AMININ MAHAIFINA
CHAPTER 11
“Assalamu Alaikum” sansanyar muryar shi ta doki kunnena, duk wani karfin gwiwa dana tanada da kaudin da nake na cewa Abbu ya daina firgita ni ashe aikin banza nake yi, a take muryar shi tayi raga-raga da naman jikina, yayi gyaran murya tare da ambatar sunana, na amsa a nutse kuma a hankali cikin muryar rada, shiru ya biyo bayan hakan na lokaci mai tsayi, baka jin komi sai karan iska dake wucewa ta cikin wayar. Yace “Nafeesah! Ya muka kare da maganar mu ne?” nayi shiru ina zare idanu, da me na shirya zan ce ne? Gabadaya komi ya fita daga cikin kwakwalwata, yace “umh?! Ina sauraron ki” na bude baki zan yi magana sai dai sautin dake fita kawai shine “ermm…. ermmm” na kasa yin takamaimiyar magana. Abbu ya tausasa murya, “look Nafeesah. I don’t have much time yanzu, mintuna kadan suka rage min in tashi zuwa Vancouver zan yi wani four months course acan so please do tell me, me kike tunani? Ina son ayi ayi auren mu dana dawo Nafeesah, da so samu ne a gare ni da tafiyar nan dake zan yi ta a matsayin mata ta Nafeesah don ba wani tsayawa zan yi bata lokaci wajen soyayya kamar yaro ba, kin san na tsufa da hakan koh?” wata hudu a Vancouver? A perfect timing!! Yace ina jin ki Nafeesah, an fara kiran fasinjoji, me kike tunani? Zaki iya aure na??” na lumshe ido a hankali zuciyata na suya a kirjina kamar an tsoma ta a ruwan zafi, “I Am Sorry Abbu…… I can’t!” shiru ba magana daga bangaren shi yayin da kowace wucewar dakika zuciyata take nunka gudunta har na fara tunanin idan na kara minti daya a wannan lokacin zata iya bugawa gabadaya. Bayan kaman wucewar lokutan dana kasa lissafawa, yayi gyaran murya, muryar shi lullube da wani irin embarrassment da daci yace “zan kira ki idan muka sauka Nafeesah” a hankali hannuna da wayar suka sauka akan gadona kamar wadda aka zare mata numfashi. Nayi imanin da ace Duniya da lokaci suna tsayawa da sai ince nawa sun tsaya, komi nawa ya tsaya cak. Bana fahimtar komi sai daci da sanyin jiki dana ji suna fita daga bakin Abbu, ban yiwa kaina adalci ba, sai dai ina bukatar sanyin rai dana zuciya. Ina bukatar farin cikin iyayena, nasan cewa definitely Mommy zata yi farin ciki da hakan Daddy ne dai ban sani ba, ni kuma I only need those four months, In shaa Allah kafin lokacin ya cika, “I’ll over come it!” na fada a fili cikin karfafawa kaina gwiwa. Karan bude kofa yasa nayi firgigit na kalli kofar, Mommy ta shigo tana kare min kallo, tace “kin yi bakuwa Ummiey” na kalleta da sauri, “bakuwa, wacece?” ta dan maida kanta wajen kofa tare da furta “shigo” Ikram ta shigo dakin bakinta dauke da sallama, da sauri na tashi tsaye ina amsawa, iso na mata zuwa gefen gadona ta zauna, Mommy ta juya ta fita ta barmu muna gaisawa, ruwa da lemu na dauko mata a fridge na dawo, muka zauna shiru a dakin saboda ba wani sabo muka yi da ita ba dama, can na katse awkward silence din nace “so???” ta sadda kanta kasa tana wasa da yatsun hannunta ta kasa magana, na dan yi murmushi nace “Kina son tambayar Abinda ke tsakani na da Harith koh?” ta kalleni cikin mamaki kafin ta gyada kai, nace “magana ta gaskiya Ikram babu abinda yake tsakani na dashi, duk abinda kika ga mun yi was just a plan, yana so ne yayi provoking dinki” ta nuna kanta da yatsa, “ni kuma? Why??” na zayyane mata labarin duk abinda kenan, Ikram tayi shiru kanta a kasa har na gama. Tace “yaki ya fahimce ni ne kawai, shekaru biyu kadai suka rage min a karatuna, menene a ciki idan ya hakura zuwa shekarun biyu?” nace “Ikram kina son Harith shima yana son ki saboda haka ni ban ga abin tada jijiyar wuya a wannan maganar ba. Shawarar da zan baki shine to just go for it, karatu baya hana aure kamar yadda aure baya hana karatu idan har kika maida hankalinki akan hakan” tayi shiru kamar mai tunani kafin ta kamo hannuwana ta rike, “nagode sosai Nafeesah. In shaa Allahu zan zauna in duba hakan, nagode” na danyi rubbing hannunta dake kan nawa ina murmushi Mun dan kara hira da ita kafin ta min sallama ta tashi, na raka ta har bakin titi ta samu abun hawa ta tafi ni kuma na koma gida. Da dare Daddy yake gaya min an sai min DE form a BUK, na turo baki nace “Daddy ni fa ABU nace maka ina so” yace “sun riga sun rufe saida basically ne shi yasa nasa aka nema miki BUK din” nayi shiru ina tunani, wannan shine kaka-kara-kaka din fa, ina gudun Abbu shi kuma yana kara bibiyata, nace “ni dai kawai na hakura sai next year” daga Mommy har Daddyn kallona suka yi, Mommy tace “sai mu saka ki a gaba muna kallo har shekara koh?” Daddy yace “Duk maganar zama bata ma taso ba, tunda an samu admission din ki daure ki tafi can din kawai” nace “amma a cikin hostel zan zauna koh?” Mommy tace “to in ba can ba ina? Dole can zaki zauna” Daddy ya daga baki kamar zai yi magana sai kuma yayi shiru kawai. Daga haka aka fara processing din nemar min admission a BUK. A gefe daya kuma naci gaba da karatu na. +
Sati daya, biyu, uku suka shude babu alamun kiran Abbu a cikin wayata, ban kuma sake jin magana game dashi ba. Tunanika iri-iri game da hakan babu kalar Wanda ban yi ba da wasi-wasi, kila ya hakura ne, kila maganar da nayi ta bata mishi rai, kila dama ba sona yake yi ba.”So sai kawai kika yi rejecting din golden opportunity like that?” cewar Ramlah. Zaune muke a lecture hall dinmu bayan mun gama lectures. Kwana biyu bana cikin natsuwata, walwala ta min kaura kamar yadda fara’a tayi kaura daga fuskata., a duk lokacin dana samu na kebance babu abinda nake yi sai tunani, Ramlah ta kula da yanayin da nake ciki yau dai ta rike ni sai dana fada mata abinda ke faruwa, ko babu komi naji dadin fada mata din da nayi. Tunda abin ya faru babu wanda yaji maganar, ni kadai nake juya abun a cikin raina. Fadar irin mamakin da Ramlah tayi ma bata baki ne, data hangame baki sai dana cika mata shi da popcorn sannan ta rufe. Na kai popcorn bakina tare da gyada kai, “babu wani zabi daya rage wannan Ramlah, kema kin sani” ta kura min ido, “akwai so many and n much more choices Babe, ke ce dai baki so zaba ba”. Muka yi shiru na dan lokaci, ta sake cewa “wai ba kince kina son shi ba?” na gyada mata kai, “then why did you do it? Bayan kin san zaki kasance cikin damuwa?” na kalleta sosai, “Ramlah, ina cikin rudani wallahi” ta girgiza kai, “no! Ki kike confusing din kanki dai, wannan abu ne mai sauki da cikin kiftawar ido zaki magance shi. Kina son mutum, then marry him mana, meye matsalar ki wai? You once fall for the wrong person yanzu kuma right person din yana sonki kina gudu da kafafun ki? Me kike so ne?” nace “so, kulawa, zaman lafiya Ramlah” tace “A cikin abinda kika lissafo wanne ne ba zaki same shi ba wajen Abbu?” nace “duka….. Ban sani ba ko Abbu yana so na ko baya sona ba. Ban sani ko dangin shi zasu karbe ni ko ba zasu karbe ni ba, ban sani ko iyayena zasu yi farin ciki da haka ko ba zasu yi ba….” ta katse ni, “wait don Allah. Shi Abbu da bakin shi yace baya son ki?” na girgiza mata kai, “ko Kadan. Yanayin acting dinshi towards me ne yake nuni da hakan. Ki duba ki gani tunda muka yi maganar nan dashi yau an wuce wata biyu amma koda wasa bai kira ni, bai taba nuna yana sona ba, bai taba furta cewa yana so na ba, a haka zan aure shi kuma? To ince nayi auren me?? Bayan haka alakar shi da matar shi is not in a good condition wanda hakan ya saka ni zargin cewa saboda ita yake so ya aure ni….” na zayyane mata duk irin yanayin zaman su dana sani da challenge dinsu akan karo aure, tayi shiru tana saurare na har na dasa aya. “shine nake jin tsoron na amince dashi kuma daga baya in zo ina dana sani” Ramlah hararata take yi kamar wata wadda na kashe mata da, tace “kin san Allah? Da ba don ke bace? Da sai na dalla miki mari. Wai me yasa ke kullum tunanin ki daban yake dana normal mutane?” nima na harareta, “kin fara ko? Meye laifina anan to?” ta dafe kai, “saboda kin kasa fahimta. Sai me idan Abbu baya son ki? At least yana so ya aure ki which means ko yaya ne yana admiring dinki., kuma ko ba jima zai fada tarkon son ki girl balle ma na riga dana san tuni ya fada” nace “me yasa kika ce haka?” tace “yadda ya dinga kallonki with so much tenderness and affection in his eyes ranar dinner din su Ni’imah, ke ko ba wannan ba kallon da mutumin nan yake miki da gaske na so ne” na girgiza kaina, “I doubt it Ramlah” wayana tayi karan shigowar sako, na ciro ta daga cikin jakata tare da bude sakon bakuwar number ce kuma har da karin alamun + wanda yake nuni da cewa sakon daga wajen Nigeria ne, cewa aka yi., ‘Let’s have a talk later please, I’ll call you nine pm on dot in shaa Allah. -Galadanchi’ hannu yana rawa nayi niyar maida mishi amsa Ramlah tayi saurin rike min hannu, na kalleta “meye?” tayi rolling idanu, “haba babe! Bashi kamar minti goma mana zuwa ashirin kafin kiyi reply?” nace “ban gane ba? He sent me a message, let me reply please” ta kwace wayar daga hannuna, “kin ce kin fada mishi baki son shi, then me kike so yayi tunani yanzu? Ya turo miki text, within a second kin maida reply as in you care dinnan, kinsan Allah mazan yanzu ba a musu haka koda kuwa wanda yake son ka ne balle ke da kike ikirarin kina son shi” na sadda kaina kasa, “Ramlah kin san halina sarai. Ban iya boye so ba kamar yadda bana iya boye ki, ba bazan iya yiwa Abbu haka ba” tace “at least try mana. Be like the classy girl you are, wannan yana da banbanci da son da kike yiwa normal mutane, ina gaya miki ta haka ne kadai zaki gane yana son ki ko baya son ki” na gyada mata kai a hankali. Ta dafa kafadata tana dan bubbugawa, “ban san irin son da kike mishi ba Nafeesah, amma zan baki shawarar ki dinga Addu’ah. In shi alkhairi ne a gare ki Allah ya baki shi, idan kuma ba alkhairin ki bane Allah ya canza miki da mafi Alkhairi” nace ina yi wallahi Ramlah, tace sai kici gaba dayi. Na gyada kai, “in shaa Allah, nagode sosai. Baki ji dadin da naji ba dana gaya miki wallahi” tace “kar ki damu, what are friends for after all? Naji ance BUK zasu fara registration da lectures dinsu next month, haka ne?” hirar mu ta koma ta makaranta, da yake ita university of Abuja zata koma, mun dan kara mintuna kamar ashirin muna hira kafin muka mike, na mata sallama na wuce gida ita kuma ta wuce hostel. +
Ban maidawa Abbu reply dinshi ba, amma tun kafin karfe tara ta cika na samu waje na zauna ina jiran shigowar kiran Abbu. Kamar yadda yace, karfe tara tana cika kiran shi ya shigo wayata. Na daga wayar tare da mishi sallama ya amsa, a nutse na gaida shi nan ma ya amsa tare da tambayar karatuna, ya dan ja ni da hira kadan kafin ya dulmiya cikin maganar data saka shi kira na. “Nafeesah ranar nan muna waya na katse sai kuma ban sake kira ba, na kara miki lokaci ne wanda zaki yi tunani a nutse don a tunani na a wancan lokacin baki zauna kinyi tunani bane shi yasa. Ina fata in ji different amsa daga gare ki wannan karon”. Nayi shiru ina tunani, wata marubuciyata tace wai ‘Opportunity comes once (Dama tana zuwa ne sau daya -Takori)’ ni kam yau dai ina so inyi wasa da tawa damar. Masu karatu kar kuga laifina. I am a girl in her twenties, a irin wannan age din babban abinda ‘ya Mace take bukata daga kowane namiji shine kalmar so, sai dai ni yana proposing din aurena ne kawai ba tare da nasan ainihin abinda yake cikin ran shi ba. In amince da auren shi ince nayi auren me? I can’t risk my happiness akan son zuciya irin nawa. Nayi gyaran murya a nutse nace “kayi hakuri Abbu, ina kan bakana har yanzu” ina dire aya ya tare ni, “why?” nayi shiru, yace “me yasa baki son Aurena ne?” nace “it’s obvious, saboda kai baban Hafsy dasu Abdullahi ne, kai Mijin Aunty Mubeenah ne, you are Niimah’s brother, Abby you Are My Father’s Friend…. How are you expecting me to accept your offer?” yace “just because of that?” na gyada kai kamar yana gani na, “yace but is it a sin? Abubuwan nan da kika lissafo dukan su ba wasu obstacles bane da zasu hana ni auren ki Nafeesah! Just tell me ba kya so na shi yasa ba zaki iya aure na ba” nayi shiru zuciyana tana bugawa, ina zan Iya furta wadannan maganganu? Yace “tell me Nafeesah!” cikin husky voice nashi wanda ya fara gauraya da bacin rai, nan ma shiru kawai nayi, zan iya karya akan komi amma banda karyar kin Abbu, ba zan iya ba. “Goddammit Nafeesah! Me kike son nayi for goodness sake?!” wannan Karon bacin ranshi ya fito baro-baro, ya cigaba “kina bukatar ki ganni akan gwiwa na ina rokon ki akan ki aure ni? Ko kuma so kike yi in dinga binki sahu-sahu kamar yaro ina shelantawa duniya ina son in aure ki sannan zaki yarda?” na danyi chuckling a hankali, that is so childish. Yayi shiru kafin inji ya fara magana wannan karon a hankali kuma very calm, “ok, ok. Maganar su Hafsy da kike yi Nafeesah ina tabbatar miki they will be more than happy idan suka ji cewa zaki auri baban su saboda suna Son ki Nafeesah, sun dauke ki da muhimmanci sosai fiye da tunaninki, haka ma su Ni’imah, Dad dinki kuwa has already given us his Blessings. M just trying to be a nice guy anan kin gane? Bana so ne a miki abinda ba kya so ne kawai shi yasa, Mubeenah kuma wannan ba damuwar ki bace, ba lallai sai da blessings dinta ne zamu yi aure ba, Are we good now?” nace “still Abbu…..” ya katse ni, “kina da wanda kike so ne?” nayi shiru ban amsa ba, jin shirun da nayi yasa ya sha jinin jikin shi, “akwai k akwai kenan koh?” nan ma nayi shiru, yayi kwafa “just wait till I come back. I will not let you go that easily Nafeesah, Aure a tsakanin mu kamar an daura ne Nafeesah coz you are mine! Saboda ni aka halicce ki ba dan wani ba. Zan baki sauran watanni biyu da suka rage min anan don ki tsara yadda Rayuwar ki a gidana zata kasance. Ina dawowa daurin auren mu ba xai dauki lokaci ba Nafeesah in shaa Allah…. Bari in barki haka, sai da safe” da kyar na iya daga baki nace “A tashi lafiya” kusan a lokaci daya muka katse wayar dashi. Na kai hannuwana duka biyun na tallabo kumatuna dasu, Abbu da gaske yake. Wani bangare na zuciyata yana murna da hakan yayin da wani sashen yake jimami da tantama, tantama akan in amince ko inyi akasin haka? Jimami kuma na ya makomar rayuwata zata kasance idan na amince din???
Daga wannan ranar kusan kullum sai mun yi waya da Abbu, yawancin lokuta zai kira ya tambaye ni karatuna da sauran su, bai sake tada min zancen auren ba, hakan shi yake kara jefa zuciyata cikin wasi-wasi. I mean yadda nake ji ana fada ko kuwa dai mostly yadda ake yi a cikin film, a situation irin haka zaku ga Namiji ya shiririce a gefen mace going to the moon and black, proposing ta hanyoyi daban-daban, amma shi Abbu babu alamun haka a tattare dashi. Idan text ya turo min babu kalmar so ko daya da nake tsinta a ciki haka ma idan muka yi waya dashi, amma kulawa kam ina shan ta, kullum cikin tambayar lafiyata da Al’amuran rayuwata yake. Hakan shi yake kara jefa ni cikin tunani., Abbu Wane irin mutum ne shi kam?? High waist blue jeans, shabby coffee color T-shirt, black veil rolled, black and white kimono, jakar poshter rataye a kafada, one last look a jikin mirror na tabbatar dana fita yadda nake so. Yau ne ranar da zan zana exam dina na karshe a Kasu, probably rana ta karshe da zan taka kafana zuwa cikin makarantar idan ba da wani dalili ba dai. Na saka sneakers a kafada baki tare da daukar wayar hannuna na fita, karfe tara lokacin dana fita bakin titi, kafin in isa Kasu tara da rabi tayi already don haka exam hall dinmu kawai na wuce. Kyawawan awanni biyu suka wuce kafin mu fito, daga nan bankwana muka yi da abokanan nan mu muka wuce gida, Ramlah tun a ranar ta wuce Kano zata je ta fara shirin wucewa Abuja. Nima nasan lokacin da nake dashi a Kaduna ba mai yawa bane kafin in wuce Kano saboda BUK tuni sun fara lectures dinsu tun kimanin satika biyu da suka wuce. Na koma gida na samu tarba ta musamman a wajen Iyayena, wata kwaryar liyafa suka hada min inda en uwa suka taru wajen taya ni murnar kammala karatuna, I didn’t expect it but I was happy and touched. Soyayyar da Iyayena suke min abu ne mai matukar wahala in iya fayyacewa masu karatu irinta. Kwana biyu ina gida bana fita ko nan da can ina aikin barci da relieving din stress din exams. Bayan na huta completely na fara shirye-shiryen wucewa BUK tare da iyayena. Ranar Lahadi da misalin karfe hudu na yamma, tafe muke a kan titin daya dauki hanyar fita Kaduna zuwa Kano a cikin motar Daddy Hillux, tare da Mommy, Anty Uwani da Sultan. Duk wasu abubuwa da zan bukata suna bayan motar da muke ciki, komi game da karatuna ya riga ya hattama a waje guda, abinda ya rage kawai shine shiga dakin daukar lacca a gobe litinin. Anty Uwani da Mommy bakinsu yaki rufewa wajen bani lecture Akan zamantakewar cikin makaranta, rayuwa ce da zan hadu da mutanen da ban sani ba kuma inyi rayuwa dasu, nasihohi da shawarwari dai. Mun shiga cikin BUK da misalin karfe biyar da rabi. Mommy da Anty Uwani suka taya ni shirya dakin da aka kaini, mun samu occupant daya a dakin luckily musulma ce kuma bahaushiya da alamun kuma zata yi kirki. Su Mommy suka taya ni gyara kayana da hattama su waje guda. Sai bayan sallar Magriba sannan suka juya, ni da Firdausi roommate dina muka musu rakiya har parking lot. A gabanmu Daddy yaja motar suka tafi muna daga musu kallo, ina kallon su har Motar ta bace mana daga gani. Iyayena suka tafi suka barni a bakon gari, bakon waje, again, for the second time. Na kai yatsa na dauke siririyar kwallar data tarar min a ido, wannan yana daya daga cikin challenges da ‘ya mace take fuskanta a rayuwarta, wannan temporary ne ma fa, zan iya zuwa in gansu a duk lokacin dana ga dama kuma na bushi iska, to ina ga nayi aure kuma? Muka juya muka koma cikin hostel Firdausi na min dariyar kukan da nake. Sallah muka yi naci abinci na jira aka kira isha’i nayi kafin nayi shirin kwanciya barci na kwanta. Sai dana janyo wayata kafin naga alamun shigowar sako, ban san yaushe ya shiga ba amma ina tunanin lokacin da nake sallah ne. Zuciyata ta shiga bugu da tsallen murna lokacin dana ga sakon daga Abbu yake, yaushe rabon da inji muryar shi? Tunda muka fara exams ya daina kirana sai dai yana turo min text akai-akai. Yau ma kamar koda yaushe ko ince ko wane lokaci, ya nake? Ya su Daddy na? Ya kara da min lale maraba da zuwa makarantar BUK sai abu d’aya daya kara, cewa yayi; “Kar in saba da zaman hostel dinsu da wuri, saboda soon…. Very soon zan bar hostel din, saboda yana dawowa zai dauke ni daga hostel din” na turo baki kamar yana ganina, “wai ya daukeni kamar wata er tsana” sai kuma na kwashe da dariya ina birgima akan gadona, Abbu bai san cewa nima jiran dawowar tashi nake yi ba ne kome? He kept bragging about it, koda yaushe cikin zancen in jira dawowar shi yake making me go curious akan me zai faru idan ya dawo din. Ina lissafe da kwanan wata, ya daura akan wata hudu din da yace zai yi. Mommy ta kira ni muka gaisa tare da tambayata yanayin wajen nace mata lafiya, bamu yi wani hira ba saboda yadda nake jenake jera hamma tace inje in kwanta kawai, nan muka yi sallama tare da kashe wayar. Addu’ar kwanciya barci nayi tare da lumshe idona, a tunani na barci zai kwashe ni a take saboda yadda nake a gajiye amma ina! Rayuwata a gidan Abbu, iyalinshi dashi kanshi, tun daga ranar dana fara ganin su har zuwa yau ta fara min yawo a idanu, nayi juyi akan gadona a karo na barkatai ina tambayar kaina tambayoyin dana kasa samun amsar su suma a karo na barkatai, will it be okay? Zan iya kuwa? +
*****
Zama a makarantar sam bai min wahala ba kamar yadda nayi zato, everything was simple and easy. Rana ta farko dana fara shiga lectured na ziyarci department din su Ni’imah, da kyar na iya gane matar nan. Ta kara fari, tayi kiba Masha Allah da ganinta kaga wadda take cikin afuwar rayuwa kila kuma har ma da albarkar aure. Ta jefe ni da harara lokacin dana yi maganar, “dallah ke har kina da bakin yin magana ne ma? Ai banyi niyar neman ki ba saboda naga kin manta da mutane. Wai Nafeesah kamar ni ace zaki zo Kano amma bamu samu labari ba, bayan nan yaushe rabon da muyi waya dake??” na dan rungumota ina dariya, “haba Amaryas tuba nake, bana so in katse muku amarcin ku ne shi yasa bana kira, kuma ma lately abubuwa ne suka min yawa wallahi shi yasa” ta janye jikinta daga nawa, “ke ai dama ba a kama ki da laifi, kullum kina da abun kare kanki” nayi dariya tare da kamo hannunta, “kin fa kara kyau wallahi, da alamun dai Bashir ya iya kiwo” tayi fari tana murmushi, “ai kawai ina shawartar ki ki tsunduma cikin auren nan kema Nafeesah, only then ne zaki fahimci abinda rayuwa take nufi. Nasan cewa sai kin nunka yadda kike da kyau yanzu wallahi” na sadda kaina kasa cikin tunani, ‘ko yaya zata ji idan ta samu labarin Yayanta nake so, kuma yake so ya aure ni? Kila fa zumuncin mu ya tsaya koh?’ ta zunguro ni, “lafiya?” nayi saurin girgiza mata kai. Nan na zauna na jira ta gama lecture kafin muka je wajen Sa’adiya, ita dinma dai ta kara kyau da haske da kiba. Daga nan muka wuce hostel, a can muka yi la’asar muka ci abinci kafin muka dasa dandalin hira sai wajen biyar da rabi mijin kowaccen su yazo ya dauketa suka tafi. To haka rayuwar cikin makarantar ta kasance min, kullum idan bana daki to ina lecture hall, daga lecture hall kuma sai daki. Cikin sati biyun da nayi a can tuni na saba da mates dina duk da dai har lokacin ban yi sabbin abokai ba don bani ma da ra’ayin yi, Ramlah ta ta ishe ni rayuwa. Nayi sighing a hankali tare da rausayar da kai lokacin dana tuno ta, kwana biyu ma bamu yi waya da ita ba, kewar ta na taba ni da….. Nayi saurin katse tunani na. Na tashi daga kan seat dina na fara gyara zaman jakata a kafada ta, Zakiyyah ta kalleni “har kin gama assignment din?” na girgiza mata kai, “na gaji ne, I’ll finish it anjima” ta gyada kai, na mata sallama na fita daga cikin class din. Sanye nake da da riga da zani na atamfa, dinkin zanin single ne kamar yadda rigar take fitted, ban tsaya wani daurin dankwali ba na dora hijabi akan kayan wadda ta kusan sauka har gwiwa na. Yanayin garin na yau aka rana kuma da zafie, kowa dai yasan yadda Kano take idan damina ta fara shigowa. A hankali nake takawa ba wai don yanga ko wani abu ba, saboda tsabar gajiyar dake tattare dani, yau tun karfe bakwai muka shiga lacca, gashi yanzu har to five amma ban saka abun kirki a bakina ba tun karin safe. Sai dana fito daga farfajiyar da classes dinmu suke na bi wani dan karamin corridor da zai sada ni da gate din fita daga cikin department dinmu, a bakin gate din can inda aka tanada saboda ajiye motoci, wata farar Picanto ce anyi parking dinta ta yadda duk wani wanda zai fito daga wajen da nake fitowa zai yi ido biyu da motar. Yeah motar ta hadu karshe haduwa ta kuma cancanci kallon da jefi-jefi din mutanen dake wucewa suke jifanta dashi. Sai dai a gareni ba motar bace ta dauki hankali na ba, mamallakin motar ne da yake tsaye a gefen motar ya juya min baya yana amsa waya. Sanye yake da baggy pants da shara-sharan farar T-shirt don har ana iya hango farar singiletin dake jikin shi, na ja na tsaya a hankali idanu na kafe akan mutumin. Well I didn’t want to jump into conclusion din ko waye duk da nasan cewa halitta ce da ko mutuwa nayi na dawo zan shaida ta. Sai dai wannan ta banbanta da wanda na sani, yadda fatar jikin mutumin da bakar sumar kanshi suke sheki a cikin hasken ranar ya saka ni doubting Anya shine? Kamar Wanda yaji wasi-wasi da tantamar da Zuciyata take ciki, a hankali ya juyo ya sauke idanunsa a kaina, and there He is, Abbu Galadanchi standing right in front of Me……Kamar daga sama naji saukar maganar tashi, na zaro ido sosai. Ban taba zaton zai kawo maganar yanzu ba shi yasa na rasa irin excuse din da zan bashi ma don haka nayi shiru ina jin kafafuna suna rawa a hankali, dama ta yaya nake tunanin tsayawa da kafafuna under Abbu’s gaze?? Yace “ina jin ki Nafeesah, last time dana tambaye ki baki bani amsar data gamshe ni ba, yanzu na sake tambayar ki ina bukatar jin gamsasshiyar amsa wadda zata yi convincing dina, so gaya min, me yasa baki son aurena, na miki tsufa ne?” da sauri na girgiza kaina, “baki so na?” na zaro ido ina muzurai, me ya kamata in ce? Yace “kince kina da wanda kike so kuma ni na tambaya a gidanku ance babu kowa, Nafeesah! Dana ce ina son auren ki ba wasa da hankalin mu naso muyi ba, kada kiyi tunanin nima ban hango ko tunana abubuwan da kike hangowa ba, amma meye a ciki? Babban abin bukata Anan shine ace muna son junanmu kuma muna da muradin kasancewa tare, then babu abinda zai faru, there’s no body that can criticise us saboda akan gaskiyar mu muke. Enough of all this Nafeesah, na gaji, na gama baki iya uzirin da zan baki, yanzu amsar ki nake so kawai, aure yes ko a’ah?” fuskata ta taru da kwalla, me yake so inyi a irin wannan lokacin idan yazo min da magana kai tsaye yana bukatar amsata? Ya kalle ni da mamaki, “kuka? Na bata miki rai ne?” nayi saurin girgiza kai, “to menene?” nace “I just need time to think over it” ya shafa sumar kanshi, “Lord! Wani lokaci kike so kuma bayan duk lokacin dana baki? Dana ce miki na gaji Nafeesah I mean it, and I don’t have the heart to wait any longer” na dan rausayar da kaina gefe, wannan abun fa nice zanyi shi, idan ma da wani abu I’ll be the one to take the responsibility, me yasa ba zai barni in yanke hukunci da kaina ba? Yace “ok…. ok… Naji. But believe me Nafeesah, wannan shine lokaci na karshe da zan baki, idan baki yanke shawara ba I’ll just do it on my own way, Allah yasan cewa na baki hakkinki” na dan jijjiga kai, ya bude bayan motar ya ciro dan karamin kwali ya miko min, ba musu nasa hannu na amsa tare da mishi godiya, ya bude motar ya shiga tare da mata key, na dan ja baya har yayi ribas, ya kalle ni yana murmushi, “any sako for pretty??” nima nayi murmushin, “a gaida min ita sosai, ace mata nayi kewar ta” ya gyada kai, “well, kiyi duk iya kewar ta din da zaki yi kafin kizo kema kiyi naki babyn na kanki” na zaro idanu yayin daya saki murmushi gami da min wink yaja motar ya wuce ya barni da bin shi da kallo kafin na girgiza kai ina murmushi na wuce cikin hostel. Firdausi bata dakin, na ajiye kayan hannuna akan gado naje na watsa ruwa tare da dauro alwalar sallah na fito, lotion kawai na murza a jikina na saka kayan barci tare da daura zani a saman kayan nayi sallah, dana gama na dauko Al-Qur’ani Mai Girma ina karantawa har aka kira sallar isha’i nayi tare da Shafa’i da Wutiri, ina cikin nade abun sallar Firdausi ta dawo, na mata sannu da zuwa ta amsa. Waya na dauka na kira Mom muka gaisa tana tambayana karatu na amsa mata da lafiya lau, naso in tambayeta dalilin da yasa bata son Aurena da Abbu sai kawai nayi shiru, na mata sai da safe tare da kashe wayar. Anty Shafa na kira muka gaisa, mun jima muna hira da ita tana kara bani shawarwari akan rayuwata, tace idan har ina son Abbu I should just go for it, na mata godiya muka yi sallama. Na janyo assignment dina na karasa, lokacin dana gama karfe goma tayi already, kwanciya nayi ina tunanika a cikin raina. I think I should just give it a try kamar yadda Anty Shafa tace, after all ba wani sabo ne muke shirin aikatawa ba da nake kokarin kashe kaina saboda son faranta ran mutane wanda nake tantamar ko zasu ga farin abinda nayi at the end of the day?? Nayi murmushi tare da lumshe idanuna, ba jimawa barci mai dadi ya daukeni
*****
Washegari da safe sai ga kiran Anty Ameenah a cikin wayata, da mamaki na daga muka gaisa da ita, tambayana tayi ko ina free yau? Nace mata ina da class dai amma karfe biyu zan gama, tace how about we have a cup of tea a Flower Garden by four?? Nace mata ba damuwa. Muka yi sallama tare da kashe wayar. Na ajiye wayar a hankali daga kasan raina ina tambayar ko lafiya take son ganina? Curiously.Muna fitowa daga lectures masallaci na shiga nayi sallar La’asar daga nan na wuce flower Garden. Anty Ameenah tana zaune a daya daga cikin kujerun da aka tanada, tana hangoni ta fara waving dina tana murmushi, nima murmushin nayi na karasa gareta, kujera naja na zauna ina fuskantar ta, na gaisheta ta amsa tana tambayata abinda nake so a kawo min nace a bani egg roll da lemu don tun safe da zan fita dana sha shayi ban kara komi a cikin cikina ba, aka kawo mana egg roll, meat pie burger da lemun peach. Anty ta kalleni tace “Allah yasa ban takura miki ba da nace ina son ganin ki?” nayi saurin girgiza mata kai, “haba ko kadan wallahi” tayi murmushi tare da gyara zamanta akan kujera, “da farko ban yi niyar sa baki ba akan maganar wannan sai dai ina ga lokaci yayi daya kamata in saka baki, ba shisshigi nake miki ba amma ina so inji inda maganar ku ta kwana?” na dubeta cikin mamaki, “Anty wace magana kenan?” tace “maganar ku da Ibrahim mana!” sai dana kusa zubdo da abinda nasa a bakina saboda maganar da naji cikin bazata. Ta miko min tissue na goge bakina tare da korawa da ruwa, Anty Ameenah tace “m sorry idan baki so hakan ba” kai kawai na girgiza mata, amma a kasan raina ina mitar me yasa don kawai Abbu yana son aurena sai kowa a cikin dangin sa ya sani? Kamar wadda take karanta mind dina, tace “kada fa kiyi zaton Ibrahim ne ya gaya min ko ya turo ni, bashi bane. Kwanakin baya dai ya taba neman shawarata akan cewa yana so ya aure ki, me nake gani? Naji dadin hakan sosai, wallahi abu ne wanda ya jima yana min amsa kuwwa a cikin kaina, tun ranar farko dana fara ganin ki Nafeesah na yiwa Ibrahim sha’awar kasancewar ki matar shi, sai dai sanin halin Ibrahim yasa na kame bakina nayi shiru. Ba tun yau ba nake mishi maganar kara aure amma sai ya wawantar da maganar, ba ni Kadai ba Hajiyar mu ma tayi nata kokarin ganin irin zaman da yake yi da matar shi but to no avail. Amma jin da kanshi yazo yana ce min yana sha’awar kara aure nasan cewa da gaske yake, Ibrahim baya nuna bukata akan abinda yasan baya so, musamman akan zancen nan Nafeesah, I’ve seen something different in him. To kuma tun daga lokacin har yanzu ban sake jin yayi magana game da hakan ba, last time dana mishi maganar ma sai ya sake wawantar da ita, ni kuma gaskiya na kasa mantawa da zancen shi yasa nace bari in tuntube ki da kaina inji” nayi shiru tare da sadda kaina kasa, ince me? Tunda ni a karan kaina ban san ya muke ciki ba. Anty Ameenah ta kamo hannuna ta rike cikin nata, “look Nafeesah! I am not trying to persuade you or something else…. I just…. I mean ina cikin eagerness nason ganin rayuwar kanina tayi haske, ya samu farin ciki da kwanciyar hankali a cikin rayuwar auren shi. It has been good thirteen years tun auren shi da Mubeenah, aure ne aka musu na zumunci, ita diyar wani abokin Alhajin mu ne. Tun daga auren su Ibrahim ya rasa farin cikin shi, he was young, amma bai dandani abinda matasa kamar shi suke dandana idan suka yi aure ba. Ya rasa jin dadin yarintar shi a wajen yarinyar da bata san darajar shi ba saboda kawai bata son shi. A matsayin Ibrahim na namiji ya hakura da auren dole din da aka mishi amma ita ta kasa hakura, a wajen Mubeenah ne kadai na karyata maganar bahaushe da yace duk kiyayyar da mace take wa namiji da sun fara haihuwa take dawowa so, a gareta kam sai kiyayyar ta koma har kan ‘ya’yan shi. You wouldn’t believe me Nafeesah, lokacin da ta samu cikin Abdullahi da kyar ta iya haifeshi, Allah ne kawai ya nufa zai zo duniya amma sai da tayi attempting din zubar da cikin sau biyu, haka aka zo aka sha dabi da cikin Qaseem, daga haihuwar Hafsat taje aka saka mata loop a cikinta ba tare da sani ko yardar Ibrahim ba. Bata dauke mu a tsiyar komi ba, sai mu hadu da Mubeenah a hanya idan ba dama ta gani ba ba zata mana magana ba, idan mu mun mata sai ta ga dama take amsawa. Babu yanda bamu yi da Ibrahim ba akan ya kara aure amma ya ki, yace baya so yaci amanar da marigayi mahaifin Mubeenah din ya bar mishi akan ya kula da ita da farin cikinta, shi a ganin shi cin amana ne idan ya kara aure. Haka Ibrahim ya rayu tsayin shekarun nan, ya danne farin cikin shi saboda matar da bata san yana yi ba, wadda bata appreciating dinshi da dangin sa har ma da ‘ya’yan shi. Wallahi baki ji farin cikin da nayi ba lokacin da naji cewa ya shirya fitowa daga cikin ukubar daya sa kanshi a ciki ba, shi yasa kwata kwata naji na kasa yin hakuri in zuba ido ki kubuce masa Nafeesah” jikina gabadaya yayi sanyi, ban taba sanin cewa irin rayuwar da Abbu yayi ba kenan, koma yake kan yi. Anty Mubeenah kam wace irin mace ce? Anya akwai sauran mata irin ta a duniyar mu ta yanzu? Anty Ameenah ta shafa hannuna tace “kinyi shiru?? Baki son shi ne ko kuma ya miki tsufa??” na girgiza kaina ina dan murmushi, “ban taba mafarkin kasancewar wani mutum a matsayin mijina ba sai Abbu Anty” farin cikin dana hanga a cikin idanuwanta abun baya misaltuwa, na sadda kaina kasa cike da kunya ina jin kamar kasa ta tsage in shige. Tace “amma me yake hana ki cika burin ki?” nace “ina jin tsoron abinda zai je yazo ne, my mom seems to be strictly against it. Sannan ban san me zai je yazo ba a rayuwar auren Abbu da Anty ba, bana son abinda zai tarwatsa musu rayuwar auren su da kan iyalinshi” Anty tace “believe me Nafeesah! You are not. Allah kadai yasan iya ceton ran da zaki yi, wallahi babu abinda zai faru a rayuwar gidan Ibrahim sai ma farinciki dana san zai wanzu in shaa Allah, ke kadai ce wanda zaki iya yin wannan aikin saboda na tabbata Ibrahim yana son ki. This the first time in my life da naga Ibrahim wanting something very badly kamar ki, na tabbata idan ya rasa ki sauran rayuwar shi will be shattered to pieces. Naji dadin wannan lamarin sosai, ina tabbatar miki da cewa you are the perfect match for Ibrahim. You suits each other, na tabbatar da zai kula dake, zai so ki. Kada kiyi zaton saboda shi kanina ne wai nake koda shi, ba haka bane. Saboda na yarda da Ibrahim na kuma yarda da halayen shi. Ki kwantar da hankalinki In shaa Allah babu abinda zai faru sai Alheri, in shaa Allah ba zaki taba yin nadamar Auren Ibrahim ba kamar yadda na tabbata zaki kasance a cikin farin ciki matukar kina amsa sunan Matar shi. So dear, stop holding yourself in and just go for it, kiyi abinda kike son yi kafin lokaci ya kure miki, Allah ya Albarkaci rayuwar ki” na sadda kaina kasa ina jin wani irin confidence da kwarin gwiwa yana shiga ta. In shaa Allah ba zan kara rike kaina ga yin abinda nake son yi ba, da yardar Allah zan zama mallakin Abbu tun kafin ya subuce daga hannuna ya sa in tagayyara. Anty Ameenah ta kara bani shawarwari kafin muka mike muka fita daga cikin garden din, har inda tayi parking din motar ta na raka ta. Ta bude motar ta shiga, ta mika hannunta baya ta dauko Leda mai dauke da tambarin kamfanin shop rite ta miko min, naso nokewa in ki karba amma ya kamo hannuna ta dora min ledar a tafin hannu dole na karba tare da mata godiya, tace “babu komi Ameenah, and please make sure to make it very fast” na sunne kaina a kasa ita kuma ta tashi motar ta tafi.
Tarkacen kayan makulashe ne ta kawo min, dambun nama, cookies da tarkacen biscuits sai turare masu kamshi a cikin ledar. Na bude biscuit din short bread na kai bakina na cinye tare da korawa da lemu, kwana biyun nan abubuwan dana mayar abincin cina kenan. Bayan nayi sallahr Isha’i na gama shirin kwanciya, na kwanta akan gadona tare da janyo pillow na rungume a kirji na, Maganganun Anty Ameenah suka fara dawo min a cikin kaina. Na tsinci kaina cikin mutuwar jiki tare da jina ina narkewa akan katifar da nake kwance. Allah sarki Abbu! Ban taba zaton cewa rayuwar auren shi munin ta yayi yawa har haka ba, na kara juyawa a akan gadon. Poor Abbu! Da yardar Allah sai na zama dalilin sharewar hawayen shi da yayi ta zubarwa a shekarun baya, in Allah ya yarda sai na zama haske da fitila a cikin rayuwar Auren shi. Da haka na lumshe idanuna barci ya dauke ni, idanuwa brown masu sheki da kyalli suna gagari a cikin duhu. 3
*******
Da kuzari sosai na tashi a cikin jikina ranar, tunda nayi sallahr Asubahi ban koma barci ba saboda ina da laccar safe, nayi wanka na shirya abin karyawa kafin na shirya jikina cikin riga da siket na leshi ruwan ganye dinkin yayi min cif a jikina, shi bai yi yawa ba kuma bai yi kadan ba. Ina cikin karyawa dinne na kira gida muka gaisa dasu, anan ne Daddy yake fada min cewa result dinmu na KadPoly ya fita kuma yayi kyau sosai, nayi hamdala tare da godewa Allah. Yace ya riga daya turawa Abbu da result din don a kammala shigar da takarduna a cikin BUK tunda dama awaiting result ne, nace mishi babu damuwa, daga nan ya ba Mommy muka gaisa da ita har take fada min ansa auren Hansa’u diyar Kawun su Daddy nan da watanni hudu, na musu fatan alkhairi sannan muka yi sallama da ita. A gurguje na karya naja gyale yellow mai yalwar fadi da flat din takalmi shima yellow sai jakar littafai da wayar hannuna na tafi. Kimanin mintuna arba’in muna jiran zuwan Mrs Adayi matar da take daukar mu Intro. Physiology amma shiru bata zo ba har karfe tara tayi laccar daya kamata ace tun karfe takwas aka fara ta. Na kalli agogon hannuna tare da dan jan tsaki, bana son abinda zai bata min lokaci duk da cewa bani da wani class din sai two, amma ina son ganin Abbu kafin ya tafi gida wanda nasan cewa muddin ta shigo sai ta cinye lokacin data batar a waje. Wajen karfe tara da rabi class rep yayi announcing din isowar lecturer din, nan da nan ajin yayi shiru daga hayaniyar daya dauka. Kofar hall din ta bude aka shigo, cikin takun nan nashi mai cike da kasaita da natsuwa ya taka har zuwa gaban allo. Ina jin irin sautin woah! Daya dinga fita daga bakin mates dina mata da kuma kus-kus din da suke yi sai dai hankali na baya kansu, yana gaban allo ina kallon halittar dake tsaye, sanye cikin suits navy blue da farar shirt sai navy blue din neck tie kafar shi sanye da bakin cover shoe, fuskar shi mai cike da kwarjini da ilhama tana ta shinning a cikin hasken ranar daya shigo, nasan dole dama enmatan ajinmu su rikice da ganinshi a yadda yayi kyawun nan, looking soo take away. Daga sama na dinga jin muryar shi lokacin da yayi introducing kanshi as Doctor Ibrahim Galadanchi, zan koya mana course din a madadin Mrs Adayi wadda ta samu accident din mota a daren jiya, zai daukeni course dinne har zuwa lokacin da zata warke. Ya lalubo idanuna ya rike da nashi idanun na en sakanni kafin ya janye idanunshi zuwa ga sauran dalibai yana wani smirking, “alright, can we start now?” gabadaya ajin ya dauki sowar “yes” Ya Allah! Ni kam na kasa tantance a wata duniya nake, har ya gama gabatar da darasin ranar cikin kwarewa da tataccen turancin nan nashi babu abinda na iya tsinta sai idanunshi dake karakaina a jikina suna kara hana ni natsuwa, A Father’s Friend! A Lecturer! Way to go Nafeesah!! Ta yaya zan iya dealing da responsibilities dinnan?? Ya rufe littafin hannunshi tare da maida marker dinshi cikin cover dinta yana kallon en ajin, “let’s call it a day here” kowa ya fara maida littafin shi cikin jaka, ba bata lokaci ya dauki brief case dinshi ya tunkari kofa bayan ya haske ni da wani irin kallo wanda yasa naji gabban jikina sun koma kamar ruwa, Abbu will really be the death of me!! Dalibai suka fara fita daga cikin class din amma ni ina zaune kikam kamar gunki, sai da Jalila wadda muka zauna seat daya da ita ta dan daddabe ni sannan na dawo cikin natsuwata, tace “Nafeesah lafiya? Tun dazu na kula kamar baki cikin natsuwar ki” na girgiza mata kai, “lafiya ta lau, kawai na dan gaji ne” tace muje koh? Na jinjina kai tare da mikewa tsaye, ina tashi karan shigowar message a wayata ya tsaida ni; Abbu ne. Cikin rawar hannu na daga, “meet me at room 13, Dept of Physiology, lecturers lounge” abinda yace kenan, na kalli Jalila ina dan murmushi nace “sorry, ku tafi kawai, akwai inda zan biya yanzu” tace ok, tare da wucewa. Ni kuma na tafi zuwa kiran Abbu. Ofishin shi shine na karshe cikin jerin offices din lecturers din dake wajen, na tsaya a bakin kofar ina kara kallon name tag dinshi dake rataye a jikin kofar an rubuta ‘Dr. Ibrahim Mas’ud Galadanchi’ na shafi sunan da hannuna tare da lumshe idanuna ina dan murmushi, Abbu! What have you done to my innocent soul?? A hankali nayi knocking a bakin kofar, cikin husky voice dinshi yace “yes come in please” na tura kofar a hankali na shiga, kafafuna suka nutse a cikin wani tattausan zagayayyen carpet an rubuta welcome a jiki, tattausan kamshin air freshener da sanyin split suka doke ni har sai dana saki ajiyar zuciya saboda sanyin dadin daya ratsa ni. Yana zaune a gaban desk top yana aikin typing, ya cire suit din jikin shi sai shirt din kawai ya bari, you have no idea irin kyawun da yayi mun a lokacin. Ofishin nashi babba ne, shelves shelves ne na littafai tun daga na bokon har na Arabi a kowace kusurwa ta Ofishin, sai desk da dai duk wasu tarkace da zaka samu a cikin Ofishin manyan laccarori da boko ta gama ratsa su. Ya dago kyawawan idanunshi daga kan desk top din da yake aiki a kai ya kalleni, murmushi ya saki mai sanyi wanda ban san lokacin dana mayar mishi da martani ba. Ya nuna min kujera alamun in zauna, ba musu naje na dan dosana kamar wadda za ace mata ar! Ta karta a sukwane. Na nutse nake bin Ofishin nashi da kallo, baby wasu tarkace da zasu saka mutum ciwon kai, komi a shirye kuma cikin tsari. A hankali ya daga baki yace “plss make me a cup of tea” na daga kai na kalleshi a hankali, ya wani langwabar da kai gefe kamar wani karamin yaro saura kiris in kwashe mishi da dariya. Na ajiye jakar hannuna akan kujerar na mike na kunna electric kettle dana gani a jikin socket, ya nuna min inda cups da sauran kayan shayin suke ruwa yana tafasa na hada mishi na kai na ajiye mishi, ya kalleni “thanks…. Ke fa?” na girgiza mishi kai. Aikin shi ya komawa yana yi yana dan sipping din shayin nima na koma na zauna. Ban jima ba naji ya kashe computer din, karan matsawar kujera alamun ya tashi daga inda yake, ya zauna akan kujerar shi wadda take fuskantana. Shayin shi yaci gaba da kurba idanuwan shi suna kaina, kaina yana kasa ina wasa da yatsun hannuna, ji nake kamar wanda rami zai bule daga cikin fatar fuskana saboda zazzafan kallon Abbu a kaina. Ya ajiye cup din akan teburi tare da dan matsowa daga kan kujerar da yake, yace “toh Nafeesah, yau dai ina so inji abinda kika yanke game damu, ya ake ciki? Na fada miki na gaji da jiran ki haka nan, na gaji da yawo da hankalin da kike min. This is the last time da zan tambaye ki, bayan shi ba zan kara ba Nafeesah I promise you don ni dai ba karamin yaro bane, so m asking you, me kike yanke game damu??” Zuciyata was beating very fast and erratically kamar wadda tayi gudun marathon, kaina, yatsa, gangar jikina da komi ma na jikina sun yi mun wani irin nauyi marar misaltuwa amma duk da hakan ban fasa daga kaina na nake jin ya koma kamar wani gingimemen dutse ba na kalleshi, fuskar shi was mixed of emotions, fargaba, hope, plead, idanunshi da suke matukar burge ni sun shige ciki, nasan da ace idanu suna magana dasu ne zasu yi rokon da nake gani akan fuskarshi tunda bakin shi ya gaza furtawa. A lokacin na gama yin concluding cewa farin cikina koma ince namu a yadda na karanci fuskar Abbu a lokacin, yana tattare damu ne, yayin da makullin kofar take hannuna, that means ni kadai ce zan iya bamu farin cikin da muke bukata kenan??
A hankali na sadda idanuna kasa, na tattaro duk kwarin gwiwa na tare da gyada kaina a hankali….Na kasa tantance abinda ke zane akan fuskar Abbu a lokacin, murmushi yake yi sosai, amma zan iya rantsewa akan cewa na hango alamun moistness a cikin idanunshi, ban san me zai faru ba nan gaba, ban san ya zamu kare da Mommy ba sai dai irin farincikin dana gani a tattare da Abbu yasa naji duk wata fargabata ta barni, idan dai har zan dinga ganin irin wannan kallo daga Abbu to ban damu da duk abinda zai faru ba, nasan cewa murmushin Abbu ya ishe ni. Ya dauki mintuna da dama bai yi magana ba ina jin yana containing farin cikin dake cin shi ne, yayi gyaran murya yace “nagode sosai Nafeesah, amincewar ki da yardar ki a gare ni sun dadada min sosai you have no idea, in shaa Allah na miki alkawarin ba zaki yi nadamar aurena ba, Mrs. Ibrahim Galadanchi!” na kai hannuna biyu na rufe fuskata dasu ina dan murmushi yayin da naji Abbu yana er dariya, yace “why? Baki son sunan ne ko me?” naki bude fuskata balle in kalleshi, yace “idan baki son sunan it’s okay, but bude mun fuskar ki plss” na kara kankame fuskar tawa, ina zan iya fuskanta Abbu a yanzu? Ina jin lokacin daya tashi daga inda yake ya dawo gefena ya zauna kamshin turaren shi ya cika min hanci, yace “zaki bude da kanki ne ko sai na janye da kaina?” a hankali na janye hannuwan nawa sai dai fuskana tana kasa, a yadda nake jina a lokacin nasan ba zan taba iya hada ido dashi ba. Ya rankwafo da kanshi saitin fuskata, da sauri na daga kaina na kalleshi cikin sa’a muka hada idanu dashi, wayyo Allah! Kasa tsaye in shige. Ban taba ganin Kwarjinin da yayi mun a lokacin a tattare dashi ba, wani irin magnet naji ya fara fuzgata yana kokarin hada ni dashi, da sauri na mike tsaye ina lalubar jakata tun kafin in kai ga yin abinda zan zo ina dana sani gwara in bar office din. Abbu ya bini da ido yana frowning, na tsaya a gaban shi ina rataye jakata a kafada kaina a kasa, nace “umh…. Zan tafi… In… na da class anjima” ya kalli agogon hannunshi tare da dan jan siririn tsaki, “so nayi mu tattauna game da yadda zamu tsara rayuwar auren mu dake fa, amma ba komi there’s always a second time. Amma zan sanar da Daddynki dai” na kalleshi da sauri ina zaro idanu, “tun yanzu?” yayi scrunching din brows dinshi, “tun yanzu? Me kike nufi?” nayi kasa da kaina “na ga kamar yayi kusa ne” ya girgiza kanshi “bai yi kusa ba Nafeesah, na gaya miki na kagauta ki zama mallakin, ni da so samu ne ma sai ince satin sama a daura mana aure in killace ki a gidana, Ya Allah! Na tabbata burina ya gama cika, I wouldn’t ask for anything sai dawwama dake a gidan Aljannar Firdaus” sai kawai na daga kafa na fara tafiya, Anya Abbu ne? Ban san me ya shiga kan shi da kwalwar shi ba a Kwanakin nan sai ya dinga min wasu maganganu da suke saka ni cikin ramin matsananciyar kunyar shi. Ya mike tsaye, “tunda baki son yin hira dani bari in maida ki hostel to” na fita na tsaya a bakin kofar Ofishin ina jiran shi, ya fito daga ciki ya rufe office din yayi gaba na bishi a baya har inda yayi parking din motar shi. Muka shiga yaja motar, a hankali muke tafiya yana ja na da er hira. Duk yadda nake kauce-kauce da kare-karen fuska sai dana dawo ina dariya, kafin mu karasa hostel na sake daga awkwardness din daya dabaibaye ni, a cikin motar ma mun jima muna hira a gaban hostel dinmu har sai da aka fara kiran sallar azuhur sannan muka yi sallama. Na bude murfin motar ina ce mishi ya gaida su Hafsy, yace “me zaki ce musu bayan tunda kika zo baki ziyarce su ba? Fushi ma take yi dake don ki sani… Koda yake ai na kusa ciccibar ki in kai mata ke cikin gidan gabadaya, ki fara haifo mata kanne nasan zata yi farin ciki sosai, zan gaya mata ta daina fushi dake haka nan” ni dai na ida sa kafata waje na fita ina dan murmushi, da gaske Abbu ya canza daga cool and calm Abbun dana sani zuwa Romantic, wanda yake fadar duk maganganun da suka zo bakin shi ba tare da yayi la’akari da cewa sun girmi kunnuwana ba. Ya dan leko da kanshi ta cikin motar, “baki ce komi ba fa” na dan juyo na kalleshi tare da haske shi da murmushi na juya na shige cikin hostel, ina jin hot gaze dinshi a kaina har na yi nisa a cikin hostel din, na tura kofar dakin na shiga. Firdausi na zaune akan kujera da littafi a hannunta tana karatu, ta dago tana min sannu da zuwa na amsa, kallona ta cigaba dayi kamar wadda taga wani bakon abu a jikina, na rataye jakar hannuna a jikin hanga na kalleta, “wannan kallon naki lafiya dai koh?” tayi murmushi tace “you are blushing! Did someone propose to you??” na kalli kaina a cikin madubi, I couldn’t help the chuckling daya fito min, na kalleta ina murmushi “Ina ga dan zafi zafin da ake yi ne kawai” ta kalleni tana murmushi tare da gyada kai ta maida Idanunta ga littafin hannunta. Nima nayi murmushin na fita naje nayi alwala na dawo nayi sallah, kafin in gama Firdausi ta dafa mana indomie ina gamawa muka ci na sake fita wajen lecture. 2
A daren ranar sai ga wayar Daddy ta shigo, na daga wayar cikin sanyin jiki da faduwar gaba. Ina gaida shi ya amsa ya dora da fadin, “Ibrahim ya kira ni yanzu yana fada min wani labari” na sadda kaina kasa kamar ina gaban shi, “kayi hakuri Daddy” ya danyi murmushi, “meye kike bani hakuri dear? I just call to know that you are okay with it. Are you sure zaki iya?” na gyada kaina amma ban yi magana ba, yace “naji dadin zabin da kika yanke sosai Uwata, naji dadin cewa mutumin da kika zaba ya zama abokin rayuwar ki Ibrahim ne, naji dadin cewa zan barki a hannu na gari kuma na kwarai, nasan ba zan taba yin fargaba game da yadda kike ba saboda na yarda da Ibrahim. Allah ya miki albarka Nafeesah” naji hawaye suna kokarin cika min ido, da ace ina kusa dashi da sai na rungume shi, nace “I love you Daddy, nagode” yace “You are all we have Uwata, dole mu so farincikin ki, ina Alfahari dake” nace “nima haka Daddy…. Amma Mommy fa?” yayi kasa da murya nasan sirri yake nufi, “Mommy dinnan taki fa sai a hankali, tun dazu take hawa tana kumbura kamar fulawa daga mata maganar wae ai ita bata yarda ba cin amana zata yi, shine nace mata idan haka ne itama za a turo mata yarinya kamar ki idan tayi watanni sai in aureta, don Allah ba anyi 1-1 ba?? Sai kawai ta hau kumbure-kumbure, yau ko magana bata min ba dana dawo daga aiki” duk da banji dadin abun ba sai dana yi er dariya nace kai Daddy! Yace “it will be better idan baki kira ta ba for two days, zan yi kokari in ga cewa na ganar da ita abinda take fahimta” nace toh Daddy. Yace good girl, kije kiyi alwala ki kwanta, nasan kina da darasi da safe nace “exactly Dad, goodnight” muka yi sallama na ajiye wayata jikina a sanyaye. Na jima a zaune ina tunanin yadda zan yi idan Mommy taki bamu albarkarta game da auren nan, ni dai nasan cewa ba zan iya auren Abbu ba tare da yardar Iyayena ba gaskiya. Na tashi naje na dauro alwala nayi shirin kwanciya barci. Dana daga wayata naga message din da Abbu ya turo min mintuna biyar da suka wuce, cewa yayi; “A lokacin da kowa yake neman makwanci da niyar warware gajiyar data addabe shi, a daidai lokacin bawan Allah Ibrahim yake karawa kan shi wani tarin gajiyar, why? Saboda bashi da makwanci kwanciya balle filon tada kai Ina fata wadda take karanta sakon nan zata yi gaggawar kasancewa tashi ko zai samu sanyin rai dana zuciya a tare dashi. Sai da safe, lots of love and kisses” n zan iya rantsewa naji saukar lebba a kumatuna, na kai hannu na dafe wajen ina duba gefe na, dariya na saki tare da dan dukan goshi na, silly me! I am even expecting him to kiss me, woah!! ‘Goodnight’ kawai na tura mishi as a reply na kwanta tare da lumshe idanuna. Barci mai dadi cike da kyawawan mafarkai ya daukeni ni
~So how are you doing outta there Abbu and Nafee’s fan??