). A saukake ta yi bayanin komai, ko kai da ba ka taba shiga kicin ba, za ka iya yi da kanka.”16 “Hmmm! Lallai wa ya ce miki ban taba shiga kicin ba?” “Fada min, me ka taba dafawa?” “Ina girka ruwan zafin Tea, ko shi ba a kicin a ke yi ba?” Dariya ta yi cikin wani irin salo, sannan ta dubi agogon bango ta-ce. “To ranka ya dade, sai a tashi a tafi, kar a makara, an tsaya buga santi.” “Whatever, ni dai sweet Rumaysah na damu da na sani na bar miki Potatoes din da Made-Over din duka”.4 Murmushi ta yi, idanunta suna kasa cikin jin kunya. Wani kallo yai mata da (Dreamy Eyes) dinsa ya-ce. “Dole na ne kawai idan banda haka, yau sai kin raina kanki. Don haka Malama kar a dade a makaranta.” “Na ji”. Ta fada hade da mikewa daga jikinsa, matsar da Plate din ta yi gefe, sannan ta riko hannunsa har sai da suka isa bakin kofa ta-ce. “Kamar dai ka yi mantuwa.” “Ni kuwa? Ina da ke a gefena me zan manta? Ai na gama samun komai.” Ya fada yana kallon fuskarta da sai kyalli take yi. Rumaysah ta bude hannayensa ta sa masa jakarsa ta Computer. “Jakar ofis dinka na ke nufi.” Ajiyar zuciya ya yi ya-ce. “To sai anjima, don Allah ki kula da kanki, kar ki sa ayyuka da yawa a gabanki, makarantar ma idan babu wani abu mai muhimmanci da kin hakura, kin yi zamanki kin huta.” “Kar ka damu. Allah ya bada sa’a, ya kuma kare min kai.” Shafa fuskarta ya yi, sai da ta hankada shi waje, cikin wani salo tukun, sannan ya tafi. Nan jikin kofar ta jinginu bayan ta rufe shi. Ta lumshe idanunta tana fara’a. Can dai ta dawo duniyar gaske, ta shiga tattara shirgi ta kimtsa ko ina, wajen karfe tara da rabi ta tafi makarantar. Fawzaan ko zuciyarsa fes! Ba ya tattare da wani bacin rai, domin kuwa Rumaysah ta kawar masa da wannan, sai yanzu yake jin haushin bata lokacinsu da ya tsaya yi, yana zaune da mace har mace. Amma ya kasa fayyace mata sonta. Duk da kuwa ya dai dau lokaci kan ya isa wannan matakin, tabbas Baffa ya taimake shi da ya nuna masa wannan hanyar. Ba abinda zai cewa iyayensa, sai addu’ar alkhairi. Ko a ofis, an ga canji daga Barr. Fawzaan saboda haka nan, yau fara’a yake yi wa kowa.2 To Rumaysan ma dai ba daga nan ba, tana zuwa ta ishe su Firdausi da surutu, sai fara’a take ta yi. Naja’ah dai sai kallon Firdausi take yi, can ta gaji da kallon da suke mata ta-ce. “Yaya dai, me yake damunku ne yau, na ga kun yi wani sum-sum da ku? Firdausi kar dai (Labour) ne ya tashi miki?”1 “A’a yadda ki ke cikin annashuwan nan, ai dole ki ga kowa ma a tsume yake, me ya same ki ne?” Murmushi kawai ta yi ta-ce. “Ku bar wannan kawai, ku dauka wata addu’ata ce ta karbu, shi ya sa saboda haka ku taya ni godewa Allah.” Firdausi da Naja’ah suka tafa suna dariya. Ai kuwa sai Firdausi ta damke baya tana wash! Da sauri Rumaysah ta nemi lambar Umar. Sai tambayarta suke ta yi me take ji? Ko su ce sannu ko kuma har yanzu yaya? Duk sun bi sun kidime. Can sai ga Umar. Ai Lectures daya suka samu daman yi. Rumaysah ce ke da shi karfe uku. Amma haka ta yafe suka bi kawa asibiti. Suna zuwa kuwa Likita ya-ce masu haihuwa ce. STORY CONTINUES BELOW Rumaysah ba ta san abin azimun bane, sai da ta ga Firdausi ta fita hayyacinta, kuka kaca-kaca! Kafin a shiga da ita dakin haihuwa, tausayin kawarta ya kama ta. Wayar Fawzaan ce ta shigo, sai a lokacin ta tuna ba ta ma fada masa sun taho asibiti ba. “To, a wane asibiti ku ke?” “Babban asibiti na cikin Gwagwalada. Dama a nan take awo.” “Ba damuwa. Allah ya raba lafiya.” Ayyuka ne su kai masa yawa, ya so ya taho Gwagwaladan da wuri, amma sai shida ya bar ofis, daga can ya wuce kai tsaye. Ya samu su Rumaysah sun kewaye Mai-jego. Ga Maman Firdausin ma a zaune. Ya gaida su, ya dubi Firdausi ma yai mata murna. Rumaysah ta karbi jinjira ta mika masa. Ya karbi bebin wani iri. “Kai, hankali kar ka balla masu yarinya.” Dariya suka yi gaba daya Umar ya-ce. “Kar ki damu da zarar kin haihu, zai koyi rike babies, ni ma ba ga shi ba.” Dariya suka sake masa. “Daga zama Baba na awa biyu, shi ne har ka iya rike babies?” Wata yar Umar din ta fada. Nan dai suka yi masu sai da safe. Sannan suka fito. Umar ya rako su zuwa kofa, sannan ya koma. A hanyar zuwa wurin mota ne Fawzaan ya-ce. “Ke ma nan da wata tara Insha-Allahu kin haifo min kyakkyawar Baby na.”6 Rufe fuska ta yi, sai tai maza kuma ta sauke ta dube shi ta-ce. “Ina, ai ba da ni ba, ka ga dan karen wuyar da Firdausi ta sha kuwa? Gwamma ma ka hakura, na fada maka, don ni kam ba zan haihu ba, ba na son wuya.” Kumatun ta ya ja ya-ce. “Ba a haihuwar, ke aka haife ki? Gwamma kin cire tsoro, don Baby kam ya zama miki dole yarinya”. Murmushi ta yi ta bude kofar motarta ta-ce. “Don Allah kar ka je ka fara buga waya ka na fadawa mutane ina (Labour Room). Firdausi ce ta haihu ba Rumaysah ba.” Kada harshe ya yi, ya-ce. “Lokacin ki na zuwa ai ke ma.” Dariya ta yi ta tada mota, shi ma ya shiga ta sa, sannan suka dauki hanyar gida. ****** Washegari da dare suna zaune a falo, ta yanko masu kankana suna sha. Fawzaan yana aikin nasa na buga santi, sai ta ji ya-ce. “Yawwa, na ga alama kin fara zama Unserious rabon da ki bada karatunki, tun yaushe?” Rumaysah ta taso daga kishingiden da ta yi akan kirjinsa ta-ce. “Haba Yaya Fawzaan, ni na ajiye karatu ko Malamin nawa? Ka manta rabon da ka kara min tun yaushe? Ina ce ka na can ka na fama da Meenar ka, ka bar Rumaysah ko oho.” Ta fada hade da bata fuska, cikin shagwaba. Tana kiran sunan Meena, ta ga alama fuskarsa kamar ta canza. “Ke dai ki fadi gaskiya, wani abu daban ya hana ki yin karatu, kin soma wasa, sai kin dage fa.” “To na ji zan dage Insha-Allahu, idan Malamin ya bar kallon fuskata, yayin da na ke karatun, domin kuwa yana sa ni tsarguwa.” “Anya wannan Malamin zai bar kallon kyakkyawar fuskar dalibarsa? Ai za a samu matsala, ke dai na ga alama sai kin hada da Islamiyya kawai. Don na ga mun fara samun karancin lokaci, idan ya so da asuba, sai mu rinka karatun Al qur’anin tare. Idan kuma da wani abin da ya shige mana duhu duka, sai mu yi bincike, ko me ki ka gani?” “To shi kenan hakan ya yi. Sai dai wace Islamiyya ka ga ya dace na shiga?” “Na ga Maman Fadila tana zuwa wani, ba sai ki bincika ki ji ba, idan mun ga ana karatu sosai, sai ki yi Register kawai da su.” “Wai ni Yaya Fawzaan na tambayeka, yaya aka yi ka yi karatu ne, tunda na ga dai a turai ka ci-gaba da karatunka, tun daga gama sakandire.” “Ai karatu sa kai ne, ko a ina ka ga daman yinsa za ka yi. Don haka koda na tafi ba zama na yi ba, akwai makarantu da ake gudanarwa a cikin masallatai. Bayan wasu lokutan sallah, don haka kawai sai na yi amfani da damata na shiga. Kin ga na tashi da riba biyu. Bare cikin birnin London, akwai masallatai birjik!” “Wai, ka taimake mu da yanzu ina cikin garari da na hadu da miji bi ta can. Shi ya sa na ke kara godewa Allah, da ya saka wa su Baffa da Abba, tunanin cewa ko mu na kaunar juna, har suka shirya su hada mu aure.”3 “Kin ga kuwa na ga amfanin aure Fisabilillahi! Don Allah ya hada ni da mata ta gari. Duk da dai ance ba auren sadaqa aka yi mata ba.” Rumaysah ta harare shi, cikin sigar so, ta dauko filon kan kujerar gefenta ta maka masa. Yana dariya ya-ce. “Na ga alama na kusa na kwashe filullukan gidan nan, idan ba ana so a hallakani da su ba ne.” Sauri ta yi ta shige jikinsa ta-ce. “Rufa min asiri, ina ni ina hallaka bugun zuciyata?” Tana fadin hakan. Fawzaan ya mayar mata da martani, suka koma duniyarsu. *************** Radiyya, don Allah ki zo yau kam ki wanke (Toilet) din nan, ni na gaji da ganin ko ina jirwayin kumfa a bandaki. Haba mutum, sai shegen son jiki, kamar kyanwa?” Radiyya ta taso da cikinta tsut! A gaba. “Deeni Last-weekend fa na wanke, gaskiya ni bayana yana min ciwo yanzu.”7 “Wanke miki ki ke so na yi? Ki duba fa inner wears dinki kin jibga kan washing machine maimakon ma ki zuba su a wurin tara kayan wanki, a’a, hankalinki ya fi kwanciya idan kin ga komai biji-biji. Ji cikin Sink din ki, duk abin makilin ya yi fari-fari, amma ko a jikin ki, haka za ki shiga ki yi amfani da shi, sai dai ni idan na gaji?” Har yanzu kunkuni take yi. “To gaskiya, ni ba zan iya ba, idan har ni zan kula dake, maimakon ke ki kula da al’amarin gidan ki. To Allah za ki sha mamaki, don kuwa zan je na nemo wacce za ta tsaftace min muhallina.”2 Da sauri ta saki fuska. “Allah Deeni? Kai na gode sosai.” Super ta yi za ta makale shi, ya yi saurin tsaida ita. “Ki na hauka ne? Idan ki ka buge cikin ki fa, za ki kama ki yi wannan tsallen?” Nan ya fahimci ba ta gane batunsa ba, don a wautarta ta mayar ‘yar aiki zai dauko mata. “Idan an tashi nema, zan yi wa Neighbor magana a samo min daga garin yarinyar da take mata, ka ga aikin su kuwa, kamar injina.” Hararar ta ya yi ya-ce. “‘Yar aiki a ina? Ai ni da na samo miki ‘yar aiki, sai randa ki ka iya na gidan nan da kanki, sai a samo, amma yanzu nufina aure zan je na soma nema, tunda ke ba za ki iya kula min da gidana ba.” Nan da nan ta rike baki, idanunta suka firfito, ta soma hawaye, ta yi taga-taga za ta fadi. “Yau na shiga uku! Deeni aure fa ka ce za ka nema? Watan mu biyar da aure, za kai min kishiya? Deeni daman ba so-na ka ke yi ba? Yaya za kai min haka.”8 “Ba dole nayi miki haka ba? Ki duba fa gidan nan, rabon da ki share shi tun yaushe? ga turaren wuta shirgi guda, an hado ki da shi, amma ba ki san ki kunna ba, wanke-wanke kuwa sai dai ni na zakuli kwanon da na ke so, na wanke na yi amfani da shi. Tsabar rashin goge-goge, ko ina ka taba a gidan nan kura ne.7 Ga shi ana hunturu, ba ki san ki goge komai ba. Ni kenan ban isa na kawo abokai ko ‘Yan-uwa ba gidan nan, saboda ko abinci ba ki iya dafawa ba. Yaya ki ke son na zauna dake a haka? Sannan ko a shimfida, tunda ki ka samu cikin nan, shi kenan ki ka kaurace min. So ki ke yi na fara yawo, ko me? Gaskiya ki na takurani, aure kam ya zama min dole, saboda na samu sassauci.”4 Ai Radiyya kam! Sai ta rushe da kuka. Yau nata ya sameta, dama kullum Rumaysah na mata fada, amma ba ta ji, ita dai tun da ta yi laulayin ciki, shi kenan sai ta sake da haka, tunda ta ga Deeni na mata komai, to amma da ya ga ta warke, ya kula abin nata iya shege ne. Ya daina, don haka gidan su kam kamar tsohon gida. Yayin da kanta kam, kamar tarukucen mahaukaciya, domin tunda ta zo, sau biyu ta je (Saloon) aka gyara mata. Saboda yaran gidansu dama kitso bai damesu ba, saboda yawan gashinsu, gwamma Yaya Khadija ma, kullum ita tana hanyar gidan kitso. STORY CONTINUES BELOW “Don Allah, Deeni ka yi hakuri, kar kai min kishiya. Allah zan koyi gyara. Kawai ka gwada min yadda zan yi, kar na gaji da yawa.” Fuskarsa a tsume tamau! Ya fice daga dakin nata, ya nufi nasa ya tura kofa. Haba da Radiyya ta ga da gaske yake yi fa, kawai sai ta sunduma ihu, ta rinka kuka. Tana gamawa ta nemi lambar Rumaysah, don ita-ce kawai maganin matsalarta, domin ita kam. Allah ya gani ta ki jinin kishiya, bare da wuri haka? Dole ta gyara, ta nemo tsabta ta rinka kwatanta shi. “Sis, yaya dai na ji kamar ki na kuka?” “Rumaysah na shiga uku, na lalace”. Jikin Rumaysah ya fara bari. “Me ya faru Sis? Wa ya mutu?” “Ke kin faye shirme, ba mutuwa aka yi ba, ki na ji wai yanzu Deeni kishiya zai min? Rumaysah yaushe akai mana auren? Da zai ce zai min kishiya, tun yanzu ba sai ai mana dariya ba.” “To don zai miki kishiya, shi ne ki ka shiga uku ki ka lalace?” “Tab! To me zan yi, idan ba hakan ba?” “Kin ga Yaya Radiyya, mutum fa ba kyau, ya rinka kirawo wa kansa bala’i, duk lokacin da ki ka ga kamar kin shiga rudani, to sai ki maida komai ga Allah, ba ki labto masifa ki aza a kanki ba. Yanzu meye ne damuwarki? Ki natsu ki fada min ya aka yi ta faru?” Nan dai Radiyya ta kwashe yadda suka yi da Deeni ta fada mata. Rumaysah ta nisa ta-ce. “Daman da nace ki shiga makarantar koyon girkin, ba ki masa magana bane?” “A’a ni ban fada masa ba, saboda ina jin haushin kin zubar min da abinci. Sannan kuma da na huce bayan sati biyu, na tambaye shi ina son zuwa unguwa ya-ce, wai ba inda zan je, sai na yi shara”. Rumaysah ta sauke ajiyar zuciya. “Yaya za ki bari datti yai miki yawa da har mijinki zai ce ba za ki fita ba, sai kin masa shara? Huh! Yanzu dai gaba daya (Emergency 101) ki ke da bukata, don haka zan kira Momi, gobe kar ki je ko ina, zan tambayi Yaya Fawzaan, ina zuwa gidan naki, wannan ba maganar waya bace.” Tana ajiye waya, ta kira Momi ta shaida mata, tana bukatar su Laminde washegari za su je gidan Radiyya, tayata aiki. “Ba dai jikin nata bane kuma ya tashi ba ko?” “A’a dai kawai wani aikin ne ya taso.” Rumaysah ta ki fadawa Momi, domin kuwa idan ta san Radiyya irin kazantar da take bugawa, to sai an debi ‘yan kallo. Wai ai na baya wasa ne, saboda wannan karon kam har cikin (Toilet) din ya dawo Brown, don masifar datti. Ga kayan wanke komai, a dauka, ayi ne ba zai yiwu ba. Haka su Laminde suka rinka fidda datti bola-bola. Ana gamawa, har su windo aka goge mata, yayin da Rumaysa ta sa ta a gaba ta-ce. Su wuce wurin gyaran gashi.2 Daga gashi har tafin kafa, sai da aka gyarata tas! Sannan suka koma gida. Daman ta taho mata da jan lalle, don haka yalwa ta jika shi. Yalwan ce ta zauna ta kunsa mata lalle a kafa da hannu, sai da ya yi awa guda. A gefe kuwa Rumaysah ta debi Yogurt ta kwaba da kurkum. Ta mulke mata fuska da shi, da saman jikinta. Ta kara minti talatin a haka, sannan ta-ce. “To oya shiga ki yi wanka. ” Koda take wanka tukun, wani sulbi ta ji jikinta yana yi, sai dadi take ji