AMININ MAHAIFINA
CHAPTER 10
Harith yayi parking motar shi a kofar gidanmu, da yake ya dawo tun last week. Yau tsokana muka fita, gidan su Ikram budurwar shi muka je da yake itama tazo hutu. Har kofar gidansu muka je aka mata sallama ta fito da saurinta ita ala dole masoyinta yazo, yadda tayi turus ganina akan motar shi ina wasa da keys din motar shi sai daya kusa bata mana budget, kaina na kawar gefe ina boye dariyar data kama ni. Haka ta daure ta karaso wajenmu muka gaisa Harith ya gabatar dani a matsayin sister dinshi, suka dan fara hira da ita, mintuna biyar basu cika ba na kalli Harith ina hamma nace “Hari, mu tafi gida!” da sauri ya mata sallama muka shige mota muka tafi, tana tsaye a inda take har muka bar layin. Dariyar abun muke yi har muka shiga gida kamar wasu sabbin mahaukata. Idanuna suka tsaya cak akan Abbu dake zaune akan fararen kujeru inda Daddy ya saba zama yana shan iska ko karatun jarida mostly on weekends. Kamar koda yaushe, babu abinda ya canza daga bugun da zuciyata take a duk lokacin dana ganshi, rawar da kafafuna suke da wani irin doki daya mamaye ni, makaman yakin dana tanada domin yakar zuciyar dake kayata min Abbu naji sun min nauyin dauka. Idanunshi fes akan mu suke, na kalli Harith a nutse nace “ina xuwa” ya gyada min kai. A hankali na fara tafiya zuwa inda yake zaune, kafafuna rawa suke yi saboda yadda nake jin idanun shi masu kaifi a kaina, da taimakon Allah dai na karasa inda yake. Na dan duka a hankali nace “Abbu barka da yamma” ya gyada kai, “barka dai Nafeesah. Daga ina haka?” na rasa abinda zan ce mishi saboda ba makaranta naje ba saboda ranar bamu yi exams ba, nace “mun dan fita ne” ya kalli kofar da Harith ya bi ya shiga falo ya kara kallona fuskar shi dauke da wani irin kallo daya kada min sassan jiki, “and who is he??” nima na kalli kofar, nasan da Harith yake, nace “Harith….” na rasa abin cewa saboda yadda idanunshi suke zagaye fuskata gabadaya sun dauke min kuzari, ganin nayi shiru babu amsa ya gyada kai, “well dama naso ganin Daddyn ki ne shi yasa na zauna jiran shi nayi zaton zai dawo da wuri don na biya ta ofishin shi baya nan, but bana tunanin zan cigaba da jira kam. Zan kira shi kawai” ya tashi yana gyara wuyan rigar shaddar daya saka, ya kalleni har zuwa lokacin normal kallonshi bai dawo ba, yace “Kano na nufa yanxu in shaa Allah. Nan da sati daya zaki zo bikin su Ni’imah koh?” na gyada mishi kaina a hankali, yace “good! Sai mun hadu kenan” ya fara tattaki xuwa inda ya ajiye motar shi, na samu kaina da take mishi baya har gaban motar. Ya saka makulli ya bude motar ya shiga ya kunna, sai lokacin ya juyo ya kalleni yana dan murmushi, Ya Allah! Da ba dan motar shi dana rike da hannuna ba da babu abinda zai hana ni faduwa a lokacin, na rasa irin effect din da Abbu yake dashi a tare dani. Yace “so??” nayi saurin kallonshi saboda gabadaya hankalina ya dauke daga gare shi, nayi saurin daidaita natsuwata nace “Allah ya sauke ka lafiya Abbu, a gaida su Anty Mubeenah da Hafsy” yayi murmushi wannan karon genuinely wanda tunda yaxo sai lokacin naga murmushin shi irin haka, yace “Ameen Nafeesah, zasu ji in shaa Allah!” yaja motar shi ya tafi nima na wuce cikin gida, a bakin kofa muka ci karo da Harith zai fito, yana gani na yace “sai anjima koh babe?” na harare shi ya danyi dariya saboda yasan na tsani sunan, ya wuce abinshi ni kuma na shige gida. Sai dana biya ta dakin Mommy na gaya mata na dawo, ta kalleni fuskarta babu yabo babu fallasa, “kin ga Baban Hafsat a waje kuwa?” gabana ya dan fadi, Allah dai yasa ba wani fadan zan sha ba. Nace “ehh, ya ma tafi ai” Mommy ta kalleni cikin tuhuma, na sadda kaina kasa ina wasa da jakar hannuna, tace “na tambaye ki abinda ke tsakaninku kin ce babu komi, yanzu kuma me ya kawo shi wajen ki?” na kalleta da sauri, “ni fa ba wajena yazo ba wajen Daddy yazo, ya gaji da jiran dawowar shi ne shi yasa ya tafi” tace “haka ya gaya miki?” nace “ehhh, ba haka bane?” ta dan harare ni na kauda kaina, tace “shi kenan je ki” kamar jira nake yi dama, da sauri na bar mata dakin na wuce nawa ina ajiye numfashi a hankali. Duk yadda Tunanin Abinda Mommy take nufi da Tunanin makomar rayuwata da Abbu suka so dabaibaye ni haka naki basu dama, na dage da karatun exams sosai. Cikin ikon Allah cikin sati daya muka gama exams dinmu, cikin lokacin mun kara zuwa gidan su Ikram sau biyu. Wato idan na tuno diramar da muka buga a zuwanmu na karshe gidansu dariyar dake kama ni koh??
Sai ana washegari a fara harkokin bikin su Ni’imah sannan na tafi Kano. Gidan Anty Ameenah muka sauka directly saboda a can amaren suke zaman biki, su Hafsy suka fito suka min oyoyo yaran sun wani kara girma, ban taba sanin nayi kewar su sosai ba sai dana dora idanuna a kansu. Qaseem ne ya dauki jakar hannuna na kama hannun Hafsy Abdullahi ya biyo mu a baya muka shiga gidan. Tarbar dana samu daga Anty Ameenah ta bani mamaki, har uwar dakinta ta kaini inda na samu su Anty Raliya da wasu abokan su, na gaida su suka amsa Anty Raliya na min korafin na tafi babu sallama ni dai nawa bada hakuri ne kawai don nasan cewa m at fault. Na shiga bandakin ta na watsa ruwa na fito nayi sallar Laasar, kafin in gama har an shirya min abinci a tsakiyar dakin ina gamawa na zauna na fara ci. Sai dana gama sannan aka kaini inda amaren suke. Dakine guda aka ware musu inda ake musu gyaran jiki, ina shiga hayaniya ta barke kamar me. Sai a lokacin aka min kitso da kunshi Allah ma yasa na je wankin kai a Kaduna.
Washegari aka yi kamu a Triple Crown Reception Masha Allah wajen ya tsaru iya tsaruwa, mata ne zallah a wajen mun yi shiga ta gargajiya haka ma kide-kiden da aka sa na gargajiya ne zallah. A wajen kamun ne muka hadu da Anty Mubeenah, tana nan yadda take babu abinda ya ragu a yanda take. Kibar nan tata marar fasali ta karu, table daya suka ja ita da kanwar ta Anty Shakira, ta hakimce tana ta hure-huren hanci yayin da su Anty Ameenah suke ta kai kawo suna kokarin entertaining din baki. Na ja hannun Ramlah muka nufi teburin da suke zaune, tun kafin mu karasa nake yago hakora ina murmushi har muka gaban su na musu sallama tare da gaida su, I didn’t expected her to look at me with a smile on her face, tace “Nafeesah sai a haka ake ganin ku ko?” ko babu komi naji dadin yadda tayi, nayi zaton wulakanci zan sha a wajenta kam. Nayi er dariya kawai na zauna a gefen Anty Shakira ina kara gaishe su, nan muka dan yi hirar yaushe gamo kafin na musu sallama na tashi muka cigaba da gudanar da sha’anin bikin mu. Bayan mun koma gida da dare na shiga dakin Anty Ameenah zan dauko kayan barcina da yake tunda naxo kayana suna dakinta, ina yin sallama muryar Abbu ta amsa min, sai dana yi kamar in koma da baya don dai kawai nasan yaji murya ta ne shi yasa. Na shiga cikin falon a hankali kaina a kasa kamar tsohuwar munafuka, daga can gefen shi na durkusa nace “Abbu sannu da zuwa!” muryar shi tayi kasa sosai akwai alamun gajiya sosai a tattare dashi, yace “yauwa Nafeesah, bani ruwa please!” nace toh. Na fita zuwa kicin naje na dauko mishi ruwa mai dan sanyi, har zan fito na kula da farfesun kayan cikin dake cikin warmer, na koma na dauko plate na zuba a ciki na cicciba. Na dire kayan a gaban shi, ya kalleni ya Kalli abincin, fuskar shi ta nuna alamun relaxing and amusement. Ya kalleni cikin lumsassun idanunshi, “Nafeesah!!” ya kira sunana cikin muryar rada, na kalleshi a hankali ba tare dana amsa ba, it’s not that ban amsa ba, nayi niyar amsawa sai dai muryata bata fita ne balle har yaji, yace “Nafeesah!! Zaki iya…..” maganar shi ta katse lokacin da Anty Ameenah ta shigo falon, na kalleshi da sauri cikin mamakin dalilin tsayawar maganar shi. Anty Ameenah ta zauna a gefen shi cike da tsokana tace “ya aka yi Ibu??” na sadda kaina kasa ina kokarin boye dariyar data taso min da jin sunan da Anty Ameenah ta kira shi dashi, ya dan ja tsaki kawai ya fara cin abinda na ajiye mishi. Ganin haka na tashi na shiga dakin na dauko kayana na fito na musu sai da safe na fita, idanun su suna kaina har na fita. Na kai gadon bayana akan katifar da aka shimfida mana a tsakiyar dakin na kwanta, tunanina a lokacin me Abbu yaso fada min dazu?? 8
Washegari aka yi Walimah anan farfajiyar gidan Anty Ameenah. Washegari kuma aka daura aure da dare muka tafi wajen dinner. Kamar da wasa ina juyawa daga seat din da nake zaune na hango Harith da Ikram a zaune, na zaro idanuna ina kallonsu daidai lokacin da shima ya juyo, na mishi alama da hannuna alamun “ya aka yi haka?” ya danyi shrugging kafadar shi. Wayata tayi kara a daidai lokacin da sauri na daga naga Ramlah ce take kira, na daga da sauri, tace in same ta a parking lot Fiancé dinta zai tafi mu gaisa. Nayi excusing kaina wajen wasu daga cikin abokan su Niimah da muke zaune a seat daya dasu na fita. A can parking lot na same su, muka gaisa da Ayan saurayin Ramlah, (Ban fa ce na Ummu Maryam da Ihsan ba… Don kar kusa Husna tayi daidai da naman jikina, tamm). Anan na baro su su gama sallamar su. A hankali nake tafiya saboda heel din dake kafa ta, gashi dinkin skirt din dake jikina ya dan matse ni somehow don haka bana iya daga kafata sosai inyi tafiya. Kawai ji nayi an ja hannuna anyi gefe dani, na daga baki tun karfina zan kwala ihu, aka sa wani tattausan hannu akan bakin nawa ta yadda babu yadda za ayi ihun da nayi niyar yi ya fita……”What the……. Harith meye haka?” na fada ina hararan shi, ya sake ni tare da jingina da mota. “ina so ne muyi magana in secret, can idanun mutane yayi yawa shi yasa” nace “shine kuma sai ka tsorata ni?” ya daga kafada, “sorry ok! Ikram tana hango mu fa, muje” muka fito daga wajen da yaja mu muna dan dariya muka tsaya a daidai inda zata dinga hango mu sosai, Harith ya kai hannun shi kamar zai yi cupping din fuskata., “Nafeesah?” Husky voice din Abbu ya sankame ni a wajen, bayan kamar sakan goma na juya a hankali kuma cike da tsoron irin fahimtar da zai mana. Tsaye yake a gefen mu sanye da shadda light brown da hula a kan shi, kallonmu yake daga ni har Harith din cikin alamun tambaya da kuma bacin rai. Take naji jikina yayi sanyi, na kalli Harith da a lokacin hankalinshi ya tafi da Ikram wadda ta juya zuwa cikin hall din kamar tana share hawaye daga karshe ma sai ya bi bayanta. Na kalli Abbu da har lokacin kallona yake yi, idanunshi suna fitar da wani irin tartsatsin abu cike da alamun bacin rai, ya dan matso kusa dani yace “me kike yi anan?” na dan ja baya kadan saboda kusancin dake tsakanin mu kafin in ce “umh, dama na fito ne zamu gaisa da saurayin……” wani irin kallo daya watso min ne yasa nayi shiru jikina ya dauki rawa, me ke damun Abbu ne yau? Na daure na karasa “…. Ramlah kawata” sai lokacin na ga ya dan sassauta muryar shi idan ban yi mistake bama har da sighing yayi softly wanda na lura dashi ta yanayin yadda kirjin shi ya sauka a hankali. Ya katse shirun da muka yi ta hanyar cewa “kin yi kyau sosai yau…. Kodayake kullum ma haka kike” nace “hmmm” kawai saboda gabadaya na rasa abin cewa it’s really unlike him. Na sha jin kalmar yabo daga gareshi amma ban taba jin makamanciyar wannan ba don haka naji abun so strange. Yace “zaki koma cikin hall din ne??” na gyada kaina da sauri, yace “k, ni zan koma ne yanzu” na kalli agogon hannuna kafin in kalleshi, “karfe tara ne fa kawai Abbu zaka tafi tun yanzu” yayi er dariya data saka ni shagala da kallonshi, “ban cika halartar ire-iren wadannan abubuwan ba Nafeesah…. Wannan din ma ya zamar min dole ne, naso ganin wani very badly kuma babu hanyar ganin nashi sai ta nan shi yasa” na gyada kai kamar na fahimce shi, sai dai maganar gaskiya na kasa processing maganganun shi a cikin kaina, babu abinda nake fahimta a lokacin irin daddadan kamshin turaren shi dake tashi da yadda zuciyata take bugu. Ya zura hannu a cikin aljihu ya ciro rafar kudi sababbi kar dasu ya miko min, naki saka hannu in karba har sai da yayi magana, “kudin liki ne ba wani abu ba, karbi” da sauri na hau girgiza kaina, “ina dasu nima Abbu ka bar kudin ka” ya hade fuska “akwai abinda na taba baki a duniyar nan ba tare da kin min gardama ba kuwa?” nace “Abbu Allah ba gardama bace, kawai akwai kudin likin a wajena ne nima” yace “to tunda na baki ai sai ki amsa koh?” na bude baki zan yi magana ya sake hade muryar shi, “Nafeesah karbi kudin nan kafin raina ya baci fa” yana iya? Sai kawai na saka hannu biyu na karba har da dan dukawa nace “Nagode sosai Abbu Allah ya saka da alkhairi” yace “Ameen…. Go back” ba musu na mishi sai da safe na wuce, ina jin idanun shi a kaina har na shige cikin hall din. Na koma wajen su Ramlah na zauna, lokacin da aka kira amaren suka fita wajen rawa muma muka tashi muka je muka fara liki. Sai sha biyu saura aka tashi daga wajen dinner dinnan, an daiyi komi lafiya an gama. Kafin mu isa masauki sai wajen karfe daya aikuwa mun sha fada sosai wajen Anty Ameenah kamar me! Washegari aka kai Amaren gidajen su na aure, ita Sa’adiya tana Lamido Crescent Ni’ima kuma suna Zoo road. A gidan Sa’adiya ne muka hadu da Ikram, mun gaisa da ita sama-sama tana ta wani shan kamshi ni kuwa ina mata dariya a ciki don nasan dalilin hade fuskar, sai a lokacin naji ashe cousin din mijin Sa’adiya ce. A washegari naso komawa gida Anty Ameenah tace ina! Ai sai na cinye sati daya din da aka bani daga gida, ban yarda da gaske take ba sai data dauke min jakar kaya ta kulle a bedroom dinta, ni wallahi dariya ta bani. Dole haka nan na zauna, dama kwana biyu suka rage min. Naje gidan Anty Haleemah da Anty Raliya, washegari kuma direban gidan Anty Ameenah ya kaini gidan Abbu. Da yake ranar Lahadi ce na samu Abbu a gida, na ga tarbar data bani mamaki kam. Tun daga bakin gate su Hafsy suka taro ni suna ihun murna har cikin falo. Gidan yana nan kamar yadda na tafi na barshi, matar gidan tana uwar daka. Na shiga har ciki muka gaisa na koma falo wajen su Hafsy, nan suka fara ajiye min tarkacen kayan makulashe muka shiririce anan muna hirar mu har aka kira sallar Axuhur, Abbu ya fito daga dakinshi sanye da jallabiya ruwan toka da alamun masallaci zai je, na zamo daga kan kujerar da nake zaune na gaida shi, ya amsa tare da wuce mu su Abdullahi suka tashi suka bi bayan shi ni da Hafsy kuma muka shiga dakinta muka yi tamu sallahr
Abbu ya mana odar abinci daga restaurant muka ci namu ni da Hafsy a daki. Ina nan a gidan har yamma tayi, direban Anty Ameenah ya dawo daukata, na je nawa Anty Mubeenah sallama muka fita zuwa inda direban yake jirana cikin rakiyar su Hafsy. Abbu yana zaune akan kujera da laptop a gabanshi akan dan karamin table yana ta danne-danne a ciki. Na fasa shiga motar da nayi niyar yi na taka zuwa gaban shi, ya dago ya kalleni yana murmushi. Na sadda kaina kasa cike da kunya, “Abbu zan wuce” ya gyada kai, “gobe zaki koma koh?” na gyada kaina, yace “nima ina so zan shiga Kadunar gobe in shaa Allah. I’ll drop you off goben, that is idan tafiyar tana nan” na kalleshi fuskana dauke da alamun tambaya sai dai na basar, ai yace akwai abinda zai kaishi kuma ma cewa yayi sai idan tafiyar tana nan ne sannan zai ajiye ni. Nayi murmushi nace “to Abbu, na tafi” ya gyada kai yana jifana da murmushin nan nashi, “ok Nafeesah! Mun gode da dariya” na danyi murmushi tare da juyawa na tafi. Muka sake yin sallama dasu Hafsy na shiga mota muka tafi, daidai saitin Abbu na dan saci kallonshi, idanunshi suna kaina yana kallona da wani irin yanayi da kallo with so much affection, nayi saurin sadda kaina kasa ban dago ba har sai da muka bar layin. 1
*******
Na fito jaye da trolley dina, Anty Ameenah tana zaune akan kujera a falonta ta kalleni tana murmushi, “tun kafin yamma tayi har kin gaji damu koh Nafeesah?” na girgiza kai ina murmushi nima “haba Anty ba haka bane, karfe hudu fa tayi already kuma kinsan akwai tafiya a gaban mu” tace “haka dai kika ce. Mun gode sosai duk da haka” na fara tafiya yayin data tashi ta biyo bayana. Abbu yana tsaye a jikin motar shi Toyota yana jiran fitowar mu. Hasken ranar dake haska shi ya kara haskaka shi cikin shigar Dogon wandon jeans baki da bakar shirt, hakan ya haskaka shi ba kadan ba. Kyawun shi da cikar kamalar shi suka kara fitowa sosai, ban san cewa na shagala a kallon shi ba sai da naji Anty Ameenah ta dan zungure ni, a matukar kunyace na sadda kaina kasa. Ya Allah! Abinda Bawan nan naka yake saka ni yi!! Ya bude booth muka saka akwatina a ciki. Na bude gefen mai zaman Banza na shiga na zauna, Anty Ameenah ta leko tana min addu’ar a sauka lafiya har Abbu ya shiga shima ya tashi motar muka tafi. Tuki yake yi a nutse kuma cike da kwarewa, baka jin motsin komi a cikin motar kamar babu abu mai numfashi a ciki. Ya kunna kira’ar Sudeis cikin Suratul Maryam, na dan kwantar da kaina a jikin kujerar. A matukar takure nake ji na, it felt so awkward for me, to be hooked up with someone you so much cherish, wanda nake hangowa a matsayin mijin da zan aura, wanda da kyar nake hana kaina throwing my self to him a duk lokacin dana ganshi, yanzu da muke tafiyar nan sai nake jin wani iri a jikina, gashi duk yadda naso koda barci ne inyi abun yaci tura. Muna barin cikin gari Abbu ya ware injin mota, lokaci zuwa lokaci za a kira shi a waya ya daga da wannan damar nake samu in kare mishi kallo. Abbu is really good looking and handsome man. Wajen karfe shida muka fara shiga Kaduna, na dan sauke ajiyar zuciya a hankali ina jin kamar in bude idona in ganni a tsakiyar gidanmu. Well, it has it has really been a hell of a ride (-Justin Bieber). Can u believe that tunda muka shiga mota kalma daya bata hada mu dashi ba?? Suddenly naga yayi parking din motar a gefen hanya, wani dan karamin daji ne gab da za a shiga Kaduna. Inda yayi parking din motar gaban wata korama, reflection din rana da take kokarin faduwa ya fita zane a Vikings, the view was wow! Gashi wajen babu hayaniya sai ta ababen hawa dake ta wucewa a guje. Na daga idona na kalleshi cike da mamakin dalilin da yasa muka tsaya anan, idanun shi suna ga koramar dake gaban mu, he seems out of the world, ya shige duniyar tunani. Na dan yi gyaran murya tare da cewa “Abbu.., laa…. fiya muka…. tsaya??” a hankali, bai kalleni ba, haka bai yi magana ba. Sai na tsaya kawai ina son in ga abinda xai faru. Lokaci mai tsayi muna a yanayin da muke har hasken rana ya fara daukewa duhu ya fara shigowa, tsoro ya fara shiga ta. Abbu ya kira sunana a hankali kamar mai rada, “Nafeesah!!” na kalli sashen da yake tare da amsawa, shiru ya sake biyo baya na kimanin minti guda. Kamar daga sama, kamar a duniyar mafarki naji saukar maganar, “Nafeesah! Zaki Aure ni??!”. Tsabar firgita da mamaki sai da kaina ya buge da glass din motar, ban damu da zafin da naji ba Abbu kawai nake kallo kamar wata sabuwar mahaukaciya ko kuma shine nake wa kallon sabon mahaukaci?? Ganin expression din dana nuna yasa ya dan kauda fuskar shi daga kallona, “Nasan baki taba tsammanin faruwar hakan ba Nafeesah, na sani. Ni kaina nayi hesitating fada miki maganar nan yafi sau dari, sai dai I couldn’t anymore. Auren ki nake son yi Nafeesah da gaske, ina kuma fatan cewa zaki aminta da hakan?” ya juyo ya kalleni. Allah ne kadai yasan yanayin da nake ciki a lokacin, baki nake so in daga a lokacin in amsa mishi da YES! Da duk karfin da Allah ya bani, in gaya mishi nima burina kenan sai dai ina! Na ma manta yadda ake yin magana a dan lokacin. Wasu kyawawan mintuna biyu suka wuce a haka, wasu masallatan har an fara kiran sallar magriba. Abbu yace “look Nafeesah! M not forcing you into this kin gane? Zan baki lokaci kiyi tunani da kanki don bana so in tauye miki hakkin ki Nafeesah, idan nayi haka na cuce ki. I just….. M just tired Nafeesah. I want us to get married ASAP. Hell, idan kika amsa min yanzu m ready to marry you tomorrow Nafeesah…. Na baki lokaci ki samu time ki yanke shawara akan abinda kike gani sai dai kada ya dauki lokaci pls, sannan ina so kiyi duba da Allah da soyayyar da Iyalina suke nuna miki Nafeesah, we really need u in our lives”. Da wannan ya tashi motar muka kara gaba, duk yadda naso in dawo cikin natsuwata abin yaci tura, yes! I was shocked beyond my imagination. Har yayi parking a kofar gidanmu, ina jin yana gayawa Mai gadi da yake kokarin buddy kofa ba shiga ciki zai yi ba, Mai gadin yazo ya bude saitin kofar da nake yana jera min sannu da hanya. Kamar wadda aka daddaba daga barci, sai lokacin duniyata taci gaba da juyawa da dai tsayawa tayi cak. Na zura kafana daya waje da niyar fita, Abbu ya tsayar dani ta hanyar kiran sunana. Na dakata ba tare dana juya na kalleshi ba, bani da kuzarin kallon shi, ina tsoron abinda kallon fuskar shi zai haddasa min. Nasan zan iya amsa mishi da yes a take a lokacin. Yace “please think about US carefully Nafeesah, ina fatan jin daddadan labari daga gare ki” na karasa cira daya kafar na fita daga motar. Mai gadi ya maida mishi murfin motar ya rufe, ya sungumo trolley dina ya biyo ni dashi. Da kyar nake daga kafa ta. Taimakon Allah ne kadai ya kaini cikin gida, Mommy ta fito da saurinta tana min oyoyo, gani na a haka sai data yi turus. Ta matso tana tambaya na lafiya na lau kuwa? Da kyar na iya daga baki nace mata “gajiya” tace “shine kuma kika yi zuru-xuru haka? Wuce kije kiyi sallah kici abinci sai ki kwanta” babu musu na shige dakina. Na dauro alwala nayi sallah, yadda nake jin cikina a cike nasan babu abinda zan iya ci a lokacin. Ko kayan jikina ban cire ba na haye gado tare da lashes wutar dakin. Ina jin lokacin da Mom ta leko dakin ta maida min dakin ta rufe. A gajiye nake, barci nake ji, sai dai awa daya kenan da kwanciyata babu alamun barci a tattare dani. Maganganun Abbu suke replaying a cikin kwalwa ta over and over, for once in my life da naji farin ciki yana so ya saka ni kuka, sai dai shima kukan yaki zuwa. Ya Allah!! What in the world am I suppose to do??! Ranar nasan dama babu barci, ina zan iya barci dama idan har na cigaba da hango ni zaune akan gado a cikin gidan Abbu lullube da gyale???Da murmushi na tashi akan fuskata, rabon da inyi barci mai dadin na yau har na manta. Naje nayi brush na fito falo, babu kowa a falon dama nasan ba lallai in ga kowa ba saboda karfe goma sha daya na safe ne lokacin. Break fast na fara yi kafin na shiga dakin Mommy na gaida ta. Tace inje in shirya zata aikeni gidan Aunty Uwani, da saurina naje na watsa ruwa na shirya na fito. Turaren wuta ne da kayan labule da bed sheets ban san dai kona waye ba sai da naje can take ce min na diyar kanwar mijinta ne. Can kuryar dakinta na shige na nade akan gado ina kara tunanin makomar zancen Abbu a cikin raina, wani bangare yana shawarta ta da in kira shi a yanzu in fada mishi na amince, wani kuma yana gaya min hakan bai dace ba, wani kuma yana ce min in dan bashi lokaci dai gabadaya na rasa wanda zan dauka, a haka barci ya dauke ni saboda rashin barcin da ban samu a daren jiya ba, sai wajen karfe uku Anty Uwani ta tashe ni nayi sallah, bayan la’asar na musu sallama na wuce gida. Ina zuwa na ba mommy sakon data bani in kawo mata na wuce daki, ba a jima ba na fito muka shiga kicin da ita muka fara girki.
Kamar yadda yake Al’adar gidan mu, bayan an gama muna haduwa a dakin Daddy a yawancin darare, wani lokaci muyi kallo wani lokacin hira, sometimes ma musamman idan daddy yana ayyuka zaku ga kowa abinda ke gaban shi kawai yake yi. Ina zaune a kasan kujera ina browsing Mummy kuma tana kan kujera a xaune, Daddy ya fito daga bedroom din shi ya zauna a kusa da Mommy. Daddy ya kira sunana in a serious tone, “Uwata” na amsa a nutse tare da kallon shi, yace “last two weeks da suka wuce Ibrahim ya same ni da wata magana mai Muhimmanci” yayi shiru yana kallona yayin da zuciyata ta hau duka kamar zata fado kasa, ya cigaba da magana “Yace wai Yana So Ya Aure Ki! Ni kuma nace mishi sai naji daga bakin ki don bana son tursasa ki akan abinda baki da niyar yi, me kika ce? Zaki Auri Ibrahim?” Na sadda kaina kasa ina wasa da yatsun hannuna, ban san abinda yakamata in ce ba, ina son Abbu kuma Ina son Auren shi? Ina son Abbu amma ina tunanin auren shi is not a good idea? Ko kuwa me zan ce?? Mommy tayi saurin riga ni magana, “Haba Abban Ummiey, kaima kasan cewa wannan ba abu bane mai yiwuwa. Shi bai yi tunanin abinda zai zo ya dawo bane ya kirkiro wannan magana? Wannan abu ba zai yiwu ba sam!” duka ni da Daddy muka kalleta, fuska a hade sosai take yin maganar, daga ganin yanayin idanunta nasan cewa she is strongly against it, sai jikina ya kara yin sanyi akan na da. Daddy yace “me kike cewa ne haka Habibty?” tace “Abinda ya kamata mana, Idan shi idanun shi sun makance da cin Amana bai kamata naka su rufe ba Abban Ummiey. Haba! Ace daga tura yarinya yin IT na wata shida kawai sai aji wai ta buge da aure mai gida? Kaima kasan cewa wannan ba abu bane da zai yiwu ba, sai dai idan so kake ka saka mu a bakin duniya kuma” Daddy ya danyi murmushi, “sai dai idan basa son junan su Habibty, amma idan suna so then who cares about what people will say? Su mutane ai aikin su kenan ina tabbatar miki idan kika ce zaki biye ta mutane to numfashi ma sai sun miki izinin kiyi kenan?” Mommy ta hade fuska “na kula ga gaskiya nan kana gani kuru-kuru amma kana takewa, son Kai ne ko me? Aure dai Nafeesah da Ibrahim babu shi!! Ba zan taba bada hadin kaina ga cin amanar wannan da kuke shirin yi ba” Daddy yace “ke kuma kin ki fahimtar abinda soyayya zata yi da wannan ba zata iya ba, baki tsaya kinji ta bakin yarinya ba kin zauna kina ta tada jijiyoyin wuya, be it zaman aure ko cin amana kamar yadda kika ce don ni dai ban ga komi ba a ciki, ina ga ai ya rage ga yarinyar koh?” Mommy tace “ni nasan Ummiey ba zata taba aminta da hakan ba, ga samari nan bila adadin suna karakaina a kanta sai ta buge da wani can, ga mata ga ‘ya’ya, abokinka kuma for that matter, anya Abban Ummiey ka duba maganar nan sosai?” Daddy ya kalleni yace “Uwata!” na daga kai na kalleshi, yace “kada ki damu da abinda take fada kin ji? Just tell me idan kina son Ibrahim kuma zaki iya auren shi” na kalli Daddy na kalli Mommy, toh fa! Ga sanyin Idaniyata guda biyu a gabana, ko wanne ya zuba min ido yana jiran amsa ta wanda nasan cewa amsar da zan ba daya daidai take da bacin ran daya, abinda na tsani gani da ji kenan a duniyata ace daya daga cikin Iyayena yana cikin bacin rai sabida ni. Abinda Mommy take fada gaskiya ne, shima Daddy akan gaskiyar shi yake, to me zan yi kenan? M I going to disappoint one of them? Ya Allah!! M extremely confused! Na samu kaina da girgiza kai wanda ni a karan kaina ban san dalilin yin hakan ba, Daddy yace “me kike nufi da girgiza kai, eh ko aah??” na sake girgiza kaina, “ban sani ba Daddy!” Daddy ya kura min ido na tsawon lokaci, yace “tashi ki tafi kawai Uwata, Allah ya zaba mana mafi alkhairi” ba musu kuma ba tare dana kara uffan ba na musu sai da safe na wuce dakina. Hannu dafe da kai na fada kan gadona na kwanta, na gaji! Na gaji haka nan. Haba! Kwana biyun nan kaina har ciwo yake yi tsabar tunanika da suka hana ni sukuni, abin ya ishe ni haka nan. Tashi nayi na fada toilet na dauro alwala na fito na haye kan Abin sallah, sallah na fara jerowa, dana gama na roki Allah akan yayi mun zabin abu da yafi alkhairi a cikin rayuwata, na gama nayi shirin kwanciya barci na kwanta zuciyata cike da sake-sake.
*****
Tsawon sati guda Daddy bai sake min zancen Abbu ba Mommy ma haka, haka a tsayin lokacin nan ban sake ji daga Abbu ba. Mun koma makaranta don dama ba wani hutu aka bamu mai tsayi ba. Ranar Asabar ina kwance a dakina da hantsi, mun gama waya da Harith kenan yana gaya min yadda suke shan fada shi da Ikram akan wai ni budurwar shi ce ni kuma ina ta shan dariya, na ajiye wayar tare da kurawa ceiling ido ina kallo. Wani kiran wayar ne ya dawo dani cikin hankalina, na mika hannu a sanyaye na dauki wayar. Ban san lokacin dana zabura na tashi zaune dangargar ba, Abbu. Kallon wayar kawai na dinga yi har kiran ya kusa karewa, in daga in ce mishi me? Koda yake na riga na gama yanke shawarar abinda nake ganin daidai ne a rayuwata so let’s just finish this once and for all kawai, na karfafawa kaina gwiwa. Nayi gyaran murya tare da daga kiran na kara wayar a kunnena…..