AMAREN BANA CHAPTER 1
Mummunar karar da ta taso daga wani sashi na gidan ne, ya yi sanadiyyar girgiza ilahirin gidan, da gudu jama’ar gidan suka firfito. Masu gadi da ma’aikatan gidan ne suka yi saurin kawo agaji, a inda aka fi tsammanin hatsaniyar ta fito.+ Wuta ne ke ci, ba ji ba gani, da sauri aka fara kawo agaji, wurin ya turnike da warin hayaki da kuma na gas, wanda aka fi kyautata zaton, shi ya janyo gobarar. Motoci biyu ne suka shigo. Sannan aka yi nasarar kashe wutar da ta kama kicin din. Hajiya Sogiji tana tsaye daga gefe tana mamakin faruwar wannan al’amarin ne, sai ta hango ta a tsaye a gefen ribibi, bala’i har diga yake yi daga fuskarta. Nan da nan ta harzuka ta isa inda take. “Atika, wane irin rashin hankali ne haka? Ashe haukar taki ta kai har za ki iya babbaka min muhalli na?”1 Ga mamakin Hajiya Sogiji sai ba ta musa ba, asali ma cewa ta yi. “To sai meye? An kona din, nan ma ban bi ki cikin barci na shake ki har lahira ba?”10 Hajiya Sogiji ta tabe hannunta ta-ce. “Eh, lallai na san za ki iya, ai dama dabi’ar munafuki ne ya kai maka damka ta baya ya kuma noke, baya taba fuskantarka gaba da gaba, tunda kuwa abin naki haka ne, bari yau Alhaji ya dawo, za a raba zumuncin nan, tunda baya haddasa komai, sai fitina.” “Oh! Ashe ba dadi? Duba ke fa wani bangare na dukiyar mijinki ne ya samu nakasa, shi ne za ki tada jijiyoyin wuya, ni kuma da dana yake can a kwance shame-shame. Idan kin kashe min shi fa? Sai nace me?” Kan Hajiya Sogiji ya daure. “Kashe miki Da? Kin san me ki ke fada kuwa Atika?”1 “Ko an fada miki ban san sharrin da ku ka kulla ba ke da Danki, ai ni na san da walaki, goro a miya, idan banda haka ba, ba yadda za ayi Danki ya dauki kyautar miliyoyi ya bawa jinina, ashe daman Plan dinku kenan, ya shiga motar ku hallaka shi, don kun ga shi ne Dana tilo namiji.”2 Hajiya Sogiji ta girgiza da furucin Hajiya Atika. “Ki kiyayi furucinki Atika. Yanzu daga yin alkhairi, sai ya koma sharri? Ta yaya Fawzaan zai cutar da Ra’id, bayan kasancewarsa jininsa?”3 “Idan ba haka ba, sai ki fada min ta yadda za ayi mota sabuwa dal! tayarta za ta fashe a titi, ku dai dama kun kwance wani wurin kawai, sannan ku ka dauko ku ka ba shi. Don haka ga can tsiyarku can, wurin makanikai, idan kun tashi, ku je ku dauka, ba mu so. Munafukai kawai”.1 “Yanzu daman abinda yake ranki kenan, zaman da ake yi tare? Ba abin da zance miki sai Allah ya shirya, amma ana zaune, ki na irin wannan mummunar zaton, meye amfanin zaman? Ki ji tsoron Allah ki kiyayi furucinki, domin kuwa hatsarin Ra’id qaddara ce. Ki yi wa kanki fada, ki bar dabi’ar mugunta”. STORY CONTINUES BELOW “Na ji, a wurin wa na koyi muguntar, muguwa.”1 Sajeeda dake tsaye ta kofar baya, tana hango muhawarar da ake tafkawa da mahaifiyarta, ta fito da sauri ta rike hannunta. “Mama zo mu shiga ciki, ki daina tsayawa ki na bata bakinki akan wadanda ba su san darajar kansu ba, bare na mutane.” Bin-su ta yi da banzan kallo, ta ja tsaki. “Oho dai, koma meye ne, na kona kuma na more.” Nan ta nufi wawasheshen gate din da ya raba tsakanin su, wanda tsabar masifa da muguwar gaba ya sa mijin Hajiya Atika gina katanga a gidan su, da girmansa ya yi unguwa guda.4 ********* Da gudu ta banko kofar ta shigo tana haki. “Momi! Momi!! Ke kam mun ga ta kan mu, ba ki san me yake faruwa ba, gidan Baffa… Gobara a gidan Baffa…” Nan ne ta tsaya tana shinshine-shinshine. “Yau meke faruwa Momi? Gidan nan ma yana konewa.” Nan ta shiga dudduba inda hayakin yake. Ihu ta bude baki za ta zunduma, don a kawo masu agaji. Da sauri Hajiya Atika ta toshe mata baki. “Ke kin faye shirme, ba wuta bace ke ci, ni ce na ke warin hayakin.” Da sauri cikin rudu da zare idanu, ta shiga leka uwar, don ta ga inda take konewar. “Momi ke ma kin kone?”2 “A’a, wawiya, ba ni bace na kone, ni na cinna wutar”.6 Bude baki ta yi da idanu. “Momi kin shiga uku, ke ki ka kona gidan Baffa? Yaya za ki yi, idan Abba ya dawo, kin ga ta kanki.”11 Sai a lokacin Hajiya Atika ta yi tunanin abin da zai je ya komo, amma lokacin da take aikata son ranta fushi da zuciya, sun riga sun rufe mata idanu, tabbas ta san idan Likita ya dawo gidan nan nata ya same ta, koma dai menene, gwamma da ta nunawa Mama ita ma ba kanwar lasa bace. “Ke ni kin cika ni da surutu, bace ki ba ni wuri, ko zan samu na watsa ruwa na canza kayan jiki na.” Rai a cunkushe Rumaysah ta bar dakin Momi. Dakinta ta tafi da gudu ta tsaya gaban makeken windon dakin ta da yake kallon babbakakken kicin din Mama. “Oh, ko yaushe Mama da Momi za su daina wannan muguwar gabar, sai Allah.”2 *********** “Wallahi Mama ku bar ni yau sai na je na gwadawa matar nan matsayinta a gidan nan, ai abin nata ya zamo hauka. Yaya za ta saka miki wuta a gida, bayan ta san da mutane a ciki? Wannan wace irin masifa ce? Yau sai na nuna mata ba ta da wayau.” Da sauri Hajiya Sogiji ta-ce. “Assha! Idan aka yi haka kuma meye maraban mu da ita kenan? Ya zamo ba mu da bambanci, tunda ita ta nuna ga yadda take so ayi zaman, shi kenan kowa ya yi sabgar gabansa, wataran sai labari.” Fawzaan ya fusata. “Mama kullum haka ki ke fadi, tun muna yara, amma har yau ba ta sauya zani ba, yau ko Baffa aure ya yi, iyaka gaban da matar za ta yi da ke kenan. Ni na rasa Abba da Baffa wane irin soyayya suke yi wa juna. Da duk da wannan bala’in sun kasa raba gida, sun nace sai sun zauna kusa da juna. Ni dai bari yau Baffa ya dawo gidan nan, ko ya canza miki gida ko kuwa na daukeki anan, don ba zai yiwu akan idon mu a cutar mana da ke ba. Haba ai abin nata ya kai intaha.” Murmushi ta yi kawai, saboda ta riga ta san ba canza gida ba, ko me za ayi, kiyayyar da Atika take gwada mata, da kyar idan mai karewa ne.4 *********** Alhaji Attahiru Dan-Sadau shahararren manomi ne, tun a zamanin da, wanda ya kai yankin da yake da ma kewayensa, duk suna amfani da kayayyakin amfanin gonarsa. Yana da matan aure biyu, wadanda da ikon Allah suna zaune lafiya, sun haifa masa yara mata dukkansu, kamar hadin baki, sai ko wacce ta rufe haihuwarta Da da namiji. Lamido shi ne babba, yana bawa Umar shekaru biyar a haife, amma duk da haka shakuwa ce ta daban a tsakanin su. Ga shi dai ba za ka gane wai wancan dan dakin wance bace, domin suna kaunar junan su matuka. STORY CONTINUES BELOW Yaya Shatu ce babba, tana aure a Kaduna. Yaya Hansai da Yaya Zainab kuwa suna Dan-Sadau, sai Yaya Uwa. (Fatima), ita kuma tana aure a Kano, ko wacce tana da nata zuri’ar. Allah ya albarkaci ‘ya’yansa. Alhaji Lamido ilimin noma ya karanta, shi kuma Alhaji Umar Likitanci. Allah ya yi mahaifinsu mai son ilimi sosai, don haka ya tsaya sosai don su same shi. Sai dai kafin su bunkasa, su zama abubuwa na alfahari iyayensu sun gushe. Wannan shakuwar dake tsakaninsu ne, ta sanya suka zabi daura aure a rana guda. Alhaji Lamido cikin Dan-Sadau ya samu mata, yayin da Umar kuma ‘yar cikin Gusau. Sai dai a rashin sanin su, wannan dalili ne zai yi sanadin cinnawa gidajensu wuta, domin kuwa suna angwancewa da sati biyu, bala’i ya dira a gidan. Kuma Atika matar Likita ita-ce sila. Domin a cewarta ita aka riga kawowa gidan, ta girmi Sogiji ta fi ta ilimi, ta fito daga babban gida, don me ya sa za a ce ita-ce babba? Don kawai tana auren Alhaji Lamido?3 Sannan ita da iliminta aka auro ta, don asali ma a jami’a suka hadu da Dr. Umar har suka yi aure, ita cikakkiyar Lauya ce. Gori da wulaqanci iri-iri, ba wanda ba ta mata, amma duka ta shanye. Wata rana abin ya dameta, ta samu Mai-gidanta da bukatar ci-gaba da karatu, tunda dama ta yi Sakandire.3 “Sogiji kar ki biyewa shirmen Atika, ki rabu da ita, wai me ki ka nema, ki ka rasa a cikin gidan nan? Duk wasu bukatunki, ni na dauke miki nauyinsu, ki fada kawai sai ayi miki su.” Haka ta hakura, amma daga karshe da abin Atika ya soma yawa, dole ta sa Alhaji Lamido ya sama mata gurbi a makarantar (Midwifery). Sai dai kash! Farawanta ke da wuya, laulayin ciki ya sa ta a gaba, dole ta tattara karatun ta watsar, ai shi kenan sabuwa, ko ta samu sai dai ba su hadu ba. “An fada miki daman karatun na dakikai ne masu tosasshen kwakwalwa? Ai na gaba ya yi gaba.” Wasu lokutan haka Sogiji za ta biye mata, su yi ta yi. Sai mazan sun dawo, ayi shari’a, daga baya ta gaji, ta hakura, don ta gama gane Atika mafadaciya ce ta karshe.5 Ba abinda yake gabanta, sai aikinta (Career) kawai, don haka haihuwar ma baya gabanta tukun, sai da Sogiji ta haifi yara uku, sannan ne ta samu cikin ta na farko. Ganin kullum Likita yana dawowa daga asibiti, bangaren Yaya Lamido yake tarewa wurin yara, hakan ya sa ta fuskanci shi ma yana son yaran, kawai magana ne baya yi. Yaran Hajiya Sogiji shida. Fawzaan shi ne babba, sai Bilaal, Sajjad, Sajeeda, Munira sai kuma dan auta Aasim.14 Umar kuma yaransa biyar da Atika Raa’id ne babba, sai Khadija, Khamsa’u Radiyya sai Rumaysah kuma auta. Gabaki daya sunayen yaran gidan Dr. Umar ke zaba kasancewarsa dan gaye, a cewarsa yaransu kyawawa, suna mai dadi za a sa masu. Banbancin Dr. Umar da Alhaji Lamido, shi ne Allah ya yi masa son yaransa sosai, kuma baya boyewa, duk da ya kan hada duka yaran ya masu abu, idan ya tashi, amma baya boye irin shakuwarsa da yaransa da kuma son da yake masu matuka, musamman Rumaysah kasancewarta auta. A cikin shekarun mazajen, sun samu ci-gaba sosai, domin Alhaji Lamido ya rike mukamin babban sakatare na ma’aikatr gona ta jiha, ya rike wasu mukaman kafin nan ya tako mukamin Minista ta wannan ma’aikatar a kasa. Yanzu ya fi karkatar da hankalinsa kan katafaren gonarsa da ta kunshi noma na abinci da kuma kiwon dabbobi, sosai ya karbe shi, don har (Factory) yake da shi, inda ake sarrafa kayan amafanin gonar tasa. Dr. Umar kuwa yanzu asibiti yake da shi na kashin kansa a cikin babban birnin tarayya. (Abuja), wanda yake da kayan aiki sosai da kwararrun likitoci. Duk da yanayin ayyukansu, wannan baya hana su kasancewa tare a koda yaushe su yi shawara, su kuma tattauna al’amuran rayuwarsu. Yayunsu mata ko kafin su fadi damuwarsu ma, sun wadata su da komai. Wani rafsheshen gida suka kera a (Life Camp), wanda ya kunshi gidajen sama guda biyu, komai na ciki iri daya ne, ko wane gida ya kunshi dakuna takwas da falo hudu, kicin wurin cin abinci da dakin karatu. STORY CONTINUES BELOW Ta baya kuma flats ne, masu dakuna bibbiyu guda hudu na ‘ya’yansu maza. An kawata gidan da lambuna masu kyau da bi-shiyoyi, gwanin sha’awa. Ko wane gida yana kawace da lambuna masu kyawun gani da furanni.4 Ga wurin adana motoci a kowane bangare na gidan. Sai dai tun wani lokaci, su Radiyya suna yara, sai ga Momi ta shigo gidan Baffa rike da goshin Radiyya duk jina-jina. “Ina yake? Yau sai na ga Uban da ya daure maka gindi, kai mata wannan danyan aiki, ji fa an burmawa yarinya goshi, jini sai kwarara yake yi?” Jin hayaniyarta ce, ya sa Hajiya Sogiji fitowa falon farko. “Don an ga yarinya kyakkyawa son kowa, kin wanda ya rasa.2 hi ne za a mata lahani ai mata tabo a jiki ko? Ina Aasim din yake? Yau sai na ji dalili. Wallahi kai ma ka kawo goshinka na rama mata. Yo ko uwarka ce ta ji mata ciwo, sai na rama mata bare kai dan karamin yaro, mai dan karen rashin ji.”9 “Wai ke wane irin rashin hankali ne ke damunki? Ko jahila wacce ba ta taba zama a aji ba, ba za ta aikata abin da ki ke yi ba, a haka ki ke tunkaho ke mai shari’a ce, da zan ga wanda suke daukar ki, su biyaki, don su sa ma masu adalci da na hana, don kuwa asarar kudinsu suke yi kawai”. “Oho dai, dan bakin-ciki sai dai ya mutu, na gaba ya riga ya yi gaba.” Baffa ne ya ji hayaniya ya shigo falon, ya samu abinda ke faruwa. “Duba, Atika ki yi hakuri, ina ga da kin je, an kula da ciwon nata kar ya yi tsami, har wata cuta ta shiga. Ni da kaina zan sabawa Aasim”. Ya dubi yaron da ke labe a jikin Mama ya-ce. “Wane irin abu ne za ka je ka ji wa Radiyya ciwo haka ake wasan? Ka koyi rashin ji ko? Zan saba maka, idan ka sake dama.” Cikin kuka yaron ya-ce. “Baffa fa ba ni na ji mata ciwon ba, fadowa ta yi daga kan bencin da muke (Lesson) a gareji.” Mama ta yi caraf! Ta-ce “Oh, ashe ma, ba abinda yaro ya yi za a zo ana tada mana jijiyoyin wuya.” Haushi ya cika Hajiya Atika, cikin kora kunya ta sa hannu ta zungure kan Aasim. “Munafukin yaro, wato ka ga Baffanka shi ne za ka sharta karya ko? Da wasu idanunka a wurin kamar an soya gujiya, ba abin da ka iya, sai kiriniya.” Ta sa hannu ta kara kaiwa za ta dungure shi. Mama ta buge hannun, sai kawai Momi ta kai hannu za ta mari Mama. Baffa ya daka mata tsawa ya-ce. “Ke fice ki wuce gidanki, wane irin shirme ne haka?” Jikinta a mace ta fice cikin fushi, ai kuwa Abba na dawowa. Ta fada masa abin da ya faru, ganin ya basar, saboda sanin fitinarta ne, ya sa har ta yi kari. Baffa kuwa sai cewa ya yi, “Na fice masa daga gida, kar ya kara ganin mu a gidan sa, daga yau ba shi, ba mu.”2 Zuciya ya kwashi Dr. Umar, bai yi wani bincike ba, washegari kawai sai suka ga ana tono. Baffa na tambayar ma’aikatan, sai cewa suka yi. “Likita ne ya sa a gina katanga.”2 Ran Alhaji Lamido ya baci kwarai, har asibiti ya kama Abba. “Amma lallai Umaru ka ba ni mamaki, ashe tsakanina da kai har mace za ta iya shiga tsakani, ka yi hukunci ba tunani, ba bin diddigin menene gaskiyar al’amari? Ashe haka ne iya son da Baba ya gwada mana mu yiwa juna? Tabbas ban ji dadin abin da ka yi ba gaskiya.” “A’a ba haka bane Yaya, ni dai kawai ina ga hakan ya fi, ka ga tunda yanzu ga Katanga, duk wacce ta tsallake ta shiga sashin wata da neman fada, to laifinta ne, sai a hukunta ta.” Baffa ya dube shi kasake, jiki a mace ya bar masa ofis dinsa, a takaice dai wannan sulhun sai da su Yaya Shatu suka shiga ciki, sannan Yaya da Kanin suka koma kamar da. Amma dai ga rusheshen Katanga, mai makeken gate a tsakanin gidajen na su, har yau ba a rusa ba. Alhaji Lamido idan ya tashi, gaba daya yaran yake hadawa ya yi wa kaya irin na su sallah da sauransu, amma fa da zarar an kai Momi, za ta fara sababi. “Ji don Allah, wasu local kaya, ba a iya zabe ba, dole ne, to sai an saya?” STORY CONTINUES BELOW Haka za ta yarda kayan, labari yana komawa kunnen Mama, amma bata ce komai ba, gudun kar Mai-gidan ya-ce tana hana shi abin alkahiri, na karshen dai a gaban dan aikan ta cinnawa kayan wuta, don haka Mama ta-ce. “Ba dole, an daina wannan abin, kowa ubansa yai masa, ba shi kenan ba.”4 Yaransu kuwa kowa na sabgar gabansa, musamman yaran Hajiya Atika da kunya ba ta gama isarsu ba, don sai su hadu da Mama, su banke ta, ba su san su gaisheta ba kuma.4 Fawzaan da Ra’id ne kawai na su ya zo daya, saboda ba ruwansa da shirmen sauran sai dai shi matsalarsa daya, baya son karatu, hakan ya sa Fawzaan ya ja shi a jiki yana nuna masa muhimmancin ilimi a rayuwa. Ko da Fawzan ya tashi tafiya UK karatu, sai da ya sake jaddada masa, domin lokacin yana karamar (Secondary). Fawzaan ya tafi Cambridge inda ya karanci (International Law), ya shafe kusan shekaru hudu acan, don sai da ya yi (English Bar Finals), dinsa sannan ya dawo Najeriya, inda ya yi (Law School) dinsa. Wata shida ya dauka wajen yin (Bar Part One) dinsa, sannan ya jona sauran masu yin (Law School), da suka yi karatunsu a gida, suka yi bar (Part 2). A halin yanzu shekarar sa biyar yana aiki da (United Nations).2 Sannan kuma a lokacin da yake da sarari, yana aikin bada shawara. (Consultancy), ga kamfanonin da suke harkar saye da sayarwa ciki da wajen kasar nan, wato (International Trade). Ba abinda ya ke daga masa hankali, irin yadda tun tafiyarsa har ya dawo ya zo ya samu iyayensa jiya, i yau. Ranar asabar ya zo gidan gaida iyayensa ne, ya tadda motocin (Fire Service) na fita daga gidansu. Nan ya samu labarin abinda ya faru, ransa ya yi matukar baci. “Ai wannan hauka ne, dole a dau mataki.” ******** “Wai nace ki na kwaya ne? Wane irin rashin hankali ne wannan? Za ki janyo gobara a gidan mutane da gangan, ashe za ki iya kisa kenan?” Momi dai ba abinda take yi, sai wuri-wuri da idanu. Ta gama tsorata, don daman ta san muddin Abba ya dawo, to za ta sha fada. “Iye mana za ki iya kisa, tunda ki na sane da jama’a a gidan, ki ka kunna gas kuma ki ka cinna ashana, wane irin rashin imani ne hakan?” Gyara zama ta yi tana tsuma. “Tashi mu je, ki ba su hakuri”. Lokacin ne Momi ta zabura “Tabdi! Nan ma kicin din na babbaka, ba duka gidan ba, haka kawai, ga dana ko kwakkwarar motsi baya yi, sai a zo ana cewa ni zan bada hakuri?” “Kin wuce ko kuma sai na tsitsinka miki mari? Ba na son shegantaka.”1 Haka ya sa ta a gaba, tana tuttura baki. Ran nan a murtuke, kamar an sa ta kwashe kashi. Ta iso daidai kofa ne. Mama ta hangota ta windo, da sauri ta mike ta isa. “Ke dakata ina ki ke tunanin za ki shiga? Ai ke da shiga gidana kam ya kare, don mu ba mu son neman fitina”. Ganin Abba da ta yi ne, ya sa ta koma ta zauna, sai ga Baffa ya fito, dukansu suka yi tsuru-tsuru, hankalin Momi bai gama kadewa, ya yi mummunar tashi ba, sai da ta ganta ta shigo falon, yau kam ta san kashinta ya bushe, tunda ko Yaya Shatu ta tako kafa ta zo, domin a yi shari’a, domin idan akwai wanda ba ta son shiga harkarsa, to Yaya Shatu ce, domin duk masifarta, to Yaya Shatu ta takata ta shanye. Ga shi daman ta tsaneta, ta san Sogiji za ta bawa gaskiya.3 Nan da nan duka suka russuna suka kwashi gaisuwa. Baffa ne ya zayyano duk abinda yake faruwa. Yaya Shatu ta dubi inda Momi take takure ta-ce. “Yo ba ki zuwa ki karbi aron Bomb ki dana maku, duka ku mutu kowa ya huta?”15 Makut Momi ta hadiyi wani abu. Abba ya yi caraf! Ya-ce. “Yaya Shatu, ai yanzu ma hakuri ta zo bawa Sogiji. Insha-Allahu hakan ba za ta kuma faruwa ba. Ayi hakuri”. “Kai don Allah kai min shiru, duk wa ya daure mata gindi take iya shegen da take yi? Yaya za ayi mutum kamarka, ba zai iya ladabtar da matarsa ba, sai abin da ta ga dama za ta yi.1 STORY CONTINUES BELOW Ke kuma ki na nan, baki kamar ramin asusu, ana magana kin yi mut! Idan bala’i ne ko ke ce kan gaba. Tunda kin gaji ne, sai ki koma inda aka dauko ki, don mu ba mu gaji masifa ba bare bala’i.”7 Ta dubi Abba sannan ta-ci-gaba. “Umaru dauki takarda da biro ka sallameta, ta tafi inda ta fito. Ka saketa nace, ta kara gaba can”. Nan da nan idon Momi ya raina fata sai ga ta kan gwiwarta tana kuka. “Don Allah Likita ka yi hakuri. Yaya Shatu Allah ba zan sake ba, sharrin shaidan ne, ku yi hakuri. Sogiji zan biyaki duk asarar da nai miki Insha-Allahu, na tuba ba zan sake ba.” Nan ta karya wuya, ga shi ta iya abin tausayi. Watau kyawan ce mai kwanciyar daukar rai. “Likita kai ma ka san yadda na ke son ka, yaya za ayi na rayu, ba kai? Ka taimaka kar ka daga ni kan ‘ya’yana”.7 Yaya Shatu ta harzuka. “Don Allah rufe mana baki, ki na son shi, ki ke gaba da ‘Yan-uwansa da danginsa har ki ke iya babbaka masa gidan Dan-uwa? Umaru wai ba ka ji ni bane?” Sai da Baffa ya sa baki. Yaya Shatu ta bar maganar sakin da kyar da sudin goshi. Nan gidan Baffa aka shirya mata dakin da idan ta zo take sauka, na musamman. Tana kwance akan gadonta, sai haki take yi, domin kuwa yau ta sha da kyar, ta kasa yarda wai yau saura kiris! Aurenta ya guntule. Duk duniya ba abinda take so, irin Likita. Hakan ya sa duk tsiyarta ba ta tabo shi, sai dai ta sauke kan Sogiji, tunda ko Yaya Shatu ta sa baki, to ba ta da wani zaman lafiyar da ya wuci ta natsu ta yiwa kanta fada, ta ja bakinta kuma.2 ********** Kallon sa suke yi tamkar ya ba su labarin irin wani abin tsoron nan, suka hada baki suka ce “Abba za ta kashe mu.” Ya dube su da daddaya ya-ce. “Oh, abin naku ya kai har ‘Yan-uwana za ku wulaqanta? Ba dole tai maku koma meye ne ba, ace yau kawanan ta hudu a gari, amma ba ku je kun gaishe ta ba. Dole tai maku ko ma meye ne. Momin naku tana kallo ta bar ku ai.” Khamsa’u ce ta-ce. “Abba yanzu za ta balbale mu, sannan sai mun shiga wancan gidan, ana yi mana gani-gani?”2 “Gidan Baffan ne ake maku gani-gani? Ku tashi ku wuce, tun kafin na yi maganinku.” Nan suka fice daga falon, kowacce jiki na bari, cikin dari-dari suka shiga gidan, don tunanin abin da za su tarar, don su dai ba a shigo masu, sai sun ji dalili. Don haka kai tsaye dakin da take sauka, idan ta zo suka wuce. Suna shiga, suka samu tana ta kyalkyalan dariya da su Sajeeda da Muneerah. Nan suka zube suka kwashi gaisuwa, amma haka Goggo Shatu ta share su. Sai da Sajeeda ta-ce. “Goggo ana gaishe ki”. “Bar su, na ji su sarai, sai yanzu aka zare masu jinin sarautar a jikinsu? Sai yau suka san ina gari?”1 Rumaysah ta yi caraf! Ta-ce. “Ki yi hakuri Goggo Shatu, sai dazu Abba ya-ce mana ki nanan.” ‘Yan-uwan duk suka zubo mata, ido yadda ta sharto karya ta labta, ta kanne masu ido. Goggo Shatu ta juyo ta amsa sama-sama. Nan ne Rumaysah ta tashi da sauri ta dare kan gadon tana cewa. “Matsa Yaya Muneerah”. Ta bankadeta, ta bararraje akan gadon. Ta kama kafar Goggo Shatu ta shiga mata matsa. “Kin ga tsaya na matsa miki.” “Matsa ki ba ni wuri, ni kakar ki ce? Ba na son shegiyar rashin kunya”.1 “Kuma dai sai ka ce ba kya jin dadi, idan nai miki, dubi kafarki har fatar ta fara cukurkudewa, kin koma wankan ruwan zafi naki ko?” “Ka ji min ja’irar yarinya.” Su Radiyya kam mamaki suke yi, don duk ‘ya’yan dangi kowa tsoron Goggo Shatu yake yi, tamkar yunwan cikinsa, amma banda Rumaysah. Radiyya ko sunanta ta ji an kira, sai ta ji kamar za ta saki fitsari a wando. “Ke ma da Umarun ya hada ki duka da wadannan ya aurar, kafin ke ma ki zo ki jabe mana, ki dade kamar yadda suka yi. Banda aukin tara samari, ba abinda suka iya.” “Goggo idan banda abinki, idan ba saurayin, yaya za a samu mijin? Su kuma suna tantancewa ne, su tankade su zaba.” Da daddaya su Khadija suka watse, nan suka bar Rumaysah. “Uhn! Ke din na ga kin darje ai.” Goggo ta fada. Rumaysah ta-ce. “Yaya Muneera ki fadawa Goggo, ni ina da saurayi ne?” “A’a Goggo Rumaysah fa ba ta da saurayi, sai dai idan auren sadaqa za ai mata.” Nan ta dire ta-ce. “Tab! Auren sadaqa? Lallai da za a ga tashin hankali a gidan nan.” Nan suka sa mata dariya, don har ga Allah ta dauka da gaske suke yi. A ranta kuwa tunani ne tirim! Dangane da al’amarinta. ********** Rumaysah Umar Attahir doguwace zamu iya kiranta mai matsakaicin tsawo, fatarta wankan tarwada ne, irin mai shekin nan, wasu ko zasu kirata fara, gashi yana samun kula na musamman don haka tun daga nesa zaka ga shekin da fatarta keyi, komai nata zara zara ne, tana da diri mai daukan hankali, fuskarta kuwa na dauke da madaidaitan idanu da suka kawatu da zara-zaran gashin ido da gira mai duhu da ya kwanta kaman an zana shi a fuskarta, sumul ne babu kuraje a fuskar sai sheki da yakeyi don tsabar kula da yake samu. Labbanta jajaye (pink) madaidaitane masu laushi saboda yawan wadata su da takeyi da man baki.+ Sai dai Rumaysah akwai goshi ba laifi idan su Khans suka tashi suyi ta zolayarta sai tace musu “Ai duk kyau ne, na kashe dauri ne. sannan ilimi ne a cikinsa” hancinta dogone irin siririn nan. Tana da kwancacciyar gashi a gefen kuncinta wanda ya taho har kusa da habarta. Duk cikin su itace za a kira mai duhu don sauran kaf dinsu farare ne tas Radiyya kam ma ja za a ce mata, kasancewar sun biyo farin fatar Momi.7 Tana da murya mai zaki wanda bai santa ba idan tana magana zai rantse yanga takeyi, amma haka take. Ma’abociyar tsabtace da son kamshi don duk cikin ‘yan uwanta tafi kowa rashin ganda saboda tsabtarta baya bari tayi ganda wurin kawar da kazanta. Sannan akwai ta da faram faram da mutane da saurin shiga rai, sai dai Rumaysah sarauniyar tsiwa ce. 7 Tunda ta shiga makarantar take ta aikin raba idanu domin yau ma dai bashi ba alamarsa, gaba daya hankalinta ya ki kwanciya, babbar aminiyarta Firdausi ce ta dafa ta tana fadin “Anya, Rumaysah kina da shirin lashe jarrabawarkin nan kuwa? Dubi yanda kika damu kanki, kinki ki sa salama sam a wannan al’amarin?” Ajiyar zuciya ta sauke yayinda take takure wuri guda, idanunta sun riga sun kawo ruwa “hmm Sati shida fa kenan Firdausi, ta yaya kike tsammani na mance da shi bayan ke kin san komai a gabanki komai yake faruwa kin san irin shakuwata da Saleem, ba text ba waya ta yaya hankali na zai kwanta bayan Karima har nan ta sameni tana tambaya ta ko na san in da yake tunda baya Mubi baya Abuja.” barin hawayen tayi suka satata kan kuncinta “I miss him so much, Firdausi. Ina dariya ina wasa, ina tsokana ba don komai ba sai don na koma kamar normal, na cire damuwa a raina amma kullum ni na san yanda nake ji a raina.” Firdausi ta tausaya wa Rumaysah kwarai don ba ita kadai ba hatta ‘yan ajinsu shaida ne kan irin soyayyarta da Saleem, gashi rana tsaka an neme shi an rasa. “Ki daure dai ki yi karatu saboda kinga test ne a gaban mu.” Kai kawai ta gyada mata. Tana tuna farkon haduwarta da Saleem, suna zaune a lecture hall 1 ita da Firdausi suna karatu. Domin nan ne gurin zaman su suyi dan nazari duk lokacin da suka samu sarari kafin su koma gida. Sanye take da wata doguwar riga mai ruwan daurawa a jikinta, sai siririn gyale a kanta, sunyi nisa wurin yin nazari ne sai suka ji an musu sallama. Daga idanun da zatayi suka hado idanu yace “Don Allah akwai wanda yake zaune a nan ne?” Kada masa kai sukayi dukan su biyu, murmushi yayi sannan ya zauna. Rumaysah tayi kasa da murya tace “Ko ba komai idan ka zauna a nan zaka hana wadancan masu kawo mana harin damun mu.” STORY CONTINUES BELOW Murmushi ya sake yi ya ci gaba da abun da ya kawo shi. Har lokacin da ya gama sukayi sallama kowa ya kama gaban shi. Suna fitowa Firdausi ta sa dariya tace “Ho, Rumaysah duk fadin lecture hall din nan ya rasa inda zai zauna sai kusa da ke?” “Ke fa kin faye shirme, meye ne don kawai mutum ya zauna a gefen mu shine wani abu?” “To shi kenan nayi shiru.” “Zamu nemi Naja’ah din ne ko mu tafi?” “kai yanzu kam na gaji sai dai gobe idan Allah ya kaimu.” Washegari bayan sun gama lectures, basu tafi gida ba nan wurin karatunsu na kullum suka nufa, can suka same shi ya kama musu wurin zama. Firdausi ta dan taba Rumaysah ta kashe mata idanu. Murmushi ta masa tace “Ina wuni?” “Lafiya, kun samu fitowa?” Firdausi ce ta amsa sannan suka masa godiya suka zauna, shi kenan daga wannan ranar duk wanda ya riga zuwa sai ya kamawa danuwansa sunyi abokin karatu. Haka suka kasance kusan sati biyu amma basu taba sanin sunan shi ba. Kwatsam sai ranar suka fito shiru har lokacin tafiyar su bai zo ba. Abun ya damu Rumaysah, haka washegari, tun tana shiru har ranar tacewa Firdausi. “Ni kam gaskiya abun nan ya dameni, lafiya har yau bai zo ba? kodai wani abun ne ya same shi?” Naja’ah da Firdausi suka tafa game da fadin “ko dai?” “wallahi ba haka bane, ba dadi ace muna zaune da mutum ana mutumci sannan mu kwana biyu bamu ganshi ba sannan mu ki nuna kulawarmu ai ina ga hakan bai dace ba.” “Haka ne kam, to Allah dai ya sa lafiya.” Firdausi ta fada. Suna fitowa daga wurin karatu kawai sai ta hangoshi a tsaye abokanshi sun zagaye shi, ana ta dariya suna hira. Sai taga wani abokinsa Umar tace “Don Allah, lafiya dai kwana biyu naga abokin kan can baya zuwa makaranta?” “Oh, Saleem ne? Wallahi ya dan kwanta ne ba lafiya shi yasa amma yanzu ya warware.” Nan tayiwa Umar godiya, kaman wacce aka sakata ba radin kanta ba ji tayi kawai kafafunta sun kwasheta zuwa cikin su Saleem da abokansa, sallama ta musu. Duka suka amsa kai tsaye ta dubi Saleem tace “Saleem, ashe kuma baka ji dadi ba kwanakin nan?” “Eh wallahi.” “Ayya Allah ya karo ahuwa.” Tana gama gaishe shi ta juya ta tafi. Wai ranar Saleem bai yi bacci ba tsabar murna. “Ashe dai nima ta damu dani, tunda har ta damu da kwanakin da na dauka bana nan, tabbas itama tayi kewata kaman yanda kewarta ta addabeni.” SAleem Abubakar Maccido cikakken bafulatanin jihar Adamawa ne dan usuli, dogo ne sosai sannan fari sol dashi, dan gaye ne matuka ga son tsabta. Maganarsa da sauri sauri yakeyi, sannan yana dan in-ina ga zuciya don idan ransa ya baci har bari yakeyi tsabar zuciya. Iyayensa a cikin Abuja suke, amma mahaifiyarsa Maami tafi zama a Mubi. Dukkansu a remedials suke lokacin don haka suna yawan haduwa amma wurin karatu, don daga sun gama karatu Rumaysah ke fadawa motarta tayi gida.3 Al’amarin su irin gamon jinin nan ne domin kuwa nan da nan Rumaysah da Saleem suka saba, musamman da yayi rashin lafiyar nan wata shakuwa ta shiga tsakaninsu. Kullum da yamma suke karatunsu a lecture hall. Firdausi ce abokiyar zamansu. Ko wani lokaci idan suka zauna karatu rabin hankalin Saleem na kan Rumaysah yana son ya san abubuwa da dama a game da ita, saboda tana matukar burgeshi. Ita kuwa Rumaysah ta kula da wani abu guda, kullum idan suna karatu Saleem sai ya tambayeta lokaci. Yawanci sai sun kusa tashi yake haka, kusan sau uku yana mata haka sai ranar tace “Wai ni na tambayeka, kai baka da agogone?” Dariya yayi yace “ina da shi mana, me kika gani?” “Naga ne kullum sai ka tambayeni lokaci, sannan ma tukun me kake fita kake yi a wanann lokacin?”1 STORY CONTINUES BELOW “Kina so ki san meye nake yi?” Rumaysah cikin zakuwa tace “Eh, ina son na sani.” Yana murmushi yace “To shi kenan ki bari sai gobe zan fada miki.” Ina hankalin Rumaysah ya gagara kwanciya Allah-Allah take safiya tayi domin taga meye ne. Duk da ta san sai da yamma zasu hadu da Saleem. Washegari suna karatu, kaman tace masa ya nuna mata amma dai ta daure tayi hakuri, lokaci nayi yace “Ki tashi mu tafi.” gaba daya takardunsu ta jibgawa Firdausi sannan ta bishi suka fita. Suna fita ya samu wani wurin zama sai ta ga ya fito da wayarsa (smartphone) ya bude, hoton india taga ya dallaro ya cika screen din. Dariya ta kwashe dashi tace “I can’t believe it Saleem, yanzu daman kana kallon India?” Kallonta yakeyi baki bude,”Yanzu kar dai kice min baki san dadin sa ba?” “Tab ni dai ban ga abun so ba.” “To shi kenan, ki tsaya ki gani, sai ki bada ra’ayinki” Ya kunna musu, wani series ne na Abha da Karan. Ai kafin minti talatin su cika Rumaysah ta fara Allah- Allah ta ga na gobe mai zai faru don nan take taji sun burgeta.6 “Ba na fada miki ba?” Dariya tayi sannan ta koma dauko littafanta, tun daga wannan ranar sammako takeyi da safe suyi karatu, da yamma kuma su taba karatu su taba kallo. Ta dalilin haka har Rumaysah ta gano Saleem mayen karatune irinta, don yana karance-karance sosai, duk kusan littafan (James Hardley chase) ya karantasu, yayinda ita kuma ta karanta kadan wanda bata karanta ba haka zai zauna ya bata labari tamkar ita take karantawa, don ya iya bada labari ita kuma ta iya saurare. A irin haka ne Firdause tace “Hmm, ni dai ban gane irin wannan abun ba idan ba soyayya ba menene?”7 “Sai kiyi ai tunda ni dai na gaji da fada miki iya gaskiyata, to idan soyayan nakeyi sai na boye miki? Ba wani abu tsakanina da Saleem sai mutumci da abota.”Haka Firdausi ta rabu da ita. Ranar suna zaune a love garden suna jiran lectures, sai ga Saleem dama yayi waya yaji inda suke, yana zuwa yace “tashi ki rakani shago.” Ba musu ta mike suna tafe suna tadi har suka isa, nan ya saya mata pop corn, domin idan akwai abunda Rumaisa take so to yana bayan pop corn ya hada ya saya mata da wasu cakes masu shape din zuciya. Bayan ya sayi abun da yake so ne, suka tako har inda suka bar su Firdausi, yana juyawa ta fito da snacks din da Saleem ya saya mata ai suna ganin cake din Naja’ah tace “To Firdausi kin ga abu ya fara tsami, har zuciya ya saya mata ya bata kyautar zuciyarsa kenan.”6 Haba nan suka sakata a gaba da tsiya, duk wannan abun da yake faruwa Rumaysah bata taba tadawa kowa a gidansu tayi aboki ba, hatta kuwa Abba dan hannun damanta. Sam Rumaysah bata san mahaifin Saleem wani babban mutum bane a Adamawa, kullum idan ya ambaci sunan shi sai tace “waye wannan?” Tun yana dauka tsiya takeyi har ya san hakikanin gaskiyarta kenan bata san waye mahaifinsa ba. “Baki san shi ba?” “Allah da gaske nakeyi.” “To shikenan ki binciki littafin current affairs dinki.” Kullum inda kaga Saleem nan za a samu Rumaysah sai idan sunzo tafiya suke rabuwa don wataran hatta wurin lectures makale mata yakeyi baya son yawan kallon da ‘yan ajin suke yiwa Rumaysa don tsakaninsa da Allah shi ya kamu da son Rumaysah Umar, ita kuwa bata san yana yi ba don har ga Allah aboki ta daukeshi a tunaninta.4 Ranar kawai sai ga Umar abokinsa “Babana yau yaya na ganka kai kadai? Ina abokan naka?” “Ke dai kice ina abokina? Naga sai rarraba idanu kikeyi kina nemanshi.” “Haba dai sai kace wata yarinya, me zai min idan na ganshi?” “Ni daughter sai kike ban mamaki kina ta gara mana aboki, kin ki ki dau haske.” STORY CONTINUES BELOW Abun ya bawa Rumaysah mamaki tace “wani irin haske kuma zan dauka?” “Yanzu duk kina nufin kice baki san Saleem yana mutuwar sonki ba?” Dariya yasa ta yi sosai sannan tace “Dadina da kai zolayar tsiya, naga dai ba sunan Attahir ne da kai ba bare nace kana mun wasan kakanni” “Allah, baki yarda ba ko? To shi kenan ni kuwa zan samo miki proof” Haka suka rabu ta kwana tunanin maganar Umar, ai kuwa washegari sai gashi ya sato notepad din Saleem, gaba daya ciki maganganu ne irin na AL’AMARIN ZUCI da Saleem ke fuskanta a dominta. Zama tayi ta karance su tsab. Kaf ciki ba wanda yafi tsaya mata a rai irin (‘She’s playing games with my heart’).1 Tun daga ranar idan suna tare sai take jin nauyin Saleem, da wani annashuwa suna shigarta, suna tafe yana rakata wurin da ta ajiye motarta ne yace mata “Rumy, wai menene dangantakarmu? Wani matsayi kika daukeni?” Tambayar ta girgizata amma ta daure tace “Aboki mana.” A take fuskarsa ta sauya “Aboki?” yana fadan haka yayi gaba ya barta a baya sai da ya kusa isa wurin motar ya juyo ya dawo gareta daf ita ya tsaya har sai da ta tsaya cak, kamshin turarensa kuwa tamkar ita ta shafa saboda inda ya tsaya “To ni ba haka na daukeki ba Rumy, kin wuce kawa a wurina, sosai da sosai ma kuwa, in fact i’m in love with you”3 A take a nan Rumaysah ta tsaya cak saboda rashin sanin abun fadi, domin ita hakikanin gaskiya bata taba soyayya ba. sai dai ta san yana burgeta, yana kuma sata dariya da annashuwa watakila wannan ne so? Rumaysah ta gagara amincewa Soyayya ce don haka ta samu Firdausi a dakin su Naja’ah dake offcamp. “Fiddy, don Allah me ake ji idan kana son mutum?” Firdausi ta dubi yanda Rumaysah duk tabi ta daburce sai wasa takeyi da yatsunta fuskarta ko tamkar zata yi kuka don kidima.2 “Relax, abun bayi da wuya har can fa, Kina son kasancewa dashi?” RUmaysah tayi shiru tana tuna irin yanda take kasancewa cikin kunci muddin weekend yazo ba abun da take so sai monday yayi ta shiga school su hadu don haka ta gyada mata kai. Firdausi tace “yana saki farin ciki? ya kawar miki da damuwa?” Da sauri Rumaysah tace “Eh.” “To albishir kawata, kema kina sonshi.” Shi kenan tun daga wannan lokaci kuwa babu kama hannun yaro a lamarin Rumaysah da Saleem, soyayya tukuru suke narka suna sha. Ta fadi warwas, kasancewar Saleem ya shigeta a hankali don haka ba karamin zurfi ta shiga dashi ba. Sun saba sosai domin hatta matsalolin da yake fuskanta a gida yakan fada mata su. Ita kuwa Rumaysah haka zata takarkare ta bashi shawara, abun nasu gwanin ban sha’awa. Kullum da safe suke karatu kan a fara lectures da yamma kuwa su sha hirarsu, wannan yasa Rumaysah take ALlah-Allah ta isa makaranta. Ranar tana sauri ta sauko ta samu su Abba da Momi suna shirin fita tace “Yau kam na riga ku.” Abba yace “Ai na ga kwanan nan akwai ki da kwazon zuwa makaranta da wuri, baby. Allah ya bada sa’a” Murmushi tayi Abba bai san me yake kaita da wuri ba.5 Yawanci a weekend sukan tafi Picnic ko a cikin makaranta ko kuwa a waje da abokansu da kawaye, ranar Rumaysa ce ta shirya musu a Jabi lake su biyu kawai, suna zaune suna karanta wani novel, suka iso wani wuri sai duka suka saka dariya, Saleem yayi shiru yana mata kallo na daban. Ta hure mishi idanu “Meye?” “Babu, kawai dai ina tunanin abu guda ne, yor are too romantic ina duba ta yanda za ayi ki fara karatun Statistics ne, wanda kuwa lissafi yana da yawa a ciki.” “Hmm ba ka san ni ba ko? Zan iya in sha ALlah.” “Ni ko na sanki, Laila a soyayya, Mango Park sarkin naci, Albert Einstein a kwakwalwa.” Sukayi dariya gaba daya.1 STORY CONTINUES BELOW Kullum kara shakuwa sukeyi har lokacin zana jarrabawarsu ta zo, sai dai ana saura sati biyu su fara jarrabawa wani irin zazzafar zazzabi ya kama Rumaysah don har bata zuwa makaranta. Wannan yasa musamman Saleem ya nemi address din su da ta taba bashi sai gashi a gidan Abba, ta nuna wa ‘yan gidansu abokin karatunta ne hatta Abba bata fada masa ba, bayan ya gaisheta washegari sai gashi shida Firdausi, tun daga nan kullum gidansu Rumaysah suke zuwa karatu, haka zai ajiye nashi har sai ta gane. Ranar tace masa “anya kuwa zan iya jarrabawar nan?” Saleem ya tsume yace “Meye hakan kuma? Idan Einstien bata iya ba su mu 007 kuma fa sai muyi yaya? Bana so ki zama kin karaya ki daure, in sha Allah zamu tsallake kuma kowa ya samu abun da yake so.” Murmushi Rumaysah tayi. A haka har ta koma makaranta suka zana jarrabawarsu. Sun gama jarrabawa sai dai a nan akeyinta domin Rumaysah ta takarkare ta bata rai kamar karamar yarinya “Yanzu Saleem tafiya zakayi har Mubi bazan na ganin ka ba?”1 “haba, Rumy kar ki sa damuwa kaman gobe ne zaki ga na dawo in sha Allah. ki kula min da kanki.” “Da su Maami zaku tafi?” “Eh, zaki mana rakiya ne? Akwai space” Juya idanu tayi hade da make masa kafada “Kai ba, Allah ya kiyaye hanya.” Ta juya ta shiga cikin gida, tabbas sunyi kewar junansu duk da kullum suna makale da waya. Suna haka har sakamako ya fito kowa an bashi kos dinsa, aka musu waya aka fada musu, sai dai fa bayan an koma makaranta domin registration Rumaysah ta samu kos din da take so sai dai Saleem bai samu ba, don haka ranshi a bace yace “Don me yasa baza su bawa mutum kos din da ya nema ba, ni idan ba computer science ba bazanyi registration din ba.” Ganin da gaske ya dage ne yasa Rumaysah ta tsorata da kyar ta lallabashi ya yarda yayi. A haka dai har aka fara lectures, haduwarsu ya dan ragu kasancewar shi Biological science yakeyi. Ranar suna zaune da su Firdausi da su Naja’ah sai gashi ya zo da su Umar, suna gaisawa yace “Rumy zo mu tafi.” Kaman me jiransa ta mike ta bi bayanshi, gefe kadan suka matsa ya miko mata wani kwali an nade shi da wrapping sheet mai kyau sosai. Ta dube shi “Wannan fa Saleem?” “Naki ne.” Ya fada hade da kashe mata ido nan taji wani dadi ya kamata taji ta kara sonshi. Haka suka shiga wata hirar bayan ya tafi ne ta koma ta samu su Firdausi, duk gulma na tsikarar su wai sai ta bude abun a gaban su. Dole dai ta bude da tafi so sai a sirri ta bude ta ga koma meye ne. Wani mulumulallen abu ne mai shape din duniya da ruwa a ciki kasan wani abun ne mai sheki sai yawo yakeyi a ruwan da wani farin abu a ciki an rubuta ‘Remember I love you’ Nan take taji bata taba samun kyautar da ta kai wannan burgeta ba. A gefe kuma wani agogone mai tsada na kamfanin Swatch hannun leather gareshi da farin fuskar silver, kwarai taji dadin wannan kyautar. Tana isa gida ranar a gefen gadonta ta ajiye, dashi take tashi a idanunta haka nan shine abu na karshe da take gani kan ta kwanta.1 Bayan kwana biyu Saleem ya samu RUmaysah “Rumy, ni fa na fara neman canjin kos. Don gaskiya ni dai kawai gani a ajine bana gane komai don ba abunda nake so aka bani ba. Don haka zan samu Daddy yayi wa registrar magana.” Haka suka rabu akan zai je gida. Da safe kawai tana tsaye da wasu coursemates dinta sai ga Saleem ya zo ransa a bace sai haki yakeyi, hannunta kawai ya fincika suka fara tafiya sun dade suna tafe bai ce mata komai ba bata tambaye shi komai ba. Sai da suka taka sosai sannan ya samu wurin zama suka zauna.2 “Lafiya Saleem me ya faru na ganka haka?” Ajiyar zuciya kawai yakeyi da kyar ta samu ya kwantar da hankalinsa sannan yace “Rumy, naje na samu Daddy kaman yanda mukayi dake, na fada masa komai game da canjin course dina, sai dai kafin yace komai kawai Anty caraf tace ai ba zancen wani canjin kos da zanyi, sai kace ita nakeyiwa karatun wai sai dai na bar makarantar da na canza course. Dama ba shiri mukeyi da ita ba, Daddy kuma sai abunda tace yakeyi. Baram baram muka rabu dasu” STORY CONTINUES BELOW RUmaysah ta tausaya masa kwarai zatayi magana ne yace “Wallahi tallahi Rumy sai dai na bar makarantar don ni bazan karanta abun da raina baya so ba.” Hankalinta ya tashi, don haka tace “Haba Saleem, kar kace zaka bar makarantar, Akan dalilin meye? Kai ka kwana da sanin Anty ba wai sonka takeyi ba, kawai tana frustrating dinka ne ka bar karatun gaba daya. Kai kuma idan ka biye mata kaga tayi nasara kenan ko? Don allah kayi hakuri, kayi karatunka wataran sai labari. Ka roki Allah ya kawo maka zabi na gari.” Da kyar ta lallaba Saleem ya yarda zai ci gaba da karatun. Rumaysah ta dauka magana ta wuce, a rashin saninta Saleem ya gama tsara plan din sa, satin da ya biyo kawai ya zo ya sameta. “Rumy tafiya ta kamani zuwa Mubi, Maami ba lafiya zan je dubo ta da jiki.” “Subhanallah, Allah ya karo sauki, don Allah ka gaishe ta. Idan ka isa sai muyi magana da ita” “To ba komai, sai na dawo.” Shi kenan ya tafi. Ashe wayo ya mata ya san idan ta san shirye-shiryen sa bazata taba amincewa ya tafi ba. Wasa-wasa Saleem ya shafe wata guda, hankuklan kowa ya tashi don sai ga kanwarsa Karima ta zo tana tambayar Rumaysah ko ta san inda yake, nan ne ta gama tsinkewa da al’amarin. ko yaushe cikin kuka zaka sameta, ta zama shiru shiru da ita, ko abokansa ta gani sai kuka, ba daman wani ya kira wani suna da yayi kama da na Saleem sai ta birkice. Ta daina bin duk inda ta san sun taba zuwa da Saleem sunyi wani abun tarihi. “Firdausi, hankalina ya tashi, tabbas ba lafiya idan ba haka ba me yasa har gidan su basu san inda yake ba?” “Haba ki kwantar da hankalinki in sha Allah komai zai zamo daidai.” “To ko waya ya min na san ko ya mutu ko yana da rai mana.” Firdausi ta kalleta cike da tausayi saboda irin shakuwar dasukayi har ya wuce misali a ‘yan watannin dasuka dauka tare. “To idan ya mutu yaya zai miki waya?”2 “Oho dai, just kawai ya fada mini a wani hali yake (I’m scared to death).” Yanzu kuwa Sati shida kenan da bacewar Saleem babu labarin inda ya shiga.1 ****** “Tashin hankali!” Duka suka juyo suka dubi Khansa’u dake rike da wayarta a hannu. Radiyya ce ta ce “Yaya Khans me ya faru?” “Ki bari mana, tsabaragen wulakanci da rashin mutumci wai su Sajeeda pink wedding zasuyi yanzu naga ta saka a status update dinta bayan ta dade da sanin tsarin mu kenan da muka fitar.” Rumaysah dake kwance tana duba littafi a kan cinyar Radiyya ta juyo tace “To ba sai ku canza ba?” Khansa’u tace “Tab kin san wahalan da muka ci kafin mu samu wasu abubuwa, kina ga sati na sama zamu tafi Dubai karbo bridal gowns dinmu an gama tsarawa sannan zaki ce mu canza?” Rumaysah na dariya tace “Sai kuyi anko to ai.” Khansa’u tace “Ke da Allah rufe mana baki, ana serious magana idan bazaki kawo shawara ba ki daina sa baki a acikin zancen manya.” Rumaysah ta kawo wuya nan da nan ta mike ta bar dakin nan ta bar musu takardarta, dakinta ta wuce kan kujerar dake dakin ta jibgu, “wai sai kuyi ta ce min yarinya bayan nima yanzu shekarata goma sha tara. Kowa baya sona a gidan nan Abba ne kawai yake so na.” Wayarta ta dauka sai dai ko da ta duba fuskar wayar tana nan yanda ta barta domin kuwa yau ma babu wayarsa bare sakonsa. “Duk kuyi tayi nima sai na rama” Ta fada cikin hawaye. Mikewa tayi ta fada bandaki ta saki shower daga bisani ta shirya cikin wata doguwar riga mai gajeren hannu kirar turai sannan ta yafa karamin mayafi tayi waje, bata tsaya ko ina ba sai wurin motarta kirar hyundai Elantra sabon yayi, idanunta sun rufe da fushi tun daga gate take ta sakin horn wa masu gadi don su bude mata ta samu ta fita ko zata ji sauki a ranta. Da gudu ta shara kwana ba tare da ta duba barinta na dama ba, ji kake gagau ta buga wata motar. Cikin kidima ta ja birki “Kuuuu” STORY CONTINUES BELOW Tsabar tsoro ta gagara ma bude idanunta sai da taji tana numfashi ne sannan ta dago kanta, tana ganin motar da ta kuskura ta fita daga motar cikin zafin nama, kai tsaye wurin windon shi ta tsaya. “Wai kai makaho ne baka gani zaka zo ka tsaya haka? Dubi yanda ka baza bayan motarka ka cika rabin titi da ita?” A hankali ya fito daga motar hade da zare glass din idanunsa nan take ta matsa baya kadan. “KO titin ma zaki fadawa Uwarki ta zo ta rabane? kowa ya bi gefen nasu. Kina nan yarinya karama, sai raini da tsegeranci, ba abun da kika iya sai yawo da tara yaran banza. Yanzu ina zaki fita kije wai ana kokarin sallar maghriba? Wuce ki koma cikin gida yanzun nan kafin na saba miki. Wawiya” Tsaki yaja sannan ya juya zuwa motarsa.4 Rumaysah dai tayi shiru ta gama jinsa, ba abunda take so irin ta bashi haushi amma duk da haka ba kuma wanda take tsoro irinsa, domin ya iya hada rai da nuna yafi kowa kirki da hankali, don idan ya tashi baya barin kowa wataran har Momi sai yace zai yiwa wa’azi.4 A sanyaye ta leko gaban motarta don taga irin damejin da tayi. Haka ta koma gida sai dai a waje tayi zamanta sai Abbanta ya dawo saboda shi kadai ne mai sonta, Su Khans sunce ita ba sa’ar su bace, Momi tana ce mata wawiya sannan ga yaya Fawzaan!4 ******** ************ ********** Ranar Talata Rumaysah ta fito ita da Firdausi tana sauri su isa wurin cin abinci saboda yunwar da takeji kawai sai ta hangoshi cikin abokai, sun kewayeshi ana ta murna. A nan wurin ta daskare ta gagara fadin komai bare ta motsa, a haka har Saleem ya hangota kawai ya ratso cikin mutane ya nufeta gadan-gadan. Har ya doso ta tana tsaye a nan kaman wacce aka kafa da kusa don gani takeyi kaman ba shi bane, tamkar gizo yake mata, Firdausi ma dai tsayawar tayi. Yana iso Rumaysah ya karbi books dinta ya damkawa Firdausi, kawai sai ya janyeta a wurin haba gaba daya abokansu suka sa musu shewa. Guri ya dauka, amma ko a jikinsu, can nesa da mutane suka samu suka zauna, sai dai maimakon ta masa libgin tambayoyin da suke make a cikinta sai ta fashe da kuka, shima maimakon ya mata bayani ko kuma ya rarrasheta sai shima ya sa kuka, haka sukayi tayi ba mai rarrashin dan uwansa. Can dai Saleem ya daure yayi ta maza ya ciro wani jan handkerchief mai digo-digon fari a jiki ya mika mata ta share hawayenta, har tsawon lokaci kafin su daina.8 “Na tsaneka, na tsaneka da ka sakani a halin da ka sakani, na tsaneka saboda yanda ka tayarwa su Mami da hankali na tsaneka da baka mana bayanin komai ba. Ka dauka ba mai damuwa ne idan ka tafi? Ka dauka don son kanka ya maka yawa sai kawai kayi radin kanka ba tare da damuwa da abun da zai je ya komo ba?” “Kiyi hakuri Rumy, na san na saki a cikin wani irin yanayi, dukan ku amma ina neman afuwa. Kawai ya zama dole ne na tafi na idda kudurina ba tare da na fada miki ba, saboda na san idan kika samu labari bazaki amince na tafi ba. Kawai na gano cewa Anty so takeyi ta lalata min future shi yasa na tafi. Yola na tafi wurin wani aminin Daddy Professor ne a FuTY zama nayi masa har sai da ya sama min admission a can, Computer science by the way” Har Rumaysah ta fara murna sai ta ankara da cewa shi kenan fa idan ya tafi can sun rabu kenan. Nan ta fashe masa da sabon kuka “Me kake nufi me yasa bazakayi hakuri ba da wannan makarantar mu zauna muyi rayuwarmu muna karatunmu har muyi aure ba, yanzu idan ka tafi ka san yanda zanyi? Ka san halin da na shiga kuwa da ka tafi baka nan? Ko so kakeyi sai ka ga gawata a kasa sannan zaka damu?” “Rumy, kiyi hakuri in sha Allah ba wani abu, ba abunda zai raba mu.” Da kyar Saleem ya sha kan Rumaysah ranar fuskarta duk a kumbure ta isa gida. Bayan kwana biyu suna jimamin batun tafiyarsa ne kaman daga sama Saleem yace “Rumy, me zai hana kema na sama miki admission a can, ki kawo credentials dinki sai mu tafi.”2 STORY CONTINUES BELOW Rumaysah haka ta tsaya kallonsa kasake, yau ta shigesu ta bishi suje ina? Wani irin dalili zata fadawa su Abba na barinta wannan makarantar bugu da kari shi bai yi hakuri ya zauna saboda ita ba sai itace zata bishi? gaskiya bazata iya ba. Don haka ta ce masa “Allah dai ya taimake ka kan abunda zaka je nema, follow your dreams na san ba abunda zai raba mu ba Adamawa zuwa Abuja ba ko Zaria zuwa Zimbabwe ne.”5 Murmushi yayi yace “To shi kenan, kar ki damu ni kuma na miki alqawari duk semester zan na zuwa miki yawo in sha Allah.” Haka suka rabu cikin shauki da begen juna. Farkon tafiyarshi sai ta sake jin wani daban kaman ba kwanan nan ta tsince shi ba, sai dai wannan karon kullum alkawari ne sai sunyi waya sai kuma ya turo mata sakonni. A irin haka ne ranar tana kwance a falon Abba ta kara waya a kunne sai zuba soyayya sukeyi da Saleem dinta, sam bata ji shigowar Abba falon ba don haka sai da suka kare tas, ta tashi zata hau sama ne taga Abba a zaune kan kujerar gefe ya buga uban tagumi yana kallonta.7 Kar dai Abba yaji hirarta? Ai kuwa sai ya bata amsa da cewa “Oh yanzu baby na ta girma har soyayya takeyi.” Kunya ta kama Rumaysah ta rufe idanunta, “To waye ya taki wannan sa’a haka shine ake boyewa Abba ko a fada masa.” Nan ta zube a kasan carpet kusa dashi ta fara bashi labarin soyayarta da Saleem. Tana kai aya yace “Tab ai kuwa an samu babban matsala” Da sauri ta dago tana duban Abba da alamun tambaya a fuskarta “Me ya faru Abba?” “Yanzu yaya za ayi kenan idan kukayi aure? zai raba ki da gidan Abba fa.” Nan ta sauke ajiyar zuciya tace “Abba ba sai shi ya zo nan mu zauna ba ai akwai wuri”6 Sukayi dariya har da tafawa yace “Tab wa ya ga anje daukan ango.” Suka sake yin dariya. Sai kuma Abba ya tsagaita yace “kince min ba ajinku daya, yaya za ayi kenan?”13 “Abba ya ce min ba matsala sai mun gama karatu ayi maganar biki. Tare zamu gama in sha Allah” “To shike nan amma dai kiyi karatu sosai, kinga su Khansa’u duk sun gama da sakamako mai kyau, ga Radiyya ma tana karshe.” Ta amsa masa hade da yi masa alkawarin dagewa sosai. ********** ********** ************* Yana zaune a office dinshi da ya faye fidda wani sassanyar kamshi wanda ya dace da ma’abocin office din ga sanyin da yake ratsawa na na’urar AC, ya juyawa kofar shigowa baya a cikin kujerar sa mai juyawa, yana da tsawo da kuma faffadar kirji, kana ganin fatarsa mai wankan tarwada zaka san yana samun hutu domin ya dawo tamkar wani bakin balarabe. Fuskarsa ya yalwatu da cikakken gashin gira wanda kusan a cikin zuri’arsu wannan yake, yana da manyan fararen idanu masu razanarwa idan kuwa yana cikin nishadi su kasance masu kwantar da hankali, siririn gashin baki ne a saman labbansa cikakku, kasan dogon hancinsa. Idan haduwa kake nema ta fannin gaye kuwa ka samu Barrister Fawzaan Lamido to an gama.4 Mutumne mai tsare gida, maganarsa kuwa tamkar basarake domin kaman sai ya tauna yake fitar dasu koman sa a tsanake yakeyi, yana da wata kamala da ke kara masa kwarjini, da cikan halitta.3 Wayace a manne a kunnensa ya dan rike shi nesa da kuncinsa kadan, daga gani koma da wa yake wayar nan cikin nishadi yake. “Oh, haka kikace ko? Shi kenan ni kuma I will prove you wrong.” “Ni kuma ina jira na gani, hirar ta isa haka koma kan aikin ka” Ta fada cikin nishadi.2 “Wai, ai yanzu kam bazan iya aikata komai ba, muddin ba ganin ki nayi a gabana ba to bani da sauran kwanciyar hankali ta yaya kike tsammani na iya aiki?” Yana sauraron yaji ta bashi amsa ne kawai yaji Meena ta katse layin. Murmushi yayi ya juyo da kujerar sa. A tsaye ya gan shi ya goya hannayensa a saman kirji dubansa yakeyi kawai. “What?” “Wai kai me yasa ne kake haka? Ka tsaya banda soyayya ba abunda ka keyi, ka bar aikin da yake gaban ka bare kuma ka tuno sauran abubuwa masu muhimmanci. Tun dazu ka sa mun ajiye mutum yana ta jiran mu. Sai waya yake ta min. Idan zaka iya sai ka taso mu tafi.” Fawzaan ya karewa abokinsa kallo sannan yace “Afuwa, wallahi na sha’afa ne gabaki daya Rayyan.”1 Hararar sa yayi “Dole ka sha’afa ai ka zama Romeo.” “Naga dai kanwarkace bare kuma ka ce abun nan…” Nan dai ya zari makullin motarsa da waya sannan ya mike suka fita. Guzape suka wuce inda Ibrahim ke jiran su. Bayan ya basu mukullin ya tafi ne, Fawzaan ya shiga suka kara duba gidan, can ya nisa yace “Rayyan, kai ba? Ka sani cikin damuwa, ban san yanda akayi na biye maka ba ma. All my life savings a hada da cikon kudin Baffa.” Dariya yayi yace “Na maka murna, at least wannan gidan ya zamo naka so, saura abu daya.” Fawzaan ya zaro idanu “Me kuma ya saura? Bayan ka tatseni tas bani da ko kobo a account dina.” “Saura wacce zata kawata ginin ta mai dashi gida, abun nufi matar aure. Yanzu kam lokaci yayi da za a bar harkar waya ayi babban magana dangane da Meena ko me kace?” “Ai ni yanzu gaba daya, jikina ya mutu da me zanyi auren bayan sun kare.” “Kai dai baka son tabawa amma ai suna inda suke, me kakeyi da kudi tuntuni baka isa kace min kashe su kakeyi ba.” “Ina ruwanka da abun da nayi dasu ni dai kawai ka jefa ni a damuwa.” “Muje dai mu bada kyakkywar labarin nan wa Baffa da Mama su zo su saka albarka.” Sai da suka fito harabar gidan Fawzaan ya shaki iskar wurin, Rayyan ya dube shi yace “Amma kasan baka fadi ba, wuri ga kyaun muhalli, wurin parking, hadaden generator ga isasshen ruwa ga kuma tsaro ko wani gida da kamarorin su (CCTV) me zaka nema? Kai dai kawai ka faye damuwa.” “Wai ni ko nawa suka biya ka ka musu tallen gurin nan oho” “Ko ma dai menene naga ba ni ke da gidan ba kai ne.” “Na sani, na gode ba abunda zan ce maka, da baka matsa ba kam na san da ban rufe idanu ba, ai muhalli yana da dadi kaga yanzu kam ai na gama da wannan sai dai wani abun kuma.”1 Suna dariya suka fita daga Grand Apartments dake Guzape. Farin ciki ne ya rufe ilahirin jama’ar gidan Alhaji Lamido ganin ci gaban da dansu ya samu, haka sukayi ta tururwan zuwa ganin gidan, suna sa albarka, sai da ya sa aka masa saukar al qur’ani a gidan.1 Nan fa maganar ta taso Abba da Baffa suka sashi a gaba. “To Fawzaan, kai haka akeyi ne sai a ayi muhalli babu iyali? Ai inaga ya dai kyautu a yi wani abun idan ba dai Ra’id kake so ya rigaka ba, don idan ta shi ne tun yana aji biyu a jami’a wai ayi masa aure, sai da ni da baffanka muka ce muddin ya kuskura ya sa aure a gaba bai samu abunyi ba to kuwa bazai ga kobon mu ba don haka ne ya hakura yayi karatun.” Kanshi na kasa ya gama ji Abba ya koro jawabi, ba ga shi ba yana zaman zaman shi a dan daki da falonsa na haya ba wanda ya dago masa maganar aure, amma kwana biyu da sayan gidanshi har ana dago masa zancen. “In sha Allahu Abba muna dai ta kan kokari a taya mu da addu’ar dacewa.” Alhali a zuciyarsa hoton Meena ce ya hasko shi. “Ameen, to Allah ya taimaka.” Suna gama hirar su da su Abba sama ya haura wurin Mama, nan ya samu Sajeeda sai bayani takeyi a waya. “Mama lafiyar wannan kuwa?” “Hmm, duk dai wai shirye-shirye ake ta kanyi.” “To Allah ya gyara, auren da saura watanni shine duk kun daga hankali kuna ta wani shiri? Ina laifin a shafa fatiha a watse kowa ya tafi gidansa amma sai ku tsaya kirkire kirkire” Caraf Munira dake kwance a kan cinyar mama tace “tab Yaya Fawzaan abun da fa ake yayi kenan sai mu kace kar muyi? Bikin mu ya zo ya zama dry ba armashi? Gwamma dai a dan rinka yi ana mix.” “Hmm, ana fada miki ga hanya kina baudewa, zaki san mix ai a lahira.” Duka sukayi dariya, don sun san halinshi da kin irin wadannan. Ya kusa minti talatin suna hira kafin ya musu sallama tsohon apartment dinsa na samari ya koma don tukun bai shiga gidan sa ba. Ko da yake Rayyan yace ya kusa ya fita a cikin sahun samari tunda yanzu ya tasan ma talatin da hudu.13 ******* ************ **********