ita kanta. Tana fitowa, suka banke ta da turaren wuta. Kamar dai wata amarya suke shiryawa. kayan wankinta ko sun sa mata a cikin (Washing Machine) din aka wanke. Aka shanya su a rana. Saboda ya kashe wasu kwayoyin cutar, har cikin Wardrobe dinta, sai da suka gyara mata kayanta da duk sun yi ruku’u, suna shirin kai sujjada.14 Dakin mijin ma Rumaysah da Radiyya ne suka shiga suka gyaro shi tsab! Sai da gida ya dawo fes! Sannan Rumaysah ta dube ta ta-ce. “To Yaya Radiyya, ni ma ina da gidana, kuma ina da abin yi, don haka ba zai yiwu kullum in ta daukar hanya ina zuwa miki gyara ba, don haka (Time Table), zan miki. STORY CONTINUES BELOW Idan kin ga dama, ki bi ki rinka barin wurinki da tsabta, idan kuma ki ka ki, to Deeni mata uku zai auro rana guda, ku zama ku hudu, kin san yana da kudin karo mata biyu, bare kuma idan an hada da kudin Babansa zai iya masa aure.” Haba Radiyya ta tsure. “Don Allah fada min yadda zan yi, ba na son kishiya.” “Kishiya kam ya zama dole ki cire rashin son ta, don kuwa ba haram bane, sunna ce. kuma an fada a Al qur’ani, don haka ba za ki ce ba ki son sunna ba, sai dai ki roki Allah ya hada ki da ta-gari, idan ya yi niyyar karin.5 Don ba kyau ma mace ta rinka rokon Allah ya sa mijinta kar yai mata kishiya ko kuwa ta roki Allah ya sa mijinta ya saki kishiyarta, domin Allah baya karbar addu’ar mugunta, idan ba ki yi sa’a ba, sai ya koma kanki. Kaikayi ya koma kan mashekiya kenan!”3 Nan tai mata tsarin yadda za ta a yi a saukake, tunda tana fita aiki. “Kin ga da farko duk kwanon da ki ka yi amfani da shi, kar ki bari ya kai lokacin cin wani abincin, ki wanke shi a take, sannan kullum ki share inda ku ka fi amfani da shi. Dakin da ba ku amfani da shi kuma, sai ki bari, sai bayan kwana biyu. Bandaki ma bayan kwana bibbiyu ki tabbata kin wanke shi tas! Wanki kar ki rinka bari yana kai sati a tare, musamman (Inner Wears). Ko wane Weekend kuma ki shiga Kitchen ki goge duka kayan wutanki (Electronics), ki ciro komai a Fridge ki goge tas! Ki rinka duba kuma (Expiry Dates) na kayan fridge din, abinda ba kya amfani da shi, ki rabu da shi, don kar ya zama tarkace a ciki. ki cire cobwebs bayan ko wani sati biyu. Haka zanin gado kar ki yarda yayi datti har ma ya nuna. Ranar lahadi kuwa ko asabar. Ya zama da safe ne za ki yi aiki, sai ki ci kwaras abinki, ki zauna ku sha hutu cikin nishadi da Mai-gidanki. shi kenan fa.” Radiyya ta karba tana jinjina abin. Dole ai ma tayi himma. Tana komawa gida, ita ma wankan ta yi ta kaleleye jikinta da kayan kamshi, nan ta zube kan kujera ta hau barci. Haka Fawzaan ya zo ya sameta, shafa fuskarta ya yi hakan ne, ya sa ta motsa. Tana ganin sa, ta shiga yamutsa fuska cikin shagwaba. “Sannu da dawowa”. “Sannu Madam, lafiya dai na ganki a zube a nan?” “Hmmm! Bari kawai, ba a cewa komai. Yaya ka ke da wurin aiki? Da fatan ka dawo kalau?” “Alhamdulillah! Amma dai ina fushi dake.” Da sauri ta bude idanu ta-ce. “Fushi kuma, na shige su?” “Yaya za ki je ki wahalar min da jikin ki, bayan kin san kuma ba na son a yi min hakan?” “Don Allah ka yi hakuri, ya kare daga yau Bi’iznillah”. Mikewa ta yi ta rike masa (Laptop) dinsa zuwa sama, inda ya ci-gaba da mata tsiya. “Na ga alama dai wata, sai an mata tausa.” Murmushi ta yi masa kawai. Ana gobe sunan Firdausi ne. Fawzaan ya kai Rumaysah saboda za ta kai mata dinkin kayan sunanta da ta bayar ta wurinta. Umar yana ganin sa, ya dage sai ya shigo ciki, don haka ya shiga, suka gaisa. Ai kuwa yana zaune a wurin, sai ga Saleem ya shigo, sai dai kasancewar bai san waye bane, sun gaisa lafiya lafiya. Sai dai Saleem, sai yana masa kallon sani, amma ya rasa a ina? Shi ko Umar ya-ce. “Barrister, wannan aboki na ne Saleem. Saleem, Barrister Fawzan kenan.” Ai Saleem baya bukatar karin bayani, ya gano wannan shi ne mijin Rumynsa, shi ya yi masa kwace, nan take ya ji wani zafi yana taso masa a zuciya. Haka dai ya daure, suka zauna. Rumaysah kuwa tana ciki ba ta san me yake faruwa ba, ta mika jinjirar wa Firdausi da niyyar tafiya kenan. Sai wayarta ta yi kara. Ganin mai kiran, ya sa ta daga cikin doki, ai kuwa dif! Ta yi da ta ji muryarsa. “Yaya Ra’id, lafiya, me yake faruwa?” “Rumaysah ki na ina ne?” “Ina gidan Firdausi, lafiya?” “Ke da Yaya Fawzaan ne?” STORY CONTINUES BELOW “Eh, tare muke, wani abu ne? Don Allah fada min.” “Daman na kira ne, na ji ko ku na lafiya.” Rumaysah dai ba ta amince ba, don haka suna gamawa, ta kira Yaya Khadija, ai nan take shaida mata Allah ya yi wa Baban Gusau rasuwa dazu. Ba ta san garin yaya ba, kawai sai ta ji ta rushe da kuka. Firdausi ma ta kidime ta shiga tambayarta lafiya?2 “Firdausi Baban Gusau. Allah yai masa rasuwa. Alhajin Momin mu”. “Inna-Iillahi’wa-Inna-Ilaihir-Raji’un! Allah yayi masa rahama, ya sa ya huta.” “Ameen.” A lokacin ta ji kuka ya ci karfinta, da sauri ta mike ta fita falo, kai tsaye ta samu Fawzaan, hankalinsa ne ya tashi ganinta a wannan yanayin. Riko kafadarta ya yi ya-ce. “Rumaysah lafiya?” “Yaya Fawzaan Baban Gusau. Allah yayi masa rasuwa.” “Subhanallah! Allah yai masa rahama.” Rushewa ta yi da kuka, ta sa kanta a jikin kafadarsa, shi kuwa ya ma manta da mutane a falon, ya riketa a jikinsa yana rarashinta. Su Firdausi sai hakuri suke ba ta. Saleem kuwa ya rasa yadda zai yi, ga tausayin Rumaysah ga kuma kishinta ba zai iya jure ganinta a jikin Fawzaan ba, hakan ya sa ya fice daga falon, tun kafin ta ankara da shi. Ba bata lokaci suka wuce gidan Abba. Can suka tarar da ana tsakiyar juyayin jin wannan labari. A daki ta samu Momi tana hada kayan tafiya. Kai tsaye ta shige jikinta tana matsar kwalla. “Ya isa Rumaysah addu’a za mu masa. Allah ya fi mu son shi lokacin sa ne ya yi. Allah muma ya kawo mana kyakkyawar karshe.” “Ameen Momi.” Nan ta shiga tayata suna yi suna matsar kwalla, sai da ta gama Abba ya dawo dakin inda ya bar ta dazu.Rumaysah ta gaida shi, tana masa ta’aziyya. Su Momi a ranar suka wuce Gusau har da su Mama. Rumaysah ma gida ta koma domin ta kimtsa. Fawzaan ne ya tayata, domin tana cikin yi, ta zauna ta-ce. “Ayya Baban Gusau ashe zuwansa yi mana sulhu, shi ne karshen ganinmu da shi. Allah ya jikansa da rahama, albarkacin alkhairin da ya kulla tsakanin ‘Yan-uwan juna.”3 Fawzaan dake rike da hannayenta ya-ce. “Ameen.” Sai da ta gama kimtsawa, ta kira Hajiya Atine ta gaisheta. Fawzaan ma ya karba yana gaisuwa. Sai dare suka yi waya da su Momi cewa sun isa, su kam za su bari sai da safe su hada hanya da Khadija da Labeeb. Jiki duk a mace suka wuce, abin gwanin ban tausayi. Kowa yana al’ajabin yanayin rasuwar Baban Gusau, domin kuwa, ya kwana da ciwon kai, alamun dai ciwon sa na hawan jini, lokacin sallar azahar ya-cewa Hajiya Atine zai yi sallah, yadda ta ga yanayin jikin nasa ta-ce. “Alhaji da ka dan huta tukun, akwai sauran lokaci, idan kan ya sake ka, sai ka yi. Tunda lokacin azahar akwai saura.” Kai ya girgiza mata alamun dai kawai ta sako ruwa. Don haka ta taimaka masa ya yi alwalar. Ya tada sallar, ta san dai cikin dauriya kawai yake, amma ganin ya fara sallar, ya sa ta mike, don ita ma ta bada nata faralin. Haka ta tafi ta bar shi, sai dai har dawowarta Alhaji bai idar ba. Ta zauna zaman jiran ba shi abinci. Amma shiru. Alhaji yana sujada, taba shi ke da wuya, sai ta ga ashe ya amsa kiran mahallici. Baban Gusau dai ya rasu a cikin yanayi na sujjada ga Madaukakin Sarki. Jalla Jalalu. Allahu-Akbar-Kabiran! Sai da safe wajen karfe goma, aka kai shi, kafin nan duk wani na kusa, ya samu hallara. Allah ya jikan Musulmi.3 Bayan sun koma Abuja ne. Sati daya da yin rashin, sai lokacin Momi ta kara tabbatar da cewa da gaske fa shi kenan ita da Alhajinta, nan ta shiga tunanin irin maganaganunsa na hikima da ya kan fada mata a koda yaushe suke tare, lokacin ne ta sa kuka. Abba kuwa yana ganinta a wannan halin, ya ci-gaba da yi mata nasihar ta hakura ta kasance mai masa addu’o’i. STORY CONTINUES BELOW Har zuwa lokacin jama’arta na ta zuwa mata ta’aziyya. Rumaysah ma kusan kullum sai sun zo, don debe mata kewa. Har dai ta ware ta koma bakin aikinta, ita ma. *************** A kwance ya sameta tana bitar karatunta, hannu ya sa ya sakalo wuyan ta. “Har kan ya daina ciwo ne? Na ga kin dau littafi?” “Da sauki dai, amma har yanzu ba na jin dadin jiki na.” “Uhm! Haka ne? Gyara ki ga yanzu zan miki maganin komai.” Ya sa hannu ya zare littafin a hannunta. Rumaysah ta sa dariya. “Ka ga ina zaman zamana, za ka hanani yin karatu.” “Ba sai da lafiya ake komai ba?” Yana shirin kamota ne, ya ji wayarsa tana kara. Ya dubi (Screen) din. Mamaki ne kwarai ya kama shi, ganin lambar wayar. Yatsarsa daya ya daga ya-ce. “Minti daya ina zuwa.” Yana daga wayar, ya mike, domin amsawa, kai tsaye ta ga ya nufi waje. Kusan minti ashirin ya dauka, sannan ya shigo ciki. “Sorry na dade, me na ke fadi ma?” “Babu, ka na fadin ya kamata na samu hutu ne, don haka sai da safe, na ji kaina ma yana kara wani nauyi.” Kafin ya-ce wani abu. Ta mike zuwa dakinta, abokin kukanta ta nufa wato gadonta, can ta dare ta hau sana’ar da ta zaci ta gama yin sa. Ta yi sauyi da farin-ciki, ashe da sauranta.4 Watau da sauran rina a kaba kenan. Dama Yaya Fawzaan karya yake mata? Ta kasa yarda da abinda kunnuwanta suka jiye mata, wadanda sun fi kama da sukar kibiya, a cikin dodon kunnen nata. Fawzaan kuwa ya ji mamakin tashinta haka farat daya. Domin hatta wayarta ta bar ta a nan kan kujera, don haka ya daga mata ya rufe ko ina, sannan ya bi bayanta, amma ga mamakinsa ta rufe kofar dakin da key. To wai me ke damun Rumaysah? Lokaci daya kawai ta birkice. Ya kwankwasa kofar ma, shiru ba ta bude ba, don haka ya wuce dakinsa. Yana shirin shiga wanka ne, ya ga wayarta ta yi tsuwwa. Don haka ya fasa, zai kai mata wayarta, ko ta nan zai ji ma me ya same ta. Fannin sakon da Firdausi ta turo mata ne, Ya jawo hankalinsa har ya bude sakon gaba daya. “Ke, Saleem ya addabe mu, kin tafi tun ranar kin bar mu da Drama. Yanzu dai haka ya matsawa Umar shi fa bai yarda ba, ya dawo wani abin tausayi kamar zai zare.”2 Fawzaan ya yi shiru, waye kuma Saleem? Tabbas da dadewa ya ji Umar yana mata maganar wani Saleem, lokacin bai ma damu da ya san waye ba. Juyawa ya yi ya shige ya yi wankansa. Da safe tana kicin, ya sauko zai wuce wurin aiki, daurewa ta yi ta danne zuciyarta ta gaishe shi. Wani kallo yayi mata, sannan ya ajiye mata wayarta kan fridge ba tare da ya ce mata komai ba, ya wuce ofis. “Tabdi! Ni zai nunawa shan kamshi da kora kunya da hauka? Bayan ni ya batawa rai?”3 Kwafa ta yi ta ci-gaba da aikinta, amma tana tattara kicin dinta, ta sauke tukunyar da ta yi niyyar yin (Pepper Soup), saboda ranta ya baci. Gidan Anty Safiyya ta shiga ranar ta wuni, ga shi ba ta jin dadi, amma haka ta zauna suka yi aiki, suna hirarsu. Ba ta dai ce mata ga matsalarta ba. Sai yamma da Baban Fadila ya dawo ne, ta koma gidanta. Sai dai nata Mai-gidan tukun shiru, don haka ta kissimawa ranta kawai yana inda ransa ya fi sanyi. Koda ta ji sa key dinsa a jikin kofa, ba ta yi motsin zuwa bude masa ba, kamar yadda ta saba. Ta yi niyyar share shi ne, ta-ce sai ta ji dalilin da zai sa aka bata mata rai, sannan za a tsume mata. “Yaya Fawzaan.” A fusace ya juyo ya dubeta. Rumaysah kuwa ta yi kokarin sassauto da fushinta ta-ce. “Yau kuma shareni ake yi, don an samu inda ya fi nan?” STORY CONTINUES BELOW “Idan ki na da magana ta gaggawa, ki fada, idan kuma wannan ne ba ni da lokacin shirmenki.” Mamaki ne ya hanata furta komai, maganarta ce shirme ko? Lallai ma, don ya samu abin da yake so ya samu Meenar sa, dole ya-ce mata shirme. Lokacin da yake fada mata maganganu masu dadi da kwantar da hankali. Ashe ita take rudan kanta. Amma harshensa ya sha banban da na zuciyarsa. “Dole ka kirani shirme, tunda dama can ba ni da matsayi a zuciyarka. Meena ta rufe maka idanu, wanda ya kai ko lokacina ba ka da shi, a gaba na za ka iya tashi ka amsa wayarta.” “And so what? Aurenta zan yi, ko ki na da matsala da hakan? Kin san ina da dama, yin hakan, ko mata uku bayan ke duk zan iya auro su, saboda haka ki shiga sabgarki ki fita daga tawa. Kar ki kara min bincike kuma”. “Allah ya sawwaka, na bincike ka, kar ka manta a windon kujerar da na ke zaune ka tsaya ka gama zancen ka, don haka ba sai na sha wuya wurin gano sirrinku ba.” “Kin jiyowa kanki abin da ya dace ai, tunda kin san cewa sauraron maganar da ba ayi domin ka ba baida kyau.” Sai lokacin ya tuna shi ma ya karanta sakonta, don haka laifin su daya, kai ina laifin Rumaysah ya fi nasa girma. “Kin ba ni kunya, kin kuma ba ni mamaki, ina miki shaida mai kyau, amma kin dusasar da wannan taswirar ta ki a idanuna da zuciyata.” Takaicin kalamansa ne, ya sa ta zirarar hawaye, ta juya ta haye sama abin ta, don ba ta san akan me yake mata wannan tuhuma haka ba. Alwala kawai ta yi, ta hau yin nafilfilu. A nan wurin da ta idar da sallar, ta sulale. A haka ta kwana, ruwan da ya yayyafa mata ne, ya yi sanadin farfadowarta da wani numfashi a fizge. Ajiyar zuciya ya sake yana dubanta, ita ma kallonsa take yi, cikin rashin fahimtar abin da ya sameta. “Yaya Fawzaan me ya faru?” “Ke kin san ki na da zuciya marar karfi. (Weak heart), sai ki kama ki yi ta wahalar da shi da abubuwan da babu gaira babu dalili, wai yanzun me ya sameki tun shekaranjiya, kin bi kin daga hankalinki har ga shi ki na neman ki tona min asiri. Yaya ki ke son na yi? Idan wani abu ya same ki. Idan ki ka sake kuskura ki ka yi min wasa da lafiyarki, ina tabbatar miki ba za mu shirya ba.” Tana jinsa, sai fada yake mata, yana kai aya. Ta fashe da kuka. “To ba kai bane har yanzu sai kula Meena ka ke yi ba, ban san me na maka ba, da ba za ka so-ni yadda na ke sonka ba. Sannan bayan ni ka yiwa laifi, ka kama ka dauke min wuta da wanne daya ka ke son na ji? Ba ka san yadda raina yake yi ba, muddin na ganka ka na fushi da ni. Me ya sameni, ku ke boye min da Abba?” Tausayinta ya ji ya kama shi, don haka ya yi ajiyar zuciya sannan ya-ce. “Babu komai.” Hannunsa ta riko ta-ce. “Yaya Fawzaan ka fada min koma meye?” Yana kallonta ya san ba za ta bar shi ba, sai ya fada mata. “Tun wani lokaci da Momi ta rufe ki a (Toilet). Abba ya same ki ya kai ki asibiti. To sun miki gwaje-gwaje. A nan ne suka gano akwai matsala da yanayin bugun zuciyarki, wannan ya sa akai miki wannan (Test) na (ECG), don a tunanin Abba kar wani mummunan ciwon ne. To an dai ci sa’a, duk da ciwon ya ta’allaka da zuciyarki, ba zai iya ba ki bugun zuciya ba. Ya fi kama wadanda suke cikin kunci ko kuwa suka rasa wani na su na kusa, wato. (Broken Heart Syndrome). Kwarai da mamakin yadda suka same shi a tare dake, duk da ki na cikin damuwa, amma ya fi kama mata masu matsakaitan shekaru. Sannan abin da ya sa muka tsorata, ganin yadda yake yawan tashi miki, duk da dai jiya ban san me ya sumar da ke ba. Haka na shigo na same ki da tsakar dare, don mu yi magana. Ba abin daga hankali bane, tunda an dace da magani, idan an ci sa’a ma, ki rabu da shi kwata-kwata. Shi ya sa don Allah na roke ki, ki daina sa kanki a cikin damuwa.” STORY CONTINUES BELOW Ajiyar zuciya ta yi, tana matsar kwalla. “Na ji. Insha-Allahu zan kula da lafiyata.” “Batun Meena kuma da kin tsaya kin ji hirar da muke yi da kin fahimci cewa ta fatan alkhairi na ke mata, saboda Hajiyarta ta sa ma mata miji dan kawarta, don haka sai ki yi (Party), an kayar da mijinki a wurin neman aure.” Yana fada, ya mike zai bar dakin, da sauri Rumaysah ta riko hannunsa ta-ce. “To kuma shi ne ake ta tsume min za a huce a kaina? Haba Love, please ka fada min me na yi maka ne?” “Hmm! Ku AMAREN BANAN nan akwai ku da iya salo, sai mutum ya kasa gane maku, wai ki yi abu, ki na Pretending, kamar ba ki san komai akai ba.” Kwantar da wuya ta yi ta-ce. “Ya Salam! Idan ma na sani, to Wallahi na manta, ka yi hakuri, ka kara min haske.” “Waye Saleem?” Gabanta ne ya fadi, ina kuma Yaya Fawzaan ya hadu da Saleem? “Saleem kuma?” “You see, ba ga irinta ba, yanzu ce min za ki yi ba ki san shi ba ko? Me zai sa Firdausi take miki maganarsa?” “Ni dai na san tsakani na da shi, ya dade da shudewa, kuma abokin Umar ne. May be ko wani abin ya faru, amma yaushe Firdausi tai min maganar Saleem?” “Ki duba wayarki.” Tana gama karanta sakon Firdausi, hankalinta ya tashi, “Allah, Yaya Fawzaan rabon da na gan shi ma ni na manta.” “To da alama shi bai manta ba, idan ma da gaske ki ke yi ba ku haduwa, me sakwanninsa suke yi a ma’ajiyar (Archive) cikin wayarki?” To ashe zancen kenan. Yayan nata karanto tsohon zance ya yi hankalinsa ya dugunzuma ya tashi, ashe dama ta taba son wani haka? Ko kuwa har yanzu ma dai son nasa take yi, ya hana ta rabuwa da sakwanninsa? Tunaninsa kenan. “Afuwan! Idan don wannan ne, kuskure na ne, amma yanzu ma ni sai na cire komai na kan wayar nan, amma ina tabbatar maka da rabon da na yi koda tunaninsa ne, na manta. Kai kadai NA KE SO, ba ni da na biyunka, ka riga ka rike komai”. Hannu ya sa ya karbi wayar gaba daya, ya-ce. “Anjima Insha-Allahu zan kawo miki wata wayar, ki mayar da lambobinki, amma ba na son koda ganin wani abin da zai tunatar miki da kasancewarki da shi, saboda haka kawai ki yi baya-baya da su Umar din ma, tunda a can yake ganinki.”3 Yau tana ganin ikon Allah. “Amma dai Yaya Fawzaan ka san dai Firdausi ba za ta bar wani ya kula ni ba ko? Bare ace ta taimaka wurin hakan, ka san yadda tsakanin mu yake kuma ka san halinta da tana da wata mummunar halayya da ka dade da sanin wannan.” “Na sani, amma dai ki dan rage kafa tukun.” Murmushi ta yi, ta san duk kishi ne ya motsa masa. “Insha-Allahu zan kiyaye. Allah ya huci zuciyarka. Yunwa na ke ji.” Ta karasa fada tana yamutsa fuska. Da wuri ya mike zai fita, sai kuma ya tsaya. “Me ki ke so?” “Abin da ka iya dafawa.” Dariya ya yi ya-ce. “Kar ki raina min bajintata a kicin fa, ehem.” “To, Baby ya-ce kunun farar shinkafa da gyada yake so.”7 Cak! Fawzaan ya tsaya yana kallonta, kafin nan ya dawo ciki. “Ban fahimce ki ba, me ki ke nufi da Baby ya-ce?” “Uhum! Ka ji daidai, abinda ya-ce kenan.” “Rumaysah banda zancen wasa, don Allah da gaske ki ke yi?” “Ai ka san ni ba na wasa, ba irinsu o’o bane, masu waya su baza ba tare da samun tabbaci ba.”5 Rungumota ya yi jikinsa cikin farin-ciki. “Alhamdulillah! Yau Allah ya kamaki. Amma yaya aka yi ki ka sani?” “Tun shekaranjiya na yi (Home P.T), wato gwajin gida na gano, zan fada maka ne, na ji ka ka na waya da Meena, sai na yi fushi na fasa.”12 Dungure mata kai ya yi. “Ya kai yaya girmansa?”3 “Ba ya nunawa ai, sai asibiti wannan.” Haba dadi ne, ya shiga ratsa Fawzaan, ya ma rasa abu guda da zai yi, da farko ce mata ya yi. “Ki yi wanka mu tafi asibitin, koda yake bari na kawo miki kununki, ki sha tukuna. Ko dai za mu tafi ne ma kawai yanzu? ya Allah, yaya ake hada kunun?” “To sarkin zumudi, asibitin ma ba su bude ba yanzu. Ni matsa ma na yi sallah ka cika ni da surutu.” Sai lokacin ya dubi agogo ya-ce. “Ai ni ma kuwa na makara. Bari ni ma na yi alwalar, sai na zo mu yi sallar tare.” Kallonta yake ta yi cikin ta’ajjubi, tamkar ya kasa yarda tana da ciki. Suna idar da sallah, ya yi addu’a ya shafa mata, wai Allah ya kareta da Babynsa. Kamar daga sama, ta ji ya-ce. “Wane suna za mu sa?” “Ho! Yaya Fawzaan, aje tukun a tabbatar mana, sannan ka hau zumudin suna, kuma idan ka yayata ni, wannan karon, to kai zan nuna, tunda dai yanzu kam na san mai shi.” Dariya ya yi ya ja hancinta. 2 ******** Wata ranar lahadi ne Deeni ya kira Rumaysah yake shaida mata Radiyya ta sauka, ta samu ‘yan biyu mace da na miji. Rumaysah ko kuka ta sa. Fawzaan ya tambayeta. “Yaya dai? lafiya kuwa? “Yaya Fawzaan wai Radiyya dai ta haifi Twins, ba abinda na ke hango mata irin yadda za ta fara kulawa da su. Allah dai ya kiyaye kawai. Amma Radiyya mai manta mota a ofis kam, sai a hankali ai.”11 Dariya ya yi ya-ce. “Ban gane ba?” “Ban taba fada maka ba? Ranar ta je ofis kawai, suka fito za su tafi gida da wata ‘yar ofis dinsu har sai da suka isa gate a kafa. Kawar ta tambayeta ina motarta ta? Sai lokacin ta tuna da cewa ta taho da mota ofis, ta koma ta dauko.”2 Dariya ya yi ya-ce. ‘Radiyya kenan, ai Deeni yana kokari, sai dai bai kai ni kokari ba, don gwamma shi, tawa Drama Queen ce.” 3 Rumaysah ta yi azamar janyo filon kan kujera, sai ta ji wayam! “You see? Na kwashe ai, sai ki nemo wasu.”5 ************ Suna zazzaune a dakin asibitin ne. Hajiya Sogiji ta-ce “Tab! Lalle kam da sakel, haka kawai ni da shan wuya, ke da kwace ladan Atika, to ban yarda ba.”