AMININ MAHAIFINA CHAPTER 13

AMININ MAHAIFINA







CHAPTER 13






Shiru muna cin abinci a cikin restaurant din da muke zuwa lokaci zuwa lokaci, baka jin karan komi sai karan cokali da plate din dake gaban Abbu yana cin abinci yayin da na kurawa nawa plate din idanu kawai, duk yunwar da nake ji sai naji ta tafi, babu space din komi a cikina a lokacin sai na numfashin da nake shaka. Fushin Abbu ya takura ni, ya tsorata ni, gabadaya na rasa abinda yake min dadi a lokacin. Tunda ya sadda kanshi ga plate din gabanshi bai dago idanunshi ba, na kula yana gudun kallona ne kamar yadda na kula cusa abincin kawai yake yi ba wai don yana jin dadin shi ba. A hankali nace “Abbu!” ya dakata da cin abincin da yake yi kafin ya dago ya kalleni, kyawawan idanuwan shi da a koda yaushe suke farare tas-tas suna sheki suna kallona cike da so da kulawa, sun rine daga ainihin kalar su zuwa ja-brown, gaba na ya fadi sosai ban taba ganin wannan kamar ta Abbu ba, ya maida kanshi kasa ya cigaba da cin abincin. Nace “Abbu don Allah kayi hakuri kar kayi fushi dani, kawai Harith yazo ne mu gaisa ba wani abu ba please” bai yi magana ba kamar yadda bai dakata da abinda yake yi ba, na sake cewa “kaji?? Please Abbu na!!” duk da cewa sau tari ya kan nuna bai son sunan amma na kula jin sunan daga bakina yana dadada mishi rai sai dai da alamun hakan bai yi tasiri ba yau, babu murmushin nan daya saba yi, bai yi scowling dinnan ba yana kallona dangerously kamar zai zuke ni da idanunshi, instead sai kawai ya kalleni yayi wani murmushi da bai ma gama hade fatar bakin shi ba balle fuskarshi, muryar shi tayi can kasa kamar wanda yake suffering daga cutar mura yace, “eat, Nafeesah!” ya cigaba da cin abincin, sai kawai naji gwiwoyina sun sage, me ke damun Abbu ne yau? Gabadaya ya wani rikice min kamar ba Abbun dana sani ba, ban taba ganin wannan Abbun da yake gabana ba don haka ne naji nima na gigice sosai. Na xuba duka tafukan hannuwa na biyu a cikin kumatuna kawai na kura mishi idanu, ban damu da cewa hakan zai takura shi ba ko kuma idon mutane dake cikin restaurant din, ni dai fata na da burina shine in karanto abinda yake damun Abbu inyi gaggawar magance mishi koma meye sai dai ban karanci komi ba, ya gama cin abincin ya dago ya kalli plate dina sai kuma ya tashi, yaje ya biya kudin abincin suka dawo tare da yaron wajen aka maida nawa abincin cikin take away muka fita daga restaurant din. Ko a cikin mota ma haka tafiyar ta kasance, yayi wani kicin-kicin da rai kamar wanda aka aikowa da sakon mutuwa. Har muka je bakin hostel ya samu waje a parking lot yayi parking. Na dan saci kallonshi kafin na yunkura da niyar fita daga cikin motar ya katse ni ta hanyar kiran sunana, “Nafeesah!” na dakata amma ban juya na kalleshi ba, na tsani ganin expression din fuskar shi kamar yadda na tsani mutuwata. Murya a hankali yace “kiyi hakuri don Allah” cike da tsananin mamaki na juya na kalleshi, fuskar shi nuna how apologetic he was, nace “me ya faru?” ya girgiza kanshi, “na saka ki cikin damuwa saboda son rai irin nawa, you didn’t do anything wrong amma na saka ki gaba ina hade miki fuska, na…” ya sadda kanshi kasa saboda maganar data kakare mishi ni kuma na kura mishi idanu, he looks soooooo lovely and adorable, Anya soyayyar Abbu zata barni in rayu cikin dadin rai?? Ya sake dago kanshi ya kalleni, wannan karon babu bacin rai dake tattare dashi sai idanuwanshi dake nuna tsananin so, kauna, kulawa da wani abu kamar tsoro? I’m not sure. Yace “I was afraid” cikin mamaki na kalleshi nace “of what?” ya girgiza kanshi, “I don’t know. Kawai tunda na ganki da wani a tsaye naji wani tsoro ya dabaibaye ni, I really cherish you alot Nafeesah, I was afraid of you leaving me ko wani ya juye miki tunani daga gareni, idan hakan ya faru ban san ya zan yi ba!” wannan ba Abbu Baban su Hafsat da Abdullahi bane, wannan Ibrahim ne a zamanin da yake kan ganiyar kuruciyar shi, na muskuta ta yadda zan fuskance shi sosai, “ni ko wanene kwanakin baya yake cewa ba zai zauna yana soyayya irin ta yara ba? I wonder ko wace kalar soyayya ce wannan?” ya dan jefe ni da harara, na na danyi murmushi kafin nace “nima idan hakan ta faru ban san yadda tawa rayuwar zata kasance ba Abbu, idan hakan ta faru I’ll be more shattered than u, gwanda kai kana da mata da ‘ya‘y’a ni kuwa dama daga kai sai Mommy da Daddy nake dasu” ya kura min idanu kaman wanda yake kokonton abinda nace, na saki murmushi reassuringly “kada ka damu Abbu, in shaa Allahu abinda kake tsammani ba zai taba faruwa ba, I am yours, and I’ll always be in shaa Allah!” ya lumshe idanunshi for a second, daya bude duk wani duhu da rikicin dake cikin idanunshi sun yaye, damuwar data lullube shi ta tafi, Abbuna ya dawo kamar yadda yake, ya saki kayataccen murmushin nan nashi, “you are almost mine dai but at least am relieved, God! Kin tsorata ni wallahi, amma do you really mean what you said?” wai sai a lokacin naji kunya ta dabaibaye ni, nayi gaggawar Kai hannu na rufe fuskata, ina jin er dariyar da yayi, “ana so ana kaiwa kasuwa…. Zaki yi bayani ne idan aka miki snatching” fuskana na cikin tafukan hannuna nace “ai babu wanda ya isa ya kwace min abinda nake so!” ya rankwafo kanshi kusa dani yana wani smirking, ina kallonshi ta yatsun hannuna, yace “Ashe dai ana so na?” da sauri na bude murfin motar na fita na barshi yana dariya, da alamun abin ba karamin dadi yake mishi ba, haka kawai naji murmushi ya subuce min. Ya fito daga cikin motar shima, “tambayar ki fa nayi baki amsa min ba” inaa, ai nayi gaba abina. Yace “to tsaya ki amshi abincin ki” naja tunga na tsaya, ina ji ya bude motar ya dauko takeaway din ya tako zuwa inda na tsaya ya miko min, nasa hannu na karba ina wani sinke fuska, ya wani kuta kamar gaske “zaki yi bayani ne wallahi, sai ki wani dinga sinke fuska kina cuta na wai ke kunya, Allah ya kaimu ranar da zaki shigo hannuna” na saki murmushi, yace “dariya ma kike yi koh? Allah Nafeesah kina bukatar in gyara miki zama, dazu kin ce wai I was cute, yanzu kince ina soyayyar yara and ina magana kina dariya koh?? Sai na tabbatar dana hukunta bakin nan naki da baya jin magana wata rana” dariya na dan saki kasa-kasa, da alamun yau en rigimar ne akan Abbu. Naci gaba da tafiya abina, ya tsaya a inda yake yana magana cikin korafi, “wato ma tafiya kika yi kika barni koh? Ba komi, sai kinyi sati biyu baki sake ganin mai kama dani ba, kai sai ranar auren mu zaki sake ganina ma” na juyo ina kallonshi nace “to ka gaida gida dasu Hafsy” yayi wani irin chuckling daya sa ni bude baki ina kallonshi, ji nayi kamar in ruga da gudu in fada cikin faffadan kirjin shi, sai nayi murmushi kawai tare da girgiza kaina na wuce cikin hostel. Kafin in karasa daki kiran Anty Raheena ya shigo wayata, na daga muka gaisa da ita. Tace wai kira tayi in fada mata size dina zasu siyo under wears da za a saka a cikin kayan lefena, ni wallahi kunya ma ta bani. Da kyar na iya bude baki na fada mata, ko sallama bamu yi ba na kashe wayar.Bayan kwana biyu aka kai akwatina gidanmu, guda takwas sai kit, sai ta waya Anty Uwani ta turo min akwatunan na gani, wasu azababbun akwatuna kirar kasar Italy na zallan fata kalar pink ne, kayan dake ciki kuwa kama daga shadda, lace, materials, atamfofi, takalma ma kadai daga na kamfanin vincci, dg, poshter, ga jakunkuna da jewelries duka babu kanana gaskiya ba karamin kokari Abbu yayi ba wajen hada kayan nan, na dinga gyada kai kawai lokacin dana dinga duba kayan, ‘kaya kam sun yi kyau gabadaya babu na yar wa sai dai fatan in more su a gidan aurena cikin tattali da soyayyar juna ni da mijina’., a cewar Anty Uwani, ni kam na amsa da ameen a cikin raina. +

☆☆☆☆☆☆

A hankali ya gangara motar shi cikin gareji yayi parking, “Amour, sai anjima, take care” nace “toh Abbu na, take care too” yace “mimm, wai Abbu” dariya kawai na saki wadda nasan tana saka shi cikin nishadi na kashe wayar, yayi murmushi yana bin farar Toyota data shigo cikin gidan tayi parking a daidai inda yayi parking din tashi motar. Saddiqa babbar Yayar su Mubeenah ta fito daga cikin motar, shima fita yayi ya gaidata cikin girmamawa, ta amsa a tsaitsaye tana kumburi kafin ta wuce shi fuu, ya bita da kallo cike da mamaki, matar tana da kirki unlike sauran kannen Mubeenah da ita kanta Mubeenar, duk cikin danginta daga ita sai Shafa’atu ne masu sanyin hali a cikin su, yau kam ko mai ya hau kanta? Ya tabe baki ya wuce wajen maigadi suka dan yi en maganganu ya shige cikin gida. Tun daga cikin falo yake jiyo hayaniyar dake tashi daga can dakin Mubeenah. A can dakin na Mubeenah kuwa akwatuna ne a tsakiyar dakin manya har guda shida, Saddiqa na tsaye a gabansu ta kama kugu tana kallon Mubeenah dake kwance akan gado tana latsa waya, tun kayan barcin ranar data tashi dasu ne a jikinta bata canza ba gashi lokacin har karfe hudu na yamma, gashin kanta ya cukurkude ya cure waje daya, Saddiqa ta saki kugu data kama ta fara tafa hannayenta tana sallallami bayan ta gama sauraren abinda kanwar tata Mubeenah ta fada mata, “Innalillahi…. Mubeenah?! Anya kina da hankali kuwa? Kishiya ake shirin miki amma what?? You are cool with it?? Wai ke wace irin mahaukaciyar yarinya ce Mubeenah??” ta dago ta kalli Yayar tana gunaguni, “ni fa wannan aure za zai yi gaba ya kaini ba baya ba, kina kallon akwatunan daya zube min shake da kaya a matsayin kayan fadar kishiya, 5 millions ya bani in kara jarina bayan haka yana nan yana sake gina mana sabon gida kuma ya min alkawarin zai canza min kayan daki sababbi, bayan haka ita yarinyar da zai aura ta zauna damu anan, na riga da nasan halayenta ciki da bai na tabbata da cewa ba zata taba cutar dani ba balle ‘ya‘ya na ke in fact na tabbata Ibrahim ba wai don yana son ta zai auro ta ba sai don kawai ya bani haushi kamar yadda yake fada tun ba yau ba, to kin kuwa ga menene nawa na yin fushi ko in wani kama bori kamar yadda kike cewa inyi? Kin ganni nan wallahi ko a kwalar rigata, in dai aurene yaje yayi tayi ga fili ga mai doki” bayani take zubawa tun karfinta babu ko digon aya balle comma, yayin da Saddiqa ta sake baki da hanci tana kallon kanwar tata kamar wadda tayi gamo, ta jijjiga kai cike da takaici tace “naji dai ana cewa ke mahaukaciya ce, amma ban taba zaton cewa haukan naki ya kai mataki na farko ba sai yau. Ke don kaza kazar ki, (ta kawo zagi ta lailaya mata), kowace mace tana shiga cikin tashin hankali da fargaba idan za a mata kishiya, amma ke kina zaune hankalinki kwance kina gaya min wai an baki jari kuma za a miki sabbin kayan daki. Kudin banza kudin wofi? Ke don ubanki kin manta yadda muka sha dabi da amaryar Abban mu?” ta kuta, “koda yake kina yarinya dama ya za ayi ki tuna? Ga kuma wata irin kwalwa ta kifaye da Allah ya halitta miki?” ta wani cuno baki gaba, “Na gaya miki yarinyar tana da kirki sam ba halinta daya da sauran matan da kike fada ba…” Saddiqa ta warci kofin dake kan mirror ta saita bakinta ta jefeta dashi Allah yasa ta kauce da sauri, da sai ya dauke mata hakoran gaba biyu, Saddiqa tace “banza mahaukaciya wadda bata san inda yake mata ciwo ba. Kina ta daga murya kina wani fadan cewa kin san yarinya, kin san halinta ko tasan naki halin? Tazo gidanki ta zauna ta gama sanin sirrinki dana gidanki ciki da bai, taga weakness dinki taga komi naki, taje ta gama damarar kwace miki miji daga hannun ki amma kina zaune hankalinki kwance har kina da confidence din daga min wannan bakin naki ki ce wai kin san halinta?” da alamu ko kadan maganganun Saddiqa basa shiga kunnen Mubeenah, tace “ke ce kika kasa fahimtata dai, ni nasan Abinda nake yi. Da wadda ban sani ba ai gwara wadda na sani, ko babu komi yarinyar tana da biyayya sau da kafa, hakan zai bani damar juyata yadda nake so!!” Saddiqa ta dafe kanta da hannuwa biyu kamar zata kurma ihu, Mubeenah ta kalleta cikin mamaki, “wai ni kam don Allah menene damuwar ki akan maganar auren nan, ke za a yiwa kishiya ko ni?” Saddiqa tace “Yi miki kishiya fa kamar yi mana ne, kin sani kamar yadda nima na sani, Ibrahim zama yake yi da ke kawai ba wai don yana jin dadin zama dake ba, kin sani” Mubeenah ta katse ta, “ni nasan Ibrahim yana so na” Saddiqa ta daka mata wata tsawa data sa tashi zaune dangargar akan duwawunta babu shiri, tace “ki min shiru Mubeenah!! Ke ce banza da kika kasa tantance so da dole, idan kika kuskura kishiya ta tako kafarta cikin gidan auren ki wallahi ina mai tabbatar miki da cewa kashin ki ya bushe, idan kin san ma’anar OUT to tsab zata yi waje dake kuma ina mai tabbatar miki da cewa idan har kika sa kafa kika bar gidan Ibrahim to ki tabbata cewa kinyi sallama da aure, I am as sure as hell babu wanda zai yi marmarin daukar ki a matsayin mata a yadda kike dinnan, wallahi Ibrahim kadai ne rufin asirinki” Mubeenah tace “Ibrahim yana so na, ku daina cewa wai baya so na, auren da zai yi babu abinda zai ragu daga son da yake yi min” Saddiqa ta juya ta kara juyawa a cikin dakin kamar wadda take fareti, “idan na gama da case din auren ki I’ll make sure to take you to psychiatrist for sure. Amma kafin nan bari inje in samu Haja (mahaifiyar su) babu macen data isa ta shigo gidannan wallahi” ta sa kafa ta bar dakin fuuu a matukar fusace kamar guguwa, Mubeenah ta daga kafada ta koma ta kwanta abinta. Saddiqa na fita taci Karo da Abbu a tsakiyar falo, bata damu da cewa yaji maganganun su ba ko bai ji ba ta shura kafa ta bar gidan. Ya girgiza kan shi a hankali yana murmushi amma fa can kasan xuciyar shi ji yake murmushin yafi mishi madaci ciwo, zuciyar shi kamar ana diga masa ruwan dalma saboda yadda take azalzalar shi da kuna, me yafi ciwo irin kaji cewa matar aurenka bata kishin ka??
~So what did you think about today’s chapter?
~Kuna tunanin akwai mata irin Mubeenah a cikin duniyar nan kuwa? Idan akwai, wane irin hukunci kuke ganin ya dace da ire-iren su??Na cewa Jalilah class mate dina, “ki wuce hostel kawai, akwai inda zan je” tace toh sai kin dawo. Har ta fara tafiya sai kuma ta juyo tace “naji wani rumor yana yawo a cikin class dinmu, wai zaki yi aure?” na dan jijjiga mata kai ina murmushi, tace “amma gaskiya ban ji dadi da baki fada min ba” nace “sorry, auren ne kawai za a daura kin gane? Shi yasa ma ban wani yi shela ba saboda ina makaranta ma za a daura” ta matso da bakinta saitin kunnena cikin rada, “amma naji ana cewa wai wani lecturer ne anan zaki aura, da gaske ne??” na zaro ido cike da mamakin yadda aka yi zancen ya isa garesu, koda yake dama an ce zancen duniya baya buya. Nace mata “rumors ne kawai amma ba haka bane” tace “idan ma hakan ne meye na wa ko na mutane a ciki? Allah ya baku zaman lafiya mai daurewa” na mata murmushi ina kokarin boye dariyar data ciwo ni don nasan magana ce ta fada min, nace Ameen. Ta juya ta tafi abinta. Na duba agogon hannuna naga karfe sha daya ne da rabi lokacin, da sauri na dauki hanyar da zata kaini ofishin Abbu don nasan yana can yana jira na, ranar juma’ah ce ga masallaci ga kuma cinkoson ababen hawa. Na tura kofar office din na shiga fuskana dauke da murmushi, duk lokacin da zan ga Abbu sai in dinga jin wani irin doki da farin ciki a cikin raina kamar wadda ta shekara bata ganshi ba, alhalin duka duka jiya alhamis har karfe tara na dare muna tare dashi, ranar ta Jumma’ah da safe wayar shi ta tashe ni daga barci, muka gaisa ya maimaita min how eager he was to have me as his, farin cikin da yake ciki saboda samuna da yayi a cikin rayuwar shi. A gare shi wadannan kalmomin kamar wasu routine words ne da ya saba fada min a duk sanda muke tare, a gare ni kam they were far more than golden and diamond words, suna saka ni cikin tsananin farin ciki da jin dadi, suna hana duk wata damuwa da bacin rai samun matsuguni a cikin raina, they were my remedies. Ya juyo daga gaban book shelves din dake kusa da desk din computer dinshi, wani tattausan murmushi ya sakar min da suka sa naji alamun butterflies na yawo a cikina, sanye yake da wandon jeans blue da knit shirt mai kama da sweater, irin shigar da naga samarin zamanin nan nayi kenan a wannan lokacin, shima sai ta maida shi kamar wani saurayin bayan kyawun data mishi, Abbu yasan kan fashion kamar wani fashionista shi yasa ko wane irin kaya ya sanya suke haska shi. Ya maida littafin dake hannunshi cikin jerin littafan dake cikin shelves din, ya juyo gareni gaba daya yana murmushin nan nashi dai, kallona yake kamar wanda zai tsuke ni ta cikin idanuwanshi, it was so intense and disconcerting sai dana ajiye idanuwa kasa ina jin kamar kasa zata tsage in shige, yace “tun dazu nake jiran ki yanzu nake shirin biyawa ta library din in duba ki” nace “ban kula da cewa lokaci yaja bane, sorry!” ya dauki wata jaka mai kama da box dinnan akan tebur ya miko min, nasa hannu na amsa ina kallon shi cikin alamun tambaya, ya dan jingina jikinshi da teburin yace “akwai reception da aka hada mana ranar Sunday, kayan da zaki saka ne” na bude jakar na kalli kayan ciki, shadda ce bugaggiya ruwan kasa mai haske sai jaka, takalmi, da gyale su kuma dark brown kalar zaren da aka yi amfani dashi wajen yin surfani, na kara kallon shi nace “ranar Monday fa zamu fara exams dinmu” yace “ba zai taba karatunki ko jarabawar ki ba I promise, ni kaina ban san da zancen ba sai da suka riga suka shirya komi sannan suka sanar dani. I don’t want to disappoint them, please help Nafeesah kinji?” yadda ya wani rausayar da kai yana kallona pleadingly, who m I to say no to him a yadda yayi dinnan taking my breath away?? Sai kawai na girgiza kai ina murmushi, nace “Allah ya kaimu ranar” yayi murmushi “Ameen Amour…. Mine” na sunke kai a cikin hijabina, ya wani kuta, “just wait till tomorrow, war haka kin zama tawa, mallakina ta har abada, wannan kunyar taki sai nasa kin neme ta kin rasa” ya saki murmushi mai sauti, “Allah ya kaimu goben nan dai, I really can’t wait baby” na kara kanannade fuskata a hijabin, jin abin nake yi kamar a mafarki, mafarkin ma wanda ba zai zama da gaskiya ba, wai goben ne daurin Auren mu? Oh, zan zama matar Abbu, Abbu na wanda so da qaunar sa suka mamaye jini da jijiyoyin jikina, na kauda tunanin daga cikin raina bana so in fara fayyace matsayin da gobe take a gare ni don nasan ba zan gama da wuri ba. Ya dauki key din motar shi muka fita, na jira ya rufe office din kafin muka fara tafiya a hankali zuwa inda ya ajiye motar shi. Ya bude motar ya shiga ciki ya juyo ya kalleni, “sorry, bazan iya maidaki hostel ba saboda sai na biya na dauki su Abdullahi sannan mu wuce masallaci” nace “babu komi, a gaida su” ya gyada kai, “zan kira ki anjima” na maida mishi murfin motar na rufe, ya mata key ya tafi ina daga mishi hannu, sai dana ga fitar shi sannan na daga kafa da niyar tafiya. Kamar daga sama naga tsayuwar mutum a gabana, naja baya a dan tsorace har ina dafe kirji ina jan salati, Matar nan da muka hadu da ita a ofishin Abbu ranar nan ta bayyana a gabana, da alamu shigar rashin mutunci da na ganta da ita ranar a jininta take don kuwa lokacin ma irinta ce a jikinta, zan iya cewa ta ranar tafi ta waccan lokacin bayyana surar jiki ma. Hararata take yi tun karfinta da gwala-gwalan idanuwanta da suka sha uban eye shadow da girar kanti in ka ganta kamar wata doll. Nima na mayar mata da kwatankwacin hararar da take jifana dashi, “Malama lafiya zaki tare min hanya?” ta kama kugu tana wani jijjiga jiki, “ina so ne in fada miki ki rabu da Ibrahim” nayi fuskar alamun tambaya “me yasa?” ta dan daga murya, “saboda nawa ne! Na sha alwashin babu wadda ta isa ta aure shi muddin ina raye” nace “da alamu baki samu labarin cewa gobe ne daurin auren mu dashi ba, na tabbata da kin sani kam da ba zaki tare ni a hanya kina barking kamar tsohuwar karya ba” a girmame matar ta girme ni nesa ba kadan ba, sai dai ni a rayuwa na sau daya zaka zubda daraja da kimarka a idona, abin na matar yayi yawa, ko a lokacin da nayi shirmen son Muneer ban taba tunanin zan yi kwatankwacin abinda take yi yanzu ba, bin kan namiji yana wulakanta ni kamar karya amma in ki in hakura har ta Kai ni ga bibiyar wadda zai aura ina threatening dinta. Fuskar ta tayi looking so pale saboda maganar da nayi, “ni kika kira da karya? just wait, in har ina raye sai na mayar dake abin kwatance, sai na muzanta ki fiye da kare, I’m warning u, ki fita daga rayuwar Ibrahim kafin in mayar dake abin kwatance!!” na daga kafada, “I’m not stopping you from doing whatever you will do, kawai abinda nake so yanzu shine ki matsa ki bani hanya in wuce” ta hasala iya hasala, hannu ta daga kamar zata mare ni, kallonta nake yi kamar wata kayan kashi a yatsine, ita da kanta ta janye hannunta ta maida shi kasa, nayi murmushin mugunta nace “kece kike ta shirme kina bin namijin da yake kin ki, tunda yace baya yi let him be, ana so dole ne malama?” ta wani zare ido tare da buga tsawa “ke…!!” nayi saurin katseta kafin ma ta gama fadin abinda tayi niyar cewa ta hanyar zare ido nima, nace “malama kin ganni nan ban yi kama da matan da threats dinki zasu yi tasiri a kan su ba, kiyi duk abinda zaki yi wanda kike ikirarin mallaka ba zaki taba mallakar shi ba saboda ba don ke aka yi shi ba, a shawarce zan gaya miki ki fita daga rayuwar shi, Idan kuma kin ki ji sai dai kiyi mutuwar da kike ikirarin yi! Abbu ne kamar na aure shi na gama” naja tsaki tare da zagayawa ta gefenta ta wuce abuna ina muttering kalmomin dani kaina bansan me nake fada ba duk don in yi provoking dinta, na kuwa yi nasara. Ina bada baya naji sautin karan data saki cike da takaici, na kuwa saki murmushi kamar zan sheke da dariya. 1

Washegari da misalin karfe daya aka daura auren a babban masallacin juma’ah dake garin Malumfashi. Muna zaune a dakinmu Ni’imah ta kawo wata yarinya tana min kunshi wanda hakan umarnin Abbu ne, text dinshi ya shigo wayata. Na mika hannu na da nake jin shi kamar ba a jikina yake ba na dauki wayar, kai gabadaya ma sauran sassan jikina haka suke tunda garin ranar ya waye, ina ji Niimah da Firdausi suna ta hira amma na kasa saka musu baki duk da cewa rabin hirar a wajen tsokanata ne. Text din cewa yayi, “Alhamdulillah. Yanzun nan aka shafa fatiha, kin zamo tawa ta har abada. Ina taya junanmu murna da farin cikin mallakar junanmu, Allah ya bani ikon rike ki cikin amana da kulawa Nafeesah” sai kuma wani da yace, “Wannan ranar rana ce da ban taba tunanin zata Riske ni ba, ranar dana mallaki abinda ban taba kawowa raina zan mallake shi ba. Jina nake kamar wani sabon halitta saboda tsananin farin cikin da nake ciki wanda na kasa misalta shi, Nafeesah kina da gurbi mai matukar girma da fadi a cikin zuciyata, na roki Allah mai Girma akan ya bamu zaman lafiya mai dorewa. You’ve Completed My Puzzled and Shattered Life, I really Cherish You Nafeesah” naji hawaye sun cika min idanu, nayi saurin runtse idanun ina kokarin maida hawayen, Allah abin godiya da Girmamawa, wai ni ce yau na zama matar Abbu?? Naji ina narkewa kamar wata jelly akan kujerar da nake zaune, na tabbata da ace ina tsaye ne da sai na fadi. Rangadediyar gudar da Ni’imah ta rangada ce ta dawo dani cikin tunani na, guda take tun karfinta da waya a hannunta ta hau kiran waya tana bada albishir din an daura aure. Wayana ya shiga kara na daga, Daddy ne. Cikin rawar hannu na daga, “Uwata! Amarya!!” abinda na fara dokar kunnena kenan, na kasa magana sai kai dana jijjiga, yace “Nagode Allah da yasa naga wannan rana, ranar dana damka amanar ki a hannun wanda na tabbatar zai rike ki dari bisa dari, dama babu burin duk wani uba na kwarai daya wuce wannan. Yau dai kin zama matar Ibrahim, kin fita daga karkashin kulawar mu kin koma karkashin shi, yanzu shi zai yi sanadiyar ki zuwa gidan Aljannah wadda nasan babu haufi zaki sameta da yardar Allah uwata, Allah ya miki Albarka, Ya Albarkaci Rayuwar Auren ki, Allah ya baku zuriya Dayyiba!” muryar shi tayi kasa can kamar wanda yake so yayi kuka, ni kam kasa daurewa nayi kawai na fashe da kuka, gabadaya wani iri nake jina a tunanina idan nayi kukan zan samu sanyin zuciya. Ya shiga lallashina har na samu nayi shiru kafin ya min sallama. Yana kashe wayar kiran Mommy ya shigo, itama dai Addu’ah ta min kamar yadda Daddy yayi, zuciyar Mace mai rauni, sai tasa kuka, nima kukan nake yanzu sosai su Ni’imah na aikin bani hakuri, ina ji daga wayar Anty Uwani da muryar wasu mata suna ba Mommy hakuri, Anty Uwani cikin fada tace “sai kisa hankalinta ya tashi ai, gashi nan itama kin sata kuka, ina amfanin haka?” tace “kukan farin ciki ne” tace “ai godiyar Allah ya kamata kiyi ba wai kuka ba, shima Abban nata yanzu na baro shi a waje yana share kwallah Allah yasa ba ita ya kira yana kukan ba…. Wannan ai sai ku sanyayar mata da gwiwa….” daga haka dai suka kashe wayar. A hankali nima nawa kukan ya fara yin kasa har ya dawo shessheka kafin nayi shiru ina ajiyar rai. A ranar dai har ba zan iya lissafa iyaka mutanen da suka kira ni suna taya ni murnar yin aure ba, tun daga kan abokaina da yan uwa har wasu daga cikin abokan Mom. Da yamma sai ga Ramlah ta dira a Kanon kamar daga sama, muka yi tsalle muka rungume juna ni da ita muna ihun murna, watanni biyar ciff tunda muka rabu da ita bamu sake haduwa face to face ba sai dai a Video call. Muka zube akan gado muna maida numfashi daya bayan daya, kallona take tun daga sama har kasa ta kyalkyale da dariya, “kaga Amarya a gidan Ibrahim Galadanchi, kin ga wani kyau da kika yi kuwa??” na kai mata duka ina dariya, “meye haka zuwa babu sanarwa?” tace “surprise, dazu na dawo har mun yi hutu abinmu” nace “kun huta ku kam” nan muka shiga hirar yaushe gamo, tana nan tare dani har aka kira sallar magriba, ganinta ne yasa na warware har na samu naci abinci. Nan dai ta min sallama ta tafi akan cewa zata dawo Washegari, bayan na rakata zuwa bakin kofar hostel din na koma daki nayi sallar isha’i, bayan na gama na zauna nayi ta jero addu’o’i game da neman albarkar Allah da zaman lafiya a cikin sabuwar rayuwar da nake tunkara a cikin rayuwata. Abbu ya kira ni yace yana jirana a parking lot inda muka saba tsayawa, na tsinci kaina cikin faduwar gaba da sanyin jiki, cikin sanyin jikin na tashi na gyara zaman hijabin jikina na sauka kasa. Jingine yake da motar shi yana danna wayar shi, sanye yake cikin shadda ruwan Makuba yau kam har da hula a kanshi, akwai wadataccen haske a wajen hakan ne ya bani damar ganin fuskar shi sosai kamar cikin rana. Tunda na hango shi naji kafafuna sun fara hardewa, ban taba tsintar kaina cikin fargaba da tsoron fuskantar Abbu ba tunda nake a rayuwata sai ranar, da kyar na iya karasawa gaban shi ina maida numfashi kamar wadda ta sha gudu, babu abinda yayi motsi a jikinshi sai idanun shi da suke kare min kallo tun daga sama har kasa, kafafuna ba zasu taba iya daukana a haka ba sai nima na jingina da jikin motar ina kallon zara-zaran yatsun kafar shi da suka fito ta cikin kyakkyawan bakin budadden takalmin kafar shi yana ta sheki…..
~Yau dai Allah yayi Dare Gari ya waye An Daura Auren Nafeesah da Abbu, Woah!A hankali ya sauke ajiyar zuciya wadda take nuna tsananin farin cikin da yake ciki, “Hii there My Queen, My Happiness, My Amour, My Bride! Sunayen naki suna da yawa fa, amma kullum zan dinga kiran ki da guda daya wanda nasan sai mun dauki shekara basu kare ba, how are you?” kunya ta kama ni na sadda kaina kasa, yau ko sallama ban iya nayi ba balle in gaida shi, haka kawai naji wani nauyi da matsananciyar kunyar shi sun dabibaye ni.
A hankali kuma kamar wadda aka tursasa na bude baki nace “Ina yini Abbu?!” ni kaina sai da nayi mamakin muryata, it was very low kamar wadda take rada, ban yi tunanin yaji abinda nace ba sai da naji yaja wani sharp breath har yana hadawa da lumshe ido, “Masha Allah!” ya furta a hankali yana kallona da lumsassun idanuwan shi, ya Allah!! Da ace yasan yadda kallon yayi affecting dina da yayi gaggawar dauke idanunshi daga kaina saboda nasan ba zai so amaryar shi ta zube kasa kila hakan yayi sanadiyar karyewar kafarta ba, sai ya ci gaba da kallona kawai. Na samu nace “Ya hanya?” duk don in katse kallon da yake jifa na dashi da kuma hirar da zukatanmu suke yi, yace “Alhamdulillah, akwai gajiya kam amma tunda mun iso lafiya ai shikenan, besides ni tunda na ganki ma naji ni kamar an dauke min duk gajiyar dake tattare dani” nayi kasa da kaina, yace “Dad dinki ya bada sakon gaisuwa a kawo miki, ya damka min amanar ki har sai da sashen karbar sakonni a kwalwata ya cika, he even threatens me, heol!!” ya wani yi rolling idanu tare da dan chuckling, na kalle shi ya haske ni da murmushin nan nashi da yake sa ni yin abin da ban shirya ba, ba shiri na sakar mishi murmushin. Yayi cocking kanshi gefe guda, “ko ke fa! Keep smiling like that baby, yau fa rana ce ta musamman a gare mu bai kamata ace murmushi ya kau daga kan fuskar ki ba…. Hmm, how I wish gidana za a kaiki yau din nan, da sai na nuna miki kaunar da babu namijin daya taba nunawa wata ‘ya Mace a duniyar nan, na saka ki a cikin farin cikin da baki taba tsintar kanki a ciki ba, amma tunda hakan ba zai samu ba zan rike komi har sai an kaiki gidana baby, ranar….” sai kuma yayi shiru yana girgiza kai, “it will be a surprise, sai kin zo kawai zaki gani” ya duba agogon hannunshi, motar ya bude ya fito da leda ya miko min, tun kafin in amsa nasan ko menene a ciki, kaza ce gasasshiya sai tashin kamshi da tururi take yi, yace “bana son farin cikin ciyar da amaryata a daren aurenmu ya wuce ni duk da cewa ba ni da kaina zan ciyar dake ba” nasa hannu na amsa tare da mishi godiya, yace “you must be tired, jeki ki kwanta, nima zuwa zan yi inyi barci don ji na nake yi very exhausted Allah ma dai yasa in iya yin barcin” ni dai ban tanka mishi ba na daga Baki da kafa a lokaci guda nace “sai da safe”.
    Suddenly naji an janyo hannuna an dawo baya dani, kafin inyi yunkurin kwace hannuna da kaina gabadaya ko kuma ma in tantance abinda ya faru na tsinci kaina akan faffadan kirjin Abbu, yasa hannu daya ya dago habata ya kalli tsakiyar idanu na, abubuwan dana karanta a idanunshi a lokacin suna da yawa, zallan so, tsabar kawa, raw lust Ya Allah I couldn’t take it, idanuwana na kame don ba zan iya cigaba da karbar sakonnin dake fita daga cikin idanunshi ba, naji hucin numfashin shi akan fuskana ban taba kawo komi ba sai da naji bakin shi akan nawa, it was as if duniya ta tsaya cak da juyawa, ya dago ya kalli fuskana da idanuwan suke rufe yace “it’s something that I’ve wanted to do decades ago but being the good man I am holding it in, I Love You Nafeesah!!” abubuwan sun yi wa kwalwa ta yawa a lokacin har na rasa da wanne iri ne zan ji, his sudden kiss ko kuma sudden kalmar yana so na daya furta?? Na daga idanuna da suka min nauyi na sauke su a fuskar shi, kallona yake fervently, sai naji ni kamar wata danyar nama a gaban zaki, da dan sauri na janye hannuna daga nashi hannun, cikin sauri na juya na fara tafiya ina jin kamar wadda ake turawa don har ga Allah ban san ina nake jefa kafa na ba, ni kaina nasan ikon Allah ne ya kaini daki, nayi jifa da ledar daya bani akan slab na zube akan gado kamar kayan wanki na rufe kaina rikib da bargo, Firdausi ta bini da kallo baki a bude naji dadi da bata yi magana ba. Allah kadai yasan lokacin dana share a kwance a cikin bargon nan, daga karshe dai na mike saboda ihun da cikina yake yi na yunwa, tun macaroni din da muka ci da Ramlah da rana ban kara cin komi ba, na sauka daga kan gadon na dauki plate na bude ledar har da yoghurt a ciki mai sanyi duk da zafin kazar ya rage mishi sanyi, na dora ta akan plate da fork da er wuka na kai kan dan karamin bench da muka mayar kamar dinning na dora, na dauko kofuna da yoghurt din suma na ajiye, da hannu na wa Firdausi nuni alamun ta taso don ba zan iya daga baki in mata magana ba ma. Ta taso ta zauna a gefena tana wabi smirking, “Anya zan iya cin kazar amarcin nan kuwa? Idan aka tashi tambayana ita ya zan yi kenan?” nayi banza da ita na fara cin kazar, itama ta fara ci. Tace “ni naga kin wani firgice ne ko dai anyi abin ne?” na harareta tayi dariya kasa-kasa tace “dama sai dana gaya miki ai, mu dai ki rufa mana asiri ki bari sai mun kaiki kafin ki samu ciki kinji??” nan ma ban tanka mata ba, to ai ko nayi niyar tanka mata ma bani da kuzarin yin hakan. Ita kanta kazar jin ta nake yi tayi wani iri na bakina bana jin dadinta, sai yoghurt nayi ta kwankwada don shine mai sauki tunda hadiya kawai zanyi, sauran kazar Firdausi ta nade a cikin takardar ta ta saka a cikin fridge dinta. Littafai na dauko na dare kan study table ni ala dole zan yi karatu, koda na zauna babu abinda yake yawo akan littafin sai fuskar Abbu da murmushin shi, duk yadda naso inyi karatu a daren ranar abin yaci tura dole na hakura na koma kan gado na kwanta hannuna dafe da lebena wanda har lokacin nake jin tausasan lebunan Abbu akan su, it felt so awkward yet so good my body was shaking with desire. 10

                Sai bayan da nayi sallar asubahi sannan na samu na kara bitar karatu. Karfe tara muka fara exam dinmu muka fito kafin sha biyu, daga nan barci nayi don jiya kam ban samu nayi barcin kirki ba. Sai da su Ni’ima suka zo sannan na tashi daga barci lokacin wajen karfe biyu ne, sai da nayi sallah sannan muka shiga shirye-shiryen zuwa wajen Reception din. Suka wanke min kai suka kafar dashi kafin suka gyara min shi sai sheki yake yi da tashin kamshi, nayi wanka na fito nan ma aka shiga yin kwalliya kuma. Da aka kira la’asar muka yi saurara muka yi sallah sannan muka ci gaba, na zura doguwar rigar shaddar da Abbu ya kawo min, Ramlah ta daura min dankwalin rigar yayi kamar gwaggwaro, na saka dankunne, sarka da awarwaro masu ratsin brown a ciki, muna cikin yin shirin wanda aka turo ya dauke mu ya yi waya yace ya iso, da yake suma a shirye suke sai duk muka rankaya muka tafi. Wata er ubansun Range Rover ce baka tana ta sheki tazo daukar mu, aka bude mana muka shiga maza biyu ne a gaban motar don haka muka shiga baya muka tafi, daya daga cikinsu ya juyo muka gaisa har da yin shakiyancin su na abokanan ango, su Firdausi ne masu tare min ni kam kaina yana kasa, duk inda muka wuce sai an bimu da kallo wanda probably nasan cewa motar suke kallo don kuwa haduwarta ya wuce misali. 
              Tafiya muke yi a hankali har Hotoro, aka yi horn a kofar wani gida aka bude muka tura hancin motar muka shiga, anyi decorating din wajen da kayan ado da ake yi wajen bukukuwa ga kujeru an shirya, wajen cike yake da mutane ana ta hada-hada, aka yi parking sannan muka fita. Wasu mata gungu guda suka zo suka ja mu har wajen da na tabbatar saboda ango da Amarya aka yi shi saboda wajen ya fita daban, wasu royal kujeru guda biyu a kasan canopy an sa tuntu akai a kasa kuma an shimfida wani babban carpet me fadi da laushi. Mai gayya mai aiki Abbu yana zaune a kujera daya, munyi anko da kayan jikinshi shadda light brown mai surfanin zare dark brown, leather brown cover shoes da hular zanna bukar itama brown, kaina a kasa yake ban yi gigin daga ido na dubi Abbu ko tarin mutanen da hankulan su ya dawo gare mu har suka taimaka min na zauna a kujerar kusa da Abbu, in a wink sun bace daga wajen, photographer yazo ya fara haskemu da flashes ya dauki kamar guda goma kafin ya tafi. Abbu ya dan matso saitin kunnena ya rada min “kin yi kyau sosai amaryata” na danyi murmushi ina wasa da yatsun hannuna. Mutanen wajen basu da yawa duk da haka na hango wasu daga cikin dangina na Malumfashi mazan, Aminu, Haruna da Samir duk diyan kanne da Yayin Daddy ne, a matan wajen kuma na hangi Anty Amina da Anty Rahina, Sadiya, Saratu, Da Halima su kuma cousin din su Sadiya dinne, sauran matan kuwa da zasu kai guda goma ban san su ba na dai yi zaton kila matan abokan Abbu dinne. Ba wani bata lokaci aka fara gabatar da walimar, wani daga cikinsu ya bude taro da addu’ah, ya mana fatan alkhairi ana yi ana raha ana ta shan dariya saboda jokes din da mutumin ya dinga cracking, daga nan kuma aka yi en ciye-ciyen snacks da aka raba da kuma drinks, daya bayan daya suka dinga zuwa kowa da matar shi, mu gaisa dasu su mana fatan alkhairi su bamu kyauta, wani a cikin wrapping sheet wani kuma a envelope har su Anty Aminah dasu Ni’imah, daga nan kuma aka shiga daukar hotuna kamar me?! A haka har duhu ya fara shigowa, sannan ne fa aka kara rufe taro da addu’ah muka fara sallama dasu suna shiga motocin su suna tafiya, kafin dai a kira magriba an barmu daga mu sai mu, su Anty Ameenah ma suka mana sallama suka tafi, su Ni’imah sun bi mazajen su sun tafi sai Ramlah tabi bayan su Sadiya. Muka shiga falon matar gidan mai suna Farha ta mana jagora ni da Firdausi har cikin bedroom dinta muka yi sallah, matar tana da fara’ah ga kirki, muna gama sallah muka fara hira wadda yawancin ta akan rayuwar aure ne, challenges din dake cikin shi da shawarce-shawarce akan zamantakewa da kuma wasu shawarwarin da suka sa ni sunke kaina cikin gyale na, tace “kunya kike ji? Wallahi idan kika ce zaki saka kunya cikin rayuwar aurenki to zaki samu cikas kuwa more especially ke mai kishiya, ai wallahi dagewa zaki yi ki cire kunyar nan ki kama mijinki tsam kafin kishiya ko wata a waje ta miki kwacen shi” na gyada kaina cikin yarda da maganganunta. Su Abbu basu shigo gidan ba sai bayan sallar Isha, Farha tayi-tayi damu akan mu tsaya mu ci abinci muka ce a’ah, ta bude wani karamin Kit, tana bude shi wani kamshi mai dadi ya hade dakin, ta dauko kwalaben humra guda biyu ta bani ita kuma Firdausi ta bata turare, tace min “sai dai humra din nan ki bari sai kin tare kafin ki fara amfani da ita Zai fi” muka mata sallama muka fita waje inda Abbu yake jiranmu, muka sake sallama da Farha da maigidanta muka shiga mota muka tafi. Babu wanda yayi magana a cikin motar har muka isa makaranta, Abbu yana yin parking Firdausi ta bude motar ta fita bayan ta wa Abbu sai da safe shi kuma ya mata Allah huta gajiya. Tana fita kamar wanda yake jira ya kamo hannuna, bai damu da yadda nayi gaggawar kwace hannuna ba ya sake janyo hannun yayi kyawu sosai, idan ya goge ki sake yin wani kinji? Shima idan ya goge ki sake wani, I’d like to be seeing it kinji??” na gyada mishi kai a hankali, yayi murmushi “good girl, amma ni sai wani noke-noke kike yi da wani kauda fuska, kin daina min magana, laifin me na miki iye?” ban yi magana ba sai kaina dana girgiza yace “ikon Allah! Aikuwa ba zamu yi haka dake ba, za kina bude baki ne kina min magana idan ba haka ba kuma raina zai baci fa, and u wouldn’t like me idan hakan ya faru, ok?” na sake gyada kai, sai kuma nayi sauri nace “toh” yace “na fara nema mana visa fa, wani gari kike so kije for our honeymoon?” na dan zare ido, “honeymoon?” yace “ehh mana, da kin gama exams kin koma za a dawo min dake daga nan kuma zamu tafi honeymoon dinmu” nace “amma da aka ce sai session dinnan ya kare?” ya wani zaro ido kamar wadda ta fadi wani sabo, “ses… me? Ni dai nasan da bakina baki ji na fadi haka ba koh?” nace “ai nayi zaton haka ne” tun kafin in gama yake girgiza kai, “no! Ba haka bane. Gidan da zamu zauna is ready, komi ya riga ya kammala, kun gama jarabawar ku to me zan jira kuma? kin dai san ba zan barki kici gaba da zaman hostel ba kuma yanzun ma don we’ve already agreed on it ne shi yasa kika ga nayi shiru amma maganar gaskiya ban jin dadin zaman ki anan” na wani yi rau-rau da idanu, ya dage gira, “Allah baby kina jin dadin ki, kuka zaki yi kuma, me na miki?” ya kai hannunshi na dama ya tallabo kuncina dashi yana caressing din kuncina, hannunshi was very warm, na lumshe idanu na a hankali, na jiyo yatsar shi a saman idanu na yana shafawa, “zan ga yadda zamu kare da rigimar ki baby, dama ana haka ne? Daga magana sai ki kama kuka irin daddyn ki ya shagwaba ki koh?” na turo baki tare da janye fuskata daga hannunshi wadanda suka fara sanya min sayingsanyin jiki, murmushi kawai yayi. “Wadannan kyautukan da kika samu ban san ya zanyi dasu ba, do u have any idea ko wajen da zaki ajiye su?” nace “ka ajiye min su a wajenka” yace “to shikenan, zan kaisu gidanmu in ajiye, idan kin zo sai mu bude tare koh?” na rufe fuskata shi kuma yayi dariya, “nasan akwai kudi a ciki su kuma zan saka su cikin account ko ya kika ce?” nace hakan ma yayi, nan ma yace ok. Muka dan yi shiru na dan lokaci kafin ya duba hadaddiyar agogon fata dake daure a lallausan hannunshi, “to nine, yakamata kije ki kwanta yanzu koh?” nace “to, sai da safe” dama duk a wani takure nake ji na, na kama murfin motar zan fita ya sake janyo hannuna da bai jima da saki ba ya juyo dani, “not so soon baby, babu ko sallama?” na danyi frowning in confusion, wace sallama yake so muyi bayan wadda na mishi yanzu? Ban kai ga furta abinda nayi niyya ba naji ya hade goshina da nashi waje guda, irin sallamar jiya ya min sai dai ta yau tafi zurfi da demanding, ya sake ni a hankali idanunshi a lumshe, har lokacin goshin mu a hade yake, numfashi yake ajiyewa a hankali can kuma sai ya sake ni gabadaya, “Goodnight Amour” ya fada cikin whisper, cikin salubewar jiki na fita daga cikin motar. Ina shiga daki text dinshi ya shigo wayata, “make sure to eat something kafin ki kwanta, sweet dreams” na girgiza kai kawai na ajiye wayar akan gado na fara zare kayan jikina, ruwa na watsa na dawo nayi shirin kwanciya barci. Ba wata yunwa nake ji ba don haka na kwanta kawai, Abbu da Al’amuran shi masu ban mamaki suke min yawo a kwalwa, abubuwan da yake min were very new to my innocent life, ban san ya zan kamanta abinda nake ji a cikin raina ba amma ina jin kamar abin is wrong, anya ban yi kuskure ba kuwa?? Nayi juyi akan gado tare da tura kaina cikin pillow. 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *