- AMININ MAHAIFINA
- CHAPTER 16
- Cikin tsakiyar dare muka isa birnin Las Vegas, already mota daga hotel din da Abbu ya kama mana tana jiran mu a airport din, muka zuba abubuwan da muka taho dasu a bayan motar muka shiga direban yaja muka tafi sai Bellagio Hotel, babban hotel ne dake tashe a cikin birnin LV musamman kasancewar shi a cikin tsakiyar manyan waje na shakatawa da wasanni. 3
- Garin ko ina haske tal kai kace ranar Allah Ta’ala ce, mutane suna ta shige da ficin su suna gudanar da al’amuran rayuwar su kamar ba tsakiyar dare bane. 
- Muna zuwa babu bata lokaci receptionist din wajen wata farar yamutsattsiyar baturiya mai fara’ah ta bamu keys da number din dakinmu dake can sama, kayanmu tuni suka riga mu isa don haka muma muka shiga elevator muka tafi har hawa na goma na biyu, dakin babba ne living room da bedroom duk a hade suke waje guda sai babban toilet dake hade da dakin, komi na ciki guda biyu ne alamun it was meant for couples.
- Muka rage kayan jikinmu muka fada bandakin muka yi wanka da ruwa mai dumi don warware gajiya, muka yi alwala muka fito Abbu yaja mu muka yi Shafa’i da wutiri daga nan muka haye kan babban gadon dakin ko abinci bamu nema ba don ma wai mun ci abinci a cikin jirgi, ba bata lokaci kuwa barci ya dauke mu.
- Washegari misalin karfe goma na safiyar ranar acan, mun tashi mun yi wanka mun shirya, muna zaune akan daya daga cikin sofa din dakin daya daga cikin ma’aikatan wajen ya kawo mana abincin da muka yi oda, nan muka zauna muka karya. Muna gama karyawa Abbu ya sauka kasa yace zai je ya dawo.
- Na leka ta babbar tagar dakin ta gilashi wadda ta kusa cinye rabin bangon dakin, curtains din kuma anyi gefe dasu hakan ya bani damar hango titin kasar a cikin safiyar ranar, mutane da suka koma min kamar kwari da ababen hawa suna ta kai komon su, na sarkafe hannuna a kirji ina kallon su ina sake-saken abubuwa a cikin raina har Abbu ya dawo.
- Ya zauna akan sofa tare da mika min hannunshi alamun inje, babu musu na tafi na zauna akan cinyar shi. Ya danyi kissing gashin kaina da goshina, nayi murmushi kafin ya ciro Sim Card wanda ake amfani dashi a kasar sabo ya bani, dama nashi tun a washegarin ranar da safe ya saka nashi a waya ya kira yaran har ma muka gaisa dasu. Tsallen murna nayi a jikinshi na rukunkume shi ina murna, dariya kawai ya dinga yi. Tashi nayi na saka a wayata na kira su Mommy da yake akwai credit a ciki, na sanar dasu mun sauka lafiya, na kira su Ni’ima da Ramlah muka shiga hira har sai da Abbu yazo ya kwace wayar sannan na kashe. Yinin ranar a daki muka yishi Abbu bai sake fita ba. Sai da yamma yace in shirya mu fita, na shirya cikin rigar jallabiya ocean blue, na dora gyalenta a kaina nayi rolling, Abbu kuma yasa pants na KC da riga body hock muka jera muka fita bayan mun rufe dakin.Idan ka ganmu a lokacin kasan cewa kaga perfect match couple wadanda suka dace da juna ta kowane fanni. Hannuna yana sarke ana Abbu muka fita wajen hotel din, a hankali muke tafiya ta gefen titi inda aka tanada saboda masu tafiya da masu tuka keke. Yanayin weather din surrounding din gwanin dadi da burgewa, iska mai sanyi yake kadawa yana wasa da tufar mu, wani dan karamin garden ne muka je, wajen yana ta kamshin furanni da shuke-shuke iri-iri, it was breathtakingly beautiful! Masha Allah!! Abinda na dinga maimaitawa kenan bakina a bude, Abbu dariya ya dinga min da alamun ba sau daya yazo wajen ba. Yaja hannuna muka shiga zagaya wajen, wajene na shakatawa sosai, ga masu sayar da kayan makulashe iri-iri, jefi-jefi zamu ci karo da gungun mutane a waje, either wasu suna kide-kide da raye-raye ko kuma wasu suna su karate, wasa da wuta, da sauran abubuwa dai masu kayatarwa da birgewa, mu kan tsaya mu dan yi kallo ko mu sayi wani abun na motsa baki. Da lokacin magrib yayi muka samu kebantaccen waje Abbu ya tada sallah muka fara, abin mamaki wasu couple suka yi joining dinmu, bayan mun gama muka gaisa dasu nan muka tashi muka cigaba da zagaya wajen dasu, matar Hanan shi kuma mijin Amir mutanen Syria ne, suma sun zo yawon bude idanu ne, gasu da fara’ah da son mutane nan da nan muka saba dasu
- A wata karamar restaurant muka dakata, a tsakiyar garden din take ga haske yanayin setting din wajen kanshi abin kwantar da hankali ne. Babu wasu mutane masu yawa a wajen, ga kida a hankali dake tashi daga background din wajen, very romantic. A table daya muka zauna dasu Hanan, nan ma’aikatan wajen suka zo, mazan suka yi placing order yayin da ni da Hanan muke ta kashe selfies abinmu.
- Muna hira a hankali dasu har muka gama cinye Chicken pepper soup, potato chips and salsa da Rich Maccaron da suka mana oda, bayan mun gama sun dauke kayan aka kawo mana chocolate cake guda biyu, Ya Allah! Ban san lokacin dana fara tafi ba ina giggling lokacin da naga cake dinmu dauke da sunana ni da Abbu, ansa Happy One Month Marriage Anniversary a jiki, kafin ince me! Amir ya tattaro mutanen wajen wai su zo su taya mu murna, nan suka zagaye mu suna tafi da er wakar su, muka bushe lights din candle din kafin muka yanka, Abbu ya saka min a baki nima na saka mishi, daga nan ya kama hannuna muka fita filin wajen muka dan juya haka nan, m not fond of waltz bama iya taka ta nayi ba haka nan dai nabi bayan Abbu, hannunshi daya ya rike kuguna dayan kuma ya rike hannuna na dama ya rike da nashi, yayin da nawa hannun na hagu yake kan kafadar shi, a hankali yake juyawa damu yana bin tattausan taushin kidan dake tashi, I was happy, really! Murmushi nake kamar wata sakara, Ya Allah! Farin cikin da nake ciki a lokacin ban taba tsintar kaina a makamancin shi ba, har ban so kidan ya kare ba, Abbu yaja hannuna muka koma seats dinmu, tafi da shewa da mutanen wajen keyi ya ragu kafin su koma wajen zaman su, nan muka karasa cinye cake din muka yi Sallar Isha’i kafin muka yi sallama dasu Hanan bayan mun yi alkawarin zamu hadu dasu washe gari.
- Nayi zaton daki kawai zamu koma mu kwanta, ga mamakina koda muka shiga hotel din wani wajen muka nufa, mutane na tsaitsaye sun zagaye wani abu mai kama da round about da ruwa a tsakiyar shi kamar swimming pool, wajen babu wadataccen haske sosai amma hakan bai hana ka ganin mutanen dake wajen. Abbu ya janyo ni jikinshi sosai, bakinshi ya kai saitin kunnena ya rada min “are you ready?” na bude baki na a hankali nace “for what?” kafin ya bani amsa kawai naga ruwa yayi fitar burgu daga round about dinnan yayi sama, Ya Allah!! ‘watching fountain show at Bellagio Hotel with Husby!’ abinda ya fara fado min a rai kenan a matsayin status daya dace ace nayi a lokacin, na rukunkume Abbu cikin tsananin farinciki har ma na rasa kalmar mishi magana, kyawawan mintuna shida ruwan nan na sama da kasa in a waves, wasu nata daukar hotuna da videos mu kam muna tsaye muna ta kallo har show din ya kare.Abbu ya sake ja na muka tafi cinema dake nan cikin hotel din, muka sayi popcorn da soft drink muka sayi tikitin romance movie muka shiga, sai karfe goma sha daya muka koma dakin mu, kafin mu yi wanka, Shafa’i da wutiri da sauran abubuwa sha daya da rabi tayi already. 
- Na kwantar da kaina akan gado idanuna a lumshe ina tariyo abubuwan da suka faru ranar, Abbu ya hayo gadon tare da janyo ni jikin shi, kaina ya dora akan kirjinshi yana shafa gashin kaina a hankali na kara lafewa a jikin shi, “how was today?” naji ya tambaye ni, na zagaye kugun shi da hannuwa na, “it was wonderful and unforgettable Abbu” ya danyi murmushi, fuskata ya dago daidai saitin fuskar shi, “am relieved to hear that baby!” ya fada a hankali kafin ya hade bakina da nashi…. 5
- Kwanan mu biyar a Las Vegas, mun je wajaje masu dama na shakatawa da bude ido irin su HooverDam, The Venetian, mun je The Freemount Street mun kalli light show dinsu, tafiyar mu dai kam tayi yadda ya kamata, mun huta sosai mun kuma darji soyayyar mu, a kwanan mu na shida muka wuce zuwa Paris. A can muka bar su Hanan da tuni muka saba dasu, kaya da tsarabobin da muka saya kuwa Abbu ya tura mana su zuwa Beijing inda can ne kasa ta karshe da zamu ziyarta.
- Muna kwance a dakin Hotel din da muke tunda muka isa Paris yau kwanakinmu biyu kenan, kaina yana kan cinyar Abbu shi kuma yana duba jarida, na dago na kalleshi, “wai ni Abbu ya zancen siyasar da ake cewa zaka fita naji shiru har yanzu?” ya kalleni yace “ai tuni na janye” na gyara kwanciyata a jikinshi, “me yasa Abbu?” yace “kawai…. Abin ne kawai naji ya fita daga kaina, dama kuma tun farko Hajiyar mu bata yi na’am da abin ba…. Ya ne?” nayi saurin girgiza kaina, “babu komi Abbu na… Kayi tunani me kyau sosai da kayi hakan” yayi kasa-kasa da idanuwanshi yana kallona cikin alamun tambaya, murmushi nayi tare da shafo tattausan sajen fuskar shi nace “da gaske babu komi Abbu, nima bana son siyasar nan fa!” yayi murmushi, datz very good ai. Nace “yau kuma ina zamu je Abbu?” shiru yayi kamar mai tunani, can ya duko saitin kunnena kamar zai min rada, “surprise!” baki na turo cikin shagwaba, “kai Abbu!” yayi dariya tare da maida kanshi ga jaridar hannunshi, ni kuma na lalubi wayata na kira Hafsy muna hira tana bani sakon abubuwan da zan sayo mata.
- Ranar bamu fita ba sai da yamma, muka shirya muka fita kasan hotel din wanda bashi da nisa da Eiffel Tower, daga cikin dakuna ma kana hango tower din kamar ka mika hannu ka taba ta. Tunda muka zo nake so muje amma Abbu yana cewa ba yanzu ba, mun dai yi yawace yawace sosai mun je manyan restaurants, wajajen shakatawa dana hutawa, har wani Modern Museum of Art muka je Center George’s Pompidou muka kalli hotuna iri-iri, mun shiga wata karamar Art Market inda masu zane suke baje basirar su a wajen nan aka zana hoton mu ni da Abbu, ko a haka muka tsaya it was really worth it.
- Muna sauka kasa muka hadu da Vincent wadda take guiding dinmu idan zamu fita, mata ce mai fara’ah da ban dariya wadda tasan kan aikinta sosai, cikin harshen turanci muka gaisa da ita yayin da suka juya yare ita da Abbu zuwa French. Na turo baki na tsaya a gefen shi har suka gama maganganun su kafin ya kamo hannuna yana dan murmushi, “can we?” na maida mishi martanin murmushin. Vincent na tafe muna binta a baya har gaban Tower din, lokacin dana ganni a gabanta I couldn’t believe my Eyes!! Na kai hannuna daya baki yayin dana kankame hannun Abbu da dayan cikin tsananin farin ciki, Abbu bai gajiya da bani mamaki da farin cikin dake gigitani tunda muka baro Nigeria. Sai dana yi calming down Vincent nata mun dariya, sannan ta mana nuni da matakalar da ake hawa can sama, tace “mu je!” na zaro ido ina kallonta tare da nuna mata elevator da mutane suka yi cunkuso a wajen, nace “ba dai steps dinnan kike nufi zamu hau ba koh?” tayi murmushi, “dear, believe me it’s worth it. Mutanen nan da kika gani kila sai muje mu dawo wasu basu samu sun je ba, kuma idan kika hau elevator dinnan babu abinda zaki gani ki bada labari… Mu je!” na kalli Abbu ya min murmushi, a hankali muka daga kafa muka bi bayanta.. +
- Kafin mu karasa sama na jigata kwarai da gaske, hawa steps din bene dari bakwai da hudu ba abu bane mai sauki lol, wai don ma muna dan tsayawa mu huta, ko kuma mu dan yi hotuna a wajajen da suka burge mu. At last! Bayan lokutan da suka fi awa biyu sai gamu on top of Eiffel Tower! Dana leka kasa ko tracing din mutane ba ka gani, sai kayi zaton cewa dots dots ne, but it was amazing really!!
- Na daga kai na kalli sararin samaniya, yadda ta zama soo close dani kamar in mika hannu in kamo kyakkyawar rana da take shirin faduwa saboda kusancina da ita. Mun jima a gun sosai, sai da muka huce har lokacin Magrib yayi sannan ne muka bi ta elevator muka sauka kasa, sai lokacin na yarda da maganar Vincent, sam banji dadin tafiya ta cikin elevator ba.
- Sai data raka mu har hotel kafin ta mana sallama ta tafi, muka tsaya a wata restaurant anan wajen Hotel din, na zauna a lounge wajen da aka tanada don hutu yayin da Abbu ya tafi yayi sallah kasancewar ina fashi, bayan ya dawo muka ci abinci, Bhajia, steak da lemu mai sanyi. Daga nan muka sake komawa kasan Tower din inda bamu fi minti biyar da zuwa ba aka fara Fire Work! Woah, sai lokacin na fahimci dalilin da yasa Abbu yake ce min in jira ashe saboda show din ne
- Naji dadin hakan sosai kuwa ba kadan ba, ban taba ganin abinda ya burge ni ba kamar kallon fireworks dinnan, idan ina kallo a cikin film jikina har rawa yake yi don burgewa, yau da aka yi displaying abin a gabana sai naji na rasa bakin magana in fayyace wa Abbu halin da nake ciki, kawai na sarkafo wuyan shi na hade bakina da nashi, ina ji ya fahimci sakon da nake son isar mishi, ya rungume ni sosai yana shafa bayana, a hankali na janye daga jikinshi ina dan murmushi cike da jin kunya, sai lokacin da ihu da iface ifacen mutanen wajen ya shiga kunnena na tuna inda muke, nan na karkata hankalina ga display din.Bayan mintuna sha biyar aka gama display din muka koma dakinmu, Abbu yana Sallah na kira Daddy na fara bashi labari, ranar kam har sai daya gaji da saurare ya min sai da safe, na turo baki nace “Daddy har ka gaji dani koh?” dariya yayi yace ni na isa in gaji da jin story daga bakin Uwata? Na gaji ne, ga kuma Mommy dinki can tana jirana mu ci abinci” nace “to Daddy sai da safe, a gaida Mommy” muka yi sallama na ajiye wayar. Toilet na shiga na yi wanka na fito na shirya, already Abbu na kan gado don haka na bi bayan shi muka kwanta.
- Daga Paris muka wuce Sao Paulo, Brazil. Kwanan mu biyar a can muka wuce Amsterdam, can kuma muka yi kwana hudu muka karasa Beijing. Kwananmu biyu a can bana lekawa ko can da nan saboda tsananin gajiya, sai a kwanaki na uku muka fita muka je kamfanin su Abbu.
- Babban Kamfani ne Masha Allah! Shi kanshi ofishin Abbun wani wawakeken ofishi ne daya isa ace an gina wani karamin gida. Muna zuwa suka shiga meeting, ya hada ni da PA dinshi, Chao Shang muka zagaya kamfanin wanda ya dauke mu lokaci mai tsawo sosai kafin muka sake komawa ofis dinshi, har sai da nayi barci akan kujerar hutu kafin ya dawo, nan ya tashe ni muka koma hotel din da muka sauka.
- Mun sha yawo a Beijing kamar Hauka, satin mu daya, mun je kananun garuruwa da kauyukan su mun bude idanu, mun shiga kasuwa mun yi siyayyar tarkace iri-iri da kayayyaki, Abbu dai duk inda muka je kayan jarirai ne yake saya unisex har da kayan wasanni inyi ta mishi dariya. Satinmu daya cif muka hada namu-i-namu muka dawo bayan Abbu ya hada mana kayayyakinmu an auna su a container amma fa sai da muka biya ta Bangladesh wajen Aminu kanin su. Kamanninsu da Abbu har ta baci, gashi da fara’ah da dan banzan tsokana, yana karantar Mechanical engineering ne a nan University dinsu. Already ya mana booking daki a hotel, don haka yana dauko mu daga airport can ya wuce damu, muka yi wanka muka yi Sallah muka yi abinci muka kwanta. Ranar duk nacin Abbu sai kyaleni yayi don ina jin kaina akan gado barci yayi awon gaba dani, ina jin yana lalubata amma na ma kasa daga hannu balle in maida mishi Martani, ina ji yayi kuta tare da furta bashi naci kafin ya janyo ni jikinshi. Aikuwa sai daya biya bashin nan da asubahi har sai daya kara min da alakoro. 5
- Kwananmu biyu a can muka harhada namu ya namu muka wuce Najeriya cike da kewar Aminu da muka saba dashi sosai, shi ya zama idanun mu a can duk da cewa ba wasu yawace-yawace ne muka yi a can ba na azo a gani.
- Saukar dare muka yi don haka muna yin Sallah sai barci, washegari aka yi ta zuwa sannu da zuwa da ganin gidan Amarya da wasu basu zo sun gani ba. Tsawon kwanaki uku ana ta shiga da fita kafin kafa ta daga, na tunkari Abbu da zancen ina so in je gida in ga su Daddy, idanu ya kura min a nutse lokacin kwanan shi daya a gidana, kamar ba zai yi magana ba can kuma yace “yaushe kike son zuwa?” nace “idan ka tafi gidan Anty Mubeenah gobe sai in tafi in dawo jibi” idanu ya xubo min sosai yana kallona kamar wadda notin kanta ya kunce dinnan, “haba Nafeesah! Kwana kuma? A’ah sam ban yarda ba gaskiya, za dai kije ki yini a can wannan kam na yarda amma ban da kwana” na turo baki gaba, “haba don Allah ka bar ni, yaushe rabon da in gansu har na manta fa, kuma ma sai fa nayi ziyarce-ziyarce idan naje can” yace “gaskiya ba zan iya ba Baby, kawai kije ki yini sai ki dawo” tashi nayi ina dira kafafu ni ban yarda ba nayi fushi na fada daki, ya bini da kallo yana dan murmushi. 1
- Da yake dare ne mun gama cin abinci already, wanka na shiga nayi na shafa lotion mai kamshi sosai na aloe Vera, na shafa wani Arabian perfume mai kamshi sosai na fito dakin daure da towel a kirjina, Abbu yana zaune a gefen gado cikin pyjamas ya rungume hannuwa a kirji yana kallona, dauke kai nayi naje na bude wardrobe na fara binciken kayan barci, ban ji lokacin daya tashi daga kan gadon ba sai ji nayi an daga ni sama cak! Na dan saki kara cikin tsoro tare da kara rukunkume shi, kan gado ya dora ni tare da biyo bayana. Na fara mirginawa zan sauka yayi saurin zan sauka yayi saurin janyo ni tare da pinning dina akan gadon ta hanyar rike min hannuwa. Kallon juna muka tsaya muna yi, a hankali ya saukar da bakinshi kan nawa ya fara tsotsa a hankali, da fari mutsu-mutsu na fara amma daga baya, wadannan effects da charming na Abbu a duk lokacin da fatar shi ta hadu da tawa suka sa na manta da zancen fushi na biye mishi…
+ - A hankali yace “kiyi hakuri” nace “umh?” cikin daukewar hankali don bansan akan abinda yake ba da hakuri akai ba, yace “maganar xuwan ki gida, please ki daure kije ki musu yini kawai kinji Baby, please?” nayi shiru ina sauraren bugun da zuciyar shi take yi a hankali, numfashi naja nace to shikenan! Ya kara jana cikin jikinshi sosai, “oh Nafeesah! Shi yasa nake kara sonki a cikin raina kullum. Jibi zaki tafi da safe sai ki dawo da yamma ya miki?” na gyada mishi kai tare da kara shigewa cikin jikin shi. 1
- Ranar Assabar muka dauki hanya ni dashi sai Kaduna. Misalin karfe Goma muna cikin gidanmu, kasa bari nayi mu shiga tare, na bazama da gudu nayi cikin gidan ina kwalawa su Daddy kira, a kofar falo muka ci karo dasu, nan na hada su duka su biyun na rungume a jikina, sai lokacin nasan ashe ba karamar kewar su nayi ba, har da yan guntun hawaye na. Sai da muka gama murnar ganin juna sannan muka karasa cikin falo, Daddy ya fita suka gaisa da Abbu wanda yace xai je ya dawo da yamma mu tafi, ya tafi bayan ya sauke tulin tsaraba da nayo musu daga sassa-sassa na garuruwan da muka da muka je…..Yinin ranar dungurungum a tsakiyar Mommy da Daddy nayi shi, sai bayan Azuhur ne naje gidan Anty Uwani, daga gidan Anty Uwani na lelleka gidajen kawaye na da abokan Mommy muka gaggaisa, bayan La’asar na koma gida inda muka sake dasa wata hirar dasu Dad, har wajen karfe biyar da rabi sannan Abbu ya dawo daukana. Gabadaya ji nayi yinin ranar yayi min saurin karewa, nan nayi narai narai da idanuna kamar zan saki kuka, Mommy taja hannuna muka shiga daki muka bar su Abbu da Daddy suna hira. Mommy ta saka ni a gaba tana bani shawarwari da tambayana game da rayuwar aurena, Daddy ya leko yace in tashi mu tafi, Mommy ta ciro ingantattun turaruka da magunguna ta bani a cikin leda tace sauran bayani zata kira ni. Haka muka yi sallama dasu Daddy kamar kar mu rabu dasu, muka shiga mota suna daga mana hannu muka tafi. Sai gab da Isha’i muka karasa gida kuwa….
- *Washegari…..!*
- “Yauwa, datz good…. Oya, juya shi a hankali mu karya kwanar can…..” a nutse, hankalina gabadaya a kanshi nake bin instructions din da yake bani. Wai mota ce yake koya min duk da cewa dai dama ko a gida Daddy ya fara koya min motar dama, ban dai maida hankali bane wajen koyon kawai. A haka yana bani instructions har na maida mu gida, bayan maigadi ya bude mana gate mun shiga, na yi parking tare da kashe motar na juya ina kallon Abbu da yake kallona yana grinning ear to ear, thumbs up ya min nayi giggling, ya kamo hannuna yayi kissing bayan hannun yace “you are really a fast learner Amour, da alamu gobe da kan ki zaki je ki dawo” murmushi nayi na shafa bayan hannunshi dake rike da hannuna tsam nace “ai dama fa kaine kaki yarda, amma tuni na kware, n yes, I’m a very fast learner, always smart!” ya wani yamutse fuska tare da scrunching hanci, “anya?? Akwai abinda na koya miki amma har yau kin kasa kwarewa” baki na daga zan yi musu kafin na tuna abinda yake nufi, da sauri na bude murfin motar na fita a kunyace, bayana ya biyo yana “tsaya mana baby” amma ban tsaya ba sai a cikin daki, ya shigo yana er dariya kasa-kasa, baki na turo ina kallonshi, ya tsaya a gefena tare da kamo fuskana ya rike, “fushi kika yi koh? Ai gaskiya na fada ko karya nayi?” na ciza lebena na kasa, “haka kace koh? Ni kuwa sai na baka mamaki” gira ya dage sama alamun yana challenging dina, “oh really? Bring it on then” murmushin mugunta na saki tare da matsawa gaban shi seductively ina kallon fuskar shi, ga kunya ina ji amma I don’t want to lose don haka na jefa kunyar a cikin kwandon shara na rufe for the time being, in yaso daga baya na dauko ta sai in wanke…
- Bayan kamar awa daya na fito daga bayi ina goge jikakken gashina da towel, yana zaune a gefen gadona yana kallona cikin murmushi. Naja kujera na zauna tare da jona dryer ina kafe gashin kaina, yayi gyaran murya, “I admit” na juya na kalleshi tare da yin murmushi cike da kunya, “na fada maka ai!” yayi er dariya “yes Babe, shi fa dayan?” idanu na zaro sosai, ya daga min gira yana er dariya, wani dan tuntu mai kama da soso na dauka na jefa mishi, ya cafe tare da komawa kan gadon rigingine ya kwanta, na girgiza kai tare da cigaba da goge gashina.
- Cikin kwana biyu kuwa na kware sosai, yau da kaina na kai shi gidan Anty Mubeenah da yake ranar girki yake komawa hannunta, bata nan ma lokacin da muka je sai yaran, bayan mun gaisa da Harira na dauki yaran muka je gidan Anty Rahina data sha zazzabi kwana biyu muka duba ta, daga can muka wuce gidan Ni’imah dake ta laulayi, muka karasa gidan Anty Ameenah, a takaice sai da yamma na maida su gida har lokacin kuma Anty Mubeenah bata dawo ba. Na musu sallama na wuce gidana inda na tarda Zainab tana jirana.
- **** ****
- Bayan sati daya muka koma makaranta, da kaina nake tuka kaina zuwa lectures wata rana kuma Abbu ne yake kaini. Yanxu en class dinmu duk sun san wanda na aura, na share kwanaki kafin su daina tsokana, shakiyanci da taya ni murnar aure, a haka dai muka ci gaba da karatun mu
- Yau Abbu zai yi wata tafiya zuwa birnin Ikko taron karawa juna sani, daga wannan taron ne muke fata za a bashi matsayin Professor idan ya dawo. Da yake kwana na ne ranar ni na taya shi hada kayan shi wadanda zai bukata. Tafiyar kwanaki shida ce zai yi. Ni na raka shi har airport, sai da naga tashin jirgin su sannan na koma gida cike da kewar Abbu na, har yau na kasa sabawa da rashin shi a kusa dani.
- Kasancewar muna waya dashi, chatting, sometimes ma har video call, shi yasa ban ga tsayin kwanakin da yayi ba, kwanaki shidan na cika kuwa ya dawo, zai karasa kwana daya a gidana kafin ya koma gidan Anty Mubeenah. Na tare shi da murnata da tarin delicious abinci dana hada mishi kafin muka dire a gado inda muka nunawa juna tsananin kewar juna da muka yi. Washegari ya koma gidan Anty Mubeenah.
- *****
- Muna gama lectures da misalin karfe biyar na ranar Alhamis, na fito daga class din a dan gajiye na nufi parking lot inda nayi parking Vibe dita, na bude murfin motar kenan zan shiga naji an kira sunana, “Malama Nafeesah??” na juya ina kallon matashin saurayin daya kira sunana cikin mamaki da alamun tambaya, nace “na’am, lafiya??” Wata envelope brown ya miko min, “sako ne?” na kalleshi “sako? Daga wa??” ya girgiza kai, “I was just asked to pass it to you” na jijjiga kai, hannu nasa na amshi envelope din tare da mishi godiya, “ok thanks” yayi nodding kan shi kawai ya juya ya tafi. Na bishi da kallo kafin na gyada kaina kawai na bude motar na shiga tare da mata key bayan na jefa envelope din a bayan motar, ina kokarin yin kwana na juya na dan kalli gefe na na dama kadan kafin na wuce.
- Koda na isa gida wanka na fara yi tare da dora abinci naci, Abbu yana gidan Anty Mubeenah Zainab kuma taje gida da yake yanzu na saba da zama ni kadai. Da dare Abbu ya leko ya min sai da safe kafin ya tafi da yake sai washegari ne zai dawo gidana. Yana tafiya na kashe wutar gidan naje na kwanta. Haka kawai envelope din da aka bani ta fado min a rai, na tsinci gabana da faduwa sosai. A raina na raya sai washegari zan duba. Washegari Abbu ya dawo, da yake sai karfe goma nake da class bayan mun karya ya wuce dani makaranta. Da aka tashi sai na biyo adaidaita ya dawo dani gida don shi Abbu ya wuce masallaci.Zan wuce ta gaban motar idanuna ya sauka a bayan motar na hangi envelope din nan, motar na bude na dauki envelope din na shige cikin gida, abincin rana na daura bayan na gama nayi wanka na kimtsa jikina na zauna jiran Abbu. Out of frustration na jira, na janyo envelope dinnan na bude. Hotuna suka fado daga ciki lokacin dana bude ta, na dauki hoto daya na bude. Abbu ne sanye da kayan dana gane su riga shirt brown mai bakaken lines da wando trouser baki, suna daga cikin kayan dana hada mishi lokacin da zai tafi Lagos. Yana zaune a wani waje kamar na shakatawa suna magana da what? Wata Mace ce amma ta juya bayan ta don haka babu fuska, na dan yamutse fuska tare da bude wani hoton, su dinne dai a waje guda amma a tsaye da alamu zasu tafi, na bude wani, ido na zaro ganin matar nan a jikin Abbuna!! Ya dora hannunshi akan kafadar ta, cikin rawar hannu na bude wani hoton… Da sauri na runtse idona ina jin ana min wani lugude a kirjina, Abbu shi da wata kwance a kan gado babu riga a jikin su, Abbu shi da wata kwance akan gado wata Watsattsiya tana shafa shi da filthy hannuwanta, Abbu na!! Abbu na…. Abbu dai mijina shi da wata akan gado…. Gado dai a kwance wata banzar bazara ta dora filthy mouth dinta akan precious and luscious lips din Abbu na!! Innalillaahi Wa Inna Ilaihi Raji’un….. Na kwala ihu tare da yin watsi da hotunan suka zube a tsakiyar dakin ko wanne yayi nashi wurin, wasu zafafan hawaye suka shiga zubo min a kan kumatuna…, does that mean Abbu has been lying to me?? Haba, biri yayi kama da mutum, sau tari na kan tambayi kaina taya Abbu mutum mai matsananciyar sha’awa yake iya rike kanshi daga matan banza bayan baya samun yadda yake so daga wajen matar shi?? Na yarda dashi, nayi amanna dashi, nayi zaton cewa idanun shi suna ga halalin sa ne, Ashe……!!
- Ghen! Ghenn!! Ghennn!!! Toh fa!! Ga wata sabuwa inji en caca!! Me kuke tunanin zai faru da wannan hargitsi da rikici daya danno kai cikin rayuwar Auren su??
- Wai shin! Me Nafeesah ya kamata tayi ne yanzu? Lokacin da aka kira sallar La’asar lokacin ne hankalina ya dawo cikin jikina, na tashi da kyar da bin bango ina jin jiri na shiga toilet nayi alwala na fito nayi sallah, akan abin sallah naci gaba da zama na kurawa hotunan dake watse a tsakiyar dakin idanu gabadaya kwalwata ta kasa nema min mafita akan abinda ya kamata inyi. 1
- Nayi tunanin in jira Abbun ya dawo in kwashi hotunan in watsa mishi a fuska, wata zuciyar tace shake shi zan yi har sai ya gaya min gaskiyar abinda ya faru, wata tace kawai in tashi in bar mishi gidan shi bai kamata in ci gaba da zama da maha’inci ba, tunanika barkatai har ta kai ga bana fahimtar abinda zuciyoyina suke kullawa da warwarewa. Cikin wannan halin na jiyo karar mota alamun dawowar Abbu daga masallaci, na tashi da kyar naje bakin kofa na tsaya ina hangen shi yana fitowa daga cikin mota hannunshi dauke da leda, agogo na duba. Awowi uku da suka wuce ya kamata ace ya dawo gidan, ina ya tsaya? Na samu zuciyata da saka tunanika marasa dadi, ina kallon shi ya taho da waya makale a kunnenshi, at the last step da zai hada shi da kofar falon, wani tunani ya dar su a cikin raina. Abbu na ne fa? Abbu na dai the gentle and good man dana sani ba wani ba, mutumin dana zauna a gidan shi na tsayin watanni shida ba tare daya taba rike yatsan Hannuna idan ba mistake ba, da ace dan iska ne kamar yadda nayi zato anya zai iya kyale ni kuwa bayan da ace yaso ya lalata ni da tuni yayi hakan? Mutumin da ko bayan aurenmu sai daya jira da ixini na da komi kafin ya kusance ni?? Dana kara tuno wasu abubuwan sai na samu kaina da sake kallon hotunan idanuna na hango katon question akan kowannen su zuciyata na tamvaya na anya kuwa babu lauje a cikin nadi??. 5
- Da sauri na koma na hau tattare hotunan na janyo drawer ta gefen gado na watsa su ciki tare da fadawa toilet da sauri na, dole in zauna in sake tunani kafin in yanke hukuncin abinda ya dace inyi, ina rufe kofar bayin naji shigowar Abbu dakin….
- Ganin bana dakin yasa ya fita daga dakin tare da maida min kofar dakin ya rufe. Na kurawa kaina idanu a jikin mirror ina kallon reflection dina, kwalliyar da nayi ta hade da ruwa da hawaye ta maida ni kamar zombie. Ruwa da sabulu nasa na wanke fuskana na kara yin wata kwalliyar kafin na fita, akan kujera na gan shi a zaune. Yana ganina ya saki murmushi mai taushi, yayin da naji gabana ya fadi sosai, anya zan iya daurewa kuwa? Don a daidai lokacin zuciyata tana kitsa min in ci kwalar shi ne kawai. Na daure na kakalo murmushi wanda nasan ko fatar bakina bai gama hadewa bama, a sanyaye na karasa kusa dashi na dan duka tare da cewa “Abbu sannu da zuwa” ya amsa yana murmushi, “kin ga na dade koh?” na gyada mishi kai kawai, yace “wai gidan Rahina na biya, shine ta hado ni da kaya ma tace in kawo miki” ya miko min ledar daya shigo da ita na amsa tare da dubawa, turaren wuta ne sai wani kamar na tsuguno idan ban manta ba naga irin shi cikin kayayyakin da aka hado min daga gida. Na maida ledar na rufe tare da kallon shi nace “abinci?” ya lumshe idanu tare da gyada kai, “please, m hungry… Very” da ace zuciyana cikin kwanciyar hankali take da babu abinda zai hana ni kamo fuskar shi in bashi sumba a baki, a yanzu kam koda tunanin ya fado cikin raina I found it disgusting sosai. Sai kawai nayi wajen dinning table ban ko yi magana ba yayin da naji lokacin daya tashi ya biyo bayana.
- Abincin na hau zuba mishi, gabadaya cikina a cushe yake nasan sam babu abinda zai shiga cikina a lokacin don haka na zuba mishi iya wanda zai iya ci kawai, ina gamawa na tura mishi su gaban shi na juya da niyar tafiya yayi saurin sa hannu ya riko hannuna, ji nayi kamar garwashi ya taba ni, kallona yayi sosai, “ina zaki je haka? Ba zaki ci abincin bane?” na girgiza kai tare da kallon shi, “naci tun dazu da naga baka dawo ba” ya kara kallona kamar wanda bai yarda da abinda nace ba kafin naga yayi murmushi tare da jan kujerar gefen shi tayi baya ya zaunar dani, “ok, zauna ki taya ni hira toh, kin san cewa dai bana jin dadin cin abinci idan ba kya gefena koh?”. 1
- Haka na zauna tare da kurawa kasan carpet din idanu ina ta saka da warwara, ban san lokacin daya gama cin abincin ba, ya juyo dani na fuskance shi, “baby, me ke damun ki ne?” ya fada cikin nuna damuwa da halin da rashin walwalata a gare shi, nima nasan cewa yaudarar kaina kawai nake yi idan har nace wai zan iya pretending inyi behaving kamar yadda na saba. 2
- Na girgiza kaina kawai, “babu komi Abbu, bana jin dadin jikina ne kawai” da sauri ya dora hannun shi akan goshina yaji babu zafi, ya dawo dashi wuya nan ma komi normal, yace “amma jikin ki lafiya lau… Are you sure ba sai mun je asibiti ba??” nayi saurin gyada kai, “m ok” yace “idan kin ji da wani abu don’t hesitate fa, ki sanar dani” na gyada mishi kai, yayi murmushi tare da cewa “good girl” fuskana ya matso daidai tashi tare da kawo bakin shi saitin nawa, ina fahimtar abinda yake shirin yi nayi saurin kauda kaina gefe ta yadda leben shi ya kare da sauka akan kumatuna ba lebe na ba, ya dago ya kalleni cike da alamun tambaya, da sauri na tashi na tattara kayan da yayi amfani dasu na kai kicin. Wanke su nayi tare da dora abincin dare, ya leko kicin din ganin ina girki yazo ya kashe gas din, a hankali na dago na kalleshi amma ban yi magana ba, kafada ya daga cikin alamun tsokana “hey chill! Ba sai kinyi girki ba yau, zan fita in sayo mana abinci” sai kawai na juya na sauke tukunyar dana dora na zubar da ruwan tare da rabawa ta gefen shi na fita
- Ina gaban wardrobe dina ina shirya kayan ciki wadanda na ciro su daga ciki musamman saboda in dauke hankalina daga tunanika, Abbu ya sake shigowa dakin. Gefen gado ya samu ya zauna yayi tagumi tare da zuba min idanu wadanda seriously na dinga jin su a cikin jikina kamar me?? Kokari nake kawai naci gaba da aikina. Can kasan zuciyata ina so in mishi maganar, sai dai ina matukar tsoron abinda xai fito daga bakinshi, ina tsoron ya amsa min da ehh shine don a hakikanin gaskiya ban san ina zan jefa rayuwata idan hakan ta kasance ba.
- Haka muka wanzu har aka kira sallar Magrib, Abbu ya tashi ya shiga toilet dina ya fito daure da alwala ya wuce masallaci, sai dana ga fitar shi sannan ne nima na dauro alwalar naxo na tada kabbarar sallah, anan kan sallayar na zauna bayan na gama ina laxumi har aka yi Isha’i nayi sallah. Tashi nayi na nade abin sallar, ina ta en kimtse-kimtse na wanda a zahirin gaskiya basu da amfani ina yi kawai don kada su dauke mun tunani, Abbu ya dawo daga masallaci. Dakin kawai ya leko yace in fita mu ci abinci. Na fita falon na same shi har ya fiddo plates waje, naje gefen shi na zauna kawai.
- Gashin nama ya xuba mana cikin plate din da yoghurt a cikin cups, na sa cokali muka fara ci daga cikin kwano daya. Ba wai don wani abu ko yunwa nake cin abincin ba, kawai saboda bana so Abbu ya dame ni da korafi ne don a lokacin ko kadan bana so inyi magana, gabadaya raina a jagule yake. Abu na karshe da nake bukatar yi shine in kadaice a waje guda in nemi mafita a cikin rayuwata data aurena gabadaya.
- Duk da halin da nake ciki hakan bai hana ni jin dadin naman ba har ma ban san lokacin dana bude ciki naci naman sosai ba, sai dana ji cikina ya cika kafin na kora da yogurt din, lokacin Abbu ya ture kwanon gefe alamun ya koshi don haka na tattara kayan na kai kicin, sauran kayan duk na saka su a cikin freezer na fita falo. Abbu yana zaune akan kujera yana kallon labaran kasa, na shige shi zuwa dakinshi da yake yanzu yawancin kayana ma suna dakin don ragewa kaina wahalar je ka dawo daga wannan dakin zuwa wancan. Toilet na shiga nayi brush na fito na shirya cikin kayan barci tare da fesa en turaruka na kwanta. Not that barci nake ji ko kuma gajiya, kawai ina gujewa Abbu ne.
- Misalin karfe tara Abbu ya shigo dakin, ina jin alamun shigowar shi na kara lafewa akan gado kamar mai barci. Ina ji ya gama duk abubuwan da zai yi kamar su brush, shafa turare, sa kayan barci da sauran su. Ina jin lokacin daya kashe wutar dakin kafin inji alamun hawan shi kan gadon, na kara sakankance jikina sosai. Ina jin lokacin daya janyo ni jikinsa, duk da ihun da naji ana min a kunne akan in kwace jikina sharewa nayi, bana so inyi abinda zai sa Abbu yayi zaton idanu na biyu. Ina jin shi yana lalubata wanda da da ne tashi zanyi koda barcin nake yi in shige cikin kirjin Abbuna mai fadi, yau kam ban yi hakan ba. +
- Bayan lokaci mai tsayi naji alamun yayi barci, a hankali na zare jikina daga nashi tare da juya mishi baya, wasu siraran hawaye suna gangaro min a kumatu, ban san yaushe barci ya kwashe ni ba. Da asubahi Abbu ya tashe ni daga barci ya wuce masallaci. Ina kan sallaya ina karatu lokacin daya dawo daga masallacin, kan gado ya hau ya kwanta rigingine, ban motsa daga inda nake ba har sai da gari yayi sha, na rufe al-qur’anin na mayar dashi inda ake ajiye shi na fita daga dakin. Kicin na shiga na fara shirya break fast.
- Abbu ya shigo kicin din, ina tsaye ina wanke hanta a jikin sink, ya tsaya a daidai gefena na dama. Kwana daya kacal daga ni har shi mun yi wani zuru-zuru damu, hannu yasa ya kamo habata a kokarin shi nason mu hada ido, sai nayi kasa da nawa idanun na hana shi ganin kwayar idanu na. Muryar shi tayi kasa sosai cike da damuwa yace “hey, me ke faruwa da ke ne Nafeesah?” na kara yin kasa da kaina na kasa magana, ya kara matsowa kusa dani sosai har ina jin saukar numfashin shi a kaina, fuskana ya sake dagawa sama, “talk to me Nafeesah please….. Look at me” yadda yayi maganar kamar wanda yake rokona yasa na daga idanuna na kalli nashi idanun, tsananin damuwa da kulawa dana hanga a cikin idanunshi suka sa ban san lokacin da hawaye suka zubo min ba, sai dana ji dumin su akan kumatuna sannan na ankara… 
- Abbu ya ida hade er tazarar dake tsakaninmu tare da rungume ni kam a jikinsa, a hamkali ya kai hannu bayana yana shafawa a hankali alamun rarrashi, hakan ya kara karya min xuciya sosai… Na zagaye hannuwana a bayan shi tare da fashewa da kuka ba tare dana shiryawa hakan ba…
.