+ “Ke ma dai yanzu kam sai dai ki ci girma, amma wannan kam tawa ce.” “A’a ke ma kin san wanda ya kamata ya ci girma kam. Amma an wuce nan, ba ki ga yadda na ci wuya na daddage Baby ta yi kama da ni ba, za ki wani kama ki ce a sa mata sunanki?” “Gaskiya abin kuma ai sai ya yi miki yawa, watanni biyu da suka shige. Sajeeda ta sa mai sunanki, yanzu kuma idan an kuma ai, sai abin ya yi miki yawa, ke har nawa za ki tara?” Muneera ce ta yi caraf! Ta-ce. “Ikon Allah, ku jira masu shi su yi wa yarinyar ma tukun kyakkyawan kallo kun ki, kun tsaya ku na ta musun sunan da za a sa, bayan kwata-kwata awar yarinyar guda da zuwa duniya.” Hannu ta sa ta daga Baby ta-ce. “Sai hakuri kin ji? Kishiyoyin naki sun yi kos wurin fada, naki idanu, rabu da su Goggonki ce za ta zaba miki suna.”2 Rumaysah dai tana kwance kan gadon asibitin tana ta binsu da idanu, wani farin-ciki yana lullubeta, wai yau ga Momi tana farin-cikin samun karuwarta daga jinin Mama Sogiji. Ikon Allah. Babu abin mamaki.2 Da wuri uban yarinya ya-ce. “Lah, rike ta da kyau Muneerah, wannan cikin naki yana zungure mini ‘ya fa.”10 Salati Mama ta sa ta-ce. “Yau ina ganin abu a nan. Fawzaan haka aka ce maka ake yi ne, sai ka yi ta wani nuna iko kai tsaye, sai ka bari ai mu bar wurin tukuna, kun ga min shegiyar rashin kunya.”9 Fawzaan ya sosa keya ya-ce. “Mama ba dole ba, nakudar nan fa da ni aka yi ta.”7 Kowa a dakin ya sa masa dariya, da ya ga sun masa yawa ne, ya sa ya fita a dakin, ba wai don ya gaji da kallonta ba. Sai can da dare ne ya shigo dakin, ya samu Rumaysah ta tashi a barci, ta yi wankanta fes! Kamar ba wacce ta haihu yau ba. A bakin gadon ya zauna yana kare mata kallo. “Sannu, love. Yanzu kam kin huta ai, ba sauran damuwa Ko?” Ya fada yana shafa gefen fuskarta. “Damuwa kam ai akwai su kala-kala, sai dai hamdala. Yaya ofis? Na ga alama dai yau ba ka zauna ba, kai ga ka an maka haihuwa”. “Su ma sun sani ai, su kansu murna suke yi, tsabar yadda na matsa masu da hirar Baby din da za mu haifa”. Rumaysah ta yi murmushi, kallon su, ya koma kan Baby dake kwance cikin dan gadon ta. “Da gaske fa da ni take kama.” “Wa ya-ce maka ana gane kamannin Babies da wuri? Kuma idan ma kai ne, ka san ni ne, an taba fada maka muna kama?” Dariya ya yi, ya make goshinta ya-ce. “Da wannan zungureren goshin naki muka yi kama?”6 Juya idanunta ta yi cikin fada. “Ni ce mai zungureren goshi? Na ga dai a haka ake sona kuma ba yadda aka iya”. “Yau idan ban so goshin nan ba, ai nawa ta sameni, ta yaya zan samu ayi taurin kan makale min har na samu Love of my life?” Ta buge hannunsa kenan, sai suka ji an bude kofa. Rayyan ne ya shigo da wani abokinsu Fawzaan, Musa. “Maasha-Allah! Madam kin sauka lafiya?” Rayyan ya fada yana kallon Baby a kwance “Lafiya kalau. Alhamdulillah! Yaya A’isha?” “Lafiyansu kalau, ga Baby nan Maa-sha Allah! Allah ya raya mana ita. A’ishan ma tana gaishe ku, wai sai kun koma gida ta zo.” “Ameen. Muna amsawa.” Sun gama gaisawa ne. Musa ma ya daga Baby yayi mata addu’a. Rumaysah ta-ce. “Yaya Labarin Meena, ni dai ta share ni, har yau shiru ta kasa zuwa?” STORY CONTINUES BELOW “Tana can lafiyarta kalau, suna Kaduna.” “To don Allah ka gaisheta, banda lambarta yanzu, ko za ka ba ni, sai na ba ta labarin haihuwar.” “To ba matsala.” Nan Rayyan ya bata lambar, su kai masu sallama suka wuce. Fawzaan ya dawo daga raka su ne. Ya yi mata wani kallo tukun. Ita kuwa ta-ce. “Meye? na yi laifi ne, don kawai na karbi lambarta? Ka ji ko tana ma Kaduna, idan ma…” “Na kula ke kullum ma kin maida abin nan abin dariya, ba ki san yadda na ke ji ba ko? Na kula ma ba ki damu ba. Ki na ji, ki na gani an kwace min abin da na ke so, maimakon ki tayani samota, kin tsaya ki na min dariya.” “A’ah, yo me ya yi zafi, shi ba wuta ba? Idan ka ga dama ka dauki Baby ma ka hada da kai kanka ku je na ba ta kyauta, ka ga ni ko za ta amshe ku. Ai yanzu kam sai dai wata Meenar.” Ta fada tana dariya. “Yau na ji halinki. Ba damuwa, tunda ita tayi min nisa, akwai wasu ai, wanda suke shirye.” Rumaysah ta ga kamar da gaske yake yi ta-ce. “To Malam, ka ma daina sa komai a ranka, domin kuwa za muyi maka taron dangi ni da Baby. Kar ma ka fara wasa daga haka yake zama gaskiya, ehem.” Yana kallon yadda ta yi narai-narai! Sai wani kaunarta ta kara kama zuciyarsa, saman kanta ya sumbata, yana murmushi, bai fadi abin da zai ce ba, sai ga Mama ta shigo dakin, ta-ce. “Kai yi waje, meye haka ka zo ka damesu? Don Allah tafi gida, su samu su huta. Tunda yarinyar nan ta haihu, idanunta biyu saboda baki, sannan dare na Allah ma ba za ka bar su su huta ba Gandoki?”4 “To Mama, yanzu ma daman na ke shirin tafiya. Sai da safe, daman na tsaya na ji koda abin da suke bukata ne.” Ya dubi Rumaysah, ya kashe mata ido ta gefe. Sannan ya wuce, ita kuwa ya bar ta da aukin murmushi. Washegari aka sallame su, suka koma gidan Baffa, an riga an shirga tarkacen Baby ko ta ina. Mama ta hada komai haka Momi, wai su a dole Campaign. Su Khamsa’u duk sun taho suna, hankalinta ya kwanta ita ma yanzu kam ta fara gano kan Sa’ad dinta. Sajeeda ma haka ta taho da Bebinta Mumtaaz. Sai ana gobe suna ne Fawzaan da Rumaysah suka fadawa su Abba takwarar Goggo Shatu aka samu, wato A’isha (HISHMA).2 Su Baffa sun ji dadi kwarai da suka nuna wannan karar. Goggo Shatu ko sai hawaye kawai ta fara da ta ji wai ita suka yi wa takwara. A’isha Hishma dai ta yi goshi, domin irin alkhairan da suka samu, a dalilinta. Tunda taron suna ya watse. Fawzaan ya mai da gidan Baffa wurin hirarsa, shi a dole ya zo ganin ‘ya. Tun Mama tana shiru har ta soma fadin. “Idan ba ka bar mana sintiri a gida ba, za mu canja masu wurin zama, wato mu ba ka jin nauyin mu ko?” “Mama, so ki ke yi kuma ta manta Babanta ne, idan ba na zuwa?”2 Dariya ta yi tana kallon Fawzan, a zuciyarta ko dadi ne fal! Ta san har da ganin uwar ke kawo shi. Sai ta tuna yadda ya kafe kai da fata ya-ce sam shi baya sonta, ga wacce yake so, yanzu kuwa komai ya zamo labari.4 ************ “Don Allah ku koma gida, har yanzu ba ku gama wankan bane? Komai mutum baya yinsa ta dadi, ban san wace mata bace ma ta kirkiro zuwa wankan gidan nan Wallahi.”4 “Oh, don ka samu ma ban tafi gidan Abba na ba? Kai ma ka san da a can ne ko sakewa ba za ka samu daman yi ba, bare ka sheke ayarka, yadda ka ke so, kalla fa yanzu sha daya saura. Amma ba za ka koma gida ba, kai ba ka tsoro ma yanzu yadda kasar nan ta dawo babu tsaro. Amma kullum kai kenan cikin sintiri, ga unguwa ba kusa ba. Ni gaskiya idan haka ka ke min, sai na ce Mama zan tafi gidan Goggo Zainabu a Dan-sadau.” “Tabdi! Yarinya kamar da gaske, ina za ki tafi min da ‘ya ta? Ke din ma ba iya zaman can za ki yi ba, bare Hishma ‘yar AC.”1 “Ko za ka yi yaya dai, ta can aka fi kauri. Da gaske na ke yi, ka rinka komawa gida da wuri don Allah.” STORY CONTINUES BELOW “To na ji, ranki ya dade, ni ma da gaske na ke yi, ki tattara ki koma gidanki, sai na daina damunku”. “Ai yanzu muka yi sati uku, sauran mu sati uku kuma, don haka rabi kenan, saura rabi.” “Amma dai Rumaysah ban taba sanin da gaske ke muguwa bace sai yau, yanzu sati uku ki ke son na kara ba ni da mata? Lalle kam.”6 “Allah da gaske haka ake yi, sai na yi arba’in na gama yawon arba’in, sannan na koma, wasu kam har sittin suke yi ma.”2 “Ai dai ni kam ko arba’in din ki ka ce za ki cika, zan dauke ‘yata sai ke ki sha zaman ki, don Allah ya gani, ina da bukatarki kusa, ki ka takura min kuma dole na nemi abin yi.” Kallon sa ta yi ta-ce. “Kai ma dai sai dai ka yi hakuri kam, amma su Mama ba za su taba yarda na tafi ba, kafin arba’in.” Wani kallo yayi mata wanda ya gwada mata wasa fa ya kare, yanzu zancen gaskiya yake mata “To shi kenan, ni dai zan masu magana, amma idan suka ce za su ci-gaba da rike ki, sai su gwada min inda addini ya-ce ayi hakan. Don akan haka siddan! Ba za a jefa mutum cikin wani hali ba.”2 Ya mike ya bar dakin, ranta ya sosu, to don me Yaya Fawzaan zai dau wannan zancen da zafi? Sai ka ce ita ta kafa al’adar? Ta san ransa a bace yake, don ko sake daga Hishma, bai yi ba ya bar dakin. Washegari, Radiyya ta shigo masu, da yake a gidan Abba take, sai take ganin ga shi ita ma ta yi har kwanaki arba’in dinta, kuma tana karawa, saboda ta koyi kula da yaranta Nidaa da Nabeel. Bare ita kam mai biyu ma. Koda suka gama gaisawa, suna hira da Mama, kamar ta dago mata yadda suka yi da Fawzaan jiya. Amma ta yi shiru, gwamma dai shi ya yi masu magana, waka a bakin mai ita, ta fi dadi. Bayan kwana biyu Radiyya ta koma gidanta. Amma sai da aka hada ta da mai aiki. Sai dai a cikin kwanaki biyun nan Fawzaan bai zo ba, asali da Rumaysah ta ji shiru ne ya sa ta neme shi a waya, sai ce mata ya yi tafiya ce ta kama shi, baya ma gari ya tafi Lagos saboda wasu Clients da yake masu aikin (Consulting). Ranta ya baci sosai, me ya sa Yaya Fawzaan yake mata haka ne? “Wai yaya yake son na yi ne shi kam?” Haka suka yi sati bai zo ba, tun tana boye damuwarta har ta kan zauna ta buga tagumi tana tunani, don gaskiya daga ita har Hishma sun yi kewarsa.4 Ranar da ya cika sati ne, tana zaune a daki tana aikin tunani, ta sa Hishma a gaba da kallo, kwatsam! Ta ji muryarsa a falon Mama, kamar ta fito da gudu ta gan shi, amma ta yi zamanta, saboda ita ma tana fushi, don me zai share su? A dakin ya shigo ya samesu, bayan ya gaisa da Mama, sai da ya ji wani abu ya bi ilahirin jikinsa, domin kuwa gani ya yi kamar an canza masa su, sun kara kyau da cika, da alama dai su hankalinsu a kwance, ba su ma damu da shi ba. Wata doguwar riga ce a jikin Rumaysah ta amfa mai kalar Orange da dan ratsin kore a jiki. Ya bi jikinta ya lafe ko ta ina, ya fito da kyawun surarta, cikin nan shafal! Kamar ba ita bace ta haihu, siririn hannu ne da shi, an masa dinki tamkar (Ready Made). Sai ta gaban rigar aka sa boyayyiyar Zip, saboda shayarwa, yawanci dinkunan da ta yi kenan kafin haihuwarta da atamfa masu laushi, duk da ta fi son sa (English Wears), ta kula Fawzaan yana son atamfa. Shi ya sa sai ta bayar a dinka mata yadda ita kuma take son tsarin su. Ta tufke gashinta, ta keya jelar kuwa na tabo bayanta, fuskarta sumul! Sai sheki! Yake yi, tamkar yadda fatar jikinta ya kara wani sheki shi ma, don daga nesa, ya san idan ya taba fuskarta laushin da zai ji, ko meye sirrin, oho?9 Wata zuciyar ta-ce masa, wane sirri kuma? Kawai dai ba ta damu da kai bane, ta kwantar da hankalinta, shi yasa ta kara kyau, gwamma Hishma jinjira ce, ba ta san me kake ciki ba. Amma ai Uwarta ta sani sarai, kuma ta share ka. STORY CONTINUES BELOW Kallon sa ta yi ta-ce. “Sannu da dawowa.” A ranta ita ma kallon nasa take yi, bai damu da su ba, tunda har ya iya tafiya ya yi sati, sai dai ita ta kira wayarsa, shi bai damu ya kira ba, ta ga har wani bulbul! Ya yi, wai shi a dole ya je aiki.4 Kai tsaye zuwa ya yi ya dauki diyarsa tana barci, ya kare mata kallo, ya sumbaci fuskarta hade da shafa kanta, sannan ya kwantar da ita a kan gado. “Yaya muna zaman mu kalau! Za ka zo ka dauke min ita?” “Yaya za ki ganni, ki nuna ba ki damu da ni ba?” Ya fada shi ma idanunsa cike da al’amura, idan ta tsaya biye masa hawayen da take makale da su ne kawai za su biyo fuskarta. Don haka ta mike, za ta fice daga dakin gaba daya, tunda ‘yarsa ya zo gani, sai ya karasa lafiya. Hannunta ya janyo da karfi, sai da ta taho gare shi, ya riko bayanta ya hada da jikinsa, idanu ya zuba mata yana kallonta, ita din ma shi take kallo, tana haki tamkar wacce ta ciyo gudun famfalaki. Za ta yi magana ne, ya sa yatsarsa daya ya rufe mata baki, hade da shafa labbanta da yake matukar so. Gani ya yi kamar sun kara zama wani (Light Pink) haka, sai wani kamshin turare take yi na musamman. Kamar wani hadin baki, lokaci guda suka shiga nunawa juna wasu al’amura da yake bayyana sirrin zukatansu, can ya daure ya saki labbanta, ya-ce. “Za ki shirya mu tafi ko kuwa kin zabi ki ci-gaba da azabtar da mu?” Kunya ne ya rufeta sosai, ita kanta ba ta san ta yi kewarsa haka ba, sai yanzu, don haka bayanta ta juya masa tana murmushi, sannan ta fice daga dakin cikin sassarfa. Fawzaan ya bi bayanta da murmushi, yana shafa kansa. Tabbas yau ba zai bar gidan nan ba, sai da matarsa, ko sun gama da ita, ko ba su gama da ita ba, dole su ba shi abinsa, ehem, haka kawai. Ai gara su gyara mai gammo, ko ya ji dadin dauko, ai ya hakuru.7 Sai dai duk zakewarsa, ya kasa musawa Mama da ta kafe, sai ya kara masu sati guda. Shi ya rasa me Rumaysah take masu ne a gidan da suka rike ta, haka kawai sun sa ta yi wani kyau, sannan sai faman hanasa abinsa suke yi. Idan ba tsoron karya ba, da ya ganta dazu sai da yawunsa ya tsinke. Amma haka kawai a bi ayi ta wahalar da shi, ita ma da za a ritsata, ya tabbata tana son komawa. Don bisa dukkan alamu, ita ma sai a hankali “Ai Wallahi an yi na farko, an yi na karshe, ba dai ki kara zuwa gida wanka ba.” Ya fada yayin da ya zo fita daga dakin bayan Issha.17 Murmushi ta yi, amma har cikin ranta ita ma ya ba ta tausayi, sai dai ba ta isa ta-ce komai ba, manya sun yi magana. Koda satin ya zagayo, kada keyarta aka yi suka wuce Dan-Sadau gaishe-gaishen arba’in. Wata sabuwa, in-ji ‘yan caca. Wayyo Allah! Fawzaan dai ya kusa ya fashe masu, don har wurin Baffa ya kai kara yau kam. Baffan ne ya ba shi hakuri ya-ce. “Suna dawowa, ba zan bar su su shiga ciki ba, za ka wuce da iyalinka, rabu da su.” Ai koda magriba suka iso, sun zo sun samu ya tattara duka kayansu ya tafi da su gida. Rumaysah kam kunya duk ya bi ya cikata. Ai zakewar ta yi yawa. Shi kuwa ko a jikinsa. Yanzu ko share-share ba zai bari ta yi ba?6 “Gobe Momi za ta turo su Yalwa su zo su miki sharar, yau kam hutu ya kare.” Ya rungumi diyarsa suka yi gaba. Rumaysah ko ta tsorata da Yaya Fawzaan, don ta san ita kam sai yadda hali ya yi da ita, nan ma wai a shirye take da ba kanta. 5 ******** Baby Hishma ana da watanni shida Rumaysah ta gama bautar kasarta. Fawzaan kuwa karin ci-gaba da yake samu abin ba a cewa komai, domin kuwa yanzu shi yake shugabantar bangaren ofis din su na Abuja a matsayin babban lauya.2 Har dai yanzu ana nan tare da Firdausi da Naja’ah, domin kuwa watan da ya gabata aka yi bikin Naja’ah da wani saurayinta Dan Yemen. Mas’ud An-Naaji. Su Rumaysah su ne a gaba, saboda auren babbar kawa, a nan dai aka sha shagali irin na AMAREN BANA!!!2 STORY CONTINUES BELOW *************** Ana ta hidimar sallah gidan Rumaysah. Firdausi ce ta zo da yaranta uku, da kuma mijinta Umar, domin sada zumunci, a yanzu dai a Lagos suke da zama. “Hmm! Rumaysah, yanzu dai na yarda ba a wasa da al’amarin Ubangiji, wato dai yanzu rabon wadannan yaran ne, ya sa aka kada abokin mu ko?”6 “Kai dai Baban Farisa ba ka gajiya da wannan zancen, daman haka rabo yake. Yanzu yana ina ne abokin naka?” “Firdausi kin ji kawarki da wata magana kuma, yana can Lagos yana tare da CAC (Cooperate Affairs Commision). Ya dai samu ya yi aure da kyar da sudin goshi, ‘yar su ma daya yanzu. Har gobe idan muna tadi, sai ya-ce ke ki kasa Mami ta yi masa baki, wai ba zai samu macen da ta so shi kamar ki ba, domin dai wannan kam tana gwara kansa ba laifi.”4 Firdausi da Rumaysah suka kalli juna suka yi dariya. “Allah ya daidaita kansu, saboda Rumaysah kam hankalinta ya kwanta da zabin Abbanta. Yaya Fawzaan ya tare mata komai, sai hamdala ga ta da yaranta tubarkallah Mashaa-Allah! Ya je dai can ya lallaba da ta sa, daman an ce idan ka tsaya kallon ruwa…”7 Haka dai suka ci-gaba da hira. Can sai ga Fawzaan ya iso ya bawa Umar hakuri akan Traffic ne ya tsaida shi. Sun masu sallama. Rumaysah kuwa ta hado yaran da tsaraba kala-kala ta ba su. Ai nan su Hishma da Hisham suka dage sai sun bi su Farisa, Hayaa ita-ce karamar ita-ce a hannun Rumaysah. Da kyar Dadin na su ya yaudaresu ya tafi da su shawagi a tasa motar, sannan ya dawo da su gida. Suna dawowa kuwa suka duru gidan Anty Safiyya. Rumaysah ta ga ya shigo shi kadai. “Yaya ina su Hisham din?” “Suna can gidan Maman Fadila, kai wannan yaran naki ba?” “Oh, yanzu kuma yara na ne, da suke kiriniya ko? Ba damuwa bari su jika wataran.” “Ba za su ji ba Insha-Allahu, na yi kuskure yaran mu na ke da nufin fadi, kin san ke din ce, idan mutum yana kallon ki. Sai ya rasa ma me yake furtawa, saboda yadda ki ke kidima ni.”2 Juyo da fuskarta ta yi ta gefe kadan, ta yi wani salo da idanunta tana murmushi, nan ya hado da ita da Hayaa ya rungume su, sai suka ji an banko kofa, an shigo falon. Da gudu Hisham ya biyo Hishma. Rumaysah ta-ce. ‘Kai kai, ku tsaya zo nan meye haka? Ban ce maku idan za ku shiga wuri ku yi sallama ba?” “Mami Sorry! Ba za mu sake ba. To ba kin ga Hisham bane Maman Fadila ta ba mu abu, shi ne wai sai dai na ba shi ya soma ci daga can?” “Kai Hisham da dai na dauka ka zama Big boy, ashe dai kai har yanzu karami ne, tunda ka na cin abu a waje.” “A’a Mami na girma fa, wasa na ke mata dama.” Nan suka sa masa dariya, saboda ba abinda yake so irin girma. Rumaysah ta dubi Fawzaan ya matso kusa da ita ya rada mata. “Later”. A kunnenta muryarsa cike da alkawuran abubuwan da za su biyo baya, sannan ya wuce sama. Bayan ta kammala da yaran ne ta shigo dakinsa, da kofuna biyu a hannunta da shayin da ya ji su citta da kanunfari, sai tururi yake yi yana fitar da daddadan kamshi. Yana zaune a kujerun budadden Terrace dinsu littafin hannunsa ya rufe. Ya riko hannunta ya zaunar da ita a kan kafafunsa a hankali, yayin da ya sa daya hannun ya karbi kofi daya daga hannunta. “Hankali fa ruwan da zafi.” “Hmm! Ko na kone, ba matsala ko ba komai na samu an cika min burina na shan shayi da Rumaysata a nan. Duk da dai yanzu ba yamma bane”. Ya tsaya ya dan kurbi ruwan zafin sannan ya-ce. “Hmm, Magic, wai meye sirrin hannunki ne, komai ki ka taba shi daban yake?” STORY CONTINUES BELOW “Kai ne sirrin, saboda ka na ganin kyawun komai, ba tare da ka samo matsala ko kushe a cikinsa ba.” “To yaya? Na samu shan Tea, za mu raba Wardrobe din ne ko kuwa?”2 Murmushi ta yi, ta rausayar da idanu. “Na kauro na yi yaya da ‘yan yarana?” Tsumewa ya yi ya yi mata kallon tuhuma. “Ni sai na rasa wannan irin abu naki, kullum yaranki kawai ki ka sani ko?” “Ko daya, kai ma na san da kai wannan ya sa da zarar Hishma ta cika shekara bakwai Insha-Allahu, sai na rinka barinsu suna kwana su kadai, amma yanzu ya yi wuri da yawa.” Murmushi ya mata, ya sa hancinsa yana jin daddadar kamshin jikinta, wanda baya gajiya da ji koda yaushe. “Tea dinka zai yi sanyi.” Fawzaan ya yi wata dariya ya-ce. “Ai ina ga yanzu kam ba na bukatar Tea, duminki kawai ya isheni.”2 Ajiye kofin hannunta ya yi ya sunkumeta zuwa ciki, suna shiga ya juyar da ita setin kofar sannan ya-ce. “Tura mana kofar.”4 Kallon sa ta tsaya yi tana tuno farkon shigowarta wannan dakin, sai murmushi ya kawata mata fuska. Fawzaan kuwa ya-ce. “Really! Kin san kin kara kimanin kilo sha biyar akan da ko? So ki ke yi ki kada mu ko me? Kulle kofar”. Make kafadar sa ta yi cikin sigar so, sannan ta shige cikin jikinsa. “Asuba ta gari!” Washegari suka wuce gidan Abba da Baffa, duka ana tare gidan Baffa, kasancewar yaran kaf! Sun zo wunin sallah, ko wacce da nata bataliyar. Wai hayaniya ba a cewa komai. A lokacin ne aka tsaida ranar auren Bilal da Ra’id, nan da wata biyu. Ra’id dai gidan Maman Fadila ya gano ‘yar Gombe, ‘yar kyakkyawar Bateriya da ita ga kyau, ga alkunya ga ilimi, Nafeesa. Don haka nan ya makale, ya-ce sai ya kai ta Gusau ta Sambo dandin hausa, ko wazzo Gusau abi nai ya gusa. Farin-ciki ne a cike da su gabaki daya, hade da kaunar juna. Sai dai duk cikin dimbin jama’ar nan, duk inda Fawzaan ya juya idanunsa suna kan Rumaysah, domin ta zame masa tauraruwa, ta zame masa abin so. Koda gasar AMAREN BANA, za ayi har yanzu yana da tabbacin za ta lashe wannan gasar. Haka dai ya-ce.5 ~~~~~~~~~~~ Ni kuma nace Alhamdulillah!

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *