AMININ MAHAIFINA CHAPTER 12

AMININ MAHAIFINA





CHAPTER 12






Kwana biyu kuwa ban yarda na latsa sunan Mom a wayana da sunan kira ba sanin halinta na sauka daga fushi da kanta idan ta hau don sau tari idan tana fushi bata cika son ana bin kanta ana bata hakuri ba ma, she prefers a kyaleta har sai ta sauka don kanta, don haka ban tarki kiranta ba sai dai na tura mata text message which of course bata yi replying ba.
Ina fitowa daga class na koma daki, su Ni’ima suka kira ni suka ce suna dakina. Ina shiga suka tare ni da shewa ni har suka sa gabana ya fadi ina tunanin ko zancen mu da Abbu ya kai kunnensu ne, sai da muka gaisa har muka fara hira naga basu yi maganar ba sannan na dan saki jikina. Na kunna stove ina kallonsu, “me zan dora muku?” Ni’ima tace Indomie noodles, Sadiya kuma tace Spaghetti, na kallesu “guys, idan zaku daidaita akan abu daya ku daidaita don kun san bani da lokacin yin girki biyu” suka kwashe da dariya, Sadiya tace “dora mana noodles, wannan maman Babyn ba zata barmu mu shaki iska mai dadi ba idan ba a dafa noodles dinnan ba” nace “kema ai Maman Babyn ce” ta wani zare ido, wa?? Muka kwashe mata da dariya ni da Ni’ima. Nan da nan na dora Indomie na ta dahu na juye mana a tray muka fara ci. Muna cikin ci kiran Abbu ya shigo wayata, na kalli wayar tare da kallon su Ni’ima dake kallona suma, na ci mur tare da janye wayar na kife ta akan gado, suka yi sharing glancing a tsakaninsu. Sadiya ce tace “wai ni me ke tsakanin mutanen nan biyu ne? I’ve started putting a big question mark a tsakanin su” Ni’imah tace “kamar kin shiga zuciyata wallahi… Ni kaina na kasa fahimta” na kara hade fuska ina cusa indomie bakina ba tare da nayi magana ba, sam bana so maganar mu da Abbu ta fita ta shiga cikin dangin sa don tsakanina da Allah ban san da wani ido zan kallesu ba, ban shirya ba. Ni’imah tace “idan tayi wari dai mun ji” ni dai na kyale su ban tankasu ba. Muka gama na wanke kwanuka na kai mana soft drinks muka sha, daga nan na koma class bayan nayi sallah na bar su a dakin, dana dawo ban same su ba sun bar mun sako dai kan cewa sun tafi. Da dare Abbu ya sake kirana, na daga wayar da sallamata ya amsa ya dora da cewa “me bawan Allah yayi aka ki daga kiran shi dazu” nace “bana kusa da wayar ne Abbu…. Ina yini?” ya amsa, anan yake fada min wae washegari zai tafi Ilorin zai yi sati daya a can. Yace “me zai hana idan na dawo kawai a daura mana aure Nafeesah?” nace “Abbu baka tunanin it’s too sudden?” yayi sighing, “Nafeesah, y do u always keep saying yayi sudden? Kina tunanin haka zan ci gaba da kallonki Ina kauda kai har zuwa yaushe? Har ki gama makaranta ko me?” nayi kasa da murya nace “at least in dan yi nisa a karatu na mana!” yace “really? Kin san? Ko session dinnan ba zan bari ya kare ba ba tare dana aure ki ba Nafeesah, idan kuma ba so kike yi in….. God! Nafeesah wae me kike nufi da rayuwata ne??” muryar shi ta dan fara yin sama alamun ranshi ya fara baci, nayi shiru ban bashi amsa ba. Lokacin dana gama yanke shawarar yarda da Abba, kamuwa da son shi da amincewa akan cewa zan aure shi, ban yi tunanin zancen aure ba, ban yi tunanin cewa zai taso zancen aure nan kusa ba, ban yi tunanin zai so ya aure ni ina cikin karatu na ba, nayi tunanin zai bar ni in karasa karatuna ko kuma at the very least ya bari sai na kusa kammala karatuna sai kuma gashi yana zancen aure in the next two weeks when I’m not even ready for it, hell ban ma san meye ma’anar auren ba, me zan yi kenan?? Ga zancen mu da Mommy ga…. Ya katse ni ta hanyar cewa “just forget about it Nafeesah, bana son tursasaki yin abinda baki yi niyar yi ba. Na hakura da zancen auren, idan muka ci gaba da zama a haka ma ya ishe ni, I want your happiness” naji kwallah ta tsattsafo min a idanu, nace “Abbu kayi hakuri” yace “don’t mind Amour, na fahimce ki” nayi murmushi mai sauti wanda na tabbata ya jiyo sautin shi, ya maido min da martanin wani wanda yasa naji gwiwoyin kafana sun yi wani sanyi, yace “Pretty na tana ta cigiyar ki, yaushe zaki zo ki ganta?” na zaro ido kamar yana gabana, har sai da naji gabana ya fadi nace “ni?? A’ah gaskiya” ya danyi er dariya, “tsoron me kike ji ne? Na manta ma dazu in fada musu you are now my wife to be” nayi saurin cewa “pls Abbu no! Don Allah ba yanzu ba!” yace y? Na dan turo baki, “ni dai don Allah a’ah” yace “naki, sai na fada musu” na kula tsokana ta kawai yake yi don haka na kyale shi yayi ya gaji sannan muka danyi hira kafin muka yi sallama na mishi Allah ya kiyaye hanya muka ajiye wayar. Abin mamaki sai ga kiran Mommy ya shigo wayana, nayi tsuru Ina kallon wayar kamar ba zan daga ba, Ina tsoron abinda zai faru idan na daga kiran. Sai daya kusa tsinkewa sannan na daga, a hankali kamar mai tsoronta nayi sallama tare da gaida ta, cikin usual tone dinta ta amsa yadda take min, ta tambayeni karatu da sauran abubuwa duk na amsa mata da lafiya lau, tace “naji abinda kika yi Nafeesah, kina ganin daidai ne hakan?” nace “Mommy kiyi hakuri don Allah” tayi shiru kafin tayi ajiyar numfashi, “to tell you the truth naji haushin Abin daga farko, daga baya sai naga cewa abinda kike so kenan and I don’t have the right da zan hana ki yin auren da kike so ba Ummiey. I really hope decision din da kika yanke shine daidai kuma zai kawo miki farinciki mai dorewa a cikin rayuwar auren ki” naji zuciyata tayi wani irin sanyi, na saki sansanyar ajiyar zuciya Ina jan hamdala a cikin raina, nace “Mommy nagode sosai” tace “Ni me ma zaki ce mun ne? Kwana biyu baki kira ni ba saboda kina gudun kar in hana ki yin soyayya ko?” nace “mommy ba haka bane” tace “idan haka ne ma ya zanyi? Tunda daddyn ki ya kitsa miki kin hau kai kin zauna, ina jinshi ai yana baki shawarar kar ki kira ni shine ke kuma kika ki kirana” na sake cewa “kiyi hakuri” ina danne dariyar data taso min, ta kuta, “he was even threatening me wai zai iya karo aure, bai san cewa abinda matar shi Ibrahim din zata yi da halin da zata shiga idan taji zancen auren bane nake gujewa ba, yayi zaton son raina ne nake shirin shiga tsakaninki da abinda kike so ba. Ummiey mata da kike gani baki san irin tashin hankali da fargaba da suke shiga idan suka ji zancen kishiya ba balle ita data zauna dake a gida daya ta rike ki cikin amana, dare daya ace zaki aure mata miji kin san ba zata ji dadi ba dai koh?” jikina yayi sanyi na sadda kaina kasa, wannan yana daya daga cikin abinda ya saka ni hesitating at first amma ya zamu yi? Ba zamu danne farinciki cikinmu don faranta ran wadda bata san namu farin cikin ba. Mommy tace “kada ki damu fa, kuma kada ki saka maganar a cikin zuciyar ki babu abinda zai faru da yardar Allah. Amma ya miki zancen aure? Yaushe yace za ayi?” nayi wuri-wuri da ido, tace “baki sani bane? Zan yiwa Daddyn ki magana, ya kamata ace anyi auren nan kawai” nayi saurin cewa, “Mom, ba zaku bari in gama karatu bane?” shiru ya biyo baya kafin tayi magana, “kina da hankali kuwa Ummiey? Shekaru nawa suka rage miki kafin ki gama karatunki, kina tunanin zamu zuba miki ido ko kuma shi Ibrahim din ne yace sai kin gama karatu?” nace A’ah, tace “to ai ko shine Ummiey ba zamu zuba miki ido ba zan yiwa Daddynki magana a zauna ayi maganar auren ku don gaskiya hankalina ba zai kwanta ba kina karatu a Kano shima wanda ke son naki yana Kano mu muna nan Kaduna bamu san abinda ke faruwa ba a yadda duniyar nan ta baci” nace “Mommy baki yarda dani bane?” tace na yarda dake Ummiey, nasan irin tarbiyar dana baki, but still, hankalina ba zai kwanta ba gaskiya” nayi rolling eyes, “ai shikenan Mom” tace “zan dai tuntubi Daddynki inji, goodnight baby” na mata sai da safe tare da kashe wayar. +

Babu ranar da bamu yi waya da Abbu ba tunda ya tafi, idan ma bamu yi wayar ba muna tare ta hanyar text message yana kashe ni da dadadan kalamai da suke kara narka zuciyata zuwa gare shi. Sai a dan tsakanin na fahimci ainihin ma’anar Soyayya, ashe da shirme nayi, ashe ba son Muneer nake yi ba tunda ko a lokacin dana yi tashen son shi ban taba kawowa raina bazan iya rayuwa idan babu Muneer ba, amma a yanzu, na tabbata cewa muddin babu Abbu a cikin rayuwata to tabbas rayuwa ba zata yiwu a gare ni ba, ko zan yi ta to mara gardi da dandano ce. A yanzu bana taba iya tunanin runtsa idanu matukar ban ji muryar Abbu a yini ba saboda nasan cewa ba zan iya barci ba, nayi wani irin sabo da muryar Abbu wanda sau tari hakan yake bani mamaki. A kowace rana kuma a kowane lokaci wata kofa a cikin zuciyata sai ta bude da sunan Abbu rubuce a jikinta Ina da tabbacin nan da dan lokaci kankani kila numfashina ma idan aka kula sunan Abbu ne zai dinga fita daga cikin shi. Duk da dai ance wai sanin gaibu sai Allah amma zan iya cewa ta bangaren Abbun ma hakan take koma fiye da haka. A yadda na fahimce shi cikin dan lokacin, yana daga cikin mutanen da baiyana halin da zuciyoyin su ke ciki abu ne mai matukar wahala da wuya a gare su, sai dai su baiyana shi through their actions kawai. Baya zama yana wani tsara min kalamai na soyayya kamar yadda yace bai iya irin wannan Abun ba but I am comfortable da yanayin yadda yake tafiyar dani, yadda yake tattalina da yadda yake nuna kamar duk duniyar nan babu wata ‘ya mace mai gashi a cikin idanun shi sai ni, wannan kadai ya ishe ni numfashi mai dadi a rayuwa sanin cewa abinda nake matukar so da qauna shima yana sona da kaunata equally. Shi yasa ko a lokacin da Mommy ta sake tuntuba na da zancen aure a karo na biyu, tace “bikin Hansa’u yana matsowa, me zai hana a hada auren ku gabadaya kawai a daura a can Malumfashi? Bai fi watanni biyu ba za a daura in yaso ko bayan kun karar da session dinnan ko semester din sai ayi biki da tarewa ko?” nace “Mommy sai wani saurin ku aurar dani kuke yi kamar wadda kuka gaji dani? Wane irin aure ne kuke shirin yi mun haka daura aure kafin tarewa?” tace “to ai gani nayi hakan zai fi mana sauki da mutanen da zasu zo daurin auren, ace anyi aure da wata daya wasu ko gama kafe gajiya basu yi ba a sake juyowa yin wani auren kin ga ai akwai takura, ba gwara ayi a wuce wajen ba?” nace “Mommy ni bani da zabi, kuyi duk abinda kuke ganin daidai ne” tace “to Allah ya miki albarka, Yasa hakan shi yafi alkhairi…. Oh su Ummiey za a zama matar aure!” da sauri na kife wayar a kan gado na fara juyi akan gadon idanuna akan fuskata kamar Ina gaban ta. Abbu ya kira ni a daren ranar cikin tsananin farin ciki da murna, yace “kin gama yi mun komi Nafeesah, kin saka zuciyata cikin farincikin da bata taba shiga ba, Allah ya miki albarka Nafeesah! I’ll definitely compensate you Amour, yau zan ma iya barci kuwa saboda murna?” da wadannan kalamai nashi na kwanta suna min amsa kuwwa a cikin kaina, tabbas I’ll be the luckiest bastard on earth matukar na auri Abbu, Abbu!! Allah ya nuna min ranar da zan zama matar shi lalle zan kere sa’ah. +

Bayan kwanaki biyu Abbu ya dawo daga Ilorin, da yake dawowar safe yayi gida ya wuce ya dan huta ya shirya kafin ya shigo cikin makaranta, lokacin muna cikin lab muna practical don haka yace in same shi a office dinshi idan mun gama. Sai karfe biyar muka fito, ban tsaya yin komi ba na tunkari ofishin Abbu cikin wani irin doki, ji nake kamar in yi fuffuke ko in bude idanuna in ganni a gaban shi, in dora idanuna akan kamilalliyar fuskar shi mai saka ni cikin nishadi, nayi kewar shi, ban taba kewar abu a rayuwata har nake ji numfashina yana daukewa saboda rashin wani abu kamar yadda nayi kewar shi ba, how I can survive without Abbu a rayuwata yanzu, only Allah knows. Jikina har rawa yake lokacin dana hau corridor da jerin offices yake ba, naja nayi burki a kofar ofishin shi Ina kokarin saita kaina kila idan na shiga kai tsaye a yadda nake zai iya zaton ko gudu nayi naxo gare shi. Na daga hannu da niyar yin knocking na jiyo wata murya tana magana, cikin Jan hankali, cikin kissa da kisisina, cikin wata murya dake baiyana tsananin bukatuwa da roko….. Zuciyata ce ta bada wani irin sauti da naji shi tamkar saukar aradu……
~Me kuke tunani game da chapter din Yau?
~Mommy fa? Ya kuka gani? Ta burge ku?? “Dr. Ibrahim baka tunanin lokaci yayi da xaka yi recognising din soyayya ta zuwa gare ka? Kana sane da halin da ruhina yake ciki saboda kai, soyayyar ka na azabtar da zuciyata a kowace rana amma kayi kunnen uwar shegu dani kana nuna kamar baka san komi ba, haba Ibrahim, ka tausaya min mana please!!” kafafuna suka shiga rawa na kasa yin knocking din da nayi niyar yi, a hankali na matsa ta jikin tagar office din da yake a bude take. Abbu yana tsaye ya juyawa tagar baya, ya rungume hannayen shi a kirji yana fuskantar ta yayin da ita kuma take fuskantar tagar duk da cewa dai bana iya hango fuskar ta amma yanayin shigar da tayi m not satisfied with it. Ko dai tayi kwalliya ne don tayi seducing din Abbu na ko kuma ta saba yin tambadaddiyar shiga ta marasa mutunci kamar yadda tayi yanzu. Abbu yace “Dr. Luba Ina ga wannan abu ai yana gare ki ne, ba tun yau ba na riga da na fada miki cewa Ina da aure har da ‘ya’ya….” ta katse shi, “nima ai nace maka zan iya aurenka a hakan, meye hadina da matar ka ni? Kai zan aura ba ita ba!” yace “am getting married, in the next two months in shaa Allah!” ta laulayo wani ashar ta maka, “says who? Karya ne Dr Ibrahim, wallahi Karya ne! Babu ‘ya macen data isa ta aureka Ina tsaye Ina kallo, idan ma wasa kake yi tunda wuri ka fadi kafin in aikata abinda ran mu ba zai mana dadi ba” yace “me yasa zan miki wasa? Ba tsoron ki nake ji ba kuma ba shakkar ki nake yi ba, ban san ko sau dubu nawa kike so in fada miki cewa bana son auren ki ba, you are not my type Ramlah” tace “but you are my type, and there’s no way da zan zauna ina kallo a gaban idona wata ta dauke abinda nake so ba, Karya ne wallahi….” ta kara taku zuwa gaban shi ta kai bakin ta daidai kunnen shi, ban san me ta rada mishi ba, naga dai taja da baya yayin da Abbu yayi shiru kawai, can kuma naji yace a hankali, “get out please Dr Luba” tace “ba kai kace in zo ofishinka ba ra’ayin kaina ne, don haka idan zan fita ma yanzu sai nayi ra’ayi, gashi kuma ban gaji da ganin fuskar ka ba, ya za ayi kenan?” na hangame baki cike da tsananin mamaki, lallai duniyar Allah mai fadi, xaka ga mutane daban-daban masu hali iri-iri, ita kuma wannan wacece? Zuciyata ta hau wani suya kamar zata fito daga kirjina, ji nayi kamar in banka kofar ofishin in shiga in jawo ta by her hair in fada mata Abbu nawa ne, in ma ta kai ga tofa mata yawu a fuska duk zan yi matukar zata fita daga cikin rayuwar Abin sona. Na koma ga kofar na fara knocking da karfina kamar zan balla ta, Abbu ne ya min izinin shiga. Na tura kofar na shiga with full of attitude and Charisma, so that wadda take ikirarin mallakar Abbu na ta karfi da yaji taga cewa am not the type of people da ake musu kwacen abinda suke so, abinda suke Jin cewa ba zasu rayu ba tare dashi ba right in front of their eyes ba tare da sun yi abu ba. Abbu ya juyo yana kallona, murmushin daya saki kadai yasa naji wani irin kwarin gwiwa ya mamaye ni, naji duk wata fargabar kada fa matar dake gabanshi ta kwace min shi ta tafi ta barni a take, tabbas Abbu shine mahadin rayuwata. Nima na mayar mishi da martanin murmushin wanda yake kunshe da zallar so da nuna tsananin kewar shi da nayi kafin idanuna suka sauka akan matar dake ikirarin claiming din abinda yake nawa. Ta sha uwar kwalliya a fuska saboda tsabar kwalliya ba zaka tantance ainihin kala ko kamanninta ba, tasha adon izgar doki wanda ya sauko a kafada da gadon bayanta, wani material ne a jikinta an mishi wani irin watsattsen dinki na Allah wadai wanda ya fito da shafaffen kirjinta kamar shafaffen silifas, dinkin ya matse ta tun daga kirjinta har cinyoyinta, ta wani kalleni tun daga sama har kasa yayin da nake kallonta disgustingly cikin nuna kyama kamar wadda taga abin kyankyami wanda na tabbatar da cewa sai ya kada mata ‘ya’yan hanji. Abbu ya katse mana kallo-kallon da muke wa juna ta hanyar cewa “Dr Luba meet my dearing wife, Nafeesah. Nafeesah she’s my co worker” nace “sannu, ya kike?” ta tabe baki tana wani yamutse fuska, “wannan abar ce dama kake wani tada jijiyoyin wuya kana cewa wai zaka aura? Me ta fini dashi?” Abbu yace “ko zaki iya bamu waje, Ina son sirri” ta buda kofofin hanci har suna naso, “ko baka ce ba yanzu zan bar maka ofishin ka kafin ka wulakantani a gaban wannan er yarinyar, sai dai kada kayi tunanin na hakura ne, ko ta halin yaya sai na mallake ka Ibrahim saboda kai nawa ne!” ta warci jakar hannunta ta fita tana murguda kugu kamar wani shafaffen plate saboda rashin cikowar shi, na bita da kallo Ina murmushin mugunta, matar nan ta rainawa kanta hankali da yawa, ni ta kira da yarinya koh? Allah ya kara hada ni da ita wani lokacin, ni kuma nayi alkawarin nuna mata aikin yarinta. Na maida kallona ga Abbu lokacin data fita daga office din ta maida kofar tayi banging kamar tashin duniya. Murmushi na sakar mishi softly, duk da cewa har zuwa lokacin zuciyana tana itching game da Luba ce ko Bana yace sunanta? Bana so in sani. Yaja kujera ya zauna a kusa dani tare da nuna min wata kujerar nima na zauna, yace “kiyi hakuri da abinda ya faru, kada kuma ki sa maganar ta a cikin ranki, ta saba irin wadannan maganganun duk burga ce da tauna tsakuwa don aya taji tsoro” nace “wai wace? Ni ban ma fahimci abinda take fada ba balle in saka shi a cikin raina…,” ya kura min idanu yana murmushi, “kin san abinda yasa nake kara jin ki a cikin raina kenan? Nafeesah my other being” na sadda kaina kasa Ina dan murmushi, Abbu with his flirtations, a hankali nace “sannu da dawowa, ya hanya?” yace “it was tiresome, amma yanzu na dawo normal dana gan ki, my wife!” wayyo kunya! Na rufe fuska ta da hannuwana ina er dariya, shi kuwa dariya ya saki sosai, a tausashe. Nayi shiru Ina jin dariyar da yake yi, he sound so relieved and happy, and I feel proud knowing that ni ce sanadin farincikin da yake ciki. +

Cikin barci na kai hannu kasan filona na lalubo wayata dake vibrating, duka-duka karfe goma ne da rabi na safiyar ranar Assabar, da yake ranar hutu ce kuma ban samu nayi barci da wuri a daren jiya ba shi yasa na ke jina kamar wadda ta kwanta a lokacin saboda tsabar barci. Ban ko tsaya duba caller ID ba na dauka, muryar Sadiya ce ta doki kunnena, “Asslm, Nafeesah hope ban katse miki barci ba?” cikin muryar barci nace “kin katse min mana” tace “sorry, dama muna nan AKTH ne shine zan fada miki” na tashi zaune a sukwane nace “Teaching Hospital kuma? Waye babu lafiya?” tace “Ni’imah ce wallahi, ta samu miscarriage yau da safen nan” jikina yayi sanyi sosai, Allah sarki Ni’imah. Nace “ki turo min da number din dakin da kuke, gani nan zuwa” na ajiye wayar tare da dirowa daga kan gado. Wanka nayi na fito na Karya, ban wani tsaya yin kwalliya ba na saka kayana kawai na fita, sai a cikin mota ne na kira Ramlah Ina fada mata, tayi jimamin abin sosai tace zata kira ta mata jaje. Ban samu Sadiya ba a dakin da aka ajiye su lokacin da naje, Anty Ameenah da Anty Rayyah suna nan a dakin tare da wata dattijuwa sai kannen Bashir mata su biyu, Ni’imahr na kwance tana barci an sa mata drip, ta wani dashe tayi fari tas kamar wadda babu jini a tattare da ita. Muka gaisa dasu Anty Ameenah cikin mutunci har tana bani hakuri akan wai an taso ni daga makaranta, nace a kunyace haba Anty, Ni’imah tafi karfin haka a wajena ai…. Allah ya mayar mata da mafi alkhairi, suka amsa da ameen. Sadiya ta shigo dakin hannunta rike da na Jameel dan Anty Jameelah wanda yake tafiyar ta-ta-ta, muka gaisa da ita itama na musu jaje, naja Jameel a jikina ina tambayar shi inda yaje yana ta min gwaranci ina murmushi. Ni’imahr bata farka ba sai bayan azuhur, su Anty Ameenah suna waje suna sallah da yake ni fashin ta nake yi, na matsa gefen gadonta Ina mata sannu tare da tambayar ta abinda take bukata? Kuka kawai ta saka tana shafa cikinta, na rungumo ta a jikina ina da dan jijjigata kamar nima in rushe da kukan nake ji, it’s not easy ka dauki cikin abu ka raine shi, bayan ka gama kwallafa ranka a kanshi kuma sai Allah ya jarabce ka da rashin sa, hakika Allah kadai yasan irin sakayyar daya tanadarwa irin wadannan matan. Nace “kiyi hakuri Ni’imah, haka Allah yaso. In shaa Allahu zai kawo miki mafi alkhairin sa, stop crying please kinji?” ta jijjiga kanta. Naje na xubo mata ruwa a cikin cup ta kurba, lekawa nayi na gaya musu ta farka sai gasu sun duro cikin dakin, kowa sannu yake jera mata tare da nasihar fawwalawa Allah lamuranta, nan aka zuba mata abinci muma muka zuba namu muka ci. Da yamma sai ga Bashir din yazo ashe ma baya gari saukar shi kenan daga Abuja, bawan Allahn nan har da hawayen shi abin gwanin ban tausayi wallahi. Bayan Magriba su Anty suka yi haramar tafiya gida, Anty Rahina tace in zo ta sauke ni a makaranta mana nace mata ai ni anan zan kwana, tace inah! ga Sadiya nan da Gwoggo Hinde sun isa in zo ta maida ni makaranta kawai, nace mata ni fa anan nayi niyar kwana. Tayi shiru tana kallona ganin na kafe kafin tace “kin fadawa iyayen ki?” nace “zan fada musu anjima dai” tace ai shikenan, Gwoggo Hinde zo mu wuce gida dake kawai. Da haka suka mana sai da safe suka tafi bayan sun ajiye mana duk abinda zamu bukata. Na shiga bandaki na gyara jikina, ban taho da panties bama sai dana fita waje na sayo wasu pad ce ma ban nema ba da yake ni ma’abociyar ajiyar su ce a cikin jakata saboda emergency. Na fito daga bandakin ina gyara zaman rigar jikina, daidai lokacin Abbu yayi sallama ya shigo cikin husky voice din nan nashi Hafsy na biye dashi a baya, zuciyata tayi wani irin fari da ganin shi kamar zata haske duniya da abinda ke cikinta, gabadaya ranar ban ji muryar shi ba mun dai yi exchange din messages a tsakaninmu da rana, fuskar shi ta nuna zallan mamaki da ganina kafin baiyanannen farin ciki daya gaza boyuwa ya nuna akan fuskar tashi, na ja kujerar kusa da gadon Ni’imah din na zauna. Na Kalli Hafsy dake tsaye a bakin gadon Ni’imah na mika mata hannu alamun tazo ina murmushi, ta makale kafada tare da kara lafewa a jikin Abbu alamun ba zata zo ba, na janyo ta jikina tana kokarin kwacewa amma na hana ta, nace “haba Hafsy na ni dake bata baci, Waye ya tabo min ke?” ta turo baki tana nuna ni da yatsan ta, nace “ni da kaina? Me na miki?” tace bake bace ba kike kin zuwa ki gaida ni, kullum sai nace kizo ki ganni amma baki taba zuwa ba! Na dan saci kallon Abbu dake gaisawa da kannen shi amma idanuwan shi suna kanmu yana mana dan murmushi, na janye tare da kallonta nace “kiyi hakuri kinji? In shaa Allahu zan dinga zuwa Ina ganinki, so stop frowning and smile kinji?” tace “promise?” na gyada mata kai. Aka kwala kiran sallahr Isha’i a daidai lokacin, Abbu ya zube min wayoyin hannunshi a gabana ya fita da niyar yin sallah….
Suka kalli juna kafin suka kalleni, Sadiya ta dage gira daya “me kenan?” “me fa??” na tambayeta ina wani fuskewa ni ala dole ban fahimceta ba. Tace “ki wani daina fuskewa malama, mun san abinda ke faruwa tsakanin ku biyun nan” na kada mata idanu innocently, “ni da wa??” ta kai min duka a kafada, “zaki sani ne maras M, ace kamar mu kuna cikin relationship da Yayan mu mu kasa sani?” na kallesu su duka biyun ina so in karanta yadda suka amshi zancen, ban karanci komi ba sai dai murmushin dana gani kwance akan fuskar su na farin ciki ne bana embarrassment kona takaici bane, naji sanyi ya lullube min zuciya, at least abotar mu dasu tana nan. Ni’imah tana murmushi tace “Sady ke kike wani tsayawa ma kina neman karin bayani, ni fa dama tun ba yau ba na harbo jirgin su ita dashi, they were making it obvious shi yasa ni ban tsaya jira a fada min ba nayi jumping into conclusion” na dan harareta cikin wasa nace “ni kar ki mun sharri wallahi” tace “ba wani sharri sai gaskiya. Irin kallon da kuke wa juna dama tun ba yau ba be it kuna cikin mutane ko ku kadai ne wallahi na soyayya ne, ai Anty Rahina tace an kusa yin auren” na dafe kirji ina zaro idanu, nace “su Anty har sun sani??” dariya suka saki suna kallona kamar wata kuntacciya dinnan, “Allah kina kwafsi matar Babban Yaya, tunda har muka sani ai dole su Anty su sani kuwa” na rufe fuskana ina diddira kafafuwa a kasa, “Ya Allah! Da wani idanu zan kallesu ni kam?” suka sake kwashewa da dariya har da tafawa, na hade fuska ina kallonsu, “this is not funny fa!” na fada in a serious tone don su san ba wasa nake yi ba, amma ko a jikinsu sai ma wata dariyar da suka kara sawa. Ganin zasu sa min ciwon kai naja Hafsy data fara gyangyadi a zaune muka koma kan spare gadon dake dakin na zauna ita kuma ta kwanta kanta a kan cinyoyina. Hira nake janta dashi duk don in janye hankalina daga shakiyancin dasu Sady suke min, cikin dan lokaci barci ya dauketa. Na maida hankalina wajen buga game bana ko kallon inda suke, har suka gama shiriritar su da tsara yadda bikin zai kasance suka yi shiru, dinner ma sai da aka tsara kala biyu, luncheon da parties kuwa wai har da Tea Party, fruits party, Arabian nights dasu Fulani day da tarkace, ina jinsu dai ban saka musu baki ba sai dariya da nake musu kasa-kasa, da alamu wani noti a kansu ya kunce kila saboda murnar auren Yayan su ne ko wani abu? Muna nan su Abbu suka dawo daga masallaci shi da Bashir, sallama ya musu ya matso inda muke ya dauki Hafsy a kafadanshi ni kuma na kara gyara zaman gyalena na kwashi wayoyin shi nabi bayan shi. Ya bude seat din baya ya kwantar da Hafsy, ya maida seat din ya rufe tare da jingina da motar yana kallona, na sadda kaina kasa ina dan tapping kafafuna a kasan, akwai wadataccen haske sosai a wajen shi yasa naji na kasa sakewa in kalleshi, tunda maganar auren nan ta shiga tsakaninmu na kasa sakewa in kalleshi sosai koda yake ko a da can dinma idan muka yi kallon ido da ido sai dai by mistake, balle yanzu. Yace “gobe in Allah ya kaimu zan samu Alhaji Babba yayan Alhajinmu da maganar zuwa a tambayo min auren ki, zasu kai kudin na gani ina so za kuma a saka ranar auren gabadaya” nayi shiru kaina a kasa, me zan ce mishi? Shi Abbu bai san irin matsananciyar kunyar shi da nake ji bane da zai dinga zama yana tattauna maganar aurena dani ba. Ya kara jingina da jikin motar yayi alamun tagumi, “ni ai shikenan tawa ta same ni kuma. Son maso wani nake yi ko kuma ba a shirya aurena har yanzu bane?” na saci kallonshi, ba karamar dauriya nayi wajen danne dariyar data taso min ba, ya wani yamutse fuska kamar yaron dake shirin fashewa da kuka, nace “me nayi ni kuma?” yace “baki son maganar auren mu mana. Da nayi sai ki wani hade fuska kamar wadda ake tursasawa, ji yanzu ma na gaya miki magana maimakon ko ameen ki ce shine kike wani sadda kai kasa” na girgiza kaina ina dan murmushi, Abbu da rigima yake wani lokacin kamar karamin yaro haka yake. Kwanan nan haka yake, gaba daya ya zama very open to me, baya shakkar fada min duk maganar data fito bakinshi, wata rana ta saka ni jin kunyar shi duk da cewa abin yana burge ni kuma na kula hakan yana kara ja na zuwa gare shi. Nace “to ameen Abbu” yayi murmushi, “datz you my Amour…. Amma tsaya….” na kalleshi, yayi frowning face “yaushe ne kika ce kin daina kiran sunana da wani Abbu? Na gaya miki Abbu na yara na ne ba naki ba” nace “ai nace zan daina fa! amma ba yanzu ba” ya wani langwabar da kai, “har sai yaushe?” nayi shiru, ya sake cewa “ko sai mun yi aure?” na gyada mishi kai, yace “ba laifi, ni ai bawan Allah ne I can wait” nayi dan murmushi, “datz you kaima…. Wai don Allah meye ma’anar Amour?” yace “Love in french” na sadda kaina kasa ina blushing, da gaske ni Love dinshi ce? Nace “amma sauran messages da kake tura min shima French ne? Me suke nufi?” ya girgiza kai, “naaa! Ba zan gaya miki yanxu ba, zan dai koya miki French din sai ki karanta da kanki. Idan muka yi aure ma a Kasar Faransa zamu yi honeymoon dinmu ai, kila kafin mu dawo sai kin koyi yaren sosai, sai mu dinga canza yare a gaban mutane abinmu koh?” na kai hannu ina rufe fuskata ina dariya, can kasan zuciyana kuwa fata nake ina ma zan bude ido in ga har watannin da suka rage in zama mallakin Abbu sun zagayo? Ya kara jingina da jikin motar yana murmushi “ke da kunyar nan taki kuna birge ni, sai dai it’s way too much gaskiya, kiyi kokari ki rage ta ko kuma ni da kaina inyi wannan aikin…!” na kara dukunkune fuskana wannan karon a cikin gyale ma. Yayi dariya son ranshi kafin yace “ina tunanin raba muku gida ke da Mubeenah, me kike tunani?” nace “idan hakan yayi maka bani da damuwa da hakan nima” amma a can kasan raina ba karamin dadin hakan naji ba, har ga Allah dama can bani son zama gida daya da Anty Mubeenah har yanzu ina jin kaina guilty wani lokacin, har yanzu kuma ban san da wane ido zan kalleta ba balle har inyi tunanin zama a gida daya da ita, duk lokacin da nayi tunanin na kan ji hankalina bai kwanta da hakan ba. Yace “hakan ya min perfectly, zan samu inci amarcina cikin dadin rai da kwanciyar hankali abina. Amma na dan lokaci ne fa, don tuni an fara mana sabon gini” nace “sabon gini kuma?” yace “yeah, inda zamu koma da zama mu dukan mu har yaran da zamu haifa nan gaba. Da wancan gidan na gina shine a matsayin inda zan rayu da matar aurena ne, ban taba kawowa raina kara yin aure ba sai da kika shigo cikin rayuwata sannan na fara samun second thoughts. A yadda nake so kuma ki cika min gida da yara inda muke zaune yanzu ya mana kadan. Ina so iyalina su tashi da hadin kai ba tare da banbancin komi ba Nafeesah, ina fatan zaki bani goyon baya wajen ganin hakan ya tabbata?” muryar shi ta tabbatar min da cewa da gaske yake, tausayin shi ya kama ni Allah sarki Abbu na! Da haka yaso ya karasa rayuwar shi cikin takaici da rashin kulawar matar aure? Ta wani fannin sai na tsinci kaina da godewa Allah daya kawo ni cikin rayuwar su, ko babu komi nasan zan kawo haske cikin rayuwar Abbu kamar yadda name tabbata cewa shima zai kawo haske a tawa rayuwar. Nasan cewa shawarar daya yanke is not a bad idea, ni kaina nasan ba zan juri ganin rabuwar kan yayanmu ba kuma da yardar Allah ba zan bada gudunmawa wajen ganin rabuwar kansu ba kamar yadda wasu iyalan suke, na gyada kaina nace “In shaa Allah Abbu, zan yi iyaka bakin kokarina” yace “Nagode sosai Nafeesah. Allah ya bani ikon faranta miki rai kamar yadda kike iyaka bakin kokarinki wajen ganin cewa kin faranta nawa ran” na sadda kaina kasa ina murmushi, daya daga cikin halayen Abbu dake matukar burge ni kenan, saukin kai da saurin fahimta. A kasan raina kuma na amsa Addu’ar da yayi da “Ameen” 1

Bamu ankara da lokaci ya ja ba sai da muka ga Basheer ya fito zai tafi sannan Abbu ya duba agogo yaga karfe goma ta wuce, Abbu ya kama baki cike da tu’ajjibi yace “haka lokaci yake gudu dama?” na sadda kaina kasa ina magana a hankali yadda ba zai ji ba “kaine dai baka kula da lokaci yana tafiya ba saboda love ya rufe maka ido” ya mikawa Basheer hannu suka yi musabiha na mishi sai da safe nima ya karasa wajen abin hawan shi ya tafi, Abbu ya bude motar ya shiga ya zauna, ya kalleni yana kokarin yiwa motar key, “naji abinda kika fada sarai, zaki zo hannu ne ai zaki yi bayani by then” na ja da baya ina er dariya, na maida mishi murfin motar na rufe, yace “any thing for me?” na girgiza mishi kai, “babu, sai da safe Abbu na!” na juya da sauri na fara tafiya ba tare dana jira abinda zai ce ba, ina jin shi yana en maganganu har na mishi nisa kafin naji alamun yaja motar, na saki dariya a hankali. Ina shiga daki suka min caaa da magana, ni dai er dariya kawai na dinga yi da kyar na samu na kashe musu baki, Sadiya ta miko min leda mai dauke da gasasshen kaji da yoghurt, na zauna ina ci muna hira dasu har wajen karfe goma sha biyu Ni’imah tayi barci, sannan ne muma muka kwanta don dama duk saboda ita ne muke yin hirar don kar muyi barci mu barta ita kadai kadaici ya dameta, muka gyara daya gadon muka kwanta mu ma. Washegari wajen karfe goma Basheer ya kawo mana abin kari da kayan da Ni’ima zata canza, bayan su Anty Rahina sun zo mun gaida su nabi Sadiya gidanta muka je muka yi wanka muka canza kaya, sai kayan Sadiya na saka saboda ban tafi da wanda zan canza ba. Muna komawa muka tarar an sallame su, nan muka hada kaya muka wuce gidan Ni’imah. Muka gyara mata gida da komi muka mata girki, su Anty Ameenah ana kiran sallahr la’asar suka wuce, ni dai daga nan na musu sallama don a ranar zan koma makaranta. Sai bayan tafiyar su ne sannan na kira Mommy na fada mata abinda ya faru, sai da nasha fadan wai ban gaya mata da wuri ba sannan tace in hada ta a waya ita da Ni’imah, no dai na bata hakuri kafin in ba Ni’imah wayar Mommy ta mata jaje tare da kara mata da nasihu daga nan ta maido min wayar, na amsa, anan take fada min cewa wakilan Abbu zasu je gida Malumfashi tambayar aurena, nayi shiru ina gyada kai kawai, ta mim addu’ar Allah ya sanya alkhairi muka yi sallama da ita. Nima ba a jima ba na musu sallama na koma makaranta. Bayan kwana biyu aka sanya ranar auren mu ni da Abbu watanni biyu masu zuwa yayin da biki da tarewa kuma za a bari sai na gama exams dina. Wannan kenan!!
Kwanci tashi asarar mai rai, biki yana ta kara matsowa yayin da muke ta shirye-shiryen rounding off din semester dinmu. Tuni Ni’imah ta warware har ta fara shigowa school abinta, cikin Sadiya yana ta kara fitowa ni kuwa gandoki har na fara tanadar kayan jarirai, lol. 1

☆☆☆☆☆

Cikin mamaki na daga wayata dake ringing bayan na duba sunan wanda yayi kiran, “Yau ko dai batan lamba waya kayi Harith?” tunda ya samu aiki a Ibadan ya tarkata ya tafi zumuncin dake tsakaninmu yayi kasa, shi aiki ni kuma karatu don haka we were not in contact recently, yace “haba Nafeesah, har ke kina da bakin magana? Sau tari zan tura miki sako ta whatsapp amma bana ganin reply dinki, anya idan da amana ruwa ya dafa kifi??” nayi dariya nace “kasan rayuwar dalibai sai a slow wallahi, shi yasa. Ka yini lafiya?” yace “yeah, Alhamdulillahi…” nan muka gaisa dashi da tambayar juna kwana biyu, yace “Sis take fada min ranar nan wai ai an saka miki ranar aure, shine nace bari in kira in tambaya inji laifin me nayi da ban samu labari ba?” nayi murmushi nace “to kuma kawai daga sa min aure sai in hau shela? Kaima ai naji ance ka kai kudin aure gidan su Ikram” yace “yeah… Amma ya aka yi kika sani? Ko abokaina basu san da labarin ba” nace “nima a gari naji, amma daga majiya mai tushe, Ikram din ce da kanta take fada min” yace “iye lallai naga nuna wariyar jinsi, so u guys have been in contact with each other amma shine kike fada min wai wani rayuwar dan makaranta and stuffs ko?” nayi dariya nace “ai kasan zumuncin mata ko ta yaya dai in a week ba su rasa yin waya shi yasa… So what’s up?” yace “mun shigo workshop ne cikin Kano, shine nace bari in tambaye ki idan ziyara is allowed, zan leko mu gaisa” nace “why not? You are welcome!” yace “to ba laifi, goben idan zan shigo I’ll inform you” daga nan muka yi sallama kowa ya ajiye wayar. Firdausi ta dago kanta daga typing din da take yi a cikin laptop dinta ta kalleni, tace “ni yanzu meye makomar ki idan an miki aure? Zaki ci gaba da zama cikin hostel ne ko kuma zaki zauna tare da kishiyar ki ne tunda har yanxu ba a gama gyara inda zaki zauna ba?” na zauna a gefen gadona ina sighing, “ban sani ba nima wallahi, but kila, may be in ci gaba da zaman hostel” tace anya? I doubt idan mijin nan naki zai yarda, na harareta “me kuke nufi wai? Abinda Sadiya da Ramlah suka ce kenan dama” tayi dariya, “to ai yadda yake nunawa ne, he’s barely holding it in, a dokance yake kuma a kagauce da auren nan, azo kuma ace an daura amma ya barki ki zauna a hostel? Ni dai a ganina da kyar ya bari” na dauki dan karamin filo na jefeta dashi, “ke fa m dinki karama ce wallahi, sam baki da kunya” ta fashe da dariya ni kuma na maida bayana kan gado na kwantar ina kara juya maganganunta a cikin raina, gaskiya a son samuna koda ace gyaran gidan da za a ajiye ni bai kammala ba to Abbu ya barni in ci gaba da zama a cikin hostel abina har sai an gama don ni fa har ga Allah ban shirya fuskantar Anty Mubeenah a matsayin kishiya ba balle har ta kaini ga zama a gida daya da ita a matsayin kishiyoyin juna, woah! Ko ya zaman zai kasance?? Na gyara juyawa a kan gadon tare da janyo face mask na rufe idanuna, a hankali barci ya dauke ni. 4

Washegari lecture din Abbu gare mu, da wuri na tashi na shirya cikin jallabiya brown mai kwalliyar light ash a jikinta, ban yi wata kwalliya ta sosai ba na yi rolling gyale ash mai dan fadi, na zura takalmin vincci flat na fita da dan saurina, takwas saura ina cikin hall din, nayi ajiyar numfashi lokacin da nake zama a kan seat, Abbu baya tolerating late coming ko da wasa, minti biyar ya kara akan karfe takwas to ka hakura da lecture dinshi na ranar kawai, na tuna lokacin dana taba yin nauyin barci ban tashi da wuri ba, na isa wajen six minutes past eight na tarar da kofa a rufe, kuma fa Abbun yana kallona a tsaye a kofar class din amma yayi biris dani tare da sauran dalibai abokan latti na, haka muka gaji da jira muka kama gaban mu…. Na ciza bakina cike da takaici, har yau idan na tuno abinda ya faru sai naji kamar inyi me, kuma fa sabida shi nayi makarar, shi ya kira ni a daren ranar ya tsare ni da hira har dare ya tsala., ai kuwa dai da kyar ya samu ya shawo kaina. Na saki dan murmushi a hankali dana tuno irin bidirin da muka sha a lokacin. Ajin yayi tsit lokacin da Abbu ya turo kanshi cikin ajin, yayi shigar wani danyen vowel ruwan hanta, bai saka hula ba sai dai ya taje sumar kanshi da yake shi ba ma’abocin saka hula bane. As always, yayi kyau kamar ka lashe shi. Ya fara searching din hall din da idanun shi a hankali har ya lalubo ni, ya sakar min murmushi very soft and lovely, ban bata lokaci ba wajen mayar mishi da martani, yayi gyaran murya amma fa jefi-jefi idanunshi kan kalloni kamar yadda koda wasa nawa basu bar shi ba. 1

Muna gama lectures muka fita, tun saura minti sha biyar mu gama dama Harith ya min text kan cewa ya shigo cikin makatantar ina zai sameni, na tura mishi text din inda muke yace xai zo, don haka muna fita na hange shi inda ake ajiye motoci. Murmushi nayi na karasa wajenshi, ya wani kara fari ya kara zama magidanci kamar ba Harith din dana sani ba watanni hudu da suka wuce, shima mamakin da yake yi kenan yace wai na kara yin kyau nayi fresh, nan muka tsaya muna gaisawa sosai mun fara hira sama-sama ya kalli agogon hannunshi yace “I gotta go, Abuja zan wuce daga nan” nace “za aje a ga Amarya kenan? A gaishe ta” kamar ance in waiga bayana, ina juyawa na hango Abbu yana nufo mu, na zaro ido tare da juyawa ina kallon Harith dake kallona shima, fuskar nan ta Abbu a hade take murtuk, lallai yau kishin maza ya motsa. Sam banyi zaton har lokacin yana cikin department dinmu ba saboda ban ga motar shi ba, ai da banyi gangancin tsayawa da Harith a wajen ba. Harith yace “da alamun wanda zaki aura ne ke tunkaro ku” nace “ya aka yi ka gane? Ka san shi ne dama?” yace “not at all, but hararar da yake jefo min kamar zai kawo min naushi irin wadda nake wa duk namijin dana gani tsaye da Ikram” nayi er dariya, “he’s cute, isn’t he?” daga bayana naji anyi magana, “well, look who’s calling who cute” he sounds so close alamun yana bayana kenan, na ja gefe da dan saurina ina dariya cike da jin kunya, Abbu ya mikawa Hatith hannu fuskar shi babu yabo babu fallasa babu fara’ar nan dake tattare a fuskar shi, “Ibrahim Galadanchi” abinda yace mishi kenan coldly, ina ganin yadda yake glaring din Harith da hot gaze dinshi wanda zai iya grilling din kifi, da sauri Harith ya mika mishi nashi hannun suka yi musabiha yace “Harith, fiancé din Ikram cousin din Sulaiman mijin Sadiya” sai lokacin fuskar Abbu ta dan warware kadan daga hadeta din da yayi amma bata koma normal ba har lokacin, suka dan gaggaisa a tsaitsaye ya dawo da kallonshi gareni gareni da tun da naja gefe ban yi magana ba, kallon daya jefe ni dashi sai da yasa naji alamun kadawar ‘ya‘yan hanjina, yace “ki same ni a mota” da kyar na samu na iya daga mishi kai, ya wa Harith sallama ya nufi wata bakar Land Rover dake kusa da inda Harith yayi parking din tashi motar, haba ba mamaki ashe ya canza mota ne? Na kalli Harith daya jefe ni da murmushin mugunta, na harare shi ya wani yi shrugging yana daga gira sai kawai na girgiza kai don bani da lokacin biyewa tsokanar Harith, godiya na mishi muka yi sallama na wuce inda Abbu yake jirana na bude motar na shiga. Ina shiga yaja motar muka fara tafiya ba tare da yace uffan ba, na kalli fuskar shi har lokacin babu fara’ah a tattare dashi, da alamun na bata mishi rai sosai Jikina yayi sanyi, na maida kallona ga tagar motar ina jin kamar in fita ta ciki, da alamun yau Abbu na baya cikin walwala, duk saboda ni!!

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *