AMININ MAHAIFINA
CHAPTER 15
Hasken rana daya haske min idanu ne ya katse min daddadan barci mai cike da natsuwa da nake yi. Na bude idanu na a hankali na sauke su akan agogo, karfe tara da kwata. Na maida dubana zuwa ga curtains din dakin wadanda aka daga sama, hakan ya ba haske da zafin rana damar lekowa ta cikin manyan windows din dakin. Abbu baya kan gadon kuma nasan da kyar idan yana toilet, ko ina ya shiga? Na tashi a hankali na nufi tagar da niyar rufewa, wani dan guntun murmushi ya subuce min lokacin dana yi tozali da terrace garden a bayan dakin, shuke-shuken roses da different flowers and plants ne wadanda suka kawata wajen matuka, ga wooden couch nan mai raga-raga kamar anyi saka a tsakiyar wajen inda zaka zauna ka huta, naja numfashi na shaki kamshin furannin har ina lumshe ido, sai dana gaji da tsayuwa sannan na saki curtains din, komawa nayi na yaye zanin gadon na je dakina na dauko wani na dawo na shimfida shi kuma dayan na jefa a cikin washing machine na shanya shi a nan cikin toilet din wajem da aka tanada musamman for laundry. Kayana na tarkata na wuce dakina, na jiyo motsi a kicin amma ban leka ba. Ruwa na tara mai dumi na shiga na kara gasa jikina don har lokacin ina jin zafin wajen, na daura babban towel a jikina na fito na zauna a gaban dressing mirror nayi goge-goge da shafe-shafe, kwalliyata nayi kamar yadda ya zame min Al’ada, na fesa turaruka masu kamshi mai kwantar da hankali, jiya naga Anty Shafa tana jera su a kan dresser din nasan ita ta sai min tunda Arabian perfumes ne ita kuwa yawanci irin turarukan da take amfani dasu kenan
Kofar dakin aka turo aka shigo, cikin sakan daya na juya na kalli wanda ya shigo na maida kaina kasa na dukunkune a tsakanin cinyoyi na. Ya tako a hankali har ya iso gare ni, kaina ya dago nufin shi in kalle shi amma na jimke idanuna, murmushi yayi mai sauti, “yau kuma a haka zamu gaisa Baby na?” nayi shiru ina kokarin janye fuskata amma yaki bani damar hakan sai ma mikar dani tsaye da yayi ya kalmashe ni a cikin jikinsa, ya dora habar shi a kan gashin kaina yace “babu gaisuwa ne yau?” kaina na kan kirjin shi na girgiza alamun a’ah, kaina ya sake dagowa nayi saurin kara rufe idanuna, peck naji ya bani a kunci da lebena kafin ya sake ni gaba daya, “it’s okay, na fahimta. Kunya ta ake ji ko? Yanzu zan fita a dakin, yi sauri ki shirya kizo mu yi break fast, yau da kaina na tattare hannun riga ta na hada miki break fast” idanuna suka yi walai cikin rashin sanin nayi hakan da tsananin mamaki, dariya yayi tare da dan jan hancina, “thank goodness I’ve got to see this beautiful eyes, yes ni na hada break fast now yi sauri kizo muci kafin ya huce, ko In zo in shirya ki da kaina?” wayyo nayi saurin girgiza kaina, yayi er dariya ya fita. Wardrobe na bude na ciro wani tausassan yadi ruwan madara riga ne da siket na saka, na lalubi silifas mai taushi na zura tare da yafa dankwalin a kaina da yake babba ne na fita.
Yana zaune akan kujera yana duba waya ina fitowa ya tashi tsaye tare da wucewa wajen dinning nima na bi bayan shi, kujera yaja min na zauna a darare shima yaja ta kusa dani ya zauna. Kwallin kula daya ce a wajen sai flask na ruwan zafi da cups da kayan shayi. Ya hada mana tea tare da daukar plate ya bude kular ya juye abundance ke ciki, nayi shagaraa da baki ina kokarin tantance abinda yake gabana. What did you expect? Konanniyar wainar kwai ce tayi bakikkirin da ita, yasa fork ya yanki kadan ya kai bakinshi kamar mai testing, yace “kar ki samu da bakin da tayi pa, bata yi komi ba” a sanyaye na dauki fork nima na kwaikwayi yadda yayi, abu na farko daya fara ratsa min harshe shine dan banzan gishiri sai kuma dacin konewar da tayi ya biyo baya, ganin yana kallona yasa na takura tun karfina na hadiye kwan, take zuciyata ta tashi, ya daga min gira, “ya??” na dage tun karfina na kakaro yaken tare da mishi 👌 alamun good, yayi murmushi. Wata na sake cirowa na kai baki, wannan karon na jima a bakina kafin na iya hadiyeta. Na ja kofin shayin na fara sipping, gani ba gwanar shan shayi da madara bace. Shi kanshi daya kai loma ta biyu gani nayi ya dakata yana kallona, “kamar gishiri yayi yawa koh?” nace umh. Ya kara kai ta uku bakinshi na bishi da kallo tsigar jikina har tashi tayi, ba shiri ya furzar da ita ya lalubi kofin tea ya kora dashi.
Kallona yayi yace “sorry baby, ko zaki zan sama mana wani mu ci? Da alamu na manta yadda ake girki ko don na jima ban yi ba?” kamar jira nake, na tashi na hade kan kayan na nufi kicin. Store dinmu shakare yake da kayan masarufi wanda nasan kila zai iya daukarmu shekara kafin mu ci rabin kayan, murmushi kawai nayi tare da girgiza kai, Daddy!.
Cikin mintuna talatin na gama soya chips da plaintain, nayi vegetables sauce na dauka na kai mana muka yi break. Na tashi na hade kayan waje guda Abbu ya biyo ni da wasu. Na ajiye kayan tare da juyawa, da sauri Abbu ya riko hannuna, ban kalleshi ba na sadda kaina kasa, yace “are you ok Nafeesah?” na gyada mishi kai a hankali, yace “please Ki daina jin kunya na haka Baby, kin riga da kin zama ni kamar yadda na zama ke. I need you to be free, frank and comfortable idan muna tare, bana jin dadin hakan da kike yi. I know it’ll be awkward, but still kiyi trying mana kinji?” na gyada mishi kai, yace “noo, amsa min da bakinki” na daga bakin da kyar nace “toh” ya kai bakinshi kan nawa ya dan tsotsi leben nawa kafin ya dago yana murmushi, “datz you baby…., zan fita yanzu me zan kawo miki?” nace “babu komi” yace “k, ki kunna kallo ko ki shiga dakina a study room akwai kayan exercise ko kuma just do anything so that you won’t be bored don zan dan jima, sai na dawo” nace “a dawo lafiya, Allah ya kiyaye hanya” yace “Ameen Nafeesah ta” ya juya ya fita bayan ya bani peck a goshi. Ni kuma na fara wanke kayan da muka karya dasu.
Yinin ranar a kiraye-kirayen waya da chatting nayi shi, babu wanda ya leko gidan kamar yadda ban ga kiran kowa a waya na ba sai na Abbu yana tambayana me nake yi? Lokacin ina study room dinshi bayan na gama gyaran dakinshi da nawa dama gidan gabadaya, sai kuwa Anty Shafa data kira bayan rana ta daga sosai tana sanar dani a ranar da dare zata bi jirgi ta koma gida, na mata godiya game da Alkhairanta a gare mu, muka yi sallama da ita tana jaddada min in fa dinga shiga ruwan zafi har naji kunya ta kama ni. Daga nan naci gaba da gudanar da harkoki na. Abbu bai shigo gidan ba sai bayan la’asar, sai lokacin nayi lunch ko ince muka yi. Ba laifi na dan sake dashi ranar, ba wani awkwardness da strange feelings irin na jiya sai er kunya wadda itama kafin dare yayi na neme ta na rasa, not that I care don ni fa duk abinda zai saka Abbu na cikin farin ciki shi nake aiming yayin da yace shi fa kunyar nan ta dame shi don haka na jefa ta cikin kwandon shara.
Ranar ma a dakin shi na tarda shi bisa umarnin shi bayan nayi wanka na wadata jikina da turare, ya mana light off tare da jana cikin jikinsa ya fara lalubata at first shiru yayi, but lokacin da naji hannunsa a kan kirjina and things started becoming steamy, sai nayi sauri na janye bakina daga cikin nashi, jikina yana er rawa saboda tunano wahalar daren jiya, a hankali nace “Abbu ban warke ba fa!” muryar shi was hoarse and low at the same time yace “I know… Babu abinda zan miki baby, just a good night kiss” sai daya gama samun natsuwar shi ta hanyar ‘good night kiss’ kamar yadda yace sannan yayi cuddling dina a cikin jikinshi kanshi a tsakiyar kirjina barci mai dadi ya dauke mu.
Ranar kam ya daga min kafa, wadda ta biyo bayanta kuwa yaki daga kafar despite magiyata da kukan shagwaba wadanda daga baya na fahimci cewar su suka kara karfafa mishi gwiwa ma, ranar data biyo baya ma haka and the day after that…. Soon, na zama gogayyiya kuma expert a cikin sabuwar rayuwar da Abbu ya bude min kofar ta. Mun kara karfafa Rayuwar aurenmu ta hanyar girmama Juna da shimfida kyakkyawa kuma tsaftacciyar rayuwar aure, kulawa da junanmu da tausayawa. A cikin en kwanakin kam duk duk wanda ya ganmu yaga wadanda suke kan ganiyar cin amarcinsu, na dan rame kadan amma still na kara yin fresh saboda kwanciyar hankalin dana samu. Abbuna kuwa ya kara kiba, jikinshi ya kara yin fresh ko ba komi nasan dadadan girke-girken da nake mishi kadai sun isa sa shi yayi kiba.
A kwana na biyar da tarewa ta, har ranar babu wanda ya leko gidanmu, Abbu ma bai cika fita sosai ba. Ina zaune da safiyar ranar a falo sanye da wasu Pakistan riga da wandon su, na gyara gashina ya kwanto har gadon bayana yana ta sheki da kamshi. Gate naji an bude, nayi murmushi nasan Abbu ne ya dawo daga fitar da yayi. Na kara gyara zamana ina fuskantar mota, yana shigowa na tare shi da murmushi. A bakin kofar ya tsaya shima yana murmushin, hannu ya mika min alamun inje, babu musu na tashi na fara tafiya cikin jan hankali ina jujjuya jikina kamar wadda take rawa, kasa daurewa yayi in karasa ya taka da sauri ya taro ni tare da rungume ni. Sai daya gama welcome kiss dinshi and stuffs sannan ya umarce ni da in dauko hijabi zai nuna min abu a waje, na shiga daki na saka na fita na same shi yana jirana, hannuna yaja muka fita compound din gidan, dalla-dallan motoci biyu Land Rover Discovery fara da Vibe silver-golden daga ganin su sabbi ne saboda yadda suke ta sheki a cikin soft hasken ranar ta alhamis.
Ya miko min keys guda biyu, cike da tsananin mamaki nake kallon su kafin na maida kallona ga motocin, da kyar na iya kakaro “wadannan keys din fa Abbu?” yayi murmushi much like a grinning, “for you baby!” na zaro idanu na cikin mamaki, “duka?” ya zagaya ta bayana tare da rungume ni, “wannan…” ya nuna min silver/golden vibe din, “is from me…. Wannan kuma…” ya nuna farar Discovery din, “is from your Daddy” nace “Dad kuma?” ya daga kafadar shi, “yanzu aka kawo ta daga can Kaduna, sai dana fada mishi cewa na sai miki amma yace shima tunda ya siya sai ki hada duka biyun kiyi amfani dasu” Daddy, my Dad! He’s really the best. Ban fada mishi ba amma already ya riga yasan da irin motar da nake muradi, nayi tsalle na juya tare da rataye hannayena a wuyan Abbu ina dariyar dake nuna tsananin murna da godiyar da nake mishi duk da bakina bai furta ba. Ya miko min kumatun shi ba bata lokaci na bashi peck a kunatun, peck din daya koma deep mouth to mouth French kiss in a wink, in another wink na tsinci kaina a tsakiyar gadon Abbu, kayan sawa suna yin koina a cikin dakin….
Later da yamma na kira Daddy na mishi godiyar Mota, “Haba Uwata bari mana kar ki bata min rai? Meye abin godiya dan uba yayi wa diyar sa abinda yake responsibility dinshi ne? Beside saboda wa nake neman kudin idan ba ke ba uwata? All I wish for you is to be happy kin gane? Sannan zan tura miki da kudin sadakin ki ta account gobe in shaa Allah” nayi saurin cewa “Daddy ka bar su a wajenka pls” yace “aah, ai hakkin ki ne Nafeesah kuma ma ni bana son kudin ki” nace “to a ba Mommy” yace “itama bata so” ba shiri na saki dariya, nan muka yi sallama dashi.
Washegari kuwa ya turo min da kudin, dubu dari biyu bayan dubu dari ne sadakin, na kira ina tambayar shi dalili sai cewa yayi ai sabida in dinga ba baki da kuma sauran kashe-kashe saboda baya son in cika tambayar mijina, sai kawai nayi murmushi tare da mishi godiya
Ina zaune Abbu ya fito daga dakinshi yana gyara karin hularshi cikin shirin tafiya masallacin juma’ah. Na tashi na taya shi kafa hular tare da raka shi har bakin kofa, yace “In kawo miki su Hafsy ne su miki yini?” da sauri kuma cike da doki nace “ehh, please Abbu” yayi dan murmushi tare da juyawa ya tafi ina mishi Allah ya kiyaye hanya. Yana tafiya na fada kicin na hau shirya musu cookies da kayan motsa baki ga kuma abinci, ina kicin din ma suka shigo gidan su da Abbu da ihun su suna kiran sunana, da sauri na fita waje nan suka kwashi ihu suka rugo suka rungume ni, nima na rungume su ina murnar ganinsu, sai da muka nutsa sannan na dago kai ina kallon Abdullahi dake gefen Abbu a tsaye, na mishi dan murmushi ba tare dana damu da yadda bai yi joining dinsu ba. Daga baya dai muka tashi muka koma cikin falo, na dauko musu duk abubuwan dana shirya musu nan fa hira ta barke, bayan mun ci abinci Abbu ya tafi daki ya dan kwanta kafin a kira la’asar ya barmu muna ta hirarrakin mu, har baya muka fita muka danyi wasanni kafin muka dawo falon. Yini guda suka mana sai bayan magriba Abbu ya maida su gida, don Hafsy ma da kafewa tayi anan zata kwana sai da kyar Abbu ya lallasota ta hakura suka tafi. Na hada su da tarkacen sweets, chocolates da tarkace dai iri-iri suka tafi.Ban sani ba shagala ce ko kuwa mantuwa? Zancen cewa angwaye kwanaki bakwai suke yi a dakin amaren su su koma na uwargida, kai in fact na manta cewa ma ina da abokiyar zama kwata-kwata a lokacin, na manta cewa bani kadai bace wadda take da Abbu, na manta cewa Abbu yana da wasu iyalan daya kamata ya kula dasu. Muna cikin cin abinci yake fada min cewa washegari idan zai je gidan Mubeenah zai dauko cousin dinsu Zaynab diyar wata kanwar mahaifiyar su zata dinga zuwa tana taya ni kwana. Na maida spoon cikin plate dina na ajiye ina kallonshi cikin alamun tambaya, and that was when it downed on me, ranar na cika sati daya cif da tarewa which means washegari zai fita daga dakina. Jikina yayi wani irin sanyi har yana hadawa da rawa na dai daure na cije na gyada mishi kai naci gaba da tura abincin da taste dinshi ya bace a bakina.
Duk yadda naso na daure in nuna mishi hakan bai dame ni ba kasawa nayi, sai daya fahimci sanyin da jikina yayi. Ya riko hannuna ya zaunar dani akan cinyar shi tare da dago fuskata, na daga idanuna da suka fara cika da ruwa na kalleshi, yace “come on mana baby kar ki bayar dani, meye kwanaki biyu kadai? Besides, zan dinga zuwa kullum ina ganinki kinji? Kuma zamu kasance a waya a koda yaushe don haka ki daina bata ranki, ni naki ne ok? Oya, give me that gorgeous smile of yours baby” na kuwa saki murmushin tare da dora kaina akan kirjin shi.
Washegari da safe ya tattara ya tafi bayan ya jira Zainab tazo, yarinyar tana da kirki ga fara’ah, na dan girme mata da shekaru tunda shekarunta ashirin. Na raka Abbu har bakin mota duk da sallamar da muka gama yi a daki, yaso ya kaini gado a lokacin nace a’ah, ba zan shiga hakkin abokiyar zamana ba don nima bana so a shiga nawa hakkin. Haka ya tafi ina daga mishi hannu har sai daya fita daga gidan maigadi ya maida gate ya rufe kafin na juya cikin gida cike da kewar Abbu, zama nayi muka dan yi hira da Zaynab kafin na shige dakina na kwanta don jiya Abbu bai barmu mun yi barcin kirki ba.
☆☆☆☆☆ 4
“Wannan yace a cikin abinci kamar miya ko fate zaki zuba mishi yaci, manta kowa kenan. Ina mai tabbatar miki da cewa idan har yaci wannan maganin to wallahi sai dai uwarshi ta sake haihuwar wani, kin dai ga yadda mijin Umaimah (er autar su) yake mata, uwar shi ma yanzu sai Umaimah taso yake ganinta balantana wata banzar bazara wai ita kishiya, kema to haka zaki mallakeshi…, wannan kuma….” Saddiqa ta fito da wani ruwa a cikin kwalba tana nunawa Mubeenah, “…a cikin ruwan wankan shi zaki zuba mishi, shi kuma zai sanya mishi matsanancin son ki ne, ya zama babu wata ‘ya mace a cikin idanuwan shi sai ke ina fada miki, boka Saddar ya bani tabbacin a ranar zai dankarawa ita waccar banzar kishiyar taki saki uku, shi da kara aure kuma sai a lahira. Don haka ki kula sosai, ki bi komi a hankali yadda ya dace don hakan mu ya cimma ruwa kin gane?” kamar wata kadangaruwa ta gyada kai, “yauwa, ina turaren dana kawo miki last week nace kiyi tsuguno dashi?” Mubeenah ta gyada kafada, “turare? Na ma manta inda na jefa shi” Saddiqa ta maka mata harara, “wai ke banzar wani gari ce? Duk inda yake ki lalubo shi kiyi tsuguno dashi yau ba gobe ba, yaushe girkin ki zai fita?” tace “gobe da safe” tace “bamu da lokacin batawa kenan, yau yakamata yaci maganin, yayi wanka kuma ya kusance ki kina jina? Abubuwan nan da muke yi is all for u Mubeenah, kin dai san kaf danginmu babu mai kishiya sai waccan banzar yarinyar (Shakira) don kishiyar Umaimah hoto ce, don haka kema ba zaki biyo sahu ba kin gane??” Mubeenah tace “ehh”
Tayi murmushi, “yauwa., kudin aiki dubu dari da hamsin tashi maza ki dauko min” Mubeenah ta zaro ido, “dari da hamsin?” ta harareta, “to meye dari da hamsin matukar an samu biyan bukata?” Mubeenah ta gyada kai, “hakane kam. Sai dae babu kudi a hannuna sai dai idan Ibrahim ya dawo sai in amsa a wajen shi” Saddiqa ta yago hakura, “to babu damuwa, amma to dari biyu zaki tura min tunda dai nasan kema in kika tashi ba a dari biyun zaki tsaya ba” suka kwashe da dariya.
Nan taci gaba da kitsawa Mubeenah abubuwa har yamma ta gabato sannan ta mata sallama ta tafi bayan ta kwashi manyan atamfofi biyu da lesuna cikin kayan da aka kaiwa Mubeenah na fadar kishiya bayan ta gama kwashe musu albarka, ji fa!. Mubeenah ta dawo daga rakiyar ta ta tsaya ta leka dakin Abbu, tun jiya daya dawo daga gidan Nafeesah ya leka ya gaya mata ya dawo tare da fada mata ya raba musu girki kwanaki bibbiyu bata sake ganin shi ba. Yanzu ma baya nan gashi akwai maganganu da take so suyi.
Dakinta ta koma, magungunan da Saddiqa ta kai mata suna zube akan gado, ta zauna a gefen gado tare da kura musu idanu kamar wadda take muhawara, ta saki ajiyar numfashi tare da tashi tsam ta dauki magungunan. Toilet ta shiga ta zazzage su a cikin masai tare da yin flushing, dama turaren data kai mata Harira ta ba ta jefa shi cikin kwatami. Daya daga cikin manyan abubuwa da Mubeenah bata so kuma bata ma yarda dasu ba shine bin malamai da bokaye, tana mamakin yadda mata suke yarda da karerayi da soki-burutsun bokaye da malamai, a ganinta in kura na maganin zawo to tayi wa kanta mana?? Shi yasa tasu ta matukar zuwa daya da Shakira kanwar su, sam bata cikin harkar bin malaman da sauran en uwansu suke yi, ta kan ce ita tafi ganewa tayi yaki akan abu ta yadda idan ta mallakeshi zata yi alfahari da cewa saida ta share zufa ta sha wahala kafin ta same shi ba wai a ruwan sanyi ta hanyar bokaye da yan tsibbu ba, kuma gaskiyarta.
Tunda gari ya waye take leke-leke da zarya daga falo zuwa dakinta. Ta kula kwata-kwata ya daina zama a cikin gidan, tana mamakin inda yake zuwa cikin kwanaki biyun daya mata. Tana nan zaune a daki taji tashin muryoyin su dasu Qaseem wadanda suke hutun makaranta ranar, Sai data ji shiru alamun ya shiga dakinshi sannan ta tashi tsam!.
“ok baby sai na iso, kar ki manta anjima da yamma dai zamu fita in fara koya miki tuki” na danyi tsalle daga zaune din da nake, “yeyh! Abbu na, sai kazo. Please ka taho da wuri fa!” yayi er dariya, “missing me that much??” dariya kawai nayi na kashe wayar. Shima dan murmushi yayi ya ajiye wayar yaci gaba da shirya takardu a cikin brief case din shi.
‘Baram!! Karan sautin turo kofar dakin nashi kenan kamar tashin duniya. Tun kafin ya juya yasan ko waye ya shigo, haka take shigowa dakin babu knocking balle sallama, kofar dakin ma haka take turo ta, duk ranar data shigo a hankali to ranar nema take a wajen shi.
Bata yi magana ba ta coge a bakin kofa, shi kuwa yaki daga kai ya kalleta yaci gaba da abinda yake yi har ya gama ya rufe brief case din. Wardrobe ya bude ya fara ciro kaya, ta kankance idanu cike da masifa ganin yadda yake abubuwan shi kamar bai san da Allah yayi ruwan tsirarta a cikin dakin ba.
“Ibrahim! Ina so muyi magana da kai!” ta fadi kanta tsaye cikin izza, ya juya a hankali tare da kallonta. Wani malulun bakin ciki da bacin rai suka kawo mishi wuya, wasu pyjamas ne a jikinta daga ganinsu sun dauki lokuta ba a wanke ba, ta kawo wata hular beanie ta maka a kanta fara ce amma tayi bakikkirin ta dafe alamun ta kwana biyu, gashin kanta da yayi cukus-cukus a cikin hular ya maida ta kamar irin sababbin kamun nan. Ya hade fuska sosai wadda tasa ta shiga hankalinta ba shiri amma hakan bai hanata yin dibar albarkar data kawo ta ba. “Ibrahim mai kake nufi da nine, an kawo amarya ban ga kalarta ba, ka kama ka killace ta a waje guda saboda ita er goal ce, er nasiha ta hadin kai da naji mazaje na hada matansu waje guda su musu kai baka yi hakan ba, ka dawo daga gidanta kaxo nawa amma har ka gama kwanakin ka amma sau daya na saka ka a cikin idanuna, anya Ibrahim baka dauko hanyar da amaryar ka zata raina ni ba kuwa??” ya jingina da jikin wardrobe din yana watsa mata kallon uku-taro, sai data dire aya sannan ya ajiye numfashi, “killace amarya kamar yadda kika ce nayi sabida ta kai matsayin a killace ta dinne, Nafeesah ba er gwal bace er diamond ce Mubeenah. Kawo amarya gidanki damka amana ni ni na hana saboda ban ga dalili ba, ke kanki ya kike kula da taki rayuwar balle har ki kula da rayuwar er wasu? Maganar rashin gani na da baki yi ina ji kin manta ne, dama can muna daukar satika ma bamu ga juna ba alhalin muna gida daya yanzun ma ina ga ai bata canza zane ba koh?” tayi tsuru tana zare idanu, maganar daya fada haka take, ita kanta bata san dalilin sako maganar ba, kawai maganar has been eating her brain ne dole ta fade ta ko ta samu sawaba.
Tayi gyaran murya tare da cewa “whatever! Amma kasan dai saboda Allah baka kyauta ba, kuma naji ance ka sai mata manyan motoci har guda biyu bayan ni ka bar ni da tsohuwa ina fama, tun kafin tafiya tayi nisa zaka fara shimfida rashin adalcin da ake cewa dama a jinin ku maza yake?” yayi murmushi cike da takaici, dama yasan duk inda zata je ta dawo dai maganar kenan. Ya daga kafada, “mota yeah, ni na sai mata daya Daddyn ta ya sai mata daya, ina ce kema lokacin da aka kawo ki an sai miki mota?” “karya ne!” ta fadi cikin hargowa, “karya kake yi kai ka sai mata, motar da kake fada ai Mahaifinka ne ya sai min da kudinshi ba naka ba mai ya hana kai ka saya min da kudin ka ko kuma yanzu daka sai mata nima ka sai min idan ba rashin adalci ba??”
Ranshi ya baci sosai, ya sha daukar fiye da haka daga wajen Mubeenah, ya sha jin munanan kalmomi daga gareta duk yana shanyewa amma yau baya jin zai iya shanyewa. Yana da hakuri sosai, sai dai duk ranar da aka kai shi bango akwai matsala. Tun daga tsawar daya daka mata Mubeenah tasan cewa ranar ta tsallake layin hakurin Abbu. Idanunshi sun juye saboda bacin rai, “enough Mubeenah! Ya ishe ki, ya ishe ni haka nan. Mota bani na sai mata duka biyu ba amma da ace idan nayi hakan Nafeesah zata karba happily da wallahi sai na sai mata fiye da mota biyu. Kin san saboda me? Saboda Ina Son Ta!! Saboda tana kula da farin cikina, saboda ita kadai nake kallo in san cewa yes! Ina da mata, in san cewa akwai wani da zan ba umarni kai tsaye yayi, akwai wadda bata zartar da komi sai da yawuna, akwai wadda zan bugi kirji ince Matata ce in kuma nuna ta a koina cikin duniyar nan ba tare da fargabar zata muzanta ni ba. Saboda ita kadai ce take bani hakkina ba tare da na biya ta ko sisi ba, saboda itace matar da nake sa ran zata haifa min yara ta kuma shayar dasu ba tare dana biya ta kudin shayarwa ba!! Saboda… Nafeesah itace komi nawa!! Zaki ga laifina idan na sayi jirgin sama na damkawa wannan matar kuwa?”.
Mubeenah tayi shiru kanta a kasa, tunda take dashi bai taba mata ihu irin na ranar ba, bai taba daga murya kamar haka ba, duk abubuwan daya fada ta aikata har da ma wadanda bai fada ba duk tayi kuma sun faru, kalma daya data doke ta… “Kana Son ta?? Ni fa?! That means baka so na kenan?” without second thought ya gyada mata kai, “kwarai Mubeenah! Ni dake duk mun san cewa zaman hakuri da zaman ‘ya‘yanmu muke yi, amma zancen ‘so’ kin san cewa babu shi a tsakaninmu” ta fara girgiza kai, bai jira mai zata sake ce mishi ba ya warci brief case dinshi a fusace ya ratsa ta gefenta zai fita, kofar dakin ma ko albarkacin ta rufe ta bata samu ba, tsoron shi daya Allah yasa cikin yaran babu wanda yayi over hearing din conversation dinsu yasan may be ya saka confusion a cikin kansu. Ranshi ya kara baci da wannan tunanin, daga bayan shi ya juyo muryarta a kausashe “Nafeesah!….” tun ma kafin ta gama fadin abinda tayi niyya ya juyo a fusace, “don’t you ever dare drag her into this, ba irinki bace ita saboda haka ke kici gaba da laluben duniya ki barta taci gaba da laluben lahirar ta!” ya juya a fusace ya bar gidan zuciyar shi na azalzalarshi cike da bacin rai ko sallama bai wa yaran nashi ba da suke dakinsu suna kallo.
Mubeenah ta bishi da kallo cikin bacin rai na maganganun daya yaba mata yanxu, fargaba da tsoron anya bata bari kwabarta tayi ruwa ba kuwa? Dana sanin ina ma tayi amfani da magungunan da Saddiqa ta kawo mata???
******
Muna gama waya dashi falo na koma ina jiran karasowar shi. Ina cikin zaman jiran ne Zaynab ta fito daga dakin dana ware mata a sukwane tana ihu, “Anti Nafeesah…. Anty Sadiya ta haihu yanzu!!” nayi ihun nima tare da direwa cikin murna, sai da muka gama iface-ifacen na tambayeta abinda ta haifa tace Mace. Ba bata lokaci ta shirya ta tafi ganin baby. Na zauna ina jiran dawowar Abbu impatiently ina jin kamar inyi fuffuke inje inda suke. Ina dakina ina canza kaya daga shigar da nayi ta wani mini daya tsaya min a gwiwa da half vest mai hannu daya ta taryar Abbu zuwa riga da zani na atamfa, ban san ya dawo gidan ba sai dana leka waje naga motar shi a fake sannan. Abin ya bani mamaki, nayi tunanin zai shigo dakina direct idan bana falon kamar yadda yake yi, ban kawo komi a raina ba na nufin dakin da saurina cike da doki. Na tura kofar ko sallama doki bai bani damar yi ba na fara zuba mishi bayanai, “Abbu yanxu Sadiya ta haihu, kazo ka kaini in ga baby ka ji??” kwance yake yayi rub da ciki ya tura kan shi cikin filo, na zauna a gefen gadon ina dan jijjiga shi alamun ya tashi, “Abbu…. Abbu kaji?” nan ma shiru babu magana, ban sani ba common sense ne ya dauke min ko kuwa? Ban yi tunanin ina takura mishi ba ko barci yake yi naci gaba da jijjiga shi, “Abbu kazo ka kaini in ga baby kaji? Abbu??”
Juyowa yayi a fusace, cikin muryar dake hauhawa da bacin rai yace “Oh God Nafeesah!! Will you please just shut up and leave me alone??” jikina yayi sanyi ganin yadda fuskar shi take cike da bacin rai, “amma Abbu..” na fara magana in protest, “leave me alone!!” ya fada cikin karaji, sai kuma naga ya dafe kanshi da sauri, ya lumshe idanunshi na en sakanni kafin ya bude su, “please!!” ya fadi cikin sanyin murya wannan karon. Jiki na rawa na tashi na fita daga dakin ina tambayar kaina me ya hau kan shi??
Kujera na laluba na zauna cikin tsananin sanyin jiki, ban iya daurewa kwallar data taran min ba sai data gangaro kan kumatuna, gabadaya sai na dora laifin fushin Abbu a kaina. Watakila ni na dame shi da hayaniya har ranshi ya baci, kila barci yake yi na tashe shi da hayaniya kun san yadda mutane kan zama moody idan sun tashi daga barci balle shi da naje ina jijjigawa abinda Anty Shafa tace mata basa tashin mazajen su daga barci ta wannan hanyar. Ko kuma yana bukatar kadaici ne ni kuma ban kula da hakan ba? Idan haka ne kuwa ai laifi na ne. Tashi na sake yi na koma dakin, lekawa nayi kamar munafuka wannan karon yayi rigingine, na shiga dakin a hankali tare da maida kofar na rufe, barci yake yi. A hankali na dauki bargo na rufa mishi, na juya kenan naji an riko hannuna na juya da sauri. Ya bude idanunshi da suka shige ciki har sun canza kala ya kalleni dasu, take naji wani irin bacin rai na shige ni. Na samu kaina da tuhumar kaina da responsibility na bacin rai da yake ciki, a hankali nace mishi “kayi hakuri Abbu!” janyo ni yayi na fada kan gadon tare da jana jikinshi ya rungume ni, ina jin yadda zuciyar shi take bugawa da sauri, yace “noo, am sorry! I shouted at you bayan baki yi mun laifin komi ba” na kwantar da kaina akan kirjinshi ina shafa saitin zuciyar shi da hannuna, “Allah ya huci zuciyar ka Abbu na. Wanda ya bata maka rai bai kyauta min ba ni kam tunda nima yasa nawa ran ya baci” kuma gaskiya na fada, raina ya baci kwarai daga ganin bacin ran dake dankare akan fuskar shi. Yayi dan murmushi tare da jan bargo ya rufe mu dashi muka shiga barci.Koda muka tashi ran shi wasai babu bacin rai a tattare dashi. Da yamma na lallaso shi da kyar muka je gidan Sadiya muka ga baby don da cewa Yayi wai ya za ayi in fara fita ina amaryar sati daya? Da kyar da jibin goshi ya bar ni bayan na dauki alkawarurruka da dama wadanda sirrin mu ne, daga can muka wuce ya fara koya min mota sai gab da magrib muka koma gida. Kwana biyu da yin haka visar mu ta fita kasashen ketare yawon bude ido (honey moon) ta fita. Da kaina na zauna na fitar da kasashe biyar wadanda nake matukar so da burin ziyarta a rayuwata. Muka fara shirye-shiryen tafiya amma fa bayan anyi sunan Sadiya.A rana ta uku da haihuwar na kara komawa gidan Sadiya daga can bayan Abbu yaje ya dauke ni da dare muka biya ta can babban gida gidan su Abbun muka gaida iyayen shi, Hajiya Siyama mutuniyar kirki ta amshe mu da hannu bibbiyu har da dan guntun fadanta wai me yasa ya barni na fara fita yanzu? Har tana karawa da cewa wai ai su a zamanin su amarya sai tayi rabin shekara kafarta bata taka kofar gidanta ba., na kama baki a raina na kara da lallai kuwa! Bayan mun gaisa ta saka mana albarka muka wuce sashen Hajja Fati itama muka gaida ta. Nan ta hada ni dasu tarkacen daddawa da sauran su. Mahaifinsu kuwa kwaryar zuma farar saka mai kyau ya bani, daga nan muka juya gida hannu riki-riki da tsaraba.
Ranar sunan kuwa da safe na tafi. Muna ta ayyuka da tsare-tsaren wajen da baki zasu zauna bayan falo. Sai bayan la’asar su Anty Mubeenah suka iso gidan ita da yaranta lokacin muna can bayan gidan muna suyar samosa wadda ake ba baki.
Ni’imah data kai wa su Anty Ameenah wadda muka soya ta dawo, ta daddabo ni tare da rada min “ga fa uwargidan ki can tazo!” naji kamar zuciyata zata faso kirjina saboda bugawar da tayi, ganin yadda nayi kuru-kuru da ido yasa tayi dariya, “haba babe cool mana, sai kace wadda zata cinye naman jikin ki?” nayi murmushin yake kawai
Ni’imah ba zata gane halin da nake ciki ba, ba wai tsoron Anty Mubeenah nake ji ba, kawai ina fargabar yadda karon mu da ita zai kasance a matsayina na matar Abbu-Mijinta a halin yanzu, nasan ko kallon banza ba zan samu ba wannan karon, fatana daya mu rabu da ita lafiya ba tare da rayuka sun baci ba. Don haka nayi gefe daya da tunanin naci gaba da rolling din da nake yi.
Har inda muke Hafsy ta lalubo ni, nan ta zauna tana ta zuba min labarai har muka gama, aka shiga da wadanda muka yi ciki mu kuma muka shiga BQ muka yi wanka muka gyara jikinmu.
Wata uwar sun shadda muka saka a matsayin ankon suna, dark purple ta sha aikin pink din zare, Ya Allah! Zo kuga yadda na fita a cikin kayan nan. Kyawuna ya fita sosai kamar ka sace ni ka gudu, muka tsaya muka dan karkashe flashes kafin muka koma cikin gida. Bayan dogon hesitating da tunanin zanyi ko ba zan yi ba, daga karshe dai nayi sallama dakin maijego na shiga cikin dakiya duk da cewa zuciya na wani mayen tsere take yi a cikin kirjina
+
+
Ina shiga muka hada idanu da ita kamar wadda take jiran isowa ta, ni da ita muka yi stilling a waje guda, ni na fargabar abinda zai je yazo ni yayin da a nata 6angaren ban san dalili ba.
Ta janye idanunta a kaina, yayin dana daga kafa da kyar na karasa shiga cikin dakin. Gefen gado kusa da maijego na zauna nesa da inda Anty Mubeenar ta zauna ita da kanwar ta Shakirah wadda sai dana zauna na kula da ita a wajen hakan ya kara min fargabata, a tunani na ko taron dangin cin kaniyata suka yi.
Da dan murmushina cike da yake na dubi inda take zaune nace “Anty Mubeenah ina yinin ku?” ta dage kai sama yadda kasan ba da ita nake ba, sai Shakirah ce ta amsa da er fara’arta har da cewa “su amare ne?, Ai naso lekawa har gidan naki mu gaisa Allah bai nufa ba tunda bamu samu zuwa biki ba, Allah ya sanya alkhairi!” na amsa da “Ameen” a hankali kuma a dan kunyace ina satar kallon inda Anty Mubeenah take a zaune koma ince a hakimce, to ta dare kan gado tare wani baje-baje yadda kuka san kan gadonta tana kallon kowa daya bayan daya kamar wasu bayinta ko irin en duniya dinnan da daurin kallabinta ture-ni-kaga-tsiya dinnan wanda ya fito da daddagaggiyar keyar ta gashi duk a cunkushe, sosai matar take bani mamaki. Kamar ta ace tana da saloon guda amma gashinta bashi da maraba da wata Inna ko Goggo a kauye wadda bata san menene ma’anar Relaxer, Shampoo ko Stretcher da stuffs dinnan ba
Tashi tsaye tayi tana jan hannun Shakira tana magana kamar mai gunaguni, “Malama tashi mu tafi koh?” Shakirar ta maida ta ta zaunar tace “haba ke kuwa, ba mu jima da zuwa ba fa! Bari mu dan jima mana” ta koma ta zauna tana wasu guna-guni, fuskar nan tayi wani sha6ar babu kyawun gani, na kauda kallona daga gun su kafin cibi ya zama kari kuma.
Anty Ameenah ta shigo dakin, “Nafeesah kin ci abinci kuwa?” na dan girgiza mata kai, “A’ah Anty, bana jin yunwa ne” ta dan hade fuska, “a‘ah ban yarda ba, maza-maza tashi ki nemo abinci…. Ko don ma ina zuwa” ta juya ta fita daga dakin.
Tana fita su Hafsy su duka ukun suma suka shigo, dama kai tsaye Hafsy wajena ta taho, su kuma biyun sai da suka matso kusa sannan suka lura dani. Qaseem ne yayi tsallen murna ya karaso wajena shima yayin da Abdullahi yayi gefen mahaifiyar shi. Yaran suka zauna a gefena muka gaisa da Qaseem, na kalli inda Abdullahi yake zaune cikin er tsokana nace “su Abdullahi babu magana ne??” ya kalleni sosai kafin ya dauke fuskar shi ba tare da yayi magana ba. A take na sha jinin jikina, tun ranar da suka je gidana na kula da wasu canje-canje a tare dashi dama kawai ban yi tunanin wani abu bane mai girma amma yanzu kam, na hangi babban lamari a tare da yaron. 5
Muna nan Anty Ameenah ta dawo dakin hannunta dauke da plate shake da fried rice, coleslaw, da naman kaza a sama ta miko min plate din, na zare ido cike da mamaki na kalleta nace “Anty ina zan kai wannan abincin?” tace “cikin ki mana! Ni anya ma kuwa kina cin abinci yadda yakamata Nafeesah?” na sadda kaina kasa ina dan murmushi kawai. Ta zauna a gefen gado sai a lokacin ta kula dasu Mubeenah a zaune, Shakirah ce ta fara gaida ta, tayi dan murmushi ta amsa ta dauke kanta ga mayar da bakin da suke cikin dakin. Na jijjiga kai a hankali ina kara jinjina halin Mubeenah a cikin raina.
Ni dasu Hafsy muka fara cin abincin, har ga Allah turawa kawai nake yi. Ga rashin jin yunwa, ga tunanin sauyawar dabi’un Abdullahi a gare ni, abin ya daure min kai sosai. Muna cikin cin abincin naga ya tashi ya fita daga cikin dakin, da sauri na tashi na bi bayan shi.
A can bayan gidan wajen wasu shuke-shuke na same shi a zaune, ya kurawa shukokin idanuwa very lost in his thought, sai dana zauna a gefen shi sannan ya kula dani. Yayi saurin dauke kanshi ya sadda shi kasa. Dan murmushi nayi tare da gyara zama na sosai. Muka yi shiru muna kallon shukokin, can nace mishi.,
“Ka tsane ni koh Abdullahi?” da alamun tambayar tawa ta bashi mamaki sosai, da sauri ya dago ya kalleni yana girgiza kai alamun a’ah, sai dana sake ajiyar zuciyar relief a hankali kafin nace “kar ka boye min komi Abdullahi. Nasan cewa dama dole zaku tsane ni, nazo na aure muku mahaifi na zama kishiyar mahaifiyar ku, ko ba haka ba?” nan ma ya girgiza kai da sauri.
Nayi shiru tare da kura mishi idanu, idan ba haka bane ba to menene? Na juya na fuskance shi sosai tare da riko hannayen shi nace “to idan ba haka bane ba Abdullahi menene? Me yasa kake avoiding dina? Last time da kuka zo gidana dama haka kake sakewa kamar ni bakuwar ka ce wadda baka taba gani ba, you hurt my feelings you know… Now, gaya min, ni ce koh?” ya sake girgiza kai, a hankali kamar mai tsoron yin maganar yace “Abbu ne!!”.
Na zaro ido cike da mamaki ina kallon shi, “Abbu da kan shi? Me ya maka? Fada min zan mishi magana kaji??” ya kura min idanu kamar ba zai yi magana ba, can kuma yayi maganar da tasa na kusa sakin fitsari a wando saboda tsananin mamaki. “cewa yayi baya son Mommyn mu!!” ya fada muryar shi na dan rawa yayin da idanun shi suka cika da hawaye.
Da gaske gabana ya fadi, duk wata kalma ta bace daga cikin kaina. Cikin sanyin jiki na kura mishi idanu nace “shi Abbu din ne ya fada maka haka da bakinsa?” yayi saurin girgiza kai, “a’ah, Mommy ya fadawa. Ni kuma lokacin naje dakin shi ince ya kai mu gidanki mu yini, shine naji yana gaya mata cewa baya son ta ke yake so!” na dafe saitin zuciyata dake bugawa, ba wai na jin dadin maganar ko fluttering ba, na takaici da wani dan tsillin jin haushin abinda Abbu yayi. A tunani na sai mazajen da basu san inda yake musu ciwo bane suke irin wadannan halaye, ashe ba haka bane. +
A lokacin na fahimci cewa wasu iyayen su suke sa ‘ya‘yan su su tsani kishiyoyin iyayen su. Babu yadda za ayi ace a yabi wata ba uwar yaro ba, ko a fifita wata akan uwar yaro bai ji haushin abin ba koda uwar tashi bata da kyawun hali kuwa. Kamar dai abinda yake faruwa yanzu, wanda ba zan taba bari hakan ya faru ba. Mun gina amintacciyar rayuwa ni da yaran, they trust me, suna so na, suna girmama ni, ba zan taba bari hakan ya taba amintar mu ba.
Nace “shi yasa ka tsane ni kenan?” yayi shiru kan shi a kasa, “lokacin da naji labarin zaki auri Dad dinmu, frankly naji haushi. Me yasa muna kallon ki a matsayin yaya a gare mu zaki buge da auren Abbu? Daga baya kuma sai na fara tunanin hakan ai ba laifi bane ba, kuma zamu zama muna tare dake a koda yaushe saboda believe me muna son ki wallahi. Har lokacin da muka zo gidanki ina cikin confusion, daga karshe dai nazo nayi concluding cewa Kaddarar ki ce hakan don haka na kauda tunanin komi a cikin raina nayi niyar rungumar ki da zuciya daya. Saboda haka ne ma nayi niyar sa Abbu ya kaimu gidan ki mu yini in kuma baki hakurin abinda ya faru ranar farko da muka je gidan ki. Sai kuma na kare da jin maganganun dasu Abbun suke yi…, I was afraid! Naji tsoron cewa zaki iya sa wa Abbu ya tsani Mommy ya daina kula ta, muma yazo ya tsane mu ya daina son mu sai ke da baby idan kin haihu…, irin yadda Daddyn su abokina Ameer ya musu lokacin daya kara aure!”.Na fahimci irin tsoro da fargabar da yake ciki, na matsa tare da kamo hannun shi sosai. Nace “look Abdul, ni ba irin matar Baban su Ameer abokin ka bace kaji? Ba zan taba bari wani abun cutarwa yazo kusa da ku ba balle in cuce ku da kaina. Sannan Abbun ku yana son Mommyn ka kaji?” yaron ya kalleni sosai with so much hope in his eyes sai da naji kamar zan yi kuka. Fuskar shi ta washe da murmushi, “da gaske Anty Nafeesah?” na daga mishi kai da sauri, “sosai ma. Yafi son ta akai na ma. Kawai ranar ai ya fada min, yana so ne yaga abinda zata yi ne shi yasa yace haka. Wasa yake mata!!” na karasa maganar cikin cije baki.
Yayi ajiyar zuciya, “har naji dadi wallahi, da har na fara ji Abbu ya fara bani haushi!” da sauri nace mishi “kul! Kar ka sake maimaita irin haka kaji Abdul? Ko me iyayen mu suka mana bamu da damar jin haushin su a cikin ranmu kana jin mu? Duk abinda zasu yi suna da dalili don haka mu dinga musu uziri ka gane?” ya gyada kai cikin fahimta, “na gane. Nagode sosai Anty Nafeesah! Kiyi hakuri kuma” na shafa tattausar tattaurar sumar kanshi ina murmushi, “are we good now?” shima ya gyada kai yana murumushi. Nace “zo mu koma cikin gida kaga yamma tayi kila su Mommyn ka suna neman ka. Kada fa ka sanya damuwar komi a cikin ranka kaji?” ya gyada kai. Naja hannun shi muka tafi.
Aikuwa su Anty Mubeenah na waje suna neman shi, ganin mu tare fuskar ta ta danyi frowning da ban san ko na menene ba. Na daure duk da sanyin da gwiwa ta tayi muka karasa har gaban motar su, wanda kafin muje sun shige ciki, Abdullahi ya bude baya ya shiga na leka ta jikin taga ina musu Allah ya kiyaye hanya, Anty Shakira da yaran suka amsa cikin fara’ah yayin da mai gayya Mubeenah ta dauke kai gefe, ni dama nasan za a rina. Suka ja motar suka tafi, na sauke ajiyar zuciya a hankali na juya zuwa cikin gidan, lokacin an fara kiran Sallar Magriba. +
Bayan Isha’i Abbu yazo ya dauke ni, na wa su Anty Ameenah sallama na tafi suna ta min godiyar hidimata a gare su, daga ta gangar jikina har ta jakata. Na bude murfin motar gefen mai zaman banza na zauna, Abbu ya kalleni da murmushi a fuskar shi. “ya ne baby?” na kakaro murmushin yake kawai, yayi zaton gajiya ce don haka ya tashi motar muka tafi.
Muna zuwa gidan na dafa mishi jollop din Spaghetti, ban zauna ci ba don cikina a cike yake already. Daki na shiga na watsa ruwa, na dauro alwala na yi sallar Isha’i tare da yin Shafa’i da Wutiri. Yan shafe-shafe nayi tare da zura kayan barci. Wando iya gwiwa da riga mai budadden wuya, har yau ban warke daga cuta ta ta jin suffocation idan na kwanta da riga ba, saukin dana samu shine Abbu baya ma bari na na kwana da riga, idan ya tafi gidan Anty Mubeenah ne nake amfani da riguna irin wadannan saboda ina sakewa a cikin su.Nayi sallama a nutse na tura kofar dakin, yana kan sallaya yana Nafilfilin shi na duk dare daya saba yi. Na wuce kan gado tare da kwanciya na juya baya daga inda yake sallar na kalli bango zuciyana cike da sake-sake, ina so inyi mishi maganar ina kuma tsoron abinda zai auku ko yaje ya dawo, amma a ganina yin maganar kamar ya zama dole ne.
Ina jin lokacin daya gama sallar ya wuce gaban dresser yayi shafe-shafe da feshe-feshen turaruka kafin ya kashe wutar dakin. Ya hawo kan gadon ya kwanta a bayana tare da janyo ni jikinsa, hannunsa ya fara laluba na yayin daya kai bakinsa gadon bayana yana manna short short kisses zuwa bayan wuyana, kafin in lalubo hanyar yin protesting ya san yadda yayi ya batar min da hankali, da sauri na juya na sarkafe hannuwana a wuyan shi tare da sakar mishi jikina gabadaya, ina nufin mallaka mishi….
Yayi rigingine akan gado yana ajiyar numfashi, kaina yana kan kirjinshi yana shafa gashin kaina a hankali. “as usual, that was amazing baby, I love You!” ya fada tare da kissing din kaina. Ire-iren kalaman shi kenan a yawancin dararen ko ince lokutan da duk muka kasance tare dashi. Duk yadda naso kar inji dadin kalmar hakan bai yiwu ba, naji zakin ta tamkar zuma. Na kara shigewa cikin jikinshi tare da dora lebbana a tsakiyar kirjinshi na sakanni da basu fi biyar ba na kara maida kaina na kwantar a kirjin shi.
Wucewar mintuna masu dama, mun yi shiru ne kawai babu wanda yayi magana. Wata masaniya ta taba bani shawarar cewa lokuta irin wadannan wato lokutan bayan gama Auratayya, lokuta ne da suke kawo fahimtar juna da kara sa shakuwa a tsakanin ma’aurata, I tried, n it really works. Wani lokaci mu kan tattauna game da feature dinmu, rayuwar mu, idan ma da matsala sai mu tattauna akan ta mu warware ta. Na jefa mishi tambayar “me yasa kake so na Abbu?” maganar taje mishi a bazata saboda shirun da yayi na dan lokaci kafin yace “I don’t really know, amma kyawawan halayen ki, kulawar ki a gare ni da tausasawar ki ina ji sune jigon abubuwan da suka ja ra ayina game da ke” nayi dan murmushi kawai, “I am sorry to say, but idan zaka rike son da kake min a cikin zuciyar ka zan fi son hakan” yayi shiru na dan lokaci kafin yace “saboda me?” nayi shrugging, “ina so in samu farin ciki mai dorewa da kai Abbu, ina so in rayu da iyalan ka cikin aminci da lumana da yarda da juna, idan kana fadawa kishiyata kana so na a gabanta me kake tunani hakan zai jawo min??” tashi zaune yayi sosai, nima na zauna tare da jan bargo na rufe jikina.
“me kike nufi? Kun hadu da Mubeenah a wajen suna ko? Me ta fada miki? Tana kokarin ta raba ni da wadda take so na ko? That…” nayi saurin katse shi, “ba ita bace, yes mun hadu da ita amma ko kalma daya bata hada mu da ita ba” ya kalleni sosai, “idan ba Mubeenah ba a wajen wa kika ji maganar?” nace “kayi hakuri, amma ba zan iya fada maka ba” ya kalleni, “daya daga cikin yaran ne koh?” shirun da nayi ne yasa ya gaskata zarginshi, hannu ya kai yana yamutsa sumar kan shi, “God!! Abinda nake jin tsoro kenan”.
Na kara matsawa kusa dashi, “saboda haka ne nake so plssss ka daure, kada kayi sanadin da zai sa yaran su tsane mu daga ni har kai. Kaga hakan ba zai mana dadi ba” muryar shi cike da bacin rai “no way! Ita bata so na sai kuma ta hana ni son wanda yake so na??” nace “babu wanda ya hana ka son abinda ke son ka Abbu, amma kaje kana ihun kana son kishiyarta a gabanta da yayanta, hakan babu kyau. Zai jawo consequences masu dama wanda hakan ba zai mana dadi ba” ya dan girgiza kai, “I was angry!” nace “shi yasa Annabin mu SAW ya umarce mu da yin shiru idan muna cikin fushi, you should’ve just keep quite ko ka bar inda take lokacin da ranka ya fara baci. Ni dai don Allah kada ka sake yin hakan kaji Abbuna??!” na fada cikin sanyin murya mai dauke da roko, ya kura min idanu cikin duhun dakin kafin ya sake ajiyar zuciya., “naji! Na fahimta, hakan ba zai sake faruwa ba. Na gode, Allah ya miki albarka!” matsawa kusa dashi nayi na dare kan cinyar shi na kamo fuskar shi na rike cikin hannuna, “har kullum fahimtar ka a gare ni da saukin kan ka su suke kara saka min natsuwa da jin dadi Abbu na, Allah ya barmu tare ya kara mana son juna” yayi murmushi, “if you are that happy then show me!” ba bata lokaci na hade bakina da nashi. Kafin wani lokaci na tsinci kaina a karkashin shi, “you up to another round??!” ya fada hoarsely idanunshi na sheki da farin ciki da sha’awa, na daga baki zan bashi amsa but instead na buge da furta “Abbu….!!”. 12
Washegari ya koma gidan Anty Mubeenah, Zaynab ta dawo da yake idan ya tafi can ne take zuwa, ranar da zai dawo kuma sai ta koma gida. Naje gidan su Anty Ameenah na musu sallama har can babban gida sai da naje, ranar daya dawo gidana da dare jirginmu ya daga zuwa Las Vegas, daga can ne zamu wuce Paris cikin yardar Allah.