AMININ MAHAIFINA
CHAPTER 17 THEND KARSHE
Bayana yake tapping a hankali ba tare da yayi magana ba, ina jin yadda zuciyar shi take bugawa da sauri ban sani ba bacin rai ne ko tausayi na? Shi dai ya bar wa kan shi sani. Hannu yasa ya kashe gas din dana kunna, yaja hannuna ba musu na bi bayan shi muka fita daga cikin kicin din. Daki ya kaini ya zaunar dani a gefen gado yayin da shi kuma ya zauna a kasa a gabana ina fuskantar shi.
Sai dana gama shesshekar kukan da nake yi da komi, ya tashi yaje kan mirror ya dauko tissue ya miko min, hannu nasa na amsa na goge fuskata dashi. Wajen daya tashi ya koma ya zauna ya kalleni…, “ok, ina sauraronki. Fada min, me ya faru??” 1
Idanu na kura mishi cikin tunani, shin in gaya mishi ko kuwa in yi shiru? Shin in nuna mishi hotunan ko kuwa zan ci gaba da boyewa ne ina kwarar mu?? Ganin nayi shiru ba tare da nayi magana ba yasa ya kara matsowa gab dani, ya kamo hannuwana ya damke cikin nashi tare da dora su akan cinyata, murya can kasa wadda ta dakushe cike da damuwa yace “Kalle ni Nafeesah!” na dan yi hesitating na en dakikai kafin na daga kai a hankali na kalli kwayar idanun shi, take jikina yayi sanyi sosai, na kasa daurewa kallon tsananin kulawa, so da kauna da suke cikin idanun shi sai na kara yin kasa da kaina.
Yace “Nafeesah, idan ban manta ba na fada miki cewa babu boye sirri a tsakaninmu, ba zamu boyewa junan mu Abu ba komi tsananin munin shi kuwa, amma meye yanzu kike yi? You are hiding something from me Nafeesah, kin saka ni cikin damuwa gashi na rasa gane matsalar balle in magance miki ita, please tell me Nafeesah, tell me me ke damun ki??” rikon da yayi min a hannuna ya kara karfi, ajiyar zuciya na sauke a hankali. That’s it! I couldn’t do this anymore, kawai bari inji ta bakin shi in yaso komi ta fanjama shi kenan.
Naja numfashi a hankali tare da tashi cikin sanyin jiki bayan na zare hannuna daga cikin nashi, ya juya ya bini da kallo. Drawer din na bude na ciro hotunan cikin faduwar gaba na koma inda yake, sai dana lalubi gefen gado na zauna kafin na mika mishi hotunan, ya kalleni sosai kafin yasa hannu ya karba, na kura mishi idanu sosai ina so in ga yadda zai karbi ganin hotunan.
Idanun shi suka fito waje sosai kamar wadanda zasu fado kasa, nuna su yake yi da hannunshi kamar wani tababbe, da kyar ya iya kakaro sautin “Naffee..sah…. Daga ina??…” cikin rawar murya yana nuna min hotunan, na kura mishi ido ina kokarin karanta kalar tsoro dana gani a cikin idanuwan shi, na tsoron asirin shi ya tonu ne ko kuma na wani abu daban?? Nace “ba kai bane ba koh Abbu??” na kura mishi idanu cikin tsananin tsoron jin amsar da zata fito daga cikin bakin shi. Kai ya girgiza min da sauri, “bani bane ba Nafeesah., I promise you bani bane ba!”. 2
Wani irin sanyi ya xiyarci zuciyana da gangan jikina gabadaya, na silale daga kan gadon na fada cikin jikin shi na rungume shi kankam kamar zan tsaga shi, nadama ta shige ni sosai. Da ace tun a jiyar na mishi magana da hakika bamu yi kwanan rashin sukuni da bacin rai ba, da ace tun a jiya din na mishi magana da ban ji bugun zuciya da ya dinga yin kamar zai kashe ni ba, da ban kwana cikin dacin rai da fargaba ba….. Nasa kaina a cikin wuyan shi ina kuka a hankali wanda sautin shi baya fita sai jikina da yake rawa saboda danne kukan da nake yi.Abbu ya zaunar dani a kasan carpet din yasa hannu yana share min hawayen, sai da kukan yayi kasa kafin naji ya fara magana a nutse. “waye ya baki hotunan nan? Yaushe kuma?” naja shessheka kafin nace “ban san ko wanene ba, kawai dai wani yayi mun sallama sai ya bani yace wai sako ne tun shekaranjiya, sai jiya ne na bude” ya kura min idanu kamar wanda yake mamakin abinda nace mishi.. Can yayi magana a hankali, “kuma shine kika boye min, why??” +
Na girgiza kaina kawai, yace “look Nafeesah!” na daga kai na kalleshi, yace “na fahimci tsoron abinda zai biyo baya ne ya hana ki fada min. Naji dadin hakan kamar yadda naji haushin boye min din da kika yi. Daga yanzu kada ki sake yi mun irin haka don Allah kinji? Kome ya faru kada kiji tsoron fada min, ta haka ne kadai zamu gina rayuwar aure mai inganci irin wadda nake so kin gane??” na gyada mishi kaina a nutse.
Hotunan ya sake dagawa yana kara kallonsu daya bayan daya yana girgiza kai idanunshi jawur, “Wallahil-Azeem bani bane Nafeesah. Ban taba bin mata ba, ban taba kusanta kaina da zina ba, bane bani!” hannunshi na rike cikin nawa ina gyada kai, “wallahi na yarda da kai Abbu. Ban san me yasa na kasa fada maka ba tun farko, amma ba zan sake maimaita hakan ba” hancina ya dan ja a hankali yana dan murmushi, nima nayi. Hoto daya ya dago yana nuna min, “kalli nan ki gani” na kurawa hoton ido ina kallo, hoton Abbun ne a tsaye babu riga a jikin shi yayin da macen da aka nuno su tare har lokacin ba a ganin fuskarta a kwance akan gado, nace “me zan gani?” kirjin mutumin jikin hoton ya nuna min, “nan, kin ga babu alamun tabo dina” na kama baki cike da tsananin mamaki, ya aka yi ban kula da haka ba? Ba mamaki saboda idanuna sun rufe ne shi yasa. Wani tabo ne a kirjin Abbu kusa da kafadar shi, tabo ne babba wanda yace lokacin da yaji ciwon it took him almost 3 months kafin ciwon ya warke amma tabon yana nan, yanzu dana kalli mutumin jikin hoton sai naga babu alamun tabon, kai karewa ma dana kare mishi kallo sam sai naga Abbuna yafi na jikin hoton kiba, to idan ba Abbu bane waye?.
Abbu ya kuta, “da alama wani ne yake so ya shiga tsakanin rayuwar auren mu Nafeesah, shine yasa aka yi photo editing din wani da fuskana aka kawo miki don ki tada balli, koma waye yayi haka ya gina ramin kuskure mai zurfi wallahi, I wouldn’t spare him!.
Wani tunani ya darsu a cikin raina, da sauri na kauda tunanin. Abbu ya kalleni “menene?” na girgiza kai, “m not sure don zargi bashi da dadi. Amma ranar da saurayin ya bani envelope din lokacin ina kokarin karya kwana, naga the same saurayin a tsaye shi da Dr Lubah… Ganin su kawai nayi, ban sani ba ko tana da hannu akan hakan?” Abbu ya dunkuke hoton hannunshi, “Dr Lubah!!! Zata aika, ta sha fada min zata yi duk abinda zata yi duk abinda zata yi wajen ganin cewa ta raba ni da farin cikina. Ban yi zaton da gaske take ba, I thought kawai tana fada ne don cika baki ashe da gaske take? So she can stoop this low kawai don ta raba ni dake?” nace “ni fa kawai ganin su nayi tare, bani da tabbacin ko ita ce” yace “ki ma daina wani tantama, she’s the one” nace “zato dai bashi da kyawu, kamata yayi ka bincika kafin ka yanke hukunci” yayi shiru kafin ya gyada kai, “haka ne kuma, zan bincika in shaa Allah…. Now.., food!” dan murmushi nayi tare da mikewa na nufi kicin shima ya biyo bayana.Ranar tare dashi muka yi girkin, muka koma falo muka karya muna hirarrakin mu cike da nishadi, ranar ko nan da can Abbu bai fita ba, yana manne dani kamar chewing gum. Da haka rayuwar auren mu ta koma normal kamar, ko ma in ce fiye da da. 4
Bayan kamar sati biyu da yin haka, ina zaune a falo Abbu ya dawo daga office. Da murnata na tare shi, na taimaka mishi yayi wanka tare da cin abinci. A wajen cin abincin ne yake bani labarin yadda suka kare da Dr Lubah yace; “ai kin amsa laifinta tayi sai dana kai karar ta ga hukumar makaranta sannan, yanzu dai an mata warning game da haka. Ance idan ta sake a bakin aikinta, shine fa bayan mun fito wai take bani hakuri wai sharrin shaidan ne, ni dai na gaya mata idan ta kara bari ma muka hada hanya da ita to ta tabbatar sai na kai karar ta” nayi dariya nace “ashe da gaske ita din ce dai?” ya girgiza kai, “ai ki daina wasa da lamarinta, matar bata da mutunci da kike ganinta. Sai da maganar ta kai ga sauran malamai nake jin ashe an taba kwantar da wata budurwa a asibiti data taba ganinta a tsaye ita da saurayinta, itace fa ta dauka ta maka mata a kai. Sai daga baya ma ake fada mata ashe er uwar saurayin ce, sanadin rabuwar su dashi dai kenan” na kama baki cike da mamaki, nace “to Allah ya shirye ta tare da masu hali irin nata” Abbu yace “ameen”…
A karshen watan muka koma ainihin gidan da zamu zauna. Wani dankareren babban gida a cikin Lamido Crescent, flat ne da dakuna bila adadin. Babban falo daya dauke saitin kujeru biyu, kicin, store, sai wani corridor wanda idan ka bishi zai sada ka da wani karamin falon inda anan Dinning yake sai dakunan much ni da Anty Mubeenah. Dakin mu ciki ne da falo, sai dakin Abbu, na yara da kuma study room inda muke zuwa mu yi karatu abinmu. Komi na gidan sabo ne dal wanda Abbu ne ya dauki nauyin yin hakan, duk da dai akwai daki na musamman anan kusa da dakina wanda aka ajiye min jeren da Daddy yayi min.
Zaman gashi nan kadaran-kadahan. Muna zaune lafiya daga uwar har yayanta da maigidan, batun hali a wajen Anty Mubeenah har yanzu bata canza zani ba, tana nan kamar da da rashin kula da kanta, mijinta da rayuwar aurenta gabadaya. Abbu ya dauko en aiki wadanda suke zuwa suyi shara, goge-goge da sauran su, da kaina nake girki na in kuma gyara dakunan mu dana Abbu. Ina ji shi yasa hatta da yaran suke dokin zagayowar ranar girkina saboda dadadan abincin da nake dafa musu ba kamar abincin Harira da har lokacin tana manne damu ba.
Ranar va sai ga en uwan Anty Mubeenah a gidan ba?? Shakira da Umaimah kamar daga sama. Muna falo ina koyawa Hafsy assignment lokacin, na daga kai da er fara’ata saboda nasan ba abin arziki ne ya kawo su ba, na gaida su. Suka amsa suna wani yatsine yatsine, wai “ina uwargida ran gida mai babban matsayi a gidan Ibrahim Galadanchi?” abin ma ya bani dariya, na girgiza kai kawai. Umaimah taja tsaki, “kamar fa wannan dangin masu kwacen mijin kallon uku-saura take mana, irin wuyanta ya isa yanka dinnan” Saddiqar tace “kyaleta, karyar banza take. Yo ni Allah na tuba idan da ba don albarkacin Mubeenah ba wannan er tsakin ta isa in kalleta? Taci gaba da abinda take yi wallahi yanzu zan kwantar da mutum a kasa”.
Daidai lokacin Anty Mubeenah ta shigo falon, ganin en uwanta ta hau fara’ah, Umaimah tace “yauwa Yaya, wannan er iskar matar fa tana nema ta raina mana hankali, kinga wani kallo da take jefa mana ni da Anty Saddiqa??” Mubeenar ta kalle su kafin ta sake kallona, dan murmushi tayi ni na ma yi zaton ko zagi zata auna min, sai kawai naji tace musu “ko zo muje daki mana” da alamu suma abin ya basu mamaki ganin yanda suka hangame baki, can Saddiqa ta gyada kai, ta jefa min harara ta shura takalmi tayi gaba Umaimah tabi bayanta, Anty Mubeenah ta kallemu tace “kiyi hakuri fa!” tayi gaba ba tare da taga yadda na hangame baki a dimauce na bita da kallo ba, abin ya matukar bani mamaki kwarai ba kadan ba. Nayi zaton zata goyi bayan en uwanta ne su hadu su zageni kila ma har da duka kamar yadda naji ana bada labari, sai naga akasin hahaka, har da bada hakuri ma. Na jinjina kaina tare da tsintar kaina ina mata addu’ar Allah ya dawo da ita kan hanya. +
Da zasu tafi ma haka suka same mu a falon ni da Hafsy, ko er Allah ya kiyaye hanya din da na musu Allah bai basu ikon amsawa ba. Na tabe baki tare da daga kafadata, basu dameni ba ko Kaden, in dai muna zaman lafiya da abokiyar zama na to shikenan ni kam.
*****
Ba a wani jima ba aka yi auren Harith shi da Ikram, na samu da kyar an bar ni naje wajen daurin aure. Wannan shine zuwana Kaduna na uku tun bayan da aka min Aure
Ni’imah ta haifi santaleliyar yarinya mace taci sunan Halima mahaifiyar Basheer sai suke kiranta da Amal. A daren ranar ina kwance akan gadona a gajiye Abbu ya shigo dakin da yake ranar girki ta ce. Kan gadon ya hayo ya dauki kafafuna ya dora akan cinyoyin shi ya fara matsa min su, idanu na lumshe tare da kara lafewa akan gadon. Abbu yace “dube ta don Allah! Sai kije kiyi ta faman yin aiki da kai da kawo sai dare yayi kuma kizo ki dinga min raki” cikin muryar barci nace “to Abbu menene a ciki, yiwa wani yiwa kai balle su Ni’imah ne fa, idan na hidimta musu kamar kaina na hidimtawa” ya kuta, “just wait and see, idan kika haihu duk wadda bata miki wahalar da kike musu ba sai na bata musu rai” dan murmushi kawai nayi tare da maida idanuna na lumshe.
Ya juyo dani na koma rigingine, hannu ya kai yana dafa cikina, “wai ni tsaya, har yanzu ban yi ajiya anan wajen bane duk kokarin da nake yi?? Lokaci ya fara ja fa, muna bukatar jin kukan jarirai a gidan nan” nace “Allah bai kawo ba har yanzu Abbu” yace “ki ce in kara kaimi kawai” da sauri na girgiza kai, “a’ah, ba sai ka kara ba wallahi. Zan taya mu addu’ar Allah ya kawo su kawai Abbu” kai ya girgiza kamar wani karamin yaro, “naki wayon….” wuta ya kashe mana tare da janyo ni cikin jikinsa..*BAYAN SHEKARU BIYU DA RABI!*
Na fito daga dakin Abdullahi hannuna dauke da tarin kayan wankin dana fiddo mishi. Duka yaran suna zaune akan kujera, Abdullahi da Qaseem suna game na Super Mario, Hafsy kuma tana wasa da wayata. Anty Mubeenah kuma tana gefen Hafsy tana duba jarida.
Abdullahi ya kalleni yayin dana harare shi nace “kalleshi dirty guy kawai, sai aukin fi’ili da gayu, idan ya dau wani wankan sai kayi zaton abin har dakin shi ne sai ka shiga labari ya sha babban” Abdullahi yayi kasa da kai yayin da Qaseem yasa dariya, shima na harare shi.., “see who’s laughing! Jiya dana shiga dakinta kasa numfashi nayi sai dana sa mask, wai anya kuna ma yin wanka??” Anty Mubeenah ta dan saki dariya, da sauri na juya na kalleta. Ganin ina kallonta yasa ta dauke kanta da sauri, nayi dan jim ina kallonta.
Kwanaki biyun nan ina ganin wasu canji a tare da ita, fuskarta tayi rama sosai, haka zan ga ta zauna tayi shiru cikin tunani gashi har zuwa lokacin bata bani fuskar da zamu yi sabon da zan tambayeta abinda yake damunta ba. Damuwar da take ciki na damu na, I really want to help. Na juya kaina daga kanta a hankali na tunkari kofa, Shuaibu mai mana wanki da guga na ba kayan na koma falo.
Na kallesu, “daga yau duk wanda ya cire kaya kar ya kuskura ya maida su cikin drawer, a sa a laundry bin sai a wanke, kuna ji na? Manya daku saboda Allah amma wallahi Hafsy ta ma fiku tsafta” Abdullahi ya turo baki yana hararar Hafsy da take mishi gwalo, yace “ai saboda ita gyara mata daki ake yi, mu fa?” na Harare shi, “saboda ita yarinya ce, ku kuma kun girma, kayan da aka cire should always be put in a laundry bin ok??” suka gyada kai, nace “good!” na wuce dakina.
Ina shiga karan wayata ya min oyoyo, na dauki wayar tare da duba sunan mai kiran, ganin waye yasa na dauka da shakiyanci na “amarya, amarya!!” daga can cikin wayar Ramlah ta amsa, “ke dallah can! Aure fiye da wata biyar amma kina wani ce min amarya?” watanni biyar da suka wuce muka sha bikinta ita da Ayan wanda ana daurawa suka wuce states inda a can ne yake aiki, bayan bikin da wata daya muka gama karatun mu, yanzu dai fitar sakamako muke jira kawai.
Nace “haba wata biyar ne fa kawai ba wasu watanni ba, Allah na tuba ni ko da ‘yayan ki ma amarya zan dinga ce miki” taja tsaki, “to Allah ya kyauta miki, ya zancen turarukan da na turo miki? Kin amso su kuwa?” nace “ai da kanta ma ta kawo min har gida, Masha Allah sun yi kamshi sosai, kuma suna da kyau wallahi” tace “ai sai dana fada miki, yanzu ya za ayi wajen sauran abubuwan nan da nace a kawo min?” nace “idan na hada komi zan kira ita Nadiya din, sai ta taho miki dasu koh?” tace “to shikenan… Ina Abbu?” nayi murmushi, “Abbu yaje Beijing, suna da wani meeting ne a kamfani shine ya tafi” tace “ranar nan ai na kalli show din da aka bashi award din best prof na Universities din fadin Nigeria, naji ana maganar bashi VC a BUK koh?” na gyada kai, “yeah, he deserve it ai” tace “indeed, ana fadar ayyukan shi da sadaukarwar shi indai ta fannin karatu ne ai, Allah ya kara taimako” na amsa da “ameen” daga haka muka yi sallama da ita.
Toilet na fada na dauro alwala na fito nayi sallar La’asar, bayan na gama na hau en gyare-gyare a dakin babu kakkautawa da yake ba wani aikin yi ne dani ba duk da cewa ranar girki na ce dai. Wajen karfe biyar na tashi na shiga kicin din, Anty Mubeenah tana tsaye a gaban gas cooker da frying pan akai da alamu tana frying abu, na kalleta cike da mamaki ita kuma ta kalleni da blank expression, tunda muke da matar nan sai ranar na taba ganinta a kicin wai da sunan girki, sai na dake kawai na shiga cikin store na fito da duk abubuwan da zan bukata. Da yake babban kicin ne, kuma yawanci komi na amfani a kicin din guda biyu ne sai na kunna wani gas din na fara girkina. Cikin kankanin lokaci kamshi ya bade ko’ina na gidan, ta gefen ido nake kallon Anty Mubeenah ina wasi-wasin dalilinta na yin girki yanzu. Har ta gama soya dankalin ta juye a cikin plate ta kashe gas din ta fita, na tabe baki naci gaba da aiki na. Ba a jimajima sai gata ta fado kicin din, ta tangwarar da plate din a cikin sink ta juya kamar cikin fushi. +
Sai dana gama girkina idanu na ya sauka akan dankalin, na dauki kwara daya na kai bakina, frowning nayi. Dankalin tauri kamar danye ga dan banzan gishiri da yaci. Na gyada kai a hankali tare da zubar da dankalin na wanke kayan dana bata naje na jera girkin na shige daki. Wanka na fara yi kafin nayi sallah na jira aka kira Isha’i nayi kafin na fita falo muka fara dinner. Tun a wajen jikina ya fara rawa, sanyi yake shigar ko wace kofa ta jikina sosai.
Hafsy ta kalleni tace “Anty Nafee, jikinki rawa yake yi baki da lafiya ne?” nace “zazzabi ne, yanzu zan shiga in sha magani ai” tayi shiru tana kallona, can tace “ko dai in kira Anty Raliya?” nayi saurin cewa “a’ah da wannan daren? Mura ce take shirin kama ni zan sha magani” tace “to Allah ya sauwake” bayan mun gama cin abincin muka dan yi kallo kowa ya wuce dakin shi. Shirin kwanciya barci nayi naja bargo na rufe jikina, rawar sanyi nake yi ina jin kamar an watsa ni cikin ruwan kankara hakorana har haduwa suke yi waje guda. Ina cikin wannan halin Hafsy tazo ta same ni, da sauri ta hayo kan gadon tana jijjiga ni amma na kasa daga kai in kalleta, fita tayi da sauri sai gata ta dawo ita da Anty Mubeenah. Da sauri ta dago ni tana tamvayar lafiya?? Ganin na kasa yin magana yasa ta hau daga drawers har ta lalubo paracetamol, Hafsy ta miko ruwa Anty ta bani maganin nasha na koma na kwanta. Ba a jima ba barci ya dauke ni, ban san sanda suka bar dakin ba.
Da asubahi koda na tashi babu zazzabin sai mura data min mugun kamu, nayi sallah ina ta atishawa da tari ba kakkautawa. Na shirya break fast na kai kan dinning na ajiye, ina cikin shiryawa din Anty Mubeenah ta fito daga dakinta, nan ta min ya jiki na amsa da sauki tare da mata godiyar dawainiyar ta a gare ni a daren jiya, ta wuce dakinta. Nima dakina na koma na kira Abbuna muka sha hirar mu har sai da Hafsy ta leko ta kirani sannan muka yi sallama na fita muka karya. Yaran makaranta suka wuce ni kuma na zauna anan falo ina kallo Anty Mubeenah kuma ta shige dakinta, na kula kwana biyun nan bata cika fita ba.
Wajen karfe goma na safe sai ga su Anty Ameenah da Anty Rahila sun zo wai ashe Hafsy ce ta kira su a waya tace musu bani da lafiya, na kama baki ina dariya nace “Lallai ma Hafsy! Zazzabi ne nayi jiya da dare fa, mura nake yi sai kuma nayi wankan yamma ina jin shine ya saukar mun da zazzabin, amma shine har da shela??” Anty Raliya tace “ai ba shela bace ba Nafeesah, gaskiya ce. Idan wani abu fa ya faru??” nace “babu abinda zai faru ma in shaa Allah. Ai Hafsy din da Anty Mubeenah suka kula dani” na lura da kallon mamakin da suka jefe ni dashi kafin suka basar, Anty Ameenah tace “To Allah ya kara lafiya” nace “Ameen” sai ga Anty Mubeenah ta fito, nan ta samu waje ta zauna suka gaisa, basu jima ba suka mana sallama suka tafi suna jaddada min idan dai naji ciwon ya dawo in kira su fa, nace toh.
*****
Mun fito daga cikin jifatu ni da Hafsy mun je shopping, ina kokarin bude mota mu shiga naji an kira sunana daga bayanmu cikin wata irin murya da naji kamar na san ta, “Nafeesah??” ga namaki na koda na juya Muneer na gani a tsaye, dauke a kafadar shi wata dan yaro ne zai kai kimanin shekaru hudu kila. Ya matso yace “Allahu Akbar! Ashe dai ke din ce, ya kike?” nayi murmushi, shekaru masu yawa sosai rabon da mun hadu kenan tun ma kafin in bar Kadpoly. Nace “lafiya na qalau Muneer, kai fa?” ya kalli Hafsy dake tsaye a gefena tana kallon shi cikin alamun rashin sanayya, yace “diyar ki ce?” ni abin sai ma ya bani dariya, ya kalli zankadediyar budurwa kamar Hafsy yace wai diya ta?? Nace “ehh, baka ga muna kama ba?” sai yayi er dariya, ya nuna min yaron hannunshi yace “dana kenan, Suleiman… Ke fa?” na daga kafada, “Allah bai kawo ba har yanxu” yace “to Allah ya kawo masu Albarka” nace “Ameen” daga haka muka yi sallama kowa ya shiga motar shi yaja. A cikin mota nayi murmushi tare da gyada kai cikin kara sakankancewa da Girma na Subhanah! Lallai HHausawa sun yi gaskiya da suka ce wani baya auren matar wani kamar yadda wani baya haihuwar dan wani… +
A daren ranar misalin karfe sha daya na dare na fito daga dakina da niyar zuwa kicin dauko ruwa, naci karo da Anty Mubeenah Zaune akan kujera cikin duhun falon wanda hasken dake waje ne daya dan shigo ta labulaye yasa na ganta, da farko tsoro ta bani kafin na dan matsa zuwa gabanta nace “Anty Mubeenah baki da lafiya ne?” ta dan dago a firgice ta kalleni kafin ta kauda kai, kai ta girgiza tace “lafiya ta qalau… Babu komi” kamar zan yi magana sai na fasa, na tunkari kicin kafin in dakata dalilin kiran sunana da tayi “Nafeesah…!” na juya a hankali na kalleta “ma’am?” ta dan daburce, “umh… Koda yake ma ba komi, je ki kawai” na juya naje na bude fridge na dauko ruwa mara sanyi na sha anan cikin kicin din na maida goran ciki na fita.
Har lokacin Anty tana a yanayin tagumi kamar yadda na fara samunta daga farko, har zan wuce sai kuma na fasa. Na koma kusa da ita na zauna sosai ina fuskantar ta, hannunta na kamo cikin nawa na rike, a hankali nace “Anty Mubeenah…”…Nace “Anty Mubeenah…. Ni ba karamar yarinya bace ba, kina cikin damuwa naga hakan rubuce akan fuskar ki. Kai ko makaho ya shafa ki yasan cewa kina cikin damuwa.. Nasan cewa ban kai matsayi ko girman da zan zama abokiyar shawarar ki ba, amma idan kina ganin babu damuwa kuma zaki iya, y can’t u just tell me?? I’ll be a good listener and a judger” tayi shiru tana kallona cikin nuna can I trust you? Na kai daya hannuna na shafa bayan hannunta ina mata murmushi reassuringly, nace “trust me, wallahi u r safe with me… Ki yarda dani”. 2
Numfashi ta ajiye a hankali, “na yarda dake Nafeesah, ke mutum ce ta gari mai hankali da natsuwa. Ina tunanin kila ki tsane ni akan abubuwan da na aikata…!!” tayi shiru tana kallona nima na kalleta ban yi magana ba sai data yi radin kanta kafin taci gaba da magana.
“Kamar yadda nasan cewa kin kula da yanayin zamana da Ibrahim Zama ne kawai muke yi wanda babu armashi ko na kankani. Auran hadi aka mana da Ibrahim ba tare da son mu ba, lokacin ina da wanda nake so. Haka aka kaini gidan Ibrahim ba don naso ba tunda duk yadda naso inyi akan kada ayi auren abin ya faskara. Ibrahim yana kyautata min a matsayin shi na wanda baya so na ma, amma ni na kasa yakar zuciyata akan ta so shi. Ina can ina karewa Mahmud wanda nake so mutuncina wanda kullum sai mun yi waya dashi ya jaddada min in rike mishi amana dai. Duk batanci na duniya babu kalar da ban yiwa Ibrahim akan ya sake ni ba amma yayi biris dani hakan shi yake kara min jin kin shi a raina. It took us almost a year kafin mu kusanci juna, shima ni da kaina naji ina son yin hakan na kai kaina gare shi. Daga nan muka ci gaba da rayuwar ma’aurata amma fa idan naga dama don wani lokacin ko ya neme ni ma sai inyi refusing dinsa, idan kuma ya matsa to sai dai ya biya ni kudin sannan…” tayi shiru hawaye ya zubo mata, yayin da nake jijjiga kai cikin mamaki. Ban taba zaton cewa alakar Abbu da Anty Mubeenah tayi muni irin haka ba, Anty taci gaba…
“Cikin haka na samu cikin Abdullahi, yeah naji dadin samun cikin saboda a lokacin zugar en uwana tayi tasiri akaina da suka ce idan na fara haihuwa a gidan Ibrahim yayana zasu zama magada saboda duk da cewa a lokacin yana karatun masters, amma yana da kudi don bai dogara da kudin mahaifin shi ba, ya dogara da kanshi. Sai dai bayan haihuwar Abdullahi da wata takwas dana kara samun wani cikin mai dan banzan wahala sai naji ina dana sani akan amincewata akan haihuwa. Mun sha danbarwa da Ibrahim akan cikin nan, nayi yunkurin zubar dashi sau ba adadi Allah ya nufa sai da yazo duniya. Wallahi Nafeesah sai da muka tsadance da Ibrahim ya biyani sannan na shayar da jaririn. Watan shi bakwai na yaye shi, babu ruwana da harkar yaran su duka shi yasa zaki ga shakuwar mu dasu bata yi zurfi sosai ba kamar yadda suka shaku da Ibrahim.Bayan shekaru biyu na sake haihuwar Hafsy, daga nan ne naje asibiti aka saka min loop a mahaifa ta saboda bana son haihuwa da Ibrahim….” 1
Na zaro idanu waje sosai cikin tsananin mamaki, “loop Anty?” ta gyada kai, “abin ya ba Ibrahim haushi sosai, ya jima yana fushi dani kafin ya sauko ya hau lallashina akan in je a cire min ni kuma nayi biris dani har ya gaji ya daina yace zai karo aure, at first na firgita da jin haka daga karshe da naji shiru sai nayi zaton cewa tsakuwa ce yake taunawa don aya taji tsoro sai kwatsam naji zancen auren shi da ke. In fada miki na firgita ma bata baki ne, na shiga shock bana kadan ba sai dai na cije saboda a gani na bana son Ibrahim meye nawa na jin haushi don zai kara aure? Sai daga baya na fahimci I was wrong! Ina son Ibrahim rashin kulawa irin nawa ne ya hana ni gane hakan, sai daga baya ne bayan ya daga min murya a karo na farko a tarihin rayuwar auren mu, sannan na fahimci halin da zuciyata take ciki game dashi amma ban san ko ta wace hanya zan sanar dashi ba Don haka naja bakina nayi shiru. Amma a en kwanakin nan gabadaya na rasa abinda yake min dadi, shi kuma kamar ya sani, yanzu ko kiran shi nayi a waya baya dauka ma. Zuciyata tana azabtuwa da hakan ba zan iya cigaba da jurewa ba, amma da wani ido zan kalli Ubangijina bayan abubuwan dana aikatawa mijina? Tell me, bayan duk my man and abubuwan nan dana aikata, da wani ido kike so in kalli Ibrahim??”. 8
Na kalleta tun daga sama har kasa, tabbas ta banbanta da Mubeenar dana sani a da. Wannan Mubeenar ba wadda take cike da self esteem bace, sai wata Mubeenah wadda nadama take nukurkusarta. Tausayinta ya mamaye ni matuka.
Nace “kada ki ce haka Anty, shi Allah Gafurur-Raheem ne, yana yafe kuskuran damu muka aikata a gare shi matukar tuban muke nema da gaske. Abbu ma haka ne, ina tabbatar miki da cewa shi zai fi ma kowa jin dadin canzawar ki Anty” ta kalleni da sauri, “da gaske?” na gyada mata kai ina murmushi. Tace “to yanzu me kike so inyi?” nace “abu na farko daya kamata kiyi shine kije ki cire loop din jikinki, bayan hana haihuwa yana da side effects a jikinmu ba kadan ba, bana tantama kibar jikinki loop ne ya assasa miki ita” ta gyada kai cikin nuna yarda da abinda nace, “nima nayi tunanin haka. In Allah ya yarda gobe zan koma asibitin a cire min” nayi murmushin jin dadi, “we will do the other things later then… Bari inje in kwanta haka nan” na mata sai da safe na wuce.
Har na kusa kofata naji ta kira sunana, “Nafeesah!” na juya a hankali, “it was not bad opening up to you..” nayi murmushi sosai, “Anytime Anty” na shige dakin tare da rufo kofata na koma kan gado na kwanta. Tunanin yadda muka kare da Anty na dinga yi, na tsinci kaina da addu’ar Allah yasa ta dore a haka, Allah kuma ya bamu zaman lafiyar da a kullum nake mana addu’ah. Da haka barci ya dauke ni cike da mafarkai iri-iri, mafi yawa daga cikin su shine na wani kyakkyawan yaro da yake bina da tuffa a hannu, na tashi da dan murmushi a fuskata. Addu’a nayi na shafa a fuskata na tashi na fada toilet na dauro alwala nazo nayi sallah.
Da yake ranar Anty ta karbi girki, ban fita falo ba sai da karfe tara tayi. Yara sun tafi makaranta, dana tambayi Harira Anty Mubeenah tace tace a fada min ta tafi asibiti, nayi murmushi kawai. Abinci na zauna naci, nayi gefe da plates din a zuciyata ina raya lokacin barin Harira gidan yayi.
Lokacin da Anty ta dawo har dakina ta leko ta same ni, tace “sun rubuta min magunguna in sha na sati daya sai in koma a cire min” nace “to Allah yasa mu dace” tace “ameen.”
Daga ranar alakar mu da Anty Mubeenah ta canza, su kansu yaran sun yi mamaki kuma sun ji dadin hakan kada ma dai Abbu yaji labari wanda nake updating din shi da duk abinda ke faruwa. Ni’imah ta sake haihuwar diya Mace, a ranar muka je muka yi barka ni da Anty Mubeenah. A cikin mota muna dawowa nayi shiru ina tunanin anya a duniya zan ma haihu kuwa? Na tuna ina cikin shekarar aure ta uku kenan zuwa hudu amma har yau shiru babu bayani ko batan wata ban taba yi ba. Mommy tace wai itama ha itama hakan ce ta faru da ita, sai a cikin shekararta ta biyar ne sannan ta samu cikina, nayi ajiyar numfashi a hankali ina addu’ar idan da rabona Allah ya kawo masu albarka.
Anty Mubeenah taje an cire mata loop din, sai dai ance sabida jimawar abin a jikinta babu wata kulawa irin yadda ya kamata, ya taba mata mahaifa saboda haka da kyar mahaifar ta iya daukar ciki nan gaba. Hankalinta ya tashi kwarai da jin haka ni na dinga kwantar mata da hankali har ta nutsu. Ni na bata shawarar shiga From My Kitchen Institute da yake Allah ya budawa mai makarantar Hadiza Dogon Daji ta bude reshe anan Kano bayan na Abuja, inda ta fara koyon salon girke girke ina kuma taimaka mata da wasu abubuwa. A gefe guda kuma na dora ta akan weight loss da slimming. Kullum muna gym muna aikin motsa jiki. Abbu ya dawo yayi sati daya ya tafi wata seminar inda daya dawo za a bashi VC.
Cikin wata daya kacal idan ba mugun sanin Anty Mubeenah kayi ba idan ka ganta a hanya ba zaka gane ta ba. Wannan kibar marar fasali da rashin gyara duk ya tafi babu shi, ta dawo tayi wani fresh da ita Masha Allah! Duk da dai har yanzu da sauran kibar amma ta ragu sosai. Musamman ta siya form din wata islamiyah anan bayan gidanmu inda take zuwa daukar karatu kowace rana da yamma, karfe hudu zuwa shida. Ko a yanzu kam Alhamdulillah! Zama na da kishiyata ya canza, idan ka ganmu zaka yi zaton cewa wasu shakikai ne ba kishiyoyi ba. 1
Result dinmu ya fita, sakamako yayi kyau sosai. Nayi clearance da komi, Abbu kadai nake jira ya dawo in nemi izinin shi in fara aiki da Lab din Aminu Kano Teaching Hospital.
Muna zaune akan dinning muna cin abinci, ranar Anty Mubeenah ce mai girki kuma ita ta dafa mana abincin da kanta don tuni muka sallami Harira bayan mun danka mata kudi masu tsoka da zata ja jari dasu, duk da cewa har yanzu dai sai a hankali amma she’s improving sosai. Ta kalli plates dinmu, Jollop spaghetti da sauce din hanta, soyayyiyar agada, da coleslaw. Ita kuma nata taliyar ce kadai sai tulin vegetables akai, ta kai spoonful of cabbage bakinta ta taune ta hadiye da kyar, ruwa ta tsiyaya ta kai bakinta. “Nafeesah! This is a torture wallahi! Haba!! Wata na nawa bani da abincin daya wuce kabeji? Gaskiya na gaji haka nan wallahi, I want to eat chicken!!” ta fada da karfi tana watsa hannuwana sama kamar wata yarinya, aikuwa nan muka samu abin dariya, ni da yaran muka kwashe da dariya sosai, ta nuna mu da yatsa “dariya ma kuke yi koh? Just wait nauyina ya dawo 65, idan na fara cin nama a gidan nan…” Qaseem yace “Mommy, Anty Nafeesah tace ko kin kai 65 din sau daya zaki dinga cin nama a sati fa!” ta harare shi, “inji wa? Kai dai ku jira in rage nauyin, babu wanda zai hana ni cin nama” ni dariya ma ta hana ni magana. A haka dai muka gama cin abincin cikin raha, na taya Anty Mubeenah muka kwashe kayan muka kai kicin muka wanke, daga nan na koma daki na kwanta wai in dan runtsa kafin La’asar tayi.
Ihun yara na jiyo a falo suna ga Abbu, haba! Na dira daga kan gadon da sauri na fita. A karamin falo muka ci karo dashi, tsaye a tsakiyar su Hafsy cikin suits bakake da farar shirt, na danne dokin in rungume shi da naji naje gefen shi kawai na zauna ina murmushi. Sai da yaran suka gama murnar su ya basu chocolates da tarkace ya tura su dakinsu sannan ya juyo gare ni.Nade ni yayi cikin jikin shi cikin tattausar rungumar nan tashi. Nima na mayar mishi da wadda tafi tashi taushi, mun jima a haka muna jin dumin jikin juna kafin na zare jikina daga nashi a hankali, na kalleshi ina dan murmushi, “ya hanya?” ya jingina kan shi da jikin kunya, “it was tiresome but Alhamdulillah tunda na iso lafiya” nayi murmushi “you must be kam… Yakamata ka watsa ruwa koh?” na mike da brief case dinshi a hannuna. +
Ya mike shima yana sassauta neck tie din wuyan shi, daidai lokacin Anty Mubeenah ta fito daga dakinta. Sanye take da doguwar rigar Shadda wadda tabi jikinta sosai, now that I look at her very well, tana da diri da halittun jiki Masha Allah. Haka kawai naji wani abu ya makale min a wuya ganin yadda Abbu ya saki baki yana kallonta yayin da take kallon shi cike da so da kewa. Ganin kallon nasu ba mai karewa bane ba yasa na danyi gyaran murya sai lokacin suka dauke idanunshi a kan juna, na danne takaicin daya zo mun wuya nayi dan murmushi tare da cewa “dama wanka wai zai je yayi, amma tunda gaki bari in barku tare, inje in dan kwanta” na mikawa Anty brief case din, ban jira sun ce wani abu ba na shige dakina da sauri na maida kofar na rufe. 1
Numfashi na dinga ajiyewa da sauri kamar wadda tayi tsere, tabdijam! Idan har haka zan dinga ji idan naga Abbu tare da Anty Mubeenah to akwai matsala, lallai yakamata in san abin yi.
Da dare muka hadu a dinning wajen cin abinci, daga jin taste din abincin nasan cewa Anty really put her best effort don kuwa yayi dadi sosai, duk yadda taso taja Abbu da hira a wajen abun ya faskara har naji ta bani tausayi, sai dai wani sashe na zuciyata na raya min cewa kawai burga ce yake yi, amma a dokance yake da ita, hakan shi yake kara tunzura ni.
Bayan mun ci abincin muka hada kan komi muka kai kicin muka dawo falo, Abbu da yaran shi suna hirarrakin su, sai muka ja kujera ni da Anty Mubeenah muna tamu hirar har wajen karfe tara da rabi, na tashi na musu sai da safe na shige dakina.
Wanka nayi na dauro alwala, anan cikin bayin nayi shafa ina karfafawa kaina gwiwa daga munanan tunanika da zuciyata ke kitsa min, babu abinda ya canza, Abbu yana nan a yadda yake kamar yadda Anty Mubeenah take, nayi dashe a zuciyar Abbu wanda babu wata ‘ya macen data isa ta dakusar min dashi, sai dai ta nemi wani gurbin tayi nata dashen, da wannan naji karfin gwiwa ya shige ni. Don haka koda na fito nayi tozali da Abbu akan gado, murmushi nayi naje gefen shi na zauna. Lafiya lau muka yi sallama dashi, na raka shi har bakin kofa ya tafi bayan ya manna min pecks a kumatu da goshina. Na maida kofar na rufe, kan gado naje na kwanta na janyo wayata nayi en dube-dube da chatting har dare yayi kafin na kashe wayar nayi addu’ar kwanciya barci na shafa. Filo na janyo na rungume a kirjina na rufe idanuna, can kasar zuciyata Istigfar na dinga janyowa da hailala saboda korar shaidanin dake saka min abubuwa a cikin raina…Alhamdulillah! Rayuwa mai cike da inganci da zama lafiya muke shimfidawa mu da mijinmu. Mun hade kawunan mu waje guda domin samun kwanciyar hankalin mijinmu. Yes, akwai kishi, sai dai kishin zamani muke shimfidawa ba wai na dabbobi ba, kowa tana iyaka kokarinta wajen ganin ta faranta ran mijinta domin samun ragamar zuciyar shi don haka a takaice dai Abbu ya zama sha lelen mu. 1
Lokacin Hajji yazo, Abbu ya biya mana kujera mu duka banda Hafsy, muka je muka sauke farali. Bayan mun dawo naje Kaduna nayi kwana daya na dawo muka ci gaba da gudanar da rayuwar mu a nutse.
*****
Kallon shi nake yi idanuna na shekin bacin rai da tashin hankali, “ban gane ba? Kamar ya ba zan yi aiki ba, akan me??” tunda muka dawo daga aikin hajji na dame shi da maganar son fara aikina amma yayi biris dani, sai ranar ne ya bani amsa da cewa ai ba zai barni wae inyi aiki ba, duk wahalar dana sha!.
A nutse ya kalleni cikin sanyin murya mai cike da lallashi yace “to menene abin tada jijiyar wuya kuma? Kin dai san cewa ba tun yau ba nasha fada miki cewa bani son mata na su yi aiki, nafi so su zauna a gida su kula min da gidana da iyalina. Beside Nafeesah baki nemi komi kin rasa ba a gidannan, aikin me kuma zaki je kiyi saboda Allah?” 1
Na cure baki waje guda ina yamutsa fuska, “to ni nace ne dama saboda kudi zan yi aiki ne? Kawai sabida ina so inyi aikin ne, m bored to death! Baka barina ina fita ina ganin mutane sai abu mai muhimmancin gaske ya taso, baka barina inje gidanmu in musu kwanaki sai dai wuni…. Ni wallahi idan ba so ake yi mutum kadaici ya kashe shi ba a bar shi yayi aiki!” 3
Kallona yake yi baki a dage cike da mamaki, tun da muka yi aure iyakata da Abbu Nafeesah yi kaza, ince toh., ko kuma Nafeesah ba zaki yi kaza ba ince toh. Amma yau yaga gabadaya na wani canza ne, abinda bai taka kara ya karya ba, maganar aiki ba tun yau ba yayi making it very clear ba zai bar matar shi tayi aiki ba amma gashi ina tonon fada da maganar.
Na kawar da kaina daga kallon da yake min na mamaki, “a’ah! Yo mutum sai yaki fadin gaskiya haka kawai! Idab ma bazan yi aikin ba a dinga barina ina fita mana, amma kullum ni a garkame a gida kamar wata furzuna? Da yake ita er gaban goshi ce naga babu ranar banza da ba zata fita ba amma ko a jikin ka sai ni, me nayi maka ne saboda Allah??” kwalla ta ciko idanuna, da sauri na juya na shige dakina. Kan gado na kwanta ina ajiyar numfashi idanuna a lumshe. Kwana biyun nan zuciyata a wuyana take, kome aka yi da wanda ya kai da wanda bai kai bama jin haushin shi nake yi. Na dan ja siririn tsaki, meye ma na wani sako zancen Anty Mubeenah? Duk da cewa dai abin yana ci mun tuwo ne a kwarya, kun ganta nan kullum tana waje yawo, yawace-yawacen nan nata har lokacin bai ragu ba, karewa ma watarana sai ta fita sannan take fada mishi duk da cewa dai an samu saukin kin fada mishi da bata yi. To ni kuma Fisabilillah kullum ina garkame a gida, idan yara suka tafi school Anty ma ta fita ni kadai ake bari inyi ta gantali a cikin gida, abin ya dame ni sosai.Ina jin lokacin da aka taba kofa alamun an shigo cikin dakin, bayan juya baya da nayi sai na lumshe idanu na. Ya zauna a gefen gadon da nake kwance, yace “wai Nafeesah me ke faruwa ne? U never go against my words n you never raise ur voice on me, naga maganar aikin nan fa tun ba yau ba na fada miki cewa ba zan iya barin mata ta tayi aiki ba. Mubeenah tana da degree akan computer science ni na hana ta aiki but in return sai na bude mata saloon din can, ba gashi yanzu komi ya zama even ba? I’ll do the same to u, Dan Allah kar ki maida maganar nan ta zama babba ranmu ya baci Nafeesah!”
Nayi shiru kawai ina sauraronshi. A en kwanakin nan kwata-kwata zuciyata a wuya na take, abu da wanda ya kai da wanda bai kai ba sai inji raina ya baci, akwai ranar da ina jan jagira hannuna ya kubce ta bata mun fuska, wani irin bacin rai ya ziyarce ni a lokacin, duk abubuwan da suke kan dresser din sai dana yi wurgi dasu suka fado kasa, abin zai baku mamaki da dariya idan kuka ga yanda na tsaya a kansu ina wani huci kamar tsohuwar macijiya, sai daga baya da fushin ya tafi kuma na dawo ina dariya da tu’ajjibi. Akwai kuma ranar da kadan ya hana in mazge Hafsy saboda nayi abinci tace gishiri yayi yawa, bayan a hakikanin gaskiya taste din bakina ya bace nayi ta zabga uban gishiri a cikin abincin ni da kaina dama sai dana yi tunanin haka amma data fada sai naji haushi. 2
Abbu ya dan tabo ni tare da juyo ni ina fuskantar shi, shiru nayi ina kallon kyakkyawar fuskar shi, ina so in gano laifi ko aibu a cikin abubuwan daya fada amma na kasa. Ban san abinda yasa nake fada dashi akan maganar aikin nan ba, lokacin da nake gida har addu’ah nake yi akan Allah ya kawo min miji wanda zai tsaya min akan komi kamar yadda Daddy yayi wa mommy, gashi yanzu na samu amma kuma na rasa abinda yasa na kasa yarda da hakan, m behaving really strange kwana biyun nan, wasu bakin halaye dana kasa gane su.
“Nafeesah??! Talk to me mana uhm?? Bana so muyi fada akan maganar nan please, kin dai san babu abinda zaki nema a duniyar nan da ba zan kasa miki shi ba, ba zan gazawa hidimomin ki ko kadan ba kin ji? Kuma In shaa Allah ba zan taba bari kiyi dana sanin kin yin wannan aikin ba, ok?” kai na gyada mishi a hankali, yayi murmushi a hankali, “uwww thanks my baby…” ya sadda kanshi saitin fuskana zai yi rewarding dina da kiss, naja wata doguwar shakuwa data sa ya dakata yana kallona, daga haka kuma ba sai kakarin amai ba? Na tashi da gudu na shige bandaki, sai dana amayar da duk abubuwan dana ci a take, Abbu yana tsaye a gefena yana dan bubbuga bayana har na gama aman, ya taimaka min na wanke bakina ya kaini kan gado ya kwantar ya koma toilet din. 1
Kafin ya fito na dukunkune cikin bargo ina rawar sanyi sosai, hankali tashe ya tarairayo ni jikin shi yana taba wuya na, waya ya dauko ya kira family doctor dinmu, Doctor Salmah. Bayan kamar mintuna arba’in ta iso, lokacin zazzabin ya sauka sai jikina da yayi wani irin sanyi kamar an min duka, kasala duk ta lullube ni. Tayi duk wasu gwaje-gwaje da zata yi, daga karshe dai ta bani wata kwalba tace inje inyi fitsari a ciki, na dafa kafadar Anty Mubeenah muka shiga toilet, ta fita ta bar ni nayi fitsarin ina gamawa ta shigo muka koma dakin, Docta ta amsa kwalbar ni kuma na koma kan gado na kwanta, muka yi zuru-zuru muna kallonta tana saka strip a cikin kwalbar fitsarin. 6
Bayan kamar minti goma ta dago abin yadda duk zamu gani, bamu fahimci komi ba sai da muka ji tace “mashaa Allah!! Farfesa matar ka na da juna biyu!!” a rikice na kamo hannun Abbu na rirrike kamar zan tsinke mishi shi, ya kamo wuyana ya hada fuskata da tashi waje guda yana furta wasu addu’o’i da ake son mutum ya dinga furta su cikin halin tsananin farin ciki. Anty Mubeenah ta dafa kafadata ko ban fada ba nasan tana murna da abinda taji ne. Docta tayi er dariya ta fara tattara kayanta tana fadawa Abbu bata bincika ko watan nawa ba saboda haka ya kaini asibiti washegari a duba da kuma lafiyata data jaririn yace toh. Nan ta mana sallama ta tafi bayan Abbu ya mata kyautar da bai san adadinta ba don hannu kawai ya saka a cikin aljihun shi ya damko kudi ya mika mata. 4
Ranar kam naga tattali da kulawa ba daga mijina ba ba daga ‘ya’yan mijina da en uwanshi ba, ba daga kishiyata ba ba daga Iyayena ba kada ma dai Daddy yaji labari. A ranar ya kirani shi da Mommy ban ma san wanda ya sanar dasu zancen cikin ba suka taya ni murna da addu’o’i iri-iri Mommy kuma yadda zan kula da kaina take fada min tana nanatawa kamar karatu.
Cikin wata hudu ne lokacin da muka je aka duba, babu wata damuwa ko matsala a tare dani sai hawan jini wanda ba wani damuwa bani tunda dama it’s a normal thing a wajen mata masu ciki, an dai bani abubuwa da zan dings ci da kuma abubuwan daya kamata inyi da wanda ba zan yi ba domin rainon cikina cikin sauki da kwanciyar hankali. A cikin mota a hanyar mu ta dawowa daga asibitin Abbu ya riko hannuna yana shafawa a hankali yace “ya zancen aiki ya tafi koh?” na gyada mishi kai ina murmushi. Yayi er dariya tare da cewa “ai Doctor Salmah ta fada min cikin jikin ki ne yasa kika zama short tempered woman, haba! I was wondering dalilin da yasa mutum mai sanyin hali irin ki ya zama mai fada da zuciya cikin dan kankanin lokaci, amma tun da na gano kan abin, zamu dinga kiyayewa bacin ranki don tace hakan zai iya sawa jinin ki ya hau….. Allah ya sauke min ke lafiya baby” nayi murmushi nace “Ameeen Abbu nah..!”.
Cikina sai daya shiga watanninshi na bakwai sannan ya fara girma saboda da babu wani girma kuma babu laulayi ba komi sai fresh da nayi da kuma cin abinci da shan tatacciyar madara. Kafin in shiga watan haihuwa ta kuwa na zama shirgegiya, zama da kyar tashi da dabara. Kullum na kan zagaye gidan sau hudu ko biyar don ance hakan yana da kyau sosai. Yanzu dai haihuwa kadai muke jira, komi is ready, hatta da cokalin da za a ba baby ruwa dashi ranar da aka haife shi an siyo an ajiye, komi unisex Abbu yake siyowa kuma guda biyu, duk da dai naki yin scanning amma Abbu da Anty Mubeenah har ma da sauran mutane suna cewa wai girman cikina irin na en biyu ne, don Abbu ma cewa yayi wai yana mafarkin ya ganni ina wasa da yara biyu ina miko mishi su, ni dai fatana kawai Allah ya sauke ni lafiya.
Ranar wata Talata na tashi da matsananciyar nakuda, nan muka kwasa Zuwa asibiti. Nakuda nayi mai tsawo da wahala kusan yini daya ina abu daya, abin ya gigita ni. Ban taba sanin cewa zafin nakuda nake yi ba. Abbu da yayi jan ido ya shigo labour room din sai waje aka yi dashi saboda dana shiga mood din “ duk kai ne ka janyo min wannan wahalar…” abin bai yi kyawu ba. Sai zuwa bayan Maghrib Baby ya fito, nan na fara ajiye numfashi, sai dai me? Wani ciwon ne ya sake turnike ni kafin kace me?! Wani yunkurin sai ga wani babyn. Na maida kaina kan gadon asibitin na kwantar ina ajiyar numfashi da karfi, nurse din data karbi haihuwar ta duba yaran tace “Masha Allah!! Maza ne Allah ya raya miki su!!”. Tuni yaran suka hade dakin da kukan da aka san lafiyayyun jarirai nayi. Nan dai aka shirya mu muka fito tsaf damu. Throughout lokacin babu abinda nake furtawa fili da ciki sai ‘Rabbir-ham huma kamar Rabbiyaani Swigaara…!!’ wa Mommy na da duk wasu matan duniya, haihuwa is really not a simple thing.1
Ana fito damu Abbu da yara suka shigo, nan fa suka lullube yaran suna murnar samun kanne, Abbu dai ya samu ya lallabo yazo inda nake ya tallabo ni a cikin jikin shi ya rungume yana shafa bayana. Ya dago goshina ya bani peck a kumatuna, “well-done Baby, kinyi kokari really! Allah ya albarkace ku ke da ‘ya‘yanki” nace “ameen… Wani irin baby kuma? Ga babies dinka can” ya juya ya kallesu ya juyo ya kalleni yana murmushi, “me na fada miki? You were going to give me twins, next year ma haka, n the other year, n the other too…!” na zaro ido ina cewa “mutuwa kawai kake rokar min!” yayi dariya tare da saki na yaje ya dauki yaran, Anty Mubeenah kuma ta matso tana jera min sannu.
Sai washegari aka bamu sallama muka wuce gidanmu muka cigaba da karbar barka har zuwa ranar suna inda yara suka ci sunan Abdul-Qadir da Mukhtar (Sunan Daddy na) muna kiran Abdul-Qadeer Ameer shi kuma Mukhtar Daddy. Aka yi taron suna aka watse aka bar mu da yara da Dattijuwa Hanne daga Malumfashi muna wankan jego.
Cikin dan tsakanin Abbu ya bude min babbar plaza wadda Daddy na ya cike min rabin shagunan plazar da kaya ana kula min dasu, rayuwa ta ko wani fanni tana gara mana cikin dadi da kwanciyar hankali babu abinda zamu ce da Ubangijin mu sai dai Godiya….
*****
“Ameer!! Daddy!!!” na fito falo ina kwalawa yaran kira, Anty Mubeenah dake kicin tana dambun nama duk da ba girkinta ba ne, tana taya ni hada abubuwan motsa baki da muka saba yi saboda baki da kuma emergency food. Ta leko tace “ya aka yi ne ake neman dears haka?” naja tsaki, “yaran nan daure su zan fara yi a jikin gado gaskiya, kullum jan magana da barna kamar wasu beraye? Kwalbar turare na mai kyau fa kawai suka dauka daga kan mirror suka hada ta da bango, shine da suka ga ta fashe suka tsere” Anty tayi Dariya tace “aikuwa yanzu suka bi su Qaseem garden wai suna tennis” nayi kwafa, “I’ll just go and register them a makarantar su Qaseem ma kawai ko na samu sawaba da sanyin zuciya” Anty tayi dariya tana girgiza kai tace “ke da yaran nan naki koh?” ni kuma na juya zuwa dakina.Abbu yana kwance akan sofa yana karatun jarida da yake ranar hutu ce, ya miko min hannu na karasa gefen shi na zauna ina turo baki, yayi dariya “yau naji ikon Allah! Ni da bani na bata miki rai ba sai kuma fushi ya dawo kaina, dama ana haka ne?” na turo baki “Allah ni wannan yaran naka ka saka su a makaranta kafin su saka min hawan jini, kullum sai sun shigo sun min barna ni da Antyn su. Hafsy yanzu da makullin dakinta take yawo saboda Ameer. Kayan dakin yaran nan babu abin dauka duk sun bata, jiya suka balle wardrobe din da muka sayo musu last week a Prada saboda Allah meye haka??” 1
Abbu ya kwashe da dariya har da kwanciya akan kujera, nayi kuta, “na kula dama kai kake daure musu suna rainin wayau. Yara ba a isa a musu magana ba kawai sai ka hau cewa wai yara ne, har sai yaushe zasu girma??” ya juyo dani yana kallon idanuna, “sai wani kumburewa kike yi kina fada baby, Anya?? Kin san da cikin su Ameer ma fa haka kika dinga yi?” da sauri na dukunkune fuskata a kirjin shi. Ya shafa kaina yace “da gaske ne hasashe na kenan? Masha Allah La Quwwata Illaa Billah! You are going to bless me with another child again… Ohh Nafeesah the thing I have for you…. You Are Indeed a Blessing!!” na kara rungume shi a jikina sosai. Kamar yadda a shekaru masu dama da suka wuce, nake jin zill da duk farincikin duniya idan naji ni a kirjin mijina, yanzun ma hakan take. Har yau muna son junanmu, har yau muna girmama junanmu, har yau muna rungumar junanmu a halin farin ciki ko akasin sa. Babu abinda ya ragu daga son da muke wa junanmu.
Ya dago fuskata yace “that call on a celebration… Tunda yara suna nan zamu fita gobe, party and welcome our little princess… Mata zaki haifo mana yanzu baby…. Hafsy tace tana so ta koyi kitso, kinga idan muka samu mace shikenan sai ta koya a kanta koh?” na zaro ido ina dariya tare da kara shigewa cikin jikinshi, “Noo… Guda daya ta isa Abbu… En biyun nan ba sauki daga haihuwar har rainon, kana dai ganin yadda muke fama dasu a gidan nan” ya hade fuska ta da tashi har hancina yana gogar nashi… “haka kike tunani dai….”. Kokarin zurfafa abin yake yi, har na saddakar na lumshe idanuna, yana gab… Saura kiris… Kawai sai barammmm!!! Karan turo kofa da sauri….. “Mammiiieeee!!!!” nayi sighing tare da bude idanuna, fararen kayan dana saka musu yanzun nan kafin su fasa min turare, sun yi dikin-dikin da datti da yake ba a jima da gama ruwa ba. Na zaro ido, “what??!” na fara kokarin tashi, Ameer ne ya fara xubawa a guje nan Daddy ya bi bayan shi, na juya na kalli Abbu, shrugging yayi tare da daukar jaridar shi yana murmushi, na girgiza kai tare da mikewa nabi bayan yaran ina kwala musu kira kamar dai yadda na bude shafin……
*_Alhamdulillah! Masha Allah Laa Quwwata Illa Billah!!_* It has been really a very big hell of a ride, right?! But Mashaa Allah!! Mun kawo karshen shi. 1
Littafin NI DA ABOKIN BABA NA kirkirarren labari ne, baya da nasaba da rayuwar wani/wata, idan wani abu yazo daya da naki/naka, to wannan 100% arashi ne kawai.
Ina mika dimbin gaisuwa ta zuwa ga Dimbin masoya, mabiya Littafin Ni Da Abokin Baba Na! The Facebookians, Wattpadians, Whatsappians, and all, thanks ya very much da duk kaunar ku a gare ni yayin Posting din littafin, gyarerekin ku da karfin gwiwar ku, I Appreciate